diff --git "a/data/hau/test.tsv" "b/data/hau/test.tsv" new file mode 100644--- /dev/null +++ "b/data/hau/test.tsv" @@ -0,0 +1,638 @@ +category headline text url +business Najeriya: Kayan gwari sun yi kwantai a arewa bayan hana kai kaya kudu A yayin da farashin kayan gwari da dabbobi suka tashi a kudancin Najeriya, a arewacin kuma farashin kayayyakin ne ya karye. Tasirin yajin aikin Haɗaɗɗiyar ƙungiyar masu kayan gwari da dabbobi da kayan cimaka ya haifar da tashin farashin a kudancin Najeriya da kuma karyewar farashin a arewacin ƙasar. Ƴan kasuwar kayan gwari a Kano sun yi kukan faɗuwar farashin tare da tabka asara mai yawa. Akwai tarin tumatus kwando-kwando jibge a kasuwar kayan gwari a Kano bayan hana kai kayan zuwa kudancin Najeriya. Kusan ana kai kayan gwari kashi 50 waɗanda aka noma a yankin arewaci zuwa kudancin Najeriya, kuma yanzu rashin kai kayayyakin ya haifar da yawaitarsu a arewa wanda ya jefa ƴan kasuwar kayan gwari cikin wani yanayi na hasara. Tun a makon jiya ne ƴan kasuwar da ke kai kayan abinci kudancin Najeriya daga yankin arewaci suka shiga yajin aikin kafin su janye a ranar Laraba. Ƙungiyar ta janye yajin aikin ne bayan tattaunawa da tawagar gwamnatin tarayya karkahin jagorancin gwamnan jihar Kogi. Ƙungiyar ta ce ta mika bukatu guda biyar ga gwamnan domin gabatar da su ga shugaban ƙasa da take son a biya mata. Ta amince ta janye yajin aikin bayan gwamnati ta yi alkawalin diba bukatun, amma kungiyar ta yi barazanar komawa yajin aikin idan har gwamnati ba biya bukatun ba. Sun shiga yajin aikin ne domin nuna goyon baya ga ƴan uwansu mutanen arewa da rikicin kasuwar Sasa ya shafa a garin Ibadan na jihar Oyo, rikicin da ya haifar da hasarar rayuka. Yanzu yajin aikin ya yi tasiri bayan haifar da tsadar farashin kayayyakin abinci a yankin kudu maso yammacin Najeriya da kuma faɗuwarsa a arewaci. Hakan ya nuna yadda yankunan biyu na Najeriya ke dogaro da juna. Rahotanni sun ce shugabannin ƙungiyar kayan gwarin sun yi zama da wakilan gwamnatin tarayya a fadar shugaban ƙasa domin janye yajin aikin. Ƴan kasuwar kayan gwari a Kano sun ce rashin kwararowar abokan cinikayyars na yau da kullum ya sa kayan da suke da su lalacewa wanda hakan ya sa dole su karye farashin kayayyakin don gudun tafka asara. A kudancin Najeriya kuma farashin ya lunka sau uku sakamakon yajin aikin. Wakilin BBC Kalipha Shehu Dokaji ya ziyarci kasuwar kayan gwari ta Yankaba a Kano ya ce ya tarar da yadda farashin kayan gwarin ya karye. Ya ce yanzu a kasuwar ana sayar da kwandon tumatur naira 1,000 saɓanin dubu uku zuwa huɗu da ake sayarwa kafin yajin aikin na masu kai kayan gwari zuwa kudancin Najeriya. Wasu wuraren ma idan mutum ya latsa har ƙasa da naira 500 za a iya sayar masa da kwandon tumaturin. Kwanon tumatur da ake sayarwa naira 800 yanzu ya koma 200, haka ma kwanon tattasai ya koma 200 saɓanin narai 1,200. Buhun albasa anzu ya dawo naira 500 maimakon dubu 65 kafin soma yajin aikin na masu kayan gwari. Ƴan kasuwar sun alaƙatanta asarar da suka yi da ƙaranci shigowar masu siyen kayan da yajin aikin da mutanensu da ke fataucin kayan zuwa kudu. Asarar ta fi shafar ƴan tumatur, yayin da kuma masu cefene ke murna da karyewar farashin. Sai dai duk da wannan matsalar karyewar farashi da yan kasuwar da wasu daga cikin manoman ke kokawa, wasunsun sun shaida wa BBC cewa sun gwamance da hakan domin goyon bayan yajin da masu dakon kayan zuwa kudancin Najeriya ke yi. Haɗaɗɗiyar ƙungiyar masu dakon abinci da dabbobi daga arewa zuwa kudancin Najeriya sun shiga yajin aikin ne bayan karewar wa'adi da ta bai wa hukumomin Kasar na biya masu wasu bukatunsu musamman kan rkicin kasuwar Shasha a jihar Oyo. https://www.bbc.com/hausa/labarai-56269227 +business Abin da ya kamata ku sani game da kama gwamnan CBN Emefiele "Rahotannin da ke kara-kaina a wasu kafafen yada labarai na cewa hukumar tsaron farin kaya na shirin kama gwamnan babban bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele. Wata babbar kotu a Abuja babban birnin kasar ta yi watsi da bukatar DSS ta kamawa da tsare Mista Emefiele. DSS na tuhumar Godwin da laifukan da suka shafi taimakawa ta'addanci, sai dai kotun ta ce hukumar ta koma ta samo ƙwararan hujjoji da shaidu kafin ta sake dawowa gabanta kan batun. Wani mai suna US Gambarawa shi ne ya shigar da karar a madadin hukumar tsaron farin kaya ta DSS a ranar 7 ga watan Disambar 2022. Tuhumar mai lamba FHC /ABJ/CS/2255/2022, ta nuna shari'ar tsakanin DSS da gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele. DSS na zargin Godwin Emefiele, da tallafawa ta'addanci da kudade hakan ya sabawa doka ya kuma aikata laifi kan tattalin arziki. Mai shari'a John Terhemba Tsoho da aka gabatar da karar gaban shi ya yi watsi da ita. Ya ce DSS ba ta gabatar da wata kwakkwarar shaidar da ta nuna gwamnan CBN din ya aikata laifin ba, sannan kamata ya yi ace shugaba Muhammadu Buhari ya san da batun. Takardun tuhumar da kotun ta yi watsi da su, da sashen BBC Pigin ya gani, ya nuna alkalin babbar kotun ne ya dauki matakin. A hukuncin da ya zartar, Alkalin ya yi bayani kan wasu bayanai da aka yi su a dunkule da ya bukaci a warware da yin bayani dalla-dalla, inda aka ambaci Godwin Emefiele ba tare da an fadi mukaminsa na Gwamnan babban bankin Najeriya ba. Alkali Tsoho ya kara da cewa ''DSS ba su yi gamsasshen bayani kan ko wanda suke kara mai suna Godwin Emefiele gwamnann CBN ne ko kuma wani mutum mai irin sunansa na daban, don haka ana bukatar wannan bayani. ""Mutane za su yi mamaki da rudani ko wanda ake tuhumar Emefiele na CBN ne ko a'a, saboda ana magana ne fa a kan daya daga cikin babban jami'in gwamnatin tarayya.'' Mai Shari'a Tsoho, ya kuma kafe cewa kamata ya yi tuhumar da DSS suka gabatar ta samu rattaba hannun shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tun da shi ne ya nada Emefiele mukamin. ''Lamarin ya yi kama da kotun na son fakewa da guzuma ne ta harbi karsana, ta hanyar amfani da kotun wajen lullube abin da suka aikata ba daidai ba da sun san ya sabawa doka kuma ba za a amince da shi ba. ""Wannan dalilin ne ya sanya ba mu amince da karar da suka shigar ba, har sai sun gabatar da kwakkwarar hujja sannan za mu saurare su, amma ayanzu kam mun yi watsi da batun,'' in ji Alkali Tsoho. Tun lokacin da Babban Bankin Najeriya CBN ya sanar da sabunta wasu daga cikin takardun naira, aka fara matsawa Mista Godwin Emefiele lamba. Majalisar dattijan Najeriya ta nuna rashin amincewa da wasu daga cikin tsare-tsaren sabbin kudin, hakan ya biyo bayan bayanan Ministar kudin Najeriya Zainab Ahmad da ta ce sam ba ta da masaniya kan batun. Har wa yau, majalisar wakilai ma ta gayyaci gwamnan CBN domin amsa tambayoyi kan sabbin kudaden da kuma yadda zai shafi tattalin arzikin Najeriya. A ranar Litinin wasu daga cikin lauyoyin kungiyar kare hakkin dan adam, da jam'iyyun adawa da kungiyoyin farar hula sun fantsama tituna zanga-zanga. Masu boren karkashin gamayyar kungiyoyin farar hula, sun ce DSS ta maka Emiefele gaban kotu ne domin su bata masa suna. Sun yi kiran Shugaba Muhammadu Buhari da Ministan Shari'a Abubakar Malami su shiga batun. DSS ta yi karin bayanin cewa tana bincike ne kan duk wani abu da ya shafi tsaron kasa. Kuma ayyukan da suke yi ya shafi 'yan Najeriya ne baki daya. Mai magana da yawun hukumar DSS, Peter Afunanya, ya fitar da sanarwa a ciki yana cewa wasu mutane na yada farfaganda domin ɓata musu suna da aiki. “Za mu ci gaba da aiki da bayyana sakamakon bincike ga 'yan kasa ba tare da kunbiya-kunbiya ba, za mu sanar da wadanda lamarin ya shafa ba tare da boye-boye ba,'' in ji sanarwar. ''Babu wata farfaganda da za ta yi tasiri a kanmu, ko wani abu da zai tsorata ni damu ba, ba bu wata barazana da za ta yi tasiri a kanmu.''" https://www.bbc.com/hausa/articles/cz5851g5pe8o +business Elisa Loncón: Matar da ta samu ɗaukakar rubuta tsarin mulkin ƙasa bayan fama da talauci "A shekarun 1970 lokacin da Elisa Loncón ke tasowa, sai ta yi tafiyar mil 8 kafin ta isa makaranta. Iyayenta 'yan asalin yankin Mapuche ne na kasar Chile, wadanda ke rayuwa cikin bakin talauci a wani kauye da ke kudancin yankin Araucanía. Babu wanda ya ke taimakon kai ta makaranta, yawancin lokuta da kafa take takawa ta hanya mai cike da datti. Mahaifiyarta aikatau ta ke yi a gidan masu kudi, sannan ta na kaunar wakoki. Mahaifin ta kuma kafinta ne, kuma shi ya koyawa kan shi yadda zai yi rubutu da karatu lokacin da ya ke da shekara 17. Rayuwa ga wadannan iyali na cike da wahala da fadi tashi, dakyar iyayensu ke samawa Loncón da 'yan uwanta shida abincin da za su ci. Ko can a makaranta ma bakar wuya ta ke sha, saboda yadda ake cin zarafinta saboda tsatson da ta fito. Sai dai duk da hakan, ba ta karaya ba. ""Na fito daga iyalai masu saukin rayuwa, kamar sauran kabilar Mapuche muna shan bakar wuya,"" kamar yadda ta fada a kwanakin baya lokacin tattaunawa da jaridar El País ta kasar Sifaniya. ""Kabilar Mapuche 'yan asalin kasar Chile su na da yawan gaske, da kuma harshen da suke amfani da shi, su na da addini da tallafawa wajen bunkasar tattalin arzikin kasar. ""Sai dai kash, ba su da wani tabbacin 'yancin akan dukkan harkokin da suka shafi kasar. ""Mu na mutuntawa da daraja kan mu, cikin abin da muka sa ni daga tarihinmu da al'adu"". Sannu a hankali ta bar kauyen da ake kira Lefweluan, inda yawancin dangin ta suke, ta kuma kallama karatu a matsayin malamar makaranta mai koyar da harshen Ingilishi. Ta ci gaba da karatu har ta kai matakin digirin digirgir a jami'ar Leiden, da ke kasar Netherlands,ta kara yin wani digirin digirgir a fannin Adabi a jami'ar Pontifical Catholic da ke Chile, kafin daga bisani ta zama cikakkiyar Farfesa a jami'ar Santiago. Baya ga aikin da ta ke na fannin ilimi, Loncón ta shiga yakin kwatarwa kabilar Mapuche 'yanci. Ta yi suna matuka cikin masu fafutukar kare hakkin jama'arta, a farkon shekarar nan ne aka zabeta 'yar majalisa cikin kujeru 17 da aka warewa kabilu irin na ta a fannin duba kundin tsarin mulki, kuma su za su rubuta sabon kundin tsarin mulkin kasar Chile da ke fama da rarrabuwar kawuna. Lamari ne mai cike da tarihi, saboda har kawo yanzu tsirarun kabilu ba su da katabus a sha'anin tafiyar da kasa, kuma Chile ba kasa ce da ba ta tafiya da sauran kananan kabilu. 'Yan asalin kasar mazauna daji ba a sanya su cikin kundin tsarin mulkin da ake amfani da shi a kasar ba, tun zamanin mulkin mulaka'un shugaba Augusto Pinochet, da ya yi mulki daga shekarar 1973 zuwa 1990. A kokarin kawo sauyi, a wannan watan an zabe ta cikin mambobi 155 da za su shiga taron da za a yi da ya hada kabilun da aka maida saniyar ware, wanda shi ne karon farko da aka taba yi a tarihin Chile. Cikin annashuwa da farin ciki, ta dunkule hanunta tare da daga shi sama, cikin dandazon masu tayata murna ta ce: ""Ina jinjinawa al'umar Chile, daga arewaci Patagonia, daga gabar ruwa zuwa tsaunuka, har tsuburai, da dukkan wadanda suke kallonmu a halin."" Bayan nan sai ta daga tutar kabilar Mapuche. Ta ci gaba da cewa ""Ina mika sakon godiya ga wadanda suka bani goyon baya daga sassa daban-daban, ina son shaida musu yarda da amincewar da suka yi da ni, da kokarin tabbatar da mafarkin kabilar Mapuche, kuma ku ka zabi mace ta farko da ta fito daga wannan yankin, wannan abu ne da zai sauya tarihin kasarmu."" Babban taron da za a yi na sauya fasalin kundin tsarin mulkin, wanda ya kunshi mabobi maza da tsirarun mata kuma shi ne irinsa na farko a duniya, an cika shi da mutanen da ba su fito daga gwamnati ba. Wannan ya sanya ake da kyakkyawan fatan, za a samu nasarar sauyin da aka dade ana korafin ya kamata ayi tun shekarar 2019, lokacin da kasar ta fuskanci mummunar zanga-zanga. Cikin bukatun da kabilar Mapuche da sauran kabilu tara na kasar suka mika shi ne samar musu da jiha, wanda hakan zai sanya aji muryarsu da karba musu 'yanci, da amincewa da al'adunsu da kuma harsunansu. Ita kan ta Loncón, ta sha rubuta littattafai da ke koyar da harshen Mapuche wato mapudungun. Har wa yau, al'ummomin na son a karbo musu gonakin da aka kwace musu tun zamanin iyaye da kakanni, wanda hakan ke janyo rashin jituwa tsakaninsu da sauran kabilu. Loncón ta shaidawa jaridar La Tercera ta kasar cewa: ""Za mu amince ayi sasanci, don haka su daina tsoron mu. Ta yi kalaman ne gabannin gabannin zabarta, ta kara da cewa "" Ana yi wa al'ummar Mapuche rashin adalci, wannan kira ne na ba su 'yancinsu, a kuma karbe mu a yadda muke a yi mu'amala da mu cikin gaskiya da adalci.""" https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-57794870 +business Yakin Ukraine: Daliban Najeriya na biyan sama da dala 1,000 domin fita daga Ukraine' "'Yan Najeriya da suka maƙale a Ukraine na neman agajin gwamnatin ƙasarsu domin su koma gida sakamakon yadda yaƙin ke kara kazancewa tsakanin Rasha da Ukraine. Wani bidiyo da ya ɓulla a shafukan zumunta ya nuna dandazon ɗaliban na ife-ifen neman taimako, suna cewa ""we want to go home"" - ""muna so mu koma gida"". Matasan waɗanda suka ce ɗalibai ne a Jami'ar Sumy, sun ce yanzu haka ba su da ruwan sha, ba wuta sannan abincinsu ya kusa ƙarewa. ""Yanzu mun kwana kusan uku ba mu yi wanka ba,"" in ji wata ɗaliba da ta yi magana ta bidiyon. Wannan koken nasu na zuwa ne a daidai lokacin da hukumomin Najeriya sun suka ce sun fara tattaunawa da wasu ƙasashen Turai don ganin 'yan ƙasar su ci gaba da karatu a can, bayan tserewa yaƙi a Ukraine. A wani ɓangaren kuma ɗaliban da suka dawo gida da BBC ta tuntuɓa, sun shaida mana yada abokansu da suka saura a Ukraine ake cewa su bayar da sama da dala dubu kafin su fice zuwa kasashe makwabta. Ma'aikatar harkokin wajen Najeriya, ta ce hukumomin Romania sun bai wa daliban kasar damar ci gaba da karatu a jami'o'in kasar, bayan sun tsere daga Ukraine sakamakon yakin da ake tafkawa a kasar. Babban sakatare a ma'aikatar, Gabriel Aduda, ya ce suna kan tattaunawa da ministan ilimi na Romania domin karbar daliban Najeriyar. Mista Aduda ya kara da cewa yanzu haka suna tattaunawa da sauran makwaftan kasashe kamar Poland da Hungary da Girka da Slovakia da Luthuenia don su bai wa 'yan Najeriya irin wannan damar ta ci gaba da karatunsu. Sai dai duk da haka, Najeriya ta ci gaba da aikin kwaso 'yan ƙasarta daga ƙasashe makwabtan Ukraine, kafin kammala tattaunawa tsakanin hukumomin ƙasashen ta yadda za su iya komawa ƙetare don su ci gaba da karatu. Tuni daliban da suke can Ukraine da wadanda suka samu dawowa gida suka fara maida martani akan wannan dama da wasu kasashen suka fara bai wa daliban Najeriyar. Daya daga cikin su da ba ta so a bayyana sunan ta ba, ta shaidawa BBC cewa; ''Ina son a taimaka a bari mu kammala karatunmu a can saboda yawanci mun yi nisa, wasu shekarar karshe suke wasu sauran shekara Daya ta rage su kammala karatu. Kuma yanzu idan muka ce za mu dawo Najeriya baya za a maida mu, indai za a taimaka mana an yi mana adalci mu na son karasawa a can.'' Shi ma wani dalibin da ya gujewa yakin zuwa Poland daga Ukraine, yayi fatan za a sami saukin biyan kudi tare da jajircewa a tabbatar da kudirin ya kai gaci don kar karatun da suka fara ya shiririce. ""Yawanci mun zo Ukraine saboda karatun da sauki, idan kasashen za su dauke mu da ragin kudin makaranta ko ma kyauta, za mu so hakan. ""Duk da hakan mun godewa hukumomi da gwamnatin Najeriya da suka dawo da mu gida. ""Amma har yanzu akwai abokan mu dalibai a Sumy, su na cikin halin tashin hankali, sai sun biya sama da dala dubu ake fito da su, dan allah gwamnati ta taimaka ta fitar da su. ""Dalibai sun fi 1500 a can dan Allah a taimaka a kubutar da su."" Tuni aka kwaso 'yan Najeriya kusan 1,000 amma har yanzu akwai dalibai da dama a yankin Sumy na Ukraine da ke neman tallafin gwamnatin Najeriya don su koma gida ko kuma wata kasa mai aminci. Sai dai duk da wannan sabon yunkuri na baiwa daliban Najeriya wuraren da za su ci gaba da karatunsu, mai yiwuwa sai an kammala mayar da su gida ne sannan tsarin komawarsu karatun a kasashe irin su Romania da sauran kasashen zai kankama." https://www.bbc.com/hausa/labarai-60642688 +business Matsalar rashin isassun muhallai a Najeriya "A kasashen duniya da dama al'ummomi na fuskantar matsalar rashin matsugunai. Wannan ya kasance babban lamari ga gwamnatocin kasashe game da tsare-tsarensu na wadatar da jama'a da gidaje masu nagarta da inganci a yankunan birane da na karkara. A nahiyar Afirka, Najeriya ta kasance kan gaba wajen yawan al'umma, sai dai duk da kasancewarta kasa mafi girman tattalin arziki a Afirka, tana fuskantar irin wannan matsala kamar sauran kasashe marasa karfin tattalin arziki. Zuwa yanzu dai ana iya cewa Najeriya ta gaza samar da isassun matsugunai ko gidajen kwana domin gudanar da rayuwa irin ta masu matsakaicin hali ga miliyoyin al'ummarta. Kididdiga ta nuna cewa ana karancin gida a Najeriya da yawansu ya kai kimanin miliyan 22. A wata hira da BBC, Shugaban bankin bayar da lamunin gina gidaje na Najeriya Arc. Ahmed Dangiwa ya ce ""kashi 80 cikin 100 na 'yan Najeriya ba sa iya gina gida ko kuma su fitar da kudi su saya."" Haka nan matsalar na kara munana da karancin gida 900,000 a kowace shekara. A kan haka ne Najeriya ta kafa wani banki mai suna Federal Mortgage Bank, wanda ke bayar da lamunin gina gidaje ga al'umma. A wasu kasashen gwamnati na daukar nauyin gina gidaje kyauta ga masu dan karamin karfi a yayin da wasu kasashen ke gina dumbin gidaje ba tare da sun tsawwala kudi ba domin sayarwa al'umma cikin sauki. Mazauna birane a kudancin Nijeriya kamar sauren birane a sauran bangarori na kasar na fuskantar matsalar rashin wadatattun gidaje ga al'umma. A cewar wani rahoto na Majalisar Dinkin Duniya da aka gabatar gaban Majalisar kare hakkin Dan Adam da ke Geneva, ya nuna ire-iren nau'in matsalolin da ke tattare da rashin gidaje wadatattu ga jama'a. Rashin gidaje na haddasa matsaloli daban-daban a cikin rayuwar al'umma, kama daga na tattalin arziki da bunkasar rayuwa da ci gaba mai daurewa da dai sauren su. Miliyoyin mutane ne aka kora daga unguwannin talakawa a cikin shekara 20. Kuma akasari ma sanarwar da ake ba su 'yar kadan ce game da wa'adin da ake basu na su bar unguwannin ko kuma gidajen. Ko a bara, jami'ar Majalisar Dinkin Duniya da ke sa ido kan samar da gidaje Leilani Farha ta bayyana cewa fiye da kashi biyu cikin uku na 'yan Najeriya na zaune ne a gidaje irin na marasa karfi gami da rashin abubuwan more rayuwa. Hakan na faruwa ne ba tare da an tanadar masu wani wuri ba a madadi wurin da a baya suke tsugune. Najeriya dai na da dumbin kungiyoyi na kwararru ta bangarori daban-daban da kan iya taimakawa wajen samar wa al'ummar kasar gidaje. Ire -iren wadannan kungiyoyi sun hada da kungiyar masu kula da tsara birane da kungiyar masu kula da ingacin gine gine da dai sauren su. Sai dai matsaloli da dama su na hana ruwa gudu a cikin lamarin . Da dama daga cikin al'umma ba za su iya mallakar gidajen shiga ba duk tsawon rayuwarsu a duniya sabili da matsaloli da dama na rashin wadata da tattalin arziki da suka addabe su." https://www.bbc.com/hausa/labarai-51749802 +business Haƙar ma'adinai a Niger: 'Na rasa 'ya'yana uku saboda karya doka' "Wani mutum mai suna Nuhu da ke zaune a ƙauyen Shikira na jihar Naija a arewacin Najeriya na cikin jimami, shekara huɗu bayan gubar dalma ta kashe 'ya'yansa uku. Wata rana ya tashi daga barci, sai ya ga 'yarsa ta farko na cikin wani hali na rashin lafiya, farko cikinta ne ke ciwo, sai ta fara farfaɗiya, ko da aka kai ta wani asibiti, sai Allah ya yi mata cikawa. Nuhu bai gama dawowa daidai ba sai kuma 'yarsa ta biyu ta fara irin ciwon da ta farko ta yi - ba da daɗewa ba sai ta mutu haka ma ta ukun. ""Na ji zafi matuƙa da yara na har uku suka mutu a kan idona"", in ji Nuhu. ""Duk lokacin da na tuna yadda suka mutu da kuma irin wahalar da suka sha, sai na fara kuka."" Yaran Nuhu na daga cikin wasu ƙananan yara 28 da suka mutu a ƙauyen Shikira a 2015. Ƙasar ƙauyen na ɗauke da guba sakamakon haƙar ma'adinai da ake yi ciki kuwa har da gubar dalma. A farko, dabbobinsu ne suka fara mutuwa, kafin daga bisani kuma matsalar ta shafi yaransu. Wani mai suna Aliyu a ƙauyen shi ma ya rasa ɗansa, ya bayyana cewa mutanen ƙauyen na tunani kamar mayu ne suka kama yaron. Amma daga baya sun gane cewa yadda suke haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba, kuma ba tare da kulawa ba ne ya jawo musu hakan. Abin gaba ɗaya ya shafi jama'ar ƙauyen, kuma shekara huɗu bayan faruwar hakan har yanzu suna cikin tashin hankali. Har yanzu babu wani ci gaban a zo a gani a ɓangaren ayyukan haƙar ma'adinai a Najeriya. Akasarin ma'adinan da ake haƙowa a ƙasar musamman a arewacin Najeriya masu haƙar ma'adinai na gargajiya ne ke yin aikin. Lamarin ya jawo gurɓatar muhalli da kuma ƙalubale ga lafiyar al'ummar yankin. Akwai sama da mutum dubu 500 da ke haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba a Najeriya. A shekarar 2010, an samu matsala matuƙa a jihar Zamfara inda yara 400 suka mutu, sai kuma a 2013, yawan ya ƙaru zuwa 700. A 2015 kuma, sai kusan irin hakan ta faru a ƙauyen Shikira, har yanzu kuma 'yan ƙauyen na cikin jimami. A yunƙurin gwamnatin ƙasar na faɗaɗa tattalin arizƙinta da kuma juya akalarta daga man fetur, gwamnatin ƙasar ta yanke shawarar karkata hankali ga ɓangaren haƙar ma'adinai. Gwamnatin ta buƙaci masu haƙar ma'adinan da su haɗa ƙungiya wanda hakan zai sa hukumomi su iya tallafa musu. Dakta Magaji, malami a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, ya bayyana cewa gwamnati ba ta mayar da hankali ba wajen hana haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba. Ya bayyana cewa gwamnatin ba ta da wani tsari a kimiyyance da za ta jawo hankulan masu zuba jari zuwa harkar. A lokacin da wannan mummunan lamari ya faru a ƙauyen Shikira, gwamnatin ƙasar ƙarƙashin ma'aikatar lafiya ta ɗauki matakin kawar da guba da kuma lalatatun sinadaren da ke kawo matsala a ƙauyen. Ma'aikatar lafiyar ta bayar da magani ga sauran yaran garin, kuma ta koya wa jama'ar garin hanyoyin da za su bi wajen haƙo ma'adinan ba tare da sun jefa rayukansu cikin haɗari ba. Ma'aikatar ta shaida wa masu haƙar ma'adinan da kada su rinƙa kawo kayan da suka haƙa gidajensu, an kuma koya musu yadda za su rinƙa tsaftace jikin su. Ɗaya daga cikin likitocin ma'aikatar lafiya Dakta Simba Tirima ya bayyana cewa dabarun da aka koya wa masu haƙar ma'adinan ya sa yawan gubar da ke cikin ƙasa ta ragu da kuma ta cikin jinin 'yan garin. Shekaru huɗu bayan wakiliyar BBC Dooshima Abu ta ziyarci ƙauyen ,jama'ar ƙauyen sun shaida mata cewa yaransu sun daina mutuwa sakamakon dabarun da aka koya musu na haƙar ma'adinai." https://www.bbc.com/hausa/labarai-53035773 +business Bidiyon hada-hada a babbar kasuwar Kano bayan bude ta Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon: A ranar Laraba ne sausaucin dokar fita da gwamnati Kano ta yi na bai wa ‘yan kasuwa damar fita domin ci gaba da harkokin cinikinsu. Gwamnatin jihar ta ce an bude kasuwar ne bayan cimma matsaya da wakilan 'yan kasuwar wajen samar da matakan da za a a dauka a wajen ganin ba a sami yaduwar cutar ba. Ranakun Laraba da Juma’a da Lahadi ne ranakun da gwamnatin ta amince da a bude wuraren ibadu da kuma kasuwani a jihar. A wannan bidiyon abokin aikinmu a Kano Khalifa Shehu Dokaji ya dauko mana yadda Kasuwar Sabon Gari ta kasance a ranar farko ta bude ta. https://www.bbc.com/hausa/media-52911500 +business Invictus Obi: Kotun Amurka ta yanke hukuncin daurin shekara 10 kan dan kasuwar Najeriya Obinwanne Okeke "Wata kotun Amurka ta yanke hukuncin daurin shekara 10 kan dan kasuwar Najeriya Obinwanne Okeke wanda aka fi sani da 'Invictus Obi' bisa samunsa da laifin damfara a shafin intanet wace ta kai ta $11m. Antoni Janar na Gundumar Gabashin Virginia da ke kasar Raj Parekh ya ce dan kasuwar ya kwashe shekara da shekaru yana amfani da rukunin kamfaninsa mai suna Invictus Group da ke Najeriya da wasu kasashen duniya wajen damfarar mutane miliyoyin dala. Mujallar Forbes Africa ta taba sanya Obinwanne, mai shekara 33, a cikin jerin 'yan Afirka da ke kasa da shekara 30 mafiya shahara a harkokin kasuwancin. Hukumar bincike ta Amurka FBI ce ta kama shi a watan Agustan 2019. Antoni Janar Parekh ya ce: ""Ta hanyar amfani da hanyoyin yaudara da sojan-gona, Obinwanne Okeke ya gudanar da harkokin kasuwanci a duniya ta hanyar imel da kuma kutse a kwanfuta lamarin da ya kai ga damfarar mutane kimanin $11m. ""Hukuncin na yau ya nuna yadda tsarin sanya ido kan kwafutoci na EDVA da hukumar hukumar FBI suke da karfin isa duk fadin duniya domin ganin an tabbatar da adalci a madadin Amurkawan da aka damfara da kuma tabvatar da ganin an hukunta masu damfara ta intanet ko a ina suke a duniya."" Kotun ta ce Mr Okeke ya gudanar da wannan damfara ce tsakanib 2015 zuwa 2019,kuma galibin wadanda ya damfara mazauna Gundumar Gabashin Virginia ne. 'Yan Najeriya dai sun yi kaurin suna wajen damfara ta intanet. A a shekarar 2020 sai da 'yan sandan 'yan sanda a Hadaddiyar Daular Larabawa suka cafke wani dan Najeriya da ya yi suna a shafin sada zumunta na Instagram Raymond Igbalodely da aka fi sani da Hushpuppi, kan zargin damfarar Dala miliyan 435. 'Yan sandan sun kuma cafke wasu mutum 11 'yan kungiyar a samamen da suka kira Fox Hunt 2 a samame 6 da suka kai a kasar." https://www.bbc.com/hausa/labarai-56093941 +business Abin da sabon farashin burodi a Najeriya ke nufi? "Kungiyar masu burodi ta Najeriya ta umarci duka mambobinta da su ƙara farashin kayansu da kashi 30 cikin 100 saboda ƙaruwar farashin sinadaren haɗa burodin da dangoginsa. Umarnin na zuwa ne ranar Alhamis bayan da aka cimma matsayar a ƙarshen tattaunawar majalisar zartarwar kungiyar da aka yi a Abuja. Da yake bayani kan dalilan ƙara farashin, shugaban ƙungiyar na kasa Mansur Umar ya ce ƙaruwar farashin siga da bota da fulawa duka na cikin abubuwan da suka janyo ɗaukar matakin. Shugaban ya ce farashin fulawar da suke saya a ƙasa da naira miliyan shida a duk mota guda, yanzu suna sayanta kan miliyan tara. Cikin tattaunawarsa da BBC Hausa, mai magana da yawun ƙungiyar masu burodi, Kabiru Hasssan Abdullahi, ya ce an ƙara farashin ne da kashi 30 cikin 100. ""Kusan dukkan jihohi sun fara aiki da sabon farashin amma mu a Kano yau (Laraba) muka dawo, za mu kira taron masu gidan burodin,"" in ji shi. Hakan na nufin burodin da ake sayarwa N100 zai koma N130. Na N200 zai koma N260, yayin da na N400 zai zama N520. ""Mu kanmu muna cikin matsala, idan ka duba gidajen burodin da aka rufe daga shekara ɗaya zuwa yanzu suna da yawa,"" in ji Kabiru Hassan. ""Mun yi iya 'yan dabarunmu don kar a ƙara amma babu yadda za mu yi, in ana son burodin ya fita da inganci dole ya fita da nauyinsa, shi ne zai zama lafiyayyen abinci."" Ya ƙara da cewa an samiu ƙarin naira 3,000 a kan kowane buhun fulawa cikin shekara ɗaya, wanda ya kai kusan kashi 50 cikin 100. Babban Bankin Najeriya ya karya darajar Naira da kashi 7.6 cikin 100 kan dalar Amurka, abin da masana ke ganin zai taka rawa wajen hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar. Masanin tattalin arziki Dr. Muhammad Shamsuddeen na Jami'ar Bayero da ke Kano ya ce irin wannan matakin na lalata darajar kuɗi dama a kan talaka yake ƙarewa musamman tun da talaka ne yake zuwa kasuwa ya sayi kayan masarufi. Ya ce kuma da yawa kayan masarufi a Najeriya shigo da su ake yi daga ƙasashen waje kuma wannan lalata darajar kuɗi zai shafi farashin kayan sannan ya ƙara tsawwala hauhawar farashi a ƙasar. ""Idan ba a manta ba a watan da ya gabata, hauhawar farashi a Najeriya ya kai kusan kashi 18.33 cikin 100, wanda yanzu idan aka ci gaba da lalata darajar Naira, hauhawar farashin na iya kaiwa kashi 20 cikin 100 nan da watan gobe"" a cewarsa. Dokta Shamsuddeen ya ce wannan shi ne babbar wahala da talaka zai iya fuskanta. Ya ƙara da cewa lalata darajar Naira na iya haifar da rashin aikin yi a ƙasar tun da kamfanoni da masana'antu da dama a Najeriya sun dogara ne da shigo da kaya daga kasashen waje domin sarrafawa - wannan na iya nufin injina ko kayan da ake sarrafawa don samar da wasu kayayyakin. ""Idan ya zama cewa waɗannan kayayyakin sun yi tsada sakamakon faɗuwar farashin Naira, babu shakka wasu masana'antun ba za su iya ci gaba da aiki ba dole su rufe masa'antun ko su rage kayan da suke yi,"" in ji Dokta Shamsu. Ya ce wannan zai haifar da korar mutanen da suke aiki a waɗannan masana'antun." https://www.bbc.com/hausa/labarai-57279807 +business Birtaniya za ta bai wa Ukraine tallafin makamai da kudade "Birtaniya za ta bai wa Ukraine taimakon motocin yaki na igwa har 120 da makamai masu tarwatsa jiragen ruwa da na harbo jiragen sama baya ga tallafin kudi. Fadar gwamnatin Birtaniyar ce, Downing Street ta sanar da haka bayan wata tattaunawa a ziyarar bazata da Boris Jonson ya kai wa Shugaban Ukraine Volodymr Zelensky a Kyiv. Firaministan ya gana da Shugaba Zelensky, a abin da fadar gwamnatin Birtaniyar ta kira nuna goyon baya ga Ukraine. Ofishin jakadancin Ukraine a London ya sanya wani sako na tuwita mai rubutun kalmar mamaki da Ingilishi, tare da hoton Boris Johnson da Volodymr Zelensky zaune, tebur tsakaninsu a Kyiv. Daman tun kafin yanzu Firaministan ya zaku ya kai wannan ziyara, amma ya tsaya yana jiran yanayin tsaro ya inganta a babban birnin, bayan janyewar dakarun Rasha daga yankin. A yayin wannan ziyara wadda ta kasance ta baya-bayan nan ta wani shugaban kasar yamma, fadar gwamnatin Birtaniyar ta ce, kasar za ta tabbatar da bai wa Ukraine karin tallafin dala miliyan 500 ta hanyar Bankin Duniya. A jawabin da ya saba gabatarwa da dare Shugaba Zelensky ya bayyana Boris Johnson a matsayin abokin Ukraine na gaskiya, tare da yaba wa Birtaniya da Firaministan saboda taimaka wa kasarsa: Ya ce ""Boris (Johnson) na daga cikin wadanda ba su taba saurarawa ko ta dan lokaci ba kan su taimaka wa Ukraine. Jagorancin Birtaniya wajen bai wa kasarmu taimakon da ya wajaba, musamman na kayan tsaro, tare kuma da jagoranci wajen sanya takunkumi abu ne da zai dawwama a tarihi. A tarihin kare dumukuradiyya, a tarihin kare Turai. Har abada Ukraine ba za ta manta da alherin da Boris da Birtaniya suka yi mata ba'' in ji shi Volodymyr Zelensky ya kuma yaba da taron duniya na taimaka wa kasarsa da dala biliyan 11. Ya yaba wa masu bayar da tallafin da suka hada da gwamnatoci da kamfanoni da bankuna da daidaikun jama'a, wadanda suka yi alkawarin tallafawa a taron da aka yi a Poland." https://www.bbc.com/hausa/labarai-61055936 +business Johnson & Johnson: An ci tarar kamfanin biliyoyin naira Wata kotu a Amurka ta ce tilas kamfanin hada magunguna na Johnson & Johnson ya biya tarar $572m saboda rawar da ya taka na saka rayukan 'yan jihar Oklahoma cikin hadari. Jim kadan bayan yanke hukuncin. kamfanin ya ce zai daukaka kara. Wannan ce shari'a irinta ta farko cikin jerin shari'u dubbai da aka fara saurara kan kwayoyi masu sa mutane su dogara a kansu daaka kai kamfanonin da ke hadawa da raba magungunan. A farkon wanan shekarar ne kamfanin Johnson & Johnson ya cimma wata yarjejeniya da kamfanin da ke hada wani magani mai suna OxyContin, wato Purdue Pharma da kuma Teva Pharmaceutical. Ya biya kamfanonin biyu fiye da dala miliyan 360. https://www.bbc.com/hausa/labarai-49478325 +business NAPTIP ta gargaɗi ƴan Najeriya kan fataucin mutane zuwa Turai Hukumar da ke yaƙi da fataucin mutane ta Najeriya, NAPTIP ta yi gargadi mai karfi tare da ankarar da 'yan kasar kan ƙaruwar fataucin mutane ta hanyar yaudarar su da sunan karatu a Turai ko sama musu aikin yi wanda akasari ke faruwa ta shafukan intanet. NAPTIP ta ce galibin mutanen da ake fitar da su ketare da sunan karatu kyauta ko ƙarkashin wani tallafi ko samar musu aikin yi kan ƙare ne da karuwanci ko rayuwarsu ta shiga cikin uƙuba. Fataucin mutanen dai abu ne da mahukunta suka jima suna fafutukar murƙushewa a Najeriya, sai dai yayin da ake ganin a baya yaudarar ta baki ce a wannan lokacin masu wannan mugun aiki, sun sauya salo, inda suke amfani da shafukan intanet wajen cimma burinsu. Hukumar NAPTIP, da ke yaki da fataucin mutane a Najeriya ta ce galibin mutane da ke faɗawa cikin wannan yaudara matasa ne da shekarunsu ke kamawa daga 18 zuwa 20 da ɗoriya. NAPTIP ta ce ana yaudarar matasan ne da sunan gurbin karatu kyauta ko tallafi a jami'o'in kasashen ketare, ko kuma a yi masu tayin aikin yi, sai dai a ƙarshe sai su ƙare da aikatau ko karuwanci ga mata. Sannan duk matashin da ya faɗa cikin wannan tarko yana kasancewa cikin yanayi na rashin zabi kuma fitarsa takan kasance da wahalar gaske, kamar yadda Hassan Hamisu Tahir, daraktan ɓangaren shari'a da bayar da kariya na hukumar ta NAPTIP ya tabbatar. Hukumar NAPTIP ta ce duk da cewa ba ta da alkaluma kan yawan mutanen da aka yaudara ta wannan hanya, amma dai a kusan kullum ana samun nasarar ceto mutanen da suka haɗa da mata da zama. NAPTIP da ke sake jaddada jan kunnenta ga 'yan Najeriya da burinsu kawai shi ne su je Turai domin samun rayuwa mai inganci, ta ce a yanzu dai ta yi ƙoƙarin fito da shirye-shiryen wayar da kawuna 'yan kasa, inda suke bin kasuwanni, da wajen ibada da jami'o'i, sannan ta shawarci mutane su kasance masu natsuwa da bincike kafin shigar da kansu cikin abin da ka iya ruguza musu rayuwa. https://www.bbc.com/hausa/articles/clmkkmk0knjo +business Mutane na taka sayyada a Kano saboda yajin aikin masu adaidaita sahu Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon: Masu sana'ar tuka babur mai kafa uku na a daidaita sahu ne suka shiga yajin aiki a jihar Kano da ke arewacin Najeriya, kan biyan harajin naira 100 da za su dinga biyan gwamnati kullum. Hakan dai ya biyo bayan yadda hukumar Karota ta umarci masu sana'ar babur din na adaidaita sahu da su ringa biyan naira dari kullum, wani batu da masu baburan suka nuna adawarsa da shi. Ga dai bidiyon da BBC Hausa ta dauko na irin yadda birnin ya kasance sakamakon yajin aikin a ranar Litinin. https://www.bbc.com/hausa/media-56157564 +business Matsalar tsadar rayuwa: Yadda tashin farashin kayayyaki ya haifar da zanga-zanga da 'yan gudun hijira "Fusata kan tashin gwauron zabin kayayyaki ta kara ta'azzara zuwa gagarumin rikicin siyasa a kasar Sri Lanka. Wannan kasa ta tsibiri na da kudi kalilan na shigar da kayan abinci da makamashi da karancin abubuwan amfani ya haddasa zanga-zangar kan titina da ke yin barazanar hambarar da gwamnati. Labari irin wannan na faruwa a kasar Peru mai nisan dubban kilomita, inda shugaba Pedro Castillo ya kafa dokar hana zirga-zirga a Lima babban birnin kasar a makon jiya, bayan wata zanga-zangar gama-gari kan tashin farashin mai da taki. Amma wadannan sun zarta na kasa daya kacal da yanzu haka ke fuskantar matsin tattaalin arziki, yayin da yakin kasar Ukraine ya sa farashin danyen mai kara hauhawa zuwa dala 100 kan ko wace ganga. Farashin kayan abinci na duniya sun kara hauhawa tun bayan da aka fara tattara bayanai shekaru 60 da suka gabata kamar yadda alkaluman Majalisar Dinkin Duniya suka nuna, wanda ya tashi zuwa kashi 13 bisa dari a cikin watan Maris, bayan karuwa mafi girma da ya yi a cikin watan Fabrairu. BBC ta tattauna da mutane daga kasashe shida don gano yadda suke fama da tsadar rayuwa. Tsananin hauhawar farashi da karancin abubuwan amfanin yau da kullum na kara ingiza mutane zuwa daukar tsauraran matakai a kasar Sri Lanka. Lokacin yakin basasar kasar, dubban 'yan kasar ta Sri Lankan sun zabi yin bulaguron cikin teku mai cike da hadari don neman mafaka a kasar Indiya. Mary Clara na daga cikin sahun farko na 'yan gudun hijirar kasar Sri Lanka 16 da suka zo Tamil Nadu a cikin mako na uku na cikin watan Mayu. Ta tsallake tsukin hanyar cikin teku a wani karamin kwale-kwalen kamun kifi ita da jiririnta mai watanni hudu da kuma mijinta. ""Farashin kusan komai ya tashi sama. Yana da matukar wahala ka sayi abubuwan amfani kamar sun madarar gari wa jaririna,'' Clara ta bayyana. Alkaluman hukuma sun nuna hauhawar farashin kayan a Sri Lanka zuwa kashi 15 da digo daya bisa dari a cikin watan Fabrairu - mafi girma a cikin shekaru goma - kana hauhawar farashin kaya abinci ya zarta zuwa kashi 25 da digo bakwai bisa dari. Farashin shinkafa- abincin da aka fi amfani da shi- ya tashi sama zuwa sama da dala daya kan ko wane kilo. Farashin man fetur ya linka fiye da sau biyu. ""Mijina aikin fenti yake yi amma yanzu ya shafe kwanaki bai samu aikin ba. Tun bayan tashin farashin kayayyakin amfanin yau da kullum, mun kasa samun sayen abubuwan da muka fi bukata,'' Clara ta bayyana. Akasarin sassan kasar na fuskantar yawan daukewar wutar lantarki a ko wace rana har na tsawon sa'oi 10 zuwa 12. Gwamnati na kashe fitilun bakin hanyoyi don tattalin wutar lantarkin. Matsanancin daukewar wutar lantarki na nufin cewa turakun wayoyin salula ba za su iya aiki ba, kana wasu asibitocin dole suka rika soke yin aikin tiyata. Rahotannin kafafen yada labaran kasar sun ce mutane akalla biyar ne suka mutuwa sa saboda galabaita a yayin jiran dogon layin sayen man fetur da kuma man disal a cikin makon na biyu na watan Maris. Ma'aikata kamar su mijin Clara na samun dala biyar a ko wace rana amma iyalan mutum biyar na bukatar dala takwas wajen girka cikakken abinci. Clara na gab da fadawa cikin matsalar yunwa na tsawon kwanaki da danna kafin zuwanta kasar Indiya kana halin da ake ciki na kara muni a kasar Sri Lanka. Tana sa ran wasu da dama za su biyo bayanta muddin al'amura ba su daidaita ba. ""Za ka ga mutane na neman abinci a cikin bola. Abin bakin ciki ne,'' in ji Mariel Aoun. Shekarunta 64 kuma tana zaune a birnin Beirut, wanda ya danganta irin kudin da ta samu daga hayar gidaje biyu. Kasar Lebanon, wacce rikicin siyasa da matsin tattalin arziki da ake ciki suka dabibaye tun ma kafin na baya-bayan nan, na da alkaluma na hauhawar farashin kayayyaki mafi girma a duniya - sabbin alkaluma na watan Fabrairu kashi 215 bisa dari ne na alkaluman kididdigar shekara-shekara. ""Bayan fara yaki [a kasar Ukraine] al'amuran sun kara muni. Kayan abinci sun yi batan dabo a shagunan kayan masarufi, kana idan an sake samu bayan makonni biyu, farashinsu kan linka,'' in ji Aoun. Matsin tattalin arzikin kasar ya kara ta'azzara sakamakon annobar korona da kuma babbar fashewar sinadarin iskar ammonium nitrate da ta mamaye tare da lalata tashar jiragen ruwa ta birnin Beirut a watan Agustar shekarar 2020. ""Saboda fashewar, gidana ya lalace. Na so in yi amfani da kudin da na tara wajen yin gyare-gyare, amma banki ya ki dawo min da kudina.'' Amma su kan su bankuma na fuskantar karancin kudi. ""Yanzu ba za ka iya biyan kudin komai ba ta hanyar amfani da katin biyan kudi. Dole sai ka biya kashi 50 bisa dari a tsabar kudin.'' Aoun ta ajiye wasu kayyakin abincin da hatsi a gidanta. Ta kuma zaftare yawan yadda ta ke saye-sayen kayan abincin. ""Yanzu ba na sayen cukwui - na kan yi a gidana. Ba na iya sayen avocados, wanda nake matukar so.'' Matsanancin daukewar wutar lantarki sun sauya rayuwarta. Tana biyan dala 125 wajen amfani da injin janareta na tsawon sa'oi goma a rana, amma wutar lantarkin ba ta wadata ba. ""Ba zan iya amfani na firji da na'urar wankin kaya a lokaci daya ba. Dole in kashe na'urar dumama gidana idan ina bukatar yin girki. Yak an dauki tsawon lokaci kafin ka kammala ayyukan yau da kullum.'' ""Kusan duka kayayyaki farashinsu ya tashi sama zuwa linki goma a cikin shekaru biyu da suka gabata. Lita ashirin na man fetur a baya fan 20,000 ne na Lebanon - yanzu rabin miliyan!"" ta kara bayyanawa. Aoun ta ce ko wace rana na zuwa da karin sabbin munanan labarai kuma ba ta ganin abubuwa za su yi sauki nan kusa. Turkiyya: 'Muddin abubuwa suka cigaba da tafiya a haka, bani da wani wurin da zan koma' Ibrahim ya tsere daga kasar Syria zuwa Istanbul a shekarar 2016. Kamar sauran 'yan gudun hijira har yanzu bai samu matsayin takardar zama ɗan kasa ba, amma ya samu wani aikin yi. Hauhawar farashin kaya a kasar Turkiyya ya kai girman na shekaru 20 a kan kashi 54 da digo 44 bisa dari. Hakan ya haifar da koma bayan wajen yanayin kashe kudaden masu karamin karfi kamar Ibrahim. A shekarar da ta gabata ba shi da aikin yi har na tsawon watanni biyu. Dan uwansa da ke aiki a Dubai ya tallafa masa da kudi. Ya tashi daga gida mai daki biyu da yake haya tare da wani abokinsa ya koma wani wuri daban. ""Yanzu muna gida daya tare da ma'aikata da dama. Ina da karamin daki ama dole mu rika amfani da wurin dafa abinci da ban-daki daya da sauran ma'aikata.'' Shi ma Ibrahim na kokarin rage yawan kudaden da yake kashewa. ""Na kan fita sau daya zuwa uku a wata zuwa wurin cin abinci da abokaina. Bana ma taba tunanin zuwa wurare masu tsada.'' Zuwan baki 'yan yawon bude ido na karuwa, amma kuma Ibrahim gudanar da ayyuka kamar su samar musu da motocin tasi na haya, da shirya zuwa wuraren bude ido da kuma taimaka musu da zuwa wuraren sayayya don samun karin kudin shiga. ""Buri na shi ne in koma wuri mai daki daya amma ban san iya tsawon lokacin da zan shafe ina jira ba. Duba da yadda al'amura ke tafiya, abubuwa sun wuce karfina. Shi kan sa kudin hayar da nake biya kusan yawan abinda nake samu ne - wanda ba ya rage min komai na wanda dan biya wasu kudaden.'' Bayan da tuni ya zama dan gudun hijira, Ibrahim ya bayyana cewa muddin abubuwa suka cigaba da muni, ba shi da wani wurin da zai koma. ""Komai ya kasance babu wani ci gaba. Matsalolinmu na faruwa ne saboda rashin kulawa,'' in ji Aisha Falke. Mai kananan 'yaya biyu, tana zaune a Abuja, Marubuciya a shafin intanet da kuma mai zayyanawa da dinka tufafin zamani ce. ""Muna da kawo shawarwari game da harkar kasuwanci don samu karin kudin shiga. Akwai gajiyarwa. Yana nunawa a jikina - kalli furfura ta.'' ""Nan gaba za ka bukaci ka yi aiki biyu tukuru kafin samu yanayin rayuwar da kake bukata.'' Najeriya ita ce mafi girma a Afirka wajen samar man fetur, amma ta gaza wajen tace danyen mai a cikin gida kuma ta dogara ga shigowa da kaya. Tsananin tsadar man a kasuwar duniya ya riga ya haifar da karancin albarkatun man fetur a kasar, tare da ta'azzara hauhawar farashin sauran kayayyakin amfanin yau da kullum da ayyuka. Falke ta bayyana cewa kudaden da ta ke kashewa a ko wane wata tafiyar da harkokin cikin gidanta ya kara sama da kusan rabi a cikin shekara. ""Komai ya yi tsada - shinkafa, da burodi, da kayan marmari, da sufuri, da naman miya, da man girki… Mun saba cin naman kaji a kullum, amma yanzu farashin kaji ya kusa linkawa.'' Karancin wutar lantarki da na man fetur na kara mummunan tasiri kan kasuwancinta. ""Kostomomina na amfani da kudadensu wajen sayen kayan abinci da magunguna fiye da dinka sabbin tufafi. Tufafi wani abu ne na garari a yanzu."" Su kansu wadanda ke zaune a nesa da manyan biranen kasuwanci da tattalin arziki ba su tsira daga wannan halin matsi ba. 'Yan kabilar Massai na bin al'adar yanayin rayuwar makiyaya wanda galibi ke da wadatuwa, da dogaro da shanu a matsayin arzikinsu. Amma su kan su matsin tattalin arzikin duniya ya shafe su. ""Abincin gargajiyarmu ya kunshi madarar shanu da nama,'' in ji Anny Laizer. Yanzu Laizer na zaune a birnin Arusha kuma tana aiki da wata kungiya mai zaman kan ta, amma tana tuntubar mutanenta da har yanzu suna bin tsarin yanayin rayuwar zamanin da. ""A shekarar bara za ka iay safen kilogiram 5 na albasa a kan dala 2, amma yanz waken dala 5 ne. Man girki farashin say a tashi sama zuwa kashi 50 bisa dari idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata. Farashin wutar lantarki shi ma ya karu. Ba kowa yake da hali ba,'' in ji Laizer. Bushewar kasar noma da kiwo ya riga ya tilasta wa iyala rage yawan garken shanunsu, kuma The Lazier ta bayyana cewa wasu mazan a kauyenta sun kaura zuwa garuruwa don neman aiki kamar irin su gadi. Laizer na tallafa wa iyayenta da kannenta mata, amma sauran danginta ma kan nemi taimako daga gare ta su ma. ""Albashina dala 250 a ko wane wata. Galibi yak an kare bayan kwanaki 20. Fadi-tashi ne matuka - na kan rika samun wayoyi da dama a ranar da na karbi albashi ana neman taimako na.'' 'Yan kasar Korea ta Kudu na fuskantar na su adadin hauhawar farashin kayan mafi girma a cikin shekaru takwas. Manyan labaran kasar kan tsadar kayayyaki ka iya kasancewa kashi 3 da digo 7 bisa dari ne, amma farashin wasu kayayyakin abincin ya kara hauhawa fiye da hakan, da ya tilasat wa da dama kamar su Lee So-jung sauya yanayin tafiyar da rayuwarsu. ""Ni daliba ce. Na kan samu kudin kashewa daga iyayena, kuma na kan samu 'yan kudi ta hanyar yin aikin wucin-gadi. Saboda tsadar rayuwa kudina na karewa cikin sauri. A wasu lokuta na kan koma cin kayan kwadayi ko shan gahwa a maimakon cin abinci sosai na rana,'' in ji Lee So-jung. Ta rage yawan tafiye-tafiye zuwa gidajen cin abinci, kuma ko da ta je din ma ta kan zabi cin taliya a maimakon sushi. Korea Kudu ta dogara kacokan ne kan man da ta ke shigar da shi wajen bunkasa tattalin arzikinta - a shekarar bara kasar ta shigar da man da ya kai dala 67. Hauhawar farashin kayan wanda yakin kasar Ukraine ya kara haddasawa ya yi mummunan tasiri kan tattalin arzikin. ""Tsadar rayuwa a kasata karuwa yake. Hakan na nufin 'yan zamani irina ba za mu iya samun mallakar gidajen kashin mu da muke so ba, da cin irin abincin da muke so ko sayen irin tufafin da muke so.'' Iyalan Lee So-jung da wasu kawayenta na samun tallafi daga gwamnati, amma tana daukar irin na ta matakan. ""Ba zan rika karbar bashin kudi ba saboda hakan zai saka ni cikin kangin basussuka. Ina rage yawan kudaden da nake kashewa a maimakon haka.''" https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-61081056 +business Algeria: 'Sayen mai girki ya kasance tamkar sayen magani' "Ana ci gaba da fuskantar hauhawar farashin kayayyaki a Algeria, inda masu kantuna suka ce man girki da madara sun yi karanci sai ka yi da gaske kafin ka samu. Tasirin matakan da aka dauka saboda bullar annobar korona da kuma yakin Ukraine na sake jefa rayuwa cikin tsanani ga jama'ar kasar. ""Kamar muna sayen magani,"" a cewar Samiha Sammer, mai shekara 31, cikin yanayi na nuna takaici. Tana sana'ar sayar da kek ga 'yan uwanta da abokai, wani lokaci ma tana ɗan samun abin kashewa daga wannan sana'ar, sai dai a yanzu ba ta iya samun abubuwan da take bukata don hada kek din. ""Kafin ka iya sayen mai daga kowanne kantin sayar da kayayyakin amfanin gida, sai akwai sanayya tsakaninka da mai shago ko kanti,"" a cewar Sammer. Ana gudanar da hakan ne cikin yanayi na taka-tsantsan, inda ake boye wasu kayayyakin a bayan kanti. Ita da wasu 'yan Algeria sun ce abubuwa sun sauya a shekarar da ta gabata, lokacin da matakan yaki da annobar korona suka yi tsanani. A yanzu, da watan Azumin Ramadana ke karatowa, 'yan Algeria sun matsa kaimi wajen ganin sun tanadi man girki kasancewa abu ne mai muhimmanci wajen hada abinci a lokacin Ramadan. Sammer takan yi tafiya tsakanin gidanta a Bilda zuwa garuruwa makwabta irin su Kolea, inda ake samun kayan marmari da itatuwa cikin rahusa. A kwanakin nan farashin dankali ya karu da kashi 30 cikin 100 tsadar ta yi tsanani idan ka duba yadda ake saye a watannin baya, dogayen layin da ake gani wajen sayen madara na nufin mutane na yini a kan layi kafin samun madara su kai gida. ""Yanzu a daina yin haka saboda turereniyar da ake yi ga cunkosa wani lokaci har fada ake yi saboda neman madara,"" kamar yadda wani ma'aikaci yake cewa cikin yanayi na damuwa. ""Yanayin abin kunya ce."" Kuma idan ka yi kokarin kauracewa bin layi to aljihunka zai amsa. A yanzu tana biya kusan kudin kasar dinar 420 kan kilo 1 na madarar gari da ake shigowa da shi maimako dinar 25 na rangwamen da muke samu. Algeria na samar da madara amma cikin kason ba shi da yawa, don haka tsawon shekaru ta dogara ne kan madarar da ake kai mata daga Faransa, da saura kasashen Turai da kuma na baya-bayan nan daga Hadaddiyar Daular Larabawa - akasari madarar ta gari ce. Sai dai abin da ya fi damun 'yan Algeria shi ne batun man girki. Kamar yadda suke samun tallafi kan madarar da suke saye, shi ma aka man girki yake, sai dai tun kafin rikicin, da ma man ya yi tsada - ana sayar da lita biyar na mai kan dinar 600 ($4.20; £3.20). Idan aka kwatanta da matsakaicin albashin ma'aikaci na dala 240 ga ma'aikatan kamfanoni masu zaman kansu da dala 410 na ma'aikatan gwamnati, matsin na kara fitowa fili na bukatar mahukunta su tashi tsaye. Rike abinci da rashawa sun karu yayinda matsalolin tattalin arziki ke galabaita mutane, kamar yadda rahoton kwamitin da majalisa ta kafa ke nunawa. Mamba a kwamitin Hishan Safar ya shaida wa BBC cewa masu sayar da man girki sun kara kudi ne saboda su maido da kudadensu da gwamnati ta janye na tallafi. A shekarar da ta gabata, kusan mutum 150,000 aka ba da rahoton sun karya dokar mahukunta, wanda akasari suka karkare a kotu, kuma an kwace lasisin mutane da dama da ke sana'a. Sai dai akwai kuma matsala wajen fasa-kaurin kayayyakin abinci mai rahusa ta iyakokin kudancin Algeria don sayarwa kasashe makwabta, wanda kwamitin majaisa ke cewa ya ""ta'azzara"". Babu alkaluma a hukumance amma majiyoyi sun shaidawa BBC ce akwai manyan motoci da yawansu ya kai 12 cike da man girki ana fasa-kaurinsu daga Algeria zuwa Mali da Nijar a kullum. Masu aikata hakan na sayar da kayayyakin da gwamnati ke bayarwa kan farashi mai rahusa, man girkin da ake yi a Algeria a kudaden ketare - ana samun ribar kusan dala 17,800 a kowacce mota guda, kamar yada majiyoyi suka shaidawa BBC. A farkon wannan watan, Shugaba Abdelmadjid Tebboune ya haramta fitar da kayayyain abinci da ke kunshe da sinadaran da aka shigo da su - irinsu man girki da sukari da taliya da garin semalina da alkamana. Rahotanni na cewa shugaban na son a hukunta masu aikata hakan saboda suna yiwa ""tattalin arzikin kasar zagon-kasa"". Amma domin gane ainihin abin da ke haddasa waɗannan matsaloli a Algeria dole sai an yi waiwaye, a cewar kwararu. 'Mafiyoyi na sace kadarorinsa' Tattalin arzikin kasar da ya dogara kan sayar da gas da ɗanyen man fetur wanda ke kawo musu riba da hayar samun kudaden shigar gwamnati, a yanzu na zame musu matsala, a cewar masanin tattalin arziki Abdal-Rahman Hadef. Cin karensu babu-babbaka a harkokin tafiyar da gwamnati da tattalin arziki na ɗaiɗaita harkokin kasuwanci, da hauhawar farashi a cewar Mista Hadef. Akwai kuma damuwar cewa tattalin arzikin kasar na iya jefa kasar cikin ukubar rikicin siyasa. An tilasta wa tsohon Shugaba Abdelazziz Bouteflika sauka daga mulki a 2019 a wani bore da 'yan kasar suka yi. Wanda ya gaje shi, wanda ya taba zama makusancinsa, a yanzu ya yi Alla-wadai da mafiyoyin da ke ""wawushe dukiyar kasar"" karkashin mulkin Bouteflika. Duk da sauyin gwamnatin da aka samu, mutane da dama sun kasance cikin fushi da ci gaba da zanga-zanga har bullar annobar korina a Maris din 2020. Kashi daya ciki uu na 'yan kasar ba su zarta shekara 37 ba a duniya, kuma rashin aikinyi ya kai kashi 11 cikin 100 na al'ummar kasar, wanda galibinsu matasa ne da suka kammala jami'a. Yayinda aka sa ido sosai, gwamnati na cewa daga wannan watan, duk masara aikinyi da suke iya nuna cewa suna da gwazon aiki za su ke samun dala 90 a kowane wata a matsayin alawus. Sai dai zance na zahiri, tsadar da gas ta yi a kasuwar duniya saboda yakin Ukraine ya taimakawa mahukunta kasar wajen iya samun kudin biyan wannan alawus na gajeren lokaci. Amma masana tattalin arziki na nuna dagewa kan Algeria ba za ta iya cigaba da biyan waɗannan kudade ba nan gaba. Amma a matsayin da ake ciki a yanzu, masu sayayya irinsu Ms Sammer na cikin tsaka-mai-wuya na iya tantace me za su saya domin amfanin yau da kullum." https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-60911983 +business Muhammadu Buhari: PDP ta ce gwamnatin APC ta jawo ƙunci da talauci "Babbar jam`iyyar hamayya a Najeriya wato PDP ta yi zargin cewa da gangan gwamnatin Shugaba Muhamadu Buhari ta ƙara farashin man fetur da wutar lantarki domin ta ƙuntata wa al`umma. A wannan makon ne kamfanin mai da hukumar wutar lantarki suka sanar da ƙarin farashin. Sai dai jam`iyyar APC ta musanta, ta na cewa PDP ce silar matsalolin ƙasar. PDP ta yi zargin cewa ƙeta ce tsagwaro a zuciyar jam`iyyar APC mai mulki, kuma wannan ne ya sa ta ninka farashin man fetur da na wutar lantarki ba tare da la`akari da irin mawuyacin halin da `yan Najeriya suka samu kansu a ciki ba. Jam'iyyar hamayyar ta ce ko farfaɗowa ƙasar ba ta yi ba daga bugun da annobar korona ta yi ma ta. Sakataren yaɗa labaran jam`iyyar mista Kola Olagbondiyan ya shaida cewa bukatar su ita ce a gaggauta soke ƙarin farashin da aka yi, don kauce wa jefa ƙasa cikin rikici. Ya ce: ``Jam`iyyar mu na da yaƙinin cewa ƙarin farashin litar mai da aka yi, daga naira 87 a zamanin mulkin PDP a shekara 2015 zuwa naira 151 farashin dappo da wata manufa aka yi, sannan bugu-da-ƙari aka kara farashin kudin kilohat guda na wutar lantarki daga naira 30 zuwa naira 62. ''Jam`iyyar APC ta kau da dukkan shakku cewa tana aniyar gana wa `yan Najeriya azaba, don cimma wata manufarta ta son zuciya.'' Jam`iyyar PDP ta ce duk mai lissafi ya san dangantakar da ke tsakanin rayuwar al`umma da wutar lantarki da man fetur, don haka duk lokacin da farashinsu ya hau, to babu makawa sai talakawa sun galabaita. Kenan babu gwamnatin da ke tausayin jama`a da za ta kau da kai ga irin wannan hauhawar farashin! Ganin cewa mai ba wata tsada can yake yi a kasuwar duniya ba, jam`iyyar PDP ta ce ba ta san da wane mizani gwamnatin Najeriyar ta yi amfani da shi wajen kara farashin man ba, saboda haka ya kamata ta fito ta yi bayani. Jam`iyyar APC a nata martanin, ta ce jam`iyyar PDP ba ta da bakin magana, saboda a zamanin mulkinta ne ta ba da kafar tabka almundahana a harkar mai, lamarin da ya haddasa taɓarbarewar al`amura a Najeriya. Barrister Ahmed jami`i ne a kwamitin riko na kasa na jam`iyyar APC da ke shaida wa BBC cewa: Janye tallafi da PDP suka kasa yi wanda ake ɓarnatarwa suka janye. ""Kuma yanayin firashin mai a kasuwar duniya dole ya zo da irin wadanan matsaloli, amma gwamnati na hada basira da alkaluma don ganin talaka ya samu sauki. ""Sannan wayanda ke korafin kan wutan lantarki gyara aka yi ma'ana wayanda suka fi shan wuta ne su zai fi tsada kan talaka da wutar ba sosai suke samu ba."" Dangane da zargin cewa da nufi APC ke jefa al`umma cikin ƙunci kuwa, Barrister Isma`il Ahmed cewa ya yi, ""Jam'iyyar APC da shugaban kasa Buhari duk babu wanda ke jindadin halin da ake ciki"". Barrister Ahmed ya kuma ce ""ba wai don ƙeta ko cin zali hakan ke faruwa ba, kawai yanayi ne aka shiga kuma muna kokarin ganin yadda za a daidaita hakan"". Matsalar tsadar rayuwa a Najeriya ita ce damuwar mafi yawan `yan kasar, inda suke cewa ba su ga alamar gwamnati ta san irin kwakwar da suke ci ba. Sannan suna ganin da wuya su yi saurin fahinta ko karbar uzurin gwamnati a wannan yanayi da aka yi ƙarin farashin mai da wutar lantarkin a daidai lokacin suke kokarin ta da komaɗar ƙarnin korona. 'Yan Najeriya da dama dai na ta faman yanke kauna kan cika alkawuran da gwamnatin shugaba Buharin ta sha yi musu. Ko a kafafen sada zumunta musamman Twitter, mutane na amfani da maudu'in #BuhariHasFailed, wato Buhari ya gaza, domin nuna takaicinsu kan matsanacin halin da suke zargi ya jefa su a ciki." https://www.bbc.com/hausa/labarai-54025110 +business An sako ƙarin fasinjojin Abuja-Kaduna bakwai "Maharan jirgin ƙasan Abuja-Kaduna sun sako ƙarin mutum bakwai daga cikin fasinjojin da suka sace a harin da suka kai kan jirgin a watan Maris. Mai shiga tsakani a sasantawa tsakanin maharan da dangin fasinjojin Malam Tukur Mamu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba. Fasinjojin da aka saka din sun hada da mata biyu da namiji daya da kuma yara hudu. Sanarwar Tukur Mamu ta ce Sheikh Ahmad Gumi ne ya shiga tsakani a wannan karon, tun bayan bayyanar wani bidiyo mako biyu da suka wuce, da ke nuna yadda maharan ke zane fasinjojin. 'Yan bindigar sun sako uku daga cikin fasinjojin kwana biyu bayan bayyanar bidiyon ranar 24 ga watan Yuli. “Sheikh Ahmad Gumi ya tuntuɓi maharan ta hanyar mai ba shi shawara kan yaɗa labarai, ya roƙe su cewa su taimaka su saki yaran da iyayensu,"" in ji sanarwar. “An fahimci cewa yaran ba su da lafiya kuma yanayin da suke ciki na ƙara taɓarɓarewa tun bayan dukan da aka yi wa mahaifinsu.” Zuwa yanzu babu tabbaci kan ko an biya kuɗin fansa kafin a sao mutanen, amma rahotanni na cewa na baya da aka saka sun biya miliyoyin naira kafin su samu 'yan cinsu. Malam Mamu ya yi iƙirarin cewa mahaifin yaran da aka saka ɗin ma'aikacin Hukumar Majalisar Tarayya ne amma babu hannun Majasalisar Tarayyar ko kuma hukumar a sakin nasa. Tun kafin yanzu Malam Tukur Mamu ya sha bayyana cewa da taimakon shahararen malami Sheikh Ahmad Gumi ake tattaunawa da 'yan bindigar. A wannan karon ma malamin ya ce da taimakon malamin da wani ɗan Majalisar Dattawa daga arewacin Najeriya aka ceto mutanen. ""Muna sanar da duniya cewa bisa tallafin Sheikh Gumi da kuma wani sanata mai-ci daga Arewa...wanda ya nemia ɓoye sunansa, duka mutum shida sun samu 'yanci a safiyar Laraba. ""Kazalika, an saki wata mace mai shekara 60 mai suna Aisha Hassan, wadda aka ce an sake ta ne saboda dalilai na rashin lafiya mai tsanani."" Sunayen waɗanda aka sako" https://www.bbc.com/hausa/articles/c065ezxl0gpo +business Bitcoin: Abin da ya sa darajar babban kudin intanet take faduwa "Dokar farko game da yin rubutu kan Bitcoin ita ce: kar ka yi rubutu kan Bitcoin. Labarin kudin dijital mafi shahara a duniya mai matukar sauri ne kuma ba da jimawa ba masu bibiyarsa za su yi layi domin sanar da kai cewa duk abin da ka rubuta game da kudin kuskure ne. Sai dai tilas mu yi rubutu kan kudin, saboda abin da ya faru cikin sa'a 24 da suka gabata gagarumin koma-baya ne ga wannan jagora cikin kudaden dijital. Zan mayar da hankalina ga Bitcoin ne a nan - amma ko masu bibiyar kudaden dijital sun san cewa kasuwar kudaden na cikin matsala sosai. Shin mene ne ke faruwa ne? Yayin da nake wannan rubutun, ana cinikin Bitcoin kan $21, 974, kuma ya fadi da kimanin kashi 25 cikin 100 cikin kwanaki biyar da suka gabata kawai, farashi mafi kankanta cikin wata 18 da suka gabata. Ya yi tashin da ya kai kusan $70,000 a watan Nuwamba. Dukkan alamu sun koma masu jan launi, kuma dukkansu sun nufi wuri guda ne - wato kasa. Masana na cewa wannan matsalar ta afku ne bayan matsalar koma-bayan tattalin arziki da ta shafi duniya, wato ba kudin intanet kawai ta shafa ba. Akwai koma-bayan tattalin arziki, da hauhawar farashin kayayyaki da na kudin ruwa baya ga matsalar tsadar rayuwa. Kasuwannin hannayen jari ma na tangal-tangal, har ta kai ga kasuwar US S&P 500 ta rikito daga tashin da ta yi da kimanin kashi 20 cikin 100. A dalilin haka, har manyan masu zuba jari sun rage yawan kudaden da suke zubawa a kasuwannin hannayen jari. Ga yawancin mutane, zuba jari a harkar da ke faduwa da tashi kuma babu tabbas abu ne da ba za su amince da zuba makudan kudade cikinsa ba. Harka ce da babu hukumar da ke sa ido a kai, saboda haka idan ka zuba kudaden ajiyarka cikin harkar, kuma kudin ya rasa daraja, ko ka rasa makullan lalitar ajiyar kudadenka na dijital, to ka yi asarar dukkan kudadenka ke nan. Mene ne ke faruwa yanzu? A watan jiya an ga yadda darajar kudin na dijital ta fadi, ko da ba mai yawa ce ba - amma duk da haka wannan ya sa mutane masu yawa sun rasa karfin gwuiwar da suke da ita ga kasuwar. Wannan ne ya sa mutane masu dama ke yanke shawarar sayar da kudaden da suka mallaka. Amma idan haka ya faru, darajar Bitcoin za ta rika faduwa - saboda haka dama tsarinsa yake. Wadannan batutuwan ne suka zama tushen matsalolin da Bitcoin ke fuskanta - kuma cikin kwana guda da ya gabata, mun kuma ga wadannan abubuwa da suka faru: Abubuwa biyu na farko sun haifar da rudewa a kasuwar. A misali, sai kawai kaga ba ka iya ciro kudi a bankinka, ko ka ji an ki biyan wasu mutane kudinsu na ajiya a banki. Babu makawa za ka garzaya zuwa banki mafi kusa da kai tare da dukkan wadanda suka sami labarin matsalar, lamarin da zai haifar da karuwar rikici da rudewa a kasar. A takaice - idan ana son komai ya koma yadda aka saba, tilas wadanda ke rike da kudaden intanet su ci gaba da rike su, kuma tilas sauran mutane su koma sayen kudin. An taba fuskantar haka a baya. Masoya Bitcoin za su sanar da kai cewa yanzu ne lokacin da ya fi dacewa mutum ya sayi Bitcoin, saboda araharsa - daga nan sai ka yi hakuri domin ya farfado. Haka dama kasuwar ta saba gani. Daya daga cikin masoya Bitcoin ya aiko min da sako dazu: ""Haka dama lamarin yake, kuma komai zai daidaita"". Attajiri Elon Musk ya sha wallafa sakonni masu yawa kan kudaden na intanet - kuma kamfaninsa mai kera motar latironi wato Tesla ya sayi Bitcoin da darajarsa ta kai dala biliyan daya da rabi a bara. Sai dai masana kasuwar kudin intanet na jan hankalin mutane da su yi hattara matuka. ""Gaskiya wannan wuri ne da sai jarumi kawai ke iya shiga"", in ji kamfanin State Street Advisor a wani shirin BBC Radio 5 mai suna ""Wake Up To Money"". Wannan kalma ta jarumi ta kawo ni ga shahararren dan wasan fim din na na Hollywood mai suna Matt Damon, wanda a watan Oktoban 2021 ya bayyana cikin wani tallan da ke son jan hakulan al'umma domin su rungumi Bitcoin. An wallafa wani sako cikin tallan da ke cewa ""Jarumi ne ke iya zama attajiri"", an haska tallan yayin da ake wasan kwallon kafa na Super Bowl na kasar Amurka, inda mutum miliyan 28 suka kalli tallan a Twitter da kuma YouTube. Sai dai ""jaruman"" da suka sayi kudin intanet a sanadin wannan tallan na can suna ciza yatsa, saboda kudin ya rasa darajarsa har sau uku daga lokacin da aka haska tallan kawo yanzu." https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-61801600 +business 'Babu abin da zai saukar da farashin dala a Najeriya' "Tashin da farashin dala ya yi wani abu ne da ba za a iya kauce masa ba a Najeriya, saboda matsalolin da suka dabaibaye tattalin arzikin Najeriya. Daga watan Janairun 2022 da ake sayar da dala kan naira 565, zuwa wannan watan na Oktoba naira ta rasa darajarta da kashi 28, kamar yadda shafin Nairametrics’ FX da ke bibiyar darajar kudi ya bayyana. A cikin abin da ya gaza kwanaki 10, farashin dala ya karu da kusan naira 54, biyo bayan sanarwar da babban bankin kasar CBN ya fitar na sauya fasalin kudin kasar. A ranar Talata a Abuja an fara sayar da dala kan naira 839, ko da yake wasu jihohin irinsu Kano farashin bai kai haka ba dalar ba ta fi 818 ba. Da dama daga cikin masu sana'ar canji za ka tarar da shagunansu babu kowa ciki, sun zauna babu abin yi, kamar yadda Mustapha Zakariya wani mai kamfanin musayar kudi na BDC ya bayyana. ""Da yawanmu mun daina zuwa kasuwa saboda bamu da abunyi, mafi yawanmu mun fi samun dalar ne ta CBN da ake kira (beading) kuma yanzu an fi shekara rabon da a ba mu"" in ji shi. Mafi yawan abokan hulda yanzu ba sa kai dalarsu domin a ba su naira, a cewar Malam Mustapha. Suma ajiyarta suke yi domin duk kwana guda dalar daraja take karawa kamar yadda darajar naira ke zibewa. ""A baya akwai wasu hanyoyi da ke rage wahalhalun samun dala da su, kamar tallafin da bankuna ke bai wa matafiya neman lafiya ko ilimi ko kuma kasuwanci, amma yanzu babu ko daya da ake samu. ""Amma idan kana da wani makusanci za ka iya samun adadin da kake so na dubu hudu da ake bayar wa a hukumance."" a cewar Mustapha. A baya akan samun dala daga bankunan kasuwanci da CBN da kuma masu kai wa kasuwa su sayer domin samun naira, amma bincike ya nuna a yanzu babu ko daya cikin wadan nan da ke aiki. Mustapha ya ce bukatar da ake da ita ta dala yasa ""ko dubu 20,000 kake nema sai dai ka hada ta da dubu daya dubu biyu domin kuwa samun dala a dunkule ya zama tarihi a Najeriya"". Ya shaida wa BBC cewa idan kana da asusu na banki na kudaden ketare zai zama kana da kudi a ciki, amma ba za ka iya cire kudin ba a lokacin da kake so. Idan wani abokin huldarka ya yi maka aiken kuaddaen ketare daga bankin kamar ""GT"" zuwa ""First Bank"" ba zai zo ba domin babu dalar a bankunan. ""Duk tashin da dala ke yi 'yan canji ake zargi, babu mai bai wa 'yan canji dala a hukumance, kuma babu wanda ya san tayaya suke samun dalar, balle kuma ba sa samu yanzu.\n""Muna cikin tsaka mai wuya. Ta bangaren gwamnati ba mu samu abin da muke so ba, ta bangaren mutane kuma zarginsu na kara yawaita a kanmu,"" in ji Mustapha. Masana na cewa ba kowa ne ke jin dadin wannan tashin da farashin dala ke yi ba, ko da bankunan kasuwanci da suke hada-hadar kudi a fadin Najeriya, domin lamarin na shafar ayyukansu. A don haka bankunan sun dauki matakai da suke gani za su iya saukaka faduwar da naira ke yi a kasar, ta hanyar bayar da kananan kudaden kasashen ketare. Idan mutum na da asusun ajiya na kudaden ketare da ake kira (domiciliary) za ka iya ajiye kudinka ciki ko nawa ne, kuma a baya za ka iya cire ko nawa kake so a ko wanne lokaci, sai dai lamarin ya sha ban-ban a yanzu. Abokan hulda na zuwa da shirin cire kudi kamar dala 100 ko sama da haka, amma bankuna sai su kare da basu dala mai 10 ko 20 ko 5 a wasu lokutan, a dabararsu zai rage tsadar da ake fara da ita. A wasu lokutan sai dai su bayar da katin ATM, to amma a ina ne za ka iya amfani da ATM domin cire kudaden a cikin Najeriya? Ga tsarin tallafin BTA da PTA da sauransu, yanzu bankunan kasuwanci a fadin Najeriya sun daina ba yar da dala a hannu (cash) sai da kati idan an fita waje a cire.\nSai dai masana na cewa tsarin cike yake da magudi da kuma cuwa-cuwa. Ba wani abu bane ya janyo tashin dala a fadin Najeriya ba illa daina bai wa gwamnati kudi da kamfanin mai na NNPC ya yi kwata-kwata. Ta hanyarsa ne gwamnati ke samun dala mai yawa. Man fetur shi ne ""babban abin da Najeriya take sayerwa ta samu dala, kuma yanzu NNPC ya yi wata takwas zuwa tara bai bayar da komi ba"" in ji Dakta Muhammad Shamsuddeen na jami'ar Bayero da ke Kano. Hakan ya biyo bayan ikirarin da NNPC ke yi na biyan kudaden tallafi (subsidy), wanda tun daga nan aka fara fuskantar karancin dalar a hukumance. ""Hakan ya sa ita kanta gwamnati idan tana bukatar dala sai dai ta bayar da takardun lamuni da ake kira (Eurobond) ta samu kudaden. ""Dalili na baya-bayan nan shi ne, sauya fasalin kudi da CBN ya sanar da cewa zai yi a kwanakin baya, abin da zai faru shi ne mutane za su fito da kudadensu su sayi kudaden waje. ""Wannan ya kara bukatar da ake da ita na dalar, wanda ita ba a da bukatar yin wata doka a kanta a Najeriya."" in ji Dr Shamsuddeen. Ya yi zargin mutanen da suke yawan zuwa bankuna suna karbar BTA da PTA domin samun riba, tunda akwai banbancin farashi tsakanin farashin gwamnati da na kasuwa. Duk wadannan abubuwa su ne ba za su bar dala ta zauna wuri daya ba, akwai bukatarta da yawa akwai kuma karancinta a kasuwa. ""Muna fargabar daga nan zuwa watan Disamba dala za ta iya kai wa naira 1,000. ""Da barar da bankuna ke yi na bayar da dala kanana babu inda za ta kai Najeriya sai baya, domin kananan kadara babu abin da suke yi sai ta'azzara lamura,"" in ji Dr. 'Da halin da ake ciki babu abin da zai tsayar da farashin dala a Najeriya'" https://www.bbc.com/hausa/articles/c8vgl33n88vo +business Biden ya kaddamar da shirin tallafin tattalin arziki Amurka na $1.9tn "Zababben Shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana wani shirin tallafi na dala tiriliyan 1.9 ga tattalin arzikin da annobar korona ta yi wa illa matuka tun kafin ya kama a iki a mako mai zuwa. Idan majalisar Amurka ta amince da shirin, shirin zai samar da dala tiriliyan 1 da za a raba wa iyalai, wanda a ciki za a biya kowa ne iyali dala 1,400 kai tsaye ga asusun ajiyar Amurkawa. Sannan shirin zai samar da dala biliyan 415 da za a yi amfani da shi wajen yaki da annobar korona da kuma dala biliyan 440 da za a yi amfai da su wajen tallafa wa kananan kamfanoni da masana'antu farfadowa. Mista Biden, wanda dan jam'iyyar Democrat ne, ya yi alkawarin kawo karshen wannan annobar da kawo yanzu ta halaka fiye da mutum 385,000 a Amurka kawai. A bara ya yi yakin neman zabensa ne kan samar da tattalin arzikin da zai mayar da hankali wajen samar da mafita kan wannan annobar fiye da yadda Shugaba Donald Trump, wanda dan Republican ne ke yi. Wanann shirin na Mista Biden na zuwa ne a lkacin da ake kara samun karuwar masu kamuwa da cutar yayin da ake kara shiga yanayin sanyi. A kowace rana, a kan sami fiye da mutum 200,000 da ke kamuwa, ban da ma su mutuwa da yawansu kan zarce 4,000 a kullum. A wani jawabi da ya yi ta talabijin, cikin daren Alhamis daga garinsu na Wilmington a jihar Delaware, ya ce: ""Akwai wata babbar matsala da ke wahalar da al'umma a gabanmu kuma babu lokacin da za a bata."" ""Lafiyar kasarmu ne ke kan gaba,"" inji shi, ""Tilas mu dauki mataki, kuma tilas mu dauki mataki yanzu."" Shugaban mai jiran gado ya kuma ce: ""Lallai za a yi tuntube, amma na yi alkawarin sanar da ku gaskiyar halin da ake ciki kan nasarorin da muke samu da kuma cikas din da za mu ci karo da su.""" https://www.bbc.com/hausa/labarai-55671462 +business An fara amfani da sabbin takardun Naira a Najeriya A ranar Alhamis ne za a fara amfani da sabbin takardun kudi da aka sauya a karon farko cikin shekaru 20 a Najeriya. Hukumomi a kasar sun ce sun dauki matakin sauya fasalin kudin ne domin magance matsalar tsaro, da samun damar mayar da garin kudi bankunan kasar. Babban bankin Najeriya ya ce kashi 80 cikin 100 na kudin da ke hannun jama'a na wurin wasu tsirarun mutane. CBN ya bukaci 'yan Najeriya su gaggauta mayar da tsofaffin kudaden da suke hannunsu bankuna, domin a sauya musu da sabbin. Ranar 31 ga watan Janairu ne wa'adin da hukumomi suka kayyade zai cika ga mutanen da aka bai wa umarnin mayar da tsofaffin kudin banki. Yawancin 'yan Najeriya na ganin ya kamata gwamnati ta mayar da hankali kan abubuwan da suka fi damun 'yan kasa, kamar magance hauhawar farashin kayayyaki, maimakon sauya fasalin kudi. Wannan sabon tsari dai ana ganin 'yan siyasa ne za su fi kowa ji a jika, wadanda ake ganin suna shirin sayen kuri'u a babban zaben Najeriyar da za a yi a watan Fabrairun 2023. Fara amfani da sabbin kudin na zuwa ne kusan makwanni uku gabanin fito da wani tsarin da CBN ya yi na kayyade adadin kudin da masu asusun ajiya na banki za su iya fitarwa a kowacce rana, ko aikewa wani asusun da kuma amfani da POS. Adadin kudin da za a iya cirewa a kowanne mako bai wuce Naira 100,000, sai kuma kamfanoni da suke da ka'idar Naira 500,000. Lamarin da ke ci gaba da janyo zazzafar muhawara har a majalisun kasar. https://www.bbc.com/hausa/articles/c25kq7ekl4zo +business Matsalar ci-rani: Hanyoyi mafiya haɗari da mutane ke bi wajen tsallaka iyakoki "Wani tsautsayi da ya faɗa kan 'yan ci-rani da ke shirin tsallaka iyakar ƙasashe a kwanakin baya ya tashi hankalin duniya. A ranar Juma'a, mutum 23 ne suka mutu lokacin da suka yi yunƙurin tsallaka shinge daga Moroko zuwa cikin Sifaniya ta mashigar Melilla. Kwana uku bayan haka, 'yan sandan Amurka a garin San Antonio suka tsinci gawar mutum 46 a cikin wata mota da aka yasar a titi. Hanyoyin da 'yan ci-rani ke bi sun ƙara zama masu haɗari saboda annobar korona, wadda ta sa ƙasashe suka tsaurara dokokin hana zirga-zirga. Akwai yiwuwar matakin zai ƙara yawan mace-mace. Hukumar Harkokin Ci-Rani ta Majalisar Ɗinkin Duniya wato International Organization for Migration (IOM) ta ƙiyasta cewa tun daga 2014, 'yan ci-rani kusan 50,000 ne suka mutu ko suka ɓata yayin da suke ƙoƙarin zuwa inda suka nufa kamar Amurka da Turai. Hukumar ta ce akwai yiwuwar mamatan da waɗanda suka ɓata su zarta adadin. Waɗanne hanyoyi ne mafiya haɗari da 'yan ci-rani ke bi? Kuma me ya sa suke bi? A cewar IOM, wannan ce hanya mafi haɗari da 'yan ci-rani ke bi. An yi ƙiyasin mutum 19,500 ne suka mutu yayin da suke yunƙurin tsallaka Tekun Bahar Rum daga arewacin Afirka zuwa Turai tun daga 2014. Akasari sukan yi yunƙurin tsalakawa ne ta cikin jiragen ruwan da aka cika su maƙil ko kuma wasu hanyoyi da suke ƙirƙira. 'Yan daba da sauran miyagu ne akasari ke tuƙa jiragen waɗanda ke safarar mutane. A ƙasar Tunisia, wadda ke cikin hanyoyin da 'yan ci-rani ke bi zuwa Turai ta Tekun Bahar Rum, har wata maƙabarta aka tanada musamman ta waɗanda ke nutsewa a ruwan. ""Ganin waɗannan gawarwakin a nan na tayar mani da hankali,"" kamar yadda Vicky, wata 'yar Najeriya da ke son shiga Turai ta Tunisia, ta faɗa wa kamfanin labarai na AFP lokacin da ta kai ziyara maƙabartar. ""Idan na ga gawarwakin nan sai na ji kamar na fasa tsallaka tekun,"" a cewarta. Hukumar IOM na fargabar cewa sauran 'yan ci-ranin ba lallai su fahimta ba. ""Har yanzu ana ci gaba da zuwa ci-rani ta Yankin Tsakiyar Tekun Bahar Rum. Abin da ya fi tayar da hankali shi ne yadda ake tsallakawa ta ruwa a faɗin duniya. Hakan na ci gaba da salwantar da rayukan jama'a saboda sakacin ƙasashe,"" in ji Safa Msehli, mai magana da yawun IOM. Frontex, hukumar da ke tsaron iyakokin Turai, ta ce an ceto mutum kusan 300,000 da ke ƙoƙarin tsallakawa ta wannan hanyar tun daga 2015. 'Yan ci-ranin Afirka da dama da ke son shiga Turai kan kama hanya ne daga nahiyarsu, inda suke bi ta cikin sahara don isa ga ƙasashen arewacin Afirka. Yanayi mai tsanani ne babbar matsalar tafiyar: IOM ta yi ƙiyasin mutuwar mutum 5,400 sakamakon yunƙurinsu na bi ta sahara daga 2014 zuwa 2020. ""Za ku ga mutane na mutuwa a cikin sahara. Wasu saboda ƙarancin kuzari, sai su mutu a can. Wasu kuma ruwansu ne ya ƙare,"" kamar yadda wani ɗan ci-rani Abdullah Ibrahim ya faɗa wa AFP. Wata barazanar ita ce ta miyagun da ke safarar mutane a kan hanyar. ""Tashin hankalin da 'yan sumoga ke haddasawa da na masu safarar mutane da na jami'an tsaron kan iyaka, na cikin abubuwan da ke ƙara ta'azzara mace-mace da ake samu a sahara,"" a cewar IOM cikin rahotonta na baya-bayan nan. Duk da cewa ba duka 'yan ci-ranin da ke fitowa daga nahiyar Amurka ne ke nufar Amurka ba, sai dai babban burinsu ke nan na mutanen da ke son sauya wurin zama a yankin. Akwai ƙalubale mai girma a kan iyakar Amurka da Mexico: yankin ya yi ƙurin suna wajen yanayin tsarin ƙasashensu, ciki har da sahara, kuma 'yan ci-ranin kan yi yunƙurin tsallakawa Amurka ta kogin Rio Grande da ya ratsa wani ɓangare na iyakar. Nitsewa a ruwa ce babbar matsalar wannan hanya, wadda IOM ta ƙiyasta mutuwar mutum aƙalla 3,000 tun daga 2014. Waɗanda ke zabar su guje wa nitsewa ta hanyar ɓuya a cikin motoci na fuskantar wasu haɗarurrukan daban; kamar na waɗanda suka mutu a San Antonio. A watan Disamban 2021, 'yan ci-rani 56 ne suka mutu a Chiapas na Mexico bayan motar da suke tafe a cikinta ta yi hatsari. IOM ta ce fiye da mutum 4 cikin 10 na 'yan ci-rani a duniya a 2020, an haife su ne a nahiyar Asiya, kuma nahiyar na da hanyoyi da yawa da suke bi. A cewar hukumar MDD, mutum kusan 5,000 ne suka mutu ko suka ɓata a Asiya cikin shekara takwas da suka wuce. Akasarin waɗannan mace-macen sun ƙunshi Musulmai 'yan ƙabilar Rohingya da ke bin hanyar Bengal da kuma kogin Andaman don neman tsira da rayuwarsu a maƙwabtan ƙasashe, ko kuma tsallakawa Turai. ""Muna cikin yunwa, na kasa shan ruwa, babu ma ruwan. Babu abinci, ba shinkafa, ba mu iya cin komai ba. Haka muka yi ta rayuwa a kogi tsawon wata ɗaya,"" a cewar Muhammad Ilyas mai shekara 37, wanda ke cikin 'yan gudun hijirar Rohingya, cikin hirarsa da APF bayan an ceto shi daga jirginsu da ya kife. Kamar sauran 'yan ci-rani a sauran wurare, su ma waɗannan na fuskantar ƙwace da fashi daga miyagu masu safarar mutane. Wata hanyar mai haɗari ita ce iyakar Turkiyya da Iran, wadda ta fuskanci ƙaruwar 'yan ci-rani daga Afghanistan tun bayan da Taliban ta ƙwace mulki a Agustan 2021. Hukumar 'yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNHCR) ta ce an yi rajistar 'yan Afghanistan mutum fiye da miliyan biyu da ke gudun hijira a Iran." https://www.bbc.com/hausa/labarai-61979049 +business Abin da ƴan Najeriya ke cewa kan ƙarin albashin ƴan siyasa "Hukumar tarawa da rarraba kudin haraji ta kasa ta ce ta kammala shiri domin sake duba albashin masu rike da mukaman siyasa, da ma'aikatan shari'a, domin dacewa da halin da kasar ke ciki. A wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na intanet ta ce a yanzu ana aiki ne da dokar da aka tsara tun shekarar 2008, wadda ta yi la'akari da yanayin da ake ciki lokacin da aka tsara dokar. Sanarwar ta ambato shugaban hukumar Engr. Elias Mbam na cewa za su sake duba albashin zababbun shugabanni da masu rike da mukaman siyasa, kama daga shugabannin kananan hukumomi da kansiloli, da gwamnoni da kwamishinoni, da kuma albashin shugaban kasa da mataimakinsa da kuma 'yan majalisun jiha da na tarayya. Mista Mbam ya ce hakkin hukumar ne ta tsara albashin zababbun shugabanni da masu rike da mukaman siyasa, tun daga matakin kananan hukumomi da zuwa matakin tarayya. Haka kuma sanarwa ta ce aikin hukumar ya shafi zababbu da masu masu rike da mukaman siyasa, ban da albashin sauran ma'aikatan gwamnati, wanda hukumar ta ce ke hannan ma'aikatar tsara albashi ta kasa To sai dai kungiyar kwadago ta kasar ta nuna rashin jin dadinta game da matakin, tana mai cewa babu wadanda suka fi cancantar karin albashi a kasar kamar ma'aikatan gwamnati. Tana mai cewa a halin yanzu masu rike da mukaman siyasa sun fi kowa samun albashi mai gwabi a kasar. Da alama labarin ƙarin albashin ga ƴan siyasa bai yi wa wasu masu amfani da shafukan sada zumunta daɗi ba. Wani mai amfani da shafin tuwita @Pshuah ya ce ""masu kuɗi suna ƙara azurta kansu, yayin da sauran ma’aikata da al’ummar Najeriya ke cikin wahala."" Wani mai suna “josephIfenyiC7 kuwa cewa ya yi ""kalli yadda mutane ke shan wahala, amma su kuma suna batun ƙara wa kansu albashi.” Albashin ma’aikata na daga cikin abubuwan da suke haifar da cece-ku-ce a Najeriya. Bayanai na cewa yanzu haka akwai jihohi da dama na ƙasar waɗanda ba su fara aiwatar da ƙarancin albashi na naira dubu 30 ba ga ma’aikatansu. Ko a kwakanin baya sai da ƙungiyar ƙwadago reshen jihar Zamfara da ke arewacin ƙasar ta bai wa gwamnatin jihar wa’adin aiwatar da tsarin ƙarancin albashin na naira dubu 30, inda daga baya gwamnatin jihar ta yi alƙawarin aiwatarwa." https://www.bbc.com/hausa/articles/cyxypydky1go +business Shugabanni G5 Sahel sun fara taro kan matsalar tsaro a yankin Shugabannin kasashen Yammacin Afirka guda biyar da ke yaki da masu da'awar jihadi sun fara taron samar da tsaro a yankin, a Niamey, babban birnin Jamhuriyar Nijar. Taron na zuwa ne kwanaki kadan bayan mutuwar sojojin Jamhuriyar Nijar guda 71 a wani kwanton baunar da mahara suka yi wa sansanin sojojin a Inates. Shugabannin Mali da Burkina Faso da Jamhuriyar Njair da Mauritania da Chad na kar fuskantar matsin lamba domin su magance matsalar tsaro da ta yi sanadiyar mutuwar soja fiye da 230 a yankin a cikin wata hudu. Kafin fara tattaunawa kan matsalar ta tsaro, sai da shugabannin suka halarci addu'oin da aka gudanar a kusa da makabatar da aka binne sojojin Nijar da masu ikirarin jihadi suka kashe a iyakar kasar da Mali. Hakan ya jawo hankali cewa duk da girke sojojin Faransa guda 4,000 yankin, har yanzu rundunar yankin na G5 Sahel ba su samu nasara ba. An kafa rundunar G5 Sahel ne shekara hudu da suka wuce, lokacin da kusan dukkan hare-haren masu da'awar jihadin ana samunsu na Mali. Zuwa yanzu hare-haren karu sosai zuwa wasu sassan yankin na. Hakan na da nasaba da karancin kayan aiki da rashin isasshen tsaro a wurin dakarun kasashen biyar. https://www.bbc.com/hausa/labarai-50800439 +business Trump ya yi barazanar lalata tatalin arzikin Turkiyya "Amurka ta ya yi barazanar gurgunta tattalin arzikin Turkiyyan idan Turkiyyar ta wuce ka'ida. Shugaba Trump ne ya yi gargadin bayan sanar da janyewar dakarun Amurkan daga Arewa-maso-gabashin Syria ba zato, ba tsammani. A jerin sakonnin da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Trump ya kare matakin da ya dauka, wanda ke iya ba Turkiyya damar kai wa mayakan Kurdawa hari a makwabciyarta Syria. Janye dakarun ya jawo wa Trump kakkausan suka daga magoya bayansa 'yan jam'iyyar Republican. Mayakan Kurdawa na daga cikin manyan abokan Amurka da suka taimaka mata wurin murkushe mayakan kuniyar IS. Amma Turkiyya na daukar mayakan Kurdawan a matsayin 'yan ta'adda. Amurka ta girke dakaru sama da 1,000 a Syria. An janye kimanin 24 daga cikin sojojin daga iyakokin Syria, kamar yadda wani jami'in ma'aikatar harkokin wajen Amurka ya bayyana, A ranar Litinin shugaba Trump ya wallafa a shafinsa na Tuwaita cewa an an zabe shi ne domin ya ""fitar da kasar daga wannan yakin da ya ki karewa. Yanzu Turkiya da nahiyar Turai da Syria da Iraki da Rasha da Kurdawa ne za su lalubo mafita daga matsalar."" Hakan ya biyouy bayan hirar wayar da yi da shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiya. Bayan hakan ne fadar White House ta ce Turkiyya za ta ""kai hare-haren da ta dade da tsarawa a arewacin Syria, kuma sojojin ba za su kasance a yankin ba"". Bayan Kurdawan sun zargi Amurka da cin amana da kuma suka daga 'yan siyasar kasar, Trump ya kara wallafa jerin wasu sakonni a ranar Litinin, yana jan kunnen Turkiyya idan har ta kuskura ta yi wani wani abu, to zai karya tattalin arzikinta. A bara, Amurka ta kara haraji a kan wasu kayan da Turkiyya ke samarwa kuma ta kakaba takunkumi a kan wasu manyan jami'an Turkiyya bayan an samu rashin jituwa tsakanin kasashen biyu na kungiyar NATO. A gargadinsa ga Turkiyya, Trump ya ce kada Turkiyya ta sake ta yi wani abin da Amurka ke ganin rashin imani ne. Shugaban Amukan ya ce idan har aka cutar abokan nasu, to za a samu babbar matsala. A cikin wata sanarwa, kakakin ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon, Jonathan Hoffman ya ce ""ma'aikatar ta yi wa Turkiyya magana da babbar murya cewa Amurka ba ta amince da matakin da Turkiyya za ta kai a Yammacin Syria ba"". A taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya na baya-bayan nan, Shugaba Erdogan ya gabatar da taswirar wani yanki mai fadin kilomita 480 da ba a yaki a iyakar Syria da yake so kasarsa ta kula da shi. Yankin zai zama matsuguni ga 'yan Syria kimanin miliyan 3.6 da ke zaman gudun hijira a Turkiyya. A ranar Litinin ma'aikatar tsaron Turkiyya ta ce ""an kammala dukkanin shirye-shirye domin daukar matakin,"" kuma kafa irin wannan yankin na da ""muhimmanci"" ga 'yan Syria da kuma samar da aminci a yankin. Sai dai Turkiyya ta sha yin barazanar kai hari a kan mayakan Kurdawa a iyakokin Arewa-maso-yammacin Syria. Turkiyya na daukar 'yan sa kan Kurdawa na YPG a matsayin wani reshe na haramtacciyar kungiyar Kurdawa da ta kwashe shekara 30 tana neman ballewa daga Turkiyya. A wani bangare kuma a ranar Talata Iran ta bayyyana adawarta da duk wani matakin soji da Turkiyya za ta dauka a Syria. Mayakan SDF na gudanar da wasu sansanonin 'yan gudun hijira da na rike iyalen wadanda ake zargin mayakan kunigyar IS ne a ciki da wajen yanki mai amincin da Turkiyya ke bukata. Ana rike da iyalen wadanda ake zargi mayakan IS a Ain Issa da Roj da ke cikin yankin. Sansani mafi girma shi ne na Al-hol, da ke kusa da iyakar Iraki, kuma yake da nisan kilomita 60 daga Tukiya. Mutane 70,000 ne ke sansanin Al-hol, kashi 90 dinsu mata da kananan yara ne, wadanda suka hada da mutum 11,000 'yan kasashen ketare." https://www.bbc.com/hausa/labarai-49970665 +business Asarar da Saudiyya ke yi saboda rashin mahajjata daga kasashen duniya "Saudiyya na daga cikin manyan kasashen duniya da annobar cutar korona ta haifar da koma baya gahanyoyin samun kudaden shigarta. Saudiyya na samum ɗumbin kudaden shiga a lokutan ayyukan Hajji da Umara da miliyoyin Musulmai kan halarta a duk shekara daga kasashen duniya. Kamar dai a shekarar bara, bana ma haka batun yake game da rage adadin wadanda za su halarci aikin hajjin, duk da cewa yawan ya ɗara na bara din. Rashin zuwan mahajjata ƙasar daga ƙasashen duniya na nufin rage yawan kuɗaɗen shigar Saudiyya a fannoni da dama da suka haɗa da na sufuri da na otel-otel har ma fannin abinci da sauran kayayyaki. A wannan maƙalar, BBC Hausa ta yi nazari kan irin asarar da rashin zuwan mahajjatan ƙasashen duniya ke jawo mata. BBC ta tattauna da tsohon shugaban Hukumar Alhazai ta Najeriya, kuma masani kan harkokin da suka shafi ayyukan hajjin, Barista Abdullahi Mukhtar. Masanin ya ce baya ga man fetur, babu wani abu da ke bai wa al'umma da kuma gwamnatin Saudiyya kuɗin shiga kamar ayyukan Hajji da Umara. Ya kuma ƙara da cewa a ƙiyasin shekara ta 2019, wanda shi ne hajjin da aka samu mahajjata da dama daga kasashen duniya kafin annobar cutar korona, Saudiyya ta samu kudin shiga dala biliyan 12. ''Wato wannan ƙididdiga ce kawai ta gwamnati da ke rubuce, wacce ba a hada da abubuwan da watakila ba a sanya su a littafi ba kamar masu ƙananan sana'o'i ba,"" in ji shi. ''To duk wadannan idan aka ce babu aikin hajji, kuma an shekara ba a yi Umara ba yadda aka saba yi, asara ce mai yawan gaske ga ita kanta gwamnati da kuma al'umma da suke amfana daga aikin ibada da mutane ke zuwa yi''. Wasu labaran da za ku so Ko shakka babu dai ayyukan hajji da Umra in ji masanin kan harkokin ayyukan hajji da umarar Abdullahi Mukhtar na bai wa mutane da daman gaske damar samun kudin shiga, in ji masanin. Ya ƙara yin misali da aikin hajjin da aka yi a shekara ta 2019. ''An yi amfani da motocin safa-safa masu yawa domin jigilar alhazan a lokacin aikin hajjin shekaarar 2019, da kuma yadda aka samu koma baya mai yawan gaske bayan barkewar annobar korona,'' in ji shi. Ya kuma kara da cewa, an yi amfani da akalla motoci 32,978 a Aikin Hajjin shekarar 2019. ''Yanzu ko da direba ne kawai za a dauka mutum 32,000 a ce shekara ta zagayo wadannan mutane ba su samu aikin yi ba, ai ba karamar asara bace, ballantana kowace mota tana da mai rakiya da ake kira kwandasta,'' ya ce. Ma'aikatar ƙididdiga ta Saudiyyaa ta nuna cewa a hukumance ma'aikata da suke fitowa su yi aiki sun kai mutum 350,830 in ji Barista Mukhtar. ''Adadin wadannan mutane suke yi wa alhazai hidima mutum miliyan biyu da dubu hudu da suka je aikin hajjin wannan shekarar,'' in ji shi. ''To wadannan mutane akasarinsu ba su samu aikin yi ba a cikin shekaru biyu, don haka hakika asarar na da yawan gaske. ""Kuma wannan misali kadan ne daga ciki, ba a hada da misali da maganar ma'aikatan jirgi, da batun tashi da saukarsa, da sauran abubuwa da daman gaske ba."" ""Mutum miliyan 2.4 daga kasashen waje, da mutum 600,000 'yan ƙasa da suka fito Aikin Hajji, wannan fa bai hada da ma'aikata da ake zuwa da su daga kasashe domin taimaka wa mahajjatansu ba, na cikin gida ne kawai,"" a cewar Alhaji Abdullahi. Ya ƙara da cewa rashin aikin nan shi zai sanya waɗannan ma'aikatan kusan kashi 80 bisa 100 daga cikinsu ba su samu aikin yi ba. Karin labarai masu alaƙa Ko shakka babu Saudiyya ta tafka manyan asarori sakamakon dakatar da masu zuwa yin aikin hajjin daga kasashen duniya, da kuma taƙaita yawan ƴan kasar da za su halarci aikin hajjin. Kamar yadda Alhaji Abdullahi Mukhtar ya bayyana cewa girman Aikin Hajji ga gwamnatin Saudiyya da kuma al'ummar Musulman duniya za a iya ƙiyasta su ta bangaren kudi. ""Amma abu ne wanda yake zamani ya zo da dole lissafin tattalin arziki na kowace kasa da mai shiga da kuma mai fita ana duba shi ta wasu fuskoki da ake ɗora su a kan mizani na tattali arziki na kasa. ''Babu shakka rashin yin Aikin Hajji ga Saudiyya da su kansu baƙi masu shiga ya jawo manyan asarori wa gwamnati da kuma 'yan kasa. ""Saboda irin ɗumbin kudaden da ƙasar ta saba samu a irin wannan lokaci,"" ya ce. Aikin hajji na shekarar 2019 in ji masanin, ya samar wa da gwamnatin Saudiyya kuɗaɗen shiga dala biliyan 12, kana kusan kaso 20 daga tattalin arzikin da ake samu daga abin da bai shafi mai ba. ""Idan kuma aka ƙididdige gaba daya tattalin arzkin Saudiyya a wannan shekarar za a iya cewa ya kawo musu kusan kashi bakwai zuwa 12. ""Don haka ba ƙaramin koma baya da kuma tafka asara Saudiyya ta yi sakamakon annobar cutar korona da ta haifar da haramta wa miliyoyin Musulmai halartar aikin hajjin da suka saba zuwa a duk shekara ba,'' in ji shi. Lafiya da kwanciyar hankalin mahajjata fiye da kuɗin shiga Abin da Abdullahi Mukhtar ya ƙara shaida wa BBC game da yadda al'amura za su kasance shi ne ita Saudiyya Allah ya hore mata ƙarfin tattalin arziki da kuma ma'aikata masu hangen nesa. Yana ganin babu shakka za su fito da hanyoyi da dama na tallafa wa ƙasarsu domin ganin cewa sun rage musu raɗaɗin wannan asarar da suka yi. ""Na yi imanin za ta ɓullo da wasu hanyoyin da za su samar wa da mutanenta ayyukan yi. ""Kamar yanzu misali hajjin bana na shekarar 2021 an yarda mutum 60,000 su fita su yi Aikin Hajjin. ""Wannan ƙari aka samu a kan na bara, don haka adadin mutane da aka ɗauka sun ƙaru a kan na bara. ""Don haka da yardar Allah a shekara mai zuwa ta 2022 adadin wadanda za su je aikin hajjin zai ƙaru, sai dai zai dauki lokaci kafin a ce an koma yadda ake yi a baya da miliyoyin mutane ke zuwa,"" a cewarsa. Ya kuma bayyana cewa Saudiyya za ta yi kyakkawan nazarin yadda aikin zai kasance a dogon zango da kuma yadda 'yan kasar za su samu wadata. Amma kuma duk da girman wannan matsala da asarori da ake magana a kai in ji masanin, ita Saudiyya ta fi bayar da muhimmanci ga a yi Aikin Hajji lafiya fiye da saun kuɗin shiga. ""Darajar mahajjaci daya, ya shiga ya yi Aikin Hajjinsa cikin aminci, da kwanciyar hankali da kyakkyawan tsaro da kuma lafiya, ya fi mata muhimmanci fiye da abin da za ta samu. ""Don haka suna ƙoƙarin tabbatar da ganin cewa Aikin Hajji bai zama wani wuri na yaɗa cuta ba saboda mutanen da ke zuwa daga sassa daban-daban na duniya"" a cewarsa. Annobar cutar korona ta haifar da manyan matsalolin koma bayan tattalin arziki a kasashen duniya. Baya ga hakan ta kuma haifar da karin matsaloli na rashin aikin yi musamman a tsakanin matasa." https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-57895586 +business Matsalar abinci: Ko Ukraine za ta iya ciyar da duniya duk da yaƙin da ake yi? "Manoman Ukraine sun girbe amfanin gonar da ya kai tan miliyan 20 amma ba za su iya fitar da shi kasuwar duniya ba, kuma ga shi lokacin sabuwar shuka ya kawo kai. Me za a yi domin kai wa mutane da ke matsananciyar bukata abincin, yayin da farashin abinci ya yi tashin gwaron zabo a duniya? A farkon watan Fabrairu, Nadiya Stetsiuk take cike da farin ciki da fatan samun ingantacciyar shekara. An samu kyakkyawan yanayi tun shekarar 2021, ta kuma samu yabanya mai kyau domin masara da alkama da ta shuka a karamar gonarta da ke tsakiyar yankin Cherkasy da ke Ukraine sun yi kyau. Farashin kayayyaki a kasuwannin duniya sun tashi, kuma hakan take kusan kowacce rana, don haka sai ta adana amfanin gonar da nufin saidawa nan gaba. Kwatsam sai Rasha ta kai wa kasar mamaya. Yakin bai daidaita yankin da ta fito ba, kamar sauran kashi 80 cikin 100 na gonakin kasar. Har yanzu sojin Ukraine ne iko da yankin, sai dai radadin yakin ya afka wa gonarta. ""Tun fara mamayar, ba mu sayar da ko kwayar hatsi ba. Farashin a nan rabi ne kan wanda muka saba saidawa kafin fara yakin nan,"" in ji Mrs Stetsiuk. ""Za a fuskanci karancin abinci a Turai da duniya baki daya, a nan lamarin ba haka yake ba, saboda babu hanyar da za mu fitar da abincin wasu kasashe."" Ministan harkokin wajen Ukraine Dmytro Kuleba ya bayyana hakan da ""bita da kulli"" wata tayin Rasha na dage haramcin rufe tashar ruwan Ukraine, shi kuma a janye wa kasarsa takunkuman da aka kakaba ma ta. Ukraine ta kasance sahun gaba a kasashe masu fitar da abinci a duniya, tana bada gudummawar kashi 42 cikin 100 na 'ya'yan sanfulawa (sunflower) da ake amfani da shi don samar da man girki, sai kashi 16 na masara da kashi 9 na alkama. Wasu kasashen sun dogara kacokam da Ukraine. Kashi 80 cikin 100 na alkamar da kasar Labanun ke amfani da shi daga Ukraine yake fitowa, da kuma kashi 76 na man girki da aka sarrafa da sanfulawa (sunflower). Shirin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya da ke ciyar da mutanen da tsananin yunwa ke neman hallakawa a kasashe kamar Habasha da Afghanistan da kuma Yemen, yana sayen kashi 40 cikin 100 na alkamar da ake ciyar da wadannan kasashe. Gabanin yakin, an samu raguwar safarar abinci a duniya. Matsanancin fari da aka yi fama da shi ya janyo koma-baya ta fannin noman alkama da man girki a kasar Canada a shekarar da ta gabata, yayin da waken soya da masa suka yi karanci a kudancin Amurka. Annobar korona ta yi mummunar illa. A kasashen Malaysia da Indonesia raguwar ma'aikata na nufin raguwa a fannin manja, wanda ya janyo tashin gwauron zabbin farashin man girki a kasuwannin duniya. A farkon shekarar nan, farashin yawancin kayan abinci a duniya ya yi matukar tashi. Yawancin mutane na fatan amfanin gona daga Ukraine zai sassauta karancin abincin da ake fama da shi. Sai dai kash!!! mamayar Rasha ta toshe wannan dama. Ministan noma a Ukraine ya ce a yanzu haka akwai tan miliyan 20 na abinci nau'in hatsi a kasar da babu damar fitar da su waje. Gabannin yakin, kashi 90 na kayan abincin da Ukraine ke fitarwa tana amfani ne da tashar ruwan Baharul Aswad, da ke iya daukar manyan tankokin hatsi, da yin tafiya mai nisa zuwa China da Indiya, kuma ana samun riba mai tarin yawa. Amma a halin yanzu duka an rufe su. Rasha ta kwace iko da yawancin tashoshin ruwan Ukraine, yayin da ta toshe saura da hana manyan jiragen ruwan dakon kaya 20 motsi, ciki har na yaki hudu. Shugaban shirin samar da abinci na MDD David Beasley ya yi kira ga kasashen duniya su shirya jerin gwano domin bude tashoshin da Rasha ta toshe. ""Idan babu fahimta a Rasha, ta fannin soji babu wani abu da zai fuskanci turjiya,"" in ji Jonathan Bentham, mai sharhi kan sha'anin safara ta ruwa kuma jami'in Cibiyar nazari kan harkokin kasashen waje. Jerin gwanon tawagar na bukatar rakiya ta sama, da samun karfi ta sama da ta ruwa, sannan za a cimma hakan ta amfani da siyasa. ""Idan ana son kwantar da hankula, ya kamata a bukaci kasashen da ke Baharul Aswad kamar Romania da Bulgeria su yi hakan. Sai dai watakila ba su da karfin yin haka. Don haka aka bukatar shigo da kasashe mambobin Nato."" Hakan zai kawo shigar Turkiyya, wadda ke iko da wani bangare na tekun a wani yanayi mai sarkakiya. Tuni ta bayyana ba za ta taba bari a yi amfani da shi wajen safarar jiragen yaki ba. Rasha ta yi musu tayin ba da wata kafa ta shigar da jiragen kayan abinci, ita kuma a saka mata da cire takunkuman da ke kanta, hakan na zuwa ne bayan tattaunawar da Tarayyar Turai ta jagoranta a ranar Laraba wadda ta sake lafta wa Rasha sabbin takunkumai, babu kuma wata alama ta sassauci ko sauya matsaya. Ko da kuwa an kawo karshen yakin, za a dauki watanni ko shekaru kafin tekun Baharul Aswad ta koma daidai, kamar yadda Mr Bentham ya bayyana, sakamakon yadda Ukraine ta kare tashar ruwan ta da mayan nakiyoyi da wasu dabaru da suka yi ta yadda jiragen da ba su aminta da su ba za su nutse. A yanzu dai za a iya fitar da kayan abincin daga Ukraine ne kadai ta hanyar amfani da hanyar mota ko a bi ta kogin Danube. A makon da ya wuce, Tarayyar Turai ta sanar da shirin zuba jarin biliyoyin yuro a fannin ayyukan baben more rayuwa. Sai dai makofciyar Mrs Stetsiuk, Kees Huizinga - wanda ya mallaki gona eka 15,000 ya ce hakan bai wadatar ba. Ya na ta kokarin fitar da kayan abincin tun farkon fara yakin, cike-ciken takardu da EU ta bukata ya janyo tsaiko da gajiyawa, ga kuma dogayen layukan da ke iyakar kasar da ya kai kilomita 25, wato mil 16. Lamarin akwai gajiya da karaya, cikin makonni uku da suka wuce, da kyar da sidin goshi Mr Huizingaya iya fitar da tan 15 na hatsi. In da zai yi amfani da tashar ruwan Odesa cikin awoyi kalilan zai fitar da su maimakon makonni. Duk da cewa an fi batun karancin alkama a duniya, yawancin hatsin da Ukraine ke da shi dai masara ce. Wannan kuma ya samo asali saboda dalilai biyu, kamar yadda mai sharhi kan abinci dangin hatsi Elena Neroba a Ukraine ta bayyana. Ta yi amanna da cewa, manoman Ukraine sun kagu su sayar da alkamarsu, saboda sakamakon tuna zamanin bakin fari da tsananin yunwa na Holodomor a shekarar 1938, lamarin da ya hallaka miliyoyin 'yan kasar. Sannan 'yan Ukraine ba su fiye cin masara ba. Har yanzu Mrs Stetsiuk tana da kusan kashi 40 cikin dari na abin da ta noma a shekarar da ta wuce, wanda take tarawa kadan-kadan a rumbunta, kafin kaka mai zuwa. Ta ce matukar aka ci gaba da tafiya a haka, tabbas za a shiga mawuyacin hali sakamakon karancin abinci a shekara mai zuwa. ""Muna son ci gaba da noma. Muna son taimakawa, mu samar da abinci ga mutane."" Amma ta ce cikin kankanin lokaci, Rasha ta janyo musu koma-baya, ta mayar da su shekaru 20 a baya lokacin da aka yi fama da rashin wadata." https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-61596377 +business Abin da ƙaruwar hauhawar farashi da kashi 19.64 ke nufi ga ƴan Najeriya "Hukumar Ƙididdiga ta Najeriya NBS, ta ce hauhawar farashi ta ƙaru a ƙasar da kashi 19.64 cikin 100 a watan Yulin 2022. Wannan ita ce hauhawar farashi mafi yawa da aka taɓa samu a ƙasar tun shekarar 2005 - shekara 17 da suka wuce. Yawan ya wuce wanda ƙasar ta samu a watan Yuni na kashi 18.6 cikin 100. An samu bayanan hauhawar na baya-bayan nan ne ta yin la'akari da ma'aunin farashin kayan masarufi da NBS ta fitar. Amma wani ƙwararre kan harkokin tattalin arziki ya ce wannan sabon rahoton na NBS na nuna cewa ƙasar tana cikin matsala. Dr. Muda Yusuf, shugaban cibiyar bunƙasa harkokin kasuwanci a Najeriya ya ce abin da wannan rahoto yake nunawa shi ne rayuwa na ƙara tsada. Ya ce talakawa za su ƙara talaucewa ""saboda tsananin tsadar kayayyaki da hauhawar farashi."" Ƙwararren ya ce rahoton na nuna cewa ya kamata mutane su farga su gane halin da ake ciki a Najeriya ya wuce hankali."" ""Farashin kayayyaki ya ruɓanya a Najeriya a shekara ɗaya da ta gabata. ""Kun dai sa irin wahalar da mutane ke sha wajen fafutukar neman abinci. ""Wannan kaso 19.64 cikin 100 ɗin na nuna cewa lallai al'amura sun lalace sosai,"" in ji shi. Yusuf ya ƙara da cewa ""Lamarin ya munana. Mutane da yawa abinci yana musu wahalar samu saboda hauhawar farashi."" Ƙwararre kan harkar tattalin arzikin ya ce wannan ƙaruwar hawan farashin zai yi mummunan tasiri a kan mutane. Shugaban cibiyar bunƙasa harkokin kasuwancin ya lissafa waɗansu dalilai da ya ce su suka jawo matsalar tattalin arziki. ""Kun san me ake nufi ai idan aka ce da ƙyar mutane ke samun abin da za su ci."" Ya yi bayanin cewa ""Matsalar tsaro ta sa mutane ba sa iya zuwa gona. Mutanen da ke samar mana da abin da za mu ci suna can a sansanonin gudun hijira saboda hare-haren da ake kai musu. ""Shi kuwa tsadar lantarki da man fetur da ake amfani da su wajen sarrafa abinci da sauran kayayyaki na sa mutane suna kashe fiye da kuɗin da suke samu. Sannan ga tsadar man fetur da dizel da man jirgi. ""Tsadar kuɗaɗen ƙasashen waje ma a wajen musaya wata babbar matsalar ce da ke durƙusar da darajar naira,"" ya ce. Dr. Muda Yusuf ya ce ya kamata gwamnati ta saka ido a kan harkar tattalin arzikin nan. ""Ba abin da gwamnati take yi, kuma jagoran lura da harkokin tattalin arzikin ƙasar mataimakin shugaban ƙasar ne da kansa. ""Shi ma shugaban tawagar gyaran tattalin arzikin Doyin Salami kamar ba ya nan."" Ya ce kamata ya yi gwamnati ta dinga sauraron abin da ƙwararru suke cewa da shawarar da suke bayarwa. ""Gwamnati ta tattara mutanen da suka fahimci wannan batun. Wataƙila ma shugaban ƙasa bai san halin da ake ciki ba,"" ya ce. Akwai waɗanda suka ƙware a fannin tattalin arziki a Najeriya da za su iya samo mafita ga matsalar. Amma ƙwararren ya ce matakin farko na magance matsalar shi ne a fara magance matsalar rashin tsaro." https://www.bbc.com/hausa/articles/c3g026ykyrdo +business Waiwaye: ISWAP ce ta kashe mutum 41 a cocin Ondo, maniyyatan Najeriya sun fara isa Saudiyya "Kamar kowane mako, mun duba muhimman abubuwan da suka faru a makon da ya gabata. Maniyyatan Najeriya sun fara sauka a Saudiyya Jirgin farko na maniyyata daga Najeriya ya tashi daga birnin Maiduguri na Jihar Borno ranar Alhamis don gudanar da ibadar Hajji ta shekarar 2022 - 1443 bayan Hijira. Zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, maniyyatan Najeriya 1,354 ne suka sauka a Saudiyya. Jirgin farkon ya tashi ne zuwa Saudiyya da maniyyata 500 da tsakar rana. Shugaban Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya Zikrullah Kunle Hassan da Gwamnan Borno Babagana Umara Zulum na cikin waɗanda suka halarci bikin tashin jirgin. Zikrullah ya buƙaci maniyyatan su yi wa Najeriya addu'a bayan sun yi wa kansu, ""don miƙa wa sabuwar gwamnati mulki cikin kwanciyar hankali"" yayin da ake tunkarar zaɓen 2023. Jumullar maniyyata 43,000 ne aka sa ran za su je aikin daga Najeriya a bana. ISWAP ce ta kai kashe mutum 41 a cocin Jihar Ondo, in ji gwamnatin Najeriya Gwamnatin Najeriya ta yi zargin cewa kungiyar ISWAP mai tsattsauran kishin Musuluncin ce ta kai hari a wani coci da ke garin Owo na Jihar Ondo a Kudu maso yammacin kasar. Harin ya yi sanadin mutuwar akalla mutum arba'in tare da jikkatar mutane da dama. Ministan harkokin cikin gida na kasar, Rauf Aregbesola, ne ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Alhamis bayan kammala taron majalisar tsaron kasar wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta. Wannan ne karon farko da majalisar tsaron kasar ta dora alhakin harin kan kungiyar ta ISWAP. Idan hakan ya tabbata, zai kasance karon farko da kungiyar ta kai hari a kudancin kasar. ISWAP ta dade tana kai hare-hare a arewacin Najeriya musamman a arewa maso gabas. Aregbesola ya ce majalisar tsaron kasar ta damu matuka bisa kashe-kashen da ake yi da sunan batanci ga addini kuma ta umarni jami'an tsaro su cafke mutanen da ke da hannu a abubuwan da suka faru a Sokoto da Abuja kwanakin baya. Gwamnan Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya sanya dokar hana fita a wasu kananan hukumomi biyu da suka hada da Lamurde da Guyuk biyo bayan rikicin kabilanci. A wata sanarwar da ya fitar, gwamna Fintiri ya ce dokar hana fitar za ta soma aiki daga karfe 5 na yamma zuwa 6 na safe. Rahotanni na cewa rikicin ya faru ne da safiyar ranar Litinin, sai dai hankula sun kwanta bayan tura jami'an tsaro domin dawo da doka da oda. Gwamnan ya ce ba za su lamunci ɓata-gari su tarwatsa kasar ko tarwatsa zaman lafiyar al'umma ba. Fintiri ya kuma aike da sakon ta'azziya da jaje ga wadanda lamarin ya shafa. Tsohon gwamnan jihar Legas Bola Ahmad Tinubu ya lashe zaɓen fitar da gwani na shugaban ƙasa na jam'iyyar APC. Ya lashe zaɓen ne da ƙuri'a 1,271, kuma dama tun da fari shi ne ƴar manuniya ta nuna ya fi yawan ƙuri'u. Bisa alƙaluma da aka sanar a bainar jama'a, ministan sufuri Rotimi Amaechi ya samu ƙuri'a 316, yayin da Yemi Osinbajo ya samu ƙuri'a 235. Shugaban majalisar dattijan ƙasar Sanata Ahmad Lawan ya samu ƙuri'a 152. Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya samu ƙuri'a 47, shi kuwa tsohon gwamnan jihar Imo Sanata Rochas Okorocha bai samu ƙuri'a ko ɗaya ba. Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya zama ɗan takarar sanata mai wakiltar Sokoto ta Kudu ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP. Gwamnan ya koma takarar ɗan majalisar dattawa ne bayan zaɓen fitar da gwani na ɗan takarar shugaban ƙasa inda ya janye wa Atiku Abubakar. Gwamnan ya yi nasara ne ba wata hamayya, kuma zai fafata ne da Sanata Abdullahi Danbaba Dambuwa na jam'iyyar APC. Najeriya dai na da tashoshin samar da hasken lantarki 23, wanda suke samar da mega watt dubu 11,165. Kamfanonin da ke samar da wutar lantarki a kasar ne ke kula da tashoshin. Ana dai yawan smaun daukewar wutar lantarki a kai a kai a Najeriya, abin da ke janyo dakushewar harkokin kasuwanci musamman masana'antu da sauransu.Bayanai sun nuna cewa sakamakon matsalar rashin wutar da ake fama da ita a Najeriya, an gano cewa tashar samar da hasken lantarki 20 ne a kasar suka lalace, abin da ya janyo ake rasa mega wat 2000. Dalibai 701 daga jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya ba za su zana jarrabawar kammala sakandire ta WAEC ba saboda rashin ba su damar biyan kudaden da ya kamata su biya. Jaridar Punch ta ruwaito cewa daliban, wadanda suka fito daga makarantun sakandire daban-daban a jihar an i ba su damar sanya makinsu na makaranta a shafin hukumar da ake shirya jarrabawar kammala karatun sakandiren. Ko da yake, hukumar daga bisani ta yi kira ga makarantun da abin ya shafa a kan cewa za a ƙara buɗe shafin domin su sanya makin nasu. Makarantun da abin ya shafi ɗalibansu sun haɗa da Government Secondary School Kuse, wadda ɗalibanta da ke ajin karshe 290 abin ya shafa. Sai Government Secondary School Independence Way Kaduna, mai ɗalibai 150 da Government Secondary School Kagarko mai dalibai 110 da kuma Government Senior Secondary School Iddah mai dalibai 100. Sauran sun hadar da Al-Bahmeen Academy, Kaduna mai dalibai takwas da Kalhyatu AbdulRahman Bin Auf Academy, Jere mai dalibai 15 da Great Panaf Schools Kaduna mai dalibai 13 da ECWA Secondary School, Kubacha mai dalibai 10 sai kuma Government Secondary School Mato mai dalibai biyar. Rundunar ƴan sandan Najeriya ta rage wa wani jami'inta muƙami wanda ta kama yana rawa kuma yana rera wata waka da aka bayyana ta ƴan ƙungiyar asiri a wani bidiyo a kafar Tiktok, Ɗan sandan da aka bayyana sunansa a matsayin Isaac Mathew, an rage masa mukami daga kofur zuwa kurtun ɗan sanda. Jami'in hulda da jama'a na rundunar ƴan sanda, Olumuyiwa Adejobi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi. Ya ce rage wa jami'in girman muƙamin da aka yi, ya biyo bayan shari'ar da aka gudanar akansa da kuma bin tsarin doka kafin yanke masa hukuncin laifin da ya aikata. Ya ce jami'in ya aikata laifin yaɗa ayyukan ƙungiyar asiri da kuma saɓa dokar ƴan sanda ta amfani da kafafen sada zumunta na intanet. Wata kotu a Jihar Legas ta yanke wa wani ɗan shekara 73 hukuncin zaman gidan yari na shekara 24 kan laifin almundahana. Tun da farko hukumar EFCC da ke yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya ce ta gurfanar da shi a kotu kan zarge-zarge tara ciki har da batun bayar da cakin banki na bogi da satar miliyan 71. Ana zarginsa ne da damfarar wani kamfani mai suna Nepal Oil and Gas Services Limited a wani ciniki da ya shafi sayar da wani fili a Onitsha da ke Jihar Anambra." https://www.bbc.com/hausa/labarai-61771128 +business Me Kano za ta yi da tallafin Naira biliyan 10 na CBN? "Gwamnatin jihar Kano ta samu tallafin Naira biliyan 10 daga babban bankin kasar CBN don farfado da kamfanoni da masana'antun da annobar korona ta naƙasa a jihar. Darakta Janar ta hukumar lura da saka jari ta KanInvest a jihar, Hajiya Hama Ali Muhammad ce ta bayyana wa manema labarai haka a lokacin wani taron bita a kan shirin gudanar da wasu ayyukan jihar. Ta ce burin hakan shi ne a ga yadda za a farfado da kamfanonin da annobar ta shafa don bunkasa tattalin arzikin jihar. Tallafin kuɗaɗen sun shafi kamfanoni 50 da suka samu naƙasu sakamakon ɓarkewar annobar korona a ƙarƙashin ayyukan gwamnati na sake farfaɗo da masana'antu. Hajiya Hama ta ce CBN ɗin ya amince ya tallafa wa wannan shiri da ƙarin wasu kuɗaɗe idan buƙatar hakan ta taso nan gaba. ""Za mu zauna mu tattauna da kamfanonin ɗaya bayan ɗaya, ba wai a tare ba. Ta wannan hanya ce za mu tattara bayanai game da matsalolin kamfanonin don mu ga yadda za a tallafa musu.'' Hukumar ta KanInvest da 'yan jihar mazauna kasashen waje, tare da haɗin guiwar ƙungiyar masu sarrafa kayayyaki ta Najeriya MAN ne suka yanke shawarar ɓullowa da wannan shiri don tallafa wa masana'antun da annobar ta shafa. Hajiya Hama ta bayyana cewa hukumar ta samar da wani fom na nuna sha'awa ga kamfanonin, tare da sanar da cewa ranar 25 ga watan Fabrairun shekarar 2021 ne wa'adin mika fom ɗin zai zo ƙarshe. Ta kuma ƙara bayyana cewa ƙofa a buɗe take har ya zuwa lokacin da aka samu takardun neman guda 50. ""Ta nan ne za mu gano idan za su iya kashe Naira Biliyan 10 ɗin ko kuma akasin haka,"" a cewarta. Shugaban ƙungiyar masu masana'antu na Najeriya, Malam Ahmed Mansur ya yi kira ga gwamnatin jihar da sauran masu ruwa da tsaki da kada su yi ƙasa a gwuiwa wajen dawo da martabar jihar Kano da ta samu koma baya a ɓangaren harkokin ciniki da masana'antu. ""Wani bincike ya nuna cewa kusan kashi 50 bisa 100 na masana'antu a jihar Kano ko sun samu koma baya, ko kuma ma sun durƙushe baki ɗaya sakamakon annobar korona da sauran matsaloli,'' in ji shi. Ya kuma ce ''Don haka, akwai bukatar haɗin guiwa ta yadda za a sake farfaɗo da masana'antu a jihar Kano, wanda hakan zai samar da ayyukan yi ga matasa da dama a jihar, tare da haifar da wanzuwar zaman lafiya. Gwamnatin jihar Kano ta nuna jin daɗinta game da wannan yunkuri. Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatinsa ta sha ɓullo da tsare-tsare da nufin ɓunƙasa ƙananan masana'antu a jihar, sai dai ɓarkewar annobar korona a bara ta mayar da hannun agogo baya wajen cimma burin. Kano dai ta yi suna a matsayin babbar cibiyar kasuwanci a arewacin Najeriya." https://www.bbc.com/hausa/labarai-55721711 +business Adewale Wally Adeyemo: Ɗan Najeriyar da Biden ya bai wa mataimakin ma'ajin baitil malin Amurka "Wani lauya haifaffen Najeriya kuma tsohon babban mai bai wa shugaban Amurka Barack Obama shawara kan tattalin arzikin duniya, Adewale Adeyemo, zai zama sabon mataimakin ma'ajin baitil malin Amurka, a cewar kafofin yaɗa labaran ƙasar. Adeyemo zai yi aiki ne tare da Janet Yellen, bayan da zaɓaɓɓen Shugaba Joe Biden ya zaɓe su a matsayin ma'aji da mataimakin baitil malin ƙasar. Muƙamin Adeyemo na ɗaya daga cikin muƙaman da ake sa ran Biden zai sanar da su nan ba da jimawa ba. Wane ne Adewale Adeyemo? An haifi Adewale Adeyemo da aka fi sani da ""Wally"" a shekarar 1981 a Najeriya, amma ya girma a California. Ya yi karatunsa na digiri a Jami'ar California kafin daga bisani ya tafi makarantar Koyon Shari'a ta Yale. Kafin ya fara aiki a ƙarƙashin mulkin Oba,a, Adeyemo ya fara aiki ne a matsayin edita a a wani shirin bunƙasa tattalin arziƙi na Hamilton Project, sannan ya yi aiki a matsayin babban mai ba da shawara da kuma mataimakin shugaban ma'aikata na Jack Lew a baitil malin Amurka. Daga bisani ya yi aiki a matsayin mai sasantawa na yarjejeniyar kasuwanci ta ƙasasehn duniya 12 ta Trans-Pacific Partnership, sannan shi ne shugaban ma'aikata na farko a hukumar Consumer Financial Protection Bureau ƙarƙashin jagorancin Elizabeth Warren. A shekarar 2015, an naɗa shi a matsayin mataimakin mai ba da shawara kan tsaro na ƙasa a harkokin tattalin arzikin ƙasashen duniya da kuma mataimakin darakta na Cibiyar Tattalin Arziki ta ƙasa. Daga baya ya zama na farko da ya shugabanci gidauniyar Obama." https://www.bbc.com/hausa/labarai-55131256 +business Takaddama kan kogin Nilu: Amurka za ta zaftare $100m daga tallafin da take bai wa Habasha "Rahotanni na cewa Amurka na shirin zaftare Dala Miliyan 100, kwatankwacin sama da Naira Biliyan 30 daga tallafin da take bawa Habasha sakamakon takaddama a kan samar da katafariyar madatsar ruwa a kogin Nilu. Wata majiya daga gwamnatin kasar ta ce matakin na da alaka da gaban-kan da Habashan ta yi wajen soma makare madatsar ruwan tun kafin a kai ga cimma yarjejeniya da kasashen Masar da Sudan. Masar ta jima tana adawa da shirin, wanda da zai rage yawan ruwan da take samu. Ita kuwa Habasha ta jaddada cewa tana son samar da madatsar ruwan ne domin karfafa wutar lantarkinta. Da zarar an kammala aikin samar da madatsar ruwan, za ta kasance mafi girma da ke samar da wutar lantarki a Afrika, sannan za ta rika bawa al'ummar kasar Miliyan 65 wuta. Kudin da Amurkan ke shirin dakatar da bawa kasar na da nasaba da tallafin samar da abinci mai gina jiki, da tsaron yanki ko kan iyaka kamar yadda majiyar ta rawaito. Sannan wani bangaren kudin ya shafi wanda ake bayarwa da zummar yaki da cutar Sida ko Kanjamau ta HIV da matsalar kwararar 'yan cirani da 'yan gudun hijira. Wani jami'in ma'aikatar harkokin wajen kasar ya fada wa kamfanin dillacin labarai na Reuters cewa, matakin da Habasha ta dauka na fara makare madatsar ruwan yayin da take tsaka da tattaunawa da kasashen Masar da Sudan, ya janyo nakasu ga tattaunawar da ake yi, sannan ya saba da ka'idojin da aka shimfida Jakadan Habasha a Amurka ya shaida wa jaridar Financial Times cewa yana fatan Amurka za ta sauya tunaninta kan rage tallafin. Fitsum Arega ya ce, ""Mun nemi su sake tunani kuma muna jira. Muna fatan shekaru 117 na huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu ba za su tashi a banza ba"" in ji shi. Masu aiko da rahotanni sun ce da alama za a kalli lamarin a matsayin wani mataki da shugaban Amurka Donald Trump ya dauka na hukunta Habasha, bayan kasar ta ki amincewa da sasantawar da Amurka ta yi da Masar da Sudan. Tattaunawar ta tsaya kan batutuwa da dama da suka hada da bukatar da Masar da Sudan suka yi na cewa duk wata yarjejeniya ta kasance ta yi dai-dai da yadda za a gudanar da madatsar ruwan a lokutan fari. Yankin da za a samar da madatsar na da kusanci da Masar kuma iskar wurin na da karfin sarrafa kwararar ruwan da kasar ke samu. Kogin Nilu shi ne tushen ruwan sha da kuma noman rani ga kasar Masar. Manoman kasar na girbin alkama a wani kauye da ake kira Shamma a lardin al-Minufiyah, kusa da kogin na Nilu." https://www.bbc.com/hausa/labarai-54007493 +business Annobar korona da yakin Ukraine sun taɓarɓare zaman lafiyar duniya irinsa mafi muni cikin shekera 15 "Karo na 16 kenan da ake fitar da wannan rahoto na shekara-shekara kan zaman lafiya a duniya, wanda a wannan karon ya duba matsayin da ake, da kuma karuwar taɓarɓarewar zaman lafiyar duniya. Rahoton ya ce zaman lafiya ya sake dagulewa da kashi 0.3 cikin 100 a 2021. Kuma wannan shi ne karo na 11 da ake samun wannan yanayi na taɓarɓarewar zaman lafiya a cikin shekaru 15 da suka gabata, kodayake yanayin ya inganta a wasu ƙasashe 90, yayin da a ƙasashe 71 abubuwa sun sake muni. Iceland dai har yanzu ita ce kasa mafi zaman lafiya a duniya, matsayin da take rike da shi tun 2008, sai kuma New Zealand da ke bi mata da Ireland da Denmark da kuma Austria. A kuma shekaru biyar jere, Afghanista ita ce kasar da ta fi fuskantar rashin zaman lafiya, sannan Yemen ke bi mata, da kuma Syria da Rasha da Sudan ta Kudu. Kasashen 7 cikin 10 da ke sahun gaba a jadawali sun kasance na Turai, kuma Turkiyya ta kasance kasa daya tilo da ke shiga tsaka-tsakin kasashen Turan 10. Biyu daga cikin ƙasashe biyar da ke fama da rashin zaman lafiya mafi muni su ne Rasha da Ukraine, sai kuma Guinea, da Burkina Faso da Haiti. Dukkanin wadannan ƙasashe na cikin yanayi na taɓarɓarewar zaman lafiya saboda rikicin da suke fama da shi. Kasashe 23 da ke cikin wannan jadawali, yanayi mafi girma na taɓarɓarewar tsaro ana samun su ne tsakanin kasashen makwabta, rigingimun cikin gida da mulki, kwararan 'yan gudun hijira da raba mutane da muhallansu. Akwai rigingimu na siyasa da kuma dumukuradiyyar da ba ta tsaya da kafafuwarta ba. Ƙasashe 28 kididdiga ta nuna cewa suna cikin matsanancin tashin hankali, yayinda da 10 ke fama da rigingimu na siyasa. Ana ci gaba da samun karuwa kan rashin daidaito a duniya kan zaman lafiya. Tun 2008, kasashe 25 da ake ganin na fama da rashin zaman lafiya an sake samun karuwa da kashi 16 cikin 100, yayinda kasashe 25 mafi zaman lafiya suka sake inganta da kashi 5.1 cikin 100 tun 2008, an samu raguwa a kashe-kashen juna a kasashe 116. Asarar da aka tafka sakamakon rikici ya kassara tattalin arzikin duniya da dala tiriliyan 16.5 ko kashi 10.9 na ma'aunin tattalin arzikin duniya, wanda ana iya cewa kowanne mutum ya tafka asarar dala 2,117. Sannan kasashe 10 da rikici ya fi shafa, tasirin ga tattalin arzikinsu ya kai kashi 34 bisa ma'aunin tattalin arziki na GDP, idan aka kwatanta da kasi 3.6 cikin 100 a kasashen da zaman lafiya ke da sauki. Steve Killelea, na gidauniyar IEP ta zaman lafiya da tattalin arziki ya ce: ""A shekarar da ta gabata an yi gargadi kan koma bayan tattalin arziki saboda annobar korona. Yanzu suna fuskantar karanci a fanin shigar da kayayyaki, hauhawar farashi da karancin abinci da yankin Ukraine ke haifarwa. Tasirin hakan a siyasance da tattalin arziki zai dau tsawon shekara da shekaru. ""Idan aka hada wannan batu da matsalolin koma baya tsakanin kasashe makwabta, rashin tsaro da rigingimu cikin gida, gwamnataci da shugabanni da kungiyoyi dole su hada karfi wajen samar da zaman lafiya."" Kudaden da ake kashewa a fanin ayyukan soji ya ragu a kasashe 94, yayinda kasashe 112 suka rage jami'an sojoji tun daga 2008. Sai dai, yakin Ukraine da Rasha, da karuwar kudaden kashewa ayyukan soji tsakanin kasashen NATO ya kai kashi 2 cikin 100 a ma'aunin tattalin arziki na GDP, wannan na iya tabarbarewa a shekaru masu zuwa. Duk da wannan yanayi da ake ciki, China ta shirya kara yawan kudaden da take kashewa a fanin soji da kashi 7.1 cikin 100 a 2022. Kyakyawan fatan da ake yi wa makoma ya rubanya sau uku, yayinda mutane da dama ke ganin zasu iya samu rayuwa mafi inganci sama da ta 2019. Abin mamaki, kashi 20 cikin 100 na mutane ke ganin gwamnati na iya shawo kan bala'o'i. Duk da cewa ana jin tasirin yakin Rasha da Ukraine, yakin yayi mumunar tasiri ga kiddidigar duniya. Kasahen Turai da dama da ke kusa da Rasha sun fuskanci tabarbarewar alaka da makwabtansu, ciki akwai irinsu Finland, Sweden, Romania, Estonia, Latvia, Lithuania, da Moldova. Annobar korona ta jefa kasashe cikin matsalolin tattalin arziki da siyasa. Kasashen da ake ganin sun soma samun cigaba ta fanin zaman lafiya sun fuskanci zanga-zanga da rigingimu domin nuna adawa da yadda gwamnatoci suka rinka tunkarar annobar. Irin wadannan rigingimu sun karu da kashi 49 cikin 100 tun 2008, inda kasashe 126 cikin 163 kididdiga ke nuna sun fuskanci tabarbarewar. Wannan ya kasance ruwan dare, da aka ga tasirinsa a kowanne yanki na duniya ban da kalilan. Gabashin Asiya na daga cikin yankunan da aka samu karuwar rikici irinsu Indiya da Sri Lanka da Bangladesh da Pakistan da suka kai yanayi na kololuwa tun bayan soma wannan kiddidiga. A Turai, an yi ta samu zanga-zangar adawa da dokar kulle, musamman a kasashe irinsu, Belgium da Faransa da Netherlands da Austria da Croatia da Burtaniya, sai kuma Amurka ta Arewa. Rikicin da ake gani a duniya yanzu ya dagula zaman lafiya da kashi 9.3 cikin 100 idan aka kwatanta da shekarun baya tun 2008. Kasashen da ke fama da rikicin cikin gida sun karu daga 29 zuwa 38, amma kuma adadin mutanen da aka kashe a rikicin cikin gida ya ragu tun 2017. Adadin mutanen da suka rasa muhallansu a duniya ya karu daga miliyan 31 a 2008 zuwa miliyan 88 a 2022. Akwai kasashen duniya 17 da kashi 5 cikin 100 na al'ummarta na kasancewa 'yan gudun hijira ko sun rasa muhallansu. Sudan ta Kudu kusan kashi 35 cikin 100 na al'ummarta sun rasa matsugunai. Yayin da Somaliya da Afirka ta Tsakiya ke da mutane kashi 20 cikin 100 da suka rasa muhallansu." https://www.bbc.com/hausa/labarai-61798803 +business Yadda tsananin zafi ke naƙasa kananan sana'o'i a Indiya "A daidai lokacin da ake ci gaba da zabga zafi a Indiya, talakawan ƙasar da dama na cikin wani hali. Wakiliyar BBC Ayushi Shah ta haɗa wa BBC rahoto daga Mumbai. Sulachna Yevale mai sayar da kayan lambu, tana yawan zuba ruwa kan kayan lambunta da suka haɗa da lemon tsami da alayahu da take sawowa daga kasuwa domin guje wa bushewarsu. Sai dai duka waɗannan abubuwan ba su taimakawa. Tsananin zafin ya ja da dama daga cikin kayayyakin sun lalace wanda hakan ya sa ba za a iya sayar da su ba. Duk da cewa ta shafe shekaru da dama tana sayar da kayan lambu a wuri ɗaya, Ms Yevale ta bayyana cewa wannan ne karo na farko da ta yi asarar kayayyakinta da yawa - na kusan rupee 70, kusan dala ɗaya kenan - wanda wannan kuɗi ne mai yawa ga mutumin da ke rayuwa wanda abin da yake samu a matsayin riba a duk rana bai wuce rupee 800 ba. A daidai lokacin ribarta ke raguwa, ta damu matuƙa kan abin da zai faru a nan gaba. Ta dogara ne da sayar da kayan lambu domin ciyar da iyalinta, ciki har da matar ɗanta wanda ya rasu da kuma jikarta. ""Ina jin ba zan iya yin komai ba,"" in ji ta, a lokacin da take kuka. Zafi mai tsanani a halin yanzu ya takura wa rayuwar jama'a da dama a India waɗanda ke ta ƙoƙarin rayuwa a cikin zafin - wanda shi ne zafi mafi tsanani da aka yi a shekara 100. Bayan an shafe makonni ana irin wannan zafin, hukumar da ke kula da hasashen yanayi a arewa maso yammacin India ta bayyana cewa akwai alamun cewa za a samu sauƙi. Amma saukin da ake tunanin za a samu ana sa ran ba za a daɗe ba inda ake sa ran watakila a koma gidan jiya. Waɗanda ke shan wahala dai akasari talakawa ne - mutane kamar su Ms Yevale su ne irin wannan zafin ke wahalarwa sakamakon a halin yanzu suna neman yadda za su yi ne su rayu. Prameela Walikar, wadda wata mai sayar da kifi ce, tana goge zufar da ke fuskarta kuma ta bayyana cewa da ƙyar take adana kifin da take sawowa a duk rana sakamakon tsananin zafi. ""Akasarin ribar da nake samu ina kashe ta ne ta hanyar sayen ƙanƙara wadda za ta sanyaya kifi,"" in ji ta. "" Ban taɓa samun lalataccen kifi ba a tsawon shekarun da na ɗauka ina sayar da kifi. A yanzu wani lokacin ina asarar kimanin rupee 2,000 a rana. Har farashin ƙanƙara ya ƙaru inda ya ruɓanya wanda hakan na bai wa masu sana'o'i wahala. ""Akwai buƙatar gwamnati ta samar da kayayyakin aiki da kuma ƙanƙara domin taimaka wa masu sayar da kifi sakamakon zafin da ake ciki,"" in ji ta. Labarin waɗannan matan biyu yana haskaka rayuwar miliyoyin mutanen da ke rayuwa ko kuma cin abinci ta hanyar irin waɗannan sana'o'i. Sai dai a daidai lokacin da ake wannan zafi akai-akai, masana na cewa ayyuka kamar gine-gine da kuma noma za su iya zama ayyuka masu haɗari a lokacin irin wannan zafi. Wannan ba wai maganar lafiyar al'umma bace kawai, amma ga tattalin arziki sakamakon illar da zai yi wa ayyukan yi. A yanzu India na asarar dala biliyan 101 a duk shekara saboda zafi kamar yadda wani rahoto ya bayyana." https://www.bbc.com/hausa/labarai-61353580 +business Coronavirus a Najeriya: Yawancin jihohi 'ba za su iya biyan albashi a shekarar nan ba' Wani rahoton kungiyar kwararru kan tattalin arzikin Najeriya ya ce zai yi wahala yawancin jihohin kasar su iya biyan albashin ma'aikata a wannan shekara saboda rashin cimma bukatun Najeriya na kudaden shiga da ƙasar ta yi hasashe sakamakon tasirin annobar korona. Rahoton kungiyar Nigerian Economic summit group ya ce kasancewar Najeriya mai dogaro da arzikin mai, tana fuskantar manyan kalubale guda biyu na faduwar farashin mai da kuma tabarbarewar tattalin arzikin duniya da annobar korona ke ci gaba da yi wa illa. Binciken ya ce yadda jihohin Najeriya suka dogara da kason da suke samu daga gwamnatin tarayya da ke dogaro da arzikin fetir, hakan na nufin faduwar farashin mai zai sa jihohi su kasa biyan albashin ma'aikata. To sai dai kuma masana tattalin arziki na ganin akwai gyara a rahoton. Dr Muhammad Shamsuddeen, masani tattalin ariki ne a Najeriya ya kuma shaida wa BBC cewa akwai abubuwan da ya kamata ace an duba ba wai batun mai ba kawai. Ya ce da farko dai a cikin kasafin kudin 2020 da aka yi a Najeriya, an kiyasta cewa man fetur zai iya kawo naira tiliyan biyu da biliyan dari shida da arba'in. Masanin tattalin arzikin ya ce idan aka duba abin da man fetur din zai kawo bai kai kashi 30 cikin 100 na abin da gwamnatin kasar ke tunanin zata samu na kudi ba wanda ya haura naira tiliyan takwas. Ya ce, rasa abin da bai kai kashi talatin cikin 100 ba,ba lallai ya zama barazanar da har za a ce ba za a iya biyan albashi ba. Dr Muhammad Shamsudden, ya ce, ya kamata jihohi su rinka duba wadanne hanyoyi za su bi na habaka kudaden shiga da kuma rage dogaro da kudaden gwamnatin tarayya. Ya ce wani abu kuma shi ne yawan ciwo bashi ba shi da wani alfanu musamman a wannan yanayi da ake ciki na annoba wadda ta zamo ruwan dare gama duniya. https://www.bbc.com/hausa/labarai-52793880 +business Elon Musk: Abu biyar da suka kamata ku sani game da attajirin da ya fi kowa kuɗi a duniya "Attajirin nan Elon Musk, mai kamfanin Tesla da SpaceX ya zama na ɗaya cikin jerin attajiran duniya bayan hannun jarin kamfanin Tesla ya ƙaru a ranar Alhamis 7 ga watan Janairun 2021. Ya maye gurbin mai kamfanin Amazon Jeff Bezos, wanda ya fi kowa kudi a duniya tun 2017. Darajar kamfanin Tesla da ke ƙera motocin lataroni na Elon Musk ta ƙaru a bana, kuma darajarsa a kasuwa ta kai dala biliyan 700. Hakan ya sa kamfanin na motoci ya zarta Toyota da Volkswagen da Hyundai da GM da kuma Ford idan an hada su baki daya. Arzikin ɗan kasuwar mai shekara 49 ya ƙaru daga dala biliyan 127.9 zuwa dala biliyan 185 sakamakon haɓakar hannun jarin kamfanin Tesla, kamar yadda jaridar Bloomberg ta ruwaito. A shekarar 2020 kaɗai, dukiyar Musk ta ƙaru da dala biliyan 100.3, kuma babu wanda ya samu ƙaruwar dukiya kamar wannan a jerin masu kuɗin duniya guda 500 na jaridar ta Bloomberg. A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Tuwitta ya kuma bar shi daga sama-sama, mai kuɗin ya ce: ""Ina da niyyar amfani da rabin dukiyata wajen magance matsalolin da duniya ke fuskanta, sannan rabin kuma ina son samar da wani birni a duniyar Mars inda dukkan abubuwa masu rai za su iya ci gaba da rayuwa a can, ko da a ce wata rana duniyar Earth za ta ci karo da wani bala'i kamar na wasu manyan halittu irin su (dinosour) ko kuma Yaƙin Duniya Na III ta yadda za mu halaka kawunanmu."" Ga wasu abubuwa da suka kamata ku sani a game da shi: An haifi Elon Musk ranar 28 ga watan Yunin 1971 a Pretoria na Afirka ta Kudu. Tun yana yaro Musk yake yawaita tunane-tunane na ƙirƙirar abubuwa, abin da ta kai har sai da iyayensa da likitoci suka nemi a duba lafiyar kunnensa sakamakon rashin sauraron abubuwa. Bayan mahaifinsa ya rabu da mahaifiyarsa, Musk ya fara sha'awar na'urar kwamfuta. Ya koya wa kansa yadda ake ƙirƙirar shafin intanet yana shekara 10. Ya sayar da manhajar da ya ƙirƙira ta farko yana shekara 12. Ya kafa shafin X.com a 1999, wanda daga baya ya koma PayPal, sannan ya kafa SpaceX a 2002 da kuma Tesla Motors a 2003. Tun yana shekara 20 ya zama miloniya bayan ya sayar da wani kamfaninsa mai suna Zip2. A watan Janairun wannan shekara, Elon Musk yana matsayi na 35 ne a jerin masu arzikin duniya. Haɓakar dukiyar tasa ta faru ne akasari saboda kamfanin Tesla, wanda kimarsa ta kai kusan dala biliyan 500. Kusan uku cikin huɗu na dukiyar sun samu ne sakamakon hannayen jarin Tesla, wanda darajarsa ta haɓaka fiye da sau huɗu idan aka kwatanta da na kamfaninsa na Space Exploration Technologies Corp - wanda aka fi sani da SpaceX. Elon Musk na tsananin ƙaunar karanta litattafai a rayuwarsa. Lokacin da yake ɗan shekara tara da haihuwa, ya zama wani rumbun binciken ilimi kamar Encyclopaedia Britannica saboda yawaita bincike kan abubuwan da yake nema. Hatta a yanzu, idan zai ɗauki ma'aikaci a kamfaninsa sai ya tabbatar ya san kashi kaso mai yawa na ilimin mutum ta yadda ko da bai yi nasarar samun aikin ba, an ƙaru da iliminsa. A watan Mayun 2020 ne Musk ya ce ba zai sake mallakar wani matsuguni ba da sauran kayayyaki, inda ya saka gidajensa a kasuwa. An yi wa gidajensa biyu da ya saka a kasuwa farashin dala miliyan 40 - ɗaya daga ciki ya saye shi ne daga hannun tauraruwar fina-finai Gene Wilder a 2013. An yi wa gidan farashin dala miliyan tara da rabi, yayin da aka yi wa ɗayan farashin dala miliyan 30. Attajirin kan je aiki kamfaninsa kamar kowane ma'aikaci kuma har ma yakan kwana a can idan aiki ya yi masa yawa. Yakan kwana a kan kujera saɓanin katifa ko gado, duk da cewa zai iya yin hakan idan yana buƙata. Ya bayyana a wani littafinsa cewa yana iya sanin kaso mai yawa na ilimin mutum yayin da yake yi masa tambayoyin ɗaukar aiki a kamfaninsa ba don komai ba sai don gudun kar ma'aikacin ya gaza yin nasarar samun aikin." https://www.bbc.com/hausa/labarai-55061322 +business Jirgin tankar mai na Iran ya baro Gibraltar Kasar Gibraltar ta sako wani jirgin ruwan Iran mai jigilar mai wanda ta kama tun watan Yuli. Ta kama jirgin ne saboda ana tuhumar Iran da yi wa Syria jigilar mai wanda takunkmin karya tattalin arziki ya haramta haka. Bincike ya nuna cewa tankar man ta nusa gabas kan hanyarta ta shia tekun Bahar Rum, amma babu wanda ya san inda ta nufa. Kasar Gibraltar ta ki amincewa da wata bukatar da Amurka ta mika ma ta cewa ta ci gaba da tsare jirgin ruwan, wanda ya sauya sunansa daga Grace 1 zuwa Adrian Darya-1. Amurkar ta yi wannan kokarin ne ranar Jumma'a, kwana daya bayan Gibraltar ta sallami jirgin. Gibraltar ta kuma ce ba za ta iya sake tsare jirgin ba saboda takunkumin da Amurka ta sanya wa Syria ba su da tasiri a Tarayyar Turai. Iran ta sanar da cewa za ta aika da wasu jiragenta na yaki domin raka tankar ta Adrian Darya-1. https://www.bbc.com/hausa/labarai-49391558 +business Ƙalubalen da za a fuskanta idan tattalin arzikin Najeriya ya ci gaba da taɓarɓarewa "Masana tattalin arziki a Najeriya sun ce koma-bayan da tattalin arzikin ƙasar ya fada a cikin karo na biyu a shekara biyar bai zo musu da mamaki ba. Tattalin arziƙin Najeriya ya ragu da kashi 3.62 cikin 100 a tsakanin watan Yuli zuwa Satumban 2020, a cewar hukumar ƙididdiga ta ƙasar, National Bureau of Statistics (NBS). Ɗaya daga cikin masana tattalin arziƙi a Najeriya, Farfesa Mustafa Mukhtar, Malami a sashen nazarin harkar tattalin arzikin ƙasa na jami'ar Bayero ta Kano, ya shaida wa BBC cewa, ""wannan batu ba abin mamaki bane domin shi da ma tattalin arzikin ƙasa kamar igiyar ruwa ne, wata rana ya yi sama wata rana kuma ya yi ƙasa"" a cewarsa. Farfesan ya ce akwai matsalolin da suka janyo Najeriya ta sake faɗawa cikin matsalar tattalin arziki, ciki kuwa har da ɓurɓushin matsalar da cutar korona ta haifar wanda ya sa aka rufe wasu ɓangarori na tattalin arzikin ƙasa musamman harkar masana'antu a inda kasuwanci ya samu naƙasu. Masanin tattalin arzikin ya ce: ""Abu na biyu wanda yana daga cikin matsalolin da suka jefa tattalin arzikin Najeriya cikin mawuyacin yanayi shi ne matsalar da aka samu a ɓangaren sayar da man fetur a kasuwar duniya, inda farshin man ya ke kwan-gaba kwan-baya kuma har yanzu bai daidaita ba."" Ya ce sanin kowa ne tattalin arzikin Najeriya yawancinsa ya ta'allaƙa ne a kan farashi da kuma rarar kuɗi da ake samu idan an sayar da ɗanyen man fetir. Farfesa Mustapha ya ce: ""Faduwar farashin man fetir da aka samu a kasuwar duniya ta sa Najeriya ba ta samun kuɗaɗen shiga isassu wanda hakan ya janyo tattalin arzikin ƙasar ya ja baya"". Masanin tattalin arzikin ƙasar ya ce idan aka samu matsala a ɓangaren man fetur da masana'anta, to dole ne ɓangaren cinikayya da hada-hadar kuɗi da inshora da kuma harkar noma su samu naƙasu. Ya ce kasancewar duk wadannan ɓangarorin sun samu matsala shi ya sa tattalin arzikin Najeriya ma ya samu matsala. Farfesa Mustafa Mukhtar ya ce idan har aka ci gaba a haka, to ko shakka babu za a shiga mawuyacin yanayi musamman gwamnatin Najeriya da gwamnatocin jihohi da kuma na ƙananan hukumomi. Masanin tattalin arzikin ya ce ""gwamnatoci a matakan ukun ba za su iya taɓuka komai ba musamman waɗanda aka saka a cikin kasafin kuɗi, don haka dole sai a samo mafita idan an so komai ya tafi yadda ake so. Dangane da abubuwan da ya kamata ayi dan a fita daga wannan koma baya da tattalin arzikin Najeriya ya shiga, farfesan ya ce, dole ne sai gwamnatin tarayyar ta haɗa ƙarfi da ƙarfe da babban bankin ƙasa don a ƙara samar da ayyukan yi, a samar da jari, sannan a taimakawa ƙananan da manyan masana'antu, a bunƙasa harkar kasuwancin sannan kuma a samar da ababan more rayuwa. Ya ce kuma dole ne a bunƙasa harkar noma don abubuwa su tafi yadda ake so. Ƙarin bayani Bankin duniya ya ce wannan shi ne koma bayan tattalin arziki mafi muni da Najeriya ta tsinci kanta ciki a cikin shekara 36. Ƙasa dai na shiga karayar tattalin arziƙi idan adadin arziƙin da take samarwa a ƙasar ya ragu cikin wata shida a jere ba tare da ya farfaɗo ba. A daidai lokacin da Najeriyar ke ƙara shiga halin karayar tattalin arziƙi, darajar kuɗin Najeriya ta ƙara raguwa idan aka kwatanta da na sauran ƙasashe da ke gogayya da naira a kasuwannin duniya." https://www.bbc.com/hausa/labarai-55032467 +business Yadda hauhawar farashin kayan abinci take tasiri kan rayuwar 'yan Najeriya Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon: A wannan bidiyon, Madina Maishanu, ta yi mana nazari kan yadda hauhawar farashin kayan abinci take yin tasiri kan rayuwar 'yan Najeriya. Hakan na faruwa ne a yayin da Hukumar Kididdiga ta kasar ta ce an samu hauhawar farashin kayan abinci da kashi 20 cikin 100 a watan Afrilun 2021. https://www.bbc.com/hausa/media-57520376 +business Bidiyo: Bahaushiyar da ke sana'ar tuƙa Keke Napep a Kaduna Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon: Wata matashiyar Bahaushiya ta rungumi sana'ar tuka babur mai kafa uku domin neman abin kai wa bakin salati. Asiya, wadda ta shaida wa BBC hakan, ta yi kira ga mata matasa su kawar da girman kai sannan su rungumi sana'o'i domin bunkasa rayuwarsu. A cewarta, takan fito tun da sanyin safiya domin gudanar da sana'arta kuma tana samun abubuwan biyan bukata. Ta kara da cewa ba za ta daina wannan sana'a ba ko da ta yi aure. https://www.bbc.com/hausa/media-55049873 +business 'ISWAP ta kashe daya daga cikin ma'aikatan Action Against Hunger' "'Yan kungiyar IS da ke yankin Afirka ta yamma sun kashe daya daga cikin ma'aikatan jinkai guda shida na kungiyar Action Against Hunger da aka yi garkuwa da su a watan Yuli. Dan jarida a Najeriya, Ahmad Salkida wanda ya san yadda kungiyar ke gudanar da al'amuranta ne ya sanar da hakan a shafinsa na Twitter. Salkida ya ce ""an harbi ma'aikacin da bindiga a dab da dab a wani faifan bidiyo"" da shi ya samu gani. Ya kara da cewa kungiyar ta bayar da daililin kashe ma'aikacin ne saboda ""gwamnati ta yaudare su"" sakamakon watanni da aka kwashe ana tattaunawar sirri tsakanin tawagar masu sasantawa da kuma jami'an gwamnati. Sai dai kuma Salkidan bai yi bayani ba dangane da yadda ya samu faifan bidiyon ko kuma a wurin da aka kashe wannan mutum ba. Ahmed Salkida ya kuma wallafa a shafin nasa dai cewa kungiyar IS da ke yankin Afirka ta Yamma wato ISWAP din ""ta yi barazanar kashe sauran ma'aikatan na kungiyar Action Against Hunger guda biyar da suka rage."" Kungiyar ta Action Against Hunger ta tabbatar da batun kisan ma'aikacin nasu, a wata sanarwa da kungiyar ta fitar ranar Laraba. ""Mayakan da ke garkuwa da ma'aikacin Action Against Hunger da direbobi guda biyu da ma'aikatan ma'aikatar lafiya guda uku, sun kashe daya daga cikin wadanda suke garkuwar da su"". A ranar 19 ga watan Yulin 2019 ne dai 'yan kungiyar suka yi garkuwa da ma'aikatan agajin bayan 'yan kungiyar sun kai hari kan jerin gwanon motocin ma'aikatan agajin. Mako guda bayan yin garkuwa da ma'aikatan agajin, sun bayyana a wani faifan bidiyo inda alamu suka nuna lafiyarsu kalau. A makon da ya gabata rundunar sojin Najeriya ta rufe ofishin kungiyar Action Against Hunger bisa zargin tallafa wa mayakan Boko Haram da abinci da magunguna." https://www.bbc.com/hausa/labarai-49824999 +business Kudin kirifton da ba a bukatar makamashi mai yawa wajen tara shi "Kudin kirifto na biyu mafi girma, Etherium, yana shirin komawa wani sabon tsari da zai yi amfani da makamashi kasa da kashi daya cikin dari na wanda ake amfani da shi a yanzu. Tsarin, wanda ake kira The Merge, an yi shi ne don sauya wa masu korafi da ke ganin kudin kirifto na gurbata muhalli. Etherium na amfani da makamashi mai yawa a yanzu. Sauran kudaden kirifto da suka hada da Bitcoin, za su ci gaba da amfani da makamashi mai yawa. Vitalik Buterin, daya daga cikin wadanda suka kirkiro kudin kirifto, ya ce hadin na cikin wani bangare da Etherium ke shiryawa tun bayan kaddamar da kudin a 2014, amma an dage hakan lokuta da dama saboda wasu matsaloli. An kwatanta shi da kamar sake gina tubalin bene yayin da yake tsaye. Kudin kirifton na kuma tallafa wa wasu kudade har ma da daruruwan miliyoyin dala da kuma sulalla da sauran kudaden intanet na zamani. Idan wani abu na daban ya faru, hakan zai iya shafar kudin kirifto da manya da kuma kananan masu zuba jari a fadin duniya. Idan kuma tsarin da za a koma yayi kyau, kada masu amfani da kudin su lura da wani canji. “Abin farin-ciki ne da kuma babban ci gaba. Muna tunanin cewa da wuya abubuwa masu kyau har kashi 100, amma dai wannan hasashe ne,’’ a cewar wani mai bincike kan kudin kirifto, Justin Drake. “Muna da ababen more rayuwa a kasa, wadanda za su ba mu damar ci gaba ko da kuwa wasu cibiyoyin sadarwa sun samu matsala saboda wasu dailai.” Kwamfutoci sun riga sun fara aiki domin aiwatar da sabon tsarin. Ana kuma sa ran kammala shi nan da ranar Alhamis. Kudin kirifto na Etherium yana da fadin gaske, kuma ba za a iya canja bayanan ba wadanda kuma ke yin rajistar kowace mu’amala da masu amfani da shi ke gudanarwa. Zuwa yanzu, an sabunta shi, da kuma tabbatar da cewa an kiyaye ta hanyar amfani da masu aikin sa-kai a fadin duniya da kuma manyan kwamfutoci na zamani, wadanda za a bai wa ladan yin aikin da ba su sabbin tsabar kudi – tsarin da aka fi sani da mu’amalar kudin kirifto. Ana kiran wannan tsari da Hujjar yin aiki kuma yawancin sanannun kudaden intanet kamar Etherium da Bitcoin da Dogecoin da Litecoin. Kazalika, rage yawan makamashi na kudin kirifto yana rage adadin tsabar kudi da aka bayar a matsayin lada, kuma kudin na intanet ya ce hakan zai haifar da faduwar tsabar kudi da ke wanzuwa. Ba wai rage adadin kwamfutoci da ake bukata kawai hujja ta hannun jari ke yi, yana kuma rage karfin aiki na kwamfutcoi da ake bukata. Ana iya amfani da kwamfutcoin yau da kullum maimakon wadanda suke da tsada da kuma ke rike wuta da ke dauke da na’urorin sarrafa hoto. Yana da wuya a gane yawan makamashi da kudin Kirifto ke bukata kafin sarrafa shi a duniya. Gidauniyar kudin kirifto, ta ce Etherium na amfani da wutar lantarki mai yawa kamar Netherlands a watan Yuni. Gidauniyar ta kuma ce Hujjar hannun jari zai rage yawan amfani da makamashi daga sa’a 112 na Terrawatt a shekara zuwa 0.01. Sabon kiyasi da wata kungiya da ke binciken tattalin arzikin kudin digital, Digoconomist, ya nuna cewa an samu raguwar makamashi da ake amfani da shi a kudin kirifto, inda Etherium a yanzu ke amfani Terrawats 82 a shekara. Hadakar a yanzu zai sanya masu tara kudin kirifto daukar mataki mai wahala. Kudin kirifto kan fadi zuwa kasa, lokacin da darajar sulalla ya tashi, wanda kuma ke sanya tara kudin kirifto ya zamanto babu riba a ciki. Ana samun karuwar matsalar makamashi a sassan duniya da dama, wanda hakan ke rage riba da za a samu. A yanzu, masu tara kudin kirifto, za su nemi sabon hanyar samun kudi ko kuma sayar da kayakinsu. A wani kamfanin tara kudin kirifto a Dubai, jami’an kamfanin na zuba jarin dubban daloli domin maye gurbin kwamfutocin da ake amfani wajen samun Etherium da wasu sabbin kwamfutoci kuma masu tsada da ke tara kudin Bitcoin. ""Yana da wahala kwarai, saboda babu wata hujja da ta nuna cewa tsabar kudi sun fi cin kasuwa fiye da kirifto,’’ a cewar mai magana da yawun kamfanin, Ammar Lashkari. ""Za mu ajiye sauran kwamfutocin mu na kirifto, inda za mu nemi wata hanya ta fara tara sulalla, sai dai, ba zai zamanto iri daya ba, don haka ne ma za mu koma tara kudin Bitcoin.’’ A yankin Staffordshire da ke Birtaniya, Ash Andrews na fatan samun riba mai kyau ta hanyar tara tsabar kudi. ""Ina da shakkan hadakar. Lokaci mai kyau ne gare mu yanzu masu tara kudin kirifto, inda yanzu za mu sauya zuwa wani na’uin kudi. Akwai sauye-sauye da dama.’’ In ji Andrews." https://www.bbc.com/hausa/articles/c72z14jyq8eo +business 'Kudin fito ne dalilin tsadar motoci a Najeriya' Kungiyar masu sayar da motoci a Najeriya ta koka kan wani tsari da hukumar kwastam ta yi, na yi wa wasu motocin da ake shigarwa kasar kudin-goro, dangane da kudin-fiton da hukumar ke karba a kan su. Kungiyar ta ce gwamnati ta kayyade kudin fiton ne a kan motocin da ba su wuce shekara goma da kerawa ba, kenan haka za a biya ko da mota ta fi haka tsufa. Hukumar kwastan din tana karbar kudin fiton ne ta hanyar intanet da aka fi sani da e-valuation. Shugaban kungiyar masu sayar da motocin, Injiniya Prince Ajibola Adedoyin, ya shaida wa BBC cewa tsarin kudin fiton na cikin dalilan da suka sa motoci ke tsada, kuma sana`arsu na fuskantar barazana. “Mun san cewa idan aka yi wannan to za a samu matsala sosai, saboda sun ce shekara 10 da kera mota watau motoci da aka yi daga daga 2012 zuwa sama, su ne kadai zaa iya shigowa da su cikin kasar” in ji shi. Ya ce da farko hukumar kwastam ta sa kudi a kan sabbin motoci amma kungiyar ta ki amincewa da haka, amma a tattaunawar da suka yi da jami'an kwastam daga bisani sun fada musu cewa za su yi la'akari da shekarar mota. Sai dai kungiyar ta ce tun a wannan lokaci sun fada musu cewa za a samu matsala idan suka yi haka, a cewar Prince Ajibola. A yanzu kungiyar masu sayar da motocin ta ce hukumar Kwastan ta fada musu cewa za ta yarda su shigo da motocin da suka fi wadannan tsufa, amma za su biya kudi iri daya da na wadanda aka yi daga 2012 zuwa sama. “Ka ga yanzu za ka sayi mota misali miliyan daya amma za su sa ka biya duti na miliyan biyu, to ka gani ta ya mutane za su iya sayen wannan mota? shi yasa kudin motoci ya hau sosai”, in ji Prince Ajibola Kungiyar ta ce matsalar za ta sa masu sayar da motoci su rika zuwa wasu kasashe domin su sayar da motocinsu, kuma wannan na nufin cewa gwamnatin tarayya za ta samu raguwa a yawan kudaden shiga, tare da haifar da matsalar shigo da motoci ta haramtacciyar hanya. Shugaban kungiyar ya ce duk da cewa tashin farashin dala na tasiri a kan matsalar, amma kudin dutin da zasu biya shi ne ya fi tasiri. Kazalika kungiyar ta nuna fargabar cewa tsarin kan iya sa wasu mamboninta su rasa ayukkan yi, idan ba a dauki mataki ba Ta ce ta na da mambobi sama da miliyan uku masu sayar da motoci a cikin Najeriya. https://www.bbc.com/hausa/articles/c4ne3r75njyo +business Nigeria Youth Investment Fund: CBN ya fitar da tsarin shirin Buhari na raya matasa na biliyan 75 Babban Bankin Najeriya ya fitar da tsarin yadda za a tallafa wa matasa da jari karkashin shirin gwamnatin tarayya da ta ware naira biliyan 75 domin tallafa wa matasan. Babban Bankin ya fara fitar da kason farko naira biliyan 12.5 daga cikin kuɗin domin bunƙasa matasa. Sannan CBN ya bayyana ƙaramin bankin NIRSAL da ke ƙarƙashinsa a matsayin wanda zai tafiyar da shirin. Gwamnati ta ce shirin ya shafi samar wa matasa 500,000 ayyukan yi waɗanda za su amfana da shirin duk shekara tsakanin 2020 zuwa 2023. Tsarin ya shafi matasa ƴan tsakanin shekaru 18 zuwa 35 da gwamnati za ta tallafawa waɗanda ke da tunani na kasuwanci CBN ya bayyana a shafinsa na intanet cewa tsarin tallafin zai dogara ne a tsarin kasuwancin mutum, inda zai iya samu bashin naira 250,000 na jari. Tallafin Covid-19: Ana buɗe wa ƙananan ƴan kasuwa kamfani kyauta don samun tallafin Buhari Ga abubuwa uku da suka kamata ku sani game da tallafin da kuma yadda za ku tura buƙatarku: A bayanan da gwamnati ta fitar ta ce sai ƴan tsakanin shekara 18 zuwa 35 da suke da tunani na kasuwanci kuma suke buƙatar tallafin kuɗi ne za su iya neman wannan tallafi. Tallafin kuɗin ya shafi zuba jari ga tunanin matasa na kasuwanci da basirar da suke da ita. Gwamnati ta yi imanin cewa za ta sauya tunanin matasan su koma dogaro da kansu ta yadda za su taimaka wa ci gaban ƙasa. Shirin na tsawon shekara uku ne. Mai taimaka wa shugaban ƙasa kan kafofin sadarwa na intanet, Lauretta Onochie, ta bayyana cewa matasan da ke son tura buƙatarsu za su shiga wannan shafin, a nan Amma kafin cike fom ɗin tura buƙata, dole sai mutum ya tabbata yana da lambobin banki na BVN. Gwamnati za ta saki naira biliyan 25 duk shekara har shekara uku da za a kammala shirin. Shirin na gwamnatin Buhari domin magance matsalar rashin ayyukan yi ga matasa, shiri ne mai ɗorewa. https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-54735518 +business Coronavirus: Jihohi a Amurka sun fara bude harkokin kasuwanci Jihohi a Amurka sun fara bai wa wuraren kasuwanci damar budewa bayan dokokin da aka saka na dakile yaduwar cutar korona, yayin da wadanda suka mutu a kasar suka kai 51,000. Shagunan gyaran gashi da na gyran jiki za su iya budewa a Jihar Georgia da Oklahoma, inda ita kuma Alaska ta dage wa wuraren cin abinci takunkumi. A ranar Juma'a ne Shugaba Trump ya fice daga dakin taron manema labarai a lokacin da ba a saba gani ba, inda ya ki amsa tambayoyin 'yan jarida. Shugaban ya sha suka bayan ya nuna cewa yi wa mutane allura da sinadarin wanke datti wato disinfectant zai iya taimakawa wurin maganin cutar. Likitoci da masu kamfanonin samar da sinadarin sun yi watsi da kalaman nasa da cewa sinadarin yana da guba idan ya shiga cikin mutum, sannan idan ya taba jikin mutum zai iya yin illa ga fata da idanu da kuma huhu. Sai dai a ranar Juma'a ya ce kalaman nasa, wadanda ya yi a ranar Alhamis, na ba'a ne kuma an yi masa gurguwar fahimta ne. Kwastomomin da za su je shagunan kasuwancin ana sa ran za su ci gaba da bin shawarwarin bayar da tazara. Amma wasu yankunan sun zabi su ci gaba da zama a cikin kulle. https://www.bbc.com/hausa/labarai-52423913 +business Abin da 'yan Najeriya ke cewa kan dimbin bashin da ke kan kasar "Sanarwar da gwamnatin Najeriya ta bayar a wannan makon cewa za ta karbo karin bashin naira tiriliyan 11 domin tafiyar da kasafin kudin 2023 ta janyo muhawara a kasar. Dokar harkokin karbar bashi ta nuna cewa karin bashin da Najeriya za ta karbo ya zarta adadin kudin da aka amince ta ranto. Ministar harkokin Kudi da Tsare-Tsare, Zainab Ahmed wadda ta sanar da karbo bashin, ta ce za a karbo bashin ne daga cikin gida da kuma kasashen duniya. Bayanai daga ofishin da ke da ke kula da bashi da lamuni na Najeriya sun nuna cewa ya zuwa ranar 31 ga watan Maris na shekarar 2022 jimillar bashin da ake bin kasar ya kai $100bn, kwatankwacin naira tiriliyan 42. Kididdiga ta nuna cewa bashin da kasar ta karbo daga kasashen waje ya kai dala biliyan $40, kwatankwacin naira tiriliyan 17. Kazalika ta karbi bashin biliyan $60, kwatankwacin naira tiriliyan 25 a cikin gida - wanda ya kunshi gwamnatin tarayya da gwanatocin jihohi da babban birnin tarayya. Batun dai ya raba kawunan 'yan Najeriya, inda wasu ke cewa babu laifi idan kasar ta karbo bashin muddin za ta yi amfani da shi wajen harkokin gina kasa. Sai dai wasu na ganin karbo bashin a matsayin kara jefa kasar cikin kangin bashi da tsadar rayuwa, suna masu cewa duk da basukan da ta karbo a baya 'yan kasar na kara fadawa cikin mawuyacin hali. Ƴan Najeriya musamman masu bibiyar shafin Twitter da Facebook na BBC Hausa sun rika tsokaci da tafka mahawara game da batun yawan bashin da ake bin ta. Wani mai binmu a shafin Facebook, Abu Abdurrahman, ya ce: ""Lallai talaka zai sha matsa irin ta mai a jikin gyada. Allah ya sa mu wanye lafiya, domin wannan bashin duk a jikin talaka za a matso kudaden su fito ta hanyar tsadar kayan masarufi da kayan ayyukan yau da kullum."" Wani mai bin shafinmu na Twitter, Murtala Gaya ya ce: ""Bashi hanji ne. Wanda ake bin Amurka ya ninka na Najeriya. Don haka ko yanzu ta kama a karo bashi Baba [Buhari]."" Ita ma Husna Abdul cewa ta yi: ""Ba gwamnatin da ba ta cin bashi, kuma al'umma ake yi wa ayyukan raya kasa."" Amma Ayshatt Abubakar cewa ta yi: ""Allah ya kyauta, bashi kam ya kai bashi da ma bashi yana hana abu ya ci gaba, ga mu nan sai jin jiki muke."" Murtala MG ya ce: ""Babu matsala, ai bashi hanji ne yana cikin kowa. Da sannu za mu biya; kawai abin tambaya shi ne yaya aka kashe kudin?"" A nasa bangaren, Abdukadir Magaji Narimi, ya ce: ""Wannan babban abin takaici ne - mafi takaici ma shi ne daga cikin bashin talaka bai amfana da komai ba."" Ali Adamu ya ce duk da bashin da kasar take ciyowa ""babu wutar lantarki, babu hanyoyi masu kyau, babu ingantaccen kiwon lafiya, kungiyar malaman jami'a tana yajin aiki...a ina ake kashe kudin da ake karbowa bashi?""" https://www.bbc.com/hausa/articles/c06gvxjexz5o +business Mai kudin duniya Jeff Bezos: Abu biyar game da attajirin da ya fi kowa kudi a duniya "An kiyasta kudin Mista Bezos ya kai $200bn, bayan da ya karu cikin watannin farko na wannan shekarar yayin da annobar korona ke kara yaduwa a duniya. Yana cikin mutanen da ke da yakinin kai dan Adam zuwa wasu duniyoyi da sararin samaniya daga doron kasa ta hanyar rokokin da yake kerawa. Ga abubuwa biyar game da attajiri Jeff Bezos. Yaro mai hazaka Tun yana dan shekara biyar, attajiri Jeff Bezos ya fara nuna hazakarsa. Cikin abubuwan ban mamaki da ya yi shi ne kwance wani gadon kananan yara da iyayensa suka sayo masa domin ya mayar da shi tamkar gado irin na manya. Tun yana karami ya fara kwance-kwance da hade-haden na'urorin gidansu. A misali ya hada wata kararrawa mai amfani da lantarki wadda ya rika amfani da ita domin ta sanar da shi duk lokacin da kannensa suka shiga dakinsa. Wani abin da ya ce ba zai manta da shi ba shi ne yadda ya sanar da wata innarsa yawan shekarun da ta rage daga yawan shekaru rayuwarta saboda tana shan taba. Wannan ya zama masa abin damuwa daga baya saboda yadda ya sanya innar tasa ta fashe da kuka. Bezos ya ce kakansa ya ja shi gefe guda inda ya gaya masa cewa, ""Wata rana za ka gane cewa ba ko yaushe ne ya dace ka nuna wayonka ba."" Masu neman aiki a kamfanin Amazon na fuskantar kalubale iri-iri. Tun farko Mista Bezos kan nemi masu neman aiki a kamfanin nawa suka samu a jarabawar da aka yi musu. Bayan sun sanar da shi, sai ya koma ya kara wa jarabwar wahala domin wadanda suka fi masu neman aikin na farko ne kawai za su tsallake siratsin da ya gindaya musu. Da ya ga masu hazaka na karuwa a kamfanin, sai ya rika sallamar duk wadanda ba su yi kokari sosai ba a jarabawar kama aiki da kamfanin. A cikin kamfanin na Amazon, ma'aikata sun sha koka wa da yadda ake musu kiddidigan mintunan da suka dauka na zagayawa bayan gida. Akwai kuma wasu na'urori da ke auna yawan aikin da kowane ma'aikaci ya yi a tsawon yini. Aiki a kamfanin Amazon sai jajirtacce Tun kafin ya zama shahararren attaijiri, Mista Bezos ya kasance mai tafiyar da harkokinsa ta wata hanya da sauran mutane suka dauka ba daidai ba ce. A shekara ta 1994 ya bude shagonsa na farko inda ya rika sayar da littatafai a garejin ajiye mota na gidansu. Tun ba a je ko ina ba, Bezos ya rika sanar da wadanda suka zuba jarinsu cikin kamfanin nasa cewa cikin kashi 70 cikin 100 kamfanin na iya rugujewa kuma sun yi asarar dukkan jarin nasu kenan. Tun wancan lokacin ya fitar da wasu tsare-tsare da yake bi wajen tafiyar da harkokin kasuwancinsa. A misali, yafi son a rubuto masa doguwar takarda cike da bayanai a lokacin da yake ganawa da ma'aikatansa. Yana da wata dabi'a kuma da yake kira ""maitar kula da kwastomominsa"". A sane yake cewa duk wanda ke da wani korafi kan wani abu da kamfanonin Bezos suka yi na iya aika masa da sakon imel kai tsaye. ""Adireshin imel dina shi ne jeff@bezos.com, sananne ne, kuma ban taba boye shi ba."" Idan Bezos ya ga korafin da wani ya aiko masa, ya kan tura imel din ga wani daga cikin ma'aikatansa, inda a ciki ya kan rubuta alamar tambaya ne kawai. Ma'anar haka ita ce ma'aikacin ya ajiye komai a gefe domin mayar da hankali kan warware matsalar da ke cikin imel din. A shekarar 2018, Shugaba Trump na Amurka ya zargi Jeff Bezos da aikata laifuka kamar kaucewa biyan haraji da kokarin korar kishiyoyinsa ƴan kasuwa. Sukar ta Mista Trump ta sa hannayen jarin kamfanin ya fadi da kimanin kashi 9 cikin 100, inda yawan kudinsa kuma ya ragu da kimanin dala biliyan 10, amma daga baya ya mayar da kudin. Sanata Bernie Sanders ma ya dauki mataki kansa, inda ya jagoranci kafa wata doka a majalisar Amurka mai suna ""Dokar A Dakatar da Bezos"". Sanata Sanders ya soki yadda Mista Bezos ke tafiyar da harkokinsa na kasuwanci, har yana cewa ma'aikatan Amazon na talaucewa don tsabar neman riba. A sanadiyyar wannan sukar Mista Bezos ya kara yawan albashin da yake biyan ma'aikatansa zuwa dala 15 a kowace sa'a. Bezos na zuba dala biliyan daya a kowace shekara cikin kamfaninsa na Blue Origin da ke shirin fara jigilar mutane da na'urori zuwa sararin samaniya har ma da wasu duniyoyin. Ya ce, ""Wannan ne aiki mafi muhimmanci da nake yi a rayuwata. Ina dan shekara biyar da haihuwa Neil Armstrong ya sauka adoron duniyar wata, kuma tun lokacin na kallafa a zuciyata cewa sai na binciki sararin samaniya har ma in tafi can."" Tun Bezos na makarantar sakandare ya fara tunanin yadda zai kawo sauyi ga rayuwar dan Adam a wannan duniyar da ma sauran duniyoyin da ke kusa da ta mu." https://www.bbc.com/hausa/labarai-53335969 +business NBS: Jihohin da kayan abinci suka fi tsada a Najeriya "Hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya bambanta tsakanin jihohin ƙasar kamar yadda rahoton hukumar ƙididdiga ta kasar ya nuna. Rahoton na hukumar ƙididdigar ta Najeriya wato NBS ya ce an samu hauhauwar farashin da ya kai kashi 17.33 cikin ɗari a watan Fabrairun da ya wuce. Alƙaluman sun nuna cewa tashin farashin ya ƙaru ne da kashi 1.54 a Fabrairun 2021 idan aka kwatanta da kashi 1.49 a watan Janairu. Kuma farashin kayan abinci ya tashi da kashi 21.79 a Fabrairun da ya gabata idan aka kwatanta da kashi 20.57 a watan Janairu. Hukumar ta ce wannan ne karon farko da aka samu irin wannan tashin farashi a cikin shekaru hudu da suka wuce. Alƙaluman hukumar sun nuna farshin kayan abinci ya yi tashin gwauron-zabo a makwanni biyun da suka wuce lokacin da kungiyar fataken dabbobi da kayan abinci da ƴaƴanta suka yi yaji inda har ta kai ga sun datse hanyar kai kayayyaki daga yankin arewacin Najeriya zuwa kudanci. Rahoton ya nuna cewa tashin farashin kayan abinci ya shafi kayan abinci irin su burodi da nama da kifi da dankali da kuma farashin kayan miya da na kayan marmari ko kayan lambu. Alƙaluman hukumar sun ce a ma'aunin shekara shekara, jihar Kogi aka fi samun hauhawar farashin kayan abinci da kashi 30.47. Sai jihar Ebonyi da kashi 25.73 da kuma jihar Sokoto da kashi 25.68. Rahoton ya ce jihohin da farashin kayan abincin bai tashi ba sosai sun haɗa da Gombe da ke da kashi 19.32 da Bauchi da ke da kashi 18.74 da kuma Akwa Ibom da ke da kashi 18.70. Haka ma a maunin wata-wata, rahoton ya ce jihar Kogi ce aka fi samun hauhawar farashin kayan abinci tsakanin Janairu zuwa Fabrairu da kashi 3.34. Sai jihar Ondo kashi 3.33 da Ebonyi kashi 3.26. Jihohin da farashin kayan abincin bai tashi ba a wata-wata sun haɗa da Benue da Neja da ke da kashi 0.90 sai Kano mai kashi 0.70 da Oyo mai kashi 0.09 Me ya janyo hauhawar farashin? Masana na ganin dalilai da yawa ne suka janyo hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya kasar da tattalin arzikinta ke dogaro da arzikin fetir. Shuaibu Idris Mikati masanin tattalin arziki a Najeriya ya ce an samu hauhawar farashi saboda yawancin abubuwan da ake amfani da su shigowa da su ake yi a ƙasar. Sannan kuma dole idan canjin kuɗi ya karu kamar darajar naira ta yi ƙasa farashin kayayyaki dole ya ƙaru. ""An samu hauhawar farashi saboda yanayin canji a Najeriya,"" in ji shi. Haka kuma masanin na ganin tanzomar EndSars ta kara haifar da tsadar kayayyaki da kuma yajin aikin masu dakon kaya daga yankin arewaci zuwa kudancin Najeriya. Masanin ya bayyana cewa yajin da masu fataucin suka yi ya nuna yadda ɓangarorin Najeriya suke dogaro da juna ta fuskar tattalin arziki: Rahoton hukumar ƙididdigar na zuwa a yayin da ake fama da wata taƙaddama kan ƙarin farashin mai a Najeriya, bayan hukumar da ke kula da farashin mai ta kasar ta fitar da wata sanarwa da ta nuna farashin litar man fetur zai hau zuwa fiye da naira dari biyu. Ko da yake daga baya ta janye sanarwar. Ana ganin rudanin ya haddasa ƙarin farashin kayan masarufi a Najeriya inda mafi yawanci farashin fetir ke tasiri ga farashin kayayyaki a ƙasar. Kuma masana na ganin sai gwamnati ta ɗauki matakan gaggawa don magance yiwuwar dorewar wannan yanayi na tsadar rayuwa." https://www.bbc.com/hausa/labarai-56420512 +business Gwamnan Jihar Imo ya biya manoma albasa diyyar naira miliyan 10 "Kungiyar manoman albasa ta Najeriya tabbatar da cewa Gwamnan Jihar Imo da ke kudancin Najeriya Hope Uzodinma, ya biya wasu daga cikin ƴaƴan ƙungiyar naira miliyan goma diyya biyo bayan asarar da suka tafka a bara. Manoman sun tafka asarar ne lokacin da wasu 'yan bindiga suka kai masu hari a kasuwar sayar da albasa da ke Ƙaramar Hukumar Ahiazu Mbaise da ke Jihar Imo. Haka zalika an bayyana cewa gwamnan ya kuma bai wa masu sayar da shanu da lamarin ya shafa naira miliyan 20 a matsayin diyya. Halilu Muhammed, wanda shi ne shugaban kungiyar ta masu nomawa da sarrafa albasa reshen Jihar Imo, ya shaida wa BBC cewa asarar da manoman suka tafka ta wuce ta miliyan goma, inda ya ce ta kai ta sama da miliyan 13 amma a cewarsa gwamnan ya ce ""ba za a yi ɓari a kwashe duka ba"". Halilu Muhammad ya ce a halin yanzu miliyan goman da suka samu, tuni shugaban ƙungiyar manoma albasa ta Najeriya baki ɗaya Aliyu Maitasamu Isa ya kasafta su inda ya bai wa waɗanda lamarin ya shafa. ""Duk mai buhu ɗaya ya samu kuɗinshi, an kira mutanen Sokoto an tabbatar wa kowa an ba shi kuɗinshi, in ji Halilu. Haka kuma ya ce gwamnan jihar ya ba su tabbacin cewa irin haka ba za ta sake faruwa ba inda ya ce tun bayan iftila'in da ya faru da su, gwamnan ya ƙara tsaurara tsaro a wuraren da suke sana'ar tasu. Haka kuma ya ce duk da haɗurra da sukan faɗa ciki sanadiyyar hare-haren ƙungiyoyin ƴan bindiga, ƙungiyar tasu za ta ci gaba da kai hajarta zuwa kudancin kasar." https://www.bbc.com/hausa/articles/c1vgge2v4eeo +business Abubuwan karfafa gwiwa da suka faru a Afirka a 2019 "Jajircewa ita ce ta bai wa mutane da dama kwarin gwiwa a wannan shekarar a Afirka. Mun sake waiwaye kan rayuwar jajirtaccen malamin makaranta, da dalibi da lauya, wadanda suka yi amfani d basira wajen karfafa giwar al'uma a shekarar 2019. 1. 'Matasa suna da amfani sosai' Brother Peter Tabichi Ba karamin alfahari ya yi ba a lokacin da dalibansa suka daga shi sama, an yi wa Brother Peter Tabichi gagarumar tarba a kasar Kenya a lokacin da ya dawo daga Hadaddiyar Daular Larabawa, Dubai, inda ya karbo lambar yabo ta zinare a matsayin jajirtaccen malami na duniya. A watan Mayu ne dai aka ayyana shi a wannan matsayi, bayan alkalai sun tantance, sun kuma yi tankade da rairaya tsakaninsa da sauran malamai kuma shaidar da dalibansa suka yi ce ta kawo shi matsayin. A hirar da Brother Tabichi ya yi da BBC kan lambar yabon ya ce: ""A bayyane take karara matasan Afurka na da bai wa da za su iya sauya duniya.'' Wannan abu ya karfafa wa mutane da yawa gwiwa, ya kuma nuna malami yana taka muhimmiyar rawa wurin sauya rayuwar al'umma ta hanayar ilimantar da su. Har wa yau, Brother Tabichi yana kokarin karfafa wa dalibansa gwiwa, musamman mata da cusa masu kaunar ilimin kimiyya. 2. Sabuwar uwa, ta kammala makaranta Almaz Derese Alamu sun nuna babu abin da zai hana Almaz Derese mai shekara 21 'yar kasar Habasha zana jarabawar makarantar sakandare. A watan Yuni ne, ta fara nakuda sa'a daya gabannin fara jarrabawa. Ta haifi sankaceciyar 'yarta mai suna Yididiya kuma bayan minti 30 da haihuwar tata ta fara rubuta jarrabawar. ""Saboda zakuwar da na yi na zana jarrabawata, sam ban ji zafin nakuda ba,'' inji Mis Almaz a hirarta da BBC Afaan Oromoo. Mijinta, Tadese Tulu, ya kai ruwa rana da hukumomin makarantar domin su bar maidakinsa ta rubuta jarabawa a gadon asibiti. A watan Yuni, ne Mis Almaz ta samu labarin ta samu maki 75 cikin 100 na jarrabawar da ta zana. Almaz ta ce ba ta taba zaton za ta samu kyakkyawan sakamako kamar haka ba, saboda tana fama da ciwon ciki, ga kuma gajiya da ta yi saboda ba ta jima da haihuwa ba. ""Ba na iya bacci da daddare a lokacin da nake da cikin, sai na ke amfani da lokacin na yi karatu.'' Ta shaida wa BBC nasarar da ta samu na nufin za ta ci gaba da karatu nan da shekara biyu idan ta kammala sakandare, sai ta wuce har matakin jami'a. Mafarkinta shi ne zama cikakkiyar injiniya. 3. 'Yadda za ka yi zarra' Jordan Kinyera Jajircewa, da hazakar karatu a shekarar 2019 ita ce ta shekara ta musamman ga lauya Jordan Kinyera dan kasar Uganda. A shekarar 1996 Kinyera yana gani aka kwace wa mahaifinsa kadarorinsa a rikicin kwace filaye a shekarar. Shekara 23 bayan nan babbar kotun kasar ta yanke hukuncin da ya bai wa iyalansa nasara a shari'ar da ka dade ana yi. ''Mahaifina ya yi ritaya, don haka ba shi da kudi sosai,'' inji Mista Kinyera a hirarsa da BBC a watan Afirilu a lokacin da yake magana kan gagwarmayar da ya sha. Abin takaicin shi ne shari'ar ta dauki lokaci kuma hakan ya sa mahaifin Kinyera bai mori komai ba. Tsohon mai shekara 82, yana fama da ciwon mantuwa, ''a kodayaushe sai mun tuna masa wani abu da ya faru,'' inji Kinyera. Matashin lauyan yana yi wa jama'a shela musmman wadanda suke da matsalar fili kamar mahifinsa. Jajircewr da ya yi, da wallafa labarinsa da sashsen BBC Africa ya yi a shafin sada zumunta na Facebook ya ja hankalin jama'a sosai. 4. 'Jakadan Afirka abin alfahari' Ndlovu Youth Choir ""Wannan shekara ta kasance ta musamman cike da nasara,"" inji mai gabatar da shirin South Africa's Ndlovu Youth Choir, Ralf Schmitt, da ake yi na mawaka. Abubuwa sun sauya matuka, a lokacin da kungiyar matasan mawakan daga wani kauye da marasa galihu ke rayuwa ta shiga gasar talabijin ta America's Got Talent da ake yi a Amurka. Mawakan sun yi nasarar kai wa zagaye na karshe a gasar a watan Satumba. Kafin nan kusan daukacin 'yan Afirka ta Kudu sun mara masu baya. Mawakan sun rera wata tsohuwar waka ta Afirka wadda ta yi tashe a Amurka a shekarar 1980 mai salon wakar Toto, alkalai da 'yan kallo baki daya sun tsuma. Kungiyarsu ta wallafa a shafin twitter ''A daren nan muna alfahari da ku jakadun daukacin Afirka.'' 5. 'Ni dan aike ne' Alfred Brownell ""Ni dan aike ne, wadanda suka yi nasara su ne al'umma,'' lauya kuma mai fafutika dan kasar Liberiya Alfred Brownell, shi ne ya shaida wa BBC haka a watan Afirilu, bayan ya yi nasarar daukar kyauta ta musamman kan muhalli. An bai wa Mista Brownell kyautar ne saboda aikin da yake yi tukuru da ya tserar da dajin da ya kai girman eka 500,000 daga lalacewa a kasar Liberiya. Mista Brownell ya yi aiki kafada da kafada da shugabannin yankin, sun hana kamfanin yin manja na Golden Veroleum Liberia gudanar da aiki a dajin. Saboda aikin da ya yi, babban kamfanin da ke sa ido na samar da manja mai kyau mai suna Sustainable Palm Oil, ya dakatar da aikin tare da bukatar kamfanin GVL Freezing su dakatar da aikin cire bishiyoyin kwakwar manja, da kuma dakatar da aiki a wajen a nan gaba. ""Lokaci ya yi da ya kamata a hada kai, kama daga kamfanonin manja, da masu zuba jari don su fara yin wasu ayyuka da al'ummomin yankin za su ci gajiyarsu, da ba su kariya da sama masu aikin yi,'' inji Brownell a hirarsa da shirin radiyo na BBC Newsday ." https://www.bbc.com/hausa/labarai-50917697 +business Matakan kare kai daga haduran ababen hawa a Najeriya Dauda Ali Biu, muƙaddashin shugaban hukuma kiyaye aukuwar haɗura ta Najeriya, ya yi bayani game da tsare-tsaren hukumarsa game da yadda za su tunkari lokutan bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara. Ya ce hukumar ta fito da ƙarfinta da kayan aikinta ciki har da motoci da babura da motar bayar da taimakon gaggawa domin tunkarar wannan lokaci . Ya ƙara da cewa hukumar na da jumullar ma'aikata dubu 25, tare da ma'aikatan sa-kai 11,000, waɗanda a cewarsa duka hukumar ta tura su kan titunan ƙasar domin kiyaye aukuwar haɗura a lokutan bukukuwan na Kirsimeti da sabuwar shekara. Muƙaddashin shugaban hukumar ya kuma gargaɗi direbobi da su guje wa gudun wuce sa'a a kan titunan a lokutan bukukuwan, tare da kula da lafiyar ababen hawansu. https://www.bbc.com/hausa/articles/c2ev36275ylo +business Ƙa'idar cire kudin CBN ta raba kan majalisar dattawan Najeriya Kan ƴan majalisar dattawan Najeriya ya rabu biyu kan batun sabbin ƙa'idojin da babban bankin ƙsar CBN, ya fitar na ƙayyade cire kuɗaɗe. Hakan ya faru ne a yayin gabatar da rahoton kwamitin da ke lura da sha'anin banki na majalisar dattijan kan sabbin tsare-tsaren da ka'idojin CBN din. Wasu mambobin majalisar sun nuna goyon bayan tsarin na CBN yayin da wasu kuma suka nuna ƙin amincewa da sabbin ƙa'idoji cire kuɗaɗen. Shugaban kwamitin Sanata Uba Sani ne ya gabatar da wannan rahoto a zaman da majalisar ta yi na ranar Laraba. Ƴan majalisar sun shafe tsawon sa'a'o'i suna tafka muhawara a kan batun. Sanata Uba Sani ya gabatar da rahoton mai cike da rudani, wanda kuma 'yan majalisar suka yi ta jayayya akai. A karshe an buƙaci a bayar da lokaci domin sake nazari kan shawarwarin da majalisar ta bayar. Sanata Adamu Alero na daga cikin wadanda suka goyi bayan wannan sabbin ƙa'idoji. “Ina ganin abin nan yana da amfani ga jama’a, kuma zai hana sayen ƙuri’a da kuɗi. Zai ragebayar da kuɗaɗe ga masu jefa ƙuri’a, kuma zai kawo tsafta ga siyasarmu. “Saboda me? Saboda siyasar da ake yi ta kudi za ta rage har a zaɓi shugabanni kan cancantarsu ba saboda kuɗin da za su bayar ba. “Ni na yi na’am da hakan. Idan kana da jama’a kuma suna sonka ka musu alheri ka mutunta su, to za a zabe ka. Idan kuma ba ka yi ba, ka ajiye kudi ko ka saci kudi don ka bai wa mutane, to kudin ba zai samu ba,”in ji shi. Shi kuwa Sanata Adamu Muhammad Bulkacuwa daga Bauchi ta Arewa, ya ce akwai abubuwa da dama da aka bari a baya kafin aiwatar da waɗannan dokoki. “Ainihin gundarin tsarin idan har mun kai lokaci to yana da kyau, duk ƙasashen da suka ci gaba suna yin hakan. “Amma a inda muke a yanzu a Najeriya, d ayadda tattalin arzikinmu yake to ba mu kai ba, a cewar Sanata Bulkachuwa. Ya jadda cewa ƙasashen da suka ci gaba suna da wadatatun hanyoyin bin tsari, “yanzu a ƙasashen waje da suke yin wannan, ba za ka yi tafiyar kilomita 10 ba tare da ka samu banki ba. “Amma mu a Najeriya, amazaɓata gaba ɗaya ƙananan hukumomi bakwai ne, amma a ƙananan hukumomi biyu ne kawai ake da banki . Saboda haka ni ina ga tsarin bai dace da mutanenmu na ƙauye ba.” Ƴan majalisar dai sun bai wa babban bankin Najeriya shawarwari uku, amma waɗanda suka amince da rahoton sun yi watsi da ɗaya suka kuma amince su yi amfani da biyu. Na farko dai a cewarsu ya kamata a sake nazari kan wannan ƙa'idoji. Na biyu kuma shi ne bayar da cikakken lokaci ga ƴan Najeriya domin fahimta da kuma sabawa da waɗannan sabbin ƙa'idoji da babban banki ya bijiro da su. https://www.bbc.com/hausa/articles/ce70l9r9kljo +business Akinwumi Adesina: Dalilin da ya sa aka wanke shi daga zargin cin hanci da fifita 'yan Nigeria "A ranar Litinin ne wani kwamiti mai zaman kansa da aka kafa don bincike kan shugaban Bankin Ci gaban Afirka, Africa Development Bank (AfDB), Akinwumi Adesina, ya wanke shi daga zarge-zargen cin hanci da nuna ɓangaranci. Majalisar gudanawar bankin ce ta kafa kwamitin bayan ƙasar Amurka ta yi ƙorafi game da yadda wasu kwamitoci na manyan mahukuntan bankin suka wanke shi tun farko game da zarge-zargen. Akinwumi Adesina, ya zama shugaban bankin ne a shekarar 2015 bayan ya ajiye muƙamin ministan aikin gona a Najeriya ƙarƙashin gwamnatin Muhammadu Buhari - daga 2011 zuwa 2015. Kwamitin da ya wanke Mista Adesina yana da mambobi uku da suka haɗa da Mary Robinson, tsohuwar shugabar Ƙasar Ireland a matsayin shugaba, da tsohon shugaban hukumar kare haƙƙi ta Majalisar Ɗinkin Duniya kuma Alƙalin Alƙalai na Gambia, Hassan B. Jallow. Cikon na ukun shi ne Leonard McCarthy, tsohon mai bincike kuma mai gabatar da ƙara kan laifukan tattalin arziki a Afirka ta Kudu. ""Mun duba amsoshin da shugaban (bankin) ya bayar kuma mun same su ababen amincewa da suke nuna ba shi da wani laifi,"" a cewar rahoton kwamitin, wanda kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito. Baya ga duba rahoton kwamitin ladaftarwa da suka yi - wanda ya wanke Adesina tun farko - kwamitin mai zaman kansa ya kuma duba dukkanin zarge-zarge 16 da aka yi masa sannan ya duba dukkanin amsoshin da ya bayar game da su. Daga zarge-zargen akwai naɗa 'yan uwansa a kan wasu manyan muƙamai da kuma bayar da kwangiloli ga 'yan uwa da abokansa. Kazalika an zarge shi da fifita 'yan Najeriya wurin bayar da kwangiloli da kuma sauran ayuukan bankin, Sai dai Adesina ya sha musanta zarge-zargen. Kwamitin ladaftarwa na bankin ya ce ""zarge-zargen ba su da tushe"", sannan ita ma majalisar gudanarwar bankin ta amince da rahoton kwamitin farko, inda suka wanke shi daga zargin baki ɗaya. Amurka ta ce ta damu da harkokin bankin ne saboda ita ce ƙasa ta biyu mafi girman hannun jari a cikinsa bayan Najeriya. Denmark, Norway, Sweden da kuma Finland - wadanda su ma suna da hannun jari a bankin - sun aike da sakon da ke goyon bayan gudanar da bincike mai zaman kansa a kan Mista Adesina." https://www.bbc.com/hausa/labarai-53572230 +business Ambaliyar ruwa ta janyowa manoma asarar biliyoyi a birnin Kebbi "Gwamnatin Kebbi ta ce manoman jihar sun yi asarar shinkafa da sauran amfanin gona, wadanda kudinsu ya kai fiye da naira biliyan daya sanadiyyar ambaliyar ruwan da ta faru a sassa daban-daban na jihar. Hukumomi sun ce ambaliyar ruwan ta mamaye dubban hektocin filayen noma da gidaje, abin da ya haifar da asarar dukiya a yankunan da lamarin ya shafa. Kebbi na daga cikin jihohin da Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta zaɓa domin bunƙasa noman shinkafa a wani shiri da ta bullo da shi a shekarun baya. Yanayin da wasu manoma suka fada a jihar ya munana, inda wasunsu ke ganin cewa ba su taɓa fuskantar matsala kwatan-kwacin wadda suka samu kansu cikinta ba a cikin wannan damina. Zaidu Bala Kofa daya ne daga cikin manoman da wannan asara ta rutsa da su kuma ya ce rabonsu da ganin irin wanann amabaliyar tun a 2011. ""Rabommu da ganin irin wannan ambaliya tun 2011 saboda wannan fadama ba mu san yadda za mu kwatanta [girmanta] ba,"" in ji shi. Ya ƙara da cewa ""fadamar ta taso daga ƙaramar hukumar Audi zuwa Argungu zuwa Birnin Kebbi zuwa Kalgo zuwa Bunza zuwa Ɗakin Gari zuwa Kokumesi zuwa Bagudu. ""Wannan gaskiya ba ƙaramar asara ba ce."" Sauran mutanen da suka rasa albarkatun gonarsu a wannan bala'i sun koka ga gwamnatin jiha da ta tarayya. Attahiru Maccido, shi ne kwamishinan aikin gona na jihar, ya ce duk da cewa hasashe ya nuna cewa ambaliyar za ta ci gaba da barna har zuwa wani lokaci, suna shirin bayar da tallafi a gwamnatance. ""Da ya ke tun kafin yanzu muna da masaniya, ma'aikatar bayar da agajin gaggawa ta tara dukkanin ma'aikatu domin ganin yadda za a bai wa mutane agaji,"" a cewar kwamishinan. Noma musamman na shinkafa, na daga cikin manyan abin dogaro ga al'ummar jihar ta Kebbi tun bayan hawan gwamnati mai-ci ƙarƙashin shugaban Muhammadu Buhari, wanda ya kudiri aniyar farfado da bangaren noma bayan rufe kan iyakokin kasar. Sai dai hadura irin wadannan ka iya mayar da hannun agogo baya ganin irin dinbin asarar da wannan ambaliya ta haifar ga manoman yankin." https://www.bbc.com/hausa/labarai-53975867 +business Multichoice: Abin da 'yan Najeriya ke cewa kan karin kudin DSTV da GOTV "'Yan Najeriya da dama na nuna fushinsu a shafukan sada zumunta kan sanarwar karin kudin amfani da DSTV da GOTV da kamfanin talabijin na Multichoice na tauraron dan adama ya yi. A ranar Talata ce kamfanin multichoice ya fitar da sanarwa kan sabbin kuɗaɗen da kwastamominsa za su biya a matakai daban-daban. Kamfanin ya ce daga ranar 1 ga watan Afrilu, mutanen da ke amfani da nau'rar decodarsu wajen kallo za su biya N21,000 maimakon N18,400 a matakin kololuwa na premium. Sannan masu amfani da GOTV a matakin kololuwa na max na N3,600 za su koma biyan N4,150. Wannan sauyi ko karin ya zo wa 'yan kasar da dama da bazata musamman a wannan lokaci da 'yan Najeriya ke kuka da hauhawar farashi da tsadar rayuwa. Mutanan da ke kokawa na tsokaci kan da wane za su ji a wannan rayuwa da komai ke kara kudi na walwala, baya ga koken sufuri da tsadar abinci da rashin man fetur. Shi dai kamfanin Multichoice ya kare matsayarsa na wannan karin kudi kan yanayin kasuwanci a kasar da tsadar kayayyaki wanda ya ce su suka haddasa wannan sauya farashi nasa. Galibin 'yan ƙasar dai na tsokaci ne a shafukan sada zumunta irinsu Tuwita da kuma kwatanta kudaden da suke biya da yawan tashoshin da ake ba su. Sannan suna duba zabin da ya rage a garesu ko ci gaba da amfanin da kamfanin ko sauyawa zuwa ga mai sauki. Wasu kuma na kiran a kauracewa amfanin da Multichoice baki daya suna cewa akwai wasu hanyoyi ko kamfanonin da ake iya rungumar tsarinsu mai sauki. ""Kowa ya shirya, a kauracewa DSTV!!! Akwai Tstv kuma sun fahimci tattalin arzikin Najeriya, shiyasa suke bayar da kowacce tasha guda kan naira 1 a kullum. DStv bata damu da al'umma ba. Ita kasuwanci kawai. A kauracewa DStv, a saye TSTV!!! Abin da gaske ne. Na ɓarnatar da kudi wajen biyansu kudin kallo ba tare da na moresu ba saboda ina yawaita tafiya shekarar da ta gabata duk da cewa tsoffin fina-finai suke nunawa na 1960 a lokuta da dama, yanu kuma sun yi kari? Na gaji lol. Bari na makalewa @netflix na daura laifi kan TSTV ba wai@DStvNg ko @GOtvNg Masu MultiChoice, DSTC da GOTV sun kara kudi. Wannan shi ne lokaci mafi dacewa mutum ya mallaki TSTV mallakar 'yan Najeriya da biyan kasa da Naira 2 kan kowacce tasha. Naira N1000 ya ishe mutum tsawon wata 4 ga tashoshi daban-daban. Anan nake kallon karawar Elclasico tsakanin Real Madrid da Barcelona. Sanarwarsu ta nuna cewa tsarin Compact Plus da ake biya N12,400 zai koma N14,250, yayin da masu Compact zai koma N9,000 maimakon N7,900. Tsarin confam zai koma N5,300 maimakon N4,615, yayin da masu Yanga za su koma biyan N2,950 maimakon N2,565. Sannan masu amfani da dicodarsu ta GOTV za su biya N2,800 a tsarin Jolli maimakon N2,460. Sannan ma su biyan Jinja kan N1,640 zai koma N1,900, masu GoTv Lite kuma za su koma biyan N900 daga N800. Wadannan ƙarin kudi na zuwa ne 'yan kwanaki bayan hukumar kare hakkin masu sayan kayayyaki ta Najeriya ta bijiro da tsarin bai wa mutanen damar amfani da tsarin biya guda ba tare da kari ba na akalla shekara guda. Sannan mutane na da zabin dakatar da tsarin da suke biya na kallo akalla sau hudu a shekarar, sannan dole Multichice ta bijiro da layukan tuntubarta kai-tsaye tsakanin kwastamominta a ko'ina ta dukkanin kafafan sadarwa. Ko a shekara ta 2020 sai da Multichoice ya kara kudin tsarin tashoshinsa kuma sake aiwatar da irin wannan yunkuri ya fuskanci kalubale. A shekara ta 2020 hukumar ta ce ta kaddamar da bincike kan Multichoice saboda zargin kamfanin da ake yi da babakere a kasuwar kamfanonin taurarin dan adam. Multichoice dai na musanta irin wadanan zarge-zarge, sannan ya ce a kodayaushe burinsa shi ne inganta tsarikan da za su yi wa ma'abota amfani da tauraronta dadi da saukaka musu." https://www.bbc.com/hausa/labarai-60845874 +business Mata ba sa samun kudin shiga kamar mazajensu a fadin duniya "Kina samun kudi kamar yadda mijinki ke samu? Kamar yadda sabon bincike ya nuna a tsakanin ma'arauta akwai bambanci tsakanin kudaden lalura da suke samu. Kuma a mafi yawan lokuta maza sun fi mata samu. Binciken na 'new global study' ya bi diddigin bayanan da aka samar a kasashe 45 a cikin shekaru 40 daga 1973 zuwa 2016, wanda ya fayyace gibin kudin shiga tsakanin mata da maza. Masu binciken da suka hada da Farfesa Hema Swaminathan da Farfesa Deepak Malghan sun yi amfani da bayanai daga gidaje miliyan biyu masu iyalai daga shekara 18 zuwa 65. Misali a Indiya binciken ya gano cewa akwai gibi sosai na adadin ma'aikata mata da maza. Mata a Indiya ba su cika samun aiki ba, kuma koda sun samu ba aiki ba ne na a zo a gani. ""Abin da jama'a ke tunani a ko da yaushe shi ne a gidaje da dama ana hade kudin da ake samu wuri daya, amma mun fahimci cewa lamarin ba haka yake ba don kowa yana ji da kanshi ne kuma mata ake kwaruwa."" Inji Farfesa Swaminathan. Bugu da kari binciken masanan ya yi duba ga bambancin ingancin rayuwa a tsakanin iyalai. Kuma abin da ya gano shi ne akwai rashin daidaito tsakanin maza da mata a gidajen masu kudi da talakawa. ""Bincikenmu ya gano cewa babu wata kasa guda daya a duniya har ma a kasashe mafiya karfin tattalin arziki da mata suka mazajensu samun kudin lalura."" In ji Farfesa Malghan. ""Ko a kasashen Nordic da suke da karancin nuna bambanci tsakanin mata da maza a duniya mun gano cewa abin da mata ke samu bai kai kashi 50 ba. Dalilan da ke sa mata ba sa samun kwatankwacin takwarorinsu a fadin duniya sun hada da matsayin da al'ada ta basu na cewa sune shugabannin gida. A daya ɓangaren kuma al'ada ta dauki mata a matsayin masu aikin gida. Haka kuma mata na daukar hutu mai tsawo inda za su daina fita aiki bayan sun haihu. Sannan kuma mazajensu ba sa biyansu kudin aikin gida da suke yi lura da cewa hatta da renon ya'ya ma duka ya rataya ne a wuyansu. A rahoton Kungiyar Kwadago ta Duniya na shekarar 2018, kashi 76.2 na aikin kula da marasa galihu da suke yi ba a biyansu albashi. Amma kuma ana biyan takwarorinsu maza da ke irin wannan aiki musamman a kasashen nahiyar Asiya da Fasific inda hakan ke faruwa da kashe 80 cikin 100. A cewar rahoton na ILO ""babban abin da ke karyewa mata gwiwa yake kuma hana su ci gaba a harkar kwadago shi ne rashin biyansu albashi a aikin kula da al'umma a gidajen marasa galihu."" Karancin samun kudin shiga ga mata ba tattalin arziki kawai yake shafa ba hadda saka su a wani mizani na rashin gata a gidajensu. ""Mace na ba da gudummuwa wurin tafiyar da gida amma kuma ba ta more kudaden da ke shigowa a cikin gidan."" ""Kamata ya yi ace duk macen da ke da albashi za ta mori kudinta kuma ya zama cewa tana da yancin fada aji a gidan nata."" Inji Farfesa Swaminathan. Ta kara da cewa "" Ya kamata ace yawan albashin mace yawan karfin fada aji da ta ke dashi, kuma dole a daina cutar da ita tare da daga mata kafa kan wasu abubuwa."" Gibi tsakanin kudin da ke shigo ga mata da maza kan haifar da cikas ga kudin tafiyar da gidajensu, in ji Farfesa Malghan, lura da cewa mata ba su smaun damar ajiye wani kudin a zo a gani don amfanin gaba, kuma kudin fanshon su bai taka kara ya karya ba. Sai dai kuma duk da haka bincike ya nuna cewa bambancin da ake samu na kudin shiga tsakanin mata da maza a tsakanin shekarun 1973 zuwa 2016 ya ragu da kashi 20 cikin 100. ""A mafi yawan yankuna a fadin duniya an samu habakar tattalin arziki kuma mata na samun karin gurabun aiki a fadin duniya."" A cewar Farfesa Swaminathan. ""A wasu wurare mata na cin gajiyar sabbin shirye shirye da ke kokarin cike gibin da ke akwai tsakanin abin da suke samu da wanda takwarorinsu maza ke samu. Kuma ana ci gaba da fafutukar ganin an cike cike wannan gibi a fadin duniya. Hakan ya sa abubuwa sun fara sauyawa."" Inji Farfesar. Amma a cewar Swaminathan duk da haka akwai jan aiki kafin a shawo kan wannan matsala. ""Gwamnatoci ba sa aikata abubuwan da suke fada. Kamfanonin ba sa daukar mata aiki yadda ya kamata. A inda suke aikin ma ba a biyansu yadda ya dace musamman a gidajen kula da al'umma."" ""Saboda haka dole mu tambayi cewa shin yaushe za a bullo da shirye-shirye da za su yi adalci ga mata lura da ayyukan da suke yi don inganta rayuwar al'umma?"" ""Akwai kuma bukatar wayar da kan mazaje su fahimci cewa akwai ayyukan da mata ke yi da bai kamata ace suna tafiya ne a kyauta ba. Akwai babbar rawa da ya kamata gwamnatoci da al'umma su taka fiye da wadda suke takawa a yanzu.""" https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-58901807 +business Rikicin yankin Tigray : Yadda ƴan gudun hijirar yankin ke yin kalaci da ganyen bishiya don su rayu Jam'iyyun ɓangaren adawa a yankin Tigray na kasar Habasha, sun ja hankalin duniya su na cewa: da akwai babbar barazana ga rayuwar jama'a idan ba a kai taimakon gaggawa ba. Tuni dai mutane ke ta mutuwa sanadiyar rashin abinci, shi ya sa a cewar jam'iyyun su ke kira ga kasashen duniya su kai musu agaji. Gwamnatin Habasha na cewa ana kai kayan agaji, kuma tuni suka shiga hannuwan mutanan da yawan su ya kai milyan daya da rabi. Jam'iyyun sun sanar da cewa mutane dubu 52 ne aka kashe tun lokacin da ricikin ya ɓarke a cikin watan Nuwanba zuwa yanzu. To sai dai kuma ba su yi wani ƙarin bayani ba kan yadda suka yi ƙididigar yawan mutanan da suka mutun, amma sun sanar da cewa daga cikin wadanda suka mutun, sun hada da mata da yara da shugabanan addini . Daga ɓangaren gwamnatin kasar babu wasu al'kalumma da ta bayar, sai dai ta na cewa ta na kokarin daukar matakin doka kan tsohuwar jam'iyyar dake mulki a Tigray. Tashin hankali ya ɓarke ne bayan da jam'iyyar TPLF ta Tigray People's Liberation Front ta mamaye barikin sojojin ƙasar a yankin, abun da ya haddasa tabarbarewa dangantaka da gwamnatin Firai minista Abiy Ahmed. Yadda yaƙin ya raba mutane da matsugunansu Kimamin 'yan gudun hijira daga kasar Eritriya dubu dari da ke rayuwa a cikin sansanonin 'yan gudun hijira na majalasar dinkin duniya a Tigray kuma lamarin rikicin ya rutsa da su. Kakakin hukumar kula da ƴan gudun hijira ta majalasar dinkin duniya ya sanar da cewa yawancin 'yan gudun hijira da lamarin ya rutsa da su, na cin ganyayen bishiyoyi ne da kuma shan ruwan sama da suka kwanta a cikin tabkuna bayan da aka tilasta masu ficewa daga sansanonin. Rikicin na Tigray ya kuma raba aƙalla mazauna yankin miliyan biyu daga matsugunansu saboda gudun tashin hankali. A ranar Litanin,babban jami'in hukumar 'yan gudun hijira ta kasar Norway ,Jan Egeland ya sanar da cewa ,a cikin sama da shekaru 40 da ya ke aikin jinkai, bai taba ganin yadda lamarin agaji su ka yi rauni ba a filin aiki kamar wannan karo. A cikin wata sanarwar haɗin gwiwa. jam'iyun bangaren adawa guda uku da suka haɗar da Tigray Independence Party (TIP) da Salsay Weyane Tigray da kuma National Congress of Great Tigray, sun sanar da cewa abinci da magungunna ba su zuwa da wuri, kuma wannan abun ya sa tabarbarewar lamura da kuma birkicewar rayuwa a yankin. An nakasa birane da kauyukan yankin ta hanyar sakin boma-bomai da ake harbawa. An kwashe tare da wargazar da kayayakin kiwon lafiya da na bayar da illimi, kuma wani babban abin mamaki a cewar jam'iyyun adawar ,shi ne hatta da wuraren su inda suke gudanar da ibadodinsu an kai masu hari an ruguza su. Wani hoto ya nuna wasu mutane dubu 60 daga yankin Tigray na rayuwa a sansanonin 'yan gudun hijira a kasar Sudan. Ƙasashen duniya sun caccaki hukumomin Habasha A makon da ya gabata kasar Amurika ta yi kira da a janye dakarun kasar Eritreya ba tare da wani jinkira ba, ta kuma kara da cewa rahotanni marasa dadi na fitowa daga yankin wadanda suke nuna cewa an keta hakin bil adama ta hanyar gudanar da fyde da kuma kwasar ganimati. To sai dai tuni gwamnatin kasar Habasha da ta Eritereya suka musunta cewa babu dakarun kasar Eritereya a yankin Tigray. Jam'iyyar TPLF ta jagoranci yankin Tigray da kusan baradan yaki dubu dari biyu da hamsin a karkashin ikonta na kusan shekaru 30.. Jam'iyar ta sauka daga kan mulki ne bayan da dakarun gwamnatin Habasha suka karɓi mulki da babban birnin Mekelle a ranar 28 ga watan Nuwanba. Firai ministan Habasha Mista Abiy Ahmed, na zargin jam'iyyar ta TPLF da yin barazana ga mutuncin da yancin kasar Habasha, ta hanyar kokarin kifar da gwamnatin shi bayan jam'iyyar ta karbe tare da mamayar wani barikin sojoji na tsawon wata daya . A cikin watan Agusta an gudanar da zaɓen a yankin na Tigray wanda ya kasance zakaran gwajin dafi kan matakin da ya dace a dauka daga gwamnati, Gwamnatin Mista Abiy ta ayyana zaben a matsayin haramtace, a yayin da ita kuma jam'iyyar ta TPLF ke cewa gwamnatin Habasha haramtacciya ce kuma ba ta da wani hurumi na ta mulki Tigray. Ga ƙarin wasu labaran masu alaƙa da wannan. https://www.bbc.com/hausa/labarai-55913261 +business Kasashen Afirka da darajar kudinsu ta tashi saboda faduwar fan din Ingila "A daidai lokacin da darajar Fan din Ingila ta karye, su  kuwa kudaden wasu kasashen Afirka tagomashi suka samu, inda darajarsu ta dan farfado. A ranar Litinin, darajar fan din ta fadi da kashi 4, idan aka kwatanta da dalar Amurka a kasuwannin Asiya, darajar Shilling din Kenya ya farfado da 0.15, kan fan guda. A dayan bangaren kuma, an dara a wasu kasashen Afirka, inda darajar kudin Zambia kwacha, da pula na Botswana, da cefar kasashen Afurka su ma sun samu tagomashi. Sai dai, darajar kudaden Afirka ta Kudu rand, da naira ta Najeriya lamarin ba mai dadi ba ne, saboda sun kara faduwa kasa warwas. Wannan rana na zuwa ne daidai lokacin da wasu kasashen Afirka suka fuskanci asarar faduwar darajar kudaden idan aka kwatanta da dalar Amurka da fan din Ingila. Cedin Ghana shi ya fi kowanne karyewa, ya yi faduwar da ba a a taba gani ba cikin shekaru da dama, tun farkon shekarar nan ta yi kasa da kashi 40 idan aka kwatanta da dalar Amurka. Cedin ya kara yin kasa da kashi 20 kan fan din Ingila a dai wannan shekara da muke ciki. Amma cedi ya dan yi sama kadan da kashi 10.83 da safiyar ranar Litinin. “Kasashe na fadi tashi kan farfado da tattalin arzikinsu, musamman ganin kayan da suke fitarwa sun ninka wadanda ke shiga kasashen,’’ in ji Richmond Frimpong, mai sharhi kan lamura a Ghana. Wannan ya kara janyo bukatar kudaden kasashen waje, da tashin tsadar kayayyaki. Darajar fan din Ingilar ta fadi a kasuwar duniya, daidai lokacin da gwamnati ta sanar da Karin kudin haraji da ba a taba gani ba cikin shekaru 50. Fan ya fadi da kusan kashi 1.03 da safiyar Litinin, amma ya dan dago kafin faduwar rana da kashi 1.08. Sakataren baitil malin Birtaniya, Kwasi Kwarteng ya yi alkawarin rage haraji kari akan fan biliyan 45 da ya sanar a ranar Juma’a. Masu zuba hannun jari na kasashen Duniya, na saye da sayar da hajarsu da kudaden waje. Manufar ita ce samun riba, saboda za su sayi kudaden masu daraja. Darajar fan din ta fadi saboda masu zuba jari na saída ita, saboda rashin tabbacin shirin gwamnatoci da ke nuku-nuku, In ji Jabe Foley na Rabobank. ""Sun damu matuka kan sanarwar  gwamnati na rage kudin haraji kuma ba lallai su ba da cikakken tallafinsa ba,"" in ji ta. Wannan na daga cikin dalilan da ya tilastawa gwamnatoci cin bashi. Hakan zai janyo cin bashin makudan kudade, a daidai lokacin da bankin Ingila zai fara saida wasu daga cikin basukan gwamnatin. Darajar dalar Amurka da fan sun dan farfado a makwannin da suka gabata, to amma na dan lokaci baya sanar da kwarya-kwaryan kasafin kudi domin farfado da dala. A farkon watan Satumba  dalar ta fadi da kashi 1.35, karon farko da ta yi kasa da 1.14, cikin shekaru 40. Hakan na faruwa sakamakon tashin farashin makamashi da sauran kayayyaki, da ke ci gaba da sanya tattalin arzikin duniya cikin garari. An dade ba a ga tashin farashin kayan abinci cikin sauri ba cikin shekaru 40, farashin makamashi da fetur ma ba a cewa komai. A bana, darajar fan karye fiye da dalar Amurka da sauran kudade. Ita ce faduwa mafi muni cikin shekara da ka fuskanta tun bayan ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai a shekarar 2016. Ana amfani da darajar kudi a kasuwar musayar kudade, ta hanyar saye da sayarwa. Akwai kuma abubuwa da dama da suka hada da; Tattalin arziki: Bunkasar tattalin arziki na sanya darajar kudin kasar ta samu tagomashi, saboda wasu kasashe za su zuba jari a ciki, za su bukaci kudin kasashen domin hakan, hakn zai sanya bukatar ta karu. Adani: Idan bankin Ingila ya kara kudin ruwa, hakan zai ja hankalin masu zuba jari ko ajiyar kudade, su kara azamar bukatar fan din Ingila. Farashi: Idan kayan da Birtaniya ke samarwa sukai arha fiye da na wasu kasashe, ‘yan kasuwa daga ketare za su bazama domin bukatar kudin fan domin saya. Wannan zai sanya darajar kudin ta karu Harkokin kudin gwamnati: Halin da bankin gwamnati ke ciki, da abin da ke kasa, da bashin da ake bi, ka iya shafar darajar kudi. Hasashe: Tsadar kudin, da saye da sayarwa da hasashen da ake yi watakil darajar ta karu, na sanya mutane hadamar saye domin cin riba nan gaba. Abin damuwar shi ne, tsahon wane lokaci za a dauka darajar kudin na faduwa." https://www.bbc.com/hausa/articles/c25jqej1vv7o +business Ikirarin cewa tsananin talauci ya sa mutane na sayar da yatsunsu a Zimbabwe ya ja hankali a Najeriya "Wani labari marar tushe game da mutanen da ke kokarin yaƙi da talauci a ƙasar Zimbabwe ta hanyar sayar da yatsunsu a kan kudi dala 40,000 ya zama abin ce-ce-ku-ce a Najeriya. Sashen BBC mai bin diddigi ya bi diddigin labarin da ya samo asali daga shafin intanet na kafar Gambakwe a Zimbabwe. A labarin da aka wallafa a ranar 28 ga watan Mayun 2022, kafar Gambakwe ta rubuta cewa ""wasu da ake zargi ƴan Sangoma ne a Afirka ta Kudu ana zarginsu da bayar da kuɗi mai tsoka ga yatsun matasa marasa aikin yi a Harare."" Sangoma kalma ce ta Zulu da ke nufin masu maganin gargajiya ko kuma masu duba. Kafar ta yaɗa rahotonta a WhatsApp wanda ya ja hankalin masu amfani da kafofin sada zumunta a Zimbabwe. Kuma labarin ya bazu zuwa wasu ƙasashen Afirka yayin da ƴan Najeriya da Uganda suka dinga yaɗa labarin a Twitter. Wani mai amfani da Twitter @joyie7star daga Kamfala a Uganda ya yaɗa labarin ga mabiyansa 6,881. Yana mai cewa tsadar rayuwa ta sa mutane na sayar da yatsunsu kan miliyoyin daloli. A Najeriya, @InnocentZikky shi ma ya yada labarin wanda kuma wasu suka yaɗa sau 2,668 a Twitter. Wannan saƙon a Twitter ya yi amfani da wasu hotuna na labarin Gambakwe a saƙonsa na Twitter. Hotunan ne yawanci mutane suke yaɗawa a shafukan sada zumuna na Intanet domin ci gaba da yaɗa labarin. Kafar Rediyo ta Kenya 933KFM ita ma ta yaɗa labarin, tare da tambayar mabiya wane ɓangare na jikinsu ne za su iya sayarwa. Jaridar Zimbabwe H-Metro ta wallafa hira da ƴan kasuwa a kantin Ximex Mall waɗanda suka ce mutane na zuwa suna tambayar yadda za su ci gajiyar cinikin. Wasu daga cikin ƴan kasuwar sun shaida wa H-Metro cewa waɗanda suka tuntuɓe su cewa labarin jita-jita ce kawai. Sashen BBC da ke yaƙi da labaran ƙarya ya yi nazari kan wasu bidiyo guda biyu waɗanda aka ce sun sayar da yatsunsu ko kuma suna shirin sayarwa. A bidiyo ɗaya wani mutum ya jirkitar da yatsunsa ya kuma rufe da filasta domin ya nuna cewa an datse masa yatsa. A ɗaya bidiyon kuma an nuna mutum ana kamar ƙoƙarin cire masa yatsa, amma kuma babu wata alama da ke nuna cewa hanyoyin da aka bi da gaske ne, kamar yadda labarin ke bazuwa a Intanet, musamman ma yadda mutumin da aka datsewa kafa an nuna shi yana dariya a bidiyon. Labarin ya yi kama da labarai irin waɗanda suka shafi sayar da sassan jikin mutum da ke jan hankali a sauran sassan Afirka. Amma, waɗannan labaran wani lokaci suna da sarƙakiya domin wani lokaci ana yarda da su. A watan Janairun 2022, wasu matasa biyu da kuma abokinsu ɗan shekara 20 an kama su a Najeriya kan zargin kisan wata yarinya domin yin tsafi. Ɗaya daga cikinsu ya yi iƙirarin cewa wani labarin da aka yaɗa ne a kafofin sada zumunta ya ja hankalinsa. A Malawi, ana sa ran kotu za ta yanke wa wasu mutum huɗu hukunci a ranar 27 ga Yuni kan kisan wani zabaya a 2018. Ana alakanta kisan zabaya a Malawi da asiri musamman tunanin samun nasara da kuma arziki." https://www.bbc.com/hausa/labarai-61664237 +business Tsautsayi da riba a haramtacciyar masana'antar mai ta Najeriya "Mutuwar fiye da mutum 100 sakamakon wata fashewa a wata haramtacciyar matatar man fetur a kudancin Najeriya ta haska yadda ake cin kasuwar bayan-fage da ake tace man. Wakiliyar BBC Mayeni Jones da kuma Josephine Casserly sun yi bincike kan masana'antar. Bayan shafe awanni a mota da babur da kuma tafiya a ƙafa, mun isa wata haramtacciyar matatar man fetur - wani wuri da jami'an tsaro suka kai samame tare da rufe shi. Tun kafin mutum ya ga komai zai fara jin warin man fetur. Sai kuma muka zo ƙarshen korayen bishiyoyin da suka lulluɓe wurin, sai kuma ga mu a wurin da wuta ta share. Ana ganin alamun man fetur a dandariyar ƙasar wurin tare da ƙonannun saiwoyin bishiya. Ƙasar ta jigata har ma tana kama da inda aka samu aman wutar dutse. Wannan wani saƙo ne a Neja Delta da ya ƙunshi mahaɗar hanyar ruwa da ke kudancin Najeriya. Ƙyallin mai duk ya mamaye saman ruwan da kuma wurin da alama bishiyoyi ne duk mai ya shanye itatuwansu. Muna tare da wani ɗan siyasar yankin mai suna Chidi Lloyd da tawagarsa, inda ya yi mana bayani kan yadda aka kawo fetur ɗin da aka sato nan a jirgin ruwa. Ana kunna wuta a ƙarƙashin wannan diro ɗin sannan a tafasa ɗanyen man fetur kuma a ware makamashi daban-daban daga ciki, daga fetur zuwa kalanzir da disel. Daga nan kuma sai a zuba fetur ɗin cikin wani mazubi da zai hutar da shi. Sai dai ba ko yaushe ake samun nasarar yin hakan ba - kuma idan aka samu matsala, yana haifar da fashewa wadda za ta iya zama mai haɗari kamar wadda ta faru a Juma'ar da ta gabata. Yawan mutanen da suka mutu ya nuna yadda sana'ar tace haramtaccen mai take samar wa dubban matasa aiki a Neja Delta tsawon shekaru da suka wuce - a ƙasar da rashin aikin yi ke ƙaruwa. Ma'aikata kan shafe makwanni a matatun kamar wannan a lokaci guda, akasari kan yi aiki har cikin dare musamman ga waɗanda kyakkyawan tsarin aiki da ke da ƙwarewar harkokin kuɗi da ta iya aiki. Gwamnati ta yi ƙiyasin cewa an sace mai da ya kai darajar dala biliyan uku. Ana sayar da wannan man ne ta ɓarauniyar-hanya a Najeriya ko kuma a kai shi ƙasar waje bayan sun sato shi ta hanyar fasa bututan mai na gwamnati. Gurɓacewar iskar da waɗannan matatun ke haifawa ba wai a garuruwan da ke kusa kawai ake jin ta ba. Iskar gas ɗin da ake samu wajen samar da fetur na ƙonewa mafi yawan lokaci ta yadda ba za a iya sake amfani da shi ba ta hanyar abin da ake kira gas flaring wato ƙona gas. Sai dai ba haramtattun matatu ne kaɗai ke yin hakan ba - duk da sun saɓa wa doka - kamfanonin mai na yin hakan. Sai dai a daidai lokacin da haramtacciyar sana'ar tace mai ke haɓaka, ƙona gas ma ya ƙaru kuma hakan ya ƙara gurɓacewar iska. A bayyane ake jin hakan yayin da mutum ke shiga Fatakwal, wani babban birni a Neja Delta. Wani murtukeken hayaƙi ya turnuƙe sama, wani zubin abin na ta'azzara ta yadda ba za ka iya ganin gabanka ba fiye da tsawon mita 30 (tsawon ƙafa 100). Duk da an rufe tagogi, amma idan mutum ya kwana a garin sai ya fahimci hakan a hancinsa. Wani likita a asibitin yankin ya ce yana samun ƙaruwar marasa lafiya da ke da alaƙa da nimfashi, waɗanda ake alƙanatawa da gurɓacewar iskar. Sai dai mutane irin su Osaja da ke zaune a manyan gidajen da ke cikin birni, wanda ya nemi kada mu bayyana sunansa na gaskiya, ya ce wannan sakamakon ba abin ƙi ba ne. Ya faɗa mana cewa ya mallaki haramtattun matatun mai biyu kuma yana cikin masu safarar haramtaccen man da kuma tacewa da sayar da shi. Tarin motocin tsere da yake da su da kuma kogin ninƙaya da ke gidansa sun tabbatar da dukiyar da yake da ita. ""Shin ya da cewa ka zauna cikin kyakkyawan muhalli amma kuma ka mutu da yunwa? Idan kana jin yunwa za ma ka ji ka shaƙi wani abu? ""Idan dalilin da ke jawo gurɓatar iskar yana kuma sama wa mutane sai ma ka manta da wani gurɓacewar muhalli,"" in ji shi. Wasu da suka kasa samun aikin yi sun yarda da hakan. Wani mai sana'ar ɗukar hoto ya faɗa mana yadda ya fara aiki a wata haramtacciyar matata a cikin daji lokacin da ya gaza samun aikin yi. Yana ""dafa"" ɗanyen man - wanda ke haifar da hayaƙi mai yawa da ma'aikata ke shaƙa. Ya ce idan aka samu matsala sukan gudu zuwa cikin gulbi (ko mahaɗar hanyar ruwa), amma ba ko da yaushe hakan ke zama mafita ba saboda idan akwai mai shi ruwan kan kama da wuta. Haɗurran da ke cikin hakan suka sa ya haƙura da aikin. Amma wata da ta karanta ilimin kwamfuta kuma ta shiga harkokin tace fetur ɗin ta ɓarauniyar hanya bayan ta kasa samun aikin yi, ba ta damu da batun gurɓacewar muhallin ba. Matar da ke da shekara 40 da ɗoriya na amfani da jirgin ruwanta wajen safarar mai daga matatun: ""Ni mutuniyar ruwa ce, abin ba wahala a wajenmu."" Waɗanda ke sana'ar sun faɗa mana cewa idan har gwamnati za ta yi maganin tace haramtaccen fetur - kamar yadda Gwamnan Rivers Nyesom yake yi - to ya kamata a yi wani abu a kan rashin ayyukan yi. Kazalika, suna ganin haramta harkar ba abu ne mai sauƙi ba ganin irin yawan mutanen da ke cikinta, ciki har da jami'an tsaro. Osaja ya ce yana yawan biyan cin-hanci don kada a kai samame kan matatun nasa: ""Kowa na cikin harkar nan. Tsararren laifi ne."" A gefe guda kuma, 'yan sanda na binciken zargin da gwamnan Rivers ya yi cewa wani babban jami'in ɗan sanda na gudanar da haramtacciyar matata. Osaja na ganin harkar tace haramtaccen mai ba don samun kuɗi ake yi ba. Yana ganin kan sa a matsayin mai samun ganima daga kamfanonin mai kuma yana ba mutane. Ƙauyensu wata cibiya ce da kamfanonin mai ke haƙo mai sosai amma har yanzu mutanen ƙauyen ba su da komai, inda suke da ƙarancin kayan more rayuwa, a cewarsa. ""Mun gamu da rashin adalci iri-iri. Me ake ba wa mazauna ƙauyuka? Babu komai! Ziro! ""Wannan kayanmu ne. Wannan kayana ne kuke kwashewa, me kuke ba ni? Saboda haka yanzu kowa ya ji ɗanɗanon haramtacciyar zuma da kuma daɗin da take da shi.""" https://www.bbc.com/hausa/labarai-61241416 +business Coronavirus: Amurka za ta bai wa kowanne dan kasa tallafin dala 1,200 'Yan majalisar Amurka sun amince da dalar Amurka tiriliyan 2 a matsayin tallafin rage radadin cutar coronavirus, wanda ya hada da bai wa dukkan 'yan kasa matasa dala 1,200 kyauta (sama da naira 400,000). An samu tsaiko yayin kada kuri'ar amincewa da kudirin dokar sakamakon rikici tsakanin 'yan jam'iyyar Democrats da Republican a kan alfanon da marasa aikin yi za su samu a cikin kudirin. Daga cikin abin da kudirin ya kunsa akwai bai wa kusan kowanne baligi dala 1,200 a matsayin tallafi sannan kuma a taimaka wa masu matsakaitan kasuwanci biyan albashin ma'aikatansu. Wadanda suka mutu a Amurka sakamakon cutar sun kai 1,000 sannan kuma akwai kusan 70,000 da aka tabbatatar suna dauke da cutar. A duniya baki daya, fiye da mutum 21,000 ne suka mutu tun daga sanda annobar ta barke a yankin Hubei na China a watan Disamba. Wadanda suka kamu kuwa sun kusa rabin miliyan. Kudancin Nahiyar Turai ce cibiyar annobar a yanzu, inda kasashen Sifaniya da Italiya ke samun daruruwan mamata a kullum. Yarjejeniyar da aka cimma tsakanin shugabannin Democrats da Republican ta kunshi haraji da rance da kudin da za a bai wa asibitoci da kuma tanadin kayan ceto. Kudirin dokar mai shafi 900 ya kunshi zunzurutun kudin da ya kai kusan rabin kasafin kudin kasar na shekara. Daga ciki akwai: https://www.bbc.com/hausa/labarai-52048658 +business Wahalhalu biyar da 'yan Najeriya ke ciki a wannan lokaci "Masu lura da al'amuran yau da kullum na ganin ƴan Najeriya sun sake faɗawa cikin wata wahalar abubuwan more rayuwa da suka daɗe da mantawa da ita. Wahalhalun na ƙaruwa a ƙasar daga wani ɓangare zuwa sauran ɓangarori, kamar yadda wasu ƴan ƙasar ke cewa ""ana cikin wani yanayi a Najeriya"" Ko da yake hukumomi a ƙasar na nanata cewa suna ɗaukar matakai na shawo kan matsalolin da ke tagayyara ƴan Najeriya a lokacin da ƙasar ke tunkarar babban zaɓen shekarar 2023. Ga wasu wahalhalu biyar da ƴan Najeriya ke ciki: An shafe makonni ana fama da matsananciyar wahalar man fetur a jihohi da dama na Najeriya, lamarin da ya haddasa wahalhalu ga masu ababen hawa baya ga ƙaruwar farashin sufuri. Najeriya ce kasar da ta fi kowace kasa samar da man fetur a nahiyar Afirka wadda kuma take samar da kusan ganga miliyan biyu ta ɗanyen mai. Duk da arzikin mai da Allah ya ba ƙasar amma wahalar fetur ba sabon abu ba ne a Najeriya. Ko da yake an daɗe ba a shiga wahalar fetur ba a ƙasar. Ƴan ƙasar sun shiga wahala ne tun lokacin da aka shigo da wani gurɓataccen mai ɗauke da wani adadin sinadarin methanol da ya zarce abin da ƙasar ta iyakance a kasuwa. Ƴan ƙasar da dama sun yin kukan cewa man da suka saya a gidajen mai ya lalata musu abubuwan hawa. Daga baya hukumomin sun ce an magance matsalar. Matsalar ta jefa ƴan Najeriya cikin wahala, inda ake samu dogayen layukan ababen hawa a gidajen mai. Wahalar mai na shafar ɓangarori da dama na buƙatun yau da kullum da ke dogaro da fetur, lamarin da ke ƙara haifar da wahala ga ƴan Najeriya a ɓangarori da dama. Ƙungiyar dillalan man fetur masu zaman kansu wato IPMAN ta musanta cewa ɓoye man fetur da ake zargin wasu dillalai ke yi shi ne ya ƙara ta'azzara ƙarancin man fetur da ake yi a Najeriya. Wata matsala da ta kunno kai a baya-bayan ita ce ta karancin man dizel, inda a yanzu haka farashin sa ya tashi zuwa naira 700 a kan kowace lita. Yawanci manya da matsakaitan masana'antu da tsirarun gidaje duk sun dogara man dizel wajen gudanar da harkokin yau da kullum. Harajin da gwamnatin kasar take samu daga kamfanonin man fetur da kuma kudaden da take samu na kasashen waje ta hanyar fitar da man yana taka muhimmiyar rawa ga tattalin arzikin kasar. Sai dai wasu masu ruwa-da-tsaki akan man fetur sun ce matsalar tana da nasaba da tashin da farashin man fetur ya yi a kasuwannin duniya. Masu ruwa-da-tsaki a kan harkar man fetur, sun danganta tashin da man dizel ya yi da tashin farashin man fetur a kasuwannin duniya, sakamakon yakin da Rasha ke yi a Ukraine, da kuma cire tallafin mai da gwamnatin Najeriya ta yi. Tsadar farashin tikitin jirgin sama na ɗaya daga cikin wahalar da ƴan Najeriya suka shiga. Hauhawar farashin tikitin jirgin sama da kuma rashin tabbas sun jefa fasinjoji cikin halin damuwa da ƙaƙa-ni-ka-yi. Tun a watan Fabrairu dukkanin jiragen Najeriya sun ƙara farashi inda suka mayar da ƙaramin tikiti zuwa na N50,000. Jiragen sun ƙara kuɗi ne sakamakon ƙarancin man da jirgin sama ke amfani da shi, lamarin ke ci gaba da kawo tsaiko a harkokin sufurin jirgin sama. Kamfanonin jiragen sama sun yi gargaɗin cewa matsalar na iya tilasta musu katse harkokin sufuri ta sama a ƙasar. Baya ga tsadar farashin jiragen, matsalar ta kuma haifar da samun jinkiri ga fasinja da soke tashin wasu jirage. Ƙarancin man jiragen ya haifar da tsadarsa a kasuwa inda wasu jiragen suka ce farashin ya tashi daga N590 zuwa N625 duk lita ɗaya. A watan Fabrairun 2021 jiragen na sayen lita ne kan N190, amma zuwa ƙarshen shekarar farashin ya kai tsakanin N350 zuwa N370. Ƙarancin kuɗaɗen ƙasashen waje da tsadar farashin mai a kasuwar duniya su suka haifar da tsadar farashin man jiragen. Satar mutane don kuɗin fansa, na cikin dalilan da suka sa ɗumbin mutane suka gwammace hawa jirgin sama duk da tsadar tikitinsa. Sai dai, ga alama duk da tsadar, a yanzu hawa jirgin sama ya fara zama, ga mai ƙaramin ƙarfi sai da wani babban dalili. Duk lokacin da ake wahalar fetur da dizel, za a fuskanci tsadar farashin kayan masarufi da sufuri. Ƴan Najeriya na fuskantar wahalar abubuwan wahalar mai da kuma tsadar kayayyaki. A rahoton da ta fitar a watan Fabrairu hukumar kididdiga ta Najeriya NBS ta ce hauhawan farashin kayayyaki ya ƙaru da kashi 1.63 a Fabrairun 2022 wato ƙarin kashi 0.16 idan aka kwatanta da watan Janairu. Al'ummar Najeriya na ci gaba da kokawa kan rashin wutar lantarki, wadda hakan ke kara haddasa matsin tattalin arziki. Al'umma a sassan ƙasar na ci gaba gaba da rayuwa cikin zafi da duhu musamman da dare saboda ƙaruwar rashin wutar lantarki. An daɗe ƴan Najeriya na fama da matsalar ƙarancin lantarki. A baya-bayan nan ɗaukewar lantarki ya ƙaru inda rahotanni a ƙasar ke cewa katsewar babban layin raba wutar ya shafi jihohi da dama ciki har da Lagos da Enugu da Kaduna da Abia da Abuja da Anambra da Ebonyi da Enugu. Ministan lantarki na Najeriya, Injiniya Abubakar Aliyu ya shaidawa BBC cewa masu fasa bututun mai ne suka taba na gas da injunan lantarkin ke amfani da su. Ya ce suna duba wasu hanyoyi na yadda za a samar da lantarkin domin amfanin jama'a. Rashin wadatacciyar wutar lantarki a Najeriya, abu ne da ke ci wa al'ummar kasar tuwo a kwarya musamman wajen tafiyar da harkokinsu na yau da kullum. Duk da kasancewar Najeriya babbar kasa mai arzikin ma'adanin kwal da man fetur da iskar gas, sannan kuma wadda ta fi kowacce fitar da danyan fetur a nahiyar Afirka, rahotannin sun nuna kashi 40 cikin 100 na al'ummar kasar ne kadai ke samun wutar lantarki. Rashin wutar lantarki dna janyo matsaloli da dama musamman wajen tafiyar da abubuwa da suka hada da kasuwanci da bangaren aikin gona da masana'antu da asibitoci da makarantu da sauransu. Hakan yakan janyo mutuwar masana'antu da kuma dakile habbakar kananan sana'o'i. Yajin aikin da malaman Jami'an ke yi, wata matsala ce da ta jefa rayuwar ɗalibai cikin rashin tabbas. Yajin aikin malaman kusan ya zama ruwan dare, wani mataki da suke ɗauka domin neman gwamnati ta biya buƙatunsu. Sai dai ya fi shafar ɗalibai da kuma makomar karatunsu, wadanda ke tsintar kansu cikin damuwa, dalilin da ya sa wasu ke ganin ya kamata kungiyar ta sauya salon tunkarar rikicinta da gwamnatin kasar ba sai lallai ta hanyar yajin aiki ba. A ranar litinin Kungiyar malaman jami'o'in ASUU, ta sanar da tsawaita wa'adin yajin aikin da suka tafi zuwa makwanni takwas sakamakon rashin cimma matsaya da gwamnati kan bukatunsu. ASUU ta shiga yajin aikin ne sakamakon abin da ta bayyana gazawar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari wajen aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla a baya game da yadda za a inganta harkokin karatun jami'a na kasar. ASUU kusan ta shiga yajin aiki sau 15 tun bayan komawar Najeriya mulkin dimokuradiyya a 1999, lamarin da kan jefa harkokin karatu cikin mawuyacin hali." https://www.bbc.com/hausa/labarai-60754083 +business 'Mun yi farin-ciki da sake bude iyakokin kan tudu na Najeriya' "Mazauna garuruwan da ke kan iyakokin Najeriya da aka rufe na ci gaba da bayyana farin-cikinsu bayan da hukumomin ƙasar a hukumance suka buɗe iyakokin da ke kan tudu a ranar Litinin. Hukumar hana fasa-ƙwauri ta ce gwamnatin tarayya ce ta ba da umarnin buɗe iyakokin huɗu a ƙarshen makon jiya. An dai amince a bude iyakokin Idoroko a jihar Ogun da Jibiya dake jihar Katsina sai kuma iyakar Kamba a Kebbi da kuma iyakar Ikom a jihar Cross River. Bayan bude iyakar Jibiya a Katsina, mutanen da ke yankin sun bayyana jin dadinsu kasancewar harkokin kasuwanci zai farfado a cewarsu. Alhaji Salisu O I Jibiya, ya shaida wa BBC cewa, bude iyakokin nan ya sanya su cikin jin dadi da raha saboda sun shafe shekaru uku suna rufe abin da ya sanya su cikin takura. Ya ce, duk da ka'idojin da hukumomi suka gindaya musu na irin abubuwan da za a rinka safararsu ta iyakokin, su kam sai san barka saboda koba komai za su ci gaba da kasuwancinsu da suka jima basa yi. Alhaji Salisu O I Jibiya, ya ce "" A yanzu an yarda mu shigo da abubuwa da suka hada da wake da aya da kuma dabino, amma duk sai mun biya kudin fito."" To amma ba suce mu biya kudin fito a kan kayan abinci kamar shinkafa da taliya da cous cous da dai makamantansu ba, in ji shi. Ya ce, duk wadannan sharadai su kam ba su damu ba domin ba bu wani alfanu da rufe iyakokin ya kawo musu sai bakar wahala da suka sha. A jihar Kebbi ma, an bude iyakar Kamba, inda al'ummar garin suka shaida wa BBC cewa suna cikin farin ciki marar misaltuwa saboda abin da suka jima suna jira ne ya faru. Yahuza Sahabi, mazaunin garin Kamba ne inda aka bude iyakar, ya kuma shaida wa BBC cewa, bude iyakar nan shi ne babban alfanu garesu, domin za su samu saukin farashin kayayyaki musamman na abinci. Ya ce,"" A gaskiya mu mutanen da ke rayuwa a garuruwan da ke kan iyaka, rufe su ya yi matukar taba mana rayuwa musamman ta fuskar tattalin arziki."" Yahuza Sahabi, ya ce a lokacin da aka rufe iyakarsu sun ga kalubale kala-kala, saboda yadda farashin kayan abinci ya tashi sosai, ba karamin kuncin rayuwa muka shiga ba inji shi. Ya ce, amma a yanzu tunda an bude iyakar, farashin kayan abinci da ma sauran kayan bukatun yau da kullum zai sauko. Hukumomin Najeriya dai sun sha fada cewa, rufe iyakokin ya taimaka wajen bunkasa harkokin masana'antun cikin gida da noma musamman na shinkafa. A karshen shekarar 2020 ne, shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya bayar da umarnin bude iyakokin kasar hudu na kan tudu da suka hada da Semi da Ilela da Maigatari da ku ma Ofong. A watan Agustan 2019 ne gwamnatin kasar ta rufe iyakokin nata da zummar daƙile yawaitar fasa-kwauri da kuma bunƙasa tattalin arziki, ko da yake 'yan kasar da dama sun koka kan matakin. Hukumar hana fasa-ƙwauri, wadda ta yi ruwa ta yi tsaki wajen ganin an yi aiki da rufe iyakokin, ta bugi ƙirji game da irin nasarorin da ƙasar ta samu saboda matakin da ta dauka na rufe iyakokin tudu ta fuskoki daban-daban na rayuwa." https://www.bbc.com/hausa/labarai-61225190 +business Narendra Modi: Firaiministan India ya janye dokokin noma da suka jawo ce-ce-ku-ce bayan shekara guda ana zanga-zanga "Firaiministan Indiya Narendra Modi ya sanar da batun soke dokoki uku da suka shafi noma waɗanda aka shafe shekara ana taƙaddama a kansu. Dubban manoma ne suka yada zango a kan iyakar Delhi tun Nuwambar bara kuma gwammai daga cikinsu sun rasu sakamakon zafi da sanyi da kuma annobar korona. Manoman sun ce dokar za ta ba wasu masu zaman kansu damar su shigo harkar noman kuma hakan zai iya kawo cikas ga ribar da suke samu. Sanarwar da firaiministan ya fitar a ranar Juma'a mai ban mamaki tamkar an yi amai ne an lashe ganin cewa gwamnatin ƙasar ba ta fito da wasu tsare-tsare ba na tattaunawa da manoman a cikin yan watannin nan. Haka kuma ministocin Mista Modi sun yi ta dagewa kan cewa wannan tsarin yana da kyau ga manoma kuma babu amfanin yanye dokokin. Ƙungiyoyin manoma na kallon wannan mataki a matsayin babbar nasara. Sai dai masana na ganin cewa zaɓen jihohin da za a yi a Punjab da Uttar Pradesh ne ya sa aka soke dokar ganin cewa akwai manoma dayawa daga wurin. Sanarwar da aka yi a safiyar Juma'a na zuwa ne a ranar da masu bin addinin Sikh - waɗanda su ke da rinjaye a Punjab - ke murnar zagayowar ranar haihuwar Guru Nanak wanda shi ne ya ƙirƙiro addinin Sikh. Me dokokin suka tanada? Duka dokokin sun kawo sauyi a ɓangaren sayar da amfanin gona da farashinsu da yadda za a ajiye su - inda ake ganin sabbin dokokin na barazana ga tsoffin dokokin da suka kare manoman Indiya na tsawon shekaru. Daga cikin manyan sauye-sauyen akwai batun da ake cewa manoman za su iya sayar da kayayyakinsu ne kaɗai a farashin da aka ƙayyade ga yan kasuwa masu zaman kansu - da suka haɗa da masu sayen kayan gona da manyan shaguna da kuma masu sayar da kayayyaki ta intanet. Akasarin manoman Indiya na sayar da kayayyakinsu ne ga kasuwannin dillalai da gwamnati ke da iko a kansu. Dokokin za su bayar da dama ga ƴan kasuwa masu zaman kansu su ɓoye kayayyaki kamar su shinkafa da alkama domin su sayar a gaba, wanda a baya waɗanda gwamnati ta amince mawa ne kaɗai za su iya haka. Irin waɗannan sauye-sauyen, aƙalla a rubuce kan takarda zai bai wa manoma damar sayar da kayayyakin su a kasuwannin yankuna. Sai dai masu zanga-zangar sun bayyana cewa waɗannan dokokin za su sanyaya gwiwar manoma da kuma barin ƴan kasuwa masu zaman kansu su fitar da farashinsu da kuma iko da manoman. Sun ce kasuwannin yankunan da suke da su ne ke taimaka wa manoman, waɗanda su ke taimaka musu su ci gaba da rayuwa. Sun bayyana cewa dokokin Indiya da suka shafi sayar da kayayyakin gona sun taimaki manoma daga ƴan kasuwa na tsawon shekaru kuma babu amfanin sauya dokokin. Sai dai gwamnatin ƙasar ta kafe kan cewa lokaci ya yi da ya kamata a ci riba da noma ko ma ga ƙananan manoma kuma sabbin dokokin da aka kawo za su tabbatar da hakan. Mista Chaudhary na daga cikin ɗaruruwan manoma waɗanda suke yajin aiki a kan iyakar Delhi da Ghazipur sama da shekara guda. Rakesh Tikait ne ya yi magana a madadinsa, wanda shi ma wani sannanen manomi ne wanda ya ce za su janye yajin aikin ne kaɗai idan an soke dokokin a lokacin hunturu a majalisa. Wannan sanarwar ta dugunzuma masu sa ido kan harkokin siyasa a kuma waɗanda suke adawa da kuma goyon bayan waɗannan dokoki - mutane da dama sun wallafa saƙonni a shafukan Twitter inda suka ce wannan babbar nasarar ce ga manoma. Sai dai wasu shugabannin manoma da kuma masu fashin baƙi kan tattalin arziƙi waɗanda suka hangi alfanun da ke cikin dokokin sun nuna rashin jin daɗinsu kan soke dokokin. Anil Ghanwat, wanda shi ne shugaban ƙungiyar manoma a yammacin Indiya, ya bayanna cewa matakin abin takaici ne kuma siyasa ce ta jawo hakan. Jam'iyyun adawa sun yi maraba da wannan matakin inda shugaban jam'iyar Congress Party, Rahul Gandhi ya kira wannan lamari da ""nasara kan rashin adalci. Haka ma Babban ministan Yammacin Bengal, Mamata Banerjee ta je shafukan sada zumunta inda ta jinjina wa manoma. Mambobin Jam'iyyar BJP mai mulki a ƙasar sun bayyana cewa matakin da aka ɗauka na dakatar da dokokin ba shi da wata alaƙa da zaɓe mai zuwa kuma an ɗauki matakin ne domin kawo ƙarshen zanga-zangar da ake yi. Haka kuma ba su bayyana ko akwai niyyar dawo da dokokin a nan gaba ba. Matakin da gwamnatin Narendra Modi ta ɗauka na soke waɗannan dokoki, ana ganin cewa wani mataki ne da dabara ce a siyasance kuma tamkar gwamnatin ta yarda cewa ta yi azarɓaɓi ne wajen yin dokar. Waɗannan dokokin sun jawo zanga-zanga a jihohin Punjab da Uttar Pradesh haka kuma sun kasance babban ƙalubale ga Modi. Sun tattara manoma da ƙungiyoyi masu zaman kansu a mabiya addinin Sikh mai rinjaye a Punjab da kuma bazuwa a yankunan Uttar Pradesh, jihohin da za a gudanar da zaɓe ba da daɗewa ba. Jam'iyyar BJP, wadda ba ta taɓa tsammanin za ta fuskanci wannan matsala ba, na ta ƙoƙarin shawo kan mabiya addinin Sikh. Kusan duka tarurrukan da jam'iyyar ta yi a watan nan an gudanar da su ne domin kwnatar da hankalin mabiya addinin: ta hanyar ƙara kasafin kuɗi noma da kuma farashin amfanin gona, da sake buɗe ɗaya daga cikin manyan wuraren tarihi na mabiya addinin Sikh a Pakistan da kuma ƙaddamar da sabon bincike kan waɗanda suke da hannu a zanga-zangar ƙin jinin mabiya addini Sikh da aka yi a 1984. Gwamnatin ƙasar tana fargabar ƙara tara maƙiya daga bangaren ƴan Sikh kan waɗannan dokoki. Ta hanyar soke waɗannan dokoki, Mista Modi na da burin sake samun amincewar manoma musamman mabiya addinin Sikh. Haka kuma matakin zai ƙara jawowa Jam'iyyar BJP a zaɓe mai zuwa. Ga waɗanda suka goyi bayan wannan doka, hakan babban darasi ne da ke nuna cewa tattalin arziƙi mai kyau a wani lokaci ya zai zama siyasa ga manoma. Ƙungiyar Samyukta Kisan Morcha, wadda ƙungiya ce da ke da manoma 40, ta ƙi yarda ta janye yajin aikinta duk da roƙon da gwamnati ke yi na dakatar da zanga-zangar su. Manoman sun ci gaba da toshe hanyoyi da ke zuwa Delhi a lokacin hunturu da bazara har a lokacin da ake tsaka da fama da matsananciyar annobar korona . Sun ta kiran a yi yajin aiki a faɗin ƙasar haka kuma gwammai daga cikinsu sun mutu. Tun a farko dai gwamnatin ƙasar ta soma tattaunawa da su da kuma ƙoƙarin amfani da dokar ta wucin gadi na shekara biyu. Amma bayan da manoman suka yi watsi da hakan, hukumomin sai suka janye kudirin nasu inda suka ce bari su zura ido su ga ƙarshen yajin aikin manoman. Sai dai abubuwa biyu sun sauya lamarin a watannin da suka gabata. Na farko, ana zargin ɗan ministan tarayyar ƙasar da kutsa motarsa cikin masu zanga-zangar a Lakhimpur da ke Uttar Pradesh a watan Oktoba Ya musanta zargin da ake yi masa amma an kama shi. Mutum takwas ciki har da manoma biyu da ɗan jarida suka mutu a lamarin wanda ya jawo ɓacin ran jama'a a faɗin ƙasar. Na biyu kuma Jam'iyar BJP na ƙoƙarin yaƙi da manyan jam'iyyun adawa na yankuna a zaɓe mai zuwa da za a yi a Punjab da Uttar Pradesh haka kuma ana ganin cewa manoma waɗanda suke cikin ɓacin rai za su iya jawo cikas ga Jam'iyyar BJP a zaɓen da ke tafe" https://www.bbc.com/hausa/labarai-59344547 +business An nemi a ƙara ɗagewa ƙasashe matalauta lokacin biyan bashi "Shugaban Bankin Duniya ya yi gargaɗin cewa annobar korona na ƙara haddasa wata matsalar nauyin bashi ido rufe ga ƙasashe masu tasowa. David Malpass ya yi wannan jawabi ne yayin wani taron ministocin kuɗi na ƙungiyar ƙasashen G20 ta hanyar intanet. Ya ce nauyin basukan da ke kan ƙasashe matalauta na ƙaruwa zuwa wani mataki na tagayyara. Don haka Mista David Malpass ya buƙaci ƙungiyar G20 ta ƙasashen da ke kan ganiyar bunƙasar tattalin arziƙi su tsawaita matakin jingine biyan basukan da suka amince da shi a baya da ƙarin shekara ɗaya. Mai masaukin baƙi ministan harkokin Saudiyya, Mohammed Al Jadaan, ya ce annobar ta haifar da wani ƙalubale da ya karaɗe duniya. A cewarsa ƙungiyar ƙasashen na aiki cikin hanzari don tunkarar tasirin da cutar ta haddasa wa tattalin arziƙi. Annobar kobid-19 ta zama wata matsala mafi girma da ke fuskantar tattalin arziƙin duniya tun daga lokacin Gagarumar kiɗimewar duniya a shekarun 1930, in ji shi ""Don kai ɗauki game da haliin da aka shiga saboda wannan annoba, ƙasashen G20 na ɗaukar matakai namusamman kuma cikin hanzari wajen tunkarar al'amarin wannan annoba da kuma yadda ta yi tasiri cikin harkokin lafiya da na zamantakewa da ma tattalin arziƙi, ciki har da matakan daidaita harkoki da tsare-tsaren al'amuran kuɗi."" Ministan yYa kuma bayyana fatan ƙasashen za su amsa kiran Bankin Duniyar ta hanyar ci gaba da jingine biyan basukan: ""Mun fahimci tasirin abin da kuma rashin daidaiton shi kansa tasirin, da cutar kobid-19 ta haddasa kuma a gaskiya ta fi haifar da lahani ga ƙasashe masu rauni don haka muke son samar da tallafi. Mun ɗauki matakai cikin hanzari kuma na tarihi a wannan ƙungiya ta G20 lokacin da muka bijiro da shirin dakatar da biyan basukan. Kuma ban ga abin da zai hana wannan yunƙuri ci gaba ba""." https://www.bbc.com/hausa/labarai-53462170 +business Yadda India ta taso keyar 'yan Najeriya 196 zuwa gida "Kasar Indiya ta taso keyar wasu 'yan Najeriya kusan dari biyu da sauka hada da maza da mata da kananan yara zuwa gida, sakamakon rashin gamsuwa da yanayin zamansu a kasar ta Indiya. A maraicen jiya Juma'a ne hukumomin Najeriya suka karbi wadannan mutane a Abuja, babban birnin tarayyar kasar, wadanda hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar, wato NEMA, ta yi dawainiyar kwaso su daga Indiyar. Bashir Idris Garga, babban jami'in kai dauki na hukumar ta NEMA, ya yi wa BBC karin bayani. ""Akwai wasu 'yan Najeriya da ke zaune a Indiya, wadanda hukumomin kasar ba su gamsu da zamansu ba, ko kuma sun zama musu damuwa a kasar. Wannan ne yasa suka bukaci gwamnatin Najeriya ta gaggauta dawo da su gida."" Ya ce Najeriya ta dauki matakin kwaso 'yan Najeriyan su 196 zuwa Abuja. ""Maza ana da 152, sannan mata ana da 44, ciki har da kananan yara su biyar, kuma yawancinsu ba su wuce shekara biyar da haihuwa ba."" Bashir Garga ya kuma bayyana matakan da aka dauka na binciken lafiyar 'yan Najeriyan da aka kwaso daga Indiya. ""An binciki lafiyarsu domin a kuma a tabbatar da ba su shigo mana da wasu cututtuka ba. Sauran hukumomi kamar na shige da fice ma sun duba su, sannan a karshe aka ba kowannensu dala 100 ta Amurka domin su yi kudin mota zuwa garuruwansu na asali."" Sai dai jami'in na NEMA ya tabbatar wa BBC cewa yawancin 'yan Najeriyan 'yan asalin jihohin kudancin Najeriya ne, amam akwai wasu kadan cikinsu daga yankin arewacin kasar. Ya kara da cewa hukumomin kasar Indiya sun koro wadannan 'yan Najeriyan ne saboda dalilai kamar na takardun zama da suka kare amma ba su sabunta su ba. Sai dai ya ce har zuwa wannan lokaci, akwai wasu 'yan Najeriyan da ba a kwaso ba saboda suna da wasu batutuwan da ba su kammala yi ba kamar sauke nauyin wata hidima da gwamnatin Indiya ta yi musu kamar biyan kudaden da aka kashe a kansu, ko biyan wani bashi da ke kansu kafin a bari su koma Najeriya." https://www.bbc.com/hausa/articles/cmlk7wmv1pxo +business Wasu 'yan Najeriya na caccakar ma'aikatan wutar lantarki kan yajin aiki "Wasu 'yan Najeriya, musamman masu amfani da shafukan sada zumunta, sun harzuka sakamakon matakin da ma'aikatan wutar lantarkin kasar suka dauka na tafiya yajin aiki. Sun fara yajin aikin ne ta hanyar hana shiga da fita a hedikwatar kamfanin dillancin wutar lantarkin na Najeriya TCN a Abuja, babban birnin ƙasar ranar Laraba da safe. Sun kashe makunnan lantarki a ofisoshin da ke faɗin ƙasar, domin bijire wa umarnin da hukumar da ke sanya ido kan harkokin wutar lantarki ta bayar ga wasu shugabannin riko domin yin jarrabawar karin girma. A watan sanarwa da Sakatare Janar na kungiyar ma'aikatan wutar lantarki, Mista Joe Ajaero ya sanya wa hannu ya umarci dukkan ma'aikatan wutar lantarki su yi zanga-zanga a hedikwatar ma'aikatar wutar lantarki da rassanta da ke fadin kasar saboda umarnin cewa dole su yi ""jarrabawar karin girma."" Ma'aikatan kamfanin dillancin lantarkin na son a dakatar da tsarin aikin da ake bi na ci gaban ma'aikata. Mista Ajaero ya kara da cewa matakin ya saba wa dokokin aiki kuma an dauke shi ne ba tare da dukkan masu ruwa da tsaki ba. Sai dai daga bisani Joe Ajaero ya ce ""An janye yajin aikin da aka fara na mako biyu. A wannan daren, wuta za ta dawo."" Ya bayyana haka ne bayan sun gana da Ministan Kwadago, Chris Ngige, wanda ya sha alwashin duba korafe-korafen 'yan kungiyar. Shi ma Ministan Harkokin Lantarki Abubakar Aliyu ya ce batutuwan da ake taƙaddama a kansu na batun ɗaukar aiki ne da suke cikin hurumin shugaban ma'aikatan gwamnati na Najeriya ba ma'aikatar lantarki ba. 'Rashin sanin ya kamata' Sai dai 'yan kasar sun yi kakkausan suka kan ma'aikatan wutar lantarkin bisa abin da suka kira rashin sanin ya kamata da rashin duba halin da kasar ke ciki na kunci. Maudu'ai irin su #NEPA da PHCN da #electricity na cikin batutuwan da aka fi tattaunawa a kansu a shafin Twitter ranar Laraba zuwa Alhamis. An rika amfani da maudu'an wajen nuna irin rashin bin doka da ke faruwa a Najeriya. Wani fitaccen mai amfani da Twitter, Dr Joe Abah, ""Gaskiya ban taba ganin wata kasa da mutane za su je su kashe makunnin wutar lantarki saboda ba sa so a yi musu jarrabawar karin girma ba, kuma ba a kama su an daure su nan take ba."" Shi ma Gimba Kakanda cewa ya yi bai ga wata hikima ba a matakin da ma'aikatan wutar lantarki suka dauka na kashe makunnin wutar lantarkin kasar kawai saboda an umarce su su yi jarrabawar karin girma. Ita kuwa Zahrah Musa ta ce kashe makunnin wutar lantarkin wani zagon-kasa ne da ma'aikatan suka kitsa ga gwamnatin Najeriya tana mai yin kira ga Shugaba Buhari ya dauki mataki a kansu ""domin kuwa ba su fi karfin Najeriya ba.""" https://www.bbc.com/hausa/labarai-62588095 +business Tallafin Covid-19: Ana buɗe wa ƙananan ƴan kasuwa kamfani kyauta don samun tallafin Buhari Gwamnatin Najeriya ta fara yi wa mutane rijistar kamfani kyauta domin samun tallafin rage raɗaɗin da suka samu kansu a ciki sakamakon annobar cutar korona. Tallafin na gwamnatin tarayya ya shafi bai wa ƙananan ƴan kasuwa jarin naira 250,000 domin damar yin rijistar kasuwancinsu. A ranar Litinin hukumar CAC da ke kula da rijistar kamfanoni ta fara aikin na yi wa mutane rijistar kamfani kyauta, kuma hukumar ta bayyana a shafinta na intanet cewa jami'anta za su shafe tsawon wata uku suna aikin rjistar. Gwamnati ta ce dole kafin mutum ya samu tallafin wanda aka ware naira biliyan 75 domin farfaɗowa da bunƙasa masu kanana da matakaitan masana'antu a Najeriya, dole sai yana da kamfani. Hukumar CAC ta ce gwamnatin Najeriya ta amince a yi wa mutane rijistar kamfani kyauta a jihohin ƙasar 36 haɗi da Abuja. A Najeriya akwai kudi da dole sai mutum ya biya kafin a bude masa kamfani a hukumar CAC da ke kula da rijistar kamfanoni. Tallafin Covid-19: Ga yadda za ku samu tallafin Buhari na biliyan 75 ga ƴan kasuwa Ga abubuwa da suka kamata ku sani game da tsarin gwamnati na yi wa mutane rijistar kamfani kyauta: Gwamnatin tarayya ta amince a yi wa mutum 6,606 rijistar kamfani kyauta a jihohi 34 na ƙasar. Amma a Kano adadin mutum 8,406gwamnati ta amince a yi wa rijistar kamfani kyauta, jihar Legas kuma mutum 9,084, sai jihar Abia mutum 7,906. Gwamnantin ta ce wannan dama ce ga dukkanin masu sha'awar yi wa kasuwancinsu rijista musamman masu sana'o'in hannu domin inganta kasuwancinsu a hanyoyin da suka kamata. Hukumar CAC ta ce kowa yana da damar zuwa a yi masa rijistar kamfaninsa a kyauta Amma tsarin kuma ya shafi gwamnatocin jihohi da za su gabatar da sunayen wadanda suke so a yi masu rijista. Mutum ɗaya ko biyu suna iya rijistar kamfani na haɗin guiwa tsakaninsu. Ana buƙatar mutum ya zabi sunaye uku ga wanda ke son yin rijistar kamfaninsa A ciki za a zaɓi suna ɗaya amma sai idan ya kasance babu wanda ke amfani da sunan a matsayin kamfani Ana buƙatar adreshi na gida ko na kamfani Mutum zai faɗi irin kasuwancin da yake so ya yi kamar tela ko kanikanci ko duk irin sana'ar da yake yi. Ana buƙatar hoto guda biyu da lambar waya da kuma adireshin imel idan mutum yana da shi. Ana kuma buƙatar katin sheda, kamar katin ɗan ƙasa ko na lasisin tuƙi ko fasfo ko kuma katin zaɓe. Hukumar CAC ta ware cibiyoyin yin rijistar a dukkanin jihohi, kuma za a iya ziyartar reshenta na jihohi. Hukumar ta kuma wallafa sunayen jami'anta da ke jagorantar aikin rijistar a dukkanin jihohi da lambobinsu na salula da za a iya tuntuba, wanda za ku iya samu idan kuka danna nan Za a ci gaba da rijistar har zuwa watan Disamban shekarar nan. Wannan naira biliyan 75 ɗin za a bai wa ƙanana da matsakaitan masana'antu ne don su samu damar biyan ma'aikatansu ko duk wani da ke aiki da su. Gwamnati ta ce za a raba kuɗin ne ga masana'antu miliyan 1.3 da ƴan kasuwa 35,000 a kowace jiha daga cikin 36 na ƙasar da kuma babban birnin ƙasar Abuja. Gwamnatin Najeriya za ta bai wa mutum 250,000 damar yin rijistar kasuwancinsu kyauta. zangon farko na wannan tallafi, zai ɗauki wata uku. Dokoki https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-54697938 +business Dabarar da sojojin Mali suka yi wa Ecowas ta janye musu takunkumi Sojojin da ke mulki a Mali sun yi nasarar janyo hankalin ‘yan kasar tare da tayar musu da tsimi na kishin kasa. Sun yi nasarar sanya shugabannin kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma, Ecowas, sun janye takunkumin da suka sanya wa kasar, sakamakon juyin mulkin da suka yi, kamar yadda Paul Melly ya yi nazari. Bayan tsayar da watan Fabrairu na 2024 a matsayin lokacin da za su gudanar da zabe, gwamnatin sojin ta Mali ta yi nasarar shawo kan Ecowas ta cire mata takunkumin da ta sanya wa kasar. Ga talakawan Mali, musamman mazauna babban birnin kasar Bamako, wadanda yawancinsu sun dogara ne da kayan abincin da ake shigarwa kasar daga waje, wannan labari ne mai dadin ji a gare su. Ko da yake  matakin ba wai yana nufin dakatar da shigar da kayan masarufi ba ne, a zahiri wani karin nauyi ne ga ‘yan kasuwa da iyalai, wadanda suke fama da tsadar kayan abinci da mai da duniya ke fama da ita a yanzu, sakamakon bukatarsu da ta karu a duniya saboda annobar korona da yakin Ukraine. An sanya wa kasar takunkumin ne a watan janairu bayan da sojojin da suka kwace a mulki suka sanar da jinkirta mayar da kasar hannun farar-hula da shekara hudu. A yanzu sun rage wannan wa’adi da kasa da shekara biyu, inda za a yi zabe a watan Fabrairu na 2024. Shugabannin Ecowas sun amince da wannan mataki a yayin taron kolinsu da suka yi a babban birnin Ghana, Accra a karshen mako. Wannan ba karamar nasara ba ce ga gwamnatin sojin ta Mali kadai har ma ita kanta Ecowas, wadda yawancin ‘yan Mali da sauran mutane ke wa kallon gungu ne na shugabannin kasashe masu ji da kai, wadanda ke yi wa sojoji masu juyin mulki kallon hadarin-kaji, su kuma su kawar da kai daga laifukansu. Shugabannin mulkin soji na Mali da Firaministan kasar Choguel Maïga sun yi dabara inda suka tafi a kan doron wannan kallo da ake yi wa shugabannin na Ecowas, inda suke nuna wa al’ummar kasar cewa su masu kishin kasarsu ne tare da kare ta da jama’arta daga makwabtansu masu cin zali. Makwabtan da ba sa maraba da duk wani yunkuri na samar da gagarumin sauyi a kasar da  shugabanninta da suka babbake al’amura suka kasance cikin almundahana da rashawa iya wuya. A cikin watanni shida da suka gabata duk wani sako mai tsauri da ya fito daga Ecowas ko Turai ko kuma Majalisar Dinkin Duniya, yana haduwa da tirjiya da kakkausar suka daga al’ummar Mali. A tsakiyar watan Mayu, gwamnatin sojin ta sanar da cewa za ta fice daga kungiyar G5 Sahel, wadda aka kirkira a 2014, domin yaki da masu ikirarin jihadi. Gwamnatin sojin ta ci gaba da mu’amalarta da kamfanin tsaron nan na kasar Rasha Wagner, duk da irin zargin da ake yi wa kamfanin kan yadda sojojin hayarsa ke take hakkin dan-Adam da cin zarafin farar-hula. Tabarbarewar mu’amala tsakanin kasar da Faransa da kuma sauran kasashen Turai, inda Faransa ta sanar da janye sojojinta da ta kai domin yakar masu ikirarin jihadi, janyewar da sojojin za su kammala a wata mai zuwa. Haka kuma a halin da ake ciki sojojin na Mali sun tsaurara dokokinsu a kan sojojin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya, da ake kira Minusma. Sun hana masu bincike kan cin zarafi da sauransu na jama’a, kamar wanda ake yi wa sojojin haya na kamfanin na Rasha da sojin kasar, na kashe mutane kusan 300 a kauyen Moura a karshen watan Maris. Duk da wannan tirjiya ta sojin na Mali, suna nasara sannu a hankali wajen wanzar da shirinsu na siyasa, wanda Ecowas ka iya yarda da shi. Da farko shugabannin kasashen Afirka ta Yamma sun so sun una dan sassauci. Wakilinsu a kan rikicin Mali, kuma tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, ya rika kai gwauro yana kai mari a Mali. Sai dai kuma daga bisani kungiyar ta Ecowas ta ga ya kamata ta taka birki kan yadda ake samun yawan juyin mulki a yankin, wanda kafin yanzu zai yi tunkahon cewa yawancin kasashensa na karkashin mulkin farar-hula ne na jam’iyuyu da dama. An samu juyin mulki na biyu a watan Mayu na shekarar da ta gabata, bayan na farko  na watan Agusta 2020. Sai kuma ga Guinea, ita ma a watan Satumba Kanar Mamady Doumbouya ya hambarar da gwamnatin Shugaba Alpha Condé. Haka ita ma Burkina Faso, a watan Janairu sai kwatsam sojoji suka hambarar da Shugaba Roch Marc Christian Kaboré, wanda aka zaba a wa’adi na biyu a karbabben zabe, watanni 14 baya, saboda zargin gazawar gwamnatin na dakile yawan hare-haren masu ikirarin jihadi. Daga nan sai kuma aka samu abin da ake kallo a matsayin wani yunkuri na juyin mulki da bai yi nasara ba a Guinea-Bissau. Mutane goma sha daya ne suka rasa ransu, yayin da sojojin da ke biyayya ga Shugaba Umaro Sissoco Umbaló suka yi nasarar kawar da masu yunkurin kawar da shi daga mulkin, da suka kai hari fadar gwamnatin kasar. Akwai kuma jita-jitar cewa wasu kasashen ma na yankin na Afirka ta Yamma za su iya bin sahu na juyin mulkin na soji. Saboda haka wajibi ne Ecowas ta dauki matakin taka birki ga wannan ta’ada ta hambarar da gwamnatocin farar-hula. Haka kuma dole ne kungiyar ta samu yadda za ta sake mayar da wadancan kasashe kan mulkin farar-hula, kasashen da suka hada da Mali da Guinea da kuma Burkina Faso. Wannan ba wai kawai domin amfanin mulkin farar-hula a yankin Afirka ta Yamma ba kawai, saboda cewa ita Mali tana tsakiyar rikicin yankin Sahel da kuma kokarin dakile tashin hankalin kungiyoyin mayaka da rikicin kabilu a yankin. A don haka ci gaba da mayar da kasar saniyar-ware ba abin da zai ta’zara sai wadannan rikice-rikice da kuma matsin lamba da gwamnatocin kasashe a yankin ke sha na karancin abinci da sauyin yanayi. Sannu a hankali gwamantin sojojin ta Mali, na daukar matakan sasantawa da kuma samun karbuwa da ke tabbatar wa da kungiyar Ecowas cewa da gaske suke. Daga cikin matakan akwai sabuwar dokar zabe da samar da hukumar zabe da kuma bayani ko matakan mayar da kasar kan mulkin farar-hula, muhimma ma daga cikinsu shi ne fitar da jadawalin gudanar da zaben shugaban kasa a watan Fabrairu na 2024. To amma duk da haka kuma akwai rashin tabbas na cewa ko tsarin zai hana shugaban mulkin sojin kasar na yanzu Assimi Goïta, tsayawa takara. Ko ma dai mene ne, alamun da aka gani na mayar da kasar mulkin dimokuradiyya zuwa yanzu sun ba wa Ecowas karfin halin ci gaba da tattaunawa da shugabannin sojin na Mali, a kan sauran bayanan da suke bukata. Wannan ya sa shugabannin na kasashen Afirka ta Yamma suka yanke shawarar cewa, ya kamata su dage takunkumin da suka sanya wa kasar. Kuma suna ganin hakan ko ba komai wata galaba ce a wurinsu, wadda kuma za ta kai ga dawowa daga turbar da ake kai ta yin fito-na-fito da shugabanin sojin na Mali da ke nuna kansu a matsayin ‘yan kishin kasa, da kuma makwabtanta. Wannan kuwa suna ganin abu ne da ake matukar bukata a yankin da ke fama da matsaloli da dama. Da hakan ne kuma shugabannin na Ecowas suka cimma yarjejeniya da shugabannin soji na Burkina Faso, wajen samar da jadawalin mayar da kasar kan mulkin farar-hula a watan Yuli na 2024. Ecowas na fatan wannan nasara da ta yi a tsakanin da wadannan shugabanni na soji, zai karfafa wa suma sojin Guinea su bi sahu. Hakan ya sa kungiyar ta zabi tsohon shugaban kasar Jamhuriyar Benin Thomas Boni Yayi a matsayin mai shiga Tsakani, domin tattaunawa da hukumomin sojin na  Conakry. https://www.bbc.com/hausa/articles/c1e9de2pqy0o +business Kasafin Kuɗin Najeriya na 2021: Buhari ya gabatar wa majalisa kasafin naira tiriliyan 13.08 Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kuɗin ƙasar kimanin naira tiriliyan 13.08 na shekarar 2021 a gaban Majalisar Dokokin ƙasar - a zaman hadin gwiwa tsakanin majalisar dattawa da ta wakilai. Hasashen kuɗin ya fi na bara da tiriliyan 2.28, inda na baran ya kasance naira tiriliyan 10.805. A yayin da yake gabatar da kuɗin Shugaba Buhari ya ce samun kuɗaɗen shiga don amfani da su wajen kasafin kuɗin shi ne babbar matsalar da gwamnatinsa ke cin karo da shi. Sannan kuma ya ce ministoci za su dinga sa ido don tabatar da cewa hukumomin karɓar kuɗaɗen haraji na ayyukansu yadda ya kamata. Shugaba Buhari ya bayyana ƙudurin kasafin kuɗin da cewa na farfaɗo da tattalin arzikin kasa ne, bisa la'akari da ƙalubalen da Najeriya, kamar sauran kasashen duniya ta fuskanta daga annobar korona, wadda ta durƙusar da tattalin arziki ta ɓangarorin rayuwa daban-daban. Kuma wannan ya sa gwamnati ta zurfafa tunani wajen tsara hanyoyin raya tattalin arzikin da kasafin kuɗin da ake sa ran zai ci mukuɗan kudaɗe. Shugaba Buhari ya bayyana ƙudurin kasafin kuɗin da cewa na farfaɗo da tattalin arzikin kasa ne, bisa la'akari da ƙalubalen da Najeriya, kamar sauran kasashen duniya ta fuskanta daga annobar korona, wadda ta durƙusar da tattalin arziki ta ɓangarorin rayuwa daban-daban. Kuma wannan ya sa gwamnati ta zurfafa tunani wajen tsara hanyoyin raya tattalin arzikin da kasafin kuɗin da ake sa ran zai ci mukuɗan kudaɗe. Ana jimullar kuɗin da gwamnatin tarayya za ta kashe a shekara mai zuwa da ya kai naira tiriliyan goma sha uku, da miliyon dari takwas, wanda ya hada da naira tiriliyin biyar da naira biliyan sittin da biyar da za a kashe a kan harkokin gudanarwa na yau da kullum. Da albashin ma'aikata da ya ki naira tiriliyon uku da biliyon saba'in da shida, da kuma naira tiriliyan uku da biliyon goma sha biyu na ɗawainiyar biyan bashi. Wasu hidimomin da za su lashe biliyoyin naira, ciki har da biyan kudin fansho da sauran wajiban da suka rataya ga wuyan gwamnati. Shugaban Najeriyar ya bayyana cewa an tsara kudurin kasafin kudin ne ta hanyar ƙeƙe-da-ƙeƙe, wato sai da aka lura da samun gwamnati ta fuskar kudin-shiga, da rance ko bashin da za ta ciwo da kuma tallafin da za ta yi, ko wanda zai shiga hannunta. Kuma wannan ne ma ya sa gwamnati ta ƙiyasta farashin gangar mai a kan dala 40. Shugaba Buhari ya jaddada cewa gwamnati ta duƙufa wajen fitar da 'yan Najeriya miliyan 100 daga ƙangin talauci nan da shekara 10 masu zuwa. Ya gabatar da kasafin ne da misalin ƙarfe 11 na safiyar Alhamis. Rahotanni sun ce an jibge jami'an tsaro da yawa a harabar Majalisar Dokokin da ke Abuja, inda Shugaba Buharin ya gabatar. Jaridar Punch ta ruwaito cewa cikin jami'an tsaron da aka kai har da na hukumar tsaro ta farin kaya da ƴan sanda da na hukumar hukumar tsaron farin kaya da kare al'umma wato Civil Defense da na hukumar kare afkuwar haɗura. Sannan an rage yawan masu shiga cikin majalisar. An yi zaman majalisar lafiya-lafiya ba tare da wata turjiya daga wajen 'yan majalisar ba, kuma wannan bai ba da mamaki ba, idan aka yi laka'ari da irin dasawar da bangaren zartarwa ke yi da na majalisar dokokin. Shugaban majalisar dattawa, Senata Ahmed Lawan, ya tabbatar da wa shugaban kasar cewa da majalisar dattawa da ta wakilai duka za su gaggauta zartar da kasafin kudin, kamar yadda suka yi bara. ''Mun yi maka alkawari da 'yan Najeriya cewa mun shirya, kuma mun duƙufa wajen nazari da zartar da kasafin kudin nan da karshen shekara. ''Muna la'akari da cewa yin hakan ya zama wajibi domin mun kawar da yanayin nan na rashin tabbas da ke tattare da aiwatar da kasafin kudi, wanda ya yi illa ga tattalin arzikinmu a shekarun da suka wuce, ta yadda za mu dore da shekarar kasafin kudin aka fi so, mai farawa daga watan Janairu, ya kare a watan Disamba. Shugaban Najeriyar ya shaida wa 'yan majalisar dokokin cewa, jawabin da ya yi taƙaitacce ne, don haka ma'aikatar kudi ce za ta yi cikakken bayani a kan duk wani ƙabli da badin da kasafin kudin ya ƙunsa. Tun da farko a ranar Laraba shugaban kwamitin kasafin kuɗi na Majalisar Dattijan Najeriya Sanata Barau Jibril ya ce, gabatar da kasafin kuɗin na wannan shekarar zai sha bamban da na sauran shekaru sakamakon annobar cutar korona. A cewarsa, za a bi ƙa'idojin kare yaɗuwar cutar da kuma yin tanadi ta yadda ba za a samu cunkoso ba yayin gabatar da kasafin kuɗin, hakazalika ba za a daɗe wurin gabatar da kasafin kudin ba kamar yadda ake yi ba a da. An dai ɗora ƙudurin kasafin kuɗin na 2021 kan hasashen musayar dalar Amurka ɗaya ga naira 379 da kuma mizanin gangar man fetur guda a kan dala 40, bisa hasashen haƙo ganga miliyan 1.86 a kullum. A bara dai an amince da kasafin kudin ne kan hasashen musayar dalar Amurka ɗaya ga naira 305, haka kuma an saka mizanin gangar man fetur guda a kan dala 57, bisa hasashen haƙo ganga miliyan 2.18 a kullum. An sa ran shugaban yayin gabatar da kasafin kuɗin a ranar Alhamis, zai nanata wasu kalaman ministar kuɗin ƙasar wadda ta bayyana cewa ƙudirin kasafin 2021 yana cike da burin bai wa ƙasar damar samun bunƙasa ta kowane ɓangare da kuma zaburar da tattalin arziƙin Najeriya da samar da ayyuka. Kalaman nata sun kuma haɗa da yauƙaƙa bunƙasar ƙasar, da samar da hanyoyin zuba jari ga ababen more rayuwa, da inganta masana'antu da sana'o'in cikin gida. Sannan an sa ran wannan kasafin kuɗin na 2021 zai jaddada hasashen samun jumullar kuɗin shiga naira tiriliyan 7.89 da kuma ƙunshin kasafin kamfanoni 60 mallakar gwamnati. A bara dai, Shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ya sanya hannu a kan kasafin kuɗin ƙasar na shekarar 2020, wanda ya kai naira tiriliyan 10,594,362,364,830. https://www.bbc.com/hausa/labarai-54461767 +business Iran ta sake 'kwace jirgin da ke fasa-kaurin mai' "Kasar Iran ta sake tare wani jirgin dakon mai na kasashen waje a yanking Gulf, kamar yadda gidan talbijin din kasar ya sanar. An rawaito kwamandan sojojin kundumbala na juyin juya-halin kasar yana cewa sojojinsu na ruwa ne suka ""kwace jirgin mai dauke da mai domin yin fasakauri zuwa wasu kasashen labarawa"", a yankin Gulf. Ya ce jirgin na dauke da litar mai dubu 700, inda ya kara da cewa sun kuma tsare matuka jirgin guda bakwai. Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da ake ci gaba da tayar da jijiyoyin wuya kan jerin takunkuman da Amurka ta kakaba wa man kasar Iran. Amurka ta sanya takunkuman ne dai bayan da ta sanar da ficewa daga yarjejeniyar da aka rattaba wa hannu a 2015 kan dakatar da ayyukan samar da makaman nukiliyar iran. Wannan ne karo na biyu da Iran take zargin wani jirgin ruwa da fasakaurin mai. A watan da ya gabata ne dai Iran ta kwace jirgin kasar Burtaniya a ruwan in the Strait of Hormuz. Amurka ta dora alhakin kai harin bam a kan wasu jiragen dakon mai guda biyu a yankin Gulf a watannin Mayu da Yuni, zargin da Iran din ta sha musantawa. Latsa alamar bidiyo da ke kasa domin kallon yadda sojojin Iran suka ""kwace jirgin da ke fasa-kaurin mai""." https://www.bbc.com/hausa/labarai-49222329 +business Abu biyar game da sabon mai kuɗin duniya Arnault da ya sauke Elon Musk A makon da ya gabata ne Elon Musk ya sauka daga matsayi na ɗaya a jerin masu arziki na duniya baki ɗaya bayan raguwar darajar hannun jari a kamfaninsa na Tesla. A cewar mujallun Forbes da Bloomberg, Bernard Arnault ne ya sauke Mista Musk daga matsayin, wanda shi ne shugaban kamfanin ƙera kayan ƙasaita na LVMH. Mista Musk ne ke da mafi girman hannun jari a kamfanin ƙera motoci masu aiki da lantarki na Tesla, inda yake da kashi 14 cikin 100. A cewar Forbes, dukiyar Mista Musk yanzu tana wajen dala biliyan 178. Shi kuwa Bernard Arnault na da biliyan 188. Mista Arnault na kula da hamshaƙin kamfanin LVMH da ke samar da kayayyakin ƙwa da tufafi 70, cikinsu har da Louis Vuitton da kuma Sephora. An haifi Bernard Arnault a shekarar 1949 a ƙasar Faransa. Mazaunin birnin Paris ne, wanda ya tara akasarin dukiyarsa ta hanyar kamfaninsa na LVMH. Shi ne Bature na farko da ya taɓa zama attajiri mafi arziki a duniya. Yana da 'ya'ya biyar kuma huɗu daga ciki suna aiki a LVMH. Da zarar mutum ya duba sunan Mista Arnault a dandalin sada zumunta zai ga shafuka masu yawa ɗauke da sunansa, amma kusan dukkansu na boge ne. Rayuwarsa ta sha bamban da ta tsohon mai kuɗi Elon Musk wajen nuna kai da kuma fantamawa. Hasali ma, Bernard Arnault ya ce ya sayar da jirginsa da ya mallaka saboda ana yawan tsokanarsa a Twitter cewa yana yawan amfani da shi. Arnault sananne ne wajen kaɗa garayar turawa da ake piano. Wannan dalilin ne ya sa matarsa Helene Mercier ta ƙyasa saboda irin yadda yake buga kiɗan Copin da sauran salon kiɗa na zamanin baya a piano. Kazalika, ɗan yawon neman zane-zane ne wanda ake kira art collector a turance. Attajirin mai shekara 73 kan za ga kantinansa da na abokan gogayyar kasuwanci duk ranar Asabar. Rahotanni sun ce dattijon kan je kanti 25 jimilla a duk irin wannan rana. Kazalika, tsohon ya daɗe yana ba da kuɗaɗe wajen gudanar da ayyukan al'umma a faɗin duniya. An ruwaito cewa Bernard Arnault ya ba da kuɗi dala miliyan 212 don sake gina gagarumin ginin coci na Notre-Dame Cathedral da ke birnin Paris na Faransa bayan gobarar da ta afku a Afrilun 2019. https://www.bbc.com/hausa/articles/c9e19r9d3ljo +business Ra'ayi Riga: Fafutikar mallakar gidaje a Najeriya Shirin Ra'ayi Riga na wannan makon ya tattauna ne a kan fafutikar mallakar gidaje a Najeriya https://www.bbc.com/hausa/articles/c4np34xzlxko +business Najeriya za ta rasa 45% na kudin shiga saboda faduwar farashin mai "Ministar Kudi ta Najeriya Zainab Ahmed Shamsuna ta ce Najeriya za ta rasa kusan kashi 45 cikin 100 na kudin shigarta da ta tsara za ta samu sakamakon faduwar farashin man fetur a kasuwar duniya. Farashin danyen man fetur ya yi faduwar bakar tasa ne saboda kamun kazar kuku da annobar coronavirus ta yi wa manyan kasashen da suka fi sayen man irinsu China da kuma rashin cimma matsaya tsakanin Saudiyya da Rasha kan yawan man da za su rika fitarwa a kullum. Ministar kudin tana wannan batu ne a ranar Laraba, inda ta ce hakan ya tilasta wa Najeriya ragewa da kuma kwaskwarima ga ayyukan da gwamnatin Buhari ta tsara za ta yi. ""Raguwar farashin man fetur daga dala 57 a kan kowacce ganga zuwa dala 30 da muka saka a kasafin kudi yana nufin cewa za mu yi asarar kusan kashi 45 cikin 100 na kudin shigarmu,"" in ji ministar. ""Saboda haka wajibi ne mu yi kwaskwarima ga wasu ayyuka da kuma kasafin kudi domin ya dace da abin da ke kasa."" Ministar ta kuma ce shugaban kasa ya bayar da umarnin a yi shirin ko-ta-kwana kan yadda za a yi ayyuka da farashin man na yanzu kan dala 30 a kowacce ganga daya. ""Wannan shirin gaggawa da za mu yi ya tilasta mu rage wasu ayyukan raya kasa duk da cewa muna ci gaba da duba hanyoyin habaka kudaden shigar da farashin man bai shafe su ba. ""Saboda haka za mu tabbatar cewa an ci gaba da hako ganga miliyan 1.8 da muka yi hasashe a kasafin kudi. ""Sannan kuma mun rage yawan kudin shigar da hukumar kwastam za ta samu daga tiriliyan 1.5 saboda mun fuskanci cewa kasuwanci zai ragu kuma idan kasuwanci ya ragu kudin shiga ma zai ragu.""" https://www.bbc.com/hausa/labarai-51981920 +business Shugaba Buhari ya bayar da umarnin buɗe iyakokin Najeriya huɗu na kan tudu "Shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin buɗe iyakokin Najeriya huɗu na kan tudu da suka haɗa da Seme da Illela da Maigatari da kuma Mfun. Mai taimaka wa Shugaba Buharin kan shafukan sada zumunta Bashir Ahmad ne ya wallafa hakan a Tuwita a ranar Laraba da yamma. Sai dai sanarwar ba ta bayyana dalilan da suka sa aka buɗe iyakokin ba, duk da cewa ƴan ƙasar sun daɗe suna fata ganin hakan. Amma mai bai wa Shugaba Buharin shawara kan yada labarai Garba Shehu ya cewa BBC dalilin buɗe iyakar shi ne sakamakon shawarar da wani kwamiti na musamman da shugaban ƙasar ya kafa kan matsalar rufe iyakar. Amma kafin nan sai da aka samu hadin kai daga makwabtan kasashe kan matsalolin da suka sa aka rufe iyakokin. A watan Agustan 2019 ne gwamnatin Shugaba Buharin ta rufe dukkan iyakokin ƙasar na kan tudu sakamakon abin da ta kira barin su a buɗe na jawo fasa ƙwaurin miyagun ƙwayoyi da maamai waɗanda suke barazana ga tsaro. Sannan gwamnatin ta ce cikin dalilan har da ƙoƙarinta na hana shiga da shinkafa ƴar waje cikin ƙasar a ƙoƙarinta na bunƙasa noman shinkafar a cikin gida.Shugabannin ƙasashe maƙwabtan Najeriya sun daɗe suna roƙonsa da ya buɗe iyakokin. Dukkan iyakokin da aka bayar da izinin buɗewa ɗin waɗanda suke kan iyakar ƙasar ne da jamhuriyyar Nijar da ta Benin. Tuni dai masana suka fara sharhi inda Dr Abdurrazak Ibrahim Fagge, shugaban sashen nazarin tattalin arziki a jami`ar Yusuf Maitama Sule da ke Kano, ya shaida wa BBC cewa bude iyakokin shi ne mafi alheri. ""Dama bisa kuskure aka rufe iyakokin nan, maimakon haka gara a saka wasu matakan kamar su haraji da saka lasisi da rage yawan kayan da ake shiga da su, amma ba a rufe boda gaba ɗaya. ""Sannan rufewar ta janyo matsaloli d dama da su kansu gwamnatin suka ga cewa a baya-bayan nan ita cibiyar da take fitar da alƙaluman tattalin arziƙin kasa ta gao cewa an samu kma baya sosai a zango na uku na wannan shekarar a wajen cinikayya tsakanin Najeriya da ƙasashen ƙetare. ""Hakan ya jawo faɗuwa ta sama da naira tiriliyan biyu. To yanzu an zao daidai gaɓar da ita kanta gwamnati ke so ta fara shigo da tataccen mai daga Nijar, kenan babu yadda za ta ci gaba da rufe iyakoki ita kuma ana ganinta tana fita tana sayowa,"" in ji masanin. Bayan cika shekara da rufe kan iyakokin ƙasar, BBC ta jiyo ta bakin wasu al'ummomin da ke zaune a garuruwan da ke kan iyakokin Najeriyar inda suka bayyana cewa kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba shekara guda bayan gwamnatin ƙasar ta rufe iyakokinta da ke kan tudu. Sai dai hukumar hana fasa-ƙwauri, wadda ta yi ruwa ta yi tsaki wajen ganin an yi aiki da rufe iyakokin, ta bugi ƙirji game da irin nasarorin da ƙasar ta samu saboda matakin da ta dauka na rufe iyakokin tudu ta fuskoki daban-daban na rayuwa. Joseph Attah, kakakin hukumar kwastam na ƙasa, a watan Agustan 2020 ya shaida wa BBC cewa da Najeriya ba ta ɗauki matakin rufe iyakokin nata wanda ya taimaka wajen inganta noma ba, to da ta fuskanci matsala ta ɓangaren abinci bayan ɓullar annobar korona, da ta tilasta wa ƙasashen duniya rufe ƙofofinsu. ""Harkar noma ta samu inganci, shi ya sa (matakin) ya rage wahalar da ake sha sakamakon zuwa koronabairus." https://www.bbc.com/hausa/labarai-55338394 +business Ya kamata Shugaba Buhari ya buɗe bodojin Najeriya - Ahmad Gumi Fitaccen malamin addinin Musulunci a Najeriya Sheikh Ahmad Mahmud Gumi ya buƙaci gwamnatin Najeriya da ta buɗe iyakokin ƙasar saboda a samu sauƙi a wahalhalun hauhawar farashin kayayyaki da ake fuskanta a ƙasar. Babban malamin, wanda ke zaune a jihar Kaduna da ke arewar ƙasar, ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da BBC Hausa a faron makon nan. Malamin ya ce matsalar tattalin arzikin kasa abu ne mai wahala ƙwarai da gaske, inda ya ƙara da cewa dole sai gwamnati ta ɗauki matakan da suka dace. ''Na farko dai bai kamata a kulle boda a lokacin da mutane ke buƙatar abinci ba. Barin boda a buɗe na bai wa manoman duniya damar kawo abincinsu kuma hakan zai sa abinci ya yi araha, domin kowa na so ya sayar. ''Yanzu misali a Thailand ga shi nan sun yi shinkafa jibgi guda amma tana neman ta ɓaci. Ka ga idan suka ga za ta ɓaci kafin akai ga hakan sai su kawo ta da araha. A Amurka mun gani har madara ake zubarwa. To ka kulle boda kuma ba ka da isasshe ba dole a yi ɓarna ai.'' To amma a na ta bangaren, gwamnatin ta ce ba za ta budo boda ba a wannan karon. Sheikh Gumi ya ci gaba da cewa ya kamata gwamnati ta duba batun wutar lantarki tare da rage kuɗin da ta ƙara. ''Ai mun san cewa ruwan Allah ne da na dam suke taimaka wa wajen bunƙsar lantarkin nan. ''Ba wani makuɗan kuɗi ake kashewa a harkar ba, to don me za a tsawwalawa mutane da albashinsu ma bai taka kara ya karya ba. ''Don haka ya kamata a sake lale a tsarin, ba mutane za a ƙuntatawa ba,'' a cewarsa. To sai dai a nata bangaren gwamnatin ta ce tana kashe makudan kudade duk wata wajen biyan masu samar da wutar, kasancewar kamfanonin rarraba wutar lantarki ba sa iya biyan kudin wutar da ake tura musu. Ana yi wa Dr Gumi kallon wani mai yawan sukar gwamnatin Shugaba Buhari tun kafin ma shugaban ya ɗare mulkin ƙasar. Maganganun nasa na zuwa ne a lokacin da ƴan ƙasar da dama ke tsaka da guna-guni kan halin da aka tsinci kai a ciki na hauhawar farashin wasu kayayyakin abinci da ƙarin kuɗin lantarki da na man fetur. Tun a ƙarshen watan Agustan da ya gabata ƴan Najeriyar ke ce-ce-ku-ce a shafukan sada sumunta kan yanayin da ake ciki na hauhuwar farashin kayayyaki. Sai dai ko a ranar Litinin ma hukumar ƙididdiga ta ƙasar, NBS ta fitar da wani rahoto da ta ce annobar Covid-19 ta ƙara assasa matsalar ƙarancin abinci a Lagos da Kano da Ribas da Abuja. A watan Agustan 2019 ne gwamnatin Najeriya ta rufe iyakokinta da zummar daƙile yawaitar fasa-kwauri da kuma bunƙasa tattalin arziki, ko da yake 'yan kasar da dama sun koka kan matakin. A watan Maris din shekarar 2020 gwamnatin Najeriya ta ce 'yan kasar sun ga irin amfanin da rufe iyakokin ƙasar ya yi a fannin tattalin arzikinta. Sai dai 'yan Najeriya musamman a arewacin ƙasar na bayyana takaici kan tsadar kayan abinci wanda suka yi tunanin a baya cewa ana iya samun rangwame la'akari da tsare-tsaren gwamnatin. https://www.bbc.com/hausa/labarai-54087368 +business Sauyin Yanayi: 'Ruɓaɓɓun motoci masu haɗari' ake sayar wa 'yan Afrika "Manyan kasashe masu arziki na duniya na yasar da motoci masu fitar da gurbataccen hayaki a kasashe masu tasowa, in ji Majalisar Dinkin Duniya. Daga shekarar 2015 zuwa 2018, an yi safarar irin wadannan motoci miliyan 14 daga Turai zuwa wasu nahiyoyi, kuma an kai rabinsu Afrika ne. An sayar da hudu daga cikin dukkanin biyar ga kasashe matalauta musamman a Afrika. Kwararru sun ce kusan kashi 80 cikin 100 na motocin ba su cika ka'idar ingancin fitar da su zuwa wasu kasashe ba. Baya ga haifar da hadurra, irin wadannan motoci kan taimaka wajen gurbata yanayi sannan suna ta'azzara sauyin yanayi. Dalilin da ya sa nake son sanya gwanjo - Sadiq Sani Sadiq Wani rahoto da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ya yi kira ga kasashen da ke fitar da irin wadannan kaya da ma wadanda ke karbarsu da su kara tsaurara matakai wajen shigo da motoci. A yanzu kowa na iya mallakar mota domin akwai akalla mota biliyan daya da miliyan dari hudu da ke yawo a titunan fadin duniya. Yawancin wannan na faruwa ne a kasashe masu tasowa da ke Afrika da Asiya da kuma Latin Amurka. A sharhinsu na shekara uku, masu bincike sun gano cewa dokokin shiga da motoci a wasu kasashe 146 na duniya ba su da karfi sosai. Wani bincike na biyu dangane da al'amarin da hukumar kula da muhalli ta Neitherlands ta gudanar, ya gano cewa yawancin motocin da ake shigar da su Afrika daga kasar lokacin aikinsu ya wuce. ""Abin da za mu ce kawai shi ne, cikin wadannan motoci miliyan 14 kashi 80 cikin 100 ba su da ingancin da ake kira Euro 4,"" in ji Rob de Jong, daya daga cikin masu binciken. A cewar masu binciken, wadannan motoci na da haɗari kuma suna dauke da datti. Sun yi imanin cewa shigar da irin wadannan motoci ne ke kara haifar da hadurra a kasashen Afrika da dama da kuma nahiyar Asiya. Sannan suna fitar da gurbataccen hayaki da kan taimaka wajen kara barazanar sauyin yanayi. Haka abin yake a Zimbabwe. A zahiri, kusan kasa 30 na Afirka ba sa iyakance shekarun mota, saboda haka, kowace irin mota daga kowane irin zamani za ta iya shigowa. ""Haka ma game da rashin cika ka'idojin kiyaye hanya da muhalli, an lalata adadi mai yawa kuma an cire muhimman kayan aikinsu."" Kashi 54 cikin 100 na motocin, ana kai su Afrika ne ta Neitherlands. Hukumomi a kasar na nuna damuwa game da lamarin, kana suna son bijiro da sabbin matakai domin dakile shi. ""Kasar Neitherlands ba za ta iya shawo kan wannan al'amari ita kadai ba,"" a cewar Stientje van Veldhoven, ministan muhalli na kasar. ""Don haka zan bukaci kasashen Turai su bijiro da matakin bai daya tare da hadin kai da kasashen Afrika don ganin motocin da suka cika ka'ida ne kadai kasashen Turai ke kaiwa Afrika."" Morocco na kyale motocin da ba su haura shekara biyar ba ne shiga kasar, ita ma Kenya na da shekarun da ta iyakance ga motoci domin shiga kasar. A matakin yanki kuwa, kungiyar kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS wadda ke da mambobi 15, ta shimfida ka'idoji ga motocin da za'a shigar da su kasashen daga shekarar 2021. ""Ina ganin babu adalci a ce wadannan kasashen da suka ci gaba su rika kai motocin da ba su cika ka'ida ba zuwa kasashe masu tasowa,"" in ji Rob de Jong. A daya bangaren kuma me ya sa kasashen da ake shigar da motocin cikinsu ba za su sanya dokoki ba?." https://www.bbc.com/hausa/labarai-54694750 +business Ƙungiyar manoma ta ƙaddamar da dalar masara a Kaduna "Ƙungiyar manoma ta kaddamar da dalar buhunan masara a jihar Kaduna, a wani yunƙuri da hukumomi ke cewa na nuna irin ci gaban da aka samu a ƙasar ta fuskar noman masarar. Shirin dalar masara tsari ne na hadin-gwiwa tsakanin ƙungiyar manoman masara da Babban bankin Najeriya wato CBN, karkashin shirin bada tallafi ga manoma na Anchor Borrower Programme. Ana saran tattara dalar da ta kai kimanin buhunan masara dubu dari biyar da aka karɓa daga manoma a faɗin ƙasar wadanda suka samu tallafin Anchor Borrower Programme. Wannan na zuwa ne sama da mako biyu bayan shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yaye kallabin dalar buhunan shinkafa mafi girma da aka taɓa tattarawa a tarihin ƙasar, in ji gwamnatinsa. Shugaban kungiyar manoman masara ta Najeriya, Alhaji Bello Abubakar Funtuwa ya shaidawa BBC cewa an tara dalar masara ce don bayyana wa duniya irin nasarorin da aka samu a noman masara a ƙasar. Ya ce rancen da ake bai wa manoma ya taka rawa wajen bai wa manoma damar tara irin wannan masara, kuma wannan somin-taɓi ne. ""Duk da cewa suna fuskantar matsalolin tsaro a kauyuka, hakan bai hanasu tara masara ba. Amma muna fatan tsaro ya inganta, saboda noman ya fi wanda aka gani a yanzu."" Shirin na gwamnatin na zuwa ne adaidai lokacin da 'yan kasa ke kokawa da yadda kayan abinci ke tashin gauron-zabi, inda a yanzu haka buhun masarar na kai wa dubu 22. Wannan dalilin ne ya sanya BBC ji daga bakin mahukunta kan ko kaddamar da wannan dala za ta sauya farashi ko akwai wani sauyi da za a gani. Mal Ibrahim Husseini, shi ne kwamishinan Noma da ya wakilci gwamnan Kaduna a wajen kaddamar da dalar masarar, wanda ya shaida mana cewa kasuwa ce ke tabbatar da farashi. Kwamishinan ya ce abu muhimmin a yanzu shi ne kokarin tabbatar da wadatuwar abinci a kasar. ""Wannan tsari tabbas farashi ya sauka da lokaci, kuma manoma ke sayar da kayansu ba za a kayyade musu ba, ya danganta amma suna kan tsrai."" Karin haske Gwamnatin Najeriya ta sha nanata cewa tana daukan matakan bunkasa harkar noma domin rage abinci da ake shigar da su kasar daga ketare Shugaba Buhari a lokacin kaddamar da irin wannan dala amma ta shinkafa a watan Janairu ya ce ana samun irin wannan nasara ne sakamako juye-juyen halin da gwamnatinsa ta ƙaddamar ta fuskar noma domin tabbatar da cewa ƴan Najeriya na iya noma abin da za su ci kuma su ci abin suka noma. Gwamnati dai ta ce kawo yanzu shirin Anchor Borrowers ya tallafa wa ƙananan manoma miliyan 4.8; wajen noma nau'ukan amfanin gona har iri 23 da suka haɗa da shinkafa, da masara da kwakwar manja, da koko, da auduga, da rogo da tumatur da kuma wajen kiwon dabbobi." https://www.bbc.com/hausa/labarai-60239065 +business Binciken Gaskiya: Da gaske CBN ya rage kuɗin da bankuna ke cazar 'yan Najeriya? "Wasu rahotanni da jaridu a Najeriya suka wallafa ya yi iƙirarin cewa Babban Bankin Najeriya CBN ya umarci bankuna da su rage cajin da suke yi wa 'yan ƙasar wajen cira da kuma tura kuɗaɗe. Sai dai wani binciken kamfanin dillancin labarai na AFP ya gano cewa umarnin ba sabo ba ne, cajin kuɗin da bankunan ke yi bai sauya ba. Rahotannin rage cajin ba gaskiya ba ne kasancewar tun 2019 bankin ya fitar da jerin umarnin game da tura kuɗi ta intanet da kuma cire su ta na'urar ATM. Kawunan labarin da mutane suka yaɗa na nuna cewa kamar an rage yawan kuɗaɗen da ake caza ne sakamakon sabbin dokokin na CBN. Binciken na AFP ya kwatanta dokokin CBN da aka wallafa a 2019 da na 2022, kuma ya gano cewa iri ɗaya ne. Dokokin na 2019 su ne dai suke aiki, inda suka maye gurbin na 2017 da 2013 da kuma na farko da aka samar a 2004. Tun a 2018 ne 'yan Najeriya suka fara ƙorafi da zanga-zanga a shafukan zumunta ƙarƙashin maudu'in #Reform9jabanks (a gyara bankunan Najeriya) da zimmar neman a daina ɗaukar musu kuɗaɗe, ciki har da N50 ta kula da katin ATM duk wata. Bayan 'yan majalisar ƙasar sun saka baki, sai CBN ya sake duba dokoin. An rage cajin cirar kuɗi ta ATM na bankin da ba na mutum ba, sannan aka rage cajin tura kuɗi ta intanet daga N300 zuwa N50 a matsayin mafi yawan adadi. Bugu da ƙari, CBN ya cire kuɗin kula da ATM daga babban asusun ajiya wato current sannan ya rage caji a kan ƙaramin asusu wato savings zuwa N50 cikin wata uku maimakon a wata ɗaya. Kuɗin kula da kati wato maintenance fee a Turance, shi ne kuɗin da kowane mai riƙe da katin ATM ke biya saboda ba shi kulawa da bankinsa ke yi. ""An cire caji a kan asusun current ne saboda da ma ana cirar kuɗin kula da asusun,"" a cewar CBN. A watan Janairu da ya gabata ne CBN ya sake wallafa bayanai game da dokokin da ya tsara wa bankunan ƙasar a kan kuɗaɗen da ya kamata su caji 'yan Najeriya, wanda hakan ne ya sa wasu jaridu suka zaci cewa dokokin sababbi ne. Wani rahoton jaridar Daily Independent a ranar 28 ga watan Janairu ya yi iƙirarin cewa CBN ya cire cajin da bankuna ke yi kan kuɗin kula da katin ATM baki ɗaya. Ta wallafa rahoton ne bayan bankin ya sake wallafa kundin dokokin na 2019 a shafinsa, wanda har sai a Janairun 2020 aka fara aiki da su. An yaɗa labarin a manyan shafukan sada zumunta da suka haɗa da Facebook da Twitter. Wasu rahotannin sun ce bankin ya rage wasu kuɗaɗen cajin da bankuna ke yi a 2022, kamar yadda jaridar The Guardina ta wallafa. Wasu magoya bayan gwamnatin APC sun yi ta yaɗa labarin a shafukan zumunta. Mai taimaka wa Shugaba Buhari kan kafafen yaɗa labarai na zamani, Bashir Ahmad ya wallafa cewa: ""CBN ya rage cajin cirar kuɗi ta ATM da kuma tura kuɗi tsakanin bankuna. Cire ta ATM yanzu ya zama N35 maimakon N65 bayan cirar kuɗi sau uku a wata ɗaya, yayin da cajin tura kuɗi ta intanet ya zama N50 mafi yawa daga N300." https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-60241007 +business Yadda rage darajar Naira zai shafi rayuwar talaka a Najeriya "Babban bankin Najeriya ya karya darajar Naira da kashi 7.6 cikin 100 kan dalar Amurka a dai-dai lokacin da ƙasar ke shirin amfani da dalar Amurka kawai wajen auna kadarin kuɗinta. Babban bankin ya karya darajar daga Naira 370 ga dala 1 da ake amfani da shi a hukumance a sabon tsarin canji na Nigerian Autonomous Foreign Exchange (NAFEX), wanda a yanzu ya kai naira 410.25 ga dala 1 a cewar bankin. Bankin ya bayyana sauyin a shafinsa kuma gwamnan bankin Godwin Emefiele ya bayyana cewa ""mun gano cewa an daina sauya Naira da farashin da CBN a hukunmance, don haka yanzu muna sa ido kan kasuwar kuma shi ya sa muka dauki wannan matakin."" Najeriya ta fara amfani da tsarin amfani da kuɗaɗen ƙasashe da dama wajen auna kadarin kuɗinta don gujewa karya farashinta. Asusun Lamuni na Duniya ya soki wannan tsarin kuma Babban Bankin Duniya ya dakatar da bayar da bashin dala biliyan 1.5 a wani mataki na son ingiza Najeriyar ta sauya manufofinta kan farashin Naira. Masanin tattalin arziki Dokta Muhammad Shamsuddeen na Jami'ar Bayero da ke Kano ya ce irin wannan matakin na lalata darajar kuɗi dama a kan talaka ya ke ƙarewa musamman tun da talaka ne yake zuwa kasuwa ya sai kayan masarufi. Ya ce kuma da yawa kayan masarufi a Najeriya shigo da su a ke yi daga ƙasashen waje kuma wannan lalata darajar kuɗi zai shafi farashin kayan sannan ya ƙara tsawwala hauhawar farashi a ƙasar. ""Idan ba a manta ba a watan da ya gabata, hauhawar farashi a Najeriya ta kai kusan kashi 18.33 cikin ɗari wanda yanzu idan aka ci gaba da lalata darajar Naira, hauhawar farashin na iya kai wa kashi 20 cikin ɗari nan da watan gobe"" a cewarsa. Dokta Shamsuddeen ya ce wannan shi ne babbar wahala da talaka zai iya fuskanta. Haka kuma, ya ce lalata darajar Naira na iya haifar da rashin aikin yi a ƙasar tun da kamfanoni da masana'antu da dama a Najeriya sun dogara ne da shigo da kaya daga kasashen waje domin sarrafawa - wannan na iya nufin injina ko kayan da ake sarrafawa don samar da wasu kayayyakin. ""Idan ya zama cewa waɗannan kayayyakin sun yi tsada sakamakon faɗuwar farashin Naira, babu shakka wasu masana'antun ba za su iya ci gaba da aiki ba dole su rufe masa'antun ko su rage kayan da suke yi,"" in ji Dokta Shamsu. Ya ce wannan zai haifar da korar mutanen da suke aiki a waɗannan masana'antun. Masanin ya ce ta ko wace fuska aka kalli wannan matakin an CBN, talaka zai wahala walau ta rashin aikin yi ko kuma ta hauhawar farashi. Dokta Muhammad Shamsuddeen ya ce gwamnatin Najeriya na ƙoƙarin karya farshin ne saboda bashi da take so ta karɓa daga babban Bankin Duniya na dala biliyan 1.5 kuma bankin ya bai wa Najeriya Ƙa'idar haɗe farashin Naira na gwamnati da na kasuwa waje guda kafin ya ba da bashin. Shi ya sa Najeriyar ke ta fafutukar ganin ta rage wa Naira daraja, farashin gwamnati ya dawo dai-dai da na kasuwa. Sai dai Dokta Shamsuddeen ya ce yana ganin babu ma wata buƙatar rage darajar naira da babban bankin ya yi tun da har an zo matakin da naira 495-500 yake dai-dai da dala ɗaya a kasuwar bayan fage. ""Babu wata daraja da ta rage wa naira da har babban banki zai kare ta, kamata ya yi a saki kasuwa kawai ta yi wa naira ƙaidi. Yin hakan zai taimaka ta hanyoyi daban-daban,"" a cewarsa. Ya ce hanya ta farko ita ce shi babban bankin ba zai riƙa bai wa wasu shafaffu da mai dala a farashin gwamnati ba kamar yadda ake zargi. Su kuma mutanen su sayar wa ƴan kasuwa a farashi mai tsada. Ya ce wannan ne ke sawa kullum darajar naira tana ƙara faduwa. ""Abu na biyu shi ne Babban Banki CBN ya sauke wa kansa nauyin matsawa kansa sai ya sama wa naira daraja. Wannan na barazana ga ƴan kasuwa kuma yana hana masu zuba jari na ƙasashen waje shigowa Najeriya,"" in ji Dokta Shamsuddeen. Ya ce abun da ya fi dacewa tun da an kai wannan matakin shi ne CBN ya cire hannunsa daga harkar sama wa naira daraja, ya bari kasuwa ta yi mata daraja kawai. Kusan wannan ne karo na huɗu ko na biyar cikin shekara ɗaya da ta gabata da aka rage darajar naira a Najeriya. Wannan ya haura kashi 30 cikin 100 na darajar nairar da aka rage cikin shekara guda - un tana naira 306 a watan Maris ɗin shekarar da ta gabata yanzu ta kai naira 410." https://www.bbc.com/hausa/labarai-57253511 +entertainment Daga baƙonmu na mako: Shin kwalliya na biyan kuɗin sabulu game da fina-finai masu dogon zango? "Kamar yadda jiki ke buƙatar abinci don ya ƙarfafa haka zuciya ke buƙatuwa da abubuwan nishaɗi don samun hutu. Abubuwan da kan nishaɗantar sun bambanta daga al'umma zuwa al'umma, haka ma a tsakanin mutane. Wasu kan karanta littafi domin nishaɗantuwa, wasu sauraron kaɗe-kaɗe da raye-raye, wasu su yi wasa, wasu su kalli fina-finai da makamantansu. Haka kuma wasu kan yi abubuwa sama da ɗaya don nishaɗantar da rayukansu. Wannan ne ya sanya Bahaushe kan kira ""rai da dangin goro."" Wasannin kwaikwayo ko drama ko fim hanya ce ta samun nishaɗi wadda al'ummomi da yawa ke amfani da ita. A tsowon tarihin rayuwa an sami sauye-sauye bisa yadda akan yi wasan na kwaikwayo. Kafin ci gaban zamani ya zo da hanyoyi sadarwa kamar rediyo da bidiyo akan yi wasannin ne ta hanyar ana yi ana kallo da ido, wannan shi ne asalin abin da ake kira da drama. A irin wannan ne aka sami wasannin dandali da tashe har ya zo ga wasannin daɓe (Stage Drama). A baya akan yi wasannin ne kai tsaye ko ta hanyar abin da aka kiyaye daga magabata tare da ɗora wani abu da zai nishaɗantar ta hanyar duba da zamani ko wuri da ake gudanar da wasan. Daga baya aka fara rubuta wasannin kwaikwayo a bai wa 'yan wasa su karanta sannan su yi aiki da abin da suka karanto. A irin wannan tsari akan sami mai bayar da urmarni ko darakta wanda zai tabbatar da 'yan wasa sun bi tsarin da rubutun ya ɗora su. Fim tsari ne na gudanar da kwaikwayo wanda ci gaban zamani ya haifar. Ba a fara yin fina-finai ba sai ƙarshen ƙarni na sha-tara a lokacin da ci gaban fasahar zamani ta zo da hoto mai motsi. A wannan lokaci an fara yin fina-finan ne a gidajen sinima inda 'yan kallo kan biya kuɗi don su kalla. Masana'antar farko da ta yi suna a wurin shirya fina-finai ita ce Hollywood ta Amurka. Daga nan sauran sassan duniya suka ara suka yafa. Kamar yadda Farfesa Yusuf Adamu ya bayyana a wata maƙalarsa, an fara ƙyanƙyasar fina-finan Hausa ne a cikin farkon shekarun Alif Ɗari Tara Da Tamanin (1980s), lokacin da wasu matasa uku a Kano - Sani Lamma da Hamisu Gurgu da Sadiya baƙar Indiya suka yi ƙoƙarin yin wasa film cikin Hausa. A wajejen tsakiyar waɗannan shekaru (na Alif Ɗari Tara Da Tamanin), an kafa wasu kungiyoyi na wasan kwaikwayo kamar Turmbin Giwa, Gyaranya Drama da Jigon Hausa Drama wanda suka fara yin fina-finai masu dogon zango a da tashar NTA da CTV 67 (ana kiran da STV a yanzu) da gidan Talabijin na Katsina. A wannan lokacin an yi fina-finai kamar su Bakan Gizo da Jamila da Jamilu, Hadarin Кasa da Farin Wata. Ba na mantawa a matsayina na yaro a wancan lokacin ina mutukar son kalon waɗannan fina-finai musaman na Aminun Bose da Malam Ibrahim Mandawari Ya fito a matsayin tauraron shirin. Wasu fina-finan da aka gudanar a wannan tsari sun hadar da Turmin Danya da Cin Amana. Waɗannan fina-finai an gudanar da su ne a gidajen Talabijin na gwamnati kuma cikin harshen Hausa, a bisa tsari da ke da ƙarancin saɓawa al'ada; ta inda mai gida yana iya kallo tare da iyalansa da ma surukansa. Daga shekarar 1993 fina-finan Hausa na masu Gajeran Zango suka fara kunno kai. Irin waɗannan fina-finai sun sha bamban da na farko kasancewar su ba a gidajen talabijin ake yin su ba. Ana yin su ne a gidajen aro ko otal-otal da makarantu da makamantansu. Kuma kasancewar sinima ta ja baya, ya sanya ana yin su ne a kaset, mai sha'awa ya saya. Wasu cikin fina-finan sun kasance litattafai ne da aka rubutasu kafin daga baya a mayar da su fina-finai kamar su Kwabon Masoyi na Adamu Muhammad da In da so da ƙauna na Ado Ahmad Gidan Dabino da Tsutu mai wayo na Bala Anas Babinlata da Alhaki Kyuikyuyo na Balaraba Ramat Yakubu da Rikicin duniya na Ɗan'azaumi Baba Chediyar 'Yan gurasa. Duk waɗannan na karanta su a matsayin litattafi kafin daga baya na kalle su a matsayin fim. Fina-finan da suka biyo bayan waɗannan sun kasance fina-finai ne da za ka iya cewa ko dai an yi su ne kai tsaye ba tare da an rubuta su a matsayin littafi ba ko kuma ba a sansu a matsayin litattafai ba yayin da wasu cikinsu tatsuniyoyi ne. Irin waɗannan fina-finai sun haɗar da Daskin da ridi da Sumbuƙa da Gagare da Allura da zare da Sangaya da Zarge. Galibinsu an gudanar da su ne a bisa tsarin gargajiya da sanya waƙoƙi masu kama da na dandali. Samun nasarar da waɗannan fina-finai masu gajeren zango suka yi, ya sanya kwararowar masu shiryawa da 'yan wasa zuwa Birnin Kano, wadda ake ɗauka jigo a Кasar Hausa kasancewarta mafi yawan jama'a kuma babbar cibiyar kasuwanci ta wannan al'umma. Wannan ya sanya harkar wasan Hausa ta haɓaka a garin inda aka yi ta shirya fina-finai, mutane suka yi ta sanya jarinsu, masu fasaha kuma na yin rubutu, bayar da umarni da fitowa cikin fina-finan. Wannan ne ya haifar da kafuwar masana'antar fim da ake kira da suna Kannywood. Kasancewar adabin zamani na Bahaushe ya fara da kwaikwaiyo ya sanya su ma masu fim galibi ba 'ƙirƙira' fim suke ba. Da yawansu ɗauraya ne ko jiƙo ko wanki na fina-finan waje, musamman Indiyawa. Кari a kan haka kuma shi ne saboda kasancewar masu shirin matasa ya sanya tunaninsu bai wuce na soyayya wadda suke gani a fim ɗin Indiya. Irin waɗannan fina-finai sun haɗa da Abun Sirri ne da Sauran Ƙiris da allura da zare da makamantansu. Saboda cin da kasuwar take a wannan lokaci, fina-finan na fita tamkar guguwa ta koro shara; don haka mai kallo bai ma iya tuna sunayen da yawan abin da ya kalla. Duk da cewa ba dole ne dukkan sauran al'umma su yi wa fim fahimtar haka ba, da yawan al'ummar ƙasar Hausa na buƙatar fim ɗin Hausa ya zamto ba wai kawai ya nishaɗantar ba; a a da buƙatar bayan nishaɗantarwa, fim ya faɗakar, ya ilimtar tare da yin daidai da al'ada 'Bahaushiya'. A bisa wannan dalili ne mai kallon fim ke duba shiga da aikin 'yan wasan fim kan gudanar. Misali mai kallo kan yi ƙorafi idan ɗan wasa ya yi shiga da ke nuna tsiraici ko sassan jiki da a al'ada akan ɓoye su. Hakanan masu kallo kan so su ji maganganun da ake yi ba su 'shallake' tsari da ajiyar al'ada ba. A irin wannan tsari ne wasu ke cewa fim ɗin baya wakiltar al'umma da al'ada Bahaushiya. Kasancewar galibin al'ammar Hausawa mabiyan addinin Islama ne kuma addini ya daɗe tare da yin tasiri a al'adarsu, ya sanya komai a cikin fim ana nemansa ya zamto bisa daidaito da yadda addinin ya tsara ko al'ummar ta fahimce shi. Misali tillas ne a ɓoye tsiraici, ba a kama yin hannu mace da namiji ko runguma ko kuma zantutukan batsa. Maimakon haka an sami yawaita amfani da matsatsun kaya da yin amfani da zantutuka masu motsa sha'awa a cikin fina-finai da sanya mata su kaɗa jikinsu ta hanyar yin rawa da rausaya da maza da ba mazansu ba ko muharammansu ba. A bisa wannan ƙoƙori na daidaita fim da addini ko al'ada ya sanya jihoyi, musamman Kano kanwa uwar gami ta kafa hukumar tace fina-finan Hausa, wadda a shekarun baya ta sha kafsawa da 'yan fim da shugabannin masana'antar fim ɗin. Wannan ba karami ka-ce-na-ce ya janyo ba, wanda hakan har ya yi sanadiyar tsarewa da ɗaure wasu cikin 'yan wasa da masu shirya wasan. Daga wurin 'yan wasan kuma sun yi ta mayar da martani a cikin fina-finai, waƙoƙi da rubuce-rubuce. A irin wannan za mu iya tuna Marigayi Rabilu Ɗan-Ibro da yadda ya dinga shaguɓe ga shugabannin gwamnati da hukumar da ta matsa wurin abin da ta kira tacewa da tsabtace fim ɗin hausa. Hakanan akwai wasu cikin mawaƙan masana'antar da suka rera wasu waƙoƙi kamar rabo yai rabo da hazbunallahu da makamantansu. Wannan abin bai tsaya ga masu fim ba kawai, ya shafi har abokan tagwaitakarsu marubutan littatafan Hausa da Farfesa Ibrahim Malumfashi ya kira da ""Adabin Kasuwar Kano"". Haka kuma ana yawan zargin fina-finan masana'antar da cewa an gina su ne a kan jigo guda, wato soyayya ko abin da ake kira da Nanaye. Wannan ba ya rasa nasaba da tushen fina-finan wanda galibi ana ɗaurayo su ne daga fina-finan Hindi. Hakana kasancewar mafiya yawan masu fina-finan matasa ne, musumman limaman fari na fim wanda sun diro ne daga 'Adabin Kasuwar Kano' mai jigo guda wato soyayya. Masana kan ce abincinka kamaninka don haka matasa galibi abin da ya fi jan hankalinsu shi ne soyayya, saboda haka ba laifi idan 'yawu zuba ta inda baki ya karkata.' Wani suka da ake yiwa fina-finan shi ne na rashin ƙwarewa da gina labari mai ban ƙayi. A bisa haka galibi zaren kan tsinke, sa'annan mai kallo kan iya fahimtar mai zai biyo baya ko ma ina fim zai ƙare. Da yawan masana kan ɗora zargin hakan a bisa rashin zurfin sani na marubata, daraktoci da masu shirya fim ɗin. Misali, ina tuna wani zama da ƙungiya Marubuta ta Jihar Kano ta shirya da fitacciyar marubuciyar nan Hajiya Balaraba Ramat inda ta yi zargin matasan da rashin ƙwarewa har ta ce da yawa sukan ɓata maka rubutunka idan ka nemi mai da shi fim. Hakanan na iya tuna a cikin shekarar 2006 Farfesa Abdallah Uba Adamu ya taɓa gaya mana yayin da yake koyar da mu a aji cewa ya taɓa ƙoƙarin koyawa wasu ɗalibai al'adar Bahaushe ta hanyar fim ɗin Hausa, amma sai suka yi zargin cewa al'adar ta Indiya ce kuma suka tuhumi taurarin fina-finan da rashin rai saboda kasancewar ba sa nuna damuwa ko farin ciki yadda taurari 'yan gaske' kan yi a fina-finan 'gaske'. Wata ƙarin matsala game da fina-finan na Kannywood shi ne inda wasu tsirarun fuskoki suka zamto su kawai ake gani kumar ba masana'anta ba. Dalilin da ya sanya na ce kamar ba masana'anta shine ita masana'antar yadda muka sani tsari ce cikakke don haka kowa yana iya hawa ya yi tafiya a kai. Amma maimakon haka fuskoki tsiraru, musamman na maza su ne suke fitowa a fina-finan. Don haka duk mai so yi su zai nema. Wannan ya sanya sun fara gazawa wurin gamsar da me kallo tare da jin cewa su kaɗai suka iya don haka ba su da kishiyoyo da za su zaburar da su don su yi himma kamar yadda aka saba gani a manyan masana'antu fim. Wata matsala kuma ita ce yin fina-finan cike da gaggawa saboda kowa na son ya sami kuɗi. Galibi ɗaiɗaikun mutane ke yin fina-finan ko da sun kira kansu da kamfani. Saboda haka babu isasshen kuɗi wanda zai sanya a yi abu da inganci. Haka kuma babu cikakken nazari don haka sai sanya al'amura ba inda suka dace ba. Sa'annan yawan fitar fina-finan ya sanya an rasa tsari wurin kasuwanci da tallata su. Wannan ya sanya masana'antar ta kasa samun ci gaba kamar ta abokiyar tagwaitata da ke kudancin Nijeriya. Duk da a farkon fina-finan Hausa sun fara a gidajen Talabijin bisa tsarin dogon zango, tsawon shekaru sun sauka daga kan wannan. Musamman daga shekara ta 1993 inda aka koma yin fina-finai a fefe (home Videos) kuma wannan tsari shi ya fi shura da kafuwa har kusan an manta da wancan tsari. Kwatsam kuma sai nan baya-bayan nan, daga shekara 2015 lokacin tashoshin Arewa 24 da Tararuwa da makamantansu suka fito ungulu na neman komawa gidanta na tsamiya. A wannan lokaci an sami ɓullar wasu fina-finai masu dogon zango da suka fara ɗaukar hankalin masu kallo. Irin wannan fina-finai sun fara ne a tashoshin da ke kan tauraron ɗan-adam, inda daga baya aka fara ɗora su a tashoshin YouTube. Jagora kuma fim da ya fara zuwa a wannan sabon salo shine fim ɗin Daɗin Kowa wanda har yau bai kai ga ƙarewaba duk an yanzu ya shiga zango na uku, kuma an yi kashi sama da ɗari biyu da hamsin. Karɓuwa Daɗin Kowa ya yi ya sanya shirya wasu fina-finan masu dogon zangon kamar Kwana Casa'in da Gidan Badamasi da Labarina da Danbirni wanda dukkaninsu ana gudanar da su ne a tasoshin tauraron ɗan adam. Bayan waɗannan kuma an sami wasu fina-finan masu dogon zango wanda suke a kan kafofin sadarwa na YouTube kamar su Izar so da Bugun zuciyar masoyi da A duniya da sauransu. Babbar tambaya a nan ita ce ko an sami sauyi daga abubuwan da aka zargi fina-finai masu gajeren zango da su ko kuwa? Shin idan an sami sauyi, a ina da ina ne? Idan kuma ba a sami sauyi ba ya za a yi a gyara? Haƙiƙa idan aka yi duba ta ɓangaren kyawun labari da ƙwarewar tsara labari ma iya cewa an sami ci gaban. Misali duk mai kallon fina-finan masu dogon zangon kamar Daɗin kowa ko Gidan Badamasi zai ga yadda marubutan ke sarrafa zaren labari ba tare da ya tsinke ba. Hakanan za a ga yadda ake sanyawa mai kallo sha'awar ci gaba da kallo ta hanyar rikita tunaninsa game da mai zai faru a fitowa ta gaba ko shiri na gaba. Wannan yana cikin abin da fina-finan baya suka rasa ta inda mai kallo kan iya gane inda labari zai dire tun daga fitowar farko. A fahimtata wannan nasara ta samu ne saboda yin amfani da ƙwararrun marubuta waɗanda suka san jiya da yau ɗin rubutu kamar Nazir Adam Saleh da Bala Anas da Fauziyya D. Sulaiman da Ibrahim Birniwa da Zuwairiyya Gerei da makamantansu. Waɗannan maruba litattafan adabi ne ba wai masu rubuta script kawai ba. Don haka suna da ƙwarewa idan aka kamanta su da na gajerun fina-finai wadanda galibi ba su da ƙwarewa. Duk da su ma waɗannan ɗin ba ka raba su da wasu kura-kurai ko tuntuɓe. Misali duk wanda ya kalli fim ɗin Labarina zai fahimci mai rubutun bai yi bincike game da yanayin jami'a ba. Na faɗi haka saboda shi ne tsarin da na fi ido a kai. Hakanan za mu iya cewa ana samun ci gaba ta hanyar jigon labari ta inda yanzu za ka ga jigo kala-kala da suka shafi rayuwa, saɓanin soyayya zalla mai ƙarancin kama da ta Bahaushen mutum. Misali duk da Gidan Badamasi cike yake da barkwanci da har ka iya cewa shi ne babban jigonsa, amma akwai rayuwar iyali da zamantakewa a gidan auri-saki na Malam Bahaushe; haka nan akwai maganar tarbiyya; da cin amana da ma yadda aikin tsaro ya ɓaci a ƙasa. Daɗin Kowa sha kundum ne wurin game jigogi kamar maganar tsaro, ilimi da karantarwa (almajiranci), cin haci da rashawa; zamantakewar iyali da al'umma, rayuwar birni ko bariki da makamantansu. Kwana Casa'in ya fara ne da siyasa, amma yanzu ban san inda ya dosa ba, ko dai dan na daina kallo ko kuma zaren bai saƙu irin na biyun da na ambata kafinsa ba. Wata nasara da aka sake samu ita ce na yin amfani da sabbin fuskoki da jarumai, ta inda yanzu matasa kan shigo su kuma taka rawar da dama ta su ce. Wannan ya saɓawa baya inda wasu ke fitowa ko da yaushe. Wannan kuma ya faru domin masu shirya fim ɗin kan tallata ne da ɗaukan waɗanda suka dace da rawar da suke so a taka a fim. Yanzu kam tabbas mun fahimci ko cewa magaji ma zai iya gaje gwani in ya kau ko ya gaza. Ta fuskar daidaito da al'adar Bahaushe kuwa, idan muka duba waɗannan fina-finai masu dogon zango muna iya cewa an sami ci gaba a wani ɓangaren, a wani sashen kuma ana nan jiya ya yau. Misali, mun daina ganin waƙa da rawa da samari da 'yan mata kan ɓuya su yi a bayan bishiya, wanda wannan ya rusa zaton masu cewa sai an yi rawa za a kalli fim. Sa'annan a waɗannan fina-finai ana amfani da gida da ma gari da ya fi kama da irin namu. A waɗancan galibi otel da gidan attajirai ake nuna mana, amma yanzu za mu ga ƙauye da birni da talaka da akurkinsa, da mai kuɗi da shigifunsa. Amma kuma game da sittira ka iya cewa, har yanzu da sauran rina a kaba musamman a fina-finan na YouTube. Hakan bai rasa nasaba da rashin tace su da akan yi. Haka nan waɗannan fina-finai suna ɗauke da wasu abubuwa na taɓara da rashin kunya. Kammalawa Duba da abin da ya gabata za mu iya cewa fim ɗin Hausa ya fara da dogon zango kafin ya koma mai gajere zango, wanda a lokacin ne ya shahara har ya kafa masana'anta ta kansa. Daga baya-bayan nan da alama ungulu ta fara komawa gidanta na tsamiya. A lokacin ganiyar finai-finai masu gajeren zango ana zargin masu gudanar da fim ɗin da gazawa wurin wasu abubuwa kamar cika da kyan jigo da rashin daidaito da addini ko al'ada da rashin sauyin fuska. Duk waɗannan sun sami inganci a fina-finai masu dogon zango idan aka kamanta da gajerun. Sai dai har yanzu da buƙatar daidaita fina-finan da haƙiƙanin al'ada da ingantasu ta inda wanda ba Bahaushe zai iya kallonsu ya yi nazari cikin rayuwarsa, kasancewa fim adabi, yana nuna kasancewarsa hoto ko mudibi na rayuwa. Wannan maƙala ce ta musamman daga baƙonmu na mako: Murtala Uba Mohammed (PhD), malami ne a Sashen Jogorafi na Jami'ar Bayero ta Kano kuma mamba a ƙungiyar marubuta ta ƙasa (ANA) reshen Jihar Kano. Murtala yana da sha'awar rubuce-rubuce cikin Harshen Hausa da na Turanci." https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-54657758 +entertainment Asarar da Kanye West ya yi bayan ɓatancin da ya yi wa Yahudawa Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon: Fitaccen mawaƙin nan Kanye West da aka fi sani da Ye a yanzu ba biloniya ba ne. Ya yi asarar miliyoyin daloli bayan da kamfanin Adidas ya dakatar da haɗin giwiwarsu, sakamakon kalaman ɓatancin da ya yi a kan Yahudawa a shafukan sada zumunta. A nan mun yi duban kan kalaman da suka jawo masa asarar dukiyar. https://www.bbc.com/hausa/articles/c0k548zg5v9o +entertainment Ladin Cima: Yadda batun biyan 'yan fim ya raba kawunan 'yan Kannywood "Batun yawan kudin da ake biyan 'yan fim a masana'antar shirya fina-finan ta arewacin Najeriya ga alama ya raba kan 'yan Kannywood biyu. Tun bayan da BBC Hausa ta wallafa bidiyon hirarta da Hajiya Ladin Cima a filin Daga Bakin Mai Ita, sai ce-ce-ku-ce ya barke kan batun nawa ake biyan jarumai. Ainihin hirar an yi ta ne ranar Lahadi 14 ga watan Nuwamban 2021, a lokacin da BBC ta aika ma'aikatanta biyu Kano don tattaro shirin Daga Bakin Mai Ita da wasu 'yan Kannywood 11. Amma da yake ana saka shirin daya bayan daya ne a kowace Alhamis, shi ya sa na Ladin Cima bai fito ba sai bayan wata biyu da yin hirar. Hajiya Ladi da aka fi sani da Tambaya ta Malam Mamman ko Mama Tambaya kamar yadda abokan aikinta ke kiranta, ta shaida wa BBC ne cewa ana biyanta kudin da ba su haura naira dubu biyar ba. Wannan magana ce ta ja hankalin masu bin shafukan BBC Hausa na intanet inda suka dinga zargin furodusoshi da daraktoci da rashin tausayin tsofaffin 'yan fim din. Lamarin da ya sosa ran wasu furodusoshin irin su Ali Nuhu da Falalu Dorayi, har suka shaida wa BBC cewa ko su sun taba ba ta kudade masu yawa na fita a fim dinsu da ta yi. Inda kuma Mama Tambaya ta jaddada wa BBCn cewa an yi haka, bayan sake tuntubarta da muka yi. Duk da dai Ali Nuhu da aka fi kira da Sarkin Kannywood da kansa ya ce ba za a rasa masu biyan 2,000 ko 5,000 ba, amma bai kamata Ladin Cima ta yi wa duka furodusoshi kudin goro ba. Wannan hira dai ta zama tamkar bude kofa ne ga wasu abubuwa da suka dade suna ci wa wasu 'yan masana'antar tuwo a kwarya. Domin tun daga ranar Alhamis, batun dai da ake ta tattaunawa kenan a shafuka daban-daban. Su ma sauran al'umma ba a bar su a baya ba don sun shiga zancen dumu-dumu tare da bijiro da tambayoyi kan abubuwa da dama da suka shafi Kannywood. Girma da habaka irin ta masana'antar Kannywood a wannan zamanin, ta wajen nishadantar da al'umma da samar da ayyukan yi da kudaden shiga ga hukumomi, ya sa bai zama abin mamaki ba don wannan batu ya ja hankalin mutane. Manyan jarumai irin su Nafisa Abdullahi da Nuhu Abdullahi da Hadiza Gabon da Rukayya Dawayya da Tijjani Asase duk sun dan yi gugar zana a shafukansu na sada zumunta. Wasu kuwa irin su Adam Zango da Rahama Sadau sai suka nuna alamar bakinsu da goro, wato sun dinke shi duk da dai akwai magana. Wasu na ganin abin da Hajiya Tambaya ta fada gaskiya ne, wasu na ganin ba ta yi daidai ba yayin da wasu kuma ke nuna babu ruwansu kawai dai suna kallon abin da ke faruwa. A ranar Juma'a Rahama a shafinta na Instagram ta wallafa Hmmmmmmmmmm da alamar rufe baki. Adam Zango kuwa a ranar Asabar sai ya wallafa wani bidiyo da 'yan amshi a bayansa yana wata waka mai taken ""Shiru"", inda yake cewa ""duk abin da babu ruwanka ka koma gefe ka yi shiru."" Nafisa Abdullahi a nata sakon kira ta yi ga 'yan fim cewa su daina karbar aiki idan har farashin da furoduso ya yanka musu bai musu ba. Duk da cewa 'yar wasan a shafinta na Tuwita ta bayyana shakku kan batun Ladin Cima, amma ta ce watakila ba abin mamaki ba ne hakan na faruwa. ""Idan ba a biyanka da kyau a aikin da kake yi, kuma kai ka san ka fi karfin hakan, mene ne abin wahala wajen fahimtar da wadanda suka ba ka aikin cewa ka san hakkokinka? ""Mene ne abin wahala ka gaya musu cewa kudin da suke son ba ka bai maka ba? Wani bidiyo da Naziru Sarkin Waka ya yi a shafinsa ranar Alhamis za a iya cewa shi ya kara tunzura wasu 'yan Kannywood din har rabuwar kawunansu ta kara fitowa fili. A bidiyon ya tabbatar da ikirarin Hajiya Tambaya tare da sukar wasu furodusoshin kan rashin biyan 'yan wasa. 'Yan masana'antar irin su Nuhu Abdullahi da Abba Mai Shadda da Alhajin Sheshe da wasu da dama sun yi masa martani a nasu shafukan. Nuhu Abdullahi ma cewa ya yi ""da za mu fito mu yi bayani da mutuncinku ya zube."" Wasu kuma irin su Ali Artwork sun goyi bayan maganganun Sarkin Waka duk da dai ya yi wasu zarge-zarge kan wasu 'yan fim din. Sai dai duk da wannan tataburza da ake yi, akwai 'yan Kannywood din da abin bai musu dadi ba ta kowane bangare. Masu irin wannan ra'ayin na kira ne da a yi sulhu don kar magauta su yi wa masana'antar dariya. Tijjani Asase da Sahir Abdul na daga cikin masu irin wannan ra'ayi. Musbahu M Ahmad kuwa wanda yaya ne ga Naziru Sarkin Waka, jan hankalin 'yan fim ya yi kan su guji furta kalamai marasa dadi da yin gori ga manya daga cikinsu kamar yadda wasu suka rinƙa yi wa Tambaya. Masu sharhi sun tofa tasuMasu sharhi a lamarin masana'antar irin su Muhsin Ibrahim sun tofa albarkacin bakinsu. A nasa shafin na Facebook ya rubuta cewa ba mamaki karancin kudin da masana'antar ke fama da shi ne ya sa furodusoshi ba sa iya biyan 'yan wasa da kyau. ""Tabbas Kannywood akwai ƙarancin kuɗi, musamman ga maza da kuma dattijan mata, amma lalacewar bata kai yadda ta faɗa ba. ""Ko don tausayi, na san masu abin hannu a cikin su ba za su ƙyale tsofaffi irin Tambaya ba haka."" Aliyu Samba ma a nasa sharhi cewa ya yi: ""Rigimar yan Kannywood ta bar batun Ladin Cima ta koma siyasa. Hamayya ce tasa ake ta jan maganar nan. ""Sanda ake bukatar kalamansu akan muhimman al'amura basu ce komai ba, sai yanzu da suke son sauke haushin su akan junan su saboda kowa da indararon da yake kwankwaɗar ruwa.""" https://www.bbc.com/hausa/labarai-60361973 +entertainment ...Daga Bakin Mai Ita tare da Fatima Isah Muhammed, Teema Makamashi Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon: Daga Bakin Mai Ita wani shiri ne na BBC Hausa da ke kawo muku hira da fitattun mutane kan wasu abubuwan da suka shafi rayuwarsu zallah. A wannan kashi na 40, shirin ya tattauna da wata ƴar fim Fatima Isah Muhammed da aka fi sani da Teema Makamashi, inda ta amsa tambayoyin da suka shafi rayuwarta. Ɗaukar bidiyo da Tacewa: Abdulsalam Usman Abdulkadir Tsarawa: Umar Rayyan https://www.bbc.com/hausa/media-56431976 +entertainment ...Daga Bakin Mai Ita Tare da Fati Baffa Fagge 'Fati Bararoji' Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon: Daga bakin mai ita wani shiri na BBC Hausa da ke kawo muku hira da fitattun mutane kan wasu abubuwan da suka shafi rayuwarsu zallah. A wannan kashi na 32, shirin ya tattauna da Fati Baffa Fagge da aka fi sani da Fati Bararoji, wata tauraruwar fina-finan Hausa da aka daɗe ba a ji ɗuriyarta ba. A cikin hirar, ta bayyana abubuwa da yawa da suka shafi rayuwarta da za su saku dariya da al'ajabi, ciki har yadda ta shiga harkar fim, da yadda aka yi mata aure a shekara 13. Ɗaukar bidiyo: Yusuf Yakasai Tacewa: Fatima Othman Ga wasu na baya da za ku so ku kalla: https://www.bbc.com/hausa/media-55652239 +entertainment 'Tashin hankalin da labarin ƙarya da aka sa hotona ya jefa ni a ciki' Dannan hoton sama don kallon bidiyon: Wannan bidiyon hira ce da BBC ta yi da ɗan jaridar nan na Najeriya Ayodeji Rotinwa, wanda aka yi amfani da hotonsa aka yaɗa labaran ƙarya da aka alaƙanta da wani mai suna Christopher Uche-Ayodeji (Dr Chris) a Facebook, da aka ce ya yi wasu kalamai bayan kisan Deborah Samuel da ake zarginta da zagin Annabi Muhammad a Sokoto. Ya bayyana yadda ya ga hotonsa na yawo har ya yaɗu kamar ruwan dare a shafukan sada zumunta da kuma tasirin da hakan ya yi na tarwatsa nutsuwarsa. An ce matashin ya wallafa wani saƙo ne da ke cewa a lokacin yana hidimar ƙasa a arewacin Najeriya a matsayin likita, ya yi ta barin Musulmai suna mutuwa a kan idonsa tare da ƙin taimaka musu, don ramuwa ga wani rikicin addini da ya taɓa shafar danginsa. Daga baya an gano babu mai wancan sunan nan Christopher Uche-Ayodeji da aka ce ya fadi hakan. https://www.bbc.com/hausa/media-61559709 +entertainment Duniya ta farko da aka gano bayan tarin na cikin birninmu na Milky Way "Masana ilimin sararin samaniya sun gano wata alama wadda ke nuni da gano wata duniyar bayan dandazon taurarin da duniyarmu ke ciki wato a wajen birninmu na Milky Way. Akalla an gano kusan taurari guda 5,000 a saman taurarinmu, amma dukkansu suna kusa da hasken dandazon taurarin da muke ciki ne. Duniyar da aka gano alamarta, babba ce kamar girman duniyar Saturn. An gano ta ne ta hanyar amfani da na'urar hangen nesar Chandra X-Ray, kuma tana cikin babban dandazon taurari na 51 ne. Kuma tana da nisan kimanin tafiyar haske na shekara miliyan 28 daga hasken taurarinmu. Wannan sabon binciken ya ta'allaka ne da yanayin tafiya, inda wucewar sabuwar duniyar ta gaban wani tauraro ya tare hasken wasu taurari, wanda hakan ya haifar da dusashewar haskensu. Wannan ne ya taimaka wa na'urar hangen nesan wajen dauko hoton. An kuma yi amfani da wannan salon wajen gano dubban wasu duniyoyin daban. Dakta Rosanne Di Stefano da abokan aikinta sun nemi gano yadda hoton da aka dauko na wasu abubuwa suka dusashe. A cikin wannan hasken da aka dauko na wannan layin, akwai wani karamin tauraro ko baƙin rami da ke jan iskar gas daga taurarin da suke zagaye a kusa da shi. Wani abu da ke kusa da karamin tauraron ko baƙin ramin sai ya dauki zafi sosai, sannan ya ƙara haske a sanadiyar hasken daukar hoto. Saboda wajen da ke bayar da hasken daukar hoton ƙarami ne, duk wata duniya da za ta wuce ta gabansa, za ta iya tare da yawa daga cikin hasken ko kuma ta ma tare shi baki daya, wanda ya saukaka gano wucewar wani abu. Masu binciken sun yi amfani da wannan tsarin ne domin gano duniyar da suke binciken mai suna M51-ULS-1. ""Tsarin da muka bi shi kadai ne a yanzu tsarin da za a iya bi wajen gano wasu dandazon taurarin,"" kamar yadda Dokta Di Stefano ta Cibiyar Binciken Taurari na Harvard-Smithsonian da ke Jami'ar Cambridge da ke Amurka ta bayyanawa BBC. ""Tsari ne na daban, wanda kuma yake da yanayi mai kyau da za a gano wasu duniyar masu makwabtaka da layukan hotunan da muka gano duk nisansu, wanda daga nan kuma za mu iya gwada yanayin haskensu."" Wannan layin yana dauke da wani baƙin rami ko karamin tauraro da yake zagaya wani tauraron mai nauyi da ke kusa da shi kusan ninki 20 sama da yadda rana ke yi. Wannan karamin tauraron, babban tauraro ne ya rage girma ya koma haka. Yana zagayan ne na awa uku, wanda a wannan lokacin ne hasken daukar hoton yake komawa farko. Da wannan ne da kuma sauran bayanai, masu ilimin sararin samaniyar suka gano cewa duniyar da suke bincike a kanta din girmanta ya yi kusa da Saturn, kuma tana manne ne da karamin tauraron ko baƙin rami da nisan kusan ninki biyu da nisan da Saturn din take daga rana. Dakta Di Stefano ta ce wannan tsarin da ya taimaka wajen samun nasarar gano wasu duniyar a hasken dandazon taurarinmu, yana daina aiki idan ana amfani da shi a wasu dandazon taurarin. Wannan ba zai rasa nasaba ba da cewa girman nisan da ke tsakani yana rage karfin hasken da ke kaiwa ga na'urar hangen nesan. Sannan kuma yana nufin akwai wasu abubuwa da suka taru a cikin dan ramanin wajen (kamar yadda aka gano daga duniyar nan da muke ciki) wanda hakan ya sa ake shan wahala wajen gano wasu taurarin. Da wadannan hotunan, ta ce, ""watakila akwai wasu alamun da dama da za a iya gani a dandazon taurarin. Amma dai wasu daga cikin alamun suna da haske matuka da za su isa mu dauko hoton hasken da ke ciki. ""A karshe, manyan hasken da ke fita daga karamin wajen, wucewar wata duniyar za ta iya dan tare shi, ko kuma ta tare dukan haskensa kamar muka gani a namu binciken."" Masu binciken sun kara da cewa ana bukatar karin bayani domin tabbatar da binciken nasu. Sai dai wani kalubale shi ne yanayin girman layin duniyar ya sa ba za ta sake wucewa ba sai nan da kusan shekara 70, wanda hakan ke nufin takaita yiwuwar bibiyar binciken a nan kusa. Wani karin bayanin kuma da masana sararin samaniyar suka gano shi ne kasancewar iskar gas da ƙura da ke wucewa ta gaban wajen da aka dauko hoton ma na iya janyo dusashewar hasken da suka gani. Amma dai sun ce suna tunanin da wahala hakan ya faru domin alamun da suka gani ba su yi daidai da yanayin iskar gas ba. ""Muna sane cewa wannan bincike ne mai muhimmanci, don haka muke kira ga sauran masana sararin samaniya su yi dubi ga bayanan cikin tsanaki,"" in ji Julia Berndtsson na Jami'ar Princeton da ke New Jersey, wanda ke cikin wadanda suka wallafa binciken. ""Muna tunanin muna da hujja mai karfi, kuma wannan shi ne tsarin binciken kimiyya."" Dakta Di Stefano ta ce sababbun na'urorin hangen nesa ba za su iya magance matsalar da ake fuskanta ba ta duhu da taruwar abubuwa a waje daya, don haka suke tunanin amfani da daukar hoto din ne zai cigaba da zama mafi sauki wajen gano wasu duniyar a cikin wasu dandazon taurari. Sai dai ta ce akwai wani tsari da ake kira microlensing da zai iya taimaka wajen saukake gano wasu duniyar. An wallafa wannan binciken a Mujallar Nature Astronomy." https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-59067002 +entertainment Shin Rahama Sadau ta sauya sana'a ne? Jarumar fina-finan Kannywood da Nollywood Rahama Sadau, ta raba kafa inda ta bude wani wajen ciye-ciye da shaye-shaye a Kaduna mai suna Sadauz's lounge. Jarumar wadda fitacciya ce a cikin fina-finan Hausa na kannywood, ta bude wajen ne musamman domin matasa. Ana gudanar da abubuwa da dama a wajen, kamar gasa nama da kifi da kuma shan lemuna da shisha. Kazalika akwai kuma wajen gyaran gashin mata da na maza da wajen kwalliya da kuma wasanni kala-kala domin nishadi. A shafinta na twitter, Rahama Sadau ta wallafa wasu daga cikin hotunan bude wajen, inda ta gayyaci 'yan uwa da abokan arziki domin su ta ya ta murna. An ci an sha a wannan waje. Jama'a na ganin cewa kamar Rahama Sadau ta raba kafa ne shi ya sa ta bude wannan waje, kasancewa ba kasafai ta ke fitowa a fina-finai ba a yanzu. A shekarun baya, tauraruwar fina-finan Hausa Rahama Sadau ta sha suka musamman a kafofin sada zumunta sakamakon rungumar mawakin nan, Classiq da ta yi. Wannan ya jawo suka matuka ga Rahama Sadau da Kannywood baki daya, inda akasarin jama'a ke nuna cewa abin da ta yi ya saba wa addininta da kuma al'adar Bahaushe. Wannan ne ya ja har hukumar da ke sa ido kan tace fina-finai ta dakatar da ita duk da cewa wasu sun yi korafi kan cewa wasu 'yan wasan sun yi abin da ya fi na Rahama, kuma ba a dauki mataki a kansu ba. https://www.bbc.com/hausa/labarai-50728321 +entertainment Tunanin wasu 'yan Afirka kan Sarauniya Elizabeth ta biyu "Rasuwar Sarauniya Elizabeth na biyu ya jefa mutane cikin jimami da aike sakonni ta’azziya masu sosai rai daga shugabanni duniya da sauran daidaikun mutane. Da dama a kasahen da Burtaniya ta mulka na tunawa da mulki da kuma alakarsu da Sarauniyar, wasu kuma na dauko tsofaffin hotunan da suke yi tare da mai alfarma Elizabeth a kasashensu. Sai dai ba kowa ne ke yabonta ba. Wasu mutuwarta ta tuna musu da kazamin jinin da aka zubar a lokacin mulkin mallaka – cin zarafin da aka aikata a kasashen Afirka, satar kadarori da kayayyakin tarihi daga kasashen yammacin Afirka, gwala-gwalai da daiman daga Kudancin Afirka da Indiya, bautarwa da musgunawa. Yayinda Shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, ya bayyana Sarauniyar a matsayin mace ta daban da ta yi fice a duniya, da za a ci gaba da tunawa da ita a fadin duniya, dan jam’iyyar gwagwarmayar ‘yanci ta Economic Freedom Fighters party (EFF), ya ce ba ya cikin mutanen da ke wannan juyayi. ""A shekaru 70 da ta kwashe tana mulki, ba ta taba yarda da laifukan da Burtaniya da ‘yan gidan sarautar suka aikata a sassan duniya ba, kuma ta kasance wacce ke alfahari wajen daga tutar cin zali, "" a cewar sanarwar da jam’iyyar da ke ta uku mafi karfi a kasar ke cewa. ""A wajenmu mutuwarta ta tunasar da mu mumunan yanayi na bakin ciki a wannan kasa da kuma tarihin Afirka. "" A shafukan sada zumunta ma, wasu masu sukan sun tsananta kalamansu. Wani sakon tuwita da wata 'yar Najeriya amma haifafiyar Amurka, Farfesa Uju Anya ta wallafa, sa'o'i bayan mutuwar Sarauniyar, ya haifar da muhawara mai zafi. Akwai sakon da shafin tuwita ma ya goge saboda saba ka'idojinsa. A sakonta na biyu, ta rubuta: ""Idan akwai wanda ya ke tunanin na ce wani abu face kyamar da nake yiwa masarautar da ta goyi-bayan gwamnati da ta dau nauyin kisan kare dangi da ya daidaita kusan rabin dangina, wanda har yanzu wadanda suka rayu na tattare da tasiri wannan ayyuka, za a jima ana mafarki."" Sakonta na nufin abin da ya faru a lokacin yakin Biafara a shekarun 1960, lokacin da gwamnatin Burtaniya ta goyi-bayan gwamnatin Najeriya da ba ta makamai wajen murkushe masu neman ballewa domin kafa kasar Biafra. Wani a shafin tuwita din mai suna, @ParrenEssential, ya mayar da martani, yana mai cewa wannan ba da'ar 'yan Najeriya ce ba, ya kara da cewa: ""Ba kya wakilartar al'adunmu da dabi'un 'yan kasa."" Wasu na cewa aibata mutum a lokacin mutuwarsa ba ""halayen 'yan Afirka ba ne."" An kuma rinka wallafa sakon neman a dawowa da daiman din Afirka, wanda aka gano a Afirka ta Kudu a 1905 da yanzu ake ganinsa kan kambin sarautar Burtaniya, har lokacin mutuwar Sarauniyar. Da dama daga cikin mutane sun rinka cewa na ""sata"" ne. Duk da cewa gwamnatin wancan lokaci ne suka bai wa gidan Sarautar Burtaniya a matsayin tukuicin nuna biyayyarsu, abin da ake cewa a shafukan sada zumunta shi ne kaddara 'yan Afirka ta Kudu ne. Wani mai amfani da shafin tuwita @Qban_Linx ya ce daiman din da kudinsa ya kai dala miliyan 400 - irinsa mafi girma makale a jikin sandar girmar da sarakuna ke rikewa a lokacin nadi - na iya biyan kudin jami'a na dalibai dubu 75 a Afirka ta Kudu. Hakazalika an samu irin wannan koke a Indiya, inda maudu'in ""Kohinoor"" ya rinka jan hankali a shafin tuwita bayan mutuwar Sarauniya Elizabeth - wannan na nufin daiman din da ke jikin kambin sarautar da matar sarki wato 'Queen Consort' za ta rinka sa wa. Wasu masu suka sun ce ya kamata Sarauniyar ta yi amfani da karfinta da tasirinta wajen tabbatar da cewa an mayar da kadarorin mutanen da suka yi yaki da Burtaniya lokacin mulkin mallaka. Kenya da Afrika ta Kudu sun bukace a maido mu su da kawunan gwarazansu irinsu Koitalel Samoei, da ya jagoranci bijirewa mulkin mallaka a Kenya ta yanzu a karshe karni na 19, da Sarki Hinstsa kaKhawula na masarautar Xhosa a Afirka ta Kudu, da aka kashe a 1835. An file kawunansu, sannan aka ta fi da su Burtaniya a matsayin lambar yabon nasara a yaki. ""Sun mamaye kasata, inda aka haifeni,"" kamar yada ya shaidawa kamfanin dilanci labarai na Reuters. ""Amma dai muna makokinta saboda ita ma 'yar adam ce,"" a cewarsa. ""Muna tausayin wadanda suka mutu."" Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta, wanda ya bayyana Sarauniya a matsayin ""wacce ta yi fice sosai wajen bautawa al'umma"", ya fuskanci caccaka daga wasu 'yan Kenya bayan ayyana makokin kwana hudu a fadin kasar. ""Tsohon shugaban Botswana, Ian Khama, shi ma ya kasance wani mutum da ya kare martabar Sarauniyar, yana mai cewa maye gurbinta da wuya. ""Ya ce mulkin mallaka ba abu ne da muke son mu tuna da shi ba, yanayi ne mafi muni,"" a cewarsa. ""Sarauniya ta gaji wannan tsari ne, ba wai ita ce ta kirkiro hakan ba...amma da ta bayyana sai ya kasance kamar ta gyara barnar da aka aikata ne, abubuwan da mulkin mallaka ya haifar, ta nuna cewa babu wanda yake saman wani, ta nuna tana son aiki da kowa saboda cigaba da taimakwa kasashe su habbaka."" Nahiyar Afirka tayi mata kallo a matsayin wacce ta kawo sauyi da bude sabon babin rayuwa daga kuncin da aka fuskanta a baya"" a cewarsa. Mutane da dama na cewa Sarauniyar ba ta taba neman afuwa ba kan laifukan da aka aikata da sunan masarautar. Kodayake ta taba magana kan yanayi mai wahala da kisan gilla da aka aikata a Amritsar, na arewacin India, a 1919. Kafin ziyartar yankin a 1997, yankin da wani janar din sojin Burtaniya ta umarci a bude wuta kan masu zanga-zanga a wurin da ba za su iya guduwa ba, ta yi tsokaci nadama kan abin da ya faru., ""Ba sa a iya sauya abin da ya faru a baya ba, duk da cewa ba hakan aka so ba. Komai na da bangaren bakin ciki da kuma na farin ciki. Dole mu koyi darasi daga bakin ciki domin gina farin ciki a gaba." https://www.bbc.com/hausa/articles/c72zlr5356lo +entertainment Prince Philip: An sallami mijin Sarauniyar Ingila daga asibiti bayan kwashe wata guda Mijin Sarauniyar Ingila ya bar asibiti da ke tsakiyar birnin London bayan an yi nasarar yi masa tiyata a zuciyarsa. An kwantar da Yarima Philip, mai shekara 99, a asibitin King Edward VII's da ke yankin Marylebone ranar 16 ga watan Fabrairu sakamakon rashin lafiyar da yake fama da ita. An yi nasarar yi masa tiyata a bangaren zuciyarsa a wani asibitin London - St Bartholomew's. Yariman ya koma fadar Windsor Castle bayan ya kwashe kwana 28, wanda shi ne lokaci mafi tsawo da ya taba kwashewa a asibiti. Da farko ba a bayyana dalilin kwantar da shi a asibiti ba, sai dai a lokacin fadar Buckingham Palace ta ce rashin lafiyar tasa ba ta da alaka da cutar korona. Yarima Philip da Sarauniyar Ingila, mai shekara 94, sun kwashe tsawon kullun da aka yi na baya bayan nan kan cutar korona a Ingila inda suka zauna a fadar Windsor Castle tare da ma'aikatansu marasa yawa wadanda ake yi wa lakabi da HMS Bubble. Ma'auratan, wadanda suka kwashe shekara 73 tare, an yi musu allurar riga-kafin Covid-19 karon farko a watan Janairu. Lokacin da yake jinya a asibitin King Edward VII's, dansa Prince of Wales. https://www.bbc.com/hausa/labarai-56413349 +entertainment Bidiyon nadin Sarauniya Elizabeth II Sarauniyar Ingila Elizabeth ta II, basarakiyar da ta fi dadewa a kan karagar mulkin Birtaniya, ta rasu a Balmoral tana da shekaru 96. Ta rasu ne bayan ta shafe shekaru 70 a kan mulki.Iyalanta sun taru a fadarta da ke Scotland bayan an rika nuna damuwa game da yanayin koshin lafiyarta ranar Alhamis. Sarauniyar Ingila ta hau kan mulki ne a 1952 kuma ta ga sauye-sauye da dama. An gudanar da bikin nadin Sarauniya Elizabeth II ne a Westminster Abbey ranar 2 ga watan Yunin 1953. https://www.bbc.com/hausa/articles/crgwnjz9qn0o +entertainment ...Daga bakin mai ita tare da Adamar Kamaye; Shirmen da na yi ina amarya Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon: Daga bakin mai ita wani shiri na BBC Hausa da ke kawo muku hira da fitattun mutane kan wasu abubuwan da suka shafi rayuwarsu zallah. A wannan kashi na 11, shirin ya tattauna da Zahra'u Saleh wadda aka fi sani da Adamar Kamaye, ta kuma bayyana irin abubuwan da suka fi burge ta a rayuwarta da wata kwaba da ta taba yi lokacin tana amarya mai karancin shekaru. Bidiyo: Fatima Othman https://www.bbc.com/hausa/labarai-51150025 +entertainment Wane hali Adam Zango ke ciki bayan barinsa Kannywood? "A kwanakin baya ne dai fitaccen jarumin fina-finan Hausan nan wato Adam A Zango ya fito karara ya bayyana ficewarsa daga masana'antar shirya fina-finai ta Kannywood. Bayan fitarsa daga masana'antar, ya bayyana cewa zai fara cin gashin kansa ne, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Instagram. Sai dai a wani sakon bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Instagram, ya bayyana cewa a yanzu ya samar da hanyar da zai rinka fitar da sabbin fina-finansa ta intanet, inda masu kallo za su je su siya kuma su kalla. A cewar Zango, babu yadda za a yi mutum ya kashe miliyoyin kudi wurin hada fim, kuma ya sake shi kara zube ko ya sa shi a Sinima, ""da wuya kudaden su dawo"". Da dama daga cikin 'yan kannywood sun dade suna korafi kan satar fasaha ta yadda mutum zai kashe kudi ya yi fim amma daga baya wasu su sace fim din su sayar. A lokacin da Zango ya fita daga masana'antar, ya ce ya yanke wannan hukuncin ne saboda zargin yadda ake shugabancin ""kama karya da rashin hukunta mai karfi ko arziki, saboda kwadayi da son zuciya."" Sai dai duk da cewa bai yi karin haske ba sosai game da abin da yake nufi da fita daga kungiyar ba, ganin cewa akwai kungiyoyi da dama da suke cikin Kannywood, wata kila wannan hanya da ya fitar ta sayar da fina-finai ta intanet na cikin hangen da ya yi ya fita domin fara cin gashin kansa." https://www.bbc.com/hausa/labarai-49596350 +entertainment Mawakin Iran da zai iya shan dauri kan saka mata Turawa a wakarsa "Mawakin kasar Iran Mehdi Rajabian, zai fuskanci zaman gidan yari kan yin wata waka. Ya riga ya shafe shekaru biyu a tsare - hadi da kadaice kansa da kuma yajin cin abinci - sakamakon sakin wakokin da mahukuntan Iran ba su amince da su ba. Amma ya jajirce. ''Ba zan ja da baya ba kuma ba zan tantance kai na ba,'' kamar yadda ya shaida wa BBC. Haka kuma, ya jima yana aiki a boye daga wani dakinsa na karkashin kasa a gidansa da ke Sari, a arewacin kasar Iran, don fitar da sabuwar waka. Wacce aka yi wa take da 'Coup Of The Gods', wakar ta kunshi kungiyar mawaka ta kasar Brazil, tare da mawaka daga kasashen Turkiya da Rasha da Indiya da Argentina da kuma mawaka mata biyu daga Amurka, Lizzy O'Very da Aubrey Johnson. Wadannan muryoyi sun kara wa wakokin Rajabian na bakin-ciki da gwagwarmaya armashi. Amma kuma suna kunshe da wasu kausasan kalamai na siyasa - saboda an haramta saka muryoyin mawaka mata a kasar Iran. Lokacin da Rajabian ya sanar da aniyarsa ta aiki tare da mata mawaka a shekarar da ta gabata, an cafke shi aka gurfanar da shi a gaban kotu, inda alkalin ya shaida masa cewa ''yana karfafa yin karuwanci''. Bayan da aka yi belinsa, ya ci gaba da hada wakokinsa, duk kuwa da barazanar daure shi a gidan yari da ake yi. Yanzu na kammala wakokin,''yanzu za su sake zargina'', kamar yadda ya shaida wa BBC,. ''Babu ko tantama a kai. Amma ba zan ja da baya ba. ""Abin takaici ne a ce a irin wannan zamanin muna maganar haramcin wakoki.'' Rajabian ya fara fuskantar matsaloli a shekarar 2013, lokacin da dakarun juyin juya hali suka kai samame ofishinsa, suka rufe wurin da yake shirya wakokin kuma suka kwashe na'urorinsa. A can baya yana amfani da wani suna da ke da'awar mata mawaka kuma yana aiki kan wakokin. Tarihin Iran daga Setar, wanda ya bayyana ya shafi abin ya faru a yakin Iran da Iraqi. An zarge shi da rarraba ''wakokin da ya hada a boye, da dama da suka kunshi kalmomi da sakonnin da ba su yi wa mahukuntan kasar Iran ko addinin kasar dadi ba,'' aka kulle shi a gidan yari. Rajabian ya ce ya shafe kwanaki 90 a tsare a kuma kadaice, tare da rufe masa idanu ta yadda ba zai iya sanin da abubuwan da ke kewaye da shi ba. Daga bisani ne aka bayar da shibeli, amma an sake cafke shi a shekarar 2015 - a wancan karon tare da dan uwansa mai shirya fina-finai, Hossein Rajabian - aka yanke musu hukuncin daurin shekaru shida a gidan yari, bayan shari'ar minti uku. Saboda nuna rashin jin dadi, duka 'yan uwan junan suka shiga yajin cin abinci har na tsawon kwanaki 40 days. Rajabian ya ce nauyinsa ya ragu da kilo 15, kuma ya rika yin aman jini. Abubuwan da ya fuskanta suna kara karfafa bude hanyar shirya sabuwar waka, mai taken ""The Whip On A Lifeless Body."" ''A rana ta 19 ta yajin cin abincin, na bude idanuna kuma ban san ko a mace nake ko a raye ba, a duniya nake ko a lahira. Na shiga wani hali na gushewar hankali. Wani irin yanayi ne."" Yajin cin abinci ya kuma sa gabobin Rajabian sun kumbura, hakan na nufin ba zai iya yin waka da kan sa ba. A maimakon haka, ya hada wakokinsa ya tura wa mawaka masu tausaya masa a fadin duniya. Sun shirya na su bangaren suka sake tura masa zuwa kasar Iran, inda ya sake harhada wakokin wuri guda, cikin fama da matsalar rashin karfin intanet da kuma sa idon da mahukuntan Iran ke yi akan sa. Wani mai shirya wakoki BaAmurke Harvey Mason Jr wanda ya taba rubutawa tare da hada waka da mawaka irin su Aretha Franklin da Michael Jackson da Beyoncé da kuma Britney Spears ne ya hada tare da sarrafa wakokin. ""A lokacin da na fara magana da Mehdi na ji sha'awar batun, daga nan ne lokacin da na ji labarinsa ya kara ba ni sha'awa,'' kamar yadda ya ya shaida wa BBC. ''Daga karshe lokacin da na saurari wakar, na ji wani irin dadi. ""Mehdi ya yi wani abu mai jan hankali da kuma kyau a cikin wani yanayi matsananci.'' Ana sa ran wakokin za su fita a ranar Juma'a, kuma hakan na zuwa ne makonni bayan da kungiyar Taliban ta karbe mulki a Afghanistan makwabciyar kasar Iran. Tuni dai sabuwar gwamnatin ta haramta saka wakoki a bainar jama'a, da suka kira a matsayin ''haramun a addinin Musulunci''; yayin da dakarun Taliban suka harbe mawakin gargajiya Fawad Andarabi bayan da suka janyo shi daga cikin gidansa. Rajabian ya bayyana cewa jajircewa ce kadai magani. ""A yankin Gabas ta Tsakiya, kayan kida kan zama wani makami mai karfi kamar bindiga,'' kamar yadda ya shaida wa BBC lokacin da a karon farko ya sanar da wakarsa a cikin watan Janairun shekarar 2020. A yanzu ya ce: ""Wata rana, mutane za su tuna baya su fahimci cewa ba waka kadai muke yi ba. Mun samar da ilimin falsafa da tunani mai zurfi game da rayuwar bil'adama ta hanyar waka. ""Yin shiru game da zalunci tamkar hada kai ne da masu zalunci. Ba zan taba yin shiru ba, Waka ta ita kadai ce makamin gaskiya, na jajirce wa duk wani camfi.'' A yayin da ba za a rika sauraron wakokin Rajabian a kasarsa ba, yana cike da fatan mutane a wasu kasashen za su rungume wakokin da kuma sakonnin tausayi da karfafa gwiwa. ""Muddin mutane za su saurari wakokina su kuma rika bibiya ta, zai taimaka min kasancewa a raye, ba a tauye muryata ba,'' in ji shi. ""Zan iya shaida wa duniya cewa babu wani mulkin danniya da zai hana 'yancin yin waka. Na fuskanci duka haramci da kuma kasancewa a gidan yari, kuma a yau na fitar da sabbin wakoki ga masu sauraro. Ko da kuwa zan kare a tsare.''" https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-58577793 +entertainment Nafisa Abdullahi: Tauraruwar Kannywood ta janye daga shirin 'Labarina' "Tauraruwar fina-finan Kannywood, Nafisa Abdullahi, ta ce daga yanzu ba za ta ci gaba da fitowa a shirin nan mai dogon zango mai suna 'Labarina' ba. A sakon da ta wallafa a shafinta na Intagram ranar Asabar da daddare, tauraruwar ta ce ta ji dadin rawar da ta taka a cikin shirin, sai dai ta ce ba za ta iya ci gaba da shi ba saboda wasu dalilai na kashin kanta. Amma wasu majiyoyi sun tabbatar wa BBC Hausa cewa ta dauki matakin ne saboda rashin jituwar da aka samu tsakaninta da mai shirya shirin kuma shugaban kamfanin Saira Movies, Malam Aminu Saira. Nafisa ita ce babbar tauraruwa a shirin na Labarina mai farin jini a tsakanin 'yan kallo inda take taka rawa a matsayin Sumayya. ""Janyewata daga [shirin] a wannan lokaci ya faru ne saboda yawan da ayyuka suka yi mini, ganin cewa hakan ba zai ba ni damar zuwa a dauki shirin na 'Labarina' ba. Ba kamar yadda ake tunani ba, aiki wajen daukar shirin 'Labarina' ya kasance wani abin jin dadi, na yi aiki a fayyace tare da masu daukar shirin, da furodusa da ma dukkan wadanda suka shiga wannan babban shiri, kuma ina cike da farin cikin ganin cewa zan bar shirin ba tare da wata tsana ga kowa ba,"" a cewar tauraruwar. Sai dai masu sharhi a masana'antar Kannywood na ganin fitar Nafisa daga cikin shirin zai yi matukar tasiri ganin cewa ta janye ne a yayin da ake kan wata gaɓa mai matukar muhimmanci. Hasalima tun kafin wannan sanarwa da Nafisa ta fitar, masu bibiyar shirin sun kosa a bayyana musu yiwuwar ci gaba da taka rawarta ko akasin hakan, bayan da aka nuna an sace ta kuma aka rika jan-kafa wajen nuna halin da take ciki." https://www.bbc.com/hausa/labarai-59849719 +entertainment Yadda masu kaurin murya suka fi jan hankalin mutane "Ƴan Faransa na kiransa ""voix de chambre à coucher"". Murya ce mai nauyi, mai ɗaukar hankali da ke bai wa wasu mutane ikon jan hankali. Akwai cikakken bayani kan wannan. Wasu na da murya mai daɗi fiye da wasu, kuma tun da kusan duka ƙasashen duniya sun amince da haka, wannan na nuna cewa wannan na da muhimmanci ga tarihin ɗan Adam. Karin harshe hanya ce ta gane mutane. Ana ganin masu magana da muryoyi masu daɗi a matsayin mutanen da suka san abin da suke yi kuma masu tausayi da riƙon amana. Wannan na sanya wa a yi masu kallon mutane masu ban sha'awa. Don haka, me ya sa wasu karin harshe ke da ɗaukar hankali? Akwai wani abu na musamman game da murya da kowa ke da shi. ""Duk al'adarka, duk macen da ta fito daga Japan ko Amurka ko Faransa ko ma wace ƙasa ce a duniya - sun fi son maza masu kaurin murya,"" in ji Melissa Barkat-Defradas, wata mai bincike kan harsuna a Jami'ar Montpellier. An gano cewa son kasancewa da maza masu kaurin murya a ko in ane kama daga dajin Amazon zuwa Tanzania da daruruwan wasu ƙasashen na Yamma da waɗanda ba na Yamma ba. Mutane na alaƙanta kaurin murya da iya farauta da nasara a wurin aiki da ƙarfi. Muna ganin ƴan siyasa masu kaurin murya a matsayin masu mayar da hankali kuma waɗanda za mu iya zaɓa, ko mace ko namiji. Mata da maza masu neman aiki da ke da kaurin murya sun fi saurin samun aiki. Me wannan ke nufi kan yadda muke kallon halayyar mutum? Hawan sautin muryar maza da mata na raguwa a lokacin balaga. Amma kana iya gane yadda hawan sautin muryar namiji zai kasance dangane da yadda take a lokacin da yake shekara bakwai. Sautin murya ya danganta ne da yawan sinadarin testosterone a jiki, wanda ke taka muhimmiyar rawa a zaɓen wanda za a yi tarayya da shi. Yawan sinadarin testosterone ga maza manya ya danganta da yawan sinadren androgens da suka samu daga mahaifiyarsu a makonnin takwas zuwa 24 na ciki. Wannan na nufin cewa wani abu da ka iya taka rawa a yawan ƴaƴanmu ya samo asali ne tun daga kuruciya kuma yana da alaƙa da sinadrin hormones da iyayenmu mata ke da su kafin a haife mu. Sai dai irin muryoyin da maza su ka fi so a mata sun sha banbam. Tsawon lokaci an yi tunnain cewa maza sun fi son mata masu zaƙin murya. Sai dai kallon da ake yi wa mata masu kaurin murya a matsayin masu jajircewa ya janyo wani tunani mai zurfi daga masana Pisanki da Barkat-Defradas: Shin muna iya sauka sautin muryarmu zuwa yadda muke so? Bincike ya gano cewa muna sauya sautin muryarmu ta zo dai-dai da wanda muke magana da shi, kuma idan muna so mu nuna soyayyarmu ko kulawarmu ga wanda muke tare da shi a lokacin, sai mu karya sautin muryarmu ta yi kama da nasu, a cewar Pisanki. Haka kuma, saukewa ko ɗaga sautin muryarmu na iya zama alama ta yadda mu ke son mutum, kuma yana jan hankalin wanda mu ke tare da shi. Muna amfani da muryarmu wajen karkatar da tunanin wasu mutane. Idan muna hira mai daɗi da wani, mu na sauya muryarmu. Amma idan muna hira da wanda ya ɗauki hankalinmu, lamarin na sauyawa. Ga maza, sai muryarsu ta ƙara yin ƙasa yayin da a mata kuma, sai muryarsu ta ƙara sama. Wani bincike da aka yi kan wasu ƴan Faransa, ya nuna cewa maza sun fi son mata masu kaurin murya - abin da Pisanki ya ce hakan na iya nuna cewa abubuwan da maza ke so a mata na sauyawa, wato sun fi son mata masu son mata masu cike da buri kuma masu son yin aiki sosai. ""Babu mamaki mata na so ne su mayar da muryarsu kamar ta maza - mai hazaƙa. Mata yanzu sun fara magana a hankali,"" a cewar Pisanki. ""Kuma babu mamaki, a wasu al'adun maza na son matan da ke nuna girma da hazaƙa."" Idan kuna neman wani dalilin da zai hana ku karya harshe, akwai shaidar cewa idan ba ku yi ba ya fi. Ana ganin mutanen da ba su cika kyau ba kuma ba su fiye muni ba kuma muryoyinsu ma haka suna da wasu ƙwayoyin halitta da ke taimaka wa garkuwar jikin da ke gano waɗanne ƙwayoyin halittar ne na jikinmu kuma waɗanne ne ba namu ba. Yin hakan na nufin saurin gano ƙwayoyin cuta da kashe su. Da aka tambayi Pisanki, ta amince akwai wariya da ake nuna wa wajen bincike kan muryar maza. Waɗannan bincike-binciken sun kafu ne kan yadda jikinmu ke aiki da abin da muke so. Don haka, ga mu sauran mutane, watakil kawai mu samu gamsuwa a wanda ya iya hira." https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-57382264 +entertainment Shekara saba'in na mulkin Sarauniya: Dan Najeriya da ya nemi zama ma'aikacin Sarauniyar Ingila Elizabeth "A cikin jerin wasikun da muke samu daga Afrika, marubuciya Adaobi Tricia Nwaubani ta yi duba ne dangane da ko ana murnar cikar Sarauniyar Ingila shekara 70 kan karagar mulki a Najeriya. Najeriya ce ƙasa mafi girma da Ingila ta mulka a zamanin mulkin mallaka kuma ƙasa ce mai tasiri a cikin ƙasashen rainon Ingila. ""Abu mai muhimmanci a gare ni shi ne har yanzu sarautar bata mutu ba,"" in ji Chuka Mordi, wanda ya nemi ya zama dogarin Sarauniya shekarun baya da suka wuce bayan ya tafi London daga Benin da ke kudancin Najeriya domin ya yi karatu. A yanzu da yake cikin shekarunsa na 50, wanda kuma ya kammala King's College da ke London, shugaban wani kamfanin zuba jari ne a Legas, kuma ya yi waiwaye kan neman aikin da ya yi da kuma takardar ƙin amincewa da ya samu daga fadar Sarauniya. ""Ina tunanin na yi wani abu na shashanci da na tambayi albashi mai gwaɓi sakamakon irin cancantar da na yi fiye da kima,"" in ji shi. Ijay Uwakwe-Okoronkwo, wadda mai aikin tuntuɓa ce a ɓangaren ilimi a Abuja, ta saka hoton Sarauniya Elizabeth a matsayin hotonta na Whatsapp. ""Abu ne mai kyau da na ga Sarauniya a cikin ƙoshin lafiya,"" in ji shi. An haifi Ms Uwakwe-Okoronkwo shekara 50 da suka gabata a lokacin da iyayenta ke karatu a Ingila. Ta dawo da iyalanta Najeriya a cikin shekarun 1970 kuma tun daga lokacin ta koma ƙasar haihuwarta ne ba sosai ba domin hutu. ""Bari mu gani, na samu tagomashi sakamakon haihuwata da aka yi a Ingila,"" in ji ta. "" Ina da fasfo ɗin Birtaniya, a wannan lokacin da muke samun matsalolin siyasa a Najeriya, babu wanda ya damu. Muna fama da matsalolin wuta da ƴan bindiga, ana yin garkuwa da mutane kuma kuma ana maganar cika shekara 70?"" Mutanen Duke town da ke kudancin Najeriya a birnin Calabar na da alaƙa mai ƙarfi da iyalan gidan sarauta, wanda wannan alaƙa ta samo asali ne tun daga ƙarni na 19 a lokacin da ɗaya daga cikin sarakan yankin ya shiga kasuwanci da Sarauniya Victoria. Akwai kwafi na takardun kasuwancin da aka yi a tsakanin Sarauniya Victoria da Sarki Eyamba da Sarki Honesty waɗanda suna nan ajiye a gidan tarihi na Calabar, wanda gidan tarihin a baya ya kasance hedikwatar gudanarwa ta Birtaniya a kudancin Najeriya. Kuma a kodayaushe akwai kujerar da babu kowa da aka ajiye wa sarki ko sarauniyar Birtaniya idan za a yi naɗin sarki a Calabar wanda aka fi sani da Obong. Sai dai batun cika shekara 70 ya kasance wani abu da ya yi nisa da zukatan mutane. ""A gaskiya, babu wasu shirye-shirye,"" in ji Charles Effion Offiong-Obo, wanda shi ma babba ne a garin Duke. ""Najeriya na da abubuwan da take fama da su. Muna cikin shirin sauya sabuwar gwamnati ba da daɗewa ba. An kaɗa gangar siyasa kuma jama'a sun zaƙu su ga abin da zai biyo baya kuma ba su cika mayar da hankali kan nishaɗi ba,"" in ji Charles, inda yake nufin jam'iyyun da ke zaɓen waɗanda ke takarar shugabancin ƙasa a zaɓen baɗi. Ko dai ƴan Najeriya sun damu ko ba su damu da batun cikar Sarauniya shekara 70 kan karagar mulki ba, ƙarsarmu na da alaƙa mai ƙarfi da ita. Birtaniya tana da ƙasashe 54 waɗanda ta rena. An kafa ƙungiyar ƙasashen renon Ingila a 1931, ƙungiya ce da aka kafa a zamanin mulkin mallakar Birtaniya. Shiga cikin ƙungiyar zaɓi ne, akwai wasu ƙasashe masu ƴancin kai na Afrika 18 da suke cikin ƙasar har da Najeriya. Ƙasashen da suka shiga ƙungiyar daga baya sun haɗa da Rwanda da Mozambique kuma ba su da wani tarihi da ya haɗa su da Birtaniya, kuma sun nemi su shiga ƙungiyar inda aka bar su kuma suka shiga. Ana jinjina wa Sarauniya Elizabeth da shawo kan shugabannin farko na Afrika bayan samun yancin kai da su shiga ƙungiyar renon Ingila. Shekara biyu bayan da Ghana ta zama ƙasar Afrika ta farko da ta samu ƴancin kai daga Birtaniya, Sarauniya ta kai ziyara ƙasar a 1961. A ƙarshen ziyarar da ta kai ta kwanaki 11, an bayyana cewa shugaban Ghana na lokacin kuma ɗan gwagwarmayar neman ƴancin Afrika wato Kwame Nkrumah ya alaƙanta ƙungiyar ƙasashen rainon Ingila a matsayin ƙungiya mai ɗauke da ƙasashe da ke da akidu iri ɗaya da alƙibila wadda za ta taimaka wa burinsa na yaƙar wariyar launin fata da kuma rashin adalci. A lokacin sai lamarin ya zama abu mai sauƙi ga shugabannin Afrika su bi sahunsa. Haka kuma tsoffin shugabanni sun yi amfani da ƙungiyar wurin yaƙi da wariyar launin fata a Afrika Ta Kudu. Duk da cewa shugabancin ƙungiyar ba wani abin gado bane, Amma Sarki George VI shi ne shugaban ƙungiyar na farko haka kuma Sarauniya Elizabeth ita ce ta karɓi jagorancin daga gare shi." https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-61708597 +entertainment Waƙar 'Mai Waƙa' Waƙar Mai Waƙa https://www.bbc.com/hausa/labarai-59808203 +entertainment Hannafi Dan Ibro: Abin da ya sa na gaji mahaifina "Latsa hoto da ke sama domin kallon hira da Hannafi Rabilu Musa: Hannafi Rabilu Musa, dan marigayi Rabilu Musa Dan Ibro, ya ce ya gaji mahaifinsa a harkar wasan kwaikwayo ne saboda abubuwan alherin da ya yi lokacin rayuwarsa. Hannafi, wanda shi ne na biyar cikin 'ya'yan Dan Ibro 19, ya shaida wa BBC Hausa cewa ""abin da ya sa na zabi fannin wasan kwaikwayo shi ne saboda ina ganin abubuwa kala-kala da ake yi wa mahaifina kamar addu'a; rana ba za ta fito ta fadi ba tare da an yi masa addu'a ba da fatan alheri."" Ya kara da cewa ya zabi fannin barkwanci ne saboda ya zama silar yaye wa mutane oirin damuwar da ke damunsu sanna ya sanya su nishadi." https://www.bbc.com/hausa/media-58460642 +entertainment Daga Bakin Mai Ita tare da Ali Jita Daga Bakin Mai Ita wani shiri ne na BBC Hausa da ke kawo muku hira da fitattun mutane kan wasu abubuwan da suka shafi rayuwarsu zalla. A wannan kashi na 75, shirin ya tattauna da fitaccen mawakin nan na Hausa Ali Jita, inda ya amsa tambayoyin da suka shafi rayuwarsa da fina-finai. Ɗaukar bidiyo: Fatima Othman Tace bidiyo: Umar Rayyan https://www.bbc.com/hausa/media-59498591 +entertainment Abin da ya sa nake taka rawar Baba Dan Audu a shirin Labarina Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon: Rabi'u Rikadawa wanda ke fitowa a matsayin Baba Dan Audu a shirin Labarin mai dogon zango ya bayyana wa BBC dalilin da ya sa yake yin rawar da yake takawa a shirin. https://www.bbc.com/hausa/labarai-59204152 +entertainment Yadda matan Sudan Hausawa ke taron shan gahawa Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon: Matan Sudan Hausawa na taruwa lokaci zuwa lokaci don shan gahawa da yin hira da kuma rera waƙoƙi har ma da taka rawa, duk domin sa da zumunci. Baya ga haka kuma irin wannan taruwa sun ce na taimaka musu wajen yaye damuwarsu, tare da sanya su nishaɗi. Sannan kuma su ya su Hausawa ne suka irin wannan taro, sai dai jefi-jefi su kan gayyaci matan Larabawan Sudan ɗin su halarta. Waɗanda suka yi aiki a kan bidiyon Bidiyo: Fauziyya Kabir Tukur Tacewa: Yusuf Ibrahim Yakasai https://www.bbc.com/hausa/media-57254559 +entertainment ...Daga Bakin Mai Ita tare da Lubabatu Madaki Latsa hoton sama domin kallon bidiyon Daga Bakin Mai Ita wani shiri ne na BBC Hausa da ke kawo muku hira da fitattun mutane kan wasu abubuwan da suka shafi rayuwarsu zalla. A wannan kashi na 80, shirin ya tattauna da fitacciyar 'yar wasan Hausa Hajiya Lubabatu Madaki. A cikin hirar ta shaida mana dalilin da ya sa take yawan jefa karin magana a fina-finai. Tsarawa da gabatarwa: Halima Umar Saleh Ɗaukar bidiyo/Tacewa: Abdulsalam Usman Abdulkadir https://www.bbc.com/hausa/media-59880795 +entertainment ...Daga Bakin Mai Ita tare da Hannatu Bashir Danna hoton da ke sama domin kallon bidiyon: Daga Bakin Mai Ita wani shiri ne na BBC Hausa da ke kawo muku hira da fitattun mutane kan wasu abubuwan da suka shafi rayuwarsu zalla. A wannan kashi na 101, BBC ta tattauna da Hannatu, inda ta amsa tambayoyin da suka shafi rayuwarta. https://www.bbc.com/hausa/media-61722587 +entertainment Sean Connery: Tauraron shirin James Bond ya mutu "Tauraron nan da ya fito a fina-finan James Bond, Sean Connery, ya mutu yana da shekara 90 da haihuwa. Tauraron, wanda ɗan asalin Scotland ne a Birtaniya, ya yi fice a fim ɗin James Bond kuma ya shafe sama da shekara 50 a masana'antar fim ana gwagwarmaya da shi. Rahotanni sun bayyana cewa Mista Connery ya mutu ne a cikin baccinsa a Bahamas bayan ya shafe lokaci mai tsawo ba shi da lafiya. Wasu daga cikin fina-finan da ya yi da suka yi fice sun haɗa da The Hunt for Red October da Highlander da Indiana Jones and the Last Crusade, sai kuma The Rock. Sean Connery ya lashe kyautar Oscar a 1988 sakamakon irin rawar da ya taka a fim ɗin The Untouchables. Ɗan marigayin, Jason Connery ya bayyana cewa sai da mahaifinsa ya gayyaci 'yan uwansa da yawa zuwa ƙasar Bahamas suka zo wurinsa, inda a dare ɗaya ya mutu. Sir Sean, wanda aka haifa a Fountainbridge da ke Edinburgh, ya fara taka rawa a fim ɗin James Bond na Dr No a 1962, inda bayan nan ya yi wasu guda shida da suka haɗa da From Russia with Love da Goldfinger da Thunderball da You Only Live Twice. Bayan nan kuma sai ya yi fim ɗin Diamonds Are Forever da kuma Never Say Never Again. Mutane da dama na cewa shi ne wanda ya fi ƙwarewa ko kuma dacewa da 007, wanda shi ne tauraro a fim ɗin. Sarauniyar Ingila ta ba shi kyautar girmamawa a shekarar 2000. Masu shirya fim ɗin na James Bond, Michael G Wilson da kuma Barbara Broccoli sun ce sun kaɗu bayan jin mutuwar jarumin. Sun bayyana cewa: ""Ana ci gaba, kuma za a ci gaba da tunawa da shi a matsayin asalin wanda ya fara taka rawa a fim ɗin James Bond."" Sun kuma bayyana cewa ya bayar da gudunmawa matuƙa wurin ganin cewa wannan fim ɗin ya samu karɓuwa, haka kuma sun ce za su ci gaba da gode masa har abada. Sir Sean, na ɗaya daga cikin masu goyon bayan Scotland ta samu 'yancin kai, inda a wata hira da aka yi da shi ya ce zai iya barin gidansa da ke Bahamas domin ya koma Scotland ya ci gaba da zama idan ta zaɓi ta ɓalle daga Birtaniya." https://www.bbc.com/hausa/labarai-54762448 +entertainment Tagwayen Asali: Tagwayen da ke amfani da waya ɗaya kuma suke son auren tagwaye "Ku latsa hoton sama ku kalli Tagwayen Asali: Wasu tagwaye mawaƙa da ake kira Tagwayen Asali sun bayyana wa BBC cewa waya ɗaya suke amfani da ita saboda tsabar shaƙuwa. ""Ai duk wanda ya kira waya cewa yake zai yi magana da tagwayen asali ba guda ɗaya ba, saboda haka ba ma raba waya, da guda ɗaya muke amfani,"" a cewarsu. Tagwayen sun ce burinsu shi ne su auri Hasana da Husaina kamarsu kuma sun bayyana dalilansu game da hakan." https://www.bbc.com/hausa/media-56391584 +entertainment Durban July: Hotunan sukuwar dawaki mafi ƙayatarwa ta Afirka ta Kudu Ana sa ran dubun dubatar 'yan Afirka ta Kudu za su kama hanyar birnin Durban a ranakun ƙarshen makon nan saboda bikin shekara na Durban July, inda ake gudanar da tseren dawaki mafi girma. Sai dai da yawa daga cikinsu za su je ne saboda kwalliya da kuma tallata ƙayan ƙawa. An baje kolin kayayyakin ƙawa don nuna baiwar da masu ƙirƙira na ƙasar ke da ita. An zaƙu a ga bikin na wannan shekara saboda shekara biyu ke nan ana gudanar da shi a ɓoye saboda annobar korona da ta addabi duniya. Daga cikin fitattun da ke halartar bikin akwai tauraruwar fim Jessica Nkosi. Tabbas akwai sauran jama'a da za su kalli tseren dawakin. Bikin har wa yau, wata dama ce ta tayar da komaɗar tattalin arzikin ƙasar, wanda ya samu naƙasu sakamakon ambaliyar ruwa a kusa Durban a watan Afrilu, da kuma tarzomar da aka yi shekarar da ta wuce bayan an ɗaure tsohon Shugaban Ƙasa Jacob Zuma. Amma dai ga mafi yawan mutane, nuna kwalliya da tallata kayan ƙawa ne a gabansu. Dukkan hotunan na da haƙƙin mallaka. https://www.bbc.com/hausa/labarai-62029385 +entertainment Hotunan Afirka na mako 26 ga Maris zuwa 1 ga Afrilu 2021: Mai koyon harbi, biri mai dan kunne Wasu daga cikjin ƙayatattun hotunan sassa daban-daban na Afirka: Dukkan hotunan suna da hakkin mallaka https://www.bbc.com/hausa/labarai-56617868 +entertainment Aisha ta tuna da mahaifiyarta Maryam Babangida Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon: Diyar tsohon shugaban Najeriya Aisha Babangida, ta ce ta gayyaci dukkanin matan tsofaffin shugabannin kasar domin a koyi wani abu daga tarihinsu da ayyukan da suka yi a baya na taimaka wa kasa. Aisha ta bayyana hakan ne a wata hira da BBC ta yi da ita a bayan taron, wanda ta shirya shi don tunawa da shekara 10 na mutuwar mahaifiyarta Maryam Babangida. Ta kuma bayyana cewa ya kamata a fara tallafa wa mutane musamman na kusa, ta hanyar ba su abubuwan da zai inganta rayuwarsu. https://www.bbc.com/hausa/media-51388944 +entertainment Waƙar 'Ƙaddarar Rayuwa' Waƙar 'Ƙaddarar Rayuwa' https://www.bbc.com/hausa/labarai-59812165 +entertainment Ina hada karatun jami'a da wakar zamani - Geeboy Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon: Mawaki Abdullahi Abdullahi da aka fi sani da Geeboy ya ce waka na saka shi nishadi, kuma yana karatun jami'a da waka a lokaci guda. https://www.bbc.com/hausa/media-58596801 +entertainment Dan wasan Hausa Sani Garba SK ya rasu "Allah Ya yi wa fitaccen ɗan wasan fina-finan Hausa Sani Garba SK rasuwa a yau Laraba a birnin Kano, bayan ya sha fama da rashin lafiya. Wani fitaccen furodusa Abdul M Amart Mai Kwashewa ne ya tabbatar wa da BBC rasuwar ɗan wasan. Marigayin ya rasu ne a Asibitin Muhammadu Abdullahi Wase da ke Nasarawa a ranar Laraba da yamma. ""Sani SK ya kai kusan shekara uku yana jinya a tsattsaye, amma rashin lafiyar ta taso masa sosai ne a baya-bayan inda ya shafe mako biyar yana jinya a asibitin,"" in ji Amart. Amart ya ƙara da cewa tun asali cutar ciwon suga ce yake fama da ita, wacce daga bisani ta haifar masa da cututtuka irinsu ƙoda da hanta da hawan jini. A baya dai an sha yaɗa jita-jitar rasuwar Sani SK, inda ya dinga musantawa da kansa ma a wasu lokutan. ""A ranar yau da ya rasu ɗinnan aka fara yi masa wankin ƙoda,"" a cewar Furodusa Amart, wanda shi ke tsaye a kan kula ɗaukar nauyin kula da lafiyar marigayin. Sani Garba SK ɗan asalin unguwar Zage ne a cikin birnin Kano, kuma a baya kafin ya fara harkar fina-finai mai yabon Manzon Allah ne a ƙungiyar Usha'un Nabiyyu. Kafin kwanciyarsa a Asibitin Nasarawa sai da ya kwanta a Asibitin Murtala da ke cikin birni. Abdul Amart ya ce tuni aka tafi da gawar mamacin gida, kuma za a yi jana'izarsa a gobe Alhamis." https://www.bbc.com/hausa/labarai-59674814 +entertainment Ba a fahimce mu kan batun tace fina-finan YouTube ba - Afakallah Danna hoton sama domin kallon bidiyon Shugaban hukumar tace fina-finai da dab'i ta jihar Kano Malam Ismail Naabba Afakallah ya ce mutane sun yi musu mummunar fahimta kan batun cewa sai an tantance fina-finan Hausa da ake sa wa a YouTube. Malam Isma'ila Afakallah ya ce dokar za ta yi aiki ne kawai kan fim din da aka yi a Kano, ko kuma wanda ya yi fim din ya yi rijista da hukumar tace fina-finai ta Kano. Shugaban ya kuma ce ba ya nadamar daukar duk wani mataki a matsayinsa na shugaban hukumar ta tace fina-finai ta Kano. Ya kara da cewa ba shi da matsala da kowa a Kannywood, amma ba za su lamunci raini da keta doka ba. https://www.bbc.com/hausa/media-61224200 +entertainment Sauraron waƙoƙin kaset ne ya sa na zama mawaƙi – Jaziri Jaziri Sabon Cele mawakin Hausa ne ɗan asalin jihar Adamawa wanda ya fara shauƙin rera waƙa daga saye da sauraron waƙa a kaset. Yanzu haka Jaziri ya ce ya rera waƙa ‘kusan dubu ɗaya’, inda ya ce yana matukar ƙaunar waƙarsa mai taken ‘Kalamai Na So’. https://www.bbc.com/hausa/articles/c19vy0p7wpmo +entertainment Kannywood: ‘Yan fim na jimamin mutuwar Ahmad Tage "Ƴan wasan fina-finan Kannywood na alhinin rasuwar abokin sana'arsu Ahmad Tage wanda Allah Ya yi wa rasuwa. Ahmad Tage ya rasu ne bayan jinyar rashin lafiya a asibitin Nasarawa da ke jihar Kano. Ya fi fitowa a fina-finan barkwanci a tsawon lokacin da ya kwashe a harkar, wadda ya fara a matsayin mai daukar bidiyo, kafin daga bisani ya rikide ya zama tauraro. 'Yan uwansa sun shaida wa BBC Hausa cewa ya rasu ya bar mata biyu da 'ya'ya 21. Tuni 'yan wasan Hausa na Kannywood suka shiga alhini tare da mika ta'aziyyarsu a shafukan sada zumunta. Fitaccen jarumi Ali Nuhu ya sanar da labarin mutuwar Ahmad Tage a shafinsa na Instagram tare da yi masa rokon gafarar Allah. Taurari da sauran masu ruwa da tsaki a Kannywood da dama ne suka bayyana alhinin rasuwar Ahmad Tage. Taurari irin su Saratu Daso da Maryam Booth da Abdullahi Nuhu da mawaƙa irin su Ado Gwanja sun yi wa mamacin addu'ar Allah ya jikansa. A sakon da ta wallafa a shafinta na Instagram, Jaruma Saratu Daso ta ce mamacin wanda darakta ne kuma Jarumin kuma mai ɗaukar hoto ya rasu ne a ranar Litinin. Daso ta yi masa addu'ar rahamar Allah. Shahararren mawakin zamani kuma jarumin fina-finan Kannywood Ado Gwanja shi ma ya aika da ta'aziyyarsa a shafin na Instagram. Ya ce: ""Allah ya jaddada rahama a gareka mutumin kirki Allah ya sa ka huta."" Jarumi Saddiq Sani Saddiq ya aika da saƙon ta'aziyar rasuwar Ahmed Tage a shafinsa na Instagram inda ya ce: Allah ya maka rahama Tage, mu kuma Allah ya kyautata karshenmu."" Jaruma Maryam Booth ta sanar da rasuwar Ahmed Tega a shafinta na Instagram tare da yi masa addu'a. Jarumi Nuhu Abdullahi shi ma ya yi wa mamacin addu'a." https://www.bbc.com/hausa/labarai-58549783 +entertainment Prince Philip: Shugabannin kasashen duniya na mika sakon ta'aziyyar rasuwar mijin Sarauniya "Sarakuna, shugabannin kasashe da firaiministoci a fadin duniya, na yanzu da wadanda suka gabata, suna ta aike wa da sakon ta'aziyya kan rasuwar Yarima Philip, Duke na Edinburgh wanda ya mutu yana da shekaru 99. Sarki da Sarauniyar Sifaniya sun aike da sakon telegram da ke cewa ""Ya ke mai girma Goggo Lilibet"" domin yin alhinin rasuwar ""Mai girma Philip"". Shugabannin kungiyar kasashen rainon Ingila sun jinjina masa bisa ayyukan da ya yi na ci gaban jama'a. Sun gode masa bisa yadda ya tafiyar da rayuwar a kan aiki tukuru da sadaukarwa ga Sarauniya. Shugaban Amurka Joe Biden shi ma ya mika sakon ta'aziyyarsa, inda ya yaba wa marigayin a kan sadaukarwarsa ""ga al'ummar Birtaniya, da kungiyar kwamanwel da iyalansa"", da ma gudunmawar da ya bayar lokacin Yakin Duniya na Biyu, da rajin inganta muhalli da kuma karfafa wa matasa gwiwa. Mijin sarauniyar, wanda Fadar Buckingham ta sanar da mutuwarsa ranar Juma'a, ya yi wa Sarauniya rakiya a tafiye-tafiye daruruwa da ta yi zuwa kasashen waje. 'Jin dadin zama' Yarima Philip yana da dangantaka ta jini da gidajen sarautar kasashen Turai da dama, na da da na yanzu, kuma da yawa daga cikinsu sun aiko da sakon ta'aziyya. A sakon telegram daga Sarki Felipe da Sarauniya Letizia na Sifaniya suka aika, sun bayyana ""dukkan soyayyarmu da kaunarmu"" zuwa to Aunt Lilibet (sunan da mijin sarauniya yake kiranta da shi) da Dear Uncle Philip. ""Ba za mu taba mantawa da zaman da mua yi tare da shi ba da kuma abin alherin da ya bar wa Masarautar Birtaniya da ma kasar ba,"" in ji sakon da suka aika wa Sarauniya. Sarkin Sweden Carl Gustaf ya bayyana alhinin rasuwar Yarima Phillip, yana mai cewa shi ""babban aboki ne ga iyalina shekara da shekaru, kuma muna mutunta wannan abota"". Mai magana da yawun masarautar Sweden Margareta Thorgren ta shaida wa BBC cewa sarkinsu da yarima sun taba shiga jirgin ruwa zuwa wani waje a Ingila, tana mai karawa da cewa: ""Daga wannan lokacin abota mai kwari ta kullu a tsakaninsu."" Iyalan masarautar Netherlands sun ce ba za su manta da Yarima Philip saboda yadda suke girmama shi, suna masu karawa da cewa: ""Ya sadaukar da rayuwarsa mai tsawo wajen bauta ga al'ummar Birtaniya da kuma ayyukansa masu dama."" Sarkin Belgium Philippe ya ce shi da Sarauniya Mathilde za su ""ci gaba da tuna abubuwan alherin da ya yi musu yayin da suka hadu"". 'Madogarar Sarauniya' Kungiyar Kwamanwel - guda 54, wadanda akasarinsu kasashe rainon Ingila ne da ke da mutum biyan 2.4, ta aike sakon ta'aziyyarta. Firaministan Australia Scott Morrison ya bayyana a wata sanarwa cewa: ""Yarima yana cikin 'yan mazan jiya da ba za mu taba ganin kamarsu ba."" Ya yaba wa yariman bisa kasancewarsa uba ga kungiyoyi da dama a Australia. Ita ma Firaiministar New Zealand Jacinda Ardern ta yaba wa marigayin, tana mai cewa ""dubban matasa sun cimma manufofi da dama"" ta hanyar lambar yabo ta Hillary Award wadda yariman ya assasa. Firaministan India Narendra Modi shi ma ya mika ta'aziyyarsa game da ""ayyukan ci gaban al'umma da dama"" da yarima ya yi. Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta ya ce rayuwar yariman ""wata alama ce ta kaunar iyali da kuma hadin kan Birtaniya da ma kasashen duniya"" - mutumin da ya yi aiki tukuru wajen ""tabbatar da zaman lafiyar dan adam""." https://www.bbc.com/hausa/labarai-56695967 +entertainment ...Daga Bakin Mai Ita tare da Matar Bawa Maikada ta Kwana Casa'in Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon: Daga Bakin Mai Ita wani shiri ne na BBC Hausa da ke kawo muku hira da fitattun mutane kan wasu abubuwan da suka shafi rayuwarsu zalla. A wannan kashi na 49, shirin ya tattauna da Rahama MK Sulaiman, wacce aka fi sani da Hajiya Rabi Bawa Maikada ta shirin Kwana Casa'in, inda ta amsa tambayoyin da suka shafi rayuwarta. Ɗaukar bidiyo da Tacewa: Abdulsalam Usman Abdulkadir Tsarawa da gabatarwa: Halima Umar Saleh https://www.bbc.com/hausa/media-57173471 +entertainment Dangantakar Sarauniya Elizabeth II da kasashen Turai Sarauniyar Ingila, Elizabeth II, wadda ta mutu ranar Alhamis tana da shekara 96, tana da kyakkyawar dangataka da kasashen Turai. Sarauniya Elizabeth II ta hau kan mulki ne shekara bakwai bayan Yakin Duniya na II. A tsawon mulkinta na shekara 70, Sarauniyar ta yi tafiye-tafiye zuwa kasashen Turai. https://www.bbc.com/hausa/articles/c72zl0gemzeo +entertainment Nafisa Abdullahi: Ku daina haihuwar ‘ya’yan da ba za ku iya kula da su ba "Fitacciyar tauraruwar fina-finan Kannywood, Nafisa Abdullahi, ta yi kira ga masu haihuwar 'ya'ya ba tare da kula da su ba da su guji yin haka. Ta bayyana haka ne a wasu sakonni da ta wallafa a shafinta na Tuwita ranar Asabar. ""Ku daina haihuwar 'ya'yan da kuka san ba ku da halin kula da su,"" in ji Nafisa. Ta kara da cewa Allah zai tuhumi mutanen da suke haifar 'ya'ya ba tare da sauke nauyin da ya dora musu ba. A cewarta: ""Kun ga dukkan mutanen da ke haifar 'ya'yan da ba su ji ba ba su gani ba, domin kawai su aika da su almajiranci, kuma su ci gaba da haifar karin 'ya'ya, Allah sai ya saka wa yaran nan!!!"" Ta bayyana matukar bacin ranta kan yadda wasu iyaye suke tura 'ya'yansu 'yan shekara biyu zuwa uku almajirci. Tauraruwar ba ta ambaci sunayen wadanda take yi wa wannan gargadi ba, sai dai dama ba sabon abu ba ne yadda a kasar Hausa ake tura kananan yara almajirci. Wannan lamari ya dade yana bata wa mutane da dama rai, musamman ganin cewa wasu na zargi ana amfani da irin wadannan yara wajen aikata laifuka. Sai dai kalaman tauraruwar sun jawo martani daban-daban inda wasu suke yaba mata yayin da wasu suke sukar ta. Da yake tsokaci, M.M Dambatta, ya jinjina wa tauraruwar sannan ya ce ""har yanzu na kasa fahimtar yadda uba zai aika dansa dan shekara biyar domin ya kula da kansa da sunan almajirci. Ya kamata a tsayar da wannan lamari."" Shi ma IAOgundele ya ce haihuwa barkatai ba tare da lura da 'ya'ya ba ita ce sanadin matsalolin rashin tsaro da ke addabar Najeriya yana mai cewa ""albarkatun da ake da su sun gaza ciyar da yawan mutanen da ake haifa."" Sai dai Murtala Ubale ya tambayi tauraruwar cewa ""wacce gudunmawa za ki bayar dan a daƙile cigaban hakan?"" Shi kuwa Autan Gwaggo cewa ya yi ""kina kwance a kan gadonki, kina wani cewa Allah sai ya saka ma yaran nan.""" https://www.bbc.com/hausa/labarai-61133771 +entertainment Duke na Edinburgh: Kaunar da Yarima ke yi wa wasanni "Watakila irin kazar-kazar din da Yarima Philip yake da shi a lokacin yarinta ne ya ba shi damar kutsawa cikin harkokin wasanni. Saboda gwanintar da yake da ita da kuma yadda yake matukar son wasanni, hakan ya ba shi damar karawa a manyan matakai gami da taka rawa sosai a bangaren tsare-tsaren wasannin daban-daban. Bayan matarsa ta zama sarauniya, sai ya kasance matukar son da yake yi wa wasanni ne ya sa har yake mantawa da wasu abubuwa da dama suke damunsa musamman a bangaren mulki. Philip ya halarci makarantar Cheam, wadda ita ce makarantar kwana ta farko da ya yi a 1928. Shugaban makarantar mai suna Harold Taylor mutum ne mai son wasannin motsa jiki, kwararre ne sosai, ga shi kuma gwanin doki, yakan karfafi guiwar dalibansa wajen yin wasanni daban-daban. Philip ya yi fice sosai a tsakanin tsararrakinsa. Ya ci gasa da yawa a wasannin motsa jiki da ninkaya, haka nan kwararren mai tsaron raga ne a kulob dinsu na bal na makarantar. Har ila-yau, yakan yi wasa Kiriket a wannan makaranta tun yana dan shekara 11. A lokacin da ya kai shekara 13 ne aka mayar da shi makarntar Salem da ke kudancin Jamus, wadda sirikinsa Yaria Mad na Baden ya bude. Wani kwararren malami mai suna Kurt Hahn ne shugaban makarantar a wancan lokaci. Akan fara hidimar karatu a kullum a makarantar ta hanyar wanka da ruwan sanyi, sannan a tafi gudu na rabin mil. Akan kara da 'yan tsalle-tsalle da sauran wasanni. Malam Hahn ya yi amanna da cewa wannan motsa jikin na zahiri yana da matukar muhimmanci wajen sa yara su murmure daga sangartar samartaka. Haka nan Malam Hahn ya ci gaba da horar da yaran nan har bayan da aka mayar da makarantar zuwa lardin Gordonstoun da ke arewacin Scotland. Gallazawar da 'yan wariyar launin fata suka yi ne ya sa ya bar kasar. Malam Hahn ya yi amfani da damar da yake da ita, ta kasancewar makarantar tana kusa da (tafkin) Moray Firth, wanda hakan ya ba shi damar sa kowane yaro sai ya koyi ninkaya, haka kuma dole su dinga yin sauran wasannin da ake yi a filayen wasannin. Taron jama'ar da ke halartar wannan wasan daga wurare daban-daban, ya kara wa Philip nacin son shawagi a kan ruwa, kuma hakan ya taimake shi sosai, domin sam ba ya fama da wasu cututtukan da suka shafi ruwa. A lokacin da Philip ya auri gimbiya Elizabeth, a 1947, sai aka ba wa ango da amarya kyautar wani jirgin ruwa mai suna Bluebottle a matsayin kyautar murnar aure, amma fa ita sarauniya ba kasafai take bin mijin nata wajen yawo a jirgin ruwan ba. Babban abokin Yarima a wajen yin fito shi ne Uffa Fod, wanda ya zama abokinsa sosai har lokacin rasuwarsa a 1972. Sukan yi tsere sosai tare da Fod a jiragensu na ruwa. Akwai lokacin da Fod yake fada dangane da abokin fiton nasa: ""Ban taba sanin wani da ya lakanci haye igiyar ruwa a jirgi, cikin kwarewa ba, sama da shi."" Haka dai Philip ya dinga kece raini a wassanin ruwa da ake yi da suka kebanci fada, kuma zuwansa yana kara wa wasannin armashi. Kwarewarsa a wajen wasan Kiriket kuwa ya sa manyan mutane da dama sun dinga yaba masa a lokuta daban-daban. Kwararren dan wasan Kiriket din nan na kasar Australiya mai suna Sa Donald Bradman ya taba cewa, Philip kwararren badame ne a harkar wasan Kiriket, wanda ya kware sosai a tafiyar da wasan. ""Duk da cewa a yanzu ana cewa mu mutanen Austireliya ba mu da adalci, to don haka zan iya mika wadannan bayanan ga mutanen Birtaniya domin su duba su ga abin da muka bayyana na kwarewarsa."" Amma kuma a fannin kwallon doki, a nan ma fa, mai alfarma Yarima ya yi fice, ta yadda sai da ya zama daya daga cikin 'yan wasa hudu mafiya daukaka a Birtaniya a tsakiyar 1960, duk da cewa bai fara harkar wasan da wuri ba. Ba wai kawai wasan ya iya ba, har sai da ta kai ya kara daga kimar was an, har ya kara shahara sosai. Duk lokacin da ya zo filin wasan, take za ka ji ana ta yamadidi da labarain wasan a wurare daban-daban. Kamar yadda yake a dukkanin sauran wasanni, yakan zage sosai a wasan kwallon doki, kuma shi ma, wani lokacin akan samu akasi ya fado ko ya zame, kamar dai yadda abin yake a wasan kwallon doki. An tilasta shi ya daina yin wasan kwallon doki a lokacin da ya sami hadarin kumburi a hannunsa, lokacin kuwa ya kai shekara 50. Amma duk da haka, sai ga shi ya sake komawa wani wasan saboda karsashin da yake da shi, wato wasan keken doki. Tseren keken-doki fitaccen wasa ne a kasashe irin su Jamus da Hungary, amma wasan bai shahara ba a Birtaniya, don haka Philip ya yi yunkurin kafawa da tallata shi. Mai martaba ya kasance wani fitacce kuma jagora a wajen wasan tuka keken doki, ta yadda ya yi kokari sosai wajen kafa dokoki da daga likkafar wasan a kasar Birtaniya, sannan kuma ya dinga shiga gasa a rukunin wasan kasar. Daga cikin abubuwan mamakin da suka faru a rayuwarsa ta wasanni shi ne yadda ya yi abota da George Bowman, wanda suke a rukuni daya. Bowman ya taba cewa: ""ni fa ba kowa ba ne, kuma shi ne fa Yarima, don haka wani lokaci za ka ga mutane suna cecekuce a kan abotar. Amma bai taba nuna min wani bambanci dangane da hakan ba. Yakan dauke ni ba tare da wani bambanci ba. ""Wannan na daya daga cikin abubuwan da nake matukar so dangane da shi."" Duk da cewa an dan sami tataburza a lokacin da yake gudanar da wadannan wasannin, misali shi ne kamar wani lokacin da keken dokinsa ya bugi wani kankaren dutse, har sai da ya hantsila da su, amma wannan bai sa ya daina ba, har lokacin tsufansa. A duk fadin rayuwarsa, ya yi ta fadi tashi wajen ganin ya karfafa guiwar wasu domin su ma su dandani lagwadar motsa jiki, yadda shi ma yake jin dadin hakan. Yana matukar son kungiyar wasanni ta kasa, wadda ake kira da Fields in Trust, wadda ta dinga rajin karen hakkin samar da wadatattun filaye domin wasanni da harkokin motsa jiki. Kyautarsa ta girmawa da ya samar wadda aka fara a 1956 a sakamakon horon da ya samu daga Kurt Hahn, ta kara azamar samari wajen kara dagewa da shiga ayyukan da suka shafi motsa jiki. Saboda tsananin yadda yake son gasa, hakan ya bai wa Yarima Philip damar cimma babbar nasara a kusan dukkanin wani fannin wasannin da ya yi. Duk da haka, za a iya ganin irin namijin kokarin da ya yi a fannin wasanni ta fuskar yadda ya kimsa wa matasa son harkar, da kuma irin goyon bayan da ya bayar ga kungiyoyin wasanni da yawa. Dukkan hotunan suna da hakkin mallaka." https://www.bbc.com/hausa/labarai-47256085 +entertainment ...Daga Bakin Mai Ita tare da Karima ta Izzar So Daga Bakin Mai Ita shiri ne na BBC Hausa da ke kawo muku hira da fitattun taurari da mawakan harkar fim din Hausa na Kannywood kan abubuwan da suka shafi rayuwarsu zalla. A wannan kashi na 117, mun tattauna da tauraruwar fina-finan Hausa, Khadija Yobe, wadda aka fi sani Karima a Izzar So inda ta amsa tambayoyi da dama da suka shafi rayuwarta. https://www.bbc.com/hausa/articles/c9ep0n4n128o +entertainment Breonna Taylor: Jerin baƙaƙen fata da ‘yan sandan Amurka suka kashe "Kotu a Amurka ta samu wani ɗan sanda da laifi sakamakon harbe Breonna Taylor a farkon shekarar nan yayin wani samame da 'yan sandan suka kai a gidanta. 'Yan sandan sun je binciken ne sakamakon zargin safarar miyagun ƙwayoyi. Ranar Laraba an harbi 'yan sanda biyu a jerin zanga-zangar da ake yi a birnin Louisville saboda matakin da aka ɗauka na ƙin hukunta masu laifin. Ga wasu daga cikin jerin lamura da suka yi sanadiyar harbe 'yan Amurka baƙaƙen fata tun daga 2014. 17 ga Yulin 2014: Eric Garner Eric Garner ya mutu ne bayan ya yi kokawa da wani ɗan sandan birnin New York, ana zargin Mista Garner ne da sayar da taba sigari ba bisa ƙa'ida ba. Bayan an shaƙe wuyan Mista Garner, ya dinga furta cewa ""Ban iya numfashi"" har sau 11. Lamarin wanda wani da ke tsaye a gefen titi ya naɗa a wayarsa - ya jawo zanga-zanga a faɗin ƙasar. Ɗan sandan da ya yi sanadin mutuwarsa daga baya an kore shi daga aiki, amma ba a ɗauki wani mataki a kansa ba. Hakan kuma ya faru ne kusan shekara guda bayan da aka fara zanga-zangar Black Lives Matter sakamakon martani kan sakin da hukumomi a ƙasar suka yi wa wani mutum da ya kashe wani matashi Trayvon Martin a Florida. 9 ga Agustan 2014: Michael Brown Wani ɗan sanda ne ya kashe Michael Brown, ɗan shekara 18 a birnin Ferguson da ke Missouri, inda ɗan sandan ya ce ya ji labarin Mista Michael, wanda bai ɗauke da makami ya saci kwalin sigari. Takamaiman abin da ya faru har Michael ya mutu babu tabbaci a kai, sai dai an harbi Mista Michael ɗin har sau shida, kamar yadda binciken likitoci ya bayyana. Ɗan sandan da ya yi kisan daga baya ya ajiye aikinsa, amma kuma ba a yanke wani hukunci a kansa ba. Lamarin ya jawo zanga-zanga daban-daban da kuma tayar da zaune tsaye a Ferguson, kuma hakan ya ƙara zafin zanga-zangar Black Lives Matter. 22 ga Nuwambar 2014: Tamir Rice Tamir Rice, wani yaro ne mai shekara 12, wanda aka harba a Cleveland, kuma wani ɗan sandan jihar Ohio ne ya harbe shi sakamakon wani rahoto da ɗan sandan ya samu kan cewa wani yaro na bin mutanen da ke wucewa kan titi da bindiga, bindigar ma da a ake zargi ba ta gaske bace. 'Yan sandan sun bayyana cewa sun faɗa wa Rice ya ajiye makaminsa - amma a maimakon ya ajiye bindigar, sai ya nuna wa 'yan sandan bindigar kamar zai harbe su. Sai da 'yan sandan suka kashe Rice tukuna suka tabbatar da cewa bindigar da yake ɗauke da ita ta wasa ce. Babu wanda aka hukunta bayan faruwar wannan lamarin. Bayan shekara uku da faruwar abin ne aka kori ɗan sandan daga aiki sakamakon samunsa da laifin yin ƙarya a fom ɗin da ya sa hannu a kai kafin a ɗauke shi aiki. 4 ga Afrilun 2015: Walter Scott Walter Scott was shot in the back five times by a white police officer, who was later fired and eventually sentenced to 20 years in prison. Mr Scott had been pulled over for having a defective light on his car in North Charleston, South Carolina, and ran away from the police officer after a brief scuffle. The killing sparked protests in North Charleston, with chants of ""No justice, no peace"". Wani ɗan sanda ne ya harbi Walter Scott a baya har sau biyar, wanda daga baya an kori ɗan sandan kuma har aka yanke masa hukuncin zaman gidan yari na shekara 20. Lamarin ya faru ne a Arewacin Charleston da ke Kudancin Carolina inda ɗan sandan ya fito da Mista Scott daga motarsa sakamakon fitilar motarsa ba ta da kyau. Bayan gardama tsakaninsu, sai Mista Scott ya gudu. Kisan da aka yi masa ta jawo zanga-zanga matuƙa inda masu zanga-zangar ke cewa ""babu adalci ba zaman lafiya"". 5 ga Yulin 2016: Alton Sterling Mutuwar Alton Sterling ta sa an shafe kwanaki ana zanga-zanga a Baton Rouge da ke Louisiana. An kashe Mista Sterling ne bayan 'yan sanda sun samu rahoton cewa ana samun hayaniya a waje wani shago. An naɗi duka abin da ya faru a waya kuma aka baza a shafukan intanet. 'Yan sandan biyu da suka aikata kisan ba a kama su da wani laifi ba, sai dai an kori guda, ɗayan kuma an dakatar da shi daga aikin. 6 ga watan Yulin 2016: Philando Castile An kashe Philando Castile ne a lokacin da ya fita yawo a mota da budurwarsa a St Paul da ke jihar Minnesota. 'Yan sanda ne suka jawo shi daga cikin motar ya yin da suke wani bincike, inda ya ce musu yana da lasisin riƙe bindiga bayan sun kama shi da ita a wurinsa. Sun harbe shi a daidai lokacin da yake ƙoƙarin ɗauko lasisinsa, kamar yadda budurwarsa ta bayyana. Ta ɗauki lamarin kai tsaye a Facebook, haka kuma an wanke ɗan sandan da aka samu da laifi daga duk wasu zarge-zarge na kisan kai. 18 ga Maris ɗin 2018: Stephon Clark An kashe Stephon Clark bayan an harbe shi aƙalla sau bakwai a Sacramento da ke California, rahotanni sun ce wasu 'yan sanda ne da suke bincike kan fashi a wani gida ne suka aikata aika-aikar. Babban lauyin gundumar ya bayyana cewa 'yan sandan ba su aikata wani laifi ba, sakamakon 'yan sandan suna ƙoƙarin kare kansu don suna tunanin Mista Clark na ɗauke da bindiga. Wayar salula kaɗai aka gano a wurin da lamarin ya faru. Bidiyon da aka yaɗa a shafukan intanent na yadda lamarin ya faru ya jawo zanga-zanga matuƙa. 25 ga Mayun 2020: George Floyd George Floyd ya mutu ne bayan da aka kama shi a Minneapolis, inda 'yan sanda suka murƙushe shi, inda ɗaya daga cikin 'yan sandan ya yi amfani da gwiwar ƙafarsa ya ɗorata kan wuyan Mista Floyd. A lokacin, Mista Floyd ya ta ihun cewa bai iya numfashi. An ta gudanar da zanga-zanga a jihohin Amurka, hakazalika, an yi zanga-zanga a ƙasashe daban-daban na duniya. An samu ɗaya daga cikin 'yan sandan da laifin kisa ba dagangan ba, haka kuma sauran ukun za su fuskanci hukuncin taimakawa wurin aikata kisa," https://www.bbc.com/hausa/labarai-54277410 +entertainment Dauda Kahutu Rarara: Dalilin da ya sa nake yi wa Buhari waka "Latsa hoton sama domin kallon hirar da BBC ta yi da Rarara Fitaccen mawakin siyasa a Najeriya Dauda Adamu Kahutu Rarara ya ce gaskiyar Buhari ce ya sa yake yi wa shugaban na Najeriya waka. Rarara ya bayyana haka ne cikin wata tattaunawa da ya yi ta musamman da BBC, inda yake cewa tun yana yaro ake nusantar da shi kan gaskiya da amanar Buhari kuma har yanzu da ya taso ya gani. Dauda ya kara da cewa burin da Buhari yake da shi na gyara Najeriya da ayyukan da yake yi a yanzu ba za su kirgu ba. Ko da yake a yanzu ya ce yana dab da sakin wasu wakoki da za su bayyana irin ayyukan da Shugaba Buhari yake yi da wadanda ya kammala, wanda a cewarsa ""mutane za su gamsu da ceton Najeriya da Buhari ke yunkurin yi."" Rarara wanda ya karɓi kuɗin wasu ƴan Najeriya don rera wa Buhari waƙa, kuma har yanzu bai saki waƙar ba, ya ce idan da ƴan Najeriya za su karɓi ra'ayinsa da sun bari gwanin nasa ya zarce ya ƙara shekara biyar kan mulki - ""don ya kammala ayyukan da ya fara."" Mawaƙin siyasar ya ce ba daɗewa ba zai saki wasu waƙoƙi guda uku kan ayyukan Buhari. Sai dai bai bayyana lokacin da zai saki waƙoƙin ba, ciki har da wadda ya kira mai taken ""shidan Buhari ta fi sha shidan gangan"" Duk da shugaba Buhari na dab da kammala wa'adin mulkinsa amma Rarara ya ce bai san lokacin da zai daina yi wa shugaban waƙa ba. Rarara ya ce ya yi wa Buhari waƙa 68, kuma a cewarsa bai sa yawan adadin wakokin da ya yi ba a rayuwarsa. ""Amma yanzu mun fara hada kan wakokin da na yi baki daya,"" in ji shi. A cewar Rarara: ""Yawancin wakokin da nake yi wa Buhari suna zuwa ne daidai da lokaci, ba wai zama nake na rubuta waka akan shi ba. ""Misali ai na yi wakar Masu gudu su gudu na yi ta lokacin da Buhari ya ci mulki, a lokacin ana maganar idan PDP ta ci mulki sai dai mu gudu mu bar Najeriya. ""To Buhari ya ci mulki muma sai muka mayar da marta ni, a wakar, muka ce in kasan ka yi sata ka gudu. Rarara ya ce a haka aka yi wakar 'Ga Buhari ya dawo'lokacin Shugaban kasa ya yi rashin lafiya ya je Landan sai aka yi sa a ya ji sauki zai dawo, to a wannan lokacin cikin dare aka yi waƙar da aka ce washegari zai dawo, gaskiya ba na rubuta wakokin Buhari."" Dalilin karɓar kudin ƴan Najeriya don yi wa Buhari waƙa? Rarara fashewa ya yi da dariya lokacin da aka yi masa wannan tambaya, inda ya ce mun yi kokarin tabbatar wa da masu cewa farin jnin Buhari ya dushe. Talakawa sun amsa kira domin kuwa sun tara kudade masu yawa, in ji mawakin, amma bai fadi nawa aka tara ba. Ya ce wakar da ya karbi kudin ƴan Najeriya tana nan fitowa ba da dadewa ba cikin wakokin da ya yi kan ayyukan Buhari. Rarara ya ce ya taba kin karbar naira miliyan 500 don ya daina yi wa Buhari waka. ""An taba ba ni naira miliyan 500 domin na daina yi wa Buhari waka amma na ki karba, saboda duk abin da nake yi ina yi ne domin kasata"". Ya ce an sha ba shi kudi domin ya hakura da tafiyar Buhari amma a cewarsa bai taba sa shi jin ya yi gezau ba. ""Babban burina na ga ƙasata ta gyaru kamar yadda sauran kasashen duniya suke, kama daga ci gabanta da habbakarta, yaranmu idan sun zo su rika yin alfahari da ita, in ji mawakin." https://www.bbc.com/hausa/59023891 +entertainment An saki Sanusi Oscar "Wata kotun majistire a jihar Kano ta bayar da belin darakta Sanusi Oscar a masana'antar Kannywood bayan hukumar tace fina-finai ta gurfanar da shi a gabanta bisa zargin saba kai'dar aiki. Hukumar ta gurfanar da Oscar a gaban kotun ne saboda ya ""saba ka'idojin gudanar da sana'arsa a Kano, inda ya saki wata waka wadda akwai badala a ciki"", kamar yadda shugaban hukumar Isma'ila Na'abba Afakallahu ya shaida wa BBC. Alkali Aminu Fagge na kotun majistire mai lamba 34 da ke Rijiyar Zaki ne ya jagoranci zaman kotun, inda ya bayar da belin Oscar bisa sharudda. Sharuddan sun hada da cewa wajibi ne mutum biyu su tsaya masa kuma daya daga cikinsu ya zama dan uwansa na jini, tare da haramcin magana da kowacce irin kafar yada labarai. Kotun har wa yau, ta sanya ranar 10 ga watan Satumba domin zamanta na gaba. Tuni abokan aikinsa suka fara mayar da martani game da sakin nasa. Misbahu M. Ahmad ya wallafa bidiyo a shafinsa na Instagram yana maraba da hukuncin kotun. Akasarin 'yan fim din sun rabu gida biyu - masu goyon bayan jam'iyyar APC mai mulki da kuma bangaren hamayya na PDP (wato Kwankwasiyya a Kano), kuma siyasa kan fito fili a wasu ayyukansu. Tun bayan kamun nasa ne manyan taurari a masana'antar suka rika mayar da zafafan martani, inda Adam Zango ya ce ""ya fice daga kannywood"" sannan shi ma Mustapha Nabraska ya ce ya ""daina wasan Hausa har sai an sako abokin aikin nasu"". Tauraro fina-finan Hausa kuma mawaki, Adam A. Zango, yana daya daga cikin mutanen da suka fara bayyana bacin ransu dangane da batun. Abin da ya sa shi fita daga kungiyar masu shirya fina-finan Hausa ta Kannywood. Jarumi Mustapha Nabraska shi ma ya bayyana cewa ya daina wasan Hausa saboda kama abokin aikinsu. Sai dai Sani Danja ya bukaci a warware matsalar ta hanyar maslaha, ""ba tare da cin zarafin mutum ba,"" kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Instagram. Ya ce kama Oscar ""ba daidai ba ne,"" hakazalika ya bukaci duka 'yan Kannywood da su dauki kansu a matsayin 'yan uwan juna kuma su kasance tsintsiya madaurinki daya. Ita ma shahararriyar jarumar Kate Henshaw wacce take fitowa a fina-finan kudancin Najeriya wato Nollywood, ta yi Allah-wadai da kama daraktan, kamar yadda ta wallafa a shafinta na Instagram." https://www.bbc.com/hausa/labarai-49401752 +entertainment Kasaitacciyar Jana'iza - su wane ne a gaba-gaba a binne Sarauniya Elizabeth II? Dubun dubatar sojojin Burtaniya da na kasashen waje ne za su kasance a sahun gaba yayin jana'izar kasa da ake yi wa Sarauniya Elizabeth a taro mai cike da tarihi. Taron ya kunshi duk rundunonin soji, da 'yan gidan sarauta, da manyan hadiman Sarauniya ne za su yi wa basarakiyar mai dogon zamani bankwanan karshe inda za a binne ta a Windsor. Ga wasu daga cikin abubuwan da suka kamata ku sani kan ainihin yadda jana'izar za ta kasance. Sojojin Burtaniya da kasashen Commonwealth za su yi maci a birnin London da Windsor. Za kuma su yi jerin gwano, tare da bai wa dakarun ban girma damar gudanar da tasu hidimar. Sarauniya dai ta kasance babbar kwamandar askarawan Burtaniya kuma tana da alaka ta kukut da sojoji, don haka za su yi wa gawarta rakiya tun daga birnin London har zuwa Windor, inda a nan ne wurin karshe da za a yi binne ta. Rukunin farko kuma gajerun zaratan sojoji za su dauki gawar tun daga Westminster Abbey zuwa zauren addu'o'i, daga Westminster Abbey kuma sai Wellington Arch, kafin a dangana da ita Windsor. Da zarar gawar ta isa Windsor, sai sashe na uku na sojojin fsdsr St George's Chapel su dora daga inda suka tsaya. Abin da za a mai da hankali a kai shi ne kashi na biyu, wato tafiya da gawar tun daga birnin London bayan gama addu'o'i, inda 'yan sanda na musamman wato Canadian Mounted Police, za su raba kansu zuwa rukuni shida, da rakiyar makadan badujala. Mambobin rundunar sojin Burtaniya da na kasashen Commonwealth, da 'yan sanda har da jami'an NHS za su shiga wannan biki. Ana sa ran dakarun za su bar Westminster Abbey da tsakar rana cikin mintuna 45. Za a sa akwatin gawar Sarauniya, da aka yi wa adon ban mamaki, a tsakiya kuma za a dora kambun masarautar a kan gawar, zagaye da runduna ta musamman ta sojin ruwa da za su harba bindiga domin girmama ta. Tun cikin 1979 aka kera igwar da ta dauko gawar kawun Yarima Philip, wato Lord Mountbatten, sannan da ita aka dau gawar mahaifin Sarauniya wato Sarki George VI, a 1952. Sojojin Grenadier Guards ne za su take mata baya, da dakarun tsaron Sarki da wani bangare na sojojin Gentlemen at Arms, da na Yeomen na kamfanin sojin masarauta na Archers. Manyan masu sarauta, ciki har da Sarki Charles na III da 'ya'yansa Yarima William da Yarima Harry ne, za su take wa gawar Sarauniya baya. Sauran 'ya'yan gidan sarauta su kuma za su kasance a baya.\n\nSarauniya Consort Camilla, Yariman Wales, da Countess ta Wessex da Duchess ta Sussex na cikin wadanda za su yi wa gawar Sarauniya rakiya a cikin mota. 'Yan sandan dawakai na Burtaniya da dakarun kasashe kamar sojin saman New Zealand • 'Yan sandan masarauta na Canada • Makadan badujala da maharban bindiga na Gurkhas • Wakilan George Cross daga Malta, 'Yan sandan Constabulary da hukumar lafiyar Burtaniya • Da duk wata rundunar masu damara daga sassa daban-daban na duniya na cikin wadanda za su yi wannan kasaitaccen biki mai cike da tarihi da za a dade ba a ga irinsa nan kusa a fadin duniya ba. Wakilan sojin sama na masarauta: 603 (daga birnin Edinburgh) da tawagar makadan badujalarsu, da sojin sama na Marham, da na kwalejin sojoji da ke Cranwel da sauraunsu Wakilan sojoji: Kamfanin Artillery • Masu mukamin janar-janar • Makadan badujalar Burtaniya na Sandhurst da Colchester • Injiniyoyin Gurkha na Sarauniya • Dakarun fadar Welsh • Rundunar Duke din Lancaster • Da ta Scotland • Rundunar Wales • Rundunar Ireland • Makadan badujalar Ireland, da sauransu Wakilan sojin ruwan Burtaniya: Tun daga kan manya da kanana da makadan badujalarsu Masu ba da shawara kan harkokin tsaro: Daga kasashen Jamaica • New Zealand • Australia • Canada Wakilan kasashen Commonwealth da Sarauniya ke jagoranta Wakilan rundunonin tsaron da Sarauniya ke jagoranta. Wakilan jiragen ruwan Sarauniya\n\nMasarauta; Mataimakin sarkin gida • Mai jan ragamar ma'aikatan masarauta • Wazirin baitul malin masarauta • Masu takewa Saraunuiya baya • Mai kula da fannin ruwa • Masu kula da walwalar Sarauniya Masu dafawa keken dokin baya: Wakilan Cavalry Iyalan Masarauta: Earl na Wessex da Forfar • Duke na York • Gimbiya Anne • Sarki • Peter Phillips • Duke na Sussex • Yariman Wales • Mataimakin Admiral Sir Tim Laurence • Duke na Gloucester • Earl din Snowdon Mota ta 1: Matar Sarki • Gimbiyar Wales\nMota ta 2: Duchess ta Sussex • Matar Countess na Wessex da Forfar\nRundunar soji • Masu bai wa masarauta tsaro, ayarin gidan sarki: Sarkin gida • Mai tsaro • Babban sakataren masarauta • Ma'aji Runduna kasa ta biyu\nWakilan farar hula: Sojin ruwa • Sojin ruwa na masarauta • Hukumar masu tsaron teku • Rundunar 'yan sanda • Rundunar 'yan kwana-kwana • Hukumar gidajen yari • Hukumar motocin daukar marasa lafiya • Kungiyar agaji ta Red Cross • Motocin daukar marasa lafiya na St John • Ma'aikatan sa-kai na Masarauta • Matasan sojojin da aka bai wa horo da ke baya: 'Yan sanda masu hawa doki.\nAn samo bayanan nan daga: Fadar Buckingham Palace, da rundunar sojoji Da zarar tafiyar ta kai Wellington Arch da ke Hyde Park Corner, da misalin karfe 1 na rana agogon Burtaniya, za a maida akwatin gawar cikin wata sabuwar mota, daga nan a yi tafiyar karshe da ita zuwa hubbaren sarakuna da ke cikin Fadar Windsor, inda za a binne Sarauniyar. Da misalin karfe 3 na rana, ake sa ran motar gawar za ta isa inda ta nufa, sai kuma doguwar tafiyar da za a yi da kafa har zuwa Fadar Windsor. Tafiya ce ta nisan mil uku, da wakilan rundunonin soji za su yi jerin gwano tare da dafewa gawar Sarauniya baya. Ana sa ran Sarki da manyan 'ya'yan sarauta za su isa Fadar Windsor, don addu'o'in karshe, daga nan kuma sai a binne Sarauniya Elizabeth ta II a bangaren hubbaren St George wanda Sarauniyar ce da kanta ta jagoranci bikin bude shi a shekarar 1962. https://www.bbc.com/hausa/articles/c4nel06kjdgo +entertainment Ludacris ya zama dan kasar Gabon "Mawakin 'rap' bakar fata kuma mai fitowa a fina-finai Ludacris shi ne fittacen Ba'amurke da ya zama dan wata kasa a nahiyar Afirka a baya-bayan nan. Ludacris, wanda sunansa na asali Christopher Brian Bridges, ya yi bukukuwan Kirsimeti da na shiga sabuwar shekara a kasar Gabon, inda ya karbi shaidar zama dan kasar. Matar Ludacris wato Eudoxie Mbouguiengue 'yar Gabon ce. An ga mawakin dauke da takardarsa ta fasfon kasar Gabon a wani bidiyo da aka wallafa a Twitter. A cikin bidiyon mawakin ya ce mahaifiyarsa tare da 'ya'yansa mata biyu sun karbi takardunsu na shaidar zama 'yan karamar kasar mai arzikin mai da ke yankin tsakiyar Afirka. A shekarun baya-bayan nan dai an samu karuwar taurari Amurkawa 'yan asalin Afirka da suka karbi takardun shaidar zama 'yan kasahen Afirka. Wasunsu kuma sun ziyarci wasu kasashe a nahiyar domin gano asalinsu. A watan Agustan shekarar 2019 ne dan wasa kuma Frodusan Samuel L Jackson ya karbi takardar fasfonsa na kasar Gabon bayan shugaba Ali Bongo ya karbi bakuncinsa. Mahaifin shugaban wato Omar Bongo ya mulki Gabon na tsawon fiye da shekara 40. Bayan Gabon, wasu kasashen Afirka ma sun karbi wasu Amurkawa 'yan asalin Afirka a matsayin 'yan kasashensu. A watan Mayun shekarar 2019, mai barkwanci kuma 'yar wasa Tiffany Haddish ta je kasar Eritrea, inda ta samu shaidar zama 'yar kasar. Sai dai wasu sun soki matakin nata a matsayin amincewa da mulkin kama karya a Eritrea. Haka kuma a watan Nuwamban bara, Ghana ta yi bikin bai wa Amurkawa da 'yan kasashen Caribbean 'yan asalin Afirka 126 shaidar zama 'yan kasar. Hakan ya faru ne a yayin bikin da kasar ta yi na cika shekara 400 da dawowar 'yan Afirka na farko daga Amurka ta Arewa, wadan aka bautar. Wani kamfanin binciken tsaro da ya mallaki adadi mafi girma na bayanan tsaron 'yan asalin Afirka mai suna African Ancestry a Amurka ya gano cewa galibin Amurkawa 'yan asalin Afirka na hankoron gano tushensu da silsilar danginsu. Cinikin bayin da Amurka ta yi a Afirka wanda aka yi jigilar 'yan Afirka miliyan 12.5 zuwa Amurka a matsayin bayi, ya sa mutanen rasa asalinsu. Hakan ya taimaka wajen shafe tarihinsu a tsawon shekara 400. ""Kakanninmu ba su taba debe tsammani ba. Ba za ku iya dankwafe tunaninmu ko ruhinmu ba. Sun ba ni kwarin gwiwar in koma"", kamar yadda Ludacrs ya rubuta a shafinsa na Instagram. A wani hoto da Ludacris ya dauka a gaban wani wurin jibge bayi da Turawa suka gina a Cape Coast da ke Ghana, Ludacris ya bai wa kyamara baya, sanye da wata riga da a bayanta aka rubuta: ""Ni ba dan Afirka ba ne saboda an haife ni a Afirka. Ni dan Afirka ne saboda Afirka na cikin jinina. Na dawo."" Wannan wani take ke na shirin kasar Ghana na ""Year of Return."" Samuel L. Jackson ya zabi karbar shaidar zama dan kasar Gabon bayan gwajin kwayoyin halittarsa a wani shirin bincike na musamman da Amurka ke yi na bayyana tarihin iyalan fitattun taurari, mai suna 'Gano Asalinka' (Finding Your Roots). Shirin ya gano cewa Samuel L Jackson dan asalin kabilar Benga ne da ke Gabon. Tsohon dan wasan na Amurka ya wallafa hotuna da dama na kasar Gabon, ciki har da wanda ya dauka tare da Sarkin al'ummar Benga. ""Yayin da kake kan hanyarka ta gano asalinka kuma hakan ta bayyana karara!"" ya rubuta. Gwamnatin Ghana ta kaddamar da shirin ""The Year of Return"" ne domin karfafa wa Amurkawa 'yan asalin Afirka da sauran bakaken fata mazauna kasashen waje gwiwar komawa ""gida"". ""Isowar 'yan Afirka da aka bautar a Arewacin Amurka ya dawo mana da jimami da bakin cikin danginmu da aka dauke daga Afirka da karfin tuwo, aka jefa su cikin muzgunawa da azabtarwa na tsawon shekaru,"" inji shafin shirin na intanet. Shirin na alfahari da ""karuwar jajircewar"" 'yan Afirka wadanda cinikin bayi ya shafa ya kuma ""warwatsa su sannan ya raba su da gidajensu"" a nahiyoyin duniya. 'Dawo da martabarmu' Da dama daga cikin taurarin bakar fata sun yi bikin shiga sabuwar shekarar nan ne a Ghana. Shahararriyar 'yar wasa Naomi Campbell da 'yar wasa Lupita Nyong'o da mawaki Akon da kuma mahaifiyar fitacciyar mawakiya Beyonce Tina Knowles Lawson, na daga cikin manyan taurari da suka halarci bikin murnar dawowar 'yan Afirka gida 'Afrofest'. A lokacin gagarumin bikin da aka yi a watan Nuwamba ne malamin addinin Yahudu Kohain Halev, wanda Ba'amurke ne dan asalin Afirka ya dunkule matsayin samun takardar shaidar zama dan kasar Afirka ke nufi a cikin bayaninsa. ""Abu mafi daraja da aka kwace mana shi ne asalinmu da dangantakarmu; yin hakan kamar yanke mahaifa ne"". Sai dai ya ce samun takardar shaidar zama dan kasar Ghana ya warkar da wannan ciwo: ""Asalinmu da martabarmu da kuma tinkahonmu da muka rasa duk sun dawo"". Yawancin Amurkawa 'yan asalin Afirka ba sa daukar kansu cikakkun 'yan Amurka, a cewar Dwayne Wong, wani kwararren marubucin tarihin Afirka da na 'yan Afirka mazauna wasu kasashe. Mista Wong ya yi imani cewa daruruwan shekarun da aka kwashe ana nuna wa 'yan asalin Afirka bambamci da fifiko da kuma gwagwarmayar neman amincewa da samun karbuwa da ya ki ci ya ki cinyewa. Kungiyoyi irin su ""Black Lives Matter"" masu rajin kare bakaken fata ya sa Amurkawa 'yan asalin Afirka fahimtar cewa su ba cikakkun 'yan Amurka ba ne. Ga wasunsu kuma, samun takardar shaidar zama dan kasar Afirka ko kuma gano asalinsu da wasu kabilun Afirka, na iya zame masu muhimmin abu na gano asalinsu." https://www.bbc.com/hausa/labarai-51028076 +entertainment ...Daga Bakin Mai Ita tare da Umma Shehu Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon: Daga bakin mai ita wani shiri na BBC Hausa da ke kawo muku hira da fitattun mutane kan wasu abubuwan da suka shafi rayuwarsu zallah. A wannan kashi na 27, shirin ya tattauna da Umma Shehu, wata tauraruwar fina-finan Hausa. A cikin hirar, ta bayyana abubuwa da yawa da suka shafi rayuwarta da za su saku dariya da al'ajabi, ciki har da baƙin cikin da ta shiga yayin da hirarta Momo bayan ta yaɗu. Ta yi bayanin irin kyakkyawar alaƙar da tke tsakaninta da mahaifiyarta da sauran 'yan uwanta. Ɗaukar bidiyo: Yusuf Yakasai Tacewa: Fatima Othman https://www.bbc.com/hausa/media-55251077 +entertainment Hadiza Gabon ta roki gafarar Allah kan 'kakkausan' martanin da ta yi a Twitter "Fitaccen malamin addinin Musulincin nan a Najeriya, kuma ministan sadarwar kasar, Sheikh Ali Isa Pantami ya ce ya yaba da yadda fitacciyar jarumar fina-finan Kannywood, Hadiza Gabon ta roki Allah gafara kan wata ""katobara"" da ta ce ta yi da na sanin yin ta a shafin Twitter ranar Lahadi. Gabon dai ta mayar wa wani mutum martani ne a shafin Twitter wanda ya zage ta a wani hotonta da na kawayenta da kuma abokan aikinta Rahama Sadau da Fati Washa da Rahamar ta wallafa a Twitter. Wannan abu da Hadiza ta yi dai ga dukkan alamu ya burge ma'abota shafukan sada zumunta da muhawara a Najeriya, inda daga wallafa sakon da misalin karfe 5.58 na yammacin Lahadi zuwa 9.30 na safiyar litinin an sake yada shi sau 638 an kuma so shi sau 3,600 sannan wadanda suka bayar da amsa ga sakon suna da dumbin yawa. Za a iya cewa kashi 95 cikin 100 na wadanda suka ba da amsa sun yabe ta ne kan tuban da ta yi, amma duk da haka akwai 'yan tsiraru da ke ganin cewa ""aikin gama ya gama, ta makaro, abin da suke ganin ya nuna zahirin wace ce ita."" Sakon nata ya ce: ""Astaghfirul Laah kan martanin da na mayar marar kyau kan wata amsar rashin da'a da wani ya ba ni. Na goge sakon kuma na nemi gafarar Allah kan kokarin mayar da martani cikin fushi kan wani kuskuren da aka yi."" Ministan Sadarwa na Najeriya kuma fitaccen malamin addini Sheikh Isa Ali Pnatmi ma ya bayar da amsa a kasan sakon Hadizan. Sakon ministan dai na cewa ne ""Wannan babban abin a yaba ne a nemi gafarar Allah bayan yin wani kuskure. Allah Madaukakin Sarki ya yafe mana ya kuma yi mana jagora tare da kare mu a gaba."" Sai dai shi ma ministan ya sha martani daga wasu mabiya Twitter din inda wasu ke cewa me ya kawo shi cikin wannan maganar, yayin da wasu kuma ke yaba masa. Hoton dai ya jawo ce-ce-ku ce a shafukan sada zumunta musamman na Twitter da Instagram inda dukkan jaruman suka sanya a shafukansu. Wani matashi ne ya fara cin zarafin jaruman inda ya zarge su da yin zina kafin su dauki hoton. Ba da jimawa ba ne ita kuma Hadizan ta mayar masa da martani da cewa da mahifinsa ma suka yi zinar. Tuni dai Hadiza ta goge wannan sako ta kuma wallafa wani na neman gararar Allah SWT da yin da na sanin mayar da wancan martanin tun da fari. A ranar Asabar ne Rahama Sadau ta wallafa hoton mai dauke da ita da Hadiza Gabon da Fati Washa a shafin Twitter inda ta yi masa take da ""ma ki gani ya kauda idonsa"". Sannan ta sake wallafa irinsa a shafin Instagram inda kuma nan da nan hotunan kala uku suka yadu kamar wutar daji. Sun dauki hoton ne a birnin Landan yayin da suka je karbar wata karramawa da aka yi musu. Sun sha caccaka sakamakon sanya hoton inda aka dinga yi musu zargi iri-iri na zina da madigo, abin da ya tunzura Gabon mayar da ""kakkasaun martanin"" ga wani Bala Boyi. Nan da nan ita ma Rahama ta sake sanya martani a kan na Gabon din. Mutane da dama na ganin bai dace jaruman su yi haka ba, kamata ya yi su kau da ido kan irin wadannan zarge-zarge. Daga baya ne a ranar Lahadi da yamma ita Hadizan ta goge martani tare da bayar da hakuri, sai dai duk da cewa ita ma Rahama ta goge nata martanin amma dai ba ta bayar da hakurin ba sannan ba ta cire hoton ba." https://www.bbc.com/hausa/labarai-50286569 +entertainment Yadda mawakan K-pop da magoya bayansu ke yaki da gurbata muhalli Danna hoton da ke sama don kallon bidiyon: Duk da yake an kwashe shekaru ana jin waka a intanet amma har yanzu masu sha'awar wakokin K-pop suna sayen faifan CD masu tarin yawa na mawakan. Hakan ya haddasa tarin sharar robobi. Don haka, me ya sa maso son wakokin K-pop suke sayen faifan CD kuma me K-pop da masu sha'awar wakokinsu suke yi wajen kawo karshen matsalar? https://www.bbc.com/hausa/articles/cn4qq89rjvlo +entertainment Hanyoyi biyar da coronavirus ta shafi Bollywood Yayin da cutar coronavirus ke ci gaba da yaduwa a duniya, masana'antar Bollywood ta tanadi matakan kariya daga kamuwa da ma yaduwar cutar. Daga cikin matakan, Bollywood ta dakatar da daukar duk wani fim da ake yi a yanzu har zuwa 31 ga watan Maris 2020. Matakin ya biyo bayan tattaunawar da masu ruwa da tsaki a masana'antar suka yi. An umarci dukkan masu shirya fim da su dawo daga inda suka je daukar fim ko a cikin kasar ko kuma a wajen kasar. Masana'antar ta ce ta dauki wannan matakin ne domin kauce wa kamuwa da yaduwar cutar. Kasancewar coronavirus na saurin yaduwa, hakan babbar barazana ce ga rayuwar al'umma a ko ina. Wannan dalilin ne ya sa yawancin masu gidajen kallo a India wato sinima suka rufe gidajen kallonsu saboda tsoron yaduwarta a wajen jama'a. Rufe gidajen kallon kuwa ya janyo ala tilas aka dage sakin wasu fina-finai da ya kamata a ce an sake su a wannan watan. Fina-finai kamar Baaghi 3 da Angrezi Medium da Sooryavanshi da Sandeep Aur Pinky Faraar, an dage fitar da su zuwa wani lokaci saboda abin d ake faruwa a duniya na annobar coronavirus. Bisa al'ada dai idan mai shirya fim zai fitar da fim dinsa sai an fara haska shi a sinima kafin daga bisani a fitar da shi ko ina. To a dalilin rufe gidajen kallon ko sinimun dole masu shirya fim suka dage fitar da fina-finansu har sai abin da hali ya yi saboda gudun yaudwar cutar coronavirus tun da mutane da dama ne za su hadu a gidan kallon domin kallon fim din. Bisa la'akari da yadda cutar coronavirus ke yaduwa a kasashen duniya, masu fada a ji a masana'antar Bollywood suka tattauna inda suka tsaida matsaya a kan dage daukar duk wani fim a ciki ko a wajen kasar. Akwai fina-finai da dama da aka shirya daukarsu a wajen kasar Indiya, amma sakamakon yaduwar cutar, yanzu an soke Haka fina-finan da ake dauka ma a cikin kasar an soke har zuwa 31 ga watan Maris 2020. Wannan mataki ya zama dole saboda kaucewa kamuwa da yaduwar cutar coronavirus a tsakanin 'yan fim. Saboda yaduwar da cutar coronavirus ke yi a duniya, ya sa da yawa daga cikin jaruman Bollywood sun kasance a gida ba sa fita. Hakan kuwa ya shafi irin gwanayen nan ma su daukar hoton jarumai a kasar, wanda ke bibiyar yadda jaruman ke tafiyar da rayuwarsu ta yau da kullum. Irin wadannan masu daukar hoton idan sun dauka su kan wallafa shi a shafukansu na sada zumunta domin masu bibiyarsu. Ta haka ne kuma suke suna, sannan kuma suke samun masu bibiyarsu da dama. To yanzu jaruman ba sa fita suna zaune a gida, don haka irin wadannan masu daukar hoton ba su da abin dauka balle su wallafa a shafukansu na sada zumunta. An dakatar da gudanar da duk wasu manyan taruka da aka shirya yi kamar na tallata fim da bikin bayar da kyautuka da dai makamantansu. Yaduwar da coronavirus ke yi ya sa ala tilas an dakatar duk wasu manyan taruka saboda gudun kamuwa d aita. Tuni da dama daga cikin jaruman Bollywood suka soke fita wajen kasar domin yawon bude idanu ko shakatawa. Jarumi Hrithik Roshan ya shirya zuwa Amurka a wata mai zuwa domin ya je ya gaisa da masu sha'awar kallon fina-finansa, amma yanzu ya soke wannan tafiya. Haka shi ma Salman Khan akwai tafiyar da ya yi niyyar yi zuwa Amurka da Canada amma ya fasa. Shima Varun Dhawan, ya dage wata tafiya da ya yi niyyar yi zuwa wata mai zuwa. https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-51966097 +entertainment An shiga rana ta biyu ta mutuwar Yarima Philip Duke na Edinburgh Gaba a yau Asabar ne ake sa ran Fadar Masarautar Ingila za ta fitar da bayanai game da jana'izar Duke na Edinburgh kuma za a yi harbin bindiga na girmamawa sau 41 a sassan Burtaniya. Shirye-shiryen da aka yi tun da farko ya shafi baki 800 amma da alamu hakan zai sauya saboda ka'idojin da aka gindaya saboda cutar korona. Ana sa ran gudanar da jana'izar a Fadar Windsor sai dai za a takaita adadin mutanen da za su halarta. Cikin dare an rika ajiye furanni a wajen Fadar Buckingham da Windsor. An bukaci mutane su guji taruwa saboda annobar korona. An dai shiga rana ta biyu da Burtaniya da Masarautar Ingila ke jimamin mutuwar Duke na Edinburgh. Yarima Philip wanda ya kasance tare da Sarauniyar Ingila fiye da shekara 70 ya mutu ne a Fadar Windsor jiya Juma'a. Za a yi kasa-kasa da tutoci har zuwa lokacin jana'izar. Babban dan Sarauniyar Ingila, Yarima Charles cikin wani shiri na musamman da aka nada kafin mutuwar Yarima Philip, ya ce irin gudummawar da mahaifinsa ke bai wa Sarauniyar Ingila abin jinjinawa ne. Yarima Charles ke cewa ya kasance mai jajircewa wajen tallafawa mahaifiyata da yadda ya yi hakan na tsawon lokaci, kuma, ta wata hanya mai ban mamaki, yadda ya ci gaba da yin hakan tsawon lokaci ba tare da gajiyawa ba. Yarsu daya tilo Gimbiya Anne ita ma tana da irin wannan ra'ayin. Wata sanarwa da aka wallafa a shafin intanet na jikan marigayin wato Duke na Sussex Yarima Harry da matarsa Meghan da a yanzu haka suke zaune a Amurka ta bayyana yadda za a yi kewar Yarima Philip inda kuma ya yaba masa bisa irin jajircewarsa a lokacin da yake raye. Ana kuma ci gaba da mika sakonnin ta'aziyya bisa mutuwar Duke na Edinburgh daga sassan duniya. Firaministan Australiya, Scott Morrison ya ce Yarima Phillip mutum ne da ya sadaukar da rayuwarsa ga aiki inda ya ce Kungiyar kasashen Commonwealth suna tare da Masarautar Ingila a wannan lokaci. Tun da farko tsofaffin shugabannin Amurka sun mika sakon ta'aziyyar mutuwar Yarima Philip kuma mijin sarauniyar Ingila. Joe Biden ya yaba da yadda marigayin ya sadaukar da kansa wajen hidimtawa Sarauniyar Ingila . A Turai, shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana rayuwar marigayin a matsayin abin koyi https://www.bbc.com/hausa/56698942 +entertainment Coronavirus ta sa kasuwar Netflix ta bude a duniya "Kamfanin Netflix mai samar da manhajar kallon fina-finai ya ga karuwar masu amfani da shi a wannan shekarar, yayin da kasashe da yawa a fadin duniya suka sanya dokar nan ta kulle mutane a gida, kuma mutanen ke neman hanyoyin nishadantar da kansu. Kusan mutane miliyan 16 ne suka yi rijista da manhajar a watanni ukun farko na shekarar, in ji kamfanin. Wannan ya kusa ninka yawan mutanen da suka yi rijista da manhajar a watannin karshen shekarar 2019. Sai dai kamfanin, wanda kan shirya fina-finai na miliyoyin dala, ya ce dokar kulle a fadin duniya ta dakatar da daukar ""kusan duka"" fina-finai a fadin duniya. Kuma faduwar farashin kudaden kasashe da yawa na nufin sabbin masu rijista a manhajar da yawa da ke wajen Amurka, inda Netflix yake, ba za su kara wa kamfanin wani abin a zo a gani ba, ba kamar yadda za su kara ba kafin a shiga halin annobar. Kuma wannan ya yi mummunan tasiri kan kudin da aka samar a duniya gaba daya. Sai dai duk da haka, darajar kamfanin ya karu da kusan kashi 30 cikin 100 a wannan shekarar, yayin da masu zuba jari ke ganin cewa kamfanin zai iya yi wa mutane amfani a lokacin da suke kulle a gida. ""Netflix shi ne, kuma zai ci gaba da kasancewa kamfanin sadarwar da Covid-19 ba ta yi wa tasiri sosai ba,"" in ji wani mai sharhi kan kasuwanci a kan intanet Eric Haggstrom. ""Masan'antarsu ta yi dai-dai da al'ummar da suka tsinci kansu da zaman gidan dole."" Bukatar kallon fina-finai a intanet ta yi karuwar da a watan jiya Netflix ya ce zai rage ingancin hotunan bidoyinsa a Tarayyar Turai don rage wa kamfanonin samar da layukan intanet nauyi. Haka kuma, sai da kamfanin ya dauki karin ma'aikata 2,000 don tallafa wa sauran ma'aikatan kamfanin. Netflix ya ce mutum miliyan 85 ne suka kalli fim dinsa mai suna Spenser Confidential, tsawon a kalla minti biyu - ma'aunin da yake amfani da shi don ganin alkalumansa. Haka kuma, an kalli fim dinsa na dogon zango mai suna Tiger King a gidaje miliyan 64. Kamfanin na sa rai zai kara mambobi miliyan 7.5 nan da wata uku zuwa karshen watan Yuni - fiye da yadda masu sharhi ke sa rai. Amma ya yi gargadin masu zuba jari cewa masu bibiyar manhajar da darajar kamfanin za su ragu idan gwamnatoci suka dage dokar kulle a fadin duniya. Natflix ya ce yana sa rai ya ci gaba da bin jadawalinsa har zuwa karshen watan Yuni kuma yana ci gaba da mallakar wasu fina-finan da ba shi ya shirya ba don samar wa masu bibiyarsa sabbin fina-finan da za su kalla. Amma ya ce nan gaba za a fuskanci koma-baya a yawan mutanen da ke kallon sabbin fina-finai. Paolo Pescatore, mai sharhi a kamfanin PP Foresight, ya ce tsayawa cik da aka yi da shirya finai-finai zai shafi karuwar mutanen da ke kallon fina-finai a intanet a watanni masu zuwa. ""Amma Netflix ba zai fuskanci matsaloli sosai ba saboda yawan fina-finan da ke kansa,"" a cewarsa. Daga Zoe Thomas, Wakilin BBC News kan Fasaha Yadda masu rijista da kamfanin Netflix daga farko-farko suka rika karuwa, ya ja hankalin masu zuba jari a Amurka. Amma karuwar masu amfani da manhajar a lokacin da mafi yawan masu amfani da intanet na duniya ke kulle a gida ba wani abin a yaba ba ne. Babban abin tambaya shi ne, Netflix zai iya rike wadannan sabbin kwastomomin bayan an dage dokar hana fita ta Covid-19? Kamfanin na fuskantar karuwar kamfanoni masu gogayya kamar Disney Plus da Amazon Prime, wadanda ke tinkaho da yawan fina-finai don jawo sabbin kwastomomi. A halin da ake ciki, sabon tsarin kallon fina-finai na Quibi ya kasha biliyoyi don sakin fina-finai da manyan 'yan wasa suka fito a ciki. Kuma a karshen shekarar nan, HBO Max da NBCUniversal za su kaddamar da tsarin Peacock a Amurka. A duniyar kallo ta shafin intanet, fina-finai su ne mafi muhimmanci kuma karuwar masu gogoya na nufin Netflix zai kara matsa kaimi wajen fitar da fina-finai masu inganci. A nan ne kuma batun cutar korona ya shigo. Dole Netflix ya dakatar da dauka da shirya sabbin fina-finansa a wannan lokaci. Abokanan gogoyyarsa ma na fuskantar wannan kalubalen. Amma manyan kamfanoni kamar NBCUniversal da Disney, suna janye shirye-shiryensu da ake kallo sosai, wadanda suka bai wa Netflix aro kuma suna dorawa a mahnajojinsu. Turai da Gabas Ta Tsakiya da Afrika ne yankunan da mafi yawan sabbin mambobin Netflix miliyan 7 suka fito. A Amurka da Canada, ba a ga karuwar masu amfani da manhajar ba a shekarun baya amma a baya-bayan nan, mutane miliyan 2.3 ne suka yi rijista da ita, idan aka hada da mutane 550,000 da suka yi rijista a watannin karshe na 2019. Yanzu kamfanin na da masu amfani da shi sama da miliyan 182 a fadin duniya. Netflix ya ce kudin shigarsa ya karu da dala biliyan 5.76, wato ya karu da kashi 27 cikin dari, idan aka hada abin da ya samu a shekarar 2019. Ribarsa ta rubanya daga dala miliyan 344 a watannin farko na 2019 zuwa dala miliyan 709." https://www.bbc.com/hausa/labarai-52403038 +entertainment Aminu Ado Bayero: Tarihin Sarkin Kano na 15 a jerin Sarakunan Fulani A ranar Litinin ne gwamnatin jihar Kano ta nada Aminu Ado Bayero a matsayin Sarkin Kano bayan sauke Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II. Gwamnatin Kano ta ce ta sauke Sanusi ne saboda rashin biyayya ga gwamnati. Aminu Ado Bayero ne aka nada domin ya gaje shi, inda ya zama sarkin Kano na 15 a jerin Sarakunan Fulani. An haifi Alhaji Aminu Bayero a kwaryar birnin Kano ranar 21 ga watan Agusta, 1961, gabanin mahaifinsa Ado Bayero ya zama sarkin Kano da shekara biyu. A 1990 mahaifinsa Alhaji Ado Bayero ya fara ba shi mukamin sarauta, inda aka nada shi Dan Majen Kano kuma Hakimin Nassarawa. Daga nan ne kuma aka kara masa girma zuwa Dan Majen Kano Hakimin Gwale a dai shekarar ta 1990. A shekrar 1991 kuma likkafa ta kara gaba inda aka nada shi Turakin Kano kuma Hakimin Dala a watan Janairun 1991 zuwa Janairun 2001, ma'ana dai ya shekara 10 a wannan mukami. Alhaji Aminu Ado Bayero ya zama Sarkin Dawakin Tsakar Gida, Hakimin Dala daga watan Janairun 2001 mukamin da ya rike har zuwa 2014. A watan Oktobar 2014 Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya nada shi a matsayin Wamban Kano kuma dan majalisar sarki. Ya rike mukamin har zuwa watan Mayun 2019. A watan Disambar 2019 ne kuma Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya nada shi Sarkin Bichi na farrko bayan kirkirar sabbin masarautu. Alhaji Aminu Ado Bayero ya fara karatu a makarantar firamare ta Kofar Kudu daga 1967 inda ya kammala a 1974. Daga nan ne kuma ya tafi zuwa kwalejin gwamnati ta Birnin ta Birnin Kudu a jihar Jigawa a yanzu, inda ya yi karatunsa na sakandare. Alhaji Aminu Bayero ya halarci Jami'ar Bayero inda ya samu digiri a fannin aikin jarida da kimiyyar siyasa daga 1979 zuwa 1984. Haka kuma ya yi aikin hidimar kasa a jihar Benue inda ya yi aiki a gidan talabijin na kasa NTA. Sabon Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado ya fara aiki a kamfanin jiragen sama na Kabo Air, a matsayin jami'in hulda da jama'a daga 1985 zuwa 1990 inda ya riki matsayin darakta a kamafanin. A bangaren kungiyoyi kuwa, Sarkin Kano Aminu Ado Bayero shi ne shugaban kungiyar masu wasan kwallon kwando ta jihar Kano, kuma shi ne uban kungiyar 'yan asalin Ilorin. https://www.bbc.com/hausa/labarai-51809298 +entertainment Ra'ayi riga na 21 10 2022 Ra'ayi riga kan taron tattaunawa da 'yan takarar shugabancin Najeriya a zaben baɗi da ke tafe, wanda gamayyar kungiyoyin arewa suka shirya https://www.bbc.com/hausa/articles/c3gxng11jwzo +entertainment Mai yi wa Sarauniya Elizabeth kwalliya ta fallasa sirrin sarauniya "An fallasa sirrin Sarauniya Ezabel II, a wani sabon littafin da daya daga cikin mutanen da suka fi kusanci da ita ta wallafa. Angela Kelly ta rubuta littafin wanda ya yi bayani a kan abubuwan da suka faru na sirri, a tsawon shekarun da ta yi tana taimaka wa sarauniyar Ingila wajen sanya kayanta, haka kuma a matsayinta na kawarta. Hasali dai abin da aka saba gani shi ne, Sarauniya da mai yi mata dinki da kuma tufafin da za ta sanya duka masarauta ce ke amincewa da su. Dan takaitaccen bayani a kan littafin ya ce ""Sarauniyar da kanta ta amince wa Angela ta bayyana wa duniya irin shakuwar da suka yi"". Mujallar Hello ta fara wallafa wasu daga cikin abubuwan da suka ja hankali da littafin ya kunsa. 1. Sai wata ta gwada sabon takalmanin sarauniya A cikin littafin, Ms Kelly, wadda ke yi wa sarauniya kwalliya tun daga shekarar 2002, ta tabbatar da cewa sarauniyar na da wadda ke taimaka mata wajen gwada sabon takalminta ko zai yi daidai. Kuma mai taimaka mata wajen kwalliyar ce ke yin hakan. Ms Kelly ta rubuta cewa: ""Sarauniya ba ta da lokaci sosai don haka ba ta gwada sabon takalminta, kuma da yake kafarmu daya, sai faduwa ta zo daidai da zama. "" 2. Sarauniya ce ta bukaci ta yi magana a wasan James Bond a lokacin bikin bude gasar Olympics a London a shekarar 2012 Ms Kelly ta ce cikin kankanin lokaci ""mintoci biyar"" da yi wa sarauniya tayin fitowa tare da tauraron fim din James Bond, Daniel Craig ta amince da hakan. ""Batun ya nishadartar da ita sosai, abin da yasa nan da nan ta amince. Sai na tambaye ta ko za ta so ta yi magana? Bata ko musa ba, sai ta amsa da cewa: ' Ai dole na ce wani abu, domin zai zo ceto na ne,"" A cewar Ms Kelly. ""Na tambaye ta ko za ta so ta ce: 'Barka da maraice, James,' ko kuma: ' Barka da yamma, Mr Bond,' to sai ta zabi na biyun saboda fina-finan Bond din da ta sani. Kafin ka ce wani abu na sanar da labarin ga daraka [Danny Boyle] - Ina ganin sai da ya ji kamar zai fado daga kujerar da yake zaune, saboda na gaya masa cewa sarauniya zata fadi: ' Barka da yamma Mr. Bond. 3. Zuwan sarauniya filin gasar tseren dawaki na Royal Ascot Mutane kan zuba ido su sha kallon irin dawakin gidan sarauta da sarauniya ke zuwa da su wajen gasar tseren dawaki na Royal Ascot da ake yi duk shekara. Sai dai ba kawai dawakan mutane ke kallo ba - ta kai har sun zuba kudaden caca kan launin hular da sarauniyar ta sanya. Ms Kelly ta rubuta cewa: "" Na yi wata ganawa da mai shirya cacar, inda muka amince kan lokacin da za a rufe don kada a cuci wasu, amma muka bar mutane suka ci gaba da cankar launin hulal sarauniya domin wanda zai lashe gasar ya samu wasu 'yan kudade."" 4. Rungumar Michelle Obama Rahotanni sun ce sarauniya ta yi ""watsi "" da al'adar masarauta da ta rungumi matar tsohon shugaban Amurka, Michelle Obama, a lokacin da suka gaisa a shekarar 2009, batun ba haka ya ke ba a cewar, Ms Kelly. ""A zahiri, dabi'a ce ga sarauniya ta girmama macen da ake ganin girmanta, haka kuma babu wata al'adar da ta zama dole a bi. "" kamar yadda ta rubuta. Mrs Obama ta yi rubutu kan abubuwan da suka faru a rayuwarta cewa, su biyun sun amince su sanya takalma masu tsini kuma hakan ya sanya kafafuwansu sun yi tsami. Mun kasance ""mata biyu da takalmanmu suka wahalar da mu"", 5. Akwai wani sirrin da ba a sani ba, game da rigar sarauta ta radin suna Ms Kelly ta bayyana yadda aka yi amfani da ""ganyen shayi wajen yin irin rigar da aka taba amfani da ita a radin sunan James, Viscount Severn, a shekarar 2008. ""Don tabbatar da cewa ya yi kama da wancan, an rina rigar a ruwan ganyen shayin da ake shukawa a Yorkshire,"" Ms Kelly ta rubuta hakan a littafin. ""Mun saka kowane yadin leshin a wani karamin mazubi, muka cika shi da ruwa aka kuma saka ganyen shayin ya tsumu kamar tsawon mintoci biyar, aka ringa dubawa a kai a kai har sai da launin ya yi daidai.""" https://www.bbc.com/hausa/labarai-50286570 +entertainment Me ya sa gwamnatin Ganduje ke takun-saka da mawakan Kannywood? "Kamun da rundunar 'yan sanda ta jihar Kano ta yi wa Naziru M. Ahmed ranar Laraba da yamma ya sake tado da sabuwar kura kan rikicin siyasar da yake faruwa a jihar. Kakakin rundunar 'yan sandan, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya shaida wa BBC cewa sun kama mawakin ne ""saboda kalaman batanci"" da ya yi a cikin wasu wakokinsa. Ya kara da cewa ana tuhumar mawakin da gudanar da dakin yin waka, wato sutudiyo, a gidansa, zargin da Naziru M. Ahmed ya musanta. Malam Aminu Saira, dan uwan mawakin, ya gaya wa BBC cewa 'yan sanda sun sanar da su cewa ""gwamnatin jihar Kano ce ta sa aka kama shi ta hannun hukumar tace fina-finai ta jihar."" ""An kama Naziru ne saboda fitar da wani kundin waka da ya yi mai suna 'Gidan Sarauta' da kuma 'Sai Hakuri'. Mun yi kokari a ba mu belinsa ranar Laraba da daddare amma an ki,"" in ji Saira -- a lokacin Naziru yana gidan yari kafin a sako shi. Hasalima, a cewarsa, an fitar da kundin wakar ne shekara hudu da suka gabata kuma a wancan lokacin, hukumar tace fina-finan bata yi korafi ba. Tuni dai Naziru ya bayyana a gaban wata kotun Majistare a birnin Kano. An bayar da belinsa da sharuda wadanda suka hada da bayar da kudi naira dubu 500, da mika fasfo dinsa na tafiye-tafiye, da kuma gabatar da mutane uku da za su tsaya masa, wadanda dole su kasance ma'aikatan gwamnatin jihar Kano da kuma dagacin yankin da yake zaune. Mun yi kokarin jin ta bakin shugaban hukumar tace fina-finan, Isma'ila Na'abba Afakallah, amma bai amsa kiran wayar da muka yi masa sau da dama ba. Kazalika bai yi martani kan sakon text da na WhatsApp din da muka aika masa ba. Sai dai jaridar Daily Trust ta ambato shi yana musanta cewa siyasa ce ta sa ake cin zarafin mawakan yana mai cewa sun keta dokokin hukumar tace fina-finai ne. 'Alaka da Sarki Sanusi da Kwankwasiyya' Naziru shi ne Sarkin Wakar Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II, mutumin da ya dade yana kai ruwa rana tsakaninsa da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje lamarin da ya kai ga rarraba masarautarsa zuwa gida biyar. Kazalika, mawakin fitaccen dan kungiyar Kwankwasiyya ne, wato bangaren siyasar jam'iyyar hamayya ta PDP da tsohon gwamnan jihar, Rabi'u Musa Kwankwaso ke jagoranta ne. A 2015 dai tsohon gwamna Kwankwaso ya yi ruwa ya yi tsaki wurin ganin Gwamna Ganduje ya ci zabe - kuma sun yi nasara. Amma daga bisani sun raba gari. Aminu Saira na ganin cewa kama kanin nasa bai rasa nasaba da siyasa, domin kuwa, a cewarsa, ""idan dan uwan nasa ya yi waka 'yan kasuwa yake sayarwa. Don haka su ya kamata a tuhuma. Kazalika kamfanin da yake buga wakar ""nawa ne ba na Naziru ba, don haka idan suna da matsala da wakokin ni ya kamata su tuntuba."" Wannan dai ba shi ne karo na farko da hukumar tace wakoki da fina-finai ta Jihar Kano ke kama jarumai da mawakan Kannywood ba. Wasu jarumai da masu ruwa da tsaki a masana'antar Kannywood na ganin a yanzu hukumar ta mayar da hankali ne wajen musgunawa wadanda ake jin suna adawa da gwamnati. Kafin kamun da aka yi wa Naziru sarkin waka, hukumar tace fina-finan ta kama Sadiq Zazzabi da kuma a baya bayan nan Sunusi Oscar bisa zarge-zarge da suka hada da saba kai'dar aiki. A takaice, hukumar ta ce ta kama Sanusi Oscar ne saboda ""ya fitar da wata waka wadda ke nuna badala"", yayin da shi kuma Sadiq Zazzabi aka kama shi saboda zargin saba wa dokar da ta ce wajibi ne duk sabuwar wakar da za a fitar sai an gabatar da ita ga hukumar don tacewa da kuma samun sahalewarta. Za mu sanya kafar wando daya da Afakallah Sai dai jarumi kuma mai bayar da umarni, Falalu Dorayi, ya shaida wa BBC cewa kamen da aka yi wa dukkan mawakan uku na da alaka da siyasa. ""Da farko ya kamata ka sani cewa dukkan wadannan mawaka 'yan PDP ne kuma sun yi shura wajen caccakar gwamnatin Kano ta APC. Idan har da gaske ne cewa an kama su ne domin sun saba doka, me ya sa ba a taba kama Dauda Kahutu Rarara ba? Babu wanda ba ya zagi a cikin wakarsa amma tun da dan jam'iyyar APC ne sun kasa kama shi."" Tuni dai fitattun jarumai irin su Adam Zango da Mustafa Naburaska suka bayyana cewa sun dakatar da yin fim a jihar Kano, har sai lokacin da gwamnati ta daina cin zarafin 'yan fim. Kazalika, jarumai irin su Sani Danja da Ali Nuhu sun yi kira a bi a hankali kan yadda ake kama mawaka da 'yan fim. Su ma jaruman fina-finan Nollywood da ake yi a kudancin Najeriya ba a bar su a baya ba wajen sukar gwamnati kan kamun da aka yi wa mawakan Kannywood. Fitacciyar jarumar nan Kate Henshaw ta gargadi hukumar tace fina-finan jihar Kano kan musgunawa mawaka. Su ma masu sharhi a masana'antar Kannywood sun ce wadannan kame-kame take hakkin dan adam ne da 'yancin fadin albarkacin baki, kuma za su iya jawo mummunar gaba a masana'antar. Muhsin Ibrahim mai nazari ne kan fina-finan Kannywood, kuma ya shaida wa BBC cewa ""kama mawaƙa da gwamnatin Kano take abin takaici ne ga Kannywood. Yana ƙara jawo rarrabuwar kai da gaba a tsakanin mutanen masana'antar wadda dama tuni alaƙa ta yi tsami a tsakaninsu. Ya kara da cewa ""hakan zai kashe bunƙasar masana'antar da kuma sa tsoro a zukatan mawaƙa da sauran mutane. A hankalce, ba dole ne kowa ya bi bayan gwamnati mai ci ba. Cusgunawa mawaƙa na nufin a daina adawa, wadda kuma ba zai yiwu ba."" Sai dai ya yi kira ga mawakan da su bi doka ""su kuma yi adawa mai tsafta da kuma hankali"". Amma Falalu Dorayi ya ce idan har gwamnati ta ci gaba da amfani da hukumar tace fina-finai wurin cin zarafin 'yan fim, to ba za su yi kasa a gwiwa wajen adawa da ita ba. ""Muna kira ga shugaban hukumar tace fina-finai ya sani cewa ya daina bari 'yan siyasa suna amfani da shi wurin cimma burinsu. Amma idan ba haka ba, za mu sanya kafar wando daya da shi kuma za mu yi galaba a kansa kamar yadda muka yi a kan magabacinsa,"" in ji Dorayi." https://www.bbc.com/hausa/49687890 +entertainment 'Yan Kannywood na jimamin mutuwar Ubale Wanke-Wanke Masu fitowa a fina-finan Hausa na Kannywood suna ta mika ta'aziyarsu tare da jimamin mutuwar abokin aikinsu Ubale Ibrahimda aka fi sani da Ubale Wanke-Wanke. Ubale ya rasu ne ranar Alhamis da yamma a Kano, kuma tuni aka yi jana'izarsa a ranar Juma'a da misalin karfe takwas na safe a Rangaza, a Kano. Ubale ya shafe tsawon lokaci yana fama da hawan jini da ciwon zuciya da suke yawan taso masa akai-akai. Mansura Isah matar Sani Danja ta shaida wa BBC cewa ''Sai dai a wannan karon da ciwon ya tashi sai ya zama jalinsa. ''Ba mu taba tsammanin cewa ba zai tashi ba, mun zaci ciwon zai yi sauki kamar yadda ya saba tashi ya kuma lafa tsawon shekaru,'' in ji ta. Sani Danja da matarsa Mansura wadanda su ne iyayen gidan Ubale a masana'antar su ne suka fara sanar da mutuwar tasa a shafukansu na sada zumunta. Taurarin Kannywood kamar su Ali Nuhu da Yakubu Mummahd da Rahama Sadau da Maryam Booth da Falalu Dorayi da kuma Ado Gwanja duk sun wallafa sakon ta'aziyyarsu da jimami a shafukansu na Instagram. Duk da cewa Ubale ya dade a harkar Kannywood, amma bai shahara sosai ba, kuma bai yi wasu tarin fina-finan masu yawa ba. Kazalika Ubale ya fi fitowa ne a fina-finan kamfanin Sani Danja, amma ya kan fito a wasu ma jefi-jefi, sai dai ya shafe lokaci ba ya fitowa a fim a baya-bayan nan. ''Ya dade bai yi fim ba gaskiya, sai dai muna aiki tare a kungiyar NGO dita da muke taimaka wa marasa galihu,'' in ji Ansura. Ubale dan asalin Unguwar Tudun Murtala ne a birnin Kano. Ya mutu ya bar mace daya da 'ya'ya shida. https://www.bbc.com/hausa/labarai-52504319 +entertainment Abin da ya sa na yi rigista da hukumar fina-finan Kano Adam A. Zango ya ce ya yi rijista da hukumar tace fina-finai da dab'i ta jihar Kano ne domin kawo karshen matsalolin da abokan sana'arsa suke fada wa a ciki. https://www.bbc.com/hausa/labarai-52220435 +entertainment ...Daga Bakin Mai Ita tare da Teemah Yola, Rukayya ta Labarina Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon: Daga Bakin Mai Ita wani shiri ne na BBC Hausa da ke kawo muku hira da fitattun mutane kan wasu abubuwan da suka shafi rayuwarsu zalla. A wannan kashi na 58, shirin ya tattauna da Teemah Yola, Rukayya ta Labarina Series, kuma jaruma a Kannywood. A wannan shiri ta amsa tambayoyin da suka shafi rayuwarta da rawar da take takawa a masana'antar fina-finai. Ɗaukar bidiyo: Abdulsalam Usman Abdulkadir Tacewa: Yusuf Yakasai Tsarawa da gabatarwa: Buhari Fagge https://www.bbc.com/hausa/media-57919897 +entertainment Ali Nuhu: Me ya sa aka naɗa jarumin a matsayin jakadan La Liga a Arewa? "An naɗa fitaccen jarumin fina-finan Hausa na Kannywood Ali Nuhu a matsayin jakadan La Liga a Arewacin Najeriya. An yi naɗin ne a wani taro da La Liga da kuma rediyon Arewa suka shirya a jihar Kano da ke arewa maso yammacin kasar. A cewar Sheriff Abdallah wanda ya shriya taron, Kano ita ce gidan gasar La Liga sannan shirin wanda shi ne irinsa na farko mafari ne na zuwan wasu abubuwan ci gaba a Najeriya da ma Arewacin ƙasar. ""Mun kusanto da La Liga kusa da magoya baya, yanzu aka soma kakar wasannin kuma ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba saboda za mu ci gaba da inganta alaƙa tsakanin (La Liga) da kuma magoya bayansu a Najeriya,"" a cewar Abdallah. Shi ma tsohon ɗan wasan Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Super Eagles kuma jakadan La Liga a Najeriya, Mutiu Adepoju ya bayyana jin daɗinsa kan yadda ake samun dumbin magoya bayan gasar a Kano da sauran wasu yankunan Arewacin Najeriya. Tsohon ɗan wasan ya buƙaci masu kallon gasar da su ci gaba da karfafa haɗin kai a tsakaninsu duk da banbancin ra'ayi da suke da shi a ƙwallon ƙafa. Sabon jakadan, Ali Nuhu ya shaida wa BBC cewa La Liga ta shirya taron kasancewar akasarin magoya bayanta a yankin Arewacin Najeriya suke kuma Hausa ce harshen da aka fi amfani da shi a yankin. Kuma a cewarsa, kasancewar harshen Hausa na da faɗi, La Liga na son ta zama kusa da magoya bayanta da ke Najeriya musamman a Arewacin ƙasar. Ya ce hakan zai sa magoya baya su san cewa La Liga na tare da su. Wannan muƙamin wata dama ce ta zama jigo tsakanin magoya baya da La Liga, in ji Ali Nuhu. A yanzu haka Ali Nuhu ya ce yana shirin tafiya kasar Spaniya domin kallon wasa biyu na La Liga, da zarar an ci gaba da zirga-zirga tsakanin Najeriya da Spaniya. A cewar fitaccen jarumin akwai alfanu da dama da ke tattare da naɗin nasa a matsayin jakadan La Liga a yankin Arewacin Najeriya kuma sun haɗa da:" https://www.bbc.com/hausa/54159747 +entertainment Queen Elizabeth II: Rayuwar Gimbiya a filin daga "A nazarin mafi yawan harkokin rayuwarta, Yakin Duniya na Biyu shi ya bude mata babin rayuwa da ya haskata na kasancewarta Sarauniya Elizabeth II Tana da shekara 13, inda shekaru shida da aka shafe na rikicin yaki suka share mata fagen hada-hadar harkokin rayuwa, inda ta fara fita bainar jama'a a matsayin sarauniyar da za ta gaji sarautar mulki. Zuri'ar gidan sarauta - Sarki da Sarauniya da 'ya'yansu biyu Elizabeth da Margret su ne tambarin alamar sarautar Birtaniya, wadanda a dalilinsu ne Birtaniya da abokan hadin gwiwarta ke yakar Jamus karkashin jagorancin Adolf Hitler. An cimma dimbin nasarori saboda a gaskiyar lamari Adolf Hitler ba shi da hakikanin iyali na kashin kansa. A Oktobar 1940, lokacin da Birtaniya ta yi fama da luguden bama-bamai mafi muni, Elizabeth ta fara yi wa al'ummar kasar jawabi ta kafar yada labarai. An dai tsara jawabin ne a matsayin sako ga kananan yara, wadanda aka kai su Arewacin Amurka don samun mafakar tsira daga illar luguden bama-baman da aka rika jefa wa biranen Birtaniya. Kuma an tsara hakan ne don zaburarwa da daukar hankalin Amurkawa su goyi bayan shigar Amurka yakin. ""Mu yaran da ke zaune a gida muna cike da karsashi da kwarin gwiwa,"" in ji ta. ""Muna iya kokarin ganin mun yi abin da za mu iya yi don taimaka wa jaruman sojojinmu na ruwa da na sama. Sannan mun shirya tarairayar hadari da takaicin bakin cikin da ke tattare da yaki."" Hakikanin gaskiya kasancewar Elizabeth da Margaret a cikin kasar lamarin ya yi matukar bayar da karsashin kwarin gwiwa. An bayar da shawarar ganin iyalan gidan sarauta su nemi mafaka a kasar wajen, musamman Kanada, amma Sarki da Sarauniya suka nuna ko-in-kula ""Yaran ba za su fice daga kasar ba in ban fice ba,"" yadda Sarauniya Elizabeth ta yi ikirari. ""Ba zan fice ba sai dai in iyayensu ne suka yi hakan, kuma Sarki bai zai fice daga kasar ba a kowane irin hali ta kasance."" Wuri mafi nisa da aka kai yaran shi ne gidan sarautar Windsor. ""Mun je hutun karshen mako, sai muka zauna har tsawon shekara biyar,"" in ji su. Suna da matukar kusanci da inda za su rika hango tartsatsin wuta a sararin samaniyar Landan lokacin da ake ruwan bama-bamai. Akwai lokacin da bam ya fado daf da gidan sarauta. ""Daukacinmu mun kasance cikin damuwa lokacin da muka ji karar,"" kamar yadda Gimbiya Margaret ta tuna, lokacin da suke zaune a mafakarsu ake kawo hari ta sama. Wadannan 'yan uwa a mafi yawan yammaci da kwanakin karshen mako iyayensu kan kasance tare da su, sannan an ci gaba da koyar da su karatu, tare da malaman da ke koya musu darussa. A lokacin Kirsimeti don su bai wa mahaifinsu kwarin gwiwa - wanda ya dugunzuma cikin damuwa bisa la'akari da dimbin asarar rayukan mutanen kasarsa maza da mata - sai wadannan 'yan mata suka gudanar da wasannin kwaikwayon nuni cikin nishadi (babu furucin kalamai sai nunin abin da ake nufi). A Kadaicin shekara guda, Aladdin tare da Gimbiya kusan kodayaushe ya kan zama gwarzon tauraro. A shekarar 1942 gimbiya Elizabeth ta fara gudanar da harkokin mulki a bainar jama'a, inda ta duba faretin ban girma na rundunar 'yan gadin Grenadier (masu gadin kula da tsaron Sarki da Sarauniya), inda ta samu karramawar mai matsayin Kanar. Mafi kimar mukamin gudanar da aiki da ta samu ya fito karara cikin al'amuran da suka faru a wadannan shekarun. A shekarar 1944, inda kacokam Sarki ya kasance cikin bacin rai game da asaratr da aka yi a yakin Arnhem, Elizabeth 'yar shekara 18 da Margaret 'yar shekara 14 dsuka rubuta wasan kwaikwayon nuni cikin nishadi mai taken Kananan jajaye mahaya kofatai - 'Little Red Riding Boots- tare da taimakon mahaifiyarsu. Masu gadin gidan sarautar da ke bakin aiki, su uku an dan tsarma fitowarsu a wasan. Daya daga cikinsu, Bill Davies, ya tuna yadda aka auna shi, don dinka masa kayan sarki masu walwalin hasken jajaye da fatar yanyawa. ""Wasan ya yi matukar kayatarwa, har ta kai ga iyalan (gidan sarautar) sun tattara hankalinsu wuri guda,"" kamar yadda ya iya tunawa. ""Hikaya ce ta wucin-gadi (wani dan takin lokaci). Mun manta da yaki na tsawon sa'a guda ko biyu."" A shekarar karshe ta zamanin yaki, Elizabeth ta fito cikin kayan damarar baraden yi wa iyakar kasa hidima, wadanda ake yi wa lakabin ATS. An yi mata rajistar shiga rundunar da lambar 230873, da lakabin sunan Second Subaltern Elizabeth Windsor, kuma ta shafe makonni uku tare da da wata tawagar rundunar da aka yi matukar lura da su, inda ta koyi kanikancin gyaran mota da tukin babbar mota. An ce dai lamarin shi ne karo na farko da aka taba samun mace 'yar gidan sarauta ta halarci kwas din koyon aiki tare da ""sauran gama-garin mutane."" Kuma shekarun da suka biyo bayan yakin a cikinsu ne ta tsunduma a cikin soyayya tare da Laftanar Philip Mountbatten, daga bisani ya zama mai sarautar gargajiya na magajin garin Duke na Edingburgh, bayan da ya zama mijinta, har ya kasance mai matukar tasiri a harkokin mulkinta. A Mayun 1945, dubban mutane sun taru a fadar Buckingham don murnar bikin zagayowar ranar samun nasarar Turai. Winston Churchill ya kasance tare da iyalan gidan sarautar a wannan farfajiyar, inda gimbiyoyi biyu suka fice daga wurin suka shiga cikin taron mutane. Bayan shekara 40, Sarauniya duk ta tuna wadannan al'amura da suka faru. ""Na tuna jerin gwanon mutanen da ban sani ba dauke da makamai, suna tafiya zuwa titin hanyar zuwa gidan sarauta mai lakabin 'Whitehall.' Daukacinmu kawai mun kasance cikin farin ciki da annashuwa."" ""Bayan da muka keta wurin shakatawa na Green Park, sai muka tsaya a waje muna ta kwalla kara, ""Muna son Sarki."" Ina jin cewa wannan shi ne al'amari mafi muhimmaci a wannan dare da ba zan manta da shi a rayuwata ba."" ©Hakkin mallakar hotunan abun kiyayewa ne" https://www.bbc.com/hausa/labarai-47247260 +entertainment Coronavirus: Mawaƙiya Madonna ta kamu da cutar "Shahararriyar mawakiyar nan ta Amurka, Madonna, ta ce ta yi fama da cutar korona lokacin da ta yi tafiya zuwa wasu kasashen duniya. A sakon da ta wallafa ranar Laraba a Instagram, ta ce ta harbu da cutar ne lokacin da ta yi balaguro na kasashen duniya mai suna Madame X. Sai dai ta ce yanzu haka lafiyarta kalau amma dai gwajin da aka yi mata a baya ya nuna cewa tana da garkuwar jiki ta Covid-19 a cikin jininta. ""Idan gwaji ya gano cewa kana da garkuwar jikin, hakan yana nufin ka taba KAMUWA da cutar kuma na yi fama da rashin lafiya a kusan karshen balaguron da na yi zuwa Paris mako bakwai da suka wuce tare da 'yan rakiya ta, amma a lokacin mun yi tsammani mura ce mai zafi ta kama mu,"" in ji sakon da mawakiyar ta wallafa a Instagram, tana mai cewa yanzu dukkansu sun samu sauki kuma lafiyar lau. Madonna ta katse balaguron da take yi bayan gwamnatin Faransa ta haramta gudanar da dukkan tarukan jama'a. Mawakiyar, mai shekara 61, ta bayar da tallafin $1m domin samar da riga-kafin cutar korona." https://www.bbc.com/hausa/labarai-52573455 +entertainment Yadda na taimaka wa Safara'u shiga waƙa - Mr 442 Fitaccen matashin mawakin nan na arewacin Najeriya, Mubarak Abdulkarim wanda aka fi sani da 442 ya bayyana alakarsa da Safiya Yusuf wato Safa. A hirarsa da BBC, 442 ya bayyana cewa ya karfafa wa Safiya gwiwa ne sakamakon mawuyacin halin da ta shiga bayan fitar bidiyon tsiraicinta. https://www.bbc.com/hausa/articles/cn0v4v4zeyno +entertainment ...Daga Bakin Mai Ita tare da Nomiis Gee Ku latsa hoton sama domin kallon bidiyon: Daga Bakin Mai Ita wani shiri ne na BBC Hausa da ke kawo muku hira da fitattun mutane kan wasu abubuwan da suka shafi rayuwarsu zalla. A wannan kashi na 83, shirin ya tattauna da fitaccen mai gabatar shirin nan na Zafafa 10 a tashar Arewa 24, wato Aminu Abba da aka fi sani da Nomiis Gee. A cikin hirar, Nomiis Gee ya yi mana bayani game da rayuwarsa. Tsarawa da gabatarwa: Yusuf Yakasai Ɗaukar bidiyo/Tacewa: Yusuf Yakasai https://www.bbc.com/hausa/media-60144507 +entertainment Mene ne aikin Sarki a Masarautar Birtaniya? Sarki Charles na III ya gaji mahaifiyarsa, Sarauniya Elizabeth ta II, bayan rasuwarta a fadar Balmoral tana da shekara 96. A farkon shekarar da muke ciki, Sarauniyar ta yi bikin cika shekara 70 a kan karagar mulki abin da ya sa ta zama Sarauniyar da ta fi daɗewa a kan karagar mulkin Birtaniya. Bayan Sarauniyar ta mutu, nan take sarauta ta koma kan ɗanta wanda shi ne magajinta wato tsohon Yariman Wales. A ranar Asabar aka naɗa Charles a matsayin sarkin Birtaniya a hukumance a fadar St James da ke birnin Landan a wani biki da aka yi. Sarki shi ne shugaban ƙasa na Birtaniya, sai dai ikonsa ba ya tasiri kuma zai kasance ba ya goyon bayan wani ɓangare a harkokin siyasa. Zai riƙa karɓar saƙonni a kowace rana daga gwamnati a cikin wani jan akwati gabanin tarurruka masu muhimanci ko takardun da ke buƙatar sa hannunsa. Haka kuma a kowace Laraba Firaiminista yake ganawa da Sarki a fadar Buckingham domin ya yi masa bayani a kan al’amuran gwamnati. Waɗannan tarurruka duk na sirri ne kuma babu wani bayani a hukumance game da abin da aka faɗa. Haka kuma Sarki na taka muhimmiyar rawa a ɓangaren Majalisar Dokokin ƙasar. Bugu da ƙari, Sarkin zai karɓi baƙuncin shugabannin ƙasashe duniya masu ziyara tare da ganawa da jakadun ƙasashen waje da ke zaune a Birtaniya. Shi ne zai jagoranci taron tunawa da mazan jiya da ake yi a watan Nuwamba ta kowace shekara a birnin Landan. Sabon Sarkin shi ne shugaban ƙungiyar Commonwealth wadda ƙungiya ce mai mambobi kasashe 56 da kuma mazauna biliyan 2.4. Sai dai tun bayan lokacin da Barbados ta zama Jamhuriya a 2021 an samu wasu ƙasashen Caribbean da ke cikin ƙungiyar da sun nuna alamun su ma za su bi sahun ƙasar ta Barbados. Hoton Sarki Charles na uku zai maye gurbin na mahaifiyarsa a kan sabon tambari na Royal Mail da kuma takardun kudi kuma za a sabunta kalmomin da ke cikin sabon fasfo ɗin ƙasar ya koma mai martaba. Taken ƙasar zai koma “Allah ya ja zamanin sarki” Tsarin gadon sarauta ya bayyana wanda zai karɓi sarauta daga iyalin gidan sarauta bayan wanda ke kan mulki ya mutu ko ya sauka daga sarautar ƙasar. Na farko a layi - magajin sarauta - shi ne babban ɗan sarki. A matsayin ɗan fari na Sarauniya Elizabeth, Charles ya zama sarki a lokacin mutuwar mahaifiyarsa kuma matarsa ta koma Sarauniya da ake kira Queen Consort. Dokokin gadon sarauta da aka yi wa kwaskwarima a 2013 sun sa ba za a ba ƴaƴa maza fifiko fiye da yayyensu mata ba. Magajin Charles shi ne babban ɗansa, Yarima William wanda ya gaji sarautar mahaifinsa na Duke na Cornwall. Sai dai ba a nan take zai zama Yariman Wales ba - wannan wani muƙami ne da sarkin ne kawai zai ba shi. Babban ɗan Yarima William, Yarima George shi ne na biyu a matsayin magajin sarauta sannan babbar ƴarsa Gimbiya Charlotte ita ce ta uku. A bikin naɗin sarauta ne ake naɗa sarki a hukumance. Ana gudanar da shi ne bayan wani lokaci na zaman makoki na sarkin da ya gabata. Elizabeth ta biyu ta zama Sarauniya a ranar 6 ga watan Fabrairu 1952 bayan mutuwar mahaifinta Sarki George na shida amma ba a naɗa ta ba sai a ranar 2 ga watan Yuni 1953. Naɗin sarautarta shi ne na farko da aka yaɗa kai-tsaye ta talibijin kuma mutum sama da miliyan 20 ne suka kalli bikin. A cikin shekaru 900 da suka gabata a Westminster Abbey ne aka riƙa gudanar da naɗin sarauta-William the Conqueror shi ne sarki na farko da aka naɗa a wannan wuri kuma Charles shi ne na 40. Biki ne da ke gudana a cocin Ingila na Anglican karkashin jagorancin  babban limamin cocin wato Archbishop of Canterbury. Ana shafe sarki fa “mai tsarki” kuma yana karɓar sandar sarauta. Babban limamin cocin Ingila zai sanya masa kambun St Edward a kai da aka yi  da zinari tun 1661. Ba kamar bukukuwan aure na sarauta ba, naɗin sarautar wata al'ada ce ta jiha, Gwamnati ce take ɗaukar nauyinsa kuma ita ce take yanke shawara a kan waɗanda za su halarci bikin. Duke na Cornwall da Cambridge (Yarima William) shi ne babban dan Sarki Charles da matarsa ta farko Diana gimbiyar Wales. Yana auren Duchess ta Cornwall da Cambridge (Catherine) Suna da ƴaƴa uku: Yarima George da Gimbiya Charlotte da Yarima Louis. Gimbiya Anne ita ce ƴa ta biyu da Sarauniyar ta haifa. Ta auri Vice Adm Timothy Laurence. Tana da yara biyu da mijinta na farko Kyafin Mark Philips: Peter Philips da Zara Tindall. Earl na Wessex ( Yarima Edward) shi ne autan Sarauniya. Yana auren Countess ta Wessex (Sophie Rhys Jones) Suna da yara biyu: Loiuse da James Mountbatten-Windsor Duke na York (Yarima Andrew) shi ne ɗan sauraniya na biyu. Yana da yara mata biyu da tsohuwar matarsa, Duchess ta York ( Sarah Ferguson): Gimbiya Beatrice da gimbiya Eugenie. Sai dai Yarima Andrew ya ajiye mukaminsa na yi wa jama a hidima sakamakon hirar da ya yi da Newsnight a 2019 kan zargin ya ci zarafin wata mata ta hanyar lalata. A 2022 ya biya kuɗin da ba a bayyana adadinsu ba a matsyin diyya ga Virginia Giufrre wadda ta kai ƙara kotu a Amurka. Duke na Sussex (Yarima Harry) shi ne ƙanin William. Yana auren Duchess ta Sussex (Meghan Markle). Suna da yara biyu: Archie da Lilibet. A 2020 sun sanar cewa za su ajiye muƙamansu a matsayin manyan masu sarauta kuma za su koma Amurka da zama. Ana sa ran Sarki Charles da Sarauniya Camilla za su koma Fadar Buckinham da zama. A baya suna zaune ne a Clarence House da ke Landan. Yarima William da Catherine Duchess ta Cornwall da Cambridge a baya-bayan nan sun koma West London daga Kensington domin su zauna a Adelaide Cottage da ke Windsor Estate. Yarima Harry da Meghan Markle na zama a California. Kuri’ar jin ra’ayoyin jama'a da aka gudanar a lokacin da aka yi bikin cikar Sarauniya shekara70 kan karagar mulki ta nuna cewa kashi 62 cikin 100 na mutane na ganin ya kamata masauratar ta ci gaba da mulkin ƙasar. Kashi 22 ke cewa ya kamata a samu zaɓaɓɓen shugaban ƙasa a maimakon haka. https://www.bbc.com/hausa/articles/c2j4gy9n2dvo +entertainment Dangantakar Sarauniya Elizabeth da Diana "A wajen Sarauniya dai, karshen lamarin shi ne ""yarinyar da ba za ta taba samun shiga (a wajenta) ba."" Ita kuwa Diana a wajenta, ta yi ikirarin nuna ""kauna"" ga surukarta, kuma za ta iya yin komai dominta. Sai dai ta yiwu ba haka lamarin yake ba a wajen Sarauniya, bisa la'akari da irin tasirin Gimbiyar Wales ga sarauta, a daukacin rayuwa da mutuwa. Auren da ta yi a gidan sarauta wani babban yunkuri ne a wajen kowane mutumin da ke hange daga gefe, kai hatta ma wadanda suka shaku da rayuwar Diana. Matashiya Diana, haifaffiyar madaukakiyar zuri'a ce, wadda ta shafe shakarun rayuwarta na farko a farfajiyar Park House, wani gini dan taki ne daura da gidan Sarauniya na Norfolk da ke Sandringham. Sai dai ta bayyana karara ba tare da bata lokaci ba, cewa Diana mai shekara 20 ba ta shirya yin rayuwa irin ta wadanda suka dan manyanta a harkar fada. Ba ta samu agajin mutumin da zai kasance mijinta a cikin rayuwa ba. Ya kasance mai ra'ayin rikau, kuma dabi'arsa ta yi matukar saba wa na amaryarsa mai karsashi da far-far da jin kunya, sannan ga shi ya darsu da kaunar tsohuwar masoyiyarsa Camilla Parker-Bowles. Rashin karsashinsa kan ""dukkan abin da ya danganci soyayya,"" a amsar da ya bai wa mai neman labari da ya bijiro masa da tambaya kan yadda yake ji lokacin baikonsa, don share fagen kulla alakar (da abokiyar zaman) nan gaba a cikin rayuwa. Sarauniya dai ta yi wa kanta sharadin ba kasafai takan tsoma baki a harkar auren 'ya'yanta ba. Wasu masu sharhi sun yi nuna cewa kamata ya yi a ce ta shiga harkokin sarauta ka'in da na'in duk da kasancewarta sabon shiga da an tallafa mata. Diana ta yi fama da kadaici, tare da rashin sanin inda ta dosa - kuma ba ta da tabbacin abin da ake bukata daga gareta, don haka ta kasance cikin bacin rai, saboda rashin yaba wa nagartar kyakkyawan aikinta. Sarauniya, tamfar Yarima Charles, ta dauki babatu (cika da batsewar) Gimbiya abin takaici, kuma mawuyacin abin da za a iya shawo kansa.. Lamarin ya sha gabanta gogewarta a rayuwa, bisa la'akari da yadda ta taso, inda ba a baje abin da sosuwar zuciya ko damuwar mutum a bainar jama'a. Kai tsaye dai ba su san yadda za su tarairayi irin yanayinta da irin yadda ta darsu da son a ba ta cikakkiyar kulawa - kamar yadda takan bararraje a matattakalar bene lokacin da take dauke da cikin William. Ba haka ake yin irin wannan a zuri'ar gidan sarauta ba. Kuma ba su shirya wa yadda Diana ta rika juya akalar 'yan jarida suka yi ta haifar da ce-ce-ku-cen jan ra'ayin jama'a game da ita ba. Sarauniya ta yi takaicin tarwatsewar auren da aka yi wa alwashin samun dimbin alfanu. Daga nesa ta yi ta nazarin al'amuran da ke faruwa, inda ta yi kokarin kamewa - bisa tabbacin da take da shi cewa kasa kai ga gacin danta da auren magajinta na iya yin mummunar illa ga sarauta. Lokacin da dangantakar Charles da Diana ta yi tsami, sai ta yi watsi da dabi'arta ta rashin yin katsalandan (tsoma baki a harkar auren 'ya'yanta), sai ta kira su don tatttaunawa, inda ta shawarce su kan su yi kokari na karshe wajen shawo kan matsalar aurensu.. Lamarin dai ya ki yiwuwa, har sai da ta kai ga ba da dadewa ba, Diana ta yanke matsaya wajen bayyana wa al'umma halin da take ciki a shirin hangen nesa na BBC (Panorama), sai Sarauniya ta sake shiga cikin lamarin, inda ta rubuta wa kowanensu wasika, tare da nunin cewa rabuwar aurensu a halin da ake ciki ita ce kawai mafita. Saboda jikokinta, Sarauniya ta yi matukar iya kokarinta wajen kyautata dangnatakarta da Diana, amma bayan da auren ya rabu, sai ta kara nesanta kanta da ita. Bayan mutuwar Diana, an zargi Sarauniya da rashin fahimtar yadda mutanen kasar ke ji lokacin da ta tare a Baltimore don kwantar da hankalin jikokinta da ke cike da alhinin rashi. Karshe dai aka karke da kambama labarin a jaridu da dama, al'amarin da ya tursasata ta komo Landan. Lokacin da aka yi nisa da jana'izar Diana sai kwatsam ta yi wani jawabi kai tsaye ta talabijin, inda ta yi bayani kai tsaye game da surukarta. An ji cewa tamkar Sarauniya ta jefa harkokin sarauta cikin musifa. Taro ne mai matukar kayatarwa da ke nuna tausasawa da gudunmuwa ga al'umma. Lokacin da aka wuce da makarar gawar Diana ta gaban Fadar Buckingham, sai Sarauniya ta yi mata karramawar ban kwana.. Ta russuna don karrama wannan matashiya da ta samu kauna da girmama a wajen mutane da dama, amma dai sanadiyyar surukarta, wadda ta kasance mai ban mammaki tsawon rayuwarta. ©Hakkin mallakar hotunan abun kiyayewa ne" https://www.bbc.com/hausa/labarai-47254543 +entertainment Sarkin Kano Aminu Ado ya sake naɗa waɗanda Ado Bayero da Sarki Sunusi II suka tuɓe A naɗe-naɗen farko da ya yi tun bayan zamansa Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya naɗa ɗan uwansa Alhaji Sanusi Ado Bayero a matsayin Wamban Kano, kuma Ɗan Majsalisar Sarki. A baya dai, Sanusi Lamido Ado Bayero ne ke riƙe da muƙamin Ciroman Kano, wanda tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II ya sauke saboda ya ƙi yi masa mubaya'a bayan zamansa sarkin Kano. Hakan ta sa Sarki Sanusi ya maye gurbinsa da Nasiru Ado Bayero a matsayin Ciroman Kano, wanda yanzu shi ne Sarkin Bichi. Tuni Sunusi Ado Bayero ya yi mubaya'a ga Sarkin Kano Aminu Ado Bayero, wanda hakan kamar wata sanarwa ce ga sarkin cewa ya dawo gida da zama. Wata sanarwa da Alhaji Sarki Waziri, Ɗan Rimin Kano ya aike wa Sakataren Gwamnatin Kano ta kuma tabbatar da naɗa Aminu Babba Ɗan Agundi a matsayin Sarkin Dawaki Babba, wanda Marigayi Sarki Ado Bayero ya sauke daga muƙamin Sarkin Dawaki Mai Tuta shekara 16 da suka gabata. A shekarar 2003 ne Ado Bayero ya sauke Aminu Babba daga sarautar Sarkin Dawaki Mai Tuta kuma Hakimin Gabasawa sakamakon bijire wa umarnin da ya ba shi na bayyana a gabansa. Marigayi Ado Bayero - mahaifin sarkin Kano na yanzu - ya kuma zargi Aminu Babba da laifin shiga harkokin siyasa da rashin ɗa'a ga Masarautar Kano. Sai dai Kotun Ƙoli ta tabbatar da hukuncin da Masarautar Kano ta ɗauka na tuɓe rawanin Aminu Babba a ranar 5 ga watan Yuni bayan nasarar da ya samu a kotun Jihar Kano da kuma ta Ɗaukaka Ƙara. Ya zuwa yanzu Masarautar Kano ba ta bayyana dalilin dawo da Aminu Babba Ɗan Agundi cikin masarautar ba a matsayin Sarkin Dawaki Babba kuma Ɗan Majalisar Sarki. Sai dai wasu makusantan sarkin da ba su yarda a ambaci sunansu ba sun bayyana wa BBC cewa Sarkin Dawaki Babba sabuwar sarauta ce, wadda sarkin ke da ikon ƙirƙirowa ko arowa daga wata masarauta. Suka ƙara da cewa irin hakan ta taɓa faruwa ga kawun sarkin Kano na yanzu - Aminu Ado Bayero - inda aka ƙirƙiri sarautar Barde Kerariya kuma aka naɗa Alhaji Kabiru Bayero. Har yanzu gwamnatin Kano ba ta ce komai ba kan wasiƙar da masarautar ta Kano ta aike mata bisa buƙatar sarkin ta naɗa mutanen biyu. https://www.bbc.com/hausa/labarai-53394227 +entertainment Rasuwar Sarauniya Elizabeth II: Shekarar faɗi tashi Kawun Elizabeth, Yariman Wales, ya zama sarki a 1936, amma ba shi da ɗa ko ɗaya. Sai Elizabeth wadda ba ta da yayye maza, ta zama ta biyu a kan layin gadon sarauta. Amma kawun nata, ya so ya auri wata bazawara ƴar Amurka, Wallis Simpson duk da ƙin amincewar masarautar Birtaniya. A wannan shekarar ɗan uwansa mahaifin Elizabeth ya zama Sarki George na shida. Sai kuma Elizabeth tana shekara 10 ta zama mai jiran gadon sarautar. https://www.bbc.com/hausa/articles/cmln001dymvo +entertainment Abin da ya sa masana ke ganin mawakan zamani na wulakanta rubutun Hausa "Daga baƙon marubuci, Dr Muhammad Suleiman Abdullahi, malami a Sashen Koyar da Harsunan Najeriya, Jami'ar Bayero, Kano. Waƙa tana ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin isar da saƙwanni da taskace harshe da sanya annashuwa da karsashi ga zukatan masu sauraro, musamman idan aka sami zaƙwaƙuran da suke aiwatar da waƙoƙin ta hanyoyin da suka dace. A ɗaya ɓangaren kuma, rubutu hanya ce ta bayyana tunani da muradun zuciya, ta yadda ko da ma'abocin wannan tunanin ba ya nan, wani zai iya gane wannan tunani har ma ya amfana daga abin da wannan tunani da fasaha suka ƙunsa. A fuska ta nazari, akwai waƙoƙin da aka fi sani da rubutattun waƙoƙi. Su irin waɗannan waƙoƙi sun sha bamban da waƙoƙin baka saboda masu aiwatar da su galibi sai sun rubuta su (to a nan gizo yake saƙa) sannan suke aiwatar da su. Akwai sama da dokoki da ƙa'idoji sama da guda ɗari (100) da suka shafi yadda tsarin rubutun Hausa yake, amma ga alama, waɗanda suke rubuta irin waɗannan waƙoƙi ba su ma san ko da kashi goma cikin waɗannan ɗarin ba. Don haka za ka ga an rubuta wani abu wanda idan mutum bai yi a hankali ba, sai wannan abu ya sabbabawa mai karatu rashin fahimta ko mummunar fahimta ko ma ya lahanta tunani bakiɗaya. Masu rera irin waɗannan waƙoƙi, sukan rubuta su, ko kuma su rubuta sunayen taken waƙoƙin, amma abin mamaki, a sunan da bai wuce kalma biyar ba, sai ka ga an sami kurakurai da yawa. Irin waɗannan waƙoƙi da kuma mummunar hanyar da ake rubuta su, takan yaɗu kamar wutar daji, tare da cewa a kan kuskure rubutun yake, wani lokaci har ma su sake su a shafukan sadarwa, kamar su Yutub ko Fesbuk da su Tuwita da makamantansu. Akwai misalai da dama na irin wannan taƙadarin tsarin rubutu na taken waƙoƙin zamani, waɗanda za a kawo su a nan, tare da bayyana irin kurakuran da suke ƙunshe a cikin wasunsu. Misali a wata waƙa ta Ado Gwanja wadda ta yi suna a tsakanin matasa a 'yan kwanakin nan, wadda ya sa wa suna, kuma aka rubuta sunan waƙar da ""Chass"", duk da cewa taken waƙar kalma ɗaya ne kawai, amma ba a rubuta shi daidai ba. Kalma ɗaya fa! A Daidaitacciyar Hausa ba a amfani da baƙin [ch] wanda yake a Ingilishi a matsayin baƙin [c] na Hausa. Sai dai fa a wasu ɗaiɗaikun wurare da tasirin mulkin mallaka ya yi mana kaka-gida. Don haka dai, kamata ya yi taken wannan waƙa a rubuce ya zama ""Cass"" ba ""Chass""! Sannan abin da ya faru na samuwar ""ss"" a ƙarshen kalmar ""Cass"", wata doka ce da za a iya tattauna ta a ilimin Tsarin Sauti na Hausa. Chass – Ado Gwanja 2022 A wata waƙar kuma ta wani mawaƙin mai suna Umar M Shareef, wadda aka yi wa taken ""Kibani Soyayya"", nan ma akwai gaggan kurakurai da yawa. Misali, a Hausa ba wata kalma ""Kibani"" amma ga shi an yi amfani da ita a nan, kuma wai Hausar ake yi. To amma daga cikin abin da ake faɗa a cikin waƙar, sai muka gano ashe wai so suke su ce ""Ki ba ni"" wanda kuma waɗannan kalmomi ne guda uku masu cin gashin kansu a tsarin Nahawun Hausa. Wakilin Suna ne a farko, sai Aikatau da kuma wani Wakilin Sunan. Ko me ye dalilin da ya da marubucin taken waƙar ya rubuta ""Kibani""? Wannan kuma shi ya sani. Kibani Soyayya - Umar M Shareef 2022 Haka nan, akwai wata waƙar ta shi Umar M Shareef ɗin wadda aka rubutawa taken ""Nafada"", wadda har zuwa yanzu dai ban gano me yake so ya rubuta ba, domin ban saurari waƙar ba. Nafada  - Umar M Shareef 2022 A wata waƙar kuwa ta Lilin Baba da Ummi Rahab wadda aka yi wa taken ""Zanyi Wuff"", a nan ma za a iya cewa ba wata kalma a Hausa da ya dace a rubuta ta da ""Zanyi"". To amma a lokacin rerawa suna faɗar ""Zan yi"" ne, amma a rubuce, sai suka rubuta wani abu daban mara ma'ana. Zanyi Wuff - Lilin Baba Ummi Rahab Ita kuwa wata waƙa ta Hamisu Breaker, wadda aka rubuta takenta da ""Yadda Kunne Yaji"", wato a nan dole masanin ƙa'idar rubutu da sauran ɗaliban harshe, musamman ɗaliban Hausa waɗanda asalinsu ba Hausawa ba ne, su shiga tashin hankali. Domin ba Hausawa ba ne kawai suke karanta irin waɗannan rubuce-rubucen. Abin da zai fara zuwa zuciyar mai karatu shi ne wai shin me ye alaƙar kunne da yaji? Kunne dai wata kafa ce da mutane suke jin magana da ita. Shi kuwa yaji, wani sinadari ne da ake sa wa a abinci domin inganta ɗanɗano. To a nan an haɗa kunne da yaji... Ka ga ai sai tafiya asibiti. To amma daga baya sai muka fahimci ana so a rubuta ""Yadda Kunne Ya Ji"" ne, amma saboda ba a damu da sanin ƙa'idar ba, kawai sai aka rubuta abin da aka ga dama, kuma wannan zai iya zamewa masu koyo babbar matsala. Yadda Kunne Yaji – Hamisu Breaker 2021 Haka ma wata waƙar ta shi Hamisun da aka rubuta takenta da ""Nayi Saa"", wanda duk waɗannan kalmomin guda biyu, babu su a Hausa. Abin da suke so su rubuta, kamar yadda suka faɗa a waƙar, shi ne ""Na Yi Sa'a""! Nayi Saa – Hamisu Breaker ""Sai dake"" ta Hamisu Breaker ma ba daidai ba ce. Daidai ɗin shi ne ""Sai Da Ke"". Sai dake – Hamisu Breaker 2021 Shi ma Ghazali Miko da Rakiya Musa haka suka tafka nasu kuskuren a wajen rubuta taken tasu waƙar, inda suka yi amfani da wata kalma wadda babu ita a harshen Hausa, alhali kuma waƙar Hausa suke yi. Sun rubuta ""Sona Amana"" a maimakon ""So Na Amana"". Sona Amana – Ghazali Miko da Rakiya Musa Waƙar Garzali Miko ta ""Badan dake ba"", ita ma kuskure aka rubuta. Daidai ɗin shi ne a rubuta ""Ba Don Da Ke Ba"". Badan dake ba – Garzali Miko Haka ma waƙarsa ta ""Abun wani sirine"" kamata ya yi a rubuta ""Abin Wani Sirri Ne"". Abun wani sirine – Garzali Miko Auta MG Boy kuwa, kalmomi ne guda huɗu cur, ya haɗe su ya mayar da su guda biyu kacal, kuma ya rubuta hakan abinsa. A maimakon a rubuta ""Ina Ji Da Ke"" wanda shi ne daidai, sai aka rubuta wani gwarantaccen rubutu wai ""Inaji Dake"", wanda wannan ba mutunci ba ne. Inaji Dake – Auta MG Boy 2022 https://youtu.be/B1h5dFJh6yA A wata waƙar ta Sadiq Saleh, wai ita ""Zanayo Shagwaba"", wato a nan rashin daidai ɗin ma har ya yi yawa, domin ba wata kalma da aka rubuta daidai. Kamata ya yi a rubuta ""Za Na Yo Shagwaɓa""! Zanayo Shagwaba (Abin ya motsa remix  – Sadiq Saleh https://youtu.be/_RagGuN0T6M Ita ma waƙar ""Soyayya ce ta Hadamu"" ta Mg Boy, kamata ya yi su rubuta ""Soyayya Ce Ta Haɗa Mu"", ba kamar yadda suka rubuta ba. Soyayya ce ta Hadamu – Auta Mg Boy 2021x https://youtu.be/VT0mXu-8evo Ga wasu sauran waƙoƙin da su ma duk ba a rubuta su daidai ba. ""Ayimini Aure"" ta Auta Mg Boy, kamata ya yi a rubuta ta kamar ""A Yi Mini Aure"". Ayimini Aure – Auta Mg Boy da Rakiya Musa – 2020 https://youtu.be/mbOgGbn4vrg Akwai wasu waƙoƙin da dama da mai karatu ma da kansa idan ya duba, zai tabbatar da cewa lallai waɗannan mawaƙa kawai rubutawa suke yi ba tare da sun bi dokoki da ƙa'idojin rubutun Hausa ba. Duk da cewa a wasu lokutan za su iya cewa ba su suke rubutawa ba, to amma wannan ba hujja ba ce, domin suna tutiyar cewa waƙoƙinsu ne, don haka dole su ɗauki duk abin da ya biyo baya, mai kyau ko akasinsa. Haka kuma, ya kamata in dai mutum so yake ya inganta abin da yake yi, to ba da ka kawai ake yin abubuwa ba, akwai buƙatar a tuntuɓi masana domin su dinga dubawa don ganin an ƙara inganta wannan harshe na Hausa. Ya kamata masu irin waɗannan rubuce-rubuce su sani, akwai masu karanta su da yawa, wasu daga ƙasar Hausa wasu kuma daga sauran sassan duniya. Rashin inganta rubutun yana ba wa masu koyo matuƙar wahala wajen ganewa. Don haka, a ƙarshe, nake shawartar dukkanin marubuta da su dan inda ya kamata a haɗe kalma da kuma inda ya kamata a rabata, da kuma dalilan da suke sa wa a yi hakan. Sannan kuma dole ne a dinga amfani da baƙaƙe masu lanƙwasa, kamar su ""ƙ"" da ""ɓ"" da ""ƙy"" da makamantansu. Sannan kuma a san baƙaƙen da ake amfani da su da na waɗanda ba a amfani da su. Duk waɗannan za su taimaka wajen inganta rubutu a harshen Hausa. Ko za ku iya tantance matsalolin da suke cikin taken waɗannan waƙoƙin da aka kawo a ƙasa?" https://www.bbc.com/hausa/articles/crg3wl9dwyeo +entertainment Aminu Ala: Mawakin ya ce Hukumar fina-finan Kano ba ta da hurumin tace waƙoƙi "Fitaccen mawakin Hausa, Aminu Abubakar, wanda aka fi sani da Aminu Ala ya ce hukumar tace fina-finan jihar Kano ba ta da hurumin tace waƙoƙin yabon Annabi. Aminu Ala ya shaida wa BBC Hausa cewa yin hakan daidai yake da ""matse tunanin"" mawaƙa saboda ""ba a tace fasaha"". A kwanakin baya ne, hukumar tace fina-fanai ta Kano ta ce babu wani sha'iri da zai ƙara fitar da waƙa a jihar, sai ta ba shi lasisi. Shugaban hukumar Isma'il Muhammad Na'abba wanda aka fi sani da Afakallah ne ya bayyana hakan a wata hira da BBC." https://www.bbc.com/hausa/labarai-53828666 +entertainment Irrfan Khan: Tarihin marigayi Irrfan Khan, tauraron fina-finan Indiya "A ranar Talata da yamma 29 ga watan Afrilu ne Allah Ya yi wa fitaccen jarumin fina-finan Bollywood da Hollywood Irrfan Khan rasuwa bayan ya sha fama da cutar daji. Jarumin mai shekara 53 a duniya ya rasu ne a wani asibiti da ke birnin Mumbai a Indiya. Irrfan Khan na daya daga cikin kwararrun 'yan fim a Indiya kuma yana cikin manyan 'yan Bollywood da suka yi fice a fina-finan Hollywood. Shaharraren dan wasan ya fito a fina-finai kusan 80, kuma a lokacin da yake cikin shekarunsa na 30 da 'yan kai, ya kusa barin harkar fina-finai bayan kwashe tsawon shekara 10 yana fitowa a fim amma bai yi fice ba. Irrfan Khan ba shi da kamannin da aka fi so a taurarin fina-finan soyayya na Bollywood, amma ya yi fice a masana'antar da ma wasu fina-finan Hollywood kamar Life of Pi, Slumdog Millionaire da Jurassic World. Khan ya kasance mutum mai zurfin tunani, kuma yana tofa albarkacin bakinsa kan batutuwa masu jawo ce-ce-ku-ce da suka danganci addininsa na Musulunci da masana'antar da ya yi wa aiki. ""Bana son Kalmar Bollywood,"" ya taba shaida wa Jaridar Guardian. ""Wannan masana'antar na da nata salon wanda ba shi da alaka da Hollywood. Ta samo asali ne daga wasannin dandali na Parsi. A gaskiya, taurari kalilan ne za su iya bugun kirji su ce sun kware a masana'antun biyu kamar Irrfan Khan. An rada masa suna Sahabzada Irfan Ali Khan ran 7 ga watan Janairu a shekarar 1967 a kauyen Rajasthan da ke Tonk. Dangin mahaifiyarsa sun fito ne daga gidan sarauta kuma mahaifinsa attajirin dan kasuwa ne mai sayar da taya. Khan ya cire ""Sahabzada"" daga sunansa saboda yana bayyana cewa shi dan babban gida ne - ya yi tunanin wannan zai hana shi cimma burinsa. Ya kuma sauya sunansa da ""Irfan"" zuwa ""Irrfan"" - ba don komai ba - sai don kawai ya fi son yadda sautinsa yake. Da mahaifinsa ya rasu, ya bijire wa burin danginsa na cin gajiyar sana'ar sayar da taya. Ya dage a kan zama dan wasan fim, duk da cewa 'yan uwansa da abokansa ba su da burin haka a kansa. ""Babu wanda ya taba tunanin zan zama dan fim saboda ina da kunya, ga ni siriri. Amma burin da nake da shi ya tauye komai."" A 1984, ya nemi tallafin karatu a Makarantar Koyon wasan kwaikwayo ta kasa da ke Delhi. ""Na yi tunanin zan mutu idan ban samu shiga makarantar ba,"" ya shaida wa wani dan jarida. A wannan makarantar ya hadu da matar da ya aura - marubuciya Sutapa Sikdar. ""Yana da mayar da hankali. Na tuna lokacin da yake dan makaranta idan ya dawo gida kai tsaye zai wuce dakin baccinsa, ya zauna a kasa ya kama karanta littafansa. ""Mu kuwa sauran sai mu zauna mu yi ta hira muna gulmace-gulmace,"" a cewarta. Ya nace zai yi aiki a masana'antar fina-finai amma ayyukan da ya rika samu daga farko-farko a kananan fina-finai ne. Shi kuma ba abin da yake so ba kenan. Tsawon shekara 10, irin wadannan ayyukan ya yi ta yi musamman a tashoshin Zee da Star Plus. Ya yi tunani mai zurfi kan barin harkar fim kwata-kwata. ""Akwai lokacin da aka ki biya na saboda suna ganin ban iya fim ba gaba daya,"" a cewarsa. Ya samu damar fitowa a wani babban fim wanda aka zaba cikin fina-finan da suka yi fice don ba da lambar girma ta Oscar mai suna Salaam Bombay!, amma ransa ya yi mugun baci da aka cire wuraren da ya fito a fim din a lokacin tacewa. Wanda ya rubuta fim din ya tausaya masa amma ya gaya masa cewa ""wani lokaci za ka yi nasara, wani lokaci za ka fadi"". Ya yi fice bayan da ya fito a wani fim din Indiya da Burtaniya mai suna The warrior. An dauki fim din ne a Tsaunukan Himalayas da Hamadar Rajasthan. Shi ne fim din farko da mai ba da umarni dan Burtaniya Asif Kapadia ya shirya. Ba shi da kudin biyan manyan taurarin Bollywood kuma yana neman fasihan 'yan wasa. Irrfan Khan ya fito a matsayin wani gagarumin shugaban yaki. Fim din ya ci lambar yabo ta Alexander Korda na fim din da ya fi kowanne a Bikin Karrama Fina-Finai na Burtaniya, BAFTAS. Nasarar da fim din 'The Warrior' ya samu ya zama silar shigar Irrfan harkar fina-finai ka'in da na'in, kuma shekaru 20 da suka biyo baya, ya tsinci kansa yana fitowa a fina-finai biyar zuwa shida a shekara. Michael Winterbottom ya sa shi a fim dinsa na 'A Mighty Heart' a matsayin dan sanda da kasar Pakistan, kuma ya fito a fim din 'The Darjeeling Limited.' A shekarar 2008, ya hada kai da Danny Boyle suka shirya fim din 'Slumdog Millionaire.' Khan ya fito a matsayin dan sanda da ke yi wa Dev Patel (Jamal) duka - saboda ya yi tunanin macuci ne. Boyle ya bayyana kwarewarsa a matsayin ""gwanin sha'awa"". Bayan nan, Khan ya kai matakin da sai ya zabi irin rawar da yake so ya taka a fina-finai. ""Ina kokarin yin fina-finan da za su yi tasiri mai dorewa, masu ma'ana, wadanda za ka so ka sake kallo bayan ka gansu a karon farko,"" ya shaida wa wani dan jarida. Ya kan ki yarda ya fito a fina-finan da suka danganci addini ko al'ada - ya ki amincewa ya taka rawa a fim din'Deepa Mehta'na Midnight's Children da fim din'Mira Nair' na Reluctant Fundamentalist. Bayan harin 11 ga Satumba da aka kai a New York da Washington, sau biyu 'yan sanda na tsare shi a tashar jirgin sama ta Los Angeles saboda sunansa na kama da na daya daga cikin wadanda ake zargi da kai harin. Ya yi kokarin cire sunan gidansu na Khan - inda ya fi so a rubuta masa Irrfan kawai ko a karshen fina-finan da ya fito. Ya samu rashin jituwa da shugabannin Musulmi bayan da ya soki yin yanka da mabiya mazhabar Shi'a ke yi a watan Muharram. ""Muna yin wadannan abubuwan ba tare da sanin manufarsu ba,"" in ji shi. Sun mayar masa da martani a fusace cewar ya mayar da hankali kan shirin fim kuma ya daina cewa komai kan addini. A 2011, an ba shi lambar girma ta Padma Shri - lambar girma ta hudu mafi girma a Indiya, saboda gudumawar da ya bayar ga bangaren nishadi. Bayan shekara guda, ya fito a fim din Life of Pi. Kuma ya taka rawar kwararren masanin kimiyyar nan Rajit Ratha a fim din'The Amazing Spiderman'da Simon Masrani, attajirin nan mai gandun namun daji a fim din 'Jurassic World.' Ya fito a fina-finan Blackmail da Puzzle na Abhinay Deo. A shekarar 2018, an gano cewar yana da ciwon daji da ya shafi kwayoyin halittarsa da ke fitar da sinadarai a cikin jini. Ya wallafa wani sako a Twitter, yana cewa ""Ba dole ne rayuwa ta ba mu abin da muke sa rai ba."" Ya nemi magani a London kuma ya wallafa wata kasida a shafinsa na Instagram da ke nuna cewa addininsa na taka muhimmiyar rawa a yadda ya karbi labarin cutar tasa. ""Allah na nuna mana alama kamar yadda ya halicce mu, sai ya tafi da mu sannu a hankali daga cikin duhu.""" https://www.bbc.com/hausa/labarai-52423376 +entertainment Daga baƙonmu na mako: Shirin Gidan Badamasi a mahangar nazari Daga bakonmu na wannan makon Auwal G. Danborno Fim din Hausa wani abu ne da tarihin rayuwata ba zai cika ba sai an sanyo shi. Bayan kasancewa ta marubuci, na kasance dan wasan Hausa na dabe. Wannan ta sanya a duk lokacin da nake kallon fim din Hausa, ina kallonsa da fuska biyu. Fuskar farko a matsayina na marubuci. Ina kallon yadda marubucin fim din ke kulla zaren labari da yadda yake hawa da sauka. Fuska ta biyu kuma yadda 'yan wasan ke taka rawa a fim din. Shekaru da dama da suka shude tun ina kallo ina uzuri, har ya zama na fara kiran marubutan ina korafi, daga karshe dai na hakura da kallon fim kwata-kwata. Salon Gidan Badamasi Shi ne wasan Hausar da ya dawo da ruhina daga dogon suman da ya yi. Gidan Badamasi labari ne na wani Alhajin Birni da ya yi yawon duniya, wanda cire hula ya fi masa wahala a kan sauya mata. Ko da yake a gwanancewa da kwarewa ta marubucin bai hasko yawan aure auren da ya yi ba, amma yawan yaransa da kuma dan furucin da 'yan wasan kan furta shi ya nuna yawan auri sakin da ya yi duk da ba a fadi adadi ba. Alhaji Badamasi ya tara kudin da har yanzu a zaren tafiyar labarin ba a san adadinsu ba. Sannan ya tara yara marasa tarbiyyar da fatansu da burinsu shi ne ya rasu domin su mallaki dukiyar da ya tara. Shirin kunshe yake da kwararru kuma gogaggun 'yan wasan da suka hada da Nura Dandolo, Magaji Mijinyawa, Hadiza Gabon Mustapha Naburaska, Sani DanGwari, Umma Shehu, Falalu A. Dorayi, Hadiza Kabara, Tijjani Asase da sauran su. Tarbiyyar da ba su samu ba ya sa suka shiga kulle-kullen yadda za su sami dukiyar mahaifinsu ta kowace hanya. Babu jin kai irin wanda ake samu tsakanin 'Da da Mahaifi ko tausayawar da Soyayya da ake samu Tsakanin Mahaifi da 'Da. Ana tsaka da kulle-kullen yadda za a sami dukiyar Alhaji sai ga wata sabuwar fuska ta Ado Gwanja wanda ya fito da sunan ''Na Allah'' ta bayyana. Na Allah ya fito ne a matsayin Dan sanda wanda ya juya akalar shirin da sabon salon kama karya irin na wasu gurbatattun 'yan sanda. Bayan ma su kallo sun tafi a kan tunanin an sami wanda zai kawo cikas wajen neman yadda za a sami dukiya, sai marubucin ya kara dawo da mu karatun baya. Na Allah shi ma ya bi sahun 'yan uwansa wajen hada kai da su a neman dukiyar. Wani abu da yanzu muka zuba ido wanda ke neman jefa mu wasuwasi shi ne yadda aka fara sansano cewa Na Allah ba Dan sandan Gaskiya ba ne. Tambayoyin da ke zukatanmu yanzu wadanda marubucin ne kadai ya san yadda zai warware su shi ne yadda Na Allah ya sami bindiga ta 'yan sanda a matsayinsa na dan sandan gona. Bayyanar Na Allah ta kara armasa shirin ta yadda marubucin ya sami damar kara jan zaren labarin da kuma sauya akalar tafiyar, maimakon a baya ana abu guda na neman dukiyar kawai. Abubuwan da ya dinga aikatawa kuma wani nuni ne cikin nishadi da hannunka mai sanda kan irin yadda gurbatattun 'yan sanda ke amfani da dama da kuma khaki wajen aikata wani abu wanda bai dace ba a cikin al.'umma. Ko ba komai hakan zai zama wani haske ga masu biye da shirin. Da dama suna kallon shirin Gidan Badamasi a matsayin shiri na nishadantarwa, amma ga dukkan mai hange da nazari ya san fim din kunshe yake da ilimantarwa da fadakarwa da nusarwa bisa mummunar rayuwar rashin zabarwa 'ya'ya uwa tagari da kuma illar rashin tarbiyyantar da 'ya'yan. Duk wanda ya ga tarkacen 'ya'yan Alhaji Badamasi zai tabbatar ba wanda ya sami karatu a cikin su, karatun arabi da boko. Ban da illar yawan aure-auren mataye marasa tarbiyya da kuma illar rashin yi wa 'ya'ya Tarbiyya da ilmi, Marubucin ya nuna yadda illar Maqe kudi da rashin amfani da su ta hanyar da ta dace. Ga dai kudi sun samu amma kasancewar Alhaji bai tarbiyyantar da 'ya'yansa ba, kudaden na neman zamar masa tashin hankali da rashin tabbas. Shirin ya yi tasiri kwarai da gaske a cikin al.'umma ta yadda hatta sunayen 'yan wasan na cikin shirin, mutanen gari sun fara amfani da shi wajen habaici da shagube ga masu irin wadannan halaye. Yadda ake yin shirin cikin mutunci da tsari da barkwanci, ya kama zukatan yara da magidanta. A 'yan shekarun nan babu wani shiri da ya tasirantu cikin jama'a wanda duk wajen da ka shiga maganarsa ake kamar Gidan Badamasi. Na yaba kwarai ga marubucin da yadda yake tafiyar da zaren labarin cikin salon jan hankalin mai kallo da kwarewa. Zaren labarin na tafiya sambal ba tare da gundura ko ginsa ba. Zan yi amfani da wannan dama na sosa wajen da ke min kaikayi. Daya daga cikin abinda ya fara ba fim na Hausa matsala shi ne rashin girmama rubutu daga marubutan fim. Wannan ta sa aka dinga samun fina-finai da suka zama marasa kan gado. Marubuci zai tsara labari cikin baiwa da kwarewar da Allah ya ba shi, amma sai mai shiryawa ko darakta ya cire abinda ya ga dama a duk lokacin da ya so da sunan wai ba shi kasuwar ke so ba. Marubuta ya dace su juya akalar masu kallo ba da baiwarsu, ba wai kasuwa ko mai shirya fim ya juya marubuci daga baiwar da Allah ya yi masa ba. Shirye-shiryen da Arewa 24 ke yi na wasan Hausa ya shiga zukata kuma ya tasirantu a cikin al'umma saboda girmama fasahar marubuci da dama da ake ba marubuta su juya alkalumansu bisa baiwar da Allah ya yi masu. Fatana ga Nazir Adam Salihi a cikin shirin Gidan Badamasi Allah ya ba shi ikon ci gaba da sakar zaren labarin cikin salon nishadantarwa da fadakarwa. Auwal G. Danborno Kano, Marubuci kuma manazarcin Al'amuran yau da kullum. Kuma wannan maƙala ra'ayinsa ne ba na BBC ba. https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-54030155 +entertainment Ƙayatattun hotunan Afrika: Daga 12 zuwa18 ga watan Nuwambar 2021 Wasu daga cikin zaɓaɓɓun hotuna daga Afrika da na ƴan Afrika daga wasu sassan duniya Duka waɗannan hotunan suna da haƙƙin mallaka https://www.bbc.com/hausa/labarai-59344546 +entertainment Abin da ya sa Adam Zango ya yi rijista da hukumar fina-finan Kano "Latsa alamar lasifika da ke hoton sama don sauraron hira da Adam A. Zango: Tauraron fina-finan Kannywood Adam A. Zango ya ce ya yi rijista da hukumar tace fina-finai da dab'i ta jihar Kano ne domin kawo karshen matsalolin da abokan sana'arsa suke fada wa a cikin na rashin amincewa da fina-finansu. Tauraron ya shaida wa Nasidi Adamu Yahaya cewa yin rijistar tasa zai ba shi damar zuwa Kano domin gudanar da sana'arsa ba tare da shamaki ba. A cewarsa, ""Na dawo na yi rijista da censorship board ne saboda dalilai biyu: na farko shi ne, furodusas dina da suke yin fina-finai da ni a jihar Kano a nan suka fi yawa. ''Sannan kuma yarana da nake tare da su da wadanda nake mu'amala da su dukka suna samun matsaloli wajen ba a kiran su ayyuka a dalilin wannan abu da ban yi ba. Wadansu ma sun yi rijista amma ba sa samun aiki saboda suna tare da ni."" Tauraron ya kara da cewa bai kamata son zuciya ya sanya shi ya zama silar hana wasu da ke kusa da shi samun aiki ba. Sai dai ya kara da cewa har yanzu bai koma kungiyar Kannywood ba, yana mai cewa ""ina nan a matsayin dan wasan fina-finai mai zaman kansa da ke Kaduna."" A watan Fabrairu ne hukumar tace fina-finai ta ce dole tauraron ya bi dokokinta idan yana so ya je jihar domin gudanar da harkokin fim. A wancan lokacin Adam A. Zango ya fito a wani bidiyo da tauraruwa Rahama Sadau ta wallafa a Instagram yana yi wa masoyansa Kanawa albishirin cewa zai je jihar domin kallon fim din 'Mati A Zazzau'. Sai dai jim kadan bayan hakan ne wasu kafafen sadarwa na zamani suka ambato shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar, Isma'ila Na'abba Afakallah, yana shan alwashin kama tauraron idan ya sanya kafarsa a jihar. Amma a tattaunawarsa da BBC, Afakallah ya ce ba su hana tauraron shiga jihar ba amma suna da dokoki game da zuwansa. ""Idan zuwa zai yi ya kalli fim kawai ya tafi shikenan, akwai wadanda ba su da rajista kuma suke zuwa su yi kallon su tafi babu ruwanmu da su. ""Kwanakin baya wannan hukumar ta yi kokarin tantancewa da tsafetace masu ruwa da tsaki a wannan harka kamar yadda doka ta ba ta dama."" A watan Agustan 2019 ne Adam A. Zango ya ce ya fita daga kungiyar masu shirya fina-finan Hausa ta Kannywood. Tauraron fim din kuma mawaki ya ce daga yanzu zai fara cin gashin kansa ne, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Instagram. Sai dai bai yi karin haske ba game da abin da yake nufi da fita daga kungiyar, ganin cewa akwai kungiyoyi da dama da suke cikin Kannywood. Amma ya yi zargin cewa ""ana yin shugabancin kama karya da rashin hukunta mai karfi ko arziki saboda kwadayi da son zuciya. Kazalika, a watan Disamba dan wasan ya shaida wa jaridar Aminiya cewa shi fa ya koma jihar Legas da harkokinsa. ""Kamar dalibin ilimi ne da ya kammala karatun sakandare, idan yana so ya ci gaba da karatu sai ya tafi makarantar gaba da sakandare ko ya je jami'a, wannan ita ce manufata. ""Tuni na fara harkokina (a Legas), komai ya kankama. Ina shirin cikin wata shida zuwa shekara ɗaya zan dawo da iyalina gaba ɗaya nan Legas, har da mahaifiyata, cikin yardar Allah."" Karin labarai da za ku so karantawa:" https://www.bbc.com/hausa/labarai-52213173 +entertainment An saki Naziru Sarkin Waka bayan cika sharudan beli "Wata kotun majistre a Kano ta saki Nazir Ahmad Sarkin Waka, bayan ya cika sharudan belin da kotun ta yanka masa. Da yammacin Juma'ar nan ne dai aka cika sharudan da kotun ta sanya masa a jiya Alhamis. Sharudan sun kunshi ajiye N500,000 da samun manyan ma'aikatan gwamnati biyu da mai unguwa da za su tsaya masa, da kuma mika wa kotu fasfo din sa na tafiye-tafiye. Bayanan da BBC ta samu daga wasu na hannun daman Nazirun sun ce an sha matukar wuya kafin cimma wadannan sharuda. A ranar Laraba ne 'yan sandan suka kama Naziru a gidansa da ke Kano, bisa umarnin kotu, wacce ta samu korafi a kan mawakin. Kotun ta sanya ranar 30 ga wannan watan na Satumba domin ci gaba da shari'ar. Ana zargin Nazirun ne da sakin wani kundin wakoki ba tare da hukumar tace fina-finai da dab'i ta jihar Kano ta sahhale masa ba. Kamfanin Saira Movies ne dai ya saki wakokin, abin da ya sa wasu suke ganin cewa kamfanin na Saira ya kamata a tuhuma tunda shi ne ke da hakkin mallakar kundin. A cikin shekarar nan ne Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II ya nada Naziru a matsayin Sarkin Wakar sarkin Kano. Nadin na sa ya zo ne a dai dai lokacin da ake samun rashin jituwa tsakanin Sarkin Kano da gwamnan Kano. Wasu dai na ganin kamun na sa da tuhumar da aka yi masa na da dangantaka da siyasa. To sai dai shugaban hukumar tace fina-finai da dab'i ta Kano Ismail Na Abba Afakallah ya ce babu sisaya a cikin batun, an dauki matakin ne saboda ya saba ka'ida. A baya dai Naziru da wani mawaki Ibrahim Ibrahim sun yi wa gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje wakar yabo ta "" A sha shayi"", lokacin da gwamnan ya rabawa masu sayar da shayi tallafi. Daga baya kuma Nazirun ya koma yi wa bangaren Kwankwasiyya waka, abin da ke nuna sun raba tafiya da bangaren Gandujiyya. A watan Agusta ma hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta kama Sanusi Oscar bisa zargin sakin wata waka da za ta lalata tarbiyya, ba kuma tare da an tantance wakar ba. 'Yan Kannywood da dama dai sun yi Allah wadai da kamun da ake yi wa mutane da ake gani suna da sabanin akidar siyasa da gwamnatin Kano. Sai dai gwamnatin na musanta cewa akwai siyasa a lamarin." https://www.bbc.com/hausa/labarai-49694733 +entertainment Pushpa: Abin da ya sa wakar da aka dinga ambaton maza ta tayar da kura a Indiya "Wata mata da ke rawa da yin wata waƙa wadda ake ganin tana nuna wariya ta jawo ce-ce-ku-ce matuƙa a India. A lokacin da aka saki sabuwar waƙa daga wani kamfanin fim na Telegu a Disamba, a cikin waƙar wadda aka yi ikirarin kawo sauyi ga yadda maza ke kallon mata. An yi waƙar ne a harsuna biyar da suka haɗa da Telugu da Tamil da Kannada da Malayalam da Hindi inda kuma aka yi bidiyo na daƙiƙoƙi 19 na waƙar. Waƙar da aka yi a duka harsunan na ɗauke da saƙo iri ɗaya: Waƙar na bayyana cewa mace ko tsohuwa ce ko matashiya ko doguwa ko kajera ko ta saka doguwar riga ko gajera ba za ta iya kauce wa kallon namiji ba. Sai dai mata da dama ba su ji daɗin hakan ba, suna kallon hakan a matsayin ɓatanci. Wakar ta yi iƙirarin cewa mata na ɗauke hankalin maza matuƙa su kuma mazan ba su iya haƙuri kamar yadda wasu masu sharhi suka bayyana. ""Na duba duka waƙoƙin waɗanda aka yi su da harsuna daban-daban. Akwai wani baiti a ciki wanda ya kwatanta mata da abinci."" in ji Sowmya Rajendran, wadda edita ce ta The News Minute inda take yawan rubuce-rubuce kan fina-finai. ""A harshen Tamil, ana nufin abinci a Telugu kuma ana nufin inabi, a Malayalam kuma ana nufin sukari. Alaƙanta mata da abinci ya ƙara tabbatar da batun da ake yi na maza na kallonsu. Waɗanda suka rinƙa kallon bidiyon waƙar waɗanda akasarinsu maza ne suna son waƙar. Sun yaba wa Samantha Ruth Prabhu, wadda ta yi waƙar kuma tana cikin manyan mawaƙa mata na kudancin ƙasar kan irin rawa da waƙar da ta yi a bidiyon. Har yanzu ba a saki cikakkiyar waƙar ba duk da cewa an fitar da fim ɗin, sai dai a halin yanzu an kalli bidiyon waƙar sama da sau miliyan 100 a Youtube a harshen Telugu kaɗai. Haka kuma taken waƙar na ya shafe kwanaki ana tattauna shi a shafukan sada zumunta. Sai dai abin mamaki, irin wannan waƙar ba ta yawan jawo ce-ce-ku-ce. Akasarin irin waƙoƙin nan na alaƙanta mata da abinci kamar nama ko kuma a nuna a bidiyo, in ji Ms Rajendran. Ta bayar da misali da ɗaya daga cikin waƙoƙin da take kallo a matsayin ɓatanci wadda a ciki akwai Kareena Kapoor Khan inda ta rinƙa alaƙanta kanta da kaza wadda za a iya wankewa da barasa. ""A lokuta da dama, ba mu san komai ba dangane da matar da ke cikin waƙar ba. Babu wani labari a kanta, an nuna ta ne kawai aka ɗauke ta a cikin fim ɗin,"" in ji Ms Rajendran., Irin waɗannan waƙoƙin da daɗewa sun sha jawo ce-ce-ku-ce musamman kan alaƙanta mata da wasu abubuwa - inda suke saka matsatsun kaya da faɗan wasu irin kalamai. Amma irin waɗannan waƙoƙin ana son su musamman a ƙasashe waɗanda masu kallon maza ne. Waƙa mai daɗi a cikin fim a baya na yawan jawo wa fim ɗin farin jini, wanda yake jawo hankalin mutane zuwa wajen kallo da kuma jawo a samu kuɗin shiga da riba mai yawa. A wannan zamani kuma da ake da YouTube da Instagram, waƙoƙin kuma sun fi tafiya. A shekarar 1994, ɗan jarida Arun Katiyar yayi rubutu inda ya ce suna da nasarar da wata waƙa mai ce-ce-ku-ce ta yi a 1993 ya taimaka wajen samar da wata al'ada da ambatar halittar ɗan adam da wani abu wanda mutane suka yi ta rubuta waƙoƙi domin kwatanta ɗan adam da wani abu. Waƙar ita ce choli ke peeche kya hai, wadda aka fassara ta da me ke bayan rigarki? Amasar a cikin waƙar ita ce: Zuciyata. Sai dai a wata fassara ta daban, Madhuri Dixit, wanda shahararren ɗan Bollywood ne a lokacin ya bayyana cewa akwai wata amsa ta daban dangane da waɗannan kalaman. Irin waɗannan kalaman sun jawo ran mutane da dama ya ɓaci, ciki har da ƴan siyasa waɗanda suka ce irin hakan ya tunzura maza cin zarafin mata." https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-59880654 +entertainment Sarauniya Elizabeth II: Abin da ya sa matasan Afirka ke kira ga Turawa su nemi afuwarsu Matasan Afirka sun shaida wa BBC cewa suna bukatar gidan Sarautar Birtaniya ya nemi afuwar su saboda mulkin mallaka da kasar ta yi wa nahiyar. A wani gidan rediyon da ke tsakiyar birnin Johannesburg na Afirka ta kudu, MJ Mojalefa na gabatar da wani shiri game da mutuwar Sarauniya, wanda masu sauraro ke bugo waya domin bayyana ra'ayoyinsu. DJ, mai shekara 22, ya bukaci 'yan uwansa matasa da su tuno da irin ukubar da Birtaniya ta jefa kasashen Afirka ciki har da Afirka ta kudu. “Birtaniya [Sarauniya] ta yi mana mulkin mallaka, ba za mu iya sauya wannan dangantaka ba,” in ji wani wanda ya kira a waya yayin gabatar da shirin. ''Ya kamata mu manta, abin da ya faru, ya riga ya faru,” in ji wani kuma daban. To amma a ganin MJ Mojafela, yana bukatar neman afuwa ne daga Sarki Charles lll. ''Mutane da dama sun ce Sarauniya ba ta nemi afuwarmu ba, to mu yanzu wannan afuwar muke so a zo a nema.” Afirka ta kudu ta zama jamhuriyya a shekarar 1961. Daga nan aka shiga kangin wariyar launin fata na tsawon shekara 13. Wannan batu ya bar mutanen Afirka ta kudu da dama da tunanin yadda za su manta da shi. Yayin da yake magana game da yadda kakarsa ta sha bakar azaba a zamanin wariyar launin fata, Mayongo cewa ya yi abu ne da tabonsa ba zai taba warkewa ba daga zukatanmu. To amma duka sun ce wannan ne lokacin da ya fi dacewa ga sabon Sarkin da ya gina sabuwar dagantaka da nahiyar. De Oliveira, ya ce ''Muna tunanin sabuwar dangantakarmu da sabon Sarkin za ta ba shi damar sauke nauyin da ke kansa, na zuwa nahiyarmu domin mu yi sulhu da shi. Da aka tambaye shi ko ya za a yi wannan sulhu? sai ya ce a dawo mana da ma'adinanmu da aka kwashe mana, ciki har da katon lu'u-lu'un da suka sace mana, wanda a yanzu yana daya daga cikin manyan sarkokin gidan sarautar Birtaniya. Haka kuma masu kiraye-kirayen neman afuwar Afirka na ci gaba da fafutuka a arewacin birnin Nairobi na kasar Kenya. A makon da ya gabata ne dai kasar ta samu sabon shugaban kasa, wanda kuma shi ne shugaban kasa na biyar tun bayan samun 'yancin kai daga Birtaniya a shekarar 1963. Duk da cewa hankulan 'yan kasar ya karkata ga batun sabon shugaban kasar, amma mutuwar Sarauniyar Ingila Elizabeth ll ne ya mamaye kanun labaran manyan jaridun kasar. Lamarin da kuma ya sabunta muhawara game da dangantakar kasar da sabon Sarkin Birtaniya. ''Abin bakin ciki ne mun rasa rai,” in ji Nelson Njau mai shekara 30. Ya ce: “Amma abin da suka yi wa kasashen Afirka na gurbata mana al'adunmu da sace mana dukiyarmu, da al'umarmu, tabbas ya kamata su zo su nemi afuwarmu.” A kusa da shi Sammy Musyoka ne mai shekarar 29, jinjina kansa kawai ya yi yana mai ishara ga amincewa da maganar dan'uwansa, sannan ya ce ''Har yanzu muna jin radadin yadda suka yi mu'amala da mu a matsayin bayi''. A shekarar 2013, gwamnatin Birtaniya ta amince ta biya tsofaffin Kenya har mutum 5,000 , fam miliyan 19.9 a matsayin diyya saboda ukubar da aka ba su lokacin mulkin mallaka. To amma su tsoffin Kenya ba kamar matasan kasar ba, suna matukar nuna damuwarsu ga mutuwar Sarauniyar, saboda har yanzu tana da farin jini a zukatansu. Caroline Murigo, mai shekara 50, ya ce mutuwar Sarauniyar abin bakin ciki ne, saboda ya santa. ''Ba mu ji dadin mutuwarta ba , amma ba yadda muka iya lokacinta ne ya yi, kuma muna yi wa sabon Sarki fatan alkairi, saboda zai amfani kasarmu,” in ji Mary Muthoni, mai shekarar 46. Ta kara da cewa ''Za su taimaka mana mu inganta tattalin arzikinmu, da abubuwan more rayuwa a kasar.” A Najeriya ma wata cocin Angalikan ce ta shirya taron addu'o'in tunawa da Sarauniyar a Abuja babban birnin kasar. Shugaban Cocin Reverend Ali Buba Lamido, ya ce ''Cocin Angalikan ta samo asali ne daga Cocin Ingila, kuma tarihi ya nuna cewa Sarauniya ko Sarki shi ne babban shugaban Cocin, don haka ita ce shugabar Cocinmu.” Wakiliyar BBC da ta halarci taron addu'o'in ta ce mutanen na cikin yanayi na alhini, to amma wasu da dama sun ki halarta, saboda tunawa da suke yi da mulkin mallaka da Sarauniyar ta jagoranta a Afirka. https://www.bbc.com/hausa/articles/c5145el493go +entertainment Taba Kidi Taba Karatu na 16/10/2022 Auwal Ahmad Janyan Da Ahmad Abba Abdullahi ne suka gabatar da shirin a wannan makon. https://www.bbc.com/hausa/articles/c06xxpdv716o +entertainment Matan Indiya da ke alfahari da kasancewarsu 'marasa aure' "A Indiya, ana girmar da ‘ya’ya mata na su zamo matan aure na gari da kuma uwaye sannan abu mafi muhimmanci a rayuwarsu kuma shi ne aure. Sai dai, a yanzu mata da dama na da ra’ayin zama ba tare da aure ba wato zaman gwauranci. A ranar Lahadi, na halarci taron cin abincin rana na mata 24 a wani shagon sayar da abinci na Caribbean da ke kudancin Delhi. Dakin ya cika makil, inda matan ke ta sowa da cacewa. Dukkanin matan mambobi ne wata kungiyar gwagware – kungiya kuma da ke da shafi a dandalin Facebook na matan birni da basu da aure a India. ""Mu daina kiran kan mu da matan da suka rasa mazajen su ko wadanda aka sake ko zawarawa,’’ a cewar Sreemoyee Piu Kundu, wacce ta kirkiro da kungiyar, yayin Magana a wajen taron. ‘Kawai mu yi tinkaho cewa mu wadanda basu da aure ne.’’ Matan sun yi ta tafi da kuma nuna farin ciki. Indiya dai ta ƙasance ƙasa da matan ta ke da burin yin aure, inda har yanzu ake nuna tsangwama ga wadanda basu yi aure ba. A yankunan ƙarkara a Indiya, ana ganin mata gwagware na zama ɗawainiya ga ‘yan uwansu – damarmaki da matan da basu yi aure ba ke da shi ba ta da yawa sannan dubban zawarawa kuma ake kwashe su zuwa garuruwa masu sarki kamar Vrindavan da Varanasi. Miss Kundu da sauran matan da na samu a wajen cin abincin su na daban ne. Yawanci sun fito ne daga gidajen da ke rufin asiri wanda ya hada da malamai da likitoci da lauyoyi da kwararru da ‘yan kasuwa da masu fafutuka da marubuta da kuma ‘yan jarida. Wasu sun rabu da juna yayin da wasu kuma aurensu ya mutu ko zawarawa, inda wasu kuma basu ma taba aure ba. Matan da basu da samari da ke zama cikin biranen da kuma ke da arziki, na ci gaba da jan hankalin mutane – kamar masu aiki a bankuna da masu yin ‘yan kunne da masu kamfanonin kasuwanci har ma da na tafiye-tafiye. Matan da basu da samari na kuma samun karbuwa cikin al’adu – inda fina-finan Bollywood na Queen da Piku wadanda suka nuna matan da basu da samari na iya dogaro da kansu saboda suna da kudi. A watan Oktoba, Kotun Kolin ƙasar ta yanke hukuncin cewa dukkanin mata wanda ya hada da wadanda basu yi aure ba, na da damar zub da ciki, abu kuma da matan da basu da samari suka ce abin a yaba ne domin kotun ta san da zamansu. Sai dai duk da wadannan sauye-sauye, al’ummomi sun ki yin na’am da batun, inda miss Kundu ta ce zama ba tare da yin aure, ba abu ne mai sauki ba har ma ga wadanda ke da arziki, kuma ana yi musu mummunar fahimta a ko yaushe. ''Na fuskanci tsangwama da wulakanci a matsayina na mace mara aure. Lokacin da nake neman hayar gida a Mumbai, mambobin wasu gidaje sun yi mani tambayoyi kamar kina shaye-shaye? Kina yin jima’i?’’ Ta hadu da likitan mata wanda ya kasance kamar makwabci sannan shekaru kadan da suka wuce lokacin da mahaifiyarta ta saka talla a wani shafi a madadinta, ta hadu wani mutum wanda ya tambayeta ‘ko ita cikakkiyar budurwa ce a cikin mintuna 15 na farko’’? ""A gaskiya wannan tambaya ce da ake tambayar matan da basu da aure a ko da yaushe,"" in ji miss Kundu. Sai dai tsangwamar matan da basu da samari ko wadanda basu yi aure ba a Indiya abu ne da bai kamata a yi ba, saboda kidaya da aka yi a 2011, ya nuna cewa ana da matan da basu yi aure ba sama da miliyan 71.4 – alkaluma kuma da suka ɗara yawan al’ummomin Birtaniya ko Faransa. Wannan ya ƙaru da kashi 39 – daga miliyan 51.2 da aka samu a 2001. An jinkirta yin kiɗayar 2021 saboda annobar korona, sai dai miss Kundu ta ce kawo yanzu, ‘yawan mu ya kai miliyan 100’’. Ƙaruwar yawan matan da basu da aure ya faru ne saboda ƙara shekarun masu yin aure a Indiya. Alkaluman sun kuma hada na zawarawa saboda yawanci matan sun fi maza tsawon rayuwa. Sai dai, miss Kundu ta ce tana ganin yawancin matan da basu da aure sune suka zabi haka. ""Na hadu da mata da yawa da suka ce su suka zabi zama ba tare da aure ba, sun ki yarda da batun aure saboda maza sun mamaye ko’ina wanda ba adalci bane ga matan.’’ Mayar da hankali kan matan da basu da aure da Kundu ta yi – ya janyo wa mahaifiyarta wacce ta kasance bazawara a shekaru 29 tsangama. ""A lokacin tashiwa na, na ga yadda aka zamar da wata mata saniyar ware. Duk lokacin da halarci wani biki ko ma na auren ‘yan uwanta, basa ma ko so su ganta, inda ake fada mata cewa kada ta shiga lamuran amarya tun da ko kuruwar bazawara ba abu ne mai kyau ba ga amarya.’’ A lokacin da take shekara 44, lokacin da mahaifiyarta ta sake yin aure, miss Kundu ta zama abin magana cikin al’umma – ‘Me ya sa bazawara ta zama mace mai bakin ciki da shashanci da rashin jin dadi? Ta ce tsangwamar da aka yi wa mahaifiyarta, ya shafeta matuka. ""Na girma da buƙatar ganin na yi aure. Na yi imani cewa aure zai kawo min karbuwa a cikin al’umma da kuma kore mani duhu. Sai dai bayan rabuwa da samarinta har sau biyu wadanda kuma basu kare da da daɗi ba -  da kuma bukatar ganin ta yi aure a shekaru 26, miss Kundu ta ce ta gano cewa auren gargajiya inda ake son mace ta yi wa mijinta biyayya, wannan ba nata bane. Ta ce soyayya da ta yi, bai shafi al’adu ko addini ko ma al’umma ba, amma ta gina shi kan girmama wanda take so da mutuntawa juna. Matan da basu da aure da na hadu da su a wurin cin abincin a ranar Lahadi, dukkansu sun yi na’am da hakan. Sai dai, Indiya ta kasance al’umma da kashi 90 na aure da ake gudanar wa, ‘yan uwa ne ke shiryawa, inda mata basu da ta cewa kan wanda za su aura – balle kuma batun ko suna son aure ko a’a. Amma Bhawana Dahiya, mai shekara 44, da ke da wata kungiya ta bayar da shawarwari kan soyayya kusa da Delhi, wanda kuma bai taɓa aure ba, ya ce abubuwa na sauyawa kuma ƙaruwar matan da basu da aure abin farin ciki ne." https://www.bbc.com/hausa/articles/c4n6448k0yyo +entertainment Wasu ƴan wasan fina-finan da aka sauya ana tsaka da ɗaukar shiri "Batun sauya 'yan fim ana tsaka da nuna fina-finai musamman masu dogon zango ba sabon abu ba ne a harkar fina-finan Amurka wato Hollywood da ma sauran masana'antun fina-finai na duniya. Sau da dama ana samun lokacin da ana tsaka da shiri sai a sauya ɗan wasa ko ƴar wasa, wannan lamari da alama yana ba wasu masu kallo haushi ganin irin ƙorafin da suke yawan yi. Sai dai akasari ba kasafai kawai ake sauya taurarin ba sai da dalili. Dalilan kuwa sun haɗa da mutuwa da aure ko kuma rashin jituwa tsakanin mai shirya fim ɗin da tauraro, a wani lokaci kuma hakanan dan fim zai yi gaba-gaɗi ya fita sakamakon wasu dalilai nasa. Ganin cewa yanzu ne harkar fina-finai ke tasowa a ƙasar Hausa, shi ya sa ake yawan mamaki da kuma kawo sukar fim ko darakta a duk lokacin da aka samu sauyin wani ɗan wasa. Alal misali, a fim mai dogon zango na Game Of Thrones, an sauya taurari da dama ciki har da Callum Wharry wanda shi ne ɗan autan Cersei Lannister inda aka sauya shi da Dean Charles. Haka ma a fim mai dogon zango na ƙasar Turkiyya ɗin nan wato Dirilis Ertugrul, an sauya babban tauraron fim ɗin wato Engin Altan Düzyatan wanda shi ne Ertugrul ɗin inda aka sauya shi da Tamer Yigit. Haka ma a fim ɗin Fast and Furious, an sauya Paul Walker da ƙaninsa a ƙarshen zango na bakwai bayan Paul ɗin ya yi hatsarin mota ya rasu. Salma kwana casa'in Salisu T. Balarabe, daraktan shirin nan mai farin jini na Kwana Casa'in, ya bayyana dalilinsu na sauya tauraruwar da ke taka rawa a matsayin Salma. A wata hira da BBC Hausa, daraktan ya ce ita da kanta ce ta bayyana cewa ba za ta ci gaba da fitowa a shirin ba. A cewarsa: ""A tsarinmu na Kwana Casa'in duk lokacin da za a gabatar da wani zango, akan tuntubi jarumai kafin lokaci cewa an sa lokacin da za a dauki wannan zangon; wadansu sukan fadi cewa ba za su samu yi ba saboda yanayi na karatu ko kuma wani dalili da su suka bar wa kansu sani. Lokacin da muka tuntubi ita Salma a kan cewa za mu dauki shirin Kwana Casa'in Zango na shida ta fada mana cewa gaskiya ba za ta samu dama ba, mun so mu san dalili sai ta fada mana cewa yana da nasaba da iyayenta wanda ba lallai ne ta iya bayyanawa ba.'' Safara'u Kwana Casa'in Ita ma Safiyya Yusuf wadda aka fi sani da Safara'u a shirin Kwana Casa'in na Arewa 24 na daga cikin waɗanda aka sauya ana tsakiyar nuna shirin. An shiga cikin sabon zango kwatsam sai masu kallo suka ga an sauya Safara'u, wanda hakan ya jawo ce-ce-ku-ce a wurin jama'a. Jama'a da dama dai sun alaƙanta cire ta daga fim ɗin kan wani bidiyo na tsiraici wanda ake zargin ita ce a ciki bidiyon. Sai dai bayan BBC ta tuntuɓi Arewa 24, ta shaida mana cewa ta cire Safara'u ne saboda ""wasu dalilai"". Amma a wata hira da jaridar Aminiya ta kamfanin Media Trust a Najeriya, Safiyya Yusuf ta bayyana cewa lokacin da ake cikin ɗaukar shirin ta kwanta rashin lafiya. ""Sun fara aiki, ni kuma ina kwance ba ni da lafiya, don haka ne a lokacin suka ga ba za su iya jirana ba, sai suka ɗauko wata ta ci gaba a matsayina domin a gaskiya a lokacin ba zan iya yin aiki ba domin ba ni da lafiya sosai,"" kamar yadda ta shaida wa Jaridar Aminiya. Furera matar Sallau a shirin Daɗin Kowa Ita ma Ummi Uba wadda aka fi sani da Furera matar Sallau na daga cikin waɗanda aka sauya inda aka maye gurbinta da Amina Muhammad. Tashar Arewa 24 ta tabatar mana da cewa an sauya ta ne sakamakon aure da ta yi. Daraktan shirin Salisu T Balarabe ya bayyana cewa lokacin da za ta yi aure sai suka samu wata da za ta maye gurbinta. Mary a shirin Daɗin Kowa Ita kuma Abigail Samuel wato Mary a shirin Daɗin Kowa ta samu gurbin karatu ne a jami'a wanda hakan ya sa ta koma karatu a Jami'ar Amadu Bello da ke Zaria kuma ba za ta iya samun lokaci ta rinƙa zuwa aikin tana komawa ba. Baban Nazir a shirin Daɗin Kowa Shi kuma baban Abdullahi Ligidi wanda shi ne baban Nazir rashin lokaci ne ya sa aka sauya shi sakamakon yana yawan yin fina-finai na Kannywood. ""Abubuwa sun yi masa yawa ba shi da lokaci shi ya sa muka sauya shi"", in ji Salisu T Balarabe na Arewa 24. Goshi a shirin Daɗin Kowa Ruqayya Goni Usman wadda aka fi sani da Goshi a shirin Daɗin Kowa aure ta yi ana tsaka da shirin. Salisu ya bayyana mana cewa wurin da ta yi auren wuri ne mai nisa kuma ba za ta iya zuwa Kano a ci gaba da aikin da ita ba. Kakar Rayya a shirin Kwana Ita ma kakar Rayya a shirin kwana casa'in tafiya ta yi ta bar Najeriya kuma ta daɗe ba ta dawo ba shi ya sa aka sauya ta." https://www.bbc.com/hausa/labarai-59575820 +entertainment Ta'aziyyar Sarauniya Elizabeth: Tarihin rayuwar Sarauniyar Ingila "Tsawon zamanin mulkin Sarauniya Elizabeth na nuni da karfin halin jajircewar, tare da sadaukar da rayuwa wajen aikin sarauta da tallafa wa rayuwar mutanenta. A wajen mutane da dama ta zama wajen fuskantar matsayarsu a duniyar da ake samu sauyin cikin sauri, a daidai lokacin da tasirin ikon Birtaniya ya yi kasa warwas, al'umma ta samu sauyi fiye da yadda ake iya fahimta, al'umma na jefa alamar tambaya kan kimar matsayin sarauta (ta gargajiya). Nasarar da ta samu wajen riritawa da jan ragamar sarauta a wadannan mawuyatan lokuta, na da matukar ban mamaki, bisa la'akari da cewa a lokacin haihuwarta, babu wanda ya hango cewa za ta kasance mai jan ragama a karagar mulki. An haifi Elizabeth Alexandra Mary Windsor a ranar 21 ga Afirilun 1926, a wani gida da ke gefen dandalin Berkely a Landan,inda ta kasance 'ya ta farko ga Albert, Basarake Duke na York, wanda shi ne da na biyu a wajen Sarki George V da maidakinsa, mai lakabin martabar sarauta ta Duchess, wadda a da sunanta ُ Elizabeth Bowes Lyon. Elizabeth da 'yar uwarta Margaret Rose, wadda aka haifa a shekarar 1930 sun yi karatu a gida, karkashin kulawar zuri'arsu a yanayi mai annashuwa da nuna kauna. Elizabeth ta samu matukar kusanci da mahaifinta da kakanta George V. Tana da shekara 6, Elizabeth ta fada wa mai ba ta horon sukuwar doki, cewa, 'tana da burin zama mace mai kimar matsayin daraja da ta mallaki dawakai da karnuka."" An bayyana cewa ta nuna alamun iya jan ragamar al'umma tun tana karama. Winston Churchill, wanda a zamanin yake hankoron zama Firayiministan kasar, an jiyo daga gare shi, cewa, ""tana da kwarjinin mulki, al'amarin da ke da ban mamaki ga yarinya karama."" An samar da kungiyar 'yan mata masu aikin agaji na ""Girl Guides"" irinta ta farko a fadar Buckinhgham, wadda aka kafa da manufar (Elizabeth) ta saba mu'amala da rukunin 'yan matan da ke matakin shekarunta. Bayan mutuwar George V a shekarar 1936, babban dansa, da aka sani da David, ya zama (Sarki) Edward VII. Sai dai zabar auren matar da aka taba sakinta (ta raba) aure har sau biyu, wato Ba'Amurkiyya Wallis Simpson lamari ne da ba a amince da shi ba, bisa dalilain siyasa da na addini, inda karshen wannan shekarar ya yi murabus. Basarake Duke na York, wanda bai sa a kaba, sai ya zama Sarki George VI. Nadin sarautarsa ya bai wa Elizabeth kafar nuni da al'amarin da ke shirin faruwa da ita, inda daga bisani ta rubuta cewa ta samu aikin hidima (ga al'umma) ""cike da ban mamaki."" Sabanin Karin tashe-tashen hankulan da aka yi fama da su a Turai, sabon Sarki, tare da matarsa Sarauniya Elizabeth, sun yi kokarin dawo da martabar sarauta a idon al'umma. Kwatankwacin kokarinsa bai fadi kasa ba, tare da babbar 'yarsa. A shekarar 1939, Gimbiya 'yar shekara 13 ta raka sarki da sarauniya ziyarar kwalejin horar da jami'an sojan ruwa ta Dartmonth. Ita da 'yar uwarta sun samu rakiyar dan uwanta na nesa, Yarima Philip na kasar Girka (tsohuwar daular Greece). Wannan ba shi ne karon farko na haduwarsu ba, amma shi ne karon farko da ta ji tana kaunarsa. Yarima Philip ya rika kai ziyara ga danginsa 'yan sarauta a duk sa'adda ya samu hutu daga aikin sojan ruwa, ta yadda zuwa shekarar 1944, lokacin Elizabeth na da shekara 18 ta bayyana karara tana sonsa. Ta aje hotonsa a dakinta, kuma sun rika yin musayar wasiku (a tsakaninsu). Wannan matashiyar Gimbiya ta shiga aikin wucin gadi na ATS a karshen yaki, inda ta koyi tuki da gyaran babbar mota. A ranar VE ta hadu da iyalan gidan sarauta a fadar Buckingham lokacin da dubban mutane suka taru don murnar bikin kawo karshen yaki a Turai. Mun nemi izinin iyayena kan ko mun iya fita daga fada mun gane wa idonmu,'"" kamar yadda ta tuna daga bisani."" Na tuna muna jin tsoro a gane mu. Na tuna jerin mutanen da ba mu san su ba, sun hada makamai suna sakowa daga dakin taron Whitehall, daukacinmu duk muna cike da farin ciki da annashuwar samun sa'ida. Bayan kammala yaki burinta na son auren Philip ya hadu da tarnaki daga bangarori da dama. Sarki na dar-dar din rabuwa da 'yarsa, wadda ke da kusanci da shi, kuma lallai sai Philip ya sauya kasarsa ta haihuwa, al'amarin da ya haifar masa da kyara a wajen al'umma. Burin wadannan ma'aurata ya cika, inda a ranar 20 ga Nuwambar 1947 suka yi aure a Westminster Abbey. Basarake Duke na Edinburgh, mukamin da Philip ya samu, ya ci gaba da kasancewa jami'in sojan ruwa. A dan wani takaitaccen lokaci, aka tura shi Malta, lamarin da ya nuna yadda matasan ma'auratan suka dandana dadin rayuwar aure. An haifi dansu na farko, Charles a shekarar 1948, sai 'yar uwarsa Anne da aka haifa a shekarar 1950. Amma da Sarki ya yi fama da laulayin rashin jin dadi a shekarun yaki, har cutarsa ta zama ta ajali, inda ya yi fama da ciwon dajin huhu da ta zama ta ajali, sanadiyyar yawan bankar hayakin taba. A Janairun 1952, Elizabeth, lokacin tana da shekara 25 tare da Philip suka shirya tafiya yawon bude ido kasar waje. Sarkin ya ki bin umarnin likita, inda ya tafi filin jirgin sama don ganin tashin ma'auratan. Wannan dai ya kasance karshen ganin da Elizabeth ta yi wa mahaifinta. Elizabeth ta samu labarin rasuwar mahaifinta Sarki lokacin da suke zaune a wajen shakatawa na kasar Kenya, kuma ba da wani bata lokaci ba ta koma Landan a matsayin sabuwar Sarauniya. Haka ta tuna al'amuran da suka wakana (a wancan zamanin). ""A haka dai, ban samu koyon dabarun gudanar da al'amura (harkokin sarauta). Domin mahaifina ya mutu da sauran karfinsa, al'amari ne da ya auku kwatsam, shi ya sa na kama rikon ragamar tare da yin iya kokarin abin da mutum ke iya yi iya yinsa."" Nadin sarautarta da aka gudanar a Yunin 1953 an nuna shi a talabijin, duk da adawar Firayiminista Winston Churchill, miliyoyin mutane sun taru a gaban talabijin, wadanda mafi yawansu shi ne karon farko da suka ga Sarauniya Elizabeth II ta yi rantsuwar kama ragamar aiki. Birtaniya dai har zuwa lokacin tana fama da matsin tsuke bakin aljihu bayan kammala yaki, kuma masu sharhi sun yi nuni da cewa wannan shi ne sabon babin mulkin Elizabeth. Yakin Duniya na Biyu ya kasance al'amarin da ya hanzarta kawo karshen Daular Birtaniya, kuma a daidai lokacin sabuwar Sarauniya ta yi ziyarar karade kasashen da ke karkashin mulkinta a Nuwambar 1953, wanda mafi yawan kasashen da suka taba kasancewa karkashin mulkin Birtaniya suka samu 'yancin kansu, wato kasashen da suka hada da Indiya. Elizabeth ta zama Basarakiya ta farko da ta ziyarci Austiraliya da New Zealand. An dai kiyasta cewa kimanin uku bisa hudu (3/4) na 'yan Austiraliya sun fito don kallonta. A daukacin shekarun 1950, kasashe da dama sun sauke tutar hadin gwiwa, sannan kasashen da aka taba yi wa mulkin mallaka sun shiga kungiyar sa-kai ta hadin gwiwar kasashen. 'Yan siyasa da dama sun rika ganin kungiyar kasashen ta commonwealth na iya zama tarnaki ga sabuwar kungiyar hadin gwiwar bunkasa tattalin arzikin Turai, kuma ta wani bangaren a iya cewa an yi watsi da tsare-tsaren Birtaniya a nahiyar. Faduwar tasirin karfin ikon Birtaniya ya zuzuta wutar ricikin mashigin rowan suez a shekarar1956, lokacin da ta bayyana karara kungiyar kasashen rainon Birtaniya sun kasa yin katabus wajen hadin gwiwar daukar matakin da ya dace a lokacin rikici. Shirin da aka yi na tura sojoji su shawo kan kasar Masar ya kasance barazana wajen mayar da mashigin ruwan Suez Canal mallakar kasa , inda aka karke da nade tabarmar kunyar janyewa (daga farmakin), al'amarin da ya haifar da murabus din Firayiminista Anthony Eden. Lamarin ya jefa Sarauniya cikin rikicin siyasa. Jam'iyyar Conservative ba ta da tsarin zabar sabon shugaba, sai dai bayan an yi ta tuntubar shawarwarin daidait a al'amura, sai Sarauniya ta gayyato Harold Mcmillan don ya kafa sabuwar gwamnati. A nan ne Lord Altrincham ya yi ta sukar lamirin Sarauniya da cin zarafinta. A wata makala da ya rubuta a wata mujalla, ya yi ikirarin cewa fadarta ""makurar Birtaniyanci"" da ""manya a cikin al'umma"" sannan ya zargeta da nuna gazawar yin jawabi cikin sauki ba tare da rubutaciyar takarda ba. Kalamansa sun tayar da kura a kafafen yada labarai, har ta kai ga an kai wa Lord Altrincham hari, inda magoya bayan Daular sarauta suka tare shi a kan titi. Duk da haka dai lamarin da ya faru ya nuna yadda al'ummar Birtaniya suka dauki sarauta, amma an samu sauyi cikin sauri, ta yadda rashin tabbacin da aka dade a kai ya zama abin jefa alamar tambaya. Bisa kwarin gwiwar da ta samu daga mijinta, sai ta kasa hakuri da ra'ayin rikau na fadarta, don haka Sarauniya ta fara daukar sabon salon tafiya a doron zamani. An kawar da al'adar kawar karramawa ga mace mai daraja a fada, sannan aka shafe sunan 'martabar sarauta,' inda aka maye makwafinta da 'iyalan gidan sarauta."" Sarauniya ta sake shiga tsaka mai wuya a rudanin rikicin siyasa a shekarar 1963, inda Harold Macmillan ya sauka daga mukamin Firayiminista. Saboda bukatar da ake da ita na ganin jam'iyyar Conservative ta fito da tsarin zaben sabon shugaba, sai ta amince da shawararsa ta nada Earl of Home a madadinsa. Sarauniya ta shiga mawuyacin hali, inda daukacin mulkinta ya ta'allaka wajen gyara tsarin mulki, har ta kai ga an tsame hannun sarautar (kasar) daga harkokin gwamnatin lokacin. Sarauniya ta rike matsayinta da gaske wajen saurare (na halin da ake ciki), ta bayar da shawara, tare da yin gargadi - baya ga haka, ba ta yarda ta ketara iyaka ba. Wannan shi ne karo na karshe da aka taba jefata cikin irin wannan hali. Karshe dai Jam'iyyar Conservative ta watsar da al'adar cewa sabon shugaban jam'iyya ""fitowa kawai"" yake yi, inda aka fito da managarcin tsarin da ake amfani da shi. Zuwa karshen shekarun 1960, Fadar Buckingham ta cimma matsayar fitar da managarcin tsarin da ake bukata don nuna yadda iyalan gidan sarauta ke tafiya da salon zamani, kuma cikin sauki za a iya hulda da su. Sakamakon hakan ya bayyana a fim din kundin bayanai mai taken Iyalan gidan sarauta.' An bai wa BBC damar yin fim din gidan zuri'ar Windsors. Akwai hotunan iyalan wajen cin abincin alfama (da mutum ke zabar abin da yake son ci), tare da kwalliyar bishiyar Kirsimeti, inda suke tuka 'ya'yansu a mota - kusan dai daukacin harkokinsu, wadanda a da ba a taba gani ba. 'Yan adawa sun ce fim din Rchard Cawsto ya balbalta sirrin zuri'ar gidan sarauta, ta hanyar nuna su a matsayin gama-garin mutane, al'amarin da ya hada da nuna Duke na Edingburgh yana dibar romon miya a wajen cin abincin alfarma a kasan farfajiyar Balmoral. Sai dai fim din ya nuna saukin kai a wadannan lokuta, sannan ya kara musu dimbin magoya bayan sarauta. Zuwa shekarar 1977 an yi bikin cikarta shekara 25 bisa karagar mulki, inda aka shirya dafdala a tituna, tare da bukukuwa a daukacin fadin masarautar. Sarauta ta samu karbuwa da kariya daga al'umma, kuma mafi yawan al'amuran an yi su ne saboda Sarauniya. Shekaru biyu daga bisani Birtaniya ta samar da Firayiminista mace ta farko. Dangantaka tsakanin Shugabar kasa mace da shugaba macen da ke jan ragamar gwamnati, a wasu lokutan lamarin kan rincabe. Daya daga mafi wuyar al'amura ga Sarauniya shi ne dukufarta wajen kula da kasashe rainon Ingila, inda aka kaddarata a matsayin shugaba. Elizabeth ta san shugabannin Afirka da kyau, sannan tana tausaya wa fafutikarsu. An ruwaito cewa ta dauki halin Thatcher na tunkrar gaba-da-gaba a matsayin al'amari mai ""daure kai"" baya ma ga kin amincewa Firayiministar wajen kakaba wa Gwamnatin wariyar launin fata ta Afirka ta Kudu takunkumi. Daga shekara zuwa shekara Sarauniya ta ci gaba da hidimta wa al'umma. Bayan yakin tekun Pasha a shekarar 1991, ta ziyarci Amurka, a inda ta kasance Mai-sarautar Birtaniya ta farko da ta yi jawabi ga taron majalisar kasa. Shugaban kasa George HW Bush cewa ya yi, ita 'ma'abociyar son 'yanci ce a tsawon lokacin da za mu iya tunawa.' Sai dai wata shekara daga bisani, an samu dimbin abin kunya da musifu da suka fara bibiyar iyalan gidan sarauta. Dan Sarauniya na biyu, Basarake Duke na York ya rabu da matarsa Sarah, yayin da auren Gimbiya Anne da Mark Philips ya karke da saki. Sannan Yarima da Gimbiyar Wales an bayyana yadda suka rika zaman raba gari, har ta kai ga sun rabu. A shekarar dai an yi mummunar gobara a gidan alfarma na Sarauniya, wato 'Windsor castle'. Ta bayyana karara cewa gidan sarauta na cikin matsala. Ga tsangwamar hayagagar al'umma kan ko kudin harajinsu za a dauka ko Sarauniya za ta biya kudin gyaran (gidan). Sarauniya ta kwatanta shekarar 1992 a matsayin ""shekarar firgici"" kuma wani jawabin da ta gabatar a birnin Landan, ta yi nuni da amincewa da tsarin sarauta da zai baje al'amura a bayyane, ta yadda za a shawo kan muzantawar kafafen yada labarai. ""Babu wata hukuma ko birni ko sarauta, kowace iri ce da za ta ki amincewa a bibiyi kadin al'amuranta daga wadanda ke martabata da goyon bayanta, baya ma ga wadanda suka barranta da ita. ""Amma dai mu ma wani bangare ne na al'ummar kasa, don haka za a iya bibiyar kadin al'amura yadda ya kamata, matukar akwai girmamawa da fahimta."" Masarauta tana da kariya.Fadar Buckingham dai a bude take ga masu kawo ziyara. Dangane da tara kudin da za a biya don gyaran Windsor, shi ya sa aka bayyana cewa Sarauniya da Yariman Wales za su biya kudin gyaran Windsor, kuma an bayyana cewa Sarauniya da Yariman Wales za su biya haraji daga kudin shigar da aka samu daga jarin da aka zuba. A waje dai tana da kwarin gwiwa ga kasashen rainon Ingila don ta yi matukar ba su muhimmanci a farkon mulkinta, ba ta samu cimma burinta ba. Birtaniya ta juya wa tsofafin abokan hadin gwiwarta, wadanda suka kulla sabuwar yarjejeniya a Turai. Har yanzu Sarauniya na bai wa kungiyar kasasen rainon Ingila muhimmanci, kuma ta nuna matukar farin cikinta lokacin da Afirka ta Kudu ta yi watsi da tsarin nuna wariyar launin fata. Ta yi murnar faruwar lamarin ta hanyar kai ziyara cikin watan Maris din 1995. A gida kuwa, Sarauniya ta yi kokarin kare martabar sarauta,yayin da al'umma ke ci gaba da takaddama kan makomar wannan hukuma. Yayin da Birtaniya ke fafutikar samun sabuwar makoma, ta yi matukar dogewa a matsayin jigon al'umma mai bayar da tabbaci, inda kwatsam sai ta yi murmushi don samar da yanayi mai annashuwa. Babbar gudunmuwar da ta bai wa al'umma shi ne kasancewarta tambarin kimar kasa. Sai dai sarauta ta girgiza, kuma Sarauniya ta yi fama da suka bayan mutuwar Diana, Gimbiyar Wales, a wani hadarin mota a Paris cikin Agustan 1997. Yayin da cincirindon mutane suka kewaye fadojin Landan suna ta'aziyya da furannin kallo, Sarauniya ta yi biris sabanin yadda takan kasance mafuskantar al'umma a lokacin da kasa ta shiga mawuyacin hali. Mafi yawan masu sukarta sun kasa fahimtar cewa ta keto wani zamani da bai cika nuna damuwa a lokacn rudanin jimamin zaman makokin mutuwa, a irin al'amarin da ya jibinci abin da ya faru bayan mutuwar gimbiya. Sannan ta kasance kaka mai nuna kulawa ga jikokinta, 'ya'yan Diana da ke bukatar tausasawa a kebance karkashin kulawar iyalan. Kwatsam sai ta gabatar da jawabi kaitsaye, inda ta yi ta'aziyar surukarta, tare da ta nuna jajircewar masarautar na juriyar rashi. Rasuwar mahaifiyar Sarauniya da Gimbiya Margaret, daidai lokacin da Sarauniya ta cika shekara 50 a karagar mulki, a shekarar 2002, ya haifar da takaici a fadin kasar kan bukukuwan murnar tsawon shekarun mulkinta. Amma duk da haka, tare da yawan kai-kawon takaddamar makomar sarauta, miliyoyin mutane a katafaren shagon da ke gaban fadar Buckingham a yammacin ranar bikin cikarta shekara 50 a karaga. A Afirilun 2006, dubban magoya baya sun jeru a titin Windsor don murnar zagayowar haihuwar Sarauniya shekara 80. Kuma a Nuwambar 2007, ita da Yarima Philip sun yi bikin zagayowar ranar aurensu shekara 60, tare da aikin ibadar da mutane 2,000 suka halarta a dakin taron Westminster Abbey. Sannan an samu wani yanayin farin ciki a Afrilun 2011 lokacin da Sarauniya ta halarci bikin auren jikanta, William, Duke na Cambridge, inda ya auri Catherine Middleton. A Mayun wannan shekarar ta zamo mai sarautar Birtaniya ta farko da ta kai ziyarar aiki Jamhuriyar Ireland, al'amarin da ya kasance mai matukar muhimmanci a tarihi. A jawabinta, ta fara cikin harshen Irish, inda ta yi kira kan hakuri da masalahar warware matsalar rikici (ai sasanci), har ta yi nuni da cewa ""al'amuran da muke fatansu sukan kasance sabanin yadda ake zato, ko ma su ki faruwa kwata-kwata."" Wata shekara daga bisani a ziyarar da ta kai Arewacin Ireland, a wani yanki na bikin cikarta shekara 60 a karaga, ta yi musafiha hannu da hannu da tsohon kwamandan 'yan tawayen IRA Martin McGuiness. Lamarin na da ban takaici ga mai sarauta, wadda bom din 'yan tawayen IRA ya kashe mata dan uwa, Louis Mountbatten a shekarar 1979. Bikin cikarta shekara 60 a karaga ya tattaro dubban mutane, wadanda suka yi dandazo a kan tituna, al'amarin da ya haifar aka yi ta yaukaka bukukuwa a hutun karshen mako a Landan. Kada kuri'ar raba gardama kan 'yancin Scotland cikin Satumbar 2014, wata jarrabawa ce a zamanin Sarauniya. Mutane kadan ne suka manta da jawabin da ta gabatar wa majalisa a shekarar 1977, inda ta bayyana karara irin jajicewarta kan tabbatar da dunkulalliyar kasar Birtaniya. ""Ni da dimbin sarakuna da sarauniyoyin Ingila da Scotlnd da Yarima-Yarima na Wales a jerin kakanina, ina da kwarin gwiwar fahimtar kan irin wadannan burace-buracen. Amma ba zan iya mantawa da cewa na kasance sarauniyar da ta mulki Hadadiyar Masarauta (UK) Birtaniya da Northern Ireland."" Cikin kalaman da ta yi wa magoya baya a Balmoral a daidai lokacin kada kuri'ar raba gardama kan 'yancin Scotland, wadda kawai aka yi da manufar son a ji, ta ce ta yi fatan mutane za su yi tunani mai kyau da takatsantsan kan makomarsu. Lokacin da sakamon zaben ya fito, abin da ta fada a bainar jama'a, ya nuna gamsuwarta da samun natsuwarta kan cewa tarayyar na nan daram, kodayake an fahimci sauyin yanayin harkokin siyasa. ""Yanzu, yadda za mu ci gaba, shi ne mu tuna cewa duk da dimbin ra'ayoyin da aka baje, abin da muka yadda da shi, shi ne kaunarmu tabbatacciya ga kasar Scotland, al'amarin da ya kasance daya daga al'amuran da suka tabbatar da hadin kanmu. ""Ranar 9 ga Satumbar2015 ta zamo mai sarautar da tsawon shekarun mulkinta ya zarta na kowa a tarihin Birtaniya, inda ta dara kakar-kakarta Sarauniya Victoria. A wani irin salo, taki jinjina matsayin, wato da cewar matsayin ""ba shi ne abin da na damfaru da burinsa ba."" Kasa da shekara guda, cikin Afirilun 2016 ta yi bikin cika shekara 90 da haihuwa. Ko da yake akwai yiwuwar sarauta ba za ta yi martaba da kimar daraja a karshen mulkin Sarauniya ba kamar yadda ta faro, don haka ta jajirce wajen ganin ta cusa kauna da girmamawa a zukatan 'yan Birtaniya. A lokacin bikin cikarta shekara 25 a karaga, ta tuno alkawarin da ta yi lokacin da ta kai ziyara Afirka ta Kudu shekaru 30 a baya. ""Lokacin ina da shekaru 21 na yi alkawari a rayuwata ta yin hidima ga mutanenmu, na kuma roki Ubangiji ya taimake ni in cika wannan alkawari da na dauka lokacin ina matashiya, inda nike yanke hukunci kaitsaye, ba na yin nadama ko janye abin da na nufa ko da kalma guda.""" https://www.bbc.com/hausa/labarai-45012129 +entertainment Cikinmu ya duri ruwa don tsoron rushewar Kannywood - Falalu Dorayi "Latsa lasifikar da ke sama don sauraron hirar: Masana'antar fina-finan Hausa ta Kannywood a Najeriya na fuskantar barazanar durkushewa kamar yadda masu sharhi kan al'amura suke cewa. Masana'antar dai na fuskantar matsaloli da suka hada da satar fasaha da rashin zuba jari daga masu wadata da kuma rashin kulawar gwamnati, duk kuwa da cewa ta shafe gomman shekaru da kafuwa. Falalu Dorayi wanda babban mai bayar da umarni ne kuma ya kan fito a matsayin tauraro a wasu fina-finan, ya shaida wa BBC cewa wannan hasashe na masu sharhi gaskiya ne. Ya ce a yanzu halin da masana'antar ke ciki ya haifar da karayar arziki da durkushewar jari da kuma rufe wasu kamfanonin shirya fina-finai masu girma. Jarumin ya kara da cewa tun farkon kafa masana'antar sun dogara ne a kan sayar da fina-finansu ta hanyar CD, ""amma da yake yanzu an samu ci gaban fasaha sosai mutane kusan sun daina kallon fim a CD sai a wayoyin hannunsu da sauran sabbin hanyoyi,"" in ji shi. ""Idan a da kana yin kwafi na CD 100,000 to yanzu da wahala ka iya yin 5,000 kuma ko ka yi ba za su sayu duka ba. Don kana zaune wani zai sauke fim din (dowloading) daga manhaja ya aike wa mutum 100 a lokaci daya. ""Sannan kuma ko sinima ka kai fim dinka da wahala ka samu riba don kuwa babu sinima din da yawa a arewacin Najeriya kamar kudanci,"" a cewar Falalu. Duk da cewa dai yanzu a duniya an yi ci gaban da dora bidiyo a shafin YouTube kadai na sa wadansu samun makudan kudade da shafin ke biyansu, har yanzu a masana'antar Kannywood ba a fara cin gajiyar abin sosai ba. ""Ai ko ka dora a Youtube din ba za ka samu irin kudin da zai samar maka riba ba, don wata tashar taka ta Youtube ma idan ba ka da masu kallonta da yawa ai ba wani talla da za ka samu balle har kudi su shigo. ""A takaice dai Youtube ba zai sa mu mayar da kudi har mu ci riba ba,"" in ji daraktan. Karin labaran da za ku so ku karanta Falalu na ganin idan dai ba a tashi tsaye ba to lallai wannan na iya zamowa silar rushewar wannan masana'anta da dubban mutane ke cin abinci a cikinta. ""Sai dai kawai yawan mutanen da ke cikinta da yawan fadada tunani da ake yi to zai iya taimakawa a farfado da ita. ""Gaskiya akwai faduwar gaba don kuwa inda abincinka yake a ce yau yana tangal-tangal ai dole ciki ya duri ruwa. ""Fatanmu yanzu gwamnati ta shigo cikin lamarin, sannan masu kudi su zo su zuba jari su bude sinimu da yawa a yankinmu. Don kuwa masu harkar sinima sun ma fi masu shirya fina-finan samun kudi,"" kamar yadda daraktan ya ce." https://www.bbc.com/hausa/labarai-50300213 +entertainment ...Daga Bakin Mai Ita tare da Excellency na Labarina Ku latsa hoton sama domin kallon bidiyon: Daga Bakin Mai Ita wani shiri ne na BBC Hausa da ke kawo muku hira da fitattun mutane kan wasu abubuwan da suka shafi rayuwarsu zalla. A wannan kashi na 66, shirin ya tattauna da Abdullah Amdaz da aka fi sani da Excellency a shirin Labarina. A wannan shiri ya amsa tambayoyin da suka shafi rayuwarsa. Ɗaukar bidiyo: Abdussalam Usman Tacewa: Yusuf Ibrahim Yakasai Gabatarwa: Buhari Fagge https://www.bbc.com/hausa/media-58574375 +entertainment Ashiru Nagoma: Mene ne ke damun tsohon darakta a Kannywood? "Tun bayan da hotunan wani tsohon darakta a masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood Ashiru Nagoma suka bayyana da ke nuna shi cikin hali na fitar hayyaci, maganganu suka fara yaɗuwa a tsakanin al'umma kan ainihin abin da ke damunsa. Rahotanni dai sun ce Ashiru Nagoma ya daɗe a cikin yanayi mai kama da matsalar ƙwaƙwalwa, inda a wasu lokutan har za a gan shi tamkar ""ba ya cikin hankalinsa."" Sai dai a ranar Alhamis ne Fauziyya D Sulaiman da ke da cibiyar taimaka wa marasa lafiya ta Creative Helping Needy Foundation CHNF, ta nemi izinin ƴan uwansa inda ta ɗauke shi zuwa asibiti don kula da shi. Hajiya Fauziyya ta ce kafin sannan sai da ta fara tuntubar ƴan Kannywood a wani zaurensu na Whatsapp don jin ko sun yi wata hoɓɓasa ta taimaka wa Nagoma tun da ya shiga wannan matsala shekaru da dama da suka gabata. ""Sai suka ce min tun lokacin da suka ga halin da yake ciki sun yi ƙoƙarin taimaka masa don kai shi asibiti amma mahaifiyarsa ta hana, ta ce Allah Ya isa duk wanda ya kai shi asibitin masu matsalar ƙwaƙwalwa. ""Da suka ga abu ya so ya zama rigima sai suka bar batun,"" a cewar Fauziyya. Tuni dai ƙarƙashin ƙungiyar tata ta CHNF, Fauziyya D Sulaiman ta kai Nagoma asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano AKTH, ɓangaren masu matsalar ƙwaƙwalwa. Ta ce: ""A gida muka same shi amma fa sai da aka haɗa da dabara sannan ya yarda aka tafi da shi, ƴan sanda aka je da su aka ce an zo kama shi ya yi laifi, don shi bai taɓa yarda yana da matsalar ƙwaƙwalwa ba. ""A hakan ma ya yi ta maganganu yana cewa laifin me ya yi, a haka dai a muka lallaɓa aka kai shi,"" in ji Fauziyya. Fauziyya ta shaida wa BBC cewa yanayin da Nagoma yake ciki da gani lamari ne na tsananin damuwa da ake kira depression. Sai dai duk da haka ta ce yana hira sosai har da amfani da waya, duk da cewa da an fara hirar za a ji ya saki layi. Kazalika duk da yanayin da yake ciki Nagoma bai daina alaƙanta kansa da ƴan Kannywood ba don kusan ko yaushe yana zuwa matattararsu da ke Gidan Ɗan Asabe a Zoo Road da ke Kano. ""Ya kan je su ba shi ɗan abin ɓatarwa har su kan sa shi a talla ma. Wani lokaci ya dinga ce musu 'don Allah ku ba ni naira 100,000 zan yi fim,' in ji Fauziyya kamar yadda wasu ƴan Kannywood ɗin suka shaida mata. Ashiru Nagoma fitaccen mai bayar da umarni ne a masana'antar Kannywood. A shekarun baya ya yi tashe sosai wajen shirya manyan fina-finai kamar su Tutar So da Zakka da Bajinta da Ƙwalele da Tagwayen Mata da sauran su. Wani fitaccen mawaƙin fina-finai a Kannywood Abubakar Sani ya shaida wa BBC cewa Ashiru Nagoma mutum ne da ya yi ƙoƙarin haɗa kan jaruman Kannywood sosai a baya da kuma jan kowa a jiki wajen saka su a dukkan fina-finansa. ""Ya yi ƙoƙari wajen haɗa kan jaruman Kannywood ta wajen saka da dama a duk fim ɗin da zai yi. Haka kuma yana ƙoƙari wajen saka waƙokin mawaƙa da dama na lokacin. ""Ya raya al'ada da bunƙasa harshen Hausa a fina-finansa. Sannan ya ringa yin fina-finai a kan matsalolin zamantakewa,"" in ji Abubakar Sani. Mawaƙin ya ce da suka ga halin da yake ciki sun saurara ne don su ga me waɗanda suka fi kusanci da shi za su yi, don kar a ce sun yi azarɓaɓi, ""amma yanzu an zo daidai kan gaɓar da za mu sa hannu a lamarin,"" in ji shi. Shi ma fitaccen Darakta Falalu Ɗorayi da muka tuntuɓe shi ya ce a lokacin da yake kan shahararsa, Nagoma ya fi kowa yawan bayar da aiki a Kannywood. ""Za a iya cewa a lokacin Kannywood kamar One Man Industry ce, ya kan iya haɗa dukkan jaruman Kannywood a fim ɗaya kamar irin su Tutar So da Nagoma. ""Kuma mutum ne da ya taimaka wajen bunƙasa kalmomin Hausa a cikin fina-finansa sosai,"" in ji Falalu. Jarumin kuma babban daraktan ya ƙara da cewa ""Na yi imani da abu ɗaya, kowane abu ya kan yi lokaci da tashensa sannan ya shuɗe, Allah ne kaɗai Dauwamamme. Don haka kowa ma lokacin shahararsa za ta zo ta wuce. ""Masu ganin su ma lokacinsu ne yanzu, to zai shuɗe,"" in ji Falalu. Shi kuwa fitaccen darakta Aminu Saira cewa ya yi tabbas Ashiru Nagoma babban jarumi ne ba na yasarwa ba da ya jima yana jan zarensa. ""Ba mu yi zamani da shi ba a Kannywood, domin yana gaba da mu, amma dai mun ga irin ayyukan da ya yi,"" in ji Saira. Fauziyya D Sulaiman ta cewa BBC ƴan uwan Nagoma sun ce mata abin ya samo asali ne tun shekarar 2007 lokacin da bidiyon Maryam Hiyana ya yaɗu. ""To a cewarsu a lokacin ya saka kuɗaɗensa ya yi fina-finai wajen bakwai, sai lamarin ya faru inda hukumar tace fina-finai ta ce kar a sake sakin fim ɗin da Maryam Hiyana ta fito a ciki. ""A lokacin ne fa ya shiga ruɗani don rashin madafa ganin cewa ya narka kuɗi ya yi fina-finai da ita, amma dole zai yi asararsu tun ba su fita kasuwa ya mayar da kuɗ ba balle cin riba. ""Lamarin dai ya dagule masa ga asara da ya tafka wacce dole ta sa ya janye daga masana'antar, a hankali damuwar ta dinga tsananta har ta taɓa masa lafiyar ƙwaƙwalwarsa,"" in ji Fauziyya. Ashiru Nagoma dai ɗan asalin jihar Kano ne kuma bai taɓa aure ba, An samu damar kai Ashiru asibiti ne a yanzu tun da babu ran mahaifiyarsa da ta ƙi yarda a kai shi. Ta rasu shekara bakwai da suka gabata, ""amma rashin lafiyar tasa ta tsananta ne shekara biyu da suka wuce,"" in ji Fauziyyya Sulaiman." https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-55666802 +entertainment 'Yan Kannywood na murna kan sinimar da El-Rufai zai gina musu "Masu ruwa da tsaki a masana'antar Kannywood sun cika da murna sakamakon matakin da gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya dauka na ba su fili da kuma kudin da za su aza ginin sinima a jihar. Gwamnan ya ba su fili mai fadin murabba'i dubu 8000 domin gina babbar sinima ta zamani, da kuma gudunmawar kudin na fara aza harsashi, a cewar wani fitaccen tauraro kuma furodusa na Kannywood, Malam Falalu Dorayi. A cewarsa, masu ruwa da tsaki na Kannywood karkasin wata kungiya da ake kira Movie Hope ne suka nemi gwamna ya ba su filin da za su gina katafariyar sinima wadda a cikinta za a iya daukar fina-finai sannan a nuna su. ""Da ma an dade da kai masa kuka cewa akwai bukatar a samu fili a Kaduna wanda za a gina sinima, kamar yadda aka bukaci wasu gwamnoni su ma su yi a jihohinsu. Ginin zai kunshi sinima da wurin koyon sana'o'i da wurin yin daukar muryar mawaka da kuma sutudiyo, da wuraren cin abinci da wuraren shakatawa,"" in ji Falalu Dorayi. Ya ce a makon nan ne kungiyar tasu ta samu jagorancin Musa Halilu (Dujiman Adamawa) inda suka ziyarci Gwamna El-Rufai wanda ya cika musu alkawarin ba su fili da kuma wani bangare na kudin gina sinimar. Fitattun taurari maza da mata - na da da na yanzu - ne suka je yi wa gwamnan na Kaduna godiya. Cikinsu akwai Ibrahim Mandawari, Saratu Gidado(Daso), Hadizan Saima, Rabi'u Rikadawa, Maryam Yahaya, Musa Mai Sana'a, Bello Muhammad Bello, da dai sauransu. Masu ruwa da tsaki a masana'antar Kannywood sun dade suna kishirwar wuraren da za su rika shirya fina-finai da kuma sinimomin da za a rika nuna su. A shekarar 2016 ne gwamnatin tarayyar kasar ta so gina katafaren dandalin yin fim a jihar Kano da ke arewacin Najeriya. A wancan lokacin, masu harkar fina-finai sun yi maraba da matakin, inda suka bayyana shi da cewa wata hanya ce da za ta bunkasa harkar fina-finai a Najeriya da samar wa dubban mutane ayyukan yi. Sai dai masu adawa da wannan mataki sun yi ta sukansa suna mai cewa zai ruguza tarbiyyar al'umma, wadanda da ma wasun su ba sa ga-maciji da masu harkar fina-finai. Daga bisani gwamnati ta dakatar da shirin lamarin da ya yi matukar bata ran 'yan Kannywood." https://www.bbc.com/hausa/labarai-54195538 +entertainment Tsangayar Asali: Yadda fim kan asalin almajirci ya ja hankalin Gwamnan Kano Ganduje Gidauniyar KDC da kungiyar Motion Pictures Production sun hada gwiwa da gwamntin Jihar Kano da ke Najeriya wajen kaddamar da wani fim kan almajirci. Fim din mai suna Tsangayar Asali an shirya shi ne domin yin waiwaye kan asalin almajirci a arewacin Najeriya da kuma irin tasirinsa ga rayuwar al'ummar yankin, a cewar daraktansa Hassan Giggs. Ya kara da cewa wani abin ban sha'awa shi ne yadda fim din yake nuni da irin sauye-sauyen da suka kamata a yi wajen inganta almajirci. Tsangayar Asali, wanda aka kaddamar da shi a wurin wani biki da aka yi a fadar gwamnatin jihar Kano, yana fadakarwa kan yadda za a gina wa almajirai azuzuwa da sanya tsarin boko a cikin manhajarsu da kuma bayar da kudin makaranta kamar yadda ake yi a tsarin makarantun boko. Hassan Giggs ya ce hakan zai sa almajirai su samu nutsuwa wajen koyon karatun Alkur'ani ba tare da sun rika fita yawon barace-barace ba. Manyan masu ruwa da tsaki ne suka halarci wurin kaddamar da fim din na Tsangayar Asali cikinsu har da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, da mataimakinsa Nasiru Gawuna, Sarkin Bichi Nasiru Ado Bayero da kuma malaman addini. Jaruman da suka fito a fim din sun hada da Hadizan Saima, Malam Inuwa, Abdul U. Zada, Nura Sharu da Baba Sadiq. https://www.bbc.com/hausa/labarai-56062776 +entertainment ...Daga Bakin Mai Ita tare da Ibrahim Nasir, Saminu Baba na Kwana 90 Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon: Daga Bakin Mai Ita wani shiri ne na BBC Hausa da ke kawo muku hira da fitattun mutane kan wasu abubuwan da suka shafi rayuwarsu zalla. A wannan kashi na 52, shirin ya tattauna da Ibrahim Nasir, Alhaji Saminu Baba na Kwana 90, inda ya amsa tambayoyin da suka shafi rayuwarsa. Ɗaukar bidiyo da Tacewa: Abdulsalam Usman Abdulkadir Tsarawa da gabatarwa: Umar Rayyan https://www.bbc.com/hausa/media-57420666 +entertainment Sarauniya Elizabeth II: Sarauniya mai dogon zamani "Sarauniya ta rasu. Ran Sarki ya dade."" Wannan shi ne hakikanin abin miliyoyinmu ba su taba ji ba. Mafi yawanmu ba sau san wani Basarake/Basarakiya ba. Daidai lokacin da duniya ke sauyawa shekaru da dama, haka ta dade a kan karaga. Ta yiwu ita ce mace mafi ƙimar daraja da aka sani a doron kasa. Ta yi matukar shahara, a Birtaniya da kasashen waje, a matsayin Sarauniya. Ba mulki ta yi ba, sarauta ta yi. Gidan sarautarta na Windsor zai sha caccaka. Bisa la'akari da yawan rikicinsa, wasu ma har jefa alamar tambaya suke kan karkon dadewarsa. Amma Sarauniya dai ta kai ga gaci ne bisa jajircewa. Yayin da al'umma ta samu matukar sauyi, ta tsare martabarta ta matsayin tambarin hadin kan kasa. An dauki duk abin da ta aikata a matsayin jajircewar aiki. Ta kalubalanci kanta a ranar zagayowar haihuwarta shekara 21 a jawabin da ta gabatar a ziyarar da ta kai Afirka ta Kudu. Lamarin ya kasance mafi muhimmancin abin tinkaho da ta tsayu a kai, a tsarin manufar rayuwarta ta kashin kanta. ""Na yi ikirari a gabanku dgaba daya,"" Gimbiya ta fada wa masu suararenta, ""daukacin rayuwata ta yi tsawo ko ta takaita zan saraiyar da ita da jajircewa wajen hidimta wa hamshakiyar zuri'ata wadda daukacinmu muka fito daga gareta."" Tabbas babu daya daga al'amuran da aka tsara ya kasance. Sakataren Harkokin cikin gida ya halarci bikin zagayowar ranar haihuwarta a ranar 21 ga Afirilun 1926 lokacin da yake fama da mummunar tashintashintar masu hakar kwal - amma a wancan lokacin, Gimbiya Elizabeth Alexandra Mary ba a kaddara mata zama Sarauniya ba. Mahaifinta mutum mai ne kawaici, wanda ke in-ina, wato shi ne da na biyu ga Sarki George V. Ba don kakkabar murabus ba, da Elizabeth sai dai ta yi rayuwa irin ta kaskantattu a kasar, kewaye da dabbobi. Ta yi yarintarta cike da annashuwa, ta ji dadi tun tasowarta lamarin da ya baibaye tsawon sha'awar rayuwarta. ""Lokacin da suke kananan mafi yawancin wasanninsu na dokuna ne,"" kamar yadda Marigayiya Margret Rohodes ta iya tunawa, wadda ta girma tare da 'yan uwanta maza na gidan sarauta da Elizabeth da 'yar uwarta, Gimbiya Margaret. ""Mun rika yin sukuwar dawakail, ko hawan kananan dokuna ko wani abu da kake so, amma lamarin na tatare da hargagin dawaki da sukuwa da hanzari."" Matsayinta na 'yar sarauta ya samu karin karfin sauyii ne a shekarar 1936 lokacin da mahaifinta ya hau gadon sarauta, bayan da kawunta Edward VIII ya yi murabus, saboda wata Ba'Amurkiya Wallis Simpson ( 'yar kwalisa, wadda aurenta ya taba rabuwa, da yake son ya aura). Kawarta da suka tashin tun yarintarta, Sonia Berry ta fara haduwa da Elizabeth lokacin da suke a hannun masu rainonsu, sun fito titin shakatawa da ke tsakiyar birnin Landan Sai Gimbiya ta tashi ta je wajenta ta ce: ""Kina son yin wasa?"" Misis Berry ta tuna yadda alk'amura suka kasance ""bisa tsarin daidaito,"" inda tsohuwar abokiyar wasanta 'yar sarauta an kaddara mata gadon gadon sarauta. ""Muna kiranta da Gimbiya. Mu kan durkusa don girmamata. Yta tashi tare da dimbin mutane. Ta kasance komai da gaske take yi."" Mai nufi na gaskiyar share fagen cimma manufa. Mahaifinta ya yi mulki a zamanin yakin duniya na biyu. ''Yarsa ta kasance mai dabarun yada farfaganda. A shekarar 1940, Elizabeth tare da Margaret tana take mata baya, ta yi jawabi a rediyo don sanar da yaran da suka gudu kasar waje cewa an samu nasarar yaki. ""Yayin da aka samu zaman lafiya, ku tuna cewa jin dadinmu ne, yaran wannan zamani, don kyautata duniya ta zama wurin walwala da karin farin ciki."" An shafe tsawon shekaru biyar kafin a samu wannan damar. Da aka gudanar da bikin ranar samun nasarar yaki a Turai a nfarfajiyar fadar Buckingham, Gimbiyoyi biyu suka fice ba tare da sanin kowa suka shige cikin taron jama'a. Daga bisani Sarauniya ta rika yi wa al'amarin lakabin ""daren da za a dade ana tunawa"" a rayuwarta. Jean Woodroffe na tare da ita. ""Abin dariyar a nan shi ne sun shige cikin Otal din Ritz ta wata kofa, suka fita ta wata kofa, inda a karshe suka rika rawar kamun kugu ta Amurka da ake kira conga,"" a kmar yadda Misis Woodroffe ta fada wa BBC. ""Abin mamakin dai shi ne babu wanda ya lura da su. ""Daga bisani muka koma wajen fadar Buckingham tare da cincirindon jama'a muna ta kururuwar cewa ""Muna son Sarki tare da kowa-da-kowa, har zuwa lokacin da Sarki da Sarauniya suka fito wajen farfajiyar."" A lokacin rikici, Elizabeth ta tsunduma cikin soyayya da wani kyakkyawan Yariman kasar Girka. Bayan haduwarsu ta farko, cikin shekarar 1939 ta yi matukar kamuwa da soyayya. Sai dai ya zama dole ta shawo kan mahaifinta game da wannan ""Yariman kasar waje da ba bai mallaki komai ba"" tamkar yadda wani jami'in gidan sarauta ya siffanta shi. Ta jajirce da hakuri har ta samu mafita Shekarun farko na auren Elizabeth da Philips sun kasance mafi annashuwar farin ciki a rayuwarsu. Sun tsunduma ""cikin tsananin soyayya"" a cewar daya daga cikin barorin Philips. Lokacin da yake aiki a kasar Malta, a matsayin jami'in sojan ruwa, ta rika tuka mota tana kewaya tsibirin, ta halarci wuraren rawa, ta je wajen shakatawa. Lamarin ya sa ta yi irin rayuwar da ba ta jin za ta sake kwata irinta. Lamarin dai bai yi wani tsawo ba. Sai rashin lafiyar mahaifinta ya rika bijiro mata da alamu. Ta fahimci yadda ya mutu farar daya sanadiyyar yawan shan taba, daidai lokacin da take hutu a gandun namun daji a kasar Kenya.. Sai matsayin darajarta ya daga, wato ta bar kasar a matsayin Gimbiya ta dawo Birtaniya a matsayin Sarauniya. A cewarta, ""ba ta taba koyon harkokin mulki ba."" Wannan shi ne abin da ta bayyana wa shirin kundin bayanai na talabijin kan yadda aka yi ta gudanar da managarcin aiki, al'amarin da aka danganta a matsayin irin kadararta ke nan. Wadanda suka yi makokin rasuwarta a halin yanzu da masana tarihi za su fitar da darussan rayuwarta nan gaba, har ta kai ga sujn karkare da cewa ta yi matukar nasara wajen cimma manufofinta. Ta ji dadin kasancewarta Saruaniya. Ta ji dadin harkokin mulki, al'amarin da aka yi hasashen kasancewarta a cikinsa. Ta yi ta samun dimbin nasarori kamar yadda suke tattare a cikin jajayen akwatunanta, wadanda suka tara dimbin takardun bayanan hukuma. Hatta lokacin da aka yi fama da rudani a shekarun 1990, an yi ta bude su. Ana karanta takardu da ke cikinsu. Tana da hakkin a sanar da ita, ta bayar da shawara, ta yi gargadi. Ta dauki al'amarin da matukar muhimmanci, ineda takan nuna matukar kwarewa wajen tarairayar harkokin siyasa a zamanin mulkinta. Firai ministocin da ta yi aiki da su daya bayan daya duk suna karkashin ikon sarautarta. Daya daga babbar matsalar da ta yi fama da ita, ita ce amincewar da ta yi da shawarar Harold Macmillan lokacin da yake jinya a gadon asibiti, cewa, Lord Home ya gaje shi a matsayin Firayiminista. Mutane da dama sun yi tunanin cewa kamata ya yi a ce ta fadada tuntubarta, amma dai Jam'iyyar Conservative daga bisani ta sauya tsarinta, inda ta samar da hanyar zaben shugabaninta, ta yadda ta samu kariya daga sake afkawa cikin rudanin abin takaici. Zamanin mulkinta an smau suayi, a hankali, a hankali. Danfaruwarta da ra'ayin rikau ya nuna ba ita ta haifar da shi ba, sai dia an shawo kanta ne game da alfanun (fa'idar) da ke tattare da lamarin. A hankali, a hankali sai kawai iya;lan gidan sarauta suka kulla abota da talabijin. An kyale a rika daukar hotuna, wasu lokutan ma masu muni. Cikin shekarun 1960, lamarin ya yi matukar kayatarwa yadda aka nuna hoton 'yan gidan sarauta suna aiki da wasa. Amma cikin shekarun 1980, lamarin na da ban takaici ganin iyalanta sun shiga cikin masu caccakar sarauta. Kodayake hakan ya kasance bisa tarbiya, domin ba zai ma yiwu lamarin bai sha wa Sarauniya kai ba. Daidai wannan lokaci hakikanin matsaloli na ta taruwa dankare a cikin fada. Sun bayyana ne kawai a cikin 'yan shekarun nan. Auren 'ya'yanta da dama ya watse, kuma duk an baje bayanan a jaridu. Karshen lamari ma dai a shekarar 1992, fadar Windsor ta yi gobara. Gidan sarautar na ta kokarin kare martabarsa. A cikin gidan dai, iyalan sun kasa yin wnai katabus. Domin Sarauniya a matsayint ana uwa, ana sa ran ta dauki alhaki aukuwasu al'amuran. Wajen biyan asarar da gobara ta haifar a wnai gidan sarautar - a bude kafar biyan kudin al'umma ga Fadar Buckingham. And the Queen and her heir belatedly followed the example of millions of others and started to pay income tax. Worse was to come. August 1997 produced the most difficult week the Queen ever experienced. It began with a fatal car crash in a French underpass and it ended with wailing and weeping on London's streets as the coffin of a princess was carried past. The Queen was not comfortable with public displays of emotion. The reaction to the death of Diana, Princess of Wales, startled her. She believed her duty was to look after the princess's grieving sons in Scotland. Many people disagreed and eventually she travelled down to London to deliver a live television address in which she spoke as a ""grandmother"" and promised to learn from Diana's example. Rugugin musifu sun bace. Masu manufar akidar zaben shugabanni sun yunkuro. Dimbin nasarori sun shude - zuwa shekar 2002 an smau cukurkudaddun al'amuran farin ciki da na bakin ciki. Farko dai 'yar uwarta, sia mahaifiyarta suka rasu. Sarauniya ba ta da isasshen lokacin yin makoki, kodayake dai dubban mutane sun cika da damuwar yadda aka gudanar da bikin cikarta shekara 50 a karagar mulki. Da bazara a wannan shekarar, bukukuwan kayatarwar bukukuwan ta kwaranya sakamakon watsi da shari'ar Paul Burell (mai hidima a gidan sarauta, wanda ya ce ya sanar da Sarauniya kafin ya dauki wasu takardu daga gidan marigayiya Diana, bayan mutuwarta). An wanke shi daga laifin satar kayan gidan sarauta, bayan da Sarauniya ta tuna da tattaunawar da ta yi da tsohon baran Diana. Shekaru uku (bayan mutuwarta), Yarima Charles ya auri Camilla Parker Bowles. Akwai sauran muhimman al'amura da ke tattare da ryauwarta, wadanda suka hada bikin cikar haihuwarta shekara 80; cikar aurenta shekara 60, wata ziyarar tarihi da ta kai Jamhuriyar Ireland; Karin tarihin shi ne musafihar da suka yi da ta yi da mataimakin Firai ministan Ireland ta Arewa, marigayi Martin McGuinness wanda a da ya taba zaman kwamandan 'yan na IRA da bikin auren jikanta Yarima William, wanda aka ayyana a matsayin makomar sarautar Birtaniya. Karin wata muhimmiyar nasarar da ta cimmawa ita ce bikin da ta yi na cika shekara 60 a kan karagar mulki. Ita ce mai sarauta ta biyu da ta kai ga irin wannan gacin (a rayuwa) bayan Sarauniya Victoria. Yulin 2013 ta kasance zagayowar ranar haihuwar tattaba-kunnenta, Yarima George na Cambridge. Shi ne karo na farko fiye d ashekara 100 da aka samu kwararan masu jiran gado uku da ke raye a lokaci guda. Kuma shekaru biyu kadai ta dara Sarauniya Victoria, al'amarin da ya snaya ta zama mai sarautar Birtaniya da ta fi dadewa a karagar mulki. Ta ce ba ta da burin cimma wnanan matsayi. Duk mun san sarauniyar al'umma Sarauniyar da take a kebe, abokan huldarta sun ce tana da Kankan da kai, a cewar wani, tana ""karsashin"" barkwanci da baiwar kwikwayo. Mace ce mai wuyar sha'ani, amma tana da karfin halin bayyana cike da annashuwa da fara'a. A lokuta da dama, a kan ga mulkinta da kayatarwar annashuwa. Masu sukar lamirinta sun dauka an kangeta daga jama'a. Sai dai dimbin masu kareta sun doge kan cewa mutane ba su taba daina ganin mutuncinta tare da girmamata ba,, bis la'akari da cewa ba ta da wani abin fada na kunya irin wnada ya baibaye 'ya'yan sarautar Windsor. A tsawon rayuwarta, wadda mafi akasari ta yi aiki cikin kadaici, ta samu tallafin karfin imaninta da addinin Kiristanci da mijinta. Gidan sarautar Windsor a halin yanzu yana hannun dnata, kuma wa'adin mulkinsa ba shi da tsawo. Ko da yake yanzu dama ta samu na yin kai-kawo wajen nazarin tsawon rayuwar Sarauniya mai kunya, wadda ta samu kaunar mutane. Zamanin sarautar Elizabeth ya sake zagayowa. ©Dukkan hotunan suna da hakkin mallaka" https://www.bbc.com/hausa/labarai-47239508 +entertainment ...Daga Bakin Mai Ita tare da Rashida Mai Sa'a Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon: Daga Bakin Mai Ita wani shiri ne na BBC Hausa da ke kawo muku hira da fitattun mutane kan wasu abubuwan da suka shafi rayuwarsu zalla. A wannan kashi na 53, shirin ya tattauna da Rashida Adamu wadda aka fi sani da Rashida Mai Sa'a a fina-finan Kannywood , inda ta amsa tambayoyin da suka shafi rayuwarta. Ɗaukar bidiyo da Tacewa: Abdulsalam Usman Abdulkadir Tsarawa da gabatarwa: Umar Rayyan https://www.bbc.com/hausa/media-57505572 +entertainment Kun san wanda ya kirkiri kalmar Kannywood? "Wani dan jarida kuma mai sharhi kan harkokin fina-finan Kannywood, Ibrahim Sheme, ya ce kalmar ta Kannywood wadda aka samar da ita a 2002, ta samo asali ne daga Malam Sunusi Shehu Daneji, wani marubucin Hausa a jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya. Sheme ya shaida wa BBC cewa Malam Shehu ya fara amfani da kalmar ta Kannywood cikin wata mujalla mai bayar da labaran fina-finan Hausa, mai suna Tauraruwa. A cewar Sheme, ""ni ma na bayar da gudummawa wajen kirkiro wannan kalma, a lokacin da Malam Sunusi ya kirkiro wannan kalma yana amfani da 'N' guda daya a cikin kalmar Kanny din."" ""Wato Kany ya rika amfani da ita. Da na ga yana amfani da kalmar Kannywood da 'N' guda daya, sai nake tunanin ba dai-dai ba ne,"" in ji Sheme. Ya kara da cewa asalin kalmar daga Hollywood aka dauko ta sannan ""masu yin harkar fina-finai na kudancin Najeriya suna amfani da Nollywood."" Sheme ya bayyana cewa a lokacin ""na ga kamata ya yi a ce Kalliwood don haka sai na fara amfani da kalmar Kalliwood a cikin mujallar fim."" Ya ce a wancan lokacin shi Malam Shehu yana amfani da Kanywood da N guda daya sai dai daga baya ne kuma ya gane cewa mutane sun fi sabawa da kalmar da shi Malam Shehun ya kirkiro ta Kanywood. Ya ce ""don haka sai na koma amfani da Kannywood amma kuma sai na ki amfani da tasa a yadda yake rubuta ta."" ""Sai na kara 'N' guda daya don ya zama Kannywood kamar yadda can yake Hollywood da Nollywood da 'L' guda biyu, toh sai naga ya kamata a rika amfani da N guda biyu."" kamar yadda Sheme ya ce. Tuni dai wannan kalma ta zama shahararriya a yanzu, ta yadda har aka sanya ta a kamus din Turanci na Oxford da ake wallafawa a Birtaniya a baya-bayan nan." https://www.bbc.com/hausa/labarai-51308229 +entertainment Ban san ina da baiwa ba sai da wasu suka hango min - Sani Maiƙafiya "Mawaƙin Hausa Sani Saminu Plumber - wanda aka fi sani da Sani Maiƙafiya - ya faɗa wa BBC Hausa cewa tsautsayi ne ya sa waƙar da ya yi ta karaɗe gari. Cikin wata hira ta musamman, mawaƙin ya ce bai san cewa yana da baiwar waƙa ba sai da wasu mawaƙa a faɗin duniya suka ga waƙarsa ta ""talaka yana magana"" kuma suka ce yana da baiwar. Sani wanda har wa yau ake yi wa laƙabi da talaka, ya ce shi ""almajiri"" ne mai sana'ar gyaran famfo. A sha kallo lafiya." https://www.bbc.com/hausa/articles/c19mxkxz0lxo +entertainment Daga Bakin Mai Ita tare da Sulaiman Bosho Latsa hoton sama don kallon bidiyon: Daga Bakin Mai Ita wani shiri ne na BBC Hausa da ke kawo muku hira da fitattun mutane kan wasu abubuwan da suka shafi rayuwarsu zalla. Shirin ya dawo ne bayan tafiya ɗan hutu sakamakon kullen annobar cutar korona. A wannan kashi na 20, shirin ya tattauna da fitaccen tauraron fina-finan barkwanci na Hausa Sulaiman Bosho, inda ya amsa tambayoyin da za su sa ku dariya. A cikin wannan hira mun tambayi Bosho ko an taɓa marinsa, sanna kuma ko zai yi wa matarsa kishiya. Kun san abin da ya ce? Sai kun kalli bidiyon har ƙarshe za ku ji. Ɗaukar bidiyo da Gabatarwa: Yusuf Ibrahim Yakasai Tacewa: Fatima Othman https://www.bbc.com/hausa/labarai-54544591 +entertainment Asalin wakar Hamisu Breaker da ta sa matan aure gasar rawa "Tun bayan da bidiyon gasar rawar matan aure ya zama ruwan dare gama duniya a arewacin Najeriya da aka yi lokacin bikin sallah, sai hankalin mutane ya koma kan wakar da ta sa suka taka rawar. Wannan waka dai takenta shi ne 'Jarumar Mata' wadda Hamisu Breaker Dorayi ya rera. Duk da cewa mawakin ya ce ya yi wakar ne a karshen shekarar 2019, kuma ya sake ta a farkon 2020, za a iya cewa dubban mutane ba su san ta ba sai a makon bikin karamar sallah, bayan da wasu matan aure suka yi yayin yin rawarta. A wata hirar bidiyo kai tsaye da BBC Hausa ta yi da Hamisu Breaker a shafinta na Instagram, matashin mawakin ya ce wannan gasa da mata suka yi ba karamin farin jini ta kara masa shi da wakar ba. Ya ce: ''Wakar ta yi matukar tashe a lokacin da ta fito amma na yi tunanin ma tashenta ya dan ja baya, kawai kwanan nan sai na ji ta sake karade duniya.'' ""Abin da ya sa na yi wakar jarumar mata na yi duba ne kan mutane. Idan zan yi waka ina duba halayyar mutane ne, misali wani na zurfafawa wajen soyayya wasu kuma ba su da. ''Kuma na ga na kwana biyu ban yi wa masoya waka ba, shi ya sa na ce bari nai musu. Ba budurwata na yi wa ba gaskiya."" '' Idan zan yi waka ba na tunanin samari da 'yan mata kawai, ina farawa ne tun daga kan tsoho mai shekaru da yawa, haka-haka har zuwa kan masu karancin shekaru yadda kowa zai ji wani abu da ya dangance shi."" Hamisu ya ce ya tsaya tsaf ne ya zabi kalaman da ya yi amfani da su a cikin wakar. ''Alal misali baitin farko da nake cewa ashe da rai nake sonki Jaruma ba da zuciyata ba. Kin ga hakan na nufin wannan soyayyar sai ranar da aka mutu za a daina ta tun da ba da zuciya mai sauye-sauye ake yin ta ba. To ko yaya Breaker ya ji bayan da wakar ta sake shahara a baya-bayan nan? ''Ban taba tsammanin wakar za ta zaburar da matan aure ba har su yi gasa a kanta. Na yi ne don masoyana da kuma fatan za ta shahara, sai kuma ga shi ta yi irin farin jinin da ban yi tsammani ba,'' in ji shi. Ya ci gaba da cewa: ''A lokacin da na ga mata sun fara gasar sai na ji dadi sosai, na ce na zama daya daga cikin mutanen da suke ba da gudunmuwa a cikin gyaran aure. Ban taba tunanin ganin haka ba gaskiya."" A ranar ina ta tunanin kamar na sanya bidiyon matan a shafina, amma kuma sai na yi tunanin hakan bai dace ba. Amma na ji dadi kuma na musu fatan alkhairi. Breaker ya ce bai san adadin mutanen da suka kira shi a waya don sanar da shi cewa ya ga yadda wakarsa ta yi tashe a wannan dan tsakanin na bikin sallah ba. BBC ta tambaye shi kan ra'ayinsa kan rawar matan aure a bidiyo a saka a shafukan sada zumunta. Sai ya ce duk da dai a tunaninsa sanya rawar a social media din na iya zama kuskure. Amma tun da ni ba malamin addini ba ne ba zan iya fashin baki kan hakan ba. Wakar dai tana da baituka tara ne masu sadara hudu, kuma tana karewa da kafiya. Hamisun ya ce baitin da ya fi so shi ne na bakwai da yake cewa: ''Yau ga ni a ruwa kusa da kasa zo ki ceci karkona Komai da mafita kada ki saba da furta bankwana Ina ji ina gani yadda nake sonki ya fi karfina Na san a duniya da wanda yake janye duk tunanina. Sunansa Hamisu Breaker Dorayi, kuma dan asalin jihar Kano ne, shekarunsa 27. Ya yi karatun firamare da sakandare a unguwar Dorayi. Ya fara waka tun yana makarantar Islamiyya lokacin yana yaro, amma a shekarar 2016 aka fara sanin sa. Zuwa yanzu ya yi wakokin da shi kansa ya ce bai kirga yawansu ba.Ya yi wakoki irinsu ""So"", da ""Shimfidar Fuska"" da ""Hauwa"" da sauransu." https://www.bbc.com/hausa/labarai-52864273 +entertainment Daga Bakin Mai Ita tare da Aminu S Bono Danna hoton da ke sama don kallon bidiyon: Daga Bakin Mai Ita shiri ne na BBC Hausa da ke kawo maku hira da fitattun mutane kan wasu abubuwa da suka shafi rayuwarsu zalla. A wannan kashi na 108, mun tattauna da wani fitaccen darakta na Kannywood Aminu S Bono, inda ya amsa tambayoyin da suka shafi rayuwarsa. https://www.bbc.com/hausa/articles/cmm1jv1ryneo +entertainment Hikayata 2019: Saurari labarin 'Awa 48' na Fareeda Abdullahi "Ku latsa alamar hoton da ke sama don sauraro A wannan mako za mu kawo maku labarin ""Awa 48"" na Fareeda Abdullahi, wanda Badriyya Tijjani Kalarawi ta karanta. Labarin yana cikin labari 12 na Gasar Hikayata ta 2019 da suka cancanci yabo." https://www.bbc.com/hausa/labarai-50685386 +entertainment Adam Zango ya kashe N46m kan karatun marayu Shahararren tauraron fina-finan Hausa, Adam Zango ya biya kudin karatun wasu dalibai na shekara uku, inda ya kashe fiye da naira miliyan 46. Mawakin ya wallafa takardar tabbatar da samun tallafin da ta fito daga makarantar Farfesa Ango Abdullahi da ke Zaria, a shafinsa na Instagram. Haka kuma takardar ta nuna cewa ya biya kudin karatun yara 101 ne, wadanda yawancinsu marayu ne da kuma yaran da suka fito daga gidajen marasa galihu. Bayanan da ke kunshe a takardar sun kuma nuna cewa Zango ya biya kudin karatun yaran ne tun daga aji hudu zuwa kammala karatunsu na sakandare. Ko da yake tauraron fina-finan bai yi wani karin bayanin kan dalilan da suka sa ya yi hakan ba, wasu masu mu'amala da shafukan sada zumunta da ke yada hotunan takardun, sun bayyana cewa mataki ne mai kyau da ya kamata a yi koyi da shi. Tuni dai wannan mataki na Adam Zango ya janyo martani a kafafen sada zumuta. Ba wannan ne dai karon farko da taurarin Kannywood ke tallafawa marasa karfi ba, sai dai a iya cewa wannan ne karon farko da wani tauraro ya yi irin wannan bajinta a lokaci daya. https://www.bbc.com/hausa/labarai-50155965 +entertainment Coronavirus: Mu gudu tare, mu tsira tare – Nuhu Abdullahi Latsa bidiyon sama domin kallo Tauraron masana'antar wasan Hausa Kannywood Nuhu Abdullahi, ya nemi mutane su bi abin da likitoci da masana ke cewa domin gujewa kamuwa da cutar coronavirus. Nuhu ya nemi mutane da su rika wanke hannuwansu, sannan su je asibiti idan suka ji wasu alamu na rashin lafiya. https://www.bbc.com/hausa/media-51969368 +entertainment ...Daga Bakin Mai Ita tare da Diamond Zahra Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon: Daga bakin mai ita wani shiri na BBC Hausa da ke kawo muku hira da fitattun mutane kan wasu abubuwan da suka shafi rayuwarsu zallah. A wannan kashi na 34, shirin ya tattauna da Diamond Zahra, wata tauraruwar fina-finan Hausa ƴar asalin ƙasar Nijar. A cikin hirar, ta bayyana yadda son harkar fim ya sa ta zo Najeriya daga ƙasarta Nijar. Ɗaukar bidiyo da Gabatarwa: Yusuf Ibrahim Yakasai Tacewa: Fatima Othman Ga wasu na baya da za ku so ku kalla: https://www.bbc.com/hausa/55823749 +entertainment Ado Gwanja: Da ka nake rera kusan dukkan waƙoƙina "Fitaccen mawakin nan na Hausa kuma wanda yake fitowa a fina-finan Kannywood Ado Gwanja ya ce ya rera kusan wakoki 600 tun da ya soma sana'arsa ta waka kuma galibinsu da ka ya rera su. Ado Gwanjo ya bayyana haka ne a hirarsa da BBC Hausa Instagram Live ranar Alhamis. Da aka tambaye shi ko yin waka yana da wahala, sai ya ce ""gaskiya babu abin da yake ba ni wahala"" idan ya zo rera waka. ""Ina kiran mai kida na ce 'buga min kida yanayi kaza, ko yanayi kaza', sai a yi min kida sikeleton...ina cikin ji wakar za ta zo. Idan ta zo sai na ce 'samo min furodusoshi,"" a cewar Ado Gwanja. Ado Gwanja ya ce cikin kusan waka dari shida da ya yi, wakoki ba su wuce biyu ba wadanda ya zauna ya rubuta saboda wasu sun ba shi shawarar yin hakan. Ya ce wakar da ya soma yi ita ce Gawasa ""kuma da na yi ta ni kadai aka bari na yi ta jin kaya ta. Na ji kayata ta ishe ni, na kuna mnata inda na ajiye ta"". Wakokinsa da dama sun yi tashe musamman Kujerar Tsakar Gida, Asha Rawa, da Salon Kida. Mawakin ya ce baya ga sana'ar waka, babu sana'ar da yake so kamar ta shayi. ""Saboda mu asali a gidanmu - ko mace ko namiji, har iyayenmu da sana'ar shayi aka auro su,' in ji Ado Gwanja. Ado Gwanja ya ce ya daina fitowa a matsayin dan daudu a fina-finan Kanyywood saboda ""na fi so matata ta dan yi dariyarta ta fadi ta tashi daga ni sai ita."" A baya dai ya shaida wa BBC Hausa cewa tsabar yadda ya iya kwaikwayon 'yan daudu ne ya sa ake sa shi a fim din da ya danganci haka." https://www.bbc.com/hausa/labarai-53189258 +entertainment Cikin Hotuna: Kannywood a makon jiya Ga hotunan wasu abubuwan da suka faru a masana'antar Kannywwood da muka zabo muku daga makon da ya gabata: https://www.bbc.com/hausa/labarai-51697533 +health Koriya Ta Arewa ta karyata rade-radin rashin lafiyar Shugaba Kim Jong-un "Hukumomi a Koriya Ta Kudu sun ce rahotannin da ake ta yadawa kan cewa shugaban kasar Koriya Ta Arewa Kim Jong-un na fama da matsananciyar rashin lafiya bayan tiyatar da aka yi masa a zuciya ba gaskiya ba ne. Kanun labaran da ke cewa Kim na cikin halin rai-kwakwai-mutu-kwakwai ko kuma yana samun sauki daga aikin da aka yi masa, na da wahalar tabbatarwa. Sai dai Ofishin fadar shugaban kasar Koriya Ta Kudu ya ce babu wata kwakkwarar shaida daga Arewa da ke nuna shugaban mai shekara 36 na fama da rashin lafiya. Ba wannan ne karon farko da ake yada irin wannan jita-jitar ba kan lafiyar shugaban, wanda kuma kusan ya karade ko ina - sai dai daga baya aka yi watsi da wannan batu. A baya-bayan nan Kim bai halarci bikin murnar zagayowar ranar haihuwar kakansa na wajen mahaifi ba da ya gudana a ranar 15 ga watan Afrilu. Wannan daya ne daga cikin manyan bukukuwa da ake yi a kowacce shekara, bikin murnar zagayowar ranar haihuwar wanda ya kafa kasar. Kim Jong-un bai taba kin halarta bikin ba - kuma abu ne mai wahala ya ki halartar bikin kan radin kansa. Rashin halartar tasa ne ya janyo wannan jita-jita da shaci-fadi da ba za a iya kaucewa ba - wanda ke da wuyar gano dalili. Tun ranar 12 ga watan Afrilu rabon da Kim Jong-un ya bayyana a kafafen labarai na kasar ""a lokacin da yake duba wasu jiragen yaki"". Kamar ko yaushe hotunan lokacin sun nuna shi cikin natsuwa da kwanciyar hankali."" Mun sani shi ne ya jagoranci wani babban taron siyasa da ya gudana kwana daya gabanin nan, kamar yadda kafar yada labaran kasa ta bayyana. Amma ba a ganshi ba. Kafafen yada labarai ba su ambaci zuwansa ba wajen gwajin makamin nukiliyar da aka yi a makon da ya gabata ba. Wanda kusan yake halarta ko da yaushe. Rahoto kan Koriya Ta Arewa abu ne mai matukar wuya a lokacin da ya kamata, anma an fara samun bullar jita-jitan ne daga rashin halartarsa wannan bikin da ya gabata. Amma yanzu, yadda ake gudanar da abubuwa a asirce ya fi sama da yadda ake yi bayan an kulle kasar - a karshen watan Janairu saboda cutar korona. Wannan ikirarin da ake yi wa Kim Jong-un an fara ne daga wani rahoton intanet da ya samo asali daga wasu 'yan kasar da ba sa zaune a kasar ranar Talata. Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta shaida wa Daily NK, sun fahimci cewa ""shugaban yana fama da matsalar zuciya tun watan Agustan bara, amma abin ya kazanta bayan ziyarar da ya kai Mount Paektu"". Wannan ce madogarar da kafafen yada labarai na duniya suka rike kan tushen jita- jitar. Kamfanin dillancin labarai sai suka fara yada wannan labari, wannan ce kuma madogarar labaran da suke ta wallafawa, har sai da ma'aikatar sirri da Koriya Ta Kudu da Amurka suka fara bibiyar wannan ikirari. Sannan wasu kanun labarai masu daukar hankali daga kafafen labarai na Amurka da ke cewa shugaban Koriya Ta Arewa na fama rashin lafiya tun bayan tiyatar ciwon zuciyar da aka yi masa. Kazalika, wani bayanin da gwamnatin Koriya Ta Arewa ta fitar, da wata majiyar China ta sirri - ta bayyana wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa - wannan labaran ba gaskiya ba ne. Ba wani abu ba ne mai muhimmanci a ko wanne irin lokaci wani ya musanta cewa Kim Jong-un an masa tiyatar zuciya. Bayanai daga Koriya Ta Kudu da China sun musanta zargin cewa shugaban Koriya Ta Kudu na cikin matsananciyar rashin lafiya. Mafi yawan mutanen Koriya Ta Arewa ba sa sanin bayanin halin lafiyar shugbansu. Ba wannan ne karon farko ba da ya yi batan dabo A 2014, Kim ya taba shafe har kwana 40 daga farkon watan Satumba ba a ji duriyarsa - wanda ya haifar da wata jita-jita cikin gaggawa, wanda har aka ce an yi masa juyin mulki. Sannan sai ya kara bayyana a wani hoto da sandarsa. Kafofin yada labaran kasar a lokacin, sun amsa cewa yana fama da rashin lafiya, sai dai ba su yi magana kan jita-jitar da ke cewa yana fama da ciwon kafa ba. Mene ne shirin Kim dame da me gadarsa? Idan wani abu ya faru ga shugaban Koriya Ta Arewa, babu bayani kwata-kwata game da wanda zai gaje shi. Dama mahaifin Kim Jong-un ya raine shi ne na tsawon shekaru domin ya shugabanci kasar. Wanda hakan zai iya tseratar da Daular Kim. Ana ganin 'yar uwarsa Kim Yo-jong ce zabin da za ta hau wannan matsayi. Ba kawai don ta fito daga zuri'ar Paektu ba ne wadda ta kafa daular iyalan Kim, a'a don ita ma tana janyo kanun labarai a kafafen yada labarai na kasar. A watan da ya gabata ne ta gabatar da wani jawabi a cikin mutane a karon farko, amma ana ganinta a kowane lokacin manyan taruka a gefen dan uwan nata. Yanzu dai za mu jira ne mu zuba ido ko Koriya Ta Arewa za ta yi magana kan wannan jita-jitar da ake yada wa game da rashin lafiyar shugabanta. Amma maganar gaskiya in ana maganar samun bayanai kan shugabanci Koriya Ta Arewa, kawai dai dukkan mu lalube muke cikin duhu." https://www.bbc.com/hausa/labarai-52371979 +health Masana kimiyya sun sako sauraye cikin jama'a Sakin saurayen da aka jirkita kwayoyin halittun nasu cikin jama'a, wani bangare ne na gangamin yaki da cutar maleriya baya-bayan nan a nahiyar Afirka. Cutar zazzabin cizon sauro ta kashe fiye da mutum 4000 bara a Burkina Faso kuma ta kama fiye da mutum 12, 000 Yayin da masu sukar shirin ke bayyana damuwa, masana kimiyyan da ke cikinsa sun ce sakin saurayen wanda shi ne irinsa na farko a Afirka, manuniya ce ta wani muhimmin ci gaba a yakin da ake yi da sauro mai yada zazzabi. Cibiyar binciken kimiyyar lafiya ta Burkina Faso ta saki saurayen da aka jirkita kwayoyin halittunsu cikin garin Bana wanda ke kudu maso yammacin kasar. Matakin wani bangare ne na shirin gidauniyar Target Malaria mai bincike a kan harkokin lafiya karkashin jagorancin Jami'ar Bincike ta Imperial College da ke birnin London. Ko da yake, sakin saurayen ya samu amincewar hukumar kare al'umma daga halittu ko sinadarai masu cutarwa ta Burkina Faso, amma masu sukar shirin sun bayyana damuwa game da hatsarin da ke tattare. Inda suka tuhumi sahihancin shirin, da suka ce ba sa tsammanin yana da wani alfanu wajen takaita yaduwar cutar zazzabin cizon sauro. Gidauniyar Target Malaria ta ce ba a saki mazajen saurayen da nufin rage bazuwar cutar maleriya ba amma matakin zai taimaka wa kwararru wajen tattara muhimman alkaluman da za su tallafi bincikensu. Cibiyar Binciken ta Burkina Faso ta ce an saki saurayen ne bayan an yi la'akari da duk wasu sharuddan ya kamata da tsare-tsaren hukuma, haka zalika al'ummomin yankin su ma sun amince da wannan shirin bayan tuntubarsu da aka yi. https://www.bbc.com/hausa/labarai-48835241 +health Yawan amfani da shafukan sada zumunta na hana bacci "Akwai yiwuwar cewa matasan da ke kashe sama da awa uku a rana a kan shafukan sada zumunta ba za su yi bacci ba sai bayan karfe sha daya na dare kuma za su iya farkawa cikin daren, in ji wani bincike da aka gudanar a Birtaniya. Wannan na shafar matashi daya cikin uku- inda matashi daya cikin biyar ke kashe sa'o'i biyar ko fiye a manhajoji kamar su Instagram da Whatsapp da Facebook kullum, a cewar binciken. Masu bincike a jamai'ar Glasgow sun ce akwai yiwuwar cewa matasa 'yan shekara 13 zuwa 15 na jan kafa wajen kwanciya bacci saboda suna amfani da wayoyinsu. Likitocin lafiyar kwakwalwa sun ce a daina amfani da waya awa daya kafin a kwanta bacci. Sai dai binciken da aka gudanar na matasa 12,000 ya gano cewa hana matasa amfani da waya zai iya zama babbar matsala saboda lokaci ne na cin gashin kansu, lokaci mai muhimmanci da suke zumunci da abokansu. Binciken ya kara tabbatar da wani hasashe na cewa lokacin da matasa ke batawa a kan shafukan sada zumunta na rage lokutan da suke dauka suna bacci- kuma rashin bacci na tasiri a kan lafiyar kwakwalwa da kokarin makaranta. Dakta Holly Scott ta bangaren ilimin halayyar dan Adam na Jami'ar Glasgow, ta ce binciken bai iya tabbatar da cewa yawan amfani da shafukan sada zumunta na jawo rashin isasshen bacci ba, amma da alama yana takara sosai da bacci. ""Matasa na iya kwanciya amma idonsu biyu saboda basu shirya yin baccin ba kuma suna fargabar cewa idan suka yi bacci suka fita daga shafukan za a yi ba su"" Dakta Max Davie ta Kwalejin lafiyar yara ta ce isasshen bacci mai inganci na da muhimmanci ga yara da matasa. ""Muna bayara da shawarar cewa matasa sun daina amfani da wayoyinsu a kalla awa daya kafin su kwanta bacci saboda kwakwalwarsu ta samu ta huta. ""Rashin bacci na da mummunan tasiri ga lafiyar matasa da dangantakarsu da sauran 'yan uwansu da abokansu da kuma kokarinsu a makaranta.""" https://www.bbc.com/hausa/labarai-50146724 +health Covid-19: Fiye da Amurkawa 800,000 sun mutu sanadiyyar Covid Fiye da Amurkawa 800,000 sun rasa rayukansu ga annobar korona, alkaluma mafi yawa da aka samu daga kasa daya tun bayyanar annobar a fadin duniya. Wannan mummunan labarin na zuwa ne yayin da Amurka ke cewa mutum miliyan 50 ne suka kamu da Covid-19 zuwa ranar Litinin da ta gabata. Yawancin mamatan na daga cikin manyan mutane ne da ba su riga sun karbi alluran rigakafi ba, kuma Amurkawan da suka mutu a 2021 sun zarce na 2020. Kawo yanzu Amurka na samin karuwar masu kamuwa da cutar, lamarin da ke tayar da hankula. Alkaluman mutum 800,000 sun zarce yawan al'ummar birane kamar Boston ko Washington DC. Sannan yawan Amurkawa da suka mutu ya zarce na dukkan sojojinta da suka mutu a yakin Duniya na Biyu. Kasar da ke bi ma ta ita ce Brazil mai mamata fiye da 616,000, sai Indiya mai mamata fiye da 475,000. https://www.bbc.com/hausa/labarai-59661915 +health ‘Karancin albashi ya sa wasu ma'aikatan asibiti na tsanar aikinsu’ Wani ƙaramin ma’aikacin lafiya a Najeriya ya koka kan yadda rashin isasshen albashi ke karya gwiwar ma’aikata irinsa, na rashin son zuwa wajen aiki a wasu lokutan, duk kuwa da irin ɗimbin marasa lafiyan da ke buƙatar taimako. Mutumin, ya aiko da labarinsa ne daga jihar Katsina a Najeriya, a cikin jerin labaran da BBC Hausa take samu daga ƴan ƙasar, bayan wallafa neman jin ra’ayin mutane a wani shirin tattara labarai na musamman gabanin zaɓukan 2023. Ma’aikacin lafiyar wanda muka ɓoye cikakken sunansa saboda tsaro, ya ce a lokuta da dama “ina da sha'awar zuwa wurin aiki to amma babu yadda na iya sai dai na haƙura, saboda albashin ba ya isa cefane, balle har na rage na abin hawa,” kamar yadda Nura ya faɗa. Ɓangaren lafiyar na cikin halin taɓarɓarewa a faɗin Najeriya musamman a shekarun baya-bayan nan, duk da irin yadda gwamnati ke shan alwashin inganta shi. Matsalolin da suke jawo rushewar ɓangaren lafiyar kamar yadda ma’aikacin ya nuna, sun haɗa da ƙarancin albashi da sauran alawus-alawus da kuma rashin isassu da ingantattun kayan aiki. Wannan lamari ya sanya ƙananan ma’aikata suke ɗaukar matakin ƙaurace wa zuwa aikin, su kuwa ƙwararrun likitoci barin ƙasar suke yi suna neman aiki a ƙasashen waje. Wasu bayanai da jaridar Punch ta wallafa a watan Oktoban da ya gabata sun nuna cewa daga 1 ga watan Janairu zuwa 30 ga watan Satumban 2022, kusan likitoci 1,307 ne suka bar ƙasar zuwa Birtaniya. Hakan, kamar yadda masana suka bayyana, guduwar ƙwararru domin neman ingantacciyar rayuwa, ba ƙaramar illa za ta ci gaba da yi wa fannin lafiyar ƙasar ba. Nura ya yi karatunsa ne a Makarantar Koyon Fasahar Lafiya a jihar Katsina, inda ya samu satifiket na zama jami’in lafiyar muhalli a 2010. Tun daga wancan lokacin aka ɗauke shi aiki na wucin-gadi a wata ƙaramar cibiyar lafiya, inda ake biyan shi naira 10,000 duk wata. Ma’aikacin ya ce ainihin aikinsa na yin riga-kafi ne na cututtuka, amma daga baya saboda ƙarancin ƙwararru sai da ta kai yana haɗawa da sauran ayyuka da ƙwararrun ma’aikatan jinya ko likitoci ne ya kamata su yi. “Saboda ƙarancin ma’aikata muna taimakawa ta wasu fannonin, kamar yin allura da ƙarin ruwa da duba marasa lafiya da bayar da magunguna,” in ji shi. Sai dai ya koka da cewa duk da tsawon lokacin da suka ɗauka suna wannan aiki har yanzu ba a tabbatar da su a matsayin cikakkun ma’aikata ba sannan ba a taɓa ƙara masu albashi ba, a kan naira dubu goman da ake ba su. “Tun shekarar 2012 aka ɗauke mu wannan aiki na wucin-gadi, mu da yawa, amma har yau ɗin nan babu wani sauyi. Kuma a hakan har aikin kwana muke yi tamkar cikakkun ma’aikata.” Ma’aikacin yana aiki ne a ƙarƙashin gwamnatin jiha amma kuma a asusun ƙaramar hukuma ake biyan shi. “A yanzu, da ni da ire-irena wannan dubu goman ko kashi 30 cikin 100 na cefanen gidana ba ta isa, kuma a haka hukumomin da muke wa aiki suke so mu ci gaba da gudanar da aiki yadda muka saba. “Lokuta da dama ina da sha’awar zuwa wurin aiki to amma babu yadda na iya sai dai na haƙura saboda rashin abin da zan yi cefane har in rage na abin hawa,” ya faɗa cikin alhini. A baya ma’aikata irin su Nura masu wannan ƙorafi har zanga-zanga sun taɓa yi, amma haƙarsu ba ta cimma ruwa ba. Ya koka kan yadda sai lokacin zaɓe ya zo sai ƴan siyasa su yi ta yi masu daɗin baki, a karɓi bayanansu da zimmar za a duba matsalarsu, “amma da zarar an kammala zaɓe sai a manta da mu,” ya faɗa. Ba rashin isasshen albashi ga ma’aikata ne kawai matsalar fannin lafiya ba, akwai rashin isassu da kuma ingantattun kayan aiki. Kamar yadda wannan ma’aikaci ya shaida wa BBC, sa’a ɗaya da aka ci ita ce ta yadda ƙungiyoyin ƙasashen waje masu zaman kansu ke yin matuƙar ƙoƙari wajen samar da kayan aiki da magunguna. Dama a 2020 an bayyana tsarin kiwon lafiyar Najeriya a matsayin na 142 cikin kasashen duniya 195, a wurin inganci. Idan aka waiwaya baya, a shekarar 2001, Najeriya tana daga cikin ƙasashen Afirka da ta yi alkawarin ƙara kuɗin da take warewa a fannin lafiya da kashi 15 cikin 100 na kasafin kuɗinta. Amma shekara 21 ke nan ƙasar ta gaza cimma wannan ƙuduri. A shekarar 2012 ne kawai aka ware kashi 6 cikin 100. Idan kuma aka duba yawan kuɗaɗen da ƙasashen Afirka ke kashewa a ɓangaren lafiya cikin jimillar kasafinsu, to Najeriya na can ƙasa a jerin, domin ita ce ta 38. Sannan ya koka a kan yadda a yanzu matsalar rashin tsaron da ke addabar wasu jihohin ƙasar, ciki har da inda yake aiki, wato Katsina, take shafar su da saka masu tsoron zuwa wajen aiki. “Musamman ma dai mu da muke asibitocin da ke yankunan karkara, inda da a can ne ƴan bindiga ke cin karensu babu babbaka wajen kai hare-haren da ke sa rayuwarmu cikin haɗari. “Hakan ya sa da yawan ma’aikata irina ba sa zuwa wajen aiki akai-akai musamman ganin albashin bai taka kara ya karya ba ga shi ba mu da tabbacin tsaron rayukanmu da na marasa lafiyan. “A yanzu haka asibitoci da yawa ma babu ma’aikatan domin haka ko marasa lafiya sun je ba lallai su samu kowa ba” kamar yadda ya ƙara da cewa. Ma’aikacin, wanda ya ce ya yi karatu ne domin taimakon al’ummarsa, a yanzu wannan yanayi yana karya masa gwiwa ƙwarai. “Ba mu da zaɓi sai barin wannan fanni idan abu ya ci tura, duk da muna son taimakon al’umma.” https://www.bbc.com/hausa/articles/cnewekmenzzo +health Lafiya Zinariya: Taɓin hankalin da ke samun mutum bayan shiga tashin hankali "Latsa hoton da ke sama don saurarar hirar da Fauziyya Kabir Tukur ta yi da likita. Sau da yawa, bayan fuskantar tashin hankali kamar hatsari ko gobara ko 'yan fashi ko yaƙi mutum kan shiga wani irin yanayi na firgici da fargaba. Likitoci sun ce wannan wani nai'i ne ana taɓin hankali wanda a turance a ke cewa Post Traumatic Stress Disorder ko PTSD. Sai dai ƙwararriya a ɓangaren lafiyar ƙwaƙwalwa Dokta Dayyiba Shaibu ta asibitin The Oleaster da ke Abuja a Najeriya ta ce sai an yi a ƙalla wata guda da fuskantar tashin hankali kafin a ce mutum na da cutar. ""Ba wai daga faruwar lamarin ake ganin alamomin cutar PTSD ba. Wani ma sai bayan watanni sannan alamomin za su bayyana a tattarre da shi,"" a cewarta. Dokta Dayyiba ta ce manyan lamaonin cutar sun haɗa da: Dokta Ɗayyiba ta ce idan mutum ya fuskanci wani tashin hankali, bai kamata a riƙa yawan yi masa maganar lamarin ba. Ta ce wannan zai zama kamar ana masa famin ciwon da ke ransa ne. Abin da ya fi dacewa shi ne a nemar masa taimakon ƙwararru a asibitin masu fama da taɓin hankali. ""Wannan cuta ce da dole sai an nemi maganinta, saboda wannan firgici ba ya taɓa rabuwa da mutum idan ba a magance shi ba. ""Sau da yawa mun fi bayar da shawrwari da ɗebe wa marar lafiyar kewa. Ba lallai sai ya sha magunguna ba ma,"" a cewar Dokta Ɗayyiba. Haka kuma, likitar ta ce ba sai mutum ya nuna alamomin wannan cuta sannan za a kai shi asibiti ba. ""In dai mutum ya shiga ko ya fuskanci wani tashin hankali, ko bai fara nuna alamomin PTSD ba ya kamata a nemi taimakon ƙwararru tun wuri,"" in ji ta. Ta ce tunda shi ma nau'i ne na taɓin hankali kuma kowa da irin halittarsa wani ba shi da juriyar fuskantar mummunan tashin hankali ba tare da ya shafi lafiyar ƙwaƙwalwarsa ba. Shi ya sa zuwa asibiti ke da amfani, a cewarta." https://www.bbc.com/hausa/shirye-shirye-na-musamman-54838802 +health Ramadan: Amfanin azumi ga lafiyar jiki Latsa hoton sama domin kallon bidiyon Baya ga fa’idar azumi a addinance, masana lafiya na cewa azumi yana da fa’ida ga lafiyar ɗan-Adam. Masanan kuma sun bayar da shawara kan irin lokaci da nau’in abincin da ya kamata mai azumi ya ci lokacin buda-baki. Nau’ukan abincin sun haɗa da abu mai zafi da ƴaƴan itace da ganyayyaki da kuma ruwa. Aisha Sharif Baffa ta tattauna da masaniyar lafiyar abinci, Zainab Ujudud Shariff. https://www.bbc.com/hausa/media-60977362 +health Yarinyar da kashinta ke yawan karyewa, kuma tana son rawa Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon: Ayeyi na fama ne da cutar rashin kwarin kashi inda kashinta kan karye a duk lokacin da ta mikar da hannunta. Ga shi kuma tana da son yin rawa, amma tana amfani da basirarta domin yin abubuwa na bajinta. https://www.bbc.com/hausa/50331377 +health Masana sun ce ciwon basir ba ya hana ƙarfin jima’i "Ga yawancin mutane musamman Hausawa da sauran kabilu a Afrika, basir ciwo ne da ya zama ruwan dare da ake alaƙantawa da haifar da matsaloli da dama ga lafiya. Wani lokaci yakan zama abin tsarguwa idan aka ce mutum yana da basir, saboda tasirin basir da yadda ake yawan ambatarsa a maganganun mutane na yau da kullum. Basir wata babbar matsala ce da ke da fadi ga bahaushe da sauran kabilun Afrika musamman yadda likitoci ke mamakin yadda suke jin masu maganin gargajiya ke kambama ciwon na basir ga al'umma. Yawanci mutanen da ke fama da matsalar basir ba su damu da zuwa asibiti ba, sun fi dogara da jikon itace na masu maganin gargajiya, waɗanda suka faɗaɗa tunani tare da dasa wa mutane tunani kan matsalar fiye da yadda mutane suka ɗauke ta. A wani cikakken bayani da ta wallafa kan matsalar ciwon basir da abin da ke janyo shi da hanyoyin magance shi. Mujallar kiwon lafiya ta jami'ar Harvard ta ce basir matsala ce da ake yawan magana kai tsaye tsakanin mutane. Mujallar ta ce kusan rabin al'ummar duniya daga shekara 50 sun ji daya ko fiye daga cikin alamomin basir. Kuma babu wasu alkalumma kan yawan masu fama da basir a duniya saboda yawanci mutane ba su cika fitowa suna gabatar da kansu a asibiti ba a duk lokacin da suke fama da matsalar. A cikin wannan makalar za ku fahimci basir da mana'arsa da abin da ke janyo shi da alamominsa da illolinsa da kuma hanyoyin kaucewa kamuwa da matsalar. BBC ta tattauna da kwararren likita Dakta Tasiu Ibrahim, malami a tsangayar koyar da aikin likita a Jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria kuma shugaban asibitin Sultan a unguwar Rigasa a Kaduna. Ciwon basir, lalura ce da ta shafi kowa. Dr. Tasiu ya ce matsalar basir tana da alaka da dubura, amma ba duk matsalar da ta shafi dubura ba ake jingina wa ga matsalar basir. Likitan ya ce an takaita mana'ar basir da kumburin jijiyoyi jini da ke iya haifar da zubar da jini ko samar da kaikaiyi ko ya fito har sai an mayar. Majallar lafiya ta Jami'ar Harvard ta ce yanayin da yawancinmu muke kira basir yana tasowa ne lokacin da jijiyoyi suka kumbura musamman jijiyoyin ƙafafu. Saboda jijiyoyin da suke ciki dole ne su ci gaba da yaƙi da nauyi don samun jini ya dawo ga zuciya. Jijiyoyin tsari ne na halitar dan Adam da kowa yake da su. Likita ya ce lalurar basir kan samu ne a lokacin da jijiyoyin jini suka kumbura da ake kira hemorrhoids inda idan suka kumbura suke samar da matsala ta rashin sukuni a wurin zama da kaikayi da zubar majina a dubura har ya kai ga zubar jini. Wani lokaci idan suka kumbura, duburar tana iya fitowa har ta murde ta matse ta ki komawa wanda hakan ke haifar da babban ciwon da har sai an yi tiyata. Sai dai alakanta wata lalura da dubura yana da kashe-kashe daban-daban a likitance da zai iya zama ba lalle basir ba ne da yawanci ake alakantawa. Dr Tasiu ya ce akwai matsaloli da dama da suka shafi dubura kamar tsaga da yanka da ake kira Anal Fissure wanda duka ba basir ba ne. Akwai kuma ciwon da ake kira Anal Fistula wanda shi ma ba basir ba ne - amma ga mutane duk matsalolin da suka shafi dubura sunansu basir. Likitan ya ce ba basir ba ne ke daukar alhakin dukkanin matsalolin da suka shafi dubura, kamar yadda ake yawan alakawanta Basir ya sha bamban da cutar murdawar ciki ko yawan ba haya da zawo da ake kira Dysentery. Dakta Tasiu ya ce ciwon murdawan ciki - ruruwa ne na 'yan hanji wanda kwayar cuta ce ke janyo shi - basir kuma jijiyoyin jine ke kumbara a dubura. Yawanci an dauki dukkanin wandannan a matsayin matsala daya wato basir. Likita ya ce yawan kumburin ciki da yawan tusa da yawan jin yunwa da yawan rama ba su cikin alamomi na basir a likitance- ya ce wadannan matsalolin za su iya fadawa cikin rukunin matsalolin da suka shafi kwayoyin cuta da za a iya gano matsalar da ta haifar da su idan an yi bincike. ""Matsaloli da dama kan iya janyo matsalar da ta shafi kashi da jini - kamar ulsa da ciwon hanta da ciwon daji a kofar dubura."" A cewar likita murdawan ciki lalura ce mai zaman kanta - wato yawan zawo da majina wani lokaci da jini wanda kwayoyin cuta ke jawo wa kuma idan an sha magani na kwayoyin cutar nan take za a rabu da matsalar. A daya bangaren kuma - basir lalura ce da halittar dan adam ke janyo wa idan aka samu wasu matsaloli da ke sa su bayyana ga mutum. Abubuwan da ke janyo basir suna da yawa ba kuma kwayoyin cuta ba ne kamar yadda suke faruwa a cutar murdawan ciki da ake kira dysentery. Akwai dalilai daban-daban da kan iya jawo kashi da jini, a cewar likita. Likita ya kuma ce cutar murdawan ciki ta dysentery takan yadu ne ta hanyar gurbatar abinci ko ruwan sha da ke dauke da kwayoyin cuta wanda ke haifar da ciwon ciki da murdawa da kasala da kuma zawo da jini. Kuma da an yi maganin dysentery za a iya rabuwa da cutar. Basir halitta ce da kan dauki lokaci kuma akwai yiyuwar matsalar ta dawo ko da an magance ta. Likita ya bayyana jijiyoyin jini na dubura, kamar wani soso da ke samar da tasuhi ta yadda mutum zai iya zama ba tare da wata damuwa ba. Mujallar lafiya ta Harvard ta ce basur yawanci yana faruwa ne sakamakon takura da matsin da jijiyoyin jinin suka samu musamman ga mata masu ciki da masu kiba, ko kuma ga mai yawan nishi a yayin bahaya. Dakta Tasiu ya ce idan jini ya kasance ba ya koma wa ga zuciya yana jawo kumburar wadannan jijiyoyi. ""Kamar mutum ya daure wurin duwawunsa ne inda ya zauna - irin wannan yana samar da matsalar komawar jini wanda zai iya assasa ci gaba da samun matsalar basir,"" in ji Dakta Tasiu. Mujallar Harvard ta ce basir da ake kira Hemorrhoids ya kasu kashi biyu - akwai na cikin dubura da kuma na wajen dubura. Na cikin dubura yana iya boye wa, ba tare da mutum ya san yana dauke da shi ba har sai wani lokaci da zai fara zubar jini. Dakta Tasiu y ace yadda mutum zai gane yana da basir shi ne idan ya zauna zai ji kaikayi wajen duburar ko radadi ko ya ji naso da majina na taruwa har yakai lokacin da zai ji yana son bullokowa a dubura. Wani lokaci idan ya je bahaya duburar za ta fito, takan iya komawa idan ya gama. Kuma akan kai matakin da ba za ta koma ba. Likita ya ce mata masu juna biyu yawanci sukan ce duburarsu tana fitowa - wannan ya sa ake ba su shawara a lokacin awo su daina kwanciya rigingine. An fi so mata masu juna biyu dinga kwanciya gefe d don dauke wa babbar jijiyar jini nauyin jaririn da ke cikinsu wanda ke rage tasirin samuwar lalurar basir. 'Basir na sa hauka' Ko da yake mujallar lafiya ta jami'ar Harvard ta ce ciwon basir ba shi da hadari, amma lalura ce da ke haifar da radadi saboda tafiya yake ya dawo. Dakta Tasiu ya ce radadin ciwon basir na iya taba tunanin mutane saboda damuwar da lalurar ciwon ta jefa su. ""Mai ciwon basir zai iya yin sabbatu kamar mai ciwon hauka,"" in ji likitan. Ya kara da cewa idan matsalar basir ta yi tsanani saboda tsananin ciwo yakan jefa mutum cikin lalurar damuwa har yakai kamar ya fita hayyacinsa. Basir kan tsananta idan ba a yi gaggawar zuwa asibiti ba. Basir kusan shi ne abu na farko da aka fi dangantawa da matsalar kwanciyar aure musamman tsakanin Hausawa da sauran kabilu na Afirka. Likitoci sun ce kambama matsalar basir ake musamman masu maganin gargajiya da ke danganta matsaloli da dama da basir. Ga yawancin mutane, rashin ƙarfin sha'awa ko kankancewar al'aura duk matsaloli ne da ake dangantawa da basir ko sanyi ko yawan shan zaki. Haka ma ciwon gwiwa da sauran cututtukan da suka shafi rayuwar aure duk ana alakanta su da basir. Tallan maganin gargajiya da lasifika ba sabon abu ba ne a kasuwannin kauye, inda za a ji mai tallan maganin gargajiya yana zayyano matsaloli da dama da basir ya haifar kamar haka: ""Maganin Damisa ikon Allah, jiko madarar icce, A rabu da atuni, kashi da jini da ciwon fitar baya Maigida za ka ji kana cinye malmalen tuwo, har uwar gida ta kara ma da kankare Ciki ya yi dadi, ciki ya yi lafiya Don dadin fitsari mai gida har da susan keya Can sai ka ji gabanka na harbawa din-din-din"" Dakta Tasiu ya ce matsalar rashin ko karancin sha'awa matsala ce ta daban da ya kamata a yi bincikenta a likatance haka ma matsalar basir. ""Kuma basir ba ya da wata nasaba da matsalar kwanciyar aure,"" in ji likitan. Likita ya ce yawancin maganin basir a likitance shawarwari ne ake bayar wa kan yadda mutum zai sauya yanayin ruwaya don kan kaucewa basir. Ya ce babban maganin basir shi ne cin abinci mai sinadarin fibre wato ganyayyaki da wake da alkama, maimakon kayan kwalama, irinsu kayan gwangwani ko na ruwan kwalba. An fi son a ci abinci mai dussa dussa da kayan itace kamar toton lemu - ba ruwan kawai ake son mutum sha ba. Nau'in abincin da ake ci ba gayyayaki na kara sa basir. Yawan motsa jiki a ko da yaushe yana maganin basir, musamman ga waɗanda ke yawan zama a wuri ɗaya kamar ma'aikata. Sannan a mataki na tsabta ana son mutum ya taftace duburar shi. Ga wanda yake fito masa da ake kira fitar baya, akwai magunguna da za a ba shi da allurai da za a iya magance matsalar Wani lokaci basir yakan kai wani mataki na yin tiyata idan ya fito domin cire tsironsa." https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-54657759 +health Buhari ya kori shugaban hukumar inshorar lafiya Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da korar babban sakataren hukumar Inshorar lafiya ta kasar wanda ya sha fama da dambarwa. An tura Farfesa Usman Yusuf hutun dole ne a watan Oktoban bara, bayan majalisar gudanarwar hukumar ta dakatar da shi. Daraktar yada labarai a ma'aikatar lafiyar Najeriya, Boade Akinola ta cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, ta ce korarsa ta zo ne bayan shawarar da kwamitin binciken da aka kafa don gano sanadin rikicin da ya dabaibaye hukumar, ya bayar. Tun farko a shekara ta 2017 ne tsohon Ministan Lafiyan kasar, Farfesa Isaac Adewole ya dakatar da Farfesa Yusuf bisa zargin aikata ba daidai ba, da kuma tafka almundahana da dukiyar al'umma. Sai dai kwararren likitan ya sha musanta wadannan zarge-zarge, yana mai cewa masu adawa da auye-sayen da ya bullo da su ne suke yakarsa. An nada Mohammed Sambo domin ya maye gurbinsa. Sai dai tamkar abin nan da Hausawa ke cewa abin da ya ci doma, to ba ya barin awai, ita ma majalisar gudanarwar hukumar da ta ba da shawarar a kori babban sakataren, Shugaba Buhari ya amince da rusa ta. Korar Farfesa a yanzu, wanda ya shafe tsawon wata 10 yana hutun dole tamkar sauya shawara ce daga wurin Shugaba Buhari wanda ya dawo da shi aiki lokacin da tsohon minista Adewole ya dakatar shi a watan Yulin 2017. A shekarar 2017 ne dai Majalisar Wakilan kasar ta nemi a mayar da Farfesa Usman Yusuf kan mukaminsa. Kwamitin lafiya na Majalisar ya nuna cewa matakin dakatar da shi tamkar wani bi-ta-da-kulli ne kan bayanan da babban sakataren ya bayar a wani zaman sauraron jama'a da kwamitin ya yi. Yayin zaman cikin watan Yunin 2017, ya zargi manyan dillalan inshorar lafiya da karbar makudan kudade ba tare da mutane na amfana da shirin ba, ya kuma yi ikirarin cewa an cusa sunayen bogi na mutane sama da 23,000 wadanda ake amfani da su domin fitar da kudade. Wasu na ganin wannan ki-ki-kakar da aka samu ta yi illa ga harkar samar da insorar lafiya a kasar, tare da zargin Shuguba Buhari da jan kafa wurin daukar mataki. https://www.bbc.com/hausa/labarai-48835240 +health Coronavirus: Yadda cutar korona ta jawo ƙarancin iskar oxygen a ƙasashe masu tasowa "Kafin iskar oxygen ta ƙare a asibitin, Maria Auxiliadora da Cruz ta yi ta nuna alamun ƙrfin gwiwa na cin galabar cutar korona. A ranar 14 ga watan Janairu sai yawan iskar da take shaƙa ya haura yadda ake so na kashi 95 cikin 100 - amma cikin sa'o'i kaɗan sai ya sauƙa zuwa kashi 35 cikin 100, kuma hakan na iya haifar mata da illa. A wannan gaɓar, marasa lafiya yawanci sai dai a taimaka musu da iskar oxygen ta inji. A maimakon haka, sai Maria wacce ma'aikaciyar jinya ce ta mutu. ""Abin na da ban tsoro,"" in ji surukarta Thalita Rocha. ""Babban bala'i ne. Marasa lafiya da dama masu yawan shekaru sun shiga wani yanayi."" A wani bidiyo mai ban tausayi da ya yaɗau a shafukan sada zumunta kamar wutar daji, ta bayyana abin da ya faru a Policlínica Redenção a birnbin Manaus da ke yankin arewacin Brazil. ""Muna cikin wani yanayi na tashin hankali. Babu iskar oxygen ko kaɗan a kafatnin ɓangaren gaggawa... Mutane da dama na mutuwa."" Ta shaida wa sahen BBC Brazil cewa mutum 10 ne suka mutu a rana ɗaya a ɗakin asibiti ɗaya, kuma ta yi amannar cewa da surukarta na iya tsira. ""Ba cutar korona ce ta kashe ta ba. Abin taƙaici, ta mutu ne sakamakon rashin iskar oxygen. Brazil ce ƙasar da ta fi yawan masu cutar korona a duniya inda fiye da mutum 219,000 suka mutu. A Manaus, tsarin lafiyar birnin ya taɓarɓare har sau biyu a lokacin annobar cutar korona, sannan yawan mace-mace ya ruɓanya daga tsakanin watan Disamba zuwa Janairu, abin da ya sa ƙaramar hukumar ta sanar da shirin samar da sabbin ƙaburbura har 22,000. Amma kuma asibitoci da dakunan shan maganin kasar ba su kadai ne ke fuskantar matsalar karancin samun iskar ta oxygen ba. A kasar Mexico, inda mutane fiye da 152,000 suka mutu a annobar, akwai rahotannin cewa ɓarayi na sace tukwanen iskar ta oxygen din daga asibitoci da dakunan shan magani. Ga misali, an cafke wasu mutane biyu bayan sace wata babbar motar daukar kaya maƙare da tukwanen iskar ta oxygen din da aka sace a arewacin birnin Mexico. A baya cikin wannan watan, wasu faya-fayen bidiyo da suka bayyana, sun musanta ƙarancin isakar ta oxygen a aƙalla asibitoci biyu a kasar Masar. A daya daga ciki, wani mutum ya naɗi faifen bidiyon wasu gadaje da aka lulluɓe da barguna a asibitin al-Husseiniya a arewa maso gabashin yankin mulki na Sharqia, kana ya yi ikirarin cewa ''duk waɗanda ke sashen lura da marasa lafiya na gaggawa a asibitin sun mutu''. Mahukuntan kasar Masar sun ce marasa lafiya hudu ne suka mutu saboda tsananin kamuwa da cutar - ba saboda karancin iskar ta oxygen ba - kana sun musanta cewa akwai matsaloli wajen samarwa. Amma kuma rahotanni masu kama da haka a kasashe da dama sun yi nuni da matsin lamba kan gwamnatoci su samar da wannan muhimmiyar hanya ta ceton rayuka. Kamar yadda kungiyar lafiya ta duniya (WHO) ta bayyana, daya a cikin mutane biyar da suka kamu da cutar korona na bukatar iskar oxygen. A yanayi matsananci, yana kai wa har mutane uku cikin biyar. Hukumar ta ce ba ta da cikakkun bayanai da aka tattara daga kasashe, amma ta ce wasu asibitoci sun shaida karuwar bukatar samun karin iskar ta oxygen a tsakanin sau biyar zuwa bakwai saboda karuwar wadanda suka kamu da cutar mai tsanani. Kungiyar PATH, mai taimaka wa gwamnatoci wajen yaki da annobar, ta gano cewa bukatar isakar ta oxygen ''ta karu matuka'' a shekarar 2020, saboda karuwar yawan adadin wadanda suka kamu da matsanancin sarkewar numfashi - karancin oxygen a cikin jininsu - saboda cutar ta korona. ""Muna bukatar yin tunani game da iskar oxygen kamar yadda muke tunani game da samar da wutar lantarki, da ruwa da sauran abubuwa na buƙatu,'' in ji Lisa Smith, ta kungiyar ta PATH. ""Wannan ba zai zama abu da za mu damu da shi idan abubuwa suka ɓaci ba, saboda lokacin da abubuwa da suka ɓaci, mutane za su mutu.'' Yanzu haka, ana bukatar tukwanen iskar ta oxyegen kusan miliyan daya da rabi a kullum a fadin kasashe matsakaita da matalauta, don bukatun da suka shafi matsalolin da annobar ta haifar kamar yadda na'urar bin diddigin kan yadda al'amuran samar da iskar ta oxygen din ta nuna. Na'urar ta shafin intanet, wacce ke taimaka wa wajen ƙididdigar ma'aunin ƙalubalen da ke gaban mahukunta, cibiyar lura da cututtukan da suka shafi numfashi mai alaƙa da cutar korona da hadin gwiwa da kungiyar PATH da ta 'Every Breath Counts', da ke fafutikar ganin kasashe masu ƙaramin ƙarfi sun samu iskar ta oxygen ne suka ƙirƙiro ta. ""Akwai matsalar samun iskar oxygen a fadin yankin Kudu da Saharar Afirka da Asia da Latin Amurka,'' in ji Leith Greenslade, daga kungiyar 'Every Breath Counts'."" Kasashen ba sa nuna muhimmanci kan ko iskar oxygen nawa wadanda suka kamu da cutar korona ke bukata: wasu na bukatar goma, sau 20 fiye da yadda sauran marasa lafiyar da ke bukatar oxygen din za su nema."" Kamar yadda na'urar bin diddigin ta gano, ƙasar Brazil ta kasance daya daga cikin kasashen mafi fuskantar ƙaruwar buƙatar iskar ta oxygen tun a cikin watan Nuwamba - tana buƙatar tukwanen iskar oxygen aƙalla 340,000 a kowace rana don masu fama da cutar da korona. Bayan da matsala a jihar Manaus ta kai maƙura, an aike da gudumawar iskar oxygen daga sauran jihohin da tsallaken kan iyakar kasar Venezuela. Amma a jihar Jesem Orellana,wani kwararre a fannin cututtuka masu yaduwa a kungiyar Oswaldo Cruz Foundation, ya shaida wa BBC hadarin karancin zai ci gaba, kuma karuwar mabukatan ce ta haifar da haka. A sauran kasashe masu tasowa, kamar Indiya, akwai ƙaruwar kashi 60 bisa 100 na bukatar iskar ta oxygen tsakanin watan Afrilu zuwa Yuli, kana ƙaruwar kashi 84 bisa dari tsakanin watan Yuli zuwa Satumba. Adamu Isah daga kungiya Save the Children a Najeriya - inda ake buƙatar karin tukwanen iskar oxyegen 10,000 a ko wace rana - ya bayyana ''""buƙatar ƙarin oxygen din da cewa ƙarancin ya karaɗe kusan duka sassan kasar''. A Afirka Ta Kudu, na'urar bin diddigin ta ƙididdiga cewa kasar na buƙatar ƙarin tukwanen iskar oxygen 100,000 a kowace rana. Ministan lafiya Zweli Mkhize y ace gwamnati ''na iya bakin kokarinta ta tabbatar an samar da isassun tukwanen iskar oxygen din'' kana ta nemi ƙari daga kamfanoni. Daga ina ake samun iskar oxygen ta marasa lafiya? Kamar yadda kungiyar PATH ta bayyana, iskar oxyegen ta marasa lafiya na samar da kashi 5 zuwa 10 bisar dari kacal na iskar oxygen din da ake samarwa a duniya. Ana amfani da sauran ne a masana'antu da dama, kamar na haƙar ma'adinai, da na hada sinadarai da na magunguna. Ana samar da ita da daman gaske a masana'antu kuma ana samar wa da asibitoci ta hanyoyi biyu: ko a cikin tankunan iskar mai ruwa, ko kuma a cikin tukwanen iskar gas da ke ɗaukar adadi marar yawa. Oxygen mai ruwa ita ce ta fi saukin kudi da kuma hanyar fasaha mafi inganci, amma kuma asibitoci na buƙatar su samu kayan aikin da suka dace ta yadda za su iya tura iskar ta cikin bututai zuwa gefen gadon marar lafiya. An fi samun irin wannan a kasashen da suka ci gaba kamar Amurka da Turai. Tukwanen na da buƙatar bututai kuma za a iya kai wa dakunan shan magani ba tare da wasu kayan aiki masu wahala ba. Amma kuma, rarraba su kadan-kadan na nufin babu kashe kudi sosau, haka kuma kasancewa masu nauyi wajen tafiya da su ko dauka, wanda kuma ke tattare da hadarin gurabcewa. ""Wasu kasashen sun dogara kacokan kan shigowa da iskar oxygen daga waje zuwa asibitoci ta hanyar amfani da tukwanen a kan hanyoyi masu gargada da kuma dogon zango,'' in ji Farfesa Mike English, wanda ya taimaka wajen jagorantar sashen ayyukan kiwon lafiya a cibiyar bincike ta KEMRI-Wellcome a birnin Nairobi, wadda ke da hadin gwiwa da Jami'ar Oxford a Birtaniya. ""Wannan babbar matsala ce kuma adadin da ake bukata na da wahala wajen samarwa.'' Ya ce samar da iskar ta oxygen matsala ce a Afirka kafin barkewar annobar. ""Kafin annobar Covid, akwai lokuta da dama da ko da a manyan asibitoci karamin yaro marar lafiya, ko jariri ko kuma wani wanda ke bukatar taimakon gaggawa, ba za su iya samun iskar oxygen din da suke bukata ba,'' ya bayyana. ""Korona ta kara fito da matsalar a fili saboda yanzu tana shafar manya su ma.'' Tun a shekarar 2017 ne kungiyar lafiya ta duniya WHO na daukar iskar oxygen a matsayin muhimmin magani. Amma kuma Ms Smith ta ce ana daukar samar da ita a matsayin ''bayan tunani'' - tare da bayyana matsalar da cewa '' batun bangaren kiwon lafiya ne'' mai kunshe da da ''abubuwa da dama''da ake bukata su yi daidai wajen shawo kan matsalar. Kowane ƙwararre da ya yi hira da BBC ya fadi abu iri daya, da suka hada da bukatar kayan aiki, horarwa da kuma shawo kan matsaloli na tsawon lokaci a sharhinsu. Asibitoci ga misali, za su iya gina masana'antar samar da iskar ta oxygen da za a iya samu a ko da yaushe. Amma kuma suna da tsada, suna bukatar wadatuwar wutar lantarki da kuma ƙwarewa da kuma ƙwararrun injiniyoyi masu lura, wanda da lallai ba ne a samu in ji Farfesa English. ""Kamar sauran bayyanannun abubuwa 'masu sauƙin kafawa', masana'antun sarrafa iskar oxygen na bukatar duk wani bangare na kiwon lafiya ya zamanto yana aiki,'' ya kara cewa. A kasar Malawi, akwai irin wadannan masana'antu uku - a babban asibiti na Blantyre Queen Elizabeth, da asibitin Nkhata Bay da kuma babban asibitin Kamuzu a birnin Lilongwe. Saboda gina su, kasar ta bukaci shigo da kayayyaki daga Afirka Ta Kudu, in ji Grycian Mussa, babban injiniya a asibitin. ""Lokacin kullen korona, ya kasance matsala babba, saboda komai na zuwa ne daga Afirka Ta Kudu, kuma Afirka Ta Kudu na cikin kullen korona, kana Malawi ma na cikin kullen,'' ya bayyana. ""Ina ga lokaci ya yi da kasashen Afirka za su horar da injiniyoyi a kasashenmu, kana mu duba yadda za mu riƙe kanmu. In ba haka ba, haka za mu ci gaba da dogara da wasu kasashen wajen neman taimako a tsakiyar wannan annoba."" Bukatar horar da injiniyoyin an taɓa yin shi a baya a Najeriya daga wani kwamitin samar da iskar oxygen da aka kafa tare da tallafi kungiyoyi masu zaman kansu da wasu hukumomi don bayar da shawarwari kan amfani da isakar oxygen din, in ji Malam Isah. ""Ko da ka kawo duka iskar oxygen din dake duniya, idan ba ka horar da mutane kan yadda za su yi amfani da it aba, kana bata lokacinka ne,'' ya ce. Na'urorin auna mitocin oxygen din, da ke maƙale a jikin yatsa don auna yawan iskar da ke cikin jini, hanya ce mai sauƙi ta lura da marasa lafiyar idan aka horar da mutane yadda za a iya amfani da su. Amma har yanzu akwai batun matsalar samar da oxygen din. ""Ko da irin wannan, da mafi sauƙi ce wajen sarrafawa da kuma samarwa, ba a cika samu a kasashe masu ƙananan ƙarfi ba a Afirka,"" in ji Farfesa English. Kungiyar Lafiya Ta Duniya WHO, ta rarraba wasu kimanin 16,000 a kasashen duniya lokacin ɓarkewar annobar amma ta yi gargaɗin cewa ""ba su wadata ba ga marasa lafiyar da cutar ta yi musu tsanani da ke bukatar karin oxyegen din''. Ko kafin ɓarkewar annobar, hukumomi kamar su UNICEF sun yi ta rarraba iskar ta oxygen tare da zuba jari a masana'antun sarrafa isakar ta oxygen a asibitoci a kasashen da suka ci gaba don yaƙar cututtuka irin su sarƙewar numfashi kamar 'pneumonia' - ""mai kisan mummuke"" da aka ƙiyasta na kashe yara kimanin 800,000 a kowace shekara. Yanzu akwai damuwa, da kungiyoyi kamar Save the Children da ƙwararru irin Farfesa English suka yi la'akari cewa matsalar da cutar korona ta haifar kan samar da iskar ta oxygen ka iya yin nakasu ga lura da sauran cututtuka. ""Oxygen na taimakawa kan matsaloli da dama, daga jarirai da ke buƙatar oxygen zuwa wani wanda ke da matsanancinin ciwon huhu a tsakanin masu yawan shekaru,'' in ji Ms Greenslade. ""Cutar korona ta nuna mana muhimmancin da ke tattare a kasashen da babu alluran rigakafi, babu magani. Ya kuma kai ga cewa ko mun samu oxygen ko bamu samu ba, ko mu mutu ko mu rayi.'' *Karin rahoto daga Vinicius Lemos a Sao Paulo" https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-55918615 +health Coronavirus: Ta yaya mutum zai san yana da cutar? Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon: Bayanai kan yadda mutum zai san ko yana tare da wasu alamomi masu nuna cewa ko yana dauke da coronavirus. https://www.bbc.com/hausa/media-51980540 +health Annobar coronavirus za ta shafi tattalin arzikin Afirka "Cutar Coronavirus na iya shafar rayuwar mutane a fannin da ba na lafiya ba. Saurin yaduwar da cutar ke yi, ya sa kamfanonin sufurin jiragen sama dakatar da jigilarsu zuwa China, inda cutar ta fara bulla. Kamfanin jirage na Kenya Airways ya sanar da dakatar da jigilar fasinjoji har sai nan gaba, haka ma kamfanonin jirage na RwandAir da Air Madagascar da Air Mauritus da sauransu. Kamfanin na Kenya Airways ya ce ya dauki wannan matakin ne domin lafiyar kwastomominsa. Amma masana tattalin arziki dai na ganin cewa wannan zai haifar da nakasu a tattalin arzikin Afrika da na China da ma duniya baki daya. Farfesa Muhammad Muttaka Usman, wani masani kan harkar tattalin arziki da ke Jami'ar Ahmadu Bello ta Zaria ya ce rashin zirga-zirga tsakanin nahiyar da China zai takaita kasuwanci. ""Kasashen Afrika da dama sun ta'allaka a China da samun abubuwan amfani don haka idan jiragen nahiyar suka soke zuwa to lallai wannan zai shafi kasuwanci da tattalin arzikinsu,"" a cewarsa. Farfesa Muttaka ya ce kawo yanzu barkewar cutar Coronavirus ta jawo wa China asarar kusan dala miliyan 60, don haka ""dole zai shafi tattalin arzikin duniya."" Ya ce zai yi wuya tattalin arzikin kasashen Afrika ya iya ci gaba ba tare da kasuwanci da China ba. Ranar Alhamis ne Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta ayyana cutar coronavirus a matsayin babbar barazar lafiya a duniya. Kawo yanzu cutar ta kashe sama da mutane 300 a China kuma tana ci gaba da yaduwa inda hukumomin China suka tabbatar da cewa an sake gano wasu mutum dubu biyu sun kamu da cutar. Kasashe da dama sun rufe iyakokinsu daga baki masu zuwa daga China, yayin da jami'ai ke aiki don shawo kan yaduwar cutar. Amurka da Australiya sun ce za su hana duka bakin da suka je China kwanan nan biza. Kasashe kamar Rasha da Japan da Pakistan sun sanar da irin wadannan sabbin dokoki da suka sa don dakile yaduwar coronavirus." https://www.bbc.com/hausa/labarai-51345717 +health Maganin tsarin iyali na maza: Wadanne hanyoyi suka dace a yi amfani da su? "Akwai hanyoyi da dama da maza za su iya bi domin kare kai daga samun jaririn da ba a shirya haihuwar sa ba. Bari mu fara da hanyoyi uku da kuka fi sani; Amfani da kwaroron roba sananniyar hanya ce da maza ke amfani da shi domin kare kai daga yin cikin da ba a shirya ma sa ba. Ana ganin kwaroron roba na ba da kariya daga daukar ciki da kashi 98 cikin 100, kuma ita ce kadai hanya daya tilo da ake ganin na bayar da kariya daga kamuwa da cutukkan da ake dauka ta jima'i. Domin tabbatar da an yi amfani da su ta hanyar da ta dace, dole a duba lokacin da za su lalace, da tabbatar da cewa ba ta da wata illa misali budewar ainahin ledar da kwaroron ke ciki. Sannan Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bada shawarar sayan kwaroron roba daga kamfanonin da suke da ke kima, da kuma wadanda asusun Majalisar Dinkin Duniya ya san da su. Duk da amfaninsu, dalilan da ake bayar wa na kin amfani da kwaroron roba ya danganta ne daga tsadarsu ko rashin samun gamsuwa a lokacin jima'i da sauransu. Sassaukar hanya ce amma kuma ba ta da tabbas, saboda kashi 27 cikin 100 na maza wannan lokacin na kubuce musu, kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bayyana. Wannan hanya ita ce ta saurin yin Inzali gabannin lokaci domin kaucewa yin ciki. Hukumar lafiya ta Birtaniya NHS, ba ta aminta da wannan hanya a matsayin ta tsarin iyali ko takaita haihuwa ko kaucewa yin ciki ba. Dalili kuwa shi ne, ruwan maniyyi ka iya fita gabannin lokacin gansuwa yayin jima'in, wanda kankani ne daman ke shiga mahaifa tare da zama Da. Sai dai duk da haka, Moussa Diabaté kwararre a fannin lafiyar kwayayen haihuwa a Senegal, ya bayyana cewa matakin amfani da kwaroron roba, da janye azzakari gabannin fitar maniyyi na da tabbas, domin hanya ce da aka dade ana amfani da ita a kasar, kuma kwalliya na biyan kudin sabulu. Sai dai ga Dakta Mobile Kampanga, kwararren likitan maza a Congo, ya ce ba wannan ce hanyar da ya ke bai wa abokan huldarsa shawarar amfani da ita. ''Hakikanin gaskiya, tsohuwar hanyar da ake amfani da ita ba ta aiki, sakamakon yawancin mazan da suka yi amfani da ita sun bada bayanai mabambanta. Wasu daga ciki sun ce ba za su kara amfani da ita ba, yayin da wasu suka ce sam ba za su gwada yin hakan ba. Ma'aurata, ko abokan rayuwa ka iya sake yin jima'i a karo na biyu, kuma ta yiwu wani daga cikin maniyyin namijin ya makale, sai a lokacin saduwa zai shiga mahaifar mace daga nan kuma ciki ya shiga. Wannan wata hanya ce ta yin tiyata da ta hada yanke hanyar da maniyyi ke bi wajen fita, tare da toshe wajen. Yawanci idan za a yi wa irin wannan tiyatar ana yi wa mutum allurar da ke kafe wani bangare na jiki, ma'ana mutum zai kasance idonsa a bude amma ba zai taba jin zafi ko sanin abin da ke faruwa, kuma aikin na daukar tsawon mintina 15 kacal. Kamar yadda shafin hukumar lafiya ta Birtaniya NHS ta tabbatar, ta amfani da hanyar tiyata kwalliya na biyan kudin sabulu da kusan kashi 99. Ana kallon wannan hanya da dawwamammiya, ko da yake ana iya komawa a sake mayar da komai yadda yake idan bukatar hakan ta taso. Sai dai abin lura a nan shi ne ba a cika amfani da wannan hanyar ba a nahiyar Afirka, kamar yadda Dakta Kampanga ya bayyana cewa yawancin maza ba su yadda da wannan aikin tiyata ba. Ya kara da cewa cikin shekaru 27 da ya dauka yana aiki a matsayin likitan fida da ya shafi mafitsarar maza, sau 10 kacal ya taba yin aikin tiyatar. ''Maza kalilan ne ke yadda da hakan,'' kamar yadda ya shaidawa shashen Afirka na BBC. ""Yawanci na fakewa da mahangar addini domin kaucewa aikin, yayin da wasu ke kaucewa hadarin aikin. Don haka ne suke tilastawa mata shan maganin tsarin iyali, domin su kubuta daga waccan tiyatar.'' BBC ta tattauna da maza a birane daban-daban na Afirka kamar Kwatano, da Kinshasa da Dakar, kan yadda suke kallon maganin tsarin iyali. Ga abin da uku daga ciki suka bayyana, amma mun boye sunayensu saboda ba su kariya. ''Ba na amfani da duk wani nau'in tsarin iyali, kamar yadda muka aminta ni da matata, ba ta damu da shi ba kwata-kwata… Na san hanyar da na ke bi don kaucewa hakan, na san lokacin da ya kamata mu yi Jima'I, da lokacin da zan yi Inzali. ""Ina da 'ya'ya da yawa, da ba ma zan iya kirga yawansu ba, amma na riga na zabi tsarin da ya kwanta min a rai, ba yanzu ne zan dauki mataki ba. Idan matata ta dauki ciki, shi kenan haka Allah ya tsara.'' ''Tun da na yi aure na daina amfani da kwaroron roba. Matata ta san yadda za ta kirga kwanakin da mahaifarta ke budewa da shirin daukar ciki, don haka muna kaucewa yin jima'I a wadannan ranakun. A duk lokacin da muka san akwai hadarin daukar ciki, muna daukar mataki kamar yadda jami'an lafiya ke bayyanawa, wato za mu iya amfani da tsarin yin azalu, matukar ba mu yi hakan ba za ta iya daukar ciki.'' ''Tiyatar tsarin iyali... Tiyatar tsarin iyali.. kai daga jin sunan kadai ya isa bata min rai, sam bai dace ba. Ina da Da mai shekara 1, don haka ina amfani da kwaroron roba a duk lokacin da zan sadu da matata, domin kare ta daga daukar wani cikin, saboda ban amince da sauran hanyoyin tsarin iyali ba.'' A iya cewa baki daya a nahiyar Afirka, maza ba sa amfani da hanyoyin tsarin iyali ko dai na shan kwayar magani ko amfani da kwaroron roba, sai tsiraru daga ciki ne ke bin hanyoyin da jami'an lafiya suka bada shawara domin kaucewa yin cikin da ba a shirya ma sa ba. Misali, Nazari na baya-bayan da asibitin Fartick da ke Senegal ya gano sama da kashi biyu na mazan kasar na amfani da tsarin iyali. Yayin da sama da kashi biyar ke amfani da tsarin Azalu domin takaita haihuwa, sai kuma sama da kashi bakwai da ke amfani da kwaroron roba. Ana ganin hanyoyin kare kai daga daukar ciki, ya dogara ne baki daya akan Mata, ko dai shan kwayar magani, ko sanya zaren da ke toshe bakin mahaifa, domin hana daukar ciki da kidayar lokacin jinin al'ada, ko yin allura, ko maganin gargajiya da sauransu. Dakta Madina Ndoye, kwararriyar likitar mata a asibin Grand-Yoff a birnin Dakar na kasar Senegal, ta ce yawancin bayanin da maza ke yi yana da alaka da addini da al'ada kan batun tsarin iyali, domin haka ne suke fakewa, tare da nade hannu sai dai mata ne kadai suke yin tsain iyali. Wani mutum mai suna Bolozi Kalombo mazaunin birnin Kinshasa ya shaida mana cewa ya haramtawa matarsa shan maganin hana daukar ciki. ''Saboda ina son ganin mata na yin abu da gaske ba kulumboto ba, sannan jikinsu na sauyawa idan suna amfani da magani ko allura da sauran hanyoyin tsarin iyali. Wannan dalilin ne ya sanya ni da matata ba mu amfani da duk wani nau'in tsarin iyali, saboda ni mabiyin addinin Kirista ne kuma littafin mu mai tsarki ya fayyace muna abu mai kyau da maras kyau.'' Ita kuwa Dakta Ndeye Khady Babou ta ce dorawa mata alhakin tsarin iyali ya samo asali ne tun iyaye da kakanni, kuma hakan za a yi ta tafiya kan wannan tsarin. Ta kara da cewa idan har ana son a karfafa maza su yi amfani da hanyoyin tsarin iyali, to dole sai an sauyawa al'umma yadda suke kallon lamarin. ''Idan mutane suka fara Magana kan hakan, masu fafutuka suka ci gaba da daga murya, watakila hakan ya janyo hankalin hukumomi su dauki matakin da ya dace, na tsayar da kan al'umma musamman maza muhimmancin yin tsarin iyali, da sanin ba wai mata kadai ya shafa ba har da mazan.'' Likitar ta yi bayanin cewa dadewa ko yawan amfani da magungunan tsarin iyali ga mata yana da illa da ke janyo wa mata babbar matsala. Sannan kamfanonin da ke yin magunguna a kasashe kamar Amurka da Faransa sun sha gurfana gaban kuliya saboda matsalar da wasu daga cikin matan da suka sha maganin tsarin iyali na kamfaninsu ya samar. Babban malamin darikar katolika, Father Alfred Wally Sarr, jagoran gidauniyar Parish da ke Kounoune a Senegal, ya bayyana cewa a fannin katolika an amince da tsarin iyali ta hanyar duba dumin jikin dan adam, da lokacin shayarwa, da yin azalu matukar ma'aurata sun aminta da hakan. Ya kara da cewa, Cocin katolika ba ta amince da duk wani abu da ya kaucewa koyarwar addinin kirista ba. ''Don me namiji zai sha maganin tsarin iyali? Jin dadin duniya ya ta'allaka ne ga aure da haihuwa. Coci na bai wa ma'aurata kwarin gwiwar yin tsarin iyalin da bai sabawa addini ko al'ada ba, '' in ji Abbé Alfred. Sai dai Imam Ahmadou Makhtar Kanté, ya ce addinin musulunci ya amince da tsarin iyali idan dukkan bangarorin biyu sun aminta da hakan. Sai dai wasu na ganin cewa, idan aka zo batun yin tiyata ko dandaka addinin musulunci bai aminta da hakan ba. Imam ya kara da cewa; ''babu wanda yake da ikon sauya yadda wani bangare na jikin dan adam yake yin aiki da sunan tsarin iyali. ""Dole mu maida hankali kan hanyoyin da ba su haramta ba kuma aka amince da su, domin samun ingantaccen sakamako, hanyar da ba za ta cutar da kowa ba. Amma bisa dalilai na kiwon lafiya, addinin musulunci ya amince da yin aikin tiyata. Ana ci gaba da gwaji da nazari kan hanyoyi da dama na tsarin iyali a sassa daban-daban na duniya. Wato amfani da kwayar magani ko sauyin jiki na Homourns(CHM) Sama da shekaru 50 kenan da masana kimiyya suka dukufa suna nazari, sai di har yanzu kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba, kuma babu ko guda daya da aka fitar kasuwa. Masana kimiyyar sun yi gwajin maganin tsarin iyali kan maza 100, sakamakon yana nuna ana da kyakkyawar fata, kamar yadda Farfesa Stephanie Page ta jami'ar Washington daya daga cikin marubutan nazarin da aka wallafa a shafin intanet na Endocrine Society ta bayyana. Wani nazari da hukumar lafiya ta duniya WHO ta yi a shekarun 1990 zuwa 1996, ya nuna tasirin da allurar CHM ta mako-mako mai adadin mili giran 200 ga maza za ta yi gare su. Wani bincike da China ta guda har sau biyu, a shekarun 2003 zuwa 2009, ya yi bayani kan ingancin yi wa maza tsarin iyali ta hanyar allura daya cikin watanni hudu. Dakta Mobile Kampanga, ya shaida mana cewa likitoci ba sa bayar da shawarar yin allurar saboda illarta da ta ke yi a sauyin halittar dan adam, da rashin tabbas ga wanda aka yi wa. Wata hanya da maza ke amfani da ita wajen kayyade iyali ita ce ta hanyar sanya matsattsen duros, na akalla sao'i 15 a kowacce rana na tsahon watanni uku, da nufin dumama maniyyin yadda ba zai yi tasirin fitar da kwan haihuwa ba. Wannan tsari ya nuna tasiri kan mazaje 51 da akai gwaji akan su, daya daga ciki ne kadai aka samu kuskure ciki ya shiga, shi ma din bai yi amfani da tsarin yadda ya dace ba, kamar yadda kungiyar likitocin fidar mafitsara na kasar Faransa suka bayyana. Wata kungiya mai zaman kan ta a Amirka, Parsemus Foundation ta dade tana nazari akan allurar da ake yi wa 'ya'yan gwailo, wadda a hankali cikin shekaru take yin tasirin toshe hanyar da maniyyi ke fita. Hanya ce mai sauki kuma marar hadari da za a iya sake yin wata allurar domin narkar da toshewar, kamar yadda kungiyar likitocin fidar mafitsara na kasar Faransa suka bayyana. Kawo yanzu an yi gwajin allurar kan Birrai da zomaye, kuma alamu sun nuna tasirinta, amma sai har yanzun ba a samu cikakken sakamako kan sake yin allurar da kuma narkar da toshewar hanyar da miniyyin ke fita ba. Maganin da ake shaka Tun shekarar 2016 masu bincike a Birtaniya suka dukufa domin nazari, kan maganin tsarin iyali na shaka, da zi yi tasirin rage karfin maniyyi. Wannan aikin wasu kwararru biyu ne na jami'ar Wolverhampton, Farfesa John Howl da Dakta Sarah Jones. Sun yi aikin hadin gwiwa da jami'ar Aveiro, ta Portugal, a wani bangare na binciken shekaru uku da aka warewa Yuro 194,000 domin aiwatar da shi, domin gano illar da maganin shakar ka iya yi wa kwayoyin halittar dan adam, da yadda za su kayyade maniyyin da namiji ke fitarwa." https://www.bbc.com/hausa/labarai-59293876 +health Coronavirus: China za ta taimaka wa Najeriya da kasashen Afirka "Gwamnatin China ta ce a shirye take ta taimaka wa Najeriya da sauran kasashen Afirka idan cutar Coronavirus mai shafar nimfashi ta bulla a nahiyar. Jakadan kasar China a Najeriya, Zhou Pinjian ne ya sanar da haka yayin wata ganawa da manema labarai a ofishin jakadancin kasar da ke Abuja. Ya bayyana cewa: ""China na kokarin samar da mafita ga wannan annobar kuma ko bayan annobar ta shude, za ta ci gaba da duba hanyoyin da za ta taimaka wa kasashen Afirka domin mun dauki dangantakarmu da Afirka da muhimmanci. ""A fadin kasar ta China, mutum 17,205 ne aka tabbatar sun kamu da cutar kuma fiye da 17,200 a ke hasashen suna dauke da kwayar cutar ta coronavirus mai shafar numfashi, wadda kawo yanzu ba a sami maganinta ba ballantana rigakafi."" in ji Pinjian. Jakadan ya ce akwai 'yan China kusan mutum 40,000 zuwa 50,000 da ke zaune a Najeriya saboda dalilan kasuwanci kuma akasarinsu suna zaune ne a Legas da ke yankin Kudu maso Yammacin kasar. A cewarsa, kimanin 'yan Najeriya 60 ne a yankin Wuhan - garin da annobar ta coronavirus ta bulla a kasar China. Ya ce mafi yawan 'yan Najeriya sun fi zuwa birnin Guagzhou ne da ke Arewa maso Yammacin yankin Hong Kong. Jakada Pinjian ya kuma nuna jimami kan irin asarar da kasar ta China da kasashen duniya ke fuskanta sakamakon annobar coronavirus. Mutum na farko da ya mutu sakamakon cutar a wajen China ya rasu ne a kasar Philippines. Tuni dai hukumar lafiya ta duniya WHO ta ayyana cutar a matsayin babbar annoba a duniya." https://www.bbc.com/hausa/labarai-51356162 +health An gano maganin ciwon so "Wani mai bincike ya ce ya samo hanyar da za a magance damuwar da ke biyo bayan rabuwa da masoyi ta hanyar bayar da shawarwari da lallami da kuma shafe tunanin wannan masoyin. Dakta Alain Brunet, ya shafe fiye da shekara 15 yana nazari a kan irin damuwar da ke biyo bayan rabuwa da masoyi ko masoyiya inda ya yi aiki tare da kwararru kan soyayya da kuma wadanda suka taba shiga irin wannan matsala. A binciken nasa dai ya fi mayar da hankali a kan yadda za a lallashe shi tare da bayar da shawara ga wanda ya shiga matukar damuwa bayan rabuwa da masoyi/masoyiya. Ya gano cewa kwayar propranolol ita ce kwaya mafi dacewa da mutum zai yi amfani da ita wajen maganin hawan jini da ciwon zuciya da ciwon kai mai tsanani idan ya tsinci kansa a cikin damuwar so. A tsarin bayar da shawarwari, idan mutum ya samu kansa a cikin ciwon so, ana so mutumin ya fara shan kwayar Propranolol awa daya kafin a fara bashi shawarar da kuma lallashi. Idan aka zo wajen bayar da shawarar, akan fara sa mutum ya rubuta irin abin da ke damunsa, sannan kuma ya karanta da karfi idan ya kammala rubutun. Wani likitan kwakwalwa dan kasar Canada, ya shaida wa BBC cewa, "" irin wannan karatu da karfi zai sa mutum kwakwalwarsa ta bude sosai, sannan kuma idan akwai abin da ya manta zai iya tunawa"". Irin wannan tsari wata dama ce ga wanda ya tsinci kansa cikin wannan matsala ya samu sauki a kan abin da ke damunsa. Dr Brunet ya ce "" Muna amfani da wannan hanya wajen fahimtar ya yanayin matsalar mutum ta ke, ta ina za a fara magance ta da kuma yadda mutum zai manta da duk wata damuwar soyayyar da ya shiga"". Yawanci kwakwalwa na rike abubuwa da dama kamar abubuwa na hakika, amma kuma abin tausayi ko na ban haushi shi ma kwakwalwa kan rike shi sosai. Kwayar propranolol na taimakawa matuka gaya wajen rage radadin damuwar so ko tunanin abubuwan da suka faru a lokacin da mutum ke kan ganiyar soyayya. Dakta Brunet ya ce a binciken da ya yi, za a iya samun kaso 70 cikin 100 na mutanen da suka shiga cikin damuwar so da za su warke ta hanyar basu shawarwari akai-akai amma ba sai an dauki dogon lokaci ba. A kwanakin baya-bayannan, likitan ya kaddamar da wani shiri a Faransa wanda ya taimaka wajen farfado da wadanda mummunan harin nan na birnin Paris ya rutsa da su. Ya taimaka wa wadannan mutanen ne ta hanyar ba wa wasu likitoci 200 horo na musamman a kan yadda za su rinka kula da irin mutanen da harin ya rutsa da su inda ya koyar da su yadda za su rinka ba su shawarwari da lallami da dai sauran dabaru domin mantawa da wani mummunan abu da ya samu mutu. Ya zuwa yanzu, an yi wa fiye da mutum 400 maganin damuwarsu ta hanyar lallami da shawarwari kamar yadda Dakta Brunet ya tsara. Dakta Brunet ya ce wasu da suka tsinci kansu a irin wannan matsala, sukan halarci wajen bayar da shawarwari sau biyar kafin su warke daga ciwon so, ma'ana kafin su manta da damuwar da suke ciki ko kuma su daina tunanin da suke yi a kan masoyi/masoyiya. A yanzu haka Dakta Brunet na da ma'aikatan da ke taimaka masa wajen warkar da wadanda suka fada cikin kogon so guda 60, kuma yawancinsu wadanda suka warke ne daga irin wannan cuta ta ciwon so. Ya ce yana fata zai fadada wajen bayar da shawarwarinsa tare da fadada ayyukansa nan ba da jimawa ba." https://www.bbc.com/hausa/labarai-51543162 +health Da gaske an gano maganin Coronavirus a Najeriya? Shugaban hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya, NCDC, Dakta Chikwe Ihekweazu ya yi watsi da ikirarin tsohon Shugaban Hukumar zabe ta Najeriya Farfesa Maurice Iwu na cewa ya gano maganin cutar Coronavirus. Dakta Chikwe ya bayyana wa BBC cewa babu yadda za a yi a gano maganin cutar da ba ta dade da bulla ba a duniya. Ya ce sabuwar cuta ce kuma ba a taba sanin da ita ba ko a fannin lafiya, sai watanni biyu da suka gabata. Hakazalika ya ce kafin a gane tasirin maganin dole sai an gwada kan marasa lafiya, wanda da yawansu a China suke. Farfesa Iwu ya yi ikirarin gano maganin cutar ta numfashi, wadda ta kashe fiye da mutum 3,000 a fadin duniya, inda kuma kasarsa Najeriya ta kasance cikin kasashen da cutar ta bulla. A ranar Litinin Farfesa Maurice Iwu, wanda ke shugabantar cibiyar bincike ta Bio-Resources Institute of Nigeria, ya gana da ministan lafiya da na kimiyya domin neman tallafinsu kan maganin da ya ce ya gano. Tun da cutar ta bulla a China shekarar da ta wuce, babu wani maganinta da aka amince da shi. Ya zuwa wannan lokaci, cutar ta kashe fiye da mutum 3,000 a fadin duniya, inda kuma Najeriya tana cikin kasashen da cutar ta bulla. Sai dai hukumar dakile bazuwar cututtuka a Najeriya NCDC ta ce gwamnati ta shirya gina wurin gwaji da kula da kuma kebe masu cuta a dukkanin jihohin kasar. A karshe ya ce gwamnatin kasar za ta fitar da wasu ka'idoji domin makarantun da ke sassan kasar. https://www.bbc.com/hausa/51725659 +health Ko kun san nau'in abincin da ke inganta rayuwar aure? "Inda akwai kwararan hujojji masu bayyana yadda wani takamaimen abinci zai iya bunkasa gamsuwa yayin jima'i, da zai yi kasuwa sosai. Cin abinci mai kyau da motsa jiki da kuma yawaita tunani mai kyau za su iya inganta rayuwar aurenku. Amma shin gaskiya ne cewa akwai nau'in abincin da za su iya bunkasa rayuwar taku ta aure? Sinadaran abinci wadanda ke dauke da kwayoyi masu faranta wa mutane rai sun kunshi wasu abubuwan gina jiki masu alaka da bunkasa gamsuwa ko kuma arziki. Ana tunanin cewa wadanan sinadaran za su iya bunkasa gamsuwa yayin jima'i. To bari mu duba tarihi ko akwai abin da ke goya wa wadanan ka'idojin baya, sai mu gani ko sinadaran za su iya bunkasa gamsuwa yayin jima'i. Shin cin kumba (oyster) na aiki? An kiyasta cewa Casanova, wanda ake yi wa lakabi da dan soyayya mafi shahara a tarihi yana cin kumbuna 50 a kullum a matsayin karin kumallo. Sai dai babu wata tabbatacciyar alaka tsakanin kumbuna da habaka gamsuwa yayin saduwa. To ina wannan labarin ya samo asali? Masana na cewa lokacin da aka haifi Aphrodite - wato abar bautar soyayya - ta bullo ne daga cikin kumfar ruwan teku... shi yasa ake kiyasta cewa naman ruwa zai iya bunkasa gamsuwa yayin jima'i. Amma bari mu bai wa masu kaunar kumba wani labari mai dadi, akwai sinadarin zinc a kumba sosai, wato wani abin gina jiki mai habaka sinadarin halittar da namji wato testosterone. Bincike ya nuna cewa sinadarin zinc zai iya taimakawa wajen magance matsalar rashin haihuwa tsakanin maza da kuma kara yawan maniyyin da namiji ke samarwa. Ga kuma wasu abubuwan da za a iya samun sinadarin zinc a cikinsu: Akwai jan nama da naman ruwa masu kwanso da 'ya 'yan kabewa da gyada da kuma madara. Cin cakulet mai duhu zai iya sanyawa ka ji kamar ka fada soyayya a cewar masu bincike, saboda cakulet tana dauke da sinadarin soyayya wato ""phenylethylamine"" (PEA). Sinadarin PEA yana yawo a cikin jikin mutum a watannin farko da mutum ya shiga soyayya - yana habaka jin dadi a ran mutum wanda kuma ke da alaka da bangaren nishadin kwakwalwa. Sai dai sinadarin PEA kadan kawai ake samu a cakulet, kuma har yanzu ba a tabbatar da ko sinadarin na aiki idan an sha cakulet ba. Ana kuma iya samun sinadarin amino acid tryptophan a koko, wanda ake cewa yana bunkasa gudanar jini da kuma sinadarin serotonin wanda shi ma ke habaka farin ciki. To amma yaushe aka samu alaka tsakanin cakulet da bunkasa gamsuwa yayin saduwa? Ana ganin cewa ya fara ne a karni na 16. Hernán Cortés wani sojan karni na 16 dan kasar Sifaniya ne wanda ya jagoranci yaki zuwa cikin Masarautun Maya da Aztec, kuma ya kwace dukkannin yankunan da aka fi sani a Mexico yanzu a karkashin mulkin sarautar Castile. Ana kuma tunanin cewa shi ne Baturen farko da ya ga cakulet. Ya rubuta wasika zuwa sarkinsa cewa ya ga Masarautar Maya suna shan wani hadin koko wanda ke kara wa jiki karfi kuma yake kore gajiya. Amma dattijai a Masarautar Castilia sun alakanta amfanin cakulet da wasu abubuwa daban da 'yan Masautar Maya ba su sani ba su ma, kuma babu wata kwakkwarar hujja mai nuna cewa ana iya amfani da cakulet wurin inganta gamsuwa yayin saduwa. Ga wasu abubuwan da ake iya samun sinadarin tryptophan cikinsu: kifi da kwai da gyada da alayyahu da kaji da 'ya'yan itace da kuma abincin da aka samu daga waken suya. Dafaffen attaruhu na dauke da sinadarin capsaicin, wanda bincike ya nuna cewa yana samar da sinadarin endorphins (wanda ke samar da jin dadi a cikin jiki). Sannan kuma yana temakawa wajen sarrafa abinci a jiki kuma ya kara yawan zafin jiki da kuma bugawar zuciya cikin sauri kamar yadda muke ji yayin saduwa da iyali. Amma kar ku manta da wanke hannayenku bayan amfani da shi! Giya kan taso wa mutum da sha'awa ta hanyar dauke masa kunya, amma kamar yadda tauraron littafin adabin nan na Turanci Macbeth ya fada tana ""tana saka wa mutum sha'awa kuma a lokaci guda ta rage masa karfi"". Sha'awa tsakanin maza da mata kan ragu idan aka sha giya da yawa daga bisani kuma ta dauke wa mutum sha'awar baki daya. Kuma ma dai warin giya ba zai bar mutum sukuni ba a gado. Bincike ya nuna cewa abinci mai dauke da wasu sinadarai da ake samu daga ganyayyaki yana taimaka wa jikin mutum yayin jima'i, kuma ya magance cutar daukewar sha'awa da ake kira erectile dysfunction (ED). Binciken ya tabbatar cewa sinadaran anthocyanin, wanda ake samu a dan itaciyar blueberry da kuma wadanda ake samu a itacen citrus, suna magance ED. Yiwuwar kamuwa da cutar ED tana raguwa da kashi 14% idana ana cin abinci mai dauke da sinadaran da ke cikin ganyayyaki, inda shi kuma motsa jiki ya rage wa da kashi 21%. Saboda haka, maza ku cika cikinku da kayan marmari! Wasu masu binciken sun nuna cewa abincin yankin tekun Bahar Rum (Mediterranean Sea) suna bayar da kariya daga ED saboda kusan baki dayansu na ganye ne da 'ya'yan itatuwa. Kayan kara karfin sha'awa Za a iya kasa kayan kara sha'awa na Aphrodisiacs zuwa kashi uku: wadanda suke taimaka wa azzakarin namiji da wadanda ke bayar da karfi yayin jima'i da kuma gamsuwa yayin jima'i. Sai dai a kimiyyance ba a tabbatar da cewa ko suna aiki a kan dan Adam ba saboda karancin ma'aunin da za a iya auna nasararsu. Hasali ma, wanda aka tabbatar yana aiki shi ne kanshin 'ya'yan itatuwa nunannu da kuma rubabbu kuma su ma suna aiki ne kawai ga kwarin da suke cin itatuwan. Dr Krychman masani ne kan ilimin jima'i. Ya ce mutane suna cin kayan kara karfin sha'awa ne kawai saboda sun yi imanin cewa za su yi masu aiki, sannan ya ce idan abu yana yi maka aiki ai ba sai ka tambayi dalili ba. Akasarin abin da ake kira kayan kara karfin sha'awa ba su da illa amma ana bayar da shawarar a kauce wa duk wani abu da ba na 'ya'yan itatuwa ba musamman magungunan komai-da-ruwanka. Sharadi Idan kana fama da matsalar daukewar sha'awa da alama kana fama ne da wata cuta. Saboda haka ana so a ko da yaushe a rika tuntubar likita." https://www.bbc.com/hausa/labarai-49003506 +health Ranar sikila ta duniya: 'A tabbatar an yi gwajin jini kafin aure' "Latsa hoton da ke sama domin kallon wannan bidiyon A ranar Lahadi, 19 ga watan Yuni ce ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin masu fama da cutar amosanin jini wato sikila. An ware ranar ce domin wayar da kan al'umma muhimmancin kula da masu fama da cutar da kuma taimaka musu. Albarkacin ranar ta bana, Hajiya Badiyya Magaji Inuwa mai gidauniyar Sickle Cell Patient Health Promotion Centre da ke kula da masu lalurar amosanin jini a Najeriya ta ce abu mafi muhimmanci shi ne mutane su rika yin gwajin jini kafin su yi aure domin hana kamuwa da cutar. ""Da ka ja wa kanka wahala gwamma a rika auna jini, domin da muguwar rawa gwamma kin tashi. Muna rokon mutane su ci gaba da gwaji domin babu dadi ka haifi yaro ya rika shan wahala a duniya,"" a cewarta. Hajiya Badiya ta kara da cewa dawainiyar masu sikila akwai matukar wahala, domin samun sauki gwamma mutane su yi gwaji tun farko. ""Hadarin samun da mai sikila yana da wahala, domin ba shi magani da dawainiyar asibiti ma abin tausayi ne""." https://www.bbc.com/hausa/shirye-shirye-na-musamman-61856454 +health Lafiya Zinariya hira da likita kan Cutar tsananin damuwa Cutar tsananin damuwa na shafar mutane ta hanyoti daban-daban kuma ta kan zo da alamomi da dama. Sai dai alamin da aka fi gani su ne tsananin bakin ciki da yawan kuka da kebe kai daga cikin mutane. https://www.bbc.com/hausa/shirye-shirye-na-musamman-54664885 +health Ko ana iya warkewa daga cutar sikila? "An ware ko wane 19 ga watan Yunin kowace shekara don wayar da kan mutane kan cutar sikila ko amosanin jini da hanyoyin magance ta. Amosanin jini, cuta ce da ake gado daga kwayoyin halittar iyaye, inda suke haduwa su fito ba dai-dai ba, a jikin dan da suka haifa. kwayar halittar na fitowa da siffar lauje maimakon a kewaye kamar yadda ya dace. A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya, rikirkicewar kwayoyin halittar na janyo daskarewar jini a kananan jijiyoyi a cikin jikin mutum, wanda hakan ke jinkirta wucewar jini da iskar oxygen da aka harba daga wani bangare na jiki zuwa wani. Daskarewar jinin na janyo matsanancin radadi a baya da kirji da hannuwa da kafafuwa. Najeriya da daya daga cikin kasashen duniya da aka fi samun wannan cutar musamman ma a arewacin kasar. A cewar Farfesa Aisha Indo Mamman wata kwararriyar likita kan cututtukan da suka shafi jini a asibitin koyarwa na Jami'ar Ahmadu Bello Zaria , ana haifar jarirai dubu 150 da cutar, a kowace shekara. Masu fama da cutar na yawan gajiya, sannan su kan nuna alamun jikkata ko rashin kuzari. Haka kuma idanuwansu da fatarsu kan sauya zuwa kalar ruwan kwai. Cutar sikila na da alamomi da dama wadanda suka hada da rashin jini da ciwon jiki mai tsanani wanda ka iya janwo matsaloli kamar jiri da ciwon kirji da bugun zuciya da ciwon koda da dai sauransu. Haka kuma gabobi na lalacewa dalilin wannna cuta sannan tana sa rashin girman jiki da yawan samun raunuka musamman a kafa. A kasahe kamar kamaru da Jamhuriyar Congo da Gabon da Ghana da Najeriya, yawan afkuwar cutar yana kai wa kashi 20 cikin dari zuwa kashi 30 cikin dari. Wata mai fama da cutar, Aisha Saleh ta yi wa BBC bayani kan yadda take ji idan ciwon ya tashi inda ta ce misalta radadin ciwon sikila ba zai misaltu ba, sai dai ayi kwatanta. ""Radadi ne a cikin kasusuwanmu, misali kafa ko hannu ko baya. Idan a kafa ne ciwon ya tashi sai ka ji kamar ana sara kafar ko ana raba ta biyu. Radadi ne mai wahalar fassarawa."" a cewar Aisha. Ta kuma ce tana fuskantar kalubale da dama musamman a bangaren karatu dalilin cutar sikilan. Ta ce ciwon ya kan tashi a lokuttan jarabawa wanda har ya kan ja ta gaza zana jarabawar. ""Sai dai ina samun taimako daga wajen iyaye na da 'yan uwana maza da mata."" a cewarta. Farfesa Aisha Indo Mamman ta ce har yanzu mutane na da karancin sanin girman cutar sikila. Ta ce mutane sun dogara da camfi da danganta cutar kan aljannu ko maita. Sai dai ta ce ba a warkewa daga wannan cutar ta sikila har abada, illa dai a samu sauki ko kuma a gujewa kamuwa da ita ta hanyar yin gwajin kwayoyin halitta kafin ayi aure. ""Wadanda suka ce sun warke sau da yawa sun dauki wani mataki ne na dashe bargo, a bisa fahimtar kimiyya."" Ta ce akan dauki bargon dan uwa ko iyaye ko wani makusancin mai fama da cutar sai a dasa masa, kuma daga nan idan aka yi nasara an rabu da cutar kenan. Sai dai ta ce bayan dashen, mai fama da cutar ne kawia zai samu kariya daga amosanin jinin amma za su iya haifar 'ya'ya masu dauke da cutar." https://www.bbc.com/hausa/labarai-48689867 +health Abin da ya kamata ku sani game da atishawa "Yadda atishawa takan zo wa mutum kwatsam ba shiri, wasu ke alaƙanta hakan da mugun abu ko ma kusa da mutuwa. Likitoci sun ce atishawa wani yanayi ne da ke kare huhu a lokacin da wani abu da ba iska ba ke ƙoƙarin shiga. Iska ce kawai aka yarda ta shiga cikin huhu - idan akwai wani abu da ya zo kusa da hanci wanda ba iska ba ne shi ita za ta yi kokarin fitar da shi da karfi, wanda hakan ke haifar da atishawa. A wani cikakken bayani da ta wallafa game da atishawa Mujallar lafiya ta Healthline ta ce atishawa taimako ne ga jikin ɗan Adam, kuma yawanci ba ta zama sanadin wata babbar matsala ga lafiya. Mujallar ta ce atishawa hanya ce ta fitar da wasu abubuwa da ba su dace ba daga hanci ko makogaro. kuma takan zo da ƙarfi lokacin fitar da iska ba tare da mutum ya shirya ba. Ɗaya daga cikin aikin hanci shi ne tsabtace iskar da muke shaƙa, wato tabbatar da ba datti ko wata cuta. Wani lokaci kuma datti zai iya shiga hanci ya zama matsala wadda kuma ke haddasa atishawa. Wasu na cewa atishawa ta fi kusa da mutuwa saboda yadda mutum ke fita hayyacinsa. Amma likita ya ce magana ce kawai ake faɗi a likitance ba haka ba ne. Ya ce atishawa kamar kariya ce ga lafiyar mutum amma sai jiki ya yi ƙoƙari ya fitar da karfi. ""Ba batun mutuwa ba ne batun ƙarin lafiya ne."" ""Ana fita hayyaci ne saboda maƙoshi yana rufewa cikin daƙiƙa amma da an yi atishawa sai ya buɗe."" ""Ba a son wani abin da ba iska ba ya shiga shi ya sa wurin ke rufewa shi ya sa mutum yake ji kamar sheƙawa lahira zai yi,"" in ji Dr Manya. Abubuwa da dama ne ke haddasa atishawa, kamar yadda Dr Celeb Manya kwararen likita a babban asibitin Gusau a jihar Zamfara ya bayyana. Abubuwan sun haɗa da tsarin yanayin jikin mutum da cutuka kamar mura da shaƙar sinadarai kamar turare da sauransu. Masu bincike a Jami'ar Saarland sun ce a binciken da suka gudanar wasu mutane sun ce sukan yi atishawa da zarar sun ci abinci sun ƙoshi. Haka kuma wasu sun ce sha'awar jima'i ma tana saka su shiga yanayin atishawa. Bisa ga yanayin jikin mutum- abin da bai dace da jiki ba sai ya sa mutum ya shiga damuwa yana atishawa sosai. Likitan ya ce wasu yadda jikinsu yake ba ya son suna kusa da wasu abubuwa, kamar ƙura daga shara ko hayaƙi inda ake abinci ko ƙamshin wani abu wasu kuma daga dabbobi kamar mage da kaji idan sun kusance su, za su dinga atishawa - wasu kuma har Kyankyaso yana saka su atishawa. Wani yakan yi atishawa a lokaci guda, wani kuma zai dinga yi da yawa a lokaci guda wanda ke nuna akwai matsala. Sannan atishawa takan zo da ƙaiƙayin ido da makogaro wata kuma har da majina. ""Wanda zai yi so ɗaya bai ƙara ba, wannan ba damuwa ba ne amma wanda zai yi fiye da biyu ko uku - irin wannan akwai bukatar ya ga likita,"" in ji Dr Manya. Ya ƙara da cewa akwai wasu nau'ukan atishawa da suka bambanta da wadanda aka fi yi kuma tsarinsu daban yake. Kamar masu ninkaya suna da nasu nau'in atishawa da suke wanda wurin iska yake toshewa saboda ba a son ruwa ya shiga. Mutane kan yi kokarin rike atishawa saboda tsarguwa a cikin jama'a ko wasu dalilai nasu. Wasu kan buɗe baki iskar ta fita a hankali wasu kuma za su riƙe har atishawar ta tafi a hankali. Amma Likitoci sun ce ba a iya rike atishawa idan har ta zo. Abu ne mai wuya riƙe atishawa ya zama sanadin ajalin mutu, kamar yadda likita ya bayyana. Ko da yake Mujallar Lafiya ta Healthline ta ce duk da ba ta taɓa cin karo da rahotannin cewa atishawa ta kashe wani mutum ba amma ba za a ce ba zai yiwu mutum ya mutu ba sakamakon riƙe atishawa. Ta ce matsalolin da za a iya samu sakamakon riƙe atishawa za su iya muni sosai, kamar matsalar ƙwaƙwalwa da fasa makogaro da matsalar huhu, waɗanda dukkaninsu za su iya munin da za su iya haifar da mutuwa. A cewar Dr Manya, idan mutum ya rike atishawa ya hana wa kansa fitar da wata cutar da ya kamata ya fitar. Ya ce abubuwan da ke sa mutum yin atishawa ƙanana ne da ba su da mummunar illa ga mutum, kamar kura sai idan masu ciwon asma. ""Hana fitar da ƙanana ciwo zai iya haifar da babban ciwo"" Mujallar lafiya ta Healthline ta ce akwai aƙalla mutum ɗaya da ya taɓa fasa makogaronsa ta sanadin riƙe atishawa, wanda har ta kai ba ya iya magana ko haɗiye abinci. Sauran matsalolin d riƙe atishawa ke haifarwa da mujallar ta bayyana sun haɗa da karya haƙarƙari da matsalar kunne da ido da hanci. Lokacin da mutum yake atishawa likita ya ce mutum yana samun raguwar bugawar zuciya sannan jinin shi zai sauka. Ya ce misali idan bugun zuciyar mutum ya kai sau 100 a minti daya - lokacin da za a yi atishawa zai sauka zuwa 90 ko 80, haka ma jinin mutum yana sauka. Mujallar lafiya ta ce atishawa ba ta haifar da bugawar zuciya, illa kawai bugawar zuciyar na raguwa. Atishawa kamar yadda likitoci suka bayyana hanya ce ta kariya ga lafiya, kuma yawancin lokaci riƙe atishawa ba ya haifar da wani mummunan abu da ya wuce ciwon kai da ciwon gaɓɓai, amma a wani lokacin riƙewa kan yi muni. Abin da ya kamata shi ne mutum ya kauce wa abin da zai sa atishawa, kuma a bar jiki ya yi atishawa a lokacin da ya buƙata." https://www.bbc.com/hausa/labarai-59062879 +health Amfanin yalo da muhimmancinsa ga lafiyar jikin dan adam Bincike da dama da masana suka gudanar ya nuna cewa yalo ya samo asali ne daga kasashen India da kuma Afirka, amma kuma yanzu ana noma shi a fadin duniya. A Najeriya an fi noma yalon ne a yankin arewacin kasar inda akan kuma same shi a kasuwanni daban-daban a fadin kasar. Za a iya cin danyensa wanda wasu sukan hada da soyayyiyar gyada ko su rika dangwalawa a hadadden garin yaji ko kuma soyayyiyar miya su rika ci. Daya daga cikin abubuwan ban mamaki game da yalo shi ne yana fitowa a nau'uka daban-daban, wanda ya danganta da yanayi da kuma wurin da ake nomawa. Yana kuma fitowa a launuka da kuma fasali da girma da kuma dandano daban-daban. Akan samu masu launkan fari, da ruwan goro, da kore, da algashi da dai wasu launuka. A kudancin jihar Borno arewa maso gabashin Najeriya akwai kabilar Baburawa da kan yi amfani da gauta wato daya daga cikin nau'in na yalo wajen abinci, su kan rika hadawa da tuwo suna gutsura suna ci. Malama Adama Hassan wacce 'yar kabilar Babur din ce da ke zaune a garin Biu na jihar Borno inda Baburawan suka fi yawa, ta shaida wa BBC cewa suna matukar muhimmantar da Yalo ko data, ko kuma gauta a matsayin cimaka. ''A ko da yaushe ba za ka taba rasa gidan Baburawa da gauta ko yalo ba, saboda muna hada shi da abinci, musamman tuwo, yana a matsayin miya ne, mu kan rika gutsurar shi mu hada da tuwo muna ci.'' Galibin mutane na cin Yalo ne kawai don nishadi ko kashe yunwa ba tare da fahimtar irin dimbin amfanin da yake da shi a jikinsu ba. A nan za mu duba amfanin yalo da kuma muhimmancin sa a jikinmu. Ba zai yiwu mu kawo duka ba, to amma za mu tsakuro kadan daga cikin amfaninsa: Kamar yadda mujallar kiwon lafiya ta Medical News Today da ke Amurka ta wallafa, binciken da masana da dama suka gudanar game da yalon ya nuna cewa yana da matukar amfani ga lafiyar jikin dan adam kamar yadda 'ya'yan itace suke da shi. 1. Rage kiba Kamar yadda Mis Megan Ware wata kwararriya a fannin abinci mai gina jiki a Amurka kuma manomiyar kayan lambu ta wallafa a mujallar Medical News Today, yalo na da matukar amfani wajen rage kiba saboda yana kunshe da sinadaran da ke taimaka wa kona kitsen jikin mutum wanda kan sa a rage kibar. Malama Husna Abubakar wacce ke zaune a garin Abuja babban birnin Najeriya ta shaida wa BBC cewa maigidanta wanda ke da kiba sosai ba ya rabuwa da sayen yalo saboda yana da yakinin cewa yana da matukar amfani wajen rage kiba. ''Na ga yana yawan sayen yalo kuma yakan saka ni in yanka masa kanana kamar yadda ake yanka su kankana in kawo masa a ko wane dare ya ji kafin ya kwanta,'' in ji Husna. 2. Kare garkuwar jikin dan adam Kamar yadda mujallar Healthline ta Birtaniya ta wallafa a wata majalar kiwon lafiya, sinadaran Anthocyanins, da nasunin da kuma flavonoids sinaran kashe kwayoyin cuta ne masu karfi da ke kunshe cikin yalo da kuma kan taimaka wajen bayar da kariya ga garkuwar jikin dan adam tare da kara inganta lafiyar jikin. Sinadarin Anthocyanins na tainama wa wajen bayar da kariya daga yaduwar kwayoyin halittar da ke haddasa cutar kansa har ma da sauran cututtukan da kwayar cutar bacteria ke haddasawa. 3. Inganta aikin jijiyoyin jini Yalo yana kunshe da sinadaran vitamin B kamar su thiamin, da niacin, da B6 da kuma pantothenic acid wadanda ke taimakawa wajen amfani da sinadaran fat da na protein; kana suna bayar da gudumawa mai amfani ga hanyoyin jijiyoyin sadarwar kwakwalwa. Sinadarin vitamin B na taka muhimmiyar rawa wajen inganta kiwon lafiya. Yana taimaka wa wajen inganta aikin kwakwalwa tare da tabbatar da cewa hanyoyin jijiyoyin sadarwar kwakwalwa da na garkuwar jikin dan adam na aiki yadda ya kamata. 4. Karfi da lafiyar kashi Saboda sinadaran minerals irin su folate, da manganese, da vitamin K, da magnesium, da vitamin da kuma Copper da yalon ke kunshe da shi, yana taimaka wa wajen kara karfi da lafiyar kasha in ji Mujallar Medical News Today ta Amurka. Cin yalo a ko da yaushe yana da matukar muhimmanci wajen bayar da kariya daga hadarin lalacewar kashi da kuma rashin kwarin kashi. 5. Narkar da abinci a jiki Kamar yadda bayanai suka nuna daga farko, yalo na da sinadarin da ke taimaka wa sosai wajen narkar da abinci a jikin dan adam (fibre) tare da taimakawa a yanayin yin bayan gida. Saboda wannan sinadarin da ya kunsa, suna rage yawan kumburin ciki da rashin yin bayan gida sosai ta hanyar inganta narkewar abincin. Sinadarin na matukar taimakawa a lafiyar cikin dan adam da kuma motsawar dattin ciki da yin bayan gida cikin sauki. 6. Amfani ga mata masu juna biyu Wannan cimaka na kunshe da sinadaran minerals, da vitamins da kuma sauran abubuwan gina jiki da ke taka muhimmiyar rawa a lokacin da mace ke dauke da juna biyu. Abubuwan da ke kunshe cikin yalo na taimaka wa mata masu juna biyu da jariran da ke cikinsu wajen kasasncewa cikin koshin lafiya. Suna kuma kunshe da sinadarin folic acid wanda ke da amfani ga masu juna biyu. Folic acid na bayar da kariya ga jarirai daga samun wata tawaya ta wasu lokuta kan faru. 7. Bayar da kariya daga matsalar karancin jini Masana sun gano cewa yalo ka iya zama wani magani na warkar da cututtuka kamar na numfashi, da kumburin ciki, da ciwon kai, da sauran su idan ana ci a ko da yaushe. Yalo kan taimaka wajen kara yawan kwayoyin halittar jini a jiki, don haka yana yaki da matsalolin da ke haddasa karancin jini ko kuma sinadarin iron. Yana kuma kunshe da sinadaran copper, tare da taimakawa wajen inganta kara yawan zagayawar kwayoyin halittar jini sosai ta hanyar jijiyoyin jinin dan adam, don haka yana kara karfi da kuzari. 8. Kariya daga kamuwa da ciwon suga (Diabetes) Ta bangaren ciwon suga ko kuma diabetes kuma, yalo na taimakawa wajen bayar da kariya saboda yana kunshe da sinadarin fibre mai saurin narkewa da kuma carbohydrates da kan shi ma kan taimaka. Na'ukan abinci masu kunshe da fibre da carbohydrates na taimakawa wajen tantance yanayin tsotsewar suga da bulkodin jini. Abinci ne mai kyau ga masu fama da ciwon suga, saboda yana ragewa tare da bayar da kariya daga kamuwa daga cutar suga ko diabetes mataki na 2. 9. Daidaita hawan jini (BP) da kitsen cikin jini (cholesterol) Har ila yau yalo na kunshe da sinadarai minerals masu yawa na calcium, da magnesium, da potassium, da kuma phosphorus da ke taimakawa wajen daidaita ayyukan kwayoyin halitta da sinadaran jiki a cikin jiki, don haka yana daidaita yanayin adadin karfin zagayawar jini wanda ke bayar da kariya daga cutar hawan jini. Don haka yawan cin yalo na taimakawa wajen daidata karfin hawa da saukar jini da kuma kitsen cikin jinin. 10. Bayar da kariya daga cututtukan zuciya Ta bangaren cutattukan da ke shafar zuciya kuma, yalo wanda ke kunshe da sinadaran vitamin B1 da B6 (thiamine da niacin). Wadannan sinadarai na vitamins na da muhimmanci a cikin jiki wajen ayyukan zuciya da kuma fitar da zufar jiki. Suna kuma kunshe da sinadarin potassium da ke taimakawa wajen daidaita karfin aikin jinin jiki. Duk da irin dumbin amfanin da aka bayyana cewa yalo na da shi ga lafiyar jikin dan adam, akwai kuma gargadi da masana ke yi na matsalolin da ka iya faruwa idan aka rika cin yalon da ya wuce kima. Don haka yana da kyau idan za a ci yalo a rika ci daidai gwargwado don kaucewa matsalolin da ka iya biyo baya cin shi da yawa. https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-58512977 +health Hawan jini a shekarun kuruciya ka iya janyo dimaucewa "Ya kamata masu shekaru 30 da 'yan kai su rinka sa ido kan yanayin hawa da saukar jininsu domin riga-kafi daga matsalar kwakwalwa da ka iya samun mutum idan ya manyanta, kamar dai yadda wani nazari ya nuna. Nazarin dai ya duba yanayin mutum 500 da aka haifa a shekarar 1946, inda ya alakanta hawan jini a shekarun kuruciya da samun matsalar kwakwalwa a lokacin girma. Kwararru sun ce hawan jini a lokacin da mutum yake ganiyarsa a shekaru 30 zuwa 40 na janyo samun matsala a tunanin mutum sakamakon taba kwakwalwa da yake yi. Wannan dai ba shi ne karon farko da ake alakanta hawan jini da a shekarun ganiya da matsalar mantuwa ko kuma dimaucewa ba, To sai dai masana ilimin kimiyya sun zaku su san yaushe ne da kuma ta yaya hakan ke faruwa a rayuwa. A cikin wannan nazarin, wanda aka buga a mujallar Lancet Neurology, wadanda aka tattauna da su an gwada hawan jininsu sannan an dauki hoton kwakwalwarsu. A nan aka gano cewa samun hawan jini a shekaru 36 zuwa 43 ka iya samun alaka da kankancewar kwakwalwa. Abu ne da aka sani cewa kowa kwakwalwarsa na kankancewa saboda shekaru, to sai dai an fi samun matsalar kankancewar ne ga wadanda suke da rashin lafiyar kwakwalwar kamar masu cutar dimauta. Duk da cewa nazarin bai fito da wasu alamu na dimaucewa ba, masu nazarin sun ce kankancewar kwakwalwa ce ke haddasa dimaucewa. Yanzu haka masanan za su ci gaba da sa ido a kan mutanen da ake nazarin a kansu domin ganin ko za a samu alamun dimaucewa a rayuwarsu nan gaba. An kuma alakanta hawan jini a tsakanin shekaru 43 da 53 da alamun lalacewar jijiyoyin jini ko kuma bugun jini a lokacin da mutum ya kai shekara 70. Farfesa Jonathan Schott, kwararre a kan kwakwalwa a Cibiyar Nazarin Cututtukan Kwakwalwa ta UCL Queen Square Institute of Neurology ne ya jagoranci nazarin. Ya ce ""Hawan jini ko da a shekara 30 da doriya ka iya haddasa wa kwakwalwa matsala a shekaru 40 masu zuwa. Saboda haka kula da ingancin kwakwalwa ya kamata ya fara daga shekarun kuruciya ne."" Paul Leeson, wanda shi kuma farfesa ne na abin da ya shafi zuciya a jami'ar Oxford, ya ce, ""Mun gano cewa akwai yiwuwar masu hawan jini ka iya samun matsalar kwakwalwa a lokacin da suka manyanta. ""Abin da likitoci suka dade suna muhawara a kai shi ne ko magance hawan jini ga masu karancin shekaru na maganin kamuwa da matsalar kwakwalwar."" Dr Carol Routledge, darakta a cibiyar nazari ta Alzheimer's Research da ke Burtaniya, ta ce, ""Hawan jini a matsakaitan shekaru na cikin abubuwan da ke haddasa cutar dimuwa a lokacin girma, wani al'amari da lura da shi ke hannunmu. ""Bincike ya nuna cewa hanya sahihiya ta magance hawan jini ita ce inganta lafiyar kwakwalwar matasan yanzu wadanda su ne dattijan gobe.""" https://www.bbc.com/hausa/labarai-49467046 +health Mece ce cutar polio kuma yaya take yaɗuwa? Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon: A baya-bayan nan an gano ƙwayar cutar polio a kwatami a wasu manyan biranen duniya. Cutar, wacce ba a faye samunta ba, wata ƙwayar cuta ce ke samar da ita, kuma a yanzu an kusa kawar da ita a duniya. Cutar na yaduwa ne idan mai ɗauke da ita ya taɓa marar ita - ko kuma ta hanyar gurɓataccen ruwa ko abinci - ko kuma ta hanyar atishawa da tari. Wannan bidiyon an yi shi ne albarkacin ranar yaki da cutar polio ta duniya da ke faɗowa duk ranar 24 ga watan Oktoban 2022. https://www.bbc.com/hausa/articles/c048mkx0y51o +health Cutar korona : Biden zai buƙaci Amurkawa su sanya takunkumi tsawon kwana 100 Zabaɓɓen shugaban Amurka mai jran gado Joe Biden, faɗa wa CNN cewa zai buƙaci Amurkawa su sanya takunkumi a kwanaki dari na farkon gwamnatinsa don hana yaɗuwar annobar korona a fadin ƙsar. Ya ce ko tantama babu, za a samu raguwar masu kamuwa da cutar idan jama'a suka amsa kiran. Ya ce zai yi odar takunkuman da ma'aikata za su riƙa amfani da su a dukkanin gine-ginen gwamnati, kama daga kan ma'aikatu da sauran hukumomi. Zuwa yanzu an samu masu cutar miliyan 14 a Amurka, yayin da yawan wadanda suka mutu ya tasamma 300,000. Me Biden yace a kan takunkumi? Yayin hira da mai gabatar da shirye-shirye na kafar CNN Jake Tapper, Mista Biden ya ce ranar da aka rantsar da shi zai bukaci al'ummar ƙasar su sanya takunkumin kwana 100, ''Kwana 100 kacal ba wai har abada ba'' inji shi. Ya ce yana fatan cewa za a samu raguwar mutanen da ke kamuwa kwarai da gaske, musamman tunda zuwa lokacin an fara yiwa jama'a rigakafi. Masana kundin tsarin mulki a Amurka dai sun ce shugaban ƙasar bashi da ikon tursasawa jama'a sanya takunkumi, amma Mista Biden ya bayyana cewa shi da mataimakiyarsa Kamala Harris za su yi jagoranci abin koyi, ta hanyar sanya takunkumi a ko da yaushe. Zaɓaɓɓen shugaban ya bayyana cewa ya nemi kwararran jami'in yaƙi da cutuka masu yaɗuwa na ƙasar Dakta Anthony Fauchi ya ci gaba da kasancewa a matsayin mai ba gwamnatinsa shawara a kan yaƙi da annobar. Ya ce ci gaba da kasancewa da shi zai ƙara sanya wa jama'a ƙarfin guiwar cewa da gaske gwamnatinsa ta ke, a ƙudurinta na yaƙi da cutar korona. https://www.bbc.com/hausa/labarai-55183012 +health Tattaunawa akan cutar Sikila tare da Farfesa Abdullahi Ibrahim Musa Masana kiwon lafiya sun yi bayar da shawarwari kan hanyoyin da al'umma za ta bi domin rage yaduwar cutar amosanin jini, wato sikila a yayin da ake wayar da kan mutane kan cutar a duk ranar 19 ga watan Yuni. Farfesa Abdullahi Ibrahim Musa na Jami'ar jihar Kaduna da ke Najeriya ya yi wa BBC karin bayani a cikin wannan bidiyon: https://www.bbc.com/hausa/labarai-53115566 +health Ebola: Najeriya ta shirya yaki da bala'in da ke tunkarar Afirka "Cibiyar kiyaye yaduwar cutuka ta Najeriya ta bayyana cewa kwamitin da ke yaki da cutar ebola za ta ci gaba da aiki domin shiryawa barkewar cutar. Jami'an lafiyan sun furta hakan ne a matsayin martani kan hukuncin da Hukumar Lafiya Ta Duniya, WHO ta dauka na kadammar da dokar ta bacci kan ebola a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo. WHO ta dauki matakin ne bayan matsin lamba da ta fuskanta saboda yadda cutar ke bazuwa a sassan Congo da kuma makwabta, inda ake ganin kuma za ta yadu a kasashen duniya kamar yadda ta faru a baya. Karkashin dokar, WHO ta bukaci kasashe su tsaurara binciken lafiya a kan iyakoki a matsayin matakan kariya ga barazanar cutar. Sai dai mai magana da yawun hukumar Dakta Margaret Harris, ta yi kira ga kasashen duniya da su kwantar da hankulansu ka da a samu irin rudanin da aka samu a baya. Ta ce ""Mun ga yadda a baya aka yi wa lamarin mummunar fahimta, abinda ya sa ya rikita jama'a. ""A cikin sanarwar da suka fitar mambobin kwamitin gaggawa na hukumar sun bayar da shawarwarri ga dukkan kasashen duniya da kada su rufe hanyoyin sufuri, da kawo tsaiko ga harkokin yau da gobe. ""Akwai abubuwa da dama da za a iya yi kuma wannan shi ne lokacin da ya kamata a fara aiki."" in ji Dakta Margaret. WHO ta kaddamar da dokar ta bacci kan ebola wacce ta riga ta kashe mutane da dama a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo bayan wani zaman tattaunawa da suka yi a ranar laraba. Wannan zaman dai na zuwa ne bayan da WHO ta gano cewar cutar ta barke a birnin Goma da ke gabashin DRC, wanda ke da mazauna a kalla mutum miliyan 1. A cewar WHO ""Kwamitin gaggawa na hukumar ya shawrci duka kasashen duniya da kada su rufe hanyoyin sufuri, da kawo tsaiko ga harkokin yau da gobe."" Ministan lafiya a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo Dakta Oly Illunga ya yi maraba da hukuncin kuma ya ce hukunci ba shi da bambanci da matakan da jami'an lafiya ke bi domin yaki da cutar. Najeriya ita ce kasar Afirka mafi yawan mutane kuma ta ce a shirye ta ke don yakar cutar. ""Kwamitin da ke yaki da cutar ebola zai ci gaba da aiki domin yaki da kuma shiryawa cutar ta Ebola'', a cewar Cibiyar kiyaye yaduwar cutuka ta Najeriya." https://www.bbc.com/hausa/49032005 +health Zafin wuta na janyo tsufan mata da wuri Masu kwashe tsawon lokaci suna aiki da wuta mai zafi matuka kan fuskanci matsalar yamushewar fata, wanda hakan kan janyo tsufan wasu mata da wuri. Tsananin zafin kuma kann shafi lafiyar kwakwalwa, lamarin da ke janyo matsalar damuwa da yawan fushi ga mace wanda ta kwashe shekaru tana sana’ar da ta shafi wuta. Sai dai shan madara ba ya maganin zafin wuta, kamar yadda wasu suka dauka a al’adance. Dr. Rukayya Muhammed Babandi ta ce babu wata hujja a likitance da ke gaskata haka. Haka kuma kasancewa wuri mai hayaki da yawa ba tare da iska sosai ba yana da illoli ga masu aikin wuta. Illolin da hayaki kan haddasa sun hada da tari, sauyi a launin idanu da yanar ido da kuma matsalolin hanyoyin numfashi da gurbatar jini da cutukan zuciya da sauransu. Sai dai wasu hanyoyin da likita ta ce mata da duk masu amfani da wuta za su iya bi wajen rage zafi da kuma hayakinta sun hada da rage  zama na tsawon lokaci a gaban wuta da yin girki a wurin da ake samun isasshiyar iska. https://www.bbc.com/hausa/articles/cw4n9wz29zjo +health Ranar Mata ta Duniya: 'Yaran da ake haifa da larurar kwakwalwa ba ƴaƴan aljannu ba ne' "Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon: A matsayinta na uwa kuma wadda ta sadaukar da rayuwarta gaba ɗaya wajen kula da ƴaƴanta biyu masu buƙata ta musamman, kusan ta fi shan wahala fiye da sauran iyaye mata. Fatima Ahmed, mahaifiyar ƴaƴa uku ce, takan shafe yininta tana hidimar kula da ƴaƴanta biyu -- daga ciyarwa da tsaftace su da kuma yin wasa tare da su. Ta shaida wa BBC cewa ƴaƴanta biyu suna da fama da nau'in ciwon da ya shafi ƙwaƙwalwa. Danta na biyu dan shekara biyar yana da wani nau'in ciwo da ya shafi kwakwalwa da ake kira Cerebral Palsy. Haka ma ƴarta ta uku kuma yar shekara ɗaya da rabi tana fama da ciwon da ya shafi kwakwalwa da ake kira Downs' Syndrome a turance. ""Ina rayuwa mai cike da ƙunci da ƙalubale. Amma bayan na haifi ƴata, ta biyu da ke da matsala, sai na yanke shawarar zama a gida don fahimtar girman matsalar da kuma hanya mafi dacewa da kula da ƴaƴana,"" in ji ta. Ta ce ko wannensu ba ta samu matsala ba na laulayin ciki, kuma har zuwa lokacin da ta gama zuwa awon ciki ba a gane cewa akwai matsala ba har sai da ta haihu sannan aka gano yaran suna dauke da matsala ta daban. An kiyasta cewa kimanin mutum miliyan 25 ne ke fama da nakasa a Najeriya, amma duk da girman matsalar ba a damu da kula da buƙatunsu ba, musamman samun kulawar lafiya da ilimin da ya dace. Babban ƙalubalen shi ne yadda ake nuna musu ƙyama, musamman yaran da aka haifa da nakasa. Dalilin wannan rayuwa da Fatima ta tsinci kanta a ciki ne ya sa ta ƙirkiri wata ƙungiya domin wayar da kan iyaye da ke da yara masu buƙata ta musamman domin fadakar da su kan irin waɗannan nau'in cutukan da kuma yadda za su tafiyar da rayuwarsu ba tare da sun samu matsala ba. A matsayinta na uwa, burinta shi ne sauya yanayin musamman ga yaran da kuma masu kula da su. Fatima na wayar da kan mutane ne a shafukan sada zumunta. ""Na lura yawanci a arewa ba a maganarsu musamman kan wannan nau'in cuta da ake akalantawa da aljannu ko a ce ƴaƴan ruwa ne."" ""Ina amfani da ilimina da kuma yadda na yi rayuwa da ƴaƴana, domin wayar da kan mutane cewa wannan matsala ce ta asibiti idan ana kulawa za su rayu har su yi aure. Fatima ta ce babban kalubalen da ta fuskanta ya shafi ɓangaren lafiya ne. ""Ba a cika samun maganin da zai tafi daidai da ciwonsu ba ko kuma kulawar da suke bukata dole sai an fita zuwa kasashen waje."" ""Ba mu samun kulawar da ta dace musamman wannan da ke tattare da matsaloli. Kuma wannan matsala ce da ke buƙatar kuɗi."" ""Akwai yausayi a matsayina na uwa saboda rashin samun kulawar da ta dace musamman a asibiti da kuma tsadar ilimi da makarantu da suke tsawwala hidimar ilimin yaran,"" in ji ta. Babu dai wasu alƙaluma na hukuma da suka tabbatar da yawan masu buƙata ta musamman a Najeriya, amma yawanci suna fuskantar kyara da kuma dnaganta su da matsaloli da suka shafi al'adu." https://www.bbc.com/hausa/labarai-60651219 +health Ciwon koda: Mu 10 muka rayu cikin mutum 160 a Najeriya "Yayin da aka gudanar da bikin ranar koda a fadin duniya don wayar da kan jama'a game da illon da ke tatattare da ciwon, wani mai fama da ciwon koda kuma Shugaban masu fama da ciwon a jihar Kano da ke arewacin Najeriya, Malam Wali Ado Rano ya ce masu fama da wannan larura na fuskantar kalubale da dama. Malam Wali Ado Rano ya fada wa BBC hakan ranar bikin koda ta duniya da ake gudanarwa ranar 12 ga watan Maris din kowace shekara. Ya ce sai da aka yi masa wankin koda na tsawon shekara guda kuma hakan ba wai yana nufin mutum ya samu lafiya ba ne saboda mara lafiyar zai ci gaba da shan magunguna ne har tsawon rayuwarsa. ""Da farko ana yi min wankin koda sau daya a sati, aka koma sau biyu sai da aka kai kuma sau uku, a lokacin ana yi min wankin koda sau daya akan naira dubu 14,"" in ji shi. Ya kuma bayyana halin da mara lafiya ke shiga idan za a yi masa wankin kodar ""lokacin da ake cikin yin wankin kodar, jinin mutum na daukewa sannan akwai allura naira dubu shida zuwa dubu takwas,"" Malam Wali Ado Rano ya ce ya kashe sama da naira miliyan 15 domin a yi masa dashen koda a India kuma ""ba ni da wata matsala sai ta sayen magani kuma maganin babu shi a Najeriya."" ""A wata ina shan maganin kimanin naira dubu dari da hamsin."" a cewarsa. Matsalar da masu ciwon ke fuskanta Malam Wali Ado Rano ya ce ""wadanda muka rika yin wankin koda kusan mu 160 a lokacin, kusan ba mu fi mu 10 ba wadanda muka rayu, wadanda bas u samu an je an yi musu dashen kodar ba.'' Ya bayyana cewa ciwon koda harka ce ta kudi saboda ""wannan wankin kodar ya zama wajibi idan har mutum na son ya ci gaba da rayuwa, rayuwa ce ba a cikin dadi ba."" Sai dai Malam Ado Rano ya roki gwamnatin Najeriya ta inganta asibitocin kasar tare da mayar da wankin kodar ya zama a kyauta domin sawwake wa mara lafiya. A cewarsa, ""an yi wani bincike wadanda manyan masana suka yi a Hadeja, ya kamata a fito da sakamakon binciken a gano dalilin da yasa mutane suke fama da ciwon, ciwo ne da a yanzu babu tsoho babu yaro babu mace babu namiji.""" https://www.bbc.com/hausa/labarai-51869915 +health Lafiya Zinariya: Abin da ya sa jarirai ke samun matsalar zubar gashi Danna hoton da ke sama domin sauraren shirin: Likitoci sun bayyana cewa jarirai suna samun matsalar zubewar gashi kamar yadda ake gani a manya. Dalilai da dama ne ke janyo zubar gashi ga jarirai wadanda suka hada da cututtuka da gado. https://www.bbc.com/hausa/shirye-shirye-na-musamman-61256018 +health Daliban Ghana sun kosa su bar China saboda Coronavirus "Wani dalibi dan kasar Ghana ya bayyana wa BBC halin dimuwa da daliban wasu kasashe ke ciki a birnin Wuhan na kasar China, wanda ke rufe biyo bayan barkewar cutar coronavirus mai saurin kisa. A ranar Litinin ne, babban jami'in gwamnatin China Li Keqiang ya ziyarci Wuhan, babban birnin lardin Hubei, inda aka samu barkewar cutar. Adadin mutanen da cutar ta halaka a China ya karu zuwa 81, sannan kusan mutum 3,000 ne aka tabbatar ba su da lafiya. A hirarsa da BBC, dalibin wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya ce: ''Muna cikin fargaba saboda adadin kullum karuwa yake. ""A dakunan kwananmu, idan ka hadu da mutum, sai ya matsa can gefe. Babu mai son ya kusanci wani. ''Mata na kuka, suna so su koma gida. Suna cikin fargaba. Ba su da sauran tabbas. Ba ma so mu zauna a nan''." https://www.bbc.com/hausa/labarai-51267721 +health Riga-kafin Coronavirus: Matar da ke jagorantar samar da maganin coronavirus Farfesa Sarah Gilbert, ta shaida wa BBC cewa dole su yi aiki cikin sauri domin samar da magani ko riga-kafin cutar korona. Masanar kimiyyar wadda ke aiki a Jami'ar Oxford, na cikin hanzari wajen ganin ta samar da riga-kafin cutar korona wadda ta shafi mutum fiye da miliyan 15 tare da kashe wasu fiye da dubu 630 a duniya. Tare da 'yan tawagarta su 300 a Jami'ar ta Oxford, sun yi kokari wajen bin hanyoyi daki-daki na samar da riga-kafin wanda ake ganin samar da itan zai dauki dogon lokaci. Ta ce ' Mun yi kokari mun yi aikin a cikin watanni hudu kawai'. Sakamakon farko sun ba da kwarin gwiwa: gwajin da aka yi kan mutane ya nuna alamun nasara cewar riga-kafin ka iya aiki ba tare da matsala ba kuma zai inganta karfin garkuwar jikin da zai yaki kwayar cutar. Ko da yake ba a tabbatar da sahihancin abin da aka samar ba a yanzu, amma kuma za a fara amfani da shi ne zuwa nan da karshen shekarar da muke ciki, kuma akwai fatan cewa an kai wa gaci. Wacece Sarah Gilbert? Farfesa Gilbert na jagorantar tawagar da ke kokarin samar da riga-kafin cutar korona. Tawagarta a Jami'ar Oxford, ta hada gwiwa da kamfanin samar da magunguna na AstraZeneca, sun kuma yi gwajin riga-kafin a kan mutum 1,077. Tun lokacin da riga-kafin da suka samar aka ga alamun nasararta bayan mutanen da aka yi wa gwajin garkuwar jikinsu ta nuna cewa za ta iya yakar kwayar cutar koronar, ta zamo abin kwatance da alfahari. Ko da yake ya yi wuri a gane cewa ko riga-kafin ta isa ta kare mutane daga cutar. Sunan Farfesa Gilbert ya watsu ko ina a kafafen yada labarai, sannan kuma ana ta nemanta don a yi hira da ita a kafafen yada labarai. Amma, kamar sauran abokan aikinta, ta saba zuwa aikinta ne kawai amma ba ta son a nunata a kamara. Farfesa Gilbert ta ce, a ko da yaushe tana son tayi aiki a bangaren bincike na bangaren lafiya, amma a lokacin da ta ke shekara 17 ba ta san ta inda za ta fara ba. Matakin farko shi ne ta samu takardar shaidar kammala karatun digirinta a bangaren nazarin kimiyyar halittu daga jami'ar gabashin Anglia, sai ta wuce ta ci gaba da karatu inda ta kai matakin da ta samu matsayin farfesa a bangaren Biochemistry. Daga bisani kuma ta je ta yi nazari a bangaren bincike a kan magunguna da ma yadda za a hada mgani. A shekarar 1994, Farfesa Gilbert, ta zama kwararriya a bangaren bincike da samar da magunguna a Jami'ar Oxford. Mafi yawancin bincikenta ta yi su ne a kan samar da riga-kafin cututtuka. Farfesa Gilbert, ta haifi 'ya'yanta 'yan uku a 1998, da shekara ta zagayo kuma ta zama malama a jami'a. Ta ce 'Abu ne mai matukar wuya ka hada aiki da kuma kula da iyali, a lokacin ba ni da wani mataimaki, makarantar kula da yara da ya kamata na kai 'ya'yana kudin ya yi yawa don yafi albashina'. Mijinta shi ne ya yanke shawarar ajiye aikinsa domin ya kula da 'ya'yan nasu, amma ta ce gaskiya abun da wuya matuka. Ta ce, 'Na dauki tsawon watanni 18 a matsayin hutun haihuwa domin na kula da 'ya'yana wadanda na haifa bakwaini, kai na sha wahala sosai'. To sai dai farfesar ta ce wani abu da aikin kimiyya shi ne ba dole ne ka yi aiki kullum ba ko kuma tsawon sa'o'i. A shekarar 2004, ta kara samun ci gaba a jami'ar da take aiki, shekaru uku bayan nan ta yi wani bincike a kan riga-kafin cutar mura wanda ta yiwa wani wajen bincike a Landan aiki, a nan ta kara samun daukaka. Yayin da 'yan ukunta ke girma, sai take samun saukin abubuwa in ji ta. Yanzu shekarun 'ya'yanta 21. Dukkansu suna karatu a fannin kimiyyar sarrafa sinadaran kwayoyin halitta wato Biochemistry, ma'ana suna bin sawun mahaifiyarsu. Suna kuma sha'awar aikin mahaifiyarsu na yadda take kokarin samar da riga-kafin cutar korona inda har dukkansu suka amince a yi gwajin riga-kafin da su. Farfesar ta ce, a yanzu abu mai muhimmanci shi ne mun fi mayar da hankali a kan gwajin riga-kafin da kuma tunanin yadda za a samar da shi isasshe domin a rage yaduwar cutar a duniya baki daya. https://www.bbc.com/hausa/labarai-53557485 +health Lafiya Zinariya: Abin da ya sa mata suka fi fuskantar ciwon kai mai tsanani Danna hoton da ke sama don sauraron shirin: Ciwon kai kan zamo alamu na wasu cututtuka, amma wannan matsancin ciwon kan da ake kira Migraine a likitance, ciwo ne na kashin kansa kuma ya fi addabar mata. Alamomin ciwon kan sun hada da ciwo mai tsanani a bangare daya na kai, kuma yana zuwa kamar ana buga wa mutum abu ko kuma sara. Ga wasu ya kan shafi idanunsu ta yadda ba sa gani sosai ko gani bibbiyu. Ciwon ya kan zo ne ko matsakaici ko kuma mai tsanani. Hukumar lafiya ta Burtaniya, NHS ta ce mace daya cikin kowace biyar na fuskantar matsanancin ciwon kan a kasar. A maza kuwa ana samun namiji daya ne cikin kowane 15 da ke fama da cutar. Hukumar ta bayyana cewa akwai wasu abubuwa da ke tayar da ciwon ga wasu masu fama da shi, kamar misali zuwan jinin ala’ada ga wasu mata. Matsananciyar gajiya ko wasu nau’ukan abinci ko abin sha da rashin samun isasshen barci ko matukar murna. Alamomin cutar na iya kasancewa tare da mutum na tsawon sa’oi uku zuwa kwana hudu, inji hukumar. Duk kuwa da cewa ana iya jin gajiya har tsawon mako guda bayan ciwon ya yi sauki. NHS ta ce yawan shekaru na sa cutar ta yi sauki ga mafiya yawan masu fama da ita. Amma wasu kuwa suna girma cutar na kara ta’azzara. https://www.bbc.com/hausa/shirye-shirye-na-musamman-61829032 +health Mutum 4 sun mutu bayan kwalekwale ya kife da su a Sengal Hatsarin jirgin ruwa ya yi sanadiyyar mutuwar mutane hudu a gabar ruwan Dakhar babban birnin kasar Senegal. An kai wasu mutum 35 daga cikin fasinjojin kwalekwalen asbiti, yayin da ake ci gada da aikin neman sauran fasinjojin. Hukumar bayar da agaji ta kasar ta ce kwalekwalen ya kife ne sakamakon wata mahaukaciyar guguwa a daren Litinin. Hukumar ta shaida wa BBC cewa fasinjojin na kan hanyarsu ta zuwa yawon bude ido ne a tsibirin Madeleine, duk da cewa an samu gargadin rashin kyan yanayi. Jami'an hukumar sun ce fasinjojin sun hada da Faransawa shida, Jamusawa biyu, da 'yan kasar Sweden biyu da kuma mutum daya dan kasar Guinea Bissau. Laftanar Kanar Pape Ange Michel Diatta, ya ce duk da cewa babu tabbacin musabbabin hatsarin, akwai yiwuwar ruwan sama kamar da bakin kwarya da iska mai karfi ne suka sa kwalekwalen kifewa. Zuwa lokacin da ake hada rahoton, ba a san kasashen da hudu daga cikin wadanda suka rasu a hatsarin suka fito ba. https://www.bbc.com/hausa/labarai-49730451 +health Malaria: Yadda ake fama da ƙarancin maganin cutar a Jigawa "Duk da yake, yanayin sanyi ya kankama a sassan Najeriya, zazzaɓin cizon sauro na ci gaba da yin mummunar illa a jihar Jigawa da ke arewa maso yammacin kasar. Ƙanana da manyan asibitocin jihar kan cika maƙil a kowacce rana saboda yawan marassa lafiyan da ke tururuwa don neman magani. Lamarin dai ya fi shafar ƙananan yara da mata masu juna biyu waɗanda a wasu lokutan kan zo da rashin jini a jika ko kuma suma. Iyayen yaran da suka kamu da cutar sannan kuma suka kai su asibiti sun yi korafin cewa duk da yake gwamnatin jihar ta bayar da magungunan cutar zazzabin cizon sauron kyauta don a rabawa mutane, su basa samu. Wani mahaifin wata yarinya da ta kamu da cutar ya shaida wa BBC cewa, ya samu wasu magungunan kyauta amma kuma da yawa daga cikin wadanda likita ya rubuta musu shi ya siya da kansa kuma ya kashe makudan kuɗaɗe kafin 'yar tasa ta warke. Marassa lafiya da dama da BBC ta tattauna da su sun ce ba wani abu ke damunsu ba illa rashin isassun magunguna a asibitocin jihar da kuma ƙarancin gadajen kwanciya. Kazalika cutar kuma a wannan karon tazo da wani sabon salo wanda ba a taba gani ba a wannna shekarar inda yawancin wadanda suka kamu da cutar ta maleriya a kan same su da karancin jini wasu kuma har ta kan kai su ga suma ko jijjiga. Ba kasafai ake kamuwa da cutar maleriya a lokacin sanyi ba saboda sauron shi kansa ba ya tasiri saboda sanyi, amma a wannan karon batun ya sauya. Masana a bangaren kiwon lafiya sun yi bayani a kan dalilin da ya sa ake kamuwa da cutar maleriya a lokacin sanyi, Dakta Kabir Ibrahim,kwararre ne kan kula da lafiyar al'umma ya kuma shaida wa BBC cewa, ""Kwayar cutar maleriya a wasu lokutan kan rikiɗa inda lokaci-lokaci sai aga ta fito da wasu irin halitta wanda yake bijirewa magungunan da aka saba da su na yau da kullum"". Likitan ya ce a wasu lokuta kuma mutane suke haddasa duk wata matsala wajen kamuwa da maleriya saboda basa kiyayewa da ƙa'idojin da aka gindiya na kiyayewa. Don haka Dakta Kabir Ibrahim ya yi kira ga iyaye da su rinka kiyayewa da duk wasu ƙa'idoji da aka shimfiɗa musu. Ba a jihar Jigawa kaɗai ake fama da wannan cuta ta maleriya ba, kusan jihohin Najeriya na fama da wannan matsalar ta cutar maleriya. Hukumar Lafiya ta Duniya dai ta ce cutar zazzabin cizon sauro ita ce ta ɗaya wajen kashe ƙananan yara a Afirkam kuma idan har aka samu mutum huɗu sun kamu da cutar to ko shakka babu ɗayansu a Najeriya ya ke." https://www.bbc.com/hausa/labarai-55211089 +health Lafiya Zinariya: Ana warkewa daga cutar taɓin hankali? Latsa hoton da ke sama da sauraron hirar da Fauziyya Kabir Tukur ta yi da Dokta Ɗayyiba Shaibu Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta ce cutar gushewar hankali ko ciwon hauka matsala ce mai wahala da ke shafar aƙalla mutum miliyan 20 a faɗin duniya. Cutar gushewar hankali cuta ce ta ƙwaƙwalwa da kan iya janyo gane-gane da jin muryoyin mutanen da ba sa nan da sa wa rai wani abu da ba shi ne ba da tsoro na babu gaira babu dalili. WHO ta ce har yanzu bincike bai gano taƙamaimai abin da ke janyo cutar gushewar hankali ba. Amma ana tunanin cewa ana gadonta kuma halittar mutum da al'amuran da ke faruwa a rayuwarsa na yau da kullum na haifar da cutar. WHO ta ce akwai yiwuwar mutanen da ke fama da cutar gushewar hankali za su riga masu lafiya mutuwa. Wannan na da nasaba da cutukan zuciya da rashin wadataccen abinci da sauran cutuka da kan kama sassan jiki. Masu fama da wannan matsala na fuskantar tsangwama da kyara da wulaƙanci wanda a lokuta da dama hakan kan ƙara jefa su cikin mawuyacin hali. Amma hukumar ta ce ana warkewa daga hauka idan aka je asibiti. Akwai taimako na musamman da ake ba su kamar magunguna da ɗebe kewa da shawarwari da ke taimaka wa wajen samun lafiyarsu. https://www.bbc.com/hausa/shirye-shirye-na-musamman-54929325 +health Sabbin hanyoyi biyu masu sauki na rage matsananciyar ƙiba daga Ingila da Amurka "Nan ba daɗewa ba mutanen da ke fama da narkekiyar ƙiba za su samu sauƙi saboda za a samar da wata allura da za su dinga yi duk sati da za ta taimaka musu wajen rage kitse. Allurar ta semaglutide na kamfanin Wegovy, kan sa mutum ya ji shi a ƙoshe ta yadda ba zai dinga buƙatar cin abinci sosai ba kuma ba zai dinga jin yunwa sosai ba. A yayin gwajin samar da allurar, wanda aka haɗa shi da cin abinci mai kyau da motsa jiki, ya taimaka wa mutane masu matuƙar ƙiba su rage kashi 10 cikin 100 na ƙibarsu. Kuma Cibiyar Lafiya ta kasa a Ingila wato National Institute for Health and Care Excellence NICE, ta bayar da shawarar cewa ya kamata a sanya allurar a tsarin hukumar lafiya ta Birtaniya NHS. Sai dai har yanzu ba a kai ga amincewa da shawarwarin da NICE ta gabatar a Ingila da Wales ba, har sai an bi waɗannan ƙa'idojin: Mutum zai yi wa kansa allurar ne. Yana da kyau mutane masu matsananciyar ƙiba su dinga tuntuɓar likitocinsu a kan batun rage ƙiba ba tare da wata illa ba. Wasu kuma suna rage ƙiba ne ta hanyar kula da irin abincin da ya kamata su ci da kuma motsa jiki. Masana kimiyya a Amurka sun ce kara sa'o'in baccin ka da sa'a guda da kwata a kowanne dare na iya taimaka maka wajen kona kitsen calories 270 a rana guda. Tawagar masana daga cibiyar bincike kan bacci da ke Jami'ar Chicago ta ce kwanciya da wuri na taimaka wa wajen rage kwaɗayi da ciye-ciyen dare, kuma sannan samun hutu sosai na rage kwaɗayi. Binciken ya yi nazari kan mutum 80 da suka haɗa da maza 41 da mata 39 waɗanda dukkansu mutane ne da ke fama da ƙiba, sannan sun ksance suna yin baccin ƙasa da sa'a shida rabi a kowane dare, ƙasa da sa'a takwas da ake buƙatar mutum ya samu a kowane dare. An ɗora wadannan mutane a kan starin ingantaccen bacci ta hanyar tattaunawa da su da shawarwari domin ƙara sa'o'in barcinsu. An yi amfani da wannan tsarin wajen gwada sauyin da ke tafiya da jikinsu da lissafin adadin kitsen da suke ƙonewa a kowane dare. Farfesa Esra Tasali da ta jagoranci binciken ta ce samun wadataccen bacci na kawo sauyi a rayuwa, musamman ga mutanen da ke fama da matsalar ƙiba. ""Wannan bincike ya kawo ƙarshen nazarin da aka kwashe sama da shekara 15 ana yi a kan alaƙar barci da ƙiba da kuma kuzari. ""Ɗaya daga cikin abubuwan da ke ɓata bacci ko rage yawan bacci na da alaƙa da na'urorin zamani ko wayoyi da galibin mutane ba sa iya rayuwa sai da su, ko kuma baa lokaci wajen amfani da su kafin kwanciya bacci Sauran hanyoyin rage ƙiba sun haɗa da: Kusan mutum ɗaya cikin huɗu ne ke fama da matsananciyar ƙiba a Birtaniya kuma hajkan yana sa su fuskantar barazanar kamuwa da wasu cututtuka. A shekarar 2018 zuwa 2019, mutum 11,117 aka kwantar a asibiti a Ingila saboda matsananciyar ƙibarsu. Helen Knight ta Cibiyar Lafiya ta Ingila ta ce: ""Mun san cewa matsananciyar kiba na ɗaya daga cikin matsalolin da muke fuskanta a fannin lafiya. ""Matsalar lafiya ce da ke buƙatar likitoci su shiga ciki, saboda tana taɓa lafiyar hankali da na tunani.""" https://www.bbc.com/hausa/labarai-60315712 +health Illar Coronavirus: Yadda cutar take lalata ƙwaƙwalwa "Wasu masana kimiyya sun ce cutar korona mai haifar da sarkewar numfashi ba ta huhu kawai take ƙisa ba, takan lalata ƙwaƙwalwa, kuma alamominta sun hada da ciwon kai da shanyewar barin jiki. Wata kwararriyar likita da ta yi nazari kan batun, Julie Helms, ta ce bincikenta ya soma ne lokacin da aka kwantar da marasa lafiya a fannin bayar da kulawar gaggawa da ke asibitin Jami'ar Strasbourg na arewacin Faransa a farkon watan Maris din 2020. A cikin 'yan kwanaki, duk wani mara lafiya da aka kwantar a wannan sashen na dauke da Covid-19 - kuma ba wai sarkewar numfashin da suke fama da ita ba ce ya ankarar da ita. ""Sun shiga mummunan yanayi, kuma da damansu na da matsalar ƙwaƙwalwa - mai rikitarwa da jefa damuwa,'' a cewarta. ""Hakan ba daidai ba ne. Akwai tsoratarwa, musamman ganin yadda akasarin mutanen da aka yi wa magani matasa ne -shekarunsu bai haura 30 zuwa 40 ba, har da 'yan 18."" Helms da abokan aikinta sun wallafa wani dan binciken da suka yi a jaridar kiwon lafiya ta New England Journal of Medicine inda suka bayyana alamomin matsalar ƙwaƙwala ga marasa lafiya da ke dauke da Covid-19. Duk alamomin da suka nuna sun yi daidai da na wadanda ƙwaƙwalwarsu ta lalace - wani abu da dama masu bincike a birnin Wuhan na China suka gano tun a watan Fabarairu. Yanzu haka akwai bincike sama da 300 da aka aiwatar a sassan daban-daban na duniya, kuma sun gano cewa matsalar ƙwaƙwalwa na tattare da masu Covid-19, ciki akwai 'yan alamomi kamar na ciwon kai, rashin jin wari ko kanshi, wanda hakan kuma na kai wa ga shanyewar barin jiki ko daukewar numfashi. Wannan wani kari ne kan bincike da aka yi kan cutar, wanda a baya ake ganin kawai ta matsalar numfashi ce, sannan an gano tana lalata ƙoda da hanci da zuciya da kuma kowanne sashe na jiki. ""Sai dai har yanzu ba mu sani ba ko cutar da ke shafar ƙwaƙwalwa takan yi tsanani idan mutum yana dauke da Covid-19 kan wasu cutuka, amma ina shaida muku mun ga yadda take illa a yanzu,'' a cewar Elissa Fory likitar ƙwaƙwalwa a gidauniyar Henry Ford da ke Detroit, a Michigan. ""Yayin da alkaluman masu dauke da wannan cuta ke ƙaruwa, za a rika ci gaba da ganin wasu sabbin alamomi wadannda a baya ba a taba tunaninsu ba - kuma duk muna ganinsu ne lokaci guda, wanda ba abu ne da wasu daga cikin mu suka taba gamuwa da shi a rayuwa ba."" Ƙiyasin dai ya bambanta, sai dai da alama kusan kashi 50 cikin 100 na mutanen da aka gano suna dauke da cutar korona sun fuskanci matsalolin da ke da alaka da ƙwaƙwalwa. Girman matsalar da yawaitar ta abu ne da har yanzu akwai sauran bincike a kai. Akasarin mutane, har da likitoci ba su fiye ganin matsalolin ƙwaƙwalwa da zarar sun bayyana ba -wasu mutane ba sa nuna alamomin kafin barin jikinsu ko numfashinsu ya dauke. Akwai wasu matsalolin da ake fuskanta, akasarin mutane da ke fama da Covid-19 gwaji bai cika nuna suna dauke da cutar ba, musamman idan ba su nuna alamomin tari ko zazzabi ba. Hakan na nufin idan aka gano suna da alamomin matsalar ƙwaƙwala ba lallai a alaƙanta hakan da korona ba. ''A zahiri, akwai mutane da ke dauke da korona amma alamomin da suke nuna akawai shi na rikidewa,'' a cewar Robert Stevens ƙwarrare kan irin wadannan cutuka a Jami'ar Johns Hopkins. ""Muna fuskantar matsala a wani mataki na daban wanda ke da alaka da ƙwaƙwalwa."" Masu bincike da dama sun yarda cewa watakila matsalar ƙwaƙwalwar tana tasowa ne saboda ƙarancin iskar da ke taimaka wa numfashi zuwa ƙwaƙwalwa. Sai dai Fory da Helms ba su gamsu da hakan ba. Akwai kuma wadanda ba su yarda cewa cutar tana shiga ƙwaƙwalwa ba. ""Idan kun tambaye ni a watan da ya gabata cewa akwai alaka tsakanin korona da ƙwaƙwalwa da amsar da zan baku ita ce A'a - amma yanzu sai ga rahotannin da ke neman tabbatar da hakan,"" a cewar Stevens. A Japan, masu bincike sun bayar da rahotan wani mutum mai shekara 24 da aka tsinta kwance cikin aman da ya kwarara. Numfashinsa ya dauke lokacin da aka yi kokarin gaggawar kai shi asibiti. Gwaje-gwajen da aka yi a ƙwaƙwalwarsa sun nuna alamomin sanƙarau mai tsanani wanda kuma aka alakanta da Covid-19. Masu bincike na China sun gano irin wannan matsalar kan wani mutum mai shekara 56 da ya zo musu da korafi kan maƙoshinsa. Kuma bincike da dama kan Covid-19 a Italiya ya gano marasa lafiya sun fuskanci matsalolin ƙwaƙwalwa. Hasali ma, yanzu wasu masu bincike na zargin cutar korona da ke haddasa daukewar numfashi ba ta hanyar lalata huhu take kisa ba, takan lalata ƙwaƙwalwa ne, kuma alamominta sun hada da ciwon kai da shanyewar barin jiki. Akwai cutuka da tabonsu kan zauna tare da mutum har karshen rayuwa. Kashi 30 cikin 100 na mutane da suka yi ƙyanda a lokacin yarantarsu suna iya zama da tabo har karshen rayuwarsu. Wasu cutuka tasirinsu ko barnar suna har abada ne. Daya daga cikin misalai na irin wadanan cutuka shi ne annobar Influenza ta shekarar 1918, ta yi wa mutane barnar da har abada a ƙwaƙwalwa da kuma jikinsu. Mutum miliyan biyar a duniya aka ƙiyasta cewa suna dauke da wasu nau'ukan cutuka da ake alakantawa da rashin bacci. Cikin wadanda suka rasu akwai kalilan da ake ganin har yanzu ba su dawo daidai ba. David Nutt, wani farfesa lafiya ne a kwalajen Imperial na Landan, ya ce shi da kansa ya yi wa mutane da dama magani tsakanin 1970 zuwa 1980 bayan sun gamu da damuwa sakamokon wata annoba da ta taba barkewa a Burtaniya a shekara ta 1957. ""Damuwar da suke ciki ya wuce wanda a lokaci guda a shawo kanta,"" in ji shi. Nutt ya gargadi cewa irin wannan yanayi na sake iya maimaita kansa, watakila ya haura abin da aka gani a baya. ""Mutanen da suka warke daga cutar korona akwai bukatar a sanya musu ido sosai na tsawon lokaci domin tabbatar da cewa ba su da matsala ko ba ta shafi lafiyar ƙwaƙwalwarsu ba. ""Abin damuwa shi ne kusan kowanne jami'in lafiya a Burtaniya kokarinsa bai wuce gano alamomin korona ba - babu wanda ke mayar da hankali kan lafiyar ƙwaƙwalwa."" Nutt ya tsara aiwatar da gwaji ta hanyar samun mutane 20 da suka yi korona kuma ta haddasa musu damuwa ko wata matsala da ta shafi lafiyar ƙwakwalwarsu. A Baltimore, Steven, na son ya gwada irin wannan bincike kan marasa lafiya da suka yi fama da korona kuma ba a jima da sallamarsu daga sashen samun kulawar gaggawa ba. A Pittsburgh, Shery Chou wanda shi ma ƙwararren likita ne ya gayyato ƙwararru daga kasashe 17 domin yin irin wannan nazari tare da gwaje-gwaje ƙwaƙwalwa." https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-53268372 +health 'Yadda na tsani kowa har mijina bayan na haihu' "Karima (ba sunanta na gaskiya ba) ta tsinci kanta a cikin wani yanayi na tsananin bakin ciki da damuwa da fargaba wanda ba ta taba tunanin dan Adam na iya shiga ya wanye lafiya ba. Kamar kowa ce mace mai ciki, Karima ta yi farin ciki a lokacin da ta fahimci tana dauke da juna biyu, inda ta fara shirye-shiryen tarbar jaririyarta cikin doki da zakuwa. Sai dai da lokacin haihuwarta ya yi, sai likitoci suka ce mata ba za su bari ta haihu da kanta ba sai dai su yi mata tiyata saboda dalilai masu karfi. Karima ta bayyana cewa ba ta taba tunanin haihuwar za ta zo mata da wata matsala ba amma likitocinta sun nuna mata yin tiyatar shi zai fi. Ita da maigidanta suka amince da wannan shawara, aka sa ranar da za ta je asibiti domin yin aikin. A lokacin da za ayi tiyatar, sai likitoci suka yi mata allurar kashe zafi mai karfi, wato anaesthesia da Ingilishi, wadda za ta ba su damar yanka cikin Karima ba tare da sun sa ta bacci ba kuma su ciro jaririyar ba tare da ta ji zafi ba. Dan lokaci bayan yi mata wannan allurar, sai Karima ta fara jijjiga, alamun jikinta bai amince da allurar ba. Nan da nan likitocin suka yi mata wata allurar da ta sa ta bacci mai nauyin gaske. Ashe wasa farin girki a matsalolin da suka dabaibaye haihuwar Karima. Yin allurar baccin ke da wuya jini ya balle mata, don haka dole likitocin suka shiga aiki tukuru don kokarin ceto ranta. ""Likitocin kansu sun yi tunanin mutuwa zan yi saboda matsalolin da suka rika tasowa bi da bi,"" in ji Karima. Amma an yi nasarar ceto ta, kuma an ciro jaririya mai koshin lafiya. Wanshekare, ko da Karima ta tashi daga bacci sai ta fahimci cewa ba ta iya magana sai da kyar da sidin goshi kalma daya za ta fita daga bakinta. Karima ta ce ""Kamar a fim, kafin kalma daya ta fita daga bakina sai na tattaro numfashi da kyar, na rika haki. ""Sai da aka rubuta min wasu magunguna na fara sha sannan na fara samun sauki. Ashe allurar baccin nan da aka yi min ce ta jawo min daukewar numfashin saboda jikina ba ya sonta."" Karima ta ce bayan ta farfado daga baccin, ta yi matukar farin cikin ganin jaririyarta fiye da yadda take tsammani kuma ta ji ba ta so a matsa da ita ko nan da can. Amma kan a je ko ina sai ta tsinci kanta cikin wani irin yanayi na tsananin bakin ciki da bata taba jin irinsa ba, amma wannan bai hana ta matse jaririyarta a jikinta ba. Sai dai ta ji ta tsani ganin mutane a kusa da ita gaba daya. ""Na ji bana son ganin kowa. Na kira likita na ce masa ya hana baki shigowa dakin da na ke, na ce su rubuta a jikin kofar dakina cewar an hana baki shiga."" Karima ta ce kawai sai ta fara tunanin yadda za ta gudu saboda tsananin bacin ran da take ciki, bacin ran da ba ta san abinda ya haifar mata da shi ba. ""Na shaida wa mahaifiyata da ke zaune da ni a asibiti cewa da an sallame mu daga asibiti zan gudu in bar nan ni da jaririyata. ""A yanzu idan na tuna na kan yi dariya amma a lokacin da gaske na yi wannan shirin. ""Bakin ciki ne da ba ya misaltuwa, na ji kamar an sa ni a wani daki mai matukar duhu."" Karima ta ce mahaifiyarta ce ta rika tarairayarta tare da ba ta baki, har aka sallamesu suka koma gida. Sai dai bata samu sassaucin wannan bakin ciki da ta tsinci kanta a ciki ba har bayan da ta koma gida. ""Wata rana, mahiafiyata ta shigo daki ta samu na dora jaririyata a kan kirjina, haka ya zama abin da nake yi kullum. Idan ban dora ta a kirjina na rike ta ba, bana iya bacci. ""Hawaye na ta gangarowa daga idanuna, kuma nima kaina ban san dalilin kukan ba gaskiya."" Karima ta ce mahaifiyarta ta zamo mata abin dogaro, don ita kadai ce ta fahimci halin da take ciki kuma take jurewa ta ba ta baki. ""Maigidana bai fahimci abin da ke faruwa da ni ba, don haka bai san ta wace hanya zai bullo min ba. ""Bai san irin halin matukar takaicin babu gairi babu dalili da nake ciki ba, sai da ta kai ba ma yi wa juna magana. Idan ya ce abu fari ne sai in dage in ce a'a baki ne,"" ta bayyana tana dariya. ""Idan ina tuna wannan lokacin ni kaina ina mamakin yadda na rika mu'amala da shi. Sai da ta kai mun daina magana da juna sai dai mu aika wa juna sako ta manhajar Whatsapp."" in ji Karima. Cutar tsananin damuwa bayan haihuwa Cutar tsananin damuwa bayan haihuwa ciwo ne da kan samu iyaye mata bayan haihuwa. Ana yawan samun mata masu kamuwa da wannan ciwo sai dai ba su cika fada ba, kuma da wuya su je asibiti. An gudanar da wani bincike a jami'ar Jos da ke yankin tsakiyar Najeriya inda aka duba sabbin iyaye mata 392. Binciken ya gano cewa kashi 55 cikin 100 na wadannan mata na fuskantar wasu alamu na wannan cutar, kuma tana da alaka da tunanin kashe kai. Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta ce kusan kashi 10 cikin 100 na mata masu ciki da kashi 13 cikin 100 na matan da basu dade da haihuwa ba na fuskantar rashin lafiyar kwakwalwa, musamman ma cutar tsananin damuwa. Yagana Gambo- Dauda wata kwararriya ce kan lafiyar kwakwalwa kuma ta bayyana cewa cutar tsananin damuwa bayan haihuwa na faruwa ne idan wasu sinadarai a kwakwalwar uwa suka sauya. ""Wani lokaci kuma sauye-sauyen da kan zo a lokacin haihuwa ko bayan haihuwa kan haifar wa uwa wannan cuta,"" in ji Yagana. Ta ce wani lokaci, sabbin iyaye mata kan fuskanci gajiya ko saurin hushi da dai sauransu idan sun haihu kuma wannan ba abin damuwa bane. Amma tsananin fushi da bakin ciki da tsanar rayuwa manyan alamomi ne na cewa uwa ba ta da lafiya. Yagana Gambo- Dauda ta ce alamominta na da yawa amma manyan alamominta sun hada da: Yagana Gambo- Dauda ta ce gano cutar ba shi da wahala amma likita zai duba: Cutar tana da magani, kuma ana nasarar warkewa idan aka mayar da hankali wajen shan magani. Bincike ya nuna cewa sau da yawa, samun tallafi daga 'yan uwa ko maigida ko makusantan mai fama da wannan cuta na taimakawa wajen samun waraka. A al'umarmu ba a cika samun masu fitowa su bayyana cewa suna fama da wannan cuta ba, ko kuma suna jin alamunta. Wannan ba ya rasa nasaba da tsangwama ko kyara da a kan nuna wa masu rashin lafiyar kwakwalwa, don haka ko mace ta ji alamun cutar tsananin damuwa bayan ta haihu ba ta iya gaya wa kowa bare ta je asibiti. Wani lokaci kuma, mata ba su san cewa cuta ce suke fama da ita ba, sai su yi ta wahala su kadai. Haka kuma, wasu matan na tsoron kada a ga sun gaza ko kuma sun haukace. Rashin fahimtar cutar da abubuwan da ke haifar da ita kan haifar da rashin jituwa tsakanin mahaifiyar da maigidanta, ko mutanen gidan ko ma sauran 'ya'yanta idan tana da su kamar yadda Karima ta samu matsala da maigidanta. Yagana Gambo- Dauda ta ce matan da ke fama da wannan cuta kan ji tsanar jariransu amma a zahiri ba tsana ba ce. ""Sau da yawa, rashin sanin yadda za su yi da jaririn ne saboda za su ga abin sabo. Ga wasu kuma shayar da jariransu nono ne ke sanya masu damuwa a ransu,"" a cewarta. Yagana ta ce matan da ke fama da wannan cutar kan ji gajiya a jikinsu, kuma wannan ma kan haifar masu da jin haushin jaririn a wani lokaci. ""Cutar kan sa wasu mata su ji alamominta sosai a lokacin da suke shayar da jaririnsu nono, don haka sai su ji takaici a lokacin kuma saboda jaririn ne a kusa da su sukan yi hushin ne da jariran,"" in ji Yagana. Haka kuma, ta ce akwai matan da kan gamu da cutar idan haihuwa ta zo masu da tangarda, kamar ta Karima. ""A nazarin lafiyar kwakwalwa akwai abin da muke ce wa 'Post Traumatic Stress Disorder', kuma wannan kan jefa mata cikin kangin wannan cuta. Karima ta samu lafiya yanzu amma ta ce ba za ta taba mantawa da abin da ya faru da ita ba a baya. ""Ba zan taba mantawa da wannan lokaci ba saboda yanayi ne marar dadi. Amma dalilin cutar, na kara kusantuwa da Allah kuma na kara kaimi wajen addini,"" in ji Karima. Duk da cewa wasu na alakanta cutar tsananin damuwa da rashin ibada ko rashin sanin addini, likitoci na cewa babu wata dangantaka tsakanin abubuwan biyu. Sau da yawa a al'umarmu, a kan ce mutanen da ke fama da cutar tsananin damuwa na da aljanu ko kuma a ce mayu ne suka kama su. Wani lokacin ma a kan yi tunanin sun haukace ne. Amma Yagana Gambo- Dauda ta ce ""Cutar tsananin damuwa cuta ce kamar ko wacce da kan kama dan Adam, babu abin da ya hada ta da rashin mayar da hankali kan addini ko maita."" Karima ta ce nan gaba idan ta tashi yin wata haihuwar, ba za ta sake amincewa a yi mata tiyata ba. ""Gara in haihu a gida da in je asibiti, saboda na dandana kudata. Likitocin sun gaya min a lokacin wai jaririyar ba ta kwanda yadda ya kamata ba a cikina amma daga baya na gano ashe akwai dabarun da za su iya yi su juya ta. ""Na fahimci kawai sun dai so su yi min tiyatar ne,"" in ji Karima. A yanzu, tana gudanar da rayuwarta cikin farin ciki da kwanciyar hankali ita da mijinta da 'yarta. Nigeria: Yadda tsarki da sabulu ya jawo wa wata mace matsala Intanet na 'shafar' walwalar 'yan mata Bincike: Mata a Najeriya na shiga tasku a lokacin haihuwa" https://www.bbc.com/hausa/labarai-50070045 +health 'Yar Tiktok din da ke taimaka wa masu matsalar ƙwaƙwalwa tsaftace gidajensu Wannan 'yar TikTok din tana taimaka wa mutanen da ke da matsalar kwakwalwa tsaftace gidansu. https://www.bbc.com/hausa/articles/cnd5rd11ky2o +health Ra'ayi Riga: Cutar tarin fuka Latsa lasifikar da ke sama domin sauraren shirin https://www.bbc.com/hausa/shirye-shirye-na-musamman-56546190 +health Coronavirus a Najeriya: Shin ƙasar na cin galaba a yaƙi da annobar? "Tun bayan da cutar korona ta ɓulla a Najeriya ranar 27 ga watan Fabarairun 2020 aka riƙa dasa ayar tambayar ko ƙasar za ta iya yaƙi da annobar kamar sauran ƙasashen duniya. A faɗi a tashi, wata biyar kenan har yanzu waɗanda suka kamu da cutar ta korona a ƙasar ba su kai 50,000. Idan aka kwatanta da wasu ƙasashe, za a iya cewa Najeriya ta sha duk da cewa annobar ba ta wuce ba, hasali ma ƙaruwa take yi a Brazil da Mexico da Amurka. To ko hakan nasara ce da ƙasar ta yi a yaƙin ko kuwa dai kawai sa'a ce? Adadi mafi girma na rana guda Ranar Laraba 16 ga watan Yuni ne Najeriya ta ba da rahoton mutuwar mutum 31 sakamakon cutar ta korona, shi ne adadi mafi yawa na mace-macen da aka samu cikin sa'a 24 a ƙasar. Sai kuma Laraba 1 ga watan Yuli, inda aka samu adadi mafi yawa zuwa yanzu na mutum 790 da suka kamu da cutar. Adadin na raguwa Kwana bakwai kenan a jere adadin masu kamuwa da cutar na raguwa a Najeriya, inda alƙaluman ranar Litinin suka nuna 288 ne suka kamu - rabon da a samu mutum ƙasa da 300 tun 7 ga watan Yuni. Yaya batun yin gwaji kuma? Najeriya mai mutum kusan miliyan 200 ta yi wa mutum 289,133 gwajin cutar korona ya zuwa daren ranar Talata. Idan aka kwatanta da ƙasar Afirka ta Kudu sai a ce Najeriya ba ta yi ƙoƙari ba. Ya zuwa ranar Talata an yi wa mutum 3,058,695 a ƙasar mai mutum kusan miliyan 60. Afirka ta Kudu na da mutum 516,862 da aka tabbatar sun kamu da cutar, sai 8,539 da suka mutu da kuma 358,037 da suka warke. ""Ni ina ganin duk da haka ana samun nasara a yaƙi da wannan cuta duk da cewa ba wai mun ƙarshenta ba ne,"" in Ji Farfesa Isa Abubakar na Jami'ar Bayero ta Kano. Masanin kan cutuka masu yaɗuwa ya ƙara da cewa da ma a bayyane ta ke cewa Najeriya ba ta yin gwaji kamar sauran wasu ƙasashe. ""Amma duk da haka a cikin irin ɗan gwajin da muke yi ɗin aka samu wannan raguwar, sannan kuma su ma ɗakunan gwaje-gwajen ƙara yawansu ake yi ba raguwa suke ba. Yanzu muna da kusan 51 a ƙasa baki ɗaya."" Malamin jami'ar kuma mamba a kwamitin yaƙi da cutar a Jihar Kano, Farfesa Isa ya ce matakan da gwamnatocin jiha da na tarayya suke ɗauka su ma suna tasiri sosai." https://www.bbc.com/hausa/labarai-53657918 +health 'Yadda cutar sikila ta sa na shafe shekara takwas a karatun difloma' Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon: To duk da ci gaban da aka samu a fagen magance jinyar da masu lalurar sikila ke yi, musamman a bangaren dashen da ake yi musu na bargon kashi wanda ke iya warkar da su sarai, har yanzu mawuyacin halin da wasunsu ke ciki sai kara ta'azzara yake yi. Cikin irin wadannan masu jinyar akwai wata matashiya mazauniyar birnin Zariya, wadda lamarinta ya kasance mai sosa rai, amma ta kasance wadda ta jajirce a fagen neman ilimi, har a bana ta kai ga zama mai yi wa kasa hidima bayan ta shafe shekaru takwas tana kokarin kammala karatun babbar difloma. Abokin aikinmu Sani Aliyu ya ziyarci wannan matashiyar a gidansu, ga kuma yadda hirarsu da ita ta kasance. https://www.bbc.com/hausa/articles/c3g1vdjj6zvo +health Kalli yadda asibitin cutar Coronavirus yake a Legas Latsa bodiyon sama domin kallo Ziyarar da BBC ta kai asibitin da aka ware na musamman domin magance yaduwar cutar COVID-19 a birnin Legas a Najeriya. A ranar Juma'a 28 Fabrairu 2020 ne gwamnatin Najeriya ta sanar da bullar cutar a kasar. COVID-19 ta yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane a duniya tun bayan bullarta a watan Disamban 2019 a kasar China. Zuwa yanzu an samu bullar cutar a kasashe sama da 50. Najeriya ce kasar farko da aka samu bullar cutar a kasashen da ke Kudu da Hamadar Sahara. Wasu kasashe sun hana shigowar baki daga wuraren da ke fama da cutar. Annobar ta kuma sa hukumomi killace wasu garuruwa da makarantu da taruka domin dakile yaduwarta. https://www.bbc.com/hausa/labarai-51682040 +health Abin da ya sa masu gajeren barci suka fi masu dogon barci karsashi "Barcin sa’o’i nawa ya kamata mutum ya yi kafin ya samu koshin lafiya? Idan amsar ka ita ce sa’o’i takwas, to ba lallai ya zamanto daidai ba idan aka yi la’akari da sabbin bincike na kimiyya. ""Wannan ai rashin fahimta ne. Kamar a ce kowa tsayinsa ya kai mita 1.65. Idan kuma mutum gajere ne, za a samu matsala,"" a cewar malami a Sashen Nazarin Cutukan Kwakwalwa da kuma Cutar Laka da ke Jami’ar Jihar California a Amurka. Ba dukkanmu ne ke bukatar yawan barci ba domin samun koshin lafiya. Kuma ba batun dabi’a ba ce ko zabi. Abin yana da dangantaka da kwayar halittar mutum. Za a iya cewa wasu sun guji yin gajeren barci. Wannan na nufin cewa idan baccin awa uku zuwa shida kadai za su yi, su kuma farka su ji garau komai lafiya. ""Akwai wasu mutane da ake kira masu ‘mugun barcin’, kuma ina ga hakan yana da kyau. Suna gudanar da rayuwarsu lami lafiya tare da yin gajeren barci , inda zaka ga suna aiwatar da ayyukansu na yau da kullum cikin zimma. Kuma gaskiya ne hakan yana fa’ida ba mai kadan ba a wannan duniyar ta mu ta aiki da muke ciki,’’ a cewar Dr Ptacek. A tsawon shekara 25 da suka gabata, Dr Ptacek da jami’ansa sun yi bincike kan irin yanayin barci na iyalai sama da 100. ""A lokacin da muka fara, mun mayar da hankali kacokan a kan me ya kamata ya zama ma’auni kan abin da muke kira da 'mutumin da ya ci gaba da barci'. Irin wadannan mutane kuma ana kiransu da ‘masu tashi kan kari’. Sukan kwanta da wuri su kuma tashi da wuri. Wasu mutane na shiga idonmu saboda tashi da wuri, amma ba za su kwanta barci a kan lokaci ba don cika ka’idojinmu. A lokacin ne muka samu labarin cewa akwai wasu iyalai da suke da ‘yan safiya da kuma ‘yan dare. Hakan ne ya sa muke tunanin cewa watakila akwai wasu abubuwa na iyalan – kamar na yin gajeren barci – wanda ke sa wasu ba sa kwanciya da wuri, amma za su tashi da wuri, su kuma gudanar da aiki ba tare da wata matsala ba. Wasu dai sun bayyana abubuwa hudu na kwayoyin halittar mutum da suka danganci yin barci kadan, sai dai yakan iya zarta wannan. Matsalar ita ce kwayoyin halittar sun bambanta. Dr Ptacek ya kiyasta cewa watakila mutum daya cikin mutane dubu ke cikin sahun ‘masu mugun barci.’ Labari mai dadin shi ne za mu iya ganin alamu na  rashin isasshen barci a tattare da su. Binciken da Dr Ptacek da tawagarsa suka gudanar ya nuna cewa masu yin wannan irin barcin za su fi sabawa da hakan a kan wasu. ""Muna da yakinin cewa wadannan mutane suna da koshin lafiya,"" a cewar mai binciken. ""Suna gajeren barci kuma suna gudanar da harkokinsu ba tare da matsala ba, saboda haka barcinsu yana da amfani a gare su. Tambayar a nan ita ce mai hakan ke nufi?"" Kamar muna kusa da amsar wannan tambaya. A wani sabon bincike, an yi duba kan kwayoyin halitta da ke da ‘alaka da yin gajeren barci ’ tare da wasu beraye da ke dauke da cutar Alzheimer ta saurin mantuwa. ""Yana da kyau saboda yana yiwuwa mu yi amfani da ilimin halittu don samun waraka, ba kawai ga cutukan da suka shafi jijiyoyin jiki da suka daina aiki ba. Har ma da cututtukan da suka shafi hauka da ciwon sukari da yawan kiba da kuma ciwon daji,"" a cewar Dr Ptacek. Ga wasunmu da ke daukar kashi daya bisa uku na rayuwarsu don yin aiki, akwai abubuwa da dama da suka kamata mu sani a kan barci. ""Wani abu na faruwa idan muka yi barci wanda zai ba mu damar yin ayyukan mu cikin kuzari idan muka tashi washegari. ""Idan muka dauki lokaci don sanin alfanun samun adadin barci da ake bukata, hakan zai yi tasiri mai kyau ga lafiyarmu.""" https://www.bbc.com/hausa/articles/czr3ej9j0k8o +health Coronavirus: Masu dauke da cutar sun haura miliyan 4 a duniya Sama da mutum miliyan 4 aka rawaito na dauke da cutar korona yanzu haka a fadin duniya. Alkaluman da Jami'ar John Hopkins ta fitar sun ce mamata sun karu zuwa 277,000 sakamakon annobar. Amurka ce kan gaba wajen yawan masu dauke da cutar, inda kashi 1 bisa 4 na adadin masu dauke da cutar da kashi 1 bisa 3 na mamata 'yan kasar ne. Kwararu sun yi gargadi sake samun karuwar wadanda za su kamu da cutar, yayinda kasashen ke fuskantar karancin gwaje-gwaje da bayanai. An samu ragin rasa rayuka a wasu kasashen, ciki akwai Spaniya, sai dai akwai fargabar da ke nuna sassauta dokar kulle ka iya sake fantsama annobar a ''karo na biyu''. Bugu da kari, gwamnatoci na rungumar matakan farfado da tattalin arziki, yayinda annobar ta yi illa ga kasuwanci a duniya da kassara duk wasu hada-hada. A wasu daga cikin manyan ci gaba da aka samu a baya-bayanan: A wannan makon, An dage dokar kulle a Italiya, wacce ta taba zama cibiyar annobar a duniya. 'Yan Italiya sun samu damar fitowa motsa jiki da ziyarta 'yan uwa a yankunansu. Faransa sama da wata guda yanzu ana samun raguwar masu mutuwa sakamakon wannan cuta, inda mutum 80 kawai suka mutu a cikin sa'o'i 24. Mahukunta na shirin sassauta dokar hana fita daga Litinin, kamar yadda makociyarta Spaniya ta yi. A kasashen irinsu Afirka ta Kudu kuwa dokar hana fita na ci gaba da aiki, duk da kiraye-kirayen da 'yan adawa ke yi na a kawo karshen dokar. A Korea ta Kudu, an sake daukan sabbin matakai a kan shagunan sayar da barasa da gidan rawa, bayan sake samun rahotan yaduwar cutar a irin wadanan wurare a Seoul. Shugabannin kasashe da dama na cigaba da bayyana fatansu na shawo kan annoba da alfannu dokar kulle. A Belarus, dubban sojoji sun gudanar da faretin bikin cika shekara 75 da nasara a yakin duniya na biyu, bayan Shugaba Alexander Lukashenko ya yi watsi da bukatar daukan matakai masu tsauri kan annobar. Mujallar kiwon lafiya ta Lancet a Burtaniya ta wallafa wata makala kan shugaban Brazil Jair Bolsonaro, wanda ta bayyana a matsayin babban barazana ga kasar sa kan gaza shawo yaduwar annobar korona. Brazil a yanzu ita ce mai yawan masu dauke da wannan cuta a kasashen Latin Amurka, sai dai shugabanta har yanzu bai yadda akwai cutar ba, sanna ya sha rigima da gwamnoni kan daukan matakan hana zirga-zirga. https://www.bbc.com/hausa/52603200 +health Yawaitar shan shisha a tsakanin ‘yan mata 'Yan mata matasa, musamman dalibai da ke makarantun sakandare da jami'oi na daga cikin masu wannan al'adar. Ko da yake wasu shan tabar a gidajensu, yawaitar wuraren shan wannan taba na kara yawa a wasu biranen kasar. Yayin da ake fito da wasu nau'ukan shisha na lataroni da ake iya ajiya a jaka kuma a yi yawo da shi. Hukumar yaki da cututtuka ta Amurka, CDC, ta ce binciken da aka yi a kan shisha mai sinadarin tobacco da na gargajiya sun nuna cewa duka suna kunshe da gurbataccen iskar carbon monoxide, da wasu abubuwa masu guba da ke kara hadarin kamuwa da cutar kansa da ciwon zuciya da na huhu. Sinadarin tobacco da ake amfani da shi a shishan da kuma hayakin da tabar ke fitarwa na dauke da abubuwa masu guba da ke janyo sankarar huhu da ta mafitsara da kuma ta baki. Hukumar ta kuma kwatanta illolin shisha da ta taba sigari, inda ta ce bincike-binciken da aka yi sun nuna cewa hayakin shisha na dauke da sinadaran nicotine da tar da kuma karafa masu yawa. Shafe sa'a guda ana shan shisha tamkar shan hayakin sigari 100 ne zuwa 200. \nYayin da a zaman shan tukunyar shisha, mutane ke fuskantar hadarin shakar gurbatacciyar iskar carbon monoxide da kuma kashi daya da digo bakwai na sinadarin nicotine da ake samu a karan sigari guda. Haka zalika hayakin da mutane ke shaka, a wannan zama ya kai mililita 90,000 idan aka kwatanta da 500 zuwa 600 da ake shaka a sigari guda. https://www.bbc.com/hausa/articles/c51g1rde196o +health Lafiya Zinariya: Alamomin cutar tsananin damuwa "Latsa hoton sama don sauraron shirin wanda Fauziyya Kabir Tukur ta gabatar Sau da yawa, mutane kan shiga cikin halin damuwa da rashin walwala saboda wasu abubuwa na yau da kullum na rayuwa. Amma idan mutum ya ci gaba da kasancewa a wannan hali na damuwa tsawon makonni ko watanni, likitoci kan ce ya gamu da cutar matsananciyar damuwa. A kan yi wa wannan cuta kallon ƙaramin abu ko wasu ma su ce rashin hakuri ne ko rashin tawakkalin wanda ya gamu da ita. Sai dai masana sun ce abin da mutane ba su gane ba shi ne cuta ce kamar ko wace irin cuta da kan kama wani ɓangare na jikin mutum. Haka kuma cuta ce da ke shafar ƙwaƙwalwa da tunani wanda mai fama da ita ba shi da iko a kanta. Dokta Ɗayyibah Shaibu, ƙwararriya a ɓangaren lafiyar ƙwaƙwalwa ta ce alama ta farko da ake gani a masu wannan cuta ita ce keɓe kai. ""Idan a baya an saba ana zama da mutum a yi hira, sai a ga yanzu ya fi son zama a ɗaki shi kaɗai ba sannan zai rage walwala. ""Ko fita za a yi gaba ɗaya mutanen gidan, mai cutar tsananin damuwa zai ce shi ba za shi ba a tafi a bar shi a gida"", a cewarta. Likitar ta ce wannan da yawan bacci ko ƙauracewar bacci da tsananin cin abinci ko rashin cin abinci inda har mutum kan ƙara ƙiba ko rage ƙiba na daga cikin manyan alamomin wannan cuta. Amma ga mai fama da ita, tsanain baƙin ciki na babu gaira babu dalili ya ke ji a ransa. Haka kuma, likitar ta ce cutar hawa-hawa ce. Akwai wadda ta yi tsananin da sai an daɗe ana shan magani kafin a samu sauƙi sanna akwai wadda ɗebe kewa da bayar da shawarwari kawai ke iya magance ta. Dokta Ɗayyibah ta ce cutar tsananin damuwa na iya kama ko wane jinsi na mutane sannan ana ganinta a manya da yara duka. Sai dai ta ce an fi ganinta a mata da matasa da suke daidai shekarun balaga. Masana lafiyar ƙwaƙwalwa sun ce sau da yawa idan wani iftila'i ya samu mutum ne ya ke shiga halin tsananin damuwa kamar rasa wani makusanci ko kora daga wajen aiki ko haihuwa mai cike da tangarda da dai sauransu. Dokta Ɗayyibah ta ce yanayin halittar ɗan Adam na taka muhimmiyar rawa wajen samun wannan matsala. ""Wani Allah ya halicce shi da juriya. Ko da abin tashin hankali ya same shi zai daure kuma ba zai zauna masa a rai ba. ""Wani kuma ba shi da haka. Allah ya halicce shi yana da rauni kuma ba ya iya jure jarrabawa, to irinsu ne suka fi gamuwa da matsalar tsananin damuwa"" a cewar Dokta Ɗayyibah. Amma likitar ta ce wani lokaci ma haka kawai mutum kan shiga damuwa har ta zamar masa wannan cuta. Dokta Dayyibah ta ce ana warkewa tsaf daga wannan cuta idan aka samu taimakon da ya kamata. ""Idan aka lura wani ya fara nuna alamomin wannan cuta, abu na farko shi ne a kai shi asibiti"", a cewarta. Akwai magunguna da hanyoyin da ake bi a asibiti ga masu fama da cutar damuwa. ""Muna ba da magunguna sannan akwai likitoci na musamman da aikinsu kawai ɗebe wa masu wanann cuta kewa da ba su shawarwari kan yadda za su tafi da rayuwarsu"", in ji Dokta Ɗayyibah. Sannan ta ce maskusantansa su riƙa jansa a jiki da nuna masa kulawa. Duka waɗannan ne ke samar da kwanciyar hankali a tare da masu cutar har su samu lafiya." https://www.bbc.com/hausa/shirye-shirye-na-musamman-54664887 +health Me ya sa ake samun karuwar mutanen da ba sa cin nama? "A sassan Birtaniya, mutane suna kashe kudi wurin sayen kayayyakin abinci da ba nama a ciki sannan kuma nau'o'in abincin da wadannan mutanen ke ci sun yadu a shafukan sada zumunta. Ganin yadda manyan shaguna suke kawo irin abincin wadannan mutanen, BBC na tambayar ko menene dalilin hakan? Irin nau'in abincin bai hada da nama da kifi da kwai da madara ba. A cewar wani bincike na baya-bayan nan na kungiyar Vegan Society wanda aka gudanar a 2018, akwai kimanin mutum 600,000 da ba sa cin nama a tsibirin Great Britain. An kididdige cewa wannan adadin ya karu daga 150,000 a 2016 kuma mata sun ninka adadin mazan da ba sa cin nama. Kusan mutum 360,000 sun bayyana kan su a matsayin wadanda suka zabi tsarin daina cin nama wanda kuma suka tsarawa kansu kin sayen kayan da aka yi da fatar dabbobi. Shagunan sayar da kayayyaki a Birtaniya na kawo karin nau'o'in abincin mutanan da ba sa cin nama domin biyan bukatun wani bangare na kwastamominsu. A 2018, kamfanin Waitrose ya ware wani bangare musamman domin ajiye nau'ikan abincin mutanen da ba sa cin nama a shagunansa sama da 130, yayin da shagon Iceland ya rawaito cewa sayen irin abincin wadannan mutanen ya karu da kashi 10 cikin dari a shekarar da ta gabata. Da yawan kamfanonin da ke sarrafa abinci, daga Greggs zuwa McDonalds da kuma Burger King zuwa KFC, sun kaddamar ko sanar da bijiro da tsarin sayar da abincin mutanen da ba sa cin nama a Birtaniya. Kasuwar sayar da abincin da ba nama a ciki a Birtaniya ta samu £740m a 2018, a cewar masu bincike a Mintel. Kudin ya karu ne daga £539m shekara uku da suka gabata. Masu son abincin da ba nama a ciki na karuwa yayin da ake sa ran kudaden da dillalai ke samu za su karu zuwa £658m nan da 2021. Kafafen sada zumunta suna da rawar takawa a karuwar masu bin tsarin cin abincin da ba nama a cikinsa. Fitattun mawaka irin su Ariana Grande da Miley Cyrus da Ellen De Generes na daga cikin mutanen da suka shahara kuma ba sa cin nama yayin da mutum sama da miliyan 87 suka wallafa sako a shafin Instagram kan maudu'in #Vegan. Batun kin cin abinci maras nama babban maudu'i ne - yawan mutanen da suke bincike kan batun a fadin duniya a Google shi ma ya karu a baya-bayan nan. Google na amfani da wata lamba cikin 100 wajen gano masu sha'awar abu. A shekarar 2009, kalmar ""veganism"" tana da matukar farin jini wadda ta yi tashe sau 33 kawai amma ya karu zuwa 100 cikin shekara 10 bayan haka. Abu uku da aka fi neman karin haske a kansu game da maudu'in a Birtaniya na neman sanin ko me kalmar veganism take nufi da dorewarta da kuma yadda take shafar sauyin yanayi. Giles Quick, wani daraktan bincike a Kantar Worldpanel ya ce ""kasuwar sayar da abincin da ba nama ta samu gagarumin sauyi cikin shekara shida ko bakwai da suka gabata - yanzu abu ne da ya zama na kowa. ""Kafafen sada zumunta sun taimaka wajen kara karbuwar tsarin a zukatan mutane. Mutane sun daina daukarsa a matsayin abincin rana kadai ko na dare ko na kwana daya."" Tsarin rashin cin ganyayyaki na lokaci zuwa lokaci ko veganism a turance, yana samun karbuwa sosai. A cikin Janairun 2019, mutum 250,000 sun yi alkawarin komawa tsarin cin abincin da ba nama a farkon watan shekarar, a ƙarƙashin gangamin Veganuary. Gangamin wanda aka kaddamar a Birtaniya a 2014 wanda kuma ya samu goyon baya a kafafen sada zumunta, ya kara karfafa wa mutane gwiwa kan su gwada cin abincin da ba nama. A cewar masu nazari, matasa mata na jan ragamar tsarin na cin abincin da ba nama. Akwai wasu dalilai da suka sa aka samu karin mutanen da ba sa cin nama. Kimanin kashi 49% na mutanen da ke sha'awar rage yawan cin nama sun ce za su yi haka ne saboda lafiyarsu a cewar wani bincike da aka yi kan sama da mutum 1,000 a tsibirin Great Britain, a cewar kamfanin binciken Mintel. Batun rage kiba da kula da walwalar dabbobi da matsalolin muhalli su ma wasu manyan abubuwa ne da ka iya jan hankalin mutane ga shiga tsarin. Yayin da ake samun karuwar mutane da ke karbar wannan tsari, tsarin rashin cin ganyayyaki na lokaci zuwa lokaci na iya komawa tsarin din-din-din." https://www.bbc.com/hausa/labarai-50984038 +health Lafiya Zinariya: Bayanai kan magungunan cutar kansa Danna hoton da ke sama don sauraron shirin: Daya daga cikin manyan hanyoyin da ake maganin ciwon daji shi ne halin wasu magunguna da ake kira chemotherapy, amma dumbin mutane musamman a wasu kasashen yammacin Afrika suna fargabar bin wannan hanya. Wasu daga cikin dalilin da ke sa mutane dari-dari da magungunan su ne illolin da ke tattare da su ta fannin kiwon lafiya. A Najeriya kasar da ta fi kowa yawan al'umma a nahiyar Afrika, wadannan magunguna na da tsadar gaske, bugu da kari kuma ba a ko'ina ake samunsu ba. Wani hadarin da masu cutar sankara ke fuskanta a kasar shi ne idan aka yi rashin dace wajen zuwa ga likitocin da basu da kwarewar bayar da magungunan. Cutar sankara ita ce cuta ta biyu da tafi kashe mutane a fadin duniya, a cewar hukumar lafiya ta duniya. WHO reshen Afrika ta ce, akalla mutane 8.8 miliyan ne suka mutu sakamakon ciwon daji a shekarar 2015. Sannan akalla kashi 70 cikin dari na wadannan mace-macen ana samunsu ne a kasashen da ke karanci da matsakaicin kudin shiga. Domin jin wasu halaye biyar da hukumar ta bayar da tace suna janyo wa masu yinsu ciwon daji, sai ku saurari shirin lafiya zinariya ta hanyar latsa makunnin da ke sama. https://www.bbc.com/hausa/shirye-shirye-na-musamman-61760196 +health Amsoshin Takardunku: Abin da ke jawo haɓo Shirin Amsoshin Takardunku na wannan makon ya amsa tamabaya game da dalilin da yake jawo haɓo wato zubar jini daga hancin mutum. Nabeela Muktar Uba ce ta gabatar da shirin. https://www.bbc.com/hausa/shirye-shirye-na-musamman-55028796 +health Abin da ke haifar da cutar farfaɗiya da yadda ake magance ta "Cutar farfadiya, kamar yadda masana cututtukan da suka shafi kwakwalwa suka bayyana, cuta ce da take shafar kwakwalwar mutum ta yadda take wargaza wani saiti mai kama da wayoyin lantarki da ke cikin kwakwalwa. Hakan kan sa wanda yake fama da cutar yin wasu dabi'u na daban ko fita daga hayyacinsa. Shi ya sa da zarar cutar ta buge wanda ya kamu da ita, takan jefa shi cikin barazanar fadawa cikin hadurra idan babu wani a kusa. Kuma bugewar kan faru ne babu zato babu tsammani. Amma masanan sun ce ba a yanke hukuncin cewa mutum ya kamu da cutar ta farfadiya har sai an fahimci marar lafiyar ya fara jijjiga fiye da kima, wanda alama ce ta farko da kan bayyana a jikin mai fama da cutar. Wannan makala ta yi duba kan wanna cuta da yadda ake kamuwa da ita da camfe-camfen da ake yi a kanta da kuma ko ana warkewa daga ita. A hira da BBC, Dakta Woru Baba Goni na Asibitin Koyarwa na Jami'ar jihar Yobe a Arewa Maso Gabashin Najeriya, ya yi karin bayanin cewa farfadiyar cuta ce da wanda ya kamu da ita yake samu daga wani bangare na kwakwalwarsa. A cewarsa: ""Ita kwakwalwa tana da wasu jijiyoyi masu kama da wayoyin lantarki da kan aike da sakonni daban-daban, da a turance ake kiransu 'spikes', idan ya zamanto ba sa aiki sosai shi ne yakan kawo cutar farfadiya"". Dakta Isa Bukar, wani kwararren likita ne a fannin kula da lafiyar masu tabin hankali a yankin Arewa Maso Gabashin Najeriya, kuma ya shaida wa BBC cewa farfadiya na daya daga manyan cutukan da suka shafi kwakwalwa da ake yawan gani a tsakanin ko wane irin rukunai ko jinsin mutane a fadin duniya. ""Duk abin da ya shafi kwakwalwa ya jawo mata wani rauni har ta samu wani tabo, to wannan tabon ka iya zama tushen samun cutar farfadiya,"" in ji Dakta Bukar. Alamomin cutar farfadiya Akwai bayanai da suka fito daga binciken masana daban-daban a fadin duniya game da alamomin cutar ta farfadiya da suka hada da: - Jijjiga musamman daga hannaye da kafafuwa. - Kafewar idanuwa zuwa kallon sama. -Gushewar hankali ko rikicewa na dan kankanen lokaci. -Alamomin razana da firgici. - Jin jiri da hajijiya. - Ganin haske kamar walkiya yayin farfadiya - Tashin zuciya da yin amai, da fitsari da ba haya lokacin farfadiya. Dakta Goni ya shaida wa BBC cewa: ""Daga nan mutum yakan yanke jiki ya fadi ya rika cizon harshe, yana jijjiga, idanu su kakkafe, a wasu lokuta yakan yi fitsari da kashi a jiki ba tare da ya sani ba"". Mene ne yake kawo cutar farfadiya? Likitoci da sauran masana kan cututtukan da suka shafi kwakwalwa a duniya da dama sun yi ittifakin cewa abubuwan da suke haifar da cutar farfadiya na da sigogi daban-daban, kuma sun danganta ga yanayin yadda mutum ya samu kansa a fannin tafiyar da rayuwa. Dakta Goni ya yi wa BBC karin bayani cewa cutar farfadiyar na iya faruwa tun daga lokacin haihuwa idan ta zo da gardama ya zamanto jaririn ya fito bai yi kukan farko ba, ko kuma wasu cututtuka kamar sankarau da shi ma kan shafi kwakwalwa. Ya kuma kara bayyana cewa: ""Yakan kuma faru idan yaro ya samu rauni, misali ko ya fado daga sama ko kan gado kansa ya bugu, yakan iya samun cutar farfadiya,"" sannan kuma ita kan ta cutar sankarau idan ba a samu an yi magani da wuri ba takan shafi kwakwalwa, wanda kan haifar da cutar ta farfadiya."" Wasu masanan sun bayyana cewa cutar zazzabin cizon sauro ma idan ta tsananta takan taba kwakwalwa. ""A wasu lokutan ma, mutum yakan kamu da cutar farfadiya sanadiyyar hadarin mota idan kai ya bugu, ya fita daga hayyacinsa har na tsawon kwanaki,"" in ji Dr Goni. Haka shi ma Dakta Bukar ya yi karin haske cewa jarirai kan fuskanci barazanar kamuwa da cutar fardadiya a lokacin haihuwarsu a bisa dalilai da dama. Ya kara da cewa: ""A wajen haihuwa idan jarirai suka sha wahala, ko wata cuta ta shige su, da taruwar jini da ruwa a cikin kwakwalwa ko kuma a ji wa yaro ciwo a kai yayin da ake kokarin tiyatar fito da shi daga ciki, duk kan iya haddasa wannan cuta."" Dr Goni ya bayyana cewa akan samu hakan ne lokacin haihuwa ko kuma lokacin yaro na ciki. ""Akwai wata matsala da kan shafi ita kwakwalwar, misali akwai wasu cututtuka da a turance ake kira 'torch complex' da kan shafi kwakwalwar yaro kafin ko kuma lokacin haihuwarsa,"" in ji shi. Har ila yau, masana sun tabbatar da cewa cutar barin jiki ita ce kan gaba wajen jawo cutar farfadiya ga mutane 'yan sama da shekara 35. ""Matsalolin cikin kwakwalwa kamar su kansar kwakwalwa da cutar shanyerwar barin jiki da aka sani a turance da 'stroke', kan iya haifar da cutar farfadiya,'' in ji Dakta Goni. Yayin da wasu masanan ke cewa an samun cutar farfadiya ta hanyar gado, wasu kuma suna ganin batun ba haka yake ba. Camfe-camfe Akwai bayanai da suka shafi al'adar camfe-camfe da dama game da cutar farfadiya musamman a kasashe masu tasowa, inda galibi mutane ke danganta farfadiya da bugun aljanu ko kuma iskokai. Hakan ya sa masu fama da ita ko danginsu kan fi dogara ne da maganin gargajiya a maimakon zuwa asibiti. Sai dai masana a fannin cutukan da suka shafi kwakwalwa sun bayyana cewa cutar ta farfadiya ba ta da alaka da bugun iska, kuma rashin zuwa asibiti a kan kari na daga cikin abubuwan da ke haddasa ta'azzarar cutar. Za ka ga da zarar cutar ta buge wanda ke da ita akan rika yin nesa da shi don gudun daukar cutar, a wasu lokuta ma a kan zuba toka ko kuma kona daidai wurin da mai farfadiyar ya tashi bayan ta sake shi duk dai don kada a dauki cutar. Masana sun ce irin haka ne ya sa masu cutar farfadiyar ba sa samun taimakion da ya kamata bayan ta buge su. A lokuta da dama za ka ga idan cutar farfadiyar ta buge wanda ya kamu da ita mutane kan kewaye shi, ko kuma a rika saka masa wani karfe a baki don kada ya ciji harshensa, ko a rika dura masa wasu jike-jike. Amma kuma masana sun bayyana cewa akwai rashin fahimta sosai dangane da wannan matsala wanda hakan ya sa ake ta yin wadannan camfe-camfen. Dakta Isa Bukar na daga cikin masanan da suka shaida wa BBC cewa wannan al'ada ta camfe-camfe da ake yi dangane da cutar farfadiya ba ta da amfani. ""Ba gaskiya ba ne a ce duk wanda ya tsallaka wurin da mai farfadiya ya tashi zai dauki cutar, hasali ma ba gaskiya ba ne a ce wai bugun aljanu ne, don haka ba zai sa don ka tsallaka inda ya tashi ka kamu da cutar ba, ba gaskiya bane,"" a cewarsa. Haka shi ma Dakta Goni ya bayyana cewa ba daidai ba ne mutane su rika danganta cutar farfadiya da aljanu, yana mai cewa larura ce da ke samun kwakwalwa. Ya kara da cewa: ""Kamar yadda na fada a baya, wayoyi ne da suke hade da kwakwalwa masu kamar na lantarki da idan suka samu matsala a nan ne akan samu wannan lalura ta farfadiya."" Ko shakka babu yanayin yadda ciwon kan buge masu fama da cutar farfadiyar ne ya sa wasu ke danganta wa da bugun iska domin za ka ga a lokaci guda marar lafiyar ya yanke jiki ya fadi yana ta karkarwa yana zubar da yawu idanusa sun kakkafe. Me ya kamata a yi wa wanda farfadiya ta buge? Idan ciwon farfadiya ya buge wanda kuke tare da shi abin da ya kamata ka yi shi ne ka cire duk abubuwan da za su iya cutar da shi - kamar kujera ko teburi ko wuta - daga gabansa, sannan kada a danne shi; a bar shi ya yi jijjga ya gama, a cewar masana. Kada a kawo wani cokali ko man ja a danna a bakinsa. Mutane sukan kewaye wanda farfadiya ta buge su hana shi shan isa. Hakan ba daidai ba ne, in ji masana. Wanda farfadiya ta buge na bukatar sarari domin ya samu iska don a lokacin yana bukatarta sosai. Masana irin su Dokta Goni sun ce tsallaka mai farfadiya ko kuma yawunsa ya taba mutum ba sa sa wa mutum ya kamu da cutar kamar yadda ake camfawa. Duk rashin sani ne yake sa kawo wadannna abubuwa Idan ana shan magani za a iya warkewa gabaki daya. Idan dai ana shan maganin lokaci mai tsawo. Rukunan mutanen da suka fi kamuwa da cutar Duk da cewa kwararru da dama sun bayyana cewa ana iya samun cutar farfadiya a tsakanin ko wane irin jinsi mace ko namiji, amma galibi ta fi shafar tsofafi da masu kananan shekaru. Idan mutum ya manyanta aka samu wata cutar sankara a kwakwalwa. Shin ana warkewa daga farfadiya? Dokta Bukar ya ce idan aka gano anihin abin da ke kawo cutar farfadiya sanna aka warware shi to za a iya warkewa. ''Mukan kwantar da su a asibiti muna lura da yadda wadannan wayoyin masu kama da na lantarki ke aiki a kwakwalwarsu yayin da suke ci gaba da shan maguguna,"" in ji shi. Amma ya ce: ""Yawanci idan kamar rauni ne aka samu ko kuma lokacin haihuwa ne ba a cika warkewa ba, sai dai a rika yawan shan magani don rage yawan samun buguwa."" Sai dai kuma kamar yadda Dakta Goni ya bayyana, akwai magani da ake kira 'Anti-convulsants' a turance da hana yawan aukuwar farfadiyar, da akan bai wa masu dauke da ita . ""Muddin marar lafiya ya rika shan maganin yadda ya kamata, zai iya rage kaifin yawan aukuwar buguwar, amma idan ba haka ba zai iya kawo masa matsala,"" in ji Goni. Me ya kamata a yiwa wanda fardadiya ta buge? Masu dauke da cutar farfadiya na matukar bukatar taimako a koda yaushe, saboda irin halin da sukan samu kan su a lokacin da ta buge su. Haka ya sa kwararru ke fadakar da mutane, musamman makusantan masu dauke da cutar cewa kada su rika kasancewa cikin duhu kan matakan da suka kamata su dauka na kai daukin gaggawa ga wadanda ke dauke da cutar. Dr Goni ya bayyana cewa: ""Ana son a tabbatar da an kawar da duk wani abu da aka san zai ji wa maras lafiya barazana kamar wuta, ko kujera, teburi ko wani karfe a lokacin da cutar ta buge shi"". Ya ce: ""Kada a taru a kan maras lafiya don yana bukatar iska sosai, a kyale shi ya numfasa kafin nan a garzaya da shi asibiti"". Haka kuma in ji shi ma masani Dakta Bukar akwai masu al'adar dura wa mai farfadiya man ja ko wani jiko a baki wai don ya farfado, amma hakan ba daidai ba ne. Ya kara da cewa: ""Bai kamata a ba shi wani abu ko a dura masa magani a baki ba, hakan zai iya shake shi ya hana shi numfashi, ko a saka masa cokali ko wani abu a baki ba don zai iya kawo masa damuwa a lokacin"". Lokaci zafi ko kuma zafin rana ka iya kar yawan abkuwar bugun farfadiya ga mai dauke da cutar, idan aka samu matsala zai iya buge shi, haka ma idan sanyi ya yi yawa. Abinda wasu masu cutar farfadiya ke cewa Wani dattijo mai fama da cutar farfadiya ya shaida wa BBC cewa a da shi da danginsa suna cewa aljanu ne suka kama shi don haka ba su taba tunanin zuwa asibiti ba. ""Da muna rokon Allah ne da kuma maganin gargajiya, mun dauka aljanu ne, a da da zarar farfadiya ya buge ni sai in nemi wajen da wuta take in shiga, amma daga baya aka ba mu shawarar ganin likita,"" in ji dattijon. Ita ma mahaifiyar wani matashi mai cutar farfadiya ta ce lokacin da abin ya shafe shi mun dauka iskokai ne shi ya sa suka rika yin na gargajiya. Ta kara da cewa: ""Lokacin nan mutane sai suka rika cewa iskokai ne, har ya samu shekaru da dama, shi ne daga baya aka ba ni shawarar in kai shi asibiti don a duba lafiyarsa, saboda tun yana karami ya taba faduwa ta kai."" Ta kuma bayyana yanayin yadda farfadiyar ke buge dan nata: ''Farkon da ya fara, cutar ta kan buge shi har sau goma a rana. Wani magidanci da ya kamu da cutar da farfadiya shi ma ya bayyana yadda ya fara da cewa ya dauka ciwon ba na asibiti bane. ''Ya kai wajen shekara daya da wani abu lokacin da na fara cutar farfadiya, kuma mun fara na gargajiya ne amma abin sai ya rika karuwa shi yasa aka kai ne asibiti, yanzu ina samun sauki,'' ya ce. Lokacin da ya kamata a gagaguta kai mai farfadiya wajen likita Ya kamata wadanda ke tare da mai cutar farfadiya su rika lura sosai da yanayin da yake ciki, domin sanin lokacin da ya dace a dauki matakin gaggawa na ganin likita. Alamomin dai in ji kwararru sun hada da:" https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-56122014 +health Abu huɗu da masana suka gano game da cutar kiɗimewa "Wani sabon magani, da gwaje-gwajen jini da kuma wata alƙaryar kula da masu larura na cikin abubuwa guda huɗu da ke ba da ƙwarin gwiwa ga mutanen da ke rayuwa cikin kiɗima a tsawon sama da shekara huɗu. Kuma ƙarin ci gaba na nan tafe don taimakawa kowa da kowa - matashi da tsoho - a tsakanin dangin da ke fama da cutar kiɗimewa. Akwai ƙwaƙƙwaran ci gaba a shekarun baya-bayan nan, huɗu daga ciki mun zayyana su a nan ƙasa don tunawa da Ranar Cutar Kiɗimewa ta Duniya da ake yi duk 21 ga watan Satumba. Mece ce cutar kiɗimewa? Cutar kiɗimewa, wata larura ce da ta zama ruwan dare da ke haddasa cutar tsananin mantuwa ga tsofaffi, lamarin da ya shafi mutane sama da miliyan 55, a cewar Gidauniyar Masu Larurar Kiɗimewa ta Duniya. Da Ingilishi, ana kiran cutar da Alzheimer inda ta ci sunan Dr Alois Alzheimer. A 1906, ya lura da sauye-sauye a jijiyoyin ƙwaƙwalwar wata mata da ta mutu ɗauke da alamomin da suka haɗar da ƙwacewar tuna abubuwa da matsalolin harshe. Dr Sara Imarisio, Shugabar Bincike a Cibiyar Binciken Cutar Kiɗimewa ta Birtaniya ta shaida wa BBC cewa: ""Bincike na inganta yadda muke duba lafiyar mutane, don karewa da kuma kula da masu larurar kiɗima. ""Samar da kuɗaɗen gudanar da binciken farko a tsawon shekaru da dama, ya tallafa wa haziƙan mutane wajen samo dabaru masu ƙarfafa zuciya, lamarin da ya kawo mu ga wannan mataki, da aka samu hanyoyin yiwuwar magance cutar kiɗimewa da yawa."" 1: 'Gagarumin ci gaba' daga binciken da halittun gado suka yi tasiri a (2022) Wani ""muhimmin"" nazari a bana ya alaƙanta ƙarin wasu halittun gado guda 42 da cutar kiɗima a karon farko. Masu ilmin kimiyya a ƙasashe guda takwas ciki har da Faransa da Amurka da Burtaniya da Ostireliya sun yi nazari kan ƙwayar halittar gado ta mutum 111,000 da ke fama da cutar kiɗimewa. Kuma sun gano ƙwayoyin gado 75 masu alaƙa da ƙaruwar hatsarin da ke kawo cutar, a ciki har da guda 42 waɗanda a baya sam ba a danganta su da wannan larura ba. Abubuwan da suka gano kuma aka wallafa a mujallar [/CPS/32776360]Nature Genetics, sun nuna cewa sabubba da yawa ne ke haddasa cutar kiɗima da hujjar da aka samu ta wani taƙamaiman sinadarin furotin mai alaƙa da kumewa. Farfesa Julie Williams wadda suka yi binciken haɗin gwiwar ta bayyana aikin a matsayin ""wani gagarumin ci gaba a ƙoƙarinmu na fahimtar larurar kiɗimewa da kuma a ƙarshe mu samar da hanyoyin magani masu yawa da ake buƙata don kawo jinkiri ko kuma kare kamuwa da cutar"". ""Sakamakon binciken ya tallafa wa ilmin da ke bunƙasa na cewa cutar kiɗima, wata larura ce mai matuƙar sarƙaƙiya da sababi birjik masu janyo ta, da sauye-sauyen ƙwayoyin halittu da kuma nau'o'in ƙwayar halittar masu alaƙa da bunƙasar ta."" Sauran binciken ya nuna cewa sabubban salon rayuwa kamar shan taba sigari da ɗabi'ar cin wani nau'in abinci, na da tasiri ga mutumin da zai iya shiga kiɗimewa. Amma masu bincike sun yi imani ƙwayoyin halittun gado su ne mafi hatsari wajen kawo wannan cuta. 2: Alƙarya masu larurar kiɗimewa (2020) Wata sabuwar fahimta kuma, ta kula, da maganin larurar kiɗimewa ita ce alƙaryoyin da aka gina takanas don masu larurar, inda za su zauna su yi rayuwa kamar yadda suka saba, amma ko da yaushe a kan idon masu ba da kulawa. Faransa ta kafa wata alƙaryar da aka kebe wa masu larurar kiɗima a 2020, la'akari da wata alƙarya ta ""masu larurar tsananin mantuwa"" a ƙasar Netherlands. An kafa alƙaryar ce a Dax kudu maso yammacin Faransa, inda aka tanadi kantin sayen kayayyaki da na gyaran gashi ko aski da kuma gidajen kaɗe-kaɗe. An tsara alƙaryar ce don ta dace da irin garuruwan nan na gargajiya masu ganuwa da shimfiɗaɗɗen sarari da za a tabbatar da ganin komai na tafiya daidai. Mai tsara alƙaryar ya faɗa wa jaridar Le Monde cewa alƙaryar ba ta da ganuwa a zahiri amma tana da hanyoyi da yawa masu aminci da kuma tsarin al'adu da zamantakewar birni mai matuƙar gauraya. Madeleine Elissalde mai shekara 82 na cikin mutanen da suka fara tarewa. ""Ina jin nutsuwa,"" in ji Elissade. ""Ana matuƙar kula da mu."" ""ƙwacewar tunaninta ya rage tsanani,"" cewar Aurore, jikar Elissalde. ""Tana cikin farin ciki kuma tana sake samun nishaɗi tamkar a rayuwarta ta baya."" Daya daga cikin sakamakon kafa alƙaryar masu kiɗimewa ita ce mutanen da ke zaune kusa da ita ga alama suna canza fahimtarsu game da masu irin wannan larura. An wallafa wani safiyo na mazauna birnin da ke karbar baƙuncin alƙaryar\n[/CPS/32776361] a watan Agustan 2022. Ya nuna ƙarancin adadi na mutanen da ke nuna tsana ga masu larurar kiɗima bayan buɗe alƙaryar, idan an kwatanta da wani birni maras alƙaryar masu kiɗimewa, inda ɗabi'ar nuna tsanar ta tsaya kamar yadda aka sani a baya. 3: Amurka ta amince da wani sabon magani na farko don masu kiɗimewa a cikin shekara 20 (2021) Hukumomi karon farko a Amurka cikin watan Yunin 2021 a kusan shekara 20 sun amince da wani sabon magani ga masu larurar kiɗimewa. Maganin Aducanumab na kashe manyan sabubban da ke haddasa kiɗimewa, nau'in da ya fi zama ruwan dare na larurar tsananin mantuwa, maimakon alamomin cutar. A watan Maris na 2019 ne, aka dakatar da gwaje-gwajen ƙarshe na maganin Aducanumab, wanda ya ƙunshi marasa lafiya kimanin 3,000. Hakan ya zo ne sakamakon ƙididdigar da aka yi mai nuna maganin ɗure duk wata, ba shi da wani inganci wajen rage taɓarɓarewar tuna abubuwa da matsalolin tunani a kan wani magani makamancinsa. Sai dai daga bisani, kamfanin Biogen mai haɗa magunguna a Amurka ya ƙalailaice ƙarin bayanai kuma ya tabbatar cewa maganin yana da tasiri, matuƙar aka bai wa maras lafiya adadi mai yawa. Kamfanin ya kuma ce maganin ya yi matuƙar rage taɓarɓarewar fikira. Sai dai a watan Disamban 2021 Hukumar kula da Magunguna ta Turai ta ce ba za ta amince da shi ba. Hukumar ta ce maganin Aducanumab ga alama ba shi da tasiri wajen yi wa magidantan da ke ɗauke da alamomin farko-farko na cutar kiɗimewa magani. A lokacin da ake amincewa da maganin a Amurka, wasu masana kimiyya sun ce akwai shaida 'yar kaɗan daga gwaje-gwajen da aka yi na amfanin maganin, duk da yake yana kashe amilod - wani nau'in sinadarin furotin da ke jibge tarkace a ƙwaƙwalen mutane masu cutar kiɗimewa. Don haka yayin da ake sayar da sabon maganin a Amurka, can a wani wuri kuma ana da tababa kan tasirinsa. 4: Gwaje-gwajen jini don gano cutar kiɗimewa kafin bayyanar alamominta (2019) Masana kimiyya sun ce a 2019, suna iya ganowa daidai wa daida mutanen da ke kan hanyar samun kiɗima kafin ma alamomin cutar su bayyana. Sun yi imanin cewa hakan zai iya taimakawa wajen samun bunƙasar gwaje-gwajen magani. Masana kimiyyar Amurka na iya amfani da yawan sinadarin amilod a cikin jini don taimakawa wajen hasashen tattaruwarsa a ƙwaƙwalwa. Masu bincike daga Tsangayar Nazarin Likitanci a Jami'ar Washington ta jihar Missourin Amurka[/CPS/32773325] sun yi rubutu a mujallar Neurology inda suka gwada yawan sinadarin amilod beta furotin a cikin jinin mutum 158 'yan sama da shekara 50. Suna son ganin ko hoton ƙwaƙwalwa zai nuna makamancin wannan adadi. Hoton, tabbas ya nuna irin wannan adadi, sai dai kawai ga kashi 88 na yawan gwajin da aka yi ne, abin da bai isa zama hujjar haƙiƙa ba ga hanyar duba lafiya. Lokacin da masu binciken suka haɗa wannan bayani da sauran sababi biyu na kamuwa da cutar - kasancewar mutum ɗan sama da shekara 65 da mutane masu nau'in ƙwayar halittar gado da ake kira APOE4 - haƙiƙar gwajin jinin ya inganta zuwa kashi 94. BBC ta ambato ƙwararru a Burtaniya cikin 2019 na cewa sakamakon mai ƙarfafa zuciya ne kuma wani ci gaba ne wajen samun wani gwajin jini abin dogaro don cutar kiɗimewa, ta yadda za a hanzarta bincike kan cutar tsananin mantuwa. Sai dai, ƙwararrun likitoci kuma sun yi gargaɗi a kan dogaro da gwaje-gwajen jini a yanzu. Gidauniyar cutar Kiɗimewa ta Amurka[/CPS/32773326] ta ce ""Duk da yawan gwaje-gwajen cutar tsananin mantuwa da ake kambawa kai tsaye ga abokan hulɗa, babu ɗaya a ciki da aka tabbatar da haƙiƙar ingancinsa"". Gidauniyar ta ba da shawarar likita ya duba lafiyar mutum ta hanyar bin diddigin wasu sabubba: ""Ga waɗannan, da ma sauran wasu dalilai, Gidauniyar masu Larurar Kiɗimewa ta yi imanin cewa gwaje-gwajen da ake yi a gida ba za su iya, kuma bai kamata a yi amfani da su a matsayin wani madadin binciken ƙalailaicewa da wani ƙwararren likita zai yi ba."" A taƙaice, akwai yiwuwar samun hanyar gwajin jini don gano cutar kiɗimewa sai dai hanyar duba lafiya don gano wata halayya, muhimmiyar dabara ce ta tabbatarwa idan akwai alamomin larurar. Makomar maganin kiɗimewa da cutar tsananin mantuwa A cewar Dr Sara Imarisio Shugabar Bincike a Cibiyar harkokin Binciken cutar Kiɗimewa ta Burtaniya akwai magunguna sama da 150 da ke matakin gwaje-gwaje na cutar kiɗimewa. Sai dai ta yi gargaɗin cewa za su ɗauki lokaci kafin kammala wannan mataki zuwa samun amincewa, kuma su haɗa su don amfanin wani maras lafiya. ""Nan gaba, matakan kare kamuwa da cutar da suka haɗar da shan magani da canza salon rayuwa na iya zama hanya mafi inganci ta taƙaita illar cutar tsananin mantuwa. Yayin da sabbin magungunan za su ɗauki shekaru da yawa kafin su tabbata, canza salon rayuwa abu ne da ke kusa da mu."" A ƙarshe, rage hatsarin da mutum ke ciki ta hanyar rungumar matakan salon rayuwa masu inganta lafiya zai taimaka wajen taƙaita yiwuwar shiga kiɗima. Amma, yayin da kimiyyar aikin likitanci ke bunƙasa, kamata ya yi ita ma ta ƙara ba da gudunmawa wajen yaƙi da wannan babban sababi da ke haddasa tsananin matuwa." https://www.bbc.com/hausa/articles/cv2p1gjg9r2o +health Yadda za ka gano ko kana da kansar hanji Dame Deborah James, wadda ta rasu a sakamakon kamuwa da cutar daji ta hanji tana shekara 40, ta bayar da shawara ga kowa, da mutum ya rika duba kashinsa a matsayin wata hanya ta fadakarwa a kan wannan nau'in cutar kansa. Mun amsa tambayoyin da yawancin mutane ke yi game da wannan nau'in cutar daji da kusan galibin mutane ke gamuwa da ita a Birtaniya. Akwai muhimman abubuwa uku da za ka duba: Za a iya samun wasu karin alamun: Ganin wadannan alamomi ba wai lalle hakan na nufin kana da cutar daji ta hanji ba ne. Amma shawara ita ce ta je ka ga likita, idan har ka ga alamar ta wuce mako uku ko fi, ko kuma idan ba ka jin dadi. Hakan na nufin za a iya saurin gano matsalar a magance ta. Ita cutar daji gano ta da wuri kan sa a iya magance ta da wurwuri. Wani lokaci cutar daji na iya hana mutum bahaya, wanda hakan na iya toshe dubura. Wannan na iya sa ciwon ciki mai tsanani da rashin yin kashi da kuma rashin lafiya. Idan ka samu kanka a wannan yanayi to ba shakka kana bukatar ka garzaya zuwa asibiti da gaggawa. Ka sa ido sosai ka ga yadda kashinka yake kuma kar fa ka ji kunyar yin magana a kai. Ka duba sosai ka ga ko akwai jini a cikin kashinka ko kuma daga can kasan kasin. Jini mai haske ka iya kasancewa daga wata jijiya ce da ta kunbura a duburarka wato basir kenan, haka kuma zai iay kasancewa cutar dajin ce ta janyo. Idan jinin yana da duhu a kashinka, to hakan zai iya kasancewa daga hanjinka ko kuma tumbinka yake, shi ma kuma zai iya kasancewa abin damuwa. Za kuma ka iya samun sauyi a yanayin bahayarka, kamar kashin ya kasance ruwa-ruwa ko kuma zuwa bandaki fiye da kima. Ko kuma ka ji kamar da sauran kashi a cikinka bayan ka je bandaki. Haka kuma rashin zuwa bandaki yadda ya kamata. Kungiyar likitocin cutar kansar hanji ta Birtaniya na bayar da shawar a rika rubuta jerin bayanan alamun da mutum ya gani kafin ya je ganin likita, saboda kada ka manta da wani abin. Likitoci sun saba ganin mutane da alamun matsaloli daban-daban na hanji, saboda haka ka gaya wa likita duk wani sauyi da ka gani ko kuma jinin da ka gani domin a gano abin da ya haifar da hakan. Ba wanda zai iya cewa takamaimai ga abin da ke janyo cutar, to amma akwai abubuwan da ake ganin za su iya janyo ta: Yawanci ba a gadon cutar, to amma idan akwai wani a danginku da aka taba samu da ita kafin ya kai shekara 50 to yana da kyau ka gaya wa likita. Akwai yanayi na gado kamar matsalar kuraje ko kumburi a hanji, wanda hakan ka iya haddasa cutar. To amma likitoci za su iya magance wannan idan sun san da ita. Masana kimiyya sun ce za a iya kare kusan rabin hadarin kamuwa da cutar idan mutum yana bin hanyoyin rayuwa na lafiya. Wannan na nufin yawan motsa jiki da cin 'ya'yan itace da ganyayyaki da rage cin maiko da shan ruwa kusan kofi shida zuwa takwas a duk rana. Bayan wadanna akwai kuma bukatar zuwa ganin likita a duk lokacin da ka ga wata alama, da kuma amfani da damar yin gwajin cutar daji a duk lokacin da aka samu damar. Ana yin gwaji don gano alamun cutar daji ta hanji tun ba ta yi girma ba. Akwai kayan gwaji na gida, wanda ke gano awata lamar jini a kashinka. Gwajin da za ka iya yi a gida ka aika asibiti. Sai dai ba kowa ba ne yake samun wannan abin gwaji, sai wadanda ke rukunin shekarun da ake ganin za su iya samun cutar. Ana yin gwajin a fadin Birtaniya. Ba a samun dacewa dari bisa dari a bincike, wanda kuma zai iya kaiwa ga yin maganin da zai iya cutarwa ko kuma wanda bai kamata ba, idan ana gwajin mutane da yawa masu lafiya. Saboda haka idan kai matashi ne kuma kana da alamun cutar, yana da kyau ka san alamun kuma ka ziyarci likitanka idan har ka damu - kada ka sayi kayan gwajin ka je ka yi da kanka, saboda sakamakon ka iya ba ka wani abu mai rikitarwa. Da zaran da mayar da kayan gwajin da ka yi, za a sanar da kai idan ba ka dauke da cutar ko kuma asibitinka ya tuntube ka domin a yi maka karin gwaje-gwaje. Karin gwajin ka iya kasancewa wanda za a sanya maka wata 'yar karamar na'urar daukar hoto a cikinta wadda za ta ratsa cikin hanjinka - ko kuma daukar hoton wani gefe na hanjin. Sama da kashi 90 cikin dari na mutanen da aka gano suna dauke da cutar tun tana farko-farkonta suna iya ci gaba da rayuwa karin tsawon shekara biyar ko fi, sabanin kashi 44 cikin dari na wadanda aka gano cutar bayan da ta yi nisa. Damar rayuwa ga wadanda aka gano suna dauke da cutar a Birtaniya ta ninka sama da kashi biyu a shekara 40 da ta gabata. Sama da rabin masu cutar yanzu suna rayuwa tsawon shekara 10 ko fi sabanin yadda ake gani a shekarun 1970. Wannan cuta kamar sauran cutar daji, mutanen da ke rukunin shekara 15 zuwa 40 suna da damar rayuwa sosai, saboda cutar daji ta fi kamawa da kuma illa ga tsofaffi ko masu yawan shekaru. Ana maganin cutar daji ta hanji musamman ma idan ana gano ta da wuri. A duk matakin da aka gano mutum na dauke da cutar za a iya gaya masa abin da za a iya yi a kai. Wannan ka iya kasancewa tiyata ko gashi ko kuma amfani da magunguna domin kashe kwayoyin cutar, ya dai danganta ga yanayin cutar a jikin mutum. https://www.bbc.com/hausa/articles/cp6k7j4r31no +health Masu fama da tarin fuka sun ragu - WHO Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce ta yi nasarar yaki da cutar tarin fuka kuma mutum miliyan bakwai aka iya warkarwa daga cutar - adadin da ya haura na shekarar 2017. WHO ta ce adadin wadanda aka warkar ya haura na shekarar 2017 inda aka yi nasarar jinyar mutum miliyan shida da dubu dari hudu. Rahoton na WHO, ya nuna cewa an samu raguwar mutanen da suke mutuwa sanadiyyar kamuwa da cutar kasancewar mutum miliyan daya da dubu dari biyar ne suka mutu a shekarar da ta wuce, sabanin mutum miliyon daya da dubu dari shida da suka mutu bara. Hukumar lafiya ta duniyar ta alakanta nasarar da aka samu da yadda ake gano mutanen da suke harbuwa da cutar da kuma ingancin maganin da ake musu. Sai dai hukumar ta kara da cewa ba a yi katarin gano dukkan mutanen da ke harbuwa da cutar tarin fukar da aka yi harin cimma wa ba a duniya, kasancewar har yanzu akwai kimanin mutum miliyan uku da ke fama da cutar. Rahoton na WHO ya bayyana kasashe takwas a duniya da suka fi yawan mutanen da ke fama da cutar tarin fuka a duniya a shekarar da ta wuce, wadanda suka hada da Bangladesh da China da Indiya da Indonesiya da Najeriya da Pakistan da Philippines da kuma Afirka ta kudu. WHO ta ce rashin tsarin kiwon lafiya mai nagarta na daga cikin matsalolin da ake fuskanta a kasashe da dama wajen gano masu kamuwa da cutar da jinyar da ake musu. Ta ce wannan ya sa mafi yawan masu harbuwa da cutar a irin wadannan kasashe na shiga wani hali, kasancewar kashi 20 cikin dari na abin da suke samu na karewa ne wajen jinya. Rahoton ya jaddada muhimmancin inganta bincike da samar da karin kudi don ci gaba da yakin da ake yi da cutar, musamman ma a shekarar 2019, saboda rahoton ya nuna cewa akwai gibi ta fuskar kudi. Hukumar lafiyar ta kiyasta cewa ana bukatar cike gibin da ya kai dala biliyon uku da miliyon dari uku na kudin da ake bukata don yin kariya ga cutar tarin fuka a duniya. Sai dai duk da wannan kalubalen, wannan nasarar da aka samu a bara ta kara wa hukumar ta lafiya kwarin-gwiwar cewa za a iya cimma muradin da ake da shi na dakile cutar tarin fuka a duniya nan da shekara ta 2030, musamman ma idan aka samu hadin-gwiwar da ake bukata daga dukkan bangarorin da lamarin ya shafa. https://www.bbc.com/hausa/labarai-50093060 +health Amincewa da allurar riga-kafi na raguwa a duniya "Yadda jama'a suke ci gaba da kin amincewa da sahihancin alluran riga-kafi na jawo koma-baya a yaki da cutuka masu saurin kisa, wadanda za a iya kare su, kamar yadda masana suka yi gargadi. Wani babban nazari da aka yi kan yadda jama'a suke kallon sahihancin riga-kafi ya nuna cewa mutane da dama suna dari-dari da ita. Binciken da cibiyar Wellcome Trust ta yi ya tattara bayanai daga mutum 140,000 daga kasa 140. Wannan na zuwa ne yayin da hukumar lafiya ta duniya WHO ta zayyana dari-darin mutane ga allurar riga-kafi a matsayin daya daga cikin matsaloli 10 da suke kawo wa lafiyar duniya barazana. Wani binkicen na duniya baki daya ya gano yadda mutane masu yawan gaske suke kyamar allurar riga-kafin. Yayin da aka tambaye su ko alluran sahihai ne?: Da aka tambaye su ko riga-kafi na aiki?: Me yasa aka damu? Akwai hujjoji masu yawsan gaske da suka tabbatar cewa riga-kafi ita ce babbar hanyar kariya daga cutuka masu hatsari, kamar kyanda. Riga-kafi tana bai wa biliyoyin mutane kariya a fadin duniya. An rabu da wata cuta har abada, kamar bakon-dauro sannan kuma muna taimakawa wajen kawo karshen wasu, kamar Shan-inna. Sai dai wasu cutukan masu wuyar sha'ani kamar kyanda suna sake dawowa, kuma masana sun ce kyamar da mutane ke nuna wa riga-kafi ce bisa camfe-camfe da labaran kanzon-kurege ke jawo hakan. Dokta Ann Lindstrand kwararriyar likita kan riga-kafi a Hukumar Lafiya (WHO) ta ce matsalolin da ake ciki yanzu masu girma ne sosai. ""Kyamar riga-kafi a wasu wurare na taimakawa wajen kawo nakasu ga ci gaban da aka samu a duniya game da cutukan da ake iya mnagancewa ta hanyar riga-kafi. ""Muna ganin dawowar cutukan a matsayin ci baya kuma abu ne da ba za mu amince da shi ba."" kasashen da suka kusa kawo karshen cutar kyanda sun yi ta fama da annoba iri-iri. Bayanai sun nuna karuwar cutuka a kusan kowane yanki na duniya, inda aka samu karin kashi 30% a 2017 sama da yadda aka samu a 2016. Rashin yin riga-kafi yana kawo barazanar kamuwa da cutuka ga daidaiku da kuma daukacin jama'ar gari. Idan aka yi wa mutane isassu, riga-kafin zai taimaka wajen hana yaduwar cuta ga al'umma - abin da masana ke kira ""garkuwa ga a'umma"" ko kuma ""herd immunity"" a turance. Imran Khan na cibiyar Wellcome Trust ya ce: ""Akwai damuwa a halin yanzu a kan kyanda. In dai har ba a cim ma kashi 95% na riga-kafinta ba to za a iya samun annoba kuma abin da yake faruwa kenan a yanzu."" Iyalai wadanda ke zaune a garuruwan da ke da tattalin arziki mai kyau su ne ba su fiye dari-dari da sahihancin allurar riga-kafi ba sosai. A kasar Faransa daya daga cikin kasashen Turai da suke fama da annobar kyanda, duk mutum daya a cikin uku bai yarda da sahihancin riga-kafi ba. Wannan shi ne kaso mafi girma da za a iya samu a kowacce kasa a duniya. Ana sa ran yiwuwar cewa 'yan Faransa na cikin wadanda za su ki yarda da sahihancin riga-kafin (kashi 19%), sannan kuma su ki amincewa cewa tana da amfani ga kananan yara (kashi 10%). Yanzu haka gwamnatin kasar ta kara allurar riga-kafi takwas a kan uku da suka wajabta a yi wa kananan yara. A makwabciyar Faransa kuma wato Italiya, inda kashi 76% suka amince da sahihancin riga-kafi, an kafa dokar hana yaran da ba ayi wa riga-kafin ba shiga makaranta ko kuma cin tarar iyayensu. Burtaniya har yanzu ba ta bi sahu ba, amma sakataren lafiya Matt Hancock ya ce ""akwai yiwuwar"" bullo da allurar riga-kafi ta wajibi ga jama'a. Amurka tana fuskantar irin tata annobar kyandar, wadda ita ce mafi grima da ta barke a kasar cikin shekaru, inda aka tabbatar da mutum 980 sun kamu da cutar a jiha 26 cikin shekarar 2019 kadai. A arewacin Amurka da kudanci da kuma arewacin Turai, kashi 70% ne suka amince da sahihancin riga-kafi. Sakamakon ya yi kasa sosai da na yammacin Turai (kashi 59%) da kuma gabashin Turai (kashi 50%). A kasar Ukraine, inda aka ruwaito mafi yawan kamuwa da kyanda a nahiyar Turai a bara (53,218), kashi 50% ne kawai na mutane suka amince cewa riga-kafi tana aiki. Kashi 46% ne suke da irin wannan ra'ayi a kasar Belarus, 49% a kasar Moldova, sai kuma 62% a Rasha. Labaran yin nasara Mafi yawan al'ummar da ke zaune a wuraren da tattalin arzikinsu ba shi da yalwa sun aminta cewa allurar riga-kafi tana da sahihanci. Yankin kudancin Asiya shi ne kan gaba, inda kashi 95% na jama'a suka amince, gabashin Afirka ke biye masu da kashi 92%. Kasashen Bangladesh da Rwanda sun cim ma kusan kashi 100% wajen amincewa da sahihancin riga-kafi, sannan sun cim ma kashi mai yawa na yin allurar duk da kalubalen da suke fuskanta na kai alluran ga mutane. Rwanda a matsayinta na kasa mai tasowa ita ce farko da ta bai wa 'yan mata damar yin riga-kafin HPV wadda ke ba da kariya daga kansar mahaifa. Mista Khan ya ce: ""Hakan ya nuna irin abin da za a iya cimmawa idan aka hada karfi wuri guda wajen yin riga-kafi"". Me ya sa mutane suke da shakku? A nazarin da aka yi, mutanen da suka yarda da binciken kimiyya da likitoci da ma'aikatan jinya na da saukin kai wajen amincewa da sahihancin riga-kafi. Amma akasin haka ake samu a bangaren mutanen da suke ci gaba da neman sani game da aikace-aikacen masana kimiyya da ma'aikatan kula da lafiya. Rahoton Wellcome bai bayyana duka dalilan da suke sa wasu nuna shakku kan riga-kafi ba, amma masu nazari sun ce akwai wasu karin dalilai. Wasu na ganin yin kasa gwiwa shi ma wani dalili ne - idan aka ce cutar ta daina yaduwa, wasu sukan yi sako-sako wajen shan riga-kafinta. Dukkan magunguna ciki har da alluran riga-kafi sukan iya jawo wasu 'yan matsaloli. Amma ana gwada riga-kafi don tabbatar da sahihancinsu da amfaninsu. Intanet za ta iya zama wata kafa da ake yada wasu bayanai wadanda wasu lokuta ba gaskiya ba ne. A kasar Japan, jama'a na nuna damuwa game da riga-kafin cutar HPV kuma ana danganta ta da cutukan kwakwalwa, wanda masana suke ganin hakan ya shafi yadda mutane suka aminta da allurar riga-kafin. Haka zalika, a Faransa akwai ce-ce-ku-ce kan riga-kafin wata matsananciyar mura - inda ake zargin gwamnati da kawo adadin riga-kafi mai yawa da batun da ake cewa an samar da magungunan ne cikin sauri kuma za su iya zama marasa sahihanci. A Burtaniya ana ci gaba da samun labarai marasa sahihanci game da cutar MMR da cutar galahanga. Dokta Lindstrand ya ce: ""Babban abin da za a yi don kawar da shakku da damuwar da wasu ke nunawa game da riga-kafi shi ne bai wa ma'aikatan lafiya cikakken horo kuma su kasance cikin shirin ba da riga-kafi bisa dogaro da sahihan binciken kimiyya."" Ya ci gaba da cewa ""kuma su iya bayar da amsoshi ga damuwar da wasu iyaye da al'umma ke da ita kan allurar riga-kafi."" Becky Dale da Christine Jeavans ne suka hada wannan makala; sai Debie Loizou da Scott Jarvisda kuma Katia Artsenkova wadanda suka shirya da kuma tsarawa." https://www.bbc.com/hausa/labarai-48679077 +health Coronavirus: Me ya sa cutar korona ta mayar da ɓeraye mugaye? "Annobar korona ta sa an rufe gidajen cin abinci sannan ta tilasta wa mutane zaman gida. Hakan ya jawo abbubuwa guda biyu; wajibi ne ɓeraye su nemi abincinsu a wani wuri daban sannan kuma su sauya ɗabi'unsu. Hukumar Daƙile Yaɗuwar Cutuka ta Amurka (CDC) ta yi gargaɗi a makon da ya gabata cewa, ɓeraye mayunwata za su iya ""sabuwar ɗabi'a kuma mai cutarwa"". Gargaɗin ya nuna cewa rufe gidajen cin abinci ""ya jawo ƙarancin abinci ga ɓeraye, musamman a wuraren da ke da yawan al'umma"". Ɓerayen na neman sabbin hanyoyin samun abinci, abin da ya ƙara yawan zirga-zirgarsu a faɗin duniya. Babban misali shi ne taron casu da aka haɗa a watan Fabrairu a birnin Louisiana na ƙasar Amurka, inda dubban mutane suka taru a gidajen cin abinci da wuraren kaɗe-kaɗe, amma sai annobar korona ta tilasta musu rufe ƙofofinsu. Su kuwa ɓeraye sai suka fito daga gidajen ɓuyansu kamar a sauran sassan Amurka - kamar a Washington da New York. ""Ma'aikatan tsafta da masu kula da ɓeraye za su fuskanci hauhawar neman buƙata da kuma rahotannin sabbin halayen ɓeraye,"" a cewar CDC. Wani ƙwararre kan halayen ɓera mai suna Robert Corrigan a Amurka, ya ce wannan sabuwar ɗabi'a ba wai a kan mutane za su nuna ta ba, a kan sauran ɓeraye za ta ƙare da kuma wurare yayin da suke neman rami domin shiga da zummar samun abinci. Ya ce: ""Hakan ba ya nufin ba za su kai wa mutane hari ba."" Aƙalla kashi ɗaya bisa uku na al'ummar duniya sun sauya halayensu a 'yan watannin nan saboda wannan annoba. A ƙasashe da dama, an taƙaita zubar da shara wadda kuma ita ce ɓeraye suka dogara a kai domin samun kai wa baka, kuma hakan ya sa ɓerayen suka saba. A watan Afrilu, hukumar kula da ƙwari ta National Pest Technicians Association a Birtaniya ta yi gargaɗin cewa ""rufe wuraren taruwar jama'a da na cin abinci da otel-otel zai jawo matsaloli"". Hukumar ta ce dabbobi masu ɓarna za su iya hayayyafa a wuraren da babu jama'a ko kuma su fita neman abinci, yayin da suke samun ƙwarin gwiwa daga yunwar da ke damunsu. ""Ɓeran da ke jin yunwa zai iya zama mai haɗarin gaske ga sauran ɓeraye,"" in ji Corrigan, wanda ya yi aiki a matsayin ƙwararre kan halayen ɓera ga kamfanoni da kuma gwamnatin Amurka. Corrigan ya ce an samu hujja game da yadda ɓerayen suka riƙa kai wa juna hari da cin naman juna a wuraren da suka saba samun abinci, wanda a yanzu suka rasa. Ya ƙara da cewa wannan ba sabon abu ba ne musamman a alokuta irin waɗannan. Mayunwatan ɓeraye ""ka iya yin nisan kiwo zuwa wata unguwa da babu ɓerayen a da,"" Corrigan ya faɗa wa BBC. Masanin ya ce ɓeraye dabbobi ne masu basira wurin gano inda abinci yake sannan kuma haƙwaransu kan yi ɓula a jikin ƙofofi da robobi da ma raga. ""Suna nan a ko'ina kuma ba zai yiwu su karaɗe duniya ba idan har ba su da ƙwarewa wurin sabawa da yanayi,"" in ji shi. Sai dai ƙaruwar yawan ɓerayen ba ya nufin za su fi mutane yawa. Hasali ma, Corrigan ya ce yanzu ne ya kamata a fito da sabbin hanyoyin kariya. Tawagar ɓeraye mayunwata kan haddasa fitina, su lalata gida sannan su yaɗa cuta. ""Za su iya kasancewa a wani ɗaki mai cike da yara ko gidan gajiyayyu ko kuma asibiti,"" a cewar Corrigan. Ana alaƙanta ɓeraye da cutuka kusan 55, duk da yake babu wani rahoto da ke alaƙanta su da cutar korona. Ɗaya daga cikin hanyoyin kare kai daga ɓeraye ita ce toshe ramuka da ke kusa da ƙasa. Haka abin yake ga sauran wurare kamar fayif da ɓera zai iya samun damar shiga. A cikin gida, ku tabbata babu inda za su iya ɓuya, ta hanyar tsaftace ko'ina da ɗebe tarkace. Yana da kyau a ɓoye kayan abinci a cikin abin da ɓera ba zai iya hudawa ba." https://www.bbc.com/hausa/labarai-52847086 +health Yadda cutar Sikila ta hana Aisha aure Latsa alamar lasifikar da ke sama domin sauraron hirar Aisha Bello Yusuf tana dauke da cutar Sikila. Amosanin jini, wadda aka fi sani da cutar Sikila cuta ce da ake gado daga kwayoyin halittar iyaye, inda suke haduwa su fito ba dai-dai ba, a jikin dan da suka haifa. kwayar halittar na fitowa da siffar lauje maimakon a kewaye kamar yadda ya dace. Aisha ta bayyana kalubale da dama da take fuskanta kasancewar ta mai cutar Sikila, ciki hada matsalan yin aure. Nigeria: 'Yadda muka warke daga cutar sikila' Bidiyo: Fatima Othman https://www.bbc.com/hausa/labarai-49809719 +health Hanyoyi 5 na kare kai daga kamuwa da ciwon koda Latsa alamar lasifika don sauraren hira da Dakta Salihu Ibrahim Kwaifa kan ciwon koda Ciwon koda, ciwo ne da ke barazana ga lafiyar al'umma a duniya, kuma saboda girmansa ya sa majalisar dinkin duniya ta ware rana domin tunawa da cutar koda ta duniya, Alkalumma sun nuna cikin mutum 10 a duniya daya daga cikinsu za a same shi da ciwon koda wanda ya nuna girman barazanar ciwon a duniya. An kebe ranar domin fadakar da al'umma da yunkurin rage yawan masu kamuwa da cutar da sauran dangoginta a fadin duniya. A kan tuna da ranar ce duk Alhamis ta biyu na watan Maris. A Najeriya wani rahoton kungiyar masu kula da lalurar koda ya ce 'yan kasar miliyan ashirin da biyar ne ke fama da ciwon, abin da kan sa kodar ba ta aiki yadda ya kamata har sai an rika zuwa wanki. Kididdigar da kungiyar ta fitar ya nuna cewa akasarin masu fama da cutar matasa ne. Alamomin ciwon koda kamar yadda likitoci suka bayyana sun hada da kumburi da yawan kasala da fitsari mai kumfa da yawan amai har zuwa jijjiga. Dr Abdurrashid Sarki Iliyasu ƙwararren likitan koda a asibitin kasa da ke Abuja, ya yi bayani kan hanyoyin kare kai daga kamuwa da ciwon koda Ya ce kariya daga kamuwa da ciwon ba wani abu ba ne mai wahala ko tsada domin ba abubuwa ne masu girma ba da za a ce ba za a iya yi ba. Ya ce mutane za su iya kare kansu daga kamuwa da cutar koda ta hanyar cin abinci mai gina jiki da kuma kiyaye duk abubuwan da aka ce suna janyo cutar. Amma duk wanda ya samu ciwon koda zai sha wahala ta tsadar magunguna da sauran matakai na waraka. Matakan kariya sun hada da: Ana son mutum ya kiyaye magungun da yake sha, ya kare kansa da shan magungunan da ba a san sahihancinsu ba, da suka shafi na gargajiya da shan na Bature da ya wuce kima. Likita ya ce shan wasu magunguna na bature fiye da kima na haifar da ciwon koda. Sannan ya ce ya kamata duk maganin da mutum zai sha ya kasance ya nemi shawarar likita domin kiyaye lafiyar koda. Duk lokacin da mutum ya samu rashin lafiya ko da zazabi ne, ya kamata ya yi kokarin zuwa asibiti domin tabbatar da ya samu kulawar da ta dace ta kwararrun likita don samun maganin da ba zai taba masa koda ba. Likita ya ce hawan jini da ciwon suga na cikin cututtukan da ke haddasa ciwon koda - ya kamata mutum ya dinga kokarin zuwa asibiti don a ba shi magungunan da suka dace da kuma kula da ciwonsa na hawan jini ko ciwon sugari don kare shi daga kamuwa da ciwon koda. Zuwa asibiti, a cewar liktita zai taimaka duba duk wasu abubuwa da za su kawo ciwon koda domin a magance su da wuri ba tare da an kai yanayin da kodar ta mutu gaba daya ba ta aiki a jiki ba. Ana son mutum ya yawaita shan ruwa, likitoci na bada shawarar shan ruwa akalla gora uku wato lita uku a rana daga safe zuwa washegari. Rashin shan isasshen ruwa a lokacin gumi kan janyo ciwon koda. Yawan shan ruwa zai sa mutum ya samu isasshen ruwa a jikinsa kuma jini yana zuwa kodarsa don ta yi aiki sosai. Cin gishiri da yawa yana cikin abubuwan da ke janyo hawan jini, likitoci na bada shawarar rage yawan cin gishi domin idan ya yi yawa a jiki yakan taba koda. Motsa jiki hanya ce ta waraka daga cuttuka da za su kare koda. Likita ya bada shawarar a dinga motsa jiki domin zai taimakawa wajen magance hawan jini da ciwon suga tare da kare koda. https://www.bbc.com/hausa/labarai-60679921 +health Annobar Coronavirus ta yi kisan farko a wajen China Coronovirus ta yi kisan farko a daya cikin kasashen da aka samu bullar annobar bayan kasar China inda cutar ta samo asali. Mutum na farko da ya mutu sakamakon cutar a wajen China ya rasu ne a kasar Filifins. Hukumar lafiya ta duninya WHO ta ce da alama mutumin mai shekara 44 ya kamu da cutar ne kafin zuwansa Filifins. Mutumin ya isa Filifins ne daga Hong Kong bayan ya baro yankin Wuhan tare da wata mata da a makon da ya gabata aka gano cewa tana dauke da cutar. An fara kwantar da mutumin ne a asibiti a birnin Manila inda daga bisani rashin lafiyarsa ta tsananta. WHO ta ce zuwa yanzu annobar ta kashe mutum fiye da 300, galibinsu a yanin Hubei, yayin da wasu fiye da 14,000 suka maku da cutar. Kasashen Amurka da Australia da New Zealand da Rasha da Japan da Pakistan da Italy da Indonisia da Singapore da Koriya ta Kudu sun dakatar da shigowar baki daga China. Amurka na killace 'yan kasarta da suka dawo daga yankin Hubei na kasar China na tsawon kwana 14. Wadanda suka dawo daga wasu sassan kuma za a bar su su rika lura da yanayin lafiyarsu. Yawan wadanda suka kamu a barkewar annobar coronavirus ya haura na wadanda suka kamu da kwayar cutar Sars a shekarar 2003, inda mutum kimanin 30 suka kamu da annobar. https://www.bbc.com/hausa/labarai-51347428 +health ‘Mutum ɗaya cikin huɗu da ke da ciwon suga ba su samun taimakon da ya dace’ "Wani bincike wanda aka fitar da shi a ranar yaƙi da ciwon suga ta duniya ya bayyana cewa mutum ɗaya cikin huɗu a faɗin duniya da ke fama da ciwon suga ba su samun taimakon da suke buƙata. Hukumar yaƙi da ciwon suga ta duniya ta bayyana cewa kusan kashi 26 cikin 100 na masu cutar ba su samu isassun bayanai ba kan halin da suke ciki a lokacin da aka gano suna da cutar wanda hakan zai iya sa su kasa kula da kansu. Hakan zai iya jawo musu matsaloli kamar shanyewar rabin jiki da ciwon koda da makanta da kuma jawo matsala ga lafiyar ƙwaƙwalwa. An gudanar da wannan bincike ne ta intanet ga mutum 3,208 waɗanda ko dai sun taɓa samun ciwon suga ko kuma malaman lafiya ne daga wasu ƙasashe kamar Brazil da India da Najeriya. Amma ga wanda yake da ciwon suga, abubuwan da wannan binciken ya gano ba wani abin mamaki bane a gare ni, wani abu ne da na sani. Ganin cewa ina da ciwon suga nau'in Type 1, an gano ina da ciwon ina ɗan shekara bakwai a Costa Rica, zan iya danganta yadda na ji da wahalar da na sha a lokacin da nake girma ba tare da ina da wata masaniya ba kan abin da ke damu na. An gano ina da ciwon suga kuma na same shi ne sakamakon irin illar da wani magani ya yi mani inda a lokacin ina da wani ciwon ƙashi wanda da keken guragu nake tafiya. A lokacin da nake tasowa, lokacin da ba ni da na'urar auna sindarin glucose da ke jikina, ina yawan samun tashin hankali kada ciwona ya tashi inda wani lokaci nake mantuwa idan na yi allurar sukari ko na manta na yi sau biyu wanda hakan zai iya sa adadin sukarin da ke cikin jinina ya yi ƙasa kuma ya yi barazana ga rayuwata. Bayan mun koma Birtaniya da zama lokacin ina da shekara 25, a lokacin ne na ƙara samun bayani a kan ciwon. Amma a yau sakamakon irin ilimi da kuma kayayyaki da na samu daga hukumar lafiya ta Birtaniya NHS, ina jin dadi matuka sakamakon irin matakan da nake dauka a kullum domin na zauna lafiya saboda cutar da nake fama da ita. Na yi magana da wata mai cutar domin sanin ko ta shiga irin halin da na shiga, inda na yi magana da Ana Lucia daga Chihuahua da ke Mexico. Ta yi mani bayanin cewa bayan an gano tana da ciwon suga, rayuwa ta sauya mata matuƙa, ba wai gareta ba amma ga iyalanta. An gano Ana Lucia tana da ciwon suga nau'in Type 1 a lokacin da take shekara takwas da haihuwa bayan an kai ta sashen kula da marasa lafiya na musamman. Mahaifiyarta, Clementina ta bayyana mana yadda ta ji sakamakon ba a masu bayanai sosai ba lokacin da ƴarta ta shafe kwana biyar a asibiti. ""Sun bayyana mani akwai buƙatar na koyi yadda zan yi mata allura saboda yarinya ce. A lokacin ne dukanmu muka soma samun ilimi kan ciwon suga. Sai dai ƙarancin taimako da wayar da kai kan ciwon sukari ya yi tasiri matuƙa kan Clementina da ƴarta, a daidai lokacin da suke ƙoƙarin kawo sauyi ga halin da ake ciki. Zuwa yanzu dai Ana Lucia ta shafe shekara 17 tana fama da matsalar ciwon na sukari, akasari kuma ita ke kula da kanta. Duk da cewa ta bayyana mutum zai iya gajiya: ""Ba na bacci sosai sakamakon ina yawan duba adadin sukarin da ke jinina ko kuma na jira bayan wasu sa'o'i domin na yi allura,"" Ba da daɗewa ba ta soma saka na'urar awon sindarin glucose wanda na'ura ce da ake amfani da ita ba sai ta huda yatsanta ba domin ɗibar jini ta yi awo. Ta bayyana cewa da tun can dama tana da wannan na'urar da ta taimaka mata wurin kula da lafiyarta. Duk da cewa ƴan uwa da abokan arziki na Lucia suna ba ta goyon bayan da ya kamata, amma tana ganin ƙalubalen da take fuskanta sakamakon makaranta da sauran wahalhalun yau da kullum ƙalubale ne gare mu Binciken da aka yi kuma ya duba batun tasirin ciwon suga kan lafiyar ƙwaƙwalwa musamman idan mutum ba shi da ilimi sosai kan ciwon. Shugaban hukumar yaƙi da ciwon suga ta duniya Farfesa Andrew Boulton ya bayyana cewa an gano idan mutum bai samu ilimi kan ciwon yadda ya kamata ba, hakan zai iya jawo damuwa da baƙin ciki. Binciken da aka yi ya gano cewa akwai buƙatar su ma hukumomin lafiya a wayar musu da kai kuma rabin waɗanda aka yi bincike a kansu sun bayyana cewa sun gano damuwa na daga cikin abubuwan da ke ƙara ta'azzara ciwon suga. ""Mutanen da ke fama da damuwa, akwai yiwuwar ba za su iya bin shawarwarin likitoci ba...misali idan suna da matsala a ƙafa, kada su saka wasu takalma,"" in ji Farfesa Boulton" https://www.bbc.com/hausa/articles/c9ep9djnd9xo +health Sinadarin hada lemo na dan tsami ya 'kashe mutum goma a Kano' "Gwamnatin jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta tabbatar da cewa mutum 10 ne suka mutu sakamako shan sinadarin lemon dan tsami na jabu. Kwamishinan lafiya na jihar, Dr Aminu Ibrahim Tsanyawa ya shaida wa manema labarai cewa, binciken da aka gudanar kan bakuwar cutar nan da ta bulla a jihar a makonnin da suka gabata, ya nuna cewa shan sinadarin ne ya haddasa ta. A cewarsa, fiye da mutum 400 aka kwantar a asibiti sakamakon kamuwa da cutar. ""Shan wadannan sinadarai na da matukar illa ga lafiyar dan adam, yana kuma janyo matsala a koda, da janyo matsala a sassan jikin dan adam, idan da karar kwana har mutuwa mutum zai yi. Kawo yanzu ma'aikatar lafiya na kula da sama da mutum 400 da suka kamu da matsananciyar rashin lafiya sanadin shan wadannan abubuwa. Sama da mutum 50 ana yi musu wankin koda baya ga mutum sama da 10 da suka mutu,"" a cewar Dr. Tsanyawa. ""Ganin yanayin zafi da ake ciki, da kuma watan azumin Ramadan da aka fara, akwai yiwuwar za a ci gaba da amfani da wadannan nau'ukan na kayan lemo. Domin haka muke kira ga al'ummar jihar Kano su kiyaye da gujewa ta'ammali da irin wadannan sinadaran na hada lemo,"" in ji Dakta Tsanyawa. A kwanakin baya ne dai akai ta kwantar da mutane da dama a asibitocin da ke birnin Kano, sakamakon fitsarin jini da amai da suke yi sakamakon shan lemon da aka hada da sinadarin dan tsami. Hukumomin jihar sun haramta sayar da sinadarin, suna masu gargadin jama'a su daina amfani da shi. Kazalika hukumar kare hakkin masu sayen kayan masarufi ta jihar Kano ta sanar da kama mutane hudu da ake zargi da sayar da lemon dan tsami. Hukumar ta ce an kama mutanen a garin Minjibir da ke Kano, inda aka same su da dan tsami kusan buhu 600, wanda dukkansu lokacin amfani da su ya wuce." https://www.bbc.com/hausa/labarai-56770846 +health 'Yadda malariya ta kashe min 'yata mai shekara 18' "Latsa alamar lasifika don sauraren hirar da Aisha Shariff Baffa ta yi da mahaifiyar yarinya Wata mahaifiya da ta rasa 'yarta mai shekara 18 da dalilin zazzabin maleriya ta bayyana irin wahalar da 'yar ta shiga kafin kwananta ya kare. Matar ta bayyana cewa zazzabi ne mai zafi ya rufe yarinyar da ya kai har jinin jikinta ya janye kuma sai da aka kara mata ruwa. Sannan ta ce ko da suka je asibiti, an dauki lokaci mai tsawo kafin ma'aikatan lafiyar su bai wa 'yarta kulawar da ta dace. ""Da farko da muka je saboda tsananin cikowar asibitin mun wahala kafin mu ga likita sannan kuma suka ce mana babu gadon da za a kwantar da ita. Sai da muka rika roko sannan suka ba ta taimakon gaggawa,"" in ji mahaifiyar. ""A zaune a kan wani benci aka sa mata ruwa, babanta na tsaye ya rike ta don ko a lokacinma kanta ya fara langabewa, kafin daga bisani muka samu gado da kyar."" ""Sai da wata mata ta mutu shi ne muka roka aka dauke gawar sannan aka ba mu gadonta"" a cewarta. Mahaifiyar ta ce a gida aka fara ba ta kulawa don a gida ma aka fara sa mata ruwan kafin daga baya su je asibiti. A asibiti kuma an yi mata karin jini bayan da aka fahimci cewa jinin jikinta ya ja baya amma saboda illar da cutar ta yi a jikinta, ta rasu a asibitin. Mahaifiyar ta bayyana cewa ta kadu matuka da rasuwar 'yarta saboda yarinya ce mai ladabi da hangen nesa kuma mai son taimako. Ta ce ""Ta kan ce min, mama in shaa Allahu sai na yi karatu ko don nan gaba ki huta."" Zazzabin maleriya dai na daya daga cikin manyan cututtukan da ke saurin kisa musamman a kasashe masu tasowa kuma wadnda da ke yanki mai zafi. Wadannan yankuna na fama da rashin asibitoci masu kyau ko kwararrun likitoci ko kuma kayan aiki, don haka ba a bayar da kulawar da ta dace. Wani lokaci kuma a kan yi tsaikon zuwa asibiti ko kuma a sayi magunguna a shagunan siyar da magunguna ba tare da an san takamaimai tsananin cutar ba. Wani rahoton Hukumar Lafiya ta Duniya ya nuna cewa Najeriya ce kan gaba da kashi 25 cikin 100 na yawan maleriya." https://www.bbc.com/hausa/labarai-50657006 +health Najeriya: Likitoci na tururuwar barin ƙasar ana tsaka da yajin aiki Yayin da likitoci masu neman kwarewa a Najeriya ke ci gaba da yajin aiki a manyan asibitoci, a bangare guda ma'aikatan kiwon lafiyar da dama na yunkurin ficewa daga kasar zuwa kasashen waje. Kawo yanzu babu tabbas kan adadin likitoci da ke wannan yunkuri amma wasunsu na cewa matsalolin da suka haifar da yajin aikin na daga cikin abubuwan da suka sanya su daukar matakin gwada sa'arsu a kasashen waje. BBC Hausa ta ziyarci wani wuri a Abuja babban birnin Najeriya, inda ake tantance tarin likitocin da ke zuwa domin tantance su, da niyyar samun aiki a kasar Saudiyya. Likitoci maza da mata daga sassa daban-daban na Najeriya na zuwa wajen dauke da takardunsu, domin ganin sun samu damar tafiya Saudiyyar domin gwada sa'arsu. Wani likita da ke kan layi yana jiran a tantance shi, ya shaida wa BBC Hausa cewa yana son ya je waje ne domin ya ji labarin cewa an fi kula da likitoci a can. Ya ce akwai matsaloli da dama da suke fuskanta a Najeriya, kamar wutar lantarki da kan tsayar da al'amura cik, yayin da suke tsaka da aiki, ga kuma karancin albashin da suke fama da shi, da baya isarsu wajen biyan bukatun yau da kullum. A kullum dai gwamnatin Najeriya na cewa tana iya bakin kokarinta wajen inganta bangaren na lafiya, abin da likitocin ke cewa zance ne kawai da ba ya wuce fatar baka. Ba sabuwar matsala ba ce Likitoci a Najeriya dai sun jima suna fita wasu kasashen duniya domin gwada sa'arsu, abun da masharhanta ke alakantawa da rashin kyakkyawan tsarin kula da lafiya a Najeriya. Rahotanni daban-daban sun sha nuna cewa akwai daruruwan likitoci 'yan Najeriya da ke aiki a kasashen waje, wasu ma har sun yi fice saboda kwarewarsu da kuma gudummawar da suke bayarwa wajen kare lafiyar jama'ar kasashen da suka je. Wasu daga cikin jama'a dai na da ra'ayin cewa akwai tsantsar rashin kishin kasa tattare da wadannan likitoci da ke barin ƙasarsu don zuwa su yi aiki a wasu kasashen yayin da aka fi bukatarsu a gida. Yajin aiki da korafe-korafe a bangaren lafiya ba sabon abu ba ne, kuma ana ganin cewa hakan ya taimaka wajen sake durkushewar bangaren, musamman a wannan lokaci da ake tsaka da fama da annobar korona. https://www.bbc.com/hausa/labarai-58325281 +health Alamomi 4 na kansar bakin mahaifa "Cutar daji kan kama bakin mahaifar mace, wato hanyar da ɗa ke fitowa daga mahaifarta. Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware ranar 17 ga Nuwamba domin yaƙi da cutar kansar bakin mahaifa ta duniya kuma domin tunawa da ranar farko da aka fara fafutikar kawo karshen cutar a duniya. A wannan rana dai ana kokarin wayar da kan mata domin sanin yadda za su kare kai daga kamuwa da cutar, da muhimmancin yin gwaji da zarar sun fara fuskantar wasu sauye-sauye a jikinsu musamman zubar jini. Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa a shekarar da ta gabata akalla akwai mata dubu 604,237 da aka tabbatar sun kamu da cutar Kansar bakin mahaifa a duniya. Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta ce kashi 99 cikin ɗari na matan da ke kamuwa da kansar bakin mahaifa na da ƙwayar cutar 'human papillomavirus ko HPV, wadda ƙwayar cuta ce da ake saurin ɗauka ta hanyar saduwa. Duk da cewa sau da yawa ƙwayar cutar kan mutu da kanta kuma ba lallai ta jawo wasu alamomi ba a jiki, idan ta daɗe a jikin mace ta kan haifar da kansar bakin mahaifa. Kansar bakin mahaifa ita ce cutar daji ta huɗu mafi shahara da ke kama mata. Shi ya sa ma aka ware watan Janairu don wayar da kan al'umma kan wannan cuta. WHO ta ce a shekarar 2018, an yi ƙiyasin mata 570,000 ne aka gano suna ɗauke da kansar bakin mahaifa a faɗin duniya kuma mata 311,000 ne cutar ta kashe. Dokta Zainab Shinkafi-Bagudu, shugabar ƙungiyar Medicaid mai bincike da tattara alƙaluma kan cutar daji a Najeriya ta ce ya fi dacewa mata su riƙa zuwa ana tantance su ba sai sun ga alamomin cutar ba. ""Da zarar mace ta fara saduwa da namiji ya kamata ta riƙa zuwa asibiti ana mata gwaji a kai a kai. Ta hanyar gwajin nan ne za a gani idan da cutar a jikinta. ""Kuma kansar bakin mahaifa na da saurin warkewa idan har an gano ta wuri, wato idan ba a bari ta yi yawa ba. Shi ya sa muke cewa a riƙa tantancewa,"" a cewar likitar. Waɗanne ne manyan alamomin kansar bakin mahaifa? Wannan na ɗaya daga cikin alamomin farko-farko da mace za ta gani. Ta kan ga jini kafin ko bayan al'ada a matan da ke shekaru haihuwa, wato dai a lokacin da ba su saba ganin jininsu na al'ada ba. Wannan jinin na iya zama da yawa ko kaɗan. Wani lokaci, jinin kan fara zuba ne da zarar an gama saduwa. A matan da suka kai shekarun ɗaukewar al'ada ma, zubar jinin ne alama ta farko. Likitoci sun ce idan mace ta kai shekarun ɗaukewar al'ada, ko yaya ta ga jini daga al'aurarta ta gaggauta zuwa asibiti saboda alama ce da ke nuna cewa akwai wata matsala. Sai dai ba ko yaushe ne wannan alama ke zama ta kansar bakin mahaifa ba. Akwai cutukan da kan zo da irin waɗannan alamomin. Wata alama da dajin bakin mahaifa kan zo da shi iat ce ruwan da ke zuba daga al'aurar mace kan ƙara yawa fiye da yadda ta saba gani. Kuma wani lokaci ya kan zo da wari. Idan kansar bakin mahaifa ta fara yaɗuwa sosai, mace kan ji ciwon ƙafa da ciwon baya da ciwon mara sosai. Wani lokaci ma ƙafa ɗaya ko duka ƙafafuwan biyu kan kumbura baya ga yawan ciwo da zugi. Wannan na faruwa ne idan cutar dajin ta danno wata jijiya da ke haɗe da ƙafa da mara da baya. Haka kuma, a kan ji zugi ko nauyi a mara daga ƙasan cibiya. Mata da yawa masu wannan cuta na bayyana yadda suke ji a mararsu kamar ana tsira masu wani abu mai tsini, sannan zugin kan daɗe wani lokaci kuma ya kan ɗauke sannan ya dawo. Wannan na iya zama jin zafi a lokacin yin fitsari ko bayan gida. Wani lokaci kuma, fitsari ko bayan gida kan fita daga jikin mace ba tare da saninta ba. Wato zai zamo ba ta iya riƙe fitsari da bayan gida. Wannan na faruwa ne idan dajin ya yi girman da har ya shafi ƙoda da mafitsara da hanji. Duk da dai ba a fiye gani ba, kansar bakin mahaifa kan danne hanyoyin fitsari da bayan gida har mace ta kasa yin ko wanne daga cikinsu. Kansar bakin mahaifa kan sa mace jin zafi ko raɗaɗi a lokacin saduwa. Wannan raɗadi na iya kasancewa a al'aura ko a mara. Likitoci sun ce da zarar mace ta ji haka, ta je asibiti ta bayyana wa likita. Da yawa daga cikin waɗannan alamomi na bayyana ne idan cutar ta yi nisa. Amma Dokta Zainab Bagudu ta ce tun kafin a ji alamomi ya kamata a je asibiti. ""Yanzu akwai riga-kafi da aka samu na wannan cuta. Da zarar yarinya ta kai shekara 9, kafin ta fara saduwa da namiji ake yi mata. ""Wannan zai rage yaɗuwar wannan cuta sosai, saboda riga-kafin na matuƙara taƙaita illar da cutar ke yi a jiki,"" a cewarta. ""Asali ma, idan aka dage da karabar allurar za mu iya kawo ƙarshen cutar kansar bakin mahaifa gaba ɗaya a duniya,"" in ji Dokta Zainab. Amma ga matan da suka riga suka fara saduwa, likitar ta ce abin da ya fi shi ne yawan tantancewa da ake yi a asibiti. Da an ga alamomin cutar a bakin mahaifarta, akwai taimako da ake bayarwa wanda zai hana ta yaɗuwa ta zama daji." https://www.bbc.com/hausa/labarai-55721710 +health Yadda tunani mara kyau ke sanya mutane shiga bala'i "Alal misali, ashe ka nemi gurbin aiki, sannan aka zabe ka domin zuwa gwaji a zagaye na biyu. Kana alfahari da hakan, sannan ka fara shirin tunkarar sabon kalubale? Ko kuma kana tunanin ba zaka samu aikin ba, da tunanin yadda hakan zai shafi kimar ka? ""Idan na kasa samun aikin, na fadi a rayuwa,’’ ka fadawa kan ka. Ko watakila kana jiran amsar sakon da ka tura wa abokinka. Idan ka kasa samun amsa nan take, za ka fara tunanin dukkanin abubuwan da ka yi ya bata wa mutumin rai – ba tare da la’akari da watakila ayyuka ne suka yi musu yawa ba. Watakila al’amuran yankuna ne ka fi damuwa da su. Kana daukar tsawon awanni a ko wane dare tunani kan barazanar yakin Nukliya, bullowar wata mummunar annoba mai kisa ko kuma yiwuwar tabarbarewar tattalin arziki. Barazanar da hakan zai jawo za ta ci gaba da rayawa a cikin zuciyarka. Cikin dukkan wadannan al’amura ka dauka ka saba da hakan, sannan barazanar za ta saukaka. Wani abu da tunanin ka zai baka cewa wani abu mara kyau ba zai faru da kai ba, da yayata yiwuwar faruwar lamarin. Bincike mai yawa ya nuna cewa bala’i na iya haifar da barazana ga lafiyar kwakwalwa, kuma yana iya kara sa mutum jin damuwa tare da yanayin ciwo mai tsanani. Bala’i na iya faruwa a kowane lokaci a rayuwarmu – amma fargabar da ke tattare da cutar Covid-19, hade da rashin tabbas na siyasa da kuma tattalin arziki, na iya kara tsananta yanayin. Neman hanyoyin kauce wa tunani maras kyau ya kamata ya karfafa juriyar kowa – kuma watakila babu lokacin da ya fi dacewa don yin koyo. Masana halayyar dan adam sun gano cewa bala’i a matsayin babbar barazana ga kwakwalwa ya faro ne daga lokacin haihuwa samun waraka na kwawalwar. A farkon karni na 20, masana halayyar dan adam – wanda Sigmund Freud da wasu suka kirkira – ya kasance hanyar farko ta magance tabin hankali. Manufar ita ce ta kauce wa fargaba da abubuwan da mutane ke so – galibi abubuwa da suka faru tun lokacin yarinta da jinsi – wadanda ke haifar da matsaloli na tunani. A cikin tsakiyar karni, masana halayyar ta dan adam kamar Albert Ellis da Aaron Beck, sun fara duba wasu hanyoyi na taimaka wa mutane lokacin da suke cikin damuwa. Maimakon kokarin bijiro da matsaloli na tunani, sun mayar da hankali kan abubuwan da mutane ke tunani a kai, ta hanyar kaiwa ga wadanda ke tunani mara-kyau ko rashin fahimta da ke janyo wa mutane matsaloli. Tun da fari, an bayyana bala’i a matsayin wani abu na rashin fahimta – inda wani masani Beck ya yi rubutu a kan rawar da yake takawa na janyo fargaba. Wani da ke da fargabar shiga jirgin sama, alal misali, zai dauka cewa akwai damuwa cikin dakin matukin jirgin. Idan basa cikin barazanar shiga bala’i, za su lura cewa ma’aikatan jirgin basu san me yake faruwa ba, amma wanda yake ganin za a iya shiga bala’i zai dauka cewa ma’aikatan cikin jirgin ba sa sa ido yadda ya kamata – idan karar ta ci gaba da faruwa, za su fara tunanin cewa za su mutu. Bincike ya ci gaba da nuna cewa tunanin kan bala’i, na cikin abubuwa da ke janyo wa mutum matsaloli ko ta rashin lafiya. Alal misali, a wajen aiki, mai nuna halayen bala’i na iya bata rai kan karamin kuskure. Keelan ya ce: ‘Za su iya tunani mai ban tsoro kamar ‘za a iya kora ta daga wajen aiki, ba zan iya jure hakan ba,’’ a cewar Keelan. A wasu lokutan, tsoro da mutum yake ji zai iya kaiwa matakin da ba zai iya aiki ba, Bala’i na iya sa mutum ya gano kansa ga kowane dan canji da aka samu a jikinsa a matsayin alamar ciwon daji. A wasu lokuta, mutane na iya fara barnar abubuwan jiki wadanda ke tare da damuwa. Alal misali, Idan suna cikin fargaban gabatar da jawabi a wurin taros, suna tunanin cewa bugun zuciyarsu wata alama ce da ke nuna cewa za su kamu da ciwon zuciya. Sakamakon shi ne karkatar da tunani maras-kyau wanda zai haifar da yanayi na tsoro. Barnabas Ohst, wani masani kan halayyar dan adam a Freiburg da ke Jamus, kuma marubucin wata takadda da ta yi nazari kan halin dan adam, ya ce jikin mutum na haifar da damuwa da kuma tsoro, wanda hakan zai sa ya fi dacewa a dauka matsayin bala’i. A cikin tsawon shekaru da suka gabata, bincike ya nuna cewa tunani a kan bala’i zai iya sanya mu cikin barazanar kamuwa da cutukan kwakwalwa – wanda ya hada da rashin lafiya ta kwakwalwa da cuta mai rudarwa har ma da wasu nau'ukan tunani. Tunanin bala’i na iya kara tsananta zafin jiki. A cikin wannan yanayin, za ayi tunanin cewa wani tsawon lokaci da rashin jin dadi zai kasance – ‘ba zai taba tafiya ba’ – ko dalilinsa. Alal misali. Za ku iya dauka cewa tsananin ciwon kai na nufin kana dauke da cutar daji na kwakwalwa. Gwaje-gwaje sun nuna irin wannan tunanin kawai yana kara alamar jin zafi a kwakwalwa, don haka damuwa ya fi tsanani kuma yana daukar tsawon lokaci  kafin ya wuce. Kamar yadda masanin radadin zafi na jami’ar Stanford Beth Darnall da Luana Colloca na jami’ar Maryland, suka rubuta a wata takarda ta baya-bayan nan, wannan mummunan tunani yana ‘kamar daukar gwangwanin man fetur a zuba kan wuta’. Abubuwa da dama sun bayyana abin da ya sa wasu mutane ke fama da tunani na bala’i fiye da wasu. Halaye daban-daban na mutane – wadanda ke cikin kwayoyin halitta – za su bayyana wasu bambance-bambancen. Za mu kuma gano yanayin tunani na ‘yan uwan mu. Idan kana yawan tuna cewa iyayen ka na duba yiwuwar samun mummunar bala’i a kowani biki, za ka iya tunanin hakan ga kowani al’amari na rayuwa. Bayanin mu zai iya taka rawa. Dalilai na rashin tsaro na nufin mutum zai iya shiga yanayin tunani maras-kyau. Idan ka fara ganin tunanin ka ya fara raguwa a tsawon shekara Daya ko biyu da suka gabata, hakan ba zai zamanto wani al’amari ba: akwai wasu hujjoji cewa labaran duniya ka iya tsananta bala’in da muke fuskanta. A wani lokaci, za ka yi tunanin bala’i kan al’amuran – kamar yakin Ukraine da bullowar wani nau’i na annobar korona ko kuma durkushewar tattalin arziki. A wasu lokutan kuma, hakan kan janyo mutum ya nuna damuwa kan matsaloli da yake fuskanta. Wani bincike daga jami’ar Sussex da ke Burtaniya, ya tambayi masu yanke shari’a da ke zaman kansu, su bayyana yadda suke ji lokacin kallon labarai daga gidajen talabijin – ko labaran masu dadi ne ko mara dadi ko suna debe-kewa ko kuma basa debewa, masu sanyaya rai ko masu tayar da hankali – sannan da nuna fefe guda 30 da aka zaba ga wadanda aka tambaya su 30. Kafin su kalli fyafyen da kuma bayan sun kalla, wadanda aka tambayan sun amsa tambayoyi kan manyan damuwowi uku a rayuwarsu, sannan a karshe, sun kuma shiga wata tattaunawa, inda suka tattauna kan Daya daga cikin matsalolinsu. Kamar yadda ake sa rai, mutanen da suka kalli labarai maras-dadi, su suka fi shiga damuwa kafin kammala kallon fefen kuma sun fi tunani kan bala’i lokacin da suke tattaunawa kan matsalolinsu idan aka kwatanta da wadanda suka kalli fina-finai masu kyau. Wannan dai bincike ne kan mutane kadan. Sai dai karin bincike ya nuna cewa kallon labarai na yin tasiri kan yanayin mutane wanda hakan kuma zai sauya tunanin mutane. Ko ma me ya haddasa ma ka damuwa, masana lafiyar kwakwalwa kamar Keelan, ta ce za a iya sanin me yake sa mutane shiga cikin damuwa. Fadakarwa yana da muhimmanci, don haka mataki na farko ya kamata dakar da tunanin ku da kuma gane lokacin hankalin ku ke tafiya cikin duhu. Kuna iya lura da cewa kuna jin damuwa game da tattaunawa, misali. Idan tunaninku na gaba shi ne ‘Zan juya shi’, duk da haka, kuna iya tambayar tushen wannan zato. Wadanne dalilai kuke tunanin za su sa ku gaza? Kuma ta yaya za ku fahimci lamarin bis aga shaidar da ke hannunku? Idan ka yi kokarin dauka daga wajen mai sanya ido, za ka gane cewa ana iya nuna gazawa, maimakon rashin tabbas – sannan akwai matakai da za ka dauka domin kara baka damar fafatawa yadda ake so. Ya kamata ku lura game da maganganun da ba su da amfani da kuma wuce gona da iri – yin tunani kamar ‘Na kasa kuma ba zan taba samun aiki ba’’. A cikin wannan yanayin, kana iya kokarin la’akari da gaskiyar cewa kowa na yin munanan tambayoyi lokaci zuwa lokaci – ba yana nufin sun kasa kwata-kwata ba. Idan ka gaza, zaka iya koyon wani abu daga wannan gazawar don inganta shirin ka a gaba. Domin yin la’akari da wani misali, yi tunanin cewa kana da matukar damuwa game da cutar Covid-19, wanda ya mamaye tunanin ku a yanzu. Duk da yake yana da kyau a gane hadarin kamuwa da cutuka, za ka iya karkarewa da cewa ka kamu da cutar a duk lokacin da kaji dan wani abu cikin makogworon ka, sannan za ka firgita da tunanin yadda za ka iya jurewa idan ka kamu da cutar. A irin wannan lokaci, za ka karfafa kan ka har sai ka fara nuna alamun cutar – wannan dan abu a cikin makogworon ka na iya zama ba na gaske ba. Hakanan, kana iya tunatar da kanka cewa allurar rigakafi za ta rage barazanar kamuwa da alamomin cutar masu tsanani, da kuma tunanin yadda za ka warke idan ka kwanta rashin lafiya – ta hanyar kiran abokin ka don yi maka sayayya yayin da kake kwance babu lafiya." https://www.bbc.com/hausa/articles/c72eywvjpnyo +health Mutumin da ya shafe shekaru 50 bai yi wanka ba ya rasu Mutumin da ake gani a matsayin 'wanda ya fi kowa kazanta a duniya' ya rasu yana da shekaru 94, watanni kaɗan bayan ya yi wanka a karon farko cikin tsawon shekaru. Amou Haji ya shafe kusan shekaru hamsin bai yi wanka da soso da sabulu ba, saboda tsoron cewa zai yi rashin lafiya. Ɗan ƙasar Iran ɗin wanda ke zaune a kudancin lardin Fars, ya ƙi yarda a tsawon lokaci makwabtansa su yi masa wanka. Sai dai kafafen yaɗa labaru sun ce a watannin da suka wuce ne ya bayar da kai bori ya hau inda ya amince ya yi wanka da sabulu. A cewar kamfanin dillancin labaru na IRNA a Iran, Haji ya yi gajeruwar rashin lafiya kafin rasuwarsa a ranar Lahadi. A wata hira da jaridar Tehran Times a shekarar 2014, ya bayyana cewa yana kwana a cikin wani ɗan karamin gida da mutane suka gina masa a kauyensu da ke Dejgah. Ya faɗa wa jaridar cewa ya fuskanci koma-baya sosai a lokacin da yake yaro. Yana rayuwa ne ta hanyar cin ruɓaɓɓen nama da abincin da aka zubar a bola. Amou Haji ya kasance mutum mai yawan shan sigari. https://www.bbc.com/hausa/articles/c84g8plew03o +health Coronavirus: Shin me rashin jin ɗandano ko ƙamshi ke nufi? "Rashin jin ƙamshi ko wari da ke faruwa sanadin cutar korona ya bambanta daga yanayin da mai fama da mura zai ji, in ji masu bincike a Turai waɗanda suka yi nazari kan bayanan da suka samu daga marasa lafiya. Lokacin da masu fama da cutar korona suka daina jin ƙamshi, lamarin na zuwa ne kwatsam kuma yana ta'azzara. Sannan mafi yawa ba sa samun toshewa ko yoyon hanci - akasarin mutanen da ke da korona za su iya yin numfashi cikin sauƙi. Wani abin kuma da ya bambanta su shi ne ainahin rasa ɗandano. Ba wai ɗanɗanonsu ya samu matsala ba ne saboda sun daina jin ƙamshi ko wari, a cewar masu bincike a mujalla kan cututtukan da suka shafi hanci ta Rhinology. Masu fama da cutar korona da suka rasa ɗanɗanonsu ba sa iya tantance ɗaci da daɗi. Kwararru na zargin hakan na faruwa saboda annobar ta shafi jijiyoyin jikin mutum da suke da alaƙa da ƙamshi da ɗanɗano. Alamomin cutar korona sun haɗa da: Duk wanda ya nuna waɗannan alamomin ya kamata ya keɓe kansa sannan ya shirya zuwa a yi masa gwaji domin sanin ko yana ɗauke da cutar. Su ma 'yan uwansa sai su killace kansu domin hana yaɗuwar cutar. Mutane da dama sun ce akwai lokacin da suka tsinci kansu cikin yanayin daina jin ƙamshi ko wari ko ma ɗanɗanonsu. A zantawar da BBC ta yi da wasu mutane a Abuja da Kano, sun tabbatar da cewa sun kasance cikin wannan yanayi sai dai ba dukkansu ba ne suka ga alamun zazzabi ko mura a tare da su. A tsawon makwannin da suka ce sun kasance cikin yanayin, sun ce ba sa iya bambance ɗaci da zaƙi da tsami ko da yaji mutum ya sa a baki ba zai ji zafinsa ba - sannan kuma babu maganar jin ƙamshi ko wari. Kan haka muka tuntubi Dakta Nasir Sani Gwarzo wani ƙwararren likita a Najeriya kuma masani kan cututtuka masu yaɗuwa don jin abin da rasa ɗanɗano ko ƙamshi ko wari ke nufi. Ya ce a al'ada akwai cututtuka da dama da suke haddasa canjin yanayi a maƙogwaron mutum ko dadashinsa ko hancinsa yadda idan ciwon ya kama wannan wuri zai iya haddasa rashin jin ɗanɗano ko wari ko ƙamshi - wannan yakan faru ga cututtuka da dama musamman waɗanda suke da alaƙa da mura. Ita ma cutar korona cuta ce wadda take dangin mura amma wadda ake kira korona yanzu (Covid-19) sabuwar korona ce da ta fito a 2019. ""Idan mutum ya fara jin alamun rashin ɗnɗano ko wari wannan yakan faru galibi a kashi kusan 25 cikin waɗanda suka kamu da cutar korona, za su ji sun fara samun wannan alama - ko dai a matsayin ita kaɗai ce alamar da za su ji har su warke ko kuma ita ce alamar farko da za su bayyana idan ciwon ya kankama. Wasu idan ya kankama su kan warke bayan kwanaki, wasu sukan warke daɗe za su iya yin shekaru ma da ɗanɗanon da jin wari ko ƙamshi duk ya tafi amma yawanci ya kan dawo cikin ƙanƙnin lokaci,"" in ji ƙwararren likitan. Ya shawarci jama'a su tabbata zun ziyarci likita a duk lokacin da suka ga alamun haka a tattare da su don gano ko suna ɗauke da korona ne ko kuma wani dalilin ne daban saboda a cewarsa, a yanayin da ake ciki na annobar korona, ana samun irin wannan matsala sosai a tsakanin mutanen da ke fama da cutar. Jagoran binciken Farfesa Carl Philpott daga Jami'ar East Anglia ya gudanar da gwajin jin ƙamshi da ɗanɗano kan wasu mutum 30: 10 masu fama da cutar korona, wasu 10 kuma masu fama da mura sai ƙarin wasu 10 da suke cikin ƙoshin lafiya - ba su da alamun mura ko zazzaɓi. Rashin jin ƙamshi shi ne babban abin da aka gano tare da marasa lafiyar da ke fama da korona. Ba sa iya tantance ƙamshi sannan ba sa iya bambance ɗaci ko daɗi kwata-kwata. Farfesa Philpott - wanda ke aiki da ƙungiyar tallafa wa mutanen da suka rasa ƙamshi wadda aka kafa domin tallafa wa waɗanda suka rasa jin ƙamshi ko wari ko ɗanɗano - ya ce: ""Da gaske ne akwai alamun da ke bambanta cutar korona da sauran cututtukan numfashi. ""Wannan abun birgewa ne ƙwarai saboda hakan na nufin za a iya amfani da ƙamshi ko ɗanɗano wajen banbance masu cutar korona da mutanen da ke fama da mura."" Ya ce mutane na iya yi wa kansu wannan gwajin a gida ta hanyar amfani da gahawa da tafarnuwa da lemon zaƙi ko lemon tsami da kuma sikari. Ya jaddada cewa gwajin da ake yi a makwogaro da hanci har yanzu suna da mahimmanci idan mutum ya yi tunanin ya kamu da cutar korona. Mutanen da suka warke daga korona na iya jin ɗanɗano ko ƙamshi cikin 'yan makwanni kaɗan da warkewarsu, a cewarsa. Farfesa Andrew Lane wani ƙwararre ne kan matsalolin hanci a Jami'ar Johns Hopkins da ke Amurka. Ya ce shi da tawagarsa sun daɗe suna nazari kan samfurin da ake ɗauka daga hancin mutum domin gano yadda korona ke haddasa rashin jin ƙamshi sannan sun wallafa sakamakon bincikensu a mujallar European Respiratory. Sun gano wasu sinadarai masu yawa waɗanda ake samunsu a wurin hanci kaɗai kuma su ke sa mutum ya ji ƙamshi ko wari. Ana tunanin sinadarin da ake kira ACE-2 shi ne wajen da ke ba korona damar shiga ƙayar halittar da ke jikin mutum sannan ta haifar masa da cuta. Hanci ɗaya ne daga cikin wuraren da Sars-Cov-2, ƙayar cutar da ke janyo Covid-19, ke shiga jikin mutum. Farfesa Lane ya ce: ""Za mu ƙar gudanar da wasu gwajin domin gano ko da gaske ne ƙayar cuta na amfani da ƙayooyin halitta wajen samun damar sa wa mutum cuta. ""Idan hakan ta faru, muna iya maganin ciwon ta amfani da wasu magunguna da za a sa ta hanci.""" https://www.bbc.com/hausa/labarai-54195122 +health Mace-macen Kano: Aikin da kwararrun likitocin Abuja za su yi a Kano "Wani ayarin kwararrun likitoci ya shiga Kano da ke arewacin Najeriya daga Abuja, cibiyar gwamnatin tarayya don taimaka wa jihar game da ta samu kanta. Yawan mace-macen da ake samu a kusan daukacin unguwannin birnin Kano ya janyo ce-ce-ku-ce tsakanin al'ummar jihar da ma takwarorinsu a fadin kasar musamman na arewaci. Kano dai ita ce babbar cibiyar kasuwanci tsakanin jihohin arewa da ma wani bangare na yankin Afirka ta Yaamma, kuma dumbin mutane ne daga fadin Najeriya suke shiga suna fita kullum don harkokin ciniki. Dakta Sani Gwarzo shi ne shugaban ayarin likitocin gwamnatin tarayyar zuwa Kano, ya kuma shaida wa BBC cewa ayarin nasu ya kunshi kwararrun likitoci da dama kuma sun je ne don taimaka wa jihar wajen shawo kan matsalolin da take fuskanta da kuma dakile yaduwar korona. Ana samun mace-mace babu kakkautawa cikin 'yan kwanakin nan a Kano, kuma ko a karshen makon nan an fuskanci mutuwar wasu manyan mutane, kama daga malaman makaranta da 'yan kasuwa da ma sauran 'yan garin da ba a kai ga jin duriyar tasu mutuwar ba. Rashin sanin musabbabin mace-macen shi ne ya fi daga wa al'umma hankali, lokacin da ake tsaka da fama da annobar korona. Dakta Sani Gwarzo ya ce ""binciken gawawwakin da ke mutuwa babu gaira babu dalili, don tabbatar da ko wadannan mace-mace na da alaka da annobar korona? ko kuma ta fi alaka da zazzabin Lassa wanda jihar ta yi fama da shi a baya? Jin ra'ayoyin masana da kuma daidaikun mutane har da gwamnati don sanin me ake yi zuwa yanzu saboda a dakatar da wannan annoba (na daga cikin abubuwan da muka sanya gaba). Tattara bayanai da kuma samar da kayan aiki wadanda za a dukufa wajen tunkarar wannan cuta da su don ganin mutuwar da ake fama da ita ta ragu."" Ya kara da cewa a lokacin da ake kokarin shawo kan yawan mutuwar da ake samu, ana kuma yaki da cutar korona a lokaci guda. Mutanen da ke cikin ayarin Cikin likitocin akwai: Farfesa Abdussalam Nasidi tsohon babban daraktan farko a hukumar yaki da cutuka masu yaduwa ta kasar NCDC, wanda sanannen likita ne da ke da ilimi kan abubuwan da suka shafi kwayoyin cuta, ciki har da abin da ya danganci Ebola da Lassa da saurarnsu. Akwai shugabar asibitoci ta ma'aikatar lafiya ta kasa, Dakta Bimpe Adebiyi. Dakta Sa'id Amin, masani ne kan al'amuran da suka shafi mutuwa da gawa da kuma musabbabin mutuwa shi ma yana cikin ayarin. Akwai kuma rukunin likitoci masu ilmin cutuka masu yaduwa da ke bin diddigin yadda cuta ke bazuwa kamar mutum uku a cikin tafiyar. Sun tafi da masana daga bangarori guda uku, akwai kwararriyar ma'aikaciyar jinya da aka je da ita daga cibiyar yaki da 'yan kananan kwayoyin cutuka ta Irrua a Jihar Edo. Akwai wakilcin gwamnatin jihar Legas da kuma jami'ai daga cibiyar bincike ta Najeriya da ke jihar ta Legas. Wadannan kadan ne daga cikin mutanen da ke cikin wannan tafiya kuma su ne za a fara aikin da su. Dakta Sani Gwarzo ya ce ""An ba mu damar duk wanda muka ga zai iya taimaka wa cikin wannan tafiya, za mu iya hada hannu da shi domin kai wa ga nasara."" Ya ce ya zuwa yanzu ba su kayyade kwana nawa za su yi (a Kano) ba, amma da zuwansu, sun ziyarci a kalla wuri bakwai, ""don haka aiki ne za a yi ba dare ba rana sai an cimma gaci,"" in ji shi. Duk da yake an tanadi asibitoci da gadaje amma babbar matsalar da ake fuskanta a Kano ita ce aikin gwada mutanen da ake zargi sun kamu da korona ya tsaya cak, cibiyar da aka ware don wannan aiki ta samu matsala tsawon kwanaki. Sai dai mahukuntan sun ce ya zuwa ranar Talata komai ya daidaita kuma cibiyar ta sake budewa don ci gaba da aikin gwaje-gwaje. Duk da an samu gudunmawar wata karamar cibiya da kuma kayan aiki daga Jami'ar Bayero Kano amma ita ma ba ta fara aiki ba, sai nan da 'yan kwanaki. Kuma duk wani mataki da za a iya dauka domin dakile wannan matsaloli ya ta'allaka ne a kan gwajin cutuka da za a yi wa al'umma, don tantance hakikanin larurorin da suke fama da su. Akwai matsalar da ke kara dagula wannan hali da kano ke ciki, in ji Dakta Gwarzo, "" Yadda ake mantawa da masu kananan cutuka ko kuma cutukan yau da kullum da ake fama da su, kama daga hawan jini da irinsu ciwon kai da sauransu."" A iya cewa aikin shawo kan korona ya jefa masu kananan larurori cikin halin ni-'ya-su da garari a asibitocin Kano. Wadannan matakai na zuwa ne bayan a jawanbin shugaban kasar Muhammadu Buhari a daren Litinin, ya ce zai aika ayarin likitoci zuwa Kano don kai dauki da gudanar da bincike. Shugaban ya kuma sanar da kulle jihar na tsawon mako biyu domin dakile yaduwar korona." https://www.bbc.com/hausa/labarai-52464148 +health Wata bakuwar cuta ta bulla a jihar Benue "Hukumomin lafiya a Najeriya sun tabbatar da cewa kwararru na gudanar da bincike kan wata bakuwar cuta, wadda ake zargin ta halaka akalla mutum goma sha biyar a jihar Binuwai. Sakamakon wasu bayanai daga dakin bincike na kimiyya ya nuna cewa, bakuwar cutar ba ta zazzabin Lassa ba ce. Haka kuma, ana zargin fiye da mutum dari ne suka kamu da cutar da alamunta ke nuna kumburin kafa da ciki. Ministan lafiya na Najeriya, Dakta Osagie Ehanire ya shaida wa BBC cewa ana zargin mutane sun ci wani kifi ne da suka kama a wani rafi da aka zuba wa guba. ""Ana amfani da wata guba ta hanyar watsa ta a cikin rafi kuma sai su kama kifin su ci,"" in ji shi. Ya ce hakan na da matukar hadari ga lafiyar dan Adam. Dakta Osagie ya ce hukumomin lafiya da ke tashohin jiragen Najeriya a shirye suke tsaf don tunkarar duk wata cuta da ake iya shigowa da ita kasar. Ya ce suna bincike ""don gano mara lafiya a cikin fasinjoji masu shigowa daga wata kasa."" Ministan ya ce duk da rahotannin da wasu kafofin yada labarai ke watsawa na cewa cutar ta samu wuri a jihar Binuwai, har yanzu ba a kai ga tantance yawan asarar rayukan da cutar ta sa aka yi ba. Sannan ya ce mutane su kwantar da hankalinsu don har yanzu babu billar cutar coronavirus a kasar." https://www.bbc.com/hausa/labarai-51424103 +health Yadda anobar da ta faru shekaru 700 da suka wuce ke shafar lafiyarku Irin ɓarnar da annobar ta haifar ya yi mummunar tabo ga kakannin-kakanninmu ta yadda lamarin ke shafar lafiyarmu shekaru 700 bayan faruwar ta. Kimanin rabin al’umma ne suka mutu lokacin da annobar  da aka yi wa laƙabi da ‘Baƙar mutuwa’ ko ‘Black Death’ ta addabi ƙasashen Turai a shekarun 1300. Wani bincike a kan sinadarin ƙwayoyin halittun gado daga ƙwarangwal ɗin mutanen da suka tsira daga annobar, wanda shi ne bincike irin sa na farko, ya nuna yadda sauyi a ƙwayoyin halitta suka taimaka wa mutane suka tsira daga annobar. To amma waɗannan sauye-sauye na ƙwayoyin halitta ne kuma ake alaƙantawa da cutuka masu illa ga garkuwar jiki da ake fama da su a yanzu. ‘Black Death’ na daga cikin annoba mafi muni da aka taɓa fuskanta a tarihin ɗan’adam. Inda aka yi iyasin cewa ta hallaka mutum miliyan 200. Masu bincike sun yi zargin cewar dole ne irin wannan mummunan lamari ya sauya yanayin halittar ɗan’adam. Sun yi nazari kan ƙwayar halittar gado da ciro daga haƙoran ƙwarangwal ɗin gwarwakin mutanen da suka mutu tun tale-tale, waɗanda aka gano cewar sun rayu ne gabanin mummunar annobar, ko a lokacinta ko kuma bayan annobar. Ƙasusuwan da aka yi amfani da su wurin nazarin sun haɗa da waɗanda aka ciro daga wasu manyan ƙaburbura a London, sai kuma waɗanda aka samo daga Denmark. Sakamakon da aka samu, wanda aka wallafa a mujallar ‘Nature’ ya mayar da hankali ne kan wani sinadarin ƙwayar halittar gado da ake kira ERAP2. Idan mutum ya samu sauyi daidai yadda ya kamata, to akwai yiwuwar zai iya tsallake annobar da kimanin kashi 40%. “Wannan sauyi yana da yawa, yana da yawa sosai, abin mamaki ne a ce an samu irin wannan a cikin ƙwayar halittar gado ta ɗan’adam.” In ji farfesa Luis Barreiro na jami’ar Chicago. Saboda haka waɗanda suka ci sa’a sun gaji irin wannan sinadarin halittar gado da ya sauya daga mahaifansa biyu. Daga nan sai ƴaƴan waɗanda suka tsira daga annobar suka gaji irin wannan sinadari na gado daga iyayensu, daga nan sai mutanen da suka gaji irin wannan ƙwayar halittar gado suka yawaita. Farfesa Hendrik Poinar, masanin sauyin ƙwayoyin halittar gado na jami’r McMaster ya ce “babban lamari ne, an samu sauyi da kimanin kashi 10% a tsawon zamani uku.” Bayanan da aka samu daga jinin mutanen da suka da irin wannan ƙwayar halittar gado da ta sauya ya nuna cewa sun fi jure wa annoba fiye da waɗanda ba su da ƙwayar halittar da ta sauya. A yanzu, irin wannan sauyi da ake samu a ƙwayar halittar gado ya yawaita fiye da yadda aka samu jim kaɗan bayan annobar ‘Black Death’. To amma matsalar ita ce ana alaƙanta sauyin da cutuka masu illa ga garkuwar jikin ɗan’adam, kamar cutar kumburin ƴaƴan hanji da a turance ake kira ‘Crohn’s’. Hakan na nufin lamarin da ya kasance taimako ga kakannin-kakanninka shekaru 700 da suka gabata, yanzu ya zamo illa gare ka. Farfesa Barreiro ya ce garkuwar kashi 40% da aka gano sanadiyyar sauyin da aka samu a ƙwayar halittar gado shi ne mafi ƙarfi da aka taɓa samu tsakanin bil’adama. Ya zarta irin turjiyar da ake samu tsakanin mutanen da jikinsu ke bijire wa cutar HIV. https://www.bbc.com/hausa/articles/c5147nqzn8do +health Matar da ta sauya rayuwa saboda ziyarar da ta kai matattarar kutare "A cikin jerin wasiku daga marubutan Afirka, Adaobi Tricia Nwaubani ta yi rubutu kan wata mata wadda rayuwarta ta sauya bayan ta gamu da larurar fata sannan daga bisani ta ziyarci wata matattarar kutare a Najeriya. Iby Ikotidem, ta kasance mai son jin dadin rayuwa da zuwa walima irin ta Turawa. Tana matukar son kwalliya da kyale-kyale, tana kuma da yawan kawaye, ga yawan shirya walima a jihar New Jersey ta Amurka, inda take zaune tare da mijinta da 'ya'yanta biyu fiye da shekara 28. Ta ce: ""Na kasance mai kayatarwa a wuraren biki."" Amma duk wanann ya zo karshe jim kadan bayan ta fara samun matsala a fatarta ta gwiwa shekara 12 da ta wuce. Da farko ba ta damu ba saboda abin da ya fito mata a kan gwiwarta ba shi da yawa, amma daga bisani abin ya dinga karuwa da bazuwa zuwa sassan jikinta in banda fuskarta. Bayan gwaje-gwaje da aka yi mata, an gano ta kamu da wani nau'in karzuwa, wanda yake sa kwayoyin halitta a jikin fata su kumbura kuma fatar mutum ta dinga wani ɓawo-ɓawo, ga kaikayi da kuma bushewa. Duk da tana rufe jikinta da dogon siket da riga mai dogon hannu saboda kar a rika kallonta, yanayin da take ciki kan sa ko da ta fita sai an kalleta. A wasu lokuta, idan ta tashi daga kan kujera sai mutane su yi ta mamaki a kan yadda aka samu kura a kai da ma kasan wajen da ta zauna saboda zubar bawon karzuwar da ta fito mata a jikinta. ""Na tsani na kalli kaina, madubi ya zame mani babban makiyi,"" in ji ta. Ba a jima ba aka fara tsangwamar ta. Mrs Ikotidiem ta ce ta tuna wani abu da ya faru a lokacin da aka gayyace ta wajen wata walima a gidan kawarta. An ajiye mata katifa a dandaryar kasa a wani ɗakin karkashin kasa, yayin da sauran mahalarta walimar aka ba su dakuna a bene. Ta ce: ""A ranar na zauna na sha kuka saboda ɓacin rai"". Ba a jima ba Mrs Ikotidiem ta kebe kanta daga shiga jama'a, sannan ta aske gashin kanta, ta fita hayyacinta har sai 'yarta mai shekara 12 ta fada mata cewa ""Haba mahaifiyata abar alfaharina kar ki bari wannan larurar ta sanyaya miki gwiw.'' Daga nan ne Mrs Ikotidiem ta dawo hayyacinta ta kawar da tunanin kashe kanta da take yi. Bayan shekara da kamuwa da larurar, sai aka gayyaci 'ya'yanta su bi wata tawagar matasa a Amurka zuwa jiharsu ta asali a Najeriya wato Akwa Ibom domin gudanar da wani aikin taimako. Ɗanta mai suna Anthony a lokacin yana da shekara 15, ya roki mahaifiyarsu da ta raka su, ta amince. Sun ziyarci gidajen marayu da dama inda suka dinga bayar da taimako. Bayan sun dawo masauki a wani otal suna zaune suna cin abinci da safe, sai ga wata abokiyar karatun Mrs Ikotidiem, ta yabe ta sosai a kan yadda suka dinga bayar da taimako a gidajen marayu - saboda an nuna a gidajen talabijin na jihar. A nan ne kawarta ta bukaci da ko za su je wata matattarar kutare a jihar domin ba su taimako. Sai Mrs Ikotidiem ta ce, kai har yanzu akwai kuturta a Najeriya? Wannan shi ne lokacin da ta fara sanin cewa lallai akwai kuturta a duniya. Duk da kasancewar ana kokari wajen kawar da kuturta a Najeriya, har yanzu akwai wadanda suke da ita inda ake samun mutum 3,500 a duk shekara da ke kamuwa da ita a cewar hukumar kula da cutuka masu yaduwa ta kasar NCDC. Ana iya maganin wannan cuta idan har aka gano ta da wuri, amma idan aka bari ta jima a jikin mutum takan haddasa lalacewar wasu wurare a jikin mutum kamar kafa da hannu, wani lokaci har makanta take haifarwa. Wasu iyaye sun yi fargaba da suka ji cewa Mrs Ikotidiem za ta je asibitin kutare na Ekpene Obom, amma wannan ziyara ta sauya mata rayuwa. Kamar sauran asibitocin kutare a Najeriya, asibitin kutare na Ekpene Obom ma na samar da wajen zama ga masu larurar wadanda ba za su iya komawa gida ba saboda tsangwama. Ko da sun warke bayan an yi musu maganin cutar inda ake daukar wata 6 zuwa 12, sukan kasance a wajen tare da iyalansu har ma 'ya'yansu su dinga zuwa makaranta a harabar wajen. Mrs Ikotidem ta fada wa mazauna wajen da ma marasa lafiyar cewa ta fahimci irin halin da suke ciki. Ta ce: ""Na san yadda mutum ke ji idan aka yi watsi da shi ko kuma ake kallon sa"". A yanzu Mrs Ikotidem ta shafe fiye da shekara 10 tana kula da masu larurar kuturta. Ta bude gidauniya mai suna Hope's Door, inda take kula da masu larurar kuturta a asibiti uku a kudanci da kuma arewacin Najeriya. Bayan duk taimakon da take yi, takan samar da takalmi na musamman da kujerar guragu ga masu matsalar. Takan kuma aika da kayayyakin karatu ga 'ya'yan masu lalurar, tana gyara musu muhallai. Duk da dan tallafin da asibitocin kutare ke samu daga gwamnati, yawancin irin wadannan asibitoci a Najeriya na dogara ne da taimakon da suke samu daga kungiyoyin agaji na kasashen waje. ""Idan suna da wata matsala, sukan kira ni,"" a cewar Mrs Ikotidem. Ta sayar da sarkokinta ne da farko inda ta fara kai tallafi ga irin wadannan asibitoci, daga bisani sai ta hada wani taron tara gudunmuwa daga kawayenta, a nan ne ta tara kudade masu yawa. A yanzu abin da take son yi shi ne taimaka wa wadanda ke zaune a matattarar kutaren ta yadda za su zamo masu dogaro da kansu inda za ta ba su kayayyakin aikin noma don noman gonakinsu." https://www.bbc.com/hausa/labarai-59629507 +health Ma'aikatan lafiya na fuskantar barazanar kisa daga 'yan bindiga """Mutane suna tunanin cewa babu gaskiya a batun yaduwar cutar Ebola,"" a cewar Dokta Pascal Vahwere, wani likita da ke kokarin dakile cutar. ""Tawagata na fuskantar barazana domin aikin da muke yi"". Dakta Vahwere ya shaida wa BBC cewa a cikin watan Maris da ya gabata, wasu gungun mutane sun kai masa hari a lokacin da yake jagorantar wata kungiya ta ma'aikatan lafiya domin zuwa wani kauye domin bayar da rigakafin cutar a yankin arewacin Kivu na Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo. ""Kwatsam sai wani gungun mutane masu dauke da bindiga suka afka mana. Ba mu san dalilinsu na kawo mana hari ba. Mun tsorata. Daga baya mun yi magana da shugabanin yankin, lamarin da ya jawo mutanen suka watse."" Ma'aikatan lafiya na neman wadanda suka kamu da cutar, sai su kawo su cibiyoyin da aka ware domin kulawa da su. Suna kuma taimakawa wajen binne wadanda suka mutu. Sai dai abu ne mai hadarin gaske ga ma'aikatan lafiyar su shiga wuraren da ake fama da cutar. A yayin da cutar take ci gaba da yaduwa, tana kuma kara halaka mutane kuma ma'aikatan lafiya na fuskantar fushin masu dauke da makamai sakamakon zarge-zargen da ake yadawa musamman a dandalin Whatsapp. Akalla mutum bakwai ne suka rasa rayukansu a cikin shekarar nan kawai. BBC ta yi magana da masu yaki da cutar kan dalilin da ya sa hakan ke faruwa. Zarge-zarge da kuma rashin daukar cikakkun matakai kan cutar ne ke haifar da kiyayya tsakanin mutanen da za su iya kamuwa da cutar. ""Yaduwar labaran bogi ya jawo mutane sun yarda cewa Ebola hanya ce ta samun kudi ga 'yan siyasa,"" a cewar Dr Vahwere. Yana aiki ne da wani kwamitin ceto mutane na kasa da kasa da ke birnin Goma wanda ke gabashin DRC. Birnin ya bayyana cewa mako biyu da suka gabata ne ya fara rasa mutum daya sakamakon cutar, inda a farkon makon nan kuma aka samu mutum daya da ya kamu da cutar. ""Wasu har cewa suke yi maganin Ebolan ne ke kashe mutane,"" in ji shi. An samu karuwar hare-hare kan ma'aikatan lafiya tun bayan da aka fara yada zarge-zargen. ""Tun 1 ga watan Janairun 2019, an kai hari 198 kan cibiyoyin lafiya da kuma ma'aikata da ke karkashin hukumar kula da lafiya ta duniya WHO. ""Lamarin ya jawo mutuwar mutum 7 da kuma 58 da suka samu raunuka a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo,"" kamr yadda Sakuya Oka wani manajan sadarwa na WHO ya shaida wa BBC. A cikin wadanda suka rasa rayyukansu har da wani babban mai bincike kan cutuka na WHO, Richard Mouzoko. An kashe shi ne a yayin wani harin da aka kai kan asibitin jami'ar Butembo a ranar 19 ga watan Afrilu. Mutum biyu ne suka samu raunuka a yayin harin. A cikin watan Mayu mazaunan wani kauye da ke gabashin Kongo sun kashe wani ma'aikacin lafiya tare da kuma sace abubuwan da ke cikin cibiyar ta kula da lafiya. A ranar 15 ga watan Yuli an kashe wasu ma'aikatan lafiya masu yunkurin dakile Ebola a gidajensu da ke yankin Kivu na arewacin kasar. Yadda ake samun karuwar hare-hare na rage kaifin yadda hukumomi ke tunkarar cutar. Cutar na ci gaba da yaduwa cikin gaggawa - a cikin kwannaki 224 ne dai mutum 1000 suka kamu da cutar, cikin kwanaki 71 kuma wasu 2000 suka sake kamuwa. ""A yau mun samu nasarar dakile cutar daga kan mutum 57 a cikin wata cibiyar kula da cutar ta Beni. Hakan na nufin kenan muna aikin mu da kyau,"" a cewar Dakta Freddy Sangala. Ebola cuta ce wadda ke yaduwa ta ruwan jikin mutum kamar ruwa da kuma kayayyaki ko barguna wadanda wannan ruwan ya taba. Babu maganin Ebola, amma shan magani idan aka yi hasashen cewa mutum na dauke da ita zai iya taimakawa wajen samun nasarar dakile ta. Rigakafi An kirkiri wani sabon rigakafi wanda ake bai wa mutane a DRC domin taimakawa wajen dakile yaduwar cutar ta Ebola. An yi wa kusan mutum 170,000 wadanda suke da alaka da masu dauke da cutar rigakafi. Amma hare-haren na kawo cikas kan shirin na yi wa mutane riga kafi, wanda hakan ke baiwa cutar karin damar yaduwa. Yaduwar Ebola na faruwa ne a yankin da ke da a kalla kungiyoyin 'yan tawaye 24. A cikinsu har da wadanda gwamnati ke zargin cewa sun kai hare-hare kan ma'aikatan lafiya. Babban darakta janar na WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya wallafa wani sako a ranar 10 ga watan Mayu bayan da ma'aikatan lafiya suka fuskanci hare-hare cewa: ''Abin tausayin shi ne ba mu da yadda za mu yi mu dakile Ebola, amma idan aka ci gaba da kai hare-hare to dakile yaduwar zai fi zama abu mai wuya.'' A arewacin Kivu, wata kungiyar masu dauke da bindiga wadanda ake kira ""Mai-Mai"" ne ke da hannu a wasu hare-hare kan ma'aikatan lafiyar da kuma cibiyoyinsu, a cewar gwamnati. An zargi wata kungiyar masu bindiga mai suna Allied Defence Forces wato 'yan tawayen Uganda kenan masu aiki cikin Kongo da lalata wasu cibiyoyin lafiya. An kuma samu hare-hare daga wasu kungiyoyi da ba a san ko su wane ne ba kan cibiyoyin da ake kula da masu Ebola. An taba samun wani lamari a watan Mayu, inda wasu 'yan uwa suka ci zarafin wasu ma'aikatan lafiya wadanda ke binne daya daga cikin 'yan uwansu. Karuwar hare-haren dai ya jawo abubuwa da dama. ""Bayan kowane hari dai, ana samun karuwar mutanen da ke kamuwa da cutar,"" a cewar Amy Daffe. Domin kare ma'aikatan lafiyar, gwamnati na kara aika jami'an tsaro domin tsare su. Kate White wata nas ce kuma tana aiki da kungiyar da ke bayar da tallafi a fannin lafiya ta kasa da kasa, mai suna Doctors without Borders. Ta shaida wa BBC dalilin da ya sa ba a cika yarda da juna a yankin ba. ''Al'ummomin na fama da rashin yarda ne na tsawon shekara 20 da ake rikici a gabashin Kongo, inda ake rasa kulawar asibiti ta gari. A wasu wuraren ma ba a samu baki daya."" Ma'aikatan lafiya dai na tattaunawa da shugabbanin al'ummomi domin kawar da rashin yardar. ""Ya kamata mu saurari damuwar mutane kamar yadda muke so mu ma a ji tamu. Amsoshin da za mu samu kuma za mu yi amfani da su wajen biyan bukatunsu ta fannin lafiya,"" a cewar White. Sannan kuma ta ce za su iya yin nasara. ""Ba zai yiwu mutane su yarda da kai don ka shiga al'ummarsu so daya ba ka tattauna da su kan Ebola. Dole sai ka dauki lokaci wajen samun su yarda da kai tukunna."" Wannan gaskiya ne musamman idan muka dubi lamarin Charles Lwanga-Kikwaya, wani ma'aikacin lafiya. An kai wa tawagarsa hari a ranar farko ta wannan shekara a wata cibiyar da ake yi wa mutane riga kafi da ke DRC. Bayan da ya yi kwanaki shida a asibiti yana karbar kulawa mai tsanani, an sallame shi daga asibiti. Bayan wasu 'yan watanni har ya koma aiki da tawagarsa masu rajin dakile Ebola. ""Zan ci gaba da aiki har sai an dakile cutar baki daya,"" in ji Mista Lwanga-Kikwaya. ""Ba zan yarda abokanaina da kannena mata da maza su rasa rayukansu sakamakon cutar da zan iya yin kokari na wajen dakile ta ba,"" ya shaida wa WHO." https://www.bbc.com/hausa/labarai-49194431 +health Najeriya: An gano wadanda suka yi hulda da mai coronavirus An gano sama da mutum 100 a Najeriya da suka samu kusanci da dan kasar Italiyan da ke dauke da cutar coronavirus a kasar. Kwamishinan lafiya na jihar Legas Akin Abayomi ya ce hukumomin kasar sun tuntubi mutanen da ake kyaututa zaton sun yi hulda da mara lafiyan. Kamfanin dillancin labaru na Reuters ta ambato kwamishinan na cewa adadin mutanen da ake tantancewa saboda sun yi mu'amala da mutumin na iya karuwa. Yanzu mara lafiyan wanda dillali ne na kamafin siminti na Lafarge da ke Ogun, na killace a cibiyar kula da masu coronavirus da ke Yaba a jihar Legas. Mutumin ya isa Najeriya ne a ranar 24 ga watan Fabrairu ta filin jirgin sama da ke Legas kafin washegari ya wuce jihar Ogun mai makwabtaka. Kwanansa biyu a Najeriya kafin a gano alamun coronavirus a tare da shi, sannan aka killace shi. ■ Ku wanke hannayenku da sabulun gargajiya ko sabulun ruwa da ake wanke hannu da shi, wato hand gel, wanda zai iya kashe kwayoyin cuta ■ Ku rufe hanci da bakinku lokacin da kuke yin atishawa da kyallen fyace majina - sannan ku wanke hannayenku bayan kun yi atishawa domin hana kwayoyin cutar yaduwa. ■ Ku guji taba idanunku, ko hanci ko bakinku- idan hannunku ya taba wurin da cutar ta shafa, za ta iya yaduwa zuwa sauran sassan jikinku. ■ Kada ku rika matsawa kusa da mutanen da ke yawan atishawa ko tari da masu fama da zazzabi - za su iya watsa cutar cikin iska ta yadda ku ma za ku iya kamuwa da ita. - akalla ku matsa nesa da su ta yadda tazarar da ke tsakanin ku za ta kai kafa uku. https://www.bbc.com/hausa/labarai-51697534 +health Masana kimiyya na hasashen ɓarkewar annobar kwalara daga sararin samaniya "Masu bincike sun samo wata hanyar hasashen yaɗuwar annobar kwalara ta hanyoyin amfani da tauraron ɗan adam na sauyin yanayi da kuma basirar na'ura wato (artificial intelligence). Masu binciken suna fatan wannan zai kare rayukan mutane a yankunan da suka fi fama da annobar. ""Abu ne mai kyau ƙwarai da gaske saboda yanzu za mu iya kula da duniyarmu,"" in ji Dr Paolo Cipollini, na hukumar kula da sararin samaniya ta Turai (ESA). ""Ba za ka taɓa tunanin sararin samaniya da tauraron ɗan adam za su iya magance matsalolin kiwon lafiya ba amma wannan wani abu ne da yake samun karɓuwa sosai."" Binciken ya nuna yadda samun ɓarkewar cutar kwalara a yankunan gaɓar Tekun Indiya da za a iya hasashe da kashi 89. Tawagar ESA da kuma masu bincike na PML sun tattara bayanai na tsawon shekaru takwas daga taurarorin ɗan adam kan muhalli, kuma ta amfani da basirar na'ura da kuma ƙirƙirar hanyar da za a iya hasashen inda kwalera za ta iya ɓarkewa. Cutar kwalara cuta ce da ake samu ta hanyar cin gurɓataccen abinci ko ruwa da ɗauke da kwayar cuta ta Vibrio Cholerae. An fi samun masu cutar a kasashen da ke iyaka da arewacin Tekun Indiya, ciki har da Indiya, inda masu binciken suka mayar da hankali. Sun yi amfani da ma'auni daban-daban guda bakwai daga tauraron dan adam wajen yin hasashensu. Masana kimiya sun duba sauye-sauye a ruwa masu ɗanɗanon gishiri, inda ake samun ƙwayoyin cuta, da kuma ƙaruwar babbar ƙwayar cutar. Sun kuma auna abubuwa kamar tururin zafi, inda mutane ke hutawa a bakin ruwa, ko ruwan sama, wanda zai iya haɗuwa da gurɓataccen ruwa mara tsafta. ""Abin da bincikenmu ya sha bamban shi ne yin amfani da irin dubaru daban daban,"" in ji mai bincike Amy Campbell, wacce ta yi aiki tare da ESA da PML wajen yin hasashen. ""Ɗaya daga cikin hanyoyin shi ne ɗanɗanon gishiri a ruwa, wanda sabon abu ne da ke da matuƙar taimakawa wajen hasashen yiyuwar ɓarkewar cutar kwalara. ""Idan har za mu iya amfani da shi don fahimtar lokacin da muke tunanin ɓarkewar cutar kwalara, za mu iya tabbatar da cewa an yi shiri, kuma za a iya rage cutar ta hanyar rigakafi a yankunan da cutar ta ɓarke."" Masana sun ce sauyin yanayi da yanayin zafi ke ƙara haifar da annobar kwalara. Hukumar Lafiya Ta Duniya (WHO) ta ce duk shekara ana samun mutum sama da miliyan huɗu da masu fama da kwalara, kuma mutum 143,000 ke mutuwa sanadiyyar cutar. Duk da mutane kan nuna alamomin cutar, tana haifar da gudawa mai tsanani kuma cutar na iya kisa cikin lokaci ƙanƙani idan ba a yi gaggawar ɗaukar mataki ba. ""Ta fi shafar ƙananan yara waɗanda suka fi kamuwa da cutukan da ake samu da daga ruwa, yawancinsu ƴan ƙasa da shekara biyar. ""Muna fatan samun wannan da inganta hasashen yiyuwar ɓarkewar annobar korona zai taimaka wajen rage barazanarta ga yara,"" in ji Dr Marie-Fanny Racault, babban masanin kimiya na cibiyar bincike ta PML. Masana kimiyya sun gano cewa hasashen zai kasance hanyar da za yi dogaro da musamman lokacin damina, da kusan kashi 93.3 cikin 100. Amma sun ce ana buƙatar ingantawa don ƙara tabbatarwa." https://www.bbc.com/hausa/labarai-56184840 +health Abinci biyar masu guba da ka iya kisa A haka, ana iya cewa babu wani hadari a tattare da abinci. Amma maganar gaskiya ita ce, ba ko wane abinci ne ake ci ba tare da daukar mataki ba, kamar dubawa da kyau, ko wajen dafawa ko shiryawa - kamar cire wasu sassan jikin abincin da ke iya cutarwa. Idan ba a dauki wadannan matakan ba, akwai nau'in abincin da idan aka ci suna iya janyo cuta, kuma alamomin cutar na iya zama tashin zuciya ko gushewar hankali ko ma mutuwa. A yanayi marar kyau ko kuma abincin da ba a adana shi ko dafa shi yadda ya kamata ba, abincin na iya janyo tashin zuciya, daukewar numfashi ko gushewar hankali har ma a kai ga an mutu. Ga nau'in abinci biyar da ya kamata a duba sosai kafin a ci. Asali ma, idan ba ku da tabbas kan wadannan nau'ukan abinci, ka da ku ci su kwata-kwata. 1. Kifin Puffer Kifin Puffer na iya kisa. Yana dauke da sinadarin 'tetrodotoxin', wani sinadari mai guba wanda ake tunanin ya fi sinadarin 'cyanide' hadari. Sai dai suk da hadarinsa, ana matukar son cin Kifin Puffer a wasu kasashen. A kasar Japan, ana cin kifin (ana kiransa fugu a can) danye ko kuma a sa a miya. Ana horar da masu dafa abinci tsawon shekaru kafin a ba su damar dafa wa mutane kifin. Abin dubawa shi ne a tabbatar cewa kafin a fara ci, an cire duka sassansa masu dauke da guba, wadanda suka hada da kwakwalwarsa da fatarsa da idanunsa da kayan cikinsa. 2. Cikwi na Casu Marzu Abin da ya sa wannan abincin ya fita daban shi ne yana dauke da tsutsotsi. Wannan na iya sa wa a ji kyama, amma wannan cikwi din dan asalin garin Sardinia, na Italiya na da masoya da yawa. Ana hada wannan cukwi din ta hanyar hada tsutsar kuda a cikin cukwi din 'pecorino', wani nau'i na cukwi mai kama da cukwi din 'permesan'. A hankali, kananan tsutsotsi na sa cukwin ya yi laushi yadda idan aka zuba a kwano za a ci, cikinsa ya zama ruwa-ruwa. Cukwin Casu marzu na da dandano na daban saboda kashin tsutsotsin. Kafin a ci shi, sai an dauki wasu matakai. Daga farko, sai kana da hanzarin kama tsutsa- tana iya tsalle tsawon sentimita 15- idan ana cin cukwin. Abu na biyu shi ne, yana da wuyar samu. Casu marzu ba ya cikin jerin abiinci da Tarayyar Turai ta amince da su, domin haka ba a iya shigo da shi. Na uku, an bayyana shi a matsayin cukwi mafi hadari a duniya saboda yana iya yin illa ga lafiya. Wannan haka yake, idan tsutsotsin sun mutu (sai dai idan mutuwa suka yi bayan da aka sa cukwin a firji) saboda wannan na nufin cukwin ya lalace. Idan aka ci lalataccen cukwin, wannan na iya haifar da ciwon ciki da amai da zawo. 3. Ganyen Rhubarb Ana amfani da tsinken ganyen rhubarb sosai misali a girke-girken Birtaniya. Abinci da yawa a Birtaniya na dauke da shi. Sai dai dole a kula saboda koren ganyen rhubarb na dauke da guba. Babban abin shi ne yana dauke da sinadari mai guba da ake kira 'oxalic acid', wanda idan aka ci shi da yawa yana janyo tashin zuciya da duwatsun koda. Ana ci gaba da muhawara kan hadarin ganyen rhubarb saboda yawan sinadarin 'oxalic acid' da ke cikinsu. Ana samun 'oxalic acid' a jikin tsinkayen, amma ya fi yawa a ganyen. Sai dai sai idan an ci da yawa ne yake iya kashe mutane, amma gara kar a ci kwata-kwata. 4. Jan wake da waken soya Ana ganin wake a matsayin abinci mai inganta lafiya, amma akwai wani nau'insa da idan ba a kula ba, yana iya haifar da rashin lafiya. Jan wake da waken suya na cikin wannan nau'in. A wani bangare, suna dauke da sinadaran 'protein' da 'vitamin' masu gina jiki. Amma kuma, danyen wake na dauke da wani irin mai, mai suna 'phytohaemagglutinin' wanda jikin dan Adam ba ya iya sarrafa shi. Cin sa da yawa na janyo ciwon ciki da haraswa. Abin farin ciki shi ne dafa waken sosai yana kawar da wadannan abubuwan. Waken suya kuwa na dauke ne da wani sinadari mai guba mai suna 'trypsin', wanda ke iya hana jikin mutum sarrafa abincin. Amma idan aka jika wadannan nau'ika na wake a ruwa tsawon awa 12, sannan a tafasa su na kawar da wannan sinadari. 5. Gyadar Miya Wannan wani nau'i ne na kayan kamshi daga wata bishiya a Indonesiya. Tana da muhimmanci sosai wajen dafa wasu nau'ukan abinci kamar biskit da kunu. Baya ga haka, ana amfani da gyadar miya wajen dafa dankali da nama da miya da ganyayyaki. Sai dai, idan aka sa ta da yawa tana janyo abubuwa da dama: tashin zuciya da daukewar numfashi har ma da suma- da kuma gushewar hankali. Da wuya, rashin lafiya dalilin cin gyadar miyar (nutmeg) da yawa ya jawo kisa amma yana wahalarwa. Amma me ma zai sa mutum ya ci kayan kamshi haka da yawa a lokaci guda? To, an dade ana amfani da gyadar miya a wajen gusar da hankali. Sai dai idan aka yi la'akari da abubuwan da suke jawowa, babu ma amfanin cin gyadar ya wuce kima. https://www.bbc.com/hausa/labarai-50502811 +health Yara fiye da dubu 20 ne suka kamu da cutar HIV a Najeriya a bara- UNICEF "Rahoton na asusun kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF ya ce kananan yara daga kan jarirai zuwa 'yan shekara 9, fiye da dubu 20 ne suka kamu da ƙwayar cuta mai karya garkuwar jiki a Nijeriya a 2020. Har wa yau, rahoton ya kara da cewa kimanin 30 cikin 100 na mace-mace masu alaƙa da cuta mai karya garkuwar jiki da suka faru a bara cikin Nijeriya, ƙananan yara ne. Wannan batu dai ya zo wa 'yan Najeriya da dama da mamaki ganin yadda alkaluman suka harba sama. To sai dai Abdulƙadir Ibrahim, babban jami'in gamayyar ƙungiyoyin masu fama da cuta mai karya garkuwar jiki a Nijeriya wato NEPWHAN, ya ce alkaluman ba su zo musu da mamaki ba kasancewar yanzu haka a Najeriya da dama iyaye mata masu ciki ba sa iya samun damar yin gwajin kwayar cutar. ""Lokuta da dama za ka ga mace mai ciki ta zo asibiti amma sai ka ga babu kayan gwaji ko kuma idan ma da kayan sai a sanya kudi. Su kuma ka san matan karkara ba sa raina yawan kudi abin da zai sa su zuke su ki zuwa gwajin. Hakan ne yake sa har mace ta samu juna biyu har ta sauka ta fara shayarwa ba za a gano tana dauke da kwayar cutar ba domin dakile shafa wa dan da ta haifa."" Abdulkadir ya kara da cewa ""mu a yanzu muna da kididdigar a wannan watan kawai sama da yara dubu 150 wadanda aka dora a kan maganin kwayar cutar ta HIV."" Wadannan alkaluma dai na zuwa a dai-dai lokacin da duniya ke bikin ranar yaki da cutar mai karya garkuwar jiki ta HIV. Yau ce dai ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe domin jan hankalin al`ummar duniya ga kokarin da ake yi wajen yaki da cuta mai karya garkuwar jiki ta HIV ko SIDA. A  wannan shekarar, Majalisar Dinkin Duniyar ta ba da fifiko ne ga samar da daidaito a tsakanin masu fama da cutar fiye da mutum miliyon 37 ta fuskar samar da magani da kulawa. Har wa yau, a irin wannan rana ana kuma mayar da hankali ga mutanen da suka harbu da cutar amma ba a gano su ba,  domin cim ma kudurin dakile cutar nan da shekara ta 2030. A Najeriya ma, mutum miliyon daya da dubu dari takwas ne suke fama da cutar, kuma mahukunta a kasar sun yi alwashin takaita yaduwar cutar nan da shekaru biyu masu zuwa wato zuwa 2023." https://www.bbc.com/hausa/labarai-59486205 +health 'Ina shan maganin ciwon koda na N35,000 a kowace rana' Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon: A ranar Alhamis ta biyu ta kowane watan Maris ana bikin ranar masu ciwon koda ta duniya. Ana bikin ne don jan hankalin jama'ar duniya kan girman cutar da matakan da ya kamata a dauka wajen kare kai daga kamuwa da cutar. Nkwanko Faithful na daga mutane da suke fama da ciwon koda a Najeriya, wacce tace tana shan wahala a jikinta sannan tana fama da wahalhalun kashe kudi wajen neman magani. A cikin wannan bidiyon ta bayyana mana yadda ta kamu da cutar da da kuma yadda take jinyar cutar ta ciwon koda. Sannan wani kwararren likita ya bayyana girman cutar, da yadda ake kamuwa da ita, da matakan kariya daga cutar ta koda. https://www.bbc.com/hausa/labarai-60686137 +health Coronavirus: Wanne shiri Najeriya ta yi don dakile cutar? "Samun mutumin da ya kamu da cutar numfashi ta coronavirus karon farko a Najeriya ya sa 'yan kasar na tambaya: wanne shiri hukumomi suka yi na dakile ta? Ranar Alhamis ne Hukumomin Lafiya a Najeriya suka tabbatar da bullar coronavirus wadda ake kira Covid-19 a jihar Lagos da ke kudu maso yammacin kasar. A sanarwar da ya fitar, Ministan Lafiya na Najeriya, Dr Osagie Ehanire, ya ce wani dan kasar Italiya ne da ke aiki a kasar ya shigo da cutar bayan ya dawo Lagos daga birnin Milan. ""Sakamakon gwaji da aka gudanar a asibitin Koyarwa na Jami'ar Lagos ya tabbatar da mutumin yana dauke da cutar. ""Ana duba lafiyarsa a Asibitin Kula da Cututtuka Masu Yaduwa a Yaba, kuma marar lafiyar bai nuna alamomi masu muni ba,"" in ji shi. Wannan shi ne karon farko da aka samu bullar cutar a nahiyar Afirka kudu da hamada. Hanyoyi 4 na kare kai daga coronavirus ■ Ku wanke hannayenku da sabulun gargajiya ko sabulun ruwa da ake wanke hannu da shi, wato hand gel, wanda zai iya kashe kwayoyin cuta ■ Ku rufe hanci da bakinku lokacin da kuke yin atishawa da kyallen fyace majina - sannan ku wanke hannayenku bayan kun yi atishawa domin hana kwayoyin cutar yaduwa. ■ Ku guji taba idanunku, ko hanci ko bakinku- idan hannunku ya taba wurin da cutar ta shafa, za ta iya yaduwa zuwa sauran sassan jikinku. ■ Kada ku rika matsawa kusa da mutanen da ke yawan atishawa ko tari da masu fama da zazzabi - za su iya watsa cutar cikin iska ta yadda ku ma za ku iya kamuwa da ita. - akalla ku matsa nesa da su ta yadda tazarar da ke tsakanin ku za ta kai kafa uku. Minista Ehanire ya ce gwamnatin kasar ta hannun Ma'aikatar Lafiya ta kara tsaurara matakai don dakile cutar nan take. Ya ce sun zage damtse wurin ganin Cibiyoyin Kula da Lafiyar Gaggawa a fadin kasar sun tashi tsaye domin gudanar da ayyukansu, yana mai cewa za su hada gwiwa da cibiyar da ke Lagos don shawo kan cutar. ""Muna so mu tabbatar wa 'yan Najeriya cewa cibiyoyinmu na ko-ta-kwana sun kara kaimi wurin gudanar da ayyukansu tun da aka samu labarin bullar cutar a China, kuma za mu yi amfani da dukkan matakan da gwamnati za ta iya dauka domin dakile ta"", a cewar ministan. Ya yi kira ga 'yan Najeriya su kula da lafiyarsu, musamman tsaftar hannaye da hanci da sauran sassan jiki da ke taimakawa wurin yin numfashi. Ya bukaci duk mutumin da ya ji alamar rashin lafiya, irin su zazzabi da mura da tari, ya kira wannan lamba: 0800 970 0000-0010." https://www.bbc.com/hausa/labarai-51670452 +health Ana ja-in-ja tsakanin masu ɗorin gargajiya da na zamani a Jigawa "Sakamakon yadda ake takaddama tsakanin likitoci da masu dorin gargajiya kan gyaran karaya, wakiliyar BBC Aisha Shariff Baffa, ta yi nazari a kan haka a jihar Jigawa da ke arewa maso yammacin Najeriya. Sabon garin Madora gari ne mai nisan kilomita kusan shida daga karamar hukumar Dutse a jihar Jigawa, haka kuma gari ne mai yawan mutane kusan dubu biyu. Da ka shiga garin za ka yi karo da gidan Sarkin Madora Muhammadu Auwalu, inda a kofar gidansa akwai wani dakin kasa wanda shi ne dakin kwantar da masu karaya, wato ga Malam Auwalu Sarkin Ɗori wannan daki daidai yake da dakin kwantar da marasa lafiya a asibiti. A wannan gari sana'ar dori ba a babba ko karami ko kuma tsoho ta tsaya ba, hatta yaro ko yarinya 'yar shekara 10 zuwa sama ana koya musu ita. Da wannan sana'a ta dorin gida mutanen wannan gari kanci su sha su yi sutura kai hatta sauran bukatu kamar na aure da dai makamantansu mutanen kan yi. Mata a wannan gari ma ba a bar su a baya ba domin akwai madora da dama daga cikinsu wadanda yawancinsu kan ce sun gaji wannan sana'a ne tun kaka da kakanni. Masu dori a wannan gari a lokuta da dama kan yi ikirarin cewa duk munin karaya ko da kuwa za ta gagari likitoci, to su idan aka kawo mutum za su dora shi tsaf har ya mike. Wani abin ban al'ajabinma madoran kan ce wai a wasu lokuta idan likita zai yi wa mutum aikin karaya a kan gayyato su a shiga da su cikin dakin tiyatar likita ya yi nasa aikin, shi ma mai dori ya yi nasa. Haka kuma madoran wannan gari kan ce ko da mutum hadari ya yi kashin wani bangare na kafarsa ko hannunsa ya fita, to idan an kawo musu wannan marar lafiyar, su kan je inda aka yi wannan hadarin su nemo kashin su zo su dora mutum. Muhammadu Auwalu, shi ne shugaban madoran gari, ya ce, ita wannan sana'a ta dorin gida gada ya yi tun kaka da kakanni, kuma dukkan 'yan garin haka suka gaji wannan sana'a. Ya ce ""Ita wannan sana'a ta mu nada nasaba da kwarewar mutum kuma babu abin da yake gagararmu idan dai a kan karaya ne"". Sarkin dorin ya ce: ""Ko da karaya za ta kai shekara goma ko fin haka in dai har za a kawo mana marar lafiya to da izinin Allah za mu gyara shi ya kuma tashi."" Ya ce a rana a kan kawo masa masu karaya ya gyara kusan ashirin koma fin haka kuma daga garuruwa daban-daban. Muhammadu Auwalu, ya ce saboda iya aikinsa har dakin kwantar da marassa lafiya gare shi, inda idan aka kawo masa marar lafiya daga nesa to ya kan kwantar da shi na tsawon wasu lokuta, idan kuma a kusa ne to yana gama gyara karayar sai mutum ya tafi kawai abinsa. Ya ce saboda suna mu'amala da likitoci a aikinsu don idan likita ya kasa da karaya yakan tura musu su gyara, to wannan dalili ne ya sa a wasu lokutan su kan siyi kafso ko fanadol maganin rage radadi su bawa marar lafiya saboda ya samu saukin zugin da karayar ta ke. Sarkin dorin ya ce saboda kwarewarsu, har likitoci kance wai aikin madoran ya fi nasu. Ya ce ""Mu fa a tsarin aikinmu ba ma aikin da za a ce a je asibiti daga baya, sai dai daga asibitin a ce a zo wajenmu"". Muhammadu Auwalu ya ce "" A tsawon shekaru hamsin da na shafe ina dorin gida, ban taba yin dorin da aka kai mutum asibiti daga baya ba"". Ya ce a yanzu ya koyawa 'ya'yansa wannan sana'a ta dori saboda gadonsu ce kuma suma suna dora masu karaya da dama. 'Nazo wajen masu dori saboda likitoci sun gaza' A dakin kwantar da marasa lafiya na tarar da wani marar lafiya wanda yake a zaune kuma kafarsa ta dama a mike an nade ta cikin tsumma tana kuma tsakanin karafuna inda aka daidaita ta. Na tattauna da shi inda ya shaida mini cewa karaya ya samu a dalilin hadarin babur, da farko ya je asibiti ya shafe kwana sittin ba daya, a nan ne aka gyara masa karaya biyu, gwiwar ce taki dadi. Ya ce ""Da na ga babu sauki ga kuma kashe kudi sai na nemi sallama daga asibiti aka kuma sallame ni, ko da na koma gida jiki yaki dadi sai aka turo ni Sabon garin Madora, kuma Alhamdulillahi ga shi har ina iya lankwasa gwiwata"". Ƙafar 'yata ta zagwanye To yayin da sarkin dori Muhammadu Auwalu ke tunkahon cewar aikinsu na kyau sai dai idan sumasi aka samu, to da alama an samu sumasin a kan wata da na je na ganta. Yarinyar da na ba wa suna Binta, sikila ce kuma marainiya wadda ta samu lalurar karaya a hannu, mahaifiyarta ce ke dawainiya da ita. Mahaifiyar yarinyar ta ce dorin gida ya janyo musu babban tashin hankali saboda yadda hannun Binta ya koma duk sai kashi ba fata. Ta ce ""Saboda rashin kudi na kai 'yata wajen masu dorin gida, amma ga shi yanzu duk fatar hannun ta zagwanye don ko daga hannunta bata yi"". Dakta Mahmud Muhammad likitan kashi ne a asibin koyarwa na gwamnatin tarayya da ke Birnin Kudu ya shaida mini cewa babu wani likitan kashi da ya kware a aikinsa da zai tura marar lafiya wajen masu dorin gida. Likitan ya ce harkar kashi ba abu ne da ake yinsa ba da ka ba -- misali da zarar mutum ya karye abu na farko da ake masa shi ne a dauki hoton wajen don sanin wacce irin karaya ce. Ya ce daukar hoton ne zai baka hasken irin aikin da zaka yi wa marar lafiya. Dakta Mahmud ya ce: ""A gaskiya muna fuskantar matsaloli daga marasa lafiyar da suka karye saboda kusan kaso 60 cikin wadanda suka karye a Jigawa dorin gida suke zuwa ana musu, daga baya idan an samu tangarda kuma sai su dawo asibiti bayan an gama jagwalgwala karayar"". Ya ce ""Wannan ba karamar matsala ba ce, saboda da tun farko asibitin suke zuwa da yawanci ba za a samu matsalar ba, amma sai abu ya baci sai a rarrafo a taho asibiti"". Sannan game da batun wai suna aiki tare da masu dorin gida kuwa, wannan ba gaskiya bane, domin in dai har likita ya san aikinsa ai ba sai ya nemi daukin kowa ba inji Dakta Mahmud. To ko me yasa mutane ke zabar dorin gida musamman wadanda suka fito daga karkara? Mutane musamman mazauna yankunan karkara babbar sana'ar da suka dogara da ita ita ce noma sai kuma kiwo. To idan tsautsayi ya gifta mutum ya karye abin da ke fara zuwa ran iyalansa shi ne a kai shi wajen masu dorin gida, ganin cewa idan aka je asibiti ana kashe makudan kudade kafin mutum ya warke. Amma kuma idan dorin gida ne, dan abin da za a kashen bai kai na asibitin ba. Za a iya cewa, kudaden da asibitocin kashi ke caja idan mutum ya karye suke hana yawancin wadanda suka karye zuwa asibiti don a duba lafiyarsu. Wannan dalili shi ne ya ba wa masu dorin gida musamman a yankunan karkara ko kuma a gari kamar Sabon garin madora damar cin karensu ba bu babbaka. A lokuta da dama dai wadanda aka yi wa dorin gida kan gamu da matsala wadda dole sai an koma asibiti. Kazalika a jiha kamar Jigawa wadda akwai masu karancin ilimin boko da dama, ba lallai su fahimci illar dorin gida ba, haka talauci ma na taka muhimmiyar rawa wajen kin kai wadanda suka karye asibiti, tun da ana ta ciki wake ta karaya. Wadannan dalilai na daga cikin abubuwan da ke sa ake yawan samum wadanda suka samu matsala bayan sun karye inda a dalilin dorin gida mutane da dama kam rasa hannu ko kafarsu. Me gwamnatin jihar ke yi don kawo karshen wannan matsala da dorin gida kan haifar? Kimanin shekaru goma ke nan da gwamnatin jihar Jigawa ta bullo da dokar yi wa masu dorin gargajiya garanbawul, ga kuma abubuwan da dokar ta kunsa: Abin tambayar anan shi ne shin ko wannan doka na aiki kuwa a jihar ta Jigawa ganin yadda masu dorin ke harkokinsu ba tare da kiyaye wasu ka'idoji ba. Dakta Kabir Ibrahim, shi ne shugaban hukumar lafiya a matakin farko na jihar Jigawa, ya ce yanzu kokarin da ake shi ne a shigo da masu dorin gida cikin harkokin asibiti don su ga yadda ake yi da inda ake samun matsaloli don su kiyaye. Ya ce, "" Akwai kuma horo ga masu dorin gargajiyar da suka yi kunnen kashi, horo na farko shi ne tarar naira dubu biyar tare da jan kunne, sannan akwai matakin da mutum zai kai a tsare shi misali idan yaki sabunta takardarsa ta shaidar ya cancanci ya yi dori wadda gwamnati ta bashi. Masana dai na ganin idan har za a samar da asibitocin kashi a kusa da al'umma kuma a kan farashin da zasu iya biya tare da wayar musu da kai, za a samu sauki samun matsala sakamakon dorin gida, haka da yanayin da Binta ke ciki ka iya zama tarihi." https://www.bbc.com/hausa/labarai-52803031 +health Yadda aka yi kuskuren sanar da mutuwar mutum alhali da ransa "Wani Ba'indiye mai shekara 74 wanda aka yi kuskuren sanar da ya mutu kuma aka ajiye shi ɗakin ajiye gawa a jihar Tamil Nadu, ya mutu bayan ceto rayuwarsa. A ranar Litinin aka sanar da cewa Mista Balasubramanyam ya mutu bayan kai shi asibiti. Ba a san me yake damunsa ba. An ajiye shi a wurin ajiye gawa har kwana ɗaya kafin zuwan masu karɓar gawa da suka gano cewa bai mutu ba jikinsa yana rawa. Nan take aka ɗauke shi zuwa wani asibiti amma kuma Allah Ya karɓi ransa a ranar juma'a Shugaban asibitin ta gwamnati a kudancin birnin Salem, Dr Balajinathan, ya ce lokacin da aka kwantar da mutumin ba ya cikin hayyacinsa kuma ya rasu ne sakamakon matsalar da ta shafi numfashi. Ya shaida wa sashen BBC na Tamil cewa ba a san adadin sa'o'in da Mista Balasubramanyam ya shafe a cikin na'urar ajiye gawa ba. Bayan sanar da ya mutu a wata asibiti mai zaman kansa, iyalansa sun ɗauki gawarsa zuwa gida. Sun kuma sanar da cewa za su binne shi ranar Talata. Kamfanin da ke kula da binne gawa ya shaida wa ƴan uwan mamacin cewa ""ya sanya hannu kan wata takarda kafin ya mutu."" Shugaban ƴan sandan yankin, Senthil Kumar ya ce iyalansa sun kasa bayar da takardar shaidar rasuwarsa. Ƴan sandan sun shigar da bayanai da ke ƙalubalantar iyalan kan laifin sakaci da rayuwar ɗan Adam. Mista Balasubramanyam yana da mata da ƴaƴansa mata biyu kuma yana zama tare da ɗan uwansa. Ba a san yadda har ya rayu ba a cikin wurin ajiye gawa duk da tsananin sanyin da ke cikin akwatin - Haka kuma an kaddamar da bincike kan asibitin mai zaman kanta inda aka fara sanar da cewa ya mutu. BBC ta yi ƙoƙarin tuntubar asibitin mai zaman kanta da kuma danginsa amma dukkaninsu ba su ce komi ba, kuma babu wani bayani daga likitan da ya sanar da cewa ya mutu." https://www.bbc.com/hausa/labarai-54567145 +health Coronavirus: Me ya sa cutar ta fi kashe bakaken fata a Amurka? "A wurin mafi yawan Amurkawa, bambancin launin fata da ake nuna wa mafi yawan mutanen da suka mutu na da alaka da bakin-cikin da suke ciki wanda bai zo musu da mamaki ba. Biranen da ke Chicago da News Orleans da Las Vegas da kuma jihohin Maryland da kuma South Carolina na cikin wadanda suka ba da rahoton bayanai da ke da alaka da wariyar launin fata, wadanda kuma galibin wadanda suka kamu da wannan cuta bakake ne. Wannan na iya kasancewa saboda rashin daidaiton da ake nunawa a Amurka na tsahon lokaci da muka saba da shi, sauran dalilan watakila irin abubuwan da ba a taba zato ba wadanda za a iya magancewa. Nan bayanan mutum uku ne da wannan rikici ya shafa ta hanyoyi daban-daban - labaransu sun bayyana dalilan da ya sa bakaken Amurkawa suka fi shiga hadarin cutar. ""Yana matukar cutar da al'ummarta"" ""Yar uwata Rhoda ita ce babba a cikin iyalan gidanmu. Ita ta fara zuwa kwaleji a gidanmu, ta samu digiri kuma ta ke koyarwa a makarantar gwamnati,"" inji Rabaran Marshall Hatch da ke Chicago. ""Irin matan nan ne masu faran-faran da mutane. Tana da kwakwalwa. Ba ta kai kanta inda ba ta je ba kuma tana da mutunci sosai."" Rabaran Marshall Hatch ya matukar shakuwa da 'yar uwar tasa, wadda yawanci ta ke masa kida a cocinsa. A ranar 4 ga watan Afrilu ne Rhoda Hatch mai shekara 73 ta mutu bayan kwashe kwana takwas tana amfani da na'urar nunfashi ta Ventilator. Kwana biyu gabanin nan, babban abokin Rabaran Marshall Hatch, Larry Harris shi ma ya mutu, yana da shekara 62. duka su biyun Covid-19 ce sanadiyyarsu. A takaice mutane hudu da ke da kusanci da shi duka sun mutu ta dalilinta, Abin da ya sa ya ce tana ruguza bakaken fata 'yan Amurka da ke makwabtaka da shi a West Garfiels Park in da yake zama. ""Mun yi kokarin samun kabarin da za a binne 'yar uwata a ranar Asabar, amma abin ya yi wuya sama da ko yaushe."" in ji Rabaran. ""Amma kusan duk mun yi hasashen cewa duk lokacin da annoba irin wannan ta zo, za ta fi shafar mutanen da suke cikin kangin tattalin arziki."" Kamar yadda kididdiga ta bayyana, yankin West Garfield Park da bakaken fata suka fi yawa na da bambancin shekara 16 na tsahon rayuwar mutane, kasa da na yankin Chicago inda fararen fata suka fi yawa da ke tazarar mil uku kawai. Bayanan da aka fitar sun nuna kashi 68 cikin 100 na wadanda coronavirus ta kashe bakaken fata, lokacin da su ne kashi 30 cikin 100 na adadin mutanen birnin. Mutanen da ke zaune a yankin Rabaran Marshall Hatch suna da wahalar samun inshorar lafiya kuma suna zaune ne a gidajen da ke da cunkoson jama'a in ka kwatanta da adadin 'yan kasar baki daya. Matasa bakaken fata sun ta wallafa cin mutuncin da jami'an tsaro ke mu su a manyan shaguna a kafafen sada zumunta, ko kuma su rika korarsu idan suka gansu da takunkumin baki da hanci. ""Ko bani da lafiya, ina zuwa aiki"" ""Cikin abokan kasuwanci wadanda suke zuwa wajenmu, ba za ka taba sanin wanda ke da wata matsala ba."" Clarionta Jones mai shekara 24 daga birnin News Orleans na tsoron kamuwa da wannan cutar, amma ba ta da wani zabi mai yawa kan hakan. Tana aiki a wani kantin zamani ne kuma tana cikin mutane masu muhimmanci a wurin. ""Ni kadai ce na ke samun kudi a gidanmu, duk da cewa ba abin da kowa ya yi tsammani ba ne, kawai aka bukaci mu ba da kudin haya na watan Afrilu. ""A maganar gaskiya, idan ba ni da lafiya nakan sha magani kawai na tafi aiki. Bana son rasa kudina, ina da yara biyu. Wannan ba zabi ba ne."" Clarionta ta shaida mani cewa manajansu na cewa kada su sake su sanya safar hannu ko kuma takunkumin fuska lokacin da suke ciniki da abokan huldarsu. Tana jin bai kamata ta yi jayayya ba saboda kar ta rasa aikinta. A kasashe da yawa na duniya muna ganin yadda ma'aikata masu muhimmanci da masu gudanar da ayyuka, ke fama da karancin albashi, a lokacin da wannan cuta ta Covid-19 ke kara yaduwa. A Amurka idan kace ""karancin albashi"" babu shakka kana nufin ""bakar fata"". Amma Clarionta ta fadi wani abun mamaki. ""Da farko na ji ana cewa coronavirus ba ta kama baki. Ina nufin hakan na nuna babu bakaken fata a China amma lokacin da ta fara yaduwa a nan sai na ga mutane daban-daban na kamuwa."" Wannan labaran karyar ba iya New Orleans suka tsaya ba sun yadu har zuwa wasu sauran sassan kasar. A tsakiyar watan Maris, mawakin jihar Atlanta Waka Flocka ya shiga kafar radiyo yana cewa ""coronavirus ba ta kama bakake. A fadi wanda ta kama. Ba ta taba su kwata-kwata."" A wani bincike da aka gudanar, masana kiwon lafiya sun ce akwai bukatar cike gibin da ake da shi game da ilimi kan cutar. ""Tsarin bambancin launin da ake da shi ya kamata a zarga"" A matsayin kwamishina a birnin da kimanin kashi 40 cikin dari na mazaunansa bakake ne, yada labaran karya abu ne da Dakta Jeanette Kowalik ke fama da shi a kullum a wajen aikinta a Milwaukee da ke Wisconsin. Amma sashen da ta ke aiki na ta kokarin fitar da sabbin dabarun dakile labaran karyar da ke cewa cutar ta fi alaka da matafiya 'yan kasashen ketare, Covid-19 ta tsayar da birnin da ta ke. A makon da ya gabata an samu kimanin mutum 80 da suka kamu a birnin, kuma kaso 70 cikin dari cikinsu bakake ne,"" Dakta Kowalik ta shaida mani. Ta bayyana abin da ta ke ganin shi ne dalilin da cutar ta fi kama bakake 'yan Amurka. ""Da yawa daga bakaken fata na da wata matsalar rashin lafiya da ke kisa, kamar su ciwon zuciya, ciwon siga, asma, kiba."" in ji Dakta Kowalik. Ta kuma yi magana kan wasu boyayyun hanyoyi da ake amfani da su wajen cutar da lafiyar bakaken Amurkawa, tana kafa hujja kan wasu bincike da ke nuna rayuwar mutum na raguwa kwatankwacin dadewar sinadarin Cortisol a jikinsa, wanda yake janyo tsufa da wuri, kuma hakan na da alaka ne da damuwar da mutum ke shiga saboda matsalar nuna wariya. ""Wadannan duka abubuwa ne da za su bayu zuwa banbancin launin fata, kuma wadannan manufofi ne da ake amfani da su a kasar na tsahon lokaci,"" Dakta Kowalik ta ce yadda ake cutar da bakaken Amurkawa da wadannan rikice-rikice da kuma wahalhalun da suke fuskanta wajen gwajin da coronavirus a unguwannin marasa galihu, yasa suna jin an ana nuna cewa basu da amfani. Wani karin rahoto daga Eva Artesona Abin da ya janyo duka wadannan abubuwan - tawagar BBC kan labaran karya Jita-jitar da ake ta yadawa kan hanyoyin kariyar halittar bakaken fata game da Covid-19, dake yawo a kafafen sada zumunta tun karshen watan Janairu. Labaran sun samo asali ne saboda rashin samun bullar coronavirus a Afrika a lokacin, da kuma warkewar da dan makarantar nan dan kasar Kamaru ya yi daga cutar cikin gaggawa a China. Kan kuskure an ta wallafe-wallafe a Facebook a tsakiyar watan Faburairu, da ke ikirarin wani dan shekara 21 ya warke daga cutar ""saboda kalar fatarsa"". Amma a zahirin gaskiya, babu wata shaida da ke nuna samun lafiyarsa na da alaka da launin fatarsa. Sai dai hakan na da alaka da wani ikirari da bashi da tabbas kuma aka rika yadawa a kafafaen sada zumunta a wasu daga cikin kasashen nahiyar Afrika, da suka hadar da Najeriya, Kenya, Uganda da kuma Zambia. Almarar kan kwayoyin kariya ta yi ta yawo a intanet a yankunan bakaken fata 'yan Amurka, inda aka rika barkwanci da su da kuma ba'a a intanet." https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-52268699 +health Lafiya Zinariya: Yadda ake kare kai da yara daga cutar kyandar biri Danna hoton da ke sama don sauraron shirin: A Najeriya yayin da aka samu bullar cutar kyandar biri, masana a fannin kiwon lafiya sun bayyana wasu hanyoyi na kaucewa kamuwa daga cutar, musamman a tsakanin kananan yara. Cutar wadda asalinta ana kamuwa da ita ne daga dabbobin daji, amma tana bazuwa a tsakanin mutane, kuma tafi tsanani a tsakanin yara. Sai dai kamar sauran cutar virus, ita cutar kyandar biri bata da magani. Wasu daga cikin hanyoyin kaucewa cutar sun hada da kaucewa mu'amala da dabbobin daji wadanda ke dauke da cutar. Haka kuma tsaftar jiki, musamman wanke hannu da killace wanda ya kamu da cutar su ma hanyoyi ne na kare kai da kuma kananan yara. Alamomin cutar sun hada da zazzabi mai zafi da mura da ciwon kai da gajiya da fesowar kuraje. Sannan akwai ciwon jiki da ciwon baya da kuma matukar gajiya. Ana iya daukar cutar ta hanyar duk wani ruwa dake fita daga jikin dabba mai dauke da kwayar cutar, ko mutumin da ya kamu da cutar ta kyandar biri. A cewar hukumar lafiya ta duniya, WHO cutar kala biyu ce ake da ita a duniya, kuma sun samo asali daga yammaci da tsakiyar Afrika. Ta tsakiyar Afrika ta fi muni, inda ake samun yiwuwar mutuwa kashi goma cikin dari na wadanda suka kamu da ita. Yayin da kuma ta yammacin Afrika kashi ya ne cikin dari. https://www.bbc.com/hausa/media-61520416 +health Bayanin Dr Nasiru Sani Gwarzo kan Cutar Lassa Bayanin Dr Nasiru Sani Gwarzo kan Cutar Lassa https://www.bbc.com/hausa/labarai-51214794 +health Yadda ake tsangwamar masu cutar da ke jirkita halitta a Najeriya Dysplasia wata cuta ce da ke shafar ƙwayoyin halittar mutum har ta jirkita su. Ƙwararru sun ce cutar ba ta da alaƙa da kansa amma ta kan sauya yanayin kamannin waɗanda ta shafa. Masu fama da wannan cuta suna da yawa a Najeriya, kuma suna kokawa kan irin wariya da tsangwama da suke fuskanta daga al'umma. Hakan na faruwa ne saboda ƙarancin wayar da kan mutane. Sai dai akwai wata cibiya da ke aiki don taimakon masu cutar da kuma ƙoƙarin wayar wa da mtane kai a kanta. A wannan bidiyon, BBC Hausa ta tattauna da mai fama da irin wannan cuta da ke zaune a Abuja, babban birnin ƙasar. https://www.bbc.com/hausa/articles/cv2p4036d54o +health Christian Eriksen: Abin da ke jawo bugawar zuciya "Dan wasan kwallon kasar Denmark Christian Eriksen ya shafe daren shi na uku a asibiti ana yi masa gwaje-gwaje, bayan wani ciwon bugun zuciya a lokacin gasar wasan kwallon kafa ta zakarun Turai ranar Asabar. Amma har yanzu likitoci ba su da tabbas kan ko me ya sa babu zato babu tsammani zuciyarsa ta tsaya - kuma gano dalilan da suka sa shi ne abu mafi muhimmanci a yanzu. ""Mai shekaru 29 na kokarin ceton rayuwarsa,'' Farfesa Sanjay Sharma, likitan zuciya kuma shugaban kwamitin al'amuran da suka shafi zuciya na kungiyar kwararru a harkar wasan kwallon kafa ya shaida wa BBC. ""Yanzu muna bukatar kokarin gano ainihin abin da ya faru."" Daya daga cikin abubuwan da suka fi haifar da ciwon bugun zuciya shi ne bugawar zuciyar da ba a cika samu ba, kamar yadda kungiyar kula da masu ciwon zuciya ta Birtaniya (BHF) ta bayyana. Sauran dalilan sun hada da cardiomyopathy - wata cuta da ke shafar tsokar zuciya da ke kuma shafar girman ta, wadda akan yi gado - da kuma acute myocarditis, ko kuma radadin tsokar zuciya. Yanzu haka za a gudanar da aikin daukar hotunan kwakwaf mai cike da sarkakiya na zuciyar Mista Eriksen don gano duk wani tabo - wani abu da bai cika faruwa ba a gwajin da aka saba yi wa zuciyar 'yan wasan kwallon kafa, a cewar Farfesa Sharma. Wadannan gwaje-gwaje wajibi ne a Birtaniya, ana yin su a ko wace shekara biyu daga shekaru 16 zuwa 25. Sukan duba duk wani abu da ba a yarda da shi ba na yadda zuciya take aiki da kuma yanayin tsarin ta - amma duk da wannan namijin kokari na likitoci, wadannan gwaje-gwaje ba su da tabbacin nasara dari bisa dari cewa za a iya gano wasu boyayyun matsaloli. ""Wadannan matsaloli ba su cika nunawa ba a lokacin shekarun matasa ko daga masu shekarar 16 zuwa 25,"" in ji Farfesa Sharma. ""Ba lallai su nuna ba har sai sun kai shekara 20 zuwa 30."" Wani lokaci samun wasu alamu na daban kan faru a lokacin da 'yan kwallon suke tsakiyar buga wasa, ko kuma za a iya danganta shi da wata rashin lafiya da ba su dade da yi ba wacce ta sa zuciyar ta galabaita. Idan aka gano matsaloli, wasu za a iya magancewa - amma wasu kan kasance babu waraka. Ciwon bugun zuciya na faruwa ne idan cikin lokaci kankane zuciya ta daina kai jini jikin dan adam, tare da hana kwakwalwa samun iskar oxygen lamarin da ke sa mutum ya fadi ya suma kana ya daina numfashi. Tana da bambanci da ciwon zuciya, wanda ke faruwa a lokacin da hanyoyin samun jini zuwa tsokar zuciya suka toshe, yawanci saboda daskarewar jini a daya daga cikin manyan jijiyoyin da ke kai jinin zuwa cikin zuciya. Ba Eriksen kadai ne dan wasan kwallon kafa da ya taba samun buguwar zuciya ba. A shekarar 2012, wani dan wasan kwallon kafar, Fabrice Muamba, ya yanke jiki ya fadi a filin wasan kuma zuciyarsa ta tsaya cik har na tsawon mintuna 78. Marc-Vivien Foe ya mutu a lokacin da yake tsakiyar buga wasa ga kasar Kamaru yana da shekara 28, kana tsohon mai tsaron gid na Ingila Ugo Ehiogu, wanda kuma kocin kungiyar wasan kwallaon kafa na Spurs ne, ya mutu a shekarar 2017 yana da shekara 44. ""Tsananin motsa jiki kan saka rayuwar 'yan wasan motsa jikin cikin hadari saboda suna galabaitar da zuciyoyinsu - kana hakan ka iya haifar da babbar matsala,"" in ji Dakta Zafar Iqbal, shugaban bangaren kula da lafiyar 'yan wasa na kungiyar kwallon kafar Crystal Palace. Ya kara da cewa: ""Amma wadannan abubuwa ne da ba su cika faruwa ba."" Bugun zuciya kan faru ga kowa a kuma ko wane lokaci - ba sai 'yan kwallo ba. A ko wane mako a Birtaniya, mutane 12 masu shekaru daga 12 zuwa kasa da 35 na mutuwa sakamakon bugun zuciya. Kana a Birtaniyar a ko wace shekara, ana samun aukuwar bugun zuciya 30,000 a wajen asibitoci - duka masu bukatar taimakon gaggawa na farfadowa, inda akan samu mutane 10 kacal da ke rayuwa. Zuciyoyin 'yan wasan kwallon kafa kan kasance da girma kana da yin aiki sosai fiye da na sauran mutane, wanda ke saka su zama mafi karanci cikin na masu hadarin kamuwa da sauran matsaloli na zuciya kamar na toshewar jijiyoyin da ke kai jini cikin zuciya, da galibi aka fi samu a tsakanin masu shan taba sigari ko masu cin abincin da babu kiwon lafiya. Amma idan aka kara wa zuciya wata matsala daga rashin shan ruwa, da zafi da kuma wasu cututtuka za su iya yin mummunan tasiri. Dakta Iqbal ya ce yana da matukar muhimmanci cewa a fara yi wa Mista Eriksen aikin farfado da numfashi ta hanyar bubbuga gefen kirjinsa wato (CPR) ba tare da bata lokaci ba, daga nan sai a bi hanyar amfani da na'urar defibrillator mai wayoyin lantarki, wajen farfado da numfashin da ake kira (automated external defibrillator), kuma wata hanya ce da ya kamata kowa ya san yadda ake yi. Yana so ya ga an kai irin wadannan wayoyi da ake amfani da wutar lantarki wajen zaburar da zuciyar ko wace makarantar sakandae. Ya ce: ""Bata lokaci na ko wane minti daya na rage damar samun rayuwa da kashi 10 bisa dari."" Aikin farfado da zuciyar na CPR ka iya ninka damar ceton rayuwar mutum a wasu lokuta. ""Ko wace dakika na da amfani idan mutum na fama da bugun zuciya - idan kowa ya san yadda ake yi za a iya ceton rayuka da dama,"" in ji Dakta Sonya Babu-Narayan, wata likitar zuciya kana daraktar cibiyar lura da masu ciwon zuciya ta Birtaniya. Akan ajiye na'urori masu dauke da wayoyin lantarkin a wuraren aiki da filayen jiragen sama da kuma cibiyoyin taruwar al'umma. Kowa zai iya amfani da su, kana kwararru sun jaddada cewa babu wata hanya da za a yi amfani da su kuma a yi kuskure. Na'urar za ta zaburar da zuciya ne kawai idan bukatar hakan ta taso, bayan kai tsaye ta nuna yanayin bugawar zuciyar." https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-57486784 +health Yaushe ma'aikatan lafiya za su daina shiga yajin aiki? "Yajin aikin ma'aikatan lafiya kamar ya zama ruwan dare a Najeriya, wanda ke tasiri sosai ga al'umma a asibitocin ƙasar. A ranar Litinin ɗaya daga cikin manyan kungiyoyin ma'aikatan lafiya a Najeriya ta fara yajin aiki na tsawon mako guda kan kuɗaɗen albashi da inganta yanayin aiki. Ƙungiyar da ta ƙunshi ma'aikatan jinya da masu binciken jini da masu bayar da magani na son gwamnati ne ta biya su kuɗaɗen da suke bi na albashi. Yajin aikin na zuwa duka kwana guda bayan ƙungiyar likitoci ta janye nata yajin aikin a makon da ya gabata, ita ma game da waɗannan buƙatun. Gwamnatin Najeriya ta bayyana yajin aikin da gamayyar ƙungiyar ma'aikatan lafiya ta Joint Health Sector Unions (JOHESU) ta fara ranar Litinin a matsayin ""karya doka"". Cikin wata sanarwa, Ministan Ƙwadago da samar da ayyuka Chris Ngige ya ce "" yajin aikin bai dace ba kuma ba abu ne da ya zama dole ba."" Me ya sa ma'aikatan lafiya ke yawan shiga yajin aiki? Ƙungiyar ma'aikatan kiwon lafiya na Najeriya ta ce yajin aikin da ta ke shiga na dole ne bayan sun bi duk hanyoyin da ya kamata amma babu biyan buƙata daga hukumomi. Sakataren ƙungiyar Kwamred Silas Adamu ya shaida wa BBC cewa sun shafe lokaci suna bin gwamnati don ta biya buƙatunsu amma sai ta nuna ba ta damu da buƙatun ba. Ya ce akwai tsarin albashi da aka sauya musamman da ya shafi ƙarin albashi na likitoci da kuma ma'aikatan lafiyar. Amma a cewarsa suna ganin gwamnati ta fi kula da buƙatun likitoci fiye da bukatun ma'aikatan lafiya. ""Muna son gwamnati ta yi amfani da yarjejeniyar 2010 da aka amince, inda aka amince a yi wa ma'aikatan lafiya ƙarin albashi kamar yadda aka yi wa likitoci a tsarin. ""Muna son a gyara namu albashin kamar yadda aka yi wa likitoci,"" in ji shi. Ya ƙara da cewa suna son kuma gwamnati ta biya su alawus dinsu da ta yi alkawali lokacin yaki da korona musamman alawus na hadarin aiki. Sakataren ƙungiyar ma'aikatan na lafiya ya ce kashi 10 kawai gwamnati ta biya ma'aikatan lafiya daga cikin kudin alawus ɗin saɓanin likitoci. Ma'aikatan kiwon lafiya sun taɓa shiga yajin aiki na tsawon mako shida a 2018 kan wasu buƙatun da suka ƙulla yarjejeniya da gwamnati waɗanda kuma ba a cika ba. ""Har yanzu gwamnati ba ta aiwatar da yarjejeniyar ba,"" in ji Kwamred Silas Ƙungiyar ma'aikatan na lafiya ta ce yajin aikin na tsawon mako ɗaya, na gargaɗi ne kafin ta tsunduma cikin yajin aikin sai baba ta gani. Kuma yajin aikin ya shafi ma'aikatan asibitocin gwamnatin Tarayya ne a yanzu. Ƙungiyar ma'aikatan lafiyar na Najeriya sun yi barazanar cewa idan har gwamnati ba ta diba buƙatunsu ba - za su zauna su yanke hukunci kuma akwai yiyuwar za su sake shiga yajin aikin kwanaki 15 kafin su tsunduma cikin yajin aikin sai baba ta gani. Gwamnatin Najeriya dai ta shawarci ƙungiyar ma'aikatan na Lafiya da ta sake tunani game da yajin aikin tana mai cewa - ""Ba ya kan ƙa'ida gara a fifita mahimmancin lafiyar mutane fiye da komai"". JOHESU ta ɗauki matakin ne bayan kwamitin gudanarwarta na ƙasa ya yi wata ganawa ranar Asabar, inda ta ce ta fara yajin aikin daga 12:00 na daren Lahadi bayan ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa'adin kwana 15 domin a biya mata buƙatunta amma ""babu abin da aka yi""." https://www.bbc.com/hausa/labarai-54152273 +health Tsafta: Shin kicin ɗinku ya fi banɗaki yawan ƙwayoyin cuta? "Kimanin mutane miliyan 2 da dubu ɗari 4 na kamuwa da cutar guba a abinci a kowace shekara a Burtaniya, a cewar Hukumar Kula da Ingancin Abinci. Yayin da gidajen abinci da kantunan sayi-ka-tafi ke da alhakin yawancin matsalar, sauran na tattare ne a dakunan abinci na cikin gida. Wasu ƙwayoyin cutar ku da kanku kuke sa su a abinci lokacin da kuke girki. Shin kuna wanke hannuwanku lokacin da kuka koma gida da kafin dafa abinci? Yaushe rabonku da tsabtace wayarku - musamman ma idan kuna amfani da ita wajen koyo ko yin girke-girke? Shin kun san ko mayanin goge kwanukanku na abinci yana da tsafta? Ƙwayar cutar Norovirus, wadda ke sa amai a lokacin hunturu, ita ce mafi yawan nau'in guba a abinci. To amma sauran ƙananan ƙwayoyi ma na bakteriya da bairus da ire-irensu su ma suna sa mu rashin lafiya. Ya iya kasancewa kuna da tarin tambayoyi a game da ƙwayoyin cuta, domin akwai ƙwayoyin bakteriya a kan katakon yanke-yankenku na girki (za mu yi magana kan wannan a gaba). To a nan za mu duba hanyoyi da dama da ƙwayoyin cuta ke shiga cikin bakinku, tare da taimakon likitar tsafta, Dr Lisa Ackerley. Yawanci cututtuka masu yaduwa suna bazuwa ne ta hanyar taɓawa. Tun da hannayenku suna ɗauke da ƙwayoyin cuta kusan 3,000 na nau'ikan sama da 150 (yawancinsu ba su da lahani) a lokaci guda, to ku yi tunanin yawan ƙwayoyin cutar da za ku iya shigarwa wajen dafa abincinku idan kuna girki ba tare da wanke hannunku ba. Daɗin daɗawa ma, ƙwayoyin cuta suna yaɗuwa daga baki da hancinku zuwa hannayenku. Wanke hannuwanku ta hanyar da ta dace yana taimakawa kawar da waɗannan cututtukan. Wanke hannu da ruwa kawai yana rage yawan ƙwayoyin cuta da kashi 23 cikin dari , amma wanke hannu da sabulu da ruwa na iya rage yawan zuwa kashi 8 cikin dari, a cewar wani bincike. Sai dai fa duk da haka ba wai kuna kashe ƙwayoyin cutar ba ne, kuna kawar da su ne kawai. Wannan ne ya sa dole ku riƙa tsaftace wurin wanke-wankenku! Dr Ackerley ta ce: ""Lokacin da kuka koma gida ku wanke hannayenku. Idan kuka je aiki ku rika wanke hannayenku. Ba ku san abin da kuka ɗauka a hanya ba. Wadannan muhimmin lokuta ne.""Wannan shi ne ya sa ko da ruwan sanyi ko na zafi kuka yi amfani wajen wanke hannuwan ba wani bambanci. Ɗaya daga cikin wayoyin hannu shida na dauke da kwayoyin cuta na kashi Wataƙila kuna tare da wayarku a ko'ina hatta a bandaki. Wani bincike da kungiyar wayar da kai kan amfanin wanke hannu ta Birtaniya (UK Global Handwashing Coalition) ta sa aka yi ya nuna cewa, a duk wayar hannu shida ana samun daya mai dauke da kwayoyin cuta na kashi. Kimanin kashi 57 cikin dari na 'yan Birtaniya suna amfani da wayoyinsu a bayan gida, in ji kamfanin YouGov da ke gudanar da bincike. Ba mamaki ashe da yawancin wayoyi ke dauke da tarin ƙwayoyin cuta na kashi. Ire -iren wadannan kwayoyin cuta na iya rayuwa a hannaye da kan abubuwa har tsawon sa'o'i, musamman idan jikin abin ko wurin na da zafi kuma ba ya fuskantar hasken rana kai tsaye, kamar wayar da ta yi zafi a aljihunka. Daga nan, wasu mutanen na iya ɗaukar ƙwayoyin cuta ko kuma su yada su ga wasu abubuwan kamar abinci ko hannun ƙofa ko hannun tukunya. ""Idan kuna amfani da wayarku sosai hannunku da datti, to ya kamata ku tabbatar kun goge ta kuma ku wanke hannuwan naku kafin ku fara dafa abinci,"" in ji Dr Ackerley. Ta kuma yi gargadi kan hadarin yada kwayoyin cuta na bakteriya daga abinci zuwa jikin wayar salula: ""Idan kun taba danyen nama, ku wanke hannayenku kafin ku taba wayarku."" Kashi 60 cikin ɗari na mayanin goge kwanuka na gurɓace da ƙwayoyin cuta na E. Coli Yayin da kashi 60 cikin ɗari na mayanin goge kwanuku ke gurbace da ƙwayar cutar e. coli, a cewar wani bincike da Kungiyar Masana Harkokin Tsafta ta Duniya, haka su ma sauran mayanai da ake amfani da su a ɗakin dafa abinci suna ɗauke da tarin ƙwayoyin cuta, to me za ku iya yi domin rage yaduwar ƙwayoyin cuta? ""Mutane da yawa suna amfani da mayanin goge kwanuka barkatai. A iya cewa wataƙila su ne mafiya ƙazanta a abubuwan da ke ɗakin dafa abinci. Kuna ɗibar ƙwayoyin cuta yayin da kuke goge kwanuka da sauran abubuwa akwai kuma lokacin da za ku sanya datti a kan wurare ko abubuwa,"" in ji Dr Ackerley. Ga wasu hanyoyi na tsaftace mayani: A riƙa amfani da mayani daban-daban wajen goge kwanuka da dabe da goge hannu da sauran wurare ko abubuwa. A riƙa wanke mayani da ruwa mai dumi da ya kai zafin sama da 60 ° C (mafi dacewa sama da 80 ° C). Idan na'urarku ta wanke ko tsaftce kwanuka ba ta amfani da ruwa to sai ku sanya mayanan a wani kwano da ruwa da garin sabulu ku tafasa. Famfunan banɗaki sun fi teburin wurin dafa abinci tsabta Wani bincike na 2011 ya gano cewa kashi 32 cikin ɗari na kantar ɗakin dafa abinci na ɗauke da ƙwayoyin cutar bakteriya cikin har da wadda ake samu a cikin kashi. A wanan bincike dai an gano cewa kashi 9 cikin ɗari ne kawai na wurin kunna fanfunan banɗaki ke dauke da kwayoyin cutar. Ƴan mitsi-mitsin halittu da ba a iya gani da ido za su iya rayuwa ne daga tsakanin ƴan sa'o'i zuwa kwanaki, abin dai ya dogara ne ga yanay8insu da kuma inda aka same su. To amma ya kamata a ce mu duka mun nemi maganin kashe ƙwayoyin cuta? A 2018, shirin BBC na Trust Me I'm a Doctor ya gano cewa wani dan tsinke mai auduga naɗe a jikinsa da aka ɗauko daga kan teburin ɗakin dafa abinci na wani gida, bayan sa'a ɗaya da goge teburin sosai, yana ɗauke da ƙwayoyin cuta na bakteriya. Kuma bayan sa'o'i 12 sai aka ga yawan ƙwayoyin cutar ya yi ƙaruwa ta ban mamaki. A wata maƙala da ya rubuta ta BBC, Dakta Michael Mosley ya yi bayanin cewa: ""Idan kuka yi amfani da maganin kashe ƙwayoyin cuta na bakteriya domin kariya daga garesu, zai iya kasancewa ka yi asarar lokaci da kuɗinka. Domin ba kawai za su sake girma su dawo ba kaɗai za su yi hakan ne ma cikin sauri, to amma yawancin irin waɗannan ƙwayoyin da ke zaune a gidajensu ba masu cutarwa ba ne, hasali wasu ma suna da amfani ga lafiyarmu.'' Duk duk da haka, Dakta Ackerley ya yi amanna cewa abu ne mai muhimmanci a yi amfani da maganin kashe ƙwayoyin cuta a tsaftace wuraren aikin a muhimman lokuta, kamar lokacin da aka sarrafa ɗanyen nama ko kifi. ""Dole ne ka yi amfani da maganin kashe ƙwayoyin cuta a wuraren da nama ko kifin ya taɓa domin kada kabar wa wanda zai zo daga baya ya yi amafani da ɗakin dafa abincin wata ƴar tsaraba.'' Akwai ƙwayoyin cuta a kan katakon yanke-yankenku na girki fiye da kan salgarku (ta tangaran). ""Yawanci ana samun ƙwayoyin cuta na bakteriya na kashi kusan ninki 200 fiye da yadda ake samu a kan salgar da ake zama (ta tangaran),"" Kamar yadda Dakta Chuck Gerba, farfesa a fannin nazarin ƴan mitsi-mitsin halittu (microbiology) a Jami'ar Arizona, ya gaya wa BBC. Ba wai lalle ba ne ana samunsu ta hanyar haɗuwa da kashi, sai dai ta ɗanyen nama. Idan za a wanke kayan ɗakin girki ne da aka sarrafa nama, ""na'urar wanke-wanken kwanaku ko tangaran ita ce ta fi amfani,"" in ji Dakta Ackerley. Idan ba ka da ita to akwai hanya biyu da za ka tsaftace katakon yanke-yankenka na ɗakin girki: da ruwan magani ko kuma gashi. Idan za ka wanke katakon yanke-yanken naka, sai ka sanya shi a wurin wanke-wanke ka zuwa mishi maganin kashe cutukan, sai ka bar shi zuwa wani ɗan lokaci kafin ka wanke shi. Haka kuma za ka iya zuba masa ruwan zafi a hankali domin ka kashe ƙwayoyin cutar na bakteriya. Idan ka goge katakonka ba tare da ka wanke shi da maganin kashe ƙwayoyin cuta ko ruwan zafi ba, to kana fuskantar haɗarin yaɗa ƙwayoyin cuta ga mayani ko burushinka. Ya fi dacewa ka ware wuƙa da katakon yanke-yankenka na sarrafa kifi da dama, wani kuma ka ware shi domin wasu abubuwan. Wajen wanke-wankenka na ɗakin girki yana damunka da wari? Zai iya kasancewa akwai miliyoyin ƙwayoyin cuta a bututun wurin, to amma ta hanya da kuma yadda suke shiga jikinka ne babban abin damuwa, in ji Dakta Ackerley. Yawanci mukan wanke hannuwanmu a wurin wanke-wanke na dakin abinci , to amma ta hakan za ka iya sanya datti a wurin in ji ta. Saboda haka duk abin da ka sa za ka wanke shi a wurin wadannan kwayoyin cuta za su iya kama shi. To hanyar kauce wa gurbata kayan abincinka ko kwanuka ko kofi da wadannan kwayoyin cuta, ita ce ka wanke su a gefe a famfo, maimakon ka zuba su a wannan wuri na wanke-wanke da ake tara ruwa ka wanke, in ji Dr Ackerley. Babban amfanin firji shi ne, ya jinkirta girman kwayoyin cuta tare da tsawaita lokacin da abinci zai kai bai lalace ba. To amma idan har aka ce kwayar cuta ta riga ta hau abincin kuma ta girma, matsala ta zo, domin ana gano cewa ita kanta kwayar cuta ana samunta a cikin firji sandiyar hakan, kuma ta rayu har tsawon makonni. Saboda haka akwai bukatar a rika tsaftace firji damaganin kashe kwayoyin cuta. Shin ya dace a ci abincin da ya fadi ko da dakika uku kawai ya yi a kasa? Idan abu ne da za a bare kamar tuffa ko lemo ko kuma za a dafa to wannan ba matsala. Amma idan ba irin wadannan ba ne, misali a ce wani kosai ko burodi ko nama ko kifi da makamantansu, to bai dace ba ko da kuwa dakika nawa suka yi a kasa ko da faduwarsu aka yi sauri aka dauke, saboda zai iya kasancewa ya rigaya ya gurbata da kwayoyin cuta. Hanyoyi uku na kariya daga kwayoyin cuta Ba sai an shafe duk tsawon lokaci ana ta kokarin tsaftce dakin dafawa ko hada abinci ba. Abin da kamata kawai shi ne; Muhimmin abu a nan shi ne a kiyaye da matakan tsafta, kamar wanke hannu yadda ya dace kuma a lokacin da ya kamata. Tsaftace wuraren da aka san an dora wani abu kamar danyen nama ko kifi ko wani abu da zai iya yada kwayoyin cuta, bayan an kammala aiki. A tanadi kayan goge-goge da tsafta, kamar a ware tsumma ko mayanin goge abubuwa daban-daba a dakin dafa abinci. Haka kuma yana da kyau a guji cin abincin da ya dade a kasa !" https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-58928456 +health Coronavirus ta kama mutum 92 cikin sa'o'i 24 a Kano Cutar korona tana ci gaba da mamaya a jihar Kano da ke arewacin Najeriya inda sabbin alkaluman da hukumomi suka fitar a daren Juma'a suka nuna cewa karin mutum 92 sun harbu da cutar cikin sa'a 24. Alkaluman da ma'aikatar lafiya ta Kano ta fitar sun ce yanzu adadin masu cutar korona a jihar ya kai 311. Sannan akwai karin mutum uku da suka mutu wanda ya kawo adadin mamata zuwa mutum 8, kuma har yanzu babu mutum ko guda da ya warke daga cutar. Jadawalin jihohin da cutar ta bulla da hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa a Najeriya, NCDC, ta fitar ya nuna Kano ce ta biyu a yawan masu fama da cutar bayan Legas mai mutum 1006. Kashi 71 cikin 100 na wadanda aka samu dauke da cutar sun fito ne daga jihohin Legas da Kano da kuma birnin Tarayya Abuja. Wadannan alkaluman da hukumar NCDC ta fitar a daren Juma'a na wadanda suka kamu da cutar na nuni da yadda annobar ke kara yaduwa a cikin gaggawa a jihar Kano. A baya-bayan nan an rinka samun mace-mace masu yawa tsakanin jama'ar jihar ta Kano, sai dai gwamnatin jihar ta ce babu alakar karuwar mace-macen da cutar korona. Amma wasu likitoci masu zaman kansu sun alakanta mace-macen da cutar ta korona. Yanayin da jihar Kano ta tsinci kanta na zuwa ne a daidai lokacin da likitoci ke bayyana fargabar watakila a samu koma-baya a yakin da ake yi da annobar korona a Najeriya saboda rashin kayan aiki. Likitocin dai su na kukan rashin kayan kariya, lamarin da suka ce yana jefa su cikin hadarin harbuwa da cutar korona. A farkon makon nan ne dai gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya yi zargin cewa an watsar da jiharsa a yakin da gwamnatin Tarayya ke yi da wannan anno Wannan dalilin ne ya sanya shugaban kasar ya sanar da dokar hana fita ta mako biyu da kuma tura wani ayarin manyan jami'an kiwon lafiya zuwa jihar domin gudanar da bincike da kuma dakile matsalolin da ke fuskata. Yanzu dai akwai mutane sama da dubu biyu da ke dauke da cutar korona a Najeriya, cikinsu 351 sun warke yayin da 68 suka rasa rayukansu. https://www.bbc.com/hausa/52496835 +health Lafiya Zinariya: Abubuwan da kuke buƙatar sani kan ciwon suga Ku latsa alamar lasifikar da ke sama don sauraron cikakken shirin wanda Habiba Adamu ta gabatar. Najeriya ba ta cikin kasashe goma na duniya da ke da masu fama da ciwon suga. Sai dai sauyin da ake samu na yadda mutane ke cin abinci yasa ana samun karuwar masu cutar a kasar. Inda matsalar ta fi yawa a biranen Kano da Lagos da suka fi yawan al'umma. Masana a fannin kiwon lafiya sun ce kauracewa abincin gargajiya zuwa wasu nau'oin abinci na turawa sun taimaka wajen karuwar masu ciwon suga a kasar. Hukumar lafiya ta duniya, WHO, ta ce mutane miliyan 422 ne ke fama da wannan cuta a fadin duniya. Haka kuma masu fama da wannan larura sun fi yawa ne a kasashe masu matsakaici da kuma karancin kudin shiga. WHO ta kara da cewa akalla mutane miliyan daya da dubu dari shida ne ke mutuwa duk shekara a sanadiyyar cutar. Lamarin da ya sa ciwon ya zama daya daga cikin manyan cututtukan da ke ajalin mutane a fadin duniya. Hukumar ta kuma bayyana cewa cutar nau'i biyu ce, akwai wadda jikin mutum baya iya fitar da wani sinadari da ake kira insulin ko kuma yana fitar da kalilan ne. Sannan kuma nau'i na biyu na ciwon suga, shi kuma sinadarin na insulin ba ya wani tasiri a jiki. Kuma wannan nau'i na biyu a cewar hukumar, shi ne wanda ya fi yawa a duniya, musamman a tsakanin manya. https://www.bbc.com/hausa/shirye-shirye-na-musamman-56696961 +health Rawar da kungiyoyi ke takawa wajen taimaka wa masu larurar amosanin jini A wannan makon, shirin Lafiya Zinariya ya duba rawar da kungiyoyi masu zaman kansu ske takawa wajen taimaka wa masu fama da larurar amosanin jini. https://www.bbc.com/hausa/labarai-55855996 +health Lafiya Zinariya: Halin da ma'aikatan lafiya ke ciki a annobar cutar korona Ku latsa lasifikar d ake sama don ssauraron cikakken shirin wanda Habiba Adamu ta gabatar. Wani bincike da aka wallafa a mujallar kiwon lafiya ta The Lancet ya gano cewa, ma'aikatan kiwon lafiya na fuskantar karin barazanar kamuwa da cutar Covid-19. Sai dai hukumomi a fadin duniya, sun tunkari wannan kalubale ta hanyar fara yi musu riga-kafin cutar. A ranar 2 ga watan Maris 2021 ne, Najeriya ta karbi alluran riga-kafin cutar kusan miliyan hudu. Kuma su ne kashi na farko daga cikin allurai miliyan 16 da ake sa ran kasar za ta samu a watanni masu zuwa. Kamar a wasu kasashe, ma'aikatan lafiya na sahun farko da hukumomin kasar suka ce za a fara yi wa allurar riga-kafin Covid-19. Hukumomi a Najeriya sun ce, daga watan Fabairu zuwa watan Agustan shekarar 2020, an samu ma'aikatan kiwon lafiya 800 da suka kamu da cutar korona a kasar. Sai dai wasu alkaluman da BBC ta samu sun nuna cewa, zuwa farkon watan Maris 2021, an samu a ƙalla likitoci 1,200 da suka kamu da cutar a kasar, yayin da 45 kuma suka rasa rayukansu. Wasu daga cikin kasashen Afrika da suka samu karbar alluran riga-kafin, sun hada da Ghana da Senegal da Rwanda da Kenya da kuma Ivory Coast. Yayin da Babban Bankin Duniya ya shaida wa kamfanin dillacin labarai na Reuters cewa ya shirin samar da kudade cikin gaggawa domin tallafawa kusan kasashe 30 a nahiyar ta Afrika domin samun alluran riga-kafin. https://www.bbc.com/hausa/shirye-shirye-na-musamman-56294220 +health Kun iya maganar kurame? Wata likita ta ce yana da kyau ku koya Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon: An ware ranar 3 ga watan Maris din kowace shekara a matsayin Ranar Kurame Ta Duniya, ranar da aka ware don fadakar da mutane yadda za su kaucewa abin da zai iya haifar da kurumta ko matasalar ji. A cikin wannan bidiyon, wata likita Dakta Ameera Aliyu Aminu ta ja hankalin mutane kan amfanin maganar kurame. https://www.bbc.com/hausa/media-56267115 +health 'Wasu mazan ba sa haihuwa ko da kuwa an ga matansu da ciki’ Ku latsa wannan alamar lasifikar domin sauraron shirin Lafiya Zinariya da Habiba Adamu: Wani bincike da hukumar ta gudanar kan yawan al'umma a shekarar 2004 ya nuna cewa, kimanin kashi 30 cikin dari na mata masu shekara 25 zuwa 49 ne, ke fama da matsalar rashin haihuwa bayan sun taba samun haihuwa sau daya, a kasashen da ke kudu da Sahara a nahiyar Afrika. Ko da yake hukumar ta ce duk da cewa a tsakanin ma'aurata kashi 50 cikin dari da matsalar rashin haihuwa ta shafa, an gano cewa matsalar daga wajen maza ta ke. To sai dai a al'adance an fi dora laifin ne a kan mata. Lamarin da kan janyo wa mata kyara da tsangwama da wariya daga abokan zama, dangi da kuma al'ummar da suke zaune a ciki. Sai dai a Najeriya daya daga cikin kasashen da wasu daga cikin mutanenta ke fuskantar wannan matsala, hukumomin 'yan sanda sun sha kai samame tare da cafke gwamman matan da aka ajiye a wasu wurare domin yi musu ciki daga bisani a sayar da jariransu. 'Yan sanda sun yi zargin cewa cikin masu sayen jariran har da wasu wadanda ke fuskantar matsalar rashin haihuwa, inda wasu ma a cewar hukumomi su kan zo sayen irin wadannan jarirai ne daga makwabtan kasashe. A bayyane take cewa wasu matan kan shiga wani hali saboda rashin haihuwa, lamarin da kan sa su bi wasu hanyoyin da ba su dace ba domin magance matsalar. Sashen Hausa na BBC ya duba yadda wannan matsala ta rashin haihuwa ta ke a likitance, domin fadakar da al'umma tare da nuna musu cewa akwai hanyoyi da masu wannan matsala za su iya bi a likitance don samun dacewa. https://www.bbc.com/hausa/labarai-50864312 +health Ana zuzuta Coronavirus don a sauke Trump – Shugaban Ma'aikatan White House "Fadar White House ta Amurka ya zargi 'yan jarida da sanya wa mutane fargaba a kan Coronavirus domin ba ta wa Shugaba Donald Trump suna. Mukaddashin shugaban ma'aikatan White House Mick Mulvaney ya ce: ""Mun dauki matakai na musamman a tsawon mako hudu zuwa biyar da suka wuce, amma me ya sa ba su yada ba? ""Me ke faruwa a mako hudu zuwa biyar da suka wuce? Neman tsigewa. Shi kafafen labarai suka fi son magana a kai,"" kamar yadda ya bayyana a jawabinsa a wurin wani taro ranar Juma'a. Mick Mulvaney ya ce kafafen yada labarai sun fi ba da muhimmanci ga labarin neman tsige Trump - wanda aka wanke shi daga zargin a watan Fabrairu, saboda tunanin hakan zai karya shugaban. Ya kara da cewa, ""Abin da ya sa suke bayar da muhimmanci a kai yanzu shi ne tunanin da suke yi cewa hakan zai kawo wa Shugaba Trump cikas.'' Don haka ya shawarci kamfanonin duniya da ke nuna damuwa saboda da Coronavirus da su bar sauraron kafafen yada labarai na sa'a 24. Ana hada rigakafin Coronavirus guda 20 - WHO Ya zuwa yanzu kwararru na aikin hada magungunan rigakafin Coronavirus guda 20 a fadin duniya. Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce ana sa ran samun sakamakon gwajin farko da aka yi na magungunan a 'yan makonni masu zuwa. Shugaban WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ne ya sanar da hakan ne yayin jawabin da WHO ta saba yi a kowace rana a kan bakuwar cutar." https://www.bbc.com/hausa/labarai-51678108 +health Za a bude sabon asibitin Coronavirus a China "China ta kammala gina wani babban asibiti cikin kwana biyar domin kula da masu dauke da kwayar cutar coronavirus. Ranar Litinin ne kasar za ta bude asibitin Huoshenshan mai fadin murabba'in mita 14,000 da ta gina bayan bullar bakuwar cutar. Hukumomin China sun ce asibitin Huoshenshan zai dauki gado 1,000. Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya WHO ta ayyana coronavirus a matsayin babbar annoba a duniya. Mutum 14,000 sun kamu da ita kuma ta kashe mutum 304, inji gwamantin China. Ana zargin wasu mutun 100 a kasa 22 na dauke da kwayar cutar. A ranar 24 ga watan Janairu ne China da tura manyan motoci da kayan aiki domin aikin gina asibitin. Adadin wadanda suka kamu da coronavirus a duniya ya haura na annobar cutar Sars wadda kasa da mutum 30 suka kamu da ita a shekarar 2003. Mutum 8,000 ne suka kamu da kwayar cutar Sars a tsawon lokacin. An fara samun cutar coronavirus ne a yankin Wuhan na kasar China mai yawan al'umma 11,000,000. Gidan talabijin na gwamantin China ya ruwaito cewa sabon asibitin na Huoshenshan zai dauki gado 1,000 na kwantar da marasa lafiya. Gidan talabijin na CCTV ta rika yada wa duniya yadda aikin gina asibitin ke gudana kai tsaye domin jama'a su gani, kuma jama'a sun yi ta bibiyar tashar fiye da a kowane lokaci. Mutum miliyan arba'in ne suka kalli yadda ake aikin gina asibitin kai tsaye ta talabijin a fadin China, inji jaridar Global Times. Nuna ginin asibitocin kai tsaye ya sa jama'ar kasar kara ganin kimar motocin da ake aikin gine-gine da su. Jama'ar kasar sun rika yi wa motar kwaba siminti kirari da sunan 'Sarkin Siminti' da 'Babban Farin Zomo' da sauransu. An gina asibitin ne a wani bangare na asibitin Xiaotangshan da aka fara ginawa a birnin Beijin domin yakar cutar Sars a shekarar 2003. An gina asibitin na Xiaotangshan ne a cikin kwana bakwai, abin da ake gani a matsayin ginin asibiti mafi sauri a duniya a wancan lokacin. ""China na da tarihin kammala abubuwa cikin harzari, ciki har da manyan gine-gine kamar wannan asibiti,"" inji Yanzhong Huang, wani babban jami'in lafiya a cibiyar hulda da jama'ar kasashen waje. Asibitin Huoshenshan na dauke da wasu sassan gini da aka riga aka kera, kamar asibitin Xiaotangshan da ke Beijing din. Mista Huang ya ce za a kawo injiniyoyi daga fadin kasar domin ganin an kammala a aikin kan kari. ""Aikin injiniya shi ne abin da China ta fi kwarewa a kai, Kasar na da tarihin gina dogayen benaye cikin sauri. Kasashen yammaci na mamakin hakan, amma tana yiwuwa,'' inji shi." https://www.bbc.com/hausa/labarai-51348377 +health Mutum na biyu da ya warke daga cutar HIV a duniya "Wani mutum daga birnin London ya zama na biyu a duniya da ya warke daga cuta mai karya garkuwar jiki ta HIV, a cewar likitoci. Adam Castillejo dai ya warke daga kwayar cutar sama da kusan shekara uku bayan an daina yi masa magani. Ba wai ya warke daga cutar saboda shan magunguna ba amma ya warke ne sakamakon dashen kwayoyin halittar da aka yi masa sanadiyyar cutar daji da yake da ita, kamar yadda mujallar Lancet HIV ta rawaito. A shekarar 2011, Timothy Brown, mara lafiyar daga Berlin ne ya zamo mutum na farko da aka ruwaito ya warke daga cutar HIV, shekara uku da rabi bayan an yi masa irin wannan magani. Dashen kwayoyin halittar na hana kwayar cutar su karu a jikin mutum inda kwayoyin halittar da ke yakar HIV suke maye gurbin garkuwar jikin mara lafiyar. Adam Castillejo - wanda a yanzu yake shekara da 40 wanda kuma ya yanke shawarar ya sanar da duniya halin da yake ciki - ba shi da kwayar HIV a jininsa ko maniyyinsa ko bargonsa, a cewar likitocinsa. Shekara daya kenan bayan da likitocin suka sanar da cewa ya warke daga cutar kuma har yanzu ya samu waraka. Wanda ya jagoranci binciken Farfesa Ravindra Kumar Gupta daga Jami'ar Cambridge ya shaida wa BBC cewa: ""Wannan yana nufin maganin HIV da ake da tabbas a kai. ""Bincikenmu ya nuna cewa za a iya gwada amfani da nasarar da aka samu wajen dashen kwayoyin halittar a matsayin maganin HIV, wanda aka fara gwadawa kan mara lafiyar na Berlin shekaru tara da suka gabata."" Amma hakan ba zai zama magani ba ga miliyoyin mutanen da ke duniya wadanda kuma suke fama da HIV. An yi amfani da tsarin maganin domin warkar da cutar dajin da mara lafiyar yake da ita ba cutar HIV ba. Kuma magungunan warkar da HIV da ake da su yanzu suna da tasiri, ma'ana mutanen da ke dauke da kwayar cutar za su iya samun lafiya da tsawon rai. Farfesa Gupta ya ce: ""Abu ne mai mahimmanci a gane cewa irin wannan maganin yana da hadari sosai kuma ana amfani da shi ne a matsayin zabi na karshe ga masu dauke da HIV da kuma wanda yake da cutar daji. Amma hakan na iya sa wa mara lafiya fatan samun waraka a gaba ta hanyar yin dashen kwayoyin halittar. Yaya abin ya ke aiki? CCR5 ne sinadarin da HIV-1 (wato nau'in kwayar cutar HIV mai karya garkuwar jiki da ya fi yaduwa a duniya) ya fi samun hanyar shiga kwayoyin halitta ta hanyarsa. Sai dai wasu mutane kalilan da ke turje wa kwayar cutar HIV suna da kwafe biyu na sinadarin CCR5 wanda ya rikida. Hakan na nufin kwayar cutar ba za a iya kutsawa cikin kwayoyin halittar da bisa al'ada takan mamaye. Masu bincike sun ce zai yiwu a yi amfani da dabarar dashen kwayoyin halitta na gene don sauya sinadarin CCR5 a jikin mutanen da ke dauke da kwayar cutar HIV. Da wannan sinadarin ne dai masanin kimiyya na China wanda ke gidan yari, He Jiankul, ya yi amfani lokacin da ya samar da jarirai na farko da aka sauyawa kwayoyin halitta na gene. Gwaje-gwajen sun bayyana cewa kwayoyin halittar sun maye kashi 99 cikin 100 na garkuwar jikin Mr Castillejo. Amma har yanzu akwai burbushin kwayar cutar a jikinsa kamar yadda abin yake ga Mr Brown. Kuma ba za a iya cewa akwai tabbacin cutar HIV din ba za ta dawo jikinsa ba. Mr Castillejo ya fada wa Jaridar New York Times cewa: ""Ina son zama jakadan fatan alkahiri. Ba na son mutane su yi tunanin, 'Daman kai aka zaba.' ""A a, kawai ya faru ne. ""Ina wajen, watakila a daidai lokacin, da abin ya faru."" Farfesa Sharon Lewin daga Jami'ar Melbourne, Australiya ya ce: ""La'akari da yawan kwayoyin halittar da kuma rashin kwayar cutar, abin tambayar shi ne, shin mara lafiyar dan London ya samu waraka? ""Karin bayanin da aka fitar ya kara karfafa gwiwa amma a karshe, lokaci ne kadai zai tabbatar.""" https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-51832864 +politics Hotuna: 'Yan PDP na zanga-zangar adawa da hukuncin Kotun Koli kan zaben Imo "Wasu daga cikin masu zanga-zangar mabiya jam'iyyar PDP na dauke da tutoci da ke cewa ""Najeriya dunkulalliyar kasa ce, a yi abin da ya kamata, a agazawa Najeriya""." https://www.bbc.com/hausa/51174721 +politics Kwale-kwale ya kife da jami'an INEC a Kogi Wani kwale-kwale dauke da jami'an INEC da kuma kayan zabe ya kife a Odogwu na jihar Kogi sa'ilin da ya fito daga garin Akpanyo na karamar hukumar Ibaji. An tabbatar da mutuwar ma'aikacin zabe na wuicn-gadi guda daya a sanadiyyar hadarin. Kwamishinan hukumar zabe a jihar Kogi James Iorliam Apam ya ce ana sa ran isar gawar ma'aikacin na INEC zuwa garin Lokoja. Yanzu haka dai ana ci gaba da bayyana sakamakon zaben gwamna da aka gudanar a jihar na ranar Asabar. Masu sanya ido kan zabe sun nuna damuwa game da rikice-rikice da aka samu lokacin kada kuri'a, wanda ya yi sanadiyyar lalata kayan zabe da kuma satar akwatunan zabe. An samu rasa rayukan mutum 3 a kauyen Adankolo da ke kusa da Lokoja, bayan da 'yan bindiga suka bude wuta kan masu kada kuri'a. https://www.bbc.com/hausa/50450545 +politics Buhari ya shure masu nuna damuwar cewa ba a ganin sa a kamfe ɗin Tinubu "Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya ce a shirye yake ya taya ƴan takarar jam'iyyarsa ta APC yaƙin neman zaɓe da cikakken ƙarfi da zuciyarsa gabanin babban zaɓen ƙasar na 2023. Shugaban ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Mallam Garba Shehu ya fitar don musanta raɗe-raɗin da wasu ke yaɗawa cewa ba ya halartar gangamin da ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Ahmed Tinubu yake yi a jihohin ƙasar. Tun bayan yaƙin neman zaɓen da Tinubu ya ƙaddamar ne a Jos, babban birnin Filato cikin watan Nuwamba, ba a sake ganin ƙeyar Shugaba Buhari a sauran gangamin da APC ta yi ba. Ɗan takarar shugaba ƙasar ya ziyarci jihohi da dama a kamar Kaduna da Imo da Delta da Kuros Riba da kuma Neja, a yaƙin neman zaɓe da yake ci gaba da yi. Zuwa yanzu, ba a taɓa jin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar APC Bola Ahmed Tinubu ya yi ƙorafi a bainar jama'a game da rashin halartar Shugaba Buhari tarukansa na yaƙin neman zaɓe ba. Amma batun ya janyo ce-ce-ku-ce da gutsuri tsoma inda ɓangaren 'yan adawa da wasu ƴan ƙasar ke zargin ko Shugaba Buhari a yanzu ya raba gari da Tinubu. Idan za a iya tunawa a bikin ƙaddamar da manufofin Tinubu ne Shugaba Buhari ya bayyana cewa zai kasance kan gaba a yaƙin neman zaɓensa. Sai dai a sanarwar ta baya-bayan nan, Shugaba Buhari ya ce yin ƙarin haske kan dalilan da suka sa ba ya halartar tarukan ya zama wajibi domin kawo ƙarshen jita-jitar da ake ta yaɗawa. Bayanai na nuna cewa a lokacin da jam'iyyar ke gudanar da gangaminta a sassan ƙasar, Shugaba Buhari yana halartar taruka a ciki da wajen Najeriya ne. Kwanan ne ma Buhari ya dawo daga Amurka bayan ya halarci wani babban taro a Amurka wanda Shugaba Joe Biden ya gayyaci shugabannin Afirka. ""Da yake yi wa ƴan Najeriya da ke Washington jawabi a ziyarar da ya kai Amurka kwanan nan, Shugaba Buhari ya jaddada abin da ya sha faɗa cewa a shirye yake ya taya jam'iyyarsa kamfe domin ta yi nasara a babban zaɓen ƙasar na baɗi,"" in ji sanarwar. Sanarwar ta ƙara da cewa ""Yaƙin neman zaɓen da APC ke yi zuwa yanzu shi ne ya fi tara jama'a da karsashi inda ake yin gangami babu kama hannun yaro saɓanin na jam'iyyun adawa da suke faman faɗi-tashi,"" Shugaba Buhari dai ya bayyana kyakkyawan fatan cewa APC za ta lashe zaɓe a dukkan matakai cikin adalci da gaskiya a 2023." https://www.bbc.com/hausa/articles/cgrele8xdz7o +politics Mamman Daura: Abu 10 da ya shaida wa BBCHausa "Latsa alamar hoton da ke sama domin kallon hirar Mamman Daura da BBC Bayan shafe kusan shekara 30 ba tare da magana a kafofin watsa labarai ba, a karon farko Malam Mamman Daura mutumin da ake zargin yana juya akalar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya, ya fito fili ya musanta zarge-zargen da ake yi masa. 'Yan Najeriya da dama ne ba su taɓa jin murya ko kuma ganin hoton Malam Mamman Daura ba, wannan ba ya rasa nasaba da rashin bai wa 'yan jarida dama su tattauna da shi shekara da shekaru. Malam Mamman wanda tamkar ɗa ne ga Shugaba Buhari, ya miƙa ta'aziyya kan rasuwar manyan aminansa biyu wato Malam Abba Kyari da kuma Sama'ila Isa Funtua a ɗan wannan tsakani. A wani ɓangaren kuma, ya bayyana ra'ayinsa kan matsayin tattalin arziƙin Najeriya da kuma matsalar tsaro a ƙasar wadda ta ƙi ci ta ƙi cinyewa. Ya kuma fito fili ya yi bayani game da ra'ayinsa kan makomar shugabancin Najeriya a shekara ta 2023, inda ya ce mulkin karɓa-karba bai amshi ƙasar ba. Ga dai wasu daga cikin muhimman abubuwan da ya shaida wa BBC: A tattaunawar da BBC ta yi da Malam Mamman Daura, ya bayyana cewa ya ji jiki ƙwarai da rashin aminansa biyu, wato Malam Abba Kyari da kuma Sama'ila Isa Funtua. A cewar Malam Mamman Daura, dukkansu sun bai wa gwamnatin Najeriya gudunmawa matuƙa. A cikin hirar, ya kuma shaida yadda suka fara aminantaka da Abba Kyari da Sama'ila Isa har zuwa rasuwarsu. A cewar Malam Mamman Daura, daga shekarar 2016 zuwa yanzu, an farfaɗo da masana'antun samar da taki 31 a Najeriya, kuma duk ƙoƙarin Malam Abba Kyari ne. Malam Mamman, ya ce taki ya wadata yanzu a ƙasar. ""A da (buhu) yana ₦15,000, yanzu kuma yana ₦5,500,"" in ji shi. A cewarsa, babu dalilin da zai sa ya fito yana surutu a kafafen watsa labarai, ya ce ""lokacin da muka yi aikin jarida kowa yana jin mu, lokacin da na yi aikin gwamnati kowa ya san aikin da muka yi, to yanzu da muka gama sai na yi ta surutu? (To) na ce me""? Malam Mamman ya tambaya. Mamman Daura ya kuma fayyace dangantakarsa da Shugaba Buhari inda ya ce kamar uba yake a wurinsa. Ya kuma bayyana cewa tare suka taso da Shugaba Buhari tun suna yara ƙanana. A cewar Mamman Daura, yana zuwa wurin ɗan uwansa wato Shugaba Buhari domin su gaisa, kuma idan shugaban ya tambaye shi shawara yana ba shi, amma ba ya zaƙewa ya ce dole sai an yi yadda yake so. A cewarsa, ba a yi wa gwamnati haka. Ya ce zarge-zargen da ake yi masa cewa yana zaƙewa a wajen shugaban ƙasa ba gaskiya ba ne. A ra'ayin Malam Mamman Daura, kamata ya yi jam'iyyar da ke mulki a yanzu ta tsaya ta yi nazari domin duba mutumin da ya fi cancanta a tsakanin duk waɗanda ake ganin za su iya maye gurbin shugaban ƙasa. A cewarsa, ""za a iya dubawa ko daga arewa (ne) ko daga kudu su tsayar, abin da ya kamata su yi ke nan. Ya ce amma akwai fahimta da wasu 'yan Najeriya suke da ita duk da cewa ba a rubuce take ba ta mulkin karɓa-karɓa. A cewarsa, ""an yi karɓa-karɓa sau ɗaya, (an yi) sau biyu har sau uku, ya kamata ƙasar nan mu zama mun cuɗu, cewa wanda ya fi dacewa ya kamata, ba wanda ya zo daga wuri kaza ba"". Ganin cewa Malam Mamman Daura tsohon ma'aikacin gwamnati ne tun lokacin mulkin En'E, BBC ta tambaye shi ko akwai wani bambanci tsakanin aikin gwamnati a da, da kuma yanzu? A cewarsa akwai bambanci. A can baya idan ma'aikaci ya makara zuwa wurin aiki har shari'a za a iya yi masa, in ji shi. ""Amma a yanzu sai ka je ka ga rabin mutanen ministry ba sa nan, ko su tashi da wuri, ko ba su zo ba"". A matsayinsa na mutumin da ya karanci fannin tattalin arziƙi, Mamman Daura ya ce tun yana aiki da jaridar New Nigeria yake kira cewa kada a dogara da man fetur, domin wata rana mai zai zo ya zama ba shi ne abin dogara ba. Ya ce ga shi yanzu mai ya lalace, ""abin da wannan gwamnatin take yi shi ne daidai, a gyara noma da kiwo da (harkar) ma'adinai da masaƙu shi ne mafitarmu"", in ji shi. Malam Daura ya ce lokacin da gwamnatin Buhari ta zo akwai ƙananan hukumomi 18 na jihohin arewa maso gabashin Najeriya da ƙungiyar Boko Haram ta kafa tutocinta, inda suka kori sarakunan da ke yankin, ya ce a halin yanzu an yi maganin wannan kuma kusan an gama da su. ""Halin da ake ciki a yanzu sabuwar masifa ce, domin lokacin da aka kashe Shugaban Libiya Mu'ammar Gaddafi, sai gwamnatin ƙasar ta tarwatse, ya sayi ɗumbin makamai, duk sai aka yi ta wasoso, to shi ne duka (irin waɗannan) mutanen suke zuwa. Najeriya da Mali da Burkina Faso da Chad da Nijar duk a hargitse suke,"" in ji shi. ""Kuna zaune kawai a cikin ƙauye sai mutane su zo da babur su kashe na kashewa su ƙone na ƙonewa su ɓace."" A ra'ayin Malam Mamman Daura, mafita kan matsalar tsaro a Yammacin Afrika ita ce duk gwamnatocin ECOWAS, wato Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Ƙasashen Afirka ta Yamma su haɗu su yi babban shiri don maganin rashin tsaro." https://www.bbc.com/hausa/labarai-53613036 +politics 'Muna kokarin saye zuciyar Wike da sauran gwamnonin PDP' "Wasu makusanta ɗan takarar shugaban kasa na jam`iyyar APC a Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, sun tabbatar wa BBC cewa ya gana da Gwamnan Jihar Rivers Nyesom Wike da wasu gwamnonin PDP a shirin da yake yi na samun nasara a babban zaɓen 2023. Tawagar Gwamna Wike ta kunshi Gwamnan Oyo Seyi Makinde da na Binuwai, Samuel Ortom da na Abiya, Ikpeazu Okezie. A karshen mako ne rahotanni suka ce gwamnonin sun bar Najeriya daidai lokacin da wutar rikici da rashin haɗin kai ke sake bayyana a babbar jam’iyyar adawa ta PDP. Alhaji Ibrahim Masari na hannun daman Bola Tinubu ne, wanda a yanzu haka ke birnin Landan, ya faɗa wa BBC cewa ganawar ta mayar da hankali ne kan zaɓen 2023. A cewarsa, suna da kwarin gwiwar saye zuciyar wadannan gwamnoni da jawo hankalinsu domin yi wa APC aiki. Masari ya jaddada cewa akwai kyakkyawan zaton za su yi aiki tare da gwamnoni, musamman Wike, wajen lashe zaben APC. BBC ta tambayi Ibrahim Masari idan akwai yiwuwar Wike ya koma APC, inda ya amsa da cewa ba lallai sai mutum ya sauya jam’iyya zai iya taimaka wa wani domin nasarar zabe ba. “Wannan ba matsala ba ce, domin ba lallai sai ya koma APC ba, abin bukata shi ne Wike cikakken ɗan siyasa ne da ke da iko da gwamnoni da shiyyarsa da jihohi da dama”. Masari ya kuma ce Wike zai yi mu su amfani sosai a APC. A cewarsa: ""Ba ma fargaba domin abubuwan da muke gani ko yake bayyana a yanzu na tabbatar mana da cewa akwai gwanonin PDP da za su yi mana amfani a zaben 2023."" Alhaji Masari ya kara da cewa ""a siyasar zamani ba ka bukatar mutum ya dawo jam’iyyar ka kafin ya taimake ka"". APC dai ta nuna tana da kwarin gwiwar nasara da samun goyon-bayan wasu daga cikin jiga-jigai a PDP, sai dai da ya ke idan kana da kyau ka kara da wanka yanzu haka suna ci gaba da tuntubar sauron gwamnonin PDP domin nasara a zaɓen 2023, a cewar Masari. Kafin ganawar Tinubu da wasu gwamnonin na PDP, a ranar 8 ga watan Yuli, wasu gwamnonin APC uku, da suka hada da Kayode Fayemi na Ekiti da Babajide Sanwo-Olu na Legas da Rotimi Akeredolu na Ondo sun ziyarci Wike a kokarin shawo kan sa da neman sulhu. Kuma PDP ta kafa kwamitin sasanci domin daidaita Wike da ɗan takararsu na shugaban kasa, Atiku Abubakar. Tun lokacin da ɗan takarar shugaban kasa na PDP Atiku Abubakar ya zaɓi gwamnan Delta Ifeanyi Okowa maimakon gwamnan na Rivers a matsayin mataimakinsa ne aka fara samun takun-saƙa da Wike da wasu gwamnoni da ke goya masa baya. Wasu rahotanni dai sun ce gwamnan ya ƙi yarda ya gana da wasu manyan 'yan jam'iyyar PDP da ke da kusanci da Atiku don sasanta su. Su ma wasu muƙarraban Gwamna Wike da a halin yanzu ke nuna damuwa da halin da ake ciki a jam'iyyar, sun dage kan cewa dole ne Atiku ya ajiye Okowa ya dauki Wike idan yana son a sasanta." https://www.bbc.com/hausa/articles/c4nxn4x1x62o +politics 'Har yanzu APC ba ta cika jam'iyya ba' "Jam'iyya mai mulki a Najeriya ta APC ta kasance cikin rikici tun bayan da aka kammala manyan zabukan watan Fabarairun 2019 a kasar. Rashin jituwa tsakanin wasu gwamnoni da kuma shugabancin jam'iyyar na kasa karkashin Adams Oshiomole ya janyo rarrabuwar kai tsakanin jiga-jigan jam'iyyar. Wannan ta sa masharhanta irinsu Dakta Abubakar Umar Kari na Jami'ar Abuja ke ganin har yanzu ""APC ba ta zama cikakkiyar jam'iyya ba"". Ko a ranar Asabar rahotanni sun ambato kungiyar gwamnonin APC tana kiran kwamitin gudanarwar jam'iyyar na kasa da ya sauke Oshiomole daga mukaminsa, inda suka goyi bayan hukuncin wata kotu a Abuja. A ranar Larana ne wata kotu a Abuja ta yanke hukuncin korar Adams Oshiomole daga mukaminsa na shugaban jam'iyyar ta APC na kasa. Wannan ya biyo bayan karar da wasu suka shigar cewa tuni aka dakatar da Mista Oshiomhole daga jam'iyyar APC a jiharsa ta Edo, abin da alkalin ya dogara da shi kuma ke nan yayin bayar da hukuncin. Sai dai a daukaka karar da ya yi, wata kotu a Jihar Kano ta yi umarni da Oshiomhole ya ci gaba da zama a mukaminsa har sai bayan ta yi hukunci. ""Muna fada muna nanatawa cewa har yanzu APC ba ta zama cikakkiyar jam'iyya ba, gungu-gungu ne na mutane da ke da akidu daban-daban wadanda a baya ma fada suke yi da juna,"" in ji Dakta Abubakar Umar Kari, masanin kimiyyar siyasa a Jami'ar Abuja. Ya kara da cewa abin da kawai ya hada 'yan jam'iyyar APC shi ne ""wata dama da za su karbi mulki a shekarar 2015"". Jam'iyyar APC dai ta kafu ne bayan jam'iyyun AC da CPC da ANPP da wani bangare na APGA sun dunkule kafin a shiga babban zaben 2015, abin da ya sa suka kwace mulki daga hannun jam'iyyar PDP da dan takararta Shugaba Goodluck Jonathan. ""Idan irin wannan rikici ya ci gaba abubuwa da dama za su iya faruwa da ita (APC), wadansu ma na ganin za ta iya wargajewa,"" Kari ya fada. ""Ko da haka ba ta faru ba to ina ganin kwarjininta zai ragu kwarai da gaske."" Dakta Kari ya ce tabbas a siyasa ba a rasa yadda za a yi wurin gyara matsaloli, sai dai yana ganin cewa halin ko-in-kula na Shugaba Buhari a matsayinsa na jagora zai iya kawo tsaiko wurin saita jam'iyyar. ""Shugaba Muhammadu yana da hailin ko-in-kula, ba shi da niyyar a sasanta, ba ya wani katabus, kuma ba abin mamaki ba ne idan halin nasa ya ci gaba.""" https://www.bbc.com/hausa/labarai-51795732 +politics Jam'iyyar APC ta ware wa yankin Arewa muƙamin shugabancin jam'iyyar - El-Rufai "Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta ware wa yankin arewacin ƙasar muƙamin shugaban jam'iyyar na ƙasa yayin da ake tunkarar babban zaɓe na 2023. Gwamnan Kaduna Nasir Ahmed El-Rufai ya faɗa wa manema labarai, jim kaɗan bayan ganawarsu da Shugaba Muhammadu Buhari ranar Talata, cewa jam'iyyar ta amince ta rarraba muƙaman da babu kowa a kai a Kwamatin Ƙoli na jam'iyyar tsakanin Kudu da Arewa kafin babban taronta na ƙasa. Hakan na nufin muƙamin shugabancin wanda John Odigie-Oyegun da Adams Oshiomhole suka riƙe a baya, dukkansu 'yan Kudu, zai koma Arewa. ""Mun amince da wani tsari na karkasa muƙamai ga dukkan shiyyoyin siyasa. Shiyyoyin Arewa za su samu muƙaman da na Kudu suka riƙe a cikin shekara takwas da suka wuce, su ma (na Kudu) haka,"" a cewar Gwamna El-Rufai. Yayin taron, gwamnonin jam'iyyar ta APC sun amince da sabon lokacin da jam'iyyar ta zaɓa don gudanar da babban taronta na ƙasa duk da cewa an samu rabuwar kai tsakaninsu. Gwamna El-Rufai ya ce ba zai yiwu a tara gwamnoni har 22 ba ""kuma a ce ba a samu bambancin ra'ayi ba"". Ranar Litinin ne kwamatin riƙo na shugabancin jam'iyyar ya bayyana cewa ya fasa gudanar da babban taron a ranar 26 ga watan Fabarairu sannan ya mayar da shi 28 ga Maris. ""An samu bambancin ra'ayi tsakanin gwamnonin APC game da lokacin taron,"" in ji El-Rufai kamar yadda mai bai wa Shugaba Buhari shawara kan kafafen sada zumunta Tolu Ogunlesi ya ruwaito shi yana faɗa. Ya ƙara da cewa: ""Wannan kuma wai shi 'yan jarida ke kira gwamnoni marasa haɗin kai. Babu yadda za a yi a tara gwamnoni 22 kuma kowa ya amince da kowane irin ƙudiri. Za a iya samun bambanci amma idan aka kira shi rabuwar kai to an wuce gona da iri."" Baya ga sabuwar ranar gudanar da babban taron, APC ta shaida wa hukumar zaɓe ta INEC cewa za ta fara gudanar da taron na shiyya-shiyya tukunna daga ranar 6 ga watan Maris, inda za a zaɓi shugabanni a matakin shiyya. Jim kaɗan bayan ganawar da suka yi da Buhari, Gwamna El-Rufai ya ce gwamnonin sun amince da wani tsari ""na adalci"" ga kowane sashen siyasa na Najeriya. ""Bayan ganawarmu da shugaban ƙasa a yau (Talata), mun haɗu a kan abu ɗaya. Mun amince da wani tsari mai adalci da kuma ingantacciyar hanyar rarraba muƙamai ga dukkan sashen siyasa,"" a cewarsa. ""Cikin ikon Allah nan da 26 ga watan Maris za mu gudanar da babban taro na ƙasa. ""Babu wata tantama cewa kan gwamnonin APC a haɗe yake wajen yunƙurinmu na tabbatar da cewa 'Peoples Destruction Party' ba ta dawo kan mulki ba.""" https://www.bbc.com/hausa/labarai-60481949 +politics Rabi'u Kwankwaso: Gwamnatin Buhari ba ta damu da halin da 'yan Najeriya ke ciki ba "Tsohon gwamnan Kano kuma jigo a babbar jam'iyar hamayya ta PDP Dakta Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi kira ga gwamnatin kasar ta janye matakan da ta dauka a baya-bayan nan na kara farashin man fetur da kuma na wutar lantarki, da ya ce za su kara jefa jama'a cikin mawuyacin hali. Kwankwaso ya ce kamata ya yi gwamnatin ta toshe hanyoyin da kudade ke zurarewa a maimakon karin farashi. Tsohon gwamnan wanda yanzu haka ke ziyarar karfafa gwiwar magoya bayan jam'iyyar PDP a jihar Edo gabanin zaben gwamnan jihar da za a yi a makon gobe, ya shaida wa BBC cewa babu hujjar karin farashin a wannan lokaci. Ya ce ""Kasashe da yawa a duniya a yanzu shugabanninsu na tausaya musu inda suke fito musu da tsare-tsare ta yadda zasu samu saukin radadin wannan annoba ta korona, amma sai gashi a Najeriya a irin wannan yanayi aka shigo da duka na karin farashin mai da wutar lantarki da dai sauran abubuwa'. ''A gaskiya da wuya ka samu wani wanda zai goyi bayan wannan tsari'' in ji shi. Tsohon gwamnan na Kano ya ce baya goyon bayan wadannan matakai na gwamnati musamman a lokacin da mutane ke fama da matsaloli iri-iri. ""Duk wanda ke wannan kasa ya san da cewa wannan ba lokaci ne na dorawa mutane wannan nauyi ba, don haka ma'anar hakan shi ne sabuwar yunwa da sabuwar matsalar tsaro da sabon rashin aikin yi da dai matsaloli iri-iri da zasu biyo bayan wannan mataki na gwamnatin Najeriya"" a cewar Kwankwaso. Tsohon gwamnan ya ce idan har gwamnatin Buhari na sauraron jama'arta, to yakamata idan tayi abu ba dai-dai ba to ba abun kunya bane ta gyara don a samu ci gaba da zaman lafiya da kwanciyar hankali. "" Ita harkar gwamnati akwai maganar kudin shiga akwai kuma maganar kudin da ake kashewa, don haka abin da ake a irin wannan yanayi shine sai a duba aga wadanne kofofi na barna za a toshe, domin akwai hanyoyi da yawa da gwamnati zata iya kawo gyara a kan irin barnar da ake yi"". Ya ce ""Da irin wannan mataki gwamnati ta bi, da 'yan kasa sun yi murna, sannan sun kuma ji dadi domin kowa abin da yake so shi ne ya samu rayuwa mai kyau"". Kwankwaso ya ce, bisa la'akari da irin arzikin da Najeriya ke dashi, ba sai anje an dauki wasu matakai da za su dada hargitsa tsarin tattalin arzikin kasar ba." https://www.bbc.com/hausa/labarai-54112851 +politics Kotun koli ta soke zaben gwamnan Bayelsa na APC Kotun kolin Najeriya ta soke zaben gwamnan jihar Bayelsa da ke kudu maso kudancin kasar. Kotun ta soke zaben David Lyon, na jam'iyyar APC mai mulkin kasar ne kwana guda kafin ya sha rantsuwar kama aiki. Alkalan kotun biyar, wadanda Mai shari'a Mary Odili ta jagoranta wajen yanke hukuncin, sun ce sn soke zaben Mr Lyon ne saboda mataimakinsa Biobarakuma Degi-Eremienyo ya mika wa hukumar zaben kasar takardun bogi domin a bar shi ya tsaya takara a zaben ranar 16 ga watan Nuwambar da ya gabata. A watan Nuwambar 2019, hukumar zaben kasar INEC ta ayyana Lyon na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan ranar 16 ga watan Nuwamba, bayan ya samu kuri'u 352,552. Hakazalika hukumar zaben ta bayyana cewa Mista Douye Diri na jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 143,172. https://www.bbc.com/hausa/labarai-51493115 +politics Abin da ke faruwa a jihohin Igbo ya yi kama da yadda Boko Haram ta fara - Masana "A baya-bayan nan, an samu ƙaruwar munanan hare-hare musamman kan ƴan sanda a jihohin kudu maso gabashin Najeriya da suka haɗa da Anambra da Imo da Ebonyi da Enugu da Abia da ma wasu jihohin kudi maso kudu kamar Rivers da Akwa Ibom. Da fari, maharan sun fara ne da auka wa ɗaiɗaikun ƴan sanda musamman a inda suke aiki a shingayen duba motoci a kan tituna, su kashe su sannan su yi awon gaba da makamansu. Daga baya sai suka ƙara ƙaimi suna kai hari ofisoshin ƴan sandan inda nan ma su kashe jami'an ƴan sanda su sace makamai - lamarin ya kai ƙololuwa da waɗannan mahara suka kai hari hedikwatar ƴan sanda a jihar Imo. Sannan suka kai hari a wani gidan yari suka yi harbe-harbe kuma suka saki fursunoni sama da 1,700 duk a jihar Imo. Haka kuma, sun kai jerin hare-hare a ofisoshin hukumar zaɓe ta INEC a ɓangarori da dama na yankin. An sha alaƙanta waɗannan hare-hare da ƴan ƙungiyar IPOB masu rajin ɓallewa daga Najeriya amma kawo yanzu hukumomin Najeriya ba su tabbatar da hakan ba kuma ita ma ƙungiyar ba ta taɓa ɗaukar alhakin kai hare-haren ba. Masana harkokin tsaro a Najeriya na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu dangane da wannan lamari inda wasu ke ganin cewa da irin waɗannan hare-haren ƙungiyar Boko Haram ta fara ayyukanta a arewa maso gabashin Najeriya. Barista Audu Bulama Bukarti na Cibiyar Bincike ta Tony Blair da ke Burtaniya ya ce waɗannan hare-haren ba abu ne da ake yi ba da ka. ""Ana kai hare-haren nan ne bisa sani da kuma dabarar yadda za a yi a gurgunta yanayin tsaro a yankin sannan a lalata duk wani abu da gwamnati za ta iya amfani da shi wajen kama masu aikata laifin yadda za su ci karensu babu babbaka,"" a cewar Bukarti. Bukarti ya bayyana cewa burin maharan ya fara cika a yanzu tun da ƴan sanda a wasu ɓangarorin yankin ba sa iya zuwa aiki da rigarsu ta aiki sai dai su sa kayan gida, ya ce wannan na kamanceceniya da yadda aka fara yaƙin Boko Haram. ""A farkon yaƙin Boko Haram, sai da ta kai mutanen gari ba sa bari ƴan sanda su zo kusa da su, hatta lauya da kayansa ke kama da na ƴan sanda gudunsa ake yi a wancan lokacin saboda suna gudun ka da ya goga masu kashin kaji,"" in ji shi. Masanin ya ce idan wannan yanayi ya ci gaba a yadda ake, ƴan bindigar za su ci gaba da rusa gidajen yarin da ofisoshin ƴan sandan da suke ganin za a iya sa su idan an kama su sannan za su ci gaba da kashewa ko korar jami'an tsaron da za su kama su. Ya ce wannan zai ba su dama su ci gaba da cin karensu babu babbaka a yankin kudu maso gabashin Najeriya. Bulama Bukarti ya ce lamarin ya fara ta'zzara amma gwamnati ba ta yi latti ba. Ya ce yaƙin Boko Haram zai iya zama darasi ga gwamnatin Najeriya, ganin yadda ta yi yi sakwa-sakwa daga farko har lamarin ya lalace aka kai ga inda ake a yanzu. ""Kamata ya yi wannan shirin a yi masa tufka tun kafin wankin hula ya kai mu dare. ""Akwai buƙatar gwamnati ta matsa ƙaimi wajen amfani da ƙarfin soja da su ƴan sanda da jami'an leƙen asiri don tabbatar da cewa an yi bincike an gano inda suke ɓuya a kuma toshe hanyoyinsu na samun makamai da kuɗaɗe,"" a cewar Bukarti. Sannan ya ce lallai ne gwamnati ta bi ƙa'idojin da suka dace ta dawo da shugaban ƙungiyar ta IPOB Nnamdi Kanu wanda a halin yanzu ya ɓoye a ƙasar waje don a yi masa hukuncin da ya dace. ""Su kansu gwamnoni da shugabannin al'ummar yankin kudu maso gabas ya kamata su koyi darasi. A lokacin da ƙungiyar Boko Haram ta fara kashe jami'an tsaro da jami'an gwamnati mutanen gari ba a ɗauka barazana ba ce a gare su. ""Wannan babban kuskure ne don mun ga abin da ya faru a arewa maso gaban. ""Haka kuma, idan aka duba sanarwar da ƙungiyar IPOB ɗin ta fitar na cewa kowa ya zauna a gida ranar Litinin alama ce da ke nuna cewa za su fara kai hare-hare kan al'umma. ""Sanarwar ta nuna cewa za su illata duk wanda bai bi wannan umarnin ba,"" in ji Bukarti. Ya ce da wannan ne gwamnati za ta fara matsawa mutanen yankin cewa su fito a yi yaƙin da su, ta hanyar ba da bayanan sirri, idan suka ƙi jami'an tsaro su fara zargin cewa suna aiki ne tare da ƙungiyar su kama su ko su kashe su. Idan kuma suka yi, su ƴan ƙungiyar su gansu a matsayin maƙiya ne su fara kai masu hare-hare, a cewar Bukarti. Ya ce don haka dole ne shugabannin al'umma a yankin kudu maso gabas su farka su fahimci cewa abin da ke faruwa yanzu babbar barazana ce ga gaba ɗaya l'ummar yankin ba wai jami'an tsaro da jami'an gwamnati ba kawai. Haka kuma, ya ce idan ba a yi wa tufkar hanci ba za ta yi wa yankin illa gaba ɗaya. Bukarti ya ce ""Ko ba komai, matakan da ƙungiyar IPOB take ɗauka da wanda gwamnati ke ɗauka sun fara shafar tattalin arzikin yankin da taƙaita ƴancin mutane na yin yawo da tafiye-tafiye kuma haka abun zai ci gaba da rurucewa kuma idan ya kai matuƙa mutanen ne za su wahala fiye da kowa."" Barrister Bukarti ya ce abubuwan da ke faruwa a jihohin Ibo za su yi mummunan tasiri ga zaɓukan 2023 da zaɓen da za a gudanar a jihar Enugu a ƙarshen shekarar nan. Ya ce baya ga nan, rikicin na barazana ga dimokuraɗiyyar Najeriya. ""Mun ga yadda mutanen nan suka matsa ƙaimi wajen kai hare-haren kan ofisohin hukumar zaɓe. ""Idan lamarin ya ci gaba nan da ƙarshen wannan shekarar ba za a iya zaɓe a jihar Enugu ba kuma idan abun yaƙara lalacewa har shekara ta 2023 ba za a iya babban zaɓe a jihohin yankin ba,"" a cewarsa. Ya ce wannan zai iya gurgunta gaba ɗaya demuraɗiyyar Najeriya sannan zai iya haifar da sabon rikici domin ƴan yankin za su yi ƙorafin cewa ce an ware su ba a yi masu zaɓe ba a shekarar 2023. Bulama Bukarti ya ce dole gwamnati ta yi dukkan mai yiwuwa don ganin an yi gaggawar shawo kan matsalar. A ƙarshen makon da ya wuce ne wasu ƴan bindiga suka harbe tsohon mai bai wa tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan shawara, Ahmed Gulak a jihar Imo a hanyarsa ta zuwa filin jirgin sama. A ranar ne kuma rundunar ƴan sanda ta jihar Imo ta bayyana cewa ta kashe wasu mutum huɗu ƴan ƙungiyar IPOB da ta ce su ne suka kashe Gulak. Rundunar ta ce ta samu bayanan sirri ne dangane da mutanen. Washegari ranar Litinin, rahotanni suka bayyana cewa wasu ƴan bindiga da ba a san ko su waye ba suka kashe tsohon alƙalin babbar kotun jihar Enugu, Justice Stanley Nnaji. Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun fitar da marigayin daga motarsa da ƙarfin tsiya sannan suka harbe shi sau da yawa har ya mutu. Jami'an tsaro sun ce suna bincike kan kisan tsohon alƙalin." https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-57321508 +politics Yadda aka yi na ci zaben fitar da gwani ina hannun ‘yan bindiga – Sadiq Ango Abdullahi Sadiq Ango Abdullahi na daya daga cikin mutanen da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su daga jirgin fasinja na Abuja zuwa Kaduna a watan Maris na 2022. Kuma tun wancan lokacin Sadiq da sauran mata da yara suke hannun masu garkuwar har zuwa watan Satumba na shekarar ta 2022 bayan biyan kudaden fansa masu yawa. Sai dai wani abu da ya faranta wa Sadiq rai shi ne yadda yana tsare a hannun ‘yan bindigar ya lashe zaben cikin gida na jam’iyyar PDP a takarar dan majlisar tarayya na mazabar Sabon Gari a jihar Kaduna. https://www.bbc.com/hausa/articles/ce4g7p78rw9o +politics Mun ɗinke ɓarakar PDP a Kano - Shekarau "Yayin da ake ƙara kusantar lokacin babban zaɓe a Najeriya, jam'iyyun siyasa na ƙasar na ci gaba da aiki domin ɗinke ɓarakar da suke da ita gabanin zaɓen. A jihar Kano, jam’iyyar PDP ta ƙaddamar da sabon shugabancin riƙon ƙwarya domin magance mastsalolin da jam'iyyar ke fama da su a jihar a daidai lokacin da ake tunkarar babban zaben 2023. Jam'iyyar a mataki na kasa ta nada tsohon gwamnan jihar Kano Ibrahim Shekarau a matsayin wanda zai jagoranci sulhu tsakanin 'ya'yanta a jihar. Kuma cikin hirarsa da BBC Shekarau ya ce yanzu sun ɗinke duk wata baraka da ke damun jam'iyyarsu a baya. ""Ko wa ya jingine sabanin cikin gida ya yarda da cewa uwa daya uba daya muke, musammam abin da ya danganci sabanin da aka ratso a baya. ""Sai ko wanne dan jam'iyya ya ji a ransa wajibi ne ya yi aiki da hukuncin kotu da na uwar jam'iyya domin cimma nasara. ""An kafa mana shugaban cin riko domin su rike shugabanci zuwa bayan zabe, wanda bayan nan za a yi zabe somin samun jagororin da za su ci gaba da jan ragamar jam'iyyar zuwa shekaru hudu,"" in ji Shekarau. Ya ce nasarar da suka samu shi ne duka bangarorin da ba sa ga maciji da juna na jam'iyyar sun halarci zaman da suka yi na sulhu da kuma kaddamar da shugabancin riƙon ƙwaryar. Shekarau ya ce gabanin wannan taron ya zauna da duka 'yan takarar gwamnan da suke wannan rikici bangaren Muhammad Abacha da na Sadik Wali ya musu nasiha cikin mutane, ya kuma tunasar da su cewa dukkansu abu daya suke yi wa. Ya yi imanin cewa idan PDP ba ta yi nasara ba faduwar su ce baki daya, babu wanda zai ce ya yi nasara, a cewarsa tun tuni an gama da wannan baraka.\nWakilin BBC ya tambayi Shekarau game da rikicin shugabancin jam'iyyar na kasa da aka ce batun na gaban ko tun koli. Shekarau ya ce ""uwar jam'iyya ta kasa ba ta sanar da mu hukuncin kotun koli ba idan aka yi hukunci tunda akwai lauyoyin jam'iyya su ne za su karbo umarnin kotun a zauna a fassara umarnin kotun sai a sanar damu."" Jam'iyyar PDP a Kano na fuskantar rikici kala biyu ne, wadanda dukansu ke da alaka da maganar shugabancin jam'iyyar a jihar. Na farko shi ne rikicin takarar gwamna na jihar, wanda Muhammad Abacha da Sadiq Wali ke ciki, kowanne cikinsu na jin shi ne halastaccen dan takarar jam'iyyar biyo bayan rikicin zaben fitar da gwani da suka yi. Shugabancin jam'iyya bangaren Shehu Wada Sagagi ya ce ya gabatar da zaben fidda gwani na jam'iyyar kuma a matsayarsa Muhammed Abacha ne ya samu nasara. Bayan zuwa kotu da aka yi, kotu ta sake ayyana Sadiq Wali a matsayin wanda shi ne zai yi wa PDP takarar gwamna a Kanon. A bangaren shugabancin jam'iyya kuwa, rikici ne tsakanin Shehu Wada Sagagi da Manina Bako Lamido wanda a karshe ko tu rushe shugabancin jam'iyyar, shi ne a yanzu ta nada Ibrahim Shekarau a matsayin jagoran kungiyar kuma ta samar da kwamitin rikon kwarya zuwa bayan babban zabe a kasar." https://www.bbc.com/hausa/articles/cv2p012mm5xo +politics Yakubu Dogara: Dalilan da suka sa ni barin jam'iyyar PDP "Tsohon kakakin majalisar wakilan Najeriya ya ce bayar da kwangiloli ba bisa ka'ida ba da gwamnatin jiharsa ta Bauchi ke yi na cikin manyan dalilan da suka sanya shi dungurar da shahadar jam'iyyar PDP zuwa jam'iyyarsa ta asali APC. Ya kuma bayyana damuwa kan rashin biyan ma'aikata albashi a kan lokaci, da kuma rashin gudanar da zabukan kananan hukumomi cikin wata shida na farko, kamar yadda gwamna Bala Muhammad ya yi alkawarin zai yi.. ''Gwamnati ta ciyo bashi na Naira biliyan hudu, daga baya aka gano kudin a asusun wani kamfani mai zaman kansa, duk da cewa an ranto su ne da sunan jihar Bauchi, sannan ana bayar da kwangiloli ba bisa ka'ida ba, baya ga ninka kudin da ake yi yadda aka ga dama ba tare da bin ka'idojin doka ba."" Yakubu Dogara ya bayyana haka ne ta bakin mai magana da yawunsa. Turaki Hassan yayin zantawa da BBC, inda ya ce ba gaskiya ba ne zargin da wasu ke yi cewa ya sauya sheka ne saboda hankoron samun wata dama a APC. Dogara ya kuma ce wata matsalar da ya gani a jagorancin gwamnatin PDPn Bauchi ita ce rashin girmama manya, da sarakuna da gwamnan ke yi, saɓanin alkawuran da ya yi a baya na cewa zai rika daraja su. Wadannnan dalilai da kuma karin wasu ne suka sanya Yakubu Dogara yaga cewa ba zai iya ci gaba da zama a inuwa daya da gwamna Bala Muhammad ba, in ji Turaki Hassan, mai magana da yawun dogara. Sai dai gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad Kaura ya mayar da martani ga Mista Dogaran, ta bakin mai magana da yawunsa Malam Mukhtar Muhammad Gidado a wata hira da BBC, inda ya ce Dogara yana da dama da ra'ayin yin abin da yake so kamar yadda tsrain mulki ya ba shi. Amma ya yi watsi da zargin rashin biyan albashi da Dogaran ya ce Gwamna Bala ba ya yi. ""Duk da wannan runtsi da tattalin arziki ke fusknata sakamakon cutar korona gwamna ya yi kokarin ci gaba da biyan ma'aikata,'' in ji Malam Gidado. Shin Dogara neman mukami ya je yi a APC? Mai magana da yawun kakakin tsohon shugaban majalisar wakilan Najeriyar ya musanta zargin cewa Dogara, na da wani ra'ayi neman sake zama shugaban majalisar wakilan Najeriya ko ma yin takarar gwamna a zabe mai zuwa. ''Ka fada wa kowa, Dogara ba shi da tunanin yin takarar gwamnan Bauchi, inda yana son ya yi takara ai da ya yi a 2019'' In ji shi. Ya kuma kara da cewa sun yi iya kokari domin jawo hankalin gwamnan dangane da wadannan matsaloli da suke gani ana samu a Bauchi amma bai yi komai a kai ba. A cewarsa, manya da dama sun yi ta kokarin shiga tsakani don warware rashin jituwar da ake samu tsakanin yan siyasar, amma lamarin ya ci tura. Yadda ya sauya sheka zuwa APC Shugaban jam'iyyar APC na riko, kuma gwamnan Yobe Mai Mala Buni ne ya sanar da komawar Dogara APC, jim kadan bayan wata ganawa da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. Mai taimaka wa shugaban kasar kan harkokin watsa labarai Femi Adesina, ya wallafa hotunan yadda ganawar ta kasance a shafukansa na sada zumunta. Rabon da a ga shugaba Buhari da Yakubu Dogara tun lokacin da yake kan matsayin shugaban majalisar wakilan Najeriya kafin ya sauka. A iya cewa a yanzu Dogara ya yi dawayya ne zuwa tsohon gidan sa, domin tun lokacin da aka kafa APC yake cikin ta, kafin ya fice ya koma PDP a shekarar 2018. Yanzu haka dan majalisar wakilai ne da ke wakiltar mazabun Bogoro da Dass, da kuma afawa Balewa, dukkanin su a jihar Bauchi." https://www.bbc.com/hausa/53549266 +politics Subul-da-bakan Tinubu ya haifar da ce-ce-ku-ce a Najeriya "'Yan Najeriya sun shafe dare har zuwa wayewar garin wannan Larabar suna ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta dangane da wasu kalamai ko subul-da-baka da ɗan takarar shugabancin kasar na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya yi a wurin yaƙin neman zaɓensa. A jiya Talata ne Bola Tinubu ya kaddamar da gangamin yaƙin neman zaɓen nasa a Jos, babban birnin jihar Filato, wanda  Shugaba Muhammadu Buhari da sauran jiga-jigan jam'iyyar suka halarta. Sai dai a jawabinsa lokacin da ya hau dandamali ya yi wasu kalamai da wasu ke gani subul-da-baka ne. Irin wadannan kalamai su ne wasu 'yan Najeriya suka rinka watsawa a shafukan sada zumunta, wasu na amfani da kalaman zolaye, wasu kuma na cewa wannan katoɓara alamomin gazawa ce. Kusan abu biyu ne suka ja hankalin ma'abota shafukan sada zumunta da kuma mutanen da suka bibbiya yadda gangamin ya kasance a garin Jos. Akwai kuskure da ɗan takarar Bola Ahmed Tinubu ya yi wajen kiran sunan jam’iyyarsu ta APC, inda aka jiyo ɗan takarar na ambato harufa biyu na babbar jam'iyyar adawa wato PDP, inda ya ce ""PD..."" amma daga bisani ya gyara ya ce ""APC"". Wannan kuskure ko subul-da-baka da Tinubu ya yi ya ja hankali sosai, inda mutane suka yanko daidai wajen suna ta sake wallafawa da takfa muhawara a kai. Wasu ma sun haɗe sunan suna cewa ko dai Najeriya ta yi sabuwar jam'iyya ce ta ""PDAPC"". @SavvyRinu ya ce: Wace jam'iyya ce kuma PDAPC kuma? @elonchorh ya ce: Mutumin da ba zai iya tuna sunan jam'iyyarsa ba, zai iya tuna kudurinsa kuwa, balantana idan aka zo kan batun alkauran zabe? Wace jam'iyya ce kuma PDAPC? Wani abu na biyu kuma da ya ja hankali shi ne lokacin da dan takarar zai ambaci sunan shugaban kasa domin yaba masa. Bola Tinubu ya ce: ""Buhari Buhari Buhari Buhari Buhari shegege Buhari"". Mutane sun rinka zolaye da tafka muhawara musamman a Tuwita da Facebook suna cewa garin neman gyara za a rasa ido. Da alama wannan subul-da-bakan na Tinubu ya yi wa jam’iyyar PDP dadi, saboda tuni ta wallafa a shafukanta tare da bayyana cewa Tinubu ya amince cewa su ne za su iya ceto Najeriya. A wata sanarwa da ta fitar, babbar jam’iyyar ta adawa, ta ce Tinubu a zuciyarsa yana da yardar cewa PDP ce za ta iya ceto Najeriya ta hanyar magance duk wasu matsaloli da hada kan kasar. Jami’in yada labaran jam’iyyar ta kasa, Honorabul Debo Olagunagba, a cikin sanarwar yana mai cewa Tinubu ya yi musu addua a Jos, kuma wannan manuniyace shi yasa har aka kai ga ya furta abin da ke cikin zuciyarsa. PDP ta ce tana fatan ‘yan Najeriya za su fahimci hakan wajen zabi nagari domin ceto kasar daga kangin tarin matsalolin da ke neman durkusar da ita. Duk da cewa Tinubu ya yi wasu kura-kurai a wajen yaƙin nema zaɓensa, akwai kuma batutuwa masu muhimmanci da ya taɓo, tare da alkawarta shawo kansu da zaran ya kasance mai nasara a zaɓen 2023. Mista Bola Tinubu ya lissafo mafi yawan matsalolin da ke damun Najeriya, ciki har da karancin abubuwan more rayuwa da durkushewar masana'antu da rashin aikin yi a tsakanin matasa. Sannan ya yi alwashin magance su ta hanyar hada kwararru kuma gogaggu a cikin gwamnatinsa idan ya samu nasarar kafawa. Ya ce: ""Mu a jam’iyyar APC da yardar Allah mun yi wa 'yan Najeriya alkawarin yin shugabanci nagari a karakashin wannan yunkuri na farfadowa ko sabunta fatan alheri a zukatan al'umma, sakamakon goyon bayan da kuke ba mu. Za mu hada ayarin jarumai don ciyar da kasa gaba"". Kazalika, ɗan takarar shugaban kasar  ya caccaki abokan hamayyarsa musamman ma na jam'iyyun adawa da ke gaba-gaba, wani lokaci har da kiran suna yana gugar-zana, yana cewa ba su san hanya ba, ballantana su yi wa wani jagora. Haka zalika da dama cikin 'ya'yan jam'iyyar da suka yi jawai sun nuna suna da kwarin gwiwa APC za ta kai labari a zabe mai zuwa. Amma Shugaban jam'iyyar na kasa Sanata Abdullahi Adamu ya shawarci 'yan jam'iyyar da kada su shagala, su bari mulki ya ruɗe su, su yi wa jam'iyya aiki idan suna so su ga alheri: Ya ce: ""Kasancewa a kan karagar mulki ba ya sa a dawwama a kan mulki. Ba zai hana faduwa ba idan ba mu dage mun yi abin da ya kamata mu yi da zai ma samu karbuwa a zukatan masu kada kuri'a ba. Wannan ne ya sa nake jaddada cewa mu kasance masu himma. Mu hada kai ta yadda za mu gudu tare mu tsira tare,"" in ji Abdullahi Adamu." https://www.bbc.com/hausa/articles/clmgl9el3jlo +politics Tsugune ba ta kare ba kan nadin mukamai a majalisar Najeriya "Har yanzu batun nadin mukaman da sabon shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Ahmed Lawan ya yi, na ci gaba da tayar da kura a jam'iyyarsa ta APC mai mulkin kasar. Matasan jam'iyyar ne dai suka kekashe kasa suka ce ba su yarda da yawancin mutanen da ya nada a matsayin masu taimaka masa ba, suna masu cewa ya gaje su ne daga mutumin da ya gada wato Sanata Bukola Saraki. Hakan ne kuma ya sa Ahmed Lawan ya janye mukamin da ya bai wa Festus Adedayo - a matsayin mai magana da yawunsa. Ba a gama da wannan ba, kwatsam a ranar Lahadi sai ga mutumin da ya nada domin ya taimaka masa a fannin kafafen sada zumunta na zamani, Olu Onemola, ya ajiye mukamin, yana mai alakanta hakan da ce-ce-ku-cen da nadin ya haifar. Sai dai daya daga cikin jagororin matasan APC wadanda suke korafi kan wannan batu, Alwan Hassan, ya shaida wa BBC cewa sun gamsu da tattaunawar da suka yi da shugaban majalisar. ''Daman batun da muke yi shi ne, wadannan mutane wato Festus Adedayo da shi Olu Onemola sun yi kaurin suna wajen zagin gwamnatin APC, da kalaman batanci ga Shugaba Muhammadu Buhari da shi kan shi Ahmed Lawan,'' inji Alwan Hassan. Karin nadin mukamin mutane biyar da shugaban majalisar ya kara yi, ya sake fusata matasan jam'iyyar ta APC wadanda suke ganin ba su cancanta ba saboda zargin suna sukar gwamnati. Ya kara da cewa ''Shi kan sa Ahmed Lawan bai san da batancin da suke wallafawa a shafin Twitter ba kan shugaban kasa sai a yanzu da aka nuna masa... Majalisa ta 'yan Najeriya ce babu dan APC ko PDP ko wata jam'iyya, amma su wadannan suna zagin shugaban kasa ne''. Sai dai anasa bangaren, Festus Adedayo, wanda fitaccen dan jarida ne, ya wallafa wani sharhi a shafin Premium Times, inda ya ce ba shi ""ya nemi mukamin ba tun asali, kuma ba zai taba sauya matsayinsa kan yadda yake kallon al'amuran yau da kullum a Najeriya ba"". Za dai a zuba ido dan ganin yaya zaman majalisar da ci gaba da nade-naden mukaman za su kaya a makon nan, wanda wasu ke ganin ya kamata wadanda suka yi wa jam'iyya halacci su zamo a sahun gaba a mukaman. Ya yin da wasu kuma ke batun a duba cancanta ba tare da la'akkari da 'yan jam'iyya mai mulki ko 'yan hamayya ba. Tun da farko dai Sanata Lawan ya fara ne da kokarin kare kansa bayan da wasu kafafen yada labarai suka lakaba masa wani labari da ke cewa ya nemi jam'iyyar APC da Shugaba Buhari da su mika mulki ga yankin Arewa maso Yamma a shekara ta 2023. Wannan ta sa sai da ya fito ya karyata labarin, inda ya ce wani takwaransa ne, wato sakataren APC na jihar Adamawa, ya yi maganar ba shi ba. Wani jigo a jam'iyyar APC wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa BBC cewa ganin irin ja-in-jar da aka yi kan takararsa da yadda ta ja hankalin 'yan kasar, wani zai yi tunanin cewa Ahmed Lawan zai yi taka-tsantsan a duk irin abubuwan da zai yi. ""Amma abin mamaki sai ga shi ya fara wa'adin nasa da haifar da rudani. Muna fatan ba za a sake maimaita irin wannan ba,"" a cewarsa. Kawo yanzu dai ba a nada wanda ko wacce za ta maye gurbin Mista Adedayo ba, sai dai da alama 'yan APC za su zura ido domin ganin mutumin da za a nada a karo na biyu." https://www.bbc.com/hausa/48740701 +politics 'Akwai jituwa tsakanina da Tambuwal da Saraki kan takarar shugaban ƙasa' "Wasu da ke neman takarar shugabancin Najeriya a karkashin Jam`iyyar PDP daga arewacin Najeriyar sun ce suna ci gaba da tuntuɓar juna da nufin mara wa guda daga cikinsu baya. A makon da ya wuce ne Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal da tsohon shugaban Majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki, suka ziyarci Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad inda suka tattauna a kan hanyoyin daidatawa da juna. Jam`iyyar ta PDP dai ba ta ce komai ba kan yankin da za ta bai wa takarar shugaban kasa. Amma a yayin hira da BBC, Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad ya ce tuntubar da suke yi ta yi nisa, kuma idan da so samu ne, arewa ce ya kamata a kebe wa takarar shugaban kasa. Ya bayyana cewa tsakaninsa da Bukola Saraki da Aminu Waziri Tambuwal akwai jituwa sosai dangane da wannan lamari kuma tattaunawarsu ta yi nisa. ""Wannan takara ba muna yi ba ne saboda kanmu, muna yi ne saboda ƙasa da kuma arewa da muke wakilta da Najeriya, kada mu yi wani abin da zai kawo mana akasi shi ya sa muka ce ya kamata mu fara tattaunawa mu ga mun samu matsaya,"" in ji Gwamna Bala. Gwamnan na Jihar Bauchi ya ce a kwanakin baya sun yi bincike domin gano dalilin da ya sa suka faɗi zaɓe a 2019 inda ya ce sun gano abubuwa da yawa. Ya bayyana cewa daya daga cikin abubuwan da suka sa suka fadi zaɓe akwai rashin haɗin kai ganin cewa mutane da dama sun fito takara yawancinsu daga arewa. Gwamnan ya ce a yanzu wannan tattaunawa sun fara ne su uku kuma suna sa ran faɗaɗa ta, ta hanyar tattaunawa da sauran masu sha'awar tsayawa takarar. Ya kuma soki tsarin da ake kai na karɓa-karɓa a Jam'iyyar PDP inda ya ce ""Ba daidai ba ne a ce PDP ta shekara 16 tana riƙe da shugabancin ƙasa kuma arewa ta yi shekara biyu ne kacal a cikin 16 kuma a ce za a rufe arewa saboda Buhari yana shugaban ƙasa, Buhari a Jam'iyyar APC yake ba a PDP yake ba,"" in ji shi." https://www.bbc.com/hausa/labarai-60869710 +politics Hotunan bikin cika shekara 59 da samun 'yancin kan Najeriya Najeriya ta samu 'yancin kanta daga Turawan mulkin mallakar Birtaniya ranar 1 ga watan Oktoban 1960 wato shekara 59 da suka gabata. https://www.bbc.com/hausa/labarai-49893555 +politics Rasha ta amince a ziyarci tashar nukiliya ta Zaporizhzhia Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya ce za a bai wa jami’an Majalisar Dinkin Duniya damar ziyara tare da duba tashar nukiliya ta Zaporizhzhia da sojin Rashar suka kwace daga Ukraine. Fadar gwamnatin Rashar ta sanar da haka bayan wata wayar tarho da Mista Putin ya yi da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron. Wannan sanarwa ta Rasha da ke zaman wani abin albishir ta zo ne bayan da Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya gaya wa BBC cewa ya damu gaya a kan halin da ake ciki a wannan tasha ta nukiliya. A lokacin ya ce dole ne a kawo karshen ayyukan soji da ake yi a kusa da wannan tasha ta Zaporizhzhia, sannan ya bukaci Rasha ta bayar da dama ga jami’ai su je su duba yanayin yadda wurin yake. Tun a farkon watan Maris Rasha ta karbe iko da tashar, amma kuma ma’aikatan Ukraine ne har yanzu suke aiki a wurin, bisa umarnin Rashar. A sanarwar da Rashar ta fitar bayan tattaunawa ta waya tsakanin shugaba Vladimir na Rasha da Emmanuel Macron na Faransa, fadar gwamnatin Rashar, Kremlin ta ce, Mista Putin ya amince a bai wa masu bincike na Majalisar Dinkin Duniya dukkanin taimakon da suke bukata su je su duba wurin. Kremlin ta ce dukkanin shugabannin biyu sun lura da muhimmancin  tura kwararrun ma’aikatan hukumar nukiliya ta duniya, IAEA zuwa tashar domin su ga yanayi da abin da ke gudana a can a yanzu. Shugaban hukumar nukiliyar ta duniya ya yi maraba da kalaman na Shugaba Putin, inda ya ce shi da kansa zai jagoranci kai ziyara cibiyar. Rafael Grossi ya ce a wannan yanayi mai tsananin hadari, abu ne mai matukar muhimmanci a ce ba wani sabon mataki da za a dauka wanda zai iya jefa tsaro da zaman lafiyar daya daga cikin manyan tashoshin nukiliya na duniya cikin hadari Jami'an Ukraine sun ce Rasha ta mayar da tashar a matsayin sansanin soji, inda take tura kayan soji da makamai ta kuma jibge dakaru kusan 500 wadanda ke amfani da tashara matsayin wata garkuwa, su kai hari kan garuruwa da ke tsallaken Kogin Dnieper. A 'yan makonnin da suka gabata an yi ruwan makaman atilare a kusa da tashar, inda gwamnatocin Rasha da Ukraine ke zargin juna da kai harin. A ranar Alhamis a yayin wani taro tsakanin Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya da shugaba Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya soki Rasha kan kai hari da gangan kan tashar. Duk da aniyar da Rasha ta nuna ta bayar da damar kai ziyara tashar, jamia'n Rasahar kememe sun ki yarda da bukatar kasashe da hukumomin duniya ta dakatarwa da kuma janye duk wasu ayyuka na soji a wurin. Mukaddashin darektan yada labarai a ma'aikatar harkokin wajen Rasha Ivan Nechayev, ya ce yin hakan zai ma sa tashar ta kasance ba ta da kariya. Sannan ya musanta zargin kasarsa na jibge kayan soji a wuri. https://www.bbc.com/hausa/articles/cjr8jxwg780o +politics Me ke faruwa a Kashmir kuma me ya sa aka damu da yankin? "Jam'iyya mai mulki ta BJP a kasar Indiya tana kara azama wajen janye wa jihar Jammu da kuma yankin Kashmir alfarmar da suke da ita ta cin gashin kansu, inda suka ce gyara ne ga ""kuskuren tarihi"". Wakiliyar BBC Geeta Pandey a Delhi ta yi bayani kan abin da ke faruwa da kuma muhimmancinsa. Me yasa Kashmir ke jawo ce-ce-ku-ce? Kashmir yana yankin Himalaya ne, wanda kasashen Indiya da Pakistan suke cewa mallakinsu ne. A shekarun baya yankin babba ne, wanda ake kira Jammu da Kashmir. Amma ya hade da Indiya a shekarar 1947 lokacin da aka raba nahiyar a karshen mulkin mallakar Birtaniya. Daga baya ne kuma Indiya da Pakistan suka shiga yaki kan yankin, inda kowacce kasa ta samu iko da wani bangare na yankin bayan an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta. An yi ta samun rikici a bangaren da Indiya ke da iko na tsawon shekara 30 saboda fafutikar neman 'yancin kai daga wurin gwamnatin Indiya. A 'yan kwanakin da suka gabata na watan Agustan nan, an ga alamun tashin hankali a Kashmir. Dubban dakarun Indiya ne aka jibge a yankin sannan kuma aka soke aikin ibadar Hindu mai matukar muhammanci, aka kuma rufe makarantu, aka umarci masu yawon bude-ido da su fice, aka katse layin waya, aka kuma tsare wasu 'yan siyasa. Sai dai abin da aka fi tsokaci a kai shi ne, za a jingine sashe na 35A da ya bai wa mutanen yankin wasu alfarmomi na musamman. Kwatsam sai gwamnati ta bai wa jama'a mamaki, inda ta ce za ta daina aiki da ayar doka ta 370 wadda ta kunshi sashe na 35A. Wannan ayar doka ita ce kashin bayan alakar Indiya da yankin na Kashmir a tsawon shekara 70. Ayar dokar ta bai wa jihar damar cin gashin kanta wadanda suka hada da yin kundin tsarin mulkinta da tutarta da dokokinta. Sai dai harkokin kasashen waje da na tsaro da na sadarwa za su ci gaba da kasancewa karkashin ikon gwamnatin tarayya. A saboda haka ne, Jammu da Kashmir suke iya samar da dokokin da suka shafi takardar zama ta dindindin da mallakar gida da kuma hakkoki. Sannan kuma za ta iya haramta wa 'yan kasar Indiya mallakar gida ko kuma ma zama a yankin. Tanadin kundin tsarin mulkin Indiya ya tallafi alakar Indiya da Kashmir mai cike da rikici, wanda shi ne yaki guda daya da Musulmai ke da rinjaye da ya yarda ya kasance a Indiya. Me ya sa gwamnati ta dauki matakin? Firaministan Indiya Narendra Modi da kuma jam'iyyar Janata Party ta 'yan kishin kasa sun dade suna adawa da ayar dokar Article 370, kuma soke sashen daga kundin tsarin mulki yana cikin manufofinsu a zaben da ya gabata. Sun hakikance cewa ya kamata a soke sashen domin a shigo da Kashmir cikin Indiya kamar sauran sassan kasar. Bayan ta samu gagarumar nasara ne a zaben, gwamnatin Modi ba ta yi wata-wata ba wajen fara aiwatar da alkawarin da ta dauka. Masu sukar wannan yunkuri suna alakanta hakan da matsalolin tattalin arziki da Indiyar ke fuskanta. Akasaarin 'yan Kashmir suna ganin cewa yunkurin na rage wa al'ummar Musulmi yawa ne ta hanyar bai wa sauran Indiyawa damar sayen gidaje a yankin. Duk da cewa sanarwar da ministan harkokin cikin gida Amit Shah ya bayar a majalisa ta bai wa jama'a mamaki, zai dauki gwamnati tsawon lokaci kafin ta kammala yanke hukunci. Kazalika, wannan ya yi daidai da manufar Mista Modi da yake so ya nuna wa 'yan kasa cewa jam'iyyarsa ta BJP ba ta sassauci kan Pakistan da Kashmir. Kashmir za ta rasa kundin tsarin mulkinta, sai dai ta ci gaba da amfani da na Indiya kamar kowacce jiha a kasar. Duk wata doka ta Indiya za ta shafi 'yan Kashmir sannan kuma wasu da ba 'yan Kashmir din ba za su iya sayan gidaje a yankin. Gwamnati ta ce hakan zai kawo ci gaba ga yankin. ""Ina son jama'a su san irin barnar da Articles 370 da 35A suka yi mana,"" Mista Sha ya fada a majalisa. ""Saboda wadannan ayoyin dokar ne har yanzu ba a taba gudanar da cikakkiyar dimokuradiyya ba, cin hanci ya yawaita a garin, sannan kuma babu ci gaban da za a samu."" Sannan kuma gwamnati na son ta raba jihar zuwa jihohi guda biyu karkashin kulawar gwamnatin tarayya, yankin zai hada da Jiha daya mai rinjayen Musulmai dayar kuma mai rinjayen Hindu 'yan Jammu. Daya bangaren kuma na Ladakh 'yan addinin Buddha ne ke da rinjaye, wanda a tarihi yake kusa da Tibet. Kundin tsarin mulki ya tanadi cewa ba za a iya sauya ayar dokar Article 370 ba har sai da amincewar ""gwamnatin jiha."" Sai dai kuma babu wata tabbatacciyar gwamnati a Jammu da Kashmir cikin sama da shekara guda yanzu. Gwamnatin Indiya ta so maye gurbin kundin tsarin mulkin da na gwamnatin tarayya bayan an kayar da gwamnatin Mehbooba Mufti a zabe. Saboda haka, gwamnatin tarayya tana bukatar samun goyon bayan gwamnan yankin ne kawai, wanda dama shi ne ya kaddamar da kundin tsarin mulkinta a yankin. Gwamnatin ta ce tana da damar yin hakan a doka. Sai dai kan masana ya rabu. Wata kwararriya kan tsarin mulkin kasar Subhash Kashyap ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na ANI cewa ""matakin yana kan doka sannan kuma babu wata matsala a ciki"". A gefe guda kuma, wani masanin AG Noorani ya shaida wa sashen Hindi na BBC cewa ""ba ya kan doka kuma daidai yake da zamba"", wadda za a iya kalubalanta a gaban kotun koli. 'Jam'iyyun adawa ka iya kalubalantar matakin amma maganar Kashmir abu ne mai girma ga Indiyawa. Sai dai akasarinsu ba za su so su yi adawa da matakin ba domin gudun kar a kalle su a matsayin makiyan Indiya. Yanzu sai dai a bar sauran 'yan kasa su yanke hukuncin daukar matakin kalubalanatar shirin." https://www.bbc.com/hausa/labarai-49267477 +politics Rikicin APC: Ɓangaren Shekarau ya yi fatali da sulhun uwar jam'iyyar kan rikicin Kano "Rikicin shugabancin jam'iyyar APC a Kano na ƙara daukar sabon salo bayan ɓangaren da Sanata Ibrahim Shekarau ke jagoranta ya yi watsi da sanarwar uwar jam'iyya kan sulhunta rikicin 'ya'yanta na jihar. Matsayar tsagin Sanata Shekarau da ya zabi Alhaji Haruna Dan-Zago a matsayin shugaban jam'iyyar a jihar Kano na da alaƙa da bai wa gwamna Abdullahi Umar Ganduje jagorancin kwamitin da zai warware matsalar. A wata hira da BBC ta yi jim kadan bayan fitowar sanarwar jam'iyyar APC ta kasa, Sanata Ibrahim Shekarau ya ce sun yi watsi da wannan sanarwa kuma ba su amince da ita ba. ""Matsayinmu akan wannan sanarwa matakai ne kamar guda uku: a duk zaman da muka yi kamar sau biyu ko sau uku, wanda mai girma gwamna Ganduje yana wurin da mukarrabansa da wadanda mu ma muka je tare da su, karkashin jagorancin shugaban jam'iyyar gwamnan jihar Yobe Maimala Buni. An nemi kowanne ɓangare ya bayyana matsayarsa da abin da suke son a yi da shawarar waraka kan wannan matsala, dukka mun bayar da na mu. ""Shugaban jam'iyya ya ce za su koma su kalli bayanan da dukka muka yi domin fito da wata mnatsaya, da shawarar abin da ya dace a yi.'' Sanata Shekarau ya kara da cewa, sanarwar da jam'iyyar APC ta fitar ba ta yi magana a kan matsayar da aka cimma tsakanin ɓangarorin biyu ba, sannan jam'iyya ba ta fadi komai tsakanin abin da ɓangarorin biyu suka bukata ba. Abu na biyu kafin a kawo takardar a matsayin wanda ya ke jagorantar ɗaya bangaren, sai da aka kai wa gwamna Ganduje takardar wadda kamata ya yi ta zama tsakanin shugaban jam'iyyar, ko hedikwatar jam'iyya, da gwamna da kuma ni shugaban ɗayan barin jam'iyyar, in ji Shekarau. Sannan ya ci gaba da cewa kafin su samu takardar ta shiga duniya tana yawo a shafukan sada zumunta. ""Yaran gwamna na cewa an danƙawa gwamna jam'iyya ai ta koma hannunsa da maganganu makamantan haka. ""Abu na uku shi ne ya ya mutane biyu su na jayayya, sai kuma a ce ɗaya daga cikin wadanda ake jayayya da shi ne zai jagoranci sasantawar, alhalin shi ya jagoranci waccan sasantawar da ba a yi mana adalci ba, da muke ganin an zalunce mu, ta ya ya za a yi mana adalci a yanzu."" Kamata ya yi uwar jam'iyya ta wakilta wanda zai jagoranci wannan zama. ""Don haka ba mu amince da shi ba, mun yi fatali da shi, ba mu yadda ba, ba kuma za mu amince ba, a karshen takardarmu mun fadawa uwar jam'iyya mu masu biyayya ne, a shirye muke a sake zama domin sasantawa,'' in ji Shekarau. Shekarau ya ce wannan dalili ya sa suka rubuta takarda suka aikawa shugaban jam'iyya, za kuma su bai wa 'yan jarida da shafukan sada zumunta cewa abin da sukayi tsammani a yi ba shi aka yi ba. A daren Litinin ne uwar jam'iyyar ta fitar da sanarwa kan yadda za a shawo kan matsalarsu da magance ta. Ta kafa kwamitin mutum biyar domin warware rikicin shugabanci da ya ki ci ya ki cinyewa a jihar Kano da ke arewacin ƙasar tsakanin ɓangaren Sanata Ibrahim Shekarau da na gwamna Abdullahi Umar Ganduje. Jam'iyyar ta sanya gwamna Ganduje a matsayin shugaban kwamitin, sai kuma Sanata malam Ibrahim Shekarau a matsayin mataimakinsa. Dukkan mutanen biyu dai na ja-in-ja kan shugabancin jam'iayar APC a jihar ta Kano, lamarin da ya janyo takun saka da sanya jam'iyyar cikin halin kaka-ni-kayi a jihar. Sauran 'yan kwamitin akwai gwamnan jihar Zamfara Bello Muhammad Matawalle, da tsohon kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara, da Sanata Abba Ali, da kuma wakilin jam'iyyar da ke sa ran za a yi zama da shi. Sanarwar ta kuma ci gaba da cewa ana san kwamitin zai yi zama a jihar Kano cikin kwanaki bakwai tare da miƙawa jam'iyyar rahoto. Sannan ta na fatan bai wa gwamna Ganduje shugabancin kwamitin a matsayinsa na kamar shugaban jam'iyyar APC a jihar Kano zai nuna kyakkyawan shugabanci a zaman da za a yi. APC ta ce an dauki matakin ne saboda kotu ta gagara warware rikicin, alhalin dukkan bangarorin biyu ba za su kai labari ba a lokacin zabe dole sai da dan uwansa. Sanarwar ta kara da cewa, domin samun warware matsalar da samun jam'iyya guda ba kungiya-kungiya a jihar ta Kano, ya na da matukar muhimmanci gwamna Ganduje ya jagoranci kwamitin. Haka kuma, adalcin anan ba wai rarraba madafun iko na jam'iyyar kadai ba ne, har da yi wa sauran 'yan jam'iyyar adalci ta fuskar shugabanci. Kano dai babbar jiha ce da APC ta daɗe tana nanata tasirinta a siyasar Najeriya, abin da yasa APCn ke ƙara ƙoƙari wajen ganin ta hana wannan ɓaraka da ta kunno kai a jihar ƙara tsawo da faɗi. Idan aka gaggara maslaha tun da wuri babu mamaki wannan rikici ya kassara tasirin da APCn za ta iya yi nan gaba. Ko da yake 'ya'yan jami'iyyar na da kwarin-gwiwar sulhu zai tabbatu a tsakaninsu." https://www.bbc.com/hausa/labarai-60297712 +politics Atiku Abubakar: Mukamin shugaban kasa ba ya bukatar mai jan-kafa wajen zaben mataimakinsa "Ɗan takarar shugaban ƙasa na babbar jam'iyyar adawa ta Najeriya, PDP, Atiku Abubakar ya bayyana cewa ofishin shugaban kasa yana bukatar mutumin da ba shi da inda-inda. A cikin wata sanarwa da ya saka wa hannu, Atiku ya bayyana cewa matakin farko da duk wani ɗan takarar babban muƙami ya kamata ya ɗauka a mulkin dimokraɗiyya shi ne ya zaɓi mataimaki. Ana kallon wadannan kalamai na Atiku a matsayin shaguɓe ga takwarorinsa na wasu jam'iyyu, musamman jam'iyyar APC da NNPP da LP, da har yanzu ba su zabi mataimakansu na dindindin ba. ""Ofishi musamman irin na shugaban ƙasa na buƙatar mutumin da ba ya inda-inda wurin ɗaukar mataki,"" in ji Atiku. ""Shi ya sa a ƙasashe da suka samu ƙwarewa a dimokraɗiyya, batun ɗan takarar shugaban ƙasa ya zaɓi mataimaki da kuma yadda ya zaɓi mataimakin na bayar da dama a gane yadda ƴan takara suka shirya tunkarar aikin da ke gabansu."" A makon jiya ne Atiku Abubakar ya ɗauki Gwamnan Jihar Delta, Sanata Ifeanyi Okowa a matsayin mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin Jam'iyyar PDP. Har yanzu dan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyyar APC Ahmed Bola Tinubu bai ɗauki mataimaki na dindindin ba sai dai ya ɗauki Ibrahim Kabiru Masari, ɗan jihar Katsina, a matsayin mataimaki na riƙo. Haka shi ma ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin Jam'iyyar Labour Party wato Peter Obi bai ɗauki ɗan takara na dindindin ba amma ya ɗauki Doyin Okupe, a matsayin mataimaki na riƙo. Sun ɗauki matakin ɗaukar mataimaka na wucin-gadi ne domin kada su wuce wa'adin da hukumar zaɓe ta Najeriya ta saka na 17 ga watan Yuni inda ta ce kada wata jam'iyya ta kuskura ta wuce lokacin ba ta bayar da sunan ɗan takara ba. Sai dai jam'iyyun na da wata guda su sauya sunan wanda suka ɗauka a matsayin mataimakin shugaban ƙasa. Amma a martanin da Bola Tinubu ya mayar kan wannan batu na Atiku, ya ce ""abin takaici ne da damuwa a maimakon PDP ta mayar da hankali kan yadda za ta sasanta cikin gidanta bayan saɓa alƙawarin da ta yi na cikin gida kan batun karɓa-karɓa inda take ta neman rigima,"" kamar yadda Tunde Rahman, mai magana da yawunsa ya bayyana wa BBC. Ya kara da cewa: ""PDP da sauran ƴan takararta na yin shishigi ga harkokin cikin gida na APC inda suke ɗaukar nauyin yaɗa farfaganda kan batun Musulmi da Musulmi su yi takara da sauran ihuce-ihuce. Ya kuma buƙaci PDP da ta yi abin da ke gabanta da kuma sasanta ƴaƴanta da ba sa ga maciji da juna." https://www.bbc.com/hausa/labarai-61863665 +politics Atiku Abubakar: Ƴan Najeriya ne ke son na tsaya takara a 2023 Latsa hoton sama domin kallon bidiyon Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Alhaji Atiku Abukabar ya ce ƴan kasar ne suka buƙaci ya tsaya takarar shugaban ƙasa a shekarar 2023. Atiku ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai a Abuja ranar Talata kwana guda kafin ya ayyana takararsa a hukumance. https://www.bbc.com/hausa/media-60838489 +politics Ƴan adawa ke yaɗa jita-jitar ɓaraka tsakanin Buhari da Tinubu - Fadar Shugaban Ƙasa "Fadar shugaban ƙasar Najeriya ta ce babu wata ɓaraka da ke tsakanin Shugaba Muhammadu Buhari da babban na hannun damarsa a siyasance kuma jagoran jam'iyyar APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu. Fadar shugaban ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da mai taimaka wa Shugaba Buhari kan yada labarai Garba Shehu ya fitar a ranar Laraba. Sanarwar ta ce Shugaba Buhari da Asiwaju dukkansu sun duƙufa wajen gina jam'iyyar APC da samar da sauyi, kuma wannan alƙawari ne da suka ɗaukar wa ƴan Najeriya. A baya-bayan nan dai ana ta yaɗa rahotanni kan cewa ɓaraka ta kunno kai tsakanin mutanen biyu, sai dai Garba Shehu ya ce rahotannin ƙarya ne kuma ""aikin wasu masu haɗa tuggu ne a shafukan sada zumunta. ""Abin kunya ne a ce wasu ɓangarori na yaɗa labarai na dogara kan ƙirƙirar ce-ce ku-ce, da ke samar da gungun masu suka waɗanda ke aiki ta bayan fage wajen assasa irin labaran nan da suke zallar ƙarya ce. Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnati na sane da duk masu mugun fata da ƴan gaza gani da ke yaɗa labaran ƙanzon kurege ga mutane, kan dangantakar shugabanninta da kuma son ganin bayan jam'iyyar. ""Babu shakka shugaban ƙasa da jam'iyyarsa na mayar da hankali ne kan ci gaba da zaman lafiya da tsaro da sake fasalin tattalin arziki da kuma yaƙi da cin hanci a ƙasar, kuma babu abin da zai ɗauke musu hankali daga hakan. ""Ƙoƙarin ruɗa mutane ba zai yi nasara ba,"" a cewar Garba Shehu. Kazalika sanarwar ta ce Bola Tinubu na daga cikin jagororin siyasar da Shugaba Buhari yake matuƙar ganin ƙimarsu a ƙasar, saboda tsayuwarsa a kan manufofinsa komai tsanani. A cewar sanarwar, Tinubu na daga cikin jigon samar da jam'iyyar APC da ci gabanta sannan ƙawancen kullum ƙara ƙarfi yake yi. Ta kuma ce rashin ganin Tinubu akai-akai a Fadar Shugaban Ƙasa ba ya nufin cewa sun ɓata sai dai don cewa shi ɗin ba ya daga cikin mambobin majalisar zartarwar gwamnatin. ""Batun cewa ba a ganinsa a Villa kullum ba shi zai sa abotarsu da shugaban ƙasa ko da wannan gwamnatin ta yi rauni ba."" Tun a watan Fabrairun da ya gabata wani sabon rikici ya fara kunno kai a jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, sakamakon wasu kalamai da aka ji sun fito daga bakin babban jigon nata Bola Ahmed Tinubu, kan batun sabunta rijistar ƴaƴan jam'iyyar. Wataƙila jita-jitar da ake yaɗa wa a yanzun kan ɓaraka tsakanin shugabannin biyu ba za ta rasa nasaba da wannan batun ba. Shi dai Tinubu wanda ake kyautata zaton zai nemi tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, ya ce aikin sabunta rijistar ƴaƴan jam'iyyar a jihohin ƙasar baki ɗaya ba shi da wani tasiri. ""Sabunta rijistar da jam'iyyar ke yi tamkar a sanya ɗaya ne kana kuma a cire ɗaya, don haka ni ina ganin ba wata ƙaruwa ba ce'', a cewar Tinubu. Wannan kalamin ya sa wasu ƴaƴan jam'iyyar na cewa da walakin goro a miya, kuma alama ce da ke nuna cewa bai ji daɗin abin da ake yi ba, saboda a cewarsu, aikin rijistar zai iya rage masa ƙarfin mamayar da ya yi wa jam'iyyar, da kuma tasirin da yake da shi a cikinta. Sai dai wasu makusantan Bola Tinubun sun cewa ba a fahimce shi ba ne, kuma babu yadda sabuwar rijistar za ta shafi ƙarfin fada ajin da yake da shi a jam'iyyar." https://www.bbc.com/hausa/labarai-56517555 +politics APC za ta ci zaben 2023 duk da matsalar tsaro a Najeriya - Abdullahi Adamu "Shugaban Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ya ce suna da yaƙinin samun nasara a babban zaɓen 2023 duk da tarin ƙalubalen da ƙasar ke ciki musamman matsalar tsaro da matsin rayuwa. Sanata Abdullahi Adamu ya shaida wa BBC cewa irin waɗannan matsalolin, musamman na tsaro, ba kawai a Najeriya ake fuskantar su ba har ma da wasu ƙasashen a duniya. Ya bayyana cewa ""Ba shakka akwai taɓarɓarewar tattalin arziki a ƙasa, amma mai hankali ya san cewa taɓarɓarewar darajar naira ba wai mu muka haddasa ta a nan ba, batun tsaro kuma babu wata ƙasa da za ka ce tana zaman lafiya."" Sai dai ya ce duk da haka gwamnati na iya ƙoƙarinta na ganin an magance matsalolin. Najeriya dai ta shafe tsawon shekaru tana fama da ƙaruwar matsalolin tsaro a sassan ƙasar. A cewarsa, Jam'iyyar APC na aiki ne domin samun nasara a zaɓen da ke tafe sai dai ya ce akwai mutanen da ba ƴan jam'iyyarsu ba da suke musu zagon ƙasa kan wannan ƙudirin nasu. Sanata Abdullahi Adamu ya ce batun haɗa ƴan takarar shugaban ƙasa da mataimaki duka Musulmai abu ne da yake ci gaba da janyo ce-ce-ku-ce sai dai ya ce suna fatan ƙara ƙaimi wajen janyo ra'ayin ƴan ƙasar ga amincewa da wannan zaɓi. Ya ce zai yi wuya a iya shawo kan al'ummar ƙasar kan wannan haɗi saboda ""an samu wani hali ne a ƙasar da ko me ka ce, akwai waɗanda suka lashi takobin ba za su yarda ba kuma ba yadda ka iya da su"" amma tun da ana kan tsarin dimokraɗiyya ne, kowa yana da ikon ya riƙe ra'ayinsa. Ya bayyana cewa Ubangiji ne kaɗai ya san abin da ya sa mutane da dama suka yarda a zuciyarsu cewa haɗin Musulmi da Musulmi shi ne alheri a halin da ƙasar ke ciki. Shugaban na jam'iyyar APC ya ce abu ne mai wahala ka iya samun goyon bayan jama'a ɗari bisa ɗari kan wani ƙudiri a don haka abin da za su fi mayar da hankali a kai shi ne yadda za su gamsar da ƴan ƙasar kan tsarin takarar Musulmi da Musulmi. Sanata Abdullahi Adamu ya ce ko kaɗan Jam'iyyarsu ta APC ba za ta sake ta yi asarar takarar sanata a mazaɓar Yobe ta Arewa da Akwa Ibom ta arewa-maso-yamma ba, inda hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasar INEC ta ce APC ba ta da ƴan takara. Ya ce ba zai yi tsokaci kan batun ba saboda yana gaban kotu. A makon jiya ne INEC ta bayyana cewa APC ba ta da 'yan takarar Sanata a mazabun Yobe ta Arewa da Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma. A cewar INEC, APC ta dora sunayen Sanata Ahmad Lawan da Godswill Akpabio cikin jerin sunayen 'yan takara a shafin intanet na INEC sai dai hukumar zaben ta yanke cewa mutanen biyu ba su aka tsayar ba a zaben fitar da gwanin Jam'iyyar." https://www.bbc.com/hausa/articles/cekn59j3rk8o +politics Patricia Etteh: EFCC ta kama tsohuwar Shugabar Majalisar Wakilan Najeriya kan zargin rashawa "Hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arziki zagon-kasa a Najeriya, EFCC, ta kama tsohuwar Shugabar Majalisar Wakilan ƙasar, Ms Patricia Etteh. Jaridun ƙasar sun ruwaito cewa EFCC ta yi awon-gaba da Ms Etteh ne kan zargin almundahanar kuɗaɗe a ma'aikatar raya yankin Neja Delta wato NDDC da yawansu ya kai naira miliyan 287. Wata majiyar EFCC ta fada wa jaridar Punch cewa Ms Etteh ta karbi naira miliyan 130 daga kamfanin Phil Jin Project Limited da NDDC ta bai wa kwangilar naira miliyan 240 a 2011. A kan haka a yanzu EFCC ta neme ta ta yi bayanin shigar kudin asusunta amma ta gaza fadar komai a kai. ''Etteh ba darakta bace ko yar kwangila, saboda haka me ya kai wannan kudi asusunta. Akan haka muke bukatar ta yi bayani kuma kawo yanzu bata yi ba,"" in ji majiyar. An zabi Patricia Etteh a matsayin Shugabar Majalisar Wakilai a 2007, to amma ta yi murabus ne bayan 'yan watanni bisa zargin karkatar da wasu kuɗaɗe. 'Yan majalisa a lokacin sun yi barazanar tsige ta daga mukamin Shugabar Majalisar kafin ta yanke shawarar sauka da kanta. A wancan lokacin ana zarginta da ware wasu makudan kuɗaɗe don bada kwangilar gyaran gidan da aka tanadar wa kakakin majalisa. Ita ce mace ta farko a Najeriya da ta taba jagorantar majalisar a tarihi. Kamen nata na zuwa ne kwana kaɗan bayan da EFCC ta cafke Akanta Janar na ƙasar, Ahmed Idris, bisa zargin sama da fadi da Naira biliyan 80. EFCC ta ce ta kama shi ne bayan ya ki amsa gayyatar da ta yi masa don amsa tambayoyi. Wasu 'yan Najeriya sun rika tsokaci kan kama Akanta Janar din da zargin wawushe biliyoyin, la'akari da cewa yana rike da babbar kujera a gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da ke ikirarin yaƙi da cin hanci da rashawa." https://www.bbc.com/hausa/labarai-61489276 +politics Yaushe rikicin cikin gida zai ƙare a jam’iyyar APC? "Babbar jam'iyya mai mulki a Najeriya, APC ta sake tsunduma cikin wani rikicin shugabanci bayan nada Bulama Waziri a matsayin babban sakatarenta na kasa. Lamarin dai ya bar baya da kura inda wani bangare na 'ƴan jam'iyyar ya ce bai lamunci nadin ba, sai dai a yi zabe kamar yadda tsarin mulkin APC ya tanada. Tun bayan da tsohon babban sakataren jam'iyyar Mai Mala Buni ya bar kujerar shekarar da ta gabata lokacin da ya samu tikitin takarar gwamnan jiha, sai yanzu ne aka maye gurbinsa. Sanata Lawal Shu'aibu wanda shi ne mataimakin shugaban jam'iyyar APC shiyyar arewacin kasar ne dai ya fito ya soki nadin Waziri Bulama, inda ya caccaki shugabancin Adams Oshiomole. Me 'yan jam'iyyar APC ke cewagame da nadin Waziri Bulama? Tun bayan sanar da nadin Waziri Bulama a matsayin baban sakataren jam'iyyar na rikon kwarya a farko wannan mako, wasu 'yan jam'iyyar irin su Sanata Lawal Shu'aibu, ke cewa ""Nadin Waziri Bulama alamu ne na yadda APC ta fada halin rashin doka da oda."" A wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba mai taken ""APC da Dorewar jam'iyyar, A yi taka-tsantsan"", Sanata Shu'aibu ya ce "" na ja hankalin Adams Oshiomole game da hatsarin da yake son jefa jam'iyyar APC a ciki. Matuƙar aka tafi a haka to alamu na nuna jam'iyyar za ta fadi a zaben jihohin Ondo da Edo kasancewar ba a sanya gaskiya a tsarin fitar da 'yan takarar cikin gida ba. Kuma hakan ya yi wa sashe na 20 na kundin mulkin jam'iyyar karan tsaye saboda haka akwai alamu ƙarara cewa jam'iyyar adawa ta PDP za ta kwace iko daga APC."" Masu fashin baki a Najeriya irin su Dr Abubakar Kari, masanin kimiyyar siyasa wanda ya ce rikicin cikin gida a jam'iyyar APC ba sabon abu ba ne illa dai ya lafa ne amma yanzu ya kara tasowa wanda kuma ya nuna karara darewar jam'iyyar. Ya ce ""rikicin ya fara tun bayan saukar Mai Mala Buni inda aka nemi nada Waziri Bulama tun a wancan lokacin amma wasu 'yan jam'iyyar suka tayar da jijiyoyin wuya, abin da ya sa aka haƙura zuwa yanzu."" Dr Kari ya ce batun nadin Waziri Bulama ne ya so yin sanadiyyar tunbuke shugaban APC na kasa, Adams Oshiomole a 'yan makonnin da suka gabata kafin daga bisani a sasanta. To sai dai masanin kimiyyar siyasar na Najeriya ya ce ""sake bijiro da batun nadin ba komai zai haifar ba illa kara jefa jam'iyyar cikin irin wancan rikicin shugabanci da ta sha fama da shi. Ya ƙara da cewa ""komai zai iya faruwa da jam'iyyar."" 'Kulle-kullen zaben 2023 ka iya rusa APC' Dr Abubakar Kari ya ce daya daga cikin manyan dalilan da ke haifar da rikicin cikin gida a APC mai mulki shi ne ""rashin mutunta tsarin mulkin jam'iyya inda ake hawan kawara wajen fitar da 'yan takara."" Ya ce babban dalilin da ke sanya 'ya'yan jam'iyyar mai mulki wannan dambarwa shi ne ""shirye-shirye da kulle-kulle kan yadda zaben 2023 zai kasance."" ""Wasu gagga-gaggan jam'iyyar ta APC ne ke ta kokarin ganin sun karbe iko ko kuma akalar jam'iyyar domin ganin cewa su ne za su yi nasara a lokacin zaben 2023."" Dangane kuma da makomar jam'iyyar, Dr Kari ya ce "" babu wanda zai iya cewa ga makomarta amma dai za ta iya darewa tun da da ma APC, jam'iyyar hadaka ce kuma har yanzu ba ta dunkule wuri guda ba.""" https://www.bbc.com/hausa/labarai-52775722 +politics Gwamnoni arewa sun fi na kudu hujja kan takarar shugaban kasa na 2023 - Masana "Masana kimiyyar siyasa a Najeriya na ci gaba da fashin baki kan matakin da kungiyar gwamnonin arewacin kasar ta dauka na yin watsi da matsayar takwarorinsu da ke kudanci na cewa dole ne shugaban kasa ya fito daga yankin na kudu a zaben 2023. A ranar Litinin ne gwamnonin arewar suka yi wani zama inda suka tattauna batutuwa da suka hada da martanin, inda suka ce babu wanda zai tilasta wa 'yan Najeriya zaben dan takara daga wani bangare na kasar. Wani masanin harkokin siyasa a kasar Dakta Abubakar Kari na Jami'ar Abuja ya ce hukuncin da gwamnonin suka yanke na yin hannun riga da matakin takwarorinsu na kudu ya yi dai dai. ""Ni ina ga hanzarin da gwamnonin Arewa suka bayar yana da karfi kwarai da gaske saboda sun yi maganar tsarin mulki ne. ""Kuma tsarin mulkin Najeriya ya fito karara ya nuna cewa hanyoyi biyu ne kawai mutum zai iya zama shugaban kasa, kuma babu maganar bangaranci ko sashe ko kabilanci a ciki."" A cewar masanin hujjar da gwamnoni kudancin suka dogara da ita ba kundin tsarin mulkin Najeriya ne ya zo da ita ba, saboda haka ba dai dai ba ne su yi kokarin tursasa ra'ayinsu na siyasa a kan masu zabe. Sai dai ya ce ba shi da haufi idan tafiya ta yi tafiya bangarorin biyu za su warware wannan matsala su goge layin da suka ja. ""Warware wadannan rigingimu da tirka-tirka shi ne siyasar. Kuma su 'yan siyasa sun san yadda suke warware kayansu."" ""Kuma yawanci irin wadannan maganganu na fatar baki ne kawai. Su kansu wadanda ke maganar ba su yi imani da abin da suke fada ba,"" in ji Dakta Abubakar Kari. Masanin siyasar ya kafa hujja da cewa wasu da ke ikirarin cewa a mika takarar shugabancin kasa a kudu a yanzu gwamnonin jam'iyyar PDP ne da ake maganar ta aminta da mika takara ga dan arewa. ""Mafi yawan gwamnonin jam'iyyar adawa ta PDP yan kudu ne, kuma da su aka yi matsayar cewa dole ne sai mulki ya koma kudu. ""To amma ka ga tun ba a je ko ina ba wasunsu suna nan suna ta kulle-kullen cewa su za su dauki dan takara daga arewa. Saboda haka ita wannan tirka-tirka da rigima warware ta ba wani abu ba ne,"" a cewar Dakta Kari. Kumfar bakin da 'yan siyasa a Najeriya ke yi kan batun takarar shugabancin kasa na zuwa a daidai lokacin da manyan jam'iyyun kasar kamar APC mai mulki da kuma babbar jam'iyyar adawa ta PDP suka kasa warware rigingimun shugabancin cikin gida, da ya haifar da rabuwar kai a tsakanin 'ya'yan jam'iyyun." https://www.bbc.com/hausa/labarai-58704922 +politics Abin da ya jawo faɗa tsakanin Murtala Garo da Ado Doguwa "Ga alama sabon rikici ya kunno kai a jam'iyyar APC a jihar Kano bayan da taƙaddama ta ɓarke tsakanin ƴaƴan jam'iyyar. Yayin wani taron jam'iyyar APC a gidan mataimakin gwamnan jihar Kano a ranar Litinin, an samu hayaniyar da ta haifar da nuna yatsa tsakanin Honorabul Alhassan Ado Doguwa da kuma Murtala Sule Garo. Sa'insa da ka-ce-na-cen ta ɓarke ne lokacin da shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin Najeriya Honorabul Doguwa ya je gidan mataimakin gwamnan Kano a ranar Litinin. Hon Doguwa ya shaida wa BBC cewa ko da ya isa wurin sai ya tarar ana wata ganawa da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC. Kuma a cewarsa da ya tambayi abin da yasa ba a gayyace su ba, sai ya ce an mayar masa da kakkausar amsa. ""Tambayar kawai da na yi ita ce, 'yanzu ya mai girma mataimakin gwamna ya kamata a ce ana taro irin wannan, ga ɓangaren gwamnati ga kwamishinoni ga ɓangaren majalisar jiha, amma mu da muke majalisar tarayya ba a gayyaci kowa daga cikinmu ba, laifin me muka yi? ""Daga faɗar hakan sai kawai yaron nan Murtala yana zaune ya ce ba za a gayyace ku ɗin ba. Waɗannan kalmomi su suka hassala ni. ""A wajen taron kuma a garin yana masifa yana zagina sai ya kifar da wani kofin shayi mai ruwa a ciki, sai santsi ya kwashe shi ya faɗi ya fasa bakinsa. ""Amma sai na ji ana ta yaɗa wani zance wan na jefe shi na ji masa rauni,"" in ji Doguwa. Wannan dambarwa dai ta fito da wataƙila ɓoyayyiyar matsalar da APC a Kano ke fama da ita, inda Honorabul Doguwa ke ganin ya kamata gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya saka baki tun da babban zaɓe ake fuskanta. Honorabul Doguwa ya ce ""Ai ɓaraka ba za ta ɗinku ba sai idan mai girma gwamna ya yarda cewa kowa ɗansa ne. Sai idan ya yarda yadda Murtala yake ɗansa muma ƴaƴa ne, saboda muna fuskantar muguwar barazana daga ƴan hamayya. ""Kowa ya san tasirin da Kwankwaso yake da shi a jihar Kano, to wannan rigimar kawai ta ishe mu,"" ya ce. Sai dai a nasa bangaren dan takarar mataimakin gwamna a APC Murtala Sule Garo, ya ce lokacin da suke tsaka da taro sai Honorubal Doguwa ya shigo wurin yana wasu maganganu. ""Abin da ya fara cewa tun da abin jin daɗi ake yi na raba kuɗaɗe shi ne ba a neme su ba, idan da abin wahala ne sai a neme shi. ""Mataimakin gwamna da kansa ya ce masa mu ba rabon kudi muke yi ba. Mu da ka ganmu a nan a ce maganar rabon kuɗi ce ta tara mu, wa zai ba mu kuɗin? ""Sai ya ce to me ya sa ba a kira shi taron ba a matsayin kujerarsa. Sai mataimakin gwamna ya ce Gwamna Ganduje ne ya gayyato mutanen. ""Ni ban tanka masa ba ma saboda da mataimakin gwamna yake. Murtala Sule Garo ya ce ya shiga maganar ne lokacin da Honorabul Doguwa ya zarge shi da cire fastocinsa. ""An sa hotunansa an cire amma da kansa ya ce ya san ba ni ne ba amma na kusa da ni ne suka yi hakan. Sai na ce ba haka aka yi ba. ""Daga fadar hakan sai ya ɗauki kofin da mataimakin gwamna ke shan shayi ya wurga min shi,"" in ji Garo. Sai dai ya ce komai na rayuwa ɗan haƙuri ne. Har zuwa lokacin rubuta wannan labari dai jam’iyyar APC a Kano ko wani daga cikin gaggan jam’iyyar ba su ce uffan ba, kan wannan yamutsi. Amma masu lura da al’amuran siyasa na ganin muddin ba a shiga tsakani tare da yi wa tufka hanci ba to akwai yiwuwar su fuskanci cikas. Kuma a gefe guda jam’iyyun adawa sun zuba ido suna lura da yadda rikicin zai kaya, wataƙila su sami wata gaɓa da za su yi amfani da ita." https://www.bbc.com/hausa/articles/cjkxp5l6024o +politics Manyan 'yan siyasa da ke fafatawa a zaben fitar da gwani na takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC na 2023 "A ranar Litinin shida ga watan Yuni ne jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, take fara gudanar da zaben fitar da gwani na masu son yi mata takarar shugabancin kasar a zaben 2023. Jam'iyyar ta APC ta kayar da jam'iyyar PDP a zaben 2015 bayan, PDPn ta kwashe shekara goma sha shida tana mulki. Manyan 'yan jam'iyyar ne suke fafatawa domin ganin sun maye gurbin shugaban kasar Muhammadu Buhari a zaɓen 2023. Kowanne ɗan takara ya bayyana manufofinsa da yake fatan ganin ya cimma idan ya yi nasara. Cikinsu akwai mataimakin shugaban kasa da tsoffin gwamnoni da tsoffin ministoci da kuma 'yan majalisar dattawa. BBC ta yi nazari kan manyan 'yan jam'iyyar APC da ke fatan ganin sun gaji Shugaba Buhari. Mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo na daya daga cikin na farko-farko da suka bayyana aniyarsu ta tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023. Farfesa Osinbajo ya bayyana tsayawa takarar ce a wani jawabi ta bidiyo da aka yada ta talabiji da sauran kafofin sada zumunta inda ya yi bayanin irin abubuwan da zai yi idan ya gaji Shugaba Muhammadu Buhari. Osinbajo, wanda daga Kwamishinan Shari'a na Jihar Legas ya zama mataimakin shugaban ƙasa, ya ce ya tsaya takara ne domin inganta rayuwar 'yan kasar yana mai cewa a matsayinsa na mataimakin shugaban kasa yana da kwarewar shugabancin Najeriya. ""A cikin shekara bakwai, na bauta wa gwamnati a matakai daban-daban, kuma bisa umarnin shugaban kasa, na wakilci kasar nan a muhimman ɓangarori a ƙasashen waje. Na ziyarci kusan kafatanin kananan hukumomin Najeriya. Na je kasuwanni, da masana'antu, da makarantu da gonaki,"" in ji Farfesa Osinbajo. Ya kara da cewa ya je gidajen talakawan kasar a yankuna daban-daba, sannan ""na tattauna da kwararru a bangaren fasaha a Lagos, Edo, da Kaduna; da kuma taurarin Nollywood da Kannywood; da mawaka daga Lagos da Onitsha da kuma Kano. Kuma na yi magana da kanana da manyan 'yan kasuwa"". Mataimakin shugaban na Najeriya da ke da shekaru 65, ya ce ya samu wannan ƙwarewa ce domin ta zama silar fahimtar matsalolon Najeriya da kuma yadda zai magance su. Baya ga kewayawa da zai yi a jihohi domin neman magoya baya, 'yan kwamitin yakin neman zaben sa za su shirya kuri'ar jin ra'ayin jama'a domin tattara shawarwari game da matakin da ya dauka na tsayawa takarar a zaben 2023. Ana ganin Farfesa Osinbajo zai samu magoya baya, amma yadda zai ɓullo a siyasance ya kalubalanci manyan masu sha'awar takarar musamman ubangidansa Bola Tinubu shi ne abin jira a gani. A farkon watan Janairun wannan shekarar tsohon gwamnan Jihar Legas kuma jigo a Jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana anniyarsa ta takarar shuagabanci kasa. Tsohon gwamnan, mai shekaru 70, ya ce ya ziyarci Shugaba Muhammadu Buhari domin fada masa anniyarsa ta karawa a zaben 2023. A cewar Tinubu ""na faɗa wa Shugaba Buhari aniyata, ban ji abin da ba shi na yi tsammanin ji daga gare shi ba, ya ƙarfafa min guiwa kamar yadda dumokuraɗiyya ta ba ni dama, amma har yanzu ban sanar da jama'ar Najeriya ba tukunna, ina ci gaba da tuntuɓa. ""Na shafe tsawon rayuwata ina fatan zama shugaban ƙasa, don haka me ya sa zan yi tsammanin jin abun da ya saɓa da wannan daga wajen shi, tsari muke yi da dimokuraɗiyya, don haka dole mu tafi a kan haka"". Bayan sanar da takarar tasa, akwai lokacin da ya fito yana shaida wa matasan Najeriya cewa za su yi shugabancin ƙasa amma sai bayan ya yi. Tinubu ya buƙaci matasa su ba magabatansu dama. ""Kun toshe wa magabatanku dama tun kafin ku zama shugaban ƙasa, idan kun zama shugaban ƙasa fa, za ku kore mu ne a gari?"" ""Sai kun tsufa za ku zama shugaban ƙasa, kuma sai na riga zama shugaban ƙasa,"" in ji Tinubu. Tun a bara ne hotunan takarar Tinubu suka fara karaɗe wasu jihohin Najeriya. Har yanzu dai bai fito ta kafofin yada labarai kai-tsaye ya yi wa al'ummar Najeriya jawabi kan neman kujerar shugabanci da kuma manufofi ko abubuwan da zai yi idan ya yi nasara. Amma ana ganin ana iya samun takun saka tsakanin Bola Tinubu da mataimakin shugaban kasa Yemi Osibanjo a neman kujerar mulki. Ahmed Lawan Sanata Ahmed Lawan shi ne shugaban majalisar dattawan Najeriya. A haife shi ranar 12 ga watan Janairun 1959 a Gashua da ke jihar Yobe a arewa maso gabashin Najeriya. Ya yi karatunsa na firamare da Sakandare a Gashua tsakanin 1974 zuwa 1979, sannan ya kammala Digirinsa na farko a fannin Ilimin Kimiyyar Kasa a Jami'ar Maiduguri in 1984. Ya yi Digirinsa na biyu a fannin Kimiyar Tattara Bayanan Doron kasa a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a 1990, sannan ya yi Digirin Digirgir a fannin Kimiyyar Tattara Bayanan Doron kasa da Fasahar Taswira a Jami'ar Cranfield da ke Birtaniya a 1996. Ahmed Lawan ya fada harkokin siyasa inda a 1999 aka zabe shi a matsayin dan majalisar wakilai da ke wakiltar Bade/Jakusko a majalisar dokokin Najeriya. An sake zabensa a 2003. Sannan a 2007 a zabe shi a matsayin dan majalisar dattawan kasar domin wakiltar Arewacin Yobe. Sanata Lawan gogaggen dan siyasa ne kuma yana daya daga cikin 'yan majalisar da suka fi sanin harkokin majalisar dokokin kasar. A yayin da yake bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasar, Sanata Lawan ya ce babban burinsa shi ne aiwatar da shirye-shirye da za su inganta rayuwar 'yan Najeriya. Tsohon Ministan Sufuri Rotimi Amaechi, mai shekaru 56, fitaccen dan siyasa ne da ya yi gwamna da kuma shugaban majalisar dokokin jihar Ribas da ke kudu maso kudancin Najeriya. Amaechi ya ayyana takararsa ne a wani taron siyasa a garin Fatakwal. Ya ce: ""Na tsaya a gabanku don bayyana aniyata tare da gabatar da bukatar zama shugabanku na gaba"". Rotimi ya ce akwai dimbin ƙalubale da ake fama da su a Najeriya kuma burinsa shi ne share wa 'yan kasar hawayensu. Ministan da ke bayani kai-tsaye ta shafinsa na Facebook ya ce abubuwan da zai mayar da hankali idan ya yi nasara su ne tsaro da rashin ayyuka da yakar talauci da kuma habbakar tattalin arziki. Ameachi ya ce ya shafe shekaru 23 yana siyasa don haka yana da ƙwarewar da ake bukata kuma nan ba da jimawa ba zai soma gangami a kowane kusurwar kasar kama daga birni har zuwa kauyuka. Mista Amaechi ya taba yin daraktan yakin neman zabe na Manjo Janar Muhammadu Buhari, lokacin da yake takarar shugabancin Najeriya. A ranar 2 ga watan Afrilu, Gwamnan Kogi Yahaya Bello ya ayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasa, ƙarƙashin tutar jam'iyyar APC. Gwamnan ya sanar da matakin ne a wani taron siyasa a Abuja. Da yake jawabi ya yi alƙawalin cewa zai mayar da ƴan Najeriya miliyan biyu masu arziki da za su mallaki miliyoyi nan da 2030. Ya ce ya fahimci cewa ci gaban Najeriya ya dogara ne da fitar da ƴan ƙasar daga talaucin da ya yi katutu. Yahaya Bello kusan shi ne ke da mafi karancin shekaru cikin mutanen da suka fito zuwa yanzu karkashin inuwar jam'iyyar APC suna neman mulkin Najeriya. Gwamnan yana da shekaru 46 a duniya. Gwamnan ya yi fice wajen yawan shirya taro da mu'amala da masu harkar fina-finai a Najeriya. Sannan yana cikin na gaba-gaba da ke yi wa shugaban kasar Muhammadu Buhari biyayya. Sai dai masana na diga ayar tambaya kan kwarewarsa, musamman diba da ci gaban da za a zo a gani a jiharsa Kogi. Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara mai shekaru 62, kuma jigo a jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya Senata Ahmed Sani Yarima ya sake ayyana aniyyarsa shi ma ta tsayawa takarar shugabancin kasar a zaben 2023. Senata Yarima wanda tun a shekara ta 2007 ya fara fitowa takarar shugabancin kasar ya yi watsi da tsarin karba-karba a zaman abin da ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar duk da cewar ana ganin lokaci ne da ya kamata yankin kudancin kasar ya fitar Shugaban kasa na gaba. Ya ce dama sun dagawa shugaba Buhari kafa ne a 2007, kuma a yanzu tun da wa'adinsa ya kare lokaci ya yi da zai fito a kara da shi. Sanatan ya ce ya san matsalolin 'yan Najeriya na talauci da jahilci, kuma shi zai mayar da hankali wajen yakar wadannan abubuwa biyu. Ya ce matsalolin tsaron da ake fama da shi duk saboda rashin ayyukan yi ne, don haka zai bijiro da tsare-tsaren da zasu saukaka wahalhalun 'yan Najeriya. Tun cikin watan Janairu tsohon Gwamnan Imo kuma ɗan Majalisar Dattawa, Sanata Rochas Okorocha, mai shekaru 59, ya bayyana sha'awarsa ta tsayawa takarar shugabancin Najeriya a babban zaɓen 2023. Ya bayyana hakan ne cikin wata wasiƙa da ya aika wa Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmad Lawan, inda shi kuma ya karanta wasiƙar a zaman majalisar. Okorocha, wanda ɗan jam'iyyar APC ne mai mulkin Najeriya, na cikin 'yan kudu maso-gabashin ƙasar da ke bayyana aniyarsa ta yin takara a APC. Rochas ya yi fice wajen ayyukansa na agaji musamman a jihohin arewacin Najeriya. Sai dai hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zangon kasa, EFCC, ta kama shi a makon jiya. David Nweze Umahi wanda aka fi sani da Dave Umahi dan siyasa ne da yanzu haka yake matsayin gwamnan Jihar Ebonyi State da ke kudu maso gabas. Mai shekara 58, Umahi ya tsunduma harkokin siyasa ne a 2007 a matsayin shugaban jam'iyyar People's Democratic Party, PDP, na riko na Jihar Ebonyi. Daga 2009 zuwa 2011, ya rike shugabancin jam'iyyar na jiha. A 2011, Umahi ya zama mataimakin gwamnan jihar Ebonyi lokacin Gwamna Martin Elechi. Sai dai ya koma jam'iyyar APC inda aka zabe shi a matsayin gwamna a 2015." https://www.bbc.com/hausa/labarai-61071263 +politics APC na tantance Osinbajo, Lawan, Bello da sauran masu neman takarar shugaban Najeriya A ranar Talata ne ake sa ran kwamitin da ke tantance masu neman tsayawa takarar shugaban ƙasar Najeriya ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban Jam'iyyar APC, John Oyegun, zai ci gaba da tantance sauran masu neman tsayawa takara. Ranar Litinin ne kwamitin ya soma tantance masu neman takarar. Ana tantance masu neman takarar ne gabannin gudanar da zaɓen fitar da gwanin da za a gudanar na jam'iyyar tsakanin shida zuwa takwas ga watan Yunin 2022. Ana gudanar da aikin tantancewar ne a otal ɗin Transcorp Hilton da ke Abuja babban birnin Najeriya. Cikin waɗanda aka tantance a karon farko akwai tsohon gwamnan Jihar Legas Bola Tinubu da Gwamnan Jigawa Abubakar Badaru da tsohon Ministan Sufuri Chibuike Amaechi da tsohon Gwamnan Ogun Ibikunle Amosun. Sauran sun haɗa da tsohon ƙaramin Ministan Ilimi Chukwuemeka Nwajiuba da Gwamnan Ebonyi Dave Umahi da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Ken Nnamani da tsohon Gwamnan Zamfara Sani Yarima. Akwai kuma Felix Nicholas da Sanata Borroffice da Mrs Uju Ken-Ohaneye da Fasto Tunde Bakare Sauran masu neman takarar da za a tantance a ranar Talata 31 ga watan Mayu kuwa sun haɗa da: Mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo na daya daga cikin na farko-farko da suka bayyana aniyarsu ta tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023. Osinbajo, wanda daga Kwamishinan Shari'a na Jihar Legas ya zama mataimakin shugaban ƙasa na ɗaya daga cikin waɗanda ake sa ran za a tantance a ranar Talata. Gwamnan Jihar Ekiti kuma shugaban gwamnonin Najeriya Kayode Fayemi na daga cikin waɗanda ake sa ran za a tantance su a ranar Talata. Gwamna Fayemi ya kasance ministan albarkatun ƙasa a lokacin mulkin Shugaba Buhari daga 2015 zuwa 2018 kafin ya tsaya takarar gwamna karo na biyu wanda dama ya taba yin gwamnan Jihar Ekiti daga 2010 zuwa 2014. Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Ahmed Lawan na daga cikin waɗanda za a tantance domin tsayawa takar shugaban ƙasa ƙarƙashin Jam'iyyar APC a ranar Talata. Sanata Lawan wanda asalin ɗan Jihar Yobe ne, ya soma wakilci tun daga 1999 a matsayin ɗan Majalisar Wakilai, inda a 2007 ya koma Majalisar Dattawa kuma har yanzu yana a majalisa. Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello na daga cikin waɗanda ke neman tsayawa takarar shugabancin Najeriya a ƙarƙashin Jam'iyyar APC. Yahaya Bello kusan shi ne ke da mafi karancin shekaru cikin mutanen da suka fito karkashin inuwar jam'iyyar APC suna neman mulkin Najeriya. Gwamnan yana da shekaru 46 a duniya. Tsohon Gwamnan Imo kuma ɗan Majalisar Dattawa, Sanata Rochas Okorocha, mai shekara 59, na daga cikin masu neman takarar shugaban ƙasa a APC. Sai dai ana ƙila wa ƙala kan ko zai iya halartar tantancewar sakamakon yana tsare a hannun hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC bayan kamun da ta yi masa kwanakin baya. Tsohon Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya, Honarabul Oladimeji Bankole na daga cikin waɗanda ake sa ran tantancewa a ranar Talata. Bankole shi ne Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya na tara kuma shi ne kakakin majalisar mafi ƙarancin shekaru a tarihin Najeriya inda ya zama kakakin yana da shekara 37. Gwamnan Cross River, Farfesa Ben Ayade Tsohon Ministan Kimiyya da Fasaha, Dr. Ogbonnaya Onu Tsohon Ministan Watsa Labarai, Chief Ikeobasi Mokelu Tsohon Ministan Harkokin Neja Delta, Sanata Godswill Akpabio Akwai kuma Mista Tein Jack-Rich https://www.bbc.com/hausa/labarai-61644373 +politics Kwankwaso ba shi da alkibla – Ganduje "Gwamnan jihar Kano da ke Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana tsohon gwamnan jihar Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso a matsayin dan siyasa 'mara alkibla' wanda ba shi da 'tsari'. Kalaman na Ganduje na zuwa ne yayin wani bikin karbar wasu jiga-jigan jam'iyyar PDP mabiya kungiyar Kwankwasiyya wadanda suka sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki a ranar Laraba. Tun bayan da kotun kolin Najeriya ta tabbatar wa da Ganduje nasararsa ne dai gwamnan ya mika goron gayyata ga 'yan hamayya kan su zo su hadu don ciyar da jihar Kano gaba. A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Abba Anwar ya aike wa manema labarai kan taron, Ganduje ya ce ""ko a lokacin da Kwankwaso yake mulki, idan ka duba irin ayyukan ci gaban da ya samar da sauran tsare-tsarensa, za ka yadda da ni cewa bai san inda ya dosa ba a matsayinsa na shugaba. "" Sai dai wasu na ganin wadannan zarge-zargen na gwamnan tamkar martani ne kan wani bidiyo da aka ga Kwankwason na jawabi bayan hukuncin Kotun Koli, inda yake tsinuwa ga ''zaluncin'' da ya ce an yi musu. Gwamnan na Kano ya kuma fada wa dandazon 'yan PDP din da suka koma APC cewa gwamnatinsa za ta tafi da su wajen samar da ci gaba a jihar Kano. Ya kuma tunasar da su yadda ya taimaka wa Kwankwaso da kuma irin zaman da suka yi da shi tun zamanin mulkin soja lokacin da aka yi zaben 'yan majalisa. BBC ta tuntubi wani na hannun daman Sanata Kwankwason, kuma tsohon shugaban ma'aikatan gidan gwamnati a zamaninsa, Dr Yunusa Adamu Dangwani kan ko mai kungiyar Kwankwasiyyar za ta ce kan wadannan zarge-zarge, sai ya ce ''ai idan mafadin magana wawa ne to majiyinta ai ba wawa ba ne.'' ''Su al'ummar jihar Kano ai sun iya rabewa tsakanin aya da tsakuwa. Don haka sun san wane ne Kwankwaso kuma sun san wane ne Ganduje da irin salon shugabancin kowannensu, sai a bar su su yi sharhi. ''Sannan kuma da yake maganar zaben fitar da gwanin 1999, ai yanzu yana tare da su Aminu Dabo da aka yi komai a gabansu lokacin, ya tambaye su mana idan ya manta, ai zabe ne sahihi aka yi ba wani magudi, sai dai idan sun bi son rai sun ki fadar gaskiya,"" in ji Dr Dangwani" https://www.bbc.com/hausa/labarai-51224993 +politics Ra'ayi Riga: Yadda matakin aika sakamakon zaɓe ta intanet ke jawo cecekuce a Najeriya Latsa hoton sama ku saurari Shirin Ra'ayi Riga Shirin Ra'ayi Riga na wannan makon ya tafka muhawara ne kan amincewar da Majalisar Dattijan Najeriya ta yi cewa hukumar zaɓe (INEC) za ta iya aikawa da sakamakon zaɓe ta intanet. https://www.bbc.com/hausa/shirye-shirye-na-musamman-58855007 +politics Gwamnatin Zamfara ta rufe kafofin yaɗa labarai shida a jihar Gwamnatin Jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya ta ba da umarnin rufe kafofin yaɗa labarai shida saboda zargin saɓa dokokin da gwamnatin ta kafa. Kwamashinan Yaɗa Labarai Ibrahim Dosara ya faɗa wa BBC Hausa cewa an rufe su ne saboda sun yaɗa taron jam'iyyar adawa ta PDP duk da cewa gwamnatin jihar ta hana tarukan siyasa saboda dalilai na tsaro. Ya ce Majalisar Tsaro ta Zamfara ce ta amince tare da ba da umarnin rufe gidajen labaran da suka ƙunshi Radio Najeriya, da Pride FM Gusau, da NTA Gusau, da Gamji Talabijin, da Vision FM, da Al Umma TV. Sai dai jam'iyyar PDP a jihar ta musanta zargin karya dokar, tana mai cewa hukumar kula da kafofin yaɗa labarai ta ƙasa, NBC, ce kaɗai ke da ikon rufe kafofin. A kwamashinan, majalisar ta kuma umarci kwamashinan 'yan sanda da ya kama dukkan 'yan jaridar da suka halarci taron wanda ɗan takarar gwamna na PDP, Dauda Lawal Dare, ya shirya. Tun farko gwamnatin Zamfara ta ba da sanarwar hana tarukan siyasa tare da ɗaukar matakan tsaro na musamman a ƙananan hukumomin Anka da Gusau da Gumi da Bukuyum - inda hare-haren 'yan fashin daji suka fi ƙamari. Sai dai PDP ta shirya taron a ranar Asabar da zimmar karɓar wasu 'yan adawa da suka sauya sheƙa zuwa jam'iyyar tasu, har ma rahotanni suka ce an samu hatsaniya tsakaninsu da 'yan jam'iyyar APC mai mulkin jihar. Al'ummar Ƙaramar Hukumar Bukkuyum a jihar ta Zamfarar na ci gaba da kokawa game da hare-haren da 'yan bindiga suke kai musu. Mazauna yankin sun ce yan bindigar sun hana su sukuni sakamakon irin ɗauki ɗai-ɗai da suke musu da hare-haren ba zata da suke kai musu. Wani mazaunin yankin na Bukuyyum ya shaida wa BBC cewa ko a ranar Juma’a sai da ƴan bindiga suka sace ƴan uwansa goma sha ɗaya a Nasarawa Burkullu da ker yankin na Bukkuyum. Haka kuma ya bayyana cewa ko a kwanakin baya sai da ƴan bindigan suka harbe wani yaro a garin. Ya bayyana cewa kusan duka jama’ar da ke wannan yankin sun yi gudun hijira saboda bala’in ƴan bindigan. Ya kuma ce a cikin Karamar Hukumar Bukkuyum ɗin sun sace shanu sama da 300 a ranar Juma’a. Gwamnatin Jihar ta Zamafara dai ta bayyana cewa tana sane da abubuwan da ke faruwa a wannan yanki da wasu wuraren ma da ke makwaftaka da Bukuyyum. Ibrahim Dosara shi ne kwamishinan watsa labarai na Jihar ta Zamfara ya kuma shaida wa BBC cewa akwai matakan da gwamnati ke ɗauka domin magance wannan matsala. Ya bayyana cewa sakamakon wannan matsala majalisar tsaro ta jihar ta yanke shawarar rufe wuraren da lamarin ya shafa domin gudanar da wasu ayyuka. Jihar Zamfara dai na daga cikin arewa maso yammacin Najeriya da ƴan bindiga suka addaba. Ko a kwanakin baya sai da ƴan bindigar suka kashe mutum tara a Ƙaramar Hukumar Maru ta jihar. https://www.bbc.com/hausa/articles/c5144g92q18o +politics 'Matakai hudu da NNPP za ta dauka don kawo tsaro a jihar Zamfara' Dan takarar gwamna Jihar Zamfara a jam’iyyar NNPP ya ce ya fito takara ne domin yin amfani da basirarsa wajen alkilta arzikin da Allah ya huwace wa jihar. Farfesa Kabir Umar Ja-Baka ya ce zai fi mayar da hankali kan abubuwa guda hudu da suka hada da inganta tsaro da noma da ilimi da kuma sana’o’i. Farfesa ya kara da cewa idan ya samu dama zai dauki matakai na musamman wadanda yanzu gwamnatoci suka gaza wajen inganta sha’anin tsaro. https://www.bbc.com/hausa/articles/c0kznvxxwn0o +politics ‘Haɗa ɗan takara da mataimaki Musulmai a Najeriya ya saba wa Musulunci’ "Wani malamin addinin Musulunci a Najeriya ya ce haɗa mabiya addini ɗaya su kasance Shugaban ƙasa da Mataimaki a ƙasar mai al'ummar Musulmi da Kirista, ya saɓa wa ƙa'idar addinin Musulunci. A hirarsu da BBC, Sheikh Halliru Abdullahi Maraya, wanda tsohon mai bai wa gwamnan jihar Kaduna shawara ne kan harkokin addinin Musulunci, ya ce adalci shi ne a tafi tare da mai kowanne addini wajen gudanar da mulkin ƙasa. Malamin ya ce a mulki gaba daya ba abin da ke sa a samu a nasara illa a yi adalci. Ya ce,"" Shi addinin Musulunci addini ne da yake so a koyaushe a yi wa wadanda ba sa yinsa adalci kuma a kyautata musu, ma'ana a ba wa kowanne mai hakki hakkinsa."" Sheikh Halliru Maraya, ya ce,""Najeriya tamu ce da Musulmi da wadanda ba Musulmi ba, don haka Kirista ya tabbatar cewa ya yi wa Musulmi adalci, haka shi ma Musulmi ya tabbatar ya yi wa wanda ba Musulmi ba adalci."" Ya ce a mataki na iko addinin Musulunci ya tanadi cewa a yi wa kowa adalci, kada kiyayya ta mutane ta sa a daina yin adalci, don haka ya kamata a yi mulki ta yadda za a tafi da kowa in ji shi. Malamin ya ce a wajen kafa shi kansa mulkin, ya kamata a ga adalci ya fito baro-baro, kada wani bangare ko wani sashe su kwashe komai baki daya. Malamin na kalaman ne a dai-dai lokacin da rahotanni ke cewa jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya na shirin ɗauko Musulmi daga arewacin ƙasar don mara baya ga ɗan takararta na shugaban ƙasa wanda shi ma Musulmi ne. A don haka malamin ya ce, idan ya zamana shugaba Kirista ne, to a tsari na adalci sai ya zamana cewa mataimakinsa ba Kirista ba ne, haka in aka samu shugaba Musulmi ma to sai ya zamana mataimakinsa ba Musulmi ne ba. Ya ce "" Idan ana samun cewa masu addini iri guda su rinka shugabanci a kasa, to a gaskiya daya addinin da ba a yi da shi zai ce ba a yi masa adalci ba, kuma yin haka zai haifar da rashin hadin kai a kasa, za a yi ta samun tashin-tashina za a yi ta samun asarar rayuka da dukiya."" Tun bayan kammala zabukan fitar da gwani na wadanda za su yi wa jam'iyyun siyasa a Najeriya takarar shugaban kasa, ake ta ce-ce-ku-ce a kan batun zabar wadanda za su yi wa 'yan takara mataimaka musamman a manyan jam'iyyun kasar biyu PDP da APC. Idan aka yi la'akari da wanda ya samu takarar shugaban kasa a jam'iyya mai mulkin kasar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya kasance Musulmi daga kudu, wanda ake gani dauko mataimaki daga arewa zai zamo mishi babban kalubale. Batun Kirista ko Musulmi zai dauka, ya zamo babban abin muhawara a tsakanin al'ummar Najeriyar. Akwai dai rahotanni da suka ambato manyan arewacin kasar na masa hannunka-mai-sanda a kan cewa daukar Musulmi mataimaki zai fi ba shi damar samun nasara musamman a yankin, a inda Kiristoci kuma ke cewa hakan ba za ta sabu ba wai bindiga a ruwa. Kafofin yada labarai dai sun ambato shugaban kungiyar Kiristoci ta CAN, a Najeriya Dakta Samson Ayokunle, na gargadin cewa daukar mataimaki Musulmi ga dan takara Musulmi, mataki ne da ka iya zama tamkar wani bala'i ga kasar. Tarihin Shugaban Kasa da Mataimakinsa Musulmi; A tarihin siyasara Najeriya sau daya ne aka taba samun dan takarar shugaban kasa Musulmi da shi da mataimakinsa. Wannan kuwa ya faru a lokacin zaben 12 ga watan Yuni, 1993. A lokacin marigayi Moshood Kashimawo Abiola (MKO) ne ɗan takarar shugaban ƙasa na SPD, Baba Gana Kingibe kuma mataimakinsa. Zaɓen ya kasance ne tsakanin Social Democratic Party, SDP, da National Republican Convention, NRC, wadda marigayi Bashir Othman Tofa da mataimakinsa Sylvester Ugoh suka yi wa takara." https://www.bbc.com/hausa/labarai-61806891 +politics Ba na son lakabin matar shugaban kasa - Aisha Buhari "Mai dakin Shugaban Najeriya Aisha Buhari ta ce daga yanzu kada wanda ya kara kiran ta da lakabin 'Matar Shugaban Kasa', sai dai ""Uwar Gidan Shugaban Kasa wato First Lady"". Aisha ta bayyana haka ne a wurin liyafar cin abinci da aka shirya domin girmama matan tsofaffin gwamnoni a fadar shugaban kasa da ke Abuja. Ta ce ta zabi a kira ta da ""Matar Shugaban Kasa"" ne don radin kanta duk da cewa ya haddasa rudani. ""Ni na zabi a kira ni da lakabin ""Matar Shugaban Kasa a 2015 amma ina fatan za ku yafe ni bisa rudanin da ya haifar. Daga yanzu ina so a kira ni da Uwar Gidan Shugaban Kasa wato First Lady"". Sai dai kafafen yada labarai a Najeriya sun ruwaito cewa Shugaba Buhari ya bayyana a 2014 cewa zai rushe ofishin First Lady idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa. Wannan ba shi ne karon farko ba da uwar gidan shugaban ke amfani da tarukan liyafa don isar da sako ba, ko dai ga 'yan kasa ko kuma mahukunta. A watan Maris, jim kadan bayan mijinta ya lashe zabe a karo na biyu ta ja kunnen shugabannin jam'iyyar APC mai mulki kan rabon mukamai a wajen liyafar da aka shirya domin murnar nasarar mai gidan nata a Daura. Mace mai jawo ce-ce-ku-ce - Sharhi daga Halima Umar Saleh Ana yi wa Hajiya Aisha Buhari kallon mace mai yawan jawo ce-ce-ku-ce kan al'amuran da suka shafi mulkin mai gidanta. A shekarar 2016 ne hakan ya fara fitowa fili bayan da ta yi wata hira da BBC Hausa inda ta ce wasu 'yan tsirarun mutane sun mamaye gwamnatin mijinta, suna hana ruwa gudu. Ta yi zargin cewa ba a tafiya da wadanda suka sha wahalar kawo mijinta kujerar tasa wajen ba su mukamai, sai dai a dauko wasu can na nesa a ba su. A wancan lokacin har ta yi ikirarin idan abubuwa ba su sauya ba to ba za ta mara masa baya a zaben 2019 ba. Akwai kuma lokacin da ta soki jam'iyya mai mulki ta APC dangane da yadda ta gudanar da zabukan fitar da gwaninta a 2018. Amma wasu da dama sun daganta hakan da rashin samun nasarar dan uwanta da ya tsaya takarar gwamnan Adamawa a APC din a zaben fitar da gwani. Ga 'yan Najeriya da dama dai suna ganin abun da Aisha take yi bai dace ba, musamman ga tarbiyya irinta kabilar Hausawa da Fulani, amma a wani bangaren wasu kuma na ganin abun da Aisha ke yi daidai ne, domin gyara kayanka ne, wanda masu magana kan ce ba ya zama sauke mu raba. Sai dai duk da sukar da take sha hakan bai hana ta yin gum da bakinta ba a duk lokacin da take zargin ana wani abu da bai dace ba a mulkin mijin nata. Amma a baya-bayan nan ana ganin hotunan Aisha da mijinta na yaduwa a shafukan sada zumunta da muhawara da ke nuna yadda suke ji da juna. Kuma ganin tun da aka fara yakin neman zabe har aka yi zabe ba ta yi korafi kan wani abu ba, ya sa wasu ke ganin kamar sun dinke barakar da ke tsakaninsu, (suna koren ganye). An haifi Aisha Halilu ran 17 ga watan Fabrairun 1971 a jihar Adamawa da ke arewa maso yammacin Najeriya. Kakanta Alhaji Muhammadu Ribadu shi ne ministan tsaron Najeriya na farko. Ta yi digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya a fannin Public Admimistration, sai ta yi digirinta na biyu a kan harkokin kasashen waje. Ta yi difloma a fannin kwalliya a makarantar koyon ado ta Carlton Institute da ke Windsor a Birtaniya, da kuma wata makarantar koyon gyaran jiki ta Academy Esthetique da ke Faransa. Aisha Muhammadu Buhari da wasu daga cikin 'ya'yan Shugaba Muhammadu Buhari Kafin maigidanta ya zama Shugaban Najeriya, tana da shagon gyaran jiki da kwalliya mai suna Hanzy Spa a jihar Kaduna. Ta wallafa wani littafi na koyar da kwalliya da gyaran jiki wanda Hukumar da ke kula ta makarantun kimiyya da fasaha ta Najeriya ta sa shi a cikin manhajar da makarantun za su yi amfani da shi. Aisha ta haifi 'ya'ya biyar da Muhammadu Buhari." https://www.bbc.com/hausa/wasanni-48638812 +politics Gane Mani Hanya: Hira da Abdullahi Adamu sabon shugaban APC Latsa hoton sama ku saurari shirin: Shirin Gane Mani Hanya na wannan makon ya yi tattaunawa ta musamman da Sanata Abdullahi Adamu, wanda aka zaɓa a matsayin sabon shugaban jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya. https://www.bbc.com/hausa/shirye-shirye-na-musamman-60965508 +politics Zaben 2023: Kwankwaso ya ce suna tattaunawa da Peter Obi "Danna hoton da ke sama domin kallon bidiyon: Dan takarar shugaban Najeriya na jam'iyyar NNPP, Sanata Rabi'u Kwankwaso, ya ce yana tattauna da takwaransa na Jam'iyyar Labour Party, Peter Obi domin yiwuwar hada gwiwa a zaben 2023. Ya bayyana haka ne a tattaunaarsa da BBC Hausa. A cewarsa ""gaskiya muna magana da shi Peter Obi, ko kuma ma in ce kwamiti yana aiki domin ya duba dukkan abin da ya kamata (kan hada gwiwa da shi), kuma abokai da 'yan uwa suna zuwa suna yi mana magana kan batun."" Tsohon gwamnan na Jihar Kano ya ce hada gwiwarsu tana da muhimmanci musamman ganin cewa jam'iyyun APC da PDP ba su tsayar da dan takarar mataimakin shugaban kasa daga yankin kabilar Igbo ba." https://www.bbc.com/hausa/media-61850641 +politics Taƙaddama ta ɓarke a APC bayan fitar da ƴan kwamitin yaƙin zaɓen 2023 "Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta yi ƙarin haske game da cece-ku-cen da ake yi musamman a shafukan sada zumunta na internet kan jerin sunayen tawagar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da ta fitar. Ƙananan maganganu sun fara ɓulla ne bayan da aka ga babu sunayen wasu jiga-jigan jam'iyyar a cikin jerin sunayen, ciki kuwa har da mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo - wani abu da masana ke ganin zai iya barin baya da ƙura. Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa wasu gwamnoni na jam’iyyar APC sun yi barazanar yin zagon kasa ga yaƙin neman zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar, Bola Tinubu, a jihohinsu. Gwamnonin sun zargi Mista Tinubu da ƙin karɓar mutanensu a kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasar. Sakataren kwamitin yaƙin neman zaɓen James Faleke, ya ce kafin a saki jerin sunayen tawagar kamfe din, sai da shugabannin kwamitin suka tuntubi gwamnonin don su zaɓi mutanen da za a saka a tawagar daga jihohinsu, inda aka buƙaci su bayar da sunan mutane biyar. Sai dai jaridar ta ce gwamnonin sun sha matuƙar mamaki da ganin yadda Tinubu ya sauya mutanensu da wasu a jihohin nasu ba tare da tuntuɓarsu ba. Bala Ibrahim shi ne Daraktan yaɗa Labaran Jam'iyyar kuma ya shaida wa BBC cewa ba lalle ba ne a ga sunan kowa da kowa a cikin jerin sunayen mambobin kwamitin saboda ""an kafa kwamiti ne domin taimakawa, kuma ba wai ana nufin mutum ɗaya shi zai iya komai ba, inda ka ji an ce mataimaki, akwai wani sama da shi,"" ""A wannan kwamiti an duba an ga babu sunan shugaban ƙasa?, idan akwai shugaban ƙasa, maganar mataimaki ya shigo ba ta taso ba,"" a cewar Bala Ibrahim. Ya bayyana cewa tun bayan fitar da jerin sunayen, jam'iyyar ba ta yi wata ganawa a kan lamarin ba. A cewarsa, an kafa kwamitin domin tsara dabarun neman ƙuri'ar ƴan Najeriya saboda akwai buƙatar waɗanda sunayensu ba sa cikin kwamitin su karkatar da kansu ga ayyuka masu muhimmanci. Ya ce akwai yiwuwar a samu sauye-sauye a Jam'iyyar - ""bayan wannan kwamitin, akwai wasu ƙananan kwamatoci da za a kafa na shiyya-shiyya, akwai wasu waɗanda ba lalle ba ne a ga sunansu ɓaro-ɓaro cikin kwamiti. ""Amma rawar da suke takawa tana da yawa, wataƙila sune fitilar da ke haska wa wannan kwamiti hanya ya ga inda zai bi."" Tuni masana suka fara tsokaci game da wannan mataki da ya janyo turka-turka. Dr Abubakar Kari na Jami'ar Abuja a Najeriya ya ce ƙaramar magana za ta iya zama babba idan gaggan Jam'iyyar ba su yi da gaske ba. ""Jam'iyyar ba ta da zaɓi sai ta fito da dabaru da hanyoyin magance wannan abu, idan ba haka ba, zai yi mata illa a zaɓukan da suke ƙaratowa, a takaice irin illar da za a masa shi ne za a kakkaɓe masa magoya baya. ""Za a yi amfani da batutuwa na addini a yi masa zagon ƙasa a sa mutane su ƙyamace shi suƙi zaɓensa."" in ji masanin." https://www.bbc.com/hausa/articles/cjl7gngxxdyo +politics Yadda batun raba katin zabe ke jan hankalin ‘yan Najeriya Soma ba da katunan zaɓe na din-din-din ga wasu daga cikin masu zaɓe a Najeriya ya ja hankalin 'yan kasa inda kowa ke bayyana ko tofa albarkacin bakinsa. A wannan Litinin din Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Inec ta soma wannan aiki kuma mutanen da za a bai wa katunan su ne mutanen da suka ba da sunayensu daga farkon 2022, zuwa lokacin da aka rufe aikin a watan Yuli. Sai dai kuma duk da irin tsare-tsare da Inec ta ce ta yi, ana ta samun masu korafi da kokawa kan dogayen layuka wajen samun katin, da kuma wadanda suka hau shafukan sada zumunta musamman Tuwita da nasu ƙorafin. Za dai a shafe kwanaki ana wannan aiki na raba katunan zabe a matakin ƙaramar hukuma kafin a koma matakin mazaɓu. Ana raba katunan ne a ofisoshin INEC na kananan hukumomi kawo yanzu, inda jama'a ke bin layi a mazaɓu. Duk mutumin da ya zo karbar katin sai ya gabatar da shaidar cewa ya yi rijista a baya sannan sai a duba sunansa a kundin rijistar zaɓe sai kuma a duba masa katin. Idan an sami katin sai kuma a rubuta sunansa ya saka hannu cewa ya karbar. Amma da farko sai mutum ya duba sunansa a kundin rijistar da aka yi baje-kolinta a jikin bango. Wadanda ba su ga sunayensu ba a kan ba su wata takarda su cike sannan sai a bukaci su dawo daga baya don karbar katinsu. Sai dai wasu rahotanni na cewa ana samun dogayen layuka wajen karbar kati, sannan akwai wadanda ba su samu katinsu ba saboda wasu dalilai. Galibi dai abin da ‘yan Najeriya a shafukan sada zumunta na Alla-wadai da kazamin harin da aka kai wa ofishin Inec da ke Imo. Mutane dai na ganin akwai bukatar gwamnati ta yi da gaske domin inganta tsaro ganin yanayin abubuwan da ke faruwa a Najeriya. Sannan akwai masu fitowa dauke da katunansu suna nuna cewa su nasu katin zaben ya shiga hannu, duk da cewa wasun su na ƙorafin shan wahala kafin karbar katin. @HiikyaaTor ya ce: A ranar da INEC ta soma raba katunan zabe, 'yan daba da bata-gari suka far wa ofishin INEC a jihar Imo-Owerri. Akwai ayar tambaya anan!!! Wane ne makiyin dimokuradiya? Me ya sa abubuwan nan ke faruwa a Kudu maso gabashi? Ya Ubangiji, ka tona asiri.. @fopara03 ya ce: Yanzu nan na karbi nawa katin zaben sannunku da kokari Inec. Don Allah ku je ku karbi naku katin @D_goodybag ta ce; Ga abubuwan da nake gani anan. Tsarin akwai gajiyarwa, dandazon jama'a ya yi yawa. Inec su inganta tsarin Sannan abu na uku da ake tattaunawa a kai shi ne yadda a wasu ofisoshin jami'an Inec din katunan ba su samu ba sai iske jami'an hukumar na ta hidimominsu. Akwai kuma masu karfafawa matasa su fita su karbi katinsu domin shi ne yancinsu wajen zaben mutumin da zai raya kasa. Inec Ta ce za a raba katunan ne daga ranar 12 ga watan Disambar 2022 zuwa 22 ga watan Janairun 2023, kuma za a yi rabon ne a dukkan kananan hukumomin Najeriya 774. Daga ranar 15 zuwa 22 ga watan na Janairu, za a sake komawa ofisoshin hukumar zaben da ke jihohi domin ci gaba da raba katunan. https://www.bbc.com/hausa/articles/crg7p451ggro +politics Bola Tinubu: Dalilan da suka sa siyasar tsohon gwamnan Lagos ta sha bamban da ta sauran ƴan siyasa "Da alama nasarar da tsohon gwamnan Jihar Lagos, Bola Ahmed Tinubu, ya samu a zaɓen fitar da gwani na shugaban ƙasa na Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta sa shahararsa ta ƙara fitowa fili. Duk da cewa nasararsa ba ta zo wa wasu ƴan Najeriya da mamaki ba, amma wasu ƴan ƙasar sun yi tsammani zai sha kaye musamman ganin yadda ake zargi wasu daga cikin shugabannin jam'iyyarsa ba su mara masa baya ba. An daɗe ana damawa da Tinubu a fagen siyasa da mulki kuma ya shahara a ƙasar Yarabawa, har ma aka ba shi sarautar Asiwaju. Za a iya cewa Tinubu ya soma shahara ne a siyasa a lokacin da ya bayar da gudunmawa wurin kafa Jam'iyar SDP. Bayan nan ne aka zaɓe shi a matsayin Sanata mai wakiltar Yammacin Jihar Legas a 1992. A Majalisar Dattijan Najeriya, ya samu nasarar zama shugaban kwamitin da ke kula da bankuna, kuɗi da kasafi na Majalisar Dattawa - wanda babban kwamiti ne na Majalisar Dattawan Najeriya. Dangane da wannan lamari, BBC ta tuntuɓi Bala Ibrahim, tsohon ma'aikacin BBC kuma mai sharhi kan harkokin siyasa inda ya ce a bayyana take cewa siyasar Tinubu ta sha bamban da siyasar sauran ƴan Najeriya. ""Siyasar Tinubu siyasa ce ta gina wasu waɗanda za a yi amfani da su a gaba saɓanin siyasar sauran iyayen gidan siyasa waɗanda suke yin amfani da waɗanda suke da amfani a lokacin da ake son amfani da su kawai,"" in ji Bala Ibrahim. Ya kuma ce ""ana ganin Tinubu yakan yi ajiya ne domin ƙyanƙyasa saboda gaba kuma yanzu gaban shi ne kamar lokacin da ake ciki yanzu, ana ganin ajiyarsa ta biya masa buƙatarsa ta yanzu. A cewarsa, ya bambanta ne da sauran masu siyasar uban-gida inda ya ce galibi shi Tinubu yakan jefa ƙwallo ne domin ya ɗauka a gaba. ""A dai wannan abin da aka yi a yanzu ana ganin ajiyar da ya yi a baya ce ta biya masa buƙatarsa ta yau, ita ta share masa hawaye ko ƙishirwarsa ta wannan lokacin a yanzu. Bala Ibrahim ya bayyana cewa Tinubu ya sha faɗar cewa yana da burin ya zama shugaban ƙasa, wanda hakan ya sa ya rinƙa tafiya yana gini kuma ginin nan da yake yi yana ajiya ne a wasu, yana gina mutane ne waɗanda yake ganin za su yi masa amfani, in ji shi. ""A wannan gini kuma, ya yi amfani da kuɗi da abubuwan duk da yake da su, idan aka kalli ƙawancesa da gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, kowa ya san wannan ƙawance ba wai soyayya ba ce ta cancanta ko kuma yana son jama'ar Jihar Kano. ""Yana son ƙuri'ar Kano ne saboda Kano ce ke da mafi yawan ƙuri'u a lokacin zaɓe, hakazalika kuma ita take da mafi yawan daliget a lokacin zaɓen fitar da ɗan takara,"" in ji shi. BBC ta tuntuɓi Mahmud Jega, mai sharhi kan harkokin siyasa a Najeriya, inda ya ce a ganinsa idan aka cire Atiku Abubakar, babu ɗan siyasar da ya yi ƙarko kamar Bola Ahmed Tinubu. ""Duk yawanci waɗanda suka yi gwamna tsakanin 1999 zuwa 2007 da yawansu an daina jin su an manta da su a sha'anin siyasa. ""Amma shi ga shi sai ƙara bunƙasa kawai yake yi, shi ya sa aka san shi fiye da duk waɗanda suka yi gwamnoni a wancan lokaci. A cewarsa, Tinubu ya nuna ƙwazo matuƙa tun a zamanin Chief MKO Abiola, kuma tun bayan rasuwar Abiola, ba a samu wani ɗan siyasa da ya yi tasiri a kudu maso yammacin Najeriya irin Tinubu ba. ""Lokacin da ya fara siyasarsa, kusan ƙasashen Yarabawa kawai ya damu da su, ba ruwansa da ƙoƙarin neman mulkin Najeriya. ""Wato gwamnatin tarayya amma daga baya shi ya zo ya yi ruwa ya yi tsaki aka samu aka haɗa wannan jam'iyya ta APC har aka kawo Yarabawa a ciki aka samu galaba.""" https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-61747977 +politics Ko me ya sa wasu ba a ganin ƙwazon gwamnatin Shugaba Buhari? "Daga Ibrahim Isa, BBC Hausa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nuna damuwa game da yadda mutane ba sa fita suna yabawa da ƙwazon gwamnatinsa, duk kuwa da ɗumbin ayyukan raya ƙasa da yake ikirarin cewa tana aiwatarwa. Shugaban kasar ya yi wannan furucin ne a jihar Imo, lokacin da ya kai wata ziyarar aiki ta kwana guda,a ranar Talata. To ko me ya sa ba a ganin kwazon gwamnatin? Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ya karbi ragamar mulkin Najeriya a wani lokaci da kasar ta samu kanta a tsaka mai wuya. Adadin man da ƙasar take haƙa ya ragu sosai, farashinsa a kasuwannin duniya ya faɗi ƙasa warwas - mma duk da haka, gwamnatinsa ta san yadda take ƙuƙutawa take aiwatar da ayyukan raya ƙasa da kuma inganta tsaro a Najeriya. Shugaban ya ƙara da cewa idan wani na kokwanto, to ya tambayi al’ummar jihar Borno don jin yadda aka karya lagon ƴan Boko Haram! Sai dai wani abin takaici, a cewar Shugaba Buharin shi ne yadda mutane ke kau da kai – ba sa yabawa - kamar yadda ƴan magana ke cewa abin kirki bai gaji kare ba - wato ko ya yi ma jifar sa ake yi. “Daidai wa daida, idan aka yi la’akari da lokaci da ɗan abin da ake samu, wannan gwamnatin ta yi rawar-gani ƙwarai da gaske. ""Dole ne na faɗa, saboda waɗanda ya kamata su faɗa ba sa faɗa, kuma ban san dalili ba,” in ji Shugaba Buharin. Wataƙila rashin sanin wannan dalilin ne ya sa shugaban ƙasar ya ari ta ƙadangare, wai da ya faɗo daga sama ya zaɓi ya jinjina wa kansa, ko da wasu ba su jinjina masa ba. A siyasa, jam’iyyun hamayya na cikin gwanayen sa-ido a kan gwamnati. Kuma na tuntubi Sanata Umar Ibrahim Tsauri, mamba na kwamitin ƙasa a PDP, don jin yadda suka ji kalamin Shugaba Buharin. Ya ce: ""Zai yi wahala a ce shugaban ƙasa na yin ƙarya, sai dai ƙila a ce abin da shugaban ƙasa ya faɗa ba gaskiya ba ne. ""Idan Buhari ya ce ya yi aiki na more rayuwa ga al’ummar Najeriya, to mu jefa wannan maganar a kotun shari’ar al’ummar ƙasa, sai su yanke hukunci, shin gaskiya ya faɗa ko ba gaskiya ba. ""Mu a arewa duk hanyoyinmu sun zama idan ka bi su, to kana so ka kashe kanka kenan, abin da kawai Buhari ya gwada, ƙila ana ba shi labari ne don ba ya bin hanyar ƙasar. Idan da yana bin hanyar ƙsar, da ya san cewa idan labari ake ba shi to ƙarya ake masa,"" a cewar Sanata Tsauri. Ya ƙara da cewa ""Mu a wurinmu a jam’iyyar PDP, abin da muke so shi ne Buhari ya mayar da mu yadda ya ɗauke mu."" Sai dai wasu masana siyasa a ɓangare guda na ganin cewa shugaban ƙasar na kokawa ne da yadda wasu muƙarrabansa da kuma magoya bayan jam’iyyar APC mai mulkin ba sa tallata ayyukan gwamnatin tasu. Ko da yake, Mallam Kabiru Sa’id Sufi masanin siyasa a kwalejin share fagen shiga jami’a ta jihar Kano, ya ce wani lokaci akan yi wa jagora watsewar ƴaƴan zabi idan zamaninsa ya tasam ma shuɗewa. ""A baya akwai ƙungiyar tallan manufofin shi Shugaba Muhammadu Buhari da suka shahara wajen ƙoƙarin zaƙulo abubuwan da wani sa’in ma ake ganin suna yin zulaƙe. ""To amma dukkansu a halin yanzu za ka ga cewa babu, tun da gwanatin ta nisa ta kuma taho ƙarshe, don haka tunanin kowa ya koma yadda zai ga an yi da shi a sabuwar gwamnati. ""Don haka hankulansu sun karkata wajen tallata yan takarar da suke goya wa baya."" A watan Fabrairun badi ne ake sa ran za a yi babban zabe a Najeriya. Kuma sabanin wasu zabukan da aka yi a baya, inda za ka ga ‘yan takara na tutiya da ayyukan shugaban kasar, har suna hada hotunansu da nasa - a wannan zagayen kusan ko wa ta-kai-takai yake yi wai gobarar bera. Alamar da ke nuna cewa an riga an ci kasuwa - sai maganar watsewa." https://www.bbc.com/hausa/articles/cldz1dqkey2o +politics ‘Ku karbi kudi idan an ba ku a lokacin zabe amma ku zabi cancanta’ Yayin da babban zabe a Najeriya ke tafe, wasu ‘yan siyasa a kasar sun ce ba laifi bane masu kada kuri’a su karbi kudi idan an basu a lokacin zabe, amma kuma su zabi cancanta. ‘Yan siyasar sun bayyana hakan ne a yayin da wasu masana da kungiyoyin kare dimokradiyya ke fargabar cewar siyasar kudi musamman sayen kuri’u na iya mamaye babban zaben kasar da ke tafe. Hon Yusuf Umar Garkuwa, matashin ɗan siyasa ne daga jihar Kaduna, ya shaida wa BBC cewa, ba bu laifi masu zaɓe su karɓi kuɗi, tun da ko sun karɓa ba wanda zai tilasta musu zaɓen wanda ba sa ra'ayi. Ya ce ya na ganin hakan zai magance matsalar siyasar kuɗi gaba ɗaya a Najeriya. Hon Yusuf Umar Garkuwa, ya ce “ Shi zabe abu ne da za ayi shi a boye, don haka don mutum ya baka kudi ka zabe shi bai isa ya bika akwatin zabe don ganin abin da zaka zaba ba.” Saboda haka ka amshi kudin, amma kuma ka zabi abin da ya dace in ji shi. Ya ce idan har ‘yan siyasa na bayar da kudi ana karba kuma ba a zabensu, ai gobe ba zaka fito ka kara bayar da kudi don a zabe ka ba. Kuma idan ma ka ga wani zai bayar da kudi don a zabe shi ai zaka bashi shawara a kan kada ya soma don kai ma kayi baka ji dadi ba in ji shi. Hon Yusuf Umar Garkuwa, ya ce idan har ana yin haka to a iya samun sauki a siyasar kudin da ake a Najeriya. Matashin dan siyasar ya ce, ‘‘Idan har ana wayar wa mutane kai a kan ‘yancinsu, da kuma zabar cancanta, za a rinka samun sauki a siyasar kudi, domin mutane za su karbi kudin dan takara amma kuma su zabi abin da suke so.” Ya ce ba wai siyasar kudi ba zata yi tasiri a zaben mai zuwa ba, zata yi a wasu wuraren, amma ba a ko ina ba, don haka in da zata yi tasirin ma yakamata mutane su gane ‘yancinsu na shekara hudu suke sayarwa. Hon Yusuf Umar Garkuwa, ya ce akwai wasu ‘yan takarar da basu da abin da zasu fada a zabe su ko kuma su nuna, don haka dole su fito da kudi a lokacin zabe saboda akwai talauci da yunwa da ke addabar mutane. Ya ce don haka ku karba ku cinye ku zabi wanda kuke ganin ya fi cancanta. https://www.bbc.com/hausa/articles/c72z9ww2r8zo +politics INEC ta fitar da jerin sunayen ƴan takarar shugaban ƙasa na 2023 da ƴan majalisar dokoki Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya INEC, ta fitar da jerin sunayen ƴan takarar shugaban ƙasa da majalisar dattawa da kuma na majalisar wakilai na dukkan jam’iyyun ƙasar da za su fafata a zaɓukan 2023. INEC ta fitar da jerin sunayen ne a ranar Talata, 20 ga watan Satumban 2022, inda ta ce jerin na ƙu she ne da sunayen ƴan takara daga jam’iyyu 18. An wallafa jerin sunayen na ƴan takara daga dukkan mazaɓun ƙasar a shafin intanet na INEC. Za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na majalisun dokokin tarayya ranar 25 ga watan Fabrairun 2023 sai na gwamnonin da majalisun dokokin jihohi ranar 11 ga watan Maris din 2023. A jerin sunayen, akwai ƴan takarar shugaban ƙasa da mataimakansu 18 daga jam’iyyu daban-daban, sai kuma ƴan takarar majalisun tarayya daga jihohi 36 da babban birnin ƙasar Abuja, ƙarƙashin jam’iyyu daban-daban. Baya ga sunayen ƴan takarar da ta wallafa, INEC ta kuma bayyana jinsi da shekaru da matakin ilimi na kowane ɗan takara. https://www.bbc.com/hausa/articles/cpey2dd9301o +politics Zan fi bai wa fannin ilimi muhimmanci a jihar Yobe - Dan takarar PDP "Dan takarar kujerar gwamna na jihar Yobe, a jam'iyyar adawa ta PDP, Alhaji Sharif Abdullahi ya ce burinsa shi ne ganin fannin ilimi ya habaka. A cewarsa "" jihar Yobe na fuskantar matsaloli da dama amma babu kamar matsalar raunin fannin ilimi kasancewar ita ce ta haifar da duk matsalar da jihar ke ciki a yanzu haka.""" https://www.bbc.com/hausa/articles/c16pn2ze1nzo +politics 'Mun yi murna da Buhari ya amince da dokar zaɓen 2023' Masu ruwa da tsaki a lamuran zabe a Najeriya sun fara tsokaci kan sa hannun da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kan kudurin dokar zabe ta 2021 da aka dade ana ce-ce-ku-ce a kai. Buhari ya saka hannu kan dokar ne a yayin wani takaitaccen buki a fadarsa a gaban idon shugaban majalisar dattawa da kakakin majalisar wakilai da kuma shugaban hukumar zaben kasar da sauransu. Shugaban majalisar tuntubar juna tsakanin jam'iyyun siyasar kasar wato Inter Party Advisory Council (IPAC), Injiniya Yusuf Yabagi San, na daga cikin wadanda suka shaidi sa hannun, kuma ya shaida wa BBC cewa wannan lokaci ne mai cike da tarihi. Injiniya Yabagi ya ce lokaci ya yi da za a tabbatar da sahihi kuma ingantaccen zaɓe a Najeriya. ''Zaɓe a Najeriya zai zamo abin da mutane za su amince da ingancinsa, za a kaucewa matsalolin da aka fuskanta a baya, da rage kashe kudi marasa ma'ana, don haka sanya hannu kan wannan doka ba karamin abu shugaba Buhari ya yi wa tarihin Najeriya ba. Saboda yawancin matsalolin da ake fama da su a kasar nan su na samo asali tun daga rashin shugabanci na gari, da zarar babu hanyar da za a fito da shugabanni na gari ta hanyar zabe, za a ci gaba da tafiya mai kunci da rashin tabbas.'' Yabagi ya kara da cewa wannan doka za ta magance matsalar satar kuri'u, ko akwatin zaben baki daya da matsalar da ake samu wajen kidaya kuri'u ta hanyar murdiya da ake yi a baya. A cewarsa wannan zai kawo sauki saboda zabe ya na nan cikin na'ura ba kamar a baya da sai kowanne baturen zabe na mazaba ya kai sakamako inda ake tattara shi ba. Sai dai kuma Injiniya Yabagi ya ce a fanin kazamin kudi da ake amfani da shi a lokacin zabe, wannan doka babu abin da za ta iya yi akai. Yana mai cewa Jami'an tsaro ne kadai suke da hurumi anan domin abi hanyoyin da za a rage aikata hakan,'' in ji Yabagi. Kafin rattaba hannu kan dokar zaɓen sai da shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci 'yan majalisa su sake komawa domin yin gyara a sashe na 84, wanda ya ce an haramtawa masu rike da mukaman gwamnati yin zaɓe a tarukan jam'iyya ko zaɓen 'yan takara. Yabagi ya ce su na goyon bayan wannan matakin ganin ya sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya, bai kuma kamata a ce an hana wani ɗan kasa damar da ya ke da ita ba. A ranar Juma'a ne, Shugaba Muhammadu Buhari ya saka wa sabuwar dokar hannu bayan da aka dauki tsawon lokaci ana kace-nace a kai. https://www.bbc.com/hausa/labarai-60533195 +politics Kotu ta ce Muhammad Abacha ne dan takarar gwamnan Kano a PDP "Babbar Kotun Tarayya a jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta yanke hukuncin cewa Muhammad Abacha ne ɗan takarar gwamnan jihar a ƙarƙashin jam'iyyar PDP. Mai Shari'a AM Liman ne ya yanke hukuncin a ranar Alhamis ta manhajar Zoom kasancewar baya gari. Ya ce bangaren da suka gudanar da zaben fitar da gwani a Lugard Road shi ne halastaccen zaben dan takarar gwamnan na jam'iyyar PDP, kasancewar jami’an hukumar INEC sun halarci wurin tare da sanya ido kan zaben. Tun bayan ficewar Rabi'u Musa Kwankwaso ne rikici ya ƙara ƙamari a jam'iyyar PDP ta Kano ta yadda har aka samu rarrabuwar kawuna a zaɓen fitar da gwani na ɗan takarar gwamna. Ɓangaren Aminu Wali ya fitar da ɗan takararsa Sadiq Wali yayin da ɓangaren Shehu Sagagi ya fitar da Muhammad Abacha a matsayin nasa ɗan takarar. A zaben fitar da gwani da aka yi a watan Mayun 2022 Mohammed Abacha ya fafata da Adamu Yunusa Ɗan Gwani da Ibrahim Al-Amin Little da Muhiyi Magaji Rimin Gado da Jafar Sani Bello da kuma Injiniya Mu'azu Magaji wato Ɗan Sarauniya. Kuma a lokacin sakamakon ya nuna Muhammad din ne ya yi nasara. Sai dai a watan Yuli kuma sai ga hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta wallafa sunan Sadiq Aminu-Wali a matsayin dan takarar PDP na jihar Kano. Barista Sa’idu Muhammad Tudun Wada shi ne lauyan Muhammad Abacha ya yi wa BBC arin bayani kan hukuncin kotun. ""A cikin hukuncin da kotun ta yi, ta yi umarni a kan cewa INEC ta cire sunan Sadiq Wali ta musanya shi da sunan Muhammad Abacha bisa hujjojin da ta dogara da su cewa shi ne sahihin dan takara wanda jam'iyya ta gabatar kuma INEC ta halatta."" Ya ce alkalin ya ƙara da cewa ""rashin bayar da sanarwa ta kwana 21 kamar yadda dokar zaɓe ta tanada, ita jam'iyyar PDP a matakin ƙasa da ta gaza yi na bai wa INEC sanarwa, wannan ya jawo tasgaro a kan sahihancin zaɓen da aka yi a filin wasa na Sani Abacha."" To sai dai lauyan Sadiq Wali wanda yanzu sunansa ke gaban hukumar zabe a matsayin dan takarar gwamna a PDP, ya ce ba su gamsu da hukuncin ba, amma za su tattauna da wanda yake karewar don daukar mataki na gaba. Farfesa Nasiru Adamu Aliyu ya ƙara da cewa ""alkali bai yi la'akari da cewa akwai hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Kano ta yanke a sati biyun da suka wuce, a kan zaɓe makamancin wannan ba. ""Dama abin guda biyu ne, ta ce duk zaɓe da jam'iyya ta yi, ta ja ba ta da hurumi, zaɓenta ba shi da tasiri, sannan wanda ya yi ƙarar ma ba shi da ikon kai wa ƙara. ""Bisa wannan abin da za mu yi shi ne zan saurari wanda nake wakilta na ji ra'ayinsa, amma zan ba shi shawara cewa akwai hujja mai ƙwari daga hukuncinsa da na ji. ""Ina ganin kamar akwai hujja 15 da ke nuna hukuncin kuskure ne. ""Domin bai kamata a yi hukunci saɓanin wanda kotunan sama suka yi ba, wato Kotun Ƙoli da Kotun Ɗaukaka Ƙara, wadanda suka ce duk zaɓen da ɓangaren jiha ya yi, to ba shi da tasiri kuma ba shi da amfani,"" a cewar Farfesa Nasiru." https://www.bbc.com/hausa/articles/c72359r3v3yo +politics Rabi'u Kwankwaso: Tsohon gwamnan Kano ya bar PDP ya koma jam'iyyar NNPP "Tsohon gwamnan Jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bar jam'iyyar PDP zuwa ta NNPP. Sai dai dama tun a farkon watan nan na Maris Sanata Kwankwaso ya shaida wa BBC cewa a lokacin dai yana PDP amma ya soma tattauna wa da jam'iyyar NNPP domin sauya sheka zuwa can. Amma a ranar Talata 29 ga watan Maris tsohon gwamnan kuma tsohon ministan tsaro a kasar ya tabbatar da ficewarsa daga PDP zuwa sabuwar jam'iyya ta NNPP. A hirarsa da BBC a farkon watan Maris, jagoran kungiyar siyasa ta Kwankwasiyya ya ce a makwannin da suka gabata ne suka kaddamar da wata sabuwar kungiya mai suna 'The National Movement', bayan nan ne aka samar da jam'iyyar NNPP wato New Nigeria People Party ma'ana dai sabuwar Najeriya. A wata wasiƙa da ya aika wa shugaban mazaɓarsa, Kwankwaso ya rubuta cewa, ""Ina so na fara da miƙa godiyata ga shugaba da dukkan ƴan uwa da abokan arziki na mazaɓata, da ma faɗin Najeriya duka, kan irin kyakkyawar dangantakar da muka yi da su da kuma goyon bayan da suka ba ni a lokacin da nake PDP. ""Na rubuta wannan wasiƙa don shaida maka cewa sakamakon rashin haɗin kai da mabambantan ra'ayoyi da muka kasa warwarewa ya sa na yanke shawarar fita daga PDP, daga ranar Talata 29 ga watan Maris din 2022, na janye zamana a matsayin ɗan jam'iyyar PDP."" Tun da fari Kwankwaso ya ce, wannan sabuwar jam'iyya ce ta mutanen da suka amince cewa akwai bukatar tsarin da aka taho da shi daga shekarar 1999 a sauya shi a kawo abin da jama'a za su amfana. Ya ce akwai bukatar nazari kan abin da kasa za ta sauya sannan ta samu sabon alkibla, sai dai yana mai jaddada cewa har yanzu ya na nan a cikin jam'iyyar PDP bai fita daga cikinta ba. ''A yanzu maganar da ake yi ina cikin jam'iyyar PDP, tun wancan lokacin mun fara abin hawa-hawa. ""Abu na farko da muka fara yi shi ne ja baya daga tsarinta, tunanin wasu masu hankali za su zo a zauna a fada musu abin da ya dame mu amma jam'iyya ba ta yi ba, muka shiga kungiya nan ma ba a yi komai ba, to gamu a matakin jam'iyya." https://www.bbc.com/hausa/labarai-60918005 +politics 'Yan Najeriya na caccakar Femi Fani-Kayode kan komawa APC "Mamaki ya cika 'yan Najeriya da yawa bayan samun labarin sauya sheƙar da Femi Fani-Kayode ya yi daga jam'iyyar PDP zuwa ta APC mai mulki. Mutumin da 'yan kasar ke yi wa kallon wanda ya fi kowa adawa da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta APC mai mulki a kasar a yanzu ya koma inuwa guda da abokin gabarsa. Kalaman Femi wanda ake taƙaita sunansa da FFK, a baya sun rika faranta wa masu adawa da APC tare da muzanta wa gwamnati mai mulki da muƙarrabanta. Wannan shi ne babban labarin da ya mamaye fuskar jaridun Najeriya a ranar Juma'a, yayin da da yawan 'yan kasar a kafafen sada zumunta su ke ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu kan wannan batu. Wani abu da ya fi bai wa 'yan kasar mamaki ya sa suke caccakar FFK shi ne cewar dalilinsa na komawa APC si ne don ""Buhari ya sauya,"" a hirarsa da gidan talabijin na Channels a nara Alhamis, wato yana nufin ba Buharin da ya riƙa suka ba ne a baya. Daga cikin masu amfani da shafukan sada zumunta, wani matashi da ake kira Mr Right@OtunMuri cewa ya yi: ""Zan so in ji dalilan FKK na koma wa APC. Watakila akwai dalilan da ba mu sani ba. Watakila hauhawar kaya ta ragu zuwa kashi 1 cikin 100 ne, kuma an fara shawo kan matsalar rashin aikin yi, ba mamaki dala ta dawo naira 100. ""Watakila miƙa kan da 'yan Boko Haram suke yi da kawo karshen 'yan bindigar daji ne ya sanya shi komawa! Ina so in ji yadda zai rera wannan waƙar. Mayor of Jos @JonnieIledun kuma dauko wata maganar tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya yi, inda yake cewa ""FFK yarona ne. Ku ba shi abinci ya ci, zai ci sannan kuma ya yi muku waƙa."" Sai ya ƙara da cewa ya nuna cewa tabbas akwai yunwa a Najeriya, amma mene ne ya faru da jam'iyyar PDP? Ya sanya wani tsohon sakon da FKK ya wallafa a shafinsa na Twitter a 2018: ""Mutumin da kuke gani a yau Jibril ne daga Sudan ba Buhari ba, Buhari ya mutu kuma bai dawo daga Landan ba, jikinsa ne kawai. Sun ciro ruhin Jibril ne suka sanya a gangar jikin Buhari. ""Wannan wani abu ne da ya zama ruwan dare a wajen shaidanu, an sarayar da rayukan mutane da yawa."" Wani matashi mai suna @Real_Suleman ya sanya tsohon bayanin da FFK ya yi a 2019, lokacin da ya musanta labarin da aka rika yaɗawa cewa ya koma jam'iyyar APC. A jikin saƙon FKK ya ce ""Maganar da ake yada wa cewa na koma APC ba gaskiya ba ce, cin zarafi ne a wurina. Wadanda suke yaɗa wannan labarin ƙaryar sai su binne kansu a ƙasa don kunya. ""Da waɗannan abubuwan da muke gani na gwammace na mutu da na koma APC me kamar wani kwale-kwale da ke cike da beraye masu cututtuka."" Da yawan 'yan Najeriya na sharhi ne kan salon 'yan siyasar kasar. DUk da dai a kan ce siyasa ba da gaba ba, amma suna ganin a yani irin na FKK akwai daure kai da al'ajabi. Masu sharhi da dama ma cewa suke yi sun dawo daga rakiyar 'yan siyasa da ""rikita-rikitarsu"". Muhsin Ibrahim wani dan Najeriya kuma malami a Jami'ar Cologne da ke Jamus ya ce wallafa a shafinsa na Facebooj cewa: ""Femi Fani-Kayode ya koma APC? Bbau wani abin mamaki a nan, Ganin yadda abubuwa ke wakana a Najeriya a yau, ina shakkar idan har akwai wani abin da zai sake kada ni. Dukkanmu mun damu ne a kan abu daya: ta yaya za mu gyara miyarmu. Duk wani abu bayan haka, ko da batun gyran kasar ne a misali, to bayan wannan zai biyo ko ma mara amfani ake ganinsa. APC da FFK burinsu daya ne, kuma shi ne ci gaba da durkusar da kasar nan. Don haka, sun cimma yarjejeniya. Mafi yawanmu da muke sukar (APC & FFK) watalika muma ba za mu iya watsi da irin wannan damar ba in an ba mu. Wasu da yawa sun yi hakan a baya."" Shi ma Idiris Hamza Yana, malami a Jam'iar Kafin-Hausa a jihar Jigawa, kuma mai kartun digiri na uku a wata jami'a a Birtaniya ya wallafa a Facebook cewa: ""Ban yi mamaki ko jin takaicin komawar FFK zuwa jam'iyyar APC ba. A takaice ma, farin ciki na ji da hakan. ""Ga alama APC na neman wawan jam'iyya ne mai baki da zai dinga yi mata aikin caccakar manyan 'yan siyasar yankin kudu maso yamma. ""Shekarar 2023 za ta yi armashi."" Cikin 'yan Najeriya da ke bibiyar siyasar sau da kafa, komawar FFK APC bai zo muku da mamaki ba, saboda wasu alamomi da suka riƙa gani. Tun daga watan Agustan da ya gabata, ake ta ganin yadda FFK yake tashi fadin bibiyar mambobin jam'iyyar APC daga masu mukamansu har wadanda ba su rike da komai. Ga jerin sakonnin da yake wallafawa na nuna goyon baya ga wannan gwamnatin a yaƙin da take yi da 'yan tada kayar baya da masu satar mutane da 'yan bindiga. A ranar 16 ga watan Agusta, FFK ya wallafa cewa ya kai wa dan uwansa Sanata Ahmad Sani Yarima kuma tsohon gwamnan Zamfara ziyara gida inda zuka tattauna kan batutuwan da za su ciyar da Najeriya gaba. Sai a ranar 19 ga watan Agustan inda ya wallafa wasu hotuna na daurin auren dan gidan shugaban Najeriya Yusuf Muhammadu Buhari da aka yi a Kano. Ya ce sun tafi Kano daurin aure tare da 'yan uwa da abokan arziki kamar Gwamna Bello Matawalle na Jihar Zamfara da Gwamna Babagana Umar Zulum na Borno da Sanata Sani Ahmed Yarima da Sanata Ali Ndume da Ambasada Bashir Yuguda da Minista Isa Pantami da Mallam Nuhu Ribadu da dai sauransu. FFK ya sanya hotuna da bidiyon Gwamnan Zamfara Bello Matawalle a shafukansa masu yawa, a wasu wuraren suna cin abinci tare a wasu kuma ya kai masa ziyara Gusau babban birnin Jihar ta Zamfara, wanda wadannan duka abubuwa ne da ba kasafai ake gani ba a wurinsa. Ya ziyarci Jihar Filato domin tattaunawa da gwamnan jihar Simon Lalong, bayan samun rikicin da aka yi tsakanin mabiya addinin Muslunci da na Kirista. Ya ce maƙasudin ziyarar shi ne jajanta wa da kuma addu'ar neman zaman lafiya mai dorewa a jihar, wadda ake fama da dokar kulle a cikinta saboda rikicin. Abin bai tsaya iya nan ba, ya ci gaba da yabon wannan gwamnatin a fakaice, inda a wasu jerin sakonninsa da yake yi akai-akai a Twitter yake yabon sojojin Najeriya kan yakin da suke yi da kuma nasarar da ake ikirarin suna samu a Jihar Zamfara. ""Ku ci gaba da kutsawa yara, ku yake su da duka karfin da kuke da shi, muna gode muku saboda kwarin gwiwarku da kuma sadaukarwarku. Dukkan yabo ya tabbata da Allah."" Kwatsam sai a ranar Alhamis abin da ake jira ya faru ya faru, labarin komaway FFK APC, hotunansa suka baza ko ina a fadin ciki da wajen Najeriya. Jaridun ƙasar da dama sun rika yin babban labarinsu da cewa "" wanda ya fi sukar jam'iyyar APC mai mulki ya koma cikinta"". Wannan daya ne daga cikin kalaman FFK wadanda suka fi shahara kuma suka kara bunkasa lokacin da ake yi masa cin fuska bayan komawarsa jam'iyyar APC. ""Maganar da ake yada wa cewa na koma APC ba gaskiya ba ce, cin zarafi ne a wuri na. ""Wadanda suke yaɗa wannan labarin ƙaryar sai su binne kansu a ƙasa don kunya. Da waɗannan abubuwan da muke gani na gwammace na mutu da na koma APC me kamar wani kwale-kwale da ke cike da beraye masu cutuka,"" in ji FFK. Wasu da yawa na cewa tuni Femi ya goge wannan sako daga cikin jerin sakunansa da ya taba wallafawa. Wannan sakon na daga cikin wadanda suka janyo ce-ce-ku-ce a Najeriya a 2018, lokacin da shugaba Buhari ya tafi Landan domin a duba lafiyarsa. Femi ya rubuta cewa ""Mutumin da kuke gani a yau Jibril ne daga Sudan ba Buhari ba, Buhari ya mutu kuma bai dawo ba daga Landan, Jikinsa ne kawai. Sun ciro ruhin Jibril ne suka sanya a gangar jikin Buhari. Wannan wani abu ne da ya zama ruwan dare a wajen shaidanu, an sarayar da rayukan mutane da yawa."" Mafi yawan abubuwan da Femi Fani-Kayode ya rika yin tsokaci a kansu musamman na harkokin tsaro babu abin da ya sauya a cikinsu sai dai ta'azzara da suka yi, idan aka kwatanta da yadda al'amura suke a 2015 zuwa 2019 lokacin da aka ƙara zaban wannan gwamnati mai ci ta Najeriya. Tambayar da take zuwa cikin zukatan mutanen kasar a mafi yawan lokuta tun bayan samun labarain komawar FFK APC ita ce, shin al'amura ne suka sauya yadda yake fatan gani ko kuma me? An samu sauƙin rayuwa ne sama da a baya ko kuma adadin marasa ayyukanyi ya ragu a Najeriya? Shin akwai wani gagarumin abu da wannan gwamnati ta yi da ya janyo hankalin FFK ya koma jam'iyyar? Wadannan dai suke tambayoyin da har yanzu babu wanda yake da amsarsu. Ko da yake a irin wannan yanayin siyasar da ake yi a Najeriya ta neman abin sa wa a baka, ba ta aƙida ba, za a iya zawarcin FFK zuwa APC, ko kuma shi a raɗin kansa ya ji cewa gwara ya koma domin bayar da gudunmawarsa ta ciyar da Najeriya gaba, Tunda a yanzu ya ce ""Buhari ya sauya""." https://www.bbc.com/hausa/labarai-58594792 +politics Ƙusoshin APC sun ja daga tsakaninsu da Ganduje "A daidai lokacin da jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ke shirin gudanar da zaɓen shugabaninta a matakin jiha, bisa ga dukkan alamu wata babbar ɓaraka ta kunno kai tsakanin manyan ƴaƴan jam'iyyar a jihar Kano. Ɓarakar na da nasaba da zargin da jiga-jigan jam'iyyar suke yi wa gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje da yin babakere tare da yin gaban kansa wajen yanke hukunci a kan al'amuran da suka shafi jam'iyyar. A ranar Talata da daddare, wasu ƙusoshin jam'iyyar ciki har da tsofoffin gwamnan jihar ta Kano, Malam Ibrahim Shekarau da Sanata Kabiru Gaya da ɗan majalisar dattijai Sanata Barau Jibrin da ɗan majalisar wakilai, Sha'aban Sharada da wasu manyan ƴaƴan jam'iyyar suka gudanar da taro inda suka yanke shawarar cewa dole ne shugabancin jam'iyyar APC ya taka wa Gwamna Ganduje birki kafin lamura su dagule. Ɗaya daga cikin jagororin APC a Kano wanda yake cikin taron da aka yi a ranar Talata ya shaida wa BBC cewa sun yanke shawarar ganawa da shugaban riƙo na jam'iyyar APC na ƙasa, Gwamna Mai Mala Buni domin bayyana masa korafe-korafensu kafin lokacin ya ƙure. Bayanai sun nuna cewa a yammacin Laraba ne za a gudanar da taron tsakanin ƙusoshin APC na Kano da shugaban na riƙo. 'Ganduje ba ya tuntuɓar kowa' Jigon na APC ba ya son a bayyana sunansa har sai sun kammala taronsu da Gwamna Buni, kafin su fitar da sanarwar da za su bai wa manema labarai. Ya ƙara da cewa ""yadda Ganduje ke jagorancin APC a Kano, ba ya neman shawarar kowa. Shi kaɗai yake yanke hukunci ba ya neman shawara."" Ba wannan ba ne karon farko da jiga-jigan APC a Kano suke nuna ɗan yatsa tare da zargin gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje da yin babakere wajen rarraba muƙaman siyasa a jihar. Wasu majiyoyi sun ce ministan tsaro, Janar Salihu Magashi ritaya wanda bai halarci taron da aka yi ba a jiya, shi ma ya nuna goyon bayansa ga taron. Jim kaɗan bayan da aka gudanar da zaɓen shugabannin mazaɓu na APC a Kano a ƙarshen watan Yuli, wasu jiga-jigan APC suka bayyana cewa ba a bi ka'ida ba wajen gudanar da zaben. 'Martanin ɓangaren Ganduje' Shugaban riƙo na jam'iyyar APC a Kano, Alhaji Abdullahi Abbas ya shaida wa BBC cewa sun ji mamakin wannan taron da aka yi. Ya bayyana cewa su ba su da wata damuwa game da wannan taron kuma zaɓe za a yi a ƙarshen mako kuma duk wanda ya samu nasara za a ba shi dama ya ja ragamar jam'iyyar a matakin jiha. ""Jam'iyyar APC haɗaka ce, kuma kowanne ɓangare an ba shi muƙami daidai da su bisa adalci,"" in ji Abbas. Shugaban na riƙo ya ƙara da cewa sun ji mamaki yadda Malam Ibrahim Shekarau ya halarci taron da aka yi a ranar Talata. A watannin da suka wuce ma sai da wani ƙusa a jam'iyyar APC, Dan Balki Kwamanda ya caccaki salon jagorancin APC a Kano inda ya ce ba za su zura ido a dunga kama-karya ba a cikin jam'iyyar." https://www.bbc.com/hausa/labarai-58898958 +politics Abu 10 da aka ambato a zaman jin bahasin yi wa kundin tsarin mulkin Najeriya gyaran fuska "Batun yi wa kundin tsarin mulkin Najeriya gyaran fuska abu ne da har yanzu ke jan hankali a ƙasar, kodayake galibin masu tsokaci na ganin lokaci ya yi na sauya ko yin gwaskwarima ga kundin. Akasarin wadanda suka tafka muhawara da bayar da bahasi a zaman da majalisar dokoki ta shirya na kwana biyu a sassan kasar na son ganin an aiwatar da sauye-sauye a kundin 1999. Daga cikin manyan batutuwan da zaman ya mayar da hankali a kansu akwai maganar sakar wa ƙananan hukumomi da ɓangaren shari`a mara, akwai batun sake fasalin ƙasa da batun samar da ƴan sanda jihohi. Jihohin da aka yi wannan zama irinsu Kaduna da Asaba da Enugu da Akure, sun yce bai kamata a ce majalisa ce za ta jagoranci gudanar da sauye-sauyen ba, suna mai cewa taron zai kasance tamkar zaman shan shayi. Ga dai abubuwa 10 da suka biyo bayan zaman neman yi wa kundin tsarin mulkin Najeriya gyaran fuska: 1. An gaggauta shirya kundin tsarin mulki na 1999 - Gwamnan Delta Gwamnan Delta, Ifeanyi Okowa, ya ce samar da sabon kundin tsarin mulki yana da muhimmanci sosai la'akari da giɓin da aka bari a kundin 1999. Gwamnan ya nuna cewa an yi gaggawar samar da kundin tsarin mulki a 1999, kuma ko da an amince da kwaskwarimar akwai wasu gyare-gyare da ba lallai a sauya ba. 2. Kundin da ake bi a yanzu na taka rawa wajen neman wargaza Najeriya, in ji Afe Babalola Ɗaya daga cikin dattijan jihar Ekiti, wanda kuma ya samar da jami'ar Afe Babalola, Aare Afe Babalola, ya ce yunƙurin majalisa na yi wa kundin 1999 gyaran fuska ba zai yi tasiri ba. Ranar Laraba Babalola ya ce abin da ya kamata majalisa ta yi shi ne ""kiran taron ƙasa domin tattauna sabon kundin tsari da zai samar da tsarin gwamnati mai Firaiminista"". Sannan ya kuma ce, ""me zai hana majalisa ta kira zaɓen raba-gardama kan zaɓi tsakanin kundin 1999 da na 1963"". 3. Bukatar neman samar da sabon kundin mulki ƙoƙari ne na haifar da ruɗani - Ekweremadu A lokacin da yake jawabi, tsohon mataimakin shugaban majalisar dattijan Najeriya, Ike Ekweremadu, ya ce masu ruruta batun samar da sabon kundin tsarin mulkin Najeriya na neman haddasa rikici da ruɗani ne. Ekweremadu ya ce ya ji ana ta tafka muhawara; wasu na cewa a dawo da tsohon kundin tsarin mulkin 1960, wasu na cewa na 1963, wasu na yin na'am, to me ya sa ba za a watsar da su ba a kawo sabon kundi? ""Tambayar a nan ita ce ta yaya hakan zai samu? Babu wannan tsarin a kundi tsarin mulkin indai ba ruɗani ake son haifarwa ba,"" in ji Ekweremadu. 4. Gwamnatin tarayya na daukan nauyin da yafi ƙarfinta, in ji El-Rufai Masu ruwa da tsaki daga jihohi hudu na arewa maso yammacin Najeriya wato Kaduna da Katsina da Kano da Jigawa duk sun hallara a Kaduna domin ba da bahasinsu. Gwamnan Kaduna, Nasir El Rufai, ya ce rage karfin ikon gwamnatin tarayya na da muhimmanci saboda tsarin da ake bi a yanzu ayyuka sun yi wa gwamnatin tarayya yawa wanda hakan ke tasiri wajen ayyukanta. Gwamnan ya kuma ce ""ya kamata mu tantance irin yadda ya kamata tsaron ƙasarmu ya kasance da ci gabanta da kuma ci gaban al'ummarmu"". 5. Kundin 1963 shi ne mafi dacewa da Najeriya - Akeredolu Gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu na da ra'ayin cewa kamata ya yi a dawo da amfani da kundin tsarin mulkin 1963, wanda ke kunshe da tsarin federaliya na ƙwarai. Gwamnan ya soki kundin tsarin mulkin 1999, yana mai cewa akwai rashin dacewa kuma ya kamata a ce tuni an sauya shi. Sannan yana mai gargaɗin cewa gaɓar da ake a yanzu na neman yiwa kundin 1999 kwaskwarima ba batu ne da za a yiwa rikon sakainar kashi ba. Shi kuwa anasa ɓangaren gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu ya buƙaci a basu matsayi na musamman a tattalin arziki, yana mai cewa ci gaba da nasarorin da ake gani a Najeriya nada alaƙa da irin ci gaba da nasarorin da Legas ta samu. Gwamnan ya kuma goyi-bayan kafa rundunar ƴan sanda jihohi da kuma rungumar tsarin federaliya a Najeriya. Shugaban ƙungiyar ƙwadago Ayuba Wabba, ya jadada bukatunsu a fanin albashi mafi ƙanƙanta, kazalika ƙungiyar ma'aikatan ƙananan hukumomi ita ma ta gabatar da bukatunta ga kwamitin majalisar dattawan da ke zama a Kaduna, inda ta jadada buƙatar sakar ma ƙananan hukumomi mara. Hakazalika shugaban ƙungiyar CAN, Rev Steven Adegbite ya nemi bayyani kan kafa kotunan shari'a tunda kundin tsarin ya ce babu addini a jihohi. 8. Akwai buƙatar ƴan a-ware su rungumi sulhu - Yahaya Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bukaci masu neman ɓallewa su bai wa majalisa dama su gyara kura-kuran da ke cikin kundin 1999, yana mai cewa sulhu shi ne abu mafi dacewa. Yahaya da ke shaida haka a zaman arewa maso gabashi da ake yi a jiharsa, ya bukaci masu kalaman ƙiyayya su nesanta kansu da ambatar abubuwan da ke rura wutar rikici yana mai cewa sulhu shi ne mafi alheri ta hanyar fuskantar gyaran da ake bukata a kundin tsarin mulkin 1999. Sai dai Antoni-Janar kuma kwamisinan shar'a a Gombe, Zubair Umar, ya ce akwai rashin dacewa a ce jihohi na neman kafa rundunar ƴan sanda jiha saboda rashin kuɗaɗe. Kalaman kwamishinan akan adawa da kafa rundunar ya ja hankali tsakani masu sauraron yada ake karbar bahasi. Ya kuma ƙara da cewa ba sa goyon-bayan tsarin ne saboda matsalolin kudi da ake ciki a jihohi, wanda ba zai bada damar nuna goyon-baya ga kafa rundunar jiha ba. A jihar Sokoto kuma batun bai wa ɓangaren shari'a cikakken yanci da daidaiton jinsi da sake fasali da rawar da sarakunan gargajiya za su iya takawa su suka ja hankalin tattaunawar. 10. Gyaran kundin tsari ba zai kawo zaman lafiya ba, in ji Lalong Ana shi martani, gwamnan Plateau kuma shugaban ƙungiyar gwamnonin Arewa, Simon Lalong, ya ce haɗin-kan Najeriya ba shi da alaka da sauya kundin tsarin mulki ko da kuwa za a sauya kundin bil adadin. ""Inda ana son ganin c igaba da zaman lafiya da shugabanci mai kyau to dukkanin wadanan sun ta'alaka ne kan irin rawar da ƴan kasa ke takawa wajen amfani da biyayya ga kundin tsrain mulki, in ji Lalong. Gwamnan da ke shaida hakan a Plateau a sauraron bahashin tsakiyar Najeriya, ya ce kowanne ɗan ƙasa na da rawar da zai taka wajen mutuntawa da kare kudin tsarin mulkin ƙasa. A kan batun sake fasalin ƙasa, Lalong ya ce lokaci ya yi da ya kamata a fuskanci hakan da tabbatar da cewa kiraye-kirayen da zakuwar da ake nunawa an shawo kan su. A wannan Larabar aka kammala zaman karbar bahasin na kwanaki biyu da ke jin ra`ayoyin jama`a game da gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin kasar ke yi. Ana dai jima ana samun korafe-korafe kan wasu gyare-gyare da ake gani da jimawa ya kamata a aiwatar da su. Sai dai yayin da wasu ke maraba da wasu batutuwan da aka gabatar, akwai masu adawa da ganin yanzu ba lokaci ba ne na neman sauyi a kundin la'akari da wasu tarin batutuwan da ke addabar ƙasar." https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-57270232 +politics Rundunar sojin Najeriya ta yi watsi da zargin cin hanci da wasu jami’anta ke yi kan manyansu Rundunar sojin Najeriya ta yi watsi da wani zargi na cin hanci da rashawa da wasu sojojin kasar suke yi wa manyansu. Sojojin sun yi kukan cewa manyansu na cinye musu kudadensu na alawus, inda suka bukaci shugaba Buhari ya dauki mataki a kai, idan ba haka ba za su yi bore. Jami'an sun zargi manyansu da cinye musu kudadensu na alawus. Rundunar sojin ta bayyana cewa tana aiki ne da tsarin biyan albashi na bai-daya ta intanet da gwamnati ta fito da shi, kuma abin da take yi bashi da bambanci da wanda takwarorinta, da sojin sama da na ruwa ke yi, don haka a cewar rundunar babu yadda za a zalunci wani a karkashin tsarin. Wani abin da rundunar ta ce yana da tayar da hankali shi ne barazanar da kananan sojojin suka yi cewa za su yi yajin aiki idan ba a biya su hakkokinsu ba, alhali a irin wannan yajin aikin a aikin damara tamkar tawaye ne ko bore ga kasa. Wata sanarwar da daraktan hulda da jama`a na sojin kasan Najeriya, Birgediya-janar Onyema Nwachukwu ya sanya wa hannu ta ce zargin da sojojin ke yi ya nuna cewa sun jahilci yadda soji ke tafiyar da harkar kudi. Ya tabbatar da cewa ana zargin ne da nufin bata wa sojin kasa suna tare da sanyaya gwiwar dakarunta, wadanda ta ce sabon Hafsansu ya dawo da armashi da karsashin aikin a zukatan zaratan kasar sakamakon yadda ake biya musu hakkokinsu. Kazalika rundunar ta lura cewa sojojin sun yi zargin ne a cikin wata kurmar wasika, wadda suka aike wa shugaba Buhari ba tare da an rubuta sunayen masu ita ba, wadda hakan a cewar rundunar alama ce ta rashin gaskiya. Amma duk da haka, rundunar sojin ta ce za ta gudanar da bincike a kan lamarin. Kananan Sojojin dai sun rubuta budaddiyyar wasika ne zuwa ga shugaba Buhari, wadda a ciki suka zargi manyan sojin Najeriya da yi musu kwange, kuma sun kwana biyu suna kokawa amma shugaban kasar da sauran wadanda abin ya shafa basu ce komi ba. A cikin wasikar, sojojin suka ce kudadensu na alawus daban-daban ba sa shiga hannunsu…har ta kai ga su suke kukutawa su saya wa kansu takalma da sauran kayan damara. Sojojin sun bayyana cewa duk da cewa wasu na raina su ba don sadaukar da rayukansu da suke yi ba da komai ya cije a Najeriya. Sun yi gargadin cewa idan tura ta kai bango, har suka yi tawaye, to manyan sojojin da suke musu cogen za su rasa inda za su sa kansu da ƴaƴansu. Haka kuma za su rasa inda za su tsuguna su ci abin da suka tara. Sannan za su rasa hanyar da za su fice daga Najeriya. Babu wani martanin da ya fito daga fadar shugaban Najeriya dangane da wannan budaddiyar wasikar. https://www.bbc.com/hausa/labarai-61495056 +politics Ba halina ba ne ku yafe min - Sanata Abbo "Dan majalisar dattijan wanda bayanai suka ambato shi cike da nadama a taron manema labaran da ya yi cikin shalkwatar jam'iyyarsa ta PDP da ke Abuja, ya nemi gafara, kuma ya ce a yafe masa. Sanata Elisha Abbo, wanda ke wakiltar shiyyar arewacin jihar Adamawa, ya ce ""ba halina ba ne tozarta mata, don haka na yi nadama"". Faifan bidiyon dai ya tayar da kura da kuma janyo tofin Allah-tsine daga masu fafutuka da dumbin 'yan Najeriya har ma da fitattun 'yan siyasa musamman a shafukan sada zumunta. Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce ta fara gudanar da bincike kan zargin cin zarafin matar. Lamarin ya faru ne a wani shagon sayar da kayan wasannin jima'i da sanatan ya ziyarta tare da rakiyar wasu mata. A taron manema labaran da ya yi, Sanata Abbo ya ce ""Ba na zo nan ba ne don yin bayani kan abin da ya faru ta bangarena. Na zo ne don neman afuwar 'yan Najeriya saboda bata musu rayukan da na yi."" ""Cikin matukar nadama da sanin ciwon kai, ni Ishaku Abbo nake matukar neman gafarar duk 'yan Najeriya da majalisar dattijai da jam'iyyar PDP da iyalina da abokaina da kuma uwayenmu, matan Najeriya. Ni da kaina kuma ina neman afuwar Bibra[wacce ya ci zarafi], da danginta saboda abin da na yi. Duk ma dai abin da kika yi mini, ba ki cancanci irin wannan mataki ba, ki yi hakuri!"" In ji Matashin sanatan mai shekara 41. Bidiyon dan majalisar a shagon sayar da kayan wasannin jima'i da ke ikirarin nuna shi yana dukan mai tsaron kanti, ya janyo fushi da bacin rayuka. Mutane da dama ciki har da dan takarar shugaban kasa na baya-bayan nan a jam'iyyar PDP Atiku Abubakar suka bukaci a gurfanar da shi gaban hukunci tare da neman majalisar dattijai ta koya masa ladabi. A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Atiku ya ce kamata jam'iyyar PDP ta dauki matakin ladaftarwa a kan sanatan. ""Ina shawartarsa da ya fito fili ya nemi afuwa sannan ya mika kansa ga 'yan sanda domin ya nuna dattako. ""Sannan kuma ina kira ga uwar jam'iyyarmu ta PDP da ta dauki matakin ladaftarwa a kansa, su ma 'yan sanda su tabbatar cewa doka ta yi aikinta."" Afuwar da sanatan ya nema ta zo ne sa'o'i kadan bayan kiran da Atiku Abubakar ya yi masa na ya yi hakan. Rundunar 'yan sandan kasar ta alkawarta sanar da 'yan Najeriya sakamakon bincike da ta fara gudanarwa. Ita ma majalisar dattijan kasar ta kafa kwamiti domin ya binciki wannan batu a daidai lokacin da jam'iyyarsa ta PDP ta fito ta yi Alla-wadai da halayyar cin zarafin da ake zargin sanatan ya yi wa wannan mata mai shayarwa." https://www.bbc.com/hausa/48864149 +politics Gwamnonin PDP sun soki Buhari kan 'mayar da fadar shugaban ƙasa hedikwatar APC' "Gwamnonin jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya sun yi Allah-wadai da Shugaba Buhari kan abin da ta kira ""mayar da Fadar Shugaban Ƙasa ta Villa matsayin sabuwar hedikwatar jam'iyyar APC"", suna masu cewa ""ta 'yan Najeriya ce"". Gwamnonin 14 sun bayyana matsayarsu ne cikin wata sanarwar bayan taro da suka gudanar a Jihar Bauchi da ke arewacin ƙasar ranar Litinin game da halin da dimokuraɗiyya ke ciki a Najeriya da kuma sauran batutuwa. Mahalarta taron ƙarƙashin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na Jihar Sokoto, sun haɗa da Gwamnan Bauchi Bala Mohammed, da Gwamnan Abia Okezie Ikpeazu, da Udom Emmanuel na Akwa Ibom, da Douye Diri na Bayelsa, da Samuel Ortom na Benue. Sauran su ne: Ifeanyi Okowa na Delta, Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu, Nyesom Wike na Rivers, Oluseyi Makinde na Oyo, Ahmadu Umaru Fintiri na Adamawa, Godwin Obaseki na Edo, Darius Ishaku na Taraba. Sai kuma Mataimakin Gwmanan Zamfara Mahdi Mohammed. Baya ga maganar siyasa, gwamnonin sun bayyana matsaya kan sauran al'amuran da suka shafi ƙasa ciki har da matsalar tsaro. Ga biyar daga cikinsu: Shugabannin na PDP sun bayyana ƙarara cewa ba su amince da tsarin 'yar tinƙe ba a zaɓen fitar da gwani da gwamnati ke yunƙurin ""tilasta wa jam'iyyu aiwatarwa"" a cikin ƙudirin gyaran dokar zaɓe da ke gaban majalisa. ""Ganawar ta yi Allah-wadai da yunƙurin tallafa wa jam'iyyun siyasa tsarin zaɓen fitar da gwani na 'yar tinƙe a cikin Kundin Dokar Zaɓe,"" a cewarsu. ""Tsarin zai bayar da damar tafka maguɗi kamar yadda Shugaba Buhari ya samu ƙuri'a miliyan 15 a zaɓen fitar da gwani na APC a 2018 amma kuma ya samu miliyan 15 kacal a babban zaɓen 2019. PDP na ba da shawarar a ƙyale jam'iyyu su yanke hukunci kan ko suna son 'yar tinƙe ko kuma a'a."" Kazalika, zauren gwamnonin ya umarci dukkan 'yan Najeriya da su ""samar wa kansu makamin siyasa domin ceto Najeriya"". Suka ce: ""Gwamnonin PDP na umartar dukkan 'yan Najeriya da su yi amfani da damar yin rajistar zaɓe da ake gudanarwa ta yadda za su samu makamin ceto Najeriya daga gwamnatin APC."" Haka nan, jam'iyyar adawar ta zargi APC da bin ""salo na rashin gaskiya"" domin ""tilasta wa"" mambobinta su koma jam'iyyar mai mulki. ""Har wa yau, mun yi Allah-wadai da salo na rashin gaskiya da ake bi wajen tilasta wa gwamnonin PDP da sauran masu ruwa da tsaki don komawa APC, jam'iyyar da ta lalata tattalin arzikin Najeriya kuma ta mayar da ƙasar filin kashe-kashe da haifar da ƙunci da rashin iya mulki."" A ɓangaren tattalin arziki, gwamnonin sun shawarci gwamnatin tarayya ƙarƙashin jam'iyyar APC da ta haɗa kai da gwamnonin jiha domin rage rashin ayyukan yi ga matasa. ""Muna jaddada cewa a dakatar da magnganu na fatar baki game da tsarin sauƙaƙa hanyoyin kasuwanci yayin da zuba jari daga ƙasashen waje ke ci gaba da raguwa saboda wahalar da kamfanonin da ke son zuba jari a Najeriya."" Jam'iyyar ta nemi gwamnatin tarayya ta ƙara azama wajen haɓaka ɓangaren fasaha da sauran fannoni don samar da ayyukan yi. Da suke magana kan matsalolin tsaro da suka addabi Najeriya, gwamnonin sun ce ""lokaci ya yi na kawo ƙarshen ayyukan 'yan fashi da masu garkuwa da mutane da 'yan ta'adda"". Kazalika sun bayar da shawarar cewa ""a yi amfani da ƙarfin soja da hanyoyin gargajiya na warware rikici da fasahar tattara bayanan sirri da kuma siyasa don zaƙulo su [masu laifi]"". ""Fashi da garkuwa da mutane da ta'addanci ba hanyar neman kuɗi ba ce kamar yadda APC ke faɗa, manyan laifuka ne ga Najeriya da ke lalata tattalin arzikinmu da ilimi da kuma rayuwar yaranmu.""" https://www.bbc.com/hausa/labarai-57977414 +politics Mu'azu Magaji: 'Yan sanda sun kama tsohon Kwamishinan Ayyuka na Kano "Wasu 'yan sanda a Abuja, babban birnin Najeriya sun kama tsohon Kwamishinan Ayyuka na jihar Kano, Mu'azu Magaji. Lauyansa da kuma iyalansa sun tabbatar wa BBC cewa an kama tsohon Kwamishinan ne ranar Alhamis da daddare lokacin da yake kan hanyarsa ta komawa masaukinsa bayan ya gama harkokinsa na ranar. Lauyansa, Barrister Garzali Datti Ahmad, ya shaida wa BBC Hausa cewa suna zargin gwamnatin Kano ce ta tura 'yan sanda Abuja suka kama shi. Mu'azu Magaji, wanda ake yi wa lakabi da Ɗan Sarauniya, ya dade yana sukar gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje tun ma kafin a sauke shi daga kan mukaminsa. Tuni dai aka kai Injiniya Mu'azu zuwa hedikwatar ƴan sanda ta Kano kuma an gabatar wa lauyoyinsa tuhume-tuhumen da ake yi masa. Lauyansa, Barrista Garzali Datti Ahmad, ya shaida wa BBC Hausa cewa akwai tuhume-tuhume aƙalla huɗu zuwa biyar da ake yi masa kuma dukansu gwamnan Jihar Kano ne ke yi masa su. Barrista Garzali ya ce tuhuma ta farko da gwamnan Kano yake yi masa ita ce zargin da yake masa na ɓata masa suna. Haka kuma Barrista ya ce gwamnan Kano ya ce Injiniya Mu'azu Magaji yana zaginsa sannan yana kuma yana zarginsa da yin abubuwan da zai kawo taɓarɓarewar zaman lafiya. Haka kuma ya ce gwamnan na zarginsa da cin mutuncin iyalinsa. Barrista ya ce an kuma ɗauko wani hoto wanda aka nuna Gwamna Ganduje a zaune da kuma wata mace a tsaye inda aka alaƙanta hoton da Ɗan Sarauniya Yadda aka kama shi Barrister Garzali ya ce 'yan sandan sun kama Mu'azu Magaji ne bayan sun bi motarsa a guje suka suka jefa shi cikin kwatami. A cewarsa, daga nan ne tsohon Kwamishinan ya tsaya inda su kuma suka cakume shi suka jefa shi a cikin motarsu suka yi gaba. Ya kara da cewa siyasa ce ya ""sanya aka turo 'yan sanda daga jihar Kano har Abuja domin su kama shi tun da ka ga ba shi da wani tarihi na aikata laifi."" Barrister Garzali ya ce za su bibiyi lamarin da zummar daukar matakin shari'a, yana mai cewa ""ba za mu bari wani mutum da yake ganin ya isa ba ya karya doka kuma a kyale shi."" Dama dai tsohon Kwamishinan ya yi fice wajen caccakar Gwamna Ganduje, musamman bayan da tsohon gwamnan Kano Sanata Ibrahim Shekarau da wasu 'yan majalisar dokoki sun balle daga jam'iyyar APC mai mulkin jihar suka kafa nasu tsagin da suka kira G-7. Kazalika Mu'azu Magaji ya sha wallafa sakonni a shafinsa na Facebook inda yake cacakar gwamnatin Ganduje, wadda ya bayyana a matsayin wacce ba ta da alkibla. A baya dai, Gwamna Ganduje, ya dakatar da tsohon Kwamishinan daga aiki bayan ya wallafa wasu sakonni da ake gani na murna ne da mutuwar Malam Abba Kyari, shugaban ma'aikatan fadar shugaban Najeriya sakamakon cutar korona. Sai dai Mu'azu Magaji ya sha cewa ba murna ya yi da mutuwar Malam Kyari ba." https://www.bbc.com/hausa/labarai-60154544 +politics Abubuwa biyar da gwamnatin Amurka ta ce game da matsalolin Najeriya "Gwamnatin Amurka ta fitar da rahotonta na shekara kan ayyukan haƙƙin ɗan Adam na ƙasashe ciki har da Najeriya. Rahoton na shekarar 2021 ya taɓo batutuwa da dama a Najeriya da suka shafi matsalar tsaro da yaƙi da rashawa da keta ƴancin ɗan adam da fararen hula da siyasa da ƴancin ma'aikata. Rahoton ya kuma yi nazari kan rikice-rikice a Najeriya da kashe-kashe da satar mutane da ƙuntatawa fararen hula da kuma shamaki ga ƴancin faɗin albarkacin baki da samun bayanai ga ƴan jarida. Wasu daga cikin batutuwan da ke ƙunshe a rahoton sun haɗa da: Rahoton ya ce hare-haren Boko Haram da Iswap sun ci gaba a yankin arewa maso gabashi. Mayaƙan sun ci gaba da kai hare-hare kan gwamnati da fararen hula wanda ya kai ga rasa rayuwakn dubban mutane da jikkata wasu da dama. Hare-haren a cewar rahoton sun raba mutum sama da miliyan uku da gidajensu tare da mayar da mutum kimanin 327,000 yin gudun hijira zuwa ƙasashe makwabta. A yankin arewa maso yammaci, ƴan bindiga sun ci gaba da zama barazana a sassan yankin. Tsarinsu ya shafi satar mutane domin kuɗin fansa inda suke kai farmaki a makarantu. Rahoton ya kuma ce akwai rahotannin cewa gwamnati ko jami'anta sun aikata kisa ba bisa ka'ida ba. A cewar rahoton a wasu lokuta hukumomi na bincike da kuma ɗaukar mataki kan ƴan sanda da sojoji ko wasu jami'an tsaro da ke da alhakin yin amfani da ƙarfin da ya wuce kima ko kuma mutuwar mutanen da ake tsare da su. ""Misalin kashe-kashen ba bisa ka'ida ba na sojoji da na sama, da na ruwa, da farko ana gudanar da bincike ta hanyar kwamandojin jami'an waɗanda za su yanke hukunci ko tuhumar da ta dace da su, ko kuma fara shari'ar kotunan soji, wadanda za a iya daukaka kara a kotunan ɗaukaka ƙara na fararen hula,"" in ji rahoton. Rahoton ya ce saboda girman ƙalubalen matsalar tsaro ya sa wasu gwamnatocin jihohi suka samar da nasu jami'an tsaro, waɗanda gwamnati ke iko da su. Sannan akwai rahotannin da ke cewa jami'an tsaron sun aikata cin zarafi da dama. Rahoton ya ambato alƙalumman hukumar agaji ta Red Cross da suka nuna cewa sama da mutum 24,000 suka ɓace a Najeriya, yawancinsu a yankin arewa maso gabashi da ke fama da rikici. Rahoton ya kuma ambato alkalumman ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Amnesty International da ta ce an kama wasu da ake zargin mambobin ƙungiyar IPOB guda 50 da har yanzu ba san inda suke ba tsakanin wtaan Oktoba zuwa Nuwamban 2020. Rahoton ya ce kuma ƴan bindiga sun saci fararen hula da dama a sassan ƙasar musamman a yankunan arewa maso yammaci da tsakiya. Hanyar Kaduna Abuja ta zama tarkon ƴan bindiga, a cewar rahoton. Rahoton ya ce satar mutane ta zama ruwan dare a yankin Neja Delta, tare da ambato wani rahoton wata kungiyr sa-kai da ta ce Yan Boko Haram da Iswap sun saci mutum 2,000 da har yanzu ba a san makomar su ba. ""Cin hanci da rashawa ya yaɗu kuma ya shafi dukkan matakan gwamnati da suka haɗa da ɓangaren shari'a da na tsaro,"" a cewar rahoton. Duk da yaki da cin hanci da rashawa na daga cikin manyan manufofin gwamnati mai ci ta shugaba Buhari, amma rahoton ya ce har yanzu rashawa ta yi katutu a hukumomin gwamnati. ""Kundin tsarin mulki ya bayar da kariya ga shugaban ƙasa da mataimakin shugaban ƙasa da gwamnoni da mataimakansu amma akwai zarge-zargen rashawa a gwamnati,"" a cewar rahoton. Rahoton ya ce duk da hukumomin yaki da cin hanci da rashawa na ICPC da EFCC sun kama tare da gurfanar da jami'an gwamnati amma tsaikun tsarin shari'a ya hana zartar masu da hukunci. Rahoton ya ce akwai ƙarancin bincike da hukunta masu cin zarafin jinsi da cin zarafi ta hanyar lalata da auren wuri da yi wa mata kaciya. Wata ƙungiya mai rajin tabbatar da ƴanci ga kowa a cewar rahoton ta ce a 2021 ƴan madigo da luwaɗi sun bayar da rahoton ƙyama da barazana ga rayuwarsu, kamar yadda wata Ƙungiyar ta ce ta tattara bayanai na cin zarafi 520 da ya shafi jinsi ɗaya a shekarar. Dokar Najeriya ta ƙungiyar ɗaurin shekara 14 ga masu auren jinsi ɗaya. Rahoton ya ce a wasu jihohin Najeriya da ke Shari'ar Musulunci, dokar ta shafi hukuncin kisa ta hanyar jifa. Sai dai rahoton ya ce a 2021 kotunan shari'a ba su zartar da hukuncin ba, amma a watan Yuli a Kano Hukumar Hisba ta kama wasu mutum biyar da ake zargi sun yi luwaɗi. Rahoton ya ce duk kundin tsarin mulki ya bayar da ƴancin faɗin albarkacin baki wanda ya shafi ƴan jarida, amma a wani lokaci gwamnati ta takaita ƴancin. A cewar rahoton na Amurka akwai rahotanni da suka bayyana cewa gwamnati ta hana ƴancin fadin albarkacin baki, musamman a jihar Kano da aka kama wasu kan zargin yin ɓatanci ga addini, wanda wasu da ake adawa suka ce hana ƴancin fadin albarkacin baki ne. Rahoton ya kuma bayar da misali da watan Yuli da wata babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta takaita yawan ƴan jaridar da za su shiga sauraren shari'ar jagoran Biafra Nnamdi Kanu saboda matakai na tsaro da annobar korona, wanda wasu kafofin yaɗa labarai suka nuna cewa hana su ƴancinsu ne na samun bayanai. Rahoton ya kuma bayar da misali da hirar BBC Hausa a watan Maris game da barazanar gwamnatin Kano kan ɗan jarida Jaafar Jaafar da ya saki wau jerin bidiyo da ke zargin gwamnan jihar Abdullahi Ganduje yana karbar cin hanci. Sai dai kawo yanzu gwamnatin Najeriya ba ta mayar da martani ba game da rahoton. Mun yi kokarin ji ta bakin wasu daga cikin jami'an gwamnatin kasar amma kawo yanzu bamu yi nasara ba." https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-61088512 +politics Ga jerin 'yan takarar shugaban ƙasa a Najeriya na 2023 "Dukkan jam'iyyun siyasa a Najeriya sun kammala zaɓukan fitar da gwani daga ranar Alhamis,9 ga watan Yunin 2022 kamar yadda hukumar zaɓe ta INEC ta umarce su don fitar da 'yan takarar da za su fafata a babban zaɓe na Fabarairun 2023. Tuni APC mai mulki ta zaɓi tsohon Gwamnan Legas Bola Ahmed Tinubu a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa, inda ita kuma babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta zaɓi Atiku Abubakar. Ga jerin sunayen 'yan takarar shugaban ƙasa da za su yi wa jam'iyyu daban-daban takara a babban zaɓen. Jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ta gudanar da babban taronta a filin wasa na Moshood Abiola da ke Abuja, kuma a can ne ta sanar da zaɓen tsohon Gwamnan Kano Ranbiu Musa Kwankwaso a matsayin ɗan takararta na shugban ƙasa. Tsohon gwamnan da ya mulki Kano shekara takwas, ya kuma wakilci Mazaɓar Kano ta Tsakiya a Majalisar Dattawan Najeriya daga 2015 zuwa 2019. Kwankwaso ya kuma riƙe ministan tsaro a gwamnatin Shugaba Olusegun Obasanjo. Wannan ne karon farko da Kwankwaso zai yi takarar shugaban ƙasa bayan ya kasa samun takarar a jam'iyyar APC a zaɓen 2015. Yayin zaɓen fitar da gwanin da ta gudanar a dandalin Eagle Square da ke Abuja, jam'iyyar All Progressive Congress (APC mai mulkin Najeriya ta zaɓi Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa. Tsohon gwamnan Legas tsawon shekara takwas, Tinubu ya kuma yi sanata a gajeriyar jamhuriyar siyasa ta uku da ba ta yi tsayi ba. Ya doke 'yan takara 13 kafin ya samu ƙuri'u mafiya yawa a zaɓen. Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar ne ya lashe zaɓen fitar da gwani na ɗan takarar shugaban ƙasa a babbar jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP). Zaɓen 2023 ne zai zama karo na shida da Atiku ke neman yin takarar shugaban ƙasa bayan ya fara neman takarar a 1993, duk da cewa bai yi nasara ba a jam'iyyarsa. Haifaffen Jihar Adamawa kuma ɗan kasuwa, Atiku ya yi takarar shugaban ƙasa a zaɓukan shugaban ƙasa na 2007, da 2011, da 2019. Tsohon Gwamnan Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya, Peter Obi ya zama ɗan takarar jam'iyyar Labour Party (LP) bayan ta gudanar da babban taronta a garin Asaba na Jihar Delta a watan da ya gabata. Farfesa Pat Utomi ya janye wa Obi yayin zaɓen, yana mai cewa ya (Obi) cancanci ya shugabanci Najeriya. Obi ya bar jam'iyyar PDP a watan da ya gabata - wadda ya yi wa takara a matsayin mataimakin shugaban ƙasa a 2019 - kuma wannan ne karon farko da zai yi takarar shugaban ƙasar. Jam'iyyar Africa Action Congress (AAC) ta zaɓi mawallafin jaridar intanet ta Sahara Reporters, Omoyele Sowore, a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa. Wannan ne karo na biyu da Sowore zai yi nemi kujerar bayan ya sha kaye a hannun Shugaba Muhammadu Buhari a zaɓen 2019 a AAC. An taɓa kamawa tare da tsare ɗan gwagwarmyar da ke jagorantar zanga-zangar Revolution Now a faɗin Najeriya, kafin daga baya kotu ta ba da belinsa. Prince Malik Ado-Ibrahim (YPP) (Yarima) Prince Malik ya zama ɗn takarar Young Progressive Party (YPP) ne bayan ya doke sauran 'yan takara a zaɓen fitar da gwani da ta gudanar a Abuja. A cewar tarihinsa da aka wallafa a shafin Wikipedia, ɗan asalin Jihar Kogi ne kuma ɗa ga attajirin ɗan kasuwa na Ebira, Ohinoyi, wanda ya kafa kamfanin makamashi na Formula One team Arrows A20. Auren da ya yi na Adama Indimi a 2020 ya jawo ce-ce-ku-ce a shafukan zumunta na Najeriya. An sanar da (Yarima) Prince Adewole Adebayo a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na Social Democratic Party (SDP) bayan taron da ta yi a Abuja. Lauya kuma mamallakin gidan talabijin na KAFTAN Television, Adebayo ya doke mace 'yar takara, Khadija Lamidi kafin ya lashe zaɓen. Yariman ya ce ""lokaci ya yi da matasa za su mulki Najeriya kuma zan je kowane lungu na ƙasar don neman ƙuri'u"". Babban ɗa ga shahararren ɗan kasuwa kuma ɗan siyasa Moshood Abiola, Kola ne ya lashe zaɓen fitar da gwani na Peoples Redemption Party (PRP) don yi wa jam'iyyar takarar shugaban ƙasa. Kamar mahaifinsa, Kola ɗan kasuwa ne kuma ya doke tsohon shugaban Bankin Arewa (Bank of The North) Falalu Bello a zaɓen. Ba wannan ne karon farko da Kola mai shekara 59 ke shiga siyasa ba. Al-Mustapha ne tsohon babban jami'in tsaro na tsohon shugaban ƙasa na mulkin soja, Sani Abacha, kuma shi ne ya lashe zaɓen fitar da gwani na Action Alliance. Al-Mustapha wanda ya shafe shekara fiye da 10 a gidan yari bayan rasuwar Abacha, ya doke abokin takararsa ɗaya tilo Samson Odupitan. Tsohon sojan mai muƙamin manjo, haifaffen Jihar Yobe ne kuma wannan ne karo na biyu da zai yi takarar shugaban ƙasa. Farfesa Christopher Imumulen (AP) Christopher Imumulen ne ya lashe zaɓen fitar da gwani na Accord Party (AP) bayan daliget sun zaɓe shi a babban taron jam'iyyar. Farfesan mai shekara 39 ya fara aiki ne a matsayin injiniya a kamfanin BOC Gases Nigeria Limited tun a 2005. A cewar bayan tarihinsa, Christopher na da digirin digirgiri biyu a fannin injiniyanci da kuma koyarwa. Lashe zaɓen da mamallakin gidan talabijin na Roots Television ya yi na African Democratic Congress (ADC) ya jawo kanun labarai iri-iri bayan ya doke Kingsley Moghalu a zaɓen. Mista Kachikwu ya samu ƙuri'a 978 da ya doke tsohon mataimakin gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) a zaɓen fitar da gwani da aka yi a Jihar Ogun. Allied Peoples Movement (APM) ta gudanar da zaɓen fitar da gwaninta a Abuja, inda ta zaɓi shugabanta Yusuf Mamman a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa. SHi kaɗai ne ya nuna sha'awar yin takarar kuma nan take sauran mambobin jam'iyyar suka zaɓi mai kamfanin Almat Farms don shiga zaɓen na 2023. Tsohon Alƙalin Alƙalai na Jihar Anambra, Peter Umaedi ne ya lashe zaɓen All Progressive Grand Alliance (APGA). Mista Peter ne kaɗai ya nuna sha'awar yin takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar. Okudili Anyajike ne ya lashe zaɓen fitar da gwani na National Rescue Movement da ta gudanar a Abuja. Ɗan kasuwar ya samu ƙuri'a 180 don doke abokin takararsa Farfesa Benedicta Egbo, wanda ya samu 30. Za mu ci gaba da sabunta wannan shafi idan akwai sabon bayani..." https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-61813380 +politics Buba Galadima: 'Ban san lokacin da aka haife ni ba' "A shirin Amsoshin Takardunku na karshen makon jiya, wani mai sauraronmu Jamilu Muhammad Haruna ya bukaci sanin tarihin fitaccen dan siyasar nan a Najeriya, Buba Galadima. Kuma BBC ta tuntubi Buba Galadima inda ya ba da tarihinsa. Wane ne Buba Galadima? Buba Galadima wanda dan siyasa ne, ya ce ba shi da tabbacin shekarun da aka haife shi sai dai ya bayyana cewa ""ya kamata a ce ina da shekara 72 ko 73."" Ya fara makaranta a wani kauye da ake kira Bizzi a shekarar 1959. A 1961 kuma ya koma Gashua inda ya kammala karatu a 1965 sannan ya tafi makarantar sakandare ta Provincial da ke Maiduguri a jihar Borno a 1966 zuwa 1970. Daga nan ya je jami'ar Ahmadu Bello inda ya yi karatu a makarantar share fage (School of Basic Studies) inda ya fara rike shugabancin shugaban dalibai na makarantar. ""Tun daga aji daya na fara siyasa. Allah ya dora mani shugabanci tun ina karami,"" a cewar Buba Galadima. Ya yi karatun digirinsa na farko a fannin injiniya na gine-ginen gidaje da hanya a shekarar 1975. Ya ce daga nan ""bai ci gaba da karaunsa ba amma ya je kwasa-kwasai a kasashen waje."" Buba Galadima ya shiga siyasa ne a 1978 ba tare da ya bar aiki ba a lokacin. A cewarsa ""ni kadai ne a jihar Borno wanda ya kawo mamba na dan majalisar wakilai na mazabarsa a zamanin NPN"" kuma wannan ne dalilin da ya sa ""aka bayar da sunansa domin zama minista daga jihar Borno."" ""Na yi shugabancin samari na jam'iyyar NPN na kasa ina da shekara 27 zuwa 28,"" in ji shi. Buba Galadima ya kara da cewa ""Na kafa wata jam'iyya ni da Alhaji Abba Dabo wadda muka sanya wa suna ANC a lokacin Abacha."" Ya kara da cewa kafin lokacin Abacha an yi jam'iyyar NRC kuma ""ni ne sakataren kudi na jam'iyyar."" Buba Galadima ya ce ""ba ni da mai gida a harkar siyasa. Kullum gashin kai na nake ci, a tsaye nake a kan kafata domin ina da ra'ayi kan duk wani abu na rayuwa."" ""A Najeriya, idan kana da mai gida ba ka da ra'ayi sai na mai gidanka. Wannan ita ce babbar matsalata a zama wani abu a siyasar Najeriya,"" kamar yadda Buba Galadima ya bayyana. ""Ina daya daga cikin mutumin da ya ba da miliyan daya na farko domin kafa jam'iyyar APP. Dan uwana Alhaji Umaru Shinkafi kuma yana daya daga cikin fitilun jam'iyyar APP har ta koma ANPP."" A cewar Buba Galadima kasancewarsa mai ra'ayi a kan duk wani batu ne ya sa ba shi da farin jini wajen shugabanni a Najeriya. Ya kara da cewa ""Dukkan mutumin da ba zai kwantar da kai idan an ce masa Allah 10 ne ya ce eh ba, toh ba zai samu farin jini a wajen shugabanni irin na Najeriya ba."" Buba Galadima ya bayyana cewa ""an tuhume ni ko kulle ni ko ja mani kunne ko an sa mani ankwa an sa ni a karkashin kasa sau 38."" Ya ce an fara kulle shi a 1984 a zamanin mulkin soja na Shugaba Buhari. Buhari na daya daga cikin mutanen da nake ganin girmansu a ido na. Mun fara mu'amala da shi tun yana gwamnan Borno, amma ""shi ba zai iya tunawa ba amma ni da yake ina karamin jami'i zan iya tunawa."" Buba Galadima ya ce sun fara harkar siyasa da Buhari tun shekarar 2002 bayan Buharin ya shiga jam'iyyar APP a lokacin." https://www.bbc.com/hausa/labarai-51018861 +politics PDP ce uwar siyasa ina nan a jam'iyyar - Yakubu Mohammed "Daya daga cikin fitattun masu shirya fina-finan Hausa kuma mawaki a Najeriya Yakubu Mohammed ya ce har gobe yana jam'iyyar PDP. Jarumin ya bayyana haka ne a hirar da BBC ta yi da shi a Instagram ranar Laraba, inda ya ya tabo batutuwa da dama da suka shafi nasarorinsa a harakarsa ta fim da waka da kuma alakarsa da abokan sana'arsa. Yakubu Mohammed ya ce tun da ya fara siyasa jam'iyyar PDP yake goyon baya. ""Tun farko da ita na fara kuma har yanzu ina PDP,"" in ji shi. Ya kare dalilinsa na goyon bayan jam'iyyar mai hamayya a Najeriya inda ya ce sun yi wa jam'iyyar ayyuka da dama, wanda shi ne ya ja ra'ayinsa, kuma ita ce uwar siyasa kuma tsohuwar jam'iyya, a cewarsa. Ya kuma ce duk da ya yi wa jam'iyyar wakokin siyasa, amma kasancewarsa jekadan hukumar zabe mai zaman kanta INEC shi ya sa bai cika yin wakokin siyasa ba kada ya nuna ra'ayinsa. ""Wannan ra'ayi na ne ba zan yi wani abu ba har na fito da abin da ke rai na a fili."" Jarumin ya kuma ce ba ya da uban gida a Kannywood, shi ne uban gidan kansa amma yana da abokan arziki. Duk da amintaka da shakuwa da ake ganin tsakaninsa da Sani Danja, amma ya ce Ibrahim Mandawari ne ya fi burge sa a harakar fim." https://www.bbc.com/hausa/labarai-53002645 +politics Zaɓen Anambra: Tarihin sabon gwamna Charles Chukwuma Soludo A yau Alhamis ne aka rantsar da zaɓaɓɓen Gwamnan Anambra Farfesa Charles Chukwuma Soludo bayan ya yi nasara a zaben da aka gudanar a watan Nuwamban 2021. Mun yi nazari kan tarihinsa. Soludo ba baƙo ba ne a harkokin mulki bayan ya shafe shekara biyar a matsayin gwamnan Babban Bankin Najeriya na CBN. Farfesa Soludo ya riƙe muƙamin gwamnan CBN daga 29 ga watan Mayun 2004 zuwa 29 ga Mayun 2009. An haife shi ranar 28 ga watan Yuli, 1960, a Ƙaramar Hukumar Aguata ta Jihar Anambra. A ranar 23 ga watan Yuni ne aka bayyana Farfesa Soludo a matsayin ɗan takarar APGA sannan kuma gwamna mai-ci Willie Obiano ya ba shi tutar takara ranar 25 ga Satumba. Bayan kammala karatunsa na sakandare, ya wuce Jami'ar Najeriya da ke Nsukka, inda ya kammala digirinsa na farko a fannin tattalin arziki da daraja mafi girma. Ya kuma yi digirinsa na biyu da na digirgir a fannin tattalin arziki a jami'ar ta Nsukka. Farfesa Soludo ya samu horo na shekara huɗu na gaba da digiri a wasu manyan cibiyoyi na duniya, ciki har da: Cibiyar Brookings da ke Washington, DC; Jami'ar Cambridge da ke Birtaniya; Damar ƙaro karatu a Smuts Research Fellow; Damar ƙaro karatu a Kwalejin Wolfson. Sauran wuraren da zaɓaɓɓen gwamnan ya je sun haɗa da; Hukumar Tattalin Arziki ta Majalisar Ɗinkin Duniya a Afirka; Jami'ar Warwick a matsayin Masanin Bincike mai Ziyara a Cibiyar Tattalin Arzikin Afirka; Jami'ar Oxford (tare da tallafin kwamitin Rhodes). Ya kuma halarci kwasa-kwasai na musamman sama da 12 kuma ya yi aikin bincike da koyarwa da tuntuɓar juna a ɓangarori daban-daban na tattalin arziki. Ya yi aiki a Bankin Duniya a matsayin mai bayar da shawara na gajere da dogon zango a 1993 da kuma a Hukumar Tattalin Arziki ta Majalisar Dinkin Duniya na Afirka a birnin Addis Ababa. Kazalika, ya yi aikin mai ba da shawara ga hukumomin; UNCTAD; Tarayyar Turai (EU); Ƙungiyar Haɗin Kan Tattalin Arziƙi da Ci Gaba (OECD); Majalisar Dinkin Duniya (MDD) New York; Hukumar Raya Kasashe ta Amurka (USAID); Bankin Raya Afirka (AfDB); Kasuwar gama-gari na Gabashi da Kudancin Afirka (COMESA); Tarayyar Afirka (AU); Majalisar Binciken Ci gaban Ƙasashen Duniya (IDRC) Canada; Majalisar Ci gaban Nazarin Kimiyyar zamantakewa a Afirka (CODESRIA); Kungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS); da sauransu. Farfesa Soludo ya yi aiki a matsayin mai ba da shawara da kuma masanin mai ziyara a hukumar ba da lamuni ta duniya (IMF) a 1994, sannan kuma ya koyar da darasin tsare-tsare na IMF ga manyan ma'aikatan Babban Bankin Afirka ta Yamma da sauran yankuna masu tasowa. Ya yi aiki a matsayin: Memba, kwamitocin fasaha waɗanda suka tsara manufofin tattalin arziki da kasuwanci ga gwamnatin tarayyar Najeriya; da Babban Darakta na Cibiyar Nazarin Tattalin Arziki ta Afirka (AlAE). Farfesa Soludo ya shiga gwamnatin tarayyar Najeriya ne a watan Yulin 2003 a matsayin mai bai wa shugaba Obasanjo shawara kan tattalin arziki da kuma shugaban hukumar tsare-tsare ta kasa (NPC). Ya kasance shugaban tawagar da ta tsara shirin gyara tattalin arziki da zamantakewar Najeriya (2003-2007), National Economic Empowerment and Development Strategy (NEEDS), sannan kuma ya jagoranci tsare-tsare na hadin gwiwa kan tsarin tarayyar Najeriya ta hanyar taimaka wa gwamnatin jihohi wajen tsara dabarun bunkasa tattalin arzikinsu (SEEDS). A matsayinsa na Gwamnan Babban Bankin Najeriya daga watan Mayun 2004, Farfesa Soludo ya sake mayar da Babban Bankin a matsayin hukumar kudi mai inganci kuma ya samu nasarar aiwatar da wani muhimmin tsari wanda ya kai ga kyautata tsarin bankin Najeriya wanda ba a taba yin irinsa ba. A saboda haka ne aka bayyana tsarin bankin Najeriya a matsayin wanda ya fi girma a Afirka ɗaya daga cikin mafi girma a duniya. Ya kuma yi nasarar kafa hukumar hada-hadar kudi ta Afirka (AFC), wato bankunan nahiya masu zaman kansu kuma na zuba jari. Shi ne kan gaba a shirin inganta tsarin dabarun hada-hadar kudi na 2020 (FSS 2020), tsarin da zai bunkasa tsarin hada-hadar kudi na Najeriya don zama cibiyar hada-hadar kudi ta Afirka da kuma fitar da tattalin arzikin Najeriya cikin jerin kasashe 20 masu karfin tattalin arziki na duniya zuwa shekarar 2020. Farfesa Soludo ya samu lambobin yabo daga ƙungiyoyin jama'a da na masu zaman kansu da na addini da na sana'a da na ɗalibai da jami'o'i da sauransu. Jaridar Financial Times ta Landan ta bayyana shi a matsayi na musamman mai laƙabin 'Ita Great Reformer'. Mamba ne na Ƙungiyar Ba da Shawara ta Duniya, UK-DFID; mamba na Babban Mashawarcin Masana Tattalin Arziki na Bankin Duniya da Ƙungiyar Ba da Shawarwari ta Ƙasashen Duniya na Ma'aikatar Raya Ƙasa ta Burtaniya (DFID). Farfesa Soludo na da riƙe da lambar yabo ta gwamnatin tarayyara Najeriya, Commander of the Order of the Federal Republic (CFR). Farfesa Soludo ya auri Nonye kuma sun samu albarkar yara. https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-59198854 +politics Bauchi: Kaura na zargin Isa Yuguda da M.A da salwantar da tiriliyan daya "Kwamitin da gwamnatin jihar Bauchi da ke Najeriya ta kafa domin bin diddigi da karbo kadarorin gwamnati da ake zargin an wawure, ya yi zargin cewa an salwantar da kudi fiye da naira tiriliyan daya. Kwamitin ya ce a zamanin tsofofin gwamnonin jihar biyu wato Malam Isa Yuguda da kuma Barista Muhammad Abdullahi Abubakar ne kudaden suka salwanta. Mutanen biyu sun yi mulki a lokuta daban-daban daga 2007 zuwa 2019. Kwamitin ya ce ko da yake ya yi nasarar karbo motoci masu yawan gaske da wasu kadarori, to amma har yanzu ya kasa bambaro fiye da naira tiriliyan daya daga gwamnatocin biyu da suka shude. Tsofofin gwamnoni biyu, Isa Yuguda da Muhammad Abdullahi Abubakar ne suka jagoranci gwamnatin jihar daga 2007 zuwa 2019. Don haka kwamitin ke bukatar tsofaffin jami'an gwamnatin su maido kudaden da ake zargin sun wawure. Malam Musa Azare shi ne mataimakin kakakin kwamitin, ya yi bayani kan abin ta'ajibi da suka bankado yayin aikinsu na watanni takwas. ""Akwai abubuwa da dama da muka gano daga kwangiloli da aka bayar da su."" Ya kara da cewa: ""Ko dai an bayar da su amma ba a yi ba bayan an fitar da kudadensu, ko kuma an yi su rabi-da-rabi. Ko ma an bayar da su kan kudaden da ake zargin sun yi yawa."" Ya ce sun kira 'yan kwangilan da suka aiwatar da wadannan ayyukan domin su gano ainihin gaskiyar lamarin. ""Wasunsu sun amsa kiran kuma sakamakon bayanan da suka bayar ne ma aka saka cikin wannan rahoton binciken,"" in ji shi. Cikin wadanda kwamitin ya kara har da wasu jami'an gwamnatocin da suka gabaci wannan. Gwamnatocin biyu da suka shude a jihar Bauchi sun fito suna musanta zargin wawure sama da naira tiriliyan dayan da wannan kwamitin binciken ya yi musu. Alhaji Salisu Ahmad Barau Tafawa Balewa, shi ne mai magana da yawun tsohuwar gwamnatin jihar ta Malam Isa Yuguda, wanda ya yi gwamna daga 2007 zuwa 2015. Ya ce ""In mai fadar magana wawa ne, ai mai jin ta ba wawa ba ne. Gwamantin Isa Yuguda karkashin jam'iyyar PDP a wancan zamanin ta sami jimillar kusan Naira biliyan 600 ne."" Ya kara da cewa cikin biliyan 600, gwamnatinsu ta kashe kimanin biliyan 500 ne wajen biyan albashin ma'aikata da sauran ayyuka na yau da kullum. ""Saura kuma ne Isa Yuguda ya yi tsimi da dabara har ya yi manyan ayyuka a jihar Bauchi kamar filin jirgin sama da jami'ar jihar, da kuma asibitin kwararru da sauran su."" Shi ma tsohon gwamnan jihar Barista Abdullahi Abubakar da ya yi mulki jihar daga 2015 zuwa 2019, cewa ya ke yi bita-da-kullin siyasa kawai gwamnatin Bala Kaura ke yi masu. Malam Ali M Ali shi ne mai magana da yawun tsohon gwamna M. Abubakar. Kakakin na tsohon gwamna ya kuma ce batun da masu mulkin jihar na yanzu ke yi, wata dabara ce ta kawar da hankali daga zarge-zargen rashawa kan jami'an gwamnatin yanzu. ""Gaba daya kudaden da aka samu a shekara biyar ba su kai biliyan 350 ba. Alkaluman suna nan. Ina aka samo batun tiriliyan? Hankali ba zai dauka ba."" Ya kuma zargi gwamnati mai ci ta Bala Muhammad, Kauran Bauchi da ""gaza aiwatar da wani abin a zo a gani cikin watannin da suka sami kansu a mulkin jihar."" To amma kwamitin ganowa da sake karbo dukiyar gwamnatin na musanta zargin bita-da-kulli da kuma kokarin badda-bami. Gwamnatoci biyu da suka gabata a jihar ta Bauchi - wadanda kwamitin ke zargi da karkatar da dukiyar jihar da ta kai sama da naira tiriliyan daya - su ma sun gudanar da irin wannan binciken a baya. Su ma sun rika zargin gwamnatocin da suka gabace su da yin ruf da ciki da dukiyar talakawa, amma daga bisani sai aka ji shiru kan lamarin." https://www.bbc.com/hausa/wasanni-51796690 +politics Wane ne sabon Gwamnan Bayelsa, Douye Diri? Sanata Douye Diri na jam'iyyar PDP ya zama gwamnan jihar Bayelsa na biyar a tarihi, inda ya shiga ofis bayan hukuncin Kotun Kolin Najeriya da ya sauke Chief David Lyon na jam'iyyar APC, wanda INEC ta ce shi ne ya ci zaben 2019. Diri ya fito ne daga mazabar Isampou kuma yana wakilcin kananan hukumomin Kolokuma/Opokuma ne a Majalisar Dattawan Najeriya kafin yanzu. An haife shi ranar 6 ga watan Afrilu na shekarar 1959. Kafin ya shiga siyasa, Sanata Diri malamin makaranta ne mai shaidar koyarwa ta NCE da ya samu daga kwalejin Rivers State College of Education a shekarar 1985. A shekarar 1990 ne ya koma makaranta, inda ya yi digiri a fannin koyarwa da kuma siyasa a College of Education, wadda yanzu ta zama jami'ar Ignatius Ajuru University of Education, a Fatakwal. Ya shiga harkokin siyasa a matsayin babban sakatare na cibiyar Centre for Youth Development daga 2000 zuwa 2002. Sannan ya zama kwamishinan matasa da wasanni a 2006-2007 karkashin gwamnatin Timipre Sylva. Sai kuma a shekarar 2008 zuwa 2012 ya zama mamba a majalsar gudanarwa ta jami'ar University of Maiduguri da ke jihar Borno. A shekarar 2012 ne Sanata Diri ya zama mataimakin shugaban ma'aikatan gidan gwamnati a lokacin Gwamna Henry Seriake Dickson, zuwa 2013 kuma ya zama babban sakataren gwamnan. Ya zama sanata a 2015 zuwa 2019 mai wakiltar mazabar Kolokuma/Opokuma. Diri ya lashe zaben Sanatan Bayelsa ta Tsakiya a 2019 kafin daga bisani ya shiga takarar gwamnan jihar karkashin PDP, inda ya fafata da 'yan takara sama da 20. A sakamakon zaben gwamnan na 16 ga Nuwamban 2019, jam'iyyarsa ta PDP ta samu kuri'u 143, 172, yayin da APC ta samu 352, 552. Sai dai Kotun Koli ta soke zaben David Lyon na APC bisa dalilin cewa mataimakinsa ya gabatar da takardun boge ga INEC kafin zaben. Hakan ya sa APC ta rasa kujerar sakamakon umarnin kotun cewa a bai wa dan takarar da ya zo na biyu a zaben, wanda kuma PDP ce da dan takararta Sanata Douye Diri. A ranar 14 ga watan Fabarairun 2020 ne kuma ya zama gwamnan jihar Bayelsa na biyar a tarihi bayan ya sha rantsuwar kama aiki da kuma ba shi shaidar lashe zabe. Yana da mata daya mai suna Misis Gloria Diri kuma sun haifi yara. https://www.bbc.com/hausa/labarai-51516420 +politics Za mu fito da sabbin hanyoyin kudin shiga ga Katsina - Nura Khalil "Danna hoton da ke sama don kallon bidiyon: Injiniya Muhammad Nura Khalil mai neman takarar gwamnan jihar Katsina a jam'iyyar NNPP, ya ce lokaci ya yi da jihohi za su daina jiran kudin dauni daga gwamnatin tarayya. Ya ce 'yan jihar Katsina za su yi san barka dangane da tsare-tsaren da zai fito da su domin sabinta hanyar samun kudin. Dangane da rashin tsaro a jihar ta Katsina, Injiniya Nura Khalil ya ce ""lokaci ya yi da al'ummar Najeriya za su koma ga Allah ubangiji ga dukkan al'amuransu.""" https://www.bbc.com/hausa/articles/cn0gpegz2m1o +politics 'Shin armashin Ranar Dimokraɗiyya na raguwa ne a Najeriya?' "A Najeriya a duk ranar 12 ga watan Yunin kowacce shekara ake bikin zagayowar Ranar Dimukuradiyya a kasar, bayan da Shugaba Buhari ya sauya daga 29 ga watan Mayu. A shekarar 2022, ranar ta zo dai-dai lokacin da jam'iyyun siyasar kasar suka kammala zabukan fitar da gwani na wadanda za su tsaya musu takara a zaben 2023. Farfesa Abubakar Mu'azu malami, a sashen koyar da aikin jarida a jami'ar Maiduguri da ke Najeriya, ya shaida wa BBC cewa, ita wannan rana ana gudanar da ita ne domin tunatar da jama'a irin gwagwarmayar da aka yi da sojoji har aka samu suka yarda suka bayar da mulki ga fararen hula. Ya ce, gudanar da bikin ranar na da muhimmancin saboda mutane su sani cewa akwai wadanda suka yi gwagwarmaya suka tsaya tsayin-daka wajen komawa tafarkin dimukuradiyya, inda har wasunsu sai da aka kai su gidan yari. Farfesan ya ce, wasu kuma har guduwa suka yi suka bar kasar saboda gwagwarmayar. Malamin jami'ar ya ce, ""Duk da ana gudanar da bikin ranar, to a gaskiya armashinsa na raguwa, saboda yawancin mutane suna tsammanin idan an koma mulkin farar hula za a samu abubuwa na walwala da tsaro da cigaba, to amma abubuwan ba sa samuwa yadda ake so."" Farfesa Abubakar Mu'azu, ya ce a yanzu yadda tabarbarewar tsaro ta addabi jama'a, ya sa mutanen Najeriyar ma ba sa ganin ayyukan da ake yi, inda har wasu ma na cewa menene ma amfanin dimukuradiyyar ma tun da ba za a samu zaman lafiya ba. Wannan rana da galibin al'ummar Najeriyar suka fi sani da June 12, rana ce da tarihin kasar ba zai manta da ita ba saboda a ranar ne aka gudanar da zaben Najeriya na 1993, kodayake har kawo yanzu hukumar zaben Najeriyar ba ta sanar da wanda ya yi nasara ba. To sai dai kuma alamu sun nuna cewa dan takarar jam'iyyar SDP, wato Moshood Kashimawo Olawale Abiola, ne ya kama hanyar cin zaben inda ya kayar da abokin takararsa na jam'iyyar NRC Bashir Othman Tofa. An dai ki sanar da sakamakon zaben ne saboda soke zaben da gwamnatin mulkin soja a karkashin Janar Ibrahim Badamasi Babangida ta yi. Soke zaben dai ya janyo gagarumar tirjiya daga 'yan jam'iyyar SDP da kuma 'yan gwagwarmaya da ke rajin kafa gwamnatin farar hula a wancan lokaci abin da ya kai ga tsare wasunsu da dama ciki har da Abiola. Wannan rana ta 12 ga watan Yuni, ta kara karfi ne bayan da gwamnatin mulkin dimukuradiyya ta tsaya da kafarta a 1999. An rinka gudanar da bikin wannan rana ne tun daga shekarar 2002, haka kuma shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kara wa wannan rana karfi a shekarar 2018 bayan da ya sauya Ranar Dimukuradiyya daga ranar 29 ga watan Mayu zuwa ranar 12 ga watan Yuni. Sauya Ranar Dimukuradiyya daga 29 ga watan Mayu zuwa 12 ga watan Yuni bai yi wa wasu 'yan Najeriyar dadi ba inda har wasu na ganin cewa siyace kawai. A kowacce rana irin wannan gwamnatin Najeriyar kan bayar da hutu ga 'yan kasa, sannan ta shirya biki a matakin tarayya, haka suma jihohin kasar musamman na shiyyar kudu maso yammaci wato na Yarabawa kan shirya irin wannan biki da nufin tunawa da ranar da aka yi zaben 12 ga watan Yuni." https://www.bbc.com/hausa/labarai-61773553 +politics Gwamna A. A. Sule: Kammala ayyukan da na fara ta fi muhimmanci sama da wa'adi na biyu Danna hoton da ke sama domin ku kalli bidiyo: Gwamnan Jihar Nasarawa da ke tsakiyar Najeriya, Abdullahi Alhaji Sule (A.A. Sule), ya ce kammala ayyukan da ya fara ita ce mafiya muhimmanci a gabansa fiye da neman wa’adi na biyu na mulkin jihar. Gwamna A. A. Sule ya ce ba ya cikin gwamnonin Najeriya da suka damu da sake samun dama karo na biyu don su kammala wasu ayyuka. A wannan hira ta musamman da abokin aikinmu Yusuf Ibrahim Yakasai, gwamna ya kuma bayyana matsayarsa kan zaben da aka yi wa Sanata Abdullahi Adamu a matsayin shugaban jam’iyyar APC. https://www.bbc.com/hausa/media-61278938 +politics Ahmad Lawan ya ce Majalisar dattawan Najeriya ba 'yar amshin shata ba ce Shugabn majalisar dattawan Najeriya Sanata Ahmad Lawan, ya musanta ikirarin da wasu yan kasar ke yi na cewa majalisar da yake shugabanta yar amshin shatar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ce. Sanata Ahmad Lawan ya shaidawa BBC cewa wasu daga cikin bukatun gwamnati da ake ganin suna amincewa da su, kamar maganar ciyo bashi dole ce kawai ta sanya, saboda babu isassun kudi a baitulmalin Najeriya. ''Ko kada mu dauki bashi, mu zauna ba mu da komai na ci gaba, ko kuma mu duba inda za a samu basussuka masu saukin ruwa, masu dogon lokaci kafin a biya, sai a ce kar a yi ?'' Ya tambaya. Ya kara da cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari na da kudurin aiwatar da manyan ayyukan raya ƙasa da suka hadar da gina hanyoyi da samar da titunan jirgin kasa a sassan kasar, sai dai ba ta da isassun kudi. Don haka ne ya ce majalisar take amincewa da bukatun ciyo bashin. Gwamnatin Najeriya dai ta ce za ta yi amfani da kuɗaɗen da za ta karɓo rancen biliyoyin daloli ne domin cike gibin kasafin kuɗin musamman yadda annobar korona ta katse mata hanzari da kuma ƙalubalen da Najeriyar ke fuskanta ta fuskar kudin-shiga, sakamakon faɗuwar farashin man fetur a kasuwannin duniya. Babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta yi zargin cewa bashin da gwamnatin APC ke ci ya wuce kima - zai iya jefa Najeriya cikin wahala. Duk da haka majalisar dokokin Najeriya ta amince da buƙatar, da za ta bai wa gwamnati damar karɓar rancen fiye da dala biliyan biyar, bayan a watan Afrilu majalisar ta amince ta karɓo rancen naira biliyan 850 a cikin gida. Amma PDP da wasu masana na sukar yawan rancen na shugaban ke yi wanda suke cewa yana tattare da hatsari ga makomar ƙasar Ita dai majalisa ta takwas da ta wuce karkashin jagorancin Sanata Bukola Saraki, ta sha yin fatali da bukatar gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta ciwo basussuka. Daya daga ciki ita ce watsi da bukatar gwamnatin ta karbo bashin dala biliyan 30 domin gudanar da wasu manyan ayyuka a shekaru biyu, bayan shugaban ya nemi amincewar majalisar domin ranto kudaden daga kasashen waje. https://www.bbc.com/hausa/labarai-53372057 +politics Zaɓen Gwamnan Ondo: Sakamakon zaben kai-tsaye Wannan shafin yana kawo bayanai kai tsaye a yayin da hukumar zaɓe ta INEC ta ke fitar da alkaluman zaɓen. Za ku iya bin rahotanni kai-tsaye game da zaɓen idan kuka latsa nan: https://www.bbc.com/hausa/labarai-54485607 +politics Waiwaye: Najeriya ta tura 'ƴan sanda Somalia da sace daliban jami'ar Greenfield "Ga wasu daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a makon da ya gabata a Najeriya, daga Lahadi 18 ga Afirilu zuwa Asabar 24 ga Afirilu. A cikin makon da ya gabata ne, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gargadi 'yan bindigar da ke kashe-kashe musamman a arewacin kasar kan cewa ""Su shiga hayyacinsu, su daina jin cewa gwamnati ba za ta iya maganinsu ba"". Buhari ya yi wannan gargadin ne a ranar Alhamis yayin da yake Allah-wadai da kisan da 'yan bindigar suka yi wa mutane sama da 50 a kauyukan Zamfara. Shugaban wanda ya yi gargadin cewa ""Za a kawo karshen Irin wannan rashin girmama rayuwar mutanen da 'yan bindigar ke yi a kusa ba da dadewa ba"", ya kara da cewa, ""Dole mu dakatar da wannan kisan da ake yi wa mutanen da ba su ji ba ba su gani ba"", Ƴan sandan Najeriya da aka kai Somaliya domin samar da tsaro Kazalika a cikin makon ne dai wata tawagar ƴan sandan Najeriya mai ƙunshe da 'yan sanda 144 ta isa ƙasar Somalia domin aikin wanzar da zaman lafiya. Tawagar, wadda ke karkashin shirin Tarayyar Afirka na samar da zaman lafiya a Somalia da a takaice ake kira (AMISOM), ta isa kasar ne tun ranar Asabar. Sanarwar da Tarayyar Afirka ta wallafa a shafinta na intanet ta ce ƴan sandan za su kwashe shekara guda suna aiki a Somalia, wadda ke fama da hare-haren mayakan ƙungiyar Al-Shabaab. ""A shekara ɗayan da za su yi za su bayar da shawarwari da kuma dabaru na aiki ga rundunar ƴan sandan Somaila,"" in ji sanarwar. Ministan watsa labaran Najeriya Lai Mohammed ya yi zargin cewa kasar Birtaniya tana yi wa Najeriya zagon-kasa a yakin da take yi da ta'addanci. Kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN, ya ambato Mr Lai Mohammed yana cewa matakin da Birtaniya ta dauka na bai wa wasu masu fafutukar ballewa daga kasar 'yan kungiyar IPOB mafaka ""rashin mutunci ne da kuma zagon-kasa"" ga Najeriya a yakin da take yi da ta'addanci. Ya kara da cewa tuni Najeriya ta ayya na 'yan kungiyar IPOB a matsayin 'yan ta'adda don haka bai ga dalilin da zai sa Birtaniya ta nemi ba su mafaka ba. ""Idan ya tabbata cewa da gaske Birtaniya za ta bayar da mafaka ga 'yan IPOB da MASSOB da ake zargi ana musgunawa, lallai akwai matsala. Ba wai kawai an haramta IPOB a Najeriya ba ne, an kuma ayyana ta a matsayin kungiyar 'yan ta'adda. Majalisar dattijan ƙasar ta ce ta amince wa gwamnatin tarayya da jihohi su karɓo bashin dala biliyan ɗaya da rabi kwatankwacin naira biliyan dari bakwai da hamsin da kuma yuro miliyan ɗari tara da casa'in da biyar, kimanin naira biliyan ɗari biyar da saba'in. Ta ce ta ga buƙatar amincewa da ciyo bashin wanda tallafin annobar korona ne saboda ƙudurin gwamnatoci na farfaɗo da harkoki bayan matsin tattalin arziƙi da annobar ta jefa duniya. 'Yan Najeriya da dama suna kokawa da yawan bashin da ƙasar ke ci a ƙarƙashin jagorancin Muhammadu Buhari Daukar fansar da mazauna kauyukan Jihar Zamfara yi kan 'yan Fashi Bayanai daga jihar Zamfara a arewacin Najeriya na cewa wasu 'yan fashin daji sun kwashi kashinsu a hannu a daren Juma'a lokacin da suke ƙoƙarin farmaki kan wasu ƙauyuka biyu da ke kusa da babban birnin jihar. Ƴan fashin a kalla 10 ne suka mutu a cikin bata kashin da suka yi da 'yan banga a ƙauyukan Kwaya da kuma Kura da ke ƙaramar hukumar Gusau. Wannan na zuwa ne yayin da mazauna ƙauyukan nan shida da suka kai wa farmaki a ranar Laraba ke cewa adadin wadanda suka mutu yanzu ya kai 80. A cewar mazauna yankin 'yan fashin dajin sun gamu da gamon nasu ne a wani artabu da 'yan banga a ƙauyukan Kwaya da kuma Kura lokacin da suka yi yunkuri afka musu da tsakar daren jiya. Wani ɗan sa kai da aka yi fafatawar da shi, ya ce turjiyar da suka nuna da kuma ɗaukin da aka kai daga maƙwabtan ƙauyuka ne suka taimaka musu suka fatattaki maharan tare da hallaka 10 daga cikinsu. Ma'aikatar tsaro ta jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya ta ce yan bindiga sun kashe dalibai uku na na Jami'ar Greenfield da aka sace a Jihar. Cikin wani sakon Twitter da Ma'aikatar ta fitar ta ruwaito Gwamnan Jihar Nasir El-Rufa'i ya yi Allah-wadai da wannan mummunan rashin imani ga rayuwar dan adam. Ya kara da cewa dole a yaki wadannan 'yan bindiga ta ko wanne hali. Ya kuma ce sharri ba zai taba yin nasara ba kan alheri. Ya kuma aika ta'aziyyarsa ga mutanen jihar da iyayen yaran da suka rasa yarukansu. Kuma gwamnati za ta gaba da shaida wa mutanen jihar halin da ake ciki game da lamarin." https://www.bbc.com/hausa/labarai-56873277 +politics SOKAPU: Muna bukatar a raba Jihar Kaduna gida biyu "Latsa lasifikar da ke sama domin sauraren rahoton da wakilin BBC Abdou Halilou ya hada. Wasu al'ummomi a Najeriya daga bangarori daban-daban na ta shirye-shiryen gabatar da kudurorinsu a game da shirin kawo gyara ga kundin tsarin mulkin kasar. A jihar Kaduna, maganar ta yi nisa wasu daga cikin al'ummomin kudancin jihar na nuna neman a ba su nasu bangaren a yayin da wasu daga cikin yan kudancin ke cewa har yanzu basu da cancantar a ce sun balle daga Kaduna. Johnathan Osake shugaban kungiyar yan kudancin Kaduna wato SOKAPU ya yi wa BBC karin bayani game da hujarsu: ""Kudancin Kaduna da bangaren arewacinsa an dade ana rashin zaman lafiya. Al'adunmu da daban, kuma mun san cewa idan aka raba jihar, kowa yaje yana cin gashin kansa, gaskiya zai kawo zaman lafiya."" Sai dai an gamu kuma an rabu. Kungiyar Fulani makiyyaya ta Mi Yati Allah da ita ma ke cikin yankin na kudancin Kaduna ta ce ba da yawunta ba a cikin wannan lamari. Ibrahim Bayero shi ne mai magana da yawun kungiyar ta Mi Yetti Allah: ""Abin da su ka rubuta mu ba ma tare da su. A matsayinmu na Fulanin Kudanci, ba su neme mu ba, saboda haka Jihar Gurara da su ke nema, mu ba mu goyi bayan haka ba. Idan za a kirkito jiha sai an dubi tattalin arzikin yankin, al'ummar nan da su ka rubuta wannan takardardun, gaba dayansu ba sa iya tara haraji.""" https://www.bbc.com/hausa/57290926 +politics Najeriya: Majalisar dokokin ƙasar na shirin janye batun zaɓen ƴan tinƙe "Ranar Larabar nan ne ake sa ran Majalisun Najeriya za su zauna domin sake nazari kan ƙudurin dokar zaɓen da shugaba Muhammadu Buhari ya mayar musu, bayan ya ƙi sa hannu, saboda ba su bai wa jam`iyyun siyasa zaɓi game da zaɓen fid da gwani ba. Ƴan majalisar sun ce ƙudurin dokar na ƙunshe da muhimman batutuwa masu yawa, saboda haka ba za su bari a yi watsi da shi a kan wani batu guda ɗaya ba. A baya dai sun yi barazanar cewa za su yi gaban kansu wajen zartar da ƙudurin ya zama doka matuƙar shugaban ƙasar ya ƙi sa hannu. Shugaban kwamitin kula da hukumar zaɓe na Majalisar Dattawan Najeriya Sanata Kabiru Ibrahin Gaya ya shaida wa BBC cewa a zaman majalisar da za su yi za a tattauna a kan batun da ya sa shugaban ƙasar ya ƙi sanya hannu a kan ƙudurin. Ɗan Majalisar Dattijan ya ce a zaman na su zasu duba batun ba wa jam'iyyu damarsu da shugaban Buhari ya ce ba bu a cikin dokar, sannan a tattauna domin a samu maslaha. Kabiru Gaya ya ce ''Dama dai kowa ya sani batun da ke da sarƙaƙiya a cikin ƙunshin dokar shi ne batun zaɓen ƴar tinƙe, to a yanzu halin da majalisar ke ciki shi ne wadanda suka dauki abun da zafi a cikinmu sun fara sakkowa, don haka akwai yiwuwar idan suka zauna suka tattauna za a iya samun maslaha a kan batun'' Sanatan ya ce"" Dole ne a samu maslaha kan batun zaɓen 'yar tinke tsakanin gwamnati da majalisar, domin muna so ayi sauri a sanya wa dokar hannu. don idan an barta ba a sanya hannu ba to ko shakka ba bu zaben 2023 zai fuskanci matsala mai yawa'' ""Mu abin da za mu yi a matsayinmu na kwamitin kula da hukumar zaɓe a majalisar dattawa shi ne zamu dawo dawo da kudurin dokar zaben a sake tattaunawa a kanta"". Dama batun zaɓen fid da gwani ta hanyar 'yar tinƙe, shi ne babban abin da ya janyo taƙaddama a gyaran-fuskar da aka yi wa dokar zaɓen. Tun da farko wasu daga cikin 'yan majalisar sun sha alwashin aiki da ikon da kundin tsarin mulkin kasar ya ba su, na tabbatar da dokar ko da shugaban bai sa mata hannu ba. Wasu na zargin gwamnonin Najeriyar da kai komo fadar Shugaban kasar don ganin cewa Shugaba Muhammadu Buhari bai amince da garambawul din ba. Masu sharhin siyasa na ganin cewa kin saka hannu da Shugaban kasar ya yi mataki ne da zai yi wa gwamnonin dadi, don ana zargin cewa da dama daga cikinsu ba sa goyon bayan zaben 'yar tinke wurin tsayar da 'yan takara a jihohinsu. A daya bangaren kuma 'yan majalisa na ganin zaben 'yar tinken hanya ce da za ta kawo wa gwamnonin cikas, a babakeren da ake ganin suna yi wurin tsayar da 'yan takara." https://www.bbc.com/hausa/labarai-60048711 +politics Zaɓen 2023: Ba sai masu zaɓe sun tsaya jiran kayan aiki ba wannan karo - INEC Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa a Najeriya, ta yi alƙawari cewa a zaɓen 2023, kayan aiki ne za su jira masu zaɓe a rumfunan kaɗa ƙuri’a saɓanin yadda aka dinga samu a baya. Shugaban INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu ne ya shaida hakan yayin wani taro don ƙulla yarjejeniya da ƙungiyoyin sufuri na NURTW da NARTO kan hanyoyin sauƙaƙa jigilar ma’aikata da kayan aikin zaɓe zuwa cibiyoyin zaɓe. A cewar shugaban hukumar, sun yi waiwaye kan matsalolin da aka dinga fuskanta a zaɓen 2019, kuma hakan ya sanya su ɗaukar matakan riga-kafi daga manyan ƙalubalen da za su iya kawo cikas ga nasarar zaɓen shekara mai zuwa. Ya ce hakan ba zai yiwu ba har sai INEC ta samu ƙarin motoci da babura da kwale-kwale musamman a yankunan da ke kusa da ruwa, inda isar ma’aikatan hukumar zuwa waɗannan wuraren a kan lokaci ke da wahala. Babban zaɓen na baɗi zai ƙunshi aikin tura jami'an zaɓe sama da miliyan 1 a duk faɗin Najeriya da ɗumbin adadi na kayan aiki sau biyu a cikin mako biyu daga ofisoshin hukumar INEC na jihohi zuwa ƙananan hukumomi 774 da mazaɓu 8,809 da cibiyoyin zaɓe 176,846. Gagarumin aikin, in ji sanarwar INEC zai buƙaci motoci sama da 100,000 da jiragen ruwa kimanin 4,200 waɗanda jiragen sojojin ruwa da aka girkawa bindigogi za su yi musu rakiya. Ta ce wannan wani jan aiki ne da za a yi shi nan da kwana 66 kuma mun ƙuduri niyyar yin haka don bai wa 'yan Najeriya damar yin zaɓe cikin farin ciki. Farfesa Mahmud Yakubu ya kuma bai wa 'yan Najeriya tabbacin cewa sun duƙufa wajen ganin an buɗe duk rumfunan zaɓe da ƙarfe 8:30 na safe ranar Asabar 25 ga watan Fabrairu don zaɓen shugaban ƙasa da na 'yan majalisun tarayya da kuma a ranar Asabar 11 ga watan Maris ɗin 2023 don zaɓen gwamna da na 'yan majalisar dokokin jihohi. A Shekarar 2015 ne INEC ta fara ƙulla yarjejeniya da ƙungiyar NURTW inda ta sake bibiyar yarjejeniyar a 2018 domin shigar da NARTO kuma hukumar ta dogara ne kan yarjejeniyar da ta ƙulla da su domin samar da motoci wajen jigilar ma’aikata da kuma kayan aiki zuwa wuraren da ake buƙata. Sai dai a baya, hukumar ba ta sa ƙungiyar MWUN ta ma’aikatan jiragen ruwa a cikin yarjejeniyar ba lamarin da a mafi yawan lokuta ke haifar da matsaloli game da turawa da kuma kwaso ma’aikata da kayan aiki daga wuraren da ke kusa da ruwa. “Hakan ne ya sa aka ƙara bibiyar yarjejeniyar don sanya su a cikin masu jigilar kayan aikin zaɓe zuwa cibiyoyin kaɗa ƙuri’a.” Farfesa Yakubu ya kuma buƙaci ƙungiyoyin su tabbatar mambobinsu sun mutunta yarjejeniyar don kauce wa abubuwan da za su iya janyo tsaiko a ranar zaɓe. Sai mai dakon kayan zaɓe ya rantse Wani sabon tanadi a sabon tsarin dokar zaɓe shi ne duk mutumin da zai shiga cikin harkokin zaɓe, sai ya rantse zai kasance ɗan ba-ruwanmu. Sanarwar ta ce don haka INEC za ta buƙaci 'ya'yan ƙungiyar masu sufurin motar su yi rantsuwa kuma su tabbatar da cikakkiyar biyayya ga wannan rantsuwa da kuma tanade-tanaden kundin tabbatar da ɗa'ar ma'aikatan INEC don kuwa shigar su cikin aikin kai kayan zaɓe na buƙatar su kasance cikakkun 'yan ba-ruwanmu waɗanda kuma babu ruwansu da kowacce jam'iyya. Haka zalika, hukumomin tsaro ba kawai za su kasance wajen raka dukkan motoci da jiragen ruwa zuwa wuraren da aka tura su ba, za kuma su tabbatar da kariya da tsaron lafiyar dukkan jami'in zaɓe da kayan aiki. Kuma kamar yadda aka saba, hukumar INEC ta ce ta riƙa bin sawun duk wani abin hawa da jiragen ruwa ta hanyar latroni kuma kai tsaye don tabbatar da ganin ba a karkatar da jami'ai ko kayan zaɓe ba. https://www.bbc.com/hausa/articles/cl7q7ppg97xo +politics Ahmed Lawan ya 'harzuka' wasu 'yan jam'iyyarsa ta APC "Jama'a da dama a Najeriya na ci gaba da muhawara kan yadda Shugaban Majalisar Dattawan kasar ya kama ragamar kujerar da aka zabe shi akai, inda wasu ke ganin ya fara da kafar hagu, yayin da wasu ke cewa dama sun san za a rina. A ranar 11 ga watan nan ne aka zabi Sanata Ahmed Lawan wanda ke wakiltar Yobe ta Arewa domin jagorantar majalisar ta tara bayan shafe watanni aka kamfe da kamun kafa, inda ya kayar da Ali Ndume daga jihar Borno. Sai dai jim kadan bayan zaben na sa, sai ya fara tsintar kansa a rudani, inda da dama daga cikin 'ya'yan jam'iyyarsa ta APC suka yi masa rufdugu kan mutumin da ya nada a matsayin mai magana da yawunsa, suna fargabar ka da ""su tura mota ta bude su da kura"". Cikin wadanda suka goyi bayan masu sukar nadin Festus Adedayo har da Uwargidan Shugaban kasa Aisha Buhari, da wasu fitattun magoya bayan gwamnati da APC. Duka sun zargi Adedayo, wanda gogaggen dan jarida ne da ya shahara wurin sharhi kan al'amura, da cewa ya yi kaurin-suna wurin sukar manufofin gwamnatin Buhari. Haka kuma masu adawa da nadin nasa sun rinka amfani da maudu'in #SackfestusAdededayo wato a kori Festus Adededayo a shafukan sada zumunta domin matsawa Ahmed Lawan lamba kan ya sauke shi. @cbngov_akin1 ya ce ya kamata @DrAhmadLawan ya sani cewa nadin Festus Adedayo abin dariya ne a wurinmu. Ba za ta sabu ba. Kalli wata makala da ya rubuta a bara yana sukar shugabanmu da kuma APC"". Yain da @KemisolaAdekun1 ta ce ""...ta yaya mutumin da ya yi kaurin suna wurin sukar gwamnati kuma zai karbi mukami a cikinta. Wannan ya fito da halinsa a zahiri. Zai iya juyawa mai gidan nasa baya"". Ana cikin hake ne kwatsam sai Sanata Lawan ya soke nadin na Adedayo, kamar yadda mai taimaka masa kan harkokin yada labarai Muhammed Isa ya sanar, ba tare da bayyana dalili ba. Sai dai anasa bangaren, dan jaridar ya wallafa wani sharhi a shafin Premium Times, inda ya ce ba shi ""ya nemi mukamin ba tun asali, kuma ba zai taba sauya matsayinsa kan yadda yake kallon al'amuran yau da kullum a Najeriya ba"". Ya ce tun ""shekarar 1998 da na fara sharhi a jaridu, kusan babu wani shugaban kasa ko manyan jagororin siyasa da suka tsira daga suka a wurina, a don haka ba ni da jam'iyya ko gwamnati"". Tun da farko dai Sanata Lawan ya fara ne da kokarin kare kansa bayan da wasu kafafen yada labarai suka lakaba masa wani labari da ke cewa ya nemi jam'iyyar APC da Shugaba Buhari da su mika mulki ga yankin Arewa maso Yamma a shekara ta 2023. Wannan ta sa sai da ya fito ya karyata labarin, inda ya ce wani takwaransa ne, wato sakataren APC na jihar Adamawa, ya yi maganar ba shi ba. Wani jigo a jam'iyyar APC wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa BBC cewa ganin irin ja-in-jar da aka yi kan takararsa da yadda ta ja hankalin 'yan kasar, wani zai yi tunanin cewa Ahmed Lawan zai yi taka-tsantsan a duk irin abubuwan da zai yi. ""Amma abin mamaki sai ga shi ya fara wa'adin nasa da haifar da rudani. Muna fatan ba za a sake maimaita irin wannan ba,"" a cewarsa. Kawo yanzu dai ba a nada wanda ko wacce za ta maye gurbin Mista Adedayo ba, sai dai da alama 'yan APC za su zura ido domin ganin mutumin da za a nada a karo na biyu." https://www.bbc.com/hausa/labarai-48719687 +politics PRP ta ce a shirye take ta yi gogayya da manyan jam'iyyun Najeriya a zabe mai zuwa "Jam'iyyar PRP mai ikirarin ta talakawa ce a Najeriya, ta ce a shirye take ta kara da manyan jam'iyyun siyasar kasar a zabe mai zuwa. PRP, wadda ta gudanar da babban taronta a ranar Asabar, ta ce yanzu ta fara shiri don tunkarar zabuka masu zuwa. Falalu Bello, shi ne shugaban jam'iyyar na kasa, ya kuma shaida wa BBC cewa, a yanzu za su zauna domin fitar da 'yan takara a dukkan jihohin Najeriya. Ya ce, bisa la'akari da cewa jam'iyyarsu ta PRP, ita ce ta fi dukkan jam'iyyun siyasa a Najeriya dadewa, dole su fitar da 'yan takarar da za suyi wa talakawa aiki. Shugaban jam'iyyar ta PRP, ya ce in banda APC da PDP, babu wata jam'iyya da ta kafa gwamnati a Najeriya sai jam'iyyarsu ta PRP. Ya ce, ""Mun yi gwamnati a tsohuwar Jihar Kaduna da tsohuwar Jihar Kano, kuma jama'a sun ga abin da muka yi, jam'iyyace ta talaka, kuma har yanzu a Jihar Kaduna ba a yi gwamnatin da ta yi wa talakawa aiki kamar PRP ba. Shi ma tsohon shugaban hukumar zabe ta Najeriya, Farfesa Attahiru Jega, wanda dan jam'iyyar ne, ya shaida wa BBC cewa, su a PRP abin da suka sanya a gaba shi ne a zabi mutanen kirki a sa su shugabanci, domin al'umma ta amfan.'' Farfesa Jega, ya ce "" Irin tabargazar da muke gani ana yi da sunan shugabanci a Najeriya, gaskiya idan har aka ci gaba a haka to za su durkusar da kasar."" Tsohon shugaban hukumar zabe ta Najeriyar, ya ce dole a samu a ceto talaka kana a biya masa bukatunsa, a kawo tsaro da sauran abubuwan da suka dace wadanda za su inganta rayuwar al'umma. Ya ce,"" Don haka jam'iyyarmu za ta dukufa wajen tabbatar da cewa wadannan zabuka da za a yi mun tsaida mutanen kirki, kuma sun ci zabe domin a inganta al'amura na zabe a kasarmu."" Farfesa Jega, ya ce za su zo da tsari dalla-dalla wanda zai nuna muhimman abubuwan da ya kamata a fara da su idan sun ci zabe. Ya ce, a shekarar 1979, da PRP ta ci zabe a wasu jihohin Najeriya, mutane sun gani domin sai da ta cika dukkan alkawuran da ta dauka. A ranar Asabar ne jam'iyyar PRP ta gudanar da babban taronta na kasa a Abuja babban birnin tarrayar Najeriya. A yayin taron an yi gyara a kundin tsarin mulkin jam'iyyar. Jam'iyyar ta kasance mafi dadewa a cikin jam'iyyun Najeriya a yanzu, kuma jam'iyyar na ikirarin cewa ita ce jam'iyyar talakawa a Najeriya." https://www.bbc.com/hausa/labarai-60970866 +politics Me ya bambanta hargitsin majalisar Amurka da abin da ya saba faruwa a Afirka? Ku latsa hoton da ƙasa don kallon bidiyon: Bayan kutsawa da wasu bata gari suka cikin majalisar dokokin Amurka har suka tayar da zaman ƴn majalisa, BBC ta yi nazari kan lamarin da abin da aka saba gani a majalisun Afirka. Halima Umar Saleh ce ta gabatar, Umar Rayyan ne ya tsara, Yusuf Yakasai ya ɗauki bidiyon da tacewa. https://www.bbc.com/hausa/media-55596840 +politics Kyautar motoci da Buhari ya bai wa Nijar ta 'harzuƙa wasu 'yan Najeriya' "Zafafan martani da shaguɓe iri-iri na ci gaba da biyo bayan matakin gwamnatin Najeriya na tallafa wa maƙwabciyarta Nijar da motocin da suka kai darajar kusan naira biliyan ɗaya da rabi. Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta ce ta bai wa maƙwabciyar tata motocin 10 da zimmar inganta ayyukan tsaro ne. Hakan na zuwa ne a lokacin da Najeriyar ke tsaka da nata matsalolin tsaron a kusan kowane saƙo. Ministar Kuɗi ta Najeriya Zainab Shamsuna Ahmed, ta faɗa wa manema labarai ranar Laraba cewa ""an ɗauki matakin ne saboda taimaka wa Nijar ta inganta tsaron iyakarta da Najeriya"". Ƙasashen biyu da kuma Kamaru da Chadi, sun haɗa iyaka a tsakaninsu mai girma sosai kuma dukkansu na fuskantar hare-haren ƙungiyar Boko Haram da sauran masu iƙirarin jihadi. A cewar ministar: ""An ɗauki lokaci Najeriya tana tallafa wa makwabtanta, musamman ma mafiya kusanci da nufin karfafa su domin su kare kasashensu ta bangaren da ka iya shafar mu. ""Kuma ba wannan ne karon farko da Najeriya ta taimaka wa Nijar ko Kamaru ko Chadi ba."" Binciken da BBC Hausa ta gudanar ya nuna cewa ba wannan ne karon ne Najeriya ta fara taimaka wa maƙwabtan nata ba kamar yadda Minista Zainab ta faɗa, amma a yanzu ne abin ya fi fitowa fili. Sanata Shehu Sani ya wallafa cewa: ""Abin tambayar shi ne, yaya aka yi ƴan majalisa ba su san da batun sayen motocin ba."" Wasu takardun bayanai da wani ɗan jarida ya wallafa a ranar Laraba na sayen motocin sun tayar da ƙura, inda wasu 'yan Najeriya ke tambayar me ya sa gwamnati za ta yi hakan alhalin ita ma tana da nata matsalolin. Kazalika, 'yan ƙasar da dama sun yi ta kwatanta ayyukan gwamnatin da kuma matsalolin, ciki har da waɗanda ke alaƙanta matakin rundunar sojan Najeriya na girmama dakarunta huɗu da sabbin babura ""bisa jajircewarsu a wurin aiki"". ""An bai wa jajirtattun dakarunmu babura, an bai wa Nijar motoci ƙirar 2022,"" a cewar ɗan jarida Abiodun Alade. Kwamandan Bataliya ta 82 na Sojojin Najeriya a Jihar Enugu, Taoreed Lagbaja, ya karrama sojojin ne don ƙarfafa musu gwiwa tare ba su wasiƙun yabo a ranar Talata. Haka nan, wasu na sukar gwamnatin saboda kasa daidaitawa da malaman jami'a, abin da ya sa suke yajin aiki na tsawon fiye da wata biyar ya zuwa yanzu. Sai dai jami'an gwamnatin na kare matakin da cewa ""idan da aka wani abu da za mu samu daga bai wa Nijar kyautar motoci shi ne wannan,"" kamar yadda Tolu Ogunlesi ya bayyana yana mai nuni da wani kan labari da ke cewa Najeriya da Nijar da Aljeriya na shirin gina bututun iskar gas zuwa Turai. Yayin da maƙwabtaka tsakanin Nijar da Najeriya ke ci gaba da yauƙaƙa kuma ake cecekuce, wasu gwamnoni da attajiran Najeriyar sun samu lambobin girmamawa a Nijar. Shugaban Nijar Mohamed Bazoum ne ya karrama mutum shida da lambar yabo kan tsaro a bikin cikar ƙasar shekara 62 da samun 'yancin kai da aka gudanar a ranar Laraba, 3 ga watan Agusta. Wadanda aka karrama sun haɗa da Gwamna Badaru Abubakar na Jigawa, da Gwamna Bello Matawalle na Zamfara, da hamshaƙan attajirai Aliko Dangote da Abdulsamad Rabi'u. Sauran su ne Ambasada Lawal Kazaure da kuma Malam Sarki Abba." https://www.bbc.com/hausa/articles/cp9m03v9v3ro +politics Zaɓen 2023: Wa'adin kwana 111 INEC ta bai wa jam’iyyu su mika sunayen ‘yan takarar shugaban kasa "Hukumar zaben Najeriya, INEC, ta umarci jam'iyyun kasar su mika mata sunayen 'yan takararsu na shugaban ƙasa daga yanzu zuwa 17 ga watan Yunin 2022. Shugaban hukumar, Farfesa Mahmoud Yakubu, shi ne ya bayyana haka yayin da yake sanar da jadawalin zaben 2023 a taron manema labarai da ya gudanar ranar Asabar a Abuja. Hakan na nufin dole APC da PDP da ma sauran jam'iyyu da za su fafata a zaben 2023 su aika sunayen masu tsaya musu takarar shugaban kasa nan da kwana 111 masu zuwa. Ya ce za a ""mika fom na tsayawa takarar shugaban kasa da majalisun dokokin tarayya ga INEC ta intanet — daga tara na safen Juma'a 10 ga wata zuwa 17 ga watan Yuni na 2022."" Daya daga cikin ɓangarorin jadawalin zaɓen masu muhimmanci shi ne; sanarwar zaɓe wadda ya kamata a yi ƙasa da kwanaki 360 kafin lokacin kaɗa ƙuri'a ba za ta yiwu ba game da zaɓen 2023 saboda lokaci ya ƙure. Wannan dalilin ne ya sa hukumar zabe ta sauya ranakun zaben shugaban ƙasa daga 18 na watan Fabarairu da kuma na gwamnoni mako biyu bayan haka kamar yadda ta tsara tun farko, domin ta tabbatar ta yi biyayya ga tanade-tanaden sabuwar dokar zabe. Game da haka, za a gudanar da zaben shugaban kasa da na majalisun dokokin tarayya a ranar Asabar 25 ga watan Fabarairu na shekarar 2023, yayin da za a gudanar da zaɓen gwamnoni da na majalisun jihohi mako biyu bayan haka a ranar Asabar 11 ga watan Maris. Shugaban INEC Farfesa Yakubu ya ce za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na 'yan majalisun tarayya ranar Asabar 25 ga watan Fabarairun 2023. A cewarsa, za a yi zaɓen gwamnoni da na 'yan majalisun jihohi zai gudana ranar 11 ga watan Maris na 2023. Shugaban INEC ya ce an zaɓi ranakun ne saboda a tabbatar an yi aiki da sabuwar dokar zaɓe, wadda ta tanadi cewa wajibi ne a bayyana ranar zaɓen aƙalla kwana 260 kafin kaɗa ƙuri'a." https://www.bbc.com/hausa/labarai-60541236 +politics Marasa daraja ne ke yaɗa cewa zan janye wa Tinubu - Kwankwaso Shirin Gane Mini Hanya na wannan makon ya tattauna da ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar NNPP, Rabi'u Musa Kwankwaso. https://www.bbc.com/hausa/articles/cg3yr2dnyrko +politics Bangaren Sanata Aleiro ya bude sabon ofishin APC a Kebbi "Rikicin shugabanci a jam'iyyar APC mai mulki a jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya ya ƙara ƙamari, bayan da tsohon gwamnan jihar Sanata Muhammadu Adamu Aleiro ya buɗe wata sabuwar hedikwatar jam'iyyar ta jihar a ranar Lahadi. Hakan kuwa na faruwa ne duk da ƙoƙarin sasanta rikicin da ke tsakanin ɓangarensa da na gwamnan jihar, Sanata Atiku Bagudu da kwamitin Abdullahi Adamu ya yi. Bangaren Gwamna Bagudu dai ya bayyana buɗe sabon ofishin a zaman haramtacce wanda aka yi ba bisa doka ba. Wasu na ganin wannan matakin na Sanata Aleiro a matsayin wanda zai iya janyo wa jihar ta Kebbi tashin hankalin siyasa, wanda a baya ake yi wa jihar kallon cewa ba a cika samu ba. Amma bude ofishin bai gudana kamar yadda aka tsara da farko ba saboda yayin isa wajen taron, an tarar da jami'an tsaro bila adadin cikin shiri domin hanawa. Sanin abin da ke iya faruwa idan suka nace sai sun bude ofishin, sai tsohon gwamnan tare da dandazon magoya bayansa ciki har Alhaji Bello Bagudu yayan Gwamna Atiku Bagudu, suka karkata akala zuwa filin Sukuwa inda suka yi taron buɗe ofishin. An bude ofishin ne a gidan jigon APC Alhaji Bello Bagudu wan Gwamna Atiku Bagudu. Sai dai a halin yanzu ko tsuntsu babu a ciki saboda jami,an ba su bari a je ko kusa da ita. Alhaji Sani Dododo shi ne kakakin ɓangare Sanata Aleiro, kuma ya bayyana wa BBC cewa babban dalilin samun wannan rabuwar kan yana da nasaba da wani taron APC da aka yi a baya inda aka cimma matsaya daban-daban, wanda ba a cimma ba kamar yadda aka zauna aka tsara. Sai dai kakakin jam'iyyar bangaren Gwamna Atiku Bagudu, Alhaji Isa Assalafi ya nace kan cewar jam'iyyar ba ta rabu ba kamar yadda ake faɗa. ""Jam'iyyar APC a Kebbi na nan tare, tsintsiya ce maɗaurinta daya.'' Ga alama dai har yanzu da sauran kallo domin kowane ɓangare ya miƙa wa hukumar zaben jihar sunayen ƴan takaransu a zaɓen shugabannin ƙananan hukumomin jihar da kansiloli da za a yi ran biyar ga watan Fabrairu." https://www.bbc.com/hausa/labarai-59941132 +politics Mun bi ƙa'ida wurin tsige Mahdi Gusau – Kakakin Majalisar Zamfara "Kakakin majalisar dokokin jihar Zamfara a Najeriya, ya yi watsi da ce-ce-ku-cen da ake yi na cewa ba su bi tsari ba wurin tsige tsohon mataimakin gwamnan jihar Barrister Mahdi Aliyu Gusau. Yayin wata hira da BBC, Honarabul Nasiru Mu'azu Magarya ya shaida cewa rashin sanin abubuwan da suka faru ne ya sa wasu ke zargin majalisar da yin ba daidai ba. Ya bayyana cewa kundin tsarin mulki ne ya ba su dama domin gudanar da bincike don tsige gwamna ko mataimakin gwamna idan sun aikata wani laifi. Honarabul Nasiru ya ce duk wanda ya soki rawar da majalisa ta taka kan wannan lamari bai fahimci majalisa ba da irin aikin da take yi. ""Majalisar dokokin Jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancina ta karɓi duk abubuwan da ya kamata ta karɓa kuma ta bi tsari da kuma dokar da ƙasa da kundin tsarin mulki suka ba mu har aka kai wurin aiwatar da wannan. ""Duk wanda ya bi wannan tsari daidai, bai kamata ya zama abin suka ba sai dai idan ba a fahimci yadda tsarin yake ba,"" in ji shi. Tun kafin tsige tsohon mataimakin gwamnan, sai da aka kafa kwamitin bincike domin ya tantance zarge-zargen da ake yi masa, sai dai kwamitin bai ji ta bakin Barrista Mahdi ba har aka tsige shi sakamakon rashin zuwan gaban kwamitin da bai yi ba. Sai dai a nasa ɓangaren Honarabul Nasiru ya bayyana cewa "" abin da tsarin doka ya ce kwamitin na da alhakin ya gayyato shi, idan ya gayyato shi bai samu zuwa ba zai sake ba shi gayyata ta biyu, wanda kuma duka wannan kwamiti sai dai ya yi masa gayyata ta ɗaya da ta biyu. ""Kundin tsarin mulki ya ba kwamitin ƙarfin gaske na cewa idan ya gayyaci wanda ake tuhuma har sau biyu bai zo ba to laifukan da ake tuhumar shi da su sun tabbata domin da ba su tabbata ba da ba zai ƙi zuwa ba,"" in ji Honarabul Nasiru. Sai dai a wata hira da BBC ta yi da tsohon mataimakin gwamnan na Zamfara a kwanakin baya, ya ce abin da ya sa ya ƙi zuwa gaban kwamitin saboda umarnin da kotu ta bayar na cewa a tsayar da abubuwa cak a yadda suke. Sai dai Honarabul Nasiru ya bayyana cewa ba su saɓa umarnin kotu ba domin abin da kotu ta ce a tsaya a kan shi sun tsaya a kan shi inda ya ce wannan wani abu ne na daban" https://www.bbc.com/hausa/labarai-60774149 +politics Wanne tasiri rikicin APC zai iya yi a kan jamiyyar? "A bayyane take cewa rikicin da ke ruruwa a APC mai mulkin Najeriya ya taso ne a kokawar da wasu 'yan jam'iyyar suke yi na tabbatar da ikonsu gabanin zaben 2023. Zaben na 2023 ne zai tabbatar ko Kuma ya kore ikirarin da wasu masu nazari kan harkokin siyasa suka yi cewa APC ba jam'iyya ba ce, illa dai kawai wata gamayyar 'yan siyasa ne masu mabambantan ra'ayoyi da suka hadu domin kawar da jam'iyyar PDP daga mulki a 2015. Rikicin baya bayan nan shi ne game da hukuncin wata kotun Abuja wadda ta tabbatar da sauke Mr Adams Oshimhole daga shugabancin jam'iyyar. Mai Shari'a Danlami Senchi ne na kotun ta Abuja ya yanke hukuncin bayan karar da wani dan jam'iyyar APC, Oluwale Afolabi, ya shigar cewa tuni aka dakatar da Mr Oshiomhole daga jam'iyyar APC a jiharsa ta Edo. Mai Shari'a Senchi ya kuma haramta wa Mr Oshiomhole shiga hedikwatar jam'iyyar. Daga bisani an jibge jami'an 'yan sanda a kofar shiga hedikwatar jam'iyyar. Da alama wannan hukunci ya tayar wa Mr Oshiomhole hankali inda ya garzaya fadar shugaban kasa domin ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari. Kuma kamar yadda aka zata, ya shaida wa manema labaran fadar shugaban kasar cewa wasu gwamnoni ne na APC da kuma wasu manyan 'yan jam'iyyar suke son cire shi daga kan mukaminsa. Watakila za a iya cewa kalaman na shugaban APC da ke cikin rigima na da kanshin gaskiya ganin cewa sakatariyar gwamnonin APC ta bakin kakakinta Abdurrahman Barkindo ta fitar da sanarwar da ke goyon bayan hukuncin kotun. Sai dai a wani mataki da ake gani na samun goyon bayan gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ne, wata kotun tarayya da ke jihar ta Kano ta yi fatali da hukuncin kotun Abuja, inda ta jaddada cewa Mr Oshiomhole shi ne halastaccen shugaban APC. Amma kamar yadda masana siyasa ke cewa, masu yunkurin kawar da Mr Oshiomhole sun riga sun ja daga. Wani bangare da ke kiran kansa reshen APC da ke kudu maso kudancin Najeriya, wanda fitattun 'yan siaysar yankin irin su gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki da tsohon gwamnan Ribas kuma ministan sufuri Rotimi Amaechi ke cikin sa, ya nada Mr Victor Giadom a matsayin shugaban riko na jam'iyyar. An dade ana kai ruwa rana tsakanin Mr Obaseki, wanda shi ne mutumin da ya maye gurbin Mr Oshiomhole a matsayin gwamnan Edo da tsohon mai gidan nasa, lamarin da wasu ke gani shi ne silar sabon rikicin da ke kokarin cin kujerar Mr Oshiomhole. Watakila wannan sa-toka-sa-katsi ne ya sa daya daga cikin jiga-jigan jam'iyyar, Bola Ahmed Tinubu, ya fusata inda a wata wasika da ya rubuta a karshen makon jiya, ya yi zargin cewa zazzabin cutar samun mulki a 2023 ne ya kama mutanen da ke yunkurin cire Mr Oshiomhole daga shugabancin APC. Mr Tinubu ya ce ya zama wajibi 'yan jam'iyyar su hada hannu ""domin kawar da duk wata cuta"" a cikin jam'iyyar. ""Wata dadaddiyar cuta ce ta bukatar 2023, wadda ta damu wasu 'yan siyasa da kuma abokansu 'yan jarida,"" in ji Tinubu. Masana harkokin siyasa, irin su Dr Abubakar Kyari na Jami'ar Abuja da ke Najeriya, sun ce rikicin APC zai iya yi mata illa sosai idan ba a shawo kansa ba. Ya ce rikicin da wuya kuma a shawo kansa ganin cewa kowa da inda ya sa gaba a jam'iyyar. Dr Kari ya shaida wa BBC cewa ""Muna fada muna nanatawa cewa har yanzu APC ba ta zama cikakkiyar jam'iyya ba, gungu-gungu ne na mutane da ke da akidu daban-daban wadanda a baya ma fada suke yi da juna,"" in ji Dakta Abubakar Umar Kari, masanin kimiyyar siyasa a Jami'ar Abuja. Ya kara da cewa abin da kawai ya hada 'yan jam'iyyar APC shi ne ""wata dama da za su karbi mulki a shekarar 2015"". Wasu masana siyasa na ganin cewa rikicin APC ya soma ne tun lokacin tsayar da 'yan takara a zaben 2019 inda wasu 'yan jam'iyyar da ma mai dakin shugaban kasa Aisha Buhari suka yi zargin cewa shugabanta Mr Oshiomhole ya yi rashin adalci ga wasu masu neman yi wa jam'iyyar takara na mukaman gwamnoni da 'yan majalisu. A cewarsu, barinsa ya ci gaba da shugabancin jam'iyyar zai iya durkusar da ita, ko da yake Mr Oshiomhole ya sha musanta hakan yana mai cewa halayyarsa ta kin bari a rika juya shi kamar yadda wasu 'yan jam'iyyar suke so ne ta sa suke son cire shi daga mulki. Wani batu kuma shi ne yadda wani bangare da ke adawa da Mr Oshimohle ya bukaci a gudanar da taron kwamitin zartarwar jam'iyyar wanda ake gani ana son yin sa ne domin yin amfani da shi wurin cire shugaban jam'iyyar. Ko da yake taron da wasu gwamnonin jam'iyyar suka yi da Shugaba Buhari ranar Litinin, ya dakatar da gudanar da taron kwamitin zartarwar, wasu masana harkokin siyasa na ganin rikicin siyasar da yake ci gaba da ci a APC zai koma na saki-ka-noke ne kawai kuma nan gaba zai sake bullowa. Amma wasu masu nazari na gani taron koli na jam'iyyar ta APC da aka gudanar ranar Talata, inda shugabanta ya jagoranci yi wa wasu manyan jami'an jam'iyyar, wato mataimakin shugaban jam'iyar a yankin arewa maso yamma Senata Lawal Shu'aibu da kuma mataimakinsa Abdulkadir Inuwa afuwa bayan dakatar da su da aka yi tsawon wata shida, zai iya zama wata hanya ta dinke barakar jam'iyyar." https://www.bbc.com/hausa/labarai-51938589 +politics Dambarwa ta barke a jam’iyyar PDP a jihar Yobe Har yanzu tana kasa tana dabo, dangane da batun takamaiman dan takarar kujerar majalisar wakilai ta tarayya a jam’iyyar PDP ta mazabar Gujba da Gulani da Damataru da kuma Tarmasuwa a jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya. Hakan ya biyo bayan ja-in-jar da ake yi tsakanin Abdullahi Idris, wanda ya ce shi ne sahihin dan takarar wannan kujerar da aka zaba ba tare da hamayya ba, da kuma wasu shugabannin reshen jam'iyyar PDP a jihar ta Yobe, da suka ce wannan dan takara shi ya janye takarar tasa, saboda haka ake kokarin maye gurbinsa da wani. Duk wannan dambarwa, har yanzu dan takarar kujerar na farko Abdullahi Idiris, na nan a kan bakansa cewa shi ne dan takarar wannan kujera. Abdullahi Idris ya shaida wa BBC cewa shi ne cikakken dan takarar da ya sayi tikitin takara ya cike, kana kuma shi ne mutumin da aka tantance a matsayin dan takara. Ya ce “Ni ne kuma mutumin da aka bai wa takardar cewa ni ne na ci zaben fitar da gwani wanda kuma babu abokin hamayya, sannan ni ne wanda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta tabbatar a matsayin halattaccen dan takara.” Abdullahi Idris, ya ce a don haka a halin da ake ciki a yanzu ya garzaya kotu inda a karshe ma har kotu ta bashi takararsa. Ya ce, “ Duk da wannan hukunci na kotu har yanzu wasu shugabannin jam’iyya wanda wasunsu ne a cikinsu ke son a tunkubeni su kawo wani wanda ba a ma sanshi sun ce basu yarda ba.” Dantakarar na PDP, ya ce saboda biyayyarsa ga jam’iyyarsa da ya ga wannan dambarwa ta kunno kai ya nemi ayi sulhu amma wasu shugabanninsu suka ki. Abdullahi Idris, ya ce sun ce wai shi da kansa ya janye, sam shi dai ya san an kira shi an zauna da shi a kan cewa akwai wanda ya dawo jam’iyyarsu daga APC, to ana so ya janye ya bar masa Takara shi kuma ya ce sam. Dan takarar kujerar majalisar wakilan a PDP, ya ce, “To muka tashi ba a cimma yarjejeniya ba, sai kawai naji cewa wai har an kai sunan wanda suke son INEC, a nan ne na dauki matakin da naga ya dace ya dauka.” Cewa suka yi wai ni na rubuta takarda a kan cewa na janye na bar wa wancan takara, ni ma sai na rubuta ta wa takaradar nace bani na rubuta takarda da hannuna ba, in ji shi. Ko da BBC ta tuntube mai bawa jam’iyyar ta PDP a Yobe shawara kan abubuwan da suka shafi shari’a, Barista Ahmed Idris Waziri, ya ce yanzu magana tana kotu har ma an yanke hukunci, to amma tuni suka daukaka kara. Ya ce,” Mu wanda muka sani a matsayin dan takararmu a wadannan kananan hukumomi shi ne Honourable Ummaru Kulluma.” Yanzu dai muna jira ranar da za a ware mana don zama a kotun da muka daukaka kara, inji shi. A yanzu dai kallo ya koma kan yadda zata kaya game da ainihin dan takarar kujerar majalisar wakilan mazabun Gujba da Gulani da Damataru da kuma Tarmasuwa a jihar ta Yobe karkashin jam’iyyar ta PDP. https://www.bbc.com/hausa/articles/ceqyqdpxn4zo +politics 'Ina da hujjojin da ke nuna Buhari na neman wa'adi na uku' "Fitaccen lauyan nan me fafutukar kare hakkin dan adam a Najeriya, Femi Falana, ya zayyana dalilan da ya ce sun nuna Shugaba Buhari na son zarcewa a karo na uku. Femi Falana ya shaida wa BBC cewa Buhari na neman zango na uku ta hanyar sauya kundin tsarin mulki da zai ba shi damar tsawaita mulkin nasa. A farkon watan Oktoban da ya gabata ne dai shugaba Buhari ya musanta rade-radin da wasu ke yi na batun sake neman wani wa'adin. Mai magana da yawun shugaban, malam Garba Shehu ya ce ""Shugaba Buhari na son kammala wa'adinsa na biyu da zai kare a 2023, lokacin da za a sake gudanar da wani babban zaben kuma ba zai sake tsayawa ba."" Amma Falana ya zayyana wasu abubuwa da ya ce dukkansu alamu ne na shugabanni masu tsawaita zamansu a kan karaga a kasashen yammacin Afirka, inda kuma ya ce suna faruwa a Najeriya. Buhari ba ya sukar masu tsawaita mulki Falana ya bayar da Misalai da wasu kasashe inda ya ce shugaba Patrice Talon na Benin ya mayar da kasar bisa tsarin mai jam'iyya daya, haka nan ma a Togo, ta yadda za su tsawaita mulkinsu, kuma Najeriya ba ta ce komai ba game da hakan. Shugaba Alpha Conde na kasar Guinea shi ma ya kawar da duk wadanda yake ganin za su iya zama masa cikas domin tabbatar da aniyarsa ta yin mulki a wa'adi na uku, a Cote d'Ivoire ma abin da ke faruwa ke nan. Femi Falana ya kara da cewa Najeriya ita ce jagorar kasashen yammacin nahiyar Afirka, amma ba ta nesanta kanta daga duk wadannan abubuwa da suka saba wa kundin tsarin mulki ba. ""Akwai dokokin kungiyar ECOWAS a kan demokuradiyya da shugabanci wadanda suka kyamaci duk wani yunkuri na sauya tsarin gwamnati ba bisa ka'ida ba."" ""Bayan na yi la'akari da tarihin abubuwan da suka faru gare mu a baya da kuma abinda ke faruwa a yanzu, na yarda cewa lallai Buhari na son ya yi wa'adi na uku,"" in ji shi. 'Yancin kafafen yada labaru - Tsare Sowore Falana ya ce a Najeriya, masu kare hakkin bil'adama sun ce alamu sun bayyana karara, domin duk gwamnatin da ta rufe bakin kafafen yada labaru, ta mayar da kasar mai bin tsarin jam'iyya daya, ta haramta zanga-zanga koda kuwa ta lumana ce, ta yi wa 'yan ta'adda afuwa, ta kuma rinka hantarar 'yan jarida, to gwamnati ce wadda ba ta martaba dokokin kasa. ""Hakan karan-tsaye ne ga kundin tsarin mulki kuma shiri ne na lalata al'amuran kasa da share hanyar yin tazarce a karo na uku."" Falana ya ce ""Sun tsare Sowore ne domin su kashe jaridar Sahara reporters, domin Sahara reporters ta taka muhimmiyar rawa wajen dakile yunkurin Obasanjo na yin tazarce."" ""Ina kare Sowore ne saboda babu wata hujja da ta tabbatar da zargin da suke masa na cin amanar kasa. Ina da hujjojina wadanda zan bayyana su nan ba da dadewa ba."" Wata jarida ta cikin gida ta yi zargin cewa a lokacin gwamnatin shugaba Buhari ne 'yan jarida suka fi shan wahala cikin shekara 34. Sai dai shugaba Buhari a baya ya fito fili yana cewa gwamnatinsa tana martaba 'yancin yada labarai. Rikici tsakanin shugaban kasa da mataimakinsa Babban lauyan ya ce a duk lokacin da shugaban kasa ya tsangwami mataimakinsa, ya raunana karfinsa domin hana shi duk wani yunkuri na yin takara, hakan na nuna cewa akwai wani abu a karkashin kasa. A makon da ya gabata ne aka rage 35 daga cikin masu taimaka wa mataimakin shugaban kasar Yemi Osinbajo. Sai dai Mallam Garba Shehu, mai magana da yawun shugaba Buhari ya ce dalilin da ya sa aka rage ma'aikatan shi ne domin a rage yawan kudin da gwamnati ke kashewa, da kuma inganta hanyoyin tafiyar da al'amuran gwamnati. Rashin biyayya ga hukuncin kotu Femi Falana ya ce ""Babu matakin da aka dauka kan masu yekuwar tazarce amma an kama wadanda ke neman a daina karya umurnin kotu."" ""Babu wata gwamnati da za ta fito fili ta ce tana neman wa'adi na uku, mutane su ne za su gano da kansu ta hanyar la'akari da abubuwan da ke faruwa wadanda suka saba wa tsari na demokradiyya."" Ya ce tsarin mulkin Najeriya bai tanadi yin wa'adi na uku ga wanda ke kan kujerar shugabancin kasar ba." https://www.bbc.com/hausa/labarai-50374370 +politics Kotun Koli ta tabbatar da takarar Abba Kabir Yusuf "Kotun Kolin Najeriya ta tabbatar da Injiniya Abba Kabir Yusuf a matsayin halattaccen dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP a jihar Kano a zaben da ya gabata. Alkalan kotun sun tabbatar da hukuncin Kotun Daukaka Kara ta Kaduna wacce ta yi watsi da bukatar Ibrahim Al'amin (Little) na cewa PDP ba ta yi zaben fitar da gwani ba. Kotun ta ce Little, wanda ya yi nasara a kotun farko a Kano, ba shi da hurumin shigar da kara kan zaben da bai shiga ba. Abba Yusuf, wanda aka fi sani da ""Abba gida-gida"", ya sha kayi a hannun Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a karashen zaben da aka yi, duk da cewa shi ne kan gaba a zaben farko wanda bai kammala ba. Sai dai masu sa ido na gida da waje sun soki yadda aka gudanar da karashen zaben suna masu cewa an tafka magudi, zargin da jam'iyyar APC da kuma hukumar zabe suka musanta. A yanzu haka dai jam'iyyar PDP da dan takararta sun shigar da kara a kotun saurarar kararrakin zabe inda suke kalubalantar nasarar ta Gwamna Ganduje. Wannan hukunci ya kawo karshen takaddamar da aka dade ana yi kan halaccin zaben fitar da gwannin da jam'iyyar PDP ta yi a Kano. Masu lura da al'amura na ganin zai kuma bawa jam'iyyar PDP da magoya bayanta damar mayar da hankali kan shari'ar da suka shigar ta zaben na watan Maris. A yanzu haka dai kotun na ci gaba da zama, amma ba a kai ga yanke hukunci ba tukunna. A fakaice hukuncin ya kuma tabbatar da matakan da bangaren Kwankwasiyya na jam'iyyra ta PDP ya dauka a lokutan zaben fitar da gwanin, wanda shi ma ya haifar da ce-ce-ku-ce a fagen siyasar ta Kano." https://www.bbc.com/hausa/labarai-48681755 +politics Me ya sa Buhari ke jan ƙafa wajen sa hannu a ƙudurin dokar zaɓe? "An fara nuna fargabar cewa mai yiwuwa Shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya ba zai sa hannu kan sabon ƙudurin dokar zaɓen da aka yi wa garambawul a 2021 ba, duk da kwaskwarimar da Majalisun Tarayya suka sake yi mata. Ƙasa da mako biyu kacal ya rage wa shugaban ƙasar bayan tun farko ƙudurin dokar ya shafe wata ɗaya curr a hannunsa ba tare da ya yi hakan ba, saboda batun zaɓen fitar da gwani. Wasu dai na fargabar cewa zaɓen 2023 na iya zama ɗaya daga cikin mafiya rashin inganci a tarihin Nijeriya matuƙar aikin gyara dokokin zaɓen da aka shafe tsawon lokaci ana yi ya tashi a banza. Ƙudirin dokar zaɓen da aka yi wa garanbawul ta 2021 wadda kuma aka aika wa Shugaba Buhari tun ranar 31 ga watan Janairun 2022, ta cika kwana 15 kenan a ranar Talata 15 ga watan Fabrairun 2022 a fadar shugaban ƙasar. A bara sai da Shugaba Buhari ya shafe wata guda kafin sanar wa majalisa cewa ba zai sa hannu kan ƙudurin dokar ba. A karon farko batun zaɓen fitar da gwani ne hujjarsa ta ƙin sanya hannu. Sai dai a wannan lokaci kuma wasu rahotanni na cewa mutanen da suka hura wa waccar wuta sun sake zagayawa inda suke ci gaba da matsa wa Shugaba Buhari lamba. Bayanan sun ambato masu matsa lambar na ikirarin cewa ƙudurin dokar cike yake da wasu shaɗarori na nuna wariya kuma ba su dace da tsarin dimokuraɗiyya ba. Cikin masu nuna damuwa game da wannan jan ƙafa har da irin su Farfesa Jibrin Ibrahim, Darakta a Cibiyar Bunƙasa Harkokin Dimokraɗiyya da Ci gaban Ƙasa wato CDD. ""Abin da ke damunmu shi ne wataƙila suna so su gaya wa shugaban ƙasa ka da ya sa hannu. ""Dalili shi ne ranar Litinin da ta wuce mun ji Ministan Shari'a Malami yana cewa, ko da yake bai karanta ba, amma ya ce idan ya ga akwai son kai a ciki, zai bai wa shugaban ƙasa shawara kar ya sa hannu. ""To abin mamaki shi ne idan bai karanta ba me ya sa zai ce zai bayar da shawara kar a sa hannu. ""Akwai wani abu da ke baya kenan wanda dai, ko da yake ba mu sani ba, amma akwai jita-jita da yawa da suka ce, ana nan ana kamun ƙafa cewa kar shugaba ƙasa ya sa hannu, dalili shi ne, an ce ministocin da suke so su yi takara su sauka daga muƙamansu. ""Kuma wannan abin ba wani sabon abu ba ne, tun da aka kafa wannan, duk jamhuriyar nan huɗu haka ake yi,"" a cewar Farfesa Jibrin. Shi kuwa mai magana da yawun shugaban Nijeriya Malam Garba Shehu cewa ya yi ƙudurin dokar zaɓen har yanzu yana gaban Shugaba Buhari, kuma yana nazari a kansa, ""don tabbatar da yin adalci a ƙasa da su kansu al'ummar ƙasa. ""Duk abin da za a yi za a tabbatar da cewa ci gaba zai kawo ba tawaya zai kawo ga ƴanci ko ga ƙasa ba. ""Haƙiƙa a wancan lokaci abin da ya fi tsone ido shi ne wannan batu da shugaban ƙasa ya gabatar ga majalisa kuma suka amince. ""Amma ga duk wanda yake sa ido ga yadda abubuwa suke gudana a ƙasar na kai da komowarsu, suna jin irin sa'insar da ake yi a ce wannan a ce wancan ""Ba so nake na ce maka zai sa hannu ko ya ƙi sa hannu saboda abubuwan da ke ta tasowa yau da gobe a kan wannan batu ba. ""Wannan ya dogara kan irin shawarwarin da ya samu musamman daga ministansa na shari'a da kuma ɓangaren shari'a da ita kanta hukumar zaɓe. Masu nuna fargabar dai sun ce matuƙar Shugaba Buhari ya ƙi sa hannu a karo na biyu kan ƙudurin dokar zaɓen da aka yi wa gyarana fuska, hakan zai tilasta wa hukumar zaɓe ta INEC ta karkaɗe tsohuwar dokar zaɓe ta 2010, wadda suka ce tana cike da matsaloli. Daga cikin matsalolin har da batun wani hukuncin Kotun Ƙoli da ya ce babu hujjar yin amfani da na'urar tantance masu zaɓe, wani lamari da ake ganin na iya kawo gagarumin naƙasu ga zaɓen 2023." https://www.bbc.com/hausa/labarai-60386361 +politics Aisha Buhari: An yi wa Aisha ca don ta kira Buhari 'Janar' "'Yan Najeriya sun sako Mai Dakin Shugaban Najeriya a gaba sakamakon kiran shugaban da ""mai gaskiya"" da kuma inkiyarsa ta ""GMB"" (General Muhammadu Buhari) maimakon ""PMB"" wato President Muhammadu Buhari a wani sakon Twitter. Aisha Buhari ta wallafa sakon ne a shafinta na Twitter domin taya mijinta murnar cika shekara 77 da haihuwa a ranar Talata. ""Barka da murnar ranar haihuwa GMB nawa mai gaskiya,"" kamar yadda Aisha ta wallafa. ""Ina yi maka fatan Allah ya kare ka, ya kara maka lafiya domin ci gaba da jagorantar kasarmu. Allah ya bar mana kai GMB. Allah ya taimaki Najeriya!"" Kamar dai Aisha ba ta san mai zai biyo baya ba a lokacin da ta wallafa sakon, amma wane ne zai zargi wani abu kawai don mata ta yi wa mijinta fatan alheri sannan ta kira shi da sunan da ta ga ya dace? Su dai 'yan Najeriya ba a bar su a abaya ba kamar yadda suka saba, kuma Haidar Aliyu (@Haidar_Michika) ya ce: ""Tun da Mama ma ta kira shi da GMB wane ne ni da zan kira shi da PMB!"" Shi kuwa Martin's Izonowei (@SIzonowei) cewa ya yi ""idan da gaske mai gaskiya ne to sai ya gina mana asibitoci masu kyau, ko kuwa wannan ba ya cikin abubuwa bakwai?"" Shi kuma Albadoh (@MAlbadoh) ya ce ne ""ai sunansa ne duka kuma ya cancanci sunayen"". Wani mai suna Blessed Beyond Measure (BBM) @Drmuzoic cewa ya yi ""ina fatan za ki samu damar tattaunawa da 'mai gaskiyar naki' GMB a daki"". Kasancewarsa tsohon shugaban mulkin sojin kasar, gabanin hawansa karagar mulkin farar hula a shekarar 2015, Buhari ya zabi yi wa kansa inkiya da GMB (General Muhammadu Buhari). Daga baya ma ya ce zai rika manna ""GMB"" a jikin duk abin da ya wallafa a shafukan sada zumunta. Bayan hawansa kan mulki ne kuma ya ce ya fi son a rika kiransa da PMB wato (President Muhammadu Buhari) maimakon GMB saboda yanzu shi mai shugabanci ne a tsarin dimokuradiyya, ba soja ba. Sai dai kuma a makon da ya gabata ne jaridar The Punch ta ce za ta ci gaba da kiran Shugaba Buhari da inkiyarsa ta da wato Janar Buhari maimakon Shugaba Buhari. Punch ta ce ta dauki wannan mataki ne ""saboda take hakkin dan Adam da gwamnatin Buhari take yi musamman ci gaba da tsare Omoyele Sowore da hukumar DSS take yi"" kuma ta kwatanta mulkinsa na yanzu da na mulkin soja. ""Shugaba Buhari"" aka ci gaba da kiransa musamman a kafafen yada labarai kafin Punch ta dauki waccen mataki. Kwatsam a ranar Talata kuma sai ga shi Mai Dakin Shugaban ta fito fili ta kira shi da GMB, abin da ya jawo martani iri-iri daga 'yan Najeriyar. Wani mai suna Young_Journalist (@Abubakar_Mhmmad) ya ce: ""General Muhammad Buhari😂😂😂 ni ma na dana"". Shi kuwa Uche Samuel (@uchesame) cewa ya yi ""lallai kuwa mai gaskiya"". General Ola Azeez. (@Azeezsaka14) ya ce ""Murnar ranar haihuwa, mun gode wa Allah, Mama ma ta bi""." https://www.bbc.com/hausa/labarai-50824533 +politics Osinbajo ne ya fi cancanta da shugabancin Najeriya - Abdurrahman Baffa Yola "Mai bai wa Mataimakin Shugaban Najeriya, Yemi Osinbajo, shawara kan harkokin siyasa ya ce suna fatan Bola Ahmed Tinubu zai ci girma ya bar wa mai gidansu takarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyya mai mulki ta APC saboda ya fi shi cancanta. Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da jagoran APC na ƙasar ya sanar da aniyarsa ta tsayawa takara kuma yake ci gaba da ziyartar muhimman mutane don neman goyon baya. Mataimakin shugaban wanda yaron siyasar Bola Tinubu ne amma ana ganin alamun cewa shi ma yana sha'awar tsayawa takarar shugabancin Najeriya a zaɓen 2023. Mai ba mataimakin Shugaban shawara Abdurrahman Baffa Yola, ya shaida wa BBC cewa Osinbajo, mutum ne mai sha'awar ci gaban kasarsa. Ya ce,""Bisa la'akari da yadda mataimakin shugaban Najeriyar ke kishin kasarsa, to idan har aka bashi damar kasancewa shugaban kasar to ko shakka ba bu zai yi wa kasarsa aiki"". Abdurrahman Baffa Yola, ya ce"" Ba wai Osinbajo ya bayyana cewa yana son takarar shugabancin Najeriya bane, to amma mu da muke aiki tare da shi muna karbar sakonni a kullum, kuma muna ganin yadda kungiyoyi ke kira gareshi da ya tsaya takarar"". Ya ce, har yanzu Osinbajo bai furta cewa zai tsaya takarar ba, aikin da aka dora masa shi ne a gabansa a ko da yaushe. ''Dangane da yadda zata kasance tsakanin mataimakin shugaban Najeriyar da kuma Bola Ahmed Tinubu, wanda uban gidansa ne kuma ya fito ya nuna sha'awar sa ta fitowa takarar shugaban kasa, mu zamu barwa lokaci, amma kuma shi kansa Tinubun ya san nagartar Osinbajo"". Ya ci gaba da cewa ""Mu muna ganin nagartar Osinbajo ta fi ta Tinubu, kuma muna sa ran idan har mataimakin shugaban kasar ya amsa kiraye-kirayen da ake masa na tsayawa takarar shugaban kasa, to shi kansa Tinubun zai iya cin girma ya bar kaninsa"". Mai bai wa mataimakin shugaban Najeriyar shawarar ya ce ''ba wai mu kadai ne muke ganin cancantar Osinbajo ba, idan aka yi la'akari da gogewarsa da iliminsa, za a iya cewa ba bu wanada ya zama ya kai shi gogewa da kuma cancantar tsayawa takarar shugaban Najeriya a jam'iyyar APC." https://www.bbc.com/hausa/labarai-60473313 +politics Godwin Obaseki: APC ta hana shi takara Kwamitin da ke tantance 'yan takara na jam'iyyar APC a jihar Edo ya haramta wa gwamnan jihar Godwin Obaseki shiga zaɓen fitar da gwani wanda za a gudanar kafin tsayar da ɗantakarar gwamna. Shugaban kwamitin, Jonathan Ayuba ne ya bayyana hakan yayin da ya ke bayar da rahoton ayyukan kwamitin ga shugaban jam'iyyar APC Adams Oshiomhole. Ya bayyana cewa an haramta wa Obaseki tsayawa takarar ne sakamakon matsalar da ake ganin akwai tattare da takardun makaranta na gwamnan. Sai dai a wani ɓangaren kuma, kafofin yaɗa labarai na Najeriyar sun ruwaito cewa Mista Obasekin ya ce ba zai ɗaukaka ƙara ba. An dai kwana biyu zaman doya da manja tsakanin Obaseki da Shugaban Jam'iyyar APC Adams Oshiomhole, wanda hakan ya kawo rabuwar kai musamman a jam'iyyar APC reshen jihar Edo. Gwamna Obaseki ne dai ya gaji Adams Oshiomhole bayan ya sauka daga gwamnan jihar a 2016. https://www.bbc.com/hausa/labarai-53030406 +politics INEC za ta ci gaba da bayar da rijistar masu zabe A farkon makon gobe ne, ake sa ran hukumar zaɓe mai zaman kanta a Nijeriya INEC za ta ci gaba da aikin ba da rijistar masu zaɓe a faɗin ƙasar a shirin tunkarar zaɓen 2023. INEC ta ce a wannan karo, waɗanda suka cancanci yin rijistar za su fara shigar da bayanansu ne ta intanet kafin daga bisani su ke ƙafa-da-ƙafa su kammala a cibiyoyin rijistar da za a samar. Hukumar zaɓen wadda nan gaba a yau ne za ta ƙarƙare shirye-shiryen aikin rijistar, ta ce burinta shi ne yi wa 'yan Nijeriya miliyan 20 rijista kafin zaɓen ƙasar mai zuwa. Daraktan hulɗa da jama'a na hukumar, Mista Nick Dazan ya shaidawa BBC cewa bayan tuntuba da suka yi da masu ruwa da tsaki a makon da ya wuce,wato shugabannin jam'iyyu 18, da kuma kungiyoyi masu zaman kansu, da 'yan jarida da shugabannin jami'an tsaro. ''Insha Allahu ranar 22 ga watan nan kwamishinoni na tarayya za su yi nazari akan tuntubar da muka yi, sannan su fitar da jadawalin yadda na yadda wannan rijista za ta kasance.Amma tabbas kamar yadda mukai bayani tun da farko, za a fara yin wannan rijista ranar Litinin 28ga watan Yuni 2021. Kuma wadanda suka cancanci yin rijistar sun hada da wadanda a baya ba su taba yin rijistar zabe ba, da kuma shekarunsu ya kai 18, da wadanda suke son sabunta rijistarsu musamman wadanda katinsu ya ke da matsala ko dai zanen rubutu ya goge da wadanda aka samu kuskure wajen rubuta sunansu, da wadanda sukai kaura daga wata jiha zuwa wata da sauransu.,'' inji Mista Nick. Mista Nick ya kara da cewa, a wannan karon ma za a yi rijistar ne ta internet, wanda akwai manhaja ta musamman da za a shiga si a sanya bayanan mutum, wato suna da unguwarka da kuma shekaru da sauransu. Bayan an gama da wannan fannin, mutum zai garzaya cibiyoyin hukumar zabe domin a dauki hoton ka da zanen yatsu. daga nan za a bai wa mutum katin wucin gadi kamar yadda ake yi a baya. Amma daga baya idan an gama tantancewa za abai wa mutum kati na dindindin da za a yi amfani da shi a lokacin zabe. Sai dai Mista Nick ya ce yankunan karkara ma ba a barsu a baya ba, sanin cewa babu internet a wuraren, ''daman makasudin amfani da internet shi ne a rage cinkoso a cibiyoyin hukumar zabe kamar yadda aka samu a baya, don haka su tsohuwar hanyar rijista za a bi wajen yi musu.'' Hukumar zaben INEC ta ce kawo yanzu an yi wa kimanin mutum miliyan 84, ana kuma sa ran za a yi wa mutum miliyan 100 nan ba da jimawa ba. Za dai a dauki shekara daya ana gudanar da wannan aiki na yi wa 'yan Najeriya rijistar zabe. https://www.bbc.com/hausa/labarai-57562350 +politics Najeriya: Jam'iyyar APC za ta sasanta rikicin 'ya'yanta a Kano "A jihar Kano, jam'iyyar APC mai mulki ta wayi gari cikin dakon wani sabon tsarin da uwar jam'iyyar ta kira ""wanda zai shigar da kowa a dama da shi"" cikin harkar shugabanci. Duka ɓangarorin biyu, tsagin Sanata Shekarau ko kuma G7, da kuma na Gwamna Ganduje na kira ga uwar jam'iyyar ta tabbatar da adalci. Jam'iyyar APC ta ce bayan sanar da wannan tsari, za ta kafa wani babban kwamiti da zai je Kano don tabbatar da cikakken aiki da shi. Tun a shekarar 2021 ne, bangaren Gwamna Ganduje da na Sanata Shekarau, suka sa zare. Zabukan shugabannin jam'iyya a matakin kananan hukumomi da na mazabu da kuma na jiha ne suka jefa jam'iyyar cikin wannan rikici. Har yanzu kowanne bangare na fatan a ce shi ne ke jagorancin APC a Kano. Bayan jerin tattaunawa da uwar jam'iyyar ke shiga tsakani, a karshe ana iya cewa za a sansanta komai. Tuni wasu jagororin jam'iyyar a Kano suka fara tausar zukatan 'ya'yan jam'iyyar, kamar sanata Ibrahim Shekarau. Sanata Shekarau ya shaida wa BBC cewa a halin yanzu suna jiran karbar wadannan ƙa'idoji da matakan sulhu daga uwar jam'iyya. Sanatan ya ce,""Ina kira ga wadanda ke cewa ba sa son sulhu da su tuna cewa maganar sulhu umarni ne daga Allah (SWA)"". A nasu bangaren tsagin gwamna Ganduje ta bakin Honourable Kabiru Alasan Rurum, ya ce suna fatan su tsarin da uwar jam'iyyar za ta kawo ya mutunta tare da daraja kowanne bangare don samun zaman lafiya da kwanciyar hankain da za su iya tunkarar babban kalubalen da ke gabansu a zaben 2023. Kano dai babbar jiha ce da APC ta daɗe tana nanata tasirinta a siyasar Najeriya, abin da yasa APCn ke ƙara ƙoƙari wajen ganin ta hana wannan ɓaraka da ta kunno kai a jihar ƙara tsawo da faɗi. To ko wannan haƙa ta Jam'iyyar APCn za ta cimma ruwa? Lokaci ne kawai zai raba wannan gardamar." https://www.bbc.com/hausa/labarai-60284001 +politics Shekarau 'ya koma' jam’iyyar PDP "Tsohon gwamnan Kano kuma ɗan majalisar dattawa Malam Ibrahim Shekarau ya koma jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya 'yan watanni bayan komawarsa NNPP. Wata majiya mai karfi da ke da kusanci da tsohon gwamnan ta shaida wa BBC Hausa cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, Atiku Abubakar, ya gabatar wa Shekarau da tsare-tsarensa kuma sun amince da su. Atiku ya isa Kano a yammacin Lahadi amma sai Litinin ake sa ran zai gana da kuma karɓar Shekarau a hukumance zuwa PDP. Shekarau ya ɗauki matakin komawa PDP sakamakon abin da ya kira ""rashin adalci"" da Rabiu Kwankwaso ya yi musu, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa kuma jagoran jam'iyyar NNPP. ""Gaskiya ne mun shirya tsaf don tarɓar Atiku a Kano don su nemi hannun Malam bayan Shekarau ya yi wa majalisar Shura bayanin halin da ake ciki a NNPP,"" a cewar majiyar. Atiku zai je Kano tare da Shugaban PDP na Ƙasa Iyorchia Ayu da sauran jiga-jigan jam'iyyar. Tun bayan da ɓangaren Shekarau ya nuna damuwa game da rashin adalcin da aka yi musu a jam'iyyar NNPP, majalisar tuntuɓa ta tsohon gwamnan - wadda ake shura - ta fara nema wa tsagin makoma ta hanyar tattaunawa da sauran jam'iyyu. Majiyar da ta zanta da BBC ta ce sun kammala shirin tarɓar Atiku tsaf a Kano ranar Litinin bayan sun yi nazari kan tsare-tsaren da ya gabatar musu. ""Sun gabatar mana da tsare-tsarensu, mun yi nazari a kansu kuma za mu karɓe su. A taƙaice dai sanarwa kawai ake jira."" Sanata Ibrahim Shekarau ya koma jam'iyyar NNPP a watan Mayun da ya gabata daga APC mai mulkin Kano bayan rikici tsakaninsa da Gwamna Ganduje, wanda ya kai ga zaɓar shugabannin jam'iyyar biyu. Daga cikin dalilan da ya zayyana akwai cewa shugabancin APC a Kano ya gaza cika alƙawuran da ya ɗauka na tafiya tare da shi da magoya bayansa a harkokin jam’iyar. Kazalika, wannan dalilin ne ya sa zai bar jam'iyyar a yanzu bayan ya zargi Kwankwaso da NNPP da ƙin cika alƙawuran da suka yi kafin su koma jam'iyyar tasu. Sai dai Kwankwaso ya ce Shekarau da jama'arsa sun shigo jam'iyyar ""a makare"". Cikin hirarsa da BBC Hausa a farkon makon nan, Shekarau ya ce babu gaskiya a batutuwan da jagoran jam’iyyar NNPP Rabi’u Musa Kwankwaso ke yi cewa sun shigo jam’iyyarsa a makare. Wata majiya ta bayyana cewa tun farko an yi yarjejeniya cewa za a bai wa ɓangaren Shekarau kashi kusan 35 na muƙamai, amma daga baya shi kaɗai aka bai wa tikitin takarar sanata. A nasa ɓangaren, Kwankwaso ya ce sun shiga jam'iyyar a makare amma sun faɗa wa Shekarau cewa su bari a kafa gwamnati don a daidaita rabon. Duk da cewa Malam Shekarau bai ambaci ko tabbatar da jam’iyyar da zai koma ba a loƙacin idan ya bar NNPP, ya nuna rashin jin daɗinsa kan hana su wasu muƙamai da kuma hana magoya bayansa damar takara a NNPP ɗin. ""Shi jagoran jam'iyyar Rabi'u ne ya faɗi cewa ba mu shigo jam'iyya da wuri ba, kuma bai yi mana adalci ba,"" a cewarsa. ""Tun daga loƙacin da aka fitar da sunayen 'yan takarar muka yi ƙorafi kuma aka ce mana za a duba, amma har loƙacin da hukumar zaɓe ta tanada na sauya sunan 'yan takara ya wuce ba a yi komai ba."" Shekarau ya ce babu mamaki kwamitin da aka kafa karkashin ɗan takarar gwamnan Kano a NNPP, Abba Kabiru Yusuf, su ne suka dinga jan kafa." https://www.bbc.com/hausa/articles/cj73k7j59zyo +politics IPOB: Sojojin-baka masu son kafa Biafra da ke kira a kashe mutane a Facebook a Najeriya "Wani gungun 'yan Najeriya a wajen ƙasar da ke son kafa ƙasar Biafra na amfani da shafukan zumunta don haddasa tashin hankali da kuma tunzura magoya bayansu don far wa masu adawa da su, kamar yadda wani binciken BBC ya gano. Gargaɗi: Wannan maƙalar na ƙunshe da bayanan tashin hanakali Yayin wani shiri kai-tsaye a Facebook da take yaɗa wa mabiyanta fiye da 40,000, Efe Uwanogho wadda kuma aka sani da Omote Biafra, na ta yin kalaman ƙiyayya ta bidiyo. ""Ku far wa waɗannan manyan maƙiyan...Su ne mutanen da ya kamata a fille wa kawuna. Su ne waɗanda ya kamata a ƙona ƙurmus,"" a cewarta. Gaban rigar da take sanye da ita na ɗauke da tutar Biafra - wadda ke ƙunshe da launin ja da baƙi da wani ɗan kore, sai kuma ƙwalln rana da ke fitowa. Tana kira ne da a kai wa masu adawa da yunƙurin kafa Biafra hari, da ke son kafa sabuwar ƙasa a yankin kudu maso gabashin Najeriya. Gwagwarmayar kafa Biafra na ƙunshe da tarihin zubar da jini. A shekarar 1967 ne 'yan aware da akasarinsu 'yan ƙabilar Igbo ne suka ayyana 'yancin kai na Jamhuriyar Biafra. Sun fafata yaƙin basasar da ba su yi nasara ba tare da gwamnatin Najeriya, inda aka kashe mutum fiye da miliyan ɗaya mafi yawansu daga ɓangaren 'yan tawayen. Kusna rabin ƙarni bayan haka, shafukan sada zumunta sun zama filin dagar waɗanda suke son kafa Biafra har yanzu. Ms Uwanogho na cikinsu. Ana yi mata laƙabi da ""gwarzuwar kafar yaɗa labarai"" ta ƙungiyar 'yan tawayen da ake kira Indigenous People of Biafra (Ipob). Tana yaɗa abubuwa daga Italiya, inda mahukuntan Najeriya ba za su iya cim mata ba. Ƙungiyar Ipob haramtaciyya ce a Najeriya kuma ta 'yan ta'adda, kodayake ƙungiyar ta dage cewa gwagwarmayarta ta zaman lafiya ce. Binciken BBC ya gano wasu manyan magoya bayan ƙungiyar da ke mata aiki a wajen Najeriya, suna yaɗa kalaman ƙarya ƙarara da kuma tunzura tashin hankali a shafukan zumunta a faɗin nahiyar Turai da Asiya da kuma wasu yankunan Afirka. Ɗan jaridar Najeriya mai biciken ƙwaƙwaf, Nicholas Ibekwe, ya siffanta ayyukan ƙungiyar a intanet da ""gonar girbe tsangwama"". ""Shafukan zumunta ne babbar hanyar da Ipob ta fi yin nasara wajen yaɗa dukkan abubuwan da ta sa a gaba,"" a cewarsa. Wasu daga cikin magoya bayan ƙungiyar na da mabiya kusan 100,0000 a shafukan zumunta. Ba mu sani ba ko wani daga cikin mabiyan Ms Uwanogho ya taɓa bin umarninta wajen kai wa mahukunta hari a kudu maso gabashin Najeriya. Ms Uwanogho ba ta amsa ba lokacin da muka nemi martaninta a lokacin haɗa wannan rahoto. Amma tashin hankalin na ci gaba da faruwa ƙarara, yayin da tuni aka kashe gwamman jami'an gwamnati a wannan shekarar a hare-haren da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana da ""mai ta da hankali sosai"". Nneka Igwenagu wata ""gwarzuwar kafar yaɗa labarai"" ce da ke fafutikar kafa Biafra, amma tana zaune a Birtaniya. Yayin wani shiri da take yaɗawa kai-tsaye daga birnin Landan a 2021, tana neman jan hankalin matasa daga kudu maso gabashin Najeriya da suka dinga ƙin bin umarnin Ipob na durƙusar da harkokin kasuwanci da makarantu don nuna goyon baya ga jagoran ƙungiyar Nnamdi Kanu da ke tsare. Yanzu haka hukumomi a Najeriya na tsare da Nnamdi Kanu da ke fuskantar tuhumar ayyukan ta'addanci, waɗanda ya musanta. Da take magana cikin harshen Igbo, harshen da aka fi yi a kudu maso gabas, Ms Igwenagu na kiran su da ""kaji"" tana mai cewa: ""Bai kamata ku rayu ba dukkanku...Kazar da ke cinye ƙwanta, ba kwa ganin bai kamata ta rayu ba?"" 'Yan makonni bayan shirin da ta yaɗa aka kashe shugaban ƙungiyar da take magana a kan sa. Babu wanda aka kama balle tuhuma da kisna nasa. Mun nemi martanin Ms Igwenagu game da wannan binciken, amma ba mu samu komai ba. Ɗaya daga cikin hanyoyin da 'yan gwagwarmayar ke amfani da su don guje wa mahukunta ita ce yin amfani da harsunansu na al'ada waɗanda ba kasafai ake iya tantance abubuwan da suke faɗa ba. Dabarar ta girmama cikin wani bidiyo da Okenna Okechukwu, wanda aka sani kuma da Biafran Child (Ɗan Biafra), yake magana da harshen Igbo inda yake neman a fille kan wani mai sukarsu, kafin daga baya ya koma magana da Ingilishi yana cewa: ""Dalilin da ya sa nake amfani da harshena shi ne ba na so su dakatar da ni. Ba na son su dakatar da ni daga wannan dandalin."" David Ajikobi, editan Najeriya na shafin bin diddigi mai suna Africa Check, ya ce ƙarancin lura da abubuwan da ake faɗa da harsunan cikin gida babbar matsala ce, kuma ba wai a Najeriya kaɗai matsalar ta tsaya ba. ""Mun lura da hakan a Indiya, da Ethiophia, inda ake fama da rikice-rikice. Mutane na amfani da harsunansu na uwa ne saboda sun san idan suka yi amfani da Ingilishi za a gane su kuma a toshe shafukansu daga dandalin."" Duk da abubwuan tashin hankali da muka gano, dandalin zumunta ba su fiya sa ido kan maganganun ba. Bisa ƙa'idojin da Facebook ya shimfiɗa wa kan sa, mun ba da rahton cewa shirye-shiryen da Efe Uwanogho da Nneka Igwenagu ke yaɗawa na ƙunshe da tashin hankali. Da farko sai aka ba mu amsar cewa Facebook ba zai goge bidiyoyin ba. Sai daga baya da BBC ta yi magana da Facebook kai-tsaye sannan aka cire su. Amma har zuwa lokaci haɗa wannan rahoton akwai bidiyo masu tunzura tashin hankali a shafukan jibge. Kamfanin Meta da ya mallaki Facebook ya faɗa mana cikin wata snaarwa cewa kiran tayar da fitina haramun ne a dandalin. Ya ce akwai mutum 15,000 da ke bincika saƙonni a harsuna fiye da 70 - ciki har da Igbo. Binciken namu kuma ya gano yadda mambobin Ipob ke yaɗa labaran ƙarya don ingiza fitina tsakanin ƙabilu a Najeriya. 'Yan gwagwarmayar na ingiza 'yan ƙabilar Igbo, waɗanda akasarinsu Kiristoci ne kuma mazauna kudanci, a ƙabilar Fulani, waɗanda akasarinsu Musulmai ne kuma mazauna arewaci. A wani bidiyon na Facebook, Ms Igwenagu ta gargaɗi Igbo cewa 'yan Arewa da Fulanin da suka shiga ""ƙasar Biafra"" na da wata manufa...""ta shafewa da kashewa da share mu baki ɗaya"". Binciken namu ya gano cewa ana ba wa ire-iren waɗan nan 'yan gwagwarmayar lada sakamakon abubuwan da suke wallafawa a shafukan zumunta. Mun ga wasu bidiyo da su kansu 'yan gwagwarmayar ke amsa cewa na biya su, ko dai daga Ipob ko kuma magoya bayansu, saboda ayyukan da suke gudanarwa, kuma mun ga bidiyon da ake yaɗa bayanan asusun ƙungiyar da ke neman a taimaka mata da kuɗi. ""Da alama Facebook barci yake kawai. Ba sa tunanin cewa waɗan nan kalaman da suke yi, waɗannan saƙonnin da ke kan Facebook na da tasiri,"" in ji ɗan jarida Nicholas Ibekwe. A ranar 30 ga watan Afrilu, an kai wa sojojin Najeriya Audu Linus da Gloria Matthew hari kan hanyarsu ta zuwa bikin gargajiya na ɗurin aurensu a Jihar Imo. An sace su, aka azabtar da su sannan aka kashe su. Daga baya wani bidiy ya ɓulla na yadda aka kashe ma'auratan, wanda Shugaba Buhari ya zargi Ipob da aikatawa. Sai kuma wasu maganganu suka fara ɓulla a intanet da magoya bayan Ipob ke cewa bidiyon ba na gaskiya ba ne kuma shirya kisan sojojin aka yi. Sai dai BBC ta tabbatar da kisan sojojin biyu daga danginsu. Ipob ta musanta hannu a kisan. Mun tuntuɓi shugabannin Ipob game da abin da muka gano. Sun amsa amma ba su ba da wani bayani ba. Mun tuntuɓi dukkan ""gwarazan kafofin yaɗa labaran"" da muka ambata a wannan labarin don su yi martani, amma ba su ce komai ba." https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-61420366 +politics Gudaji: APC ce ta yi wa takarata kafar ungulu "A Najeriya kimanin watanni uku kenan, bayan da jam'iyyar APC mai mulkin kasar ta yi tsayuwar daka wajen tabbatar da an gudanar zaben shugabannin majalisar dokokin kasar bisa tsarin da ta ga ya dace. Honarabul Muhammad Gudaji Kazaure, dan majalisar wakilai ta Tarayya daga jihar Jigawa na daga cikin wadanda suka nemi kujerar shugabancin majalisar wakilan. Ya kuma shaidawa BBC cewa bai ji dadi ba da bai samu kujerar ba, sai dai ya yi zargin jam'iyyarsu ta APC ce ta yi wa takararsa kafar ungulu. ""Ban ji dadi ba da aka dakatar dani, domin nasan idan talakawan Najeriya ne ke zabar kakakin majalisa na tabbatar ni za su zaba. Karfa-karfa ce jam'iyya tayi mana aka ce dukkan mai takara ya hakura ya bi wane, kuma dole muka yi biyayya"", inji Gudaji. Duk da cewa Honarabul Gudaji ya amince hakan ya sabawa tsarin dimukradiyya, amma ya ce jam'iyya ta koyi darasi kan halin da ta samu kanta a ciki a wancan wa'adin mulkin da ya wuce. Gudaji ya kara da cewa, ""Jam'iyya ta duba da ta bada dama a shekara ta 2015, sai aka yi kulle-kulle a majalisa aka kada ita jam'iyyar, abin da ya janyo aka samu matsaloli a majalisar dattijai yadda duk abin da shugaban kasa ya kawo sai su ce ba za su yi ba. Yanzu an yi haka sai aka dauki wannan mataki dan a samu daidaito tsakanin bangaren zartarwa da majalisa"". Kuma daga dukkan alamu kwalliya ta fara biyan kudin sabulu, idan akai la'akkari da yadda aka tantance ministoci cikin takaitaccen lokaci ba kamar wancan wa'adin mulkin ba." https://www.bbc.com/hausa/49785384 +politics Muhammadu Buhari: Ko Majalisar Dattawan Najeriya ta zama 'yar amshin shatansa? "A ranar Laraba 11 ga watan Yunin 20202 ne Majalisar Dattawan Najeriya ta tara ke cika shekara guda da fara aiki gadan-gadan. Majalisar dattawan ta tara ita ce majalisar da shugabanninta suka fi na kowace majalisa ɗasawa da bangaren zartarwa a tsakanin nan sakamakon sun fito ne daga jam'iyya ɗaya da ta shugaban kasa, waɗanda kuma suka samu tubarrakinsa. Ana ganin sakamakon dakan ɗaka, shikar ɗakan da aka yi wurin zaɓen shugabannin ne ya sa hakan ta faru. Duk da cewa ɓangaren majalisa da na zartarwa kowanne zaman kansa yake, kuma sukan taka wa juna birki idan bukatar hakan ta taso, daya daga cikin 'yan majalisar dattawan Sanata Yahaya Abdullahi ya bayyana cewa irin fahimtar da ke tsakanin shugabannin majalisar dattawa ta wannan jumhuriya da kuma ɓangaren shugaban ƙasa ta sa ba a jin kansu. Sanata Yahaya ya ce su sun fi gaban 'yan amshin shata, don a cikinsu ''akwai tsofaffin gwamnoni da ministoci da gogaggu a fannoni dabana-daban, don haka suna yin komai ne bisa kwarewa da kulawa.'' Wannan zaman lumanar ne ya sa majalisar cimma nasarori da dama, kamar yadda shugaban masu rinjayen ke cewa, ciki har da zartar da kasafin kuɗin kasar na wannan shekarar a farkon shekara, lamarin da ba kasafai yake faruwa ba, da kuma amincewa da kusan dukkan muhimman bukatun da bangaren zartarwa ya tura wa majalisar. Sai dai kuma wasu masana harkokin siyasa na sukar dangantakar da ke tsakanin bangaren majalisar dattawan da na zartarwa, wadda suka ce ta zarce ta aiki da juna inda suke cewa ta zama tana biyayya ido rufe. Farfesa Jibrin Ibrahim, jami`i ne na cibiyar raya dimokuradiyya ta CDD kuma yana da irin wannan ra'ayin inda ya bayyana cewa aikin majalisa shi ne su duba duk wasu ayyuka da bangaren zartarwa da kawo domin ganin ko akwai kurakurai su gyara. Ya ce ""wannan aikin nasu shi ne ake gani kamar ba sa yi, shi ya sa yanzu mutane ke kallonsu kamar 'yan amshin shata."" Wasu masana da 'yan Najeriyar da dama na zargin cewa 'yan majalisar sun gaza wajen yin aikinsu, saboda a cewarsu hatta kasafin kudin 2020 din ma sun zartar da shi ne ba tare da cikakken nazarinsa ba. Haka kuma, wasu 'yan ƙasar suna zargin su da cushen ayyuka. Ko bayan da aka sake mika musu kasafin kuɗin don sake masa fasali bayan bullar cutar korona, wasu na kushe majalisar da rage kason wasu ɓangarori da suka hada da kiwon lafiya da ilimi, amma ba su yi watsi da batun yi wa ginin majalisar dokokin kwaskwarima da wasu biliyoyin naira ba. Sai kuma sukarsu da ake yi da saurin amincewa da buƙatun shugaban ƙasa da dama ciki har da batun karɓar rancen biliyoyin daloli, wanda watakila sai jikokin da za a haifa gaba ne za su biya bashin, da kuma amincewa da sunayen ministoci da na hukumomi ba tare da tambaya ba. Sai dai Sanata Yahaya Abdullahi ya ce wani lokaci ana jahiltar yadda suke aikinsu, dangane da maganar rance kuma ya ce za su yi aikinsu na sa ido wajen ganin an kashe kuɗin ta hanyar da ta dace. ''Mu ba mun zo ne a yi wani kalubale da juna ba tsakanin mu da bangaren zartarwa, abin da muka zo shi ne a hada kai da wancan bangaren a yai wa Najeriya aiki. Duk wani kalubale da ba zai kawo maslaha da ci gaban kasa ba to ba shi da amfani gare mu da wadanda suka zabe mu. ''Idan akwai abin da muka ga sun kawo wanda ba zai taimaki ci gaban kasa ba, to ba za ma mu bari a zo ana fallasa a nan ba, tun daga gabatar da shi za mu mayar da shi.'' a cewar Sanata Yahaya." https://www.bbc.com/hausa/labarai-52996025 +politics Tasirin soshiyal midiya a siyasar Najeriya "Ma`abota rubutu da wallafe-wallafe da ke goyon bayan jam`iyya ko `yan siyasa a Najeriya, wadanda aka fi sani da `yan ""soshiyal midiya"" na kara karfi  a siyasar kasar. A halin da ake ciki sun kai matsayin da ana damawa da su a kusan kowanne matakin gwamnati da rukunin `yan siyasa. ‘Yan soshiyal midiya a Najeriya na da karfin gaske kasancewar suna taka muhimmiyar rawa wajen daukaka jam`iyya ko dan siyasa. Kuma su ma abubuwan da suke yi na kusanta su ga `yan siyasa, suna kuma samun rufin asiri daga harkar. To sai dai kuma ana zargin wasu daga cikinsu da zama  `yan kore ko karnukan farauta, wadanda ake amfani da su wajen  kazafi ko aibunta abokan hamayyar siyasa. Wannan dama da `yan soshiyal midiya ke samu ta ciccibawa da tura `yan siyasa zuwa kololuwar daukaka ko akasi ta sa ana kaffa-kaffa da su. Dr Kabiru Danladi Lawanti,  masanin aikin jarida a jami`ar Ahmadu Bello da ke Zaria, ya shaida wa BBC cewa ana tsoron ‘yan soshiyal midiya saboda mutane ne wadanda suna da karfin gaske musamman idan suka fara yada abubuwa wadanda ake gani kamar nakasu ne daga dan siyasa, to wannan sai ya hana dan siyasar tasiri. Ya ce haka kuma idan suna kaunar mutum suka fara yada manufofinsu masu kyau, ko ba a sonsa, sai kaga daga baya an zo ana sonsa. A halin yanzu dai `yan soshiyal midiya sun kasance tamkar sojojin baka ne, wadanda ke kokarin shan gaban `yan jarida ba don rashin kwarewa na yi musu cikas ba. Kuma ana dai zargin mafi yawan `yan soshiyal midiyan da zama `yan kanzagin `yan siyasa, saboda rashin akida. Dr Ashir Tukur Inuwa, malami a sashen nazari da koyar da aikin jarida na jami`ar Bayero ta Kano, ya ce yawancin ‘yan soshiyal midiya basu da kwarewa ko horo na aikin jarida, da ka su kan tari abin shi ya sa ake yawan samun labaran karya da na batanci. To amma Mallam Rabi`u Biyora, bai musanta ba, amma ya ce ba a taru aka zama daya ba. Ya ce ""Maganar cewa ana amfani da ‘yan soshiyal midiya a matsayin karnukan farauta da zage-zage da cin mutunci duk ana yin wadannan abubuwan, to amma ba duka aka taru aka zama Daya ba.” Mallam Rabi`u Biyora, ya ce ""Duk kaunar da nake yi wa siyasa ko wani dan siyasa bai isa ya sa na zagi ko aibata wani ba.” Wata kididdiga da aka yi a bara, ta nuna cewa ana da akalla kungiyoyin `yan soshiyal midiya  fiye da dubu ashirin da bakwai a Najeriya. Kuma a yanzu ma sai abin da ya karu kasancewar an fara shiga kakar zabe a Najeriya." https://www.bbc.com/hausa/articles/c3gx0xg7jxmo +politics Masu cewa babu kuɗi a Najeriya sai an ciyo bashi karya suke, in ji Kwankwaso Ɗan takarar shugaban kasa kuma jagoran sabuwar jam’iyyar hamayya ta NNPP a Najeriya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce babu kanshin gaskiya a batutuwan da masu mulki da gwamnatoci ke yi cewa babu kuɗi a Najeriya har sai an ciyo basussuka domin gudanar da ayyuka. A wata hira da ya yi da BBC, sanata Kwankwaso ya ce shi ya sa ni kuma ba zai daina faɗin cewa akwai isassun kuɗaɗe a Najeriya ba, duk wani bashin da ake zuwa a ciyo na karya ne. Sanata ya ce lokacin da ya samu dama ya nunawa al’ummar jihar Kano irin wadannan misalai, domin a koda yaushe mutane ne ke wacaka da dukiyar kasa. Sanata ya bada misali da lokacin mulkinsa na farko a matsayin gwamnan Kano a 1999, inda ya ke cewa ya gaji bashi kuma ya biya, kuma bai bar kowanne bashi ba lokacin da ya sauka daga mulki, sannan ko a 2011 ya tarar da manyan basuka, kuma suma ya biya. Ya ce mutanen ba sa son gaskiya ne, musamman idan ana riƙe da muƙaman gwamnati. Ɗan takarar ya ce shi ba zai iya cewa ga makin da zai bai wa gwamnati da ke ci ba, amma sanin kowa ne cewa Najeriya na cikin tasku da rashin tsaro. “Kullum ana kashe mutane, Kullum mutane na tserewa, Kullum ana raba mutane da muhallansu. “Ina dai ci gaba da jan hankalin gwamnatin Najeriya domin ta duba ta ga ta wani fanin za ta kawo wa ‘yan kasar nan sauki. “Talauci ya yi wa mutane yawa, ga malaman makaranta ga marasa galihu da kowa na cikin mumunan yanayi, in ji Kwankwaso. Sanata Kwankwaso ya kuma yi watsi da rade-radin da ake yi cewa babu mamaki ya marawa ɗaya daga cikin ‘yan takarar manyan jam’iyyun siyasar Najeriya ta APC ko PDP baya. Kwankwaso ya ce karerayin mutane ne kawai da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta, marasa daraja. Ya ce “ana dauko tsofaffin hotuna ana haɗawa, wasu kuma na rubuce-rubuce batar da mutane, da sunan yaudara. “Dama a harkar siyasa mutane ba sa kunya kuma sun iya yaɗa farfaganda da nuna rashin daraja da rashin tsoron Allah. “Amma abin jin dadin shi ne masu zaɓenmu babu ruwansu da irin waɗannan abubuwan da ake yaɗawa, kuma muna da karfin gwiwar za a zaɓe mu. Ya ce ya na samun goyon-baya, saboda kowa ya nuna fuskarsa da kuskuransu a baya kuma mutane na fahimta. Sanata ya ce duk da tunanin mutane kan yadda ake sauya sheka, su babban abin da suka sanya a gaba shi ne batun akida, wanda a baya babu irin wadannan tunanin. Tsohon gwamnan na Kano ya bada misalai irin na baya lokacin da aka kafa koma mulkin dimokuraɗiya a 1999, yana mai cewa batu da aka rinƙa yi shi ne na yada za a kori mulki soja, ba wai tunanin kafa kasa domin sama mata ci gaba ba. Sanata Kwankwaso na fatan samun nasara a zabukan 2023, domin kawo na shi sauyin. https://www.bbc.com/hausa/articles/c1vglg5q9zyo +politics Wane ne silar kashe ƙarfin ƙananan hukumomi a Najeriya? "Batun ƴancin ƙananan hukumomi na ci gaba da haifar da mahawara a Najeriya. Duk da cewa kundin tsarin mulkin Najeriya ya ayyana ƙananan hukumomi a matsayin mataki na uku a gwamnatance, amma a yau hakan na neman zama tarihi a kasar saboda zargin da ake yi wa gwamnoni na danne su. Malam Kabiru Sa'id Sufi, wani masanin kimiyyar siyasa ne a Kwalejin Share Fagen Shiga Jami'a ta CAS da ke Kano, ya ce tsarin tarayya da Najeriya ke bi ya ƙara tabbatar da wannan ƴanci na ƙananan hukumomi. ""Tun daga kundin tsarin mulki na 1979 har zuwa yanzu wato na Jamhuriya ta hudu ya tabbatar da kafuwarsu, wanda a sashe na 7 na kundin ya yi bayani daki-daki a kansu. ""Sashe na 8 da ya dauki alhakin tsara dokoki kan kananan hukumomi ya damka a hannun majalisun dokoki na jihohi, wanda wasu ke ganin hakan ne ya bai wa gwamnoni damar su shiga tsarin su yi abin da suka ga dama kamar yadda muke gani a yau,"" in ji Malam Sufi. 'Matsalar siyasa da danniya' A ganin Malam Kabiru Sufi matsalar da ta haifar da wannan koma-baya ga kananan hukumomi guda biyu ce - matsalar siyasa da kuma tattalin arziki. A cewarsa a yanzu an koma ana naɗin kantomomi a matsayin shugabannin kananan hukumomi maimakon gudanar da zaɓe. Dakta Tukur Abdulkadir na Sashen Kimiyyar Siyasa a Jami'ar Kaduna, na da irin wannan ra'ayin, inda ya ce an koma bautar da kananan hukumomi a Najeriya domin haka babu dalilin da zai sa su iya yin wani aiki da ba shi gwamnatoci suke so ba. ""Ko a lokacin mulkin soji ana ba mutane dama su zabi waɗanda za su wakilce su a mataki na kananan hukumomi, amma a yanzu da ake dimokuradiyya an hana su wannan damar da kundin tsarin mulki ya ba su,"" in ji shi Dakta Abdulkadir. Ya ƙara da cewa ƙananan hukumomin sun kasance mataki na farko da ake samar da ƴan siyasa - a cewar masanin, bincike ya nuna yadda siyasar ƙananan hukumomi ta haifar da manyan shugabannin a siyasar jihohi. Kamar 20 baya an yi manyan 'yan siyasa kamar Barnabas Bala Bantex wanda ya shugabanci karamar hukuma, daga baya kuma ya zama mataimakin gwamnan jihar Kaduna. Da irin su Salihu Sagir Takai da Lawal Sama'ila Abdullahi wadanda dukaninsu sun samar da manufofi a matakai daban-daban na rayuwar mutanen da suka wakilta a baya. A ɓagaren kason kuɗin da gwamnatin tarayya ke bayarwa, masanan sun bayyana cewa hadakar asusu tsakanin gwamnatin jiha da ta kananan hukumomi na daga cikin abin da yake hana kuɗaɗe shiga ga kananan hukumomi domin gudanar da ayyukan ci gaba. ""Kuɗaɗen da shugabannin ƙananan hukumomi suka samu a baya sun samar da manufofi masu kyau na ci gaba ga al'umarsu kamar bangaren lafiya a matakin farko da noma da kiwo da sauran ayyukan ci gaba,"" in ji Dakta Tukur. 'An kashe ƙananan hukumomi' Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a wata hirar talbijin da aka yi da shi ya bayyana cewa ""an kashe kananan hukumomi"". Buhari ya ce kananan hukumomi a Najeriya ba su da wani tsari, ba sa iya yin komai a kashin kansu, hatta kudin da ake ba su ba su da ikon sarrafa su. ''Idan da ana bai wa karmar hukuma Naira miliyan 300 domin ta yi wani aiki, a yanzu ba a ba ta abin da ya kai miliyan 100 ma, wannan fa shi ne halin da kananan hukumomin ke ciki"", in ji shugaban. Ko da yake bai fadi shirin da gwamnatinsa ke yi na ganin kananan hukumomin sun rabauta da yancin tafiyar da harkokinsu ba, sai dai ya ce idan aka ci gaba da tafiya a haka fatan da ake da shi na ganin an samar da ci gaba tun daga kasa na iya gamuwa da cikas. Sai dai Malam Kabiru Sufi ya ce wannan magana ta Shugaba Buhari za ta iya zaburar da kanannan hukumomi su nemi haƙƙinsu wurin jihohi. Amma Dakta Tukur ya ce maganar shugaban kawai ba za ta wadatar ba, domin yana da ikon da zai iya daukar matakin da ya fi haka. Ganin cewa mafi yawan gwamnonin ƴan jam'iyyarsa ne zai iya samun goyon bayansu wajen tabbatar da ƴancin kananan hukumomi ta bangaren tabbatar da zaɓe mai inganci da kuma isar da kasafin kudin da ake aike musu. Mafi yawan tsofaffin shugabannin kananan hukumomin da BBC ta tattauna da su sun bayyana cewa wannan matsala ta fara ne a 2007 amma a wasu johohi kadan kafin daga bisani ta mamaye kasar baki daya. Alhaji Tasi'u Muhammad, tsohon shugaban karamar hukumar Katagum ta Jihar Bauchi wanda ya shugabanci Katagum sau biyu a 1990 lokacin SDP da NRC da kuma a tsakanin 1999 zuwa 2003 lokacin PDP da ANPP, ya ce zaɓensu aka yi ba naɗi wanda hakan ya ba su ƙarfin kalubalantar gwamnoni idan sun zo da wasu manufofi da za su iya karya kananan hukumomi. ""A yau rubuta shugabanni ake yi a daki su karbi mulki da sahallewar gwamnoni, ta yaya kake zaton wanda aka naɗa zai iya kalubalantar wanda ya naɗa shi?"" in ji shi. Wani shugaban wata karamar hukuma da bai yarda a bayyana sunansa ba, ya shaida wa BBC cewa kudaden da ake bai wa ƙananan hukumomi daga tarayya ba su isarsu biyan albashi. Ɓangarorin ƙananan hukumomi ke kashe kudinsu sun kunshi: Malama Ibrahim Shekarau, tsohon gwamnan jihar Kano, ya musanta cewa asusun hadaka ne ya haifar da wannan matsala. Ya ce a lokacin da yake shugabantar jiharsa, idan aka aiko da kudaden da gwamnatin tarayya a baya ana bayar da bayanin yadda za a raba kudaden baki daya. ""Idan an aiko da kuɗin akwai takarda da ke dauke da bayanan yadda za a bai wa ko wacce jiha kudadenta, kuma idan aiki za a yi da kudaden wata karamar hukuma sai an tambayi izininta sannan a nemi ta bayar da wani abu domin aiwatar da aikin. ""Babu tilastawa cewa sai an yi amfani da wadannan kudade karfi da yaji,"" in ji Shekarau. Ya kuma ce bai kamata a dauki kudaden kananan hukumomi ba a zuba aiki a hedikwatar jiha wadda kawai wasu kalilan ne ke amfana. ""Wani mazaunin kauyen har ya gama rayuwarsa ba zai je inda aka zuba kudaden ba."" Masu sharhi kan lamuran yau da kullum na ganin ba ƙananan hukumomi ƴancin cin gashin kai ne kawai zai iya kawo karshen matsalarsu a Najeriya saboda su ne suka fi kusa da jama'a kuma su suka fi sanin matsalolinsu ta yadda za su magance su. Sai dai wasu na ganin su ma suna da nasu laifukan wadanda ke da alaka da zargin cin hanci da rashawa, ko da yake sun sha musantawa." https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-57612966 +politics Zan cire tallafin man fetur ko za a yi zanga-zanga a Najeriya - Tinubu "Dan takarar shugaban Najeriya na jam'iyyar APC a zaben 2023, Bola Ahmed Tinubu, ya sha alwashin janye tallafin man fetur da zarar ya zama shugaban kasar. Tinubu ya bayyana haka ne ranar Alhamis da daddare a yayin da yake gudanar da taro da wasu 'yan kasuwar kasar. ""Dokar man fetur tana nan kuma za mu duba ta a karo na biyu domin sauke nauyin da ke kanmu kuma duk zanga-zangar da za a yi, za mu cire tallafin man fetur,"" in ji Tinubu. Ya kara da cewa: ""Za mu dauki matakai masu tsauri, wannan shi ne batun gaskiya. Don haka wajibi ne mu cire tallafin man fetur."" Ya ce ba zai ci gaba da bayar da tallafin man fetur ba saboda kasashe makwabta irin su Kamaru, Jamhuriyar Nijar, Jamhuriyar Benin ne suke cin moriyar hakan. Tinubu ya kara da cewa zai sanya kudin da ake biyan tallafin man fetur a fannonin da suka kamata irin su lafiya. Kazalika ya ce zai cire jerin haraje-haraje da hukumomi suke karba yana ma cewa zai sa a rika karbar haraji daya kan mu'amalar da ta shafi a biya mata haraji. Bayanai sun nuna cewa gwamnatin Najeriya ta biya N1.9 daga watan Janairu zuwa watan Yulin 2022 kadai, lamarin da wasu ke ganin ba abu ne mai dorewa ba. Da ma dai shi ma dan takarar shugaban Najeriya na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya dade da shan alwashin janye tallafin man fetur idan ya zama shugaban kasa. Ya ce tallafin ba ya yi wa talakawa amfani. A baya dai, 'yan kasar sun gudanar da jerin zanga-zanga sakamakon matakan da gwamnatoci suka dauka na janye tallafin man fetur." https://www.bbc.com/hausa/articles/c14wgl7qy4xo +politics Zaben Najeriya na 2023: Ku ba mu labaran abubuwan da suka shafe ku Muna so mu ji daga gare ku. Labaran da za mu kawo kan zaɓukan Najeriya za su kasance na abubuwan da suka shafe ku ne kuma daga bakinku. Za mu so mu ba da labaranku. Za mu yi labaran ne kan abubuwan da suka faru da ku a kan muhimman al’amuran ƙasar. Muna so mu ba da labaran abubuwan da suke da muhimmanci a wajenku. Gamsuwar masu sauraro ce za ta zama ƙashin bayan rahotanninmu – ma’aikatanmu na bincike kan yadda rikice-rikice a Najeriya suka shafi ‘yan ƙasa kamarku. Labaranku za su iya zama rahotanninmu – idan aka samu cikakken bayani na ainihi, da kuma hira ta musamman da ƙwararru da kuma mahukunta game da al’amura daban-daban. Labaran da muke so ku aiko mana za su kasance na abin da ya faru da ku ne kan matsalar rashin tsaro ko abin da ya shafi ɓangaren ilimi ko na lafiya ko cin hanci ko tattalin arziki. Wato muna so mu ji idan akwai wani labari da kuke da shi a waɗannan fannoni da irin tasirin da ya yi muku a rayuwa. Alal misali, yadda matsalar rashin tsaro ta shafe ku, ko wani abu na harkar lafiya da ya faru da ku da sauran su. Idan kuka duba ƙasan shafin nan za ku ga fannonin da kuma inda za ku latsa don cike fom ɗin da za ku sanya bayananku. Danna adireshin da ke ƙasa ku turo mana labaranku. Ba sai kun bayyana sunanku ba idan ba kwa son hakan. Kar ku manta da sanya bayanan yadda za mu tuntuɓe ku – lambar waya da imel – don ɗaya daga cikin ma’aikatanmu su nemi ƙarin bayani. Kar ku damu: Za mu ɓoye sirrinku Wace matsalar rashin tsaro kuka samu kanku a ciki, kama daga tashe-tashen hankula a birane da karkara da satar mutane don kudin fansa da cin zarafi da fashi da makami da rikicin ƙabilanci da faɗan daba? Ku cike fom din da ke ƙasa idan kuna son ku ba mu wani labari na halin da kuka shiga dangane da matsalar rashin tsaro. Ga fom ɗin da za ku cike Za mu ɓoye sunanku idan har ba kwa so mu wallafa. Ku saka lambar waya da adireshin imel ɗinku ta yadda za mu tuntuɓe ku don samun ƙarin bayani. Idan har labarinku ya cancanci a wallafa shi, to ɗaya daga cikin ma’aikatanmu za su tuntuɓe ku. Wace matsalar tattalin arziki kuka sami kanku a ciki, kama daga tsadar kayayyaki da yunwa da wahalar man fetur da tsadar hayar gidaje da hauhawar farashi? Ku cike fom din da ke ƙasa idan kuna son ku ba mu wani labari na halin da kuka shiga dangane da matsalar tattalin arziki. Ga fom ɗin da za ku cike Za mu ɓoye sunanku idan har ba kwa so mu wallafa. Ku saka lambar waya da adireshin imel ɗinku ta yadda za mu tuntuɓe ku don samun ƙarin bayani. Idan har labarinku ya cancanci a wallafa shi, to ɗaya daga cikin ma’aikatanmu za su tuntuɓe ku. Za mu so mu ji labarai na wasu abubuwa da suka same ku masu alaƙa da matsalar ɓangaren ilimi; alal misali tarnaƙi ta ɓangaren ƙarancin kuɗaɗe ko yajin aiki ko matsalar tsaro ko cin hanci ko rashin shugabanci nagari ko ƙarancin kayan more rayuwa ko tsadar kuɗin karatu ko ƙarancin kayan koyarwa ko kuma siyasantar da harkokin Ilimi. Ku cike fom din da ke ƙasa idan kuna son ku ba mu wani labari na halin da kuka shiga dangane da matsalar ɓangaren ilimi. Ga fom ɗin da za ku cike Za mu ɓoye sunanku idan har ba kwa so mu wallafa. Ku saka lambar waya da adireshin imel ɗinku ta yadda za mu tuntuɓe ku don samun ƙarin bayani. Idan har labarinku ya cancanci a wallafa shi, to ɗaya daga cikin ma’aikatanmu za su tuntuɓe ku. Za mu so mu ji labarai na wasu abubuwa da suka same ku masu alaƙa da matsalar ɓangaren lafiya; alal misali samun tarnaki ta hanyar amfani da fasaha a harkokin lafiya ko ƙarancin albashi ga ma’aikata ko rashin fasahar sadarwa da ingantattun ayyukan lafiya ko ƙaruwar tsadar kuɗin asibiti ko ƙarancin ma’aikatan lafiya. Ku cike fom din da ke ƙasa idan kuna son ku ba mu wani labari na halin da kuka shiga dangane da matsalar ɓangaren lafiya. Ga fom ɗin da za ku cike Za mu ɓoye sunanku idan har ba kwa so mu wallafa. Ku saka lambar waya da adireshin imel ɗinku ta yadda za mu tuntuɓe ku don samun ƙarin bayani. Idan har labarinku ya cancanci a wallafa shi, to ɗaya daga cikin ma’aikatanmu za su tuntuɓe ku. Za mu so mu ji labarai na wasu abubuwa da suka same ku masu alaƙa da matsalar cin hanci da rashawa. Ko a ɓangaren rundunar ƴan sanda ko rundunar soji ko ɓangaren siyasa da ɓangaren ayyukan jin ƙai da sauran ɓangarori. Ko kun taɓa samun kanku a matsalar da ta shafi cin hanci da rashawa a Najeriya? Ku cike fom din da ke ƙasa idan kuna son ku ba mu wani labari na abin da ya danganci hakan. Ga fom ɗin da za ku cike Za mu ɓoye sunanku idan har ba kwa so mu wallafa. Ku saka lambar waya da adireshin imel ɗinku ta yadda za mu tuntuɓe ku don samun ƙarin bayani. Idan har labarinku ya cancanci a wallafa shi, to ɗaya daga cikin ma’aikatanmu za su tuntuɓe ku. https://www.bbc.com/hausa/articles/cllzej8z2j5o +politics Kofar sulhu a bude take tsakaninmu da bangaren Shekarau — Ganduje "Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya ce ƙofar sulhu a buɗe take tsakaninsu da ɓangaren Sanata Ibrahim Shekarau. A cikin wata tattauanwa da BBC ta yi da shi, Ganduje, ya ce yanzu lokaci ne na tafiya tare da mayar da hankali kan harkokin ci gaban dimokraɗiyya. Gwamnan na Kano, ya ce ""Muna rokon 'yan uwanmu a zo a hada a hannu gaba ki daya don a yi wannan tafiya tare, sannan kuma ina so na sanar da 'yan jam'iyya cewa a dauka damara don yanzu za a shiga gwagwarmayar zabe"". Ganduje ya ce ""Yana da matukar muhimmanci shugabannin jam'iyya su san aikinsu ta yadda za a tafiyar da jam'iyya akan tafarkin dimokradiyya"". Gwamnan ya ce, idan ana so a shirya ba a duba abubuwan da suka faru a baya, su fatansu azo a zama tsintsiya madaurinki daya. Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya ce duk da batun za su daukaka kara zuwa kotun koli wannan daban domin dimokradiyya ce, kuma hakan ba zai hana azo a dai-daita a ci gaba da tafiya tare ba. Ya ce."" Batun kwamitin da uwar jam'iyya ta nada ni shugabanci na yin sulhu yana nan yana jiransu domin duk mun yi tanadin yadda za a gudanar da dai-daitawar su kawai muke jira"". A ranar Alhamis ne dai kotun daukaka kara ta tabbatar da shugabancin jam'iyyar ga Abdullahi Abbas, kuma sa'o'i da yanke wannan hukuncin uwar jam'iyya ta kasa ta mika masa takardar shaidar shugabanci, matakin da bai yi wa ɓangaren Shekarau dadi ba. Bangaren da Sanata Ibrahim Shekarau ke jagoranta na jam'iyyar APC a Kano ya ce za su tafi Kotun Koli don ci gaba da kalubalantar bangaren su Gwamna Ganduje a rikicin APC na Kano. Tsohon gwamnan Kanon ya kuma nuna rashin jin dadinsa da wasu kalmomin batanci da ta ce gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi amfani da su jim kadan bayan hukuncin kotu da ke cewa bangaren gwamnan ke da halastaccen shugaba. Kano dai babbar jiha ce da APC ta daɗe tana nanata tasirinta a siyasar Najeriya, abin da yasa APCn ke ƙara ƙoƙari wajen ganin ta hana wannan ɓaraka da ta kunno kai a jihar ƙara tsawo da faɗi. Idan aka gaggara maslaha tun da wuri babu mamaki wannan rikici ya kassara tasirin da APCn za ta iya yi nan gaba. Ko da yake 'ya'yan jami'iyyar na da kwarin-gwiwar sulhu zai tabbatu a tsakaninsu." https://www.bbc.com/hausa/labarai-60457969 +politics Buhari ya gana da Mai Mala kuma ya yarda ya ci gaba da shugabancin APC "Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci kungiyar gwamnonin APC mai mulkin Najeriya ta bar gwamnan Jihar Yobe kuma shugaban rikon jam'iyyar, Mai Mala Buni, ya ci gaba da shugabancin jam'iyyar. Ya bayyana haka ne a wata wasika da ya aike wa shugaban gwamnonin jam'iyyar APC, Gwamna Abubakar Atiku Bagudu na Jihar Kebbi. Hakan na faruwa ne a yayin da Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da Mai Mala Buni a birnin Landan ranar Talata. Buhari ya ce ya fahimci rigimar da ke faruwa a cikin jam'iyyar lamarin da ya sa aka kai kara kotu, yana mai cewa duk da haka ya amince Mai Mala Buni ya ci gaba da jagorancin babban taron jam'iyyar da ake shirin gudanarwa a ranar 26 ga watan Maris, duk da wani umarnin kotu da ya ce a dakatar da taron. Kazalika a wata wasika da shugaban kasar ya aike wa shugaban gwamnonin jam'iyyar APC, Gwamna Abubakar Atiku Bagudu na Jihar Kebbi, Shugaba Buhari ya bukaci a guje wa abubuwan da za su dagula jam'iyyar yana mai cewa ""da farko batun shugabancin riko na jam'iyya zai komo kamar yadda yake a baya."" Hakan na faruwa ne a yayin da Jam'iyyar APC ta jaddada cewa Mai Mala Buni zai karɓi aikinsa da zarar ya koma gida daga tafiyar da ya yi. Shugabancin APC ya shiga ruɗani ne a ƙarshen watan Fabarairu tun bayan da aka ga Gwamnan Neja Abubaukar Sani Bello ya fara jagorancin kwamatin. Daga baya kuma wata wasiƙa ta ɓulla cewa Mai Mala ne ya ba shi riƙo saboda ya yi tafiya ƙasar waje don a duba lafiyarsa. Rikicin shugabanci a APC ya ƙara ƙamari ne tun bayan da wasu gwamnoni, ciki har da Nasir El-Rufai na Kaduna, suka ce Shugaba Muhammadu Buhari ne ya ba da umarnin a sauke Mai Mala Buni, wanda ya fara jagoranci tun watan Yuni na 2020. Lamarin na zuwa ne yayin da jam'iyyar ta fara shirin gudanar da babban taronta na ƙasa da za a yi ranar 26 ga watan Maris, inda za a zaɓi shugabanni a matakin ƙasa baki ɗaya duk da wani umarnin kotu da ya ce a dakatar da taron. ""Shirya sahihin taron ƙasa cikin nasara a ranar 26 ga watan Maris ne babban muradin kwamatin kuma za mu ci gaba da shirin yin hakan har zuwa lokacin da shugaba zai dawo kuma ya karɓi aikinsa,"" a cewar sanarwar da sakataren kwamatin ya fitar ranar Talata. Tuni aka fara sayar da fom ɗin takara ga masu son yin takarar shugabancin jam'iyyar kan naira miliyan 20. Shugabancin APC ya shiga ruɗani ne a ƙarshen watan Fabarairu tun bayan da aka ga Gwamnan Neja Abubaukar Sani Bello ya fara jagorancin kwamatin. Daga baya kuma wata wasiƙa ta ɓulla cewa Mai Mala ne ya ba shi riƙo saboda ya yi tafiya ƙasar waje don a duba lafiyarsa. Sanawar da Sakataren Riƙo na Ƙasa John James Akpanudoedehe ya fitar ta sake jaddada cewa ba a sauke Mai Mala daga muƙamin ba da kuma sauran 'yan kwamatin kamar yadda wasu gwamnonin jam'iyyar suka bayyana a baya. Rikicin shugabanci a APC ya ƙara ƙamari ne tun bayan da wasu gwamnoni, ciki har da Nasir El-Rufai na Kaduna, suka ce Shugaba Muhammadu Buhari ne ya ba da umarnin a sauke Mai Mala Buni, wanda ya fara jagoranci tun watan Yuni na 2020. Sanarwar ta Mista Akpanudoedehe ta ce babu wata ɓaraka a jam'iyyar tasu, yana mai cewa ""kanmu a haɗe yake wajen samar wa ƙasa shugabanci na gari"". Ya ƙara da cewa sun kafa wani kwamati da zai lalubo musu hanyoyin kauce wa umarnin kotun da ya dakatar da gudanar da taron. Gwamnan jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya ya ce shi da sauran gwamnonin da ke mara wa Shugaba Muhammadu Buhari baya ba su da ra'ayin kansu sai abin da shugaban ya amince da shi. Ya bayyana haka ne a tattaunwa ta musamman da BBC Hausa. Gwamnan ya ce ba shi da wani ra'ayi kan inda mulki zai koma a shekarar 2023, yana mai cewa a matsayinsa na shugaban kwamitin na jam'iyyarsu bai kamata ya bayyana ra'ayinsa ba." https://www.bbc.com/hausa/labarai-60762565 +religion Eid-al-Fitr: Kwamitin ganin wata a Najeriya 'na neman mutanen da suka ce sun ga wata' "Kwamitin duba wata na Fadar Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ya ce yana neman agajin mutane da su taimaka masa wurin neman duk wanda ya ce ya ga watan Shawwal a daren Juma'a. Shugaban kwamitin, Farfesa Usman el-Nafaty ne ya tabbatar wa BBC hakan, inda ya ce suna neman mutanen ne domin tattaunawa da su da nufin tabbatar da sahihancin abin da suka gani. Tun farko wani shafin Facebook ne mai ɗauke da sunan kwamitin ganin watan ya wallafa sanarwar cewa ana neman mutanen. ""Muna roƙo idan kuna cikin waɗanda suka ga watan Shawwal na shekarar 1441 a kowanne lungu da saƙo na Najeriya ranar Juma'a, ko kuma kun san wanda ya gani, ko kun san yadda za a cimma wanda ya gani to ku bayyana mana a nan,"" in ji sanarwar. Ta ƙara da cewa: ""Mambobin kwamitin ganin wata na son su tattauna da mutanen game da batun domin su taimaka musu (kwamitin) wurin aiwatar da aikinsu a matsayinsu na masu bai wa Mai Alfarma Sarkin Musulmi shawara."" A daren Juma'a ne dai kwamitin ya bayar da sanarwar cewa ba a samu rahoton ganin wata ba, saboda haka za a cika azumi 30, inda za a yi sallar Idi ranar Lahadi." https://www.bbc.com/hausa/labarai-52783309 +religion Ku San Malamanku tare da Malam Junaidu Abubakar Sadiq "A wannan makon, filin Ku San Malamanku, ya tattaunawa da Malam Junaidu Abubakar Sadiq. An haifin malamin a garin Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya a shekarar 1992. Malamin, wanda shi ne limamin masallacin Al-Irfan kuma manajan daraktan Al Fayda Tidjaniya TV, ya shaida wa BBC cewa ""mun taso ne a gida na karatu: iyayenmu da kakaninmu almajirai ne, musamman kakana As-Sheikh Ibrahim Mushaddidu Jos shi ne ya karantar da mahaifina. Ya ce ya soma karatu ne a wurin mahaifinsa kuma daga bisani ya sanya shi a makarantar Nizamiyyat - inda a nan ne ya yi nazare ya yi kuma firamare a markazus-sakaful Islam, kana ya yi sakandare a Kulliyatu Ibn Abbas, karkashin kulawar makarantun Sheikh Dahiru Usman Bauchi. Malam Junaidu Abubakar Sadiq ya kara da cewa a can ya ssauke Alkur'ani sanna ya yi NCE a reshen Makarantar Sa'adatu Rimi da ke Bauchi. Kazalika malamin ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar Jos. A fannin karatun zaure, Malam Junaidu ya ce ya yi karatu a wurin Sheikh Aminu Jibril Bauchi da Malam Ibrahim Zafi da sauran manyan malamai da ke Bauhci da wasu jihohin." https://www.bbc.com/hausa/articles/c0d17zk4pgvo +religion Bulli Bai app: An kama mutumin da ya kirkiri manhajar yin gwanjon matan Musulmai a Indiya "Ƴan sanda a Indiya sun kama mutumin da ake zargin shi ya ƙirƙiri wata manhaja da ta yaɗa hotunan fiye da mata Musulmai 100 da sunan ""gwanjonsu"" ake yi. Neeraj Bishnoi mai shekara 20, shi ne mutum na huɗu da aka kama kan wannan lamarin. Manhajar mai suna ""Bulli Bai"" an ɗora ta ne a kan Github, wadda tuni kuma aka cire ta sakamakon fushi da tashin hankalin da hakan ya jawo. Wannan ne karo na biyu da aka yi ƙoƙarin cin zarafin mata Musulamai cikin wata ɗaya, ta hanyar yaɗa hotunansu a gwanjon ƙarya. A watan Yulin 2021, wata manhaja da wani shafin intanet ""Sulli Deals"" sun ƙirƙiri bayanai na fiye da mata Musulmai 80 - ta hanyar ɗora hotunansu a intanet - tare da bayyana su a matsayin ""abin sayarwar ranar"". Duk da cewa ƴan sanda sun fara bincike, har yanzu babu wanda aka gurfanar. Ƴan sanda a aƙalla jihohi uku sun ƙaddamar da bincike a kan manhajar ""Bulli Bai"" kan ƙorafin da matan da ake yi wa wannan cin zarafi suka kai. Wani sashen ƴan sanda na musamman a Delhi da ke kula da abubuwan da suka shafi laifukan intanet ya kama Mr Bishnoi a arewa maso gabashin jihar Assam a ranar Alhamis. ""Shi ne babban mai kitsa, kuma wanda ya ƙirƙiri manhajar,"" in ji KPS Malhotra, mataimakin kwamishinan ƴan sanda na tawagar laifukan intanet, kamar yadda ya shaida wa BBC. Ƴan sanda sun kuma ce Mr Bishnoi ne ke kula da shafin Tuwitan da aka yaɗa hotunan matan daga manhajar. A farkon wannan makon ne, ƴan sandan Mumbai suka kama wasu mutum ukun - Vishal Kumar mai shekara 21 ɗalibi mai karatun injiniya a birnin Bangalore da ke kudancin ƙasar, da kuma wasu ɗaliban biyu Shweta Singh mai shekara 18 da Mayank Rawat mai shekara 21 a jihar Uttarakhand da ke arewaci. Wani mai magana da yawun kamfanin GitHub ya ce tuni kamfanin ya dakatar da shafin da ke amfani da manhajar ""waɗanda dukka sun take dokokinmu."" ""Bincikenmu yana kan matakin farko, don haka ba za mu iya cewa ko manhajar ""Bulli Bai"" da ""Sulli Deals"" suna da alaƙa ba,"" a cewar kwamishinan ƴan sandan Hemant Nagrale, a hirarsa da BBC Marathi. A zahirin lamari, ba sayar da matan ake yi ba, kawai ana hakan ne saboda a muzanta da wulaƙanta mata Musulmai - waɗanda da yawansu suna nuna adawarsu kan yadda ake samun ƙaruwar irin wannan abu a ƙarƙashin mulkin Firaminista Narendra Modi. ""Sulli"" kalma ce da masu tsaurin ra'ayi na addinin Hindu ke amfani da ita don cusgunawa mata Musulmai yayin da kalmar ""bulli"" ke nufin ɓata suna. ""An kuma kama wasu mutanen ma don amsa tambayoyi. Za mu binciki lamarin har zuwa ƙarshe, kamar yadda Satej Patel, ƙaramin ministan cikin gida na jihar Maharashtraya shaida wa BBC. Jerin sunayen matan da ke kan manhajar sun haɗa da ƴan jarida da dama, da jarumin Bollywood da kuma wata mata mai shekera 65 mahaifiya wani ɗalibi da ya gudu. Gwanjon matan ya kaɗa mutane tare da harzuƙa su bayan da hotunan mata da dama da aka sanya suka karaɗe shafukan sada zumunta. Wani ɗan jarida ɗan yankin Kashmir Quratulain Rehbar, da ya kai koke kan shafin ""Sulli Deals"" a bara, ya ceabin takaici ne ka ga sunanka a kan manhajar. Priyanka Chaturvedi, wata ƴar majalisa daga jam'iyyar Shiv Sena, ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na ANI cewa an ƙirƙiri manhajarne saboda har yanzu ba a hukunta waɗanda suka fara ƙirƙirar shafin e ""Sulli Deals""ba. Sannan ta aika wasiƙun da ta rubuta zuwa ga Mr Vaishnav bayan da shafin intanet ɗin ya fara aiki a watan Yulin 2021. A lokacin da labarin manhajar ya bayyana, wata mai waƙe Nabiya Khan wacce aka so kai wa hari a bara ta wallafa a tuwita cewa har a lokacin ƴan sandan Delhi ba su ɗauki mataki a kan ƙorafinta ba na 2021. A 2018 ƙungiyar Amnesty International ta ruwaito cewa cin zarafi a intanet a Indiya ya nuna idan mace ta fiye magana kan ƴancinta to an fi kai mata hari. Masu suka sun ce cin zarafin mata Musulmai ya yi muni a shekarun baya-bayan nan." https://www.bbc.com/hausa/labarai-59880800 +religion Waye ke kashe-kashe a Iraki? Yayin da Joe Biden ya kama aiki a matsayin shugaban Amurka, sashin Larabci na BBC ya ziyarci Iraki don duba tasirin janye sojojin Amurka daga Irakin. Ramita Navai da tawagarta sun bankado yadda mayakan sa kai ‘yan shi’a suke ta’annati saboda gibin da aka samu bayan tafiyar sojojin Amurka. Gargadi: Akwai wasu hotuna da za su iya ta da hankali a cikin wannan rahoto. https://www.bbc.com/hausa/55823753 +religion Musulmi na bikin Maulidi a fadin duniya "A ranar 12 ga watan Rabiul Awwal, wani bangare na al'ummar Musulmi na gudanar da bukukuwan Maulidi domin murnar zagayowar ranar da aka haifi Manzon Allah, Annabi Muhammad SAW. Sai dai ba dukkan Musulmi ne ke bikin ranar ba, saboda sabanin fahimta. Sheikh Umar Sani Fagge ya shaida wa BBC fa'idar ranar, inda ya ce wannan rana ce mai matukar muhimmanci. Ya ce rana ce ta gode wa Allah kan baiwar da ya yi wa al'ummar Musulmi ta Annabi Muhammadu. ""Musulmi sukan tuna wannan rana da aka haifi Manzon Allah domin yin godiya ga Allah kan ni'imar samun Annabi SAW,"" inji shi. Shehin malamin ya ce wannan rana na da matukar muhimmanci saboda shi kanshi Annabi SAW ya kan azuminci ranar da aka haife shi. ""An tambaye shi saboda me yake azumi Litinin, ya ce 'saboda wannan ranar aka haife ni'"". Ya ce wannan ranar ta kunshi nuna so da kauna da tunatar da Musulmi game da kyawawan halayen Annabi SAW da yadda ya rayu domin a yi koyi da shi. Shehin malamin ya ce abubuwan da ya dace a yi a wannan lokaci sun hada da karatun Al-Kur'ani da karanta Sira ta Annabi SAW da yin zikiri da salati ga Annabi SAW, da yabonsa. Akwai dai wani bangare na Musulmi da ke sukar maulidi, inda suke cewa Annabi da Sahabbansa ba su yi ba." https://www.bbc.com/hausa/labarai-50370636 +religion Ku San Malamanku tare da Dokta Zakariyya Sa'id Zakariyya "Latsa alamar lasifika da ke sama don kallon hira da Dokta Zakariyya Sa'id Zakariyya: Fitaccen malamin addinin Musulunci, Dokta Zakariyya Sa'id ya shafe shekaru yana karatun Alkur'ani a gidansu, kafin daga baya ya tafi garuruwa da dama wajen neman ilimi. An haifi Dokta Zakariyya a shekarar 1960, a wata tsangaya dake Kandi a karamar hukumar Dutse ta jihar Jigawa. Mahaifinsa Malami ne na Alkur'ani wanda yake da almajirai da dama. Dokta Sa'idu ya shafe shekaru yana karatun Alkur'ani a gidansu, kafin daga baya tafi garuwa da dama da suka hada da Takai a jihar Kano da garin Bauchi da birnin Kano da biranen Zariya da Kaduna a jihar Kaduna. Yawon karatun nasa ya kai shi ga shafe shekaru da dama yana daukar karatu a wajen babban malamin nan Sheikh Abubakar Mahmud Gumi a garin Kaduna. ""Duk karatun da na yi babu inda nake jin dadinsa nake ji na karu kamar karatun da na yi a gaban Sheikh Abubakar Mahmud Gumi,"" in ji Dokta Zakariyya. Ya haddace Alkur'ani tun yana da kuruciya. To amma fa ya ce Suratul Waki'a ta bashi wahala sosai a lokacin da yake karatu, kuma har yanzu yana gwagwagwa da ita. Ya ce a duk wuraren da ya yi karatu ba ya saka littafi a gaban duk malaman da ya yi karatu a wajensu, sai dai ya je ya zauna a inda ake karatu yana saurara, daga baya kuma ya koma gida ya yi bitar abin da ya koya. Daga baya ya koma jihar Katsina inda ya shiga makarantar horar da malamai ta Katsina bayan ya dauki jarrabawa a jihar Kaduna a 1984 inda ya kammala karatun sakandare a 1990. Ya halarci kwalejin horar da malamai ta Gumel a jihar Jigawa inda ya samu shaidar NCE, sannan ya halarci jami'ar Bayero Kano inda ya samu shaidar digir, sannan ya yi digiri na biyu da na uku a kasar Sudan. Dokta Zakariyya ya fara karantarwa a firmare, sannan ya koyar a sakandare, a yanzu kuma yana koyarwa a kwalejin shari'ar addinin Musulunci ta Ringim a jihar Jigawa. Shehin malamin yace babu abin da yake jin dadin mai da hankali a kai idan ba ya komai kamar bude littafi ya yi karatu. Sai kuma jin labarai musamman daga gidajen rediyo na duniya. Dokta Zakariyya yana da mata uku da 'ya'ya 18. Ya auri matarsa ta fari a lokacin da yake Katsina, sannan ya auri sauran biyun a Dutsen jihar Jigawa." https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-55758839 +religion Manyan malaman Kano sun yi watsi da cire Sheikh Khalil daga shugabancin Majalisar Malamai "Wani ɓangare na manyan malaman Jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya sun yi watsi da batun sauke Sheikh Ibrahim Khalil daga shugabancin Majalisar Malaman jihar da wasu malaman suka yi iƙirarin yi a ranar Litinin. Hakan ya zama tamkar samun rabuwar kai a tsakanin shugabancin Majalisar Malaman Malaman da suka yi iƙirarin sauke Malam Ibrahim Khaleel sun zargi shugabancinsa ne da shiga siyasa tare da rashin faɗaɗa Majalisar Malaman zuwa ƙananan hukumomi. Sai dai wasu masu riƙe da manyan muƙaman shugabancin Majalisar na cewa waɗanda suka sauke malamin ba ƴan Majalisar Malaman ba ne. Ɓangaren da ke iƙirarin sauke Sheikh Khalil dai ya ce sun maye gurbinsa ne da shugaban ƙungiyar Izala na jihar Sheikh Saleh Pakistan. Sai dai gwamnatin Jihar Kano ta ce babu hannunta a lamarin. Wannan lamari dai ya jawo ce-ce-ku-ce tsakanin al'umma a jihar da kuma sauran masu bayyana ra'ayoyinsu a shafukan sada zumunta, inda kowa ke fassara lamarin da irin fahimtarsa. Me ya faru tun farko? A wani taron manema labarai ranar Litinin a Kano, sakataren gamayyar ƙungiyoyin Izala da Ƙadiriya da Tijjaniya, Malam Jamilu Abubakar, ya ce sun sauke Malam Ibrahim Khalil ne saboda shiga harkokin siyasa. ""Bayan maganar da ta shafi siyasa akwai kuma wasu da suke manya-manya ne a Majalisar da ba za su iya fito na fito da jagoorancin ba''. To ko ɓangaren da ke ja da sauke Malam Khalil ya taɓa tuntuɓarsa kan waɗannan ƙorafe-ƙorafen? Sai Malam Jamilu ya ce 'an yi hakan a baya, akwai manya-manyan malamai da suka je suka tuntuɓe shi."" Wasu na ganin ba Malam Khalil ne kawai malamin da ya taɓa shiga harkar siyasa ba amma sai a wannan karon aka ɗauki mataki, sai dai Malam Jamilu ya ƙara da cewa ""mu ba mu da alaƙa da Gwamnatin jihar Kano don haka sauke shin ba shi da alaƙa da mu'amalarsa da gwamnati, damuwarmu ita ce a gyara Majalisar a samar da majalisa mai karsashi."" Sai dai wasu daga cikin malaman da suka halarci taron na Litinin sun ce ba su da masaniyar me za a yi a wajen taron kuma sun buƙaci a ba su damar magana amma aka ce an zartar da hukunci a madadinsu. Malam Sulaiman Ƙiru ɗaya ne daga cikin malaman da ke da irin wannan koke, inda ya ce: ""Ai ba taro aka kira mu za a sauke shugaba ba, kiranmu taro aka yi aka ce an zauna an sauke shugaba. ""A wajen taron ma na yi tambaya. Ba kiranmu aka yi muka sauke wani muka zaɓi wani ba."" Malam Sulaiman ya kuma yi kira ga malamai da su ji tsoron Allah a duk abin da za su yi. ""Ya kamata Malamai su sun cewa su magada Annabi Muhammadu (SAW) ne. Komai dabara komai wayo abin da babu goyon bayan Allah a cikinsa ba zai tabbata ba."" Haka zalika ɗaya daga cikin malaman wanda ya buƙaci BBC ta sakaya sunansa ya ce reshen ƙungiyar na ƙaramar hukumarsu ne ya kawo su wajen taron, sai dai ya ce abin da aka yi a wajen ba shi da maraba da siyasa. ""Wannan ƙaramar hukumarmu ce ta kira mu wannan taro bisa ga buƙatar kansu. Mu kuma muka amsa kira, sai da muka zo aka yi mana bayani aka ce ana so mu ba da goyon baya. ""Amma gaskiyar magana yaya za ka bayar da goyon baya a kan abin da ba ka da hujja a kansa? Mu dai wannan abu ya haska mana lamari ɗaya, an ce kar a yi siyasa amma kuma an zo an yi siyasar,"" a cewarsa. 'Wasu malaman sun ce ba ruwansu' Dr Sa'id Ahmad Dukawa shi ne kakakin Majalisar Malamai ta Kano, ya ce har yanzu Malam Ibrahim Khalil ne shugaban Majalisar Malamai a Kano, domin kuwa waɗanda suka bayar da wannan sanarwa ba ƴaƴan ƙungiyar ba ne. Wata sanarwa da aka fitar mai ɗauke da sa hannun Dr Dukawa a ranar Talata, ta ce malamai 10 da aka sanya sunayensu a sanarwar ba su san da maganar ba. Malaman su ne: Sanarwar ta ce ""Jagororin zauren haɗin kan malamai da ƙungiyoyin Musulunci na jihar Kano sun samu labarin wata sanarwa da wasu mutane suka bayar suna iƙirarin sauke Sheikh Ibrahim Khalil daga shugabancin Majalisar Malamai ta jihar Kano, tare da ayyana wanda suke sha'awar ya shugabance ta. ""Jagororin suna tabbatar wa al'umma cewa ba da yawunsu aka yi wannan jawabi ba kuma ba sa goyon bayansa. ""Har kullum jagororin suna neman zaman lafiya ne da haɗin kan al'umma, amma wannan yunƙurin zai haifar da saɓanin hakan ne. ""Don haka zaure yana kira ga al'umma da su ci gaba da ririta zaman lafiyar Kano su guji duk wani abu da zai iya zama barazana ga tsaro da kwanciyar hankali,"" kamar yadda sanarwar ta ce. Sanarwar ta ce ""Jagororin zauren hadin kan Malamai da kungiyoyin Musulunci na jihar Kano sun samu labarin wata sanarwa da wasu mutane suka bayar suna ikirarin sauke Sheikh Ibrahim Khalil daga shugabancin Majalisar Malamai ta jihar Kano, tare da ayyana wanda suke sha'awar ya shugabance ta. ""Jagororin suna tabbatar wa al'umma cew aba da yawunsu aka yi wannan jawabi ba kuma ba sa goyon bayansa. ""A har kullum jagororin suna neman zaman lafiya ne da hadin kan al'umma, amma wannan yunƙurin zai haifar da saɓanin hakan ne. ""Don haka zaure yana kira ga al'umma da su ciu gaba da ririta zaman lafiyar Kano su guji duk wani abu da zai iya zama barazana ga tsaro da kwanciyar hankali,"" kamar yadda sanarwar ta ce. BBC ta tuntuɓi kwamishinan harkokin addinai na jihar Kano Dr Muhammad Tahar Adamu wanda ake kira da Baba Impossible wanda ya ce bai san komai kan maganar ba. Sai dai da muka tuntuɓi Kwamishinan Ƴaɗa Labarai Muhammad Garba ya musanta zargin, yana cewa gwamnati ba ta da hannu a sauke Malam Khalil.Ya kuma musanta zargin da wasu malaman suka yi cewa shugabanninsu na ƙananan hukumomi ne suka ce su zo su halarci taron da aka yanke hukuncin sauke malamin. ""Babu wani malami da gwamnati ta nemo shi ya zo ya sauke Sheikh Ibrahim Khalil,"" in ji Kwamishina Garba Sai dai kwamishinan ya ce a yanzu su duk wanda ya fi rinjayen magoya baya daga cikin malaman biyu da ake ƙiƙi-ƙaƙa a kansu shi ne wanda gwamnatin jihar Kano za ta yi mu'amala da shi. Wannan lamari na faruwa ne makonni kaɗan da Majalisar Malaman ta Kano ta yi zargin cewar akwai yunƙurin da wasu ke yi na neman sauke shugabansu Malam Ibrahim Khalil daga kan muƙaminsa, inda suka yi wani taro na nuna goyan baya tare da yin mubaya'a a gare shi. Sai dai a wancan lokacin ba su iya fitowa sun ambaci waɗanda suke zargi da hannu a lamarin ba." https://www.bbc.com/hausa/labarai-58872972 +religion Maraba da watan Ramadan: Ga wasu abubuwa dangane da shi Latsa hoton da ke sama don kallo bidiyon: A cikin wannan bidiyon, Fatima Othman da Halima Umar Saleh sun yi duba kan wasu muhimman abubuwa dangane da Watan Ramadan. https://www.bbc.com/hausa/media-52420990 +religion Ku San Malamanku tare da Sheikh Musa Adam Mai Hula Latsa hoton da ke sama domin kallon wannan bidiyon. Sheikh Musa Adam Mai Hula ya ce ya taso ne kawai ya ganshi a makaranta yana karatu ne, inda ya ce ba zai iya tantance yaushe aka saka shi a makaranta ba. Ya ce ya soma makarantar allo a makarantar Malam Yuguda a garin Numan. A ɓangaren boko kuma, ya soma ne da makarantar Central da ke garin na Numan inda a nan ya yi firamarinsa. Bayan mahaifinsa ya koma garin Gombe, a nan ma Sheikh Musa inda a nan ma ya yi karatukan addinin musulunci da na boko. Malamin ya ce duka surorin Al-Ƙur'ani abin so ne ga Musulmi amma ya fi son Suratul Zumar saboda tauhidin da ke cikinta. https://www.bbc.com/hausa/labarai-60420433 +religion Hajj 2022: Maniyyata sun koka a kan tsadar kuɗin aikin hajjin bana a Najeriya "Maniyatta aikin hajjin bana na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu tun bayan sanarwar da hukumar alhazai ta kasa a Najeriya ta fitar kan kudin aikin hajjin. Duk da cewa an rika hasashen cewa kudin hajjin bana zai karu sakamakom matsin tattalin arziki da tsadar dala amma maniyyata ba su yi tunanin cewa al'amarim zai kasance haka ba. A ranar Alhamis ne Hukumar kula da aikin hajji ta Najeriya wato NAHCON ta bayanna cewa za a kara kudin aikin hajji da akalla kashi 50 cikin 100 kan abin da maniyyata suka biya a 2019. Hukumar ta yi hasashen cewa kudin aikin hajjin bana ba zai gaza naira miliyan biyu da rabi ba. NAHCON ta alakanta ƙaruwar farashin da yanayin tattalin arziƙi da kuma hauhawar farashin dala, sai dai wasu maniyyata na cewa ya kamata gwamnati ta yi duba na tsanaki kan lamarin. Wani maniyyaci ya shaida wa BBC cewa kusan shekara biyu ke nan da biyan kudinsa, amma karin ba zai hana shi neman hanyoyin samun ciko domin kammala biyan kudin aikin hajjin ba. ""Gwiwata ba ta yi sanyi ba. Shi abu ne na hukuncin ubangiji. Idan Allah ya yi kiran ka toh za ka amsa kiransa kuma cikin hukuncin ubangiji za mu tafi nema mu ga mai Allah zai yi mana,""in ji shi. Sai dai ya yi kira ga gwamnati a kan ta taimaka wa talakawan da ke son su je kasa mai tsarki. ""Mun ajiye kudin nan kusan shekara biyu a hannun gwamnati, toh ya kamata a ce an duba an tausaya, ta san mai za ta yi ta agazawa wannan aikin hajji da aka shafe shekara biyu ba a yi ba."" Ita kuwa wata mata waddake burin sauke farali ta gaya wa BBC cewa hankalinta ya yi matukar tashi da jin labarin karin kudin saboda kudin da ta biya a baya da kyar ta hada su. ""Gaskiya na ji kamar ba zan iya ba saboda tun lokacin da sakon ya same ni, gaba daya duk tunani na ya rikice, ina ta tunanin yaya ma zan yi na samun cikon wannan kudin."" Suma kamfanonin shirye-shiryen tafiye-tafiyen aikin hajji da Umrah duk sun sun koka da karuwar farashin kujerun aikin hajjin. Hukumomin Saudiyya sun ware wa Najeruya kujeru fiye da dubu 40 cikin maniyyata miliyan daya da ta ce zata amince su gudanar da aikin Hajjin bana. Kafar yada labaran kasar ta ruwaito mahukuntan kasar na cewa dole mahajjatan da za su je aikin Hajjin na bana su kasance 'yan kasa da shekara 65, kuma dole sai an yi musu rigakafin korona cikakke. A shekarar da ta wuce 'yan kasar dubu 60 ne kadai suka yi aikin Hajjin. A shekarun baya kafin bullar korona Musulmi daga sassan duniya kusan miliyan biyu da rabi ne ke aikin Hajjin." https://www.bbc.com/hausa/labarai-61185054 +religion Sheikh Abduljabbar: Abu 6 da ba ku sani ba kan muƙabalar Abduljabbar da Malaman Kano "A yau Asabar 10 ga watan Yuli ne za a gabatar da muƙabala tsakanin Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara da wasu malaman addinin Musulunci na jihar Kano a arewa maso yammacin Najeriya. A ranar Alhamis ne gwamnatin Kanon ta sanya ranar yin muƙabala, kwanaki kadan bayan da shugabannin zauren haɗin kan malaman jihar suka zarge ta da ""jan kafa"", game da zaman tuhumar suka ce za su yi wa Sheikh Abduljabbar a kan zargin cin zarafin Manzon Allah (SAW) da Sahabbansa. Sheikh Abduljabbar ya sha musanta wannan zargi. A farko gwamnatin ta Kano ta sanya ranar muhawarar kafin daga baya a ɗage ranar, kuma a yanzu an samu bambamace-bambamce kan yadda za a gudanar da muƙabalar daga tsarin da aka yi da farko. Ga dai wasu abubuwa shida da wataƙila ba ku sani ba da suka danganci muƙabalar: Gwamnatin jihar Kano ba ta bayyana sunayen malaman da za su fafata da Sheikh Abduljbbar Kabara ba a wannan muƙabalar. Kwamishinan Al'amuran Addinai na jihar Muhammad Tahar Adamu (Baba Impossible) ya ce sai a wajen muƙabalar ne za a fadi sunayen malaman da za su yi. Haka kuma a baya, ita ma haɗakar malaman ta Kano ta ce ta shaida wa gwamnati malaman da za su wakilce ta, amma ta ce ba za ta bayyana ba sai a zauren muƙabalar. Sai dai sanannen abu ne cewa malamai daga ɓangarorin Ahlussnnah da Izala da Tijjaniya da Kadiriyya ne suke ƙalubalantar Sheikh Abduljabbar. Wakilin Malaman Ahlussunnah shi ne Sheikh Abdulwahhab Abdullah, sai Shehi-Shehi da ke wakilatar ɓangaren Tijjaniyya, sannan sai Sheikh Ƙaribullah Nasiru Kabara da ke wakiltar ɓangaren Ƙadiriyya, wanda yaya ne ga Sheikh Abduljabbar, yayin da Sheikh Abdullahi Pakistan yake wakiltar ɓangaren Izala. Ba a faɗi su waye za su yi alƙalancin wannan muhawara ba da kuma waɗanda za su zama masu sa ido. Su ma sai a wajen taron ne sannan za a sanar kamar yadda Kwamishina Baba Impossible ya ce. Da wakilin BBC na Kano Khalifa Shehu Dokaji ya tambaye shi dalili, sai ya ce ""abin da ya sa ba za a faɗa ba saboda kar a samu uzuri daga wajen wasu da ba za su samu halarta ba a ƙurarren lokaci."" Amma da zarar an kammala taruwa a zauren muhawarar to za a bayyana sunayen alƙalai da masu sa ido kamar yadda ya ƙara da cewa. Littattafan Sheikh Abduljabbar Tuni dai gwamnatin jihar Kanon ta amince cewa Sheikh Abduljabbar Kabara na iya tafiya da ɗumbin littattafansa wajen, wadanda yake son yin amfani da su don kafa hujjoji, kamar yadda ya faɗa a wasiƙar da ya aika wa Gwamna Ganduje ta godiya. Kazalika wani hoto ya yaɗu da ke nuna shi da litattafan jibge a gabansa yana nuna alamun ya shirya. Yawan litattafan da yake shirin zuwa da su sun kai kimanin 300, kuma tuni aka shirya su aka kuma ɗaure su ta yadda za a ɗauke su cikin sauƙi. Bayan nan malamin ya buƙaci zuwa da mutum hudu da za su ringa taimaka masa wajen ɗaukar litattafan idan buƙatar hakan ta taso, sanna ya roƙi a ba da izinin nuna muhawarar kai tsaye a kafafen yaɗa labarai Sai dai ga alama gwamnatin Kano ta riga ta yanke hukunci kan yadda tsarin muhawarar zai kasance, ba za a iya sanin ko za ta amsa buƙatun Malam Kabara ko a'a ba har sai an je wajen a gani. Ba za a nuna muhawarar kai tsaye a gidajen talabijin ba kuma ba za a watsa kai tsaye a gidajen rediyo ba, sannan ba za a ɗauke ta kai tsaye a shafukan sada zumunta ba, kamar yada gwamnati ta ce. A wancan karon da aka fara sanya ranar muhawarar an bayyana cewa za a watsa ta kai tsaye domin a kalla a kuma saurara. Amma a wata wasiƙa da Sheikh Abduljabbar ya aike wa Gwamna Ganduje ta amsa gayyatar muhawarar da kuma nuna godiya, ya roƙi gwamnati da ta bari a watsa muhawarar kai tsaye a kafafen labarai. Sai dai Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar Malam Muhammad Garba ya ce an ɗauki matakin hana watsa ta kai tsayen ne a wannan karon saboda yanayin tsaro. ""Mun yi hakan ne don tabbatar da tsaron malamai da sauran mahalarta taron,"" kamar yadda ya shaida wa Khalifa Dokaji. Gwamnatin ta ce sai an kammala gaba ɗaya sannan a yaɗa yadda ta kasance. Gwamnatin jihar Kano ta ce ba za ta bar ƴan jarida da yawa su shiga ɗakin taron gudanar da muhawarar ba. Kwamishinan yaɗa labaran ya ce za su taƙaita yawan ƴan jaridar da za su shiga ciki. Daga cikin kafafen yaɗa labaran da za suka sami izinin shiga har da BBC da Murayar Amurka VOA da kuma wasu tsirarun kafafe na ciki da wajen jihar Kano da ba a bayyana sunayensu ba. Gwamnati ta ce ba za bar mutane da yawa su shiga wajen muhawarar ba. A binciken da BBC ta yi ta gano cewa waɗanda za a bari ɗin Malamai ne da jami'an tsaro da tsirarun ƴan jarida, da wasu jami'an gwamnati kamar Kwamishinan Yada Labarai da Kwamishina Kula da Harkokin Addinai. Amma a wasiƙarsa, Sheikh Abduljabbar ya roƙi gwamnati ta bar shi ya je da mutum huɗu, biyu waɗanda za su ɗauki rahoton yadda za ta kasance, sai kuma biyu masu kula da litatttafansa. Hukumar Shari'a ta jihar Kano da ke kan titin Abdullahi Bayero ne wajen da za a gudanar da wannan muhawara. A wancan lokacin da aka saka ranar muhawarar karo na farko a watan Maris, gwamnatin Kano ta ce a Fadar Sarkin Kano za a yi muhawarar. Sai dai ba ta bayyana dalilin sauya wajen yin muhawarar zuwa Hukumar Shari'a ta Jihar ba." https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-57782946 +religion Hajj 2021: Falalar goman farko na watan Dhul Hijja na Babbar Sallah "Ku latsa hoton da ke sama domin kallon hira da Sheikh Muhammad Watan Dhul Hajji shi ne wata na 12 a tsarin kwanan wata na Musulunci kuma a watan ne ake yin tsaiwar Arafat da sallar Idi. Malamai na jan hankalin Musulmi da su dage da neman rabauta a wannan wata kama daga yawan ibada da sadaka da kyauta da kuma yawan ambaton Allah da annabinsa. Sheikh Muhammad Mashhud ya ce ""ana son mutum ya dage da yawan karatun al'qur'ani da salatin annabi da yawaita azumi da kyautatawa jama'a."" Watan na Dhul Hijja dai na daya daga cikin watanni guda hudu da Allah ubangiji ya kira da 'Arba'tu Hurum.'" https://www.bbc.com/hausa/media-57784696 +religion Ana ce-ce-ku-ce kan Fatawar Mufti Shawki Allam cewa Sahabbai sun ƙayyade iyali don rage yawan jama'a "Sanarwar da hukumomin Masar suka fitar game da karuwar yawan jama'a da kuma fatawar babban shehin malamin ƙasar Mufti Shawki Allam sun janyo ce-ce-ku-ce a ƙasar musamman a kafofin sada zumunta musamman kan kalaman malamin wanda ya ce sahabbai sun yi amfani da hanyoyin hana ɗaukar ciki. Allam ya ce ""ƙididdiga na da mahimmanci kuma ya zama dole don fahimtar haƙiƙanin gaskiya da kuma fahimtar haɗarin yawan jama'a."" Ya kuma jaddada cewa ""ba mu fuskantar matsalar addini wanda zai iya kawo cikas ga fuskantar ƙaruwar jama'a, amma bayani da fahimtar zahirin gaskiya da zai ba mu damar ci gaba a hanyoyi daban daban. "" Shehin malamin na Masar ya kafa hujja da Hadisin Imam Abu Hamid Al-Ghazali kan batun, yana mai nuni da cewa ""Sahabbai sun yi amfani da hanyoyin da suke da su don hana ɗaukar ciki lokacin kwanciya da iyali, ta hanyar azalo, kuma hakan ya faru a zamanin Annabi Muhammad SAW da kuma yardarsa."" Kalaman Mufti Allam na zuwa ne a yayin da gwamnati ke wayar da kan mutane game da manufar taƙaita haihuwa a Masar da kuma ƙaruwar yawan jama'a a ƙasar. A cikin wata sanarwar daga tashar ""Echo of the Country"", shugaban Masar Abdel Fattah El-Sisi ya ce: ""Ƴan ƙasar ba za su ci moriyar rayuwarsu ba, matsawar ana samun yawan karuwar jama'a ta wannan hanyar."" Ministan tsare-tsare da raya tattalin arzikin Masar, Hala Al-Saeed, ta yi kiran ""rage yawan haihuwa a kasar,"" tana mai cewa ""a kowa ce dakika ɗaya ana haihuwar jarirai 14 a Masar."" Kalaman shehin malamin na Masar da kuma bayanan hukumomin Masar sun tayar da ƙura a shafukan sada zumunta. Wasu sun zargi malamin da ""bayar da fatawa don faranta ran manufofin siyasar ƙasar."" Wasu kuma sun kafa hujja da maganganun malamai da hadisan da ke ƙarfafa haihuwa. Rifai al-Bitar ya nuna cewa ""Idan gwamnati za ta ɗauki mataki, ya kamata ta zama abin koyi ga jama'a,"" kuma ya yi tambayar cewar: ""Yara nawa ne shugaban kasa da Firaminista da ministoci da gwamnoni ke da su?"" Nabil ya soki yadda ake amfani da gazawa inda ya ce an ci gajiyar yawan jama'a a fannoni da dama na ci gaban ƙasar kamar gina madatsun ruwa da mashigin Suez da kuma dalar Masar. Wasu sun ƙi mayar da hankali kan da'awar batun yawan jama'a tare da yin watsi da batutuwan ""cin hanci da rashawa da amfani da albarkatun ƙasa."" A gefe guda kuma, da yawa sun nuna goyon bayansu ga abin da jami'an Masar suka faɗa. Iman ta ce ƙaruwar yawan jama'a a halin yanzu bala'i ne. Dan jarida Ahmed Moussa ya bayyana ƙaruwar yawan jama'a a matsayin ""bom wanda zai iya tashi da kowa."" Ahmed Fathi ya ce duk abin da gwamnati ta faɗa ""yana da inganci kuma yana bisa hanya, amma bai isa ba, kuma dole ne a samu tsari da hanyoyin ci gaban ƙasa tare da ƙarfafa gwiwar mazaje." https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-58320568 +religion Ku san Malaman ku tare da Sheikh Muhammad Abubakar Madu Bulamari An haifi Malam Muhmmad Abubakar da aka fi sani da suna Madu Bulamari a kauyen Nariku a karamar hukumar Bama, ranar 1-1-1959. Kasancewar inda aka haife shi, a kusa da Jamhuriyar Kamaru ne, wanda Kogi ne kadai ya raba su, sai aka mika shi hannun wani shahararren malami, Goni Madu Yachammaye, amma kafin wannan lokacin sai da ya fara karatu a hannun kakanshi, da ya kai shekara bakwai zuwa takwas ne aka mika shi hannun Goni. ''Nan na yi karatu har na kai lokacin da zan kula da almajirai da jan ragamarsu, mu ne har kauyukan Banki, sai Bama da Maiduguri. Malam Madu Bulamari ya fara ba ni gudummawa ciki har da karatun Ahlari da Ishmawi da sauransu. Daga nan sai na kai ga munzalin fara yawo cikin kauyukan kasar Banki inda nake koyarwa, muka shiga Bama da Maiduguri,'' in ji Malamin. Malamin farko da ya fara ba shi gudummawa a cikin Maiduguri, shi ne Sheikh Muhammad Abba Ari, malami na uku kuma shi ne Malam Madu Fakarawi, dukkansu a nan Maiduguri suke. Wani amininsa shi ne ya ba shi wayewar hada ilimin boko da na Muhammadiyya, sun ba shi shawarar ya rubuta jarrabawar kammala makarantar Sakandare. Allah cikin ikonsa na rubuta WAEC na samu maki mai kyau a darussan Arabiyya da Hausa da kuma Ilimin addini. Malamin ya kara da cewa: ''Daga nan sai na tsunduma na yi karatun Difloma, da ita na yi amfani na kai ga shiga jami'a aka ajiye ni a matakin shekara ta biyu na karatun digiri. Gab da za mu fara jarrabawa sai Allah cikin ikonsa sai wata harkar kasuwanci ta taso, shawarar magabata na bar karatun na koma kasuwanci kuma ban kara komawa karatun jami'a ba''. Malamin ya ce ingantaccen, karatun allo da ya samu, ya yi babban tasiri gare shi, sakamakon shi ne mabudi ko wani haske mai saukakawa mutum karatun Al-Kur'ani mai girma, da sauran littafan addini. Malamin ya ce ya fi sha'awar fannin Fiqhu, na addinin Musulunci. Mutane sun fi son karatun tafsiri, amma da zarar ka san Fiqhu, zai sanya ka fahimci ainahin Al-Kur'ani. Abu mafi soyuwa a gare shi, shi ne yadda mahaifiyarsa ta kama hannunsa a ranar da ya sauke Al-Kur'ani mai girma, wannan rana ce mafi soyuwa a gare shi. ''Lokacin da ba ya karbo min wani abu, yana fita bam ya tashi a nan cikin Maiduguri, yana cikin wadanda suka rasu,'' in ji Malamin. Ya ce zaman lafiya shi ne abu mafi soyuwa a gare shi, babu tashin hankali ko tsangwamar juna. Allah ya albarkaci Malamin da mata daya da kuma 'ya'ya goma sha takwas. https://www.bbc.com/hausa/labarai-61591561 +religion Ramadan: Hotunan makon farko na watan Azumi Miliyoyin musulmi na gudanar da azumin watan Ramadan, wata guda na azumi da gudanar da addu'o'i. Wannan shi ne azumin watan Ramadan na biyu da aka yi shi cikin annobar korona, hakan na nufin wasu al'umomin za su yi azumi cikin taka-tsantsan da bin ka'idojin kariya daga cutar. Masu azumi ba za su ci abinci ko shan ruwa ba a tsawon yini guda, har sai zuwa faduwar rana. Azumi ibada ce mai matukar muhimmanci, wadda ke kusanta bawa da ubangijinsa, da kara lafiya da kuma koyarwa ta fannoni da dama. Ga wasu daga cikin hotuna daga sassa daban-daban na duniya, kan yadda wasu musulmi suke gudanar da ibada a watan azumin Ramadan. Ana yin azumin Ramadan a watan 9 na addinin Musulunci, inda ake farawa da ganin watan wanda aka fi sani da hilal. Watan Ramadan lokacin ibada ne mai matukar muhimmanci ga al'ummar musulmi. Sannan daya daga cikin shika-shikan musulunci guda biyar, wanda ya zama wajibi ga kowanne musulmi ya aikata su, kamar yadda Allah SWT ya umarta. Haka kuma kauracewa ci da sha a tsahon yin, Ramadan lokaci ne da ake son musulmai su yawaita sadaka, da kara kusanci da Ubangiji , da nuna karamci da kyautatawa. Yayin da aka fara azumin Ramadan a ranar 12 ga watan Afrilu, yawancin musulmai za su sha wuya wajen amfani da dokokin kariya daga cutar korona, da za su hana su yin wasu bukukuwan al'ada. Yawanci a Birtaniya iyalai suna zaman yin buda-baki ne tare da 'yan uwa da abokan arziki, amma saboda dokar kulle, haduwar za ta yi wuya. Har wa yau, duk da cewa an haramta taruwar mutane da yawa a lokacin Azumin Ramadan na bara, wannan shekarar watan ya zo ne daidai lokacin da aka fara sassaut dokar kulle a wasu yankunan kasar. An amince sama da mutum shida su hadu a waje, sannan gidajen sayar da abinci za su dinga sayar wa mutane abinci a waje. Amma a wasu yankunan na duniya an sanya dokokin da suka hada da sanya takunkumi a lokacin ibada da sauran wurare. A wani sako da hukumomin Hadaddiyar Daular Larabawa ta wallafa a shafin Twitter, an bukaci mutane su kiyaye taruwa a lokacin azumi, su takaita ziyarar 'yan uwa, da kiyaye rarraba abinci tsakanin gidaje da iyalai. A Bangladesh, gwamnati ta sanar da tsauraran matakan kulle na mako guda, daga 14 ga watan Afirilu. Dukkan hotunan suna da hakkin mallaka. https://www.bbc.com/hausa/labarai-56746264 +religion Yadda ƙin jinin Musulunci yake saka Indiya cikin tsaka-mai-wuya "A watan Afrilun shekarar 2020, wani taro da Musulmai suka yi da ya janyo yaduwar cutar korona a Indiya, ya zamo sila na ƙaruwar ƙin jinin Musulunci. Dubban masu wa'azi daga cikin kasar da ma waje ne suka halarci taron a Delhi, wanda wata kungiya mai suna Tablighi Jamaat ke shiryawa shekara da shekaru. Jam'iyya mai mulki ta Narendra Modi BJP, ta kira taron a matsayin taron yaɗa cuta. Masu ƙin jinin Musulmai da wasu kungiyoyi sun ɗora alhakin yaɗa cutar a kan taron, inda aka rinka yadawa a shafukan sada zumunta ana rubuta ""A kare kasarmu daga annobar korona."" Indiya dai ta tuhumi kusan mutum 1,000 da suka halarci taron da karya dokokin kullen korona. Yawancin masu wa'azin da suka je taron daga Indonesiya suke, wato abokiyar huldar kasuwancin Indiya. Indonesiya dai ta bayyana rashin dadinta game da batun a wajen wani taro da aka yi. 'Yan majalisar dokokin kasar sun yi zargin cewa ana amfani da wannan taron ne wajen muzgunawa Musulmi a Indiya. Wani jami'in diflomasiyya a Indiya ya ce wannan misali ne na irin rikicin cikin gidan da ke faruwa. Irin abin da ke faruwa a Indiya a kan batun kalaman batanci ga Musulmi a yanzu ba shi ne na farko ba da jam'iyya mai mulki ke fuskantar suka akai ba. Shekaru biyu da suka wuce, dan majalisa daga jam'iyyar BJP, Tejasvi Surya, ya fuskanci suka bayan da ya wallafa wani abu a shafinsa na tuwita a kan batun mata Larabawa. Fitattun mutane da suka hada da 'yan kasuwa da lauyoyi da ma masu sharhi a Hadaddiyar Daular Larabawa da Kuwait, sun yi Allah-wadai da kalaman nasa, abin da ya sa daga baya ya koma shafin nasa ya goge. Haka a shekarar 2018 ma, a wani taro da aka yi, ministan harkokin cikin gidan kasar Amit Shah ya yi wasu kalamai marasa daɗi ga 'yan kasar Bangladesh da suka shiga Indiya ba bisa ka'ida ba. Wannan kalamai sun harzuƙa al'ummar Bangladesh wadda ke da yawan Musulmai, ind ahar wani babban jami'i a kasar ya bayyana kalaman ministan a matsayin marassa tushe da amfani. A cikin shekara ɗayar da ta wuce an sha samun ɓarin kalaman ƙiyayya ga al'ummar Musulmai da yawansu ya kai miliyan 200, daga bakunan shugabannin al'ummar addinin Hindu masu ra'ayin riƙau Wasu daga cikinsu ma a bayyane suka dinga tunzura mabiya addinin Hindun da su ɗauki makamai su aiwatar da kisan kiyashi a kan Musulmai. Ana dai yawan samun kalamai marasa dadi da ake yi wa Musulmai a Indiya, wasu ma a shafukan sada zumunta ake wallafa su. Akwai lokacin da mata 'yan jarida Musulmai suka fusata bayan da aka rinƙa sanya hotunan mata a shafukan sada zumunta wai ana tallata su. Gwamnatin Mr Modi ba ta cika daukar mataki ba, sai dai ta yi shiru ko ta yi ta jan kafa wajen mayar da martani ko kuma ta ɗora alhakin hakan kan wasu da ba ta ambatar sunansu. Duk irin wadannan abubuwan babu abin da suke yi in ban da ƙarfafawa mabiya addinin Hindu gwiwar ci gaba da cungunawa Musulmai da ɓata musu suna a shafukan sada zumunta. Lokacin da Indiyawa mazauna Hadaddiyar Daular Larabawa suka fara sanya abubuwa da suka jiɓanci 'yan kungiyar Tablighi Jamaat a 2020, wata babbar 'yar kasuwa da ke da alaka da masauratar kasar ta wallafa a shafinta na tuwita cewa duk wani da zai rinka nuna wariya ta addini ko kabilanci to za a ci shi tara sannan kuma zai bar kasar. A wannan karon ma kalaman batancin da 'yar majalisar Indiya ta yi ya janyo suka daga kasashe 15 ciki har da Saudiyya da Iran da kuma Qatar. Wannan dalili ala dole ya sa Mr Modi ya dakatar da mai magana da yawun nasa da ta yi kalaman. Yawancin shugabannin jam'iyyar BJP sun yi amanna cewa duk ɗaga jijiyoyin wuyan da ake yi ba da jimawa ba komai zai daidaita. Gaba daya dai, akwai daɗaɗɗiyar alaƙa mai ƙarfi tsakanin India da kasashen yankin Gulf. Akwai Indiyawa kusan miliyan 8.5 da ke aiki a kasashen yankin Gulf, inda suka ruɓanya 'yan Pakistan. Haka kuma akwai Indiyawa da dama a yawancin kasashen duniya. Kuma irin wadannan Indiyawa da ke aiki a kasashe na aikewa da kudi kamar dala biliyan 35 gida a kowacce shekara inda suke tallafawa iyalansu da za su iya kai wa miliyan 40. Huldar kasuwanci tsakanin Indiya da kasashen yankin Gulf ta kai ta dala biliyan 87. Iraƙi ce ta fi shigarwa da Indiya man fetur, sai Saudiyya. Fiye da kashi 40 cikin 100 na iskar gas din Indiya na zuwa ne daga Qatar, wannan ne dalilin da ya sa Firaministan ke bai wa kasashen yankin Gulf din muhimmanci. A wannan karon gwamnatin Mista Modi da ƙwararru ba su mayar da martani da wuri ba. ""Akwai alamun cewa idan irin wadannan abubuwan suka faru, to tabbas za su zo da ƙalubale. Dole ne gwamnati ta san abin yi. Shin tana son ta shiga cikin ruɗu da ruɗani ne?"" a cewar Farfesa Raghavan." https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-61731911 +religion Muƙabalar Abduljabbar da malaman Kano: Muhimman abubuwa 10 da suka faru a muhawarar "Bayan jira na watanni da aka yi, an gudanar da muƙabala tsakanin Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara da wasu malamai a Jihar Kano ranar Asabar, 10 ga watan Yulin 2021 wadda gwamnatin jihar ta shirya. 'Yan jarida ƙalilan ne suka shiga ɗakin muƙabalar ciki har da wakilin BBC Hausa a Kano Khalifa Shehu Dokaji. Jami'an tsaro sun yi wa ofishin Hukumar Shari'a ta Kano tsinke, wurin da aka gudanar da muhawarar. Waɗannan abubuwa da za ku karanta ba su ne baki ɗayan abubuwan da suka faru yayin muƙabalar ba. Kuna iya shiga wannan shafin domin samun ƙarin bayani. Kafin tsunduma cikin muhawarar gadangadan, alƙalin muƙabala Farfesa Salisu Shehu - shugaban cibiyar Musulunci da tattaunawa tsakanin addinai ta Jami'ar Bayero - ya bayyana sharuɗa kamar haka: Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya fuskanci malamai huɗu ne yayin muƙabalar domin kare kansa daga zargin kalaman ɓatanci ga Annabi SAW. Shehin malami Abduljabbar Nasiru Kabara wanda shi ne mai kare kansa daga malamai huɗu da ke zargin da yin kalaman ɓatanci ga Annabi SAW, ya ce ba zai tuba ba a wurin wannan muƙabala ""saboda rashin ƙwararan hujjoji"". Ya faɗi hakan ne a daidai lokacin da Mallam Abubakar Madatai ya ce duk wanda ya ci mutuncin Annabi hukuncinsa kisa ne sannan ya nemi Abduljabbar da ya fito fili ya tuba. Sai malamin ya ce: ""Ba zan tuba a wurin wannan mukabala ba har sai an ba ni cikakkiyar hujja. Indai aka ba ni hujjojin da suka fi nawa zan tuba, amma yanzu mutum ba zai tuba ba bayan yana kan gaskiya. Ba'a biyo turbar da zan tuba ba."" Malam Abduljabbar Nasiru Kabara ya roƙi 'yan uwan muhawararsa da gwamnatin Kano mai shirya muƙabalar da a asake zaman yin tattaunawa jim kaɗan bayan Mallam Abubakar Madatai ya zarge cewa ya ce Annabi SAW ɗan giya ne. Mallam Abubakar Madatai: ""A wane hadisi ne ya zo cewa Annabi ɗan giya ne?; lokacin da aka yi aurensa da Nana Khadija a bige aka yi saboda sun sha giya; Annabi ya fito daga tsatson da ba tsarkakakke ba."" Abduljabbar: ""Abu ne mai sauki; ji ne ko dai ma'anar ce ba a fahimta ba. Dukkan kalaman da ake tuhuma ta a kai kore su nake yi daga Annabi SAW. Ina roƙon a sake saka rana don sake tattaunawa da waɗan nan malamai don fito da abubuwa."" Sheikh Abduljabbar ya ce shi ma Annabi yake karewa daga irin ƙagen da ake yi masa a wasu hadisai amma babu isasshen lokaci na tabbatar da hakan ""saboda minti 10 sun yi kaɗan"". ""Abin da nake yi ina yin su ne don rarrabe hadisan da ake yi wa Annabi ƙarya. Da don Annabi ake yi da an bayar da isasshen lokaci don a yi muƙabalar. Littafan da na zo da su, minti goma sun yi kaɗan a kwance su."" Farfesa Salisu Shehu wanda shi ne alƙalin muƙabalar, ya zargi Sheikh Abduljabbar da ƙin amsa wasu tambayoyi da kuma ƙin buɗe littafi don bayyana inda ya ciro wasu abubuwan yana mai fakewa da rashin isasshen lokaci. ""A kowace gaɓa, malam Abduljabbar ba ya tsayawa a kan tambayoyin da aka gabatar masa saboda na farko yana cewa babu isasshen lokaci,"" a cewarsa. ""Na biyu yana cewa a tsaya a kan maudu'i ɗaya a yi magana, amma shi ne ba ya tsayawa a kan maudu'i guda ɗayan, sai ya yi ta yawo yana haɗo mas'aloli daban-daban maimakon ya yi bayani game da tambayoyin da aka yi masa. ""Idan ya yi da'awar cewa maganar da ya yi ta kaza a littafi kaza ya gani; in an ce ya buɗe littafi ya karanto wa mutane sai ya bayar da uzurin cewa babu lokacin da zai karanto wa mutane."" Shehin malami Abduljabbar ya zargi alƙalin da ke kula da muhawarar, Farfesa Salisu Shehu, da cewa yana mara wa abokan muhawarar tasa baya. ""Kamata ya yi a ce a haɗa ni da wanda na sani amma sai ga shi na ga alƙalin muƙabalar ya goyi bayan malaman da muke mukabala da su,"" in ji shi. Ya bayyana hakan ne a daidai lokacin da Mallam Kabir Bashir ya zarge shi cewa ya ce Annabi ya tura kawaliya don ta duba masa wata budurwa, zargin da Abduljabbar ya musanta nan take. Mallam Abduljabbar ya ƙi bai wa Malam Kabir Bashir Kofar Wambai amsar wata tambaya yana mai cewa ba a yi masa adalci ba; saboda ba a ba shi damar da zai kunna murya ba kamar yadda abokan muƙabalarsa suke yi. Ya ƙara da cewa ba zai sake amsa wata tambaya kan wata muryarsa da aka kunna ba sai dai waɗanda aka kai wa gwamna da sarki waɗanda suka yi amfani da su a matsayin hujjar da kotu ta rufe masallacinsa kuma aka hana shi wa'azi. Jim kaɗan bayan kammala muhawarar ce kuma Sheikh Abduljabbar ya ce bai gamsu da muƙabalar ba amma ya ce duk sanda aka sake nemansa zai zo. ""Fisabilillahi da gyara, wannan ba tsarin yadda ake muƙabala ba ne, ban gamsu ba,"" in ji shi. Shehin malamin ya ce ba a bayyana masa tsarin yadda muƙabalar za ta kasance ba har sai da ya shiga ɗakin tattaunawar. ""Matsalar ba su ba ni tsarin yin (muƙabalar) ba, ban san yaya za a gudanar ba balle na ba su shawarwari,"" a cewarsa. ""Fatanmu dai a samu nasara a zaman, a samu mafita ga wannan addini namu. Ba ƙure ne buƙatarmu ba; ina gaskiya take domin mu samar wa addininmu mafita.""" https://www.bbc.com/hausa/labarai-57790314 +religion Majalisar Malaman Kano: Abin da ya sa muke so a rage yawan Masallatai a Kano "Majalisar Malamai ta ƙasa reshen jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta bayyana dalilanta na yin kira a rage gina Masallatai barkatai a jihar. A wata sanarwa da ta fitar bayan wani babban taron da ta gudanar na kwana biyu a ƙarshen makon da ya gabata a Kano, majalisar ta bayyana jerin sharwari da manufofin da ta cimma a wajen taron, kuma ciki har da rage yawan buɗe masallatai. ""A rage buɗe masallatai barkatai domin guje wa rarraba kai da zukatan al'umma,"" a cewar sanarwar da majalisar malaman ta fitar bayan kammala taron, Amma cikin sanarwar, an yi kira ga malamai da limamai su dinga raya masallatai da karatuttuka da lakcoci baya ga tsayar da sallah a cikinsu. Taron na haɗin gwiwa da Sashen Nazarin Addinin Musulunci da Shari'a na Jami'ar Bayero, ya ƙunshi wakilai na malamai da limamai na ƙananan hukumomin jihar Kano 44 da shugaban Jami'ar Bayero da wakilcin Kwamishinan Lamuran Addini Dr Muhammad Tahar Adamu. Majalisar Malaman ta ce taronta ya mayar da hankali ne kan gudunmawar malamai da limamai wajen samar da tarbiya da inganta zaman lafiya da dora al'amura bisa tushen shari'ar Musulunci. Kuma an gabatar da maƙaloli tare da yin ta'aliki kan makalolin da aka gabatar. Daga cikin matsayar da taron ya cimma, majalisar malaman ta ce ""yin haka zai inganta zaman lafiya a ƙasa baki ɗaya."" Sanarwar ta ƙara da cewa mahalarta taron sun yi takaicin yadda wasu malamai suke zubar da dajararsu ta hanyar yadda ""suke bin ƴan siyasa suna masu yin biyayya."" Haka kuma malaman na Kano sun ce akwai wasu bara-gurbin malamai da ke haddasa rikici da rarrabuwar kai a cikin majalisar malamai domin cimma burinsu na kashin kansu. 'A riƙa yi wa masu mulki nasiha' Majalaisar malaman ta ce malamai da limamai sun bayar da gudunmawa mai yawa a tarihin musulunci wajen jagorantar al'umma game da tarbiyya da shugabanci na gari da zaman lafiya da samar da tsaro ""Wannan ya sumu ne ta hanyar kyawawan dabi'u da taƙawa da tawali'u da gaskiya da magabata a cikin malamai da limamai da suka siffatu da ɗora al'umma kan biyayya da shugabanci da ilimi."" Amma majalisar ta ja hankalin mambobinta kan haƙƙin da ke kansu na yi wa masu mulki nasiha. Ta yi kira ga malaman cewa: ""A riƙa yi wa masu mulki a kowane mataki nasiha kan nauyin da ke kansu."" Ta kuma yi kira da a zaburar da matasa da majalisar ta ce - masu tarbiya game da shiga ayyukan tsaro da harkokin siyasa da shugabanci. Majalisar ta kuma buƙaci malamai da limamai su rika girmamawa da ziyartar junansu domin samar da hadin kai da fahimtar juna domin zaman lafiyar dalibai da sauran al'umma. Majalisar ta kuma jaddada cewa tana gudanar da ayyukanta ne bisa tsarin doka da aka yi mata rijista, don haka ta ja hankalin mambobinta cewa ""babu wanda zai yi mata karfa-karfa ya sa ta yi abin da ya saɓa wa doka da ka'idoji da sharuɗɗanta.""" https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-58492448 +religion Bidiyo: Musulmai da Kiristoci na aiki tare wajen sake gina birnin Mosul na Iraƙi. Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon: Fiye da shekara bayan mummunan yaƙin sake ƙwato Mosul daga hannun ƙungiyar IS, har yanzu tsohon birnin a lalace yake. An ɗauki mutane daga addinai daban-daban a birnin don yin aiki ƙarƙashin wani shiri mai taken “sake farfaɗo da Mosul”, kamar sake gina Masallacin Al Nuri da Cocin Al Saa and Al Tahira masu tsohon tarihi. Fafaroma Francis ya shirya kai ziyara dukkan wurare ukun a watan Maris, amma a baya-bayan nan ya fara tababar zuwa, saboda damuwar kar a tara mutane a yayin da ake fama da annobar Covid-19. Bidiyo daga Daisy Walsh da Gabriel Chaim. Wasu bidiyo da za ku so ku kalla: https://www.bbc.com/hausa/media-55956279 +religion Hotunan manyan masallatai 15 mafiya kyau a duniya "An sabunta wannan labari bayan da aka fara wallafi shi a watan Yulin 2017. Masallaci wani wuri ne na bauta ga mabiya addinin Islama, inda al'ummar Musulmi ke taruwa su yi sallah cikin jam'i. Akwai gine-ginen masallatai masu kayatarwa a duniya wadanda wata kila ba ku taba sanin da su ba, don haka muka kawo muku wasu daga cikinsu. 1. Masallacin Haramin Makkah da ke Saudiyya Al-Qur'ani ya bayyana wannan masallacin a matsayin na farko da aka gina a ban kasa domin dan Adam ya bauta wa Allah. Wannan masallacin, mai suna Al Haram, wato ""Mafificin Masallaci"" shi ne ya fi ko wanne daraja a duniya baki daya, yana da dadadden tarihi, ya fi ko wanne masallaci daraja da girma da kayatuwa. A zagaye yake d a gine-ginen manyan otal-otal masu kyau da tsari wadanda idan kana daga cikisu ma kana iya hango harabar masallacin da cikinsa. 2. Masallacin Annabi SAW da ke Madinah a kasar Saudiyya Wannan masallacin da aka fi sani da masjid An Nabawi, watau ""Masallacin Annabi,"" shi ne masallaci na biyu mafi daraja da kyau da girma bayan na Makkah. Annabi SAW da kansa ya gina masallacin a lokacin da ya yi hijira daga Makkah zuwa Madina shekara 1439 da ta gabata. A ciki kabarin fiyayyen halitta yake da na manyan abokansa biyu kuma sahabbansa Abubakar da Umar Allah ya kara musu yarda. Gidan Annabi SAW a yanzu haka duk ya shiga cikin masallacin. Ana yi wa masallacin lakabi da 'Koriyar Hubba ta Dan Abdullahi.' 3. Masallacin Kudus da ke Jerusalem a Isra'ila Masallaci na uku mafi girma da daraja a ban kasa. Ana kiransa da Al-Aqsa kamar yadda ya zo a Al-Kur'ani mai tsarki ko kuma Baytul-Muqaddas. An gina Masallacin Al-Aqsa ne a garin birnin Kudus da ke kasar Isra'ila. Masallacin shi kan sa an gina shi ne a wani yanki na Al-Haram ash-Sharif, wato ""Mafificin mafaka mai tsarki"", wanda su Yahudawa suke kira Temple Mount, wanda shi ne mafi tsarki su kuma a wurinsu. Ta Baitul Mukaddas ne Annabi SAW ya tafi Mi'iraji. 4. Masallacin Hassan na Moroko Wannan masallacin yana birnin Casablanca ne a Moroko, kuma shi ne masallaci mafi girma a kasar, haka kuma na bakwai a jerin masallatai masu girma a duniya. Hasumiyarsa ita ce wadda ta fi tsayi da kimanin mita 210. An kammala ginin masallacin ne a shekarar 1993. Masallacin Sultan Omar Ali Saifuddin a Brunei Masallacin Sultan Omar Ali Saifuddien, wani masallacin 'yan sarauta ne da ke garin Bandar Seri Begawan, babban birnin masarautar Brunei. Ana yi wa masallacin kallon wanda ya fi ban sha'awa a yankin Asiya, kuma wata matattara ce ta masu yawon bude ido a Brunei. An kammala gininsa a shekarar 1958, kuma yana daya daga cikin gine-gine da ke nuna bajintar taswirar gine-gine a duniya. 6. Masallacin Zahir da ke Kedah a Malaysia Masallacin Zahir, shi ne masallacin jihar Kedah, wanda ke kasar Malaysia, wanda ke tsakiyar garin Alor Star. An gina masallacin a shekarar 1912, da tallafin Tunku Mahmud, dan Sultan Tajuddin Mukarram Shah. Wannan masallaci babba ne sosai kuma yana da kayan kawa na zamani. 7. Masallacin Faisal da ke Islamabad a Pakistan Wannan masallacin shi ne mafi girma a kudu maso gabashi da kudancin Asiya, kazalika shi ne na hudu cikin mafi girman masallatai a duniya. A shekarun 1986 zuwa 1993 shi ne masallacin da ya fi ko wanne girma a duniya, kafin masallacin Hassan na biyu da ke Casablanca a Morocco, da kuma bunkasa Masjid Al-Haram na Makkah da aka yi daga baya, wadanda duk suka doke shi. 8. Masallacin Taj ul da ke Bhopal a Indiya Ma'anar sunan wannan masallaci, ""Sarkin duk masallatai"", kuma yana garin Bhopal ne a Indiya. Ana gudanar da karatun Qur'ani ma a masallacin, da rana. Masallacin shi ne mafi girma a nahiyar Asiya baki daya. 9. Masallacin Badshahi a Lahore, Pakistan Sarkin daular Mughal, Aurangzeb ne ya kaddamar da Masallacin Badshahi, ko kuma ""Masallacin sarauta"" da ke Lahore, a shekarar 1673, wanda shi ne masallaci mafi girma na biyu a Pakistan da kudancin Asiya. Haka kuma shi ne masallaci na biyar mafi girma a duniya. Masallacin ya yi fice a kyau, wanda ya fito da irin kasaitar daular ta Mughal. 10. Masallacin Sultan na Singapore Ana yi wa wannan masallacin da ke layin Muscat da ke gundumar Glam Rochor a Singapore, kallon mafi daraja tsakanin dukkan masallatan kasar. asallacin Sultan ya dade ba tare da an sauya masa komai ba tun da aka gina shi, sai wasu 'yan gyare-gyare da aka yi a harabarsa a shekarar 1960, da wasu kare-kare da aka yi a shekarar 1993. 11. Massalacin Hagia Sophia da ke Turkiyya A shekarar 2020 ne dai Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan, ya mayar da gidan tarihi na Hagia Sophia masallaci. Tun asali wurin coci ne wanda aka mayar masallaci sai kuma daga baya aka mayar da shi wurin tarihi. A halin yanzu bayan shekaru 85 an mayar da ginin masallaci. 12. Masallacin Qaboos da ke Oman A 1992, Qaboos bin Said al Said wanda shi ne Sarkin Oman na lokacin, ya bayar da umarnin gina katafaren masallaci a ƙasar. An fara ginin masallacin ne a 1994 bayan an fitar da taswira da surar masallacin a 1993. An shafe shekaru shida da watanni bakwai ana ginin masallacin. Masallacin dai na ɗaukar masallata 20,000 13. Masallacin Jama, Indiya Masallacin Jehan Numa wanda aka fi sani da masallacin Jama da ke Delhi, na daga cikin manyan masallatan da ke Indiya. Sarki na Daular Mughal wato Sha Jahan ne ya gina shi tsakanin shekarun 1650 zuwa 1656 kan kuɗi da suka kai rupee miliyan ɗaya. A lokacin buɗe masallaci, Imam Syed Abdul Ghafoor Shah Bukhari daga Bukhara shi ne ya buɗe masallacin. 14. Masallacin Istiqlal, Jakarta Masallacin Istiqlal da ke Jakarta a Indonesia shi ne masallaci ma fi girma a kudu maso gabashin nahiyar Asia. Masallacin wanda shi ne babba a ƙasar, an gina shi ne domin tunawa da samun 'yancin kai na ƙasar wanda aka yi masa laƙabi da Istiqlal, a Larabce hakan na nufin 'yancin kai. 15. Masallacin Putra, Malasiya Masallacin Putra shi ne Babban Masallacin birnin Putrajaya, kuma an fara ginin masallacin ne a 1997 inda aka kammala shi bayan shekaru biyu. Haka kuma yana makwaftaka ne da ofishin Firaiministan ƙasar da kuma tafkin Putrajaya. Masallacin na ɗaukar masallata kusan 15,000" https://www.bbc.com/hausa/40709120 +religion Bayanai game da rayuwar gwarazan gasar Al-Ƙur'ani ta 2021 a Najeriya "Da tsakar ranar Asabar 27 ga watan Maris na 2021 ne aka kammala musabakar Al-Ƙur'ani mai girma ta Najeriya a Jihar Kano da ke arewacin kasar. An fara musabakar ce kwana takwas da suka gabata kuma aka kammala a kwana na tara. A ɓangaren mata, wata 'yar Kano mai suna Nusaiba Shuaibu Ahmad ce ta zo ta ɗaya. Muhammad Auwal Gusau, shi ne gwarzon musabaƙar a bangaren maza, kuma ya fito ne daga Jihar Zamfara - ita ma a arewa maso yammacin ƙasar. Hafizan sun gwabza da masu karatu da yawa kuma a karshe suka samu nasara a matakin karatun izu 60 da tafsiri. An bai wa kowannensu kyautar kuɗi naira miliyan biyu da rabi bisa nasarar da suka samu. Sannan kuma za su wakilci Najeriya a musabaƙa ta duniya baki ɗaya. ""Na gode wa Allah da ya ba ni wannan nasara kuma fatana shi ne Ƙur'ani ya zama hujja a gare mu ba a kanmu ba,"" a cewar Nusaiba Shuaibu cikin hirarta da BBC. Gwarzuwar musabaƙar ta 2021 ta haddace Ƙur'ani tun tana 'yar shekara 15 bayan ta fara haddar littafin mai tsarki tana 'yar 11 zuwa 12, kamar yadda ta shaida wa BBC. Nusaiba Shuaibu Ahmad ta fara shiga gasar karatu wato musabaƙa a shekarar 2017. Daga cikin nasarorin da ta samu, ta taɓa zama gwarzuwar musabaƙa wadda cibiyar Alfijir ke shiryawa a Kano. Kazalika ta taba zuwa ta biyar a musabaƙar ƙasa, wadda aka gudanar a Jihar Katsina. Suratul Jinn - sura ta 72 - ita ce ta fi bai wa makaranciyar wahala a loƙacin da take hadda. ""Saboda tana da ayoyi masu kama da juna,"" in ji ta. An haifi Nusaiba a shekarar 2000 a garin Kano kuma tana da miji. Ta kammala sakandare, inda yanzu haka take zuwa jami'a. Gwarzon musabaƙar ta maza haifaffen Jihar Zamfara ne, wanda yanzu haka yake karatun kimiyyar dabbobi (zoology) a aji na huɗu a Jami'ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto. Da BBC ta tambayi Muhammad Auwal Gusau ko me ya sa bai zaɓi darasin Ƙur'ani ba a jami'a? Sai ya ce: ""A zamanin da muke ciki, abu ne mai wuya ka ce ɓangare ɗaya za ka yi (karatu) amma yanzu zan yi karatu a jami'ar Musulunci insha Allahu."" Ɗan shekara 24, Muhammad ya fara haddar Ƙur'ani yana da shekara 10 zuwa 11. ""A lokacin da na fara (hadda) babu abin da ya fi birge mu kamar yadda ake keɓe ɗalibai 'yan ɓangaren hadda, suna gefe daban,"" in ji shi. Ya ƙara da cewa surar da ta fi wahalar da shi a lokacin hadda ita ce wani ɓangare na Suratul Ɗur - sura ta 52. ""Burina yanzu shi ne Allah Ya ba mu nasara a musabaƙa ta duniya da za mu wakilci Najeriya kuma ina da ƙarin gwiwar da taimakon Allah za mu yi nasara,"" a cewarsa. Hafizin ya ce yana fatan ya auri makaranciyar Ƙur'ani kamarsa a nan gaba." https://www.bbc.com/hausa/labarai-56550841 +religion Bidiyon Zikirin Anfasu na mabiya ɗarikar Ƙadiriyya Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon: Babu taƙamaiman adadin mabiya ɗarikar Ƙadiriyya a Najeriya, amma ana ƙiyasin cewa sun kai miliyoyi. Ɗarikar ta Ƙadiriyya na daga manyan ɗarikun sufaye da ake bi a Najeriya, kuma ana ɗaukanta a matsayin ɗarikar da ta fi daɗewa a ƙasar. Sidi Abdulkadir Jilani ya rayu ne a birnin Bagadaza na kasar Iraki tsakanin shekarun 1078 zuwa 1166. Yana daga manyan waliyyai da mabiya ɗariƙun Sufaye suke girmamawa, har ma ana masa kirari da sarkin waliyyyai. https://www.bbc.com/hausa/labarai-54472614 +religion Bidiyon Ku San Malamanku tare da Sheikh Shettima Habib Latsa hoton sama domin kallon bidiyon Fitaccen malamin addinin musuluncin a Najeriya Sheikh Shettima, ya ce duk da bai yi karatun boko ba amma ya taimakawa masu bincike a cibiyoyin ilimi a Ingila da Jamus, musamman kan babban aikin fassara Al Kur’ani mai tsarki zuwa harshen Kanuri. Ya ce tafi Ingila sau uku kuma turawan ƙasar da suka yi wa Najeriya mulkin mallaka ne suka gayyace shi zuwa Landan. Malamin ya ce ya taimaka masu kan binciken da suke yi a Kwalejin nazarin zamantakewar kasashen gabashin duniya da na Afrika wato School of Oriental and African Studies da ke tsakiyar Landan. Ya kuma kai ziyara Jamus sau shida kan aikin fassarar Al Kur’ani mai tsarki da harshen Kanuri a Jami’ar Hamburg. https://www.bbc.com/hausa/labarai-59002741 +religion Me ya sa Indiya ke kai wa wata kungiyar Musulunci samame? "Wata kungiyar Musulmai ta Popular Front of India PFI mai janyo ce-ce-ku-ce a Indiya, na gudanar da zanga-zanga a jihar Kerala ranar Juma’a. An yi hakan ne kwana guda bayan da hukumomin kasar suka kaddamar da samame a ofisoshin kungiyar da dama a fadin kasar, tare kuma da yin awon-gaba da shugabanninta Babbar hukumar yaki da ta‘addanci ta kasar NIA, tare da hukumar ED take yaki da laifukan da suka shafi kudi ne suka kaddamar da samamen a fadin jihohin kasar 11 ranar Alhamis da safe. Aka kuma kame mambobin kungiyar 106, kamar yadda kafar yada labarai ta PTI ta kasar ta ruwaito. Gidan talbijin na News18, ya ambato wata majiya daga hukumar ta NIA na cewa ""samamen na daga cikin wani babban bincike da hukumar ta faro da dadewa. Ranar Juma’a ne dai mambobin kungiyar suka gudanar da zanga-zanga kan adawa da kamen da hukumomin suka yi wa shugabanninta a kudancin jihohin Kerala da Tamil Nadu. A wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta zargi gwamnati da kokarin amfani da hukumomi domin tauye ‘yancin marasa galihu. Sanarwar ta kara da cewa ""Ana kai samamen a gidajen shugabannin kungiyar na kasa da na jihohi da kuma na kananan hukumomi."" A wata sanarwa da hukumar NIA ta fitar ga manema labarai ta ce ta kama mambobin kungiyar 45 saboda zarginsu kan wasu batutuwa biyar. Hukumar ta ce a lokacin binciken jami’anta sun yi awon-gaba da ‘’Wasu takardu masu alaka da aikata laifi, da kudade, da adduna da kuma wasu na’urori masu yawa."" Kungiyar ta PFI – wadda aka kafa a shekarar 2006, ta bayyana kanta da cewa ""kungiya ce mai zaman kanta wadda makasudin kafa ta, shi ne kare hakkin marasa galihu, tare da adawa da zalunci da kuma tauye hakkinsu."" Kungiyar ta kafu ne bayan da kungiyar ci-gaban kasar ta National Development Front (NDF) – wata kungiya mai janyo ce-ce-ku-ce da aka kafa a jihar Kerala shekaru kadan bayan rushe masallacin Babri a shekarar 1992 – ta hade da wasu kungiyoyi biyu daga kudancin jihar. Nan da wasu shekaru masu zuwa, kungiyar PFI ka iya zama wata gawurtacciyar kungiya saboda yadda wasu kananan kungiyoyi ke ci gaba da yi mata mubaya’a. A halin da ake ciki kungiyar PFI, wacce ke da dubban daruruwan magoya baya a jihohin Kerala da Karnataka, na ci-gaba da samun karbuwa a fiye da jihohin kasar 20. A taken kungiyar da ta wallafa a shafinta na intanet, Kungiyar ta yi furucin cewa ta na so ne ta ‘’samar wa da al’umma mai cikakken ‘yanci, da wanzuwar adalci, tare da samun ingantaccen tsaro’’. To sai dai gwamnati ta gabatar da jerin tuhume-tuhume kan kungiyar tare da mambobinta, wadanda suka hadar da ‘’laifin tunzura al’umma, da yin kalaman nuna kiyayya da gaba tsakanin al’umomi, tare da kama hanyar wargaza Indiya’’. An zargi mambobin kungiyar da laifin fille kan wani dan addinin Hindu a yammacin jihar Rajasthan a watan Yuni. A ‘yan watannin da suka gabata, ‘yan sanda a gabashin jihar Bihar sun yi ikirarin cewa kungiyar na yada wasu takardu da ke maganar mayar da Indiya kasar Musulunci. Zarge-zargen da kungiyar ta musanta, tana mai cewa takardun ba na gaskiya ba ne kirkirarsu a ka yi tare da danganta su da kungiyar. Daya daga cikin manyan zarge-zargen da ake yi wa kungiyar shi ne alaka da haramtacciyar kungiyar IS, da kungiyar dalibai Musulmai ta Indiya (Simi), wadda gwamnati da haramta a shekarar 2001. Haka kuma ana zargin kungiyar da laka da kungiyar Mujahideen wata kungiyar ‘yan ta’adda da itama gwamnati ta haramta. Farfesa P Koya, wanda shi ne ya kafa kungiyar ta PFI ya musanta duka zarge-zargen tun da farko a wata tattaunawa da ya yi da BBC. A tattaunawar ya ce ya kafa kungiyar NDF a shekarar 1993, shekaru bayan da ya yanke alaka da kungiyar Simi a shekarar 1981. A shekarar 2010 ne aka fara nuna yatsa kan kungiyar bayan wani farmaki da aka kai wa Farfesa TJ Joseph a jihar Kerala. Lamarin ya zo ne bayan da kungiyoyin Musulunci da dama suka zarge shi da laifin yin tambayoyin da ke kaskantar da darajar Annabi Muhammad SAW a lokacin wata jarrabawa. Kotu ta kama wasu daga cikin ‘ya’yan kungiyar da laifin farmakin, koda yake kungiyar ta nesanta kanta game da wannan zargi. A shekarar 2018 an zargi ‘yan gwagwarmayar kungiyar PFI da laifin daba wa wani shugaban daliban jihar Kerala wuka, lamarin da yayi sanadiyyar mutuwarsa. Shugabannin kungiyar PFI sun jan hankulan kafofin yada labarai game da maganganun da wasu ke kallo a matsayin tunzuri. Kungiyar ta yi ikirarin cewa tana da dimbin mabiya a jihar Kerala, to sai dai ba ta samun ci gaba ta fannin siyasa. Tana da jam’iyyar siyasa da ta yi wa rajista mai suna Social Democratic Party of India (SDPI), wacce ta shiga zabukan jihar, ta kuma samu kwarya-kwaryar nasara a jihar, ko da yake ba ta samu ko kujera daya a majalisar dokokin kasar. Farfesa Adil Mehdi tsohon malami ne a Jami’ar Musulunci ta Jamia Millia da ke birnin Delhi, ya ce ‘’kungiyar PFI ba wata kungiya ba ce mai karfi a Indiya. Duka-duka tasirinta bai wuce jihar Kerala da wasu jihohin kudancin kasar. Musulmai da yawa da ke zaune a wasu yankunan Indiya ba su ma san da ita ba a matsayin jam’iyyar Siyasa’’. A farkon shekarar nan ne, gwamnatin jihar Karnatakata zargi kungiyar PFI da rura wutar zanga-zanga, bayan da wata makaranta a jihar ta hana dalibai mata sanya hijabi. Masu sanya ido sun ce kungiyar mata da dalibai reshen kungiyar ne ke kan gaba a zanga-zangar da aka gudanar a fadin kasar. Kungiyoyin kishin addinin Hindu tare da hadin gwiwwar jam’iyyar BJP mai Mulki, sun dade suna kiraye-kirayen haramta kungiyar PFI. Haka kuma babbar kotun Kerala ta taba ayyana kuniyar PFI a matsayin kungiyar ‘’masu kaifin kishin addini."" Kungiyar PFI na ci gaba da musanta alaka da ayyukan ta’addanci, sannan kuma masu sharhi na ganin cewa tuhumar alaka da ta’addanci da ake yi wa kungiyar - wanda shi ne ya haddasa samame tare da kamen da aka yi wa ‘yan kungiyar - ba ta da tushe balle makama." https://www.bbc.com/hausa/articles/c4ne8zvn47go +religion Yadda mata biyar suka bayyana rayuwa a karkashin tsarin shari'ar Musulunci a wasu sassan duniya "Zango na farko na mulkin Taliban ya kasance cike da cin zali da danne hakkin mata, wadanda aka tsame su daga harkar neman ilimi da aiki, da ma dukkan wasu aikace aikacen jama'a. Sai dai a wannan karon, ƙungiyar ta ce za a tafi da mata, za a mutunta 'yancinsu bisa tsarin Shari'ar Musulunci, sai dai baza a iya cewa ga yadda al'amura za su kaya ba. A ƙashin gaskiya, Shari'a tsarin zamantakewa ne bisa umarnin Ubangiji, ciki har da Sallah da azumi da sadaka ga mabukata Haka kuma wani tsari ne na shari'a, inda ake hukunta masu laifi dai dai da ka'idar addinin Islama, amma wasu kungiyoyin kare hakkin jama'a na ganin baiken tanaje-tanajen hukunci bisa tsarin shari'ar Musulunci a wurare da dama. Ko da yake akwai iyakar da aka yi wa mata ta fuskar shiga siyasa a tsarin shari'ar Musulunci, sai dai kasashe da dama da ke bin tsarin shari'ar Musulunci ba sa tsauwalawa kamar yadda Taliban ta yi a Afghanistan a shekarun 1990. BBC ta tattauna da wasu mata biyar kan yadda rayuwarsu ke kasancewa karkashin tsarin shari'ar Musulunci a kasashen Saudiyya da Najeriya da Indonesia da Brunei. Ni 'yar asalin ƙasar Tanzaniya ce, sai dai mafi yawan rayuwata na yi ta ne a Saudiyya, in ji Hannan Abubakar. Na je wata makaranar kasa da kasa da a ke koyar da dalibanta bisa tsarin koyarwar Indiya. A cikin motocin bas, yara maza da mata kan zauna daban-daban, yayin da a kantuna kuwa ake ware wajen maza daban na mata ma daban. Su kansu azuzuwanmu ma na mata daban suke da na maza, sai dai duk da haka malamai maza ne ke koyar da mu a wasu fannoni. An bai wa 'yan mata damar shiga wasanni, amma ba tare da samari ba, kuma mukan yi bikin wasanninmu a ranakun da suka sha bamban don gudun cakuduwa maza da mata. Saudiyya ta kasance wuri mai 'yanci a yanzu. Mata za su iya tafiya su kaɗai kuma su tuƙa motoci. Ina shirin samun lasisi nan ba da jimawa ba. Bayan 'yan shekarun baya ba mu da sinimomi, amma yanzu muna da su kuma muna zuwa, ina son zuwa irin wadannan wurare. Ba na rufe fuskata kuma ba ""dole"" ne sanya mayafi ba. A da, gidajen cin abinci suna da bangaren iyalai daban. Yanzu ba mu da irin wannan wariya. A wuraren taruwar jama'a, maza da mata za su iya haduwa, alal misali ina fita cin abinci tare da abokan aikina maza. 'Haramun ne shan barasa, amma ana sha a wuraren holewa' Sai dai duk da haka har yanzu ƙasa ce ta Musulmai, don haka babu kulob na dare, ba mashaya da sauransu. Ba a yarda da giya ba. Ina aiki a kamfanoni masu zaman kansu a Jidda. A cikin kamfanina, ana biyan mutane gwargwadon aikinsu ba don jinsi ba. Shekaruna 30; Zan yi aure lokacin da na hadu da kyakkyawan sahibina. Ina da iyayen da suke ƙarfafa mini gwiwa sosai, ba sa tilasta mini in yi aure. Wasu na cewa wadannan sauye-sauye sun zo a makare, amma mahaifiyata da ta kasance a Saudiyya tun kafin a haife ni ta ce ta ga saurinsu. A Iran, irin takunkumin da mace ke fuskanta ya danganta da asalin danginta in ji Mahsa. (Mahsa ta nemi kar a yi amfani da cikakken sunanta ko nuna fuskarta don tsaron lafiyarta.) Ana iya raba al'ummar Iran gida uku. Wasu masu tsananin addini ne, da masu tsaurin ra'ayi, da masu zazzafan tunani da nuna wariya, har ma za su iya kashe 'ya'yansu mata ko' yan'uwa mata saboda wata alaƙa mai sauƙi da saurayi. Rukuni na biyu kamar iyalina ne, masu matsakaicin ra'ayi, babban abin da suka mayar da hankali a kai shi ne samun ilimi da aiki. Na uku kuwa su ne attajirai ne masu arziki waɗanda doka ba ta aiki a kansu. An haife ni kuma na girma a Tehran. A makaranta da jami'a na yi karatu tare da samari. Yawancin iyaye a Iran suna son yaransu su yi karatun likitanci ko injiniya, amma na kasa samun gurbin karatu a kwalejin koyar da aikin likitan hakora, kuma na karanci Turanci. Ina koyarwa a makarantar yara. Mata a Iran na tafiya garuruwa daban -daban. Mata marasa aure za su iya yin hayar gida su zauna su kaɗai. Suna kuma iya shiga cikin otel da kansu. Ina da mota tawa kuma ina zaga gari. Babu bukatar abokin rakiya namiji, amma sanya abin rufe fuska {Nikab} wajibi ne. Idan jami'an kiyaye shari'a suka ƙyallara ido suka hango wasu matasa na lalata ko wata mace sanye da ɗan gajeren mayafi, to kuwa za su shiga matsala. Amma za a iya barinsu su tafi idan suka bada ɗan na goro. Wani lokaci ana iya kai masu laifin zuwa ofishin 'yan sanda kuma ana kiran iyayensu don a kunyata yaran. ""Na yi soyayya da saurayina ta tsawon shekaru hudu kafin in yi aure. Na kan je gidajen sinima, wuraren shakatawa da ko ina tare da shi. ""Na yi sa'a. Babu wanda ke tsayawa bin diddigin ko ma'aurata ne mu ko kuwa a'a. ""Iyayena suna da kafiya sosai, ko yaushe suna son in dawo gida kafin kare 9 na dare, kuma ba za su bar ni in yi tafi tafiye -tafiye tare da abokaina ba. Amma bayan aurena na samun 'yancin yin duk abin da nake so. An haramta barasa. Ba mu da mashaya. Amma mutane suna siyan ta a ɓoye suna sha. Ni ban taɓa ko lasa ba, don bana son wannan dacin nata. Ba na so in haifi yara, don albashinmu bai taka kara ya karya ba, Na yi imani da Allah amma ni ba na tsauwalawa a addini, ba na yin addu'a kowace rana. Ni lauya ce ta shari'a kuma na yi shekaa 18 a Kano, Abuja da Legas, in ji Huwaila Ibrahim Muhammad daga Najeriya. Na yi imani da tsarin shari'a. A cikin jihohi 12 na Najeriya, ana amfani da ita don warware laifukan da suka shafi iyali. Ina yin aiki a kotunan shari'a da kuma kotunan shari'a na gama gari, alkalai maza ne ke jagorantar kotuna amma mata suna jayayya ba tare da tsoro ba. Alƙali yana buƙatar yin la'akari da abubuwa da yawa na yin sassauci kafin bayar da mafi girman hukunci. A wasu laifuffuka, ana yanke hukunci a gaban kotu amma har yanzu ban ga an hukunta mata haka ba. Wasu hukunce-hukuncen da aka yanke na yin jifa da kisa sun sun ja hankalin duniya, amma ba a aiwatar da su ba. Idan aka zo ga rabon gado, kason maza na ninka na mata, wannan na iya zama rashin adalci, amma akwai dalili don a baya ba a ba mata nauyin kuɗi ba. Hakkin iyaye ne, 'yan'uwa da mazaje su kare su. 'Na san abun da ya dace da wanda bai sani ba'' Eh akwai dokar da ta ce mutum zai iya dukan matarsa, amma yadda fahimtar take shine miji zai dan buge ta ne amma ba yadda zai raunatata ko kuma ya illata ta ba. Wasu mata sun gurfanar da mazajensu da ke cin zarafinsu gaban kotu. Na wakilci wasunsu da yawa, kuma na ci irin nasara a irin waɗannan shari'o'in. Zan ce ana yin adalci ba tare da la'akari da jinsi ba. A Najeriya ba sai kun rufe fuska ba. Mata a nan sun saba rufe jikinsu, zai zama abin ban mamaki idan wani ya sanya ɗan gajeren siket. Hukunta mata saboda rashin sanya cikakkiyar sutura ko gyale ba daidai ba ne. Mata suna da 'yancin zaɓar abun da za su sanya a jikinsu. Idan aka yi amfani da Shari'a kamar yadda ake tsammani, ta fi kowace doka cika. Izzati Mohd Noor An haife ni kuma na girma a Brunei. Na bar ta a 2007 lokacin ina shekara 17 bayan na karɓi tallafin karatu na gwamnati zuwa Burtaniya, in ji Izzati Mohd Noor. Na yi karatun digiri, da masters da PhD a injiniyar sinadarai a London. Bayan haka na yi aiki a bankin saka jari a matsayin mai haɓaka manhajoji. Makonni kadan da suka gabata na dawo ƙasata. Mafi yawan mutane a nan suna bin addinin Islama. An dade ana amfani da dokokin Sharia a cikin abubuwan da suka shafi aure, saki da gado. Mutum zai iya ganin mata sanye da abin da suke so idan ka je gidan motsa jiki, za ka ga wata da mayafi da wata sanye da rigar wasanni. Ba mu da jami'an wanzar da shari'ar musulunci da za su hukunta mutane. ''Cikar burina'' Idan aka zo ga batun gado, 'yan'uwan mace maza kan samu ninkin abin da mata suke samu, kamar yadda Sharia ta tanada. Amma a cikin ƙasarmu, yawancin mutane kamar kakannina sun bar wasiyya a kan hakan. Ba na yin sallah sau biyar a rana kamar yadda addini ya umarce ni amma ina yin iya gwargwadon iko. Lokacin da nake ƙarama iyayena tsayayyu ne a kan addini. Na taba samun kaina a wani lokaci da bana yin sallah ko kadan. Na samu lasisin tukin jirgin sama a lokacin da nake karatu, a can na hadu da saurayina, shi daga arewacin Jamus yake. Na gaya masa tun farkon dangantakarmu cewa ni mai addini ce kuma ina so iyalina su kasance kan tsarin Musulunci. Ya mutunta burina kuma ya musulunta. Za mu yi aure nan ba da jimawa ba. Wasu malaman addinin musulunci na ganin bai kamata namiji da mace da ba addininsu daya ba su kasance tare, amma ina matukar jin cewa mutane biyu da ke son sadaukar da kansu ga aure su san juna kafin su yarda su ci gaba da rayuwarsu tare. ''Wani bangare ne na imaninmu. Na san abin da ke dai-dai ko abin da ba dai-dai ba bisa ga addini. Na kuma san abin da ke dai-dai da abin da ba dai-dai ba a gare ni. Ba na sanya mayafi. Wasu ma na iya cewa ni ba Musulmar kirki ba ce. Amma a wurina, tsakanina da Allah ne, kuma idan Allah yana ganin shi ya san komai. Neman ilimi da sabbin dabarun tafiyar da addini shine babbar darajar Musulunci. Ban san daga ina wannan masu ra'ayin hana mata neman ilimi suka samu wannan ra'ayi nasu ba. A wurina wannan bai sabawa Musulunci ba. Ina ƙoƙari in zama musulma ta gari a kowanne lokaci. Ni daliba ce mai shekaru 19, ina karantar ilimin tattalin arziki kuma ina aiki a matsayin sakatariya ga wani babban jami'i, in ji Nasyiratudina daga Indonesia. A lokacin hutuna ina koyarwa a wata makarantar yara. An haife ni kuma na girma a Aceh Besar, Indonesiya ce ta fi yawan musulmai a duniya, amma lardin Aceh ne kawai ke ƙarƙashin Sharia. Ina yin sallah sau biyar a rana. A gare ni, shari'a wani bangare ne na ban gaskiyarmu. Na yarda da duk sharuddanta. Ina sanya da dogayen riguna da gyale amma ba na rufe fuskata. A nan mata ba za su iya sanya karamar riga ko gajeren wando. Zan iya zama mai zaman kaina idan ina so. A jami'a, yara maza da mata suna karatu tare a aji ɗaya amma suna zama daban daban. Babu haramcin mu'amala da samari. Ina magana da su amma ba su da yawa. Wasu abokaina suna soyayya. Yana da kyau a kasance cikin soyayya. Samari da 'yan mata marasa aure ba sa iya fita biyu -biyu ko nuna soyayya ga junansu a bainar jama'a. Yawancin mata ba sa kusantar jukkunan junansu saboda an hana a addininmu. Samari da 'yan mata na iya fita waje tare in ana da yawa, muna hutawa a manyan kantuna, da gidajen cin abinci. Ba mu da dakunan sinima a nan, amma ina kallon Ina kallon fina-finai a talabijin kuma ina amfani da shafukan sada zumunta. ina son kida, don har na taba shiga wata gasar mawaka ma, inda na samu nasara na lashe ta. A Musulunci, mutum na iya aurar mata hudu. Amma, ba zan zama matar kowa ta biyu ko ta uku ko ta huɗu ba, ba zan iya zama haka ba. Kowace mace ta cancanci mijin kanta. Ina so in zama 'yar kasuwa, sannan in bude makarantar koyar da yara. Ina tausaya wa matan Afghanistan. Ina fatan zan rayu tsawon lokaci don ganin dukkan mata da yaran Falasdinu, da Afganistan, da Siriya, da Iran sun farka don kwatar wa kansu 'yanci." https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-58435990 +religion Ku San Malamanku tare da Sheik Hassan Abubakar Dikko "Ku latsa hoton da ke sama don kallon hirar BBC da Sheik Hassan Abubakar Dikko a shirin Ku San Malamanku, sannan kuna iya shiga shafinmu na Youtube don kallon cikakken bidiyon: Sheik Hassan Abubakar Dikko, fitaccen malami na kungiyar Jama'atu Izalatul Bidi'a wa ikamatus-sunna, ya ce ba zai iya bai wa wanda ba akidarmu daya ba auren 'yarsa. A hirarsa da BBCa cikin filinmu na Ku San Malamanku, malamin ya bayyana tarihin rayuwarsa da irin gwagwarmayarsa ta karatun addini da rayuwa. Ya ce shi cikakken dan kungiyar da aka fi sani da Izala ce assasawar Sheik Ibrahim Zakariyya wacce take a garin Jos, karkashin Sheik Sani Yahaya Jingir. Yana rike da mukamin shugaban majalisar malamai na jihar Filato na kungiyar. An haifi Sheik Hassan Abubakar Dikko a jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya, kuma ya taso ne a gaban kakansa wani shahararren malamin addinin Musulunci Idris Zakariyya, wanda shi ya tarbiyantar da shi. Ya bayyana cewa daga nan sai kawunsa mai suna Isma'ila Idris ya dauke shi zuwa garin Kaduna inda ya ci gaba da zama a gabansa har lokacin da Allah ya kaddari ya bar aiki daga kungiyar Jama'atul Nasril Islam ya shiga aikin soja. Malamin ya ce daga nan ne ya samu hanyar da zai ci gaba da rayuwa da gwagwarmayar neman karatu a gaban malamai. ""Na zauna a gaban Sheik Abubakar Mahmud Gumi na yi karatu gwargwadon hali, daga nan na samu damar zuwa makarantar koyon harshen Larabci ta Kano (SAS),"" in ji shi. Ya kuma ce bayan kammala karatun nasa a makarantar ta (SAS) Kano, ya sake dawowa garin Kaduna inda ya kama aikin gwamnati na koyarwa a makarantar firamare har ya kai matsayin shugaban makaranta (hedimaster). Sheik Dikko ya kara da cewa a wannan lokacin ne kawun nasa wanda ya shiga aikin soja wato Sheik Isma'ila Idris ya koma birnin Jos ya bar aikin soja, inda ya kafa kungiyar Jama'atu Izalatul Bidi'a wa Ikamatus Sunna. ""Wa'azi ya kankama sai ya bude makarantar ilmin addinin Islama mai zurfi, daga nan ya nemi in dawo garin Jos na zauna tare da shi domin ci gaba da karantarwa a makarantar. Dawowa Jos ta ba ni damar ina koyarwa na shiga jami'a, na yi digirina na farko, amma digirina na biyu na yi shi ne a fannin addinin Musulunci da harshen Larabci,"" in ji malamin. Sheik Hassan Dikko ya ci gaba da aikin koyarwa, inda daga bisani ya shiga aikin gwamnati a siyasance a jihar Bauchi zamanin mulkin Ahmed Adamu Mu'azu. A cewarsa: ""Bayan mun kammala shekara takwas da shi na yi shekara biyu da Malam Isa Yuguda wanda ya gaje shi, sai na sake komawa jami'a don nazarin digiri na uku a Jami'ar jihar Nassarawa a cikin garin Keffi."" Gwagwarmayar kungiyar Izala Malamin ya kuma bayyana wa BBC irin kalubale da kuma gwagwarmayar da suka sha a makaranta shi da wasu daga cikin daliban da ke da akidar Izala, ganin cewa ba ta samu karbuwa a garin Kano ba. Ya ce: ""An yi gwagawrmaya wacce ta ke ba karama ba. Lokacin da aka kafa ta ina makaranta a Kano kuma ina tare da akidarta, amma da yake lokacin ga yadda Kano take, boye akidarmu muke yi, ba ma iya bayyana ga inda muke, don haka idan ana magana a aji sai mu yi gum da bakinmu amma kuma duk da haka bai hana a gano mu ba."" Sheik Dikko ya ce: ""Allah da ikonsa daga baya wadanda suka zamanto suke fada da Izala su ne aka wayi gari su ne shuwagabanni, su ne jagorori, malaman da suke sukan Izalar aka wayi gari suke wa'azi."" Ba zan iya bai wa wanda ba mai irin akidata 'yata ya aura ba Sheik Hassan Abubakar Dikko ya shaida wa BBC cewa ba zai iya bayar da auren 'yarsa ga wanda ba akidarsu ta addini daya ba a bisa wasu dalilai da ya bayyana. ""Idan wani wanda yake da akidata da ta shi ba daya ba, ya zo yana neman auren 'yata ba zan iya ba shi ba, saboda ban amince da shi ba, saboda haka ba zan dauki jinina in ba shi ba, don ban san me za su haifa ba,"" in ji malamin. Da yake an ce rai dangin goro ne, malamin ya karkare hirar tasa da BBC yana mai cewa a lokacin da ba ya karatu ba ya wani aiki, babban abin da yake yi ya sanya shi nishadi shi ne ya zauna ya rika tuna wuraren da suka je suka yi da'awa, da adadin mutanen da suka musulunta ko kuma mutanen da suka fahimci gaskiya. ""Idan ba na karatu ba na aiki ba na komai sai kwakwalwata ta rika tuno min da mutanen alkhairi wadanda fahimtarmu ta zo daya, idan ba na karatu ba na aiki sai in rika tuna mutanen da Allah ya ciyar da su gaba ta fuskar ilimi ko ta fuskar dukiya amma a halin yanzu suna taimakon addini, in ji shi. Kana ya ce babban burinsa shi ne ya cika da kalmar shahada." https://www.bbc.com/hausa/labarai-56024864 +religion El-Zakzaky : IMN ta mayar wa El-Rufa'i martani A Najeriya, 'yan kungiyar IMN ta mazhabar Shi'a ta mayar da martani ga gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa'i. Wannan na zuwa bayan da ta zargi gwamnan da yin kalaman cewa Shugaban kungiyar Sheikh Ibrahim Elzakzaky ba zai taba fita daga gidan yari ba matsawar yana mulkin jahar. A cewar Ibrahim Musa, kakakin kungiyar a Najeriya, El-Rufa'i ya yi kalamin ne a hira da wani gidan rediyo a ranar Juma'a. Ibrahim Musa ya ce ga alama gwamnan na da wani dalili na kashin kansa na ci gaba da tsare jagoransu Sheikh Ibrahim El-Zakzaky. Ya kuma kara da cewa kotu ta ba da umarnin sakin El-Zakzaky tun a shekarar 2016 amma gwamnati ta ci gaba da tsare shi babu gaira babu dalili. Masu fafutukar kare hakkin dan Adam na yawan sukar gwamnati kan ci gaba da tsare Sheikh Ibrahim El-zakzaky, suna cewa gwamnatin ba ta mutunta umurnin kotu kuma tana karan tsaye ga dokokin kasar. Rikici tsakanin 'ya'yan 'kungiyar da hukumomin tsaro a Najeriya ya yi sanadiyyar mutuwar daruruwan musamman yan kungiyar ta IMN. https://www.bbc.com/hausa/labarai-51086787 +religion Ku San Malamanku tare da Sheikh Abubakar Mohammed Sodangi Gusau "Ku latsa hoton da ke sama don kallon hirar BBC da Sheikh Abubakar Mohammed Sodangi a shirin Ku San Malamanku, sannan kuna iya shiga shafinmu na Youtube don kallon cikakken bidiyon: Fitaccen malamin addinin Musulunci na Najeriya Sheikh Abubakar Mohammed Sodangi ya ce ya kwadaitu da neman ilimi ne tun yana karamin yaro saboda da ma gidansu gida ne na malamai. Ya bayyana haka ne a shirinmu na Ku San Malamanku. Malamin ya bayyana cewa da yake gidansu gida ne da ke da tarihi mai tsawo na ilimi don haka ya tashi ya yi karatu a gaban mahaifinsa Sheik Muhammadu Sodangi wanda ya yi musu tarbiyya a kan neman ilimi da kuma yin aiki da shi gwargwadon hali. Ya ce ""don haka na yi karatun Alkur'ani mai girma a hannun mahaifinmu har na yi nisa cikinsa inda daga baya ya mika mu a hannun kawunmu Malam Aliyu Abdullahi ya ci gaba da karantar da mu har muka sauke Alkur'ani."" Malamin, wanda aka haifa ranar sha18 ga watan Agustar shekarar 1960 a garin Gusau, babban birnin jihar Zamfara, inda kuma a nan ne ya tashi, ya ce yana da dangantaka da mujaddadi Usmanu. ''Akwai dangantaka ta jini da kakanmu na biyar da Sheik Usman Dan Fodio da malamansu da suka karantar da su, don haka kakan namu na daga cikin mukarraban Shehu Usman Dan Fodio,'' in ji malamin. Fafutikar neman ilimi. Bayan saukar karatun ne, in ji malamin, mahaifinsu ya dawo gida don zaman na din-din-din daga tafiye-tafiye zuwa garuruwa don karantarwa, sai ya ci gaba da karantar da su litattafan addinin musulunci. Daga bisani kuma mahaifin nasu ya kai shi cikin makarantar da suke karatu na litattafai wato makarantar zaure inda malamai manyan dattawa ke karatu. Ya yi karatu a makarantar malam Sulaiman Kofar Jangeme Yara da kuma makarantar malam Muhammadu Narke Sarki inda ya kasance mafi kankantar shekaru a makarantun a wancan lokacin. A cewar malamin, ""Ni kadai ne mai kananan shekaru cikin iyaye da kakanni, kuma na yi saurin haddace litatafai irin su risala, da su hadisai da sauransu saboda idan na dawo gida na kan rika maimaitawa. ""Sai mahaifina ya ce min ka ga shi ya sa na kai ka can cikin manyan malamai ka zauna ka rika karatu."" Bayan da Sheikh Abubakar Mohammed Sodangi ya ci gaba da karatun ne a garin na Gusau kuma mahaifin nasa ya dauke su shi da wasu abokansa zuwa wata makaranta da ya yi karatu a garin Zaria jihar Kaduna inda wani shahararren malamin addinin musulunci Malam Muhammadu Inuwa yake karantarwa. A garin na Zaria ne malamin ya ci gaba da karatu kuma daga bisani ya sake dawowa gida inda mahaifin na su ya kafa makaranta bayan da ya daina yawon karatun, kuma ya ci gaba da tsaron bangaren yara na makarantar a yayin da shi kuma yake bangaren masu karatun litattafai. 'Kundin Malamaina' Malamin ya kuma bayyana cewa ya yi karatu a hannun malamai da dama wanda ya rubutu sunayensu duka a wani kundi ya yi wa lakabi da Malamai na. ""Cikin su akwai Malam Muhammadu Sodangi wato mahaifina, da 'yanuwanshi su malam Aliyu, da malam Abubakar Kwaire, da Faruk Abdullahi, sai malam Isa Shuwai limamin masallacin Tudun Wada, wanda na karanci tafsiri na nahawu a wajensa da kuma fannin kimiyyar taswiarar kasa wato Geography,"" in ji shi. Malamin da kuma ce ya samu dimbin ilimi na Hadisai da Tafsiri da kuma luggar Larabci da Fiqihu, da Sarbu da ka'idojin rubuta ta tarbiyyar dalibi kan zamantakewa da sauransu dama a hannun sauran malaman. Ya kuma kara da cewa yana da wasu malamai da bai zauna karatu a wajen sub a amma ya yi amfani da litattafansu da kasidunsu da fatawowainsu da sakonninsu dama wajen yada ilimi tun kafin bullowar shafukan sada zumunta. ""Mukan yi amfani da hanyoyi aikewa da wasiku wajen aikewa da kasidu ana aiko mana da litattafai zuwa kasashen Saudi Arabia, da Misra, sudan Libya Sudan da kuma Pakistan."" 'Mahaifina na cikin masu kyamar ilimin Boko' Duk da cewa mahaifin Sheik Abubakar Sodangi na cikin wadanda ke kyamar ilmin Boko amma ya bari dansa ya yi karatu sakamakon wasu dalilai. ""Mahaifina na cikin wadanda suke kyamar ilimin Boko wanda ba ya rasa nasaba da tun da su suke da Daular Usmaniyya kuma a gabansu aka yi yakin da aka kafa Daular lokacin kakana suna matasa sun san mutanen da suka yi shahada a wannan yakin. ""A gaban su Sarkin Musulmi Attahiru ya bar Sakkwato da ayari ana kuka ya tafi da tutar Musulunci ya ce ya yi hijira,"" in ji malamin. ""A gabansu Bature ya shigo ya tara al'ummar da suka rage wadanda suka ce ba zai yiwu a watse a bar Turawa a gari su mayar da mutane kafirai ba, a gaban su duk aka yi."" A cewar malamin, ""Ka ga shi ya sa ga suka yi wa 'ya'yansu tarbiyyar kyamar Bature, don haka duk abin da zai hada su da Bature ba sa son shi."" Amma kuma, kamar yadda malamin ya bayyana, dalilan da suka sa ya samu ilimin bokon daga baya cewa a lokacin da kawunsa ya aurar da babbar yayarsu ga wani dan Boko ba tare da mahaifinsa ya sani ba, kuma ita ta dauke shi riko inda daga nan ne ya fara karatu. ""Daga baya da aka sanar da shi ina karatun Boko sai ya ce a dawo da ni bai yarda na yi boko ba, amma kuma daga baya aka fahimtar da shi cewa sai an hada da ilimin zamani za a samu cimma nasarar taimakawa da kuma yada addinin musulunci cikin sauki,"" in ji shi. Ya kara da cewa: ""Gaskiya daga baya kuma mahifinmu ya ga amfanin abin, wanda shi ya sa na kara fadada karatuna na bokon."" 'Nikaya da langa' Da muka tambaye shi game da irin wasannin da ya yi lokacin yana matashi, Sheik Abubakar Sodangi ya ce buga kwallon kafa da langa da makamantansu sai dai ""yanzu babu wasan da nake kewa kamar na iyo [ninkaya]"". Game da abinci, malamin ya ce yana sha'awar cin tuwo da miya musamman da daddare ""amma na fi son wake da shinkafa da fura da nono."" Sheik Abubakar Sodangi ya ce yana da mata biyu da 'ya'ya maza da mata." https://www.bbc.com/hausa/labarai-58189729 +religion Bidiyon Ku San Malamanku tare da Sheikh Muhammad Abubakar Kacallah Bidiyon Ku San Malamanku tare da Sheikh Muhammad Abubakar Kacallah https://www.bbc.com/hausa/media-59602210 +religion Ba a fahimci kalamai na kan ma'aikatan lafiya ba - Sheikh Gadon Kaya "Malamin addinin Musulunci Sheikh Abdallah Usman Godon Kaya ya janye ikirarin da ya yi kan ma'aikatan lafiya na Najeriya cewa wasunsu na aikata masha'a yayin da suke aikin dare a asibitocin kasar. Cikin wani jawabi da ya yi da aka gani a wani bidiyo, malamin addinin Musuluncin ya zargi ma'aikatan lafiyan da mu'amular da ba ta dace ba, ciki har da zina da cin zarafin mata. Tun da farko jaridar intanet ta Sahelian Times ta ruwaito shehin malamin yana zargin ma'aikatan lafiya da aikata zina yayin wani shirin talabijin da aka haska a tashar talabijin ta Africa TV mai zaman kanta. Sai dai daga baya ta ce baya malamin ya janye kalaman nasa, bayan da ƙungiyar ma'aikatan jinyan ta ce kalaman nasa ɓata wa ƴaƴanta suna ne, tare da neman ya janye su. Ga abin da ya shaida wa BBC baya da aka tuntuɓe shi kan kalaman nasa. Ya gaya wa BBC cikin wani sakon murya da ya aika cewa ""Ban yi niyyar cutar da kowa ba, kuma ya kamata mutane su zama masu kyautata tunanin alheri."" Sheikh Gadon Kaya ya shaida wa BBC cewa wasu ma'aikatan lafiya ne suka fara tuntuɓarsa kan wannan lamarin da ke ci gaba da jan hankalin jama'a. ""Wasu ma'aikatan kiwon lafiya biyu, namiji da mace ne suka kira ni, muna karatu ne suka yi min fatawa, inda suka fadi matsalar da suke fuskanta ta haɗa mace da namiji, wani lokacin a cikin aiki na dare. ""Suka koka, kuma na yi bayani a matsayina na almajiri, mai nusantar da mutane akan aikata daidai."" Ya ce ya yi bayani ne cewa matukar hakan na faruwa ya kamata a gyara: ""Ya kamata a tsare mutunci matan nan da iyalanmu da 'ya'yanmu gaba ɗaya."" Sheikh Gadon Kaya ya ce bayan da kalaman nasa suka tayar da hankalin jama'a, musamman ma'ikatan lafiya, ya zauna da su, inda ya ce ""sun warware min dukkan abubuwan da suka shige min duhu kan wannan lamarin."" Ya ce ma'aikatan lafiyan sun ""yi gungu kuma sun ziyarce ni"". Ya kuma ce sun sanar da shi cewa labarin da ya yada babu ƙamshin gaskiya cikinsa, kuma ya ce ya hujjarsa ita ce ""wasu ma'aikatanku ne suka kira ni, suka tambaye ni a karatu kuma na bayar da jawabi, inda na ce a gyara"". ""Laifina shi ne na ce idan wannan abin yana faruwa, na ce a gyara."" Ya ce bayan da suka ""yi min bayani, kuma na yi musu bayani, mun fahimci juna. Sai na ce mu su 'ba ku fahimci maganganun da ake yadawa ne ba'."" Ya kuma yi karin bayani, inda yace dalilinsa na biyu na furta wadannan kalaman masu tayar da hankali shi ne domin yana cikin masu yin kira ga al'umma da a rungumi karatun kiwon lafiya domin saboda akwai bukatar su cikin al'ummar kasar. Shehin ya ce bayanan da ma'aikatan lafiya suka yi kan batun, ya ƙaru da wasu abubuwan da a baya bai sani ba. Sai dai ya kare kansa inda ya ce bai ambaci sunan inda matar da ta yi masa tambayar ta fito ba. ""Ban san daga wace jiha tambayar ta fito ba kuma ban ambaci sunan wata jiha ba, ballantana wasu suce da su nake wannan maganar."" Tun da farko shugaban ƙungiyar ma'aikatan lafiya na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Maikarfi Muhamad ya mayar da martani bayan da kalaman na Sheikh Gadon Gaya suka bayyana. Yayin wata hira da ya yi da mujallar Jarida Radio ta intanet, ya yi kira ga malamin addinin Islaman da ya gaggauta janye kalaman nasa, wanda ya ce na ɓatanci ne. ""Cikin maganganunsa yana cewa ma'aikatan lafiya suna kwana a daki daya, har yana hasashe cewa wani mummunan abu yana faruwa tsakaninsu, inda ya kawo misalin wata mata mai shekara 50 da haihuwa kuma ya yi kwatanci kan wasu matasa 'yan matan da shekarunsu ba su kai 30 ba cewa suna kwana a daki daya, a bisa teburi daya a wurin da suke aiki na kwana."" Kwamared Muhammad ya yi kira ga ma'aikatan lafiya da su kwantar da hankalinsu kan munanan kalaman da Sheikh Gadon Kaya ya yi amfani da su, wadanda ya ce suna iya ɓata musu suna. ""Muna gaggauta jan hankalin wannan malami da ya yi hanzarin janye wadannan kalaman da ya furta ya kuma ba ma'aikatanmu da al'ummar jihar Kano hakuri."" Shugaban kungiyar ma'aikatan lafiyan ya ce kalaman na iya tayar da hankalin magidantan da matansu ke tafiya aikin asibiti da dare. Ya kammala jawabin nasa da yin kira ga malamin addinin da ya gaggauta janye kalaman ko kuma su dauki matakin shari'a a kansa. Wannan batu dai ya jawo ce-ce-ku-ce sosai a Najeriya musamman daga masu amfani da shafukan sada zumunta. Mutane da dama na tsokaci da batun masu iya magana da ke cewa: ""Iya ruwa fid da kai,"" kuma ""Baki shi kan yanka wuya"". Wadannan karin maganar biyu sun shafi kowane fanni na zamantakewa da na rayuwar al'umma, musamman ma a bangaren da ya shafi addini. Malaman addinin a Najeriya na da karfin fada a ji, musamman ganin yadda 'yan kasar ke bin dukkan kalaman da suke furtawa sau da kafa. Lamarin bai tsaya kan malaman addinin Musulunci ko na Kirista ba, domin dukkan mabiya manyan addinan biyu na wa malamansu biyayya. Wannan ne yasa dukkan abin da suka fada ke jan hankulan jama'arsu sosai kuma kalaman ke yin tasiri kan yadda mabiyansu ke kallon batutuwan da malaman ke yin tsokaci akai. Wannan takaddamar da ke tsakanin Sheikh Abdallah Gadon Kaya da ma'aikatan kiwon lafiya misali ne na irin wadannan batutuwan da ya dace malamai su rika yin tsantseni akai gabanin bayyana wata matsaya, kuma ba wannan ne karo na farko da kalaman nasa ke tayar da hankulan al'ummar da yake ikirarin nusantarwa daga aikata laifuka ba. Idan ba a manta ba, a bara Sheikh Abdallah Gadon Kaya ya taba furta kalaman da wasu ke kallo a matsayin na ɓatanci, kuma wadanda ka iya taɓa mutuncin babban limamin masallanci kasa da ke Abuja, wato Sheikh Ibrahim Maqari. Sai dai rahotanni sun ce an shiga tsakani kafin aka kashe wutar rikicin da ta rika ruruwa bayan da kalaman Sheikh Gadon Kaya suka bayyana, inda daga baya Sheikh Gadon Kayan ya nemi afuwa daga Sheikh Maqari, amma sai bayan da ya shigar da ƙara a kotu a watan Agustan 2021. Kuma da alama, kamar sauran al'umma, malaman addinai ma na amfani da kafofin sada zumunta wajen yaɗa ra'ayinsu kan batutuwan da suka shafi rayukan 'yan kasa. Sauƙin hawa wannan mumbari na intanet ko na sada zumunta ya haifar da dubban masana kan kowane fanni na rayuwa, ciki har da na addinai. Sai dai a wasu lokutan, mutane da dama na ganin wasu malaman kan bayyana ra'ayinsu ne ba tare da sun yi cikakken bincike ba, kuma wasunsu ba sa tauna tasirin kalamansu kan al'umomin da suke yi wa jagoranci ta bangaren addini. Wannan ne yasa masu sharhi ke ganin yake da muhimmanci jagororin al'umma - musamman ma malaman addinai - su rika cizawa kuma suna hurawa kafin su yi sharhi kan kowane batu." https://www.bbc.com/hausa/labarai-60286966 +religion Ku San Malamanku tare da Malam Adamu Girbo Muhammad "Latsa alamar lasifika da ke sama don kallon hira daMalam Girbo: An haifi Malam Adamu Girbo Muhammad a birnin Gombe da ke arewa maso gabashin Najeriya ranar 27 ga watan Disambar 1951. Ya yi karatun allo a birnin na Gombe a wurin malamai da dama da suka hada da Malam Usman da Malam Manu da Wazirin Ciroman Gombe da sauransu. Bayan ya kammala karatun Alkur'ani mai girma, Malam Girbo ya yi karatun litattafai a karkashin manyan Malamai irin su Sheikh Abubakar Mahmud Gumi da Sheikh Isma'ila Idris Zakariyya da Malam Balarabe. A shekarar 1968, malamin ya tafi Kaduna inda ya shiga sojan Najeriya domin fafatawa a Yakin Basasa. ""Da na shiga soja a garin Kaduna ina da sana'a a lokacin don na samu lasisi na tuka mota a 1967; da lasisin ya shekara daya na tafi Lagos inda a kan hanya ne na tsaya a Kaduna na shiga soja. Daga nan aka debe mu aka kai mu Enugu a jirgin kasa,"" in ji malamin. Ya kara da cewa da suka isa Enugu ne aka tambayi wadanda suka iya aikin kafinta ko tuki da wasu sana'o'i inda ya bayyana cewa shi direba ne, yana mai cewa daga nan ne aka dauke su aka koma da su Kaduna inda ya rika tuka tirela. Malam Girob ya ce yayin zamansa a Kaduna ne ya hadu da marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi da Sheikh Isma'ila Idris Zakariyya ""kuma su ne suka kwadaita mini karatu."" ""Kasancewa aikinmu yana zuwa ne lokaci zuwa lokaci, sai ya zamana ina da dama na rika karatu irin na zaure, shi ya sa na je a gaban Sheikh Abubakar Mahmud Gumi,"" a cewar malamin. Ya kara da cewa bayan babban malamin ya fahimci irin basirar ne ya samar masa gurbi a Kwalejin Koyar da Larabci da Addinin Musulunci da ke Katsina sannan ya sa aka mayar da shi fannin limamai daga bangaren direbobi. Malamin ya ce ya kammala karatunsa na shekara hudu ne a daidai lokacin da ake shirin kafa kungiyar Izala, kuma yana daya daga cikin wadanda suka kafa ta. Malam Girbo ya ce ya gudanar da wa'azuzzuka a rundunonin sojoji daban-daban a fadin Najeriya, ciki har da a Calabar. Shi ne shugaban kwamitin masallatai na kasa a kungiyar Izala. Ya ce ya yiritaya daga aikin soja a 2005 bayan ya kai mukamin Laftanar Kanar kuma ya kwashe shekaru talatin da biyar yana aiki. Malamin ya ce babu surar da yake jin dadin karantata kamar Suratul Rahman, yana mai cewa Suratul As-Saf ta fi ba shi wahalar karantawa. Malam Girbo ya ce yana matukar sha'awar dan-wake da dumamen tuwo da shinkafa da mai da yaji." https://www.bbc.com/hausa/labarai-60783242 +religion Abdulrahman Muhammad Auwal: 'Wasiyyar da mahaifina Sheikh Albaniy ya bar mana' "Latsa hoton da ke sama domin kallon hira da Abdulrahman Muhammad Auwal: Babban dan fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, marigayi Sheikh Muhammad Auwal Albaniy, ya ce babbar wasiyyar da mahaifinsu ya yi wa iyalansa ita ce su mayar da hankali wajen neman ilimi. A wata hira ta musamman da BBC Hausa yayin da ake cika shekara takwas da kisan malamin, Abdulrahman Muhammad Auwal wanda aka fi sani da Abu Huraira, ya ce rayuwarsu ta ""kasance cike da kalubale na rashin mahaifinmu"". ""Abubuwan da na fi tunawa [game da shi] su ne kiran da yake yi mu mayar da hankali wajen karatu. ""Ina yawan tuna wadannan kalmomi musamman inda yake cewa ba mu da gatan da ya wuce mu yi karatu; kuma Alhamdulillahi, daidai bakin gwargwado muna kan yi, muna yi kuma,"" in ji Abu Huraira. Ya kara da cewa abin da yake yi musu dadi shi ne ganin irin abubuwan alherin da mahaifinsu ya bari na ilimi da dalibai da har yanzu suna koyar da abubuwan da suka koya daga gare shi. Abdulrahman Muhammad Auwal ya ce maganarsa ta karsher da mahafinsa ita ce lokacin da ya je wurinsa yin bankwana zai koma makaranta. ""Sati daya kafin rasuwarsa na je na same shi na ce masa gobe za mu koma makaranta, ya yi mini addu'o'i; daga nan ne kuma bayan mun rabu, washegari na koma makaranta ranar Asabar kawuna ya kira ni... ya ce ga abin da ya faru, an kashe malam. ""A lokacin na yi kokari na fito da tsakar dare na samu mota na dawo daga makaranta,"" a cewar Abu Huraira. A shekarar 2014 wasu mahara suka harbe malamin da iyalinsa lokacin da suke cikin mota suna kan hanyarsu ta komawa gida daga makaranta a birnin Zaria na jihar Kaduna. An bayyana cewa maharan suna cikin wata mota ne kuma bayan da suka harbe shi da iyalin nasa sai da suka sake janyo shi daga cikin motar suka kara harbinsa don su tabbatar ya mutu. Sai dai wasu rahotanni sun ce anan take ne uwargidan nasa ta rasu, amma malamin da dan nasa sai bayan an kai su asibitin Wusasa da ke garin na Zaria ne rai ya yi halinsa." https://www.bbc.com/hausa/labarai-60203087 +religion Ku San malamanku tare da Sheikh Muhammad Suru Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon hira da Sheikh Ahmad Kanoma: Fitaccen malamin addinin musuluncin nan na Najeriya Sheikh Muhammad Bin Abdalah Suru, ya ce wani mafarki da ya taɓa yi ne ya sa shi rungumar ɗariƙar Tijjaniyya duk da cewa mutane da dama sun ba shi shawarar ya karɓe ta. ''Karɓar ɗarikar Shehu Tijjani a garin Suleja na daga cikin ni'imar da ubangiji ya mini, domin akwai wata muƙabala da aka yi a kan ɗarika kuma Allah ya bani gagarumar nasara, to a wannan lokaci sai wani malami ya bani shawarar ya kamata in karɓi ɗariƙa, ya yi ta min nasiha amma ni ban amsa ba'' in ji shi. Ya ci gaba da cewa ''A wannan lokaci sai bayan na koma gida na yi wani mafarki, inda a ciki na gan shi mun je taro wani wuri, ba zan iya gane wurin ba, amma dai ga shi an saukar da mu wani sabon gida an gama sama da ƙasa, ba ɗakin da yake da shimfiɗa, kowa yana ta gudu yana kama ɗaki, sai nima na faɗa wani ɗaki da aka cika shi da shimfiɗa, sai nima na ce na samu nawa ɗakin, sai wasu suka shigo suka ce ai wannan ɗakin Shehu Ibrahim ne, sai na farka ranar Laraba wayewar garin ranar Alhamis wannan abun ya faru, a ranar ne kuma na karɓi wuridin Shehu Tijjani''. Ya ce tun daga wancan lokaci har zuwa yanzu yake yin ɗarika, kuma ya samu rabo iri-iri sakamakon wannan wuridi, domin babu wani malami da zai zauna a gabansa ba tare da Allah ya sanya shaƙuwa a tsakaninsu ba. Tarihin rayuwarsa Malamin ya ce ainihin sunansa shi ne Muhammad Bin Abdullahi, babban limamin masallacin tunawa da Alhaji Muhammadu Sanusi Ɗantata da ke tsakiyar babban birnin Najerya Abuja. An haife shi ne a garin Suru, a wancan lokaci jihar Sokoto, a shekara ta 1381 bayan Hijira, dai-dai da shekarar 1962 Miladiyya. Ya ce ya tashi ne a hannun ƙanin mahaifinsa wanda shi ma babban malami ne, kuma ya yi makarantu da dama, kama daga kan wacce ya yi a garin Gafadi, inda ya yi saukar alƙur'ani. Ya ce ya shafe shekara biyu tare da shi yana karatu da neman na kai, kafin daga bisani haɗarin mota ya rutsa da su, a lokacin ne ƙanin mahaifin nasa ya rasu. Ya ce daga nan ya koma hannun wasu malamai daban-daban har zuwa lokacin da ya fara fita garuruwa irin su Sokoo, inda ya karanci Ƙawa'idi da Fiƙihu da su Ishmawi da Izziyya da Askari da dai sauransu. Kana a ɓangaren Lugga ma ya karanci manyan littattafai irinsu Zuhudu, da Badamasi da Albudda da Ishiriniyya da Muƙamatul Hariri a wajen malamai daban-daban, har zuwa lokacin Shagari, inda ya koma Suleja da sunan kasuwanci. ''A nan Suleja ɗin ne inda nake kasuwanci nake zuwa masallacin malamina limamin Malam Isyaku Turaki, limamin masallacin Juma'a na Turaki, wanda shine malamin da ya nemi in shiga Tijjaniyya ya nemi in dawo da iyalina nan, ya bani gidan da zan zauna''. in ji shi. Abun da ba zai manta da shi ba A cewar malamin babban abun baƙin cikin da ya same shi shine lokacin da ya samu labarin rasuwar Khalifa Shehu Tijjani Inyass. ''A lokacin har ina tunanin idan Shehu ba ya duniya idan na je Kaulaha na san ba ya duniya wani hali zan samu kaina ?, ko kuma in je kabarinsa in san cewa shine nan, wani irin yanayi zan samu kaina ?'' ''Har ina faɗa idan na je taro a baya cewa idan Allah ya kawo ajalin Shehu ni ya ɗauki rayuwata a ƙyale ta shi, domin shi ya fini amfani ga jama'a, sannan idan ni na tafi zai yi mun addu'a'' in ji Sheikh Muhamad Suru. Surar da ta fi ba shi wahala Malamin ya ce surar da ya jima yana shan wahala kafin ya iya ta ita ce Walfajir, domin ya shafe tsawon lokaci yana ƙoƙarin ya ga ya haddace ta. ''To amma daga baya sai ya zamana kullum ina karantata a Sallah har yanzu da yake Allah ya sauƙaƙe abun, ta ba ni wahala sosai. Iyali da buri Ya ce yana da ƴaƴa 2 da jikoki da dama, domin dama ya jima yana roƙon ubangiji ya ba shi ƴaƴa da yawa. Ya ce babban burinsa a yanzu shine Allah ya ba shi ikon gina katafariyar makaranta ta zama markazi, inda ko an ba da hutu za a samu ɗalibai masu ɗumin zuwa da za su rika karatu a cikinta''. Burina shine kullum a riƙa koyar da ɗalibai ilimin addini da sauran darussa da suka shafi addini a cikinta'' in ji malamin. https://www.bbc.com/hausa/labarai-60164737 +religion Mace mai ƙwallon kwando da ke sauya tunanin mutane a kan mata Musulmai Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon: Miliyoyin mutane ne suke kallon bidiyon da Jamad Fiin ke yi na wasan ƙwallon kwando. Kwalejin wasan ƙwallon kwando da ke Boston a Amurka, tana amfani da wasannin matar don ƙarfafa wa matasa gwiwa. Jamad Musulma ce kuma wasan kwandon da take yi ya ja hankalin mutane da dama a faɗin duniya da sanya wa su sauya tunaninsu a kan irin kallon da a baya suke yi wa mata Musulmai. https://www.bbc.com/hausa/media-59081627 +religion Ku San Malamanku tare da Malam Aliyu Hammari Walama An haifi Malam Aliyu Hammari a cikin garin Gombe a watan Satumba 1984, a nan kuma jihar ya fara karatun addinin musulunci a wajen kakansa Sarkin Malamai Abubakar Baffa wanda ya dade da rasuwa, nan ya yi karatun Al-Kur'ani da wasu littafan Fiqhu. A hannun kakan nasa ya yi karatun littafan Kawa'idi da Ahlari kamar matakin nazire kenan, daga nan aka kai su makarantar da 'ya'yan kowa ke zuwa, wato makarantar Alhaji Umaru Tudun Wada da ke cikin garin Gombe, wajen Alaramma Yakubu Bara a nan suka sauke Al-Kur'ani mai tsarki. Daga nan shi ma ya ce ya kamata su matsa wata makarantar da ta fi wadda yake koyar da su, ya ba su zabin makarantu guda uku; Daga bisani aka daidaita kan su tafi makarantar Malam Abu Waile Kole, a hannunsa ya yi kashi 70 cikin 100 na littafa addini, wasu karance-karancen na da'awa da wa'azi a wajen Malam Muhammadu Basakkwace ya yi. Bangaren Tafsir wajen Murshid Usman Baba Liman da Malam Dahiru Isa Bolari. A bangaren karatun boko ya yi karatun firamaren a makarantar Karangara a cikin Gombe da karamar sakandare makarantar Pilot, sai babbar sakandare da ya yi a makarantar kimiyya da fasaha ta Gombe, sai ya yi Difloma a makarantar Legal inda ya karanci fannin Shari'a, daga nan jami'ar Maiduguri ya karanta Shari'a and Public Law, sai makarantar koyon aikin Lauya a Yola da ke jihar Adamawa. A shekarar 2019 aka tabbatar da shi a matsayin Lauya, ya sake komawa jami'ar Maiduguri inda ya ke yin digiri na biyu duk dai a fannin shari'a. Malam Aliyu ya ce baya ga kasar Saudiyya ya na fatan kai ziyara wasu kasashen da suka shafi aikin lauyanci, saboda ana amfani da dokokin Birtaniya, don haka burinsa ya je kasar Birtaniya inda zai gano ainahin tushen inda aka kafa dokokin da ake amfani Najeriya. Malamin ya ce ya sha wuya a bangaren karatun Alkurani saboda hadda ake son yi, shi kuma ba inda ya ba shi wuya kenan. ''Akwai bambanci sosai da koyarwar lokacinmu, domin mun sha bulala idan muka gagara ba da hadda amma duk da hakan, Alhamdulillah saboda mun yi karatu mai inganci. Sai kuma lokacin da muna makarantar koyon aikin Lauya, akwai abin da ake kira Presentaion, wato tsayawa gaban mutane ka yi bayani a kan wani maudu'i da aka bukaci ku yi bincike a kai, nan ma na sha wuya domin kusan kullum sai an yi. Lokacin da aka sanar da cewa na tsallake wannan siradin ba karamin farin ciki na yi ba,'' in ji Malamin. Malam Aliyu Hammari ya ce ya na jin dadin karanta Suratu Maryam, har ta kai ya na yawan karatanta a matsayin karatun sallah, sannan ta dauki hankalinsa saboda tattaro addinai guda biyu, wato addinin Musulunci da na Kirista. https://www.bbc.com/hausa/labarai-61337113 +religion Harin Masallaci a Christchurch: Brenton Tarrant zai shafe rayuwarsa a kurkuku Wata kotu a New Zealand ta yanke hukuncin daurin rai da rai ga maharin da ya kashe musulmi masallata 51 yayin da suke ibada a Chrischurch. Alkalin kotun Cameron Mander, ya ce Brenton Tarrant, ya shirya sosai kafin kai harin kan wasu masallatai biyu. Ya ce zuciyar sa ta kekashe, kana bai nuna tausayi ko da na sanin abin da ya aikata ba. Wannan dai shine karo na farko da aka yanke hukuncin daurin rai da rai ba tare da bada wata dama ba a New Zealand. Kafin yake hukuncin dangin wadanda ya kashe sun bukaci kotu ta yi masa hukunci mafi tsanani. Firaministar New Zealand Jacinda Ardern, ta yi maraba da hukuncin da aka yankewa maharin da ya hallaka masallata a wasu masallatai a kasar, in da tace maharin ya cancanci ya karasa rayuwarsa a kurkuku, tana mai fatan daina sake jin duriyarsa har abadan abada. Ta kuma yabawa dangin wadanda suka mutu saboda hakurin da suka nuna tsawon lokaci har zuwa yanzu da aka yanke hukunci. An fara kai wa masallacin Al Noor mosque hari ne wanda yake tsakiyar birnin Christchurch. Wasu da suka shaida al'amarin sun ce sun rika gudu don neman tsira da rayuwarsu, a dai-dai lokacin da suka ga wasu mutane suna fitowa daga cikin masallacin jina-jina. https://www.bbc.com/hausa/labarai-53927667 +religion Ku San Malamanku tare da Sheikh Abdulwahab Abdallah "Ku latsa hoton da ke sama don kallon hirar BBC da Sheikh Abdulwahab Abdallah a shirin Ku San Malamanku, sannan kuna iya shiga shafinmu na Youtubedon kallon cikakken bidiyon: Fitaccen malamin addinin musuluncin nan da ke birnin Kano a Najeriya Sheikh Abdulwahab Abdallah ya ce surorin da ya fi son karantawa a cikin AlƘur'ani su ne suratul iklas da ihsan da kuma sajadah saboda yadda suke burge shi. Malamin ya bayyana hakan ne a hirarsa da BBC Hausa a shirinmu na musamman na Ku San Malamanku, inda ya ce hadisin da ya fi so shi ne wanda Manzon Allah ke cewa yana tare da mai sonsa ranar tashin alƙiyama. ""Wannan hadisin ko yaushe na wuce shi sai na gode wa Allah. Manzon Allah ba mu san shi ba amma a ranar tashin alƙiyama wanda yake son shi zai gan shi...wannan hadisin idan na karanta shi yana faranta min rai,"" in ji Sheikh Abdulwahab. Malamin ya ƙara da cewa ranar da ta fi sanya shi farin ciki a duniya ita ce lokacin da aka karɓe shi a Jami'atu Al-Islamiyya. Sai dai malamin ya ce: ""Amma babu abin da ke sanya ni baƙin ciki irin wanda ka amincewa ya je yana yi maka zangon-ƙasa."" Malamin na addinin musulunci ya ce babu garin da yake so bayan Madina da Makkah kamar Kano. ""Ina son Kano saboda gari ne wanda za ka iya isar da saƙon da kake so na ilimi da addini, kana wanda ba ka da shi za a taimake ka,"" in ji malamin. Ya ƙara da cewa akwai malamai da ɗaliban ilimi waɗanda suka waye a Kano yadda ko da mutum ya yi kuskure za su fahimtar da shi cikin hikima. An haife shi ranar 28 ga watan Agusta na shekarar 1953 a ƙasar Togo. Malamin, wanda ya ce shi Bawangare ne, ya tashi ne a hannun Limamin Waje da ke birnin Kano da ke arewacin Najeriya, Imam Umar. ""Wannan bawan Allah ko iyayena da suka haife shi ba su wahala da ni kamar shi ba,"" in ji shi. Ya soma karatu a wurin yayan mahaifinsa mai suna Imam Alhaji Yahya. Daga bisani ya yi karatu a wurin babban malami marigayi Imam Ɗan'ammu da ke birnin Kano. Galibin karatun da ya yi a wurinsa sun shafi Riyadus-salihin da kuma Hadisai. Kazalika ya ce ya yi karatu a wurin Sheikh Nasiru Kabara da Sheikh Shehu Maihula da Gida Shamsu inda akwai malamai irin su Malam Gali, da Malam Babba. Malamin ya ce daga nan ne ya tafi Saudiyya tare da matarsa inda ya yi karatu a can. Ya ce ya yi karatu a wurin Sheikh Bn Bazz da Sheikh Uthaimin, waɗanda ya ce ya koyi halaye na gari da matuƙar tsoron Allah a wurinsu. Sheikh Abdulwahab ya ce shi da Sheikh Ja'far Mahmud Adam sun yi karatu tare inda suka mayar da hankali a kansa matuƙa. ""Ni da malam Ja'far mun yi alƙawari ba mu yarda mu shiga hukuma ba; da safe karatu, da yamma karatu. Abubuwan da suke hannunmu shi Malam Ja'afar (Allah Ya jiƙan shi) yana da abokanansa da ya ba su wani abu suna juya masa, ni kuma ina da almajirai na ba su wani abu don ina Saudiyya...ina sayar da mayafai, kafin in zo ina da kuɗi a hannuna sai na bayar ana juyawa,"" a cewarsa. Malamin ya ce tun da ya tashi babu abincin da yake so kamar tuwo yana mai cewa ba ya iya yin kwana biyu bai ci shi ba. Shiekh Abdulwahab ya ce babu tambayoyin da aka fi yi masa kamar na ""zamantakewar aure, duk bala'in a nan yake."" A cewarsa: ""Jiya jiyan nan ina zaune da hankalina mutum ya zo ina yi musu sulhu a gabana ya daki matarsa."" Ya ce babu abin da ya fi sanya shi farin ciki kamar ya ga mutum ya Musulunta. Ya ƙara da cewa babban abin da yake baƙanta masa rai shi ne idan ""na ga ana fasadi."" Shiekh Abdulwahab ya ce lokacin yana matashi ya yi wasa irin wanda matasa suke yi kuma ya saurari waƙoƙin turawa irin na James Brown da na ƙabilar Igbo da na larabawa ""saboda waƙoƙi suna ɗaukar hankalin yaro."" Sai dai ya yi gargaɗi da matasa da kada su bari waƙoƙi su janye musu hankali ""domin suna maye gurbin karatu."" Amma malamin ya ce ba ya sha'awar ƙwallon ƙafa. Sheikh Abdulwahab yana da mata da ƴaƴa. Da yake burin kowanne musulmi shi ne ya gama da duniya lafiya, shi ma Sheikh Abdulwahab ya ce babban burinsa shi ne ""na cika da kalmar shahada.""" https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-55178197 +religion Ku San Malamanku tare da Sheikh Halliru Maraya "Wani fitaccen malamin addinin Musulunci a jihar Kadunan Najeriya ya ce shi ba ya siyasa, mutane na ganin kamar yana yi ne don kawai ya ta ba riƙe muƙami a gwamnatin farar hula shi ya sa ake ganin kamar shi ɗan siyasa ne. Malamin ya bayyana hakan ne a hirarsa da BBC Hausa a shirinmu na musamman na Ku San Malamanku, inda ya ce tsohon gwamnan Kaduna marigayi Patrick Yakowa ne ya naɗa shi mataimaki na musamman kan harkokin addini da aikin Hajji. ""Duk da cewa ni ba ɗan jam'iyyarsa ba ce ta PDP. Sannan sai da na sa masa sharuɗɗa sannan ya yarda da hakan. Malamin haifaffen Unguwar Tudun Wada ne a garin Kaduna, kuma an haife shi ne a watan Agustan 1969, sai dai yana da shekara biyu mahaifiyarsa ta rasu, dalilin da ya sa ya samo sunan maraya kenan. Ya fara karatun allo tun yana ɗan shekara bakwai, kuma a yanzu shi ne mai gudanarwa a Gidauniyar Zaman Lafiya Ta Duniya a arewacin Najeriya, wato Global Peace Foundation. Sheikh Maraya ya ce ya fi ƙwarewa a fannonin Fiƙihun Malikiyya da Luggar Larabci da ilimin Hadisi da ilimin Tafsiri da aka fi saninsa a kai. Ya ce malamansa da ya fi alfahari da su su ne kamar limamin Masallacin Tudun Wadan Kaduna Sheikh Abdulkarim Hashim da marigayi Malam Abubakar Tureta da marigayi Sheikh Lawal Ƙaura Zariya (wanda nake zuwa Zariya kullum tun daga Kaduna donɗaukar karatu a wajensa)." https://www.bbc.com/hausa/media-55094042 +religion Ku San Malamanku tare da Sheikh Karibullah Nasir Kabara "Fitaccen malamin addinin Musulunci a Najeriya Sheikh Karibullah Nasir Kabara kuma shugaban ɗariƙar Ƙadiriyya ta Afirka ya ce yana da gashin Annabin Allah Muhammad SAW a ajiye a wajensa. Malamin ya faɗi hakan ne a cikin shirin Ku San Malamanku na BBC Hausa, har ma kuma ya nuna wa Yusuf Ibrahim Yakasai gashin. Sheikh ya ce wannan abu shi ne wanda ya fi saka shi farin ciki a duniya fiye da komai. Kuma ya samu gashin ne daga wajen wani babban malami da ya kai masa ziyara Kano daga ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa. Sheikh Karibullah ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambaya kan abin da ya fi saka shi farin ciki a duniya inda ya ce hakan na da alaƙa ne da wani mafarki da ya ta ba yi a lokacin bai wuce shekara 10 ba a duniya. ""Na taɓa yin mafarki wani babban malami daga cikin malamanmu ya ba ni wuƙar zinare a hannun dama, sai wani babban malamin ya sake ba ni wata wuƙar, na kasa mantawa da mafarkin har sai da Allah Ya kawo wani lokaci shekara tara da suka wuce. ""Allah Ya kawo wani babban bawan Allah daga ƙasar UAE ana ce masa As-Sheikh Ahmadul Khadraji, wannan bawan Allah gidansu ya yi fice tuntuni suna gadon mallakar gashin Annabi SAW. ""Wato tun kakannin kakanninsa, saboda a zamanin Annabi SAW idan ya yi aski ya kan raba wa sahabbansa gashin nasa, wasu ya ba su da yawa wasu kaɗan. ""To gashin Manzon Allah kuma yana da wata hususiya da komai daɗewar da zai yi ba ya lalacewa ko sauya kama. Ko kwanaki na ji wani shiri da BBC ta yi kan wasu kayayyakin Manzon Allah SAW da aka samu a Turkiyya shekara 1442 amma ba abin da suka yi,"" in ji Malam. Ya ci gaba da cewa ""wannan mafarki da na yi sai Allah Ya kawo wannan mutumin da ya gaji gashin nan ya ba ni sili ɗaya da ya sako shi a wata ma'ajiya da aka yi da gwal wacce ta kai tsawon hannuna haka. Ɗaya silin kuma aka sa irin ɗaya ma'ajiyar amma ta azurfa fara. ""To sai ya sako gashin ɗaya a mai kalar gwal ɗaya a mai kalar azurfa ya zo wajen taron Maulidin Ƙadiriyya ya ba ni kyautarsa. ""To gaskiya na kasa manta wannan abu. Wannan wuƙaƙen da na yi amfarki an ba ni ashe su ne ma'ajiyoyin nan guda biyu da aka sako gashin Manzon Allah SAW aka ba ni,"" a cewar Sheikh Kabara. A ɓangaren abubuwan da Malam ya tsani gani kuwa ya ce ba su wuce biyu ba. ""Na farko na tsani na ga an saki layin da aka san matasan Musulmai a kai. Na biyu ba na jin daɗi idan na ga abubuwa na rashin daɗi suna faɗaɗa wanda kuma haƙƙi ne na hukuma amma ba a yi ƙoƙarin shawo kansu ba da za su iya jawo wa ƙasa koma baya."" Sheikh Karibullah Nasir Kabara haifaffen birnin Kano ne kuma ɗa ne ga marigayi Sheikh Nasir Kabara shugaban ɗariƙar Ƙadiriyya na Afirka Ta Yamma. Bayan rasuwar mahaifinsa sai ya gaje shi inda ya ɗare shugabancin ƙungiyar ta Ƙadriyya kusan shekara 25 kenan a yanzu. Ya fara karatu a gaban mahaifinsa a nan cikin unguwar Kabara sannan ya halarci makarantu da suka haɗa da ta Ma'ahadid Din ta mahaifinsa. Sannan ya yi makarantar addinin Musulunci ta Aliya a Shahuci, daga bisani kuma ya je Jami'ar Bayero da ke Kano inda ya karanta Arabiyya. Wace sura malam ya fi so a ƙur'ani? Al-Ƙur'ani dukkaninsa zinare ne amma Sheikh ya ce yana matuƙar son Suratu Yusufa saboda ta bayar da ilimi iri-iri, ""daga cikin abin da yake ba ni sha'awa da ita Allah Ya bayar da darasin da za a samu ilimi a kan dukkan wata rayuwa ta duniya. ""Na amfanu da yawa musamman a lokutan da na samu kaina a wannan nauyi da wannan amanar da Allah Ya ɗora min, da yawa abubuwan da suke faruwa ko na samu wata matsala ko damuwa to a ciki nake samun mafita."" Shugaban na ɗariƙar Ƙadiriyya a Afirka ya kuma ce ya rubuta litattafai da dama, musamman kan darikun sufaye a Najeriya, da kuma shigar musulunci yankin Najeriya darurwan shekaru gabanin zuwan Shehu Usmanu Dan Fodiyo. Malam ya ce shi bai samu lokacin yin wasanni na yara sosai ba a lokacin ƙuruciyarsa don ko yaushe yana tare da babansa, ""duk inda zai motsa tare muke tafiya tun daga lokacin da na kai shekara biyar."" Ya ƙara da cewa sai dai ɗan abin da ba a rasa ba a wasu lokuta da ba su da yawa. Kan batun abincin da ya fi so kuwa Sheikh ya ce yana matuƙar son shinkafa da dankalin Turawa da naman kaza da naman rago da tuffa da kuma rake. Sheikh Ƙaribullah ya je ƙasashe da dama, wasu tare da mahaifinsa wasu kuma shi kaɗai. ""A ƙasashen Larabawa Yemen ce kawai ƙasar da ban je ba. A sauran ƙasashen duniya kuwa nan gaba burina shi ne na je ƙasar Rasha."" Malam ya ce burinsa a nan gaba shi ne a kafa wani tsari a Najeriya na yadda za a tarbiyyantar da yara al'ummar Musulmai irin yadda addinin Musulunci yake a mataki sahihi. Sheikh yana da mata uku da ƴaƴa 19." https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-55263388 +religion Sheikh Abduljabbar: Ranar Lahadi za a yi muƙabala tsakanin malamin da malaman Kano "Gwamnatin Jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta tabbatar wa da BBC cewa ranar Lahadi, 7 ga watan Maris za a shirya muƙabala tsakanin Sheikh Abduljabbar Kabara da malaman Jihar. Kwamishinan Harkokin Addini Dr. Muhammad Tahar ne ya tabbatar wa da BBC saka ranar, inda ya ce za a gudanar da zaman da ƙarfe 9:00 na safiyar Lahadin. ""Ni a matsayina na kwamishina ni aka umarta da na kai wa Abduljabbar takarda, kuma na kai masa ita har gida, hannu da hannu har ma ya saka hannu na shaidar karɓa,"" a cewar Muhammad Tahar. Kwamishinan ya ce sauran malamai waɗanda suka rubuta takardar ƙorafi da murya ɗaya za su bayyana sunayen malaman da za su fafata da Abduljabbar zuwa ranar Laraba. Ya ƙara da cewa Farfesa Sani Zahradden, Babban Limamin Kano, da Farfesa Shehu Ahmad Galadanchi, Babban Limamin Abuja, su ne za su jagoranci muƙabalar wato alƙalai. Za a gudanar da muƙabalar ce a Fadar Sarkin Kano Aminu Ado Bayero. Yanzu haka gwamnatin Kano na tsare da Abduljabbar Nasiru Kabara, inda ake yi masa ɗaurin talala a gidansa. Gwamna Ganduje ya yarda a gudanar da taron muƙabalar ne biyo bayan kiran da Abduljabbar ya yi na cewa a yi masa adalci, a cewar sanarwar Muhammad Garba. Tun a ranar 7 ga Fabarairu ne Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya amince a yi taron kuma aka faɗa wa ɓangarorin biyu su shirya fuskantar juna a tattaunawar ilimi. Gwamnatin Kano ta zargi malamin ne da yin ""kalaman tayar da fitina game da addinin Musulunci"" bayan wasu malamai a jihar sun zarge shi da saɓa wa abin da Musulunci ya zo da shi. Wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai Muhammad Garba ya fitar ranar 7 ga Fabarairu ta bayyana yadda muƙabalar za ta gudana. ""An bai wa waɗanda za su fafata a muhawarar mako biyu domin su tattara bayanai da maudu'an da za su tattauna a kai,"" a cewar gwamnatin Kano. An amince cewa dukkanin ƙungiyoyin addini za su turo wakilansu yayin muƙabalar, sannan za a gayyaci wasu manyan malamai daga wajen Kano domin su shaida. Kazalika, Gwamna Ganduje ya yarda a yaɗa muhawarar kai-tsaye a gidajen rediyo na jihar da na ƙasashen waje. Gwamnan ya yi kira ga mazauna jihar da su kwantar da hankali a lokaci da kuma bayan muƙabalar." https://www.bbc.com/hausa/labarai-56228757 +religion Bidiyon Ku San Malamanku tare da Sheikh Ibrahim Disina Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon: Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na jihar Bauchi Sheikh Dokta Ibrahim Disina ya ce sabanin fahimta da na aƙida ba sa hana shi mu'amala da kowane irin musulmai. Dokta Disina ya ce tun da Allah bai hana shi mu'amala da wanda suke da saɓani a addini ba, to babu dalili da zai sa ya ƙi yin mu'amala da mabiyin dariƙun sufaye ko kuma wani da suke da saɓanin fahimta. Malamin ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da BBC a cikin shirin Ku San Malamanku. Ya ce yana alaƙa da duk wanda alaƙa ta kama a yi da shi a cikin dukkan bangarori. Sheikh Disina ya ce a cikin waɗanda yake hulɗa da su har da ƴan shi'a waɗanda suka taso tun suna yara, kuma har yanzu suna ci gaba da mu'amala. Sai dai ya ce alaƙar ba ta sa ya ɓoye aƙidarsa ko fahitarsa a kan wani abu da addini. https://www.bbc.com/hausa/labarai-56531268 +religion Ku San Malamanku tare da babban limamin Borno Sheikh Imam Laisu Ibrahim Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon: Babban limamin jihar Borno Sheikh Imam Laisu Ibrahim ya ce nuna ɓangaranci a tsarin shugabanci na daga cikin abubuwan da ke haifar da koma baya tsakanin kowacce al'umma. Imam Ibrahim, ya shaida hakan ne a lokacin wata tattanawa a cikin shirin Ku San Malamanku na BBC hausa. Ya ce bai kamata a ce shugaba na nuna bangaranci ko son rai ko zabinsa ba, akwai bukatar a tattauna a kan komai a ɗau matsaya guda. Shehin Malamin yana bayani ne kan dalilan da suka sa ba a yawan samun rikici tsakanin malaman Borno masu banbamcin aƙida. Limamin ya ce yana da nauyi sosai a gabanshi domin akwai dimbin malamai a karkashinsa, shi yasa yake kokarin hada kan darikoki da mutunta ra'ayoyi. https://www.bbc.com/hausa/media-58837770 +religion Sokoto: Zanga-zanga ta ɓarke kan kamen da 'yan sanda suka yi bayan kashe Deborah Samuel "Zanga-zanga ta ɓarke a garin Sokoto na arewacin Najeriya, inda matasa ke ci gaba da nuna ɓacin ransu kan kalaman ɓatanci da ya jawo kisan wata matashiyar ɗaliba mai suna Deborah Samuel. Masu zanga-zangar na neman jami'an tsaro su saki mutanen da suka kama da ake zargi da kisan matashiyar da ke karatu a Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari, wadda suka zarga da zagin Annabi Muhammadu (SAW). Matasan maza da mata suna aiwtar da zanga-zangar a wurare daban-daban a fadin Sokoto tare da ƙona tayoyi, da suka haɗa da Fadar Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar III. Kazalika wasu sun yi cincirundo a ƙofar gidan gwamnatin jihar. BBC ta nemi ji daga bakin rundunar 'yan sandan Sokoto amma ba su amsa kira ba. Gwamnatin jihar ta sanar da saka dokar hana fita ta tsawon awa 24 sakamakon zanga-zangar. Rahotannin da BBC ta samu sun nuna cewa da farko zanga-zangar ta lumana ce, daga bisani sai ta rikide ta zuwa tamkar rikici, inda mutane suka dinga jefa duwatsu kan gidan sarkin Musulmin. Wani da BBC ta zanta da shi da ke kusa da fadar sarkin a lokacin da abin ya faru ya ce jami'an tsaro sun yi ƙoƙarin dakatar da matasan kutsawa fadar. ""Da yawan yaran ['yan zanga-zanga] na ganin sarkin ya goyi bayan yarinyar [Deborah], shi ne suke jefe-jefe,"" in ji shi. Ya ƙara da cewa jami'an tsaro na 'yan sanda da soja na harba hayaƙi mai sa hawaye, har ma an harbi mutum biyu. Shi ma wani da muka ɓoye sunansa saboda dalilai na tsaro ya tabbatar da harbin mutum biyu, yana mai cewa har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton matasan na ci gaba da jifa, su kuma jami'an tsaro na harbi. Haka nan an kama mutane da yawa, a cewarsa. Sanarwar da 'yan sandan Sokoto suka fitar ranar Alhamis ta ce sun kama mutum biyu da ake zargi da kisan Deborah, Kirista 'yar aji 200 a Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari, Sarkin Musulmi da Shugaba Muhammadu Buhari sun yi tir da kisan, suna masu kira da a gudanar da cikakken bincike don hukunta waɗanda suka kashe ta. Wasu bidiyo da hotuna da suka karaɗe shafukan zumunta sun nuna yadda matasan suka yi wa matashiyar duka kuma suka ƙona gawarta. Lamarin na ci gaba da ta da muhawara musamman a shafukan zumunta na Najeriya." https://www.bbc.com/hausa/labarai-61449911 +religion Ku San Malamanku tare da Sheikh Adamu Muhammad Dokoro "Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon: An haifi Sheikh Adamu Muhammad Dokoro a Unguwar Bolari da ke garin Gombe a arewa maso gabashin Najeriya. Malamin ya ce ba shi da tabbaci a kan ranar haihuwarsa sai dai kwatance amma an rubuta masa cewa an haife shi ranar 15 ga watan Mayun 1964. Sheikh Dokoro bai girma a cikin gidansu ba, domin tun yana ɗan shekara uku zuwa huɗu sai aka kai shi makaranta ƙauye. Ya yi karatu a gaban malaminsa wato Malam Isma'il. Ya ce Malam Isma'il ya ga karatun ɗalibinsa Adamu Muhammad Allah ya sa albarka a ciki sakamakon cikin rukunin almajiran da ke a gabansa babu wanda ya samu fatahi da buɗi irinsa. Hakan ne ya sa Malam Isma'il ya dauke shi ya kai shi wajen wani alaramma wanda ake kira Malam Audu Mai Darasu, wanda ya kasance gangaran ne a lokacin. Sheikh Adamu ya ce ya samu karɓuwa a wajen malamin sosai wanda ko yankar farce za a yi wa Malam Audu, Sheikh Adamu ne ke yi masa inda sauran gardawa da malamai suna zaune domin babu wanda ya samu kusanci da shi kamar yadda ya samu. ""Na zauna a wannan tsangaya ɗin ta kai shekara kusan 15 ko ma 16, Allah ya bada karatun Al-Ƙur'ani kuma an yi shi kuma zan iya cewa kafin na bar wurin, mafi rinjaye a cikin kwana shida zan rubuta Al-Ƙur'ani a wannan lokaci domin duk rana idan na tashi zan iya rubuta izu goma,"" in ji Sheikh Adamu. Sheikh Adamu ya ce da ya dawo cikin garin Gombe, ya shiga wuraren harkar ilimi da yawa inda ya yi karance-karance iri daban-daban. Ya yi karatu a cikin garin Gombe a wurin Malam Sa'idu da Malam Adamu da wasu manya-manyan malamai da ya yi karatu a wajensu irin na zaure. A zaurukan da ya yi karatu a Gombe, ya sake tisa karatun Ƙawa'idi da Ahalari da Ishmawi da Iziya da Risalah da sauran litattafai. Ya ce ""malamin da na sauke tafsiri a wurinsa sau uku, ya kan naɗa ni ya ajiye ni ya ce idan ɗalibai sun zo na koya musu tafsirin Al-Ƙur'ani, shi ma na samu shekara sun kai biyar zuwa shida a ƙarƙashinsa"", in ji shi. Sheikh Adamu ya bayyana cewa babban abin farin cikin da ba zai manta da shi ba shi ne samun Al-Ƙur'ani da ya yi. Ya ce ba zai taɓa mantawa da wannan ba saboda babbar kyauta ce daga wajen Allah (S.W.A) Sheikh Adamu ya ce abin da ya fi faranta masa rai shi ne ya ga yaro yana ƙoƙarin abubuwa guda uku a cikin rayuwa, wato yana neman ilimi da riƙon addini da kuma ƙoƙarin sana'a. Malam ya ce babu abin da ya fi ba shi takaici irin kamar ganin matashi ya lalata rayuwarsa, wato ba ilimi ba addini kuma babu sana'a. ""Shi Al-Ƙur'ani ko ina idan ana karanta shi ana samun shauƙi, amma idan wani ne yake karatu, nake saurare, wato babu kamar Suratul Safat. Wato ayoyinta gajeru ne amma ina son ji daga wani yana karanta su,"" in ji Malam. Malam ya ce surar na saka shi nishaɗi amma duk da haka ita ma Suratul Waƙi'a yana jin daɗinta domin wasu lokutan yakan karanta surar a cikin sallolinsa Sheikh Adamu ya bayyana cewa tambayoyin da aka fi yi masa, tambayoyi ne da suka shafi zamantakewar aure ko mutuwar aure ko kuma yadda za a yi a gyara shi. ""Ni kaina na fi sha'awar na yi magana kan abin da zai gyara auratayyar mutane, idan na samu wannan gaɓar a cikin karatu ban cika barinta haka kawai ba saboda ina ganin idan al'umma aurenta ya yi kyau kuma ya zama cewa gidaje sun yi kyau toh al'umma ta samu dukkan abin da ya kamata kuma dukkan rayuwa za ta tafi ta zamo daidai,"" in ji shi. Malam ya ce bai cika cin abincin gargajiya ba irin su tuwo da sauransu inda ya ce yakan ɓata masa ciki ma. Malam ya ce abin da zai iya ci ko da ba daɗinsa zai ji ba kuma ba zai yi masa illa ba shi ne soyayyen dankalin Turawa da na Hausa. Ya ce duk wani abinci irin su shinkafa da tuwo har nama duk ba cinsu yake yi ba inda ya ce tun asali ma idan ya ci nama amai yake yi. Malam ya ce a halin yanzu matarsa guda ɗaya, kuma matarsa ta farko ta rasu sai ya auri wata. Malam ya ce yaransa sun kai guda goma, maza shida mata huɗu." https://www.bbc.com/hausa/labarai-60248087 +religion Ku San Malamanku Tare da Sheikh Aminu Abdullahi Yammawa Katsina "Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon: Shirin Ku San Malamanku na wannan mako ya tattauna ne da Sheikh Aminu Abdullahi Yammawa, wani malamin addinin Musulunci a jihar Katsina da ke arewacin Najeriya. An haifi Malam Aminu a unguwar Yammawa cikin jihar Katsina. Ya tashi gaban iyayensa kuma a gaban iyayensa ya fara karatu. Ya fara karatu wajen babansa na addini tun daga sanin haruffa. Daga nan ya shiga makarantar boko ta Gobarau Primary School. Malam ya ce ya fi gane karatun addini, shi ya sa babansa ya ƙi yarda ya ci gaba da karatun boko sai na addini. ""Don kar ya kasance a gaba ba a samu wanda zai gaji malunta ba a gidanmu. Amma daga baya wani malaminsa na addini ya ƙarfafa masa gwiwar haɗa karatun addinin da na zamanin don samun garaɓasa biyu. Sai ya tafi makarantar Higher Islamic Studies inda har ya samu takardar shaidar kammala karatu. ""Sannan duk sauran karatuttukana da nake yi ba su yi rauni ba kowane ya tafi yadda ya kamata, har na zo ina koyawa magidanta karatu. ""A hakan kuma har na kan tafi wajen neman abincina."" Daga baya ya samu shaidar NCE a fannin Arabic da Islamic Studies Education a FCE Katsina. Sai ya tafi Katsina Poloytechnic ya yi difloma a Public Personal Managemet, sannan ya wuce ya yi babbar difloma Public Policy and Admin. Ya kuma yi digiri na biyu a Jami'ar Karatu Daga Gida, sannan ya je Jami'ar Umaru Musa 'Yar adua ya sake digiri na biyu. Na so na sake digiri na biyu kan sanin halayyar ɗan adam amma wani malamina ya ce bokon ya isa haka gara na yi a fannin Islamic Studies. ""Daga nan sai na wuce Jami'ar An-Nahda na yi digirin-digirgir,"" in ji Malam. Malam ya ce yana yawan motsa jiki da duba lafiyarsa akai-akai. A fannin abinci kuma ya fi son naman kaji da zabbi da tuwon shinkafa da tuwon masara da miyar kuka. Ana yi wa malam kallon mai yawan sukar gwamnati da yin zafi a kanta, sai dai ya ce ba don cin mutunci yake ba sai don gyara. ""Ko su su kan bugo min waya wani lokaci, amma sai na tambaye su abin da na fada din an yi ko ba a yi ba? Sai na yi musu bayanin dalilin da ya sa na yi." https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-57514052 +religion Daga Titunanmu: A ina aka haifi Yesu Al-Masihu? Latsa hoton da ke sama domin ka kallon bidiyon: Daga Titunanmu na wannan makon ya yi duba ne a kan bikin Kirsimeti da ake yi a Najeriya da sauran kasashen duniya. Mun tambayi wasu mabiya addinin Kirista a ina aka hafi Yesu Al-Masihu domin ji daga gare su. Bidiyo: Abdulbaki Jari https://www.bbc.com/hausa/labarai-50906626 +religion Laylatul Qadr: Hotunan yadda Musulman duniya ke neman dacewa da daren rahama Asabar 20 ga watan Ramadan, wadda ta yi daidai da 1 ga watan Mayun 2021, ita ce rana ta farko da mafi yawan Musulman duniya suka fara tsayuwar dare da zummar samun dacewa da daren Lailatul Ƙadari. A Musulunci, ana yi wa daren kallon wanda ya fi wata 1,000 daraja kasancewar a cikinsa aka fara saukar da AlƘur'ani mai tsarki. Mun zabo muku hotunan yadda Musulmai a sassa daban-daban na duniya suke fafutukar dacewa da wannan dare mai tsarki: https://www.bbc.com/hausa/labarai-56971362 +religion Ko auren da aka daura a Facebook a Kano ya dauru? "'Yan Hisbah a jihar Kano da ke arewacin Najeriya suna neman wasu 'ma'aurata' bayan da suka daura aure a shafin Facebook. Sanusi Abdullahi mai shekara 29 ya shaida wa BBC cewa wasa kawai yake da yarinyar bai san cewa karamar magana za ta zama babba ba. ""Tattaunawa muke yi a wani zauren Facebook da sauran mutane, kamar wasa sai yarinyar ta ce na aure ta ni kuma na ce to, bayan wani lokaci sai ta sake aiko min da sako ta ce ta samu wanda zai yi mata alwalanci, ni ma sai abokina ya ce zai yi min alwali. ""Sai muka amince da naira 20,000 a matsayin sadaki, daga nan sai abokina da alwalin nata suka gaya mana dukkan abin da ake bukata a aure."" Sanusi ya ce jim kadan da faruwar hakan sai mutane suka fara yada zancen cewa 'Sanusi ya yi aure' daga nan sai ya kira yarinyar ya ce mata wannan auren fa kamar ya dauru, bari mu tambayi malaman musulunci saboda mutane na ta cewa auren ya tabbata. ""Da muka kira sai wasu suka ce ai aure ya dauru tun da akwai shaidu kuma na yi alkawarin biyan sadaki, amma da na tuntubi Sheik Ibrahim Daurawa, wani babban malami sai ya ce aure bai dauru ba tun da iyayen yarinya ba su sani ba. ""Ya ce yaya za a yi aure ba tare da sanin iyayen yarinya ba."" Sanusi ya ce barci ya kauracewa idonsa tsawon kwana biyu tun bayan da labarin ya bayyana. ""Wannan abun na damuna ba kadan ba, yarinyar da nake so ta ce ba ta sona yanzu kuma iyayenta ma sun yi fushi, ita ma waccar yarinyar ta rasa saurayin da za ta aura nan da watanni kadan."" Mai magana da yawun Hukumar Shari'a ta Kano Sanusi Mohammed ya shaida wa BBC cewa tuni sun bai wa Hisbah umarnin kama matasan domin ya zama misali ga masu irin wannan auren wasa a kafafen sada zumunta."" ""Abin da suka yi ya sabawa Musulunci, abu na gaba da za a yi bayan Hisbah ta kama su shi ne kai su kotu daga nan kuma alkali zai yanke hukuncin da ya dace da su. ""Shari'a ta tanadi hukunci ga kowane irin laifi."" Babban limamin Masallacin Abdullahi Abbas na Kano, Sheik Nazifi Inuwa ya shaida wa BBC cewa, yaya za a yi aure ya dauru bayan iyayen yarinya ba su sani ba. ""Manzon Allah SAW ya ce mace mai zaman kanta ce kawai za ta iya aurar da kanta, don haka aure tsarkakke irin na musulunci ba haka yake ba."" Sanusi ya ce tuni ya gudu daga gidansu saboda lamarin. ""Na ji labarin cewa Hisbah na nema na don a kama ni amma ina tattaunawa da iyayena kan ko na kai kaina gare su. ""Amma abin da nake so mutane su gane shi ne abun da ya farun kuskure ne kuma na ba da hakuri. ""Ban taba shiga masallaci don halartar daurin aure ba a rayuwata don haka ban san yadda abin yake ba, kuma na yi alkawari ba zan sake aikata irin haka ba.""" https://www.bbc.com/hausa/labarai-48871616 +religion Hagia Sophia: Bayani kan Cocin da aka mayar Masallaci Ɗumbin Musulmi ne suka tarodon fara gudanar da Sallar Juma'a karon farko a mashahurin ginin tarihin duniya na Hagia Sophia da ke birnin Santambul. Matakin na zuwa ne bayan sanarwar da gwamnatin Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya ta bayar don mayar da ginin zuwa masallaci a watan jiya. Tun ainihi dai an gina Hagia Sophia a matsayin cocin daular gabashin Roma ko kuma Byzantine, amma sai aka mayar da shi zuwa masallaci bayan cin birnin Santambul da daular Ottoman ta yi a 1453. A 1935 ne kuma, mutumin da ya assasa Turkiyyar zamani wadda ba ruwanta da addini, Kemal Ataturk, ya mayar da Hagia Sophia zuwa ginin adana kayan tarihi. https://www.bbc.com/hausa/labarai-53527007 +religion Coronavirus: Shawarwari kan yadda za a yi azumi a cikin kulle "Yayin azumin watan Ramadana na bana, intanet ce za ta zama kusan babbar abokiyar hulda, duk da cewa malamai na gargadar masu azumi a kan yin hakan a baya. ""Wannan azumin daban ne da ragowar (wadanda aka yi a baya), saboda haka dole ne a samu sauyin abubuwa"" a cewar Dr Umar Bawa, malami a sashen koyar da addinin Musulunci a Jami'ar Bayero ta Kano. Ko ba a fada ba za ku iya hasaso dalilin da ya jawo hakan - zaman gida da kusan dukkan al'ummar duniya ke yi sakamakon yakin da ake yi da yaduwar cutar korona. Wannan karon har da kamfanin Facebook a shirye-shiryen azumin, inda ya hada kai da Basma Khalifa da Mabdulle, wasu 'yan Birtaniya, da wani ma'aikacin BBC mai suna Mim Shaikh. Cikin wani shiri mai lakabin #RamadanTogether, za su rika samar da bidiyo kan yadda rayuwar azumi take yayin zaman gida. Wannan dalili ne ya sa muka duba muku shawarwari da za su taimaka muku wurin gudanar da azumi yayin da ake zaune a gida. Yin azumi a kulle a gida na iya zama abin kirki, amma sai idan mun so hakan. Me ya sa? Don samun kusanci da Allah, da tabbatar da yin mai kyau da barin marar kyau, mu'amala da masu karamin karfi da yin godiya a kai a kai. Duk shekara, kowane Musulmi na burin fahimtar Al-Kur'ani, ya fahimci sakonsa da kuma sanin wanda ya zo da shi (Annabi Muhammadu, tsira da aminci su tabbata a gare shi) sannan fiye da komai, Musulmi ya kamu da soyayyar wanda Ya aiko da Al-Kur'anin (Allah mai Girma da Daukaka). Alaka ta musamman da ke tsakanin Watan Ramalana da Al-Kur'ani Mai Tsarki ba boyayyen abu ba ne, don kuwa a wannan watan ne aka saukar da Littafin Mai Tsarki. Allah mai Girma da Daukaka yana cewa: ""Watan Ramalana shi ne watan da aka saukar da Al-Kur'ani don ya zama hanyar shiriya ga dan Adam."" [Al-Kur'ani, 2:186] Kowa, babba da yaro, na iya amfani da wannan lokaci don yin wannan aikin ibada mai albarka. Yara na iya fara koyon karatun Al-Kur'ani; wadanda suka iya karatun na iya fara koyon Harshen Larabci; wadanda suka iya Larabci sama-sama, a yanzu za su iya fara koyon fassara da Tafsiri (wato bayani kana bin da Al-Kur'ani ya kunsa) Daga karshe, akwai wani bangare na Watan Ramalana da ake mayar da hankali kansa a goman karshe na watan, ana kiransa Ittikafi. Wannan dokar zama a gidan ta ba mu damar yin Ittikafi a gidajenmu. Don haka, me zai hana mu yi amfani da wannan dama da Allah Ya ba mu, mu fahimci yadda ainihin Ittikafi yake. Karin labaran da za ku so ku karanta Lokaci abu ne mai muhimmanci kuma tsara yadda za a kashe shi ma yana da muhimmancin gaske, musamman ganin cewa azumin kwana 29 ko 30 ne kacal. Zaman gida ka iya rudar mutum ya yi tunanin cewa yana da lokaci mai yawa alhalin hannun agogo ba daina tafiya ya yi ba. Malam Dr Umar Bawa, Malami a Sashen Koyar Da Addinin Musulunci na Jami'ar Bayero, ya ce abin da mutum ya kamata ya fara yi shi ne ya tsara lokacinsa. ""Ya tsara ta yadda ba zai tozarta lokacinsa ba a kan wasu abubuwa marasa muhimmanci. Ya yi abubuwa da za su kusanta shi ga Allah. Mutane kan yi tururuwa zuwa masallatai a duk lokacin da aka ji kiran sallah da kuma sallolin nafila kamar asham ko tarawihi da kuma kiyamullaili. Sai dai Malam Dr Umar Bawa ya ce mutane za su iya yin sallolinsu a gida, kuma da ma sallar nafila a gida ta fi lada. ""Annabi ya ce sallar da ta fi falala ga mutum ita ce wadda ya yi a gidansa indai ba ta farilla ba ce,"" a cewar Umar Bawa. Kazalika, Malam Hussain Zakariyya, Limamin Masallacin Banex da ke Abuja, ya jaddada wannan magana da cewa Allah zai bai wa mutum cikakken ladansa idan ya yi sallarsa a gida saboda dalili mai karfi. ""Musulunci ya tanadi cewa duk ibadar da mutum yake yi - ta dukiya ko ta karfi ko ta harshe - sai wani abu ya sa ba zai iya yi ba saboda rashin lafiya ko tsufa ko tsoro, to Allah zai ba shi ladan wannan ibadar a duk inda yake. ""Amma kamar Tahajjud (kiyamallaili), wannan a gida ake yi ba sai an zo masallaci an hadu ba. Yin sallar farilla a gida a lokacin annoba ya fi lada."" Shi kuma Malam Umar ya kara da cewa ""Idan mutane suka fita sallah suka dauko cutar suka yada wa iyalinsu Allah ba zai kyale su ba"". Malam Hussain Zakariyya ya ce a da a kan bi masallatai domin raba kayayyakin abinci na bude-baki, amma yanzu saboda yanayi hakan ba za ta samu ba. A saboda haka ne malam ya ce bai wa mutane tallafi a gidajensu ya fi lada sama da kai wa masallatai. ""Gara ka kai wa mutum tallafi gidansa da ka kai masallaci a dafa a bayar, hakan ya fi lada domin ba a son mutum ya fito rokon abin da zai ci."" Masana harkar lafiya kan ce shan ruwa da yawa da zama a daki mai cike da iska ka iya taimaka wa mai cutar korona yayin da yake jinya. Babu mamaki saboda cutar tana da alaka sosai da numfashi sannan kuma makogwaro ma kafar numfashi ce. Sai dai Malam Umar Bawa ya ce hakan ba ya nufin cewa wanda yake azumi yana cikin hatsarin kamuwa da cutar korona ba ne. Ya ce: ""Rashin shan ruwa ba ya nufin za a kamu da cutar duk da cewa likitoci sun ce idan makogwaro yana bushewa akwai damuwa. ""Amma duk lokacin da mutum ya ji cewa bushewar makogwaron za ta iya kai shi ga cutuwa, to da ma ai Allah bai dora wa mutane abin da za su cutar da kansu ba. Wanda yake da lafiyarsa garau wajibi ne ya yi azuminsa.""" https://www.bbc.com/hausa/labarai-52386644 +religion Rikicin Kudus: Muhimmancin masallacin Kudus ga Musulmi, Kiristoci da Yahudawa An shiga ranara ta uku ana arangama tsakanin jami'an tsaron Isra'ila da Palasdinawa a wajen masallacin Al-Aqsa - wurin ibada na uku mafi tsarki ga musulmi da ke birnin Kudus. Lamarin na faruwa ne a yayin da Yahudawa suke gudanar da tattaki na nuna kishin kasa a birnin Kudus da ke fuskantar tashin hankali a yan makwannin nan. Sama da mutum 200 ne suka ji rauni sannan jama'a sun rika jefa duwatsu yayin da yan sanda suka rika harba gurneti. Duk da cewar birnin ne silar daya daga cikin abubuwan da suke jawo tayar da jijiyar wuya tsakanin mabiya addinan Musulunci da Yaduwadanci da Kiristancii, dukkansu sun yi tarayya kan girmama wannan wuri mai tsarki. Tsohon birnin Kudus yana tsakiyar birnin ne a yanzu inda kwaroro-kwaroro masu yawa da kuma tsarin gine-gine na tarihi sun bambance bangarorin Kiristoci da na Musulmai da na Yahudawa da kuma na Aarmeniyawa. Tsohon birnin yana kewaye ne da wata ganuwa mai kama ta dutse kuma tana dauke da wasu wurare mafiya tsarki ga al'ummun duniya. Ko wacce unguwa na wakiltar al'ummarta ne. Kiristoci na da unguwanni biyu saboda Armeniyawa ma Kiristoci ne kuma unguwarsu - wacce ta fi kankanta cikin hudun - daya ce daga cikin tsoffin cibiyoyin Armeniyawa a duniya. Wani abu ne na daban saboda al'ummar Armeniyawa sun adana al'adarsu cikin Majami'ay St James wadda ta kunshi da yawa daga cikin unguwarsu. A cikin unguwar Kiristoci akwai Majami'ar da ake ce wa Church of the Holy Sepulchre a turance, wadda take da muhimmanci ga Kiristoci a fadin duniya. Majami'ar na wani wuri da aka yi imanin cewar yana da alaka da labarin Annabi Isa (AS). Da yawan Kiristoci sun yi imanin cewar an gicciye Annabi Isa ne a wurin nan tsaunin Golgotha, ko kuma tsaunin Calvary, inda suka yi imanin cewar inda aka binne shi yana wajen da ake ce wa sepulchre din, kuma ta nan ne suka yi imanin cewar ya tashi. Wakilai daga majami'u daban-daban, ciki har da Cocin Girka da ta darikar Katolika da ta Armeniyawa da ta Kibdawa ne suke gudanar da lamuran cocin. Majami'ar daya ce daga cikin wuraren ibada ga miliyoyin Kiristoci da ke zuwa bauta inda suka yi imanin cewar an bunne Annabi Isa (AS) domin neman kwanciyar hankali da kuma tabarruki ta addu'a a wurin. Unguwar Musulmai ita ce unguwa mafi girma daga cikin unguwanni hudu kuma a cikinta akwai Qubbat al-Sakhrah da massalacin Al-aqsa da ke kan wani tudu wanda Musulmi suka fi sani da Haram al-Sharif, ko kuma wuri mai tsarki. Masallacin shi ne masallaci na uku a tsarki cikin addinin Musulunci kuma yana karkashin gudanarwar wani kwamitin amintattu da ake kira Waqf. Musulmi sun yi imanin cewar Annabi Muhammad [SAW] ya taho nan daga Makka a daren Isra'i da Mi'iraj kuma ya ja dukkannin Annabawa sallah. Wasu 'yan taku kadan daga wannan wuri a Qubbat al-Sakhrah akwai wani dutsen da Musulmi suka yi imanin cewar Annabi Muhammad [SAW] ya tashi zuwa sama bayan sallar. Musulmai su kan ziyarci wannan wuri mai tsarki a ko wane lokaci cikin shekara, amma ko wacce ranar Juma'a a cikin watan Ramadan dubun-dubatar musulmi na zuwa domin su yi sallah a masallacin. A cikin unguwar Yahudawa akwai wata katanga ta yammaci da ake ce wa Kotel, ko kuma katangar yammaci, sauran katangar hana zaizayar tudun da ada wurin ibadan Yahudawa ke zaune. A cikin wurin ibadar akwai inda ake ce wa Holy of Holies a turance, wato wuri mafi tsarki a addinin Yahudanci. Yahudawa sun yi imanin cewar nan ne tushen inda aka halicci duniya, kuma inda annabi Ibrahim (AS) ya nemi ya yi hadya da dansa annabi Is'hak (AS). Wasu da dama kuma sun yi imanin cewar inda Qubbat al-Sakhrah yake a yanzu nan ne wuri mafi tsarki a addininsu wanda ake ce wa Holy of Holies. A yau katangar yammaci ita ce wuri mafi kusa da Yahudawa za su iya ibada ga wuri mafi tsarki a gunsu da ake kira Holy of Holies. Limamin Yahudawa na katangar yammaci shi yake lura da lamura a wannan wuri, kuma a ko wacce shekara miliyoyin baki na zuwa wurin katangar. Yauhudawa daga fadin duniya sukan ziyarci wannan wuri a lokacin hutun Yahudawa da ake ce wa High Holidays a turance domin yin addu'a da kuma tunawa da tarihinsu. Rikicin baya-bayan nan Yan sandan Isra'ila sun ce dubban Palasdinawa sun killace kansu cikin ginin cikin tsammanin yiwuwar samun arangama a lokacin tattakin. An bai wa yan sandan umarnin shiga cikin masallacin domin tarwatsa masu tayar da hankalin bayan da aka kai wa shingen yan sanda hari sannan jama'a suka rika jefa musu duwatsu. An shafe sama da sa'a daya yan sanda na harba gurneti kan Falasdinawan da ke jefinsu da duwatsu. Yan sandan Isra'ila sun yanke shawarar hana Yahudawa zuwa inda masallacin yake a lokacin tattakin. Bikin da ake yi kowace shekara yana nuna ranar da aka mamaye Gabashin Kudus a 1967 daga baya kuma ya fada hannun Isra'ila a wani mataki da galibin kasashen duniya ba su amince da shi ba. Kudus ta Gabas ta kasance a cikin 1967 sannan daga baya Isra'ila ta hade ta - a wani matakin da galibin kasashen duniya ba su amince da shi ba. Falasdinawa na ganin gudanar da bikin wani salon takala ne. Kuma tattakin na zuwa ne yayin da aka shiga ranakun 10 na ƙarshe a watan azumin Ramadana. Rikicin na baya-bayan nan na zuwa ne bayan shafe kwanaki ana arangama tsakanin Falasdinawa da yan sandan Isra'ila a kusa da yankin Sheikh Jarrah da ke Gabashin Kudus tare da yiwuwar korar Falasdinawa daga gidajensu. A ranar Litinin ne ya kamata Kotun Kolin Isra'ila ta tattauna kan halin da ake ciki amma aka dage saboda rikicin. Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya kuma zai gana ranar Litinin domin tattauna batun. https://www.bbc.com/hausa/labarai-40715935 +religion Eid al-Fitr: Abubuwan da ake so Musulmi ya yi kafin Sallar Idi "Mutumin da ya yi azumin watan Ramadan, an so ya cika azumin da sallar Idi. Sallar Idi Ibada ce da Allah ya shar'anta a matsayin kammala Ibadah ta Azumin watan Ramadan. Ba ana yin Sallar Idi ba ne don tunawa da wata ranar haihuwa ko wata nasara da aka samu. Idi Ibadah ce ta yin godiya ga Allah. BBC ta tattauna da Malam Nura Khalid limamin masallacin Apo a birnin tarayyar Najeriya Abuja wanda ya bayyana wasu abubuwa da ake son musulmi ya yi a ranar Sallar Idi kamar haka: Bayar da zakkar fidda-kai ga mabukata Zakatur fitr wajiba ce kamar yadda SAW ya farlanta ta. Ta fi falala a fitar da ita kafin a tafi masallacin Idi. Amma an sawwaka a fitar da ita a daren Idi ko kwana biyu ko uku kafin ranar Idi, wato tun a ranar 27 na watan Ramadan musamman ga kungiyoyi ko wakilai da ke tattara zakkar domin raba wa mabukata. Fitarwa da wuri zai taimaka zakkar ta isa ga mabukata da wuri kafin lokacinta ya wuce. Annabi SAW ya ce: ""Wanda ya fitar kafin Sallar Idi, to ya samu zakkar fidda kai. Wanda kuma ya fitar bayan idar da Sallar Idi to tana matsayin sadaka ne daga cikin ayyukan sadaka amma bai samu zakkar fidda kai ba."" Wankan zuwan Idi Sunnah ne. Ana son mutum ya yi wanka a ranar Idi kamar yadda yake wankan zuwa Juma'a. Cin abinci kafin Idi Sunnah ce. Ana so mutum ya ci abinci kafin zuwa Idi domin koyi da Manzo SAW. Ba a so mutum ya jinkirta cin abinci domin ka da ya nuna kamar ana azumi, domin rana ce da ba a yin azumi. Malam ya ce Annabi SAW yana cin dabino kamar uku ko biyar ko bakwai ko tara kafin ya tafi sallar Idi. Wannan al'ada ce da musulunci ya tabbatar da ita. Kuma sunnah ce ga musulmi ya saka tufafi sabo mai kyau.Tufafi na musamman, kuma ga maza an fi son ya kasance tufafi farare. Idi ranar bayyana farin ciki ne da godiya ga Allah a kan ni'imar da ya yi wa bayinsa da dacewa da yin Azumi da ibadun da aka gudanar da kuma kyautar da ya samu na daren Lailatul Kadri. Ana son a yi ta yin kabbara a yayin tafiya Idi har idan an zauna a filin Idi zuwa sai liman ya zo. Mai tafiya idi zai dinga cewa: ""Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar,"" ko kuma ya ce "" Allahu Akbar, Allahu Akbar, Lailaha illahahu Wallahu Akbar, Allahu Akbar Walillahil Hamd. Ana kuma cewa: ""Allahu Akbar Kabira Walhamdu lillahi kasira, Walhamdulillahi bukratan wa asila."" Za a daina kabbara idan Liman ya tayar da sallah. Sallar Idi ba ta da Nafila domin ita ma Nafila ce. Amma idan a cikin masallaci ne za a yi Idi watakila saboda ruwan sama, to mutum yana iya nafilar gaisuwa ga Masallaci. Amma a filin Idi ba a nafila. Mutum yana zuwa zai zauna kuma ya ci gaba da kabbara har isowar liman. Ana hudubar Idi bayan sallame Sallah. Ana son a zauna a saurari hudubar Liman, ba a son daga sallame sallah a fice. Duk da cewa ba wajibi ba ne, amma malam ya ce yana daga cikin alherin da Annabi SAW ya yi nuni da shi domin samun albarkar addu'ar musulmi da ake yi a cikin huduba. Wannan Sunnah ce ta Manzo SAW ba a son a tsayar da hanya daya. Ana son mutum ya csauya hanya idan zai dawo daga Idi domin zai yi wa wasu mutane na daban sallama sabanin wadanda ya yi wa sallama a lokacin tafiyarsa. Ana son dukkan al'umma su tafi idi, maza da mata da yara da tsoffi. Mata masu haila za su iya zuwa amma ba za su shiga sahu ba, za su tsaya a gefen masallaci. Ana son mata idan za su tafi idi su suturta jikinsu, ka da su tafi Ibadah suna bayyana jiki kuma suna bayyana adonsu. Sannan ba a son mata su jera sahu daya da maza a filin idi. An fi son maza suna gaba mata na baya." https://www.bbc.com/hausa/labarai-57079567 +religion Abubuwa 10 da ya kamata Musulmi su yi a watan Dhu al-Hijjah Annabi muhammad (SAWA) ya ce babu wasu kwanaki a cikin shekara da suka fi muhimmanci kamar kwanakin goman farkon watan Dhu al-Hijjah. https://www.bbc.com/hausa/53510936 +religion Sheikh Abduljabbar: Kotu ta yi umarni a yi wa Malamin gwajin kwakwalwa "Wata kotun Musuluncin da ke shari'ar Malamin addinin nan Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara ta umarci a yi masa gwajin kwakwalwa da kunne a wani zaman ci gaban shari'ar da ake yi masa a birnin Kano da ke arewacin kasar. Kotu ta bayar da umarnin ne bayan Malamin addinin Musuluncin ya gaza amsa tambayoyin da alkalin kotun Mai Shari'a Sarki Ibrahim Yola ya yi masa ranar Alhamis. Ranar Juma'a 16 ga watan Yuli ne gwamnatin jihar Kano ta gurfanar da malamin a gaban kotu bisa zargin ɓatanci ga addini da kuma tunzura jama'a, zargin da ya sha musantawa. Tun da misalin karfe 9:20 na safe ne aka soma zaman kotun da ke Kofar Kudu daura da gidan Sarkin Kano tare da gabatar da wasu sabbin tuhume-tuhume kan wanda ake zargi. Lauyoyin da ke kare Abduljabbar karkashin jagorancin Barista Sale Bakaro sun soki yadda ake tsawaita shari'ar da kuma sabbin tuhume-tuhumen da aka gabatar kan Malamin. Sai dai Alkali Sarki Ibrahim Yola ya ce a fahimtarsa wadannan tuhume-tuhume da aka gabatar wajibi ne domin a karantawa wanda ake zargi laifukan da ake bukatar amsa daga gare shi. Hakan ne ya sa kotu ta amince a karanta wa wanda ake ƙara sabbin tuhume-tuhumen da ake masa - domin ya musanta ko ya amince da su. Wannan matsayi na alkali bai yi wa lauyoyin Abduljabbar dadi ba inda suka ce idan aka ci gaba da tafiya a haka to za su daukaka kara. Yadda zaman kotu ta kaya Da farko Alkalin ya gabatar da tambayoyi uku ga Sheikh Abduljabbar sai dai bai amsa ko guda daga ciki ba. Tambaya ta farko ita ce: ""Ranar 10 ga watan 8 a shekara ta 2018 Abduljabbar a unguwar Sani Mainagge a karatunka na Jauful Fara inda ka yi wa Annabi SAW kage na cewar a Hadisi na 1365 da na 1358 na sahihi Muslim cewa Annabi SAW fyade ya yi wa Nana Aisha, wanda hakan ya saba wa 382 (b) kundin tsarin shari'ar Musulunci ta 2000."" Sai dai Abduljabbar bai amsa wannan tambayar ba dalilin da ya sa kotu ta tambaye shi wanne yare yake ji, amma nan ma bai ce uffan ba. Kotu ta ci gaba da yi masa tambaya har sau uku amma bata samu kowanne amsa daga Abduljabbar ba. Tuhuma ta biyu: ""Ranar 10 ga watan 8 2018, a karatunka na Jauful fara ka yi amfani da kalaman ɓatanci inda ka yi masa kage kan aurensa da Ummu Safiya, ka ce Sahihi Muslim ya ce Annabi ya kwace wa wani mutum matarsa 1365, wanda hakan cin zarafi ne, laifi ne da ya saba wa sashe na 382(b)"" An sake tambayar Abduljabbar ko ya fahimci abin da ake tuhumarsa da aikatawa amma ya yi shiru. Alkali ya sake tambaya: ""Shin ka yarda ka aikata laifi ko ba ka yarda ba?"" Abduljabbar ya yi shiru bai ce komai ba. Tuhuma ta uku: ""A ranar 10 ga watan 8 ta shekarar 2019, a darasinka na 93 ka yi amfani da kalaman ɓatanci cewar dole manzon Allah ya yi wa matarsa Safiyya ya aureta, wanda babu wannan hadisi kai ka kirkire shi. Kuma hakan ya saɓa wa sashe na 382 (b) na kudin tsarin Shari'ar Musulunci na Kano na 2000."" Kan wannan tambayar Abduljabbar ya yi gum da bakinsa. Tuhuma ta hudu: ""A darasinka na 90 da na 98 na karatun Juful fara ga kaga wa Annabi laifin zina, inda ka ce wata mata ta nemi Annabi ya biya mata bukatarta, kuma ka ce ya yi hakan, wannan ya saɓa wa sashe na 382 na kundin hukunta laifuffuka na shari'ar Musulunci na 2000 ta jihar Kano.""Alkali Sarki Yola ya sake tambayar Abduljabbar kamar farko amma ya yi shiru bai ce uffan ba. Alkali Sarki Yola ya ɗage sauraron shari'ar bayan gabatar da waɗannan tuhume-tuhume ba tare da samun amsa daga wanda ake zargi ba. Sai dai ya bayar da umarnin bincikar lafiyar Sheikh Abduljabbar saboda rashin amsawa kotu tambayoyin da ta yi masa tare da wata takardar zuwa ga likitan kunne da ke asibitin Kwararru na Murtala, domin yin gwajin. Daga nan ya ɗage zaman shari'ar zuwa mako biyu za a dawo kotu ranar 16 ga watan Satumbar 2021 domin ci gaba da shari'ar. Ya kuma umarci a bai wa lauyoyin wanda ake kara kwafin shari'ar domin daukaka karar da suke bukata." https://www.bbc.com/hausa/labarai-58419155 +religion Bidiyon Ku San Malamanku tare da Dr Ibrahim Abdullahi Rijiyar Lemo A wannan makon shirin Ku San Malamanku ya tattauna ne da Dr Ibrahim Abdullahi Sani Rijiyar Lemo. https://www.bbc.com/hausa/labarai-59686659 +religion Falalar goman karshe Falalar goman karshe https://www.bbc.com/hausa/labarai-52642203 +religion Cikin hotuna: An bai wa dabbobin dawa kyautukan Kirsimeti A 'yan kwanakin an bai wa dabbobin gidajen namun daji kyaututtukan Kirsimeti rana guda kafin ta zo, kunshe cikin kwalaye kuma cike da abinci. Ga kadan daga cikinsu daga kasashen Faransa da New Zealand da Jamus da Colombia. Dukkan hotunan suna da hakkin mallaka https://www.bbc.com/hausa/labarai-50906279 +religion Sokoto: An rufe kwaleji a jihar bayan tarzoma kan zargin saɓo "'Yan sanda a jihar Sokoto da ke arewa maso gabashin Najeriya sun ce sun kama wasu matasa biyu da ake zarginsu da hannu a kisan da aka yi wa wata ɗaliba da aka zarga da yi wa Annabi Muhammadu S.A.W. ɓatanci. Su ma shugabannin al'umma na ci gaba da yin tir da kisan ɗalibar. A ranar Alhamis ne wasu ɗalibai da mazauna yankin suka yi wa wata ɗalibar Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari duka sannan suka ƙona gawarta saboda zargin ta zagi Annabi a dandalin sadarwa na WhatsAPP. Sai dai BBC ba ta iya tabbatar da ainahin abin da ya faru ba zuwa yanzu. 'Yan sanan Sokoto sun ce sun kama mutum biyu da ake zargi da aikata kisan. Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammadu Sa'ad Abubakar ya yi Allah-wadai da aikin mutanen da suka kashe ta, inda ya yi kira da a kama tare da gurfanar da su a gaban kotu. Wata sanarwa daga sakataren masarautar ta nemi mazauna jihar da su ""kwantar da hankali"" kuma ""su zauna lafiya"". A nasa ɓangaren, shi ma babban malamin Kirista a Sokoto Bishop Mathew Hassan Kukah ya yi tir da aikin mutanen yana mai cewa ""wannan ba shi da wata alaƙa da addini"". Cikin wata sanarwa da aka fitar a Sokoton, Kukah ya ce Musulmai da Kirista sun zauna cikin kwanciyar hankali tsawon lokaci. ""Wannan ba shi da wata alaƙa da addini. Kiristoci da Musulmai sun zauna tare cikin kwanciyar hankali tsawon lokaci a Sokoto. Dole ne a duba lamarin nan a matsayin babban laifi kuma dole ne doka ta yi aikinta,"" in ji shi. Rahotanni daga Jihar Sokoto a Najeriya na cewa wasu da ake zargin ɗalibai ne a kwalejin ilimi ta Shehu Shagari sun tayar da tarzoma bayan da aka zargi wata daliba da yin saɓo, abin da ya fusata ɗalibai suka shiga cinna wuta da hayaniya a makarantar. Rahotanni sun ce har an yi asarar rayuka sakamakon wannan lamari, sai dai babu tabbaci daga hukumomi kan lamarin. Tun bayan da aka soma wannan hayaniya aka tura sojoji da jami'an kwantar da tarzoma zuwa kwalejin ilimin domin kwantar da tarzomar. Ko da BBC ta tuntuɓi rundunar yan sanda reshen Jihar Sokoto, mai magana da yawun rundunar ASP Sanusi Abubakar ya ce jami'an da suka tura sun kwantar da tarzomar kuma komai ya lafa. Wani ɗalibin kwalejin da BBC ta tuntuɓa ya bayyana cewa a lokacin da ɗaliban suka samu labarin faruwar lamarin, rigima sai ta kaure a cikin makarantar. A cewarsa malamai da sauran shugabannin kwalejin sun yi ƙoƙarin su dakatar da ɗaliban daga wannan tarzoma amma abin ya ci tura, inda har jami'an tsaro suka je makarantar suna harba wa ɗaliban hayaƙi mai sa hawaye. Ɗalibin ya bayyana cewa idan aka harba hayaƙin sai ɗaliban su ma su ɗauka su jefa wa jami'an tsaron. Ya ce ba ɗaliban kwalejin bane kaɗai suka tayar da hargitsin har da na waje suka shiga cikin kwalejin. A cewarsa, wadda ake zargi da aikata saɓon an ɓoye ta a ɗakin jam'ian tsaro da ke ƙofar kwalejin inda masu tarzomar suka sha ƙarfin jami'an tsaron suka ɓalla ƙofar ɗakin suka ciro yarinyar. Ya ce an yi ƙone-ƙone da farfasa muhimman kayayyaki a cikin kwalejin musamman motocin malamai. Rundunar ƴan sandan Najeriya reshen Jihar Sokoto ta tabbatar da faruwar wannan tarzoma sai dai ba ta yi ƙarin bayani kan abubuwan da suka faru ba inda suka ce suna gudanar da bincike. ASP Sanusi Abubakar wanda shi ne mai magana da yawun ƴan sandan ya ce ƴan sandan tare da haɗin gwiwar wasu jami'an tsaro sun bazama a yankin kuma a yanzu akwai kwanciyar hankali. Ya ce ba su da tabbaci kan maganganun da ake yi na cewa wasu sun rasa ransu haka kuma bai tabbatar da ko an kama wani daga cikin masu tarzomar ba. Bugu-da-kari ASP Sanusi yace idan akwai wani karin bayani musamman daga binciken da suke yi za su sanar nan gaba. Tuni dai hukumomin kwalejin ilimi ta Shehu Shagari da ke Sokoto suka sanar da rufe makarnatar har sai abin da hali yayi." https://www.bbc.com/hausa/labarai-61428424 +religion Ku san malamanku tare da Sheikh Khuzaima Isma'ila Idris Iyayen Malam Khuzaima Isma'ila Idris bin Sulaiman, Ardo Abdullahi asali mutanen Jahun ne, daga bisani suka koma Jihar Bauchin Najeriya. Amma shi Malam Khuzaima an haife shi ne a garin Jos a unguwar Dodo. Ya fara neman ilimi daga wurin mahaifinsa na addini da boko. Ya yi karatun addini a wajen yayarsa mai suna Basma, saboda girma da rashin lafiya da ta samu mahaifinsu, wanda ya sanya ba zai iya ci gaba da koyar da su ba. Ya samu sakafa sosai a hannun mahaifinsu da ya tarbiyyantar da su a kan cewa karatu nishadi ne, yana yawan zama da yammaci a kofar gida inda yake rera koyar da su wakokin Shehu Usman Dan Fodio cikin harshen Larabci da Filatanci. Sun yi karatu mai zurfi na littafan addini, yayin da suka yi karatun Alkur'ani a wajen Sheikh Saleh wanda gida guda suka taso. Ita ma Kakarsu mai suna Miyangwal, ita ma sun koyi rubuta Alkur'ani da take yi, wannan ne ya ba shi damar abin da ya kira share fagen shiga makaranta. Ya shiga fagen karatun Asasul Islamiyya, sai kuma Sanawiyya. A shekarar 2006 ya tafi makarantar koyon harshen Larabci da ke kasar Sudan, ya kwashe shekara guda yana koyo, kuma da yake yana hadawa da fannin karatun Boko ya tafi British Institution, ya yi karatun karamar Diploma a fannin Kimiyyar Kwamfuta. Ya sake komawa Jami'ar Kuliyatul Jabra ya yi karatun Da'awa. Jami'atul Sudanil Maftuha da ke kasar Sudan da har yanzu yake karatu anan. Sheikh Khuzaima ya yi nasarar sauke Alkur'ani mai girma, kasancewar kakarsu marubuciyar Alkurani ce ta ruwayar Warshu, Suratul Baqra na daga cikin surorun da ke birgishe kasancewar a cikinta Ayatul Kursiyyu da Amanarrasulu da Ayatul Daim suke. Kasancewar hakan ya sanya kullum da safe sai ya karanta surar. Surar da ta fi ba shi wahalar karatu ita ce Suratul Baqra, ya kan yi tuntube sosai kafin ya samu kammalawa. Abin da ya fi komai sanya shi nishadi, shi ne sauraren mahaifinsa idan ya na karatu ko rera wakokin Shehu Usman dan Fodio, hakan ya sanya ya ke yawan kwaikwayon yadda mahaifin na sa ke karatun. Ranar da ya haddace Suratul Baqra ita ce rana mafi farin ciki gare shi. Ranar da mahaifinsa ya rasu ita ce mafi muni da bakin ciki a gare shi, ''Lokacin ina dawowa daga inda nake koyon kareti, ina kan hanya aka sanar dani rasuwar mahaifina, tun daga nan na shiga cikin tashin hankali da bakin ciki,'' in ji Malamin. Tabbatar da ci gaban Sunnah na daga cikin abu mai faranta ran Malamin, take gaskiya ko kauce wa fadar ta na bakanta wa malamin rai. Tuwon masara, da sakwara, da tuwon shinkafa na daga cikin abincin da Malamin ya fi son ya ci. Yana da mace guda daya da 'ya'ya uku. https://www.bbc.com/hausa/labarai-61427648 +religion Bidiyon Ku san Malamanku tare da Malam Muhammadu Kobuwa a Gombe "Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon: An haifi malamin a wani gari da ake kira Jollo a Karamar Hukumar Alkaleri ta jihar Bauchi arewa maso gabashin Najeriya. Ya soma karatu a hannun mahaifinsa mai suna Muhammadu, wanda bai dade da fara karatun ba Allah ya yi masa rasuwa, inda daga nan ne kawunsa da ake kira malam Kawu ya dauko shi zuwa jihar Gombe makwabciya a wani kauye da ake kira Wuro Kachalla. ""Daga garin Wuro Kachalla ne muka taso muka dawo wani gari da ake kira garin Bappa Ibrahima inda na yi saukar karatuna a hannun kawun nawa,"" in ji Malamin." https://www.bbc.com/hausa/media-61027603 +religion Coronavirus: Yadda ya kamata a yi jana'iza a Musulunci lokacin annoba "Ana bayyana fargaba kan hanyoyi da matakan da ya kamata a bi wajen binne mutanen da cutar korona ta kashe. Hukumomi a Najeriya sun dauki mataki na hana duk wani taron jama'a har da Sallar jam'i da tilasta hana fita da kwadaitar da bayar da tazara tsakanin mutane, amma wasu na ganin akwai kura-kurai da dama da suka faru yadda aka gudanar da jana'izar marigayi Malam Abba Kyari, shugaban ma'aikata a fadar shugaban kasar. Daga cikin wadanda suke ganin an saba doka da umarnin masana kiwon lafiya da kuma tanadin da musulunci ya yi idan ana cikin annoba sun hada da Babban limamin masallacin juma'a na Nagazi-Uvete da ke Okene, Jihar Kogi Imam Murtadha Muhammad Gusau. Malamin ya bayar da fatawa kan yadda ya dace a yi jana'aiza a musulunci lokacin da ake cikin annoba. Malamin ya ce ya kalli yadda aka yi jana'izar Abba Kyari kuma a cewarsa, ""tun daga yadda manyan jami'an gwamnati, har da na fadar shugaban kasa, suka yi cincirindo a filin jirgin sama domin tarbon gawarsa, bai dace ba."" Ya ce hakan ta faru duk da ana sane da irin gargadi da jan kunne da jami'an lafiya da kuma hukumar da ke kula da cututtuka masu yaduwa, NCDC ke yi na kauracewa cunkoson jama'a don dakile yaduwar cutar.. ""Mutum biyu ya kamata a ce sun tarbi gawar, duba da irin halin da ake ciki na yaduwar wannan annoba, amma ba kamar yadda jami'an gwamnati da dama, da wasu ma'aikata suka taru tun daga filin jirgi har zuwa makabarta ba,"" in ji Malamin. Imam Murtadha Muhammad Gusau ya bayyana irin tanadin da musulunci ya yi na jana'iza a lokacin yanayi na annoba kamar haka: Game da wanke mamaci, ba dole ba ne sai mutane sun sa kansu cikin matsalar cewa dole sai an yi masa wanka irin na asali. Addinin musulunci sauki ne da shi, bai tsananta ba. Duk abin da ake yi wa mamaci, idan har akwai tsoro ko yiwuwar kamuwa da cutar, to ana iya barin sa. Idan har ba za a yi wankan gawar ba da ruwa saboda cutar corona, ana iya yin taimama da kasa maimakon ruwa. Za a shafa kasa a shafe fuskar mamaci, sai hannayensa, daga nan a sa masa likkafani, a yi masa Sallar Janaza a binne shi (A diba Majmu'u Fatawa wa Maqalat Mutanawwi'ah, Kundi na 13, shafi na 123 na Shaikh Abdul-Aziz Bin Baz da Fatawa fi Ahkam Al-Jana'iz na Shaikh Muhammad Bin Salih Al-Uthaimin, shafi na 213-214] Idan kuma babu damar yi masa wanka saboda annobar Korona, ana iya lullube gawar da likafani, a yi wa gawar Sallah a binne. Wannan saboda Manzo SAW ya umurci a gaggauta kawar da mamaci kada a yi jinkiri. [Bukhari]. Idan kuma annobar cutar Korona ba ta haramta taba jikin mamaci ba, ko da safar hannu, wannan ba zai hana a yi masa dukkanin abin da ya kamata a yi wa musulmi ba da ya rasu. Babu kyau a jinkirta binne mamaci na kwanaki ko watanni, don a jira har sai hukumomi sun dage dokar takaita fita saboda an fi son a gaggauta kawar da mamaci. Idan kuma gawar ta kasance a rufe cikin jika, kuma dokar da hukumomi suka kafa ba ta bayar da damar budewa ba, don haka wankan gawa ba zai samu ba. Bisa haka ana iya lullube gawar da likafani a yi wa gawar sallah a binne ta [A diba Majmu'u Fatawa wa Maqalat Mutanawwi'ah, kundi na. 13, shafi na 128-129 na Shaikh Abdul-Aziz Bin Baz] Malamin ya ce taruwar da aka yi wurin jana'izar marigayi Malam Abba Kyari, wannan bai dace ba ace kusan mutum hamsin sun taru domin yi masa jana'izah. A cewarsa, ""Mutum uku-hudu-biyar-bakwai sun isa. Wannan kuwa ba domin komai ba sai domin kokarin kiyaye kai. Kuma irin yadda mutane suka tsaya, ba tare da wata rata mai nisa tsakaninsu ba, suka yi masa sallah, shi ma wannan an yi kuskure,"" ""Saboda su jami'an gwamnati ya kamata su zama abun koyi ga sauran gama-garin mutane, ba sune zai zama kuma suna saba dokokin da aka shinfida ba,"". ""Sannan idan mun lura, a makabarta wurin binne shi, irin yadda mutane suka taru a makabartar, domin yin rakiya ga gawar, da irin yadda mutane suka rungumi gawarsa wurin sa shi cikin kabari, duk an tabka kuskure, la'akari da irin halin da ake ciki na yaduwar wannan annoba cikin gaggawa,"" ""Idan har dokar hana fita da aka kafa kan cutar Korona ta hana jam'in Sallar jana'iza, ko da kuwa makusanta ga mamacin ne, to ya halatta wasu mutane kalilan su hadu su yi wa mamacin Sallah su kuma binne shi,"" Wadanda kuma ba su samu sallar ba suna iya kai ziyara kabarinsa su yi masa addu'a. [A diba Majmu'u Fatawa wa Maqalat Mutanawwi'ah, Kundi na. 13, shafi na 153 na Shaikh Abdul-Aziz Bin Baz] Musulmi suna iya yin sahu uku bayan Liman. Kamar yadda Abu Umamah ya ruwaito. ""Annabi Muhammad SAW ya taba yin Sallar Jana'iza kuma mutum bakwai ne kawai a bayansa. Ya sa mutum uku a sahu na gaba, biyu kuma a wani sahu, sai biyu a sahu na uku."" [At-Tabarani a cikin Al-Kabir, kuma Imamul Al-Albani ya inganta shi a cikin Ahkam Al-Jana'iz, shafi na 127]. Idan hukumomi ne suka binne mamacin ba tare da an yi masa sallah ba, musamman idan kasashen da ba na musulmi ba ne, musulmi na iya tambayar inda kabarinsa yake sai su yi masa Sallah kamar yadda aka bayyana. Idan kuma ba a san inda aka binne shi ba, za a iya yi masa Sallar Jana'iza ba sai da gawarsa ba, kamar yadda Manzo SAW ya yi wa Najjashi Sarkin Abyssinia. A wannan yanayin, ana yin Sallar Jana'iza kamar yadda ake yi, kawai gawar mamacin ce kawai babu a gaban liman. An amince a yi Sallar Jana'iza a dakin da aka yi wa mamaci wanka, amma a haraba, wajen Masallaci ya fi, ko da yake babu komi idan an yi a Masallaci [A diba Majmu'u Fatawa wa Maqalat Mutanawwi'ah, kundi na 13, shafi na 157 da kuma kundi na 13, shafi na 164 na Shaikh Abdul-Aziz Bin Baz] Idan za a yi wa mamaci Sallah, ana yin sahu kamar yadda ake yin sallah. Amma idan annobar cutar korona ta hana yin haka, to sai a bayar da tazara tsakanin mutanen da ke sallar. An amince a binne mutum fiye da daya a kabari daya idan akwai bukatar haka, musamman a yanayin da aka samu gawawwakin wadanda suka mutu da yawa, kuma wurin da za a binne su ya yi karanci. A wannan yanayin, musulmin da ya fi sanin Al Qur'ani mai tsarki ake fara saka wa a farko kusa da al kibla a kabarin, kuma ana jera su kusa da juna. Malamai sun kuma bayyana cewa tsakaninsu ana sa shamaki. [A diba Fatawar Ahkam Al-Jana'iz na Shaikh Muhammad Bin Salih Al-Uthaimin, shafi 213-214] Malamin ya bayyana cewa ""ya kamata gawar mamacin da ya rasu saboda cutar annobar kurona, bai kamata a hannunta ta ga masu ita ba, wai don yi masa jana'izah. Ko kuma a bari wai 'yan uwan mamacin su halarci jana'izar sa, ko ace dole sai sun gan shi,"" ""Dukkaninmu mun sani, babu abin da mamaci yake bukata daga wurin mu illa addu'a,""""Idan musulmi ne, hukumomi su shirya masa jana'izah ta musulunci su binne shi. Idan kirista ne, hukumomi su shirya masa jana'izah irin ta kirista su binne shi, idan dai har da gaske ake yi wurin yaki da wannan annoba,"" ""Ya kamata wani abin da ya faru a kasar Amurka ya zama izina da darasi a gare mu, yadda wasu mutane suka taru suka yi jana'izar dan uwansu da cutar annobar korona ta kashe, amma bayan sun gama jana'izar aka gwada su, sai aka tarar duk sun kamu da wannan cuta, kuma ma sun yada ta zuwa ga wasu. Don haka sai mu kiyaye,""""Wannan shi ne dan abin da zan ce, ina mai rokon Allah kiyaye mu, kuma ya sa mu dace, amin,"" kamar yadda Imam Murtadha Muhammad Gusau, babban limamin masallacin juma'ah na Nagazi-Uvete da ke Okene, Jihar Kogi ya bayyana." https://www.bbc.com/hausa/labarai-52339853 +religion Aung San Suu Kyi: Sojojin Myanmar sun hamɓarar da shugabar da ta goyi bayan yi wa Musulman Rohingya kisan kiyashi "Sojoji a Myanmar sun kifar da gwamnatin shugabar ƙasar Aung San Suu Kyi. Kakakin jam'iyya mai mulki ta National League for Democracy wato (Nasr) ya tabbatar da cewa yanzu haka tsohuwar shugabar na tsare a hannun sojoji, tare da wasu manyan ƴan majalisar zartarwarta. A halin da ake ciki dai ƙasar na tsaka da fama da tankiya tsakanin gwamnatin farar hula da jagororin soja da ke zargin cewa ana tafiyar da al'amura ba daidai ba. Hatta a zaɓen watan Nuwamban bara, jam'iyyar shugabar ta samu isassun kujeru domin kafa gwamnati, amma sojoji sun kafe a kan cewa an yi magudi a zaɓen. An baza sojoji na a kan titunan manyan biranen kasar sanna an takaita hanyoyin sadarwa. Yanzu dai babban jami'i a rundnar sojin kasar shi ne yake jan ragamar mulkinta kuma gidan talbijin na sojin kasar ya sanar da ya sanya dokar ta-baci ta tsawon shekara guda. Ms Suu Kyi ta yi kira ga magoya bayanta da kada su ""amince da wannan"" kuma su ""bijire wa juyin mulkin"". Har zuwa shakearar 2011 sojoji ne ke mulkin Myanmar, kafin daga bisani farar hula suka karba. Da ma can Shugaba Suu Kyi ta taɓa kwashe tsawon shekaru a tsare. Wanne hali ake ciki a yanzu? Sanarwar rundunar sojin ta ce an miƙa mulki ga babban kwamandan sojin ƙasar mai suna Min Aung Hlaing nan take ba tare da ɓata wani lokaci ba. Gidajen rediyo da talabijin na kasar sun kasance a kashe, kuma an katse layukan waya da na intanet. Ana iya hango sojoji na ta faman sintiri fuskokinsu a murtuƙe a kan titunan babban birnin kasar Naypyitaw da kuma babban birnin Yangon. Bayanan da muka samu na baya-bayan nan na tabbatar da cewa sojojin da suka yi wannan juyin mulki sun kafa dokar ta ɓaci a sassan ƙasar baki ɗaya. Kamata ya yi majalisar dokokin ƙasar ta sake zama don tsawaita wa'adin shugabar da aka hambarar, amma yanzu sai dai kawai ace yadda sojojin suka dama haka za a sha." https://www.bbc.com/hausa/labarai-55882165 +religion Wadanne tambayoyi kuke da su a kan Fadar Vatican? Ku aiko da tambayoyinku kan wannan batu, BBC kuma za ta gudanar da bincike tare da kawo muku cikakkiyar makala a kai. Sannan za mu muka saki makalar a ranar kirsimeti. https://www.bbc.com/hausa/labarai-50514191 +religion Sheikh Aminu Daurawa ya bayyana hanyoyin magance matsalar fyaɗe a Najeriya "Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na Najeriya, Sheikh Aminu Daurawa, ya bayyana matakan da suka kamata a dauka domin shawo kan matsalar fyade da ta addabi kasar. A tattaunawarsa da BBC, Sheikh Daurawa, ya jero matakan da suka kamata bi wajen magance wannan matsala, ciki har da haramta wa duk wanda aka samu da laifin fyade rike duk wani mukami na gwamnati. Ya kara da cewa akwai bukatar ""ilimantar da mutane da wayar da kansu. A duba a ga me yake kawo fyaden nan? Su wa ake yi wa? Meye dalilin da ake yin fyaden nan? Sannan kuma wacce hanya za a bi a dakile fyaden nan?"". Latsa bidiyon da ke sama domin kallon karin bayanin Sheikh Daurawa kan wanna batu:" https://www.bbc.com/hausa/labarai-53277014 +religion Bidiyon Ku San Malamanku tare da Sheikh Abubakar Kyari Muhammed "Latsa hoton sama ku kalli bidiyo: Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Abubakar Kyari Muhammed, ya ce ya sha wahala matuka kafin ya haddace wata sura a Al-Ƙur'ani. Malamin ya bayyana haka ne a wata hira ta musamman da BBC cikin shirin nan mai taken ""Ku San Malamanku"". Ya ce surar da ta fi ba shi wuya ita ce Suratul An'am, wadda ita ce sura ta shida daga sama a cikin littafi mai tsarki. Sai dai ya ce Allah ya sahale masa ayar da ta fi bai wa mafi yawan mahaddatan Kur'ani mai girma wuya, wato ayar rabon gado ta .... Yusi kumullahu, wadda take a cikin Suratul Nisa'i. Malamin ya ce babu abin da yake faranta masa rai a rayuwa irin ya ga mutum ya musulunta kuma ya yi ruko da addinin yadda ya kamata. Abin da kuma ya fi bakanta masa rai shi ne ""yadda mutane ke wasa da ilimi, yadda ake ba da fatawa bisa kuskure ba tare da damuwa kan abin da zai faru ba"". A lokuta da dama malamai kan yi fatawoyin da suke ingiza mutane su je su rika yi wa shugabanni tawaye ko wani abu mai kama da haka." https://www.bbc.com/hausa/media-59170094 +religion Ku San Malamanku tare da Malama Zainab Ja'afar Mahmud Adam "Latsa alamar lasifika da ke sama don kallon hira da Malama Zainab Mahmud Adam: Malamar addinin Musuluncin nan da ke Najeriya, Malama Zainab Mahmud Adam, ta ce mahafinta, marigayi Sheikh Ja'afar Mahmud Adam ya yi tasiri sosai a kan fafutikarta ta neman ilimi kuma hakan ba ya rasa nasaba da kasancewarta 'yarsa mace ta farko. Ta bayyana haka ne a wata hira ta musamman da BBC, a kuma cikin shirinmu na ""Ku San Malamanku"". ""Ban sani ba ko don ni kaɗai ce mace a farko tun da misali duk ƴan uwana maza ne a bayana kafin daga baya Allah ya sa aka samu ƴa mace,"" in ji ta. Malama Zainab Mahmud Adam, ta yi karatun nazire a makarantar 'Yan Dutse daga nan ta tafi makarantar Badar da ke unguwar Ɗan Agundi da ke Kano a Najeriya. Daga baya a shekarar 1994, lokacin da Alhaji Yusuf Abdullahi ya gina masallaci haɗe da makaranta wato Usman Bin Affan, sai ya miƙa ta a hannun mahaifinta. Hakan ya sa iyayenta suka koma unguwar Gadon Kaya da ke cikin birnin Kano wadda ta sanya suka koma karatu a makarantar Usman bin Affan, har zuwa matakin sakandare a shekarar 2005. Ta fara karatun Difiloma a makarantar Legal da ke unguwar Gadon Kaya, amma Allah bai kaddara ta kammala ba sai aka mata aure, ta tafi Madina. ""Kafin kammala Sakandare abubuwa da dama da na karanta na addini sun taimaka min sosai fannin addinin Musulunci. ""Misali karatun Daura da shaihin malaminmu Malam Dakta Muhammad Sani Rijiyar Lemo a lokacin yana Jami'ar Musulunci ta Madina, idan suka dawo hutu yana shirya Daura wato karatu mai gajeren zango, a markaz dinshi ta Imam Bukhari,"" in ji ta. Ta kara da cewa: ""Cikin daliban da muka yi karatu da su a wancan lokacin akwai Dr Hamza Aliyu Sakwaya, Sheikh Khamis Nasidi, Barr Zahra'u Ahmad, Mal Amina Sheikh Barnoma, Malama Fatima Usman da sauransu. Ta samu damar halartar karatun kusan kashi uku zuwa huɗu, hakan ya ba ta damar ƙaruwa ta fannin ilimin Islama. Cikin abubuwan da ke sanyata tunawa da mahaifinta akwai lokutan rubuta jarabawa. Ta bayyana cewa ba za ta iya tuna yawan kyaututtukan da mahifinta ya ba ta ba. 'Alƙawarin da mahaifina ya yi mini' Malama Zainab ta kuma bayyana cewa Aikin Hajjin da ta yi na farko alƙawari ne da mahaifinta ya cika mata na cewa idan ta haddace izifi talatin zai kai ta Makkah, wanda kuma ya cika mata wannan buri nata a 2004 tun kafin ta yi aure. Ta ce ba za ta iya tuna irin adadin kyaututtukan da yake yi mata ba tun tana yarinya musamman idan ta samu nasara a jarabawa. Ta bayyana cewa babban abin da ke sawa a yi shiri da mahaifinta shi ne karatu inda ta ce ta yi sa'a kuma Allah ya haɗa ta da miji mai son karatu. Malama Zainab ta ce wasicin da aminin mahaifinta Sheikh Sani Rijiyar Lemo ya yi mata kan ta dage da karatu a Madina kada ta yi wasa da damar da ta samu ya ƙara ƙarfafa mata gwiwa sosai. ""Tun da na isa Madina, ba na tsammanin na yi zama ya kai na wata huɗu ba tare da na shiga makaranta ba, na shiga makaranta ta Tahfizul Ƙur'an daban-daban kuma na yi karatu a wani Markaz wanda na yi karatun difloma tsawon shekara biyu wanda Markaz ɗin na da alaƙa da Jami'atul Ɗayyiba ta garin Madina. ""A nan na yi karatu kuma na kammala difloma a 2010 kuma mun ta ƙoƙari domin ganin an samu damar ci gaba da wannan tafiya ta karatu amma kasancewar jami'ar Madina yan ƙasa ne aka fi ba fifiko domin karatu a wajen, hakan ya sa muka yi ta ƙoƙari amma Allah bai nufa ba,"" in ji ta. Ta bayyana cewa a lokacin sai dai Jami'ar ta buƙaci ta yi abin da ake kira distant learning wato karatu daga gida amma a lokacin sai ta ƙi yarda inda take ganin ba karatu bane da za ta samu fa'ida sosai. Ta ce daga nan sai ta ci gaba da zuwa makarantar hadda wadda take zuwa da yamma a wata makaranta da ke ƙarƙashin jam'iyyar Khairiya ta garin Madina inda tana cikin wannan karatu ne sai malamar ajinsu ta yi aure wanda hakan ya sa ta maye gurbin malamar ajin. Ta ce hakan ne ya sa ta samu wata makaranta da take zuwa da safe domin ci gaba da haddar Al-Ƙur'ani wanda ta ce yinta na daga cikin manyan burikan mahaifinta a kanta. A makarantar ne ta kammala haddar inda kuma da yamma ta ci gaba da zuwa koyarwa har zuwa shekara biyu da wasu watanni kafin ta koma Najeriya. Galibin malaman da suka koyar da mu a wannan makaranta a wancan lokacin kodai malamai ne a Jami'ar Musulunci ta Madina irinsu Farfesa Sheikh Hamad Al Hammad da Farfesa Aliyu Bn Ibrahim Azzahrany. Ta ce a halin yanzu tana ƙoƙarin kammala digirinta na farko a Jam'iar da ke Kano. Kusancin Malama Zainab da mahaifinta ""Duk wanda yake da alaƙa ta kusanci da malam ya san yadda muke da kusanci da shi da irin yadda yake nuna ƙauna da tarbiyya da kulawa musamman a gareni. ""Ban sani ba ko don ni kaɗai ce mace a farko tun da misali duk ƴan uwana maza ne a bayana kafin daga baya Allah ya sa aka samu ƴa mace."" Malama Zainab ta bayyana cewa alaƙarta tsakaninta da mahaifinta ya wuce alaƙa tsakanin uba da ƴa. Ta bayyana cewa rashin mahaifinta ya zama babban giɓi a rayuwarta domin akwai abubuwa da dama da babu wanda zai iya cike mata gurbinsu idan ba shi ba saboda irin kusancin da ke tsakaninsu. Ta bayyana cewa rashin mahaifinta abu ne da ba za ta taɓa mantawa da shi a rayuwarta ba domin ba ta cika son tana magana a kan lamarin ba. Ta ce har yanzu a wani lokacin tana shiga ɗaki ta kulle ta yi ta kuka saboda a cewarta rashi ne da har ta koma ga Allah ba za ta manta da shi ba. Burin Malama Zainab Malama Zainab ta ce tana da buri a kan abin da ya shafi harkar da'awah musamman abin da ya shafi ɓangaren mata. ""Yau ina so na wayi gari na ga Allah ya azurta ni da ilimi mai zurfi da zan yi wa ƴan uwana mata tasiri wurin kawo gyara da sauye-sauye a kan munanan ɗabi'u ko halayya ko rashin tarbiyya a tsakanin mata a kowane mataki na rayuwa,"" in ji ta." https://www.bbc.com/hausa/labarai-59420315 +religion Bidiyon Ku San Malamanku tare da Sheikh Madu Bulamari Danna hoton da ke sama don kallon bidiyon: An haifi Malam Muhmmad Abubakar da aka fi dani da suna Madu Bulamari a kauyen nariku a karamar hukumar bama, ranar 1-1-1959. Kasancewar in da aka haife shi, a kusa da Jamhuriyar Kamaru ne, wanda Kogi ne kadai ya raba su. Sai aka miƙa shi hannun wani shahararren malami Shahararren malami Goni Madu Yachammaye, amma kafin wannan lokacin sai da ya fara karatu hannun kakansa, da ya kai shekara bakwai zuwa takwas ne aka miƙa shi hannun Gono. https://www.bbc.com/hausa/media-61596382 +religion Ku san Malamanku tare da Ustaz Adam Muhammad Murtadha "Latsa alamar lasifika da ke sama don kallon hira daUstaz Adam Muhammad Murtadha: An haifi Ustaz Adam Muhammad Murtadha a karamar hukumar Ajingi da ke Jihar Kano a Arewacin Najeriya a shekarar 1978. Malamin ya soma karatunsa na allo a wurin mahaifinsa, Malama Murtala, wanda shi ma malamin addinin Musulunci ne. Daga bisani ya koma Unguwar Bachirawa da ke cikin birnin Kano, inda ya yi karatu a wurin wani fitaccen Malami mai suna Malam Garba. Ustaz Adam ya kara da cewa bayan rasuwar mahaifinsa ya tafi Gombe wurin kakansa mai suna Malam Abdulhamid wanda aka fi sani da Malam Karami inda ya ci gaba da karatun Alkur'ani. ""Baya da Allah ya ba ni ikon samun karatun Alkur'ani, sai kuma na shiga makarantar gaba da firamare mai suna Government Arabic College, Gombe, inda na kammala ta a 2007.Daga nan kuma na ci gaba da karatu a wurin Malamai, sanna kuma na yi Diploma a fannin Larabci,"" a cewarsa. Ustaz Adam ya bayyana cewa babban abin da ya fi ba shi wahala a wajen karatun Alkur'ani shi ne ""yanayin yadda zan ci na sha da kuma wurin kwanciya"" yana mai cewa ko a yanzu kowa ya san irin halin da almajirai suke shiga. Ya kara da cewa yawace-yawancen bara na cikin abubuwan da suka ba shi wahala ganin cewa kafin ya bar gidansu bai rasa abinci da abin sha ba. Malamin ya ce babban abin farin ciki da ba zai manta da shi ba shi ne ""ranar da na dira kasar Saudiyya na yi arba da Ka'abah."" Sai dai ya ce babban abin da ya bata masa rai shi ne yadda aka dakatar da shi daga limanci sakamakon wasu kalamai da ya yi masu zafi game da yadda ake tafiyar da al'amuran Najeriya. Ustaz Adam ya bayyana cewa ana kiran sa da suna Albanin Gombe ne saboda ""lokacin da nake karatu akwai malaman da na tasirantu da karatunsu, amma daga cikin wadanda suka fi tasiri a rayuwata shi ne Sheikh Muhammad Awwal Albany, domin kuwa har ta kai na haddace kaset din karatunsa kamar yadda ake haddace Fatiha."" ""Har ya kai nakan zauna na yi irin yadda ya karantar da wani littafi ko ya bayar da wata lacca, kamar shi ne yake gabatarwa. To, galibi idan na zo bayani nakan ce 'Malam Awwal Albany ya ce kaza, ko kuma ya bayyana kaza; to, sauran dalibai da abokaina na karatu ya suka rika kira na da Albani'. Har ta kai ga ni da wasu dalibai mun kai masa ziyara a Zaria ana saura kusan makonni uku ya rasu. A nan ne shi da kansa ya ce lallai na tabbata Albany na Gombe"", in ji malamin. Malamin ya ce a halin yanzu yana da mata biyu da 'ya'ya goma. Ustaz Adam ya ce yana matukar son cin wake-da-shinkafa da dan wake ""musamman idan aka sa masa kwai a ciki da ganye.""" https://www.bbc.com/hausa/labarai-60684781 +religion Sheikh Ahmad Bamba, 'Kala Haddasana, na Kano ya rasu "Allah Ya yi wa babban malamin addinin nan na Kano Sheikh Ahmad Muhammad Ibrahim Bamba, wanda aka fi sani da Kala Haddasana rasuwa a yau Juma'a. Wasu iyalansa ne suka tabbatar wa da BBC Hausa labarin rasuwar. Fitaccen malamin ya yi fice ne a wajen karatuttukan Hadisi, inda a da can yake karantarwar a Masallacin BUK amma daga baya ya bude nasa wajen mai suna Darul Hadis. Malamin ya rasu ne bayan gajeriyar rashin lafiya inda ya kwana ɗaya a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano. Iyalan sun sanar da cewa za a yi jana'izar malamin a Masallacin Darul Hadis da ke unguwar Tudun Yola a birnin Kano bayan Sallar Juma'a. Wani daga cikin ƴaƴansa Abdul ya shaida wa BBC cewa ya kusan shekara 82, don an haife shi ne a shekarar 1940. Kala Haddasana kamar yadda aka fi saninsa da shi ɗan asalin ƙasar Ghana ne kuma a can aka haife shi. ""Ya dawo Najeriya ne bayan da ya yi karatun digirinsa a Saudiyya, sai ya koma Najeriya ya fara koyarwa a Jami'ar Bayero ta Kano har ya yi digirin-digirgir. ""Ya koyar a fannin Islamic Studies kuma ya jima yana koyarwar,"" a cewar ɗan nasa. Malamin ya bar yara 28 zuwa 30 kamar yadda ɗan ya shaida mana." https://www.bbc.com/hausa/labarai-59907798 +religion Aksum: Garin da aka haramta gina masallaci "Mabiya addinin Kirista Kibdawa a kasar Habasha suna kallon birnin Askum da mai tsarki, saboda nan ce mahaifar Sarauniya Sheba wadda aka amabata a cikin littafin Injila, da kuma akwatin gwal da Kibdawa suka yi amanna ya kunshi wasu muhimman abubuwa na Ubangiji. Sun yi amanna akwatin ya kunshi abubuwa guda 10 masu muhimmanci wanda suka ce Allah ya bai wa Annabi Musa AS wanda ya ke cike da matakan tsaro. Wasu kungiyoyin Musulmai na gangamin ganin an ba su damar gina masallaci a birnin, batun da shugabannin Kirista suka yi watsi da shi tare da shan alwashin da su ga wannan rana da za a gina masallacin gara a ce sun bar duniya. Wani babban limamin Kibdawa Godefa Merha ya ce suna kallon birnin Askum mai tsarki, tamkar yadda Musulmai ke kallon birnin Makka. Ya kara da cewa ''kamar yadda aka haramta gina Coci a birnin Makka da Madina haka mu ma muka haramta gina masallaci a Askum mai tsarki''. ""Aksum waje ne mai cikakken tsarki, ba za mu amince a gurbata mana shi ba"", in ji Mr Godefa, wanda shi ne mataimakin majami'ar Our Lady Mary of Zion da ke birnin. Shekara da shekaru kenan da Kireistoci Kibdawan suka ki amincewa da gina masallatai a birnin, amma a yanzu lamarin ya fi kamari saboda kiraye-kirayen sun karu. Gangamin da ya ke kara fadada an yi masa taken ''Adalci ga Musulman Aksum'', da kuma bukatar su ma a ji muryarsu su na kiran sallah cikin manyan lasifa. Mabiya addinnin Musulunci da Kirista sun yi amanna da cewa Musulmai ne suka same su a masarautar Aksum, wanda daya ce daga cikin manyan masarautu a duniya. Musulmai sun isa jim kadan bayan bayyanar addinin Musulunci a shekarar 600AD a matsayin 'yan cirani da suka gujewa kisan gillar da kafiran Makka ke musu a wancan lokacin. Kuma sun karbe su hannu biyu-biyu, tare da ba su damar gudanar da addinin Musulunci a bainar jama'a wanda nan ne wuri na farko da ya aminta da hakan a wajen yankin Larabawa. Kashi 10 cikin 100 na mutum 73,000 na birnin mabiya addinin musulunci ne, yayin da Kiristoci Kibdawa suka dauki kashi 85, sai kuma kashi 5 sauran mabiya addinin Kirista. 'An tilastawa Musulmai yin sallah a waje' Wani mazaunin birnin mai suna Abdu Mohammed Ali, mai shekara 40, ya ce shekara da shekaru zuriyar gidansu na karbar hayar gidaje ne daga Kirista dan samar da masallacin da za su yi sallah da sauran ibada. Ya kara da cewa ''muna da masallatai 13 da dukkansu haya muke biya. A duk ranakun juma'a idan mukai kiran sallah ta amfani da lasifika, sai Kiristoci su ce wai mun raina Nana Maryam mahaifiyar Annabi Isa AS''. Shi ma wani likitan gargajiya Aziz Mohammed, da yake zaune a birnin sama da shekara 20, ya ce a wasu lokutan akan tilastawa Musulmai yin sallah a bainar jama'a ba cikin masallaci ba. ""Mabiya addinin Musulumci da Kirista na zaune a wajen nan shekara da shekaru ba tare da anji kansu ba, kuma ba a taba hana Musulmai yin sallah ba. Amma a yanzu lamarin ya sauya, yawancinmu akan hanya muke sallah don haka muke bukatar a ba mu damar gina masallaci na dindindin,'' inji Aziz. 'Ya kamata mu zauna lafiya' Sama da shekara 50 da suka gabata an taba samun matsala irin wannan a lokacin mulkin Haile Selassie. Daya daga cikin iyalan masarautar ya sanya Musulmai suka gina masallaci nisan kilomita 15 daga garin Wukiro-Maray. A lokacin da BBC ta kai ziyara garin, wanda mabiya addinin Kirista suka fi rinjaye, mun gana da wata mace mai suna Keriya Mesud wadda ke dafawa Musulmai da ke ibada abinci. Ta nuna mana masallatai biyar da suke Wukiro-Maray inda nan ne kadai suke da sukunin gudanar da ibada. Ta ce duk da suna bukatar masallaci a birnin Aksum amma babu yadda za su yi, tun da suna son zaman lafiya dole su hakura. Mista Godefa ya yi amanna sauran kabilun da ke yankin na zaman lafiya, sannan babban amininsa Musulmi ne komai tare suke yi tun daga zuwa gidan biki, radin suna ko jana'iza. Sannan ana ganin mabiya addinin Musulunci da ke sauran biranen kasar Habasha suna taimakawa gangamin da ake yi a yanzu na gina masallaci a Aksum. Sai dai ya yi rantsuwa kan Kibdawa ba za su taba karya alkawarin da suka yi wa magabatansu ba kan cewa ba za su aminci a gurbata birnin ba, wanda kuma suke ganin gina masallaci tamkar gurbata addininsu ne. Mista Godefa ya ce ""Matukar muka bari aka gina masallaci a birni mai tsarki mutuwa za su yi, saboda ba a taba yin hakan ba don haka ba za mu amince ayi ba. Ya zama dole mu ci gaba da mutunta abin da muka gada daga iyaye da kakanninmu na shekaru aru-aru''. Kiristoci Kibdawa sun yi amanna da cewa bai kamata aji komai a birnin baya ga wakokin yabo da bege da addu'o'in addininsu da aka saba ji tun bayan gina Aksum shekara 7,500 da suka gabata. Shi ma wani mai wa'azin Kirista Amsale Sibuh ya bayyana cewa ""Duk addinin da bai amince da haihuwar Is al-Masiyu ba, bai amince da wankan tsarki na mabiya Kirista ba, da mutuwa, da tashin Annabi Isa, da cetonsa ba, da sake dawowarsa, to ba za mu amince da shi ba. Idan muka bari aka taka addininmu lallai za mu tabe, mu kuma ba ma fatan hakan''. Jami'an gwamnati sun ki cewa uffan kan batun gina masallacin, inda suka ce ba za su tsoma baki kan abin da ya shafi mabiya addinan biyu ba saboda sun dade suna zaune tare cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya don haka su sasanta kansu. Kiristoci Kibdawa na ganin gwamnatin kasar Habasha da Firaminista Abiy Ahmed ke jagoranta, wanda mahaifinsa Musulmi ne, mahaifiyarsa kuma Kirista, zai shiga tsakani da fatan zai kare martabar birnin Aksum mai tsarki daga tabewa. Ya yin da a bangare guda Musulmai ke ganin za su kara matsa kaimi don samun biyan bukata. Haka kuma wata kungiyar Musulmai a kasar tana shirin gudanar da babban taro domin tattauna batun, suna masu cewa mabiya addinan biyu ya kamata su amince da hakan, suna fatan ganin Kiristoci Kibdawa sun taimaka wajen gina masallacin." https://www.bbc.com/hausa/labarai-48753654 +religion Bidiyon Ku San Malamanku tare da Dr Jamil Muhammad Sadis Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon: A wannan makon shirin Ku San Malamanku ya tattauna ne da Dr Jamil Muhammad Sadis. https://www.bbc.com/hausa/media-57930138 +religion Ramadan: Abu 10 ga mai neman dacewa da daren Laylatul Qadr Latsa alamar lasifika da ke sama domin sauraron Dr Bashir Aliyu Umar A daren Lailatul Qadri da ke goman karshe na watan azumin Ramadan ne Allah ubangiji ya saukar da Alkur'ani mai girma, abin da ya sa Musulmi suke neman dacewa da wannan daren. Duk da cewa babu tabbacin wani dare da aka ware da cewa shi ne daren na Lailatul Kadri, amma hadisai da malamai sun nuna cewa daren yana wakana ne a mara ta karshen kwana goma na watan Ramadan. Dararen mara dai kan fara tun daga daren 21 da daren 23 da 25 da 27 da kuma 29. Hakan ne ma ya sa wasu Musulmin yin tsumbure dangane da ibadun da ake son yi wato idan sun yi wannan dare sai su huta a wani daren inda za su sake kaimi a daren mara na gaba. To sai dai malamai sun ce ba a yi wa ubangiji wayo, inda suke shawartar masu neman dacewa da su raya dukkanin daren goman karshen azumin Ramadan. Dr Bashir Aliyu Umar, limamin masallacin Alfurqan da ke birnin Kano, ya lissafa wasu abubuwa guda 10 da ya ce su ne jagoran mai neman dacewa da daren Lailatul Kadri, kamar haka: https://www.bbc.com/hausa/labarai-52642202 +religion Matakan da ake bi wajen buga Al Ƙur'ani "Kamfanin Darul Mus'haf na ɗaya daga cikin kamfanonin buga Al Ƙur'ani mafi girma a nahiyar Afrika. Kamfanin na daya daga cikin gine-gine mafiya girma a birnin Khartoum na ƙasar Sudan. A shekarar 1994 ne aka bude gidauniyar kafa kamfanin Darul Mus'haf kuma ta samu tallafi daga bangarori da dama a ciki da wajen Sudan. Kamfanin ya samu kafuwa a shekarar 2001 da burin samun lada ta hanyar samar da Al Ƙur'ani ga miliyoyin Musulmi 'yan Afrika da ke fama da talauci ƙarƙashin International Univerity of Africa ko Jam'atul Ifriƙiyyal Alamiyya. Kamfanin Darul Mus'haf na buga Al Ƙur'ani aƙalla 100,000 duk wata. Bugun rubutun Al Ƙur'ani mataki-mataki ne, daga shirya rubutun a komfuta zuwa wurin ɗinkewa. Shirya rubutu da zayyanar shafuka Wannan shi ne mataki na farko, inda ake shirya yadda rubutun zai fito a shafukan Al kur'anin da irin kwalliyar da za a yi a jikinsa a kan komfuta. AbdelRaazeq Yusef, babban jami'i a kamfanin ya bayyana cewa akwai salon rubutu da zayyana iri iri da su ke amfani. ""Wasu daga cikin waɗannan salon mun samo su ne daga Saudiyya, wasu daga Syria wasu ma daga Indunesiya,"" a cewarsa. ""Don haka mu kan zaɓa wanda mu ke so da kuma irin launin da za mu yi kwalliyar da shi, ko ja ko ruwan ƙwai ko kalar makuba,"" in ji shi. Sai dai ya ce wannan iyakar kwalliyar ko zayyanar shafukan ne kawai. ""Rubutun Al ƙur'ani dole da baƙar tawwada ake yin sa, haka tsarin ya ke. Don shi mutane su ka fi jin daɗin karantawa,"" in ji AbdelRaazeq Yusuf. Haka kuma, a wannan matakin ne ake aikin bitar rubutun da zai fito a shafukan Al Ƙur'ani. AbdelRaazeq ya ce akwai malami a ƙalla guda 10 zuwa 11 da ke aikin duba rubutun. Amma ba a lokacin guda su ke yi ba. ""A matakin farko mu na ba malamai biyar ɗaya bayan ɗaya su duba rubutun. Idan wannan ya duba sai ya ba wannan,"" in ji shi. Ya ce idan wadannan malaman zubin farko sun duba kuma sun yi na'am da shi ko kuma sun yi gyare gyare a kai, sa a ba wasu jerin malamai shidda kuma su ma su sake dubawa. Kuma ko wanne daga cikin waɗannan malaman za su sa hannu cewar sun duba iyakar iyawarsu. Ana yin haka ne duk don a guje wa samuwar wani kuskure a rubutun ayoyin na littafin mai tsarki. Bayan wannan matakin ne kuma sai a je mataki na gaba, wato matakin gurza rubutun daga na'urar gurzawa. Matakin gurza rubutun Al Ƙur'ani A wannan matakin, akwai wata na'ura da ke aiki da kemikal da ƙaro da ruwa inda ake sa wata takarda mai kauri wacce ke ɗauke da zayyanar da ake so. A wannan matakin ne kuma ake zaɓar launin da zayyanar za ta fito. Haka kuma, baya ga takardar mai kaur akwai wani shafi na ƙarfen aluminium mai ɗauke da kwalliyar da ɗigon ayoyi da ke fitowa a kan shafukan Al Ƙur'ani. Don haka ana ɗora shafin ƙarfen ne a kan takardar mai kauri don ta naɗi rubutun da ke jiki. Ita kuma da ita ake amfani wurin fitar da zayyanar a kan ainihin shafin AlƘur'ani. A nan, akwai na'urori biyar a jejjere kuma a haɗe da juna. Ko wacce ta dogara da ɗayar. A na'urar farko a na shirya takardun da rubutun Al Ƙur'anin zai fito a kai. Takardun manya ne masu kimanin faɗin sentimita 50 a kan ko wacce ana samun shafin madaidaicin Al Ƙur'ani 16. Na'urar ce ta ke shirya takardun sannan tana fitar da su ɗaya bayan ɗaya tana aikawa da su na'ura ta gaba. Ita kuma tana ɗauke da wani sinadari da ke goge takardan kuma yana sa ta ƙyalli. Daga nan ne sai takardar ta gangara na'ura ta gaba wadda ke ɗauke da tawaddar da ke yi rubutu a kan shafukan. A wannan matakin ne rubutu da kwalliyar jikin shafin ke fitowa. Sai na'ura ta gaba mai dauke da gam wadda ke harhada takardun wuri guda. Sannan na'ura ta ƙarshe mai fitar da takardun bi da bi, wato shafi biye shafi. Yanka takardu da kuma ɗinke su Da zarar an fitar da takardun daga na'urar da ke jera su, akwai wata babbar na'ura wadda ke ɗauke da manyan ƙarafuna masu kaifin gaske. Ana kiran ɗakin da wannan na'ura take da suna tiyata. Wadannan ƙarafunan ne ke yanka shafukan nan 16 zuwa dai dai girman da ya dace sannan ta shirya su shafi bayan shafi. Daga nan kuma akwai na'ura ta daban wadda aikinta shi ne dinkewa ko liƙe takardunsu zama kundi guda. A wannan matakin, akwai abubuwan da da hannu ake yinsu, kamar like bangon Alƙur'anin. Akwai ma'aikata na musamman da aikinsu kenan, wato amfani da gam wajen harhaɗa shafukan AlƘur'anin. A lokacin bugawa, wani lokaci a kan samu shafukan da ke fitowa ba daidai ba ko kuma a samu kuskure a bugun shafukan. Akwai ma'aikatan da aikinsu shi ne duba irin waɗannan kuma Idan aka samu irin haka, a kan ware waɗannan shafukan a tara su a wani ƙaton bokiti sannan daga baya a ƙona su. A kamfanin Darul Mus'haf, Akwai nau'ikan girman Al Ƙur'ani biyu wato da babba da ƙarami. Kuma a Darul Mus'haf a na aiki ne da ruwayoyi biyar amma yanzu waɗanda mu ke bugawa su ne ruwayar Duri da Hafs da Warshu. Babban jami'in kamfanin, AbdelRaazeq Yusef ya ce suna alfahari da kamfanin na Darul Mus'haf ko ba komai, ya ce miliyoyin Musulmi a faɗin Afrika na karanta Al Ƙur'anin da suka buga. Kuma ya ce a baya bayan nan ma, sabuwar shugabar Tanzania, Samai Suluhu Hassan ta sha rantsuwar shugabancin ƙasarta da ɗaya daga cikin Al Ƙur'anin da aka buga a wannan kamfani." https://www.bbc.com/hausa/media-57094835 +religion Yau ce ranar ƙarshe ta fitar da Zakkatul Fitr Yau 1 ga watan Shawwal na shekarar 1442 wato ranar da al'ummar Musulmi a duniya ciki har da Najeriya da Ghana ke gudanar da Sallar Idi bayan kwashe kwanaki 30 suna azumin watan Ramadan. Wani babban tsagi na ke cikasa ladan mai azumi shi ne zakkatul Fitr ko kuma Zakkar Fidda kai inda masu hali ke fitar da abinci su bai wa marasa shi domin samun zarafin abincin Sallah. Tundai daga ranar 27 ga watan Ramadan ake fara fitar da wannan zakka har zuwa kafin a fita sallar Idi. Shin ko mene ne hukuncin wanda bai fitar da zakkar ba har aka je sallar Idi aka koma? Tabbayar kenan da Buhari Muhammad Fagge ya yi wa limamin masallacin Apo a Abuja, Sheikh Muhammad Nuruddeen wanda aka fi sani da Digital Imam. Latsa hoton hatsi da ke sama domin sauraren hirar. https://www.bbc.com/hausa/labarai-57096193 +religion Bidiyon Ku San Malamanku tare da Malam Yakubu Musa Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon: Malam Yakubu Musa, shi ne shugaba na farko na majalisar Shari'ar Musulunci a Najeriya mai suna Supreme Council for Shari'a in Nigeria kuma masanin Shari'a wanda ya yi karatu a wurare daban-daban. Malamin wanda ɗan ɗariƙar Tijjaniyya ne a baya, shi ne shugaban ƙungiyar Izala na Jihar Katsina ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton. An haifi Yakubu Musa a garin Gagaryaga da ke cikin Ƙaramar Hukumar Gwaram - ta Jihar Jigawa a yanzu - ranar 1 ga watan Janairun 1950. Ya yi karatun Alƙur'ani a garuruwan Kano da Jigawa da Katsina da Jos. Yanzu mazaunin Katsina ne, inda ya shafe kusan shekara 40 a garin. https://www.bbc.com/hausa/labarai-57276589 +religion Ku San Malamanku tare da Malam Modibbo Tukur "Latsa hoton sama ku kalli bidiyo: Shirin Ku San Malamanku na wannan makon ya tattauna da Malam Muhammad Mahmud Modibbo Tukur Gombe. An haifi malamin a shekarar 1966 a garin Gombe kuma ya fara karatu a hannun mahaifinsa Modibbo Tukur, wanda shi ma malami ne. A shekarar 1973 zuwa 74 mahaifinsa ya kai su makarantar Islamiyya a garin Manzo tare da 'yan uwansa. A hirasa da BBC, malam Muhammad Mahmud ya bayyana cewa ya fara karatun allo da Alkura'ni mai girma lokacin yana da shekara bakwai. ""Na yi karatun Alkur'ani a gaban mahaifina, amma a wasu lokutan idan almajirai suka yi masa yawa yakan hada mu da wasu malamai su rika lura da mu,'' in ji shi. ''Shehu Manzo babban malami ne kuma abokin mahaifinmu ne da suke aikin da'awa tare, inda daga bisani Shehu Ibrahim Khaulaha y aba shi izinin kafa makarantar Islamaiyyar a nan garin Gombe."" Bayan bullo da shirin nan na bayar da ilimin firamare kyauta da ake kira UPE lokacin mulkin Obasonjo a shekarar 1976, malamin ya ce shi da yayansa aka kai makarantar firamare da ake kira Jan kai, inda suka fara karatu har ya zuwa shekarar 1981 lokacin da suka kammala firamare. Malam Muhammadu Modibbo ya ci gaba da karatun addini na cikin gida tun daga Kawa'idi, da Ishimawi da Iziyya zuwa Risala, da su Kurdabi da Hadisi da kuma Taudihi wanda ya ce duk a gaban mahaifinsu suka koya. Kazalika, mahaifin nasu ya sake hada su da wasu malamai daban don ci gaba da daukar karatu. ""Malaman sun hada da Alhaji Umaru Gojude wanda limamin masallaci ne, akwai kuma Alhaji Bashir Modibbo Jobbo, sai malam Ibrahim Khalil. Abin bakin cikin da na farin ciki Malamin ya kuma ce babban abin bakin cikin da ba zai taba mantawa da shi ba shi ne mutuwar mahaifinsa wanda shi ne ke rike da kowa. ""Tunanin rana tsaka muka rasa shi, yadda abubuwa za su mike bayan rasuwarsa ba karamin tashin hankali ba ne a gare mu. Lallai wannan babban abin bakin ciki ne da ba zan manta da shi ba.'' Amma kuma, babu abin da malamin ya ce ke dadada masa rai irin ya ga matasa suna karatu, suna kuma sana'ar da za su dogara da kan su. Haka nan in ji malamin, samun cikawa da imani na cikin manyan burikan da yake da su a rayuwa. Malamin ya kuma ce yana matukar son abincin nan na Bare-bari wato burabusko. Ta bangaren iyali kuma, yana da mata, da 'ya'ya mata bakwai da maza biyar." https://www.bbc.com/hausa/shirye-shirye-na-musamman-61179155 +religion Ramadan 2022: Abubuwa 11 da suka kamata mai azumi ya mayar da hankali a kai "Latsa wannan alamun hoton da ke sama domin kallon jawabin: Sheikh Jabir Maihula wanda malamin addinin Musulunci ne a Najeriya ya ce lissafa wasu abubuwan da ya ce ya kamata duk mai azumi ya mayar da hankali a kansu. Ya ce ""ma'anar azumi ita ce barin cin abinci da shan abinsha da kuma barin jima'i daga lokaci kafin fitowar alfijiri zuwa faduwar rana."" Sai dai kuma malamin ya yi karin haske dangane da wasu abubuwa da ya ce masu azumi na yin ganganci yayin da suke yin su." https://www.bbc.com/hausa/media-60946381 +religion Coronavirus: An bukaci Musulmin duniya su dinga Salloli a gida lokacin Azumi "Babbar majalisar koli ta Malamai a Saudiyya ta bukaci al'ummar Musulmin duniya a kasashen da ke fama da cutar korona su yi Sallah a gidajensu lokacin watan Azumin Ramadan. Kamfanin dillacin labaran Saudiyya na SPA ya ambato majalisar manyan malaman kasar a cikin wata sanarwa na cewa ya kamata musulmi su kauracewa duk wani taron jama'a da zai kara yaduwar cutar. Sanarwar majalisar malaman ta ce: ""Ya kamata musulmi su fahimci cewa kare rayuwa babbar ibadah ce da za ta kara kusantarsu da Mahalicci."" ""Ya kamata musulmi su zama abin misali ta hanyar gudanar da addininsu yayin da suke kiyaye matakan kariya da hukumomi suka dauka a kasashen da suke,"" in ji sanarwar. Sannan majalisar ta bukaci musulmi su kauracewa duk wani taro a lokacin buda-baki ko sahur a cikin Azumi. 'Yan kwanaki suka rage al'ummar Musulmi su fara Azumin Ramadan, a cikin wannan yanayi da aka killace kusan al'ummar duniya saboda annobar cutar korona inda sama da mutum miliyan biyu suka kamu da cutar a duniya. Kusan mutum 10,000 suka kamu da cutar a Saudiyya, yayin da ta kashe mutum 97 kawo yanzu. Tuni hukumomin Saudiyya suka hana shiga Makkah da Madina, da ma Riyadh babban birnin kasar, a kokarin da hukumomin kasar ke yi na hana yaduwar Covid-19. Ana tababa kan yiyuwar gudanar da aikin hajji a bana, yayin da gwamnatin Saudiyya ta nemi kasashen duniya su dakatar da karbar kudaden jama'a domin zuwa aikin Hajji, a yayin da annobar cutar korona ke ci gaba da mamaye duniya." https://www.bbc.com/hausa/labarai-52346932 +religion Ku San Malamanku tare da babban limamin Jigawa, Dr Abubakar Sani Birnin Kudu "Babban limamin Masallacin Juma'a na Dutse da ke jihar Jigawa a arewacin Najeriya Dr Abubakar Muhammad Sani Birnin Kudu ya ce mutane da yawa ba su fahimci Sheikh Ibn Taimiyyah ba kan aƙidunsa. Dr Abubakar ya faɗi hakan ne a hirarsa da BBC Hausa a shirin Ku San Malamanku, inda ya jaddada cewa Sheikh Ibn Taimiyya mutum ne mai son zaman lafiya. Yana wannan magana ce bayan da aka yi masa tambaya kan ko wane malami ne ya fi tasirantuwa da shi a rayuwarsa, sai ya ce Ibn Taimiyyah. ""Malami ne da ya iya bibiyar mas'ala tare da warware ta ta hanyar bin Al-Ƙur'ani da Sunnah. ""Ana koyon tausayin al'umma da haƙuri da wanda ya saɓa maka a wajen Ibn taimiyya, saɓanin yadda aka fi yaɗa wa a duniya cewa tunaninsa ne ya jawo abubuwan tashin hankalin da ke faruwa a duniya."" Dr Abubakar ya ƙara da cewa ""da an fahimce shi za a gane babu mai yi wa abokan gabarsa adalci irin Ibn Taimiyyah. Wadanda suka yi masa karatu daga nesa ko na siyasa ne suke masa wancan kallon,"" a cewar babban malamin. Da aka yi wa malam tambaya kan ko kyautar da ta fi ba shi mamaki sai ya ce ita ce wacce ɗaya daga malamansa a Madina Malam Muhammad Bin Abdullah Zarban al-Gamidi ya yi masa ta gaba daya litattafan ɗakin karantunsa. A cewar Malam Abubakar, malamin nasu wanda tsohon limamin Masallacin Ƙuba ne a Madina ya aiko masa da litattafan wadanda sun kai manyan kwalaye 133. An haifi Dr Abubakar Muhammad Sani Birnin Kudu ranar 7 ga watan Janairun 1965. Ya yi makarantar firamare a Birnin Kudu daga shekarar 1971 zuwa 1978, daga nan ya je makarantar sakandare ta Government College da ke Kaduna daga shekarar 1978 zuwa 1983. Bayan kammala sakandare sai ya fara aiki a makarantar haɓaka aikin noma da rayuwar al'umma daga 1983 zuwa 1984 a matsayin mai buga tafireta. Bayan wani lokaci sai ya samu damar ci gaba da karatun difloma a Zaria a fannin akanta daga 1984 zuwa 1986. A zamansa na Zariya ne ya samu damar yin karatun addini a wajen malaman zaure irin su Malam Muhammad Sani Gummi, limamin Masallacin Juma'a na Ɗan Ja a Kongo wanda ya yi karatun Risala a wajensa. Sannan ya karanta Ahalari da Iziyya a wajen Malam Muhammadu Bazamfare a Gyallesu. Tun a lokacin ya fara jan mutane sallah inda malam ke ƙaddama shi. Ya koma birnin kudu a 1987 sannan daga baya ya koma ya samu aiki a KNARDA a matsayin book keeper har tsawon shekara hudu. Daga baya ya samu gurbin yin digiri a Jami'ar Bayero ta Kano, sai dai shekararsa ɗaya kawai sai ya samu gurbin karatu a Jami'ar Musulunci ta Madina a shekarar 1992. Hakan ya faru ne bayan zuwan Malaman Daura daga Madina zuwa Kano a 1991 inda aka yi musu jarrabawa ya kuma ci. Malam ya ce wannan ne lokaci mafi farin ciki a rayuwarsa saboda irin ingancin karatun da Jami'ar Madina ke da shi, sannan kuma a birnin da Manzon Allah SAW ya rayu, ga kuma malamai masu ilimi. ''Farin cikin hakika ba na wasa ba ne,'' in ji malam. Malam ya ce ba zai manta da Kuruciyarsa ba don ta kasance mai cike da neman ilimi da wasanni irin na yara kamar ƙwallo. Ya ƙware ne a fannin shari'a a Saudiyya tsawon shekara hudu na digiri. Ya karancin fannin da'awa da aƙida a digiri na biyu da digirin-digirgir. Malam ya ce a Madina ya koyi Larabci sosai idan aka ɗauke karatun Nahawu da ya yi na zaure a Birnin Kudu. Sannan a Madina ya yi haddar Al-Ƙur'ani. Bayan dawowarsa daga Madina a 2010 ya yi aiki a matsayin mataimakin darakta a hukumar kula da harkokin addinin Musulunci ta jihar Jigawa, sannan Sarkin Dutse ya ba shi limanci a babban masallacin garin. Daga baya ya samu aiki a Jami'ar Ahmadu Bello Zariya tun daga 2011 zuwa yanzu a sashen ilimin addinin Musulunci. Sai dai a bara ne gwamnan Jigawa Badaru Abubakar ya ba shi babban sakatare na ma'aikatar ilimi ta jihar a matsayin aro. Har yanzu kuma shi ne babban limamin Masallacin Juma'a na Dutse. Yana da mata uku da yara 15, babban ɗansa ma ya kammala karatun digiri na biyu a Madina." https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-55354423 +religion Indiya: An kama wani Musulmi kan yunƙurin 'Musuluntar da budurwarsa ƴar addinin Hindu' "'Yan sanda a jihar Uttar Pradesh sun kama wani mutum da ake zargi da ƙoƙarin Musuluntar da wata mata 'yrn addinin Hindu. Shi ne mutumin farko da aka kama ƙarƙashin wannan doka da ke shirin kama masu ""soyayya don jihadi"" - wani lafazi da masu tsattsauran ra'ayin addinin Hindu ke zargin mazajen Musulmi da su domin auren matansu. Wannan doka ta janyo ce-ce-ku-ce, abin da masu suka suka kira nuna ƙin jinin Musulunci (Islamophobic). A ƙalla wasu jihohi huɗu na Indiya sun fara ƙaddamar da wannan ƙudurin doka. 'Yan sanda Uttar Pradesh sun tabbatar da kamun a shafinsu na Twitter a ranar Laraba. Baban matar ya shaida wa BBC Hindi cewa ya shigar da ƙarar ne saboda matsawa yarinyar da mutumin ya yi tare da yi mata barazana. An yi zargin cewa mutumin yana soyayya da matar ne sai ta yi aure da wani mutum a farkon wannan shekara. 'Yan sanda sun faɗa wa BBC cewa iyalan matar sun shigar da ƙarar ne suna zargin an sace yarinyarsu shekara ɗaya baya, amma an yi watsi da ƙarar ne bayan an gano yarinyar kuma ta musanta zargin. Bayan an kama shi a ranar Laraba, an aike da shi gidan yari na kwana 14, sai dai ya shaida wa manema labarai cewa bai aikata laifin komai ba kuma ""ba shi da alaƙa da matar"". Hukuncin dokar dai shi ne zaman gidan yari na shekara 10, kuma ba a bayar da belin laifin. Mecece dokar ""soyayya don jihadi""? A watan Nowamba, jihar Uttar Pradesh ita ce ta farko da ta fara amincewa da ƙudurin doka kan ""Tilastawa"" ko kuma ""Yaudara"" da sunan sauya wa mutum addini. Bai zama dole ta wuce jihohi huɗu ba - Madhya Pradesh da Haryana da Karnataka da kuma Assam - kuma dukansu suna buƙatar gabatar da doka kan ""soyayya don jihadi"". Duka waɗannan jihohi biyar jam'iyyar BJP mai mulki ce ke jagorantarsu, waɗanda ake zargi da kafa dokar ƙin Musulmai. Masu suka sun kira wannan doka ta cin zarafi, wasu na nuna damuwa kan cewa dokar za ta iya janyo ana cin zarafin mutane, yadda mutane ke amfani da soyayyar jihadi a matsayin wani ikirarin laifi, wanda a hukumance ba a yarda da shi ba. Masu sukar jam'iyyar BJP sun ce matsalar addini na ƙaruwa tun lokacin da Firaminista Narendra Modi ya karɓi mulki a 2014. Tun a baya dama a kan tantance auren Musulmai da 'yan addinin Hindu amma wanda ake yi a bayan nan ya ɗauki wani salo na daban." https://www.bbc.com/hausa/labarai-55170182 +religion Dalilin da ya sa muka kori Sheikh Nuru Khalid daga limaci "Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon: Sanata Sa'idu Muhammad Dansadau shugaban kwamitin Masallacin Rukunin Gidajen Yan Majalisar Najeriya na Apo, ya ce sun kori Sheikh Nuru Khalid daga limancin masallacin gaba ɗaya. Sanata Dansadau ya shaida wa BBC Hausa cewa sabon matakin ya biyo bayan dakatarwar da aka yi wa Sheikh Khalid din ne a ranar Asabar 2 ga watan Afrilun nan. A wata wasiƙa da kwamitin masallacin ya fitar a ranar Litinin mai ɗauke da sa hannun Sanata Dansadau da aka aike wa Digital Imam, ya ce an ɗauki matakin korarsa ne gaba ɗaya saboda ƙin yin nadamar da Sheikh Nuru ya nuna bayan dakatar da shi ɗin. Wasiƙar ta ce: ""Akaramakallah ka fi ni sanin koyarwar Musulunci, manufar ladabtarwa ita ce don a gyara ɗabi'ar mutum." https://www.bbc.com/hausa/media-60988242 +religion Ku San Malamanku tare da Malam Abubakar Saminaka Yauri "Abubakar Muhammad Saminaka Yauri malamin Musulunci ne da ya ƙware a harshen Larabci da Fiƙihu da kuma Usulul Fiƙihi, kamar yadda ya shaida wa BBC a cikin shirin Ku San Malamanku na wannan makon. Shehin malamin wanda ya fi shahara da Malam Saminaka, an haife shi ranar 22 ga watan Oktoban 1972 a garin Saminaka na Ƙaramar Hukumar Yauri ta jihar Kebbi a Najeriya. Malam ya yi karatu a gaban malamai da dama da suka haɗa da Malam Usman a garin Zaria, inda ya karanta litattafan Fiƙihu kamar Ahalari zuwa Muktasar da kuma waƙoƙin yabo irinsu Ishiriniya da Alburdah. Malam Saminaka ya yi karatun firamare a mahaifarsa, sai dai bai samu shiga sakandare da wuri ba saboda mahaifiyarsa ta yi fargabar cewa bai yi girman da zai iya barin gida ba domin shiga makarantar kwana. ""Daga nan ne kuma aka samu tsaiko, saboda yayyena biyu suna bayar da labarin yadda manyan ɗalibai ke aikata musu a makarantar kwana idan sun zo gida, shi ne hajiya (mahaifiya) ta ce ba zan je ba har sai na ƙara ƙwari,"" in ji shi. Bayan ya koma gida daga Zaria ne kuma sai mahaifinsa ya shaida masa cewa dole ya yi karatu domin ya yi aiki ko kuma ya nemi sana'a, abin da ya sa ya koma garin Argungu kenan a 1992, inda ya kammala sakandare. Bayan kammala sakandare, Malam ya shiga Kwalejin Ilimi ta Adamu Audi Argungu kuma ya samu shaidar karatu ta NCE. Malam Saminaka ya ce ya yi bara sosai a Zaria kuma ya sha wahala sosai kamar ko wane almajiri amma ya ce wannan bai kai ilimin da ya samu ba. Ya nemi gurbi a Jami'ar Usma Danfodiyo da ke Sokoto har sau uku amma ba tare da ya yi nasara ba. Daga baya malamin ya je Jami'ar Afirka da ke birnin Khartoum a Sudan, inda ya yi digiri a ɓangaren shari'a, sannan ya je kwalejin Peace College ya samu digiri kan fassara. Ya yi digiri kan harshen Larabci a Jami'atu Duwalil Arabiyya duk a Sudan. Kazalika, Malam Saminaka ya yi digiri na biyu a Jami'ar Sinar kuma yanzu haka yana ƙoƙarin kammala digiri na uku duka a harshen Larabcin. Haka nan, ya yi digiri na biyu a fannin alaƙar ƙasashe, wanda yake matakin kammalawa yanzu haka. Malam ya yi difiloma a fannin Hadisi a Jami'ar Jazira, sannan ya yi karatu kan hulɗa da jama'a da aikin jarida a Jamia'r Ma'amun Umaida. Malam na koyarwa a birnin na Khartoum a halin yanzu. Malam Saminaka ya ce akwai malamai da dama da suka yi tasiri sosai a rayuwarsa amma ya ce ba kamar Malam Usman wanda ya ce ya zauna a wurinsa a Zaria kuma ya rike shi bisa amana. ""Malam ya yi tasiri sosai a rayuwata wanda ya sa a lokacin da na bar Zaria, bayan na shaida wa mahaifina cewa na gaji da zaman garin. To da na koma gida na kan ji sautin muryar Malam Usman yana rera karatu saboda kewarsa da nake yi,"" a cewarsa. Ɓangaren da ya fi ƙwarewa a karatu ""Wani lokaci sai in ga kamar na fi fahimtar Fiƙihu sosai, amma ina ganin na fi kwarewa a ɓangaren Lugga ko usulul Fiƙihi,"" a cewar Malam. Amma ya ce ya fahimci Nahawu sosai da Hadisai ma. Don yana karatu ma a bangaren Hidisi kuma yana karantar da shi. Iyali Malam Abubakar Muhammad Saminaka na da mata biyu - Hafsatu Abdullahi mai 'ya'ya 13 da kuma Hauwa'u Abubakar mai 'ya'ya huɗu. Malam ya ce yana da jikoki." https://www.bbc.com/hausa/labarai-57190478 +religion Ku San Malamanku tare da Sheikh Shettima Habib Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon hira da Sheikh Shettima Habib Fitaccen malamin addinin musuluncin a Najeriya Sheikh Shettima Habib, ya ce duk da bai yi karatun boko ba amma ya taimaka wa masu bincike a cibiyoyin ilimi a Ingila da Jamus, musamman kan babban aikin fassara Al Kur’ani mai tsarki zuwa harshen Kanuri. Ya ce ya je Ingila sau uku kuma turawan ƙasar da suka yi wa Najeriya mulkin mallaka ne suka gayyace shi zuwa Landan. Malamin ya ce ya taimaka masu kan binciken da suke yi a kwalejin nazarin zamantakewar kasashen gabashin duniya da na Afrika wato School of Oriental and African Studies da ke tsakiyar Landan. Ya kuma kai ziyara Jamus sau shida kan aikin fassarar Al Kur’ani mai tsarki da harshen Kanuri a Jami’ar Hamburg. Malamin ya shaida wa BBC cewa an haife shi ne a watan Afrilun shekarar 1959 a cikin garin Maiduguri. Malamin ya ce cikakken sunansa shi ne Shettima Habib ibn Shetimma Ali Shetima Ibrahim. Ya ce tsawon shekara 23 yake limanci a babban masallacin Juma'a na GRA a Maiduguri. Kuma malamin ya ce ya gaji limanci ne daga kakansa wanda Shehu Garbai Kakan shehun Borno na yanzu ya naɗa wanda ya haifi babansa. Sheikh Shettima ya ce yana da shekara bakwai ya fara karatun Kur'ani mai tsarki a gidansu wurin Malam Abdu. Ya ce yana da shekara 15 zuwa 16 ya haddace Kur'ani. Kuma cikin shekara bakwai ya ce ya sauke tafsirin Kur'ani. Malamin ya ce ya yi karatu hannun malamai da dama a Borno. Ya yi karatun Tajwidi a wajen Goni Darma. Sheikh Shettima ya ce lokacin da ya haddace Kur'ani ne ba zai taba mantawa ba a rayuwarsa saboda irin girman shagalin da aka yi a lokacin. Kuma rashin mahaifinsa kuma malaminsa ne abin da ya fi bakanta masa rai a duniya. Abincin da Sheikh ya fi so Shehun malamin ya shaida wa BBC cewa ya fi son shinkafa da jar miya da kuma tuwo da miyar kuka da man shanu Malamin ya ce matarsa ɗaya kuma yana da ƴaƴa shida, biyu maza hudu mata. Biyu daga cikin matan sun yi aure, biyu kuma sun kammala karatu, a cewar Malamin. Babban burin malamin shi ne samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a Borno da Najeriya baki ɗaya. https://www.bbc.com/hausa/labarai-59002740 +religion Musulman Indiya sun ce an fara kai su bango kan takura musu da ake yi "Kusan shekaru 30 da suka gabata duk da shaidu 850, sannan daga bisani fiye da kasidu 7,000 da hotuna da faya-fayen bidiyo da aka gabatar, wata kotu a Indiya ba ta samu kowa da aikata laifin rushewa tare da banka wuta a wani masallacin da aka gina tun a ƙarni na 16 a kasar ba, wanda wasu gungun mutane mabiya addinin Hindu ne suka kai hari a masallacin da ke birnin Ayodya mai daraja. A cikin mutum 32 da ake zargi da yanzu haka suke a raye, akwai tsohon mukaddashin Firimiya LK Advani, da sauran jiga-jigan jam'iyyar BJP. A hukuncin da aka yanke a ranar Laraba, kotuna ta wanke duka waɗanda ake zargin, inda ta ce wasu ne da ba a san ko su wane ne ba suka kai harin tare da lalata masallacin a shekara ta 1992, ba wai an kitsa shi ne da gangan ba. Hakan ya faru duk kuwa da ɗumbin sahihan shaidun da suka gane wa idanunsu yadda aka rushe ginin masallacin, wanda ya dauki sa'o'i kadan, da ya nuna cewa sai da aka tsara aka kuma aiwatar, ba kuma tare da tunanin abinda zai biyo baya ba, wanda a kan idon wasu jami'an 'yan sanda ne a kuma gaban dubban jama'a. A shekarar da ta gabata ne kotun ƙolin Indiya ta tabbatar da cewa harin ''tsararre ne'' kana ''mummunan karya dokar kasa ce'' Ga baki daya ana ɗaukar sakamakon wannan hukunci a matsayin wani rauni da gurɓacewa a ɓangaren shari'a na kasar ta Indiya. Wasu ma na fargabar cewa lalacewar ta kai ta yadda ba zai gyaru ba saboda yawan shisshigin manyan 'yan siyasa, da rashin mayar da hankali wajen inganta ɓangaren shari'ar. Amma kuma za a iya cewa sakamakon hukuncin ya fito fili ya nuna damuwar da ake da ita na ƙaruwar nuna bambanci da wariyar da Musulman Indiya miliyan 200 ke fuskanta a kasar. A karkashin gwamnatin jam'iyyar BJP ta Narendra Modi, tura ta kai bango ga wasu al'ummomi inda suke jin cewa ana cin mutuncinsu fiye da ma a ko wane lokaci a cikin tarihin mulkin wadancan gwamnatocin Indiya da suka shude, inda suke yaba wa dimokraɗiyya mafi girma a duniya tun bayan samun 'yancin cin gashin kan kasar a shekara ta 1947. Gungun 'yan daba sun sha kashe Musulmai a kan cin naman saniya ko kuma jigilar shanu, wadanda masu bin addinin Hindu ke dauka a matsayin abin bauta. Gwamnatin Mr Modi ta yi garanbawul ga dokokin da za a bi diddigin 'yan gudun hihjirar da ba Musulmai ba da suka shigo daga kasashe maƙwabta. Ta rarraba jihar Jammu da yankin Kashmir da Musulmai suka fi rinjaye, kana ta raba su da 'yancin cin gashin kai da kundin tsarin mulki ya tanadar musu. A cikin wannan shekarar an zargi Musulmai su kadai da yada cutar korona bayan da 'yan wasu kungiyar Musulman suka halarci wani taron adddinin Musulunci a birnin Delhi. Amma kuma tarukan addinin Hindu da ake gudanarwa lokacin wannnan annoba ba su taba cin karo da irin wadannan zarge-zarge ko dora laifin da ba nasu ba, ko suka a kafafan yada labarai ba. Ba ma a nan batun ya tsaya ba, an sha yin awon gaba da dalibai Musulmai da masu fafutika ana garkame su a gidan kaso kan zargin haddasa fitina kan dokar zama dan kasa a birnin Delhi lokacin hunturun da ya gabata, yayin da mabiya addinin Hindu da suka haddasa hargitsin ba a yi musu komai ba. Musulmai da dama na kallon sakamakon hukuncin na Babri a matsayin wani ci gaba da cin mutuncinsu ne. Batun nuna wariya ya fito fili. Jam'iyar Mr Modi ta tabbatar da aƙidar mabiya addininta na Hindu. Manyan kafafen yada labaran kasar kan fito fili suna ɓata sunan Musulmai. Jam'iyyu da dama na Indiya da a baya suke da tagomashi da suka taɓa mara wa al'ummar Musulman baya, yanzu haka sun juya musu baya. Masu suka sun zargi babbar jam'iyar adawa kan amfani da Musulman wajen samun ƙuri'u ba tare da yi musu abinda ya dace ba. Ita kanta al'ummar Musulman shugabanninsu da ya kamata su fito su yi magana da yawunta ba su da yawa. ""Musulmai sun yanke ƙauna da lamarin gwamnatin. Suna ganin an kai su bango, kana jam'iyyun siyasa da ma'aikatu da kafafen yaɗa labarai sun gaza a taɓuka musu komai. Akwai rashin kwarin gwiwa a cikin al'ummar,'' in ji Asim Ali, wani masani a wata cibiyar bincike kan manufofin gwamnati da ke birnin Delhi. A gaskiya, Indiya na da dadaɗɗen tarihin nuna wariya ga al'ummar Musulmai. ''Ana daukarsu marasa kishin kasa'', kamar yadda wani rahoto ya nuna. Amma a wata daban kuma, yayin da Indiyawa da dama ke kallon ba a yi wa Musulamai adalci, al'ummar ''Musulman ba su ci gajyar komai daga al'amuran da suka shafi zamantakewa da tattalin arzikin kasar ba'', kamar yadda wasu masanan tarihi suka bayyana. An cunkushe Musulmai da daman gaske a yankuna da unguwannin marasa galihu a cikin manyan birane. A shekara ta 2016, kason da suka samu na yawan jami'an ƴan sanda a yankunan nasu kasa da kashi 3% ne, yayin da yawan al'ummar Musulman ya kai kimanin fiye da kashi 14% na yawan al'ummar kasar ne. Kana kashi 8% kacal na Musulman da ke manyan birane ne ke yin aikin da ake biyansu albashi akai-akai." https://www.bbc.com/hausa/labarai-54371750 +religion Coronavirus: Hotunan yadda aka yi buda bakin farko na azumin 2020 Ga wasu zababbun hotuna daga wasu birane na duniya na yadda aka yi bude-baki na azumin farko a shekarar 2020. Sai dai azumin na bana ya zo ne cikin dokar kulle saboada annobar cutar korona. Dukkan hotunan mallakar Getty Images ne https://www.bbc.com/hausa/labarai-52421231 +religion Aikin Hajji: Mene ne adashin gata na hukumar Alhazan Najeriya? "Hukumar alhazai ta Najeriya fito da tsarin adashin gata, da zai bai wa maniyyata aikin Hajji, masu karfi da marasa karfi damar tara kudin zuwa kasa mai tsarki. Manufar wannan tsari shi ne saukakawa maniyyata wajen tara kudin gwargwadon halin da mutum yake da shi. Hukumar alhazai ta dauko wannan tsari na adashin gata daga kasashe kamar Malaysia da Indonesia, inda 'yan kasar ke irin wannan tarin kudi don sauke faralli. Shugaban sashen adashin gata na hukumar Alhazan Najeriyar Aliyu Tanko ya shaida wa BBC cewa akwai hanyoyi guda uku da wadanda ke son shiga tsarin adashin gata za su bi, domin cin gajiyar shi. Aliyu Tanko ya kara da cewa; ''Shi wannan asusun ajiyar banki na musamman ne, da mutum zai dinga ajiye kudin gwargwadon halin da yake da shi, kama tun daga Naira 500 har abin da Allah ya hore masa. Sannan asusu ne da ba za ka sanya kudi yau, gobe ka tsakuro wani abu daga ciki ka yi sabgar gabanka ba. ''Bankin Ja'iz zai dinga juya wannan kudi ta hanyar yin kasuwancin da ya dace da tsarin addinin Musulunci, sannan ana zuba maka ribar abin da aka samu a asusunka, sannan kai ma za ka ci gaba da kai kudin. ""Zuwanka aikin hajji ya danganta da yawan kudin da ka tara, watakila ka dauki shekara 10 ko 20 kafin kudin su yi nauyin da za ka iya sauke farali. Kuma fatanmu shi ne idan kudin mutum sun rage, za mu ba shi idan ya dawo daga aikin Hajji domin ya juya su ta hanyar yin wani kasuwanci, idan kuma yana so zai iya ci gaba da adashin gata na komawa aikin hajji ko biya wa wani dan uwansa,'' in ji Aliyu Tanko. Shugaban sashen adashin gatar ya ce: ''Kawo yanzu ba a shigar da tsarin ma'aikatan hukumar alhazai ko na bankin Ja'iz su shiga kauyuka don karbar kudin shiga adashin gata ba. ""Amma suna da damar shigo birni don zuwa banki ko hukumar alhazai da kansu don shiga tsarin.'' 'Dr Tanko ya ce: 'Idan mutum yana cikin tara kudin Allah ya yi masa rasuwa, magada na da damar zuwa kotu su bukaci yadda suke son kudin ya kasance, ko dai a ba su kudin su raba shi a matsayin gado ko su wakilta mutum guda da zai maye gurbin mahaifinsu sai mu sauya suna. Sannan ba wai wanda ya rasu kadai ba, mutum yana da damar dawowa hukumarmu don sauya sunan wanda yake son ya ci gajiyar adashin. Ko dai dansa ko mata ko ma duk wanda yake son maye gurbinsa. Ya ce fatansu shi ne tsarin ya kawo sauyi ta fannin sauko da farashin kudin aikin Hajji, da sauya wa mahajjata masauki su kusanci da Masallatan Harami na Makka da Madina. Dr Tanko ya kara da cewa suna kuma fatan kawo damar samun saukin farashin kudin jirgi, ""tsari ne da muke fatan ya kawo sauyin da zai saukaka wa 'yan Najeriya a lokacin aikin hajji.''" https://www.bbc.com/hausa/labarai-56535175 +religion Bidiyon Ku San Malamanku tare da Malam Modibbo Tukur Danna hoton sama ku kalli bidiyo: Shirin Ku San Malamanku na wannan makon ya tattauna da Malam Muhammad Modibbo Tukur mazaunin garin Gombe da ke arewa maso gabashin Najeriya. https://www.bbc.com/hausa/shirye-shirye-na-musamman-61179156 +religion Coronavirus: Yadda annobar za ta sauya fasalin Tafsirin Azumi a Najeriya "Malaman addinin Musulunci da dama a Najeriya sun bayyana cewa ba za su tara jama'a a lokutan tafsirin da a al'adance ake gudanarwa a watan Ramalana ba. Malaman sun ce sun dauki matakin ne domin yin biyayya ga dokar gwamnati ta hana tarukan jama'a domin dakile yaduwar cutar korona. Gwamnati ta umarni 'yan Najeriya su dauki matakan daban-daban wajen kauce wa kamuwa da cutar korona, ciki har da kaurace wa shiga tarukan jama'a. Sheikh Dahiru Bauchi A wani taron manema labarai da ya gudanar ranar Laraba, Shieikh Dahiru Bauchi ya ce ""Ba za mu gudanar da tafsirin da muke yi a Kaduna ba inda daruruwan mutane suke halarta kowacce rana."" Ya kara da cewa zai rika gudanar da Tafsirin ne a gidansa da ke Bauchi inda za a rika watsawa ta rediyo da talbijin da kuma shafukan sada zumunta. Ko a watan Maris, Shugaban Darikar Tijjaniyyar ta Najeriya, ya sanar da jinkirta taron Maulidin Sheikh Nyass wanda da za a yi a Abuja da Sokoto saboda hana yaduwar cutar korona. Sheikh Ahmad Gumi A wani sakon bidiyo da ya fitar, Sheikh Ahmad Gumi, ya ce a wannnan shekarar ba zai gudanar da tafsirin azumin watan Ramalana ""a Masallacin Sultan Bello kamar yadda aka saba ba,"" yana mai cewa za a gudanar da shi a wurin da ya dace da tsarin kiwon lafiya. Malamin ya ce ya dauki matakin ne domin kare lafiyar kansa da ta mutanen da za su halarci wurin tafsirin, kamar yadda hukumomin lafiya suka bukaci a yi domin dakile yaduwar cutar korona. Sheikh Tijjani Bala Kalarawi Malamin, wanda yake gudanar da tafisiri duk shekara a birnin Kano da ke arewacin kasar, ya shaida wa BBC cewa bana ba zai tara jama'a a wajen tafsirin ba. Ya ce zai rika gudanar da shi ne a sutudiyon da ke gidansa inda za a nada sannan a watsa ta gidajen talbijin da rediyo da shafukan intanet. Sheikh Kalarawi ya yi kira ga sauran malaman da za su gudanar da tafsiri su yi koyi da irin su da suka yanke shawarar dakatar da tara jama'a kamar yadda gwamati ta bukaci a yi. Ita ma Kungiyar Izala ta Najeriya ta sanar da cewa a bana ba za ta aike da malamai garuruwa don gabatar da Tafsirin Azumi ba kamar yadda aka saba. Shugaban kungiyar na kasa Sheikh Bala Lau ne ya sanar da hakan a ranar Alhamis a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Whatsapp da BBC ta samu gani." https://www.bbc.com/hausa/labarai-52313303 +religion Ku San Malamaku tare da Sheikh Muhammad Khamis Muhammad "Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon: An haifi Sheikh Muhammad Khamis a ranar Juma'a, 3 ga watan Satumbar 1976, ya kuma yi karatu daban-daban tun daga karatun allo zuwa Islamiyya har zuwa karatun boko. Malamin ya haddace Al-Ƙur'ani tun yana kimanin dan shekara 14, yana da shekara 16 kuma ya shiga Islamiya mai suna Madarasatul Abdulaziz Al-Islamiyya. Malamin da ya soma karantar da shi shi ne Malam Muhammad Umar. Sheikh Khamis ya yi musabaƙar izifi daban-daban tun daga izu biyu har zuwa sittin da tafisiri. Ya bayyana cewa haddar Al-Ƙur'ani da ya yi a lokacin da yake da ƙuriciya ta ba shi damar halartar kowane irin zaure da ake yin karatu. ""Na halarci zaure irin na Malam Abubakar Tureta, sannan kafin ya rasu, yana karantarwa kuma akwai zaƙaƙuran ɗalibansa waɗanda idan ba shi nan ko yana da uzuri su ke zama kan kujerarsa su karantar, kamar Malam Umar Jibril wanda aka fi sani da Al-Basawiy kuma na yi karatu sosai a wajensa, sannan akwai Muhammad Yahya shi ma na yi karatu a wajenshi,"" in ji shi. Malamin ya bayyana cewa ya kammala karatun sakandirensa a makarantar Government College Kaduna a 1994, kuma bayan ya kammala karantunsa na sakandiren ya yi difloma a Islamic Studies da Education a Ɗanfodio Institute da ke Kaduna, sannan kuma ya yi karatun Larabci a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna, kuma a kwalejin ya yi difloma a harshen Turancin Ingilishi. Ya kuma yi NCE sa'annan ya kammala digirinsa a cikin shekara uku wanda tun kafin sakamakon digirinsa ya fito ya sayi form na masters inda nan ma ya yi ya gama, inda daga bisani ya tafi jami'ar jihar Kwara domin yin digiri na uku inda a nan ne ya zama dakta. A halin yanzu Sheikh Khamis na daga cikin masu karantar da Larabci a Jami'ar Jihar Kaduna, kuma shi ne shugaban alƙalai na gasar karatun Al-Ƙur'ani na jihar Kaduna Sheikh Khamis na da mata biyu da kuma ƴaƴa 11, duk da uwargidansa wadda ta haifi ƴaƴa biyar Allah ya yi mata rasuwa, haka kuma cikin ƴaƴa biyar da ta haifa ɗaya ya rasu. ""Ita kuma wadda nake tare da ita har yanzu ita ma akwai ƴaƴa shida, don haka ƴaƴana goma sha ɗaya yanzu Alhadulillah"". Shekih Khamis ya ce surar da ta fi ba shi wahala wajen hadda ita ce suratul Saba. ""Wa ƙalal ladhina kafaru lan nu'uminu bi hadhal Ƙur'an, waɗannan ayoyin da yake na yi hadda ne ayoyi biyar-biyar, tun daga kan waɗannan ayoyin zuwa ayoyi biyar sun zama mani yadda ka san wani dutse mai ƙarfi, yadda ka san ƙarfe, waɗannan ayoyin sun ba ni wahala ƙwarai da gaske,"" in ji shi. Ya ce akwai tambayoyin da mata suka fi yi masa da kuma waɗanda maza suka fi yi masa. Galibin tambayoyin da aka fi yi masa su ne waɗanda suka shafi zamantakewa ta auratayya ko abubuwan da suka shafi gado ko kuma abubuwan da suka shafi tarbiyya. Su kuma maza tambayoyin da suka fi yi masa su ne na bangaren tarbiyya ganin cewa al'umma tana fuskantar barazanar tarbiyyya, kamar yadda ya bayyana. Malam ya ce shi a rayuwarsa babu wani abinci na musamman da yake so, duk wani abincin da ya samu na halal zai ci. Ya ce abinci ko da nama ko ba nama zai ci, shi haka Allah ya yi shi." https://www.bbc.com/hausa/labarai-59509682 +religion Matakan da ake bi don duban watan azumi a Najeriya "Kwamitin duban wata na Najeriya ya umarci ƴan kasar da su fara duban jaririn watan azumin Ramadan daga ranar Litinin. Shugaban Kwamitin, Farfesa Sambo Wali Wazirin Sokoto ya shaida wa BBC cewa, Litinin ce 29 ga watan Sha'aban kuma idan ba a gan shi ba da yamamcin Litinin, to za a ci gaba da duban watan zuwa Talata. ""Idan kuma ba a gan shi ba a ranar Talata, to kai tsaye Laraba za ta kasance 1 ga watan azumin Ramadana,"" in ji Waziri. Farfesa Sambo ya ce babu yadda za a yi kwamitinsu ya saɓa da ka'idar duban wata da addinin musulunci ya gindaya saɓanin yadda wasu jama'a ke zato. A cewarsa, kwamiti na amfani da Hadisin Manzon Allah (SAW) ""ku yi azumi idan kun ga wata, ku ajiye idan kun ga wata - idan ba ku samu ganinsa ba kila saboda hadari to ku cika Talatin."" Ya yi watsi da zargin cewa suna tafiya tare da Saudiyya inda ya ce lokacin azumi kawai Saudiya ke duban wata saɓanin kwamitinsu da ko wane wata ke fita duban sabon wata. Kwamitin duban wata a Najeriya ya ce duk ƙarshen wata wakilan kwamitin suna zama kuma a bayar da sanarwa cewa 29 ga wata jama'a su fita duban sabon wata. Kwamiti yana aika wa dukkanin yankunan Najeriya cewa idan an ga wata a yi sauri a faɗawa mai alfarma Sarkin Musulmi Idan mutum shi kaɗai ya ga wata zai sanar da Hakimi zuwa ga Uban Kasa wanda shi kuma zai sanar da Sarkin Musulmi. Daga nan za a jira a fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi har a samu labarin ganin wata a faɗin Najeriya ko kasashen waje. Za a sanar da Mai Alfarma Sarkin Musulmi cewa an ga wata saboda haka gobe 1 ga sabon wata - idan ba a ganshi ba kuma gobe za ta kasance 30 ga wata. Idan sarkin musulmi ya gamsu da bayanan da aka ba shi bayan ya tuntuɓi sarakuna na jihohin arewa da na yamma domin tabbatar masa da ganin watan. ""Ta haka ake samun labarin an ga wata ko ba a ganshi ba,"" in ji Wazirin Sokoto Farfesa Sambo Wali, shugaban kwamitin ganin wata a Najeriya. Ya kuma ce Kwamitin ganin wata kan zauna da waɗanda suka ga wata, domin a yi masu tambayoyi cewar - ya kuka ga wata? Ina kuka gan shi? Ya ce kwamitin kan kiyaye lokaci da kuma yadda aka ga wata, da ɓangaren da aka ganshi domin a cewarsa: ""Mafadar wata ya bambanta da yanayi - lokacin hunturu ya bambanta da na bazara da kuma na damina." https://www.bbc.com/hausa/labarai-56710026 +religion Hajj 2020: Muhimmancin Ranar Arafat ga Musulmi Latsa alamar hoton da ke sama domin kallon wannan bidiyon A wannan bidiyon, Malam Jabir Sani Maihula ya bayyana muhimmancin ranar Arfa ga Musulmi https://www.bbc.com/hausa/53588865 +religion Ku San Malamanku tare da Malama Zahra'u Muhammad Umar "Wata fitacciyar malamar addinin Musulunci, Malama Zahra'u Muhammad Umar ta ce ba ta da wani buri a rayuwa kamar ganin ta sa farin ciki a fuskokin marasa galihu. Malama Zahra'u da ke aiki da hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce tana takaicin ganin mutane cikin wahala, domin har hawan-jini ta kamu da shi saboda ganin wasu yara cikin akuba. Malamar ta bayyana hakan ne a lokacin wata tattaunawa cikin shirin Ku San Malamanku na BBC. Malam Zahra'u ta ce Suratul Ma'ida na ba ta wuya a lokacin hadda, sannan ta fi son Suratul Yasin. Malama Zahra'u ta ce an haife ta a unguwar Fagge da ke Kano, kuma ta yi makarantu daban-daban har ta kai matakin digiri na uku a fanin ilimin addinin Musulunci. Sannan ta yi karatu mai zurfi a fanin fafutikar mata wajen yaye musu matsalolinsu musamman a Hukumar Hisbah. Malama Zahra'u tana da aure da ƴaƴa bakwai. Malama Zahra'u ta ce ta kasance mai girmama kowanne malami, kuma tana kokarin laƙantar kowanne malami da take ganin akwai abin da za ta koya daga wurinsa. Amma wadanda suka fi tasiri a kanta akwai Farfesa Ibrahim Muhammad na jami'ar Bayero da Dr Ahmed da Malam Abubakar Jibril wanda limamin jami'ar BUK ne. Malamanta na da yawa kowanne akwai abin da ta koya daga wajensu. Malama Zahra'u ta shaida cewa aikinta akwai matukar wahala saboda tana hada ayyukan ofis da na kula da iyali ga kuma masu yi mata kira daidaiku domin neman mafita kan matsalolin rayuwa. Ta ce matsalolin aure ta fi karo da su, kullum akalla tana karbar wayar mace 10 kan matsaloli ko tambayoyin da ya shafi zamantakewar aure. Mata na yawan kiranta suna neman shawarwari da yadda za su gyara zaman aurensu, tafiyar da maigida da addu'o'in neman mijin ya so su. Ta ce tana shan wuya sosai a gwamnatance aiki na tafiya daidai amma tafiyar da aikin gwamnati da kuma na yawan kiranta ana neman taimako da abu ne mai sauki ba. Malamar ta ce wani lokaci har ciwon-kai take yi, kuma ba ta jin dadin a kirata ba ta dauka ba, gudun ba ta san gararin da mutum ke ciki ba. Ta ce kasancewa mijinta mai wayewa ne da ilimi baya korafi, yana bata damar ayyukanta kuma yana karfafa mata gwiwa da shi mata albarka. 'Tashin hankali da na shiga' Malama Zahra'u ta ce a hukumar Hisbah ta yi karo da hawan jini saboda dimbin matsaloli da korafe-korafe da suke karba. Ta ce akwai lokacin da aka kwaso yara kanana daga wani makarantar mari, inda wani 'makirin mutum' ke lalata da yara mazan. Ta ce abin takaici ne ganin a ce yawan wannan yara sama da 30, mutum guda duk ya yi lalata da su. Da aka kawo su ofishinsu, yaran na cikin tsananin akuba, saboda ko ina a jikinsu ciwo ne da karzuwa. ""Yanayi ya kadaita ni ya sa jini na ya hau har 180, saboda abin takaici ne da tashin hankali ganin ka tura yaronka neman ilimi amma ya kasance an lalata masa rayuwa."" Sannan ta shaida cewa an taba kawo mata karar wani mutum da ya farfasa jikin dansa mai wata 7, yanayi ba dadin gani. ""An gayyaci mahaifin ya zo ya yi bayanin dalili, amma zuwansa ke da wuya sai ya soma ihu ya rinka ihu, har ya taso kamar zai doke ni, ni kuma na rinka karanta ayatul kursiyu."" ""Ai kuwa nan take ya rike bango ya farfasa jikinsa ko ina jini, daga baya da na zauna da matarsa na ji ta bakinsa, sai na ce ta koma gida kar ta koma gidan iyayenta."" Malama Zahra'u ta ci gaba da cewa: ""Nan kuma take ba ni labarin ai wai ya taba kashe ɗansa, na tsorata, saboda tana zaune da mutumin da zai iya hallakata. ""Amma wani abin mamaki ina cewa ta tafi gidansu sai ta sunkuya ta soma kuka, ta shaida mun cewa idan ta tafi gida babu inda za ta zauna. Mahaifiyarta ta yi aure kuma mijinta daki ɗaya suke haya."" Abin da ke bata farin ciki shi ne akwai yara 'yan mata guda 9 da ke cikin halin talauci ko sun yi ciki ko kwaya dangi sun koresu. To ta ɗau nauyin kula da su da sauya musu hali da tarbiyyartar da su har ta kai ga ta musu aure, kuma suna zaune lafiya. Sannan wani abin da ke sake sa ta farin ciki shine, raba abinci ko kudi da kanta, tana son taimakon mai rauni kuma ta fuskanci yana murna. Sannan abin da ke sa ta bakin ciki shi ne rashin tarbiyya, bata son ganin rashin tarbiyya a gida. Abinci da Buri Malama Zahra'u ta ce ta fi sha'awar abinci mai ruwa-ruwa don haka tana son farfesu shi ne ya fi mata dadi da kwantar mata da hankali. Babban burinta kuma shi ne neman cikawa da imani." https://www.bbc.com/hausa/58588781 +religion Jahilci ne ya sa malamai suke karyata coronavirus - JNI "Kungiyar Musulman Najeriya ta Jama'atu Nasril Islam JNI karkashin jagorancin Sarkin Musulmai ta ce jahilci ne wani malamin addini ya fito yana ikirarin cewa coronavirus karya ce. Kungiyar ta fitar da sanarwa ne ranar Litinin mai dauke da jan kunne ga malaman da sanarwar ta ce suna dulmuyar da al'umma kan cutar Covid-19 a Najeriya. Sanarwar dai martani ce ga wasu malaman addinin Islama da suka fito suna wa'azi ga mabiyansu suna karyata cewa coronavirus karya ce makirci ne, cikinsu har da wasu manyan malaman da ke da'awa. A cikin sanarwar da sakataren kungiyar JNI ya fitar Dr. Khalid Abubakar Aliyu, ya ce bai kamata irin wadannan kalamai su fito bakin duk wani malami ba da ya amsa sunansa malam. Kungiyar ta ce abin takaici ne yadda wasu malamai ke wa'azi suna yaudarar al'ummar Musulmai kan ba su yadda da cutar coronavirus ba. ""Ya zama wajibi a matsayinmu na al'umma mu kaucewa duk wani abu da zai maimaita abin da ya faru a Italiya inda cutar ta yi kamari, saboda mutane sun bijerewa gargadin masana game da cutar."" Allah Ya ce Ka tambayi wadanda suka sani idan ba ka sani ba Q16:43, saboda haka ya kamata mu sani cewa ilimi amana ne wanda dole a kiyaye a gabatar da shi yadda yake."" Kungiyar ta nesanta kanta da abin ta kira karamin tunanin malamai game da duniya, wadanda ta ce rashin fahimtarsu babbar illa ce ga lafiya da zai jefa al'umma cikin hatsari. Ta kuma kara da cewa ya kamata a fahimci cewa batun annoba ba sabon abu ba ne a tarihin duniya, inda ta ba da misalai da dama na abubuwan da suka faru a tarihi tun zamanin Sahabbai, da Tabi'ai wadanda suka gabace su. Sanarwar ta yi kira ga al'ummar Musulmai su yawaita Istigifari da neman gafarar Ubangiji. Sannan a yawaita zikiri a ko da yaushe da kuma bayar sa sadaka da yawaita addu'o'i da karatun Al Qur'ani mai tsarki da kuma Sallar dare." https://www.bbc.com/hausa/labarai-52093961 +religion Ramadan: Muhimmancin Sallar Asham ga Musulmai Latsa hoton da ke sama domin kalln bidiyon: Sheikh Muhammad Awwal, malamin addini ne a Najeriya, ya ce sallar Asham na daya daga cikin abubuwan da ake son mai azumi ya mayar da hankali a kai domin samun rabauta. Ya kara da cewa duk da cewa akwai malaman da suke siffanta sallar a matsayin bidi'a akwai nassoshi masu kwarin gaske da ke nuna kasancewar sallar sunna. Dangane kuma da ko raka'a nawa ake yi, shehin malamin ya ce bisa abin da malamai suka tafi a kai, ana yin ra'aka 13 har shafa'i da wutiri. https://www.bbc.com/hausa/media-60985097 +religion Uttar Pradesh: Musulman Indiya na fargabar hare-haren kiyayya "Yayin da jihar Uttar Pradesh ke shirin zaben sabuwar gwamnati, hankali ya koma kan al'ummar Musulmin jihar su miliyan 40 da ke rayuwa a wannan jihar da kawunan jama'arta ke rarrabe. Kirti Dubey ta BBC Hindi ta duba halin da wasu shari'oi hudu da aka yi da ke nuna yadda ake kai wa al'ummar Musulmi hare-haren kiyayya yayin wa'adin mulkin Yogi Adityanath wanda shi ne babban ministan da ke mulkin jihar. ""Yana yawo da wani dan karamin tawul a kafadarsa a kodayaushe. Sun cusa tawul din cikin bakinsa yayin da suke kashe shi,"" in ji Kamrun Ali yayin da ta ke kuka, tana bayar da labari kisan da aka yi wa mijinta. Ana tuhumar cewa wasu mabiya addinin Hindu ne suka kashe mijin nata Anwar Ali yayin wata tarzoma da suka yi a watan maris din 2019 yayin da ya yi kokari hana su rusa wani ginin masallacin da ke kusa da gidansa a gundumar Sonbhadra. 'Yan sanda sun kama mutum18 - dukkansu 'yan Hindu, ciki har da kananan yara - suna tuhumarsu da kashe shi, amma an bayar da belinsu cikin watanni bayan mutuwarsa. Uwargidan Anwar Ali ta ce har yanzu suna jiran a yi musu adalci. Kisan gilla da furta kalaman kiyayya ga Musulmi sun dade ana yinsu, musamman tun shekarar 2014, shekarar da jam'iyyar Bharatiya Janata Party (BJP) ta firaminista Narendra Modi ta lashe zaben ministan jihar. Masu sukar lamarin na cewa yawancin wadanda ake tuhuma 'yan jam'iyyar ta BJP ne, sai dai jami'an jam'iyyar sun musanta haka. Amma da wuya ka ji sun soki halayyar kai irin wadannan hare-haren. Shi kansa Mista Modi ya sha suka saboda kin cewa komai da yayi na tsawon makonni bayan da a shekarar 2015, wani gungun 'yan Hindu suka halaka wani Musulmi mai shekara 52 da haihuwa a jihar Uttar Pradesh saboda wai ya ajiye naman Sa a cikin gidansa. Kisan na 2015 ya gigita jama'a a fadin duniya, sai dai daga wancan lokacin zuwa yanzu, an ci gaba da kai iri wadannan hare-haren kan Musulmi. Wasu cikin munanan hare-haren da aka kai kan Musulmi sun auku ne a jihar ta Uttar Pradesh, inda wani malamin addinin Hindu Yogi Adityanath ya rika yin kalaman batanci da na kiyayya ga Musulmi, ya zama babban ministan jihar a 2017. Da wuya a iya sani yawan mutanen da ka hallaka ta wannan hanyar a Uttar Pradesh a kowace shekara - amma a 2017, ofishin da ke tattara bayanai kan manyan laifukan da aka aikata ya hada kan bayanan amma bai wallafa su ba. Ckin wasu hare-hare hudu da BBC ta gudanar da bincike a kai, 'yan uwa wadanda aka kashe sun ce ba su gamsu da matakan da 'yan sanda ke dauka ba, kuma sun ce hukumomi ba su nuna cewa sun damu da daukan mataki a kan koken nasu ba. Prashant Kumar wanda jami'in da ke kula da ofishin shari'a na jihar ne ya musanta zargin iyalan cewa 'yan sanda na nuna halin ko-in-kula. ""Babu wanda ke da ikon yi wa wani duka, kuma idan muka kama wani na yin haka, to muna daukan matakin shari'a kansu,"" inji shi. Sai dai wai lauya mai suna Mohammed Asad Hayat da ke wakiltar iyalan da aka kai wa hare-haren nuna kiyayya ya ce halin jami'an tsaron ya yi wa binciken da suke yi illa saboda suna gudun bata wa manyan mutane rai. Ya ce, ""an kashe mutane ne a karkashin yanayi na siyasa."" Amma wasu iyalan da kashe-kashen suka shafa sun ce suna rayuwa cikin fargaba, kuma wasunsu ma sun tsere daga gidajensu. Babban dan Anwar Ali mai suna Ain ul Haq, ya yi ikirari cewa isowar wani malamin makaranta Ravindra Kharwar ya haifar da tashin hankali a kauyensu na Parsoi. ""Ya rika tara matasa mabiya addinin Hindu, yana zuga su da su rika zagin Imam Chowk (wurin da wani ginin adinin Islama yake a da),"" iji shi. Mista Haq ya ce gubgu 'yan Hindun sun lalata wuri sau biyu, amma 'yan sanda su shiga tsakani kuma an sake gina wurin. Amma ranar 20 ga watan maris na 2019, kamar yadda 'yan sanda suka ce, Ali ya kama wasu matasa 'yan Hindu na kokari rusa ginin a karo na uku, kuma nan take suka kai ma sa hari. Dan nasa ya ce sun kashe shi. Binciken asibiti kan gawarsa ya ce an kashe shi ne da ""wani makami mai kaifi."" Binciken 'yan sanda ya gano cewa Mista Kharwar na da hannu a kisan. Sun kai wani samame a gidansa amma ba su same shi ba - kuam 'yan sanda sun ce ""ya tsere"" ne. Mista Kharwar ya musanta aikata wannan kisan. Sai dai da 'yan sanda suka shigar da kara, ba a ga sunansa cikin wadanda suke tuhuma ba. Daya daga cikin wadanda ake tuhumar Rajesh Kharwar ya shaida wa BBC malamin makarantar ya rika gaya mu su cewa Musulmai hatsari ne ga 'yan Hindu. Kusan shekara uku bayan kisan kan, Mista Haq ya bayana damuwarsa gani cewa an bayar da belin dukkan mutum 18 din da ake tuhuma. Irin wannan halin ne ke damun Shahrukh Khan, wanda aka kashe mahaifinsa a wata Yunin 2021 a gundumar mathura yayin wata takaddama da wasu kauyawan da ""ba a san ko su wane ne su ba"", yayin da yake jigilar wasu shanu. Bayan wata bakwai babu wanda aka kama, sai dai dan nasa ya zargi Chandrashekhar Baba wani malamin addini Hindu da kashe mahaifin na shi. Mista Chandrasekhar ya musanta aikata laifin. A watan Mayun bara, wani bidiyo da ya yadu kamar wutar daji ya nuna yadda wani gungun maza na dukan wani mutum a gundumar Moradabad, lamarin da ya tayar da hanula a shafukan sada zumunta. Bayan da BBC ta ziyarci gidan mutumin da aka yi wa duka mai suna Shakir Qureshi, mahaifiyarsa ta fara kuka domin fargaba. Sai dai daga baya ta kyale shi yayi magana. Mista Qureishi, wanda mahauci ne, ya ce wata rana yana kan hanyarsa ta kai wa wani abokin cinikinsa naman Bauna a bisa babur, sai wasu mutane suka tare hanya kuma suka zarge shi da jigilar naman Sa. ""Na yi kuka kuma na gaya musu cewa ba naman SA nake dauke da shi ba, amma su ci gaba da duka na."" Ya ce fargabar abin da zai biyo baya ta hana shi kai kara ga 'yan sanda - sai dai ya yi haka ne bayan da bidiyon ya yadu kamar wutar daji. 'Yan sanda sun kama mutum shida, ciki har da Manoj Thakur, wanda ke da alaka da kungiyar 'yan sa kai ta 'yan Hindu. An tsare Mista Thakur na watanni biyu kafi daga baya a ba shi beli. Sai dai baya harin da aka kai kansa, mista Qureshi ya daina sayar da nama - yanzu yana aiki ne a matsayin lebura. A watan Mayun 2017, an gano gawar Ghulam Ahmed mai shekara 60 da haihuwa cikin wani gandun da aka shuka mangwaro da yake gadi a kauyensu da ke gundumar Bulandshahr - kuma binciken asibiti kan gawarsa ya nuna cewa ya mutu ne saboda ""munanan raukukan da ya samu a cikin jikinsa"". 'Yan sanda sun kama mutum tara wadanda ke da alaka da wata kungiya ta masu tsattsauran ra'ayi - Hindu Yuva Vahini - da Mista Adityanath ya kafa a 2002. An bayar da belin dukkansu kuma sun musanta aikata laifin da ake tuhumarsu da aikatawa. Iyalan Ghulam na cikin tsirarun Musulmi a kauyen da 'yan Hindu suka mamaye. Amma tuni sun bar kauyen. ""Ya za mu ci gaba da zama a wannan kauyen?"" in ji iyalan gidan Ghulam Ahmed." https://www.bbc.com/hausa/labarai-60462985 +religion Ku San Malamanku tare da Sheikh Muhammad Bala Ahmed Ku latsa hoton da ke sama don kallon hirar BBC da Sheikh Muhammad Bala Ahmed a shirin Ku San Malamanku, sannan kuna iya shiga shafinmu na Youtube don kallon cikakken bidiyon: Shirin Ku San Malamanku na wannan mako ya zo muku da Sheikh Muhammad Bala Ahmed, malamin addinin Musulunci da ke Bauchi. An haifi Sheikh Muhammad Bala Ahmed a watan Junairun 1950 a garin Bauchi na jihar Bauchi da ke Bauchi a arewa maso gabashin Najeriya. Sunan mahaifinsa Malam Ahmad Mahmoud Baban Inna, mahaifiyarsa kuma sunanta Hajiya Fatima. Bayan ya isa yaye sai kakanshi Malam Mahmoud Muhammad Bello limamin Bauchi na wancan lokacin, ya dauke shi, ya taso a hannunsa inda ya yi karatun AlKur'ani da sauran litattafai har zuwa shekarar 1966. Malamin ya shaida wa BBC cewa a ba tare da son kakansa ba ya tafi makarantar boko - amma abokan mahaifinsa ne suka ga dacewar haka suka tsaya aka sanya shi a makarantar mai suna Kofar Nasarawa wadda aka fi sani da Senior Day Secondary School. Su ne na farko suka fara zama a aji daya, daga aji biyu aka yi masa karin aji, inda aka sanya shi a aji hudu. Amma saboda babu aji hudu sai aka mayar da shi Kobe Primary School, inda ya shekara biyu daga shekarar 1968 zuwa 69. Daga nan ya yi jarrabawa a makarantar Arabiyya da ke garin Gombe, wato Government Arabic Teachers Collage a shekarar 1970. Bayan kammala koyarwa a matsayin malamin Arabiyya na shekara biyu, sai aka ba shi malamin aji daga nan kuma ya zama Hedimasta a shekarar 1976 lokacin da ka soma UBE. Daga bisani ya ga dacewar ya karo ilimi, sai ya tafi Jami'ar Jos ya yi Babbar Difiloma a fannin mulki, ya kuma ci gaba da aiki har ya kai matsayin shugaban ma'aikatar lura da shirye-shiryen aiki da gudanar da su. Malam Bala Ahmad ya sake komawa Jami'a, amma wannan karon ta Abukatar Tafawa Balewa, inda ya kammala a shekarar 2000. Daga nan ne, aka ba shi matsayin sakataren karamar hukuma, a kuma dai lokacin ne aka ba shi na'ibin masallacin Bauchi. Duk da kakansa ya rasu a shekarar 1990 ya ci gaba da karatu a gaban mahaifinsa. A shekarar 2021 aka tabbatar masa da mukamin limamin Bauchi har zuwa wannan shekara ta 2021. Don haka sai ya yi ritaya ya mayar da hankali kan aikin limanci. https://www.bbc.com/hausa/labarai-56683232 +religion Ku San Malamanku tare da Malam Dahir Lawan Mu'az Shirin Ku San Malamanku na wannan makon ya tattauna da Malam Dahir Lawan Mu'az, inda ya fara da bayyana tarihinsa da cewa an haife shi a unguwar Zangon bare-bari, ya tashi a cikin almajirai tare kuma suka fara karatu. Ya ce ya fara karatun firamare a makarantar Mayanka special Firamare, inda da yamma kuma suke zuwa makarantar Allo. Malamin ya ci gaba da cewa bayan ya kammala firamare mahaifinsa ya kai shi makarantar Daiba unguwar Rijiyar Lemo domin ya haddace Al-qur'ani daga shekarar 1998 zuwa 2001. Sannan ya shiga makarantar Kulliyatu Abdullahi Bayero a Kano daga 2001 zuwa 2005, sannan ya wuce jami'ar Bayero ta Kano inda na yi digirinsa na farko a harshen Larabci a shekarar 2011. Sannan kuma da na biyu a harshen Larabci a dai jami'ar ta Bayero a shekarar 2016. Ya kuma je kasashen Masar da Iran domin yin digiri na uku, amma duka bai samu ya kammala ba saboda wasu matsaloli, sai kuma daga baya ya tafi kasar Italiya inda yanzu haka a can yake kokarin kammala karatun digirinsa na uku. Malamin ya ce ''duka wuraren da ke kalmomi ko ayoyi masu kamanceceniya sun bani wahala sosai wajen hadda''. ''Ina jin dadin karanta suratul Daha, ina jin dadinta kwarai da gaske, sannan duk wani wuri da Allah ya ke bayar da kissar wani abu, to idan ina karanta shi ina jin dadi'', in ji malamin Malamin ya shaida mana cewa malamansa na farko su ne malaman da ya fara tasirantuwa da su wadanda ya fara karatun Allo a wajensu, kamar Goni Hadi Goni Idris saboda a wajensa ya fara hada baki, da karatun al-qur'ani, sai kuma malam Abdullahi Uwais wanda shi kuma sai bayan na girma na yi karatu a wajensa, sai kuma malamaina na jami'ar Bayero kaffataninsu Malamin ya ce babban abin da ke saka shi farin ciki shi ne yadda ''nake ganin matasa na shiga kokarin neman ilimi na addini da na boko, saboda ci gaban rayuwarsu''. Abin da ke bata wa malamin rai shi ne zagin magabata Malamin ya ce ''shawarata ga masu amfani da shafukan sada zumunta ita ce idan za su yi, amfani da shafukan, to su yi ta hanyar da ta dace, akwai karatuttukan manyan malamai da dama a shafukan, saboda haka ina kira ga matasa da su yi amfani da wannan wajen sauraron kartuttukan''. Malamin ya shaida mana cewa Abincin da ya fi so shi ne Doya Malamin ya ce ya yi aure tun shekarar 2014, kuma yana da mata daya da 'ya'ya uku, biyu maza daya mace https://www.bbc.com/hausa/articles/cnkjz5g77dyo +religion Ku San Malamanku tare da Malam Muhammad Mahdi Sheik Haruna Rashid An haifi Mallam Muhammad Mahdi Sheik Haruna Rashid a unguwar Fagge da ke jihar Kano a Najeriya. A tattaunawarsa da BBC ya ce ya fara karatu ne a gida wajen mahaifinsa amma kuma daga baya ya tafi Daura a jihar Katsina, wajen kakarsa. Sai kuma daga baya a shekarar 1986 inda Mallam ya ce Sayyada Maryam, wato 'yar Shehu Ibrahim Nyass ta zo Najeriya, ta tafi da su Senegal. Tun da farko dai Malam ya bayyana cewa ya fara karatu ne a wajen mahaifinsa, to amma tafiyar da Sayyada Maryam ta yi da su Senegal a can ya ci gaba da karatun Al-Qur'ani a wajenta har ya sauke ya kuma yi hadda a 1991. Bayan ya yi hadda Malam Mahdi ya ci gaba da karatun sauran littattafai a wajen Sayyada Maryam da wasu malaman har 1996. A wannan shekara ta 1996 ya samu gurbin karuta a Jami'ar Al-Azhar da ke Masar, inda ya je can har zuwa 2003 lokacin da ya kammala digirinsa na farko. Daga nan sai ya sake komawa Senegal wajen Sayyada Maryam, har 2007, ya je ya yi aikin yi wa kasa hidima wato NYSC. A shekara ta 2015 ya tafi Malaysia inda ya je ya yi karatun digirinsa na biyu, wanda ya kammala ya koma Najeriya a 2018. A yanzu haka kuma yana karatun digirinsa na uku a Jami'ar Al-Nahda da ke Maradi a Jamhuriyar Nijar. Bayan mahaifinsa, daga cikin wadanda suka koyar da shi akwai ita Sayyada Maryam, wadda idan ba a manta ba ita ce 'yar Shehu Ibrahim Nyass. Akwai kuma malamai da suka karantar da shi, wadanda su ma Sayyada Maryam ce ta kai su can suke koyar da dalibai. Daga cikin wadannan malamai ya ce akwai Malam Ghali wanda a wajensa ya fara karatun nahawu. Ya ce sun yi karatun litattafai irin su Ahlari da Risala da Kawa'idi da sauransu, musamman a wajen shi Malam Ghali. Sun kuma yi karatu musamman na haddar Al-Qur'ani a hannun Malam Tijjani Sa'idu, wanda dan uwan Malam Ghali ne, duka a Senegal. Sai dai a cikin dukkanin malaman da Sayyada Maryam ta ke kaiwa suke karantar da su, Malam ya ce, wanda suka fi tasirantuwa da shi har a yanzu shi ne Ustaz Barhama Job. Malam Mahdi ya gaya wa BBC cewa bayan ya kammala aikin yi wa kasa hidima ne sai ya samu aikin koyarwa a kwalejin gwamnatin tarayya ta Najeriya da ke garin Kazaure a Jihar Jigawa, wato Hussaini Adamu Federal Polytechnic, a 2008. Haka kuma Malam yana koyarwa a Jami'ar Al-Nahda ta Maradi a Jamhuriyar Nijar, inda a can baya muka sheda muku cewa, yana kuma karatun digirinsa na uku wato PhD a makarantar. Mallam ya ce wurin da ya wahalar da shi a Al-Qur'ani, wanda ba zai manta da shi ba, shi ne wani sumuni a Sura Al-A'raf ; Ya ce ko a lokacin da suka gama hadda aka ji su, ''Sayyada ba ta nan ta yi tafiya da ta dawo ana gabatar da mu sumunin ta fara tambaya na.'' Haka lokacin da ya shiga wata musabaka a Masar, ma Malam ya ce, wani abin ban mamaki wannan sumini dai aka fara tambayarsa. Malam ya ce surorin da ya fi so suna da yawa, amma Surah Yasin da Surah An-Najm suna daga cikin wadanda ya fi so. Ya ce yana son wadannan surorin kwarai da gaske. A yayin karatunsa ya shiga gasar haddar karatun Al-Qur'ani, inda lokacin da ya fara halartar gasarsa ta farko a Masar, ya zo na biyu a wannan gasa ta kasashen Afirka. Wannan nasara da ya samu ta faranta masa rai sosai har yanzu yana alfahari da wannan abu, bai manta da shi ba. Malam dai ya ce ya halarci gasar Qur'ani kusan sau biyar, inda ya zo na biyu a zuwansa na farko ta biyu ya zo na uku ta uku kuma ya zo na daya. Haka kuma ya halarci gasar duniya a Dubai a shekara ta 2004 inda ya wakilci kasar Senegal, inda ya zo na uku a wannan gasa. Mallam ya ce akwai lokacin da suke karatu wajen su 300 a zauren karatu, inda malamin da yake koyar da su tarihin annabawa ya yi wata tamabaya. A lokacin yana koyar da su tarihin Annabi Dauda (AS) ya yi tambaya ko akwai wanda ya haddace aya ko sumunin da yake bayar da tarihin Annabi Dauda. ''To gabakidaya hol (hall) din aka yi shiru ba wanda ya daga hannu kusan mutum 300. Akwai wani abokina wani Bamisire yana kusa da ni ya san cewar na yi haddar Al-Qur'ani yana ta cewa na daga hannu na ki dagawa, shi ya rike hannuna ya daga, malamin ya hango ni ya ce ka haddace na ce e, ya ce na tashi na tsaya ya ce to na karanta....'' in ji shi. Ya ce, ''Cikin ikon Allah, Allah Ya taimake ni na karanta ban yi bata ba duk da cewa cike ake muna dalibai,'' ''Bayan na gama ya rika yabon 'yan Afirka ya rika yabon Najeriya.'' Abubuwan bakin ciki wadanda Mallam ya ce ba zai manta da su ba su ne, rasuwar mahaifinsu Shehi, da kuma rasuwar Sayyada Maryam. Abincin da mallam ya fi so, wani abinci ne na 'yan Senegal mai farin jini a kasar, wanda ake kira  Thieboudienne ko ceebu jen ko kuma thiebou dieune. Kusan shinkafa ce dafa-duka da kifi da Bahaushen Najeriya ya sani ko kuma jollof rice da Ingilishi. Mallam yana da mata daya da 'ya'ya shida. https://www.bbc.com/hausa/articles/cp32z33x306o +religion Ku San Malamanku tare da Sheik Usman Babaliman; Alkali Omo Malamin wanda shi ne shugaban bangaren da'awa da wa'azi na kungiyar Jama'atu Nasril Islam, ya shaida wa BBC cewa a aikinsa na alkalanci ya yi shari'u da yawa masu wuya a Gombe da kuma Misau, musamman ma a Misau. Daga ciki yana iya tuna wadda ya yi da ta shafi Dan-madamin Misau. ''Wadda ta shahara sosai don Dan-madamin Misau mutum ne mai jin kansa Allah Ya karbe shi, ya rasu daga baya, don an ce ba a ma kiransa a kotu. Na ce a'a ni a Misau ba wanda ba zan kira ba sai Sarkin Misau. Sarkin Misau ne idan abu ya shafe shi na shari'a zan je fada in saurari jawabinsa in ya shafi sheda, in wani ya ce shi ne shedansa, in karbi bayaninsa amma duk kowa daga baya zan kira shi kotu kuma zai zo,'' in ji shi. Ya kara bayani da cewa, ''Da na aika masa sammaci ya ki karba ya ce sai dai a aika ma lauyansa. ''Da bai amsa kiran kotu ba, a ranar da muka zauna shari'ar sai aka ce ai ya zo ya ce zai yi bankwana zai tafi Abuja. To da na fito na bada umarni a tsare shi.'' ''To wannan shari'a ta ja hankulan mutanen Misau sosai ba wanda bai sani ba wasu ma a sanadin shari'ar suka san ni, cewar wani dan Gombe ne ya zo ya tsare Dan-madami,'' in ji shi. Tarihin Rayuwarsa A hirarsa da BBC, malamin ya ce an haife shi a garin Gombe-Abba da ke jihar Gombe a yanzu a ranar 31 ga watan Disamba a 1948, amma a lokacin a tsohuwar jihar Bauchi Ya ce ya fara karatu na Islamiyya a wajen mahaifinsa, wanda a lokacin shi ne limamin Gombe, Mallam Muhammadu. ''A wajensa na yi karatun Al'Ƙur'ani na fara littattafan ilimi, har lokacin da na dawo Gombe a 1967 wajen kakannina,'' in ji shi. Ya kara da cewa kakanninsa su ne limamin Gombe Abdullahi sannan kuma da Alkalin Pindiga, Alkali Ahmadu wanda ya ce ya yi ritaya daga Pindiga. ''A nan ne na rika karatun littattafai su fikihu da hadisai da Kur'ani da tafsiri, har zuwa 1971 da na tafi Kano,'' in ji malamin. Ya je Kano ne domin ya shiga makarantar School for Higher Islamic Studies, wato Aliya domin karatun Grade II. A 1972 ya ce ya sake komawa domin karatun difiloma, inda ya shiga Kwalejin Abdullahi Bayero, wato Jami'ar Bayero a yanzu, wadda a lokacin tana karkashin Jami'ar Ahmadu Bello, ABU Zaria. Bayan shekara uku ya kammala a 1978, inda ya samu sakamako mafi daraja (distinction), da kuma kyautuka na yabo. Bayan ya koma gida ne sai ya kama aiki da Ma'aikatar Shari'a ta jihar Bauchi a matsayin mataimakin magatakarda, wato rijistara. Daga nan ne kuma ya sake komawa Kano domin karatun digiri, wanda a lokacin kwalejin ta Abdullahi Bayero ta zama, jami'a wato Bayero University, BUK, inda bayan shekara uku, a 1982 ya gana karatun digirinsa. A wannan lokacin ma ya samu sakamako mafi kyau, inda ya zama gwarzan dalibi na sashensu da kuma na tsangayar gaba daya. Bayan da aka kirkiro Jihar Gombe daga Bauchi a 1996, sai ya zama Khadi a kotun daukaka kara ta Shari'a. Yana wannan matsayi ne har zuwa 2011 ya zama Grand Khadi, wanda bayan shekara biyu a 2013 kenan watan Disamba ya yi ritaya. Gwagwarmayar Karatu Mahaifina shi ne babban mai tasiri a rayuwata kasancewar shi ne ya dora ni a wannan hanya ta karatu da ilimi, sai lokacin da na koma Gombe, wajen Alkali Ahmadu, wanda babban malami ne, wanda da shi ne ke tafsiri a kofar gidan sarki. ''Sannan kuma Kano da na je a gidan Sheikh Nasiru Kabara na zauna wanda shahararren malami a Najeriya wanda ba irinsa a lokacin a wajensa na zauna, kuma makarantar da na shiga ta Aliya din tasa ce shi ya kafa ta, da kuma tasirin karance-karancensa na gida,'' in ji shi Yadda ya samu suna ''Alkali Omo'' A shekara ta 1984 aka mayar da shi Kumo aiki, inda a lokacin ya tarar ba a barin mutane su je sauraren sharia. Sai ya ce a'a ai shari'a darasi ce ya bayar da dama a rika zuwa ana sauraren abin da yake sa kotun ta cika makil. To kuma a duk ranar Alhamis ranar kasuwa, sai 'yan kasuwa su rika kasa kaya a kan titi suna toshe hanya. Ganin haka sai ya je wajen babban jami'in 'yan-sanda na Kumo a lokacin wanda Hamma Misau ne DPO a lokacin, sai ya ba shi 'yan-sanda ya rika bi a bude hanya, duk wanda bai kwashe kayansa ba, ya sa a kama shi a kai shi caji ofis. ''Dole mu bude hanya. To daga nan aka ce lalle an samu 'Omo mai wanke Kumo'. To daga nan ne aka sa min wannan sunan,'' in ji shi. Babban burinsa a rayuwa yanzu Ya ce babban burinsa a rayuwa yanzu tun da ya yi ritaya shi ne ya mutu da imani. Ya fita daga aiki bai tuna wani hakki da suka danne ba, wanda suke tsoro kar a tono shi. Saboda haka ya gode wa Allah. Idan akwai abin da suka yi wanda ba su sani ba bisa kuskure ''muna fatan Allah Ya gafarta mana,'' in ji shi Iyali Malamin ya ce, ''To mata a yanzu dai ina da biyu ne, biyu ne nake da su da 'ya'ya kuma ko goma sha bakwai ne.'' https://www.bbc.com/hausa/labarai-60312474 +sports Paris St Germain za ta dauki Antonio Conte ya maye gurbin Pochettino Antonio Conte zai bar Tottenham a karshen kakar bana, domin maye gurbin Mauricio Pochettino in ji wata jaridar Faransa mai suna Le Parisien. Pochettino dan kasar Argentina ya lashe Ligue 1 na kakar nan, duk da ba a kammala wasannin shekarar nan ba. Duk da a cikin watan Nuwambar 2021, Conte dan kasar Italiya ya karbi aikin jan ragamar Tottenham, wasu rahotanni na cewar yana son barin kungiyar. Jaridar ta kara da cewar mahukuntan PSG na son sallamar Pochettino, bayan da ya kasa lashe Champions League a bana, inda Real Madrid ta yi waje da ita a zangon zagaye na biyu. Ta kuma ce Conte ne ya yi wa PSG tayin aiki da kungiyar zuwa kaka biyu da niyyar yin musaya ya koma Faransa, Pochettino ya sake komawa kungiyarsa Tottenham. Sauran kwantiragin kaka daya ya rage wa Pochettino, kuma PSG za ta biya kocin fam miliyan 12,6 idan ta sallamashi wa'adinsa bai cika ba. Tun a baya an yi ta alakanta Pochettino da zai karbi aikin jan ragamar Manchester United, wadda a makon jiya ta sanar da daukar kociyan Ajax, Erik ten Hag. Le Parisien ta kara da cewar Zinedine Zidane na sha'awar karbar aikin horar da PSG, amma zai so maye gurbin Didier Deschamps idan tawagar Faransa ta kammala buga gasar kofin duniya da za a yi a Qatar a 2022. Conte baya jin dadin yadda Tottenham ke gudanar da wasanninta na kwan gaba - kwan baya, bayan da kungiyar ke fatan buga Champions League a badi. Tottenham ta taka rawar gani a gasar Premier League a baya - bayan nan, wadda ta caskara Newcastle da Aston Villa, amma sai ta yi rashi nasara a hannun Brighton da canjaras da Brentford a karshen mako, hakan ya sa ta koma ta biyar a teburi. Saboda haka Tottenham na bukatar samun gurbin buga Champions League a badi, idan har kungiyar tana son Conte ya ci gaba da jan ragamarta. https://www.bbc.com/hausa/wasanni-61221568 +sports Man City za ta yi kokarin rike Silva, Masu United sun ba Ten Hag damar babban cefane Manchester City za ta yi wa Bernardo Silva tayin sabon kwantiragi mai tsoka sosai domin shawo kansa ya tsaya a kungiyar duk da sha'awar da Barcelona da Paris St-Germain ke nunawa a kan dan wasan na Portugal mai shekara 28. (Star Sunday) Chelsea da Everton sun bi sahun Manchester United wajen duba yuwuwar sayen dan wasan gaba na Brentford Ivan Toney, dan Ingila mai shekara 26. (Sunday Mirror) Masu Manchester United sun ba wa kociyan kungiyar Erik ten Hag damar zawarcin 'yan wasan Holland biyu Frenkie de Jong, na Barcelona mai shekara 25, da Cody Gakpo, dan gaba na gefe na kungiyar PSV Eindhoven mai shekara 23, tare kuma da matashin dan wasan gaba na gefe dan Brazil, Antony mai shekara 22 da ke Ajax. (Sunday Mirror) Sai dai kuma bisa ga dukkan alamu United din za ta rasa dan gaban Chelsea Christian Pulisic, saboda Ba'amurken ya zaku ya koma wata kungiya da za ta buga gasar Zakarun Turai idan ya bar Stamford Bridge. (Mail Online) Ita kuwa Real Madrid za ta yi amfani da kudin da ta samu daga cinikin sayar wa Manchester United Casemiro ta nemi sayen matashin dan wasan tsakiya Jude Bellingham, dan Ingila mai shekara 19 da ke Borussia Dortmund (Marca - in Spanish) Aston Villa ta amince ta sayar wa Watford Ismaila Sarr, dan gaban Senegal mai shekara 24. (Foot Mercato via Inside Futbol) Newcastle kuwa ta kafe tana son sayen abokin wasan Sarr Joao Pedro a kan Fam miliyan 25 bayan da Watford din ta ki yarda da tayi har biyu da aka yi wa matashin dan wasan na Brazil mai shekara 20. (Fabrizio Romano) Tottenham da Leeds da Southampton na sha'awar sayen dan wasan tsakiya na Manchester United James Garner, duk da cewa matashin dan wasan na Ingila mai shekara 24 bai fara buga wasan Premier ba daga farko. Sai dai dukkanin kungiyoyin uku ba su da niyyar biyan fam miliyan 14 da kungiyar ta Old Trafford ta sa masa. (Sun on Sunday) Everton ta fara tattaunawa da golan Ingila Jordan Pickford, mai shekara 28, kan kulla sabon kwantiragi da shi. (Mail Online) Arsenal na son zawarcin dan wasan Ukraine Mykhaylo Mudryk, mai shekara 21 daga Shakhtar Donetsk. (Foot Media, via Sun) West Ham da Newcastle da Everton da Leicester da kuma Southampton aredukkansu n sha'awar dan wasan tsakiya na Manchester United, Scott McTominay, dan Scotland mai shekara 25. (90 Min) A shirye dan wasan gaba na Holland Memphis Depay, mai shekara 28, yake ya kawo karshen kwantiraginsa da Barcelona saboda sha'awarsa da Juventus take. (Fabrizio Romano) Marseille ta cimma yarjejeniya da Manchester United a kan Eric Bailly, inda dan bayan na Ivory Coast mai shekara 28 zai je aro, amma kuma kungiyar ta Faransa tana da damar saye shi dindindin. (Fabrizio Romano) https://www.bbc.com/hausa/articles/cxxpzej1ly4o +sports 'Yan wasan La Liga da yarjejeniyarsu za ta kare a bana Kungiyoyi da yawa a Sifaniya sun fara cefanen tunkarar kakar badi a lokacin da yarjejeniyar wasu 'yan wasan za ta kare a karshen kakar nan. Ranar 1 ga watan Yuli za a bude kasuwar saye da sayar da 'yan kwallon kafa a Sifaniya, wadda ake sa karkare cinikayya ranar 2 ga watan Satumbar 2022. Real Madrid ce ta lashe kofin La Liga na bana, kuma na 35 jumulla, inda Karim Benzema ya dauki takalmin zinare a matakin wanda ke kan gaba a yawan cin kwallaye a babbar gasar tamaula ta Sifaniya, mai 27 a raga. Real Madrid ta dauki La Liga da maki 86 tun kan a karkare wasannin bana, inda Barcelona ta yi ta biyu mai maki 73. Kungiyoyin da za su wakilci Sifaniya a Champions League a badi, sun hada da Real Madrid da Barcelona da Atletico Madrid da kuma Sevilla. Ranar Asabar Real Madrid ta lashe Champions League na bana, kuma na 14 jumulla, bayan da ta doke Liverpool da ci 1-0 a karawar da suka yi a birnin Paris din Faransa. Wadanda za su buga gasar Europa League a Sifaniya a badi kuwa, sun hada da Real Betis da Real Sociedad. Haka kuma kungiyar Villareal wadda ta lashe Europa a bara ta kai daf da karshe a Champions League a bana da Liverpool ta fitar da ita, za ta fafata a Conference League. Wadanda suka yi ban kwana da La Liga a kakar nan sun hada da Granada da Levante da kuma Deportivo Alaves. Tuni wasu kungiyoyin suka fara cefane don kara karfin tunkarar kakar badi, yayin da wasu 'yan wasan yarjejeniyarsu za ta kare a karshen kakar bana. Jerin wasu 'yan wasan da kwantiraginsu zai kare a karshen kakar bana: Ousmane Dembele (Barcelona) Serge Aurier (Villarreal) Adnan Januzaj (Real Sociedad) Luis Suarez (Atletico Madrid) Luka Modric (Real Madrid) Isco (Real Madrid) Felipe (Atletico Madrid) Sergi Roberto (Barcelona) Joselu (Alaves) Cristian Tello (Real Betis) Sergio Asenjo (Villarreal) Sime Vrsaljko (Atletico Madrid) Gareth Bale (Real Madrid) Denis Cheryshev (Valencia) Marcelo (Real Madrid) Hector Herrera (Atletico Madrid) zai koma Houston Dynamo ranar 1 ga watan Yuli Radamel Falcao (Rayo Vallecano) Carlos Bacca (Granada) Joaquin (Real Betis) Nolito (Celta Vigo) Nacho Monreal (Real Sociedad) Javier Pastore (Elche) Martin Caceres (Levante) Bebe (Rayo Vallecano) Dani Alves (Barcelona) https://www.bbc.com/hausa/wasanni-61673133 +sports Wasan Liverpool da na Real Madrid da suka rage kafin su kara a Champions League Real Madrid da Liverpool za su fafata a wasan karshe a Champions League na bana ranar 28 ga watan Mayu a Faransa. Liverpool ta kawo wannan matakin bayan da ta fitar da Villareal, ita kuwa Real Madrid nasara ta yi a kan Manchester City. Tuni Real Madrid ta lashe kofin La Liga na bana, bayan da Liverpool ke harin cin kofi biyu kafin su fafata a wasan karshe a Gasar Zakarun Turai ta bana. Sauran wasa hudu ya rage da Real Madrid za ta buga a La Liga, wadda za ta fuskanci karawar hamayya da Atletico Madrid a Wanda Metropolitano ranar Lahadi. Daga nan za ta karbi bakuncin Leavante ranar Alhamis, sannan ta ziyarci Cadiz kwana uku tsakani, sai ta karkare da wasa da Real Betis a Santiago Bernabeu. Wasannin za su yi tsauri a karawa da Atletico Madrid da Real Betis, wadanda ke neman gurbin shiga Champions League a badi. Haka kuma Real za ta fuskanci kalubale a karawar da za ta yi da Levante da kuma Cadiz, wadanda ke fuskantar barin babbar gasar tamaula ta Sifaniya ta bana. Sai dai Real Madrid za ta so ta ci gaba da zama kan ganiya kafin wasan karshen, hakan ne zai sa ta ajiye wasu 'yan wasan su huta kafin karawar karshe a Champions League, damar da Liverpool ba ta da ita kenan. Liverpool tana ta biyu a teburin Premier League da tazarar maki daya tsakaninta da Manchester City mai jan ragama, kuma mai rike da kofin bara. Liverpool za ta karbi bakuncin Tottenham a Anfield ranar Asabar, daga nan ta ziyarci Aston Villa ranar Talata. Daga nan Liverpool za ta kece raini da Southampton a St Mary ranar 17 ga watan Mayu, sannan ta karkare kakar bana a Premier da karawa da Wolverhampton Wanderers ranar 22 ga watan Mayu. Liverpool za ta buga wasan karshe a FA Cup ranar 14 ga watan Mayu da Chelsea, wadda za ta dauki fansa, bayan da kungiyar Anfield ta yi nasarar cin Caraboa Cup a bana. Liverpool wadda ta lashe Caraboa Cup na fatan cin kofi hudu a bana, ba wata kungiya a Ingila da take da wannan bajintar. Liverpool na sa ran daukar FA da Premier League da kuma Champions League ta hada da Caraboa Cup da ta fara ci a bana. Real Madrid tana da Champions League 13 jumulla, ita kuwa Liverpool shida ne da ita. https://www.bbc.com/hausa/wasanni-61349600 +sports Real Madrid 0-4 Barcelona: Barca ta hada maki uku a Bernabeu Barcelona ta doke Real Madrid 4-0 a wasan mako na 29 a gasar La Liga da suka kara a Santiago Bernabeu ranar Lahadi. Pierre-Emerick Aubameyang ne ya fara cin kwallo, sai Ronald Araujo ya kara na biyu sannan suka je hutun rabin lokaci, Bayan da suka koma wasan zagaye na biyu ne Ferran Torres ya kara na uku, daga baya Pierre-Emerick Aubameyang ya ci na hudu, kuma na biyu da ya zura a raga a wasan farko da ya buga a El Clasico. Aubameyang ya ci kwallo tara a karawa 11 da ya yi wa Barcelona tun bayan da ya koma Camp Nou a watan Fabrairu daga Arsenal a matakin wanda bai da kwantiragi. Da wannan sakamakon Barcelona ta yi wasa 12 a jere ba tare da an doke ta ba, sannan ta kawo karshen fafatawa 11 da Real Madrid ta yi ba tare da an yi nasara a kanta ba. Kungiyoyin biyu sun hadu sau biyu a bana kafin ranar Lahadi, inda Real Madrid ta ci 3-2 a Spanish Super Cup a Saudi Arabia ranar 12 ga watan Janairun 2022. Kafin nan Barcelona ta yi rashin nasara da ci 2-1 a Camp nou a gasar La Liga ranar 24 ga watan Oktoban 2021. Real Madrid tana mataki na daya da maki 66 a kan teburin La Liga a kakar nan da tazarar maki 12 tsakaninta da Barcelona mai kwantan wasa mai maki 54 ta uku a teburin. Benzema bai samu damar fuskantar Barcelona ba, wadda itace ta hudu a jerin kungiyoyin idan ya hadu da su sai ya ci kwallo mai 11 a raga, ya kuma bayar da 10 aka ci Barcelona a karawar da ya yi da ita. Benzema shi ne kan gaba a cin kwallaye a gasar La Liga ta bana mai 22 kawo yanzu, sai Enes Unal na Getafe da Vinicius Junior na Real Madrid da kowanne keda 14 a raga. 'Yan wasan Real Madrid da suka fuskanci Barca: Masu tsaron raga: Courtois, Lunin, Diego. Masu tsaron baya: Carvajal, E. Militão, Alaba, Vallejo, Nacho, Marcelo. Masu buga tsakiya: Kroos, Modrić, Casemiro, Valverde, Lucas V., D. Ceballos, Isco, Camavinga. Masu cin kwallaye: Hazard, Asensio, Jović, Bale, Vini Jr., Rodrygo, Mariano. 'Yan wasan Barcelona da suka fafata da Real Madrid: Ter Stegen, Piqué, R. Araujo, Sergio, Riqui Puig, O. Dembélé, Dani Alves, Memphis, Adama da kuma Braithwaite. Sauran sun hada da Neto, Nico, Lenglet, Pedri, L. De Jong, Jordi Alba, Ferran, F. De Jong, O. Mingueza, Eric, Aubameyang, Gavi and Arnau Tenas. Wadanda ke jinya a Barcelona kawo yanzu sun hada da Dest, Ansu Fati, Sergi Roberto da kuma Samuel Umtiti. https://www.bbc.com/hausa/wasanni-60812782 +sports Nathan Redmond ya koma Besiktas daga Southampton "Dan wasan gaba na Ingila Nathan Redmond ya bar Southampton ya koma Besiktas a matsayin cikakken dan wasanta. Tun a 2016 dan wasan ya koma Southampton daga Norwich City, kuma a bara ne kwatantaraginsa ta kare a St Mary's. Ya buga wa kungiyar wasa 232 ya kuma ci mata kwallo 30. ""Sauyi ne mai kyau a wurinsa, bayan share shekaru shidda a wuri guda,"" in ji kocin kungiyar Ralph Hasenhuttl. ""Mun ji dadin kasancewa tare da shi, na tsawon kusan shekara hudu,"". ""Gaskiya muna da alaka mai kyau da shi har lokacin tafiyarsa, akwai lokacin da ya nuna kwarewarsa a fannin wasanni da dama."" Ya kara da cewa: ""Babban sauyi ne mai kyau a gare shi kuma ina ganin ya yi zabin da ya dace.""" https://www.bbc.com/hausa/articles/crg28rq6ppvo +sports Bahagon Ali Kawoji ya buge Dogon Sisco Bahagon Ali Kawoji ya yi nasarar doke Dogon Sisco a turmin farko a damben da suka yi a filin wasa da ke Ado Bayero Square a Kano, Najeriya. Shi ne karo na biyu da suka yi damben a tsakaninsu, bayan da Bahagon Ali Kawoji Guramada ke korafin cewar baya son Dogon Sisco daga Kudu ya ke yin kafa idan suna dambe. https://www.bbc.com/hausa/wasanni-61673134 +sports Aurelien Tchouameni: Real Madrid ta sayi ɗan wasan Monaco Real Madrid ta kammala ɗaukar matashin ɗan wasan tsakiya na Faransa daga ƙungiyar Monaco kan yarjejeniyar shekara shida. Ƙungiyoyin biyu sun sanar da cinikin, inda Real ta ce za ta ƙaddamar da ɗan wasan mai shekara 22 ranar Talata bayan an kammala duba lafiyarsa. Tchouameni ya buga wasa 35 a gasar Lig 1 ta Faransa ga Monaco a kakar wasa da aka kammala, inda ya ci kwallo uku da taimakawa wajen cin biyu. Kazalika, ya buga wa ƙasarsa Faransa wasa 11 tun da ya saka mata jasi a watan Satumba. Rahotanni sun ce Real za ta biya yuro miliyan 80 da kuma tsarabe-tsarabe da suka kai miliyan 20 - yuro miliyan 100 ke nan jumilla. An yi ta alaƙanta Tchouameni da Liverpool, da Manchester United, da kuma Paris St-Germain. Wasu rahotannin ma sun ce ɗan wasan har ya amince wa Liverpool kafin daga baya ya ƙulla yarjejeniya da Real. Madrid ta cefano Tchouameni bayan ta gaza samun Kylian Mbappe a ƙarshen kakar da ta gabata. https://www.bbc.com/hausa/wasanni-61771131 +sports Real Madrid ta ci wasa na biyu a jere a La Liga bayan casa Celta Real Madrid ta hada maki shida a wasa na biyu a La Liga ta bana, bayan da ta je ta casa Celta Vigo 4-1 ranar Asabar. Karim Benzema ne ya fara ci wa Real kwallo a bugun fenariti, mai masaukin baki ta farke ta hannun Iago Aspas, shima a bugun daga kai sai mai tsaron raga. Modric ne ya ci wa Real na biyu daga yadi na 25, bayan da David Alaba ya bashi kwallo. Daga nan dan wasan Croatia, mai shekara 36 ya bai wa Vinicius Jr kwallo shi kuma ya jefa a ragae Agustin Marchesin. Federico Valverde ya kara na hudu a wasan da Real ta hada makinta uku. Real ta kara samun bugun fenariti a karo na biyu, inda Eden Hazard, wanda ya shiga wasan daga baya ya buga amma mai tsaron raga Marchesin ya tare. Tsohon dan kwallon Chelsea ya ci kwallo hudu a wasa 50 da ya yi wa Real Madrid a La Liga. Kawo yanzu Real ta yi nasara a dukkan wasa uku da fara yi a kakar nan, inda ta doke Eintracht Frankfurt a Uefa Super Cup da Almeria a wasan farko a La Liga. Modric - wanda magoya bayan Celta suka yi tafi - ya ci kwallo a kalla daya a lik a gasar Bosnia da Croatia da England da Sifaniya a kowacce kaka. Kuma 19 daga kwallo 33 da ya zura a raga a La Liga daga wajen da'ira ta 18 ya ci. Rabon da Carlo Ancelotti ya yi rashin nasara a wasan La Liga a kan kungiyar da ba daga cikin birnin Madrid ba, tun doke ta Barcelona ta yi a Janairun 2021. 'Yan wasan da Real ta je da su Celta: Masu tsaron raga: Courtois, Lunin da Luis López. Masu tsaron baya: Carvajal, E. Militão, Alaba, Vallejo, Nacho, Rüdiger da F. Mendy. Masu buga tsakiya: Modrić, Camavinga, Valverde, Lucas V., Tchouameni da D. Ceballos. Masu cin kwallaye: Hazard, Benzema, Asensio, Vini Jr. da Mariano. https://www.bbc.com/hausa/articles/c4n3mp3dkzro +sports Henry ya sayi hannun jari a kungiyar Como mai buga Serie B An gabatar da Thierry Henry a matakin wanda ya sayi hannun jari a kungiyar Como mai buga gasar Italiya ajin Serie B. An gabatar da tsohon zakakurin dan kwalon tawagar Faransa da Arsenal a gaban 'yan jarida tare da tsohon kyaftin din Chelsea, Dennis Wise a matakin babban jami'i. Como ta fara daga matakin 'yan dagaji har zuwa gasar Italiya mai daraja ta biyu, wadda ta dauki Cesc Fabregas a farkon watan nan, domin ya taka mata leda. Haka shima Fabregas, mai shekara 35 yana da hannun jari a kungiyar. Wani katafaren kamfanin taba a Indonesia mai suna Djarum ne ya mallaki Como, kungiyar da ta bar gasar Serie A a 2003. Bayan da kungiyar ta tsiyace a 2016 ta sa kaimi daga matakin gasa mai daraja ta hudu har zuwa ta 13 a kan teburin Serie B a kakar da ta wuce. Kawo yanzu ba a fayyace rawar da Henry zai taka a kungiyar da ya sayi hannun jarin ba. Henry, mai shekara 45 wanda ya yi ritaya a 2015, shi ne mataimakin kociyan tawagar Belgium. Ranar Litinin Como ta sanar da daukar Patrick Cutrone daga Wolves, kungiyar na fatan sake komawa buga gasar Serie A. https://www.bbc.com/hausa/articles/cw0n9ljw708o +sports West Ham ta kammala daukar Nayef Aguerd West Ham United ta kammala daukar dan wasan Rennes, mai tsaron baya, Nayef Aguerd kan fam miliyan 30. Dan kwallon tawagar Morocco, ya buga wa Rennes wasa 66, tun bayan da ya koma kungiyar daga Dijon a 2020. Aguerd, wanda ya buga wa tawagar Morocco wasa 25, yana cikin 'yan kwallon da suka kai kasar karawar daf da na kusa da na karshe a gasar kofin nahiyar Afirka da aka yi a Kamaru. Ya kuma buga wasan cike gurbi da Morocco ta doke Congo ta kuma samu gurbin shiga gasar kofin duniya da za a yi a Qatar a 2022. Dan wasan ya zama na hudu da West Ham ta dauka kawo yanzu, bayan Sebastien Haller da Felipe Anderson da kuma Kurt Zouma. https://www.bbc.com/hausa/articles/cjr950lvqqgo +sports Ko Sadio Mane zai ci gaba da taka leda a Liverpool a badi? Kungiyoyi da dama na shirye-shiryen tunkarar kakar badi, sai dai har yanzu ba a fayyace makomar Sadio Mane a Liverpool ba. Times ta wallafa cewar kungiyar Anfield ba ta amince da tayin fam miliyan 25 da Bayern Munich ta yi wa dan kwallon Senegal mai shekara 30 ba. Liverpool ta yi wa Mane farashin sama da fam miliyan 40 ga duk mai son sayen dan kwallon, wanda ya ke Anfield tun 2016 daga Southampton, saura kaka daya yarjejeniyarsa ta kare. Ana Alakanta Mane da komawa Bayern Munich, bayan da Robert Lewawdoski ya ce zai bar kungiyar a kakar nan - watakila ya koma buga La Liga a Barcelona a badi. Haka kuma Munich ba ta da tabbas ko dan wasa Serge Gnabry zai ci gaba da taka leda a kungiyar a badi ko akasin hakan. A karshen mako ne Senegal ta doke Benin 3-1 a wasan neman gurbin shiga gasar kofin Afirka, kuma Mane ya ci biyu a karawar, daya a bugun fenariti. Hakan ne ya sa Mane ya zama kan gaba a yawan ci wa Senegal kwallaye mai 32 a raga a wasa 90 da ya yi mata. Henri Camara ne a baya mai kwallo 31 ke kan gaba a ci wa Senegal kwallaye a tarihi. Mane appeared to suggest last week he wanted to leave but he said after Senegal's 3-1 win over Benin in Africa Cup of Nations qualifying https://www.bbc.com/hausa/wasanni-61706566 +sports Morocco ta fitar da Sifaniya daga Gasar Kofin Duniya a Qatar A karon farko Morocco ta kai daf da na kusa da na karshe, bayan da ta yi nasara a kan Sifaniya a bugun fenariti a Gasar Cin Kofin Duniya da Qatar ke karbar bakunci. Tawagogin biyu sun buga minti 90 ba ci daga nan aka yi karin minti 30, sannan aka kai minti 120 ba ci aka je bugun daga kai sai mai tsaron raga. Abdelhamid Sabiri ya fara ci wa Morocco kwallo, sai Sifaniya ta barar da daya ta hannun Pablo Sarabia. Hakim Ziyech na Morocco ya kara na biyu, sai Carlos Sole daga Sifaniya ya kasa cin wadda ya buga. Sai dai kuma Badr Benoun ya kasa ci wa Morocco ta uku, kenan tawagar Afirka ta ci biyu kenan. Sifaniya ta buga ta uku ta hannun kyaftin, Sergio Busquet, amma Bono ya tare, wanda ya hana ta Sole shiga raga. Achrat Hakimi ne ya buga na uku ya kuma zura a raga, inda Morocco ta kai zagayen gaba da ci 3-0. Morocco za ta kara da duk wadda ta yi nasara tsakanin Portugal da Switzerland ranar Asabar a fafatawar Quarter finals. https://www.bbc.com/hausa/articles/c3g5e3z46nwo +sports Hankalin Ronaldo ya rabu, Man Utd na tattaunawa kan Gakpo Cristiano Ronaldo, ya samu tayi daga kungiyar Al-Nassr ta Saudiyya wadda za ta  ba shi kudin da ya kai fam miliyan 150 a shekara, bayan rabuwarsa da Manchester United. Dan wasan na Portugal na dab da cimma yarjejeniya da kungiyar ta Saudi Arabia. Sai dai kuma ana ganin tauraron na Portugal har yanzu yana son taka leda a gasar Zakarun Turai saboda haka har yanzu bai yanke shawara kan ansar wannan tayi ba. Manchester United na tattaunawa da wakilan dan gaban PSV Eindhoven Cody Gakpo kan sayen dan wasan na Netherlands a watan Janairu. Watakila matashin dan wasan tsakiya na Brighton Billy Gilmour dan Scotland ya tafi Villarreal aro a watan Janairu. Dan wasan tsakiya na Sifaniya Sergio Busquets, na sha’awar tafiya kungiyar Inter Miami ta gasar Amurka idan kwantiraginsa ya kare da Barcelona a watan Yuni. Dan gaban kungiyar Los Angeles FC Gareth Bale, zai yanke shawara game da kungiyarsa a watan Fabrairu bayan da ya gaya wa Wales cewa yana sha’awar ci gaba da taka wa yankin leda. Liverpool za ta dauki tsohon mai yi wa Arsenal zawarcin ‘yan wasa Sven Mislintat, wanda ya yi aiki da Jurgen Klopp a Borussia Dortmund, a matsayin wanda zai maye gurbin Julian Ward darektan wasanninta. Wakilin dan wasan tsakiya na Ivory Coast Franck Kessie, wanda ya bar AC Milan zuwa Barcelona a watan Yuli  ya kawar da yuwuwar komawar dan wasan Italiya sakamakon rahotannin da ke cewa Inter Milan na zawarcinsa. Manchester United ta bi sahun Arsenal a zawarcin matashin dan bayan Scotland Jack Wylie mai shekara 15 daga Rangers. Darektan wasanni na Barcelona Jordi Cruyff ya ce taurarin na Sifaniya na bin diddigin matashin dan wasan tsakiya na Ghana Mohammed Kudus dan Ajax. https://www.bbc.com/hausa/articles/cy0nr9j12e7o +sports Juventus za ta fuskanci Messi da Neymar da Mbappe a Faransa Ranar 10 ga watan Agustan 2021 duniyar kwallon kafa ta girgiza, bayan da Lionel Messi ya koma Paris St Germain da taka leda daga Barcelona. Kowa ya yadda da cewar Messi da Barcelona sun yi auren zobe ba mai raba su, sai dai bayan da kungiyar Camp Nou ta fada matsin tattalin arziki ya zama dole Messi ya bar kungiyar. Komawar kyaftin din Argentina zuwa Faransa da taka leda, kungiyar ta hada shi wasa da Neymar da Kylian Mbappe domin buga wasanni tare. A kakar farko ba su taka rawar gani ba, duk da kungiyar ta lashe Ligue 1, 'yan wasan uku sun ci karo da kalubale duk da kwarewar da suke da ita a fannin taka leda. Rashin kwazon su ya sa Real Madrid ta yi waje da PSG a Champions League a zagayen kungiyoyi 16 a bara, kofin da kungiyar Faransa ba ta taba dauka ba. Tsohon kociyan PSG, Mauricio Pochettino ya taka rawar gani wajen hada 'yan wasan da ke kungiyar a yanzu haka da ya kamata a bashi lokaci ya nuna kansa. Kociyan ya dauki salon 4-3-3, inda ya bai wa Messi da Neymar damar gara kwallo daga gefen fili su shigo da ita tsakiya, idan da hali su nemi Mbappe ko su ci kwallo da kansu. Kafin PSG ta karbi bakuncin Juventus a wasan farko a cikin rukuni a Champions League ranar Talata, menene ya canji bayan tafiyar Pochettino? Shin ko daukar sabon koci Christopher Galtier zai bai wa kungiyar samun nasarar lashe kofin Zakarun Turai a bana? Sabon kocin ya saita 'yan wasan uku a kakar nan Messi da Neymar da Mbappe sun fara kakar bana da cin kwallo 32 da taimaka wa wajen bayar wa a zura a raga a koda yaushe, bayan da kocin ya koma salon taka leeda 3-4-3. Neymar da Messi sun ci kwallo 22 a tsakaninsu a kakar nan, bayan wasa shida a babbar gasar tamaula ta Faransa, wadanda a bara suka zura 36 a raga a dukkan fafatawa a kakar da ta wuce. Yadda mai tsaron baya Sergio Ramos da Marquinhos ke raba kwallo da yadda Presnel Kimpembe ke kai kwallo ga 'yan tsakiya cikin natsuwa, ya sa PSG kan gara tamaula ta kuma mamaye wasa da kaso mafi rinjaye tun daga baya zuwa gaba. Salon da kungiyar ke takawa a bana ya dace da yadda 'yan wasan gefe daga baya Nuno Mendes da Achraf Hakimi ke taka rawar gani wajen gudu da kwallo zuwa gaba su kuma bai wa wanda ya kamata daga inda ya dace. Hakan ya kan ba su damar kai kwallo gaban, sannan su dawo tsare gida su kuma taimakawa masu buga tsakiya a PSG a sabon salon da aka dora kungiyar. Galtier ya gamsu da kwazon da Marco Verratti ke yi daga tsakiya tare da sabon dan kwallon da ta dauka Vitinha, wanda ya taka leda a Wolves a kuma gasar Premier League. A kalla Verratti kan raba kwallo sau 83 a kowanne wasa shi kuwa Vitinha kan yi sau 52, yadda suke bai wa 'yan baya daga gefe su kuma mikata ga masu cin kwallaye su ukun ya kara fito da kwazon kungiyar. Wadan nan da ke buga wa PSG tsakiya sun karbi aikin yadda ya kamata domin ba sa barin 'yan gaban su tsaya ba tare da kai musu tamaula ba a koda yaushe. Hakan ne ya sa aka bai wa Neymar da Messi da Mbappe damar watayawa a fili da suke abin da suka ga ya dace domin kungiyar ta samu nasara a wasanninta. Daman kowanne gwani ne wajen murza leda wato Messi da Neymar da Mbappe, idan suna tmurza ttamaula a bana, gwanin ban sha'awa. Koda yake sun dan samu matasala musamman daga Mbappe da ya fara son kai cewar bugun fenariti shi kadai zai ke yi, to amma yanzu an dinki barakar komai ya koma yadda ya dace. Salon da sabon koci yake yi a yanzu ya bai wa Messi da Neymar da Mbappe taka leda kusa da kusa ba wahalar da juna, hakan ya sa suke raba kwallo a tsakaninsu sannan suke cin kwallaye. Messi da Neymar kowa ya bayar da kwallo shida-shida aka zura a raga, sune kan gaba a wannan bajintar a dukkan manyan gasar Turai biyar a kakar nan. PSG tana rukuni daya da Juventus da Benfica da Maccabi Haifa a bana a Champions League.. Wannan shi ne karon farko da kungiyar ta Faransa za ta fuskanci Juventus a Champions League. PSG wadda ke fatan daukar kofin Zakarun Turai domin ake sakata cikin sahun manyan kungiyoyin tamaula a Turai za ta yi kokarin ganin ta kai zagayen gaba, wanda tuni masana suka hangi haka. Juventus da Benfica za su iya bai wa kungiyar ta Faransa matsala, domin sun lashe Champions League a baya sun san dadin kofin. Saboda haka dama ce ga PSG ta saka kwazo a kakar nan, bayan da 'yan wasanta uku fitattu Messi da Neymar da Mbappe suka kama da wuta a kakar nan. https://www.bbc.com/hausa/articles/ckmyx1nym21o +sports An ci tarar Pillars miliyan tara an kuma kwashe mata maki uku rigis Hukumar gudanar da gasar Firimiyar Najeriya ta ci tarar Kano Pillars naira miliyan tara, bayan da ta sameta da laifin karya dokar gasar. Haka kuma hukumar ta kwashe maki uku daga wanda Pillars take da shi, duk dai a cikin hukuncin da aka yanke mata. Wannan hukuncin ya biyo bayan da magoya bayan Pillars suka ragargaji motar Katsina United, bayan wasan hamayya da Katsina United karawar mako na 22 ranar Lahadi a filin wasa na Sani Abacha da ke jihar Kano. Shi ne kuma karon farko da Pillars ta yi fafatawa a gida, tun bayan kaka biyu da take buga wasanninta a jihar Kaduna, bayan da filin wasa na Sani Abacha bai cika ka'idar karbar bakuncin wasannin Firimiyar Najeriya ba. Kawo yanzu Pillars za ta biya tarar naira miliyan tara, an kuma kwashe mata maki uku, za ta koma buga wasannin da suka rage mata a filin wasa na MKO Abiola da ke babban birnin tarayya Abuja, Najeriya. Haka kuma za a sake cire mata maki uku nan gaba idan an sake samun kungiyar da tayar da hatsaniya. Cikin hukuncin an umarci Sai masu gida da ta gyara motar Katsina United da aka lalata a lokacin da za ta karkare wasanninta a Abuja. Da wannan maki ukun da aka kwashe, Pillars ta yi kasan teburi zuwa ta 16 da tazarar maki biyu tsakaninta da ƴan karshen teburi. Pillars dun za ta buga wasan mako na biyun da ba a karashi ba da Katsina United a Abuja ranar Litin. https://www.bbc.com/hausa/wasanni-61141411 +sports Bayan korar Steven Gerrard Aston Villa ta ci 4-0 a Premier Aston Villa ta doke Brentford 4-0 a wasan mako na 13 a gasar Premier League da suka kara a Villa a Park ranar Lahadi. Villa ta buga wasan na babbar gasar tamaula ta Ingila a karon farko a bana tare da kociyan rikon kwarya, Aaron Danks. Villa ta sallami Gerrard ranar Alhamis 20 ga watan Oktoba, bayan da Fulham ta ci 3-0 a wasan Premier League karawar mako na 12. Wannan shi ne karon farko da aka ci kwallaye uku cikin sauri karkashin sabon koci kuma a ranar farko da ya ja ragamar kungiya. Cikin minti 14 da fara wasa Villa ta zura kwallo uku a ragar Brentford, inda minti biyu da take leda Leaon Bailey ya fara cin kwallo. Danny Ings ne ya kara na biyu a minti bakwai, sannan ya ci na uku na biyu a wasan a bugun fenariti a minti na 14. Bayan da aka koma zagaye na biyu ne Ollie Watkins ya ci Brentford kwallo na hudu. Villa ta kori Gerrard, wanda ta dauka aiki ranar 11 ga watan Nuwambar 2021, bayan jan ragamar wasa 40 da cin karawa 13 da canjaras takawas aka doke shi fafatawa 19. Wasa biyu kacal tsohon dan wasan Liverpool ya yi nasara a bana, shi ne wanda ya doke Everton da Southampton da canjaras uku. https://www.bbc.com/hausa/articles/cek2r4l59j2o +sports Man City ta dare kan teburin Premier League Manchester City ta yi nasara a kan Leicester City da ci 1-0 a wasan mako na 14 a gasar Premier League da suka kara a King Power ranar Asabar. City ta ci kwallon ta hannun Keven de Bruyne, bayan da suka koma zagaye na biyu a wasan. De Bruyne wanda ya ci kwallon a bugun tazara ya zama na uku a Premier League cikin wadanda suka ci kwallaye daga wajen da'ira ta 18. Mai wannan bajintar shi ne David Beckham mai kaso 55 cikin 100, sai na biyu shi ne Christian Eriksen mai kaso 44 cikin 100, sannan De Bruyne mai 42 cikin 100. Erling Haaland bai buga wasan ba, bayan rauni da ya ji a gasar Champions League a fafatawa da Borussia Dortmund Da wannan sakamakon, City wadda ta yi wasa 12 tana ta daya a kan teburin Premier League da tazarar maki daya tsakaninta da Arsenal. Arsenal wadda take ta biyu mai wasa 11 mai maki 28 za ta karbi bakuncin Nottingham Forest ranar Lahadi. Forest ita ce ta karshen teburi ta 20 mai maki tara, bayan karawa 12 da ta yi. A dai ranar ta Lahadi 30 ga watan Oktober za a fafata tsakanin Manchester United da West Ham United a Old Trafford. https://www.bbc.com/hausa/articles/c1evx94j2wyo +sports Yannick ya koma Barca, bayan da kwantiraginsa ya kare a AC Milan Barcelona ta cimma yarjejeniyar daukar Franck Yannick Kessier, wanda kwantiraginsa ya kare a AC Milan a watan jiya. Dan wasan zai sa hannu kan yarjejeniyar da za ta kare ranar 30 ga watan Yunin 2026. Haka kuma Barcelona ta sa farashin yuro miliyan 500 ga duk kungiyar da ke son daukar dan wasan, idan yarjejeniyarsa ba ta kare ba a Camp Nou. Ranar Laraba 6 ga watan Yuli, Barcelona za ta gabatar da Franck Yannick Kessie a matakin dan wasanta. An haifi Franck Kessie ranar 19 ga watan Disambar 1996 a garin Ouragahio da ke Ivory Coast. Mai taka leda daga tsakiya ko tsaron baya daga tsakiya ya fara tamaula a Stella Club d'Adjame ta Ivory Coast daga baya ya koma Atalanta a 2014. Bayan da ya taka rawar gani a kakar 2016/17 a Atalanta, daga nan ne AC Milan ta yi zawarcin dan kwallo. Dan wasan ya koma Milan buga wasannin aro a 2017 daga nan ta saye shi a 2019 kan yuro miliyan 33. Kaka biyar da Kessie ya yi a Milan ya kara samun gogewa, ya kuma ci kwallaye, ya kuma bayar an zura a raga. Dan wasan tawagar Ivory Coast ya taimakawa Milan ta dauki Serie A a kakar da aka Karkare, kofin farko da ta dauka tun bayan kaka 11.. https://www.bbc.com/hausa/articles/cld2g493r9qo +sports PSG na shirin kashe kuɗi kan Rashford, Felix ya yi kasuwa Paris St-Germain na son mayar da ɗan wasan gaban Ingila Marcus Rashford ɗaya daga cikin ƴan wasan da aka fi biyan kuɗi a duniya a daidai lokacin da suke shirin sayensa, kwantiraginsa na daf da ƙarewa a Manchester United. (Mirror) Kocin Manchester United Erik ten Hag ya ce kulob ɗin zai zaɓa ko ya tsawaita kwantiragin Rashford da ɗan wasan bayan Portugal mai shekara 23 Diogo Dalot har zuwa 2024 ganin cewa sun soma tattaunawa kan batun tsawaita kwantiragin ƴan wasan. (Metro) Hukumar ƙwallon ƙafa ta Brazil na shirin neman kocin Manchester City Guardiola domin gano ko yana son zama shugaban ƙungiyar ƙasar a ƙarshen kaka. (Sport - in Spanish) Chelsea da Manchester City da Manchester United duk sun bayar da buƙatunsu na ɗan wasan Croatia mai shekara 20 Josko Gvardiol sai dai kuma ita ma Bayern Munich na neman ɗan wasan bayan na RB Leipzig. (Foot Mercato - in French) Wakilin ɗan wasan gaban Portugal Joao Felix wanda tuni ya soma tattaunawar farko da Chelsea da Manchester United na da burin magana da Aston Villa da Newcastle kan yadda suke son ɗan wasan na Athletico Madrid mai shekara 23. Spanish) Arsenal da PSG duk sun shiga jerin kulob-kulob ɗin da ke neman Felix. (AS - in Spanish) Akwai yiwuwar Juventus za ta iya sayen ɗan wasan Chelsea da Ingila Mason Mount mai shekara 23 da kuma barin ɗan wasan Faransa Adrien Rabiot mai shekara 27 tafiya, haka kuma kulob ɗin zai iya sakin ɗan wasan Argentina Leandro Paredes da na Amurka Weston Mckennie duk su tafi domin samar da kuɗin sayen ɗan wasan na Chelsea. (CalcioMercatoWeb - in Italian) Shugaban Benfica Rui Costa ya ce kulob dinsa ba zai yarda duk wani ɗan wasan su ba ciki har da ɗan wasan Portugal mai shekara 21 Goncalo Ramos barin kulob ɗin har sai an cimma matsaya kan farashin sayar da su. Ana dai alaƙanta Ramos da tafiya Manchester United. (Correio da Manha - in Portuguese) https://www.bbc.com/hausa/articles/c0dr2pk9l4vo +sports Koriya ta Kudu za ta je Gasar Cin Kofin Duniya da Son mai jinya Koriya ta Kudu ta bayyana 'yan wasa 26 da za su buga mata Gasar Cin Kofin Duniya ciki har da Son Heung-min, wanda ya ce ya warke daga jinya. Son, mai shekara 30 ya ji rauni a fuskarsa, wanda aka yi ta fargabar ba zai buga gasar cin kofin duniya da za a fara ranar 20 ga watan Nuwamba ba. Sai dai a ranar Laraba dan wasan ya bayar da tabbacin zai buga wasannin da za a yi a Qatar a cikin watan nan. Koci, Paulo Bento ya ce baya da tabbacin ranar da Son zai fara atisaye, bayan da kasar za ta fara wasa da Uruguay ranar 24 ga watan Nuwamba. Watakila dan wasan ya saka fuska ta kariya idan zai buga wasannin a Qatar din a cikin rukuni na bakwai da ya kunshi Ghana da Portugal 'Yan kwallon Koriya ta Kudu da za su buga Kofin Duniya: Masu tsaron raga: Kim Seung-gyu (Al Shabab), Jo Hyeon-woo (Ulsan Hyundai), Song Bum-keun (Jeonbuk Motors) Masu tsaron baya: Kim Min-jae (Napoli), Kim Jin-su (Jeonbuk Motors), Hong Chul (Daegu FC), Kim Moon-hwan (Jeonbuk Motors), Yoon Jong-gyu (FC Seoul), Kim Young-gwon (Ulsan Hyundai), Kim Tae-hwan (Ulsan Hyundai), Kwon Kyung-won (Gamba Osaka), Cho Yu-min (Daejon Citizen) Masu buga tsakiya: Jung Woo-young (Al Sadd), Na Sang-ho (FC Seoul), Paik Seung-ho (Jeonbuk Motors), Son Jun-ho (Shandong Taishan), Song Min-kyu (Jeonbuk Motors), Kwon Chang-hoon (Gimcheon Sangmu), Lee Jae-sung (Mainz), Hwang Hee-chan (Wolverhampton Wanderers), Hwang In-beom (Olympiacos), Jeong Woo-yeong (Freiburg), Lee Kang-in (Real Mallorca) Masu cin kwallaye: Hwang Ui-jo (Olympiacos), Cho Gue-sung (Jeonbuk Motors), Son Heung-min (Tottenham Hotspur) https://www.bbc.com/hausa/articles/cz93dl081dgo +sports Tsohon dan kwallon Chelsea Gary Cahill ya yi ritaya Tsohon dan wasan tawagar Ingila da Chelsea, Gary Cahill ya yi ritaya daga taka leda, mai shekara 36. Cahill ya lashe manyan koci takwas a kaka bakwai a Stamford Bridge ciki har da Premier League biyu da FA Cup biyu da kuma Champions League. Ya fara sana'ar taka leda a Aston Villa ya kuma buga wasa a Bolton da Crystal Palace da kuma Bournemouth da buga wa tawagar Ingila wasa 61. Cahill ya buga wa Ingila Gasar Kofin Duniya a 2014 da ta 2018 da Euro 2016 da yi mata kyaftin karo biyar. Ya zauna bai da kungiya tun bayan da Bournemouth ta kawo karshen kwantiraginsa a kakar da ta wuce. https://www.bbc.com/hausa/articles/cy7041dg002o +sports Suarez zai sake komawa kungiyarsa Nacional wadda tun yana da kuruciya Tsohon dan kwallon Liverpool da Barcelona, Luis Suarez ya ce ya amaince zai koma kungiyarsa ta Nacional, wadda ya fara tun yana da kuruciya a Uruguay. Mai shekara 35, bai da yarjejeniya kawo yanzu tun bayan da kwantiraginsa ya kare a Atletico Madrid a karshen kakar da aka kammala. Ana sa ran Suarez zai koma Nacional a kalla lokacin da za a fara gasar kofin duniya a cikin watan Nuwamba. A wani faifan video a kafar sada zumunta, Suarez ya ce ''Ina sa ran za mu kammala komai, ina fatan za mu cimma yarjejeniya kamar yadda muke da buri''. Kimanin magoya bayan Nacional 20,000 saka sa fuska ta kwali mai dauke da hoton Suarez a wasannin kungiyar a baya-bayan nan tun lokacin da aka fara alanta dan kwallon da zai koma Uruguay da wasa. Ya fara taka leda a matakin kwararren dan wasa a Nacional yana da shekara 18 a 2005, wanda ya taimaka kungiyar ta lashe lik din Uruguay daga nan kungiyar Turai, Groningen ta dauke shi. https://www.bbc.com/hausa/articles/c72z7w92705o +sports Daga wannan World Cup din zan yi murabus a Argentina "Lionel Messi ya ce daga kofin duniyar da za a yi a Qatar a watan Nuwamba, zai yi murabus daga bugawa Argentina wasa. Dan shekara 35 din da yake taka leda a Paris St-Germain ya buga wa Argentina kofin duniya hudu, ya ci ya ci kwallo shida ya kuma taimaka an ci biyar a wasa 19. A 2014, ya kai kasarsa matakin karshe na gasar, sannan a 2021 ya taimaka wa kasar ta lashe Copa America, kuma World Cup ne kawai ya zamarwa dan wasan koma baya. ""Babu shakka wannan ne kafin duniya na karshe da zan buga,"" in ji Lionel. Da yake zantawa da ESPN Messi ya kara da cewa: ""ina kirga saura kwanaki nawa a fara World Cup. Akwai kaguwa da kuma fargaba a lokaci guda. Ina son ya zama yanzu, abin da zai faru da kuma wanda kan je ya dawo. A 2005 ne messi ya fara bugawa kasarsa wasa, kuma ya buga wasa 164 ya zuwa yanzu ya ci kwallo 90. Argentina da ke matsayi na hudu na kasashen duniya da Fifa ta fitar, za ta kara da Saudiyya da Mexico da Poland a rukunin C wanda za a fara a ranar 20 ga watan Nuwamba. ""A World Cup komai zai iya faruwa. Duka wasannin na da zafi. Wanda aka fi mayar da hankali a kansa zai iya samun nasara,"" a cewar Messi. ""Ba ni da tabbas ko mu ne wadanda aka fi mayar da hanakali a kai, amma ko da yaushe Argentina na sawun gaba saboda tarihi. ""Yanzu abinma ya zarce haka saboda lokacin da muke ci. Kuma watakila akwai kasashen da suka sha gabanmu a wannan gasar.""" https://www.bbc.com/hausa/articles/cpd1r35j77xo +sports Robert Lewandowski ya lashe takalmin zinare a nahiyar Turai karo biyu a jere Robert Lewandowski shi ne kan gaba a cin kwallaye a nahiyar Turai a kakar 2021/22, hakan ya sa ya lashe kyautar takalmin zinare a bana. Dan kwallon Bayern Munich ya ci 35 a raga a Bundesliga, hakan ya sa ya samu maki 70, shi ne wanda ya karbi kyautar a bara. Dan wasan Paris Saint-Germain, Kylian Mbappé ne na biyu mai kwallo 28 da ya hada maki 56, yayin da Ciro Immobile na Lazio da Karim Benzema na Real Madrid kowanne ya ci kwallo 27, kenan kowanne ya hada maki 54. Lewandowski ya lashe kyautar takalmin zinare karo na biyu a jere, bayan da ya zura kwallo 41 a Bundesliga a kakar 2020/21. An fara bayar da kyautar wanda ke kan gaba a cin kwallaye a Turai tun daga 1968, an kuma ci karo da tsaiko a 1990 daga nan aka ciga kamar yadda aka saba. Kyautar ana bayar da ita ga duk wanda ya ci kwallo fiye da kowa a gasar mambobin hukumar kwallon kafar Turai, UEFA a kakar tamaula. Wani dan wasan Bayern Munich da ya lashe kyautar karo biyu shi ne Gerd Muller a kakar 1969/70 da kuma 1971/72. https://www.bbc.com/hausa/wasanni-61719364 +sports Man United na shirin korar Ronaldo daga ƙungiyar "Manchester United na duba hanyoyin da za ta bi da zimmar soke kwantaragin Cristiano Ronaldo a kulob ɗin ko kuma ɗaukar matakin shari'a a kansa. Wasu mahukunta a United sun amince cewa bai kamata Ronaldo ya sake buga wa ƙungiyar wasa ba a ƙarƙashin mai horarwa Erik ten Hag bayan kakkausar sukar da da ya yi wa kocin a hirarsa da Talk TV. Wata bakwai ne ya rage kafin yarjejeniyarsa ta zo ƙarshe a United, wadda ke ba shi albashin fan 500,000 duk mako. A ranar Juma'a United ta fitar da sanarwar cewa sun fara ""shirin da ya dace"" na mayar da martani kan soke-soken da Ronaldo ya yi musu. Ƙungiyar ka iya katse kwantaragin nasa, abin da zai sa ya koma wata ƙungiyar a kyauta idan aka buɗe kasuwar saye da musayar 'yan wasa a watan Janairu mai zuwa. An fahimci cewa ba sa son su biya ɗan wasan mai shekara 37 maƙudan kuɗaɗe saboda karya yarjejeniyar ganin yadda suka ji da zargen-zargen da ya yi kan masu kulob ɗin. Ƙungiyar na son ta gama da matsalar cikin sauri don kar lamarin ya kai har zuwa watan Janairu. A hirar da ya yi, Ronaldo ya ce ƙungiyar ta ""yaudare shi"" kuma ya ce ba ya ""mutunta"" mai horarwa Erik ten Hag saboda shi ma ""ba ya girmama shi"". Ya ƙara da cewa wasu na son su tilasta masa ficewa daga kulob ɗin. Ronaldo zai jagoranci tawagar ƙasarsa Portugal a wasannin Kofin Duniya bayan sun isa Qatar ranar Juma'a. Za su buɗe wasa tare da Ghana a Rukunin H ranar Alhamis." https://www.bbc.com/hausa/articles/ce92y7vml0jo +sports Messi ya lashe Kofin Duniya na uku da Argentina ta dauka Lionel Messi ya ja ragamar Argentina ta lashe Kofin Duniya a Qatar, bayan nasara a kan Faransa a bugun fenariti a wasan da ya kayatar a tarihi. Sun tashi wasan 3-3 har da karin lokaci da ya kai minti 120 daga baya Argentina ta dauki kofin kuma na farko a wajen Messi na uku a Argentina. Argentina ta fara cin kwallo ta hannun Lionel Messi a bugun fenariti, sannan ta kara na biyu ta hannun Angel Di Maria. Saura minti 10 a tashi wasan Faransa ta zare daya ta hannun Kylian Mbappe a bugun daga kai sai mai tsaron raga, sannan ya kara na biyu a minti daya tsakani. A karin lokaci Messi ya kara kwallo daga baya Mbappe ya farke da ta kai ga bugun fenarti, bayan da suka tashi 3-3. Daga nan Argentina ta lashe kofin da ci 4-2 ta dauki na uku jumulla, bayan wanda ta dauka a 1978 da kuma 1986. Kylian Mbappe ne ya lashe kyautar takalmin zinare, wanda ya ci takwas a Qatar, Messi ne na biyu mai bakwai a raga. Golan Argentina Emiliano Martinez shi ne ya karbi kyautar gwarzon mai tsaron raga a Qatar. Enzo Fernandez mai taka leda a Benfica mai shekara 21, shi ne matashin dan wasa a Gasar da aka kammala a Qatar - Messi kuwa shi ne fitatcen dan wasan Gasar. Sai dai Messi shi ne kan gaba a yawan buga wasa a babar Gasar tamaula ta duniya, wanda ya yi fafatawa 26 jumulla - wasa na karshe da ya buga kuma. Jumulla Messi ya ci kwallo 26 a manyan gasar da ya yi wa Argentina, kenan 13 a Gasar Kofin Duniya da 13 a Copa America ya haura Ronaldo mai 25. Kociyan Argentina, Lionel Scaloni ya zama na uku da ya lashe Copa America a 2021 da Kofin Duniya a 2022 - wadanda suka yi wannan bajintar sun hada da Mário Zagallo Kofin Duniya a 1970 da Copa America a 1997 da kuma Carlos Alberto Parreira da ya ci Kofin Duniya a 1994 da Copa America a 2004. An ci kwallo 172 a Gasar da aka yi a Qatar a 2022, ita ce kan gaba da aka zura da yawa a raga, bayan da aka ci 171 a 1998 da kuma a 2014. Faransa mai rike da kofin da ta dauka a Rasha ta barar da damar daukar na uku jumulla, wanda ta ci a 1998 da kuma 2018. https://www.bbc.com/hausa/articles/cjr27wz1412o +sports Wane ne George Weah? Aljihun wa kuɗin sayen 'yan ƙwallo ke shiga? Shirin Amsoshin Takardunku na wannan makon ya amsa tambayoyi kan Shugaban Ƙasar Laberiya George Weah, tsohon gwarzon ɗan ƙwallon duniya. Sai kuma tambaya kan inda ake kai kuɗin da aka sayi 'yan ƙwallo. https://www.bbc.com/hausa/articles/c848dj97r8ro +sports Rikicin Kamaru: Masoya ƙwallon ƙafar da ba sa son ƙasarsu ta yi nasara "Gasar cin Kofin Ƙasashen Afirka da aka yi ta baya-bayan nan a Kamaru ya nuna yadda mutane ke ƙaunar ƙwallon ƙafa, amma yayin da ƙasar ke shirin buga wasannin cancantar shiga Kfoin Duniya na 2022, ba duka 'yan Kamaru ne ke son ƙasar ta yi nasarar zuwa ba gasar ba, kamar yadda Tony Vinyoh ya ruwaito. Abu ne sananne cewa bai kamata a haɗa siyasa da wasanni ba, amma idan ana maganar ƙwallon ƙafa a Kamaru abubuwan biyu a haɗe suke. Rikcin shekara biyar tsakanin 'yan aware na ɓangaren rainon Ingila da kuma gwamnatin ƙasar ya zarce zuwa filin wasa. Lokacin da Masar ta doke Kamaru a wasan kusa da na ƙarshe a gasar ta Afcon, kusan duka ƙasar ta shiga makoki amma ban da yankin Bamenda - inda nan ce cibiyar adawa a yankin rainon Ingila - sun ɓarke da murna. Aka dinga busa usur tare da ife-ife, har ma da masu wasa da babura a garin Bambili, abin da ke nuna irin abin da 'yan kudancin ƙasar ke ji game da tawagar ƙasar da ake kira Indomitable Lions, wadda wasu ke kallo a matsayin ta haɗin kan ƙasa amma ban da su. Dagacikin m asu murnar doke Kamaru akwai Dr Ngwa Ebogo, wani likitan tiyata a ɓangaren mafitsara. A matsayinsa na mai son ƙwallon ƙafa, yana sane da rawar da wasanni ke takawa a siyasa a ƙasar da kuma tasirinta a kan marasa lafiyar da yake kula da su. ""Wannan ƙasar tana iya amfani da wasanni don ɓoye batutuwan da ke damun al'umma. Za su iya zuba kuɗi a harkar ƙwallon ƙafa saboda sun san tana haɗa ƙan al'umma,"" a cewarsa. Ɓacin ran da aka nuna yanzu akasi ne na abin da ya faru a 1998 lokacin da mazauna Bamenda suka cinna wa ofishin kamfanin lantarki na ƙasar wuta saboda na ɗuke wuta ana daf da take wasa tsakanin Kamaru da Austria a gasar Kofin Duniya na shekarar. Dr Ebogo ya goyi bayan Kamaru har zuwa 2016 lokacin da rikicin kudancin Kamarun ya fara. Yanzu ya yi imanin cewa nasarar da tawagar ka samu riba ce ga gwamnati wajen shirinta na kawar da hankalin 'yan ƙasa. ""Ko da a ce kana tsaka da gwagwarmaya sai Kamaru ta yi nasara, sai ka manta ma abin da kake gwagwarmayar a kai. Sun daɗe sun aikata hakan. Duk sanda 'yan wasan suka yi nasara ƙarin wahala ce kan al'umma."" Tawagar na taka muhimmiyar rawa a tsarin da Shugaban Ƙasa Paul Biya mai shekara 89, wanda ke cika shekara 40 a lkan mulki. ""Mafi yawan 'yan Kamaru na tunanin idan Kamaru ta ci wasa saboda shugaban ƙasar ne,"" in ji Dr Ebogo. ""Idan tawagar ta samu nasara sai ka ji mutane na yi wa shugaban murna."" Sai dai mazauna Bamenda na taka-tsantsan game da wanda suke faɗa wa ra'yoyinsu, saboda gwagwarmaya ce ta kullum da suke yi wajen ɓoye fushinsu idan tawagar ta yi rashin nasara. A lokacin mulkin mallaka, Faransa da Birtaniya ne suka mallake ta Kamaru, abin da ya sa suka bar al'adunsu da harsunansu a ƙasar. Tsawon shekaru bayan samun 'yancin kanta, mazauna kudancin ƙasar na ganin ana zaluntarsu ta hanyar raba su da mulki da kuma harkokin tattalin arziki a hannun masu magana da harshen Faransanci mafiya rinjaye. Abin ya zama babban rikici da kuma kiraye-kirayen neman samun 'yancin kai ga yankin rainon Ingilan. Waɗanda lamarin ya fara shafa su ne tawagar ƙwallon ƙafar mata ta ƙasar. Lokacin da Kamaru ke karɓar bakuncin gasar mata ta Kofin Ƙasashen Afirka a 2016, za ta kara ne da Najeriya. Bayan fara gasar a ranar 19 ga watan Nuwamba, akasarin wuraren shaƙatawar Bamenda sun cika da mutane na sowa da ihun goyon bayan 'yan matan Kamaru duk da rashin imanin da jami'an tsaro suka gwada wa masu zanga-zanga a yankin 'yan makonni kafin haka. Amma kafin haka, sai murna ta sauya zuwa baƙin ciki. Da yawan mazauna yankin ba su yi wani shiri ba kafin fara gasar Afcon da aka gama kwanan nan. Da yawansu kan ce kowa ya yi nasara ban da Kamaru. Dr Ebogo ma na da irin wannan ra'ayi kuma ya shafe lokaci yana kai ziyara sansanin abokan karawar Kamarun. ""A Bamenda babu wani abu da ke nunan ana gasar Afcon. Sun yi ta so su ɗauki mutane zuwa filin wasa na Bafoussam amma ba wanda ya bi su,"" a cewarsa yana magana kan tikitin kyauta da aka raba wa mutane da kuma tilasta wa mutane zuwa kallon wasannin." https://www.bbc.com/hausa/wasanni-60877822 +sports Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Jesus, Bellingham, Ward-Prowse, Eriksen, Gvardiol, Belotti, Danjuma Dan wasan Manchester City da Brazil, Gabrie Jesus, mai shekara 25, ya amince da kwantiragin kaka biyar da Arsenal a kan £45m. (Guardian) Liverpool tana da tabbacin za ta dauki dan kwallon Borussia Dortmund da tawagar Ingila, Jude Bellingham mai shekara 18. (Sun) West Ham na son daukar dan wasan Southampton da tawagar Ingila, James Ward-Prowse, mai shekara 27, a kakar nan . (Sky Sports) Dan wasan tawagar Denmark, Christian Eriksen na daf da yanke hukuncin ko zai koma Tottenham sai dai kuma Brentford na fatan tsawaita yarjejeniyar dan kwallon mai shekara 30. (Fabrizio Romano) Villarreal da West Ham sun tattauna kan batun sayen dan wasan tawagar Netherlands, Arnaut Danjuma, mai shekara 25. (Toni Juanmarti - in Spanish) Kociyan Manchester United Erik ten Hag zai iya samun fam miliyan 100 daga mahukuntan kungiyar domin sayo sabbin 'yan wasa. (Sun) Tottenham na binciken farashin dan kwallon RB Leipzig dan kasar Croatia, mai tsaron baya, Josko Gvardiol, 20. (Nabil Djellit) Atletico Madrid na bibiyar farashin dan wasan Celtic's dan kasar Croatia, mai tsaron baya, Josip Juranovic, 26. (Record) Monaco na tuntubar dan kwallon Torino da tawagar Italiya, Andrea Belotti, mai shekara 28, AC Milan na son sayen dan kwallon. (Ekrem Konur) Wakilin Sadio Mane ya musanta batun cewar dan kwallon Senegal mai shekara, 30, ya bar Liverpool zuwa Bayern Munich a kakar nan saboda baya karbar albashi mai tsoka a Anfield. (TVMondo, via Mirror) Leeds za ta dauki dan wasan RB Leipzig dan Amurka, Tyler Adams, mai shekara 23, da na RB Salzburg dan kasar Mali, Mohamed Camara, mai shekara 22, domin maye gurbin dan kwallon Ingila, Kalvin Phillips, mai shekara 26, wanda ke daf da komawa Manchester City. (Mail) Angel di Maria, wanda kwantiraginsa zai kare a Paris St-Germain a karshen watan Yuni, na dab da komawa Juventus, duk da cewar Barcelona na son daukar dan kwallo Argentina mai sheiara 34. (Calciomercato - in Italian) Dan wasan Manchester United da tawagar Portugal, Cristiano Ronaldo, mai shekara 37, ya barar da damar komawa kungiyar David Beckham Inter Miami zai ci gaba da taka leda a Old Trafford. (Star) https://www.bbc.com/hausa/labarai-61947809 +sports 'Yan wasan Real Madrid 11 aka gayyata tawagoginsu buga tamaula Bayan da aka kammala wasannin mako na 29 a gasar La Liga a karshen satin nan, za a ci gaba da karawar neman shiga gasar cin kofin duniya. Haka kuma a irin wannan lokacin wasu kasashen kan buga wasan sada zumunta, domin tantance karfin tawagar da 'yan wasanta. Tuni aka gayyaci 'yan wasan Real Madrid 11, domin buga wa tawagoginsu wasanni daga karshen mako. Cikin wadanda za su buga wasan sada zumunta sun hada da Carvajal (Spain) da Jovic (Serbia) da kuma Modrić (Croatia). Wadanda za su yi karawar neman gurbin shiga gasar kofin duniya sun hada da Bale (Wales) da Valverde (Uruguay) da Casemiro da Vini Jr, da Rodrygo da kuma Militão dukkansu daga (Brazil) da kuma Alaba (Austria). Shi kuwa Camavinga zai wakilci Faransa a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai ta matasa 'yan kasa da shekara 21. Ranar Lahadi Real Madrid ta sha kashi a hannun Barcelona da ci 4-0 a wasan mako na 29 da suka fafata a Santiago Bernabeu. Sai dai duk da wannan rashin nasarar Real Madrid ta nan a matakinta na daya a kan teburi da tazarar maki tara tsakaninta da Sevilla ta biyu. Barcelona kuwa mai kwantan wasa tana ta uku a teburin babbar gasar tamaula ta Sifaniya da tazarar maki 12 tsakaninta da Real mai jan ragama. https://www.bbc.com/hausa/wasanni-60824296 +sports Arsenal za ta yi wasa biyar cikin watan Satumba Arsenal ta fara kakar bana da kafar dama, wadda ta hada maki 12 a wasa hudu a kakar Premier League ta 2022/23. Cikin wasannin da ta yi ta ci kwallo 11 an zura mata biyu a raga da karawa biyu ba tare da kwallo ya shiga ragarta ba. Ranar 5 ga watan Agusta ta fara da cin Crystal Palace 2-0 a Selhurst Park, kuma Gabriel Martinelli ne ya ci mata kwallo sai Marc Guehi na Palace da ya ci gida. Arsenal ta fara wasa a gida ranar 13 ga watan Agusta, inda ta doke Leicester City 4-2 a Emirates, Gabriel Jesus ne ya zura biyu sai Granit Xhaka da Gabriel Martinelli da kowannensu ya ci daya. Wasa na uku kuwa Gunners zuwa ta yi ta casa Bournemouth 3-0 ranar 20 ga watan Agusta, kyaftin Martin Odegaard ne ya zura biyu a raga da kuma William Saliba. Arsenal ta ci wasa na hudu a jere ranar 27 ga watan Agusta, inda ta doke Fulham 2-1 a wasan hamayya a Emirates, Martin Odegaard da Gabriel suka samar mata maki ukun da take bukata. Arsenal ta yi wannan gwanintar bayan da ta dauko sabbin 'yan wasa a bana ciki har da Gabriel Jesus da Zinchenko. Gunners ta nuna cewar a shirye take ta yi gogayya da kungiyoyi kamar Liverpool da Chelsea da Tottenham da Manchester City wajen lashe Premier League a bana. Tottenham tana cikin wadanda za a yi gwa-gwa-gwa da ita, Manchester United ma na son yin abin a zo a gani, shi ya sa take ta yin cefane. Ranar 31 ga watan Agusta Arsenal za ta karbi bakuncin Aston Villa a wasan mako na biyar a gasar Premier League. Aston Villa ba ta kokari sosai a kakar nan, wadda ta ci wasa daya, tana ta 15 a kasan teburi mai maki uku a wasa hudun da ta kara. Daga nan Gunners za ta fuskanci karawa biyar a cikin watan Satumba, ciki har da fafatawa biyu a Europa League. Wasa biyar da Arsenal za ta yi cikin watan Satumba Arsenal za ta ziyarci Old Trafford domin fuskantar Manchester United a wasan farko cikin watan Satumba. Daga nan Arsenal za ta je Zurich, domin buga wasan farko a cikin rukuni da za ta kara a Europa League, bayan da ta yi ta biyar a kakar da ta wuce a teburin Premier League. Arsenal za ta buga wasan Premier na gaba da Everton a Emirates fafatawa ta uku a cikin watan na Satumba. Gunners za ta kara wasa na biyu a gida amma a Europa League da PSV Eindhoven. Cikin watan na Satumba, Arsenal za ta karkare da ziyartar Brentford a wasan hamayya a gasar Premier League. Arsenal na sa ran daukar Premier League da Europa da FA Cup da Carabawo da samun gurbin Champions League a badi. Jerin wasa biyar da Gunners za ta yi cikin watan Satumba Premier League Lahadi 4 ga watan Satumba Europa League Alhamis 8 ga watan Satumba Premier League Lahadi 11 ga watan Satumba Europa League Alhamis 15 ga watan Satumba Premier League Lahadi 18 ga watan Satumba https://www.bbc.com/hausa/articles/cw0gel7l4gpo +sports Kotu ta bayar da belin Greenwood wanda ake tuhuma da aikata fyade Wata kotu ta bayar da Belin dan wasan Manchester United, Mason Greenwood, wanda ake zargin aikata fyade. Ana kuma tuhamar dan wasan mai shekara 21 da ikirarin zai yi kisa da nuna munanan halayen da ba su dace ba. An tsare dan kwallon a watan Janairu, bayan wasu hotuna da bidiyon da suka bayyana a Intanet, kan abubuwan da ake tuhumarsa. An ci gaba da tasre dan wasan a kotun Majistare ta Manchester da Salford tun daga ranar Litinin. Wani mai magana da yawun kotun ya tabbatar da cewar an bayar da belin Greenwood, amma bisa kan wasu ka'idoji. Ciki har da cewar ba za a tuntubi matar da ta shigar da kara ba, sannan ba zai zauna kusa da adireshin da yake Bowdon ba. Mista Greenwood bai halarci zaman kotun ba. Tun cikin watan Janairu aka bayar da dan kwallon beli, anma an sake tsare shi ranar Asabar, bayan da ya karya dokar da aka gindaya masa ta belin.. https://www.bbc.com/hausa/articles/cn01y3v0jjro +sports Aikin koci a Premier zai iya shafar lafiyar kwakwalwa in ji Potter Graham Potter ya ce aikin horar da tamaula a Premier League na tattare da kalubalen da zai iya shafar lafiyar kwakwalwa. Kociyan wanda ke jimamin mutuwar mahaifansa na fama da kalubalen yadda zai komar da Chelsea kan ganiya. Mai shekara 47 ya maye gurbin Thomas Tuchel a watan jiya a Stamford Bridge, bayan da dan kasar Jamus ya kasa taka rawar gani a kakar nan. A wasan farko Tuchel ya yi 1-1 da RB Salzburg a Champions League daga nan ya ja ragamar wasa takwas ba a doke Chelsea ba. Tsohon kociyan Brighton ya ci wasa shida da canjaras uku tun bayan da ya karbi aikin horar da Chelsea ranar 8 ga watan Satumbar 2022. A lokacin da cutar korona ta yi kamari ne mahaifiyar Portter ta mutu, sannan wata shida tsakani, shima babansa ya bar duniya. A kuma lokacin tsohon mai tsaron bayan Birmingham da Stoke da kuma York na aikin horar da Brighton a Premier League. Da yake yanzu yana aiki da Chelsea ya ce idan za ake kwatanta shi da wanda ya gada a Chelsea ko wannan zai iya shafar lafiyar kwakwalwa. ''Kafin na koma Brighton bani da kwarewar horar da tamaula a Premier League, saboda haka na koyi yadda ya kamata na gudanar da aikin.'' Ya fadi haka ne don amsa tambayar da aka yi masa kan babban darasin da ya samu a kaka uku da ya yi a Brighton. ''Wasu lokutan sai ka sha wuya, sannan ka samu kwarewa cikin dan karen radadi, sannan yayin da kake kara yin sama a Premier League haka surutai zai karu. ''Kafofin yada labarai na son hada kwazo na da Thomas Tuchel abin da ke faruwa a yanzu haka kenan. Wanda hakan ba abu bane mai dadi, domin zai iya shafar lafiyar kwakwalwa.'' Potter wanda ya ja ragamr Brighton wasa 135 da cin karawa 42 da canjaras 46 da rashin nasara 47, ya kai kungiyar mataki na tara a bara, shi ne kololuwar da ta taba yi a gasar. Potter ya kara da cewar ''Kowanne wasa a Premier na hamayya ne mai cike da kalubale, koda yaushe sa rai ake sai ka yi nasara, bayan dole wata ran za a doke ka. ''Kana fama da zabar 'yan kwallon da za su buga maka wasa, bayan Premier ga Champions League ga FA ga League Cup, sai ka kula da 'yan wasan da ke kan ganiya.'' ''Kungiyoyi yanzu ba hakuri kowa sakamako mai kyau yake bukata, sannan magoya baya kan sa matsi ga koci da zarar wasa ya juya baya.'' Yanzu dai Chelsea na taka rawar gani a wasanninta, wadda ta kai zagayen gaba a Champions League, tana kuma ta biyar a teburin Premier League. Potter zai kara da Brighton a gasar Premier League ranar Asabar, karon farko tun bayan da ya bar kungiyar da ya ja ragama kaka uku. Wasannin Premier League na mako na 12: Asabar 29 ga watan Oktoba https://www.bbc.com/hausa/articles/cyr0mr73041o +sports Erling Haaland: Manchester City ta kammala sayen dan wasan Norway daga Borussia Dortmund "Erling Haaland ya ce yana ""wurin da ya dace da zai cika burinsa"" bayana Manchester City ta kammala sayen sa daga Borussia Dortmund a kan £51.2m. Dan wasan mai shekara 21 ya zura kwallo 86 a wasanni 89 da ya buga wa Dortmund kuma ya isa City ne a matsayin daya daga cikin 'yan wasan gaba da suka fi zura kwallo. Ya sanya hannu a kan kwangilar shekara biyar zuwa 2027 kuma zai je kungiyar ranar 1 ga watan Yuli. A watan Mayu ne dan kasar ta Norway ya kulla yarjejeniya da City. ""Wannan rana ce mai cike da alfahari a gare ni da iyayena,"" a cewar Haaland, wanda da ne ga tsohon kyaftin din City Alf-Inge, wanda ya murza mata leda tsakanin 2000 da 2003. ""Na dade ina kallon wasan City kuma na dade ina son murza musu leda. Dole mutum ya kaunaci salon su na taka leda - abin sha'awa kuma suna samar da dama ta zura kwallaye, wadda za ta kasance abin da nake so,"" in ji shi. ""Akwai fitattun 'yan kwallon duniya da dama da ke taka leda a wannan kungiyar kuma Pep [Guardiola] yana daya daga cikin kociyoyi mafi girma a tarihi, don haka na yi amannar cewa na zo wurin da ya dace domin cika burina. ""Ina so na zura kwallaye, na dauki kofuna, sannan na kara basira a matsaina na dan wasan kwallon kafa kuma ina da kwarin gwiwar zan yi hakan a nan."" Daraktan kwallon kafa na City Txiki Begiristain ya ce: ""Haaland dan wasa ne mai matukar basira kuma ya kasance daya daga cikin 'yan wasan gaba mafi kwazo a Turai a shekarun nan."" A baya dai kungiyoyin da ke buga gasar La Liga Real Madrid da Barcelona sun nemi daukar Haaland kafin ya yanke shawarar yin aiki da Guardiola. Haaland ya zura kwallaye 92 a gasar lig a wasa 121 jimilla da ya buga wa Molde, Red Bull Salzburg da kuma Dortmund." https://www.bbc.com/hausa/wasanni-61787389 +sports Atletico 1-0 Real Madrid: Atletico Madrid ta ci gaba da zama ta hudu a La Liga Atletico Madrid ta yi nasarar cin Real Madrid 1-0 a wasan mako na 35 a gasar La Liga da suka kara ranar Lahadi a Wanda Metropolitan. Atletico ta ci kwallon ta hannun Yannick Ferreira Carrasco a bugun daga kai sai mai tsaron raga saura minti biyar su je hutun rabin lokaci a karawar ta hamayya. Da wannan sakamakon Atletico mai La Liga na bara tana mataki na hudu a teburi da maki 64 da tazarar maki shida tsakaninta da Real Betis ta biyar, kuma saura wasa uku-uku suka rage a kammala wasannin bana. Real Madrid wadda tuni ta lashe La Liga na bana kuma na 35 jumulla ta yi rashin nasara a wasa na hudu a kakar nan kenan a babbar gasar tamaula ta Sifaniya. Wannan shi ne wasa na biyu da suka kece raini a gasar La Liga ta bana, bayan da Real ta ci Atletico 2-0 ranar 12 ga watan Disamba. Wadanda suka ci mata kwallayen sun hada da Karim Benzema da ya ci a minti na 16 da kuma Marco Asensio da ya zura kwallo a raga a minti na 57. 'Yan wasan da kociyan Real Madrid, Carlo Ancelotti ya je Atletico da suka buga wasan na hamayya ranar Lahadi. 'Yan wasan Real Madrid: Masu tsaron raga: Courtois, Lunin da kuma Luis López. Masu tsaron baya: Carvajal, E. Militão, Vallejo, Nacho da kuma F. Mendy. Masu buga tsakiya: Kroos, Modrić, Casemiro, Valverde, Lucas V. da kuma Camavinga. Masu cin kwallaye: Benzema, Asensio, Jović, Vini Jr., Rodrygo da kuma Mariano. https://www.bbc.com/hausa/wasanni-61371244 +sports Manchester United ta sanar da asarar £115.5m a kakar 2021-22 "Manchester United ta sanar da asarar da ta yi ta £115.5m a kakar 2021-22, duk da kuma kudin shigarta ya karu da kashi 18 zuwa £583.2m. Kungiyar ta bayyana asarar ne a bayanan da take fitarwa na hada-hadar kudinta a karshen shekara a watan Yuni, wanda ya nuna asarar ta karu zuwa £23.3m idan aka kwatanta da wadda ta yi a 2021. Bashin da ake bin kungiyar shi ma ya karu, daga £419.5m a 2021 zuwa £514.9m a wannan shekarar, ya karu da sama da kashi 22. ""Abin da kungiyar ta sanya a gaba shi ne ta yi nasa a wasanni ta kuma nishadantar da magoya bayanmu,"" in shi shugaban Richard Arnold. ""Sakamakon 'yan wasan da muka dauka a bara irinsu Cristiano Ronaldo da Jadon Sancho da kuma Raphael Varane albashi ya karu da kashi 19.1m, yanzu ya koma £616.6m daga £384.2m"". Wannan ne adadi mafi yawa da aka samu a tarihin Premeir, ya wuce na Manchester City na baya da yakai £355m ""Sakamakon da muka samu a 2022 na kudi, ya nuna muna warwarewa daga matsalar annobar korona, cikakkiyar dawowar magoya baya da kuma kara sanya kudin abokan hulda ga tawagarmu,"" in ji Cliff Baty. ""Rashin fita wasannin karshen kaka da muka yi zuwa wasu kasashen a 2021, ya kara yawan abubuwan da muke kashewa."" Kudin da aka biya tsohon kocin kungiyar Ole Gunnar Solskjaer wanda aka kora a watan Nuwamba 2021, da maganar Ralf Rangnick wanda ya rike kungiyar na rikon kwarya da sauran tawagarsa sun hada £24.7m." https://www.bbc.com/hausa/articles/c4nm65lv4jyo +sports Za a yi gwanjon kwallon da Maradona ya ci Ingila da hannu a 1986 "Za a yi gwanjon kwallon da Diego Maradona ya zura a raga – a biyu daga cikin cin kwallayen da suka fi shahara a tarihi. An yi wa kwallon da aka yi daya daga cikin fitattun wasan kofin duniya da aka yi tsakanin Ingila da Argentina a 1986 farashi da ya kai fam miliyan 3. An sayar da kwallon ga Ali Bin Nasser dan kasar Tunisia, wanda shi ne alkalin da ya busa wasan da ya bayar da kwallon da Maradona ya ci wadda ake kira 'Hand of God' a wasan. Bin Nasser ya ce: ""Wannan kwallon na bcikin tarihin kwallon kafa - wannan ne daidai lokacin da ya dace a nunawa duniya ita."" An yi amfani da kwallon na tsawon minti 90 na wasan, wadda ita ce kwallon da aka fi bayyanawa a matsayin mai cike da rudani idan ana maganar tarihin kofin duniya. Maradona ne ya fara cin kwallo a wasan - ta hanayar naushinta kuma kwallon ta wuce mai tsaron ragar Ingila Peter Shilton. Bin Nasser bai duba kwallon ba ya bayar da ita, yayin da dan wasan daga baya ya yi bayanin cewa ""rabin kwallon ya taba kan dan wasan rabi kuma kan Maradona"". Kwallo ta biyu da ya ci a wasan ta yi sunan da ake kiranta da ""kwallon karni"", inda ya yanka mutum biyar daga cikin 'yan wasan Ingila sannan ya yanka Shilton ya ci. Argentina ce ta yi nasara a wasan da ci 2-1 kuma daga karshe ta ci kofin duniyar da aka yi a Mexico." https://www.bbc.com/hausa/articles/cw9n7e49w8yo +sports 'Yan wasan Real Madrid da suka je Amurka wasan sada zumunta Real Madrid za ta buga wasan sada zumunta uku a Amurka, domin shirin tunkarar kakar tamaula ta bana da za a fara cikin watan Agusta. Real Madrid za ta yi wasannin a birnin Las Vegas da San Francisco da kuma Los Angeles. Kungiyar da Carlo Ancelotti ke jan ragama za ta fafata da Barcelona a Las Vegas da Club America a San Francisco da kuma Juventus a Los Angeles. Ga jerin 'yan wasan Real Madrid da suka sauka je Amurka: Masu tsaron raga: Courtois da Lunin da Luis Lopez da kuma Lucas Canizares. Masu tsaron baya: Carvajal da Militao da Alaba da Vallejo da Nacho da Rudiger, da Mendy da Odriozola da kuma Tobías. Masu wasa daga tsakiya: Kroos da Modric da Casemiro da Valverde da Lucas V. da Tchouameni da Ceballos da kuma Camavinga. Masu cin kwallo: Hazard da Benzema da Asensio da Vini Jr. da Rodrygo da Mariano da kuma Latasa. Jadawalin wasannin da Real Madrid za ta buga a Amurka: Ranar 23 ga watan Yuli Real Madrid za ta fara karawa da Barcelona, wato karon battar El Clasico na farko a bana da za su kece raini a Allegiant Stadium in Las Vegas. Ranar 26 ga watan Yuli Real Madrid da Club America a filin wasa na Orcale Park, San Francisco. Ranar 30 ga watan Real Madrid da Juventus a filin wasa na Rose Bowl, Los Angeles https://www.bbc.com/hausa/articles/c8487x2y4wdo +sports Hernandez na Faransa ya gama buga Gasar Kofin Duniya a Qatar Mai tsaron bayan Faransa, Lukas Hernandez ya gama buga Gasar Cin Kofin Duniya a Qatar, bayan da ya ji rauni a wasa da Australia ranar Talata. Mai shekara 26, mai taka leda a Bayern Munich ya ji rauni a lokacin da ya fadi da gwiwar kafa daf da Australia za ta ci kwallo a wasan da aka doke ta 4-1. An tabbatar da girman raunin da Hernandez ya ji ranar Laraba, bayan da aka yi masa gwaje-gwaje. An canji Hernandez da dan uwansa Theo, wanda ke taka leda a AC Milan, daga nan Faransa ta farke ta kara kwallo uku a karawar rukuni na hudu. Wadanda suka ci wa mai rike da kofin duniya kwallayen sun hada da Adrien Rabiot da Kylian Mbappe da Olivier Giroud wanda ya zuba biyu a raga. 'Yan wasan Faransa da dama na jinya daf da za a fara Gasar Cin Kofin Duniya, ciki har da dan kwallon Real Madrid, Karim Benzema. Bayan da aka sanar da raunin Benzema, Faransa bata maye gurbin dan wasan mai shekara 34 ba, hakan ya sa ta je da 'yan kwallo 25 a Qatar, yanzu saura 24. Tun farko Paul Pogba da N'Golo Kante ba sa cikin koshin lafiya da ya kamata Faransa ta gayyace su babbar Gasar Kofin Duniya da Qatar ke karbar bakunci. Haka shima mai tsaron baya, Presnel Kimpembe ya hakura da wasannin, wanda aka maye gurbinsa da Axel Disasi. Shi kuwa mai taka leda a RB Leipzig, Christopher Nkunku ya ji rauni a lokacin atisaye a tawagar Faransa, inda aka maye gurbinsa da Randal Kolo Muani. https://www.bbc.com/hausa/articles/cevdkz49yego +sports Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Timber, Mane, Nunez, Cucurella, Phillips, Richarlison Manchester United ta fara tattaunawa da Jurrien Timber, dan wasan kasar Holland mai shekara 20 wanda kungiyar Ajax ta sanya wa kudi fam miliyan 43. (Guardian) Dan wasan gaba na kasar Senegal Sadio Mane ya shaida wa kungiyarsa Liverpool cewa yana son barin kungiyar yayin da Bayern Munich ke nuna sha'awar sayensa kan fam miliyan 35.(Sky Sports) Dan wasa gaba na Benfica darwin Nunez mai shekara 22 ya fara ganawa da wasu wakilan kungiyoyin kwallon kafa na Firimiyar Ingila kan komawrsa can. Liverpool, Manchester United da Newcastle duka sun bayyana sha'awarsu kan dan kasar Uruguay din. (Football Transfers) Manchester City na son dauko dan wasan baya na Brighton da kasar Sifaniya, Marc Cucurella mai shekara 23, tare da Kalvin Philips dan wasan tsakiya na Leeds mai shekara 26. (Telegraph) Dan wasan Brazil Richarlison na sake duba zamansa a Everton, inda Chelsea da Tottenham da Arsenal ke nuna sha'awar raba dan wasan gaban mai shekara 25 da kungiyar tasa. (Mail) Dan wasan gaba na kasar Belgium, Romelu Lukaku mai shekara 29 ma na shirin tattaunawa da Chelsea kan yiwuwar barin kungiyar bayan da Ba'Amurke Todd Boehly ya kammala saye kungiyar kan fam biliyan 4.25. (Times) West Ham ta sanar a shirye ta ke ta sayar da Issa Diop, dan wasanta na baya mai shekara 25, wanda tauraruwars aba ta haskawa karkashin koci David Moyes. (Standard) Zakarun Gasar Firimiyar Ingila Manchester City na sa ido kan Ben Nelson, dan wasan baya na kungiyar Leicester City mai shekara 18. (Mail) Real Madrid ta kara kaimi domin sayo Aurelien Tchouameni, dan wasan tsakiya na Monaco mai shekara 22, wanda ta yi tayinsa kan fam miliyan 68. (Foot Mercato - in French) https://www.bbc.com/hausa/wasanni-61641638 +sports Kasuwar ‘yan kwallo: Makomar: Neymar, Eriksen, Dembele, Traore, Dennis, Asensio, Lingard, Ekitike Dan wasan gaba na Brazil Neymar, mai shekara 30, na duba yiwuwar barin Paris St-Germain a wannan kakar, bayan samun labarin da ke cewa kulob din zai bar shi ya tafi. A bangare guda kuma kungiyar Chelsea na tuntubar wakilinsa domin daukar dan wasan. (ESPN) Manchester United za ta kammala magana da Christian Eriksen kuma tuni batun ya yi nisa da dan wasan tsakiya na Denmark mai shekara idan kwantiraginsa da Brentford yak are. (Star) Chelsea, Paris St-Germain da Bayern Munich na matsa kaimin daukar dan wasan gaba na Faransa da Barcelona Ousmane Dembele, mai shekara 25. (Marca) Barcelona ta yanke shawara kan tsohon dan wasan Wolves da Sifaniya Adama Traore dan shekara 26, kan kwantiragi maimakon aro . Barca dai na da aniyar rattaba hannu kan daukar dan wasa Traore kan farashin yuro miliyan 30 (£26m). (Sport) Dan wasan Watford da Najeriya mai kai hari,  Emmanuel Dennis, dan shekara 24, na cikin jerin wadanda Everton take son dauka domin maye gurbinsa da dan wasan gaba na Brazil mai shekara 25, Richarlison, wanda ya tafi Tottenham kan fam miliyan 60. (Evening Standard) Dan wasan Real Madrid kuma na tsakiyar Sifaniya Marco Asensio, mai shekara 26, ka iya barin Bernabeu a kakar wasan bana, idan Real ba su yi masa tayin tsawaita kwantiraginsa ba, wanda zai kare a shekara mai zuwa. AC Milan na daga cikin masu zawarcin dan wasan, duk da cewa wasu daga cikin kulob-kulob din  Premier League sun fara nuna shawa’a kan daukarsa. (Marca) Tottenham da West Ham, Everton da Newcastle United na cikin kungiyoyin da ke zawarcin dan wasan tsakiyar Ingila, Jesse Lingard, dan shekara 29, bayan ya bar Manchester United sakamakon karewar kwantiraginsa. (Telegraph, subscription required) Tottenham sun kusa kammala Shirin daukar dan wasan Barcelona mai tsaron gidan Faransa, Clement Lenglet, mai shekara 27, duk da cewa makomar dan wasan baya na Brazil Emerson Royal tana-kasa-tana-dabo kan komawarsa Atletico Madrid. (Express) Dan wasan baya na Sifaniya, Hector Bellerin, mai shekara 27, na atisaye bayan musayarsa da aka yi  daga Arsenal zuwa Real Betis. Bellerin ya ce ya koyi abubuwa da dama a lokacin da ya ke Betis, hakan ya taimaka masa wajen sake kaunar wasanni. (Star) https://www.bbc.com/hausa/articles/c2engrpg0dmo +sports Lille vs Chelsea: Watakila Azpilicueta da Alonso su buga fafatawar Chelsea ta ziyarci Faransa, domin buga wasa na biyu na zagaye na biyu a gasar Champions League da za su kara ranar Laraba. Tuni koci Thomas Tuchel ya ce mai tsaron baya Cesar Azpilicueta da Marcos Alonso sun kammala shirin fuskantar kungiyar Faransa. Kyaftin Azpilicueta ya murmure daga rashin lafiya, shi kuwa Alonso ya warke bayan jinyar cutar korona. Sai dai kuma Tuchel ya ce da kyar ne idan Callum Hudson-Odoi da kuma Reece James za su iya buga karawar. 'Yan wasan biyu ba su yi wa Chelsea karawar Premier League da ta ci Newcastle 1-0 ranar Lahadi. Chelsea ce ta yi nasara a kan Lille da ci 2-0 a wasan farko da suka kara a gasar a Stamford Bridge, inda Kai Havertz da Christian Pulisic suka ci kwallayen. Gwamnatin Burtaniya ta samar da wani lasisi na musamman don ci gaba da gudanar da Chelsea, bayan da aka rufe asusun mai kungiyaer, Roman Roman Abramovich, wanda ake alakanta shi da amini ga ga shugaban Rasha, Vladimir Putin. An amince kungiyar ta Stamford Bridge ta kashe fam 500,000 a wasannin gida, ta kuma kashe fan 20,000 a wasannin waje. A kalla ana kashe fam 30,000 wajen gudanar da gasar Premier League da kuma wasannin waje a gasar Zakarun Turai da wasu karin tsarabe-tsarabe. https://www.bbc.com/hausa/wasanni-60768678 +sports Chelsea 2-4 Arsenal: Gunners ta je ta ragargaji Chelsea a Stamford Bridge Arsenal ta koma turbar neman gurbin buga Champions League a badi, bayan da ta doke Chelsea 4-2. Gunners ta ziyarci Stamford Bridge, inda ta buga kwantan wasan mako na 25 a gasar Premier League ranar Laraba. Arsenal ce ta fara cin kwallo a minti na 13 da fara wasa ta hannun Edward Keddar Nketiah, sai dai minti hudu tsakani Chelsea ta farke ta hannun Timo Werner. Emile Smith-Rowe ne kara ci wa Arsenal kwallo na biyu, amma kafin hutu Cesar Azpilicueta ya farkewa kungiyar Stamford Bridge kwallon. Bayan da suka yi hutu suka koma zango na biyu ne Gunners ta kara na uku ta hannun Edward Keddar Nketiah kuma na biyu da ya zura a raga a karawar, sannan daf da za a tashi daga wasan Bukayo Saka ya zura na hudu a raga a bugun fenariti. Da wannan sakamakon Gunners ta kawo karshen rashin nasara a karawa uku a jere da ta yi a babbar gasar tamaula ta Ingila a kwanan nan. Wasa ukun da aka doke Arsenal sun hada da kashi da sha a hannun Crystal Palace a Selhust Park da wanda Brighton ta doke ta a Emirates da rashin nasara da ta yi a St Mary a hannun Southampton ranar Asabar. Arsenal tana ta biyar a teburin Premier da maki 57 iri daya da na Tottenham ta hudu. Wannan namijin kwazon da Arsenal ta yi zai ba ta karfin gwiwar tunkarar fafatawa da Manchester United ranar Asabar a gasar ta Premier League. https://www.bbc.com/hausa/wasanni-61171174 +sports Frank Ribery ya yi ritaya daga sana'ar kwallon kafa Tsohon dan kwallon, Bayern Munich ta tawagar Faransa, Franck Ribery ya sanar da yin ritaya daga sana'ar tamaula. Mai shekara 39, ya soke sauran kunshin kwantiraginsa da kungiyar da ke buga Serie A, Salernitana, bayan da yake fama da jinyar raunin gwiwar kafa. Ya ci kwallo 124 ya kuma bayar da 182 aka zura a raga a wasa 425 da ya yi wa Bayern Munich tsakanin 2007 zuwa 2019. Dan kasar Faransa ya lashe Bundesliga tara da Champions League a 2013. Ribery ya fara zuwa Fiorentina daga nan ya koma Salernitana a bara, wanda ya taimaka kungiyar ba ta fadi daga Serie A da maki daya tal tsakani ba. Sai dai bai sake buga wasa ba tun bayan wanda kungiyar ta fara da Roma ta kuma sha kashi a wasan farko a Serie A. An dade ana ta rade-radin zai yi ritaya, yanzu ya sanar da kansa cewar ya rataye takalmansa na taka leda. Dan kasar Faransa ya koma Bayern Munich kan £17m daga Marseille a cikin watan Yunin 2007, kaka daya tsakani da ya kasance cikin 'yan kwallon tawagar Faransa da suka yi na biyu a gasar kofin duniya da Italiya ta dauka a 2014. Wanda ya lashe kyautar gwarzon dan Faransa karo uku ya ci mata kwallo 16 a wasa 25 da ya yi mata, wanda ya yi ritaya daga buga mata wasanni a 2014. Bayan kaka 12 da ya yi a Bayern Munich ya bar kungiyar tare da Arjen Robben bayan da Bayern da lashe Bundesliga na bakwai a jere a lokacin. https://www.bbc.com/hausa/articles/cd1jnn1000lo +sports Chelsea vs Real Madrid: 'Yan Real Madrid da suka je Stamford Bridge Real Madrid ta ziyarci Chelsea domin buga wasan zagayen farko a Champions League, karawar Quarter finals da za su yi ranar Laraba. Real Madrid wadda ke jan ragamar teburin La Liga a bana tana da Champions League 13, ita kuwa Chelsea wadda ke mataki na uku a teburin Premier League tana da kofin Zakarun Turai biyu. Wannan shine karo na shida da za a kece raini tsakanin kungiyoyin biyu, inda Chelsea ta yi nasara a uku da canjaras biyu. Chelsea wadda ke rike da Champions League, itace ta yi waje da Real Madrid a bara da cin kungiyar Sifaniya 2-0 a Ingila, bayan da suka fara tashi 1-1 a gidan Real Madrid. Tarihin wasa tsakanin Chelsea da Real Madrid: Kakar 2020/2021 Champions League Laraba 05 ga watan Mayu 2021 Champions League Talata 27 Afirilun 2021 Kakar 1998/1999 European Super Cup Juma'a 28 ga watan Agustan 1998 Kakar 1970/1971 Euro Cup Winners Cup Juma'a 21 ga watan Mayun 1971 Euro Cup Winners Cup ranar Laraba 19 ga watan Mayun 1971 'Yan wasan Real Madrid: Masu tsaron raga: Courtois, Lunin da kuma Fuidias. Masu tasron baya: Carvajal, E. Militão, Alaba, Vallejo, Nacho, Marcelo da kuma Mendy. Massu buga tsakiya: Kroos, Modrić, Casemiro, Valverde, Lucas V., D. Ceballos da kuma Camavinga. Massu cin kwallaye: Benzema, Asensio, Bale, Vini Jr., Rodrygo da kuma Mariano. https://www.bbc.com/hausa/wasanni-60990236 +sports Bayern Munich ta yi wa Salszburg ruwan kwallaye Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich ta kora takwararta ta FC Salszburg gida bayan ruwan kwallaye da ta yi mata a gasar Champions. Tun a minti na 12 da fara wasa dan bayan Salszburg Maximilian Wober ya bige Lewandowski a cikin da'ira ta 18 abin da ya kai ga bai wa Munich bugun daga kai sai mai tsaron raga kenan kuma Lewandowski ya ci. A minti na 21 alkalin wasa ya tabbatar wa da Bayern fenariti na biyu, wanda Maximilian Wober ya kara bige Lewandowski a karo na biyu, kuma nan take dan wasan gaban na Munich ya sake cin kwallo ta biyu, bayan duba na'urar VAR da take taimakawa alkalin wasa. Munich sun ci gaba da matsa lamba a wasan abin da ya haddasa wani kuskure tsakanin dan bayan Red bull da mai tsaron ragar kungiyar Philipp Kohn wanda ya yi kokarin cire kwallon amma ta wuce su ta karasa wajen Lewandowski kuma ya jefa ta uku a minti na 21. Da wadannan kwallaye ukun da ya ci ya karya tarihin Marco Simone da ya ci uku cikin minti 24 a wasan Milan da Rosenborg a 1996. Yanzu kyaftin din Poland yaci kwallo 40 a wannan kakar a duka gasa, kuma shi ne karo na bwakai da ya ci irin wadan nan kwallaye ko sama da su a jere. Gnabry ya jefa kwallo ta hudu a saga ta hannun Coman, wanda hakan yakai kwallayen da Munich suka ci 4-0 a cikin minti 45 na farko na wasan. Muller ne ya jefa kwallo ta biyar bayan dawowa hutun rabin lokaci, bayan nan dan wasan gaban Maurits Kjaergaard ya jefa kwallo daya da Salszburg suka ci a wasan. Muller ya kara ta shi sannan Sane ya kara ta bakwai, da wannan sakamako ne Salszburg ta fita daga gasar zakarun Turai ta bana. Kwallayen da aka ci duka tsakanin wasan biyu sun tashi Bayern Munich na da 8-2 Salszburg. https://www.bbc.com/hausa/wasanni-60669245 +sports Masu Liverpool na neman waɗanda za su sayi ƙungiyar "Shugaban ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool Tom Werner ya tabbatar da cewa masu ƙungiyar, Fenway Sports Group (FSG), na neman yadda za su sayar da ita. A kwanan nan rukunin FSG ya ce ""zai duba sabbin masu zuba hannun jari"" yayin da ake raɗe-raɗin sun saka kulob ɗin a kasuwa. ""Muna duba yadda za sayar, amma ba abu ne na gaggawa ba, ba mu saka wa'adi ba kuma ni ina ganin ba wani sabon abu ba ne,"" in ji Werner cikin hirarsa da Boston Globe. ""Ɗaya daga cikin abubuwan da zai faru shi ne mu ne za mu ci gaba da jagorancin ƙungiyar nan da lokuta."" FSG ya sayi Liverpool kan fan miliyan 300 a shekarar 2010. Werner na cikin mutanen da suka kafa FSG, wanda John Henry ke matsayin babban shugaba tun da aka kafa shi a 2001. Tauraron ɗan ƙwallon kwando LeBron James na da hannun jari a Liverpool tun daga 2011 inda yake da kashi 2 cikin 100 kan fan miliyan 4.7." https://www.bbc.com/hausa/articles/cjen4e270ylo +sports Nkunku zai koma Chelsea, Southgate zai zauna a Ingila, Azzedine ya yi kasuwa "Rahotanni sun ce Chelsea ta kamalla ƙulla yarjejeniya da ɗan wasan RB Leipzig da Faransa Christopher Nkunku kuma ɗan wasan mai shekara 25 zai koma can a hukumance a watan Yulin 2023. (Fabrizio Romano, Twitter) Gareth Southgate ya yanke hukuncin zama a matsayin kocin Ingila bayan kashin da Faransa ta ba ƙungiyarsa a wasan daf da na kusa da na ƙarshe na gasar cin kofin duniya.  (Telegraph) Shi ma Eddie Howe mai shekara 45 ya ce yana so Southgate mai shekara 52 ya ci gaba da zama a matsayin kocin Ingila duk da ce-ce-ku-cen da ake yi kan cewa shugaban Newcastle na son ɗaukarsa. (Chronicle) Youssoufa Moukoko mai shekara 18 da Liverpool da Manchester United da Chelsea ke hari bai kusa ƙulla yarjejeniya ba da Borussia Dortmund, kamar yadda wakilin ɗan wasan gaban Jamus ɗin ya tabbatar. (Sky Germany via Liverpool Echo) Shugaban Angers Said Chabane ya ce kulob din na shirin rabuwa da ɗan wasan Morocco Azzedine Ounahi mai shekara 22 a watan Janairu sakamakon Leicester da Leeds da West Ham na neman ɗan wasan.  (Talksport) A kullum Liverpool na samun ƙarin ƙwarin gwiwa kan cewa su za su yi nasara a neman ɗan wasan Borussia Dortmund da Ingila Jude Bellingham mai shekara 19. Mirror) Chelsea na shirin ƙara matsa lamba kan Real Madrid a gwagwarmayar da ake yi ta sayen ɗan wasan RB Leipzig da Croatia Josko Gvardiol mai shekara 20 ta hanyar ƙoƙarin ɗaukarsa a watan Janairu. (Mirror) Newcastle na daga cikin ƙungiyoyi da dama da ke neman ɗan wasan gaban Georgia Khivicha Kvaratskhelia mai shekara 21 amma Napoli ba ta son sayar da shi kan farashin fam miliyan 50 kamar yadda aka ruwaito. (90min) Akwai yiwuwar golan Manchester United da Sifaniya David de Gea mai shekara 32 zai bar Old Trafford a kyauta a kaka mai zuwa sakamakon kulob ɗin bai amince da tsawaita kwantiraginsa ba na tsawon watanni 12. (Sky Germany via Sun) Ɗan wasan tsakiyar Amurka Christian Pulisic mai shekara 24 ya ce ""abubuwa na sauyawa cikin gaggawa kuma komai kan iya faruwa"" bayan da aka alaƙanta shi da komawa Manchester United daga Chelsea.  (Indirect Podcast via Metro)" https://www.bbc.com/hausa/articles/cz40xjj5px1o +sports Al Nassr ta Saudi Arabia ta yi wa Ronaldo tayin albashi mai tsoka Al-Nassr ta Saudi Arabia ta yi wa Cristiano Ronaldo tayin albashi mai tsoka da zarar an kammala Gasar Cin Kofin Duniya. Kungiyoyi da dama na son daukar kyaftin din Portugal, amma Al-Nassr ce ta yi tayin Yuro 200m a duk shekara, in ji wasu rahotanni. Ronaldo, mai shekara 37, bai da wata yarjejeniya a tare da shi, bayan da dan wasan da Manchester United suka raba gari, sakamakon wata hira a talabijin da ta jawo cece-kuce. Ya soki United a hirar da cewar baya ganin martabar koci Erik ten Hag. A lokacin da ya gabatar da hirar a TalkTV ya ce wata kungiya a Saudi Arabia ta yi masa tayin £305m kan fara kakar nan - hakan da ya zama mafi karbar albashi a fanni tamaula a duniya. Ronaldo yana tare da tawagar Portugal a Gasar Cin Kofin Duniya da kyar idan zai fayyace makomarsa har sai bayan kammala babbar Gasar tamaula ta duniya. Ranar Talata Portugal za ta kara da Switzerland a wasan zagaye na biyu a wasannin da Qatar ke karbar bakunci. Duk da cewar Ronaldo bai da wani kwantiragi a tare da shi a yanzu hakan, amma baya da damar kulla yarjejeniya da wata kungiya har sai 1 ga watan Janairu. Ronaldo ya ci kwallo 145 a wasa 346 da ya yi wa United a karo biyu da ya buga mata tamaula, bayan da ya je Real Madrid a 2009, sannan ya koma Old Trafford daga Juventus a 2021. Sauran yarjejeniyar £500,000-a duk mako ta rage tsakanin Ronaldo da United, wadanda suka amaince kowa ya kama gabansa. https://www.bbc.com/hausa/articles/c4n7k842xkko +sports Carlo Ancelotti mai fuskantar kalubale ya je Stamford Bridge Chelsea za ta karbi bakuncin Real Madrid a wasan zagayen farko a Quarter finals da za su kece raini a Stamford Bridge ranar Laraba. Wannan shine wasa na shida da za su fafata a tsakaninsu a gasar Zakarun Turai, inda Chelsea ta yi nasara a uku da canjaras biyu. Carlo Ancelotti ya warke daga cutar korona ya kuma bi Real zuwa Stamford Bridge a wasan da kocin ke fuskantar kalubale a kan aikin da yake yi. Koda yake Real wadda ta lashe Spanish Super Cup a kakar nan, ta bayar da tazara da maki 12 a La Liga, sai dai kuma za a iya auna dalilin da kungiyar ta dauko kocin. Real ta shiga rudani tun bayan da Zinedine Zidane ya ajiye aikin jan ragamar kungiyar da barin kyaftin, Sergio Ramos da ya koma Paris St Germain da taka leda da kuma Raphael Varane da ya koma Manchester United.. Saboda haka shugaban Real Madrid, Florentino Perez ya kwan da sanin suna bukatar kwararren koci da zai dawo da martabar kungiyar wajen lashe manyan kofuna a koda yaushe. Hakan ne ya sa Ancelotti ya yi amfani da damar da ya samu na rashin kokarin Atletico Madrid a kakar bana da matsalar da Barcelona ta tsinci kanta da ta kai ba ta taka rawar gani, amma yanzu ta sa kwazo a wasanninta, sannan Sevilla ta kasa nuna da gaske take a kakar nan. Idan har Ancelotti ya lashe La Liga a bana zai zama na farko da ya ci kofi a kowacce babbar gasar tamaula a manyan kasashe biyar da ke kan gaba a taka leda a Turai. To sai dai yadda Barcelona mai kwantan wasa a La Liga ke kara matsar Real Madrid, idan har ba ta lashe kofin nan ba a bana, kocin zai fuskanci kalubalen kora daga Santiago Bernabeu. Haka kuma a bara Chelsea mai rike da Champions League ta yi waje da Real Madrid a gasar ta Zakarun Turai, saboda haka a wannan lokacin kungiyar Spaniya na bukatar yin nasara a kan kungiyar Stamford Bridge a wasa na shida da za su kece raini a tsakaninsu. https://www.bbc.com/hausa/wasanni-61014200 +sports Wani jami'in tsaro ya fado daga bene ya mutu a filin wasa na Lusail Wani jami'in tsaro a filin wasa na Lusail ya fado daga bene ya mutu a lokacin karawa tsakanin Argentina da Netherlands a daf da na kusa da na karshe. Dan kasar Kenya, John Njau Kibue na cikin hayyacinsa a lokacin da lamarin ya faru daga baya jikin ya motsa, bayan kwana daya da ya yi a asibitin. Masu shirya Gasar Kofin Duniya a Qatar sun sanar da cewar suna bincike kan musabbabin da ta kai jami'in ya fado ya mutu. 'Yar uwar mutumin mai shekara 24 ta sanar da CNN cewar kawo yanzu ba a sanar da su wani bayani ba da ya shafi hadarin. ''Muna son a yi mana adalci. Muna son sanin hakikanin abin da ya faru da ta kai ya mutu. Ba su aike mana da hoton wurin da ya fado ba, ba wani jawabi da muka samu har yanzu.'' in ji Ann Wanjiru. Kibue shi ne bako na biyu da yake aiki a Qatar da ya mutu tun fara Gasar Kofin Duniya ranar 20 ga watan Nuwamba. Wani dan kasar Philippines ne ya fara mutuwa a lokacin da yake gyare-gyaren sansanin Saudi Arabia, kamar yadda The Athletic ta bayar da rahoto. Wani rahoton da jaridar Guardian ta wallafa ta ce ma'aikata baki 6,500 ne suka mutu a Qatar, tun bayan da aka bai wa kasar izinin karbar bakuncin Gasar Kofin Duniya a 2010. Argentina ta kai wasan karshe a Gasar Kofin Duniya, bayan da ta ci Croatia 3-0 ranar Talata. Ranar Laraba za a buga daya wasan daf da kashe tsakanin Faransa mai rike da kofin da kuma Morocco wadda ta je wannan matakin a karon farko a tarihi. Ranar Lahadi za a buga wasan karshe daga nan a rufe Gasar Kofin Duniya, sai shekara hudu nan gaba. https://www.bbc.com/hausa/articles/cl4gxn5ky74o +sports Brentford ta kara yaga barakar Man United Manchester United ta sha kashi da ci 4-0 a gidan Brentford a wasan mako na biyu a gasar Premier League ranar Asabar. Brentford ta fara cin kwallo a minti na 10 da take leda ta hannun Pelenda Joshua Da silva, minti takwas tsakani Mathias Jensen ya zura na biyu a raga. A minti na 30 Ben Mee ya ci wa Brentford kwallo na uku, sannan Bryan Mbeumo ya kara na hudu saura minti 10 su je hutu. Erik Ten Hag ya zama na biyu a matakin sabon koci da ya yi rashin nasara a wasan farko a waje a Manchester United. Wanda ya yi wannan rashin kokarin shi ne Sir Alex Ferguson a Nuwambar 1982 a lokacin da Oxford ta ci United 2-0. Ten Hag, wanda ya fara jan ragamar kungiyar Old Trafford a bana, ya sha kashi a wasa biyu kenan a jere. 'Yan wasan Brentford 11 da suka fuskanci United Rabon da United ta yi rashin nasara a hannun Brentford shi ne 2-0 a zagaye na biyar a FA Cup a Fabrairun 1938. Tun kan wasan na ranar Asabar, Brentford ta samu maki daya kacal daga fafatawa shida a kan United, tun bayan gida da waje da ta yi 1936/37. Karo na biyu a jere kenan da aka doke United a kakar nan, bayan da Brighton ta yi nasara da ci 2-1 a Old Trafford a karawar makon farko. Brentford ta zama ta uku da ta ci United kwallo hudu tun kan hutu a Premier League, bayan Tottenham a Oktoban 2020 da Liverpool a Oktoban 2021. 'Yan wasan United 11 da ta fara karawa da Brentford da su Ranar 22 ga watan Agusta, United za ta karbi bakuncin Liverpool a Old Trafford a wasan mako na uku a gasar Premier League ta bana. Liverpool wadda ta tashi 2-2 a gidan Fulham a wasan makon farko, za ta karbi bakuncin Crystal Palace ranar Litinin 15 ga watan Agusta. Ita kuwa Brentford wadda ta ttashi 2-2 a gidan Leicester City a karawar makon farko, za ta ziyarci Fulham ranar 20 ga watan Agusta, domin buga wasan mako na uku a babbar gasar tamaula ta Ingila ta bana. https://www.bbc.com/hausa/articles/cpdxv14p1d0o +sports Arsenal za ta yi wasa tara a cikin watan Oktoba Ranar 1 ga watan Oktoba za a ci gaba da wasannin Premier League, karawar mako na takwas da za a yi fafatawa bakwai a ranar. Arsenal tana ci gaba da jan ragamar teburin babbar gasar tamaula ta Ingila da tazarar maki daya tsakaninta da Manchester City mai maki iri daya da na Tootenham ta uku. To sai dai Arsenal za ta buga wasa tara a cikin watan na Oktoba ciki har da fafatawa hudu a gasar Euuropa League. Gunners din za ta kece raini a wasa biyar a Premier League, bayan da ake sa ran dage wanda ya kamata ta yi da Manchester City ranar 19 ga watan Oktoba. Arsenal za ta karbi bakuncin PSV Eindhoven ranar 20 ga watan Oktoba, hakan ne zai sa a dage fafatawar hamayya da ya kamata ta yi da kungiyar Etihad. Wasannin mako na takwas ranar Asabar 1 ga watan Oktoba Wasannin mako na takwas ranar Lahadi 2 ga watan OOktoba Wasannin da Arsenal za ta buga a cikin watan Oktoba Premier League Asabar 1 ga watan Oktoba Arsenal da Tottenham Europa League Alhamis 6 ga watan Oktoba Arsenal da Bodo Glimt Premier League Lahadi 9 ga watan Oktoba Arsenal da Liverpool Europa League Alhamis 13 ga watan Oktoba Bodo Glimt da Arsenal Premier League Lahadi 16 ga watan Oktoba Leeds da Arsenal Premier League Laraba 19 ga watan Oktoba Arsenal da Man City Europa League Alhamis 20 ga watan Oktoba Arsenal da PSV Eindhoven Premier League Lahadi 23 ga watan Oktoba Southampton da Arsenal Europa League Alhamis 27 ga watan Oktoba PSV Eindhoven da Arsenal Premier League Asabar 30 ga watan Oktoba Arsenal da Nottm Forest https://www.bbc.com/hausa/articles/cxx93p3y1jlo +sports Tottenham na bibiyar Gordon, watakila Chamberlain zai bar Liverpool Tottenham na ci gaba da bibiyar dan wasan Everton da Ingila Anthony Gordon, mai shekara 21, kafin watan Janairu da za a bude kasuwar saye da sayar da 'yan wasa. (Football London) Ana sa ran tsohon dan wasan tsakiya na Ingila Alex Oxlade-Chamberlain, mai shekara 29, zai fice daga kungiyar Liverpool a kyauta a kakar wasan nan. (Fabrizio Romano) Kungiyar ta so sayar da dan wasan tsakiyar kan farashin fam miliyan 10, a kakar wasan da ta wuce sai kuma a kai rashin sa'a ba a kammala yarjejeniya da kowacce kungiya ba. (Mirror) Dan wasan tsakiya na Barcelona da Netherland Frenkie de Jong, mai shekara 25, ya ce kulub din La Liga ne suka kwarmatawa kafafen yada labarai bayani kan kwantiraginsa. (De Telegraaf, via Mirror) Borussia Dortmund za ta sai da dan wasan West Ham da Leeds Raphael Guerreiro, mai shekara 28, kafin kwantiragin dan Portugal din ta kare a karshen kakar wasannin da muke ciki. (Bild - in German) Chelsea ta damu matuka kan rashin tsayayyen lokaci ga dan wasa Romelu Lukaku a yanzu da ake gasar cin kofin duniya. Damuwar ta hada watakil darajar dan wasan mai shekara 28 ta yi kasa idan suka yi kokarin sai da shi a karshen dogon kwantiragin da yake na kyauta a Inter Milan. (Evening Standard) Eja din dan wasan tsakiya na Dynamo Moscow Arsen Zakharyan, ya kira sha'awar da Chelsea ta nuna kan dan wasan mai shekara 19 da wasan yara. (Championat - in Russian) AC Milan na duba yiwuwar dauko dan wasan Chelsea Hakim Ziyech, mai shekara 29, a matsayin bashi, watakil ma a kakar wasa mai zuwa za su dauko dan wasan gaba na Albania Armando Broja mai shekara 21. (Corriere Dello Sport - in Italian) Milan ta na kuma son dauko dan wasan tsakiya na Chelsea Ruben Loftus-Cheek, mai shekara 26, bayan birgesun da ya yi a lokacin Champions League a Stamford Bridge. (Calciomercato - in Italian https://www.bbc.com/hausa/articles/c1w6zz51l92o +sports Haaland na zazzabi yana kuma jin radadi a kafarsa An sauya Erling Haaland a wasan Champions League da Manchester City ta tashi 0-0 a gidan Borussia Dortmund ranar Talata. Pep Guardiola ya ce ya fitar da dan wasan domin yana fama da zazzabi da kuma jin zafi a kafarsa. Guardiola ya ce ''Ban sani ba kawo yanzu'' lokacin da aka tambaye shi ko radadin da dan kwallon ke ji mai girma ne. Haaland ya ci kwallo 22 a wasa 15 da ya fara buga wa City a kakar nan. Dan wasan ya taba kwallo sau 13 da buga tamaula zuwa raga daya amma aka tare, daga baya aka sauya shi a karawar tare da Joao Cancelo. ''Ina ganin dan wasan na bukatar hutu, yana kuma fama da dan zazzabi a tare da shi'' haka shima Joao,'' ''Haka kuma Haaland na jin radadi a kafarsa,'' shi ya sa ba zai iya buga zagaye na biyu ba a karawar da suka yi a Jamus. ''Na yi magana da likitocin kungiyar da aka yi hutu, sun nuna min fargabarsu, amma naga yana takawa yadda ya kamata. Za mu auna shi sosai.'' City ta samu gurbin shiga zagayen kungiyoyi 16 da za su buga zagayen gaba har da makin da ta samu a Jamus a gasar Zakarun Turai. Kungiyar ta Etihad za ta ziyarci Leicester City a wasan Premier League ranar Asabar da za su fafata a King Power. https://www.bbc.com/hausa/articles/cj5z1qjg4pvo +sports Tottenham ta fara Premier ta bana da cin kwallaye da yawa Tottenham ta yi nasarar cin Southampton 4-1 a wasan makon farko a gasar Premier League kakar 2022/23 da suka kara ranar Asabar. Southampton ce ta fara cin kwallo ta hannun James Ward-Prowse a minti na 12 da fara tamaula. Daga nan ne Tottenham ta farke ta hannun Ryan Sessegnon, sannan Eric Dier ya zura na biyu a raga. Tottenham ta ci kwallo na uku, bayan da Mohammed Salisu ya ci gida, sannan Dejan Kulusevski ya ci na hudu a fafatawar. Karon farko da Ryan Sessegnon ya ci wa Tottenham kwallo a Premier League, shi kansa Eric Dier na farko da ya zura a raga tun bayan shekara uku. Harry Kane bai samu cin kwallo ba, kenan karo na takwas daga wasa tara a karawar farko da bude Premier League - dayan da ci shi ne a 2019 a wasa Aston Villa. Kane mai tarihin zura kwallo 11 a wasa 14 da Southampton, ya kasa daga raga a wasan makon farko a babbar gasar tamaula ta Ingila ranar Asabar. Wannan shi ne karo na hudu da aka kara a wasan farko na bude Premier League tsakanin kungiyoyin biyu, inda Tottenham ta yi nasara a uku da canjaras daya. James Ward Prowse, wanda ya ci wa Southampton kwallo shi ne na biyu a cin kwallaye a waje a bara mai tara a raga, bayan Mohamed Salah mai 11. https://www.bbc.com/hausa/articles/c6p793eprppo +sports Klopp ya yi sanadin kokar Parker kociyan Bournemouth Bournemouth ta kori, Scott Parker, bayan da kungiyar ta sha kashi a gidan Liverpool da ci 9-0 ranar Asabar, bayan wasa hudu da ya ja ragama a Premier League. Rashin nasara da ta yi a hannun kungiyar Anfield ya zama karo na uku a jere da aka ci Bournemouth, bayan da ta fara doke Aston Villa 2-0. Tuni Bournemouth ta nada Gary O'Neil kociyan rikon kwarya, sannan Shaun Cooper da Tommy Elphick za su taimaka masa. Parker ya koma Bournemouth daga Fulham a Yunin 2021, wanda ya kai kungiyar gasar Premier League a bana, bayan da ta yi ta biyu a Championship a bara. Bayan da Bournemouth ta fara doke Aston Villa 2-0 a gida, kawo yanzu an zura mata kwallo 16 a wasa ukun da ta yi da 4-0 a hannun Manchester City da 3-0 a wurin Arsenal, sai Liverpool da ta zura 9-0 a Anfield. Rarar kwallo 14 a ragar Bournmouth shi ne rashin kokari mafi muni a babbar gasar tamaula ta Ingila, bayan fafatawa hudu da fara kaka a tarihi. Shi ne kocin farko a Premier League bayan shekara 18 da aka sallama cikin Agusta tun bayan Bobby Robson a Newcastle a 2004. Shi ne na 11 da aka kora bayan wasa hudu da fara kakar tamaula, na karshe-karshe da aka sallama shi ne Javi Gracia a Watford a 2019. https://www.bbc.com/hausa/articles/cx9gljw5nkzo +sports Ten Hag zai maye gurbin Ronaldo a watan Janairu Kociyan Manchester United, Erik ten Hag na fatan daukar madadin Cristiano Ronaldo da zarar an bude kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo a Janairu. Tun da fari Ten Hag ya ce baya son rabuwa da dan kwallon mai shekara 37, sai dai hirar da Ronaldo ya yi da Piers Morgan ta jawo dole ya hakura da shi. A hirar da kyaftin din Portugal ya yi da Talk TV, ya ce an yaudare shi a United, kuma baya ganin martabar Ten Hag. Hakan ya sa aka raba gari tsakanin United da Ronaldo, wanda ya yi ban kwana da Gasar Cin Kofin Duniya yana kuka a Qatar ranar Asabar, bayan da aka fitar da Portugal. Morooco ce ta yi nasara a kan Portugal da ci 1-0 a wasan daf da na kusa da na karshe a babbar gasar tamuala ta duniya. Tafiyar Ronaldo ta sa dole United ta nemi wanda zai maye gurbin kyaftin din tawagar Portugal, domin ta samu rarar dan wasan gaba guda daya a kungiyar. ''Za muyi dukkan abin da ya dace domin daukar fitatcen dan wasa da zai dace da mu,'' in ji Ten Hag. Koda yake ba a fayyace wanda United za ta yi zawarci ba, ana cewa watakila Ten Hag ya bukaci Cody Gakpo, mai shekara 23 na PSV Eindhoven ko kuma dan wasan Benfica mai shekara 21, Goncalo Ramos, Ramos ya ci Switzerland kwallo uku a wasan da Portugal ta ci 6-1 a wasan zagaye na biyu. ''Ba zan ce komai ba kan dan kwallon da zan so na dauka,'' in ji kociyan United. ''Dukkan 'yan wasa suna da kunshin yarjejeniya a tare da su, kuma ina martaba hakan. Yana da wahala kungiya ta saki fitatcen dan wasanta a watan Janairu, kuma kowa na jiran a kammala Gasar Kofin Duniya daga nan a fara zawarci. Kungiyar Old Trafford ta kashe kudi da dama kan fara kakar bana, inda ta dauki Antony da Casemiro da kuma Lisandro Martinez. Sai da United za ta samu kudi da yawa a kasa, bayan ta daina biyan kudin albashin Ronaldo. https://www.bbc.com/hausa/articles/cx8x10qgy2zo +sports Barcelona ta samu gurbin buga Champions League a badi Barcelona ta samu gurbin shiga gasar Champions League ta badi kai tsaye, bayan da ta doke Real Betis 2-1 a gasar La Liga ranar Asabar. Ansu Fati ne ya fara ci wa Barcelona kwallo - kuma na farko da ya zura a raga tun bayan da ya fara jinya daga 6 ga watan Nuwamba. Sai dai kuma Betis ta farke ta hannun tsohon dan kwallon Barcelona, mai tsaron baya, Marc Bartra. Saura minti hudu a tashi daga wasan Barcelona ta kara na biyu ta hannun Dani Alves. Tun kan fara wasan Barcelona ta yi wa Betis tarbar girma, wadda ta lashe Copa del Rey na bana, inda suka yi layi biyu suna musu tafi a lokacin da suke shiga tsakiyar fili. Betis ta yi nasarar daukar Copa del Rey na kakar nan, bayan da ta doke Valencia a karawar karshe. Real Madrid wadda ta lashe La Liga na bana kuma na 35 jumulla, tana mataki na daya da tazarar maki 12 tsakaninta da Barcelona. Sai dai kungiyar Camp Nou ta bai wa Betis ta biyar a teburi tazarar maki 11, kuma saura wasa uku-uku a karkare kakar bana. Barcelona tana mataki na tara a lokacin da Xavi ya maye gurbin koci Ronald Koeman a watan Nuwamba. https://www.bbc.com/hausa/wasanni-61371246 +sports Casemiro: Real Madrid ta ci wasa 150 tare da dan Brazil a cikin fili Real Madrid ta yi nasarar doke Real Mallorca 3-0 a wasan mako na 28 a gasar La Liga ranar Litinin. Vinicius Junior ne ya fara cin kwallo a minti 10 da fara zagaye na biyu, bayan da ya samu tamaula ta hannun Karim Benzema. Daga baya Benzema, dan wasan tawagar Faransa ya kara biyu daya a bugun fenariti. Dan wasan tawagar Brazil, Casemiro ya buga fafatawar a gidan Mallorca, kuma karo na 150 da Real Madrid ta yi nasara a wasan da ya buga. Mai buga wa Real Madrid wasa daga tsakiya ya yi karawa 214 a gasar da cin kwallo 23, ya kuma lashe kofin babbar gasar tamaular Sifaniya karo biyu wato a 2017 da kuma 2020. Dan wasan ya fara buga wa Real Madrid La Liga ranar 20 ga watan Afirilun 2013 a karawar da ta yi nasara a kan Real Betis 3-1. A kakar 2019/20 itace wadda Casemiro ya buga da Real Madrid da ta yi nasara a wasa 25 a La Liga. A kakar bana ya buga wasa 25 a La Liga, an kuma yi nasara da shi a wasa 17. https://www.bbc.com/hausa/wasanni-60740530 +sports Jose Mourinho ya fara darawa a wasan farko a Serie A ta bana Kungiyar da Jose Mourinho ke jan ragama Roma, ta fara Serie A ta bana da kafar dama, bayan da ta je ta doke Salernitana da ci 1-0. Tun kan hutu Bryan Cristante ya ci wa Roma kwallon da ya sa ta hada maki uku a karon farko da fara Serie A ta kakar nan. Roma ta barar da damar maki, inda sabon dan kwallon da ta dauka a bana, Paulo Dybala ya buga kwallo ya doki turke da wadda Tammy Abraham ya buga aka tare. Haka ma Nemanja Matic da Georginio Wijnaldum sabbi da suka koma kungiyar a kakar nan, sun buga wa Roma fafatawar. Tsohon dan kwallon Manchester United da Chelsea, Matic ya saka hannu kan yarjejeniyar kaka daya a Roma a watan Mayu. Shi kuwa Wijnaldum ya koma buga wasannin aro a Serie A daga Paris St Germain a makon jiya. Shima Nicolo Zaniolo ya kusan ci wa Roma kwallo a karo da dama a wasa da Salernitana, wadda ta kai bantenta da maki daya kwal a bara, kaka ta uku kenan tana Serie A. Roma ta kare kakar da ta wuce a mataki na shida a babbar gasar tamaula ta Sifaniya karkashin Mourinho, amma ya dauki Europa Conference League a kakar da ta wuce. Hakan ne ya sa kungiyar za ta fafata a Europa League a bana. Eintranch Frankfurt ce ta lashe Europa League a kakar da ta wuce, bayan da ta yi nasara a kan Rangers a bugun fenari. https://www.bbc.com/hausa/articles/cllzpne8nnlo +sports Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Mane, Salah, Bale, de Jong, Kounde, Matthijs da Botman Duk da cewa dan wasan gaba na Masar Mohamed Salah, mai shekara 29, ya shaida wa abokansa na kud da kud cewa a shirye yake ya ci gaba da zama a Liverpool, yanzu haka ya sauya tunani bayan da Barcelona ta yi masa tayin komawa Nou Camp a bazara (Mirror) Tottenham ba ta da niyyar siyan kyaftin din Wales Gareth Bale a karo na uku yayin da dan wasan mai shekara 32 ke tunanin yaddazai shirya wa gasar cin kofin duniya ta bana. (Telegraph) Dan wasan gaban Senegal Sadio Mane, mai shekara 30, ya tambayi abokin wasan Liverpool kuma tsohon dan wasan Bayern Munich Thiago Alcantara ko zai iya shiga gidansa da ke Munich idan ya koma kungiyar ta Bundesliga a bana. (Mail) Barcelona na shirin tattaunawa da Manchester United kan batun dauko dan wasan tsakiyarta na Netherlands Frenkie de Jong, mai shekara 25, zuwa Old Trafford amma har yanzu kulob din na Sifaniya bai samu tayi a hukumance daga United ba. (Sports) Chelsea na zawarcin dan wasan baya na Juventus dan kasar Holland Matthis de Ligt, mai shekara 22, amma ga kocin Blues din Thomas Tuchel, babban abin da ke gabansa shine dauko dan wasan bayan Sevilla mai shekara 23 Jules Kounde. (talkSPORT) Dan wasan baya na kasar Holland Sven Botman, mai shekara 22, wanda ake alakanta shi da komawa Newcastle, ya ce har yanzu AC Milan na kokarin kammala cinikinsa daga Lille. (Kwallon Italiya) Rahotanni sun ce dan wasan baya na Ingila James Tomkins, mai shekara 33, ya rattaba hannu kan sabon kwantiragi na shekara guda da Crystal Palace, yayin da dan wasan tsakiyar Scotland James McArthur, mai shekara 34, shi ma ya amince da sabon kwantaragi a Selhurst Park. (Sun) https://www.bbc.com/hausa/labarai-61714522 +sports Aston Villa ta nada Unai Emery sabon kociyanta Aston Villa ta nada Unai Emery a matsayin sabon kociyanta, domin maye gurbin Steven Gerrard wanda ta kora ranar Alhamis. Tsohon kocin Arsenal, wanda ke jan ragamar Villareal, zai fara aiki ranar 1 ga watan Nuwamba. Villa ta biya Villareal £5.2m kudin kunshin kwantitagin mai shekara 50, wadda aka gindaya ga duk mai son daukar shi idan wa'adinsa bai cika ba. Kociyan rikon kwarya Aaron Danks shi ne zai ja ragamar Aston Villa wasan Premier da za ta kara da Newcastle a karshen mako. Villa ta kori Gerrard bayan da Fulham ta yi nasara da ci 3-0 a wasan Premier League ranar Alhamis, wanda ya ci wasa biyu kacal a bana. Emery wanda yarjejeniyarsa za ta kare a kungiyar Sifaniya a karshen kaka badi, zai fara aiki mako mai zuwa, idan ya samu takardar izinin aiki a Burtaniya. Kociyan ya ja ragamar wasa sama da 900 yana da kwarewa a gasar Premier League, wanda ya kai Arsenal wasan karshe a Europa League. Kociyan ya lashe Europa League uku a jere a Sevilla tsakanin 2013 zuwa 2016. Ya kuma lashe Ligue 1 a Paris St Germain da French Cups biyu da French League Cups biyu da kuma Trophees des Champions biyu a kungiyar ta Faransa. https://www.bbc.com/hausa/articles/c84g1qp5wjvo +sports Dukkan 'yan wasan da aka gayyata Gasar Cin Kofin Duniya a Qatar Dukkan sunayen 'yan wasa da kasashe 32 suka gayyata, domin buga musu Gasar Cin Kofin Duniya a Qatar a 2022. Za a fara Gasar daga 20 ga watan Nuwamba zuwa 18 ga watan Disambar 2022. Ga jerin 'yan wasan da aka bayyana don buga babbar Gasar tamaula ta Duniya Australia Goalkeepers: Mathew Ryan (FC Copenhagen), Andrew Redmayne (Sydney FC), Danny Vukovic (Central Coast Mariners) Defenders: Aziz Behich (Dundee United), Milos Degenek (Columbus Crew), Thomas Deng (Aibirex Niigata), Joel King (Odense Boldklub), Nathaniel Atkinson (Hearts), Fran Karacic (Brescia), Harry Souttar (Stoke City), Kye Rowles (Hearts), Craig Goodwin (Adelaide United) Midfielders: Aaron Mooy (Celtic), Jackson Irvine (St Pauli), Ajdin Hrustic (Hellas Verona), Bailey Wright (Sunderland), Cameron Devlin (Hearts), Riley McGree (Middlesbrough), Keanu Baccus (St Mirren) Forwards: Awer Mabil (Cadiz), Mathew Leckie (Melbourne City), Martin Boyle (Hibernian), James Maclaren (Melbourne City), Jason Cummings (Central Coast Mariners), Mitchell Duke (Fagiano Okayama), Garang Kuol (Central Coast Mariners) Argentina Goalkeepers: Emiliano Martinez (Aston Villa), Franco Armani (River Plate) and Geronimo Rulli (Villarreal) Defenders: Gonzalo Montiel (Sevilla), Nahuel Molina (Atletico Madrid), German Pezzella (Real Betis), Cristian Romero (Tottenham Hotspur), Nicolas Otamendi (Benfica), Lisandro Martinez (Manchester United), Juan Foyth (Villarreal), Nicolas Tagliafico (Olympique Lyonnais), Marcos Acuna (Sevilla) Midfielders: Leandro Paredes (Juventus), Guido Rodriguez (Real Betis), Enzo Fernandez (Benfica), Rodrigo De Paul (Atletico Madrid), Exequiel Palacios (Bayer Leverkusen), Alejandro Gomez (Sevilla), Alexis Mac Allister (Brighton & Hove Albion) Forwards: Paulo Dybala (AS Roma), Lionel Messi (Paris St Germain), Angel Di Maria (Juventus), Nicolas Gonzalez (Fiorentina), Joaquin Correa (Inter Milan), Lautaro Martinez (Inter Milan), Julian Alvarez (Manchester City). Belgium Goalkeepers: Thibaut Courtois (Real Madrid), Simon Mignolet (Club Brugge), Koen Casteels (Wolfsburg) Defenders: Jan Vertonghen (Anderlecht), Toby Alderweireld (Antwerp), Leander Dendoncker (Aston Villa), Wout Faes (Leicester City), Arthur Theate (Rennes), Zeno Debast (Anderlecht), Yannick Carrasco (Atletico Madrid), Thomas Meunier (Borussia Dortmund), Timothy Castagne (Leicester City), Thorgan Hazard (Borussia Dortmund) Midfielders: Kevin de Bruyne (Manchester City), Youri Tielemans (Leicester City), Amadou Onana (Everton), Axel Witsel (Atletico Madrid), Hans Vanaken (Club Brugge) Forwards: Eden Hazard (Real Madrid), Charles De Ketelaere (AC Milan), Leandro Trossard (Brighton), Dries Mertens (Galatasaray), Jeremy Doku (Rennes), Romelu Lukaku (Inter Milan), Michy Batshuayi (Fenerbahce), Lois Openda (Lens) Brazil Goalkeepers: Alisson (Liverpool), Ederson (Manchester City), Weverton (Palmeiras) Defenders: Dani Alves (UNAM), Danilo (Juventus), Alex Sandro (Juventus), Alex Telles (Sevilla), Bremer (Juventus), Eder Militao (Real Madrid), Marquinhos (PSG), Thiago Silva (Chelsea) Midfielders: Casemiro (Manchester United), Everton Ribeiro (Flamengo), Bruno Guimaraes (Newcastle), Fabinho (Liverpool), Fred (Manchester United), Lucas Paqueta (West Ham) Forwards: Antony (Manchester United), Gabriel Jesus (Arsenal), Gabriel Martinelli (Arsenal), Neymar (PSG), Pedro (Flamengo), Raphinha (Barcelona), Rodrygo (Real Madrid), Richarlison (Tottenham Hotspur), Vinicius Jr (Real Madrid). Kamaru Goalkeepers: Devis Epassy (Abha Club), Simon Ngapandouetnbu (Marseille), Andre Onana (Inter Milan). Defenders: Jean-Charles Castelletto (Nantes), Enzo Ebosse (Udinese), Collins Fai (Al Tai), Olivier Mbaizo (Philadelphia Union), Nicolas Nkoulou (Aris Salonika), Tolo Nouhou (Seattle Sounders), Christopher Wooh (Stade Rennes). Midfielders: Martin Hongla (Verona), Pierre Kunde (Olympiakos), Olivier Ntcham (Swansea City), Gael Ondoua (Hannover 96), Samuel Oum Gouet (Mechelen), Andre-Frank Zambo Anguissa (Napoli). Forwards: Vincent Aboubakar (Al Nassr), Christian Bassogog (Shanghai Shenhua), Eric-Maxim Choupo Moting (Bayern Munich), Souaibou Marou (Coton Sport), Bryan Mbeumo (Brentford), Nicolas Moumi Ngamaleu (Young Boys Berne), Jerome Ngom (Colombe Dja), Georges-Kevin Nkoudou (Besiktas), Jean-Pierre Nsame (Young Boys Berne), Karl Toko Ekambi (Lyon). Canada Goalkeepers: Milan Borjan (Red Star Belgrade), James Pantemis (CF Montreal), Dayne St Clair (Minnesota United) Defenders: Sam Adekugbe (Hatayspor), Derek Cornelius (Vancouver Whitecaps - Panetolikos), Alistair Johnston (CF Montreal), Richie Laryea (Nottingham Forest), Kamal Miller (CF Montreal), Steven Vitoria (Chaves), Joel Waterman (CF Montreal) Midfielders: Stephen Eustaquio (FC Porto), Liam Fraser (Deinze), Atiba Hutchinson (Besiktas), Mark-Anthony Kaye (Toronto FC), Ismael Kone (CF Montreal), Jonathan Osorio (Toronto FC), Samuel Piette (CF Montreal), David Wotherspoon (St Johnstone) Forwards: Tajon Buchanan (Club Bruges), Lucas Cavallini (Vancouver Whitecaps), Jonathan David (Lille), Alphonso Davies (Bayern Munich), Junior Hoillett (Reading), Cyle Larin (Club Bruges), Liam Miller (FC Basel), Ike Ugbo (Troyes) Costa Rica Goalkeepers: Keylor Navas (Paris St-Germain), Esteban Alvarado (Herediano), Patrick Sequeira (CD Lugo) Defenders: Francisco Calvo (Konyaspor), Juan Pablo Vargas(Millonarios FC), Kendall Waston (Saprissa), Oscar Duarte (Al-Wehda), Daniel Chacon (Colorado Rapids), Keysher Fuller (Herediano), Carlos Martinez (San Carlos), Bryan Oviedo (Real Salt Lake), Ronald Matarrita (Cincinnati) Midfielders: Yeltsin Tejeda (Herediano), Celso Borges (Alajuelense), Youstin Salas (Saprissa), Roan Wilson (Grecia), Gerson Torres (Herediano), Douglas Lopez (Herediano) Jewisson Bennette (Sunderland), Alvaro Zamora (Saprissa), Anthony Hernandez (Puntarenas FC), Brandon Aguilera (Nottingham Forest), Bryan Ruiz (Alajuelense) Forwards: Joel Campbell (Leon), Anthony Contreras (Herediano) Johan Venegas (Alajuelense) Croatia Goalkeepers: Domink Livakovic (Dinamo Zagreb), Ivica Ivusic (NK Osijek), Ivo Grbic (Atletico Madrid) Defenders: Domagoj Vida (AEK Athens), Dejan Lovren (Zenit St Petersburg), Borna Barisic (Rangers), Josip Juranovic (Celtic), Josko Gvardiol (RB Leipzig), Borna Sosa (VfB Stuttgart), Josip Stanisic (Bayern Munich), Martin Erlic (Sassuolo), Josip Sutalo (Dinamo Zagreb) Midfielders: Luka Modric (Real Madrid), Mateo Kovacic (Chelsea), Marcelo Brozovic (Inter Milan), Mario Pasalic (Atalanta), Nikola Vlasic (Torino, on loan from West Ham), Lovro Majer (Rennes), Kristijan Jakic (Eintracht Frankfurt), Luka Sucic (RB Salzburg) Forwards: Ivan Perisic (Tottenham), Andrej Kramaric (1899 Hoffenheim), Bruno Petkovic (Dinamo Zagreb), Mislav Orsic (Dinamo Zagreb), Ante Budimir (Osasuna), Marko Livaja (Hajduk Split) Denmark Goalkeepers: Kasper Schmeichel (Nice), Oliver Christensen (Hertha Berlin), Frederik Ronnow (Union Berlin). Defenders: Alexander Bach (Benfica), Simon Kjaer (AC Milan), Joachim Andersen (Crystal Palace), Joakim Maehle (Atalanta), Andreas Christensen (Barcelona), Rasmus Kristensen (Leeds United), Jens Stryger Larsen (Trabzonspor), Victor Nelsson (Galatasaray), Daniel Wass (Brondby). Midfielders: Thomas Delaney (Sevilla), Mathias Jensen (Brentford), Christian Eriksen (Manchester United), Pierre-Emile Hojbjerg (Tottenham), Christian Norgaard (Brentford), Jesper Lindstrom (Eintracht Frankfurt), Mikkel Damsgaard (Brentford). Forwards: Andreas Skov Olsen (Club Bruges), Andreas Cornelius (Copenhagen), Martin Braithwaite (Espanyol), Kasper Dolberg (Sevilla), Jonas Wind (VfL Wolfsburg), Robert Forest (Hoffenheim), Yussuf Yurary Poulsen (RB Leipzig). Ecuador Goalkeepers: Moises Ramirez (Independiente del Valle), Alexander Dominguez (LDU Quito), Hernan Galindez (Aucas). Defenders: Piero Hincapie (Bayer Leverkusen), Robert Arboleda (Sao Paulo), Pervis Estupinan (Brighton), Angelo Preciado (Genk), Jackson Porozo (Troyes), Xavier Arreaga (Seattle Sounders), Diego Palacios (Los Angeles FC), Felix Torres (Santos Laguna), William Pacho (Royal Antwerp). Midfielders: Carlos Gruezo (Augsburg), Jose Cifuente (Los Angeles FC), Alan Franco (Talleres), Moises Caicedo (Brighton), Angel Mena (Club Leon), Jeremy Sarmiento (Brighton), Jhegson Mendez (Los Angeles FC), Ayrton Preciado (Santos Laguna), Gonzalo Plata (Real Valladolid), Romario Ibarra (Santos Laguna). Forwards: Djorkaeff Reasco (Newell's Old Boys), Kevin Rodriguez (Imbabura), Michael Estrada (Cruz Azul), Enner Valencia (Fenerbahce). Ingila Goalkeepers: Jordan Pickford (Everton), Nick Pope (Newcastle), Aaron Ramsdale (Arsenal) Defenders: Harry Maguire (Manchester United), Luke Shaw (Manchester United), Eric Dier (Tottenham), John Stones (Manchester City), Kyle Walker (Manchester City), Kieran Trippier (Newcastle), Conor Coady (Everton), Ben White (Arsenal), Trent Alexander-Arnold (Liverpool) Midfielders: Jude Bellingham (Borussia Dortmund), Mason Mount (Chelsea), Conor Gallagher (Chelsea), Declan Rice (West Ham), Jordan Henderson (Liverpool), Kalvin Phillips (Manchester City) Forwards: James Maddison (Leicester), Phil Foden (Manchester City), Jack Grealish (Manchester City), Harry Kane (Tottenham), Bukayo Saka (Arsenal), Raheem Sterling (Chelsea), Callum Wilson (Newcastle), Marcus Rashford (Manchester United) Faransa Goalkeepers: Alphonse Areola (West Ham), Hugo Lloris (Tottenham), Steve Mandanda (Rennes) Defenders: Axel Disasi (Monaco)*, Lucas Hernandez (Bayern Munich), Theo Hernandez (AC Milan), , Ibrahima Konate (Liverpool), Jules Kounde (Barcelona), Benjamin Pavard (Bayern Munich), William Saliba (Arsenal), Dayot Upamecano (Bayern Munich), Raphael Varane (Manchester United) Midfielders: Eduardo Camavinga (Real Madrid), Youssouf Fofana (Monaco), Matteo Guendouzi (Marseille), Adrien Rabiot (Juventus), Aurelien Tchouameni (Real Madrid), Jordan Veretout (Marseille) Forwards: Karim Benzema (Real Madrid), Kingsley Coman (Bayern Munich), Ousmane Dembele (Barcelona), Olivier Giroud (AC Milan), Antoine Griezmann (Atletico Madrid), Kylian Mbappe (Paris St-Germain), Christopher Nkunku (RB Leipzig). Marcus Thuram (Borussia Monchengladbach) Jamus Goalkeepers: Manuel Neuer (Bayern Munich), Marc-Andre ter Stegen (Barcelona), Kevin Trapp (Eintracht Frankfurt) Defenders: Armel Bella-Kotchap (Southampton), Matthias Ginter (SC Freiburg), Christian Gunter (SC Freiburg), Thilo Kehrer (West Ham), Lukas Klostermann (RB Leipzig), David Raum (RB Leipzig), Antonio Rudiger (Real Madrid), Nico Schlotterbeck (Borussia Dortmund), Niklas Sule (Borussia Dortmund) Midfielders: Julian Brandt (Borussia Dortmund), Leon Goretzka (Bayern Munich), Ilkay Gundogan (Manchester City), Jonas Hofmann (RB Leipzig), Joshua Kimmich (Bayern Munich), Jamal Musiala (Bayern Munich) Forwards: Karim Adeyemi (Borussia Dortmund), Niclas Fullkrug (Werder Bremen), Serge Gnabry (Bayern Munich), Mario Gotze (Eintracht Frankfurt), Kai Havertz (Chelsea), Youssoufa Moukoko (Borussia Dortmund), Thomas Muller (Bayern Munich), Leroy Sane (Bayern Munich) Ghana Goalkeepers: Lawrence Ati-Zigi (St Gallen), Danlad Ibrahim (Asante Kotoko), Abdul Manaf Nurudeen (Eupen). Defenders: Joseph Aidoo (Celta Vigo), Daniel Amartey (Leicester City), Alexander Djiku (Racing Strasbourg), Tariq Lamptey (Brighton & Hove Albion), Gideon Mensah (Auxerre), Denis Odoi (Club Bruges), Baba Rahman (Reading), Mohammed Salisu (Southampton), Alidu Seidu (Clermont). Midfielders: Mohammed Kudus (Ajax), Daniel-Kofi Kyereh (Freiburg), Elisha Owusu (Gent), Thomas Partey (Arsenal), Salis Abdul Samed (Lens). Forwards: Daniel Afriyie (Hearts of Oak), Andre Ayew (Al Sadd), Jordan Ayew (Crystal Palace), Osman Bukari (Red Star Belgrade), Issahaku Abdul Fatawu (Sporting Lisbon), Antoine Semenyo (Bristol City), Kamal Sowah (Club Bruges), Kamaldeen Sulemana (Rennes), Inaki Williams (Athletic Bilbao). Iran Goalkeepers: Alireza Beiranvand (Persepolis), Amir Abedzadeh (Ponferradina), Seyed Hossein Hosseini (Esteghlal), Payam Niazmand (Sepahan) Defenders: Ehsan Hajsafi (AEK Athens), Morteza Pouraliganji (Persepolis), Ramin Rezaeian (Sepahan), Milad Mohammadi (AEK Athens), Hossein Kanaanizadegan (Al Ahli), Shojae Khalilzadeh (Al Ahli), Sadegh Moharrami (Dinamo Zagreb), Rouzbeh Cheshmi (Esteghlal), Majid Hosseini (Kayserispor), Abolfazl Jalali (Esteghlal) Midfielders: Ahmad Noorollahi (Shabab Al Ahli), Saman Ghoddos (Brentford), Vahid Amiri (Persepolis), Saeid Ezatolahi (Vejle), Alireza Jahanbakhsh (Feyenoord), Mehdi Torabi (Persepolis), Ali Gholizadeh (Charleroi), Ali Karimi (Kayserispor) Forwards: Karim Ansarifard (Omonia Nicosia), Sardar Azmoun (Bayer Leverkusen), Mehdi Taremi (Porto) Japan Goalkeepers: Shuichi Gonda (Shimizu S-Pulse), Daniel Schmidt (Sint-Truiden), Eiji Kawashima (Strasbourg). Defenders: Miki Yamane (Kawasaki Frontale), Hiroki Sakai (Urawa Reds), Maya Yoshida (Schalke), Takehiro Tomiyasu (Arsenal), Shogo Taniguchi (Kawasaki Frontale), Ko Itakura (Borussia Monchengladbach), Hiroki Ito (Stuttgart), Yuto Nagatomo (FC Tokyo). Midfielders: Wataru Endo (Stuttgart), Hidemasa Morita (Sporting CP), Ao Tanaka (Fortuna Dusseldorf), Gaku Shibasaki (Leganes), Kaoru Mitoma (Brighton), Daichi Kamada (Eintracht Frankfurt), Ritsu Doan (Freiburg), Junya Ito (Reims), Takumi Minamino (Monaco), Takefusa Kubo (Real Sociedad), Yuki Soma (Nagoya Grampus). Forwards: Daizen Maeda (Celtic), Takuma Asano (Bochum), Ayase Ueda (Cercle Bruges). Mexico Goalkeepers: Guillermo Ochoa (Club America), Alfredo Talavera (Juarez), Rodolfo Cota (Leon) Defenders: Jorge Sanchez (Ajax), Kevin Alvarez (Pachuca), Nestor Araujo (Club America), Johan Vasquez (Cremonese), Hector Moreno (Monterrey), Cesar Montes (Monterrey), Gerardo Arteaga (Genk), Jesus Gallardo (Monterrey) Midfielders: Andres Guardado (Real Betis), Hector Herrera (Houston Dynamo), Charly Rodriguez (Cruz Azul), Erick Gutierrez (PSV Eindhoven), Luis Chavez (Pachuca), Edson Alvarez (Ajax), Orbelin Pineda (AEK Athens), Luis Romo (Monterrey) Forwards: Alexis Vega (Guadalajara), Hirving Lozano (Napoli), Raul Jimenez (Wolves), Roberto Alvarado (Guadalajara), Uriel Antuna (Cruz Azul), Henry Martin (Club America), Rogelio Funes Mori (Monterrey) Morocco Goalkeepers: Yassine Bounou (Sevilla), Munir El Kajoui (Al Wehda), Ahmed Reda Tagnaouti (Wydad Casablanca). Defenders: Nayef Aguerd (West Ham United), Yahia Attiat Allah (Wydad Casablanca), Badr Benoun (Qatar SC), Achraf Dari (Stade Brest), Jawad El Yamiq (Real Valladolid), Achraf Hakimi (Paris Saint-Germain), Noussair Mazraoui (Bayern Munich), Romain Saiss (Besiktas). Midfielders: Sofyan Amrabat (Fiorentina), Selim Amallah (Standard Liege), Bilal El Khannouss (Racing Genk), Yahya Jabrane (Wydad Casablanca), Azzedine Ounahi (Angers), Abdelhamid Sabiri (Sampdoria). Forwards: Zakaria Aboukhlal (Toulouse), Soufiane Boufal (Angers), Ilias Chair (Queens Park Rangers), Walid Cheddira (Bari), Youssef En-Nesyri (Sevilla), Abde Ezzalzouli (Osasuna), Abderrazak Hamdallah (Al Ittihad), Amine Harit (Olympique Marseille), Hakim Ziyech (Chelsea). Netherlands Goalkeepers: Justin Bijlow (Feyenoord), Andries Noppert (Heerenveen), Remko Pasveer (Ajax). Defenders: Nathan Ake (Manchester City), Daley Blind (Ajax), Virgil van Dijk (Liverpool), Denzel Dumfries (Inter Milan), Jeremie Frimpong (Bayer Leverkusen), Matthijs de Ligt (Bayern Munich), Tyrell Malacia (Manchester United), Jurrien Timber (Ajax), Stefan de Vrij (Inter Milan). Midfielders: Steven Berghuis (Ajax), Frenkie de Jong (Barcelona), Davy Klaassen (Ajax), Teun Koopmeiners (Atalanta), Marten de Roon (Atalanta), Xavi Simons (PSV Eindhoven), Kenneth Taylor (Ajax). Forwards: Steven Bergwijn (Ajax), Memphis Depay (Barcelona), Cody Gakpo (PSV), Vincent Janssen (Antwerp), Luuk de Jong (PSV), Noah Lang (Club Brugge), Wout Weghorst (Besiktas). Poland Goalkeepers: Bartlomiej Dragowski (Spezia), Lukasz Skorupski (Bologna), Wojciech Szczesny (Juventus). Defenders: Jan Bednarek (Aston Villa), Bartosz Bereszynski (Sampdoria), Matty Cash (Aston Villa), Kamil Glik (Benevento), Robert Gumny (FC Augsburg), Artur Jedrzejczyk (Legia Warsaw), Jakub Kiwior (Spezia), Mateusz Wieteska (Clermont), Nicola Zalewski (Roma). Midfielders: Krystian Bielik (Birmingham City), Przemyslaw Frankowski (Lens), Kamil Grosicki (Pogon Szczecin), Jakub Kaminski (VfL Wolfsburg), Grzegorz Krychowiak (Al-Shabab), Michal Skoras (Lech Poznan), Damian Szymanski (AEK Athens), Sebastian Szymanski (Feyenoord), Piotr Zielinski (Napoli), Szymon Zurkowski (Fiorentina). Forwards: Robert Lewandowski (Barcelona), Arkadiusz Milik (Juventus), Krzysztof Piatek (Salernitana), Karol Swiderski (Charlotte FC). Portugal Goalkeepers: Diogo Costa (Porto), Rui Patricio (AS Roma), Jose Sa (Wolverhampton Wanderers) Defenders: Joao Cancelo (Manchester City), Diogo Dalot (Manchester United), Ruben Dias (Manchester City), Raphael Guerreiro (Borussia Dortmund), Nuno Mendes (Paris St-Germain), Pepe (Porto), Danilo Pereira (Paris St-Germain), Antonio Silva (Benfica) Midfielders: William Carvalho (Real Betis), Bruno Fernandes (Manchester United), Joao Mario (Benfica), Ruben Neves (Wolverhampton Wanderers), Matheus Nunes (Wolverhampton Wanderers), Otavio (Porto), Joao Palhinha (Fulham), Bernardo Silva (Manchester City), Vitinha (Paris St-Germain) Forwards: Joao Felix (Atletico Madrid), Ricardo Horta (SC Braga), Rafael Leao (AC Milan), Goncalo Ramos (Benfica), Cristiano Ronaldo (Manchester United), Andre Silva (RB Leipzig) Qatar Goalkeepers: Saad Al-Sheeb (Al-Sadd), Meshaal Barsham (Al-Sadd), Yousef Hassan (Al-Gharafa) Defenders: Pedro Miguel (Al-Sadd), Musaab Khidir (Al-Sadd), Tarek Salman (Al-Sadd), Bassam Al-Rawi (Al-Duhail), Boualem Khoukhi (Al-Sadd), Abdelkarim Hassan (Al-Sadd), Ismaeel Mohammad (Al-Duhail), Homam Ahmed (Al-Gharafa), Jassem Gaber (Al-Arabi) Midfielders: Ali Asad (Al-Sadd), Assim Modibo (Al-Duhail), Mohammed Waad (Al-Sadd), Salem Al-Hajri (Al-Sadd), Moustafa Tarek (Al-Sadd), Karim Boudiaf (Al-Duhail), Abdelaziz Hatim (Al-Rayyan) Forwards: Naif Alhadhrami (Al-Rayyan), Ahmed Alaaeldin (Al-Gharafa), Hassan Al-Haydos (Al-Sadd), Khalid Muneer (Al-Wakrah), Akram Afif (Al-Sadd), Almoez Ali (Al-Duhail), Mohamed Muntari (Al-Duhail) Saudi Arabia Goalkeepers: Mohamed Al-Owais (Al-Hilal), Nawaf Al-Aqidi (Al-Nassr), Mohamed Al-Yami (Al-Ahly) Defenders: Yasser Al-Shahrani (Al-Hilal), Ali Al-Bulaihi (Al-Hilal), Abdulelah Al-Amri (Al-Nassr), Abdullah Madu (Al-Nassr), Hassan Tambakti (Al-Shabab), Sultan Al-Ghanam (Al-Nassr), Mohammed Al-Breik (Al-Hilal), Saud Abdulhamid (Al-Hilal) Midfielders: Salman Al-Faraj (Al-Hilal), Riyadh Sharahili (Abha), Ali Al-Hassan (Al-Nassr), Mohamed Kanno (Al-Hilal), Abdulelah Al-Malki (Al-Hilal), Sami Al-Najei (Al-Nassr), Abdullah Otayf (Al-Hilal), Nasser Al-Dawsari (Al-Hilal), Abdulrahman Al-Aboud (Ittihad), Salem Al-Dawsari (Al-Hilal), Hattan Bahebri (Al-Shabab) Forwards: Fahad Al-Muwallad (Al-Shabab), Haitham Asiri (Al-Ahly), Saleh Al-Shehri (Al-Hilal) Firas Al-Buraikan (Al-Fateh) Senegal Goalkeepers: Seny Dieng (Queens Park Rangers), Alfred Gomis (Rennes), Edouard Mendy (Chelsea). Defenders: Fode Ballo-Toure (AC Milan), Pape Abdou Cisse (Olympiakos), Abdou Diallo (RB Leipzig), Ismail Jakobs (Monaco), Kalidou Koulibaly (Chelsea), Formose Mendy (Amiens), Youssouf Sabaly (Real Betis). Midfielders: Pathe Ciss (Rayo Vallecano), Krepin Diatta (Monaco), Idrissa Gana Gueye (Everton), Pape Gueye (Marseille), Cheikhou Kouyate (Nottingham Forest), Mamadou Loum Ndiaye (Reading), Nampalys Mendy (Leicester City), Moustapha Name (Pafos), Pape Matar Sarr (Tottenham Hotspur). Forwards: Boulaye Dia (Salernitana), Famara Diedhiou (Alanyaspor), Bamba Dieng (Marseille), Nicolas Jackson (Villarreal), Sadio Mane (Bayern Munich), Iliman Ndiaye (Sheffield United), Ismaila Sarr (Watford). Serbia Goalkeepers: Marko Dmitrovic (Sevilla), Predrag Rajkovic (Mallorca), Vanja Milinkovic-Savic (Torino). Defenders: Stefan Mitrovic (Getafe), Nikola Milenkovic (Fiorentina), Strahinja Pavlovic (RB Salzburg), Milos Veljkovic (Werder Bremen), Filip Mladenovic (Legia Warsaw), Strahinja Erakovic (Red Star Belgrade), Srdjan Babic (Almeria). Midfielders: Nemanja Gudelj (Sevilla), Sergej Milinkovic-Savic (Lazio), Sasa Lukic (Torino), Marko Grujic (Porto), Filip Kostic (Juventus), Uros Racic (Braga), Nemanja Maksimovic (Getafe), Ivan Ilic (Hellas Verona), Andrija Zivkovic (PAOK), Darko Lazovic (Hellas Verona). Forwards: Dusan Tadic (Ajax), Aleksandar Mitrovic (Fulham), Dusan Vlahovic (Juventus), Filip Duricic (Sampdoria), Luka Jovic (Fiorentina), Nemanja Radonji (Torino). South Korea Goalkeepers: Kim Seung-gyu (Al Shabab), Jo Hyeon-woo (Ulsan Hyundai), Song Bum-keun (Jeonbuk Motors) Defenders: Kim Min-jae (Napoli), Kim Jin-su (Jeonbuk Motors), Hong Chul (Daegu FC), Kim Moon-hwan (Jeonbuk Motors), Yoon Jong-gyu (FC Seoul), Kim Young-gwon (Ulsan Hyundai), Kim Tae-hwan (Ulsan Hyundai), Kwon Kyung-won (Gamba Osaka), Cho Yu-min (Daejon Citizen) Midfielders: Jung Woo-young (Al Sadd), Na Sang-ho (FC Seoul), Paik Seung-ho (Jeonbuk Motors), Son Jun-ho (Shandong Taishan), Song Min-kyu (Jeonbuk Motors), Kwon Chang-hoon (Gimcheon Sangmu), Lee Jae-sung (Mainz), Hwang Hee-chan (Wolverhampton Wanderers), Hwang In-beom (Olympiacos), Jeong Woo-yeong (Freiburg), Lee Kang-in (Real Mallorca) Forwards: Hwang Ui-jo (Olympiacos), Cho Gue-sung (Jeonbuk Motors), Son Heung-min (Tottenham Hotspur) Sifaniya Goalkeepers: Unai Simon (Athletic Bilbao), Robert Sanchez (Brighton), David Raya (Brentford). Defenders: Cesar Azpilicueta (Chelsea), Dani Carvajal (Real Madrid), Eric Garcia (Barcelona), Hugo Guillamon (Valencia), Pau Torres (Villarreal), Aymeric Laporte (Manchester City), Jordi Alba (Barcelona), Jose Gaya (Valencia). Midfielders: Sergio Busquets (Barcelona), Rodri Hernandez (Manchester City), Gavi (Barcelona), Carlos Soler (Paris St-Germain), Marcos Llorente (Atletico Madrid), Pedri Gonzalez (Barcelona), Koke Resurreccion (Atletico Madrid). Forwards: Ferran Torres (Barcelona), Nico Williams (Athletic Bilbao), Yeremi Pino (Villarreal), Alvaro Morata (Atletico Madrid), Marco Asensio (Real Madrid), Pablo Sarabia (Paris St Germain), Dani Olmo (RB Leipzig), Ansu Fati (Barcelona) Tunisia Goalkeepers: Aymen Dahmen (Club Sportif Sfaxien), Mouez Hassan (Club Africain), Bechir Ben Said (US Monastir), Aymen Mathlouthi (Etoile du Sahel). Defenders: Ali Abdi (Caen), Mohamed Drager (FC Luzern), Ali Maaloul (Al Ahly), Wajdi Kechrida (Atromitos), Nader Ghandri (Club Africain), Yassine Meriah (Esperance), Bilel Ifa (Kuwait FC), Dylan Bronn (Salernitana), Montassar Talbi (Lorient). Midfielders: Ellyes Skhiri (FC Cologne), Ghaylen Chaalali (Esperance), Aissa Laidouni (Ferencvaros), Mohamed Ali Ben Romdhane (Esperance), Ferjani Sassi (Al-Duhail), Hannibal Mejbri (Birmingham City). Forwards: Youssef Msakni (Al Arabi SC), Seifeddine Jaziri (Zamalek), Naim Sliti (Ettifaq), Issam Jebali (Odense), Taha Yassine Khenissi (Kuwait SC), Anis Ben Slimane (Brondby), Wahbi Khazri (Montpellier). Amurka Goalkeepers: Ethan Horvath (Luton), Sean Johnson (New York City), Matt Turner (Arsenal) Defenders: Cameron Carter-Vickers (Celtic), Sergino Dest (AC Milan), Aaron Long (New York Red Bulls), Shaq Moore (Nashville), Tim Ream (Fulham), Antonee Robinson (Fulham), Joe Scally (Borussia Monchengladbach), DeAndre Yedlin (Miami), Walker Zimmerman (Nashville) Midfielders: Brenden Aaronson (Leeds), Kellyn Acosta (Los Angeles), Tyler Adams (Leeds), Luca de la Torre (Celta Vigo), Weston McKennie (Juventus), Yunus Musah (Valencia), Cristian Roldan (Seattle) Forwards: Jesus Ferreira (Dallas), Jordan Morris (Seattle), Christian Pulisic (Chelsea), Gio Reyna (Borussia Dortmund), Josh Sargent (Norwich), Tim Weah (Lille), Haji Wright (Antalyspor) Uruguay Goalkeepers: Fernando Muslera (Galatasaray), Sergio Rochet (Nacional), Sebastian Sosa (Independiente) Defenders: Jose Maria Gimenez (Atletico Madrid), Sebastian Coates (Sporting CP), Diego Godin (Velez Sarsfield), Martin Caceres (LA Galaxy), Ronald Araujo (Barcelona), Guillermo Varela (Flamengo), Jose Luis Rodriguez (Nacional), Mathias Olivera (Napoli), Matias Vina (Roma) Midfielders: Lucas Torreira (Galatasaray), Manuel Ugarte (Sporting CP), Matias Vecino (Lazio), Rodrigo Bentancur (Tottenham Hotspur), Federico Valverde (Real Madrid), Facundo Pellistri (Manchester United), Nicolas De La Cruz (River Plate) Forwards: Agustin Canobbio (Athletico Paranaense), Facundo Torres (Orlando City), Giorgian De Arrascaeta (Flamengo), Maxi Gomez (Trabzonspor), Luis Suarez (Nacional), Edinson Cavani (Valencia), Darwin Nunez (Liverpool) Wales Goalkeepers: Wayne Hennessey (Nottingham Forest), Danny Ward (Leicester City), Adam Davies (Sheffield United). Defenders: Neco Williams (Nottingham Forest), Ben Davies (Tottenham Hotspur), Ben Cabango (Swansea City), Joe Rodon (Rennes, on loan from Tottenham Hotspur), Chris Mepham (Bournemouth), Ethan Ampadu (Spezia, on loan from Chelsea), Chris Gunter (AFC Wimbledon), Connor Roberts (Burnley), Tom Lockyer (Luton Town). Midfielders: Aaron Ramsey (Nice), Joe Allen (Swansea City), Harry Wilson (Fulham), Joe Morrell (Portsmouth), Dylan Levitt (Dundee United), Rubin Colwill (Cardiff City), Jonny Williams (Swindon Town), Matthew Smith (Milton Keynes Dons), Sorba Thomas (Huddersfield Town). Forwards: Gareth Bale (Los Angeles FC), Dan James (Fulham, on loan from Leeds United), Kieffer Moore (Bournemouth), Mark Harris (Cardiff City), Brennan Johnson (Nottingham Forest). https://www.bbc.com/hausa/articles/cp47840dv8xo +sports Barcelona za ta kara da Real Madrid da Juventus a Amurka Barcelona za ta buga wasannin sada zumunta hudu a Amurka, domin shirin tunkarar kakar badi ta tamaula. Cikin karawar da za ta yi har da El Clasico, wato da Real Marid ranar 23 ga watan Yuli a Las Vegas, kwana uku tsakani ta fafata da Juventus a Dallas. Kungiyar Camp Nou za ta fara wasan sada zumunta da Inter Miami ranar 19 ga watan Yuli, wasa na hudu kuwa za ta yi ne da New York Red Bulls ranar 30 ga watan Yuli. Wasan da Barcelona za ta yi da Real Madrid, shi ne El Clasico na biyu da za su kara a Amurka. Sun fara karawa cikin Yulin 2017 a filin wasa na Hard Rock a gaban 'yan kallo 54,000. Wannan karon za su fafata a filin wasa Allegiant, mai cin 'yan kallo 65,000, kuma karon farko da Barca za ta yi wasa a Las Vegas. Idan Barca ta buga da Real Madrid, sai ta fuskanci Juventus ranar 26 ga watan Yuli a Cotton Bowl a Dallas, filin da ke daukar 'yan kallo 92,100. Kungiyar da Xavi Hernandez ke jan ragama za ta fara atisaye ranar 4 ga watan Yuli, likitoci su gwada koshin lafiyar 'yan wasan da kungiyar za ta yi amfani da su a badi - daga nan 'yan kwanaki ta ziyarci Amurka. Barcelona za ta buga Champions League a kaka mai zuwa, bayan da ta yi ta biyu a La Liga da aka kammala ta bana. https://www.bbc.com/hausa/wasanni-61776688 +sports Thomas Muller aka zaba fitatcen dan kwallon Bayern a 2021/22 Thomas Muller shi ne aka zaba a matakin dan wasan Bayern Munich da yafi taka rawar gani a kakar 2021/22 da aka karkare. Cikin watannin da aka fafata a kakar da aka karkare ya nuna mahimmacinsa a fagen tamaula a kungiyar da kwarewar da yake da ita. Dan wasan ya bayar da kwallo 22 aka zura a raga a dukkan fafatawa, bayan da ya ci 13 a kungiyar da ta lashe Bundesliga a bana na 10 a jere na 32 jumulla. Muller, mai shekara 32 ya yi nasara a kan Musiala da kuma Lewandowski a jerin 'yan wasan kungiyar da suka taka rawar gani a kakar da ta wuce. Robert Lewandowski shi ne ya lashe kyautar karo biyu baya a jere a kungiyar. Muller ya taka rawar gani a kakar 2021/22, wanda a cikin watan Mayu ya dauki kofin Bundesliga na 11, wanda ke kan gaba a yawan daukar kofin a tarihin kungiyar. Haka kuma ya buga wasan da Bayern ta casa VFB Stuttgart 5-0 a watan Disamba a gasar Bundesliga karawa ta 292 da ya yi kenan. Muller ya bayar da kwallo 18 aka zura a raga a Bundesliga, shi ne kan gaba a wannan kwazon. Haka kuma kwallo 22 da ya bayar aka zura a raga a dukkan wasannin kakar da ta wuce, shi ne kan gaba a manyan gasar Turai biyar, Kylian Mbappe ne na biyu mai 21. Tuni dan wasan ya saka hannu kan kwantiragin da zai kare a 2024 a watan Mayu a Bayern Munich, hakan zai ba shi damar kara yin wasu bajintar. https://www.bbc.com/hausa/articles/czqlnqe4pyjo +sports United ta cire Ronaldo daga cikin 'yan wasan da za su kara da Chelsea "Cristiano Ronaldo ba zai buga wasan da Manchester United za ta yi da Chelsea ba a ranar Asabar. Dan wasan gaban Portugal ya bar Old TRafford kafin kallama wasan da ta yi da Tottenham ta samu nasara da ci 2-0 a ranar Laraba - saboda an barshi a benci ba a sa shi a wasan ba. ""Sauran 'yan wasan kungiyar za su ci gaba da shirye-shirye na wasan gaba,"" kamar yadda wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta bayyana. United ta ce dan wasan mai shekara 37 na da matukar muhimmanci a tawagar, sai dai wannan mataki ne da ya shafi kwamitin ladabtarwa. Wasan da ba zai buga ba a Stamford Bridge na daya daga cikin manyan wasanni, yayin da United ke bin Chelsea da ke matsayi na hudu a baya da maki daya. Kafafen yada labarai da dama na rawaito cewa dan wasan yaki shiga canjin da za a sa shi a wasan Spurs saboda lokaci ya kure. A daidai minti na 89 Ronaldo ya fice daga filin wasan, yayin da United ta yi canji uku cikin biyar da take da shi. Kai tsaye ya shige dakin sauya kaya gabanin ficewa daga filin wasan baki daya. Bayan kammala wasan Erik ten Hag ya ce ""zai ji da lamarin"" a ranar Talata. A ranar Lahadi da United ta buga wasa da Newcastle, sai da Ronaldo ya nuna rashin jin dadinsa saboda an yi canjin shi." https://www.bbc.com/hausa/articles/cv2p6g7xlr8o +sports Lewandowski ya ci kwallo na 601 ranar Alhamis Robert Lewandowski ya ci kwallo na 600 da na 601 a wasan da Barcelona ta doke Villareal da ci 3-0 a gasar La Liga ranar Alhamis. Lewandoski ne ya ci na farko, bayan da Jordi Alba ya bugo tamaula, sannan ya kar na biyu da ya samu kwallo ta hannun Gavi, Ansu Fati ne ya zura na uku. Dan kwallon tawagar Poland mai shekara 34, ya zama na uku tun daga shekarar 2000 da ya ci kwallo sama da 600, bayan Lionel Messi da Cristiano Ronaldo. Kwallo biyun da ya ci a Nou Camp ranar Alhamis, sun cika 16 jumula a raga wasa 14 da ya yi a dukkan fafatawa, tun bayan da ya koma Barcelona a bana. Dan wasan ya koma Nou Camp daga Bayern Munich kan £42.6m a kakar nan . A kungiyar Bayern, Lewandowski ya ci 344 a wasa 375 a kungiyar Jamus, ya kuma zura 103 a wasa 186 a Borussia Dortmund. Kafin ya koma Jamus da taka leda ya ci 21 a Znicz Pruszkow da 41 a Lech Poznan kungiyoyi Poland da 76 da ya zura a raga a karawa 134 a tawagar Poland. https://www.bbc.com/hausa/articles/cg3822gpvj4o +sports Yadda 'yan Ajantina suka yi murnar cin gasar kofin duniya a kasarsu Dubban ƴan Ajantina ne suka kwarara a kan tituna a kasar don murnar nasarar cin kofin duniya. Nasarar da suka yi a kan Faransa ita ce ta uku tun fara gasar cin kofin duniya. Kuma rabonsu da yin nasara tun shekarar 1986. https://www.bbc.com/hausa/articles/c72623l8k17o +sports Mino Raiola: Wakilin Paul Pogba Mino Raiola ya musanta rahotannin mutuwarsa "Da safiyar ranar Alhamis jaridu a faɗin duniya suka fara ruwaito labarin rasuwar shahararren wakilin manyan 'yan wasan ƙwallon ƙafa a duniya, Mino Raiola. Sai dai hamshaƙin da kansa ya musanta batun daga gadon asibitin da yake kwance, inda ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa ""da alama na farfaɗo"". Ƙungiyoyi irin su Real Madrid har sun wallafa ta'aziyyarsu kan mutuwar wakilin, wanda ya yi aiki tare da wasu 'yan wasan ƙungiyar a tsawon shekaru. ""Sun ji kunya sau biyu cikin wata huɗu da suke kashe ni. Da alama na sake farfaɗowa,"" in ji Mista Raiola. Riola wanda ɗan ƙasar Italiya ne, shi ne wakilin ɗan wasan tsakiyar Manchester United Paul Pogba da tauraron ɗan wasa Zlatan Ibrahimovic da kuma matashi mai tashe Erling Haaland na ƙungiyar Dortmund. Rahotanni sun bayyana cewa Mista Riola na fama da lalura a huhunsa. Su ma danginsa sun musanta mutuwar tasa amma sun ce ""yana cikin mummunan yanayi"". Mujallar Forbes ta ƙiyasta dukiyar Riola ta kai fan miliyan 68. Shi ne ya jagoranci ƙulla yarjejeniyar Paul Pogba da Man United a karo na biyu kan fan miliyan 89 a 2016." https://www.bbc.com/hausa/wasanni-61259748 +sports 'Na yi sa'a ban mutu ba' in ji dan wasan Arsenal da aka caka wa wuka "Dan wasan bayan Arsenal Pablo Mari ya ce ya yi ""sa'a"" da za a yi masa tiyata a bayan caka masa bukar da aka yi a wani katafaren kantin zamani a kusa da Milan. Kafafen yada labarai na kasar sun ce an kashe wani matashi mai karbar kudi mai shekara 30, kuma wasu mutane na daban su biyar sun ji muggan raunuka, a harin da wani mutum ya kai a garin Assago. Tuni 'yan sanda suka kama mutumin da ake zargi da harin mai shekara 46, wanda aka ce yana da tabin hankali. ""Na yi matukar sa'a a yau, saboda a gabana mutum ya mutu,"" in ji Mari da ke zaman aro a kungiyar Monza. Jaridar Gazzetta ta wasanni ta rawaito cewa dan wasan bayan Sifaniyan Mari mai shekara 29 yana zagayawa ne da matarsa da kuma dansa lokacin da aka caka masa wukar a bayansa. ""Ba wani gwarzo ba ne ni. Ban yi wani abu ba na musamman,""kamar yadda wani mutum dan shekara 51 ya bayyana wa jaridar. Wakilin Mari Arturo Canales ya ce raunin da aka ji masa ba wani mai tayar da hankali ba ne, kamar yadda ya shaida wa BBC a ranar Alhamis. Ya ce dan wasan na cikin hayyacinsa kuma babu wata gaba mai muhimmanci a jikinsa da ta jikkata. Za a yi wa Mari tiyata a ranar Juma'a saboda raunin da aka ji masa." https://www.bbc.com/hausa/articles/ckk2x42w7zgo +sports Mane ya je Jamus domin kammala komawa Bayern Sadio Mane ya je birnin Munich ranar Talata, don kammala komawa Bayern Munich da taka leda daga Liverpol. Sky ta saka wani faifan bidiyon dan kwallon a wani jirgi na kawa da ya isa birnin a shirin auna koshin lafiyar dan wasan tawagar Senegal. Bayan auna koshin lafiyar dan wasan zai saka hannu kan yarjejeniyar kaka uku, inda mujallar Kicker sports ta ce za a gabatar da dan kwallon a ranar Laraba. Mane zai koma buga Bundesliga kan yuro miliyan 32, ana cewa kudin zai kai yuro miliyan 41 idan aka hada da tsarabe-tsarabe. Dan kwallon tawagar Senegal zai karfafa wasannin Bayern Munich, bayan da ake cewar ba a san makomar Serge Gnabry, sannan Robert Lewandowski na san zuwa Barcelona a kakar da za a fara a badi. Sau biyu Liverpool tana yin watsi da tayin da Bayern ta yi mata kafin ta amince ta sayar da dan wasan mai shekara 30, wanda kwantaraginsa da Reds za ta kare a bazara. Liverpool ta saye shi daga Southampton a shekarar 2016 a kan £31m da karin £2.5m na tsarabe-tsarabe. Tun daga wancan lokacin, Mane ya zura kwallaye 90 a Gasar Firimiya a wasannin da ya yi wa kungiyar sannan ya kammala kakar wasan da ta wuce da cin kwallaye 23 a gasa daban-daban da ya yi wa Liverpool. https://www.bbc.com/hausa/articles/cqq5226qx4qo +sports Watakila Maguire ya buga wa United wasa da FC Sheriff Harry Maguire ya koma atisaye, watakila ya buga wa Manchester United gasar Europa League da za ta fafata da Sheriff Tiraspol ranar Alhamis. Mai tsaron bayan tawagar Ingila, mai shekara 29 baya buga wasanni tun bayan raunin da ya ji a lokacin da ya yi wa kasarsa tamaula a cikin watan Satumba. Takwaransa Raphael Varane zai yi jinya zuwa bayan gasar kofin duniya, bayan da ya ji rauni a wasan Premier League da United ta tashi 1-1 da Chelsea a Stamford Bridge a karshen mako. Haka shima Donny van de Beek da Aaron Wan-Bissaka sun murmure sun kuma koma atisaye. Kocin United, Erik ten Hag ya sanar cewar Cristiano Ronaldo ya koma cikin sauran ‘yan wasan kungiyar, bayan da aka ajiye shi a karawa da Chelsea. Kyaftin din tawagar Portugal ya ki ya shiga fili ya canji dan wasa, bayan da aka umarce shi a lokacin da yake zaman benci a fafatawa da Tottenham. Rabon da Maguire ya yi wa United tamaula tun wasan da kungiyar ta je ta ci FC Sheriff 2-0 ranar 15 ga watan Satumba. Magoya bayan tawagar Ingila da na United sun yi wa Maguire ihu a bana, shi ne ya tafka kuskuren da aka ci Ingila kwallo biyu a wasan da ta tashi 3-3 da Jamus ranar 26 ga watan Satumba. https://www.bbc.com/hausa/articles/c3g871lr853o +sports Bayern Munich vs Villareal: Wasu batutuwa da ya kamat ku sani kan fafatawar Bayern Munich za ta karbi bakuncin Villareal a wasa na biyu a quarter finals a Champions League da za su fafata ranar Talata. A wasan farko da suka kece raini a Sifaniya, Villareal ce ta yi nassara da ci 1-0, kuma Arnaut Danjuma ya ci mata kwallon a minti na tara da fara wasan. To sai dai kuma da wasu batutawa biyar da ya kamat ku sani kafin wasan da za su fafata ranar Talata. 1. Bayern za ta iya cin wasa na 159 a Champions League Idan har Bayern Munich ta doke Villarael a wasan da za su kara ranar Talata, nasara ta 159 kenan a Champions League, za kuma ta hau kan Barcelona, amma ta biyu bayan Real Madrid da ke kan gaba mai nasara 172 a tarihi. 2. Bayern ta sha kai wa zagayen gaba, bayan an doke ta a wasan farko Sau uku ana cin Bayern Munich a wasan farko a waje, amma ta kai zagayen gaba idan an zo gidanta - shine wanda ta doke Porto a 2014/15 a zangon quarter finals da wanda ta yi wa Basel a 2011/12 a zagaye na biyu da wanda ta yi nasara a kan Real Madrid a 2006/07 a zagayen kungiyoyi 16. A gasar Europa Cup kuwa, sau hudu kungiyar Jamus kan kai wasan gaba, bayan da aka doke ta a karawar farko da ta yi a waje. 3, Bayern tana da karfi a gida a Champions League Bayern ta yi nasara a wasa 12 daga 13 da ta kece raini a baya a gasar ta Zakarun Turai, in banda wanda Paris St German ta doke ta 3-2 a Quarter finals a kakar bara. A kakar nan kuwa kungiyar Jamus ta ci dukkan wasa hudun da ta yi a Allianz Arena, kuma da kwallaye uku kan ci. 4. Bayern ta dade rabon da ta kasa cin wasa a karawa biyu a jere Sama da kaka uku kawo yanzu rabon da Bayern Munich ta kasa yin nasara a wasa biyu a jere - shine a kakar 2018/19, lokacin da ta yi canjaras biyu da rashin nasara a hannun Ajax da kuma sau biyu da Liverpool. Rabon da a doke kungiyar Jamus karo biyu a jere tun Afirilun 2017 a quarter finals a hannun Real Madrid. 5. Lewandowski kan ci kwallaye da yawa a Allianz Arena Robert Lewandowski kan ci kwallaye a Allianz Arena a gasar Champions League, wanda takwas daga 12 da ya ci a gasar bana a gida ya yi wannan bajintar a karawa hudu. https://www.bbc.com/hausa/wasanni-61059679 +sports Makomar Osimhen, Bellingham, Endrick, Gomez, Zaha a kasuwar yan kwallo Chelsea na duba yiwuwar sayen dan wasa a bazara mai zuwa inda dan wasan Napoli kuma mai bugawa Najeriya, Victor Osimhen mai shekara 23 ya zama zabi na farko yayin da suke duba wasu damarmakin.  (90 Min) Dan wasan tsakiya na Borussia Dortmund Jude Bellingham, 19, ya zama dan wasan da Chelsea take hange yayin da mai bugawa Ingila kuma dan wasan West Ham Declan Rice mai shekara 23, shi ma hankali ke kansa. (Evening Standard) Arsenal za ta fafata da Barcelona da Real Madrid wajen kulla yarjejeniya da dan wasa Endrick mai shekara 16 wanda aka yi wa lakabi da magajin Pele. (FourFourTwo) Kocin Manchester United Erik ten Hag yana jan kafa wajen yanke shawara kan makomar mai tsaron ragar Spaniya David de Gea mai shekara 31 da dan wasan Ingila Marcus Rashford dan shekara 24. (Guardian) Dan wasan PSV Eindhoven Cody Gakpo, 23, ya ce yunkurin komawa Manchester United bai tabbata ba inda Leeds United da Southampton suma ke sha'awar sayen dan wasan mai bugawa Netherlands kafin ya yanke shawarar zama a kungiyarsa.  (Times - subscription required) Barcelona na bibiyar halin da dan wasan Manchester United  mai shekara 23, Diogo Dalot, da kwantiraginsa zai kare a bazara mai zuwa amma akwai damar a tsawaita ta zuwa shekara daya. (Mundo Deportivo - in Spanish) Daraktan kwallon kafa na Manchester United John Murtough ya soke duk wani fata na cinikin 'yan kwallo a Janairu in da ya jaddada cewa kungiyar na dakon kasuwar musayar 'yan kwallo ta bazara mai zuwa. (Telegraph - subscription required) Wakilin Dan wasan Portugal Ruben Neves ya yi wa dan wasan tsakiya na Wolves tayin zuwa Barcelona da ke yin nazari kan dan shekara 25 din. (Mundo Deportivo - in Spanish) Dan wasan Wolves Adama Traore, 26, ya ce yana fatan wata rana zai koma buga kwallo a Spaniya.  (AS - in Spanish) Kocin Kungiyar kwallon kafa ta Ingila Gareth Southgate zai bibiyi dan wasan Liverpool Joe Gomez mai shekara 25 kafin ya fitar da jerin tawagar da za su buga gasar cin kofin duniya a watan Nuwamba. (Times - subscription required) Dan wasan Manchester United Michael Carrick, 41, a shirye yake a nada shi a matsayin sabon kocin Middlesbrough bayan da ya amince da sharuddan kungiyar.  (Mail) Kocin Crystal Palace Patrick Vieira ya ce kungiyar na cikin tattaunawa kan tsawaita kwantiragin dan wasan gaba na Ivory Coast Wilfred Zaha mai shekara 29 duk da alakarsa da Arsenal da Chelsea inda kuma kwantiraginsa ke shirin karewa a bazara mai zuwa. (Metro) https://www.bbc.com/hausa/articles/cyr0neg0d8ko +sports An tsayar da ranar wasan Barcelona da Sevilla a La Liga Mahukuntan La Liga sun bayyana ranar da za a kara tsakanin Barcelona da Sevilla a babbar gasar tamaula ta Sifaniya. Barcelona za ta karbi bakuncin Sevilla ranar Lahadi 3 ga watan Afirilu a Camp Nou, wasan mako na 30 kenan a gasar La Liga. Wasan zai yi zafi zai kuma ja hankalin masu bibiyar tamaula, bayan da Barcelona ke mataki na uku da maki 51 da kwantan wasa daya. Ita kuwa Sevilla wadda ta yi wasa 28 a gasar La Liga ta bana tana mataki na biyu a kan teburi mai maki 56. A wasan farko da suka kara a tsakaninsu a gidan Sevilla a filin wasa na Ramón Sánchez Pizjuán sun tashi 1-1 ne. Barcelona ta ci kwallo ta hannun Araujo, ita kuwa Sevilla ta zura kwallo a raga ta hannun Papu Gómez a wasan. Real Madrid ce ta daya a kan teburin babbar gasar tamaula ta Sifaniya ta bana da maki 66 da tazarar maki 10 tsakaninta da Sevilla, kuma saura wasa 10 a karkare kakar bana. https://www.bbc.com/hausa/wasanni-60740531 +sports Karim Benzema ya yi kan-kan-kan da Raul a yawan cin kwallaye Karim Benzema ya yi kan-kan-kan da Raul a mataki na biyu a yawan ci wa Real Madrid kwallaye a tarihi. Benzema ya ci kwallo daga daga 6-0 da Real Madrid ta caskara Levante a wasan mako na 36 a gasar La Liga da suka fafata ranar Alhamis. Kawo yanzu dan kasar Faransa ya ci wa Real kwallo 323, iri daya da wanda Raul ya zura a raga a kungiyar tsakanin 1994 zuwa 2010. Cristiano Ronaldo ne kan gaba a yawan ci wa Real Madrid kwallaye a tarihi mai 451. Benzema ya zura 44 a raga a kakar bana, ita ce wadda ya ci kwallaye da yawa a tarihin sana'arsa ta tamauula. Ya fara ci wa Real kwallo a wasa na uku da ya yi wa kungiyar a fafatawa da Xerez a gasar La Liga a kakar 2009-10 tun daga nan ya dora. Kawo yanzu ya lashe kofi 21 a Real Madrid da suka hada da Champions Leagues hudu da Club World Cups hudu da European Super Cups uku da La Liga hudu da Copas del Rey biyu da kuma and 4 Spanish Super Cups hudu. Cikin kwallo 323 ya zura a gasa shida sun hada da 219 a LaLiga, 74 a Champions League, 21 a Copa del Rey, 3 a Club World Cup da kuma 5 a Spanish Super Cup. Sauran sun hada da daya a European Super Cup. Kuma kungiyoyin da yafi zura musu kwallaye a raga sun hada da Athletic (18), Valencia (15) da kuma Granada (14). https://www.bbc.com/hausa/wasanni-61432408 +sports Ibrahimovic ya saka hannu kan yarjejeniyar kaka daya a AC Milan Zlatan Ibrahimovic ya saka hannu kan kwantiragin kaka daya, domin ci gaba da taka leda a AC Milan. Dan kwallon tawagar Sweden, wanda zai cika shekara 41 da haihuwa cikin watan Oktoba, ya ci kwallo takwas a bara a kakar da Milan ta lashe Serie A. Likitoci sun yi wa dan wasan tiyata a gwiwar kafa a watan Mayu, wanda ake sa ran zai yi jinyar wata takwas. Tsohon dan kwallon Manchester United da kuma Paris St-Germain ya koma Milan a 2020, inda ya taimaka mata lashe Serie A, karon farko tun bayan shekara 11. Ibrahimovic yana kungiyar a lokacin da Milan ta dauki Scudetto, bayan da ya buga mata wasannin aro daga Barcelona da cin kwallo 14 a lik a wasa 29 a kakar 2021. Daga nan kungiyar ta dauke shi, daga baya ya koma Paris St-Germain a karshen kakar 2011-12. Wanda ke kan gaba a yawan ci wa Sweden kwallaye mai 62 a raga a wasa 121 ba shi ne kadai ba mai shekara 41 da ke buga tamaula a manyan kungiyoyin Turai ba. Kyaftin din Real Betis, Joaquin, wanda ya cika sherkara 41 da kwana 21 a watan Yuli, ya saka hannu kan yarjejeniyar kaka daya a kungiyar da ke buga La Liga. https://www.bbc.com/hausa/articles/c3g1klwd21do +sports Tambayoyi da amsoshi kan Brazil a Gasar Kofin Duniya a Qatar Brazil na fatan lashe Kofin Duniya na shida jumulla a wasannin da za a gudanar a Qatar daga 20 ga watan Nuwamba zuwa 18 ga watan Disambar 2022. Ga wasu tambayoyi da amsoshi da ya kamata ku sani kan Brazil 'Yan wasa nawa aka amince Brazil ta je da su Qatar? A watan Yuni aka yanke shawarar kowacce tawaga ta je da 'yan kwallo 26 maimakon 23 a Gasar Kofin Duniya, bayan da cutar korona ta kai koma baya a fannin tamaula. Lokacin wasu kan killace kansu idan sun kamu da annobar, sannan ga yawan rauni, bayan da 'yan kwallo ke buga wasanni da yawa. Wadanne 'yan wasa ne za su wakilci Brazil a Qatar? Ranar 7 ga watan Nuwamba Brazil ta bayyana 'yan wasa 26 da za su buga mata Gasar Cin Kofin Duniya da za a yi a Qatar. Masu tsaron raga: Alisson (Liverpool), Ederson (Manchester City), Weverton (Palmeiras) Brazil kan zaba tsakanin Alisson da Ederson, amma Alisson ne kan gaba, wanda shi ne ya tsare mata raga a wasannin neman gurbin shiga gasar kofin duniyar. Masu tsaron baya: Bremer, Alex Sandro (both Juventus), Eder Militao (Real Madrid) Marquinhos (Paris St Germain), Thiago Silva (Chelsea), Danilo (Juventus), Daniel Alves (Pumas), Alex Telles (Sevilla) Zakakuri Thiago Silver da Marquinhos suna daga cikin wadanda za su tsare bayan Brazil, an yi mamaki da aka tafi da Dani Alves, mai shekara 39. Masu buga mata tsakiya: Bruno Guimaraes (Newcastle United), Casemiro, Fred (both Manchester United), Everton Ribeiro (Flamengo), Fabinho (Liverpool), Lucas Paqueta (West Ham United) Guimaraes ya shiga tawagar kan rawar da yake takawa a Newcastle United, shi kuwa mai shekara 33 da ke taka wa a Everton, Ribeiro zai je Gasar Kofin Duniya a karon farko. Masu ci mata kwallaye: Antony (Manchester United), Gabriel Jesus, Gabriel Martinelli (both Arsenal), Neymar Jr (Paris St Germain), Pedro (Flamengo), Raphinha (Barcelona), Richarlison (Tottenham Hotspur), Rodrygo, Vinicius Jr (both Real Madrid) 'Yan wasa tara aka gayyata a wannan gurbin kuma matasa masu taka leda a Turai, in banda mai wasa a Flamengo, Pedro, wanda ya taimakawa kungiyarsa ta lashe Copa Libertadores da cin kwallo 12. Wasu karin bayanai da ya kamata ku sani Matakin Brazil a jadawalin FIFA: Ta daya daga Agustan 2022 Matakin Brazil a nahiyarta ta CONMEBOL: Ta daya Kofin duniya da ta dauka: 5 Ta halarci Gasar Cin Kofin Duniya 21 na karshen nan a Rasha a 2018 Yadda ta samu gurbin zuwa Qatar: Ta ci wasa 14 da canjaras uku ta daya a CONMEBOL Kociyanta: Tite (Brazil) tun daga Yunin 2016 Fitattun ‘yan wasa: Neymar (Paris Saint-Germain / France), Marquinhos (Paris Saint-Germain / France), Vinicius Jr. (Real Madrid / Spain) Wadanne fitattun 'yan wasa ne da ba su a Brazil a Qatar? Dan wasan Liverpool, Roberto Firmino ba zai je Gasar Kofin Duniya ba, duk da cewar yana gaban wadanda aka gayyata a gurbin da yake buga wa a yawan cin kwallaye da bayar wa a zura a raga a bana a Premier League. Mai tsaron bayan Arsenal, Gabriel Magalhaes bai samu shiga tawagar ba duk da cewar yana taimakawa Arsenal, wadda yanzu ke kan teburin Premier League. Dan wasan Aston Villa ba zai je Gasar ba, sakamakon jinya da yake yi. Wadanne kasashe Brazil za ta kara da su a Qatar a wasan rukuni? Brazil tana rukuni na bakwai da ya hada da Serbia da Switzerland da kuma Kamaru. 'Yaya jadawalin wasannin rukuni na bakwai yake? Wasannin farko a rukuni ranar 24 ga watan Nuwamba Wasa na biyu a rukuni ranar 28 ga watan Nuwamba Wasa na uku a rukuni ranar 2 ga watan Disamba Wadanne 'yan wasa ne suka buga mata Gasar Kofin Duniya a 2018? Masu tsaron raga: Alisson (Roma), Ederson (Manchester City), Cassio (Corinthians). Masu tsaron baya: Thiago Silva (Paris St Germain), Miranda (Inter Milan), Marquinhos (Paris St Germain), Marcelo (Real Madrid), Filipe Luis (Atletico Madrid), Fagner (Corinthians), Pedro Geromel (Gremio), Danilo (Manchester City). Masu buga tsakiya: Paulinho (Barcelona), Casemiro (Real Madrid), Philippe Coutinho (Barcelona), Renato Augusto (Beijing Sinobo Guoan), Fred (Shakhtar Donetsk), Fernandinho (Manchester City), Willian (Cgelsea). Masu ci mata kwalllaye: Neymar (Paris St Germain), Douglas Costa (Juventus), Gabriel Jesus (Manchester City), Roberto Firmino (Liverpool), Taison (Shakhtar Donetsk). (Compiled by Rohith Nair in Bengaluru, editing by Ed Osmond) https://www.bbc.com/hausa/articles/ckr72y0eel4o +sports Arsenal ta sayi Zinchenko daga Man City "Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal ta kammala cinikin ɗan wasan tsakiya na ƙasar Ukraine, Oleksandr Zinchenko, daga Manchester City. Zinchenko wanda ya buga wasanni da dama a ɓangaren hagu na bayan Man City, wasa 15 kawai ya buga a kakar wasan da ta gabata a yunƙurin ƙungiyar na kare kambin Premier League da ta ɗauka. Ɗan ƙwallon mai shekara 25 ya je Arsenal ne daga zagayen da City ke yi a Amurka don kammala komawarsa tasa bayan Arsenal ta amince da yarjejeniyar da ta kai fan miliyan 30. Zinchenko ya saka hannu kan yarjejeniya mai tsawo kuma shi ne ɗan wasa na biyar da Arsenal ta saya kafin fara sabuwar kakar wasa. ""Wannan mafarkina ne da nake yi tun ina yaro ya zama gaskiya, saboda babban masoyin Arsenal ne ni lokacin da ina yaro,"" in ji Zinchenko. Shi ne ɗan wasa na biyu da yake komawa Arsenal daga City a bazarar nan. Tuni Gabriel Jesus ya koma Emirates kan fan miliyan 45, inda har ma ya ci mata ƙwallo wasan sada zumunta." https://www.bbc.com/hausa/articles/c51vrezyv9ko +sports Arsenal ta kammala daukar Gabriel Jesus Arsenal ta kamma daukar dan kwallon tawagar Brazil, Gabriel Jesus, daga Manchester City kan fam miliyan 45, bisa yarjejeniya mai tsawo. Dan wasan, mai shekara 25, ya zama na hudu da Mikel Arteta ya dauka a bana, bayan Fabio Vieira da Matt Turner da dan wasan Brazil, Marquinhos. Arteta, wanda ya yi aiki tare da Jesus a lokacin da ya yi mataimin Pep Guardiola a Manchester City na kokarin daukar mai cin kwallaye, bayan da Alexandre Lacazette da Pierre-Emerick Aubameyang suka bar kungiyar. Jesus, wanda zai sa riga mai lamba tara a Gunners ya bar City, bayan kaka biyar da rabi da ya yi a Etihad. Ya yi wasa 236 da cin kwallo 95 da lashe Premier League hudu da League Cup uku da FA Cup. City wadda ta dauki Premier League a kakar da ta wuce ta sayar da Jesus ne, bayan da ta dauko dan kwallon Norway, Erling Haaland daga Borussia Dortmund kan fam miliyan 51.2 a watan Yuni. Ana kuma sa ran matashin dan wasan tawagar Argentina Julian Alvarez zai fada cikin 'yan kwallon da ke yi wa City wasanni. Jesus ya bayar da kwallo takwas aka zura a raga a Manchester City a kakar 2021-22, wanda ya yi kan-kan-kan da Kevin de Bruyne a wannan bajintar. https://www.bbc.com/hausa/articles/c3g0wejlz39o +sports Chelsea ta aike wa da Real saƙo kafin ta je Santiago Bernabu Kungiyar Chelsea ta caskara Southampton da ci 6-0 a wasan mako na 32 a Premier League da suka kara a St Mary ranar Asabar. Chelsea ta ci kwallayen ta hannun Marcos Alonso da Kai Havertz da Timo Werner da Mason Mount da kowanne ya ci biyu-biyu. Karo na biyar kenan da Mason Mount ya ci kwallo ya kuma bayar aka zura a raga a Premier League a kakar nan. Ya yi kan-kan-kan da Sadio Mane da kuma Mohamed Salah a wannan bajintar. Tun a minti na 31 Chelsea ta zura kwallo 4-0 a ragar Southampton, karon farko da aka ci kwallaye da wuri a Premier League a waje, tun wanda kungiyar Stamford Bridge ta yi wa Bolton a Oktoban 2011. Wannan ne karo na 21 da aka ci Southampton kwallo hudu ko fiye da haka a Premier League, bakwai daga cikin rashin nasarar karkashin koci Ralph Hasenhüttl. Karo na bakwai kenan da Thomas Tuchel ke samun nasara a kan Hasenhuttl, inda kocin Southampton ya yi nasara a daya, tun daga karawar da suka yi a Bundesliga zuwa Premier League. Haka kuma Chelsea ta ci manyan wasa 17 a waje karkashin Tuchel wanda ya karbi aiki a cikin Fabarairun 2021. Pep Guardiola ne kan gaba a wannan bajintar da cin fafatawa 21 a wasannin waje. A makon gobe Chelsea za ta je Real Madrid domin buga wasa na biyu a quater final na gasar Zakarun Turai ta Champions League, bayan da kungiyar Sifaniya ta yi nasara da ci 3-1 a wasan farko. An fafata a gasar Zakarun Turai tsakanin Real Madrid da Chelsea sau shida, inda kungiyar Stamford Bridge ta yi nasara a uku da canjaras ɗaya. Chelsea mai rike da Champions League, ita ce ta fitar da Real Madrid daga gasar a bara, daga baya ta doke Manchester City ta lashe kofin. https://www.bbc.com/hausa/wasanni-61052415 +sports Manchester United ta casa Liverpool da ci 4-0 Manchester United ta doke Liverpool da ci 4-0 a wasan sada zumunta da suka buga ranar Talata a filin Rajamangala National a Bangkoko. Kungiyoyin biyu sun buga wasan ne don gwada 'yan wasan da za su buga musu kakar bana da za a fara a farkon makon Agusta. United ta fara cin kwallo a minti na 12 da fara tamaula ta hannun Jadon Sancho, sannan Fred ya kara na biyu a minti na biyu, minti uku tsakani Anthony Martial ya ci na uku. Bayan da suka yi hutu suka koma zagaye na biyu ne United ta kara na hudu ta hannun Facundo Pellistri. Yan wasa 11 da suka fara buga wasan sada zumuntar: Liverpool 'yan wasa 11: Alisson, Mabaya, Phillips, Gomez, Chambers, Henderson, Morton, Carvalho, Elliott, Diaz, Firmino. Man Utd 'yan wasa 11: De Gea, Dalot, Lindelof, Varane, Shaw, McTominay, Fred, Sancho, Fernandes, Rashford, Martial. Wasannin da Liverpool za ta buga kafin fara kakar bana: 12 Yuli: Liverpool 0-4 Manchester United (Rajamangala Stadium, Bangkok) 15 Yuli: Liverpool da Crystal Palace (National Stadium, Singapore) 21 Yuli: RB Leipzig da Liverpool, (Red Bull Arena, Leipzig) 27 Yuli: Salzburg da Liverpool,  (Red Bull Arena, Leipzig) 30 Yuli: Liverpool da Manchester City  (Community Shield: King Power Stadium, Leicester) 31 Yuli: Liverpool da Strasbourg (Anfield) Wasannin da Manchester United za ta yi kafin fara kakar bana: 12 Yuli: Manchester United 4-0 Liverpool (Rajamangala Stadium, Bangkok) 15 Yuli: Melbourne Victory da Manchester United (MCG, Melbourne) 19 Yuli: Manchester United da Crystal Palace (MCG, Melbourne) 23 Yuli: Manchester United da Aston Villa (Optus Stadium, Perth) 30 Yuli: Atletico Madrid da Manchester United (Ullevaal Stadion, Oslo) 31 Yuli: Manchester United da Rayo Vallecano (Old Trafford) https://www.bbc.com/hausa/articles/ckm8vl3273go +sports Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Mbappe, Haaland, Toney, Mount, Silva, Dalot Darajar ɗan wasan Faransa Kylian Mbappe za ta kai tsakanin euro milliyan 300 zuwa 350 idan wata ƙungiya tana sha'awar sayensa sai dai PSG ba ta da niyyar sayar da matashin mai shekara 23 bayan a rahotanni sun ɓulla cewa matashin yana son barinsu a watan Janairu. (Telegraph - subscription required). Chelsea ta soma tattaunawa da ɗan wasan tsakiya na Ingila Mason Mount mai shekara 23 kan ƙulla sabon kwantiragi. (Standard) Ɗan wasan baya na Brazil Thiago Silva mai shekara 38 ya ce iyalinsa suna da ruwa da tsaki kan ko zai zai tsawaita kwangilarsa a Chelsea yayin da kwangilarsa ke gab da ƙarewa a ƙarshen kakar wasan bana.  (Standard) Juventus na son sayen ɗan wasan Man U Diago Dalot inda matashin mai shekara 23 dan Portugal ke shirin barin ƙungiyar. (Calciomercato - in Italian). Tottenham tana bibiyar dan wasan Brentford dan Ingila Ivan Toney da ƙungiyar Spurs ke ta zuba ido kan dan wasan mai shekara 26. (Football Insider) Mai bawa PSG shawara Luis Campos ya koma kungiyar ne a watan Yuni amma yana iya shirin barin gasar Ligue 1.(Le Parisien, via Mail) Sir Jim Ratcliffe ya ce da ya siye Man U a bazara amma iyalin Glazer ba za su sayar ba. (Financial Times, via Goal) Kocin Wigan Leam Richardson na cikin shirin zama sabon kocin West Brom bayan s in the frame to become West Brom's new manager after the Baggies sacked Steve Bruce. (Football Insider) Kocin Wigan Leam Richardson na cikin shirin zama sabon kocin West Brom bayan da aka kori Steve Bruce.  (Football Insider) https://www.bbc.com/hausa/articles/cndwxj1g01po +sports Mbappe na jin PSG ta yi masa ''romon baka'' zai bar kungiyar a Janairu Kylian Mbappe na jin cewar Paris St Germain ta ''yaudare shi'' yana son barin kungiyar a watan Janairu in ji Julien Laurens mai sharhin tamaula a Faransa. A watan Mayu dan kwallon tawagar Faransa ya saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da taka leda kaka uku a PSG, amma yanzu yana jin ya yi ''kuskure''. Mbappe, wanda ya ci kwallo 12 a dukkan wasan da ya yi wa PSG a bana na son komawa taka leda Real Madrid. Sai dai daraktan wasanni na PSG, Luis Campos ya ce dan kwallon mai shekara 23 bai taba cewar zai bar kungiyar a Janairu ba. A hirar da aka yi da shi a BBC Radio 5 kai tsaye, Laurens ya ce ''Sun yi masa alkawarin za su sayo mai cin kwallo, domin ya koma buga gurbin da yafi kauna, za a sayar da Neymar - za su dauki mai tsaron baya daga tsakiya, sannan shi ne zai ke jagorantar dukkan abin da za a yi a kungiyar. Sai dai ba alkawarin da aka cika masa. ''Mun san cewar akwai rudani a wannan lokacin, amma yanzu ya yanke shawarar baya son ci gaba da zama a PSG. yana kuma jin yayi kuskure da ya amince ya tsawaita kwantiraginsa, wanda ya kamata ya koma wata kungiyar kan fara kakar bana, yanzu yana duba inda ya kamata ya koma idan an bude kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo a watan Janairu.'' Mbappe wanda ya lashe kofin duniya da Faransa a Rasha a 2018 ya dauki kofi 11 a PSG har da Ligue 1 hudu, tun bayan da ya koma kungiyar daga Monaco a 2017, wanda ya fara da wasanin aro. Ranar Juma'a mujallar Forbes ta bayyana shi a matakin wanda ke kan gaba a samun kudin shiga a duniya a 2022 tsakanin masu taka leda - karon farko da Lionel Messi ko Cristiano Ronaldo da suke rike gurbin. https://www.bbc.com/hausa/articles/cw0qjegnqjdo +sports Man United ta buga kurman duro karon farko karkashin Ten Hag Manchester United ta tashi 0-0 a wasan mako na 11 a gasar Premier da suka kara a Old Trafford ranar Lahadi. Kungiyoyin sun samu damar makin zura kwallo a raga tun farko, musamman Newcatle da kwallo biyu ya bugi turke. Marcus Rashford ya samu dama mai kyau a karshen lokaci, wanda ya sawa kwallo kai ta yi fadi ta fita waje. Karon farko da sabon koci, Erik ten Hag ya tashi 0-0 a dukkan wasan da ya ja ragamar United kawo yanzu a bana. Kociyan ya ja ragamar wasa 13 a dukkan fafatawar da United ke yi a kakar 2022/23 kawo yanzu. Cristiano Ronaldo ya buga wasan, wanda daga baya Rashford ya canja, an kuma ga kyaftin din Portugal na jijjiga kai a lokacin da zai fita daga filin. Da wannan sakamakon Manchester United wadda ta yi wasa tara tana da maki 16, ita kuwa Newcastle tana da 15 biye da kungiyar Old Trafford. Ranar Laraba 19 ga watan Okboba, Manchester United za ta karbi bakuncin Tottenham a wasan da zai yi zafi. A kuma ranar Newcastle United za ta yi wa Everton masauki a St Jamrs Park. https://www.bbc.com/hausa/articles/cx9770v5e5go +sports Fernandinho ya koma Athletico Paranaense Athletico Paranaense ta sake daukar Fernandinho, kungiyar da ya fara taka leda a matakin kwararren dan wasa. Tsohon kyaftin din Manchester City ya koma kungiyar Brazil, bayan da yarjejeniyarsa ta kare a karshen kakar 2021/22. Mai shekara 37, tsohon dan kwallon tawagar Brazil ya fada cewar ''Kungiyoyi da yawa sun yi zawarci na, amma na zabi tsohuwar kungiyata, domin na saka mata da abin da ta yi min.'' Fernandinho ya bar Etihad, bayan kaka tara da ya yi a City. Wanda ya lashe kofin Premier League biyar, ya koma Athletico, bayan barin kungiyar shekara 17 zuwa Shakhtar Donetsk. Tsohon kociyan Chelsea, Luiz Felipe Scolari shi ne yake horar da Athletico. https://www.bbc.com/hausa/articles/cevx4kq1g9qo +sports Ba zan daina wasa da kwallo ba, da shi aka sanni in ji Antony "Dan wasan Manchester United na gaba Antony ya ce, ""ba zai daina abin da ya fito da ni ba aka san ni"" bayan wani wasa da ya yi da kwallo a Europa wanda ya janyo masa suka. Antony ya yi zagaye biyu da kwallo a tsakanin kafafunsa a ranar Alhamis a wasan da Manchester ta yi nasara a kasan Sheriff Tiraspol da ci 3-0. Erik ten Hag bayan an kammala wasan ya ce ""za mu gyara masa"" idan ya yi wasa da kwallo mara dalili a cikin wasa. ""An samunmu kan abin da muka kware a kai, ban zan daina yin abin da ya kawo ni nan ba,"" kamar yadda Antony ya rubuta a safinsa na Instagram. A ranar Juma'a dan wasan mai shekara 22 ya wallafa wannan sako. Bayan da Antony ya yi wasan, sai ya buga kwallo wajen ragar Sheriff. Ten Hag ya musanta cewa wannan ne dalilin da ya sanya ya cire dan wasan da aka saya £85m a hutun rabin lokaci. ""Ni ba ni da matsala da wasa da kwallo matukar zai yi amfani,"" in ji kocin dan kasar Netherland wanda ya yi aiki da Antony a Ajax. ""Ina bukatar ya kara kokari - ya kara karfafa kansa, ya kara ci gaba da kai hare-hare da kuma yawan cin kwallo. ""Lokacin da zai yi irin wannan matukar zai yi amfani. Idan ba za a kwace kwallon ba, to ai babu damuwa - amma idan wasa ne da nufin wasa, to ai dole mu yi masa gyara.""" https://www.bbc.com/hausa/articles/c145zvl9j7vo +sports An sanya wa'adin karshe na kasashen da ke son daukar nauyin gasar Nations Cup 2025 "Hukumar kwallon kafa ta CAF ta sanya ranar 11 ga watan Nuwamba a matsayin wa'adin karshe ga kasashen da ke da muradin karbar bakuncin gasar Afrika ta 2025. Ana neman samun sabuwar kasar da za ta karbi bakunci bayan Guinea ta gaza cika tsammanin da ake da shi a kanta na samar da wuraren wasa da kayan aiki don gasar. CAF na sa ran samun bukata ta karshe daga kasashe da suka hada da takardunsu da kuma biranen da ake so a yi wasanni cikinsu, a kai su hedikwatarta da ke Cairo nan da ranar 16 ga watan Disamba. Wakilina CAF da za su duba wuraren za su fara aikin dubawar ne daga ranar 5 ga watan Janairu zuwa 25, a laluben da take yi na neam wadda za ta maye gurbin Guinea. \n\nZa a gabatar da bayanan da kwamitin kolin CAF su 24 suka samu, wanda kuma a ranar 10 ga watan Fabirairu za a sanar da kasar da ta samu nasara ko kasashen da za su hada gwiwa domin karbar bakuncin wasannin. Wani babban jami'in CAF ya shaida wa BBC cewa hukumarsuna kokarin kaucewa bai wa ""duk wata kasa da bata da filayen wasa da kuma karamci da za a nunawa sauran sassan duniya"". Kamaru ce ta dauki bakuncin 2021, kuma a farkon shekarar nan aka sauya Ivory Coast da za karbi bakuncin gasar a 22023 amma aka mayar da shi 2024 saboda wasu dalilai irin na yanayi. Ana tsammanin Morocc za ta nema\n\nTuni wasu kasashe suka nuna sha'awarsu ta daukar nauyin gasar kashi ta 35, amma har yanzu ba su nuna sha'awarsu a hukumance ba. Morocco wadda ta karbi bakuncin gasar Afrika Ta Mata a watan Yuli, tana da niyyar daukar bakuncin gasar ta maza ta 2025, kamar yadda wani jami'i a hukumar kwallon kafa ta Morocco ya tsegunta. Najeriya da ta nuna bukatar daukar gasar ta hadin gwiwa da Benin itama ta yi tsit tun bayan da Amaju Pinnick ya sauka daga shugaban hukumar ta NFF. Bukatar Algeriya da Afrika Ta Kudu da kuma Senegal suma an ta yada jita-jitan za su iya daukar wannan gasar." https://www.bbc.com/hausa/articles/cv2p1g73lqdo +sports Chelsea na bincike kan nuna wariyar da aka yi wa Son Chelsea ta ce za ta dauki matakin ba-sani-ba-sabo game da binciken da take yi na nuna wariyar da aka yi wa dan wasan gaban Tottenham Son Heung-min a Stamford Bridge. Wannan lamari ya faru ne lokcin da Son ya je bugo kwana a minti 45 na biyu na wasan, wanda aka tashi 2-2 a Premier. A baya kungiyar ta taba haramtawa wasu magoya bayanta shiga kallon wasanta na har abada saboda irin wannan laifi na nuna wariya. Cikin wata sanarwa Chelsea ta ce ba za ta yarda da nuna dabi’ar nuna wariya ba. Sanarwar ta kara da cewa, “Chelsea ba za ta jurewa cin zarafin abokan wasanta ba ko nuna musu wariya ba, sai dai akwai wasu bara gurbi da ke kiran kansu magoya bayan Chelsea da ke da irin wannan dabi’un, wanda kuma abin kunya ne ga kungiyar da kocinta da ‘yan wasanta da ma’aikatanda har ma da magoya bayanta na gaskiya. “Muna bincike kan wannan lamari, kuma idan aka gano wadanda suka yi wannan za su fuskanci tsattsauran hukunci daga kungiyar. “Ba za mu taba amincewa da wariyar launin fata ba a Chelsea ko kuma kasarmu.” https://www.bbc.com/hausa/articles/cz4edg22552o +sports Modric zai buga wa Croatia Gasar Cin Kofin Duniya karo na hudu Dan wasan Real Madrid, Luca Modric yana cikin wadanda za su buga wa Croatia gasar kofin duniya a Qatar, kuma karo na hudu da zai wakilci kasar. Mai shekara 37, shi ne ya lashe kyautar gwarzon dan wasan gasar kofin duniya da aka yi a Rasha a 2018, ya kuma je ta Jamus a 2006 da ta Brazil 2014. Dan kwallon Tottenham, Ivan Perisic da na Chelsea, Mateo Kovacic, suna cikin 'yan wasa 26 da Croatia ta bayyana da za su buga mata gasar ta Qatar. Za a fara gasar cin kofin duniya tsakanin 20 ga watan Nuwamba zuwa 18 ga watan Disambar 2022. Croatia, wadda ta yi ta biyu a Rasha tana rukuni na biyar a Qatar tare da Belgium da Canada da kuma Morocco. Wasu 'yan wasan da suka yi mata gasar da aka yi a Rasha da yawa za su buga ta Qatar, ta kuma samu karin matasa har da mai shekara 20 mai tsaron bayan RB Leipzig Josko Gvardiol. Croatia za ta fara wasa a cikin rukuni da Morocco ranar Laraba 23 ga watan Nuwamba. Sunayen tawagar Croatia da za ta buga kofin duniya a Qatar: Masuu tsaron raga: Domink Livakovic (Dinamo Zagreb), Ivica Ivusic (NK Osijek), Ivo Grbic (Atletico Madrid) Masu tsaron baya: Domagoj Vida (AEK Athens), Dejan Lovren (Zenit St Petersburg), Borna Barisic (Rangers), Josip Juranovic (Celtic), Josko Gvardiol (RB Leipzig), Borna Sosa (VfB Stuttgart), Josip Stanisic (Bayern Munich), Martin Erlic (Sassuolo), Josip Sutalo (Dinamo Zagreb) Masu buga tsakiya Luka Modric (Real Madrid), Mateo Kovacic (Chelsea), Marcelo Brozovic (Inter Milan), Mario Pasalic (Atalanta), Nikola Vlasic (Torino, on loan from West Ham), Lovro Majer (Rennes), Kristijan Jakic (Eintracht Frankfurt), Luka Sucic (RB Salzburg) Masu cin kwallo: Ivan Perisic (Tottenham), Andrej Kramaric (1899 Hoffenheim), Bruno Petkovic (Dinamo Zagreb), Mislav Orsic (Dinamo Zagreb), Ante Budimir (Osasuna), Marko Livaja (Hajduk Split) https://www.bbc.com/hausa/articles/crgdy74g6dqo +sports Real Madrid ce mafi daraja a kwallon kafa a duniya Real Madrid ita ce ta daya a daraja a fannin tamaula a duniya kuma karo na hudu a jere in ji wani rahoto daga Brand Finance Football 50. Kasuwancin da ake gudanar wa a kungiyar ya karu zuwa Yuro biliyan 1.5 tana gaban Manchester City Yuro biliyan 1.3 da itama Barcelona da take da Yuro biliyan 1.3. Rahoton ya fayyace cewar kasuwancin Real Madrid ya karu a shekarar nan ta yadda ta bunkasa wasanninta da rawar da ta taka da hakan ya sa ta samu karin kudin shiga. A kan samu ci gaban kasuwancin kungiya ta hanyar cinikayyar 'yan kwallo da samun manyan kamfanoni da ke daukar nauyin tallace-tallace da rawar da take takawa a gasar tamaula. Jerin kungiyoyi 10 da ke kan gaba a daraja a fanni tamaula a duniya, gaban kungiyar Yuro biliyan da ta samu a 2022 ne: https://www.bbc.com/hausa/wasanni-61577248 +sports Qatar 2022: Morocco ta tsallake amma an fitar da Belgium Morocco ta kai zagayen gaba a gasar kofin duniya da ake yi a Qatar, yayin da a ka cire Belgium bayan da ta kasa karbar maki uku hannun Croatia. Nasarar da Morocco ta yi 2-1 a wasanta da Canada na nufin ta zama zakara a rukunin F da maki bakwai, yayin da Crotia ke binta da maki biyar. Kasar ta Arewacin Afrika ta ci kwallayenta ne ta hannun Hakim Ziyech da En-Nesyri tun kafin a je hutun rabin lokaci. Kuma ta zama kasa ta biyu daga nahiyar Afrika bayan Senegal da ta kai zagayen kwaf daya na Qatar 2022. Belgium kuwa wadda ita ce ta biyu a jadawalin kwarewa na kasashen FIFA, kuma ta uku a gasar kofin duniya ta 2018, ta fita daga gasar da maki hudu. Duk da Belgium tafi Croatia wadda ta buga wasan karshe a 2018 buga wasa mai kyau da kuma samun damarmaki, hakan bai sa ta samu maki ukun da take matukar bukata ba. A yanzu Morocco da Croatia za su jira su ga wadanda za su kara da su a rukunin E, wanda ya kunshi kasashen Sfaniya da Jamus da Costa Rica da kuma Japan. Kasashen na rukunin E za su take wasa ne da karfe takwas agogon Najeriya. https://www.bbc.com/hausa/articles/c14r9nnq97vo +sports Watakila a sayar da Chelsea nan da karshen watan nan Wani kamfanin Amurka da aka bai wa alhakin sayar da Chelsea ya ce yana sa ran nan da karshen watan nan za a kammala cinikin kungiyar. Hakan ya biyo bayan karfin gwiwa da ya samu daga gwamnatin Burtaniya, bayan da suka tattauna a tsakaninsu. Gwamnatin na bukatar gyare-gyaren lasisin kungiyar kan a sayar da Chelsea, bayan da aka dora wa mamallaki Roman Abramovich takunkumi a makon jiya. An cimma matsaya cewar gwamnatin Burtaniya ce za ta bayar da izinin sayar da Chelsea kuma kudin cinikin za a zuba a gidauniyar taimakawa wadanda yakin da ake yi a Ukraine ya shafa. Gwamnatin Burtaniya ta samar da wani lasisi na musamman domin bai wa Chelsea damar ci gaba da gudanar da ita, bayan da aka rufe asusun Abramovich, wanda ake alakanta shi da shugaban Rasha, Vladimir Putin. A sabon tsarin lasisin da gwamnati ta samar, ba damar a sayar da Chelsea har sai ta bayar da izini. An dage wa'adin cimma yarjejeniyar sayar da kungiyar zuwa ranar Juma'a 18 ga watan Maris, inda sama da mutum 20 ke son mallakar kungiyar. Chelsea mai rike da Champions League za ta je gidan Lille ranar Laraba a karawar daf da na kusa da na karshe, kuma kungiyar Stamford Bridge ce ta yi nasara da ci 2-0 a wasan farko. https://www.bbc.com/hausa/wasanni-60740525 +sports Erling Braut Haaland: Man City da Real da Barca na jiran amsa daga dan wasan Dortmund Manchester City da Real Madrid da kuma Barcelona duk sun tattauna da Erling Braut Haaland, suna kuma jiran matsayar da zai yanke kan makomarsa nan da kwana 10 in ji wani rahoto daga Guillem Balague. A kakar 2024 kwantiragin dan wasan Borussia Dortmund zai kare, amma cikin kunshin yarjejeniyarsa da kungiyar Jamus, za ta iya sayar da shi kan fam miliyan 63.2 a karshen kakar bana. ''Dukkan kungiyoyi ukun ba su da masaniyar mai zai faru nan gaba kan batun makomar dan wasan,'' in ji Balague. Tun farko Bayern Munich ta yi kokarin zawarcin dan kwallon, amma yanzu ba ta bukatarsa. Balague ya ce ''batun sayen dan wasan ba kan kudi ta ta'allaka ba, kowacce kungiya ta bayar da bayanai kan yadda za ta yi amfani da shi a lokacin wasanni.'' ''Sai dai kuma akwai damar dan kwallon ya ci gaba da taka leda a Dortmund zuwa kaka daya daga nan ya je Real Madrid ko Barcelona, domin dan wasan na burin buga La Liga nan gaba. ''Real Madrid dan kwallon ke son zuwa, sai dai Manchester City tana nuna masa kada ya yi kuskuren zuwa can, domin Kyalin Mbappe zai koma Real a karshen kakar nan, sannan Karim Benzema na kokari, saboda haka zai ci zaman benci. Haka kuma City ta ja kunnensa da cewar Barcelona ta wannan lokacin ba za ta iya kalubalantar manyan kofuna ba, saboda haka zai je kungiyar ba tare da lashe kofuna ba. ''An kuma tambayi Haaland kan batun zuwa Manchester City don taka leda karkashin Pep Guardiola - sai ya ce yana tuninin inda zai dade yana buga tamaula - kwantiraginsa zai iya cika a 2023. City tana son ta rarrashe shi ya kara kaka daya a Jamus, sannan ta dauke shi. Haaland dan kwallon tawagar Norway ya ci kwallo 23 a wasa 22 a Dortmund a bana, yana kuma taka rawar gani a Dortmund tun bayan da ya koma Jamus da taka leda daga Red Bull Salzburg a Janairun 2020. https://www.bbc.com/hausa/wasanni-60784009 +sports Emile Smith Rowe zai yi jinyar watanni bayan yi masa tiyata "Dan wasan tsakiya na Arsenal Emile Smith Rowe zai yi jinyar watanni bayan tiyatar da aka yi masa a tsakanin jinyoyinsa. Dan wasan zai koma atisaye ne a watan Disamba mai zuwa. Wasa hudu dan wasan ya buga a wannan kakar, kuma duka ya shiga a canji ne. A wasan karshe da ya buga wanda suka yi da Manchester United, ya samu ""mummunan koma baya"". ""A yan watannin nan Emile Smith Rowe na fuskantar rashin nutsuwa a jinyarsa, wanda hakan ya sa ya rage yawan atisaye da buga wasanni,"" in ji Arsenal. ""Bayan wannan koma baya da ya samu a wasanmu na Premier da Manchester United a Old Trafford a ranar 4 ga watan Satumba, amma bayan tattaunawa da tuntubar likitocinmu, an yi wa Emile tiyata domin gyara masa raunin da ya ji a cinyoyinsa. ""An yi masa wannan tiyatar ne cikin nasara kuma a Landan a kwanakin da suka gabata kuma ana ci gaba da yi masa bayanai da za su kwantar masa da hankali. ""Muna sa ran Emile zai dawo atisaye a watan Disamba.""" https://www.bbc.com/hausa/articles/crgn3rvn2zyo +sports Najeriya za ta fafata da Algeria a wasan sada zumunta Tawagar kwallon kafa ta Najeriya ta na Oran, domin buga wasan sada zumunta da Algeria ranar Talata. Super Eagles ta sauka a Algeria tun a makon jiya, inda ta zauna a Constantine, wadda ta buga wasan sada zumunta da tawagar Algeria, wadda za ta buga CHAN a bana. Sun kuma tashi wasan 2-2 da suka fafata ranar Juma;a, inda Alex Iwobi da kuma Cyriel Dessers suka ci wa Najeriya kwallayen. Tawagogin biyu za su kece raini a yammacin Talata a filin wasa na Stade Olympique d’ Oran. Algeria da Najeriya sun kai zagayen karawar karshe ta neman shiga gasar kofin duniya a bana, inda Kamaru ta cire Algeria, Ghana ta yi wa Super Eagles fancale. Ranar Juma'a Algeria ta buga wasan sada zumunta da Guinea, inda ta yi nasara da ci 1-0. Karo na hudu da Algeria ta yi nasara a jere, ita kuwa Najeriya karkashin Jose Peseiro na sa ran yin nasara ta uku. Kungiyoyin biyu sun fafafata sau 21 a tsakaninsu, kowacce ta ci tara da canjaras uku. Canjaras na baya da suka yi shi ne a 1993 - daga lokacin Super Eagles ta ci wasa shida daga tara. Algeria ta doke Super Eagles a kofin Afirka a Masar a 2019 da kuma a wasan sada zumunta a 2020 a Austria. Najeriya na fama da 'yan wasan da ke jinya da suka hada da Victor Osimhen da Umar Sadiq da kyaftin Ahmed Musa. Tuni kuma Wilfred Ndidi da William Troost-Ekong suka bar sansanin 'yan wasa suka koma Ingila, don yin jinya. https://www.bbc.com/hausa/articles/crgx73rzr5xo +sports Manya-manyan asarar rayuka da aka taɓa yi a wajen kallon kwallon kafa a duniya "Yamutsin masu kallon kwallon kafa na Indonesia, wanda ya kashe akalla mutum 125 a Gabashin Java ya riga ya shiga tarihin bala'o'i manya da suka faru a tarihin wasan. Bala'in wanda ya auku a ranar Asabar, 1 ga Oktoban bana a Filin Wasan Kanjuruhan, yana kamanceceniya da irinsa da suka auku a baya, ba a rashin rayuka kadai ba. Babban dalilin aukuwar yamutsin da ke faruwa a filin wasan ƙwallon ƙafa shi ne rashin tsari mai kyau wajen tsara masu kallon. Akalla mutum 300 suka rasu a lokacin da ake buga wasa tsakanin Peru da Ajantina, inda aka samu yamutsi bayan an hana wani kwallo da Peru ta jefa a ragar Ajantina. Hakan ya sa magoya bayan Peru suka kutsa filin wasan da ake bugawa domin neman gurbin shiga Gasar Olympik na 1964 da aka buga a birnin Tokyo, wanda ya sa 'yan sanda suka rika harba barkonon tsohuwa kan mai uwa da wabi a Filin Wasa na Lima Estadio Nacional. Wannan ya jawo yamutsi a kofofin fita daga filin wasan, wadanda a kulle suke a lokacin. A hukumance, wadanda suka mutu sun kai 328, amma akwai alama an tauye adadin domin ba a hada da wadanda aka harbe ba domin magoya bayan da jami'an tsaro sun gwabza a wajen filin wasan. ""Akwai ganau da dama da suka tabbatar da mutuwar wasu a sanadiyar harbi, amma alkalin da aka nada domin bincikar lamarin. Mai shari'a Benjamin Castaneda bai samu gamsassun hujjoji da zai tabbatar da hakan ba,"" in ji wakilin wasanni na BBC, Piers Edwards a wata maƙala da ya rubuta a shekarar 2014 domin bikin cika shekara 50 da aukuwar bala'in, wanda har yanzu ake kirga shi a cikin irinsa da suka fi tsanani. Daga bisani an yanke wa kwamandan 'yan sanda mai suna Jorge Azambuja, wanda shi ne ya bayar umarnin harba barkonon tsohuwa daurin wata 30 a gidan yari. A wani wasan kece-raini tsakanin Heart Oak da Asante Kotoko, wadanda kungiyoyi ne guda biyu masu dimbin magoya baya da aka buga a Mayun 2001, an samu barkewar rikici bayan magoya bayan Kotoko sun nuna rashin jin dadinsu da farke kwallon da abokan karawansu suka yi a kusa da tashi. Wannan ya sa 'yan sanda suka shiga harba barkonon tsohuwa, wanda ya sa masu kallo suka fara rububin fita, inda suka tarar kofofin na kulle. Akalla mutum 126 suka mutu, wanda wannan ne yamutsi a wajen kallon kwallon kafa mafi muni a Afirka. ""Na ga gawarwakin matasa masu jini a jika a kwance a kasa. Na shiga tashin hankali, da har na kasa kirga yawan gawarwakin,"" in ji Karamin Ministan Wasannin Ghana na wancan lokacin  Joe Aggrey a zantawarsa da BBC. Kwamitin Bincike ya daura laifin ga 'yan sanda, wannan ya sa aka tuhumi 'yan sanda shida da kisan kai. Sai dai a shekarar 2003, an wanke su a wata shari'a da mutanen Ghana da dama suka yi na'am da shi kamar yadda Paul Adom Otchere, wanda dan jarida ne a tashar rediyo ta Joy FM wanda ya kasance a kotun lokacin shara'ar ya bayyana. ""Abin da mutanen gari suka so shi ne hukunta wadanda suka gina filin wasan, wanda ya tabbatar da ingancin ginin da wadanda suka kulle kofofin shiga filin a lokacin yamutsin,"" kamar yadda ya bayyana wa BBC bayan hukuncin. Yana cikin bala'o'i manya masu daure kai da suka faru a duniyar kwallon kafa. Ya faru ne a sanadiyar rashin tsari mai kyau wajen tsara masu kallon wasan kusa da karshe na Kofin Kalubale tsakanin Liverpool da Nottingham Forest, inda magoya bayan kungiyar Liverpool guda 96 suka mutu. Daga baya wani mai suna Andrew Devine da ya ji mummunar rauni a yamutsin ya rasu a shekarar 2021 yana da shekara 55, wanda hakan ya sa ya zama mutum na 97 da ya rasu. 'Yan sanda da wasu sashin 'yan jarida na Birtaniya suna daura laifin ne a kan magoya bayan, inda suka zarge su da zuwa filin cikin maye da rashin bin tsari. Sai dai an yi watsi da wannan bayan an gudanar da bincike-bincike a tsakanin shekaru 30 daga baya. A shekarar 2016, wani alkali ya tabbatar da cewa an kashe wadanda lamarin ya rutsa da su ne, sannan ya wanke 'yan kallon daga aikata wani laifin. Wata tsawa mai karfi ce ta firgita masu kallon wani wasa a Birnin Nepalese a Maris na 1988. Wannan ya sa masu kallon suka fara rige-rigen shiga gefen da ke da rufi a filin domin samun mafaka, amma 'yan sanda suka hana su, sannan wadanda suka nufi kofofin fita, suka tarar duk suna kulle. Wannan yamutsin ne ya jawo mutuwar mutane da dama. A hukumance an ce mutum 70 suka mutu, amma kafofin yada labarai na Nepalese sun ruwaito cewa wadanda suka mutu za su kai 93. ""Na ga takalman wadanda suka mutu ko ta ko'ina a filin,"" in ji Anil Rupakheti, wanda tsohon dan kwallo ne da ya kasance a cikin filin lokacin da lamarin ya faru a zantawarsa da Jaridar Kathmandu Post a shekarar 2020. A wani wasa da aka fafata tsakanin Al Masry da All Ahly na Masar, a birnin Port Said a Fabrailun 2012, an karkare wasan ne jina-jina, bayan magoya bayan Kungiyar Al Masry sun kutsa yankin magoya bayan Kungiyar Al Ahly, suka kai musu hari, inda suka samu nasarar cin musu-saboda 'yan sanda sun ki bude kofofin ficewa. Wannan hargitsin ya haifar da mutuwar mutum 74, sannan sama da 500 suka jikkata. An kama tare da gabatar da sama da mutum 70 ciki har da 'yan sanda tara a gaban shara'a, inda aka yanke wa 47 hukunci, ciki har da hukuncin kisa. Wasu daga cikin magoya bayan Al Ahly da ake kira 'Utras"" suna cikin wadanda suka shiga gaba lokacin zanga-zangar kiyayya ga Shugaban Kasa Hosni Mubarak, wadda ta yi sanadiyar kifar da gwamnatinsa. Hakan ya sa wasu magoya bayan wasanni suke zargin magoya bayan Hosni Mubarak da shirya yamutsin na Port Said domin ramako, sannan suka zargi 'yan sanda da rashin tabuka abin kirki. 'Har yanzu ina tuna bala'in da na gani a wannan Daren,"" in ji Fabio Junior, dan wasan Brazil da a lokacin yake buga wa Kungiyar Al-Ahly leda a lokacin a zantawarsa da ESPN Brazil a 2019. Filin Wasan Moscow wanda ba da dadewa ba aka buga Wasan Karshe na Gasar Cin Kofin Duniya na shekarar 2018, shi ma an taba shiga irin wannan bala'in a cikinsa. Kimanin shekara 40 da suka gabata, a zamanin mulkin Soviet, an yi turereniya bayan wasan Kofin Turai tsakanin Spartak Moscow ta Rasha da HFC Haarlem ta Holland, inda mutane da dama suka mutu. Sai a shekarar 1989 ce aka samu labarin adadin mutanen da suka mutu a hukumance, bayan an dade ana bayyana aukuwar lamarin ne kawai. Shaidun ganau sun ce a ranar magoya baya da yawa sun taru ne a sashe daya na filin saboda ba a halarci kallon wasan ba sosai. ""Sai ya kasance kofa daya aka bude domin saukakawa 'yan sanda su yi aikinsu,"" kamar yadda Alexander Provestov, wanda fitaccen dan jarida ne na kasar Rasha da ya kasance a filin wasan a lokacin a zantawarsa da Al Jazeera. ""Ba karamin kuskure aka tafka ba.""" https://www.bbc.com/hausa/articles/cllq2zr0z8qo +sports Mbappe ne kan gaba a takarar takalmin zinare a Gasar Kofin Duniya Ranar Talata za a ci gaba da wasannin daf da na kusa da na karshe a Qasar Cin Kofin Duniya a Qatar, bayan da aka kammala zagaye Quarter finals. Ranar Talata za a kara tsakanin Argentina da Croatia, sannan a fafata tsakanin Faransa da Morooco ranar Laraba. Kawo yanzu an ci kwallo 158 a babbar Gasar tamaula ta duniya da Qatar ke karbar bakunci, inda Kyalin Mbappe ke kan gaba mai biyar a raga kawo yanzu. Cikin masu takarar takalmin zinare a Qatar, wato kyautar da ake bai wa wanda ke kan gaba a cin kwallaye har da Lionel Messi na Argentina da Olivier Giroud na Faransa. Messi mai taka leda a PSG da kuma Giroud mai wasa a AC Milan kowanne ya ci hurhudu. Mbappe ya fara cin kwallo a Qatar a minti na 68 a karawar da Faransa ta ci Australia 4-1 ranar 22 ga watan watan Nuwamba. Daga nan ya ci biyu a fafatawar da Faransa ta doke Denmark 2-1 ranar 26 ga watan Nuwamba. Haka kuma dan kwallon PSG ya kara zura biyu a raga a wasan da Faransa ta ci Poland 3-1 ranar 4 ga watan Disamba. Ranar 18 ga watan Disamba za a kammala Gasar Cin Kofin Duniya ta 22 da Fifa ke gudanarwa. Jerin 'yan wasan da ke takarar lashe takalmin zinare a Qatar https://www.bbc.com/hausa/articles/c97q3j7gj92o +technology Milkyway Galaxy: An gano wani abu mai jujjuyawa da ba a san shi ba a can sararin samaniya "Masana kimiyya a Australiya sun gano wani abu mai jujjuyawa wanda ba a san shi ba a can sararin samaniya a birni Milkiwe Galakzi, wanda kuma suka ce ba wani abu da aka taba gani kamarsa. Abin wanda wani dalibin jami'a ya fara gano shi, an ga yana fitar da tarin tururin maganadisu tsawon minti daya a duk bayan minti 18. Yawanci abubuwan da ke fitar da wani abu da ya danganci makamashi kamar haske ko dumi ko turiri a sararin samaniya, an sansu an kuma yi rubutu a game da su. To amma masu bincike sun ce wani abu da yake jujjuyawa har tsawon minti daya, abu ne da ya zaman a daban, wanda za a ce ba a taba gani ba. Masu binciken dai sun dukufa aiki a yanzu domin kara fahimtar wannan abu da suka hanga a samaniya. Wani dalibin jami'ar Curtin, da ke yammacin Australia mai suna Tyrone O'Doherty ne ya gano abin a sararin samaniya da na'urar hangen nesa mai wata fasaha da ya kirkiro. Dalibin na cikin wani ayarin masu bincike da ke karkashin jagorancin masaniyar kimiyyar samaniya Dr Natasha Hurley-Walker, ta jami'ar ta Curtin (ICRAR). Malamar ta ce: ""Abin yana fitowa sai kuma ya bata har tsawon wasu sa'o'i a lokacin da muke duba shi.'' Ta kara da cewa : ""Wannan abu ne da ba a taba tsammani. Wannan abu ne bako mai daure kai sosai ga masanin sama jannati, saboda babu wani abu a sararin sama da aka san yana irin wannan abin."" Abubuwan da ke walkiya a samaniya ba wasu sabbi ko bakin abubuwa ba ne ga masana kimiyyar samaniya ko 'yan sama jannati, in ji masaniyar. To amma a ce ga wani abu wanda zai yi haske har tsawon minti daya sannan hasken ya dauke, to wannan bakon abu ne ga masana in ji Dr Gemma Anderson ta cibiyar da ke nazari a kan abin. Sanarwar da jami'ar ta fitar ta kara da cewa bayan da masanan suka yi bincike na bayanan da aka tattara a baya na shekara da shekaru, masanan sun ayyana cewa abin yana da nisan tafiyar haske ta kusan shekara 4,000 daga doron duniya. Sanarwar ta ce abin yana da haske sosai da kuma maganadisu mai karfin gaske. Nazariyyar da ake dangantawa da abin ta hada da cewa wata nau'in tauraruwa ce ko kuma wani bangare ne na wata tauraruwa da ta fado. To amma galibin abubuwan da aka gani a tattare da abin har yanzu suna da daure kai. Dr Hurley-Walker ta ce : ""Gano Karin wasu abubuwan dangane da wannan abu da yake fitar da wannan haske, zai kara wa kwararru fahimta su san cewa wannan wani abu ne guda daya tilo da ya faru ko kuma wata duniyar taurari ce ta daban da ba mu taba gani ba. Ta kara da cewa : ""Ina fatan kara fahimtar wannan abu sannan kuma mu kara fadada binciken domin gano Karin masaniya a kann abin.""" https://www.bbc.com/hausa/labarai-60161273 +technology Yadda CIA ke amfani da ruwa wajen yi wa jama’a tambayoyi "Wani masanin ilimin lafiyar kwakwalwa a Amurka wanda ya taimaka wa hukumar leken asiri ta CIA kirkiro wasu dabarun yin amfani da fasaha wajen yin tambayoyi, ya gabatar da jawabi gaban wata kotun soji da ke Guantánamo Bay. James Mitchell ya ce ya amince ya gabatar da bahasi ne kawai saboda iyalan mutanen da suka mutu a harin 9/11 suna kotun. Dr Mitchell da takwaransa Bruce Jessen sun samar da dabarun masu cike da takaddama ciki har da amfani da ruwa. Mutum biyar da ke tsare a Guantánamo na gab da fuskantar shari'a sakamakon hare-haren na 9/11. Mutanen biyar sun hada da Khalid Sheikh Mohammed, wanda ake zargi da kitsa hare-haren da aka kai kan Washington da New York a shekarar 2001. Mr Mohammed ya ce an sha azabtar da shi lokacin da yake tsare a gidan wakafi na Guantánamo Bay da ke Cuba. Wasu takardun hukumar CIA sun tabbatar da yadda aka rika azabtar da shi ta hanyar danna kansa cikin ruwa har sau 183. Sauran mutane hudun kuma - Walid bin Attash da Ramzi bin al-Shibh da Ammar al-Baluchi da Mustafa al-Hawsawi - suma sun sha tambayoyi a hannun CIA a wasu gidajen yari da ake kira ""black sites"" a Turance kafin a mika su hannun sojojin Amurka. Kafin fara sauraron shari'ar a Guantánamo, lauyoyin wadanda ake zargi na neman su samu hujjojin da wadanda suke karewa suka yi wa hukumar tsaro ta Amurka FBI, kuma aka yi watsi da su saboda dabarun tambayoyin da CIA ta yi amfani da su a kan mutanen. Tawagar 'yan uwan mutanen da harin 9/11 ya rutsa da su suna ganin yadda zaman kotun ke gudana duk da cewa an sa shinge kamar yadda jaridar New York Times ta ruwaito. Dr Mitchell, wanda ya bayyana a matsayin shaida, ya fadawa daya daga cikin lauyoyin masu kare kai cewa ya amince ya ba da bahasi ""ga 'yan uwa da wadanda harin ya rutsa da su. Ba ku ba"". ""Kun sha fadin abubuwa marasa tushe a kaina da Dr Jessen tsawon shekaru,"" in ji shi, a cewar Jaridar New York Times. Sai dai wadanda ake zargi sun kalle shi ne ba tare sun nuna alamun kaduwa ba, a cewar 'yan jarida. Ana sauraron za a ci gaba da sauraron shari'ar har tsawon mako biyu. Cikakkiyar shari'ar kuma an tsara gudanar da ita ne ranar 11 ga Janairun 2021. Ana zargin dukkanin mutanen biyar da aikata laifukan yaki har da ta'addanci da kisan kusan mutum 3,000. Idan har aka same su da laifi, za su iya fuskantar hukuncin kisa. Mece ce azabtarwa da ruwa? Wata hanya ce ta yin tambayoyi da ke sa wanda ake yi wa tambayoyin ya dandana yadda ake ji idan aka nutse a ruwa. Ana hada kan mutum da wani katako sannan a sa wani yanki a rufe bakin mutum. Ana zuba wa mutum ruwa a fuska, abin da ke sa mutum ya ji kamar huhunsa na cika da ruwa. CIA ta fara amfani da ruwa wajen samun bayanai daga wanda ake zargi da laifi tun bayan hare-haren 9/11. Wani kwamitin majalisar dattawa ya yanke cewa tsarin bai samar da bayanan sirri ba amma wasu jami'an CIA sun dage cewa tsarin ya bayar da bayanan da za su iya daukar mataki a kai. Tsarin ya sabawa doka. Shugaba Barack Obama ya haramta azabtarwa ta hanyar amfani da ruwa don yin tambayoyi a 2009. Shugaban Amurka Donld Trump kuma ya ce yana ganin yin amfani da tsarin zai yi tasiri saboda a cewarsa ""dole a yi hukunci ga masu muggan laifi daidai da laifinsu""." https://www.bbc.com/hausa/labarai-51206841 +technology Yadda ɗan adam ke rusa wuraren tarihi na duniya a yayin haƙar ma'adanai A duk lokacin da muka yi gini kasa domin haƙo ma'adanai, kamar ɗanyen mai ko duwatsu masu daraja, tamkar muna kawar da wani ɓari ne na tarihi. Kuma waɗannan ma'adanai su ne abin da marubuciya Astra Taylor ta kira 'dunƙulalliyar rayuwa da ta gabata'. Irin waɗannan abubuwa na ɗaukar miliyoyin shekaru kafin su taru a wuri guda, amma a yanzu ana amfani da na'urori ko nakiyoyi wurin wargaza su cikin 'ƙanƙanin lokaci. Tun bayan da ɗan adam ya gane cewa akwai arziƙi danƙare a ƙarƙashin ƙasa, yake ta haƙa domin lalubo abin da ke ciki. Haƙar ma'adanai ta taimaka wajen sauƙaƙa wa duk wasu ɓangarori na rayuwarmu ta wannan zamani, sai dai tasirin da haƙar ke yi ga asalin yadda duniya take ya yi ƙamari. Idan ka dubi tasirin da wuraren haƙar ma'adanai ke yi ga doron kasa, zai iya sauya tunaninka game da abubuwan da ka mallaka. Hatta yadda ake isar da wannan bayani - a bayan wannan na'ura da ka ke kallo, abubuwa ne waɗanda a baya suke damfare jikin duwatsu tsawon ɗaruruwan shekaru. Haka nan kuma yanzu haka a wani wurin irin wannan buƙata ta ƙarin ƙirƙire-ƙirƙire na ƙara ingiza mutane su ci gaba da binciken irin waɗannan ma'adanai da ke ƙarƙashin ƙasa. Gaba kadan za mu duba tarin hanyoyin da ha'kar ma'adanai ta sauya yanayin doron ƙasa - Idan ma'adanai da muke haƙowa na daga cikin abinda ya sanya duniya a baya ta kasance a kammale, to kuwa abubuwan da muke da su dankare a gidajenmu a yanzu wasu tabbai ne da ke nuna irin raunin da muka yi wa makomarmu. Dukkan hotunan na da haƙƙin mallaka. https://www.bbc.com/hausa/labarai-56446153 +technology Covid-19: BBC Africa ta ƙaddamar da shirin yaƙi da labaran ƙarya "Sashen da ke watsa labarai ga kasashen Afirka na BBC, BBC Africa, ya kaddamar da wani shiri na yaki da labaran karya game da cutar korona. BBC News Africa ta kaddamar da wani dakin karatu na shafin intanet wanda mutane za su iya dubawa domin ganin labaran cutar korona da aka bi diddigi wajen tantance sahihancinsu. Sashen BBC Africa da BBC Reality Check ne suka gina dakin karatun na intanet wanda ke kunshe da bayanai da ke karyata labarai kamar wanda yake cewa fasahar intanet ta 5G ta taimaka wajen yada cutar korona, ko kuma labarin da ke cewa akwai ""wata ilhama"" da ke warkar da cutar. Kazalika an fitar da bayanai cikin hotuna na yadda mutum zai tantance sahihancin labari wadanda za a wallafa a shafukan zumunta. Shugaban sashen labarai na Afirka a BBC, Solomon Mugera ya ce: ""Ganin yadda labaran karya kan annobar korona suke ta waɗari a nahiyar, muna so mu taimakawa masu bibiyarmu wajen raba tsaki da tsakuwa sannan mu ba su sahihan labarai."" A nata bangaren, Shugabar shafukan intanet na BBC Africa Digital Miriam Quansah ta ce: ""A yayin da 'yan jarida suke ci gaba da bayar da labaran irin tasirin da COVID-19 take yi a Afirka, wannan shiri zai taka muhimmiyar rawa wajen magance labaran karya ta hanyar bayar da sahihan bayanai.""" https://www.bbc.com/hausa/labarai-53012877 +technology Chang'e-5: Yadda China ta yi aike duniyar wata don a kwaso mata duwatsu "China ta ƙaddamar da wani shiri na ƙoƙarin ɗauko samfurin wasu duwatsu daga duniyar wata. Wani jirgin butun-butumi ne da aka ƙaddamar tare da harba shi a garin Wenchang zai yi wannan aiki idan kuma aka yi nasara zai dawo duniyarmu a tsakiyar watan Disamba. Kimanin shekara 40 kenan tun da Amurka da tarayyar Soviet suka ɗauko samfurin duwatsu da ƙasa daga duniyar wata domin yin nazari a kansu. China na ƙoƙarin zama ƙasa ta uku da za ta gudanar da irin wannan aiki, wanda zai zama aiki mai tattare da gwagwarmaya. Wani shiri ne mai cike da matakai daban-daban, da ya haɗar da matuƙin da zai kai na'urar falaƙi, da kuma na'urar Lander sai kuma daga ƙarshe ya dawo da sauran kayayyakin da aka yi amfani da su, a cikin fakitin domin dawo da shi cikin sauri da kuma sajewa da yanayin zafi a ƙarshen wannan aiki. Amma za a ƙara samun ƙwarin gwiwa bayan an kammaka aiwatar da wannan aiki da na'urar Lunar da aka fara aiwatarwa sama da shekara 10 da suka wuce ta hanyar amfani da tauraron ɗan adam. Chang'e-5 zai yi ƙoƙarin sauka a kusa da wani wuri da ake kira Mons Rumker, wani waje mai cike da duwatsu masu aman wuta a yankin da ake kira Oceanus Procellarum. Duwatsun da za a ɗauko a wurin ƙanana ne idan aka kwatanta da waɗanda masana ilimin taurari suka samo wa Amurka da Soviet a na'urarsu ta Lunar - misali waɗanda suka kai shekara biliyan 1.3 da kuma waɗanda suka kai shekaru biliyan 3 zuwa 4. Wannan zai bai wa masana kimiyya damar gane hanyar da za a yi amfani da ita a ƙara sanin abubuwan da suka shafi duniyar wata. Wannan butun-butumi na Chang'e-5 zai bunƙasa fahimtarmu game da tarihin duwatsu masu aman wuta da ke duniyar wata, in ji Dakta Katherine Joy da ke jami'ar Manchester. Ta shaida wa BBC cewa: ""An aika wannan na'ura ne zuwa yanki da a baya muka sani ana samun duwatsu masu aman wuta. Muna son sanin takamaimai yaushe hakan yake faruwa."" Lokacin da butun-butumin Chang'e-5 ya isa duniyar wata zai tafi ne kan layin falaƙi. Sai akwatun da ke ɗauke da shi ta sake shi ya sauka cikin yanayi mai ƙarfi. Yana sauka ƙasa, abubuwan da suke ciki za su fita su zagaye shi kafin su fara kwaso albarkatun ƙasa. Akwatun da ke ɗauke da shi da ake kira (Lander) na da ƙarfin yin haƙa a sararin wurin da za ta sauka, ko kuma ta yaye shimfiɗar da ke saman ƙasar. Abun hawan da ake amfani da shi, zai ɗauko samfurin ya dawo da shi tare da matuƙin falaƙin. Wani mataki ne da ke cike da haɗari da ya zama dole a ɗauke shi, za a haɗo duwatsun da ƙasar sannan a zuba su cikinwani mazubi a kawo wannan duniyar. Sai ayarin na'urar ya ɗauko ƙasar da aka zuba ya kawo ta cikin yankin Mongolia. Duka hanyoyin cike suke da haɗari, sai dai masu zane sun matuƙar sanin hanyar - hanya iri ɗaya ce da aka bi lokacin da mutane suka fara zuwa duniyar wata a shekarun 1960/70. China ta sanya azamar cimma wannan muradi. ""Za ka iya ganin bambanci tsakanin abin da aka yi na cimma burin butun-butumin Chang'e-5 - musamman bambaci tsakanin yadda sassansa suke da kuma yadda suke aiki tare da juna - da kuma abun da ake buƙata daga wurin dan adam,"" in ji Dakta James Capenter masanin kimiyya kuma jami'i a ma'aikatar samaniya ta Turai. Jonathan.Amos-INTERNET@bbc.co.uk and follow me on Twitter: @BBCAmos" https://www.bbc.com/hausa/labarai-55083842 +technology Dakin ajiye kayan tarihin CIA mafi sirri a duniya "Mai yiwuwa wannan shi ne gidan tarihi da ba a saba ganin irinsa ba a duniya, wanda aka cika shi da kayan tarihi da suka sauya duniya. Sai dai ba a barin al'umma su shiga cikin gidan. A nan wurin ne kawai masu ziyara za su ga bindigar da aka samu a wajen Osama bin Laden lokacin da aka kashe shi, kusa da wata rigar fata ta Saddam Hussein. Barkanmu da zuwa gidan tarihin sirri na CIA. A cikin ginin hedikwatar hukumar leken asiri ta Amurka yake a Langley Virginia. An sake yi wa gidan kwaskwarima a wani bangare na cikar hedikwatar shekara 75 da kafuwa. An bai wa wasu 'yan jarida kalilan damar shiga wurin ciki har da BBC, amma fa duka da jami'an tsaro ciki da waje da suka yi mana rakiya. Cikin kayan tarihi 600 da ake da su akwai sauran kayan aikin da 'yan leken asiri suka yi amfani da su a yakin cacar-baka - akwai wani bera da ake aika shi da sako a boye, akwai wata kyamara a jikin taba sigari da ake amfani da ita, ga wata tantabara da kyamarar leken asirin da aka makala a jikinta. Akwai kuma bayanai kan wasu ayyukan hukumar CIA da suka gabata da kuma na yanzu da ake yi. Akwai kuma hoton wani gini wanda aka gano Osama bin Laden a cikinsa a Pakistan. An nuna wa Shugaba Obama hoton ginin kafin ya amince akai harin da ya yi sanadin mutuwar shugaban na kungiyar al-Qaeda a 2011. ""Samun damar ganin abubuwa a jikin hoton fasahar tiridi (3D) yana taimakawa masu tsara dokoki... da kuma mu kanmu kan yadda za mu tsara ayyukanmu,"" kamar yadda Robert Z byer Daraktan gidan da ya zagaya da mu ya shaida mana. A ranar 30 ga watan Yulin wannan shekarar wani harin makami mai linzami ya kara dira cikin wani gida, amma a wannan karon ya samu sabon shugaban kungiyar al-Qaeda ne Ayman Zawahiri. Harin ya samu Zawahiri ne cikin wata baranda, bayan jami'an hukumar leken asiri ta Amurka sun kwashe watanni suna nazartar abubuwan da yake yi. ""Harin ya nuna karara yadda jami'an yaki da ta'addanci suka fahimci rayuwar Zawahiri,"" in ji Mista Byer. An tsara bangaren farko na gidan tarihin ne daga abubuwan da suka soma faruwa - kamar kafa ita hukumar a 1974 zuwa yakin cacar-baka, zuwa harin 11 ga watan Satumbar 2001, har da makaman da 'yan uwan wadanda aka kashe suka kawo a matsayin gudunmawa. Wadanda suke sauraren bayanin jami'an hukumar CIA ne da kuma jami'an da suka zo ziyarar. Bayanan ba su takaita ba kawai a kan nasarori, a'a akwai bangaren da yake magana a kan harin da CIA ta kai domin kifar da gwamnatin Fidel Castro a Cuba wanda bai yi nasara ba, akwai kuma hujjoji da gazawar da suka yi na nemo makaman kare-dangi a Iraki. ""Wannan ba za mu kira shi gidan tarihi ba kawai. Akwai bangaren ayyuka da muke nuna wa jami'an CIA, domin bankado tarihinmu masu kyau da marasa kyau,"" in ji Mista Byer. ""Muna tabbatar da cewa jami'anmu sun fahimci tarihinsu, domin su yi ayyuka masu kyau nan gaba. Za mu dauki darasi daga nasarorinmu, da kuma gazawarmu domin a gaba mu gyara."" Wasu daga cikin ayyukan CIA da ba a fiye ji ba ko gani - kamar su aikin hadin gwiwa da M16 domin kifar da gwamnatin dimokuradiyya da aka zaba a Iran da kuma na baya-bayan nan wanda ya hada da azabtar da mutanen da ake zargi da hannu cikin harin ta'addancin 2001. Bangare na biyu na gidan tarihin ya mayar da hankali kan wasu ayyuka na musamman. Kalmar da muke cewa 'Ba za mu iya tabbatarwa ba ko kuma mu musanta' kalma ce da wadanda suke tattarowa hukumar leken asiri bayanai, kuma an samo asalinta ne daga wani tarihi a cikin gidan wanda ake amfani da shi da ba a taba gani ba kafin yanzu. A karshen shekarun 1960, wani jirgin ruwan Tarayyar Sobiyet ya bata a wani wuri a teku. Bayan Amurka ta gano inda yake, CIA ta yi aiki da wasu manya-manyan kayayyakin fasaha domin gano tarkacensa da kuma fasahar da aka tattara cikinsa. Gidan tarihin yana kunshe da samfur na jirgin karkashin teku na Tarayyar Sobiyet da kuma tufafi, da kuma tire na ajiye guntayen taba. Akwai wani gashin doki da mataimakin daraktan CIA ya sanya domin yin bad-da-sawu yayin da ya kai ziyara wurin da jirgin yake. Nasarar da aka samu a wannan aikin ba ta da yawa saboda jirgin ya karye ko da yake an samu wasu sassansa. ""Galibin abubuwan da aka samo a cikin jirgin karkashin tekun har yanzu ba a bayyana su ba,"" a cewar Mr Byer. Lokacin da labari ya fita game da ake kira Project Azorian kafin a fitar da sauran sojojin ruwa, an shaida wa jami'ai su bayyana cewa ba ""za su iya tabbatarwa ko musanta"" abin da ya faru ba - wani zance da a yanzu aka fi sani da ""Glomar response"" kuma har yanzu ana amfani da shi. Akwai kuma wasu kayayyaki da aka tsara wasan kwaikwayon bogin nan mai suna Argo. Hakan ya bayar da dama wajen ceto wasu ma'aikatan difilomasiyya da aka tsare a Iran bayan juyin-juya halin 1979, abin da daga bisani aka juya shi zuwa fim din Hollywood. An baje-kolin wasu kayayyaki da aka tsara wajen yin fim din na bogi wadanda ma'aikatan difilomasiyyar da aka tura can kasar suka yi ikirarin yi. An tsara zane-zanen kayyakin ne ta yadda da wahala mutum ya fahimci sakon da ke cikinsu. Kuma da yake muna magana ne a kan fahimtar sakonni, a silin din gidan tarihin akwai wasu sakonni da ke dauke da wasu lambobi masu wahalar fahimta. Burin jami'an CIA shi ne a rarraba wa jama'a bayanan a shafukan sada zumunta domin ganin ko za su iya fahimtar su. Kazalika za a wallafa wasu daga cikin bayanan a shafin intanet. Don haka a iya cewa wadannan bayanai su ne mafi girma da mutane suka ganin game da hukumar leken asirin." https://www.bbc.com/hausa/articles/crg2j84e0m6o +technology Teloli na son mayar da Nairobi wani sabon birni na zamani ta fuskar tufafi A jerin wasikun da muka samu daga 'yan jaridun Afirka, Ismail Einashe ya ziyarci wasu shaguna biyu da ake amfani da matattun tsummokara domin dinka wasu sabbin nau'ukan kayan amfanin yau da kullum da kuma sabbin nau'ukan sutura. A yayin da gari ya yi lumshi a Nairobi babban birnin kasar Kenya, na ga wasu teloli guda biyu na amfani da keken dinki wajen harhada nau'ukan kayayyakin amfani kamar jakar daukar kaya, a jikin bangon shagunan kuma ana iya ganin wasu jakunkuna da aka jera wadanda aka dinka daga tsofaffin sutura. Wannan aikin da telolin ke gudanarwa a wani shago da ke unguwar Suave, wanda ke hawa na biyu na ginin Charming wanda aka yi wa fenti da launin fari da shudi, da Mohamed Awale, ya gina a shekarar 2013. Wannan shago na daya daga cikin manyan shagunan dinka kayan jakunkuna. Suna amfani da matattaun kayayyaki wajen mayar da su kayayyakin amfani kamar jakunkunan adana kaya, da jakar daukar kaya, da kananan abubuwa kamar su karamar jakar sa kudi, da karamar jakar adana hotuna. Haka kuma wannan shago ya zama wani wajen sarin kaya ga 'yan kasuwar Gikomba, daya daga cikin manyan kasuwannin kayan gwanjo a yankin gabashin Afirka, ya ce ya fara wannan sana'a ne domin rage matattun tufafi a kasar. Telolin suna mayar da kayan gwanjo kamar su wandunan jeans da kananan riguna, da rigunan kwat wadanda aka shigar kasar daga Amurka ko Turai zuwa wasu abubuwa masu masu matukar amfani ga dalibai da matasan kasar. Telan ya ce ya fara sana'arsa ne a wani dan karamin daki da ke harabar babban shagon nasa, kuma daga wannan lokacin ne kasuwancin nasa ya ci gaba da habaka. Sana'ar Awale ta ja hankalin manyan kamfanonin tallata kayayyaki ta intanet kamar su Google ya kuma rika sayar da kayayyakinsa zuwa kasashen waje. Kuma a farkon wannan shekarar ya samu tallafin karo karatu daga wata gidauniya mai suna Ethical Fashion Initiative, inda ya je ya yi wani kwas na wata biyu a birnin Florence na kasar Italiya, inda ya samu horo a fannin dinka jakunkuna da dangoginsu, tare da kuma samun horo kan yadda zai habaka sana'arsa. A daya gefen kuma wani katafaren shagon sayar da dinkakkun tufafi ne a wani babban mai dinka tufafi mai suna Kepha Maina. Ya kafa shagon nasa ne a shekarar 2013, wanda kuma yake gudanarwa daga zauren gidansa da ke tsakiyar birnin Nairobi. Maina ya samu kwarin gwiwar wannan sana'a tasa ne daga kayayyakin da manyan masu sana'ar hannu na yankin gabashin Afirka kamar su Ibrahim el-Salahi, wani fitaccen mai sana'ar fenti na kasar Sudan. Sabanin masu irin wannnan sana'a a biranen Paris da Milan, a Nairobi ba a gudanar da bikin baje-kolin irin wadannan kayayyaki saboda karancinsu a a kasar. A yanzu dai Maina ya fitar da sabbin kayan ya yi guda hudu, kuma cikin watan Satumba zai kaddamar da wani sabon nau'in ya yi na zamani, inda ya ce zai samar da sabbin nau'ikan tufafi na zamani da za su dace da al'umar kasar. Sai dai matsalar da masu sana'a irin wannan ke fuskanta a Kenya ita ce mafiya yawan al'umar kasar ba sa sayen sababbin nau'ikan tufafi na zamani wadanda 'yan Kenya suka dinka, a maimakon haka sun fi mayar da hankali kan nau'ikan da aka shigo da su daga kasashen ketare. Duk da wannan kalubale da masu irin wannan sana'a irin su Maina ke fuskanta, a cikin 'yan shekarun nan an fahimci cewa ana samun yawaitar masu irin wannan sana'a a birnin Nairobi abin da ke alamta cewa al'umar kasar suna fara karbar hajojin nasu. https://www.bbc.com/hausa/articles/c0vgnnv9lzro +technology Matashin da ke ɗaukar nauyin karatunsa ta hanyar zana hotunan mutane a Kano Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon: A yanzu matasa a arewacin Najeriya na zaburowa don magance matsalar neman ilimi ta hanyar samun aikin yi don ɗaukar nauyin karatunsu ba tare da jiran iyayensu sun yi musu ba. Da yawansu sun gwammace su nemi sana'ar hannu don ɗaukar nauyin kawunansu. Abbas Nabayi mai shekara 24 na daga cikin irin waɗannan matasa. Yana zana hotunan mutane da sauran abubuwa, inda yake sayarwa yana amfani da kuɗin wajen ɗaukar nauyin karatunsa. Yanzu yana karatun samun shaidar NCE ne a Kano. Ya shaida wa BBC tsare-tsaren da yake yi don inganta rayuwarsa a nan gaba. https://www.bbc.com/hausa/media-58186837 +technology Azare: WhatsApp ya taimaka an gano yarinyar da ta bace tsawon shekara hudu "Iyayen wata ƙaramar yarinya da aka yi zargin an sace a garin Azare na jihar Bauchi, suna ci gaba da murnar sake ganin 'yarsu Zainab bayan kimanin shekara huɗu. Hukumomi ne suka shiga tsakani wajen karɓar yarinyar wadda a yanzu ta kai shekara bakwai daga hannun wadanda suka riƙa kula da ita a garin Giade, bayan mahaifanta na ainihi sun gano ta, ta hanyar WhatsApp. Sun ce sun samu labari ne ta WhatsApp cewa akwai wata yarinya a garin Giade da aka taba tsinta tana ƴar shekara uku, sai suka buƙaci ganin hotunanta, sai aka rura musu ta WhatsApp ɗin. Daga nan ne suka gane ƴarsu ce, sai suka niƙi gari suka tafi garin Giade mai nisan tafiyar minti 15 a mota dag Azaren don ganowa da idonsu. Satar ƙananan yara na ƙara zama ruwan dare a wasu birane da garuruwan arewacin Najeriya. Mahaifin Zainab, Mallam Sama'ila Haruna ya ce bai taɓa fitar da ran sake ganin 'yarsa ba, duk da yake sun yi imanin cewa sace ta aka yi a farkon 2018. Ya ce sun yi ta neman Zainab 'yar shekara uku kafin ɓacewarta, inda nema ya kai shi har zuwa birnin Kano da Gombe, bayan samun rahoton gano wasu ƙananan yara a hannun mutanen da ake zargi sun sace su can a baya. Rashin magana na Zainab lokacin da aka tsince ta, ya sa cigiyar iyayenta na asali ya zamo wani abu mai matuƙar wahala, mai yiwuwa saboda ƙarancin shekaru da kuma ɗimuwar da ta shiga. Lokacin da suke ƙoƙarin karɓar 'yarsu, Mahaifin Zainab ya ce shaida wa BBC cewa sun same ta cikin kyakkyawan hali tare da yaba wa wanda yarinyar ke hannunsa bayan sun je garin Giaɗe. ""Ya riƙe ta kamar ƴarsa ta cikinsa, ya yi ɗawainiya da ita tare da ba ta tarbiyya mai kyau domin ba ta da wani alamar yunwa ko wahala, kuma ba ta canja kamanni ba sai girma da ta ƙara,"" in ji shi. Mutumin da ya riƙe Zainab tsawon shekara huɗu, Ahmed Adamu Giaɗe, Mai Dalan Giaɗe, ya ce an tsinto yarinyar a halin gigita da askakken kai a tsakiyar dare. Bayan mahukunta sun nemi ya riƙe ta ne, sai ya raɗa mata suna Aisha, kuma ya saka ta makarantar Boko da Islamiyya. ""Mun yi wa iyayenta na asali murnar samun ƴarsu amma ba ƙaramin tashin hankali muka shiga ba ni da iyalina saboda ɓacin ran rabuwa da ita,"" in ji Ahmed Adamu Giaɗe wanda ya riƙe Zainab. Mahaifiyar yarinyar, Rabi'a Ahmed ta ce sai da ta yi kuka a lokacin da ta sake haɗa ido da 'yar tata, saboda farin ciki. Iyayen yarinyar sun ce ta fita gida ne, kuma tun da ta fitan ba su sake ganinta ba. Ofishin kyautata jin daɗin al'umma na ƙaramar hukumar Giaɗe ya ce sun tantance duk shaidun da mahaifan Zainab na asali suka gabatar kafin su ɗauke ta, tare da damƙa ta hannun ƙaramar hukumar Azare wadda ita kuma ta miƙa yarinyar ga iyayenta. Auwal Ahmad Giaɗe mataimakin shugaba a ofishin kyautata jin daɗin al'umma na Giaɗe, ya ce yarinyar tana kama da mahaifiyarta kuma da farko ba ta gane mahaifiyarta ba sai daga baya da hankalinta ya dawo ta faɗa da bakinta cewa wannan mahaifiyarta ce. Ba duk iyayen da suka rasa ƴaƴansu ba ne ke katarin sake ganinsu ba. Mahaifan Zainab dai sun yi matuƙar auna arziƙi, bayan Allah ya kuɓutar da ƴarsu kuma ya damƙa ta hannun na gari. Uwar Zainab ta ce a shekarar da 'yarta ta ɓata, an yi fama da ɓata ko satar ƴaƴa a garin Azare. Kuma a baya-bayan nan ana ƙarin damuwa a birane kamar Kano game da ɓata ko satar ƙananan yara." https://www.bbc.com/hausa/labarai-59583703 +technology An amince Elon Musk ya sayi Twitter a kan $44bn "Shugabannin gudanarwar kamfanin Tuwita sun amince a sayar wa attajirin nan Elon Musk kamfanin kan dala biliyan 44. Mr Musk, wanda sanarwar sa ta son sayen kamfanin a makon jiya ta girgiza mutane, ya yi ikirarin zai iya bunkasa kamfanin ya ci gaba. Ya kuma sanar cewa zai kawo gagarumin sauyi a kamfanin — kama daga duba sahihanci abubuwan da ake wallafawa zuwa magance matsalar shafukan bogi. Tun da fari shugbannin kamfanin sun ki amincewa da tayin Mr Musk, na siyan kamfanin, amma daga bisani shawara ta sauya bayan an kada kuri'a tsakanin masu hannayen jari a Tuwita. Mr Musk dai shi ne attajiri mafi arziki a duniya, kuma kamar yadda mujallar Forbes ta bayyana, an yi kiyasin arzikinsa da ya kai dala biliyan 273.6b, yawanci saboda hannayen-jarin da yake da su a kamfanin Tesla mai kera mota da ke aiki da lantarki, wanda kuma shi ke gudanar da shi. Sai kuma jarin da yake da shi na jagorantar kamfanin da ke zuwa sararin samaniya na SpaceX. ""'Yancin fadar albarkacin baki, shi ne kashin-bayan ingantacciyar dimukradiyya, kuma Tuwita duniya ce guda da ta kunshi mutane daban-daban, da kuma ke tattaunawa kan batutuwa da tafka muhawara kan makomar dan adam,"" in ji Mr Musk cikin sanarwar da ya fitar da ya bayyana kammala cinikin. ''Ina kuma son inganta Tuwita fiye da lokutan baya, ta hanyar inganta abin da ake yadawa, da kara hanyoyin inganta abubuwan da ake yadawa wanda zai kara sanya yadda tsakanin mau bibiyarmu, da magance labaran karya, da inganta abubuwan da suka shafi dan adam,'' in ji shi. ""Tuwita na da matukar amfani, ina farin-ciki da zakuwar aiki tare da kamfanin da masu bibiyar shafin domin kara bunkasa shi."" Shugabar gudanarwar Tuwita Bret Taylor, ta ce ta yi cikakken aiki domin ganin kamfanin ya duba bukatar Mr Musk. Shugabannin gudanarwar kamfanin Tuwita sun amince a sayar wa attajirin nan Elon Musk kamfanin kan dala biliyan 44." https://www.bbc.com/hausa/labarai-61224206 +technology Facebook ya hana dubban manhajoji aiki a shafinsa Hukumomi sun tuhumi Cambridge Analytica da amfani da bayanan sirrin domin samar da tallace-tallacen siyasa da suka yi kokarin sauya wa ra'ayinsu kan mutumin da ya fi dacewa su zaba ya jagoranci kasashensu. A sanadiyyar badakkalar Cambridge Analytica, hukumar samar da daidaito a ciniki ta Amurka ta ci tarar Facebook dala biliyan 5 a watan Yuli. Wannan ne mataki irinsa mafi girma da aka taba cin wani kamfani da ya taka dokar boye bayanan sirrin masu hulda da shi. Badakkalar Cambridge Analytica - wadda ta shafi dubban miliyoyin mutane ya dagula wa Facebook lissafi matuka, kuma har yanzu yana fuskantar shari'a daga mutane da kamfanonin da abin ya shafa. A kan haka ne ya dauki wadansu matakan yin gyara ga yadda ya ke aiki da kuma gyara barnar da batun yayi wa dangantakarsa da masu amfani da shafin sada zumuntarsa mai matukar farin jini. A bara Facebook ya kaddamar da wani bincike kan yadda a kan yi amfani da manhajoji wajen sarrafa bayanai daga shafin nasa. Kuma ya fara da dakatar da manhajojin wasu kamfanoni 400 ne, amma ya ce ba duka manhajojin ne suka kasance masu hadari ga masu amfani da Facebook din ba. Kamfanin Facebook ya fuskanci matsanancin matsin lamba a shekarar 2018 bayan da aka bayyana cewa wani kamfani mai suna Cambridge Analytica ya yi amfani da bayanan mutane ba tare da izini ba. Har yanzu Faceook ya ci gaba da gudanar da wannan binciken, kuma bai ajiye lokacin da zai kammala shi ba. https://www.bbc.com/hausa/labarai-49779358 +technology Masana kimiyya sun yi katarin samun hoton duniyar jupiter "Masana ilimin taurari sun samar da wani sabon hoto na Jupiter da ke bibiyar yankuna masu dumi da ke buya a saman giza-gizai. Kamfanin Gemini North Telescope mai sanya ido kan taurari ne ya dauki hoton a Hawaii, wanda wannan ne sanya ido ne mafi daidai da aka yi a duniya da aka taba yi tun daga tushe. Domin cimma wannan buri na dauko hoton, masana kimiyya sun yi amfani da wata dabara da ake kira ""lucky imaging"" wanda ya nuna yadda duniyar take cikin yanayin dishi-dishi. Wannan hanyar ta hadar da samar da kariya daga abin da aka hara tare da tarrara bangarorin hoton inda iska ke matsakaiciyar kadawa. Yayin da aka dauki duka hotunan an hada su waje daya cikin wani zane, wanda ya samar da wani abu da ya fi hoto guda daya. Hoton da aka dauka na zanen duniyar, ya fi irin wanda aka saba gani na (Hubble telescope) taurari tsayi. Ana iya ganin wucewar hazo da kuma 'yan kanan giza-gizai a saman duniyar ta Jupiter, wanda zai bai wa masana kimiyya damar zurfafa bincike kan yadda cikin duniyar yake. Masu bincike na son kara fahimtar mene ne ke samar da tsarin yanayin a duniyar, kuma takamaimai doguwar guguwar da ake samu da takan kai shekara 20 zuwa 100. Cibiyar California da ke Berkeley ce ta jagoranci wannan binciken da ya samar da hoton zanen bakin wutar. Kuma wani bangare ne na wani shirin hadin gwiwa da ya hadar da Hubble da kuma Juno masu bibiyar sararin samaniya wadanda yanzu haka ke bibiyar duniya ta biyar daga rana. Abin da za mu sani game da duniyar Jupiter Jonathan.Amos-INTERNET@bbc.co.uk and follow me on Twitter: @BBCAmos" https://www.bbc.com/hausa/labarai-52619521 +technology Janar din Uganda mai nuna ci da zuci a Twitter "Bayan horo da ya samu daga makarantun horas da sojoji masu daraja na duniya, dan gidan shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni ya zama janar din soja wanda yayi kaurin suna wajen aike sakonnin Twitter da ke janyo ce-ce-ku-ce daga ciki da kasar da kuma sauran sassan yankinsu. Janar Muhoozi Kainerugaba ya cika baki kan cewa sojojinsa za su iya kama Nairobi babban birnin kasar Kenya, cikin kasa da mako biyu, ya kuma ja wa Masar da ke hamayya kunne kan cewa Uganda za ta iya shiga duk wani yaki na yankin arewacin Afirka, daya bangare da ya nuna sha'awa a kai shi ne gadar mahaifinsa mai shekara 78. Ya ki bin umarnin da aka ba shi na ya daina janyo hayaniya a Twitter yana cewa: ""Na mallaki hankalin kaina babu wanda zai hanani komai!"". Wani dan jaridar Uganda Solomon Serwanjja ya ce sakonnin Twitter da Janar Kainerugaba ke aike wa - na nufin ""madaukin fansa"" - da yake aikin soji da burin siyasa. ""Yana so ya tabbatarwa magoya bayansa cewa yana da 'yancin yanke hukuncin da ya ga dama. Kazalika zai zama dan da ke ci gaba da mayar da hankali ga umarnin mahaifinsa,"" in ji shi. Mahafinsa Mista Museveni da ke kan mulki tun 1986, ana zargin ya dade yana horas da dan nasa mai shekara 48, domin ci gaba da mulkin da ake zargin sun mayar na mulukiya a Uganda. ""Iyalin da ke juya Uganda. Mahaifiyarsa na kan gaba, shi kuma shi ne yarima, da ke jiran gadar mahaifinsa,"" in ji Peter Kagwanja da ke cibiyar siyasa ta Afrika da ke Kenya.\n\nKamar yadda shugaban Amurka Donald Trump ya taba yi, shi ma Janar din yana amfani da Twitter ne domin daga likafarsa. Farfesa Kagwanja na yi masa kallon ""wakilin da zai iya tayar da hayaniya"" wanda sakonninsa na Twitter ke kai wa ga shugabannin Afrika, su kuma kara habbaya abubuwan da siyasar Uganda ta sa a gaba, ""Muhoozi ya fusata, sannan mahaifinsa ya nemi ya je ya nemi afuwa, ta haka ne aka gabatar da shi cikin zagayen wadanda za su iya zama shugabannin."" Manufarsa ta bayyana a fili ne lokacin da Janar Kainerugaba ya fusata da gwamnatin Habasha, lokacin da ya fito fili ya nuna goyon bayansa ga Masar a lokacin da dangantaka ta yi tsami tsakanin da Habasha kan kan madatsar ruwa ta kogin Nilu. Nesa da mayar da shi saniyar ware a Habasha, daga Twitter da ya aike ya ba shi damar ziyartar Firaiminista Abiy Ahmed da kuma wasu manyan jami'ai a farkon wannan shekarar. Hakan ya sanya Janar ya sauya salonsa, ya yabi Mista Abiy mai shekara 46 a matsayin dan uwa, yana cewa: ""Mun yi imanin cewa matsalolin Afirka za a warware su ne kawai daga Afrika"", yana bayyana ra'ayinsa da yayi daidai da na shugaban Habasha kan cewa masu kishin ci gaban Afirka ne. Janar Kainerugaba da ke amfani da sunan ahalinsu, yana bayyana yadda yake ganin shugabannin Afrika a matsayi daban daban da kuma yadda alakarsu take. Ya bayyana shugaban Rwanda Paul Kagame a matsayi ""Kawuna"" kuma ya ziyarce shi a gonarsa. Lokacin da wani rikici ya sanya aka rufe iyakar Rwanda da Uganda, ya yi kokarin dawo da alakar kasashen biyu ta hanyar hada zama tsakanin mahaifin nasa da ""kawun nasa"". Yayin da abubuwa suka zo kan Kenya, Janar Kainerugaba ya wallafa cewa ya tattauna da tsohon shugaban kasar Uhuru Kenyatta bayan ya sauka a karshen wa'adin mulkinsa biyu da ya yi a watan Agusta. ""Matsala daya dai ita ce Kawuna bai nemi wa'adin mulki na uku ba. Da mun ci mulki cikin ruwan sanyi!"" Wannan ya janyo koke-koke a tsakanin mutanen Kenya a Twitter, wadanda suka rika zargin Janar din da neman dakile musu dimokradiyyarsu. Mista Museveni ya fi son Willian Ruto, wanda ya lashe zaben kasar a wani yanayi mai cike da bacin rai. ""Sakon Twitter na nuna gamsuwa da Kenyatta, da ba su so rasa shi ba saboda muhimmancin da yake da shi a siyasar Kenya,"" in ji Farfesa Kagwanja. ""Mahaifin da dan sun rika aiki tare a baya. Muhoozi ya gabatar da kansa a matsayin mai hamayya da mahaifinsa, ta yadda ya zama mai yawan janyo ce-ce-ku-ce, domin nuna mahaifinsa mutumin kirki ne."" Bayan kammala makarantar sojoji da ya yi ta Sandhurst a Birtaniya, Janar Kainerugaba ya fara darewa mukaman soji a Uganda, wanda ya shiga rundunar a 1999. Yana da matar aure tare da 'ya'ya uku, kuma ya bayyana biyayyarsa ga addinin Kirista da kuma kimar iyalansa a Twitter. Ya taka muhimmiyar rawa a wajen ilmantar da dakaru na musamman da ake kira SFC da ke ba da tsaro ga mahaifinsa, wadanda ake yawan zarga da take hakkin dan adam - ciki har da tsarewa tare da azabtar da 'yan adawa. ""A 2008 Muhoozi ya tashi ne cikin dakarun da suke bai wa mahaifinsa tsaro, wani matsayi da ya rike har 2017. Ya koma cikin tawagar a 2020 lokacin rikicin zabe,"" kamar yadda wani dan jarida Musinguzi Blanshe ke cewa. Mista Serwanjja ya ce bayan korarsa da aka yi a matsayin kwamandan sojin kasa, babu wanda zai iya fada maka irin tasirin da yake da shi a rundunar sojin kasar. Abin da ya bayyana shi ne Mista Museveni ya nuna fatan da yake da ita, cewa shi ne dan nasa ya gaje shi a zaben 2026 bayan duka abokansa - ciki har da mataimakin shugaban kasa da ministan cikin gida sun nuna goyon bayansu na ya dare bisa mukamin. Wannan wani lokaci ne a baya da ya yi murnar cikarsa shekara 48 a duniya a watan Afrilu, kuma goyon bayan da ya samu daga wurare daban-daban ya kara daukaka likafarsa tsakanin matasa." https://www.bbc.com/hausa/articles/c72z56lg1pgo +technology Yadda ma'aikatan BBC ke wallafa maku labarai a intanet Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon: Allah Ya kawo mu karshen shekarar 2019. Shin kun san yadda ma'aikatan BBC ke gudanar da ayyukansu na wallafa maku labarai a shafinmu na intanet da kuma na shafukan sada zumunta? Kallon wannan bidiyon zai ba ku karin haske. https://www.bbc.com/hausa/labarai-50907706 +technology Bidiyo: Makahon da ya yi fice a gyaran injin janareta Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon: Hausawa kan ce himma ba ta ga rago, wannan wani mutumi ne da ke zaune a birnin Kano wanda tawayar da yake da ita ta makanta ba ta hana shi zagewa ya nemi na kansa ba. Dubban masu larura irin tasa musamman a arewacin Najeriya kan rungumi harkar bara ne a duk lokacin da suka samu kansu a irin wannan hali, sai dai Malam Garba Abdullahi ya ce babban fatansa shi ne ganin ya samu na kansa. https://www.bbc.com/hausa/labarai-59795959 +technology Yadda za ku kula da tarbiyyar yaranku yayin karatu a intanet "Tun bayan da annobar korona ta ɓulla a kasashen duniya, an kulle kusan duka makarantu a duniya a yunƙurin daƙile yaɗuwar wannan cuta. Hakan ya tilasta wa ɗalibai da dama amfani da intanet domin ci gaba da karatu. Makarantu da dama a faɗin duniya sun fito da tsare-tsare ta yadda ɗalibai za su iya amfani da wayoyin salula ko kuma kwamfuta wajen karatu da kuma yin sauran ayyukan da malamansu kan ba su. Amma sai dai sakar wa yaran ragamar amfani da intanet ya jawo koma baya ta fannoni da dama a irin wannan lokaci inda akasarin iyaye ke koka wa kan cewa yaran sukan yi amfani da intanet wurin shiga wuraren da ba su kamata ba. Binciken da masana suka yi ya bayyana cewa tun farko ba a tsara intanet ba ta yadda yara za su yi amfani da ita, sakamakon sauyin zamani da kuma shigowar shafukan sada zumunta ya sa yara ƙanana suka samu damar amfani da intanet. Haka zalika, na'urorin zamani na da ɗaukar ido musamman ga yara wanda hakan na da wahalar raba su amfani da na'urorin. Wasu daga cikin iyayen yaran sun shaida wa BBC cewa suna bai wa yaransu wayoyi su yi karatu amma tare da sa ido na iyayen. Iyayen sun shaida mana cewa sukan tsare yaran a tare da su, kuma su sa musu ido har su gama domin gudun samun wata matsala. Dangane da wannan batu na sakar wa yara wayoyi da kuma kwamfuta sakaka, BBC ta tattauna da Abdullahi Salihu Baban Saddiq, wani ƙwararre kan harkokin intanet a Najeriya kuma ya bayar da shawarwari biyar kan yadda iyaye za su sa ido ga yaransu masu amfani da intanet. 1- Bibiyar abin da yaro ya ke yi Abdullahi Salihu ya bayar da shawara ga iyaye kan cewa ya kamata a kullum ya zamana suna bibiyar abubuwan da yaransu suke yi a shafukan intanet. A cewarsa, akwai hanyoyi da dama ta yadda iyaye za su iya bin diddigi da kuma bibiyar wasu daga cikin abubuwan da yaransu suke yi, idan sun yi hakan, a kalla za su san wane hali yaran ke ciki. A cewarsa, yana da kyau iyayen yara su san yadda za su buɗe wayoyin yaransu da kuma kwamfutocinsu, ma'ana su san ""password"" dinsu. Haka zalika iyayen su rinƙa shiga e-mail din 'ya'yansu domin duba da wa suke hulda kuma ta hakan za su iya sanin wasu shafukan da yaran nasu suka yi rajista da su. 2- Bibiyar abokan yara na shafukan sada zumunta A halin yanzu, shafukan sada zumunta su ne mafi sauki na yin abokantaka da mutane a faɗin duniya, jama'a daga nahiyoyi daban-daban kan iya yin abota sakamakon yadda intanet ta zagaye duniya. Ya bayyana cewa ""a intanet din mutum zai haɗu da wanda ya sani da wanda bai sani ba da wanda ake ƙasa ɗaya da wanda ba a ƙasa ɗaya ba duk ana haɗuwa"". Masana harkokin intanet na ganin ya kamata iyaye su rinka sa ido kan waɗanne irin abokai yaransu ke hulɗa da su a intanet. Ana yawan samun masu mugayen ɗabi'u da 'yan kungiyoyin asiri da 'yan zamba cikin aminci ta intanet. Masana na ganin abu ne mai sauƙi a dulmiyar da yara cikin irin waɗannan ɗabi'u. 3- Ilmantar da yara kan munin intanet A kowane lokaci, masana harkokin intanet na yawan jaddada cewa intanet na da amfani da kuma rashin amfaninta ko kuma muninta. Sanin muninta zai taimaka wa mutum matuƙa wurin sanin yadda zai iya amfani da ita. Abdullahi Salihu ya bayyana cewa ya kamata iyaye su rinƙa ilmantar da yaransu ko kuma wayar musu da kai kan munin intanet domin sanin illolinta. Ya ce akwai abin da ake kira intanet ""internet black hole"", wanda a cewarsa ""wuri ne mafi muni a intanet wanda idan mutum ya faɗa ciki ba zai iya fitowa ba, wuraren sun haɗa da wuraren batsa da caca da cuta da sauransu"". Ya ce illolin sabo da shiga irin waɗannan wurare kan yi tasiri ga mutum ƙwarai inda idan aka fara ba za a iya daina wa ba har mutum ya tsufa. Dakta Zahra'u Umar, Malamar addini ce kuma kwamishinar harkokin mata ce a jihar Kano ce inda a tattaunawarta da BBC, ta bayar da shawarwari ga iyaye a matsayinta na uwa kan yadda za su rinƙa lura da yaransu yayin da suke amfani da intanet. A cewarta, a kullum ya kamata iyaye su rinƙa tsayawa tare da yaransu a lokacin da suke karatu da waya, ta bayyana cewa a matsayinta na uwa, a duk lokacin da yaronta zai yi karatu, takan tsaya a kusa da shi domin sa ido. A cewarta, babban abu da ya kamata a ce ana yi wa yara shi ne wa'azi kan illolin intanet, ma'ana a nuna musu illoli da kuma faɗa musu abin da bai kamata su yi ba. Ta bayyana cewa dan autanta shekararsa 13, kuma idan zai yi karatu tana zama tare da shi ta taimaka masa wurin neman ilimi ana wasa da dariya. BBC ta kuma tattauna da wata uwa wadda ba ta so a bayyana sunanta inda ta bayyana cewa, tana ƙokarin duba wayoyin yaranta domin sanin waɗanne irin manhajoji ne a ciki da za su iya kai su hanyoyin da ba su da amfani. Ta kuma bayyana cewa takan saka kanta a ɓoye cikin dandalin ajin yaranta na whatsapp domin sanin me suke tattauna wa a ciki." https://www.bbc.com/hausa/labarai-52922636 +technology Boeing ya dakatar da kera jirgin 737 Max "Kamfanin jiragen sama na Boeing zai dakatar da kera samfurin jiragensa na 737 Max a farkon shekarar 2020 mai kamawa. A baya Beoing ya cigaba da kera jiragen 737 Max, bayan dakatar da tashin jiragen na tsawo wata tara, sakamakon wasu munanan hadura da jiragen suka yi. Akalla mutum 300 ne suka mutu a hadarin da wasu jiragen Beoing 737 Max suka yi a Indonesia da Ethiopia sakamon wata sabuwar matsala. Kamfanin ya yi fatan ci gaba da kera samfurin jiragen a karshen shekarar nan ta 2019. Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Amurka ta sheda wa Boeing cewa ba za a yi sauri wurin ba wa jiragen izinin fara tashi ba. Boeing wanda ke daga cikin kamfanonin Amurka da ke fitar da kaya zuwa kasuwannin duniya, ya ce ba zai sallami ma'aikatansa da ke da alaka da jiragen 737 Max. Sai dai da alama dakatar da jiragen na iya yin tasiri a kan dillalai da ma tattalin arzikin kasar. Me ya samu jiragen 737 Max? A makon jiya ne aka sheda wa majalisar dokokin Amurka cewa bayan hadarin 737 Max a Indonesia a 2018, hukumomin kula da sufurin jiragen saman Amurka na da masaniyar cewa akwai barazanar samuwar karin hadarin jiragen a nan gaba. Kwararrun hukumar sun yi hasashen yiwuwar samun gomman haduran jiragen, matukar ba'a yi wa taswirar jiragen gyare-gyare ba. Amma duk da haka ba'a dakatar da 737 Max daga tashi ba, sai bayan hadarin jirgin na biyu a Ethiopia a watan Maris na 2019. Boeing na sauya taswirar na'urar da ke sarrafa kanta a jirgin, wadda ake gani ita ce ke haifar da matsalar. Kamfanin ya ce yana da jiragen 737 Max guda 400 a rumbun ajiyarsa, kuma zai mayar da hankali wajen mika jiragen ga wadanda suka saye su. Yayin da wasu kamfanoni sun riga sun yi odar jiragen, Boeing ta dakatar da mika masu jiragen har sai injiniyoyinta sun kammala gyara a kan manhajar jiragen. Yaya ake gani? Mai sharhi a kan masana'atu Henry Harteveldt ya ce ba'a taba ganin irin matakin na dakatar da kera 737 Max ba. Yana kuma iya yin ""tasiri sosai a kan Boeing mai kera jiragen, da masu dillanci da kuma kamfanonin sufurin jiragen sama"". ""Tabbas za ta haifar da rudani ga kamfonin jirgin sama da ke da hannu a ciki da kuma kimanin kamfani 600 da ke harkar sayar da 737 Max da kamfanin Boeing kansa"". Tuni dakatar da 737 Max ya riga ya sa Boeing asarar kusan dala biliyan tara. Ranar Litinin, hannun jarin Boeing ya karye da kashi hudu cikin dari, bayan hasashen dakatar da kera jiragen. Ana sa ran dakararwar za ta yi tasiri a kasuwar jirage ta duniya. Mai sharhi kan harkokin jiragen sama na Teal Group Richard Aboulafia, ya kwatanta matakin da Boeing ya dauka a matsayin mara dadi. Ya ce da Boeing ya mika musu jiragensu, ko kuma ya mayar masu da kudadensu har sai an yarje wa jiragen su rika tashi. Kamfanonin jiragen sama na Amurka sun fi amfani da 737 Max, duk da cewa ana amfani da jiragen a sassan duniya." https://www.bbc.com/hausa/labarai-50820462 +technology Hotunan taurari masu ban sha'awa da wani dalibi ya dauka "Wani ɗalibi ɗan ƙasar Scotland ya ƙaddamar da hotunan sararin samaniya da ya ɗauka ta hanyar amfani da na'urar hangen nesa a bayan lambunsa. Bryan Shaw, dalibi a Jami'ar West of Scotland, ya shafe sa'o'i da yawa yana kallon taurari da tattara hotuna da bidiyo don wani shiri na ƙarshen shekara. Dalibin da ke ajin karatu na hudu ya sami nasarar ɗaukar cikakkun hotuna na gungun taurari da waɗanda ke da haske a shekaru da yawa, kamar Pleiades, Andromeda da Orion Nebula. Mr Shaw - wanda ya fara ɗaukar hotunan sararin samaniya a bara - yakan sadaukar da darensa kan burinsa, na ɗaukar hotunan taurari a wajen gidansa da ke c New Cumnock, gabashin Ayrshire. Ya ce: ""Yana cin lokaci, amma ina matuƙar so wannan. Ina shirin samun babbar na'urar hangen nesa domin faɗaɗa ilimi na, kuma don na iya ɗaukar wasu abubuwan da ba zan iya ɗauka ba a yanzu."" Ina son na ɗauki hotunan na duniyoyi da wata - abin da nake tsarawa kenan. ""Babban burina shi ne na ɗauki taurarin nebula."" Dr Sheona Urquhart, malamin kimiya a Open University, ya shaida wa BBC cewa hotunan da aka ɗauka ""abubuwa ne da ke nuna yanayin duniyarmu."" ""Abin da nake tunani ya fi ban sha'awa shi ne yadda ya ba sai ka je kasa da kasa ba, ka samu hotuna masu ban sha'awa - daga gida za ka iya samun abin da kake so,"" in ji shi. Dukkanin hotuna haƙƙin mallakar Bryan Shaw ne." https://www.bbc.com/hausa/labarai-61233505 +technology Amurka da Saudiyya za su ci gaba da cinikin makamai Majalisar dokokin Amurka ta kasa dakatar da cinikayyar makamai tsakanin kasar da Saudiyya wanda ya kai kudi kimanin dala biliyan 8.1. Hakan na zuwa ne kwana daya bayan da shugaban Amurka, Donald Trump ya yi amfani da ikonsa na shugabanci wajen kawar da hukuncin da zauren majalisar dokokin kasar ya yanke wajen hana siyar da makaman. Masu suka na fargabar cewa za a iya amfani da makaman wajen kai wa fararen hula da ke cikin rikicin Yemen hari. Mista Trump dai ya yi gardamar cewa hana siyar da makaman zai rage karfin Amurka a tsakanin takwarorinta. A cikin makon da ya gabata dai shugaban ya kuma jaddada cewa hana cikin ka iya bata alakar da ke tsakanin Amurka da kawayenta, bayan da ya yi watsi da hukuncin da majalisar ta dauka. To sai wasu masu fada a ji da suka da wasu 'yan jam'iyyar Republicans sun ce ba shi da dalilin da zai yi watsi da hukuncin nasu. A zaben da aka yi ranar litinin, wasu 'yan jam'iyyar Republican su 5 sun zabi da a yi watsi da abin da Trump ya ke so a yi, a yayin da suka goya wa takwarorinsu 'yan jam'iyyar Democrat baya da kashi 45 bisa 40. Sanatoci 15 dai sun ki shiga lamarin. Gwamnatin Trump ta bayyana a cikin watan Mayun da ya gabata cewa za ta siyar wa Saudiyya da kuma Hadadiyar Daular Larabawa makamai. Mr Trump ya kuma yanke dokar domin samu a aiwatar da yarjejeniyar ta siyar da makaman. Ya ce ya yanke wannan hukuncin ne saboda barazanar da Iran ta ke yi wa kasarsa. An dai jima ana fama da zaman dar-dar tsakanin Amurka da Iran, tun bayan da Amurka ta fice daga yarjejeniyar makaman nukiliyyan da ke tsakaninsu. https://www.bbc.com/hausa/labarai-49167207 +technology EFCC ta kama wanda Amurka ke zargi da zambar intanet "Hukumar EFCC mai yaki da yi wa tattalin arziki ta'annati a Najeriya ta damke wani mutum da 'yan sandan Amurka ke nema bisa zargin zamba ta kafar intanet. Sanarwar da EFCC ta fitar a ranar Litinin ta bayyana cewa ofishinta na garin Ilorin ne ya cafke Festus Akinyemi Abiona mai shekara 38, wanda ta yi wata takwas tana nema ruwa a jallo. Jami'an hukumar sun kwakulo shi ne daga gidan buyansa a garin Arepo na jihar Ogun a ranar 6 ga watan Fabarairu. A watan Yulin 2019 ne 'yan sandan FBI suka zargi Festus Akinyemi da tura sakon imel na zamba da suka kira Business Email Compromise (BEC) da sauran laifuka ta intanet. ""A watan Mayun 2016 FBI ta samu bayanai cewa wasu sun kutsa cikin asusun wani kamfanin inshora a Amurka, inda suka sace kudi kusan dala 2,500 (kusan naira 900,000),"" FBI ta bayyana. Ta kara da cewa: ""Mutanen suna da alaka sosai da Abiona da kuma sauran abokan aikinsa da ke aikata zambar BEC."" Binciken EFCC ya nuna cewa wani da ya yi alaka da Abiona ne ya aikata zambar, kuma an gano miliyoyin naira a asusunsa na banki da kuma wasu imel din da ya yi amfani da su. EFCC ta ce wanda ake zargin ya zuba dukkanin layukan wayarsa a masai da kuma katikansa na ATM lokacin da ya yi arba da jami'anta. Ta ce har yanzu ba ya ba ta hadin kai a binciken da take yi amma nan gaba kadan za ta gurfanar da shi a gaban kotu." https://www.bbc.com/hausa/labarai-51453077 +technology An cimma matsaya tsakanin China da Amurka kan Huawei An kawo karshen takaddamar diflomasiyya tsakanin China da Amurka da Canada, inda aka saki babbar jami'ar kudi ta kamfanin Huawei na China, wadda aka tsare a Canada. Tuni dai Meng Wanzhou ta tashi zuwa China haka su ma wasu 'yan Canada biyu da China ta tsare Michael Kovrig da Michael Spavor an sake su, inda suka shiga jirgin sama domin komawa Canada. An dai saki Ms Meng wadda aka kama tun 2018 daga daurin talala a gida karkashin wata yarjejeniya da masu gabatar da kara na Amurka, wadanda tun da farko suka bukaci tasa keyarta zuwa Amurkar, inda tsarewar tata ta janyo rikicin diflomasiyya. An nuna Ms Meng Wanzhou ne inda ta bayyana ta bidiyo a wata kotu a birnin New York tana musantawa ko kin amsa tarin laifukan almundahana na banki da ake mata. Wanda wannan shi ne karshe ko kololuwar yarjejeninyar da aka cimma da ma'aikatar shari'a ta Amurka, wadda ta bayar da damar barin jami'ar barin Canada inda ake tsare da ita a gida tun 2018. Sai dai a wani bangare na yarjejeniyar sakin nata babbar jami'ar kudin ta kamfanin na Huawei ta yarda cewa ta yi wa bankuna karya domin taimaka wa kamfanin saba takunkumin tattalin arziki da Amurka ta sanya wa Iran Batun nata ya zama wata alama da ke nuni da irin tsattsamar dangantakar da ke tsakanin kasashen duniya biyu mafiya karfi, China da Amurka. Ita ma dai Canada an shigar da ita rikicin, inda China ta mayar da martini ta hanyar tsare 'yan kasarta biyu. Yarjejeniyar shari'ar wadda aka dage ta wanke Meng Wanzhou, wadda diya ce ga wanda ya kafa kamfanin na Huawei. Amma kuma har yanzu katafaren kamfanin sadarwar na China n fuskantar tuhuma a Amurka wadda ta hada da ta liken asiri. Kuma har yanzu ba a sani ba ko idan wannan maslaha da aka yi za ta taimaka wa 'yan Canadan biyu. Har kullum China na musanta cewa abubuwan biyu suna da alaka. https://www.bbc.com/hausa/labarai-58688309 +technology Hanyoyi uku da aka fi yi wa mutane kutse a intanet Ana samun ƙaruwar mutanen da suke faɗawa tarkon miyagu masu yi wa kamfanoni da ɗaiɗaikun mutane kutse akowane lokaci. Wani bincike da da wani kamfanin tsaro ya fitar ya nuna cewa a watan jiya kadai an ringa yunƙurin karɓe iko da shafukan wasu kamfanoni har sau miliyan 20 akowce rana. Shafukan mutanen da aka ringa yi wa yunƙurin kutsen sun haɗa da kamfanoni kamar su Amazon, da eBay, Intagram da Facebook. Ga wasu manyan hanyoyi uku da ake yi wa mutane kutse da kuma hanyoyin da za ku kare kanku. https://www.bbc.com/hausa/labarai-60292657 +technology Fasahar 5G: Abin da zai sa sabbin wayoyinku su iya kawo cikas ga jiragen sama Manyan kamfanonin jiragen sama na Amurka na gargaɗin cewa fitar da fasahar 5G da ake yi a ƙasashe zai iya jawo bala'i. Sun bayyana cewa sabuwar fasahar za ta iya jawowa a samu jinkiri wajen tashin jiragen sama, haka kuma zai iya jawowa jirage da dama su kasa tashi kuma babu ranar tashinsu. Abu ne mai tsanani. A ƙarshen 2020, RCTA, wadda ƙungiya ce da ke Amurka, ta fitar da ƙa'idojin da ya kamata a bi kan sufurin jiragen sama - ƙungiyar ta wallafa wani rahoto kan wannan lamari. Ƙungiyar ta bayyana cewa akwai yiwuwar lamarin zai yi tasiri ga ɓangaren jiragen sama a Amurka, ciki har da matsalolin da za a iya fuskanta da za su iya jawo asarar rayuka da dama, idan aka kasa shawo kan matsalar. A ƴan kwanakin nan, hukumar da ke sa ido kan sufurin jiragen sama ta FAA ta yi gargaɗin cewa 5G za ta iya jawo matsaloli da dama ga na'urori daban-daban a jirgin sama samfarin 787 Dreamliner. Hakan zai iya jawo wa jirgin ya kasa rage gudu a wajen sauka, kuma hakan zai iya ja ya wajen sauka ya gusa daga titin jirgi. Ba za a bar jirage su yi amfani da na'urar auna nisan jirgi daga sararin samaniya zuwa ƙasa ba a lokutan da za a iya samun cikas ga hanyoyin sadarwar jirgin. Amma hakan zai iya kawo cikas ga yadda wasu jiragen za su sauka, misali a lokacin da yanayin gari yake dishi-dishi. Kamfanonin jiragen saman Amurka goma sun yi gargaɗin cewa wannan lamarin zai iya ja jiragen sama da dubu ɗaya su samu jinkiri ko kuma a soke su idan akwai yanayi mara kyau. Ba kamar yadda ƙasashen Amurka suke yi ba. Hakan na faruwa ne sakamakon yadda ake ƙaddamar da fasahar 5G ya bambanta a kowace ƙasa. A Tarayyar Turai, alal misali, kamfanonin sadarwa na aiki ne da zango mafi ƙanƙanta idan aka kwatanta da wanda kamfanonin Amurka ke shirin amfani da su - wanda hakan zai rage yiwuwar samun cikas wajen sadarwa. Haka kuma turakun watsa sabis su ma suna amfani da makamashi kaɗan. A ƙasar Faransa, akwai wasu yankuna kusa da filayen jirgin sama waɗanda aka haramta amfani da fasahar 5G, haka kuma za a rage tsawon turakun sadarwa domin rage yiwuwar kawo cikas wajen sardarwa. Tuni hukumomi a Amurka suka ɗauki matakai daban-daban. Hukumar ta ayyana wasu wurare na wucin gadi guda 50 a kusa da filin jirgi, inda masu fasahar za su rage ƙarfin 5G ɗin. Sai dai waɗannan wuraren ba su da yawa idan aka kwatanta da wuraren da ake amfani da su a Faransa inda kamfanonin sadarwar Amurka za su watsa 5G ɗin ta hanyar amfani da makamashi mai yawa. Haka kuma an sanar da filayen jirgin da za su iya amfani da manhajar GPS domin nuna hanya a maimakon na'urar nuna nisa tsakanin sararin samaniya zuwa ƙasa. Sai dai kamfanonin jirgin sun kafe kan cewa hakan bai isa ba: sun kafe kan cewa bai kamata a samar da 5G ba a duk wuri da ke da nisan mil biyu daga filin jirgi. Kamfanonin sadarwa na Verizon da AT&T sun dakatar da fitar da fasahar 5G sau biyu haka kuma sun amince da wuraren da aka ayyana da su rage ƙarfin 5G a can. https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-60081277 +technology Mene ne babban layin wutar lantarki na Najeriya kuma yaya yake aiki? "'Yan Najeriya na ci gaba da shafe ranaku da dararensu a lokuta daban-daban ba tare da wutar lantarki ba na tsawon kwanaki sakamakon lalacewar babban layin lantarki na ƙasa da ake kira National Grid a turance. Da ma dai ɗaukewar lantarki ba sabon abu ba ne a Najeriya, yayin da layin lantarkin ya lalace sau da yawa a cikin shekarar nan. A ranar Lahadi da ta gabata, kamfanonin da ke raba lantarkin ga kwastomominsu suka tura wa 'yan Najeriya da dama irin wannan saƙon cikin harshen Ingilishi: ""Gare ku abokan hulɗarmu masu daraja, muna masu baƙin cikin sanar da ku lalacewar layin wuta babban layin lantarki na ƙasa [National Grid]. ""Wannan ya shafi dukkan ayyukanmu na ƙoƙarin biyan buƙatunku da kyau. ""Muna roƙunku afuwarku yayin da muke ci gaba da aikin haɗin gwiwa da [kamfanin rarraba lantarki] TCN don shawo kan matsalar."" Ƙarshen makon da ya gabatan ya zama karo na kusan shida da babban layin lantarkin ke samun matsala cikin wata biyu. A wannan maƙalar za mu yi duba ne kan Mene ne National Grid? Me ya sa yake lalacewa? Ta yaya ake tarawa da rarraba lantarkin? Babban layin wutar lantarki na Najeriya - power grid a Turance - gungun layuka ne da suka haɗa tashoshin samar da lantarki da ke bai wa dukkan sassan Najeriya wuta. A taƙaice, wata ma'dana ce da ke ɗauke da dukkan lantarkin da ake sha a Najeriya. Haka nan, ba wani wuri ba ne guda ɗaya, tarin layuka ne a wurare daban-daban. An tsara shi ne don ya yi aiki ta wasu taƙaitattun hanyoyi musamman dangane da yawan wutar da ake da ita, da tsaron lafiyarsa. Saboda haka duk sanda ya fita daga yanayin da ya saba zama na kwanciyar hankali, ayyukan da yake za su samu matsala kuma hakan kan sa ya lalace. Na'urorin da ke ba da wutar lantarkin kan kashe kansu da zarar sun fuskanci cewa suna cikin matsala. Hakan ka iya nufin ɗaukewar wutar gaba ɗaya ko kuma na wani ɓangare. Kazalika, yanayi - iska ko ruwa ko sanyi ko zafi - kan shafi aikin babban layin a wasu lokuta, abin da ya sa ke nan ake yawan ɗauke wuta idan aka fara iska mai ƙarfi a lokuta da dama. Najeriya ta fuskanci lalacewar babban layin lantarki na ƙasa a lokuta da dama a 2022 kaɗai. Rahotanni na cewa hakan ta faru aƙalla sau biyar, wasu na cewa sau bakwai, wasu ma na cewa ya fi haka. Lalacewar watan Janairu: An samu lalacewar layin lantarkin a ranar 17 ga watan Janairu. Kwana ɗaya bayan an gyara, ya sake lalacewa tare da jefa kusan dukkan ƙasar cikin duhu. Lalacewar watan Maris: A ranar 14 ga watan Maris ma layin wutar ya sake lalacewa. Kazalika, kwana ɗaya bayan haka ya kuma lalacewa bayan an gyara. Lalacewar Afrilu: Babban layin lantarki ya lalace ranar Juma'a, 8 watan Afrilu da misalin ƙarfe 6:30 na yammacin Najeriya. A ranar Lahadi, 13 ga watan Yuni Najeriya kamfanin rarraba wutar lantarki ya fuskanci lalacewar babban layin na baya-bayan nan. Amma an gyara matsalar da misalin ƙarfe 11:00 na daren amma ba nan take wutar ta karaɗe wurare ba. Babban aikin kamfanonin da ke tattara wutar lantarki a Najeriya shi ne tara ta domin raba wa masu amfani da ita wato kwastomomi. Akwai kamfani shida da ke aikin tara lantarki, waɗanda ake kira Generating Companies (GenCos), da kuma tashoshin lantarki 28. Uku daga cikin tashoshin na amfani ne da ruwa wajen samar da lantarki, yayin da sauran 25 ɗin ke amfani da iskar gas. Dukkan kamfani shida na GenCos na 'yan kasuwa ne. Su ne ke da kashi 60 cikin 100 na hannun jari a sashen, gwamnati kuma na da kashi 40. Tsarin rarraba lantarki a Najeriya ya ƙunshi rumbu biyu na 330 kV da 132 kV da kuma ƙananan tasoshinsu. Tasoshin da ke aiki da iskar gas na yankin kudancin ƙasar - saboda sun fi kusa da wuraren haƙo man fetur - su kuma masu aiki da ruwa suna arewaci - a Jebba, da Kainji, da Shiroro duka a Jihar Neja. Bayan GenCos sun samar da lantarkin, sai kuma kamfanin raba lantarkin ya yi ɗauke ta zuwa inda za a raba wa masu amfani da ita. Daga nan kuma sai kamfanonin rarraba lantarki da ake kira Distribution Companies (DisCos) su bai wa 'yan Najeriya. Kamfanin Rarraba Lantarki na Najeriya wato Transmission Company of Nigeria (TCN), shi ne kaɗai ke da haƙƙin rarraba wutar kumana gwamnati ne, yayin da su kuma DisCos ke aiki da TCN. Kazalika, akwai hukumar Nigerian Electricity Regulatory Commission (NERC) mai kula da dukkan ayyukan samarwa da rarrabawa da amfani da lantarkin a Najeriya. A cewar kamfanin samar da lantarki na Najeriya, Nigerian Electricity System Operator (NESO), lalacewar babban layin na nufin ɗaukewar wuta a ƙasa baki ɗaya, yayin da kuma samun tangarɗar layin ke nufin rasa wuta a wasu ɓangarori na ƙasa. Wata majiya a kamfanin TCN ta faɗa wa wata kafar yaɗa labarai cewa lalacewar babban layin ba abu ne da ke buƙatar gyara ba idan hakan ta faru, sai dai a sake kunna layin wato mayar da shi bakin aiki. ""Babu wanda zai iya faɗa muku yawan kuɗin da ake kashewa saboda ba haka ake yi ba. ""Ba a kashe kuɗi, ba abin gyarawa ba ne. Kamar dai a ce kun kashe injin jannareto dinku sai kuma ku sake kunna shi,"" a cewar majiyar. ""Saboda haka ba wai ma'aikata ne ɗebo kayan aiki su aikin gyara ba.""" https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-61813381 +technology Me ya sa kwanaki hudu babu internet a Iran? Kasashen duniya sun fara nuna damuwa kan daukewar internet a kasar Iran, a dai-dai lokacin da aka shiga kwanaki hudu da daukewar. Wannan ya biyo bayan zanga-zangar da 'yan kasar ke yi kan Karin farshin man fetur da kasha 50, wanda gwamnatin shugaba Hassan Rouhani ta yyana. A daren Asabar ne internet din ta fara fuskantar tangarda, kafin wayewar garin Lahadi ta dauke baki daya. Iraniyawa mazauna kasashen ketare sun yi ta wallafwa a shafukan sada zumunta cewa daukewar internet ta raba su da 'yan uwa da abokan arziki da ke gida lamarin da ya sanya ba su san a halin da suke ciki ba. Abin ya matukar tayar da hankali a kasar mai al'umma miliyan 80 da yawancin matasa sun dogara da internet dan gudanar da rayuwar yau da kullum ciki har da karatu. Ba kamar sauran kasashen waje ba kamar Birtaniya da suke da kamfanonin sadarwa da internet daban-daban ba, wanda da wuya su iya daukewa a lokaci guda. Iran na da kamfanoni biyu kwarara da kuma suke karkashin gwamnati, dan haka ne abin ya yi matukar tasiri. Wata matashiya Arash Azizah ta wallafa a shafinta na Twitter yadda lamarin ya shafe ta; ''Kamar sauran Iraniyawa, muna da dandalin Whatsapp da zuriyar gidanmu ke amfani da shi, kakarmu a duk asubahin Allah ta na tura mana sakon fatan alkhairi da kariya daga dukkan abin ki, amma wannan matsala da aka samu ta hana mu yin hakan.'' https://www.bbc.com/hausa/50496149 +technology Adam King: Yaro ɗan shekara shida da ke da burin aiki da 'yan sama jannati ya burge NASA "Wani yaro ɗan shekara shida wanda ya burge mutane da dama da ke da burin aiki da masu zuwa sararin samaniya ya ja hankalin hukumar da ke bincike kan sararin samaniya wato NASA. Tun da farko dai, an ga Adam King a wani shirin yara na talabijin inda ya bayyana cewa yana so ya yi aiki tare da 'yan sama jannati idan ya girma. Yaron, wanda ke da matsala ta naƙasa, ya samu saƙonni sosai daga manya ko kuma sanannun 'yan sama jannati da kuma hukumomin da ke bincike kan sararin samaniya na Amurka. Hukumar NASA a shafinta na Twitter ta wallafa cewa ""mun ƙagara ya zama ɗaya daga cikinmu wata rana"". Adam na daga cikin waɗanda aka gayyata a wani shiri na musamman na Kirisimeti. Shirin dai, shiri ne na musamman da ake gudanarwa a duk shekara inda ake gayyatar yara daga gidaje daban-daban domin yin sharhi kan kayayyakin wasan da aka ƙera na baya-baya. Sai dai Adam a wannan shekarar ya zama zakara bayan ya yi magana dangane da burinsa na zama ɗan sama jannati. ""Me kake so ka zama idan ka girma?"" in ji mai gabatar da shirin Ryan Tubridy. ""Capcom a Nasa,"" in ji Adam. Capcom dai wata kalma ce da 'yan sama jannatin ke amfani da ita da ke nufin mutumin da ke taimakawa wajen magana tsakanin 'yan sama jannati da kuma waɗanda ke nan duniya. ""Kana so ka zama ɗan sama jannati a nan gaba?"" in ji mai gabatar da shirin ""Ni ba zan iya zama ɗan sama jannati ba saboda irin naƙasar da nake da ita,"" in ji Adam inda ya ce yana so ya yi aiki da waɗanda ke magana da 'yan sama jannati daga nan duniyar." https://www.bbc.com/hausa/labarai-55128414 +technology 'Yariman Saudiyya bai yi wa Jeff Bezos kutse a Whatsapp ba' Hukumomin Saudiyya sun musanta zargin da ake yi wa yariman kasar Muhammad Bin Salman na kutsa wa wayar hamshakin dan kasuwar nan mamallakin kamfanin Amazon, wato Jeff Bezos. Ofishin jakadancin kasar a Amurka ya bayyana zargin a matsayin mara tushe ballantana makama, tare da bukatar aiwatar da bincike domin tabbatar da gaskiyar lamari. Dangantaka ta yi tsami tsakanin Saudiyya da biloniyan dan kasuwar wanda kuma shi ne mamallakin fitacciyar jaridar nan ta Amurka wato 'Washington Post', bayan kisan daya daga cikin marubutanta Jamal Khashoggi da ake zargin yariman da yi. An yi kutse wayar dan kasuwar ne bayan samun wani sako ta WhatsApp dinsa a watan Mayun 2018, kuma yariman Saudiyyan Muhammad Bin Salman ne ya aika masa da sakon kamar yadda Jaridar Guardian ta ruwaito. Wani bincike da aka kaddamar dangane da laifin kutsen da ya sabawa ka'idar bayanan sirri ya nuna cewa jim kadan bayan latsa mashigin wani bidiyo da yariman ya aika masa sai kawai wayar ta fara fitar da dumbin bayanan sirrin da aka jibga mata. Saudiyya dai ta musanta zargin. Masu bincike a kan sahihancin bayanai sun kaddamar da bincike na musamman a kan wayar dan kasuwar a wannan watan, domin samun wasu karin bayanai. Kamfanin Amazon ya dan yi jinkirin yi wa BBC karin bayani kamar yadda muka nema tun da farko. An dora zargin ne kan rahoton wata cibiyar kwararru masu ba da shawara a kan harkokin tsaro da dan kasuwar ya hayo. Ana sa ran Majalisar Dinkin Duniya za ta fitar da sanarwa a kan sahihancin zarge-zargen a Larabar nan. https://www.bbc.com/hausa/labarai-51207809 +technology Makaman da China ta yi amfani da su wurin kai hari kan India "Wani hoto ya nuna makaman da China ta yi amfani da su wurin kai hari a iyakarta da Indiya a ranar Litinin. Rikicin wanda aka yi a Kwarin Galwan ya sa sojojin Indiya 20 suka rasa ransu wanda haka kuma ya kawo fargaba tsakanin ƙasashen biyu. China ba ta bayyana ko wasu daga cikin sojojinta sun ji rauni ko sun mutu ba sai dai duka ƙasashen na zargin kansu da kai wa juna hari. Iyakar ƙasashen ba a fitar da ita yadda ya kamata ba kuma sukan shiga tsakanin juna sakamakon sauyin yanayi. Hoton da aka fitar a ranar Alhamis ya nuna makaman a tsirarasu kuma da alama an yi su ne da rodi kuma aka saka musu ƙusoshi. BBC ta samu hoton ne daga wani babban hafsan soji da ke kan iyakar Indiya da China wanda ya ce China ce ke amfani da irin makaman. Wani mai sharhi kan al'amuran tsaro Ajai Shukla wanda shi ne ya fara wallafa hoton makaman a shafin Twitter ya ce rashin imani ne amfani da irin makaman wurin kai hari. Rashin amfani da makamai a yankin kan iyakar ya samo asali ne tun a wata yarjejeniya da aka cimma wa a 1996 tsakanin ɓangarorin biyu kan haramta amfani da bindigogi ko kuma abubuwan fashewa domin gudun ƙara rura wutar rikici a yankin. Hoton ya yi yawo matuƙa a Indiya, inda mutane da dama da ke amfani da shafukan sada zumunta ran su ya baci. Sai dai babu wasu jami'ai ko kuma hukumomi a Indiya ko kuma China da suka ce wani abu kan wannan hoto. Rahotanni sun bayyana cewa an samu arangama ne tsakanin jami'ai a wani tsauni mai tsawon mita 4,267, inda wasu sojoji suka rinƙa faɗawa cikin kogin Galwan. Ɓangarorin biyu sun yi ta rikici kan iyakar ƙasashen a 'yan makonnin nan, sai dai arangamar da aka yi a ranar Litinin ta zama ta farko da ta sa aka rasa rayuka masu yawa bayan shekaru 45. Wasu rahotanni da ba a tabbatar ba daga Indiya sun bayyana cewa sojojin China 40 suka mutu, sai dai China har yanzu bata fitar da wata sanarwa ba dangane da mutanen da suka mutu. Akwai wasu sojoji na Indiya da ake ganin cewa sun yi ɓatan dabo. Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen China Zhao Lijian ya bayyana cewa Indiya ta ƙetare iyakarsu har sau biyu, ""sun fusata tare da kai hari ga jami'an China wanda hakan ya jawo aka samu arangama tsakanin jami'an da ke tsaron iyakokin ƙasashen biyu,"" kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito. Jama'a da dama a ƙasashen biyu sun sha gudanar da zanga-zanga sakamakon irin arangamar da ake samu a yankin iyakar ta Himalaya, sai dai jami'a sun sha yin gargaɗi da kuma yunƙurin sasanci ta hanyar diflomasiyya. Ministan harkokin wajen Indiya Anurg Srivastava ya ce ministocin ƙasashen biyu sun tattauna ta waya a ranar Laraba kan lamarin, ""kuma sun cimma matsaya kan cewa za a magance abin ta hanyar da ta dace"". Wata sanarwa da gwamnatin Indiya ta fitar ta bayyana cewa dakarun China sun yi ƙoƙarin yin wani gini kan iyakar ƙasar da Indiya. Sanarwar ta zargi 'yan China da ɗaukar wannan mataki da gangan wanda ya jawo rikici da kuma rasa rayuka inda kuma suka buƙaci China ta kawo gyara a lamarinta." https://www.bbc.com/hausa/labarai-53097269 +technology Amurka na bincike kan wasu abubuwa da ke yawo a sararin samaniyarta "Wani rahoton gwamnatin Amurka kan ganin wasu abubuwa masu tashi sama da ba a san ko meye ba (UFOs), ya gano cewa babu wata shaidar cewa akwai wasu halittu na 'alien' amma ba su cire tsammanin akwai ba. Ana sa rai bitar da aka yi kan ganin abubuwan masu tashi sau 120 zai yanke cewa babu sa hannun fasahar Amurka a mafi yawan lokutan da abin ya faru. Baya ga haka, rahoton bai yi wani cikakken bayani kan ko mene ne abubuwa da ke tashi saman ba, a cewar jami'ai. Za amiƙa wa ƴan majalisar dokoki rahoton da ba na sirri ba a watan Yuni. Rahoton dai sakamakon wani kwamitin soji ce da aka kafa a bara don bincike kan abubuwan da ake gani a sararin samaniyar Amurka tsawon shekaru. Ma'aikatar tsaro ta ce tana so ta ""ƙara fahimtar"" lamarin ko abubuwan (UFOs) da ake gani kuma ta duba idan za su iya zama barazana ga tsaron ƙasar. Fitar da rahoton ya ja hankalin jama'a a Amurka inda aka daɗe ana tattaunawa kan ganin abubuwan masu tashi da jita-jitar cewa akwai wasu halittu da ke rayuwa a wata duniyar. Masu sha'awar batun UFO na ta ce-ce-ku-ce kan abin da rahoton ya ƙunsa kafin miƙa shi ga majalisar ranar 25 ga watan Yuni. Bayanan da ke ƙunshe cikin rahoton sun fara bayyana ne a rahoton jaridar New York Times da CNN da Washington Post ranar Alhamis. Kafofin yaɗa labaran sun ce sun yi magana da jami'an gwamnati da dama kan abin da aka gano a rahoton da aka ƙagu a fitar. Jami'an sun ce cikin ganin abubuwan da ke tashi sama da aka yi sau 120 a shekaru ashirin ɗin da suka gabata, mafi yawa jami'an sojin ruwan Amurka ne suka yi yayin da wasu kuma dakarun ƙasashen waje ne suka yi. CNN ta ce ta yi magana da wasu majiyoyi guda uku waɗanda suka ce rahoton bai cire tsammanin akwai wasu halittu da ke rayuwa a wajen duniyar mu ba. Sai dai babu shaidar cewa abubuwan da ake gani suna yawo a sararin samaniya da matuƙa jirgin rundunar soji suka gani a shekarun baya-bayan nan, jirgin halittun e, jaridar New York Times ta ruwaito. Jaridar ta ce jami'an leƙen asiri sun ce akwai yiwuwar cewa ƙasashe masu ƙarfin iko da ke adawa da Amurka kamar China ko Rasha ne ke gwajin sabbin fasahohinsu a sararin samaniyar. Jaridar da CNN sun ce jami'an leƙen asiri sun damu game da tasirin da wannan hasashe zai yi ga tsaron ƙasar. An yi magaa kan ganin wasu halittu a wani sabon rahotin CBS News kuma wannan ya sake ɗaukar hankula kan batun a watan da ya gabata. Shirin kafar yaɗa labaran na 60 Minutes ya tattauna da wani matuƙin jirgin sama na rundunar sojin ruwan Amurka wanda ya ce sun ga wani jirgi da ba su taɓa ganin irinsa ba ya wuce su da saurin gaske kuma yana kukkurɗawa ba kamar yadda aka saba gani ba. Wani matuƙin jirgi da a yanzu ya yi ritaya, Ryan Graves ya ce bataliyarsa ta matuƙa jirgin yaƙi sun fara ganin wasu abubuwa suna yawo a sararin samaniya a filin da aka taƙaita tashi kusa da Virginia a shekarar 2014. Ya ce abun ko jirgin ba shi da salansa inda hayaƙi ke fita kuma yana tafiya ne da saurin da ya wuce yadda fasahar da ake da ita yanzu ta sani. Mista Graves ya ce matuƙa jirgi da ke atisaye a gaɓar tekun Atlantic sun sha ganin irin wannan abun ""kusan kullum tsawon shekaru a ƙalla biyu"". A cikin watan da ya gabata, Luis Elizondo, wani tsohon jami'in leƙen asiri na Amurka ya shaida wa ABC NEWS cewa wasu daga cikin abubuwan ko jiragen da aka gani a saman suna tashi ""na iya zarce duk wani abu da muke da shi na fasaharmu."" ""Abin tambayar shi ne, mene ne wannan?"" ya ce. ""Gaskiyar magana ita ce, ba mu sani ba."" A watan Afrilun bara, Ma'aikatar Tsaron Amurka ta fitar da wasu bidiyo na abin da ta ce ya nuna ""wani abu a sama da ba a yi bayani a kan shi ba"". Ma'aikatar ta ce tana so ta ""goge duk wasu jita-jita da mutane ke yi kan bidiyon"", wanda aka taɓa sakinsa ba bisa ƙa'ida ba a 2007 da 2017, ""idan gaskiya ne""." https://www.bbc.com/hausa/labarai-57355775 +technology Yadda China ke shirin zama gagarumar ƴar sama jannati fiye da kowa "Ƴan sama jannatin China uku sun fara wani aiki na wata shida don kafa sabuwar tashar sararin samaniyar ƙasarsu. Wannan shi ne shiri na baya-bayan nan da China ke yi a ƙoƙarinta na fin sauran ƙasashen samun iko da zama jagora a nazarin sararin samaniya nan da gomman shekaru masu zuwa. A bara, China ta aika da kumbo na farko na tashar Tiangong zuwa sararin samaniya. Tana da shirin ƙara wasu kumbon zuwa ƙarshen shekara. Zuwa shekara mai zuwa, za ta ƙaddamar da wani kumbon zuwa sararin samaniya mai suna Xuntian. Wannan kumbon zai tashi ya sauka a kusa da Tiangong domin yi masa gyara da kuma ƙarin mai. Tiangong za ta samar wa kanta wuta da sauran abubuwa da wuraren zama. China ita ce ƙasa ta uku a tarihin duniya da ta aika da ƴan sama jannati sararin samaniya ta kuma gina tashar sararin samaniya, bayan ƙungiyar Tarayyar Soviet da kuma Amurka. China na da burin da take so cimmawa da Tiangong kuma ana sa ran za ta maye gurbin tashar sararin samaniya ta ƙasa da ƙasa wato ISS wadda za a rufe ta a 2031. An cire ƴan sama jannatin ƙasar China daga ISS sakamakon dokar Amurka da ta haramta hukumar da ke kula da sararin samaniyarta wato Nasa bai wa China bayanai. Burin da China ke da shi bai tsaya a nan ba. Shekaru kaɗan daga yanzu ana sa ran za ta ɗauki samfurin duwatsu na asteriod a kusa da duniyar Earth. Zuwa shekarar 2030, tana da burin kai ƴan sama jannatinta zuwa duniyar wata, haka kuma za ta tura a samo samfarin abubuwa daga Mars da Jupiter. A daidai lokacin da China ke ƙara faɗaɗa ayyukanta a sararin samaniya, wasu ƙasashen na ta ƙoƙarin tafiya duniyar wata. Nasa na ƙoƙarin komawa duniyar wata tare da ƴan sama jannati daga Amurka da sauran ƙasashen duniya daga 2025 zuwa sama, haka kuma tuni ta fitar da sabon babban kumbonta a Kennedy Space center. Japan Koriya Ta Kudu da Rasha da Indiya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa na ta ƙoƙarinsu na zuwa sararin samaniya, Indiya ta ƙaddamar da shirinta na biyu mafi girma na zuwa duniyar wata haka kuma tana da niyyar samun tasharta zuwa shekarar 2030. China ta fara saka tauraron ɗan adam ɗinta na farko mai zagaye a sararin samnaiya a 1970 - a yayin da ta samu wani babban sauyi sakamakon gagarumin sauyin zamani da ta fuskanta. Manyan ƙasashen duniyar da suka iya zuwa sarrain samaniya su ne Amurka da Rasha da Faransa da kuma Japan. A cikin shekara 10 da suka gabata, China ta aika fiye da roka 200. Kuma tuni ta aika wani jirgin sama jannati da ba a ba shi suna ba zuwa duniyar wata, a wani shiri na Chang'e 5, don tattaro samfurin duwatsu. Ta kafa tutar ƙasar a duniyar wata - wacce ta fi ta Amurka da ke can girma. A yanzu haka China tana da ƴan sama jannati 13 a sararin samaniya, idan aka kwatanta da 340 na Amurka da kuma fiye da 130 ɗin Rasha. Sai dai an samu ƴan matsaloli. A shekarar 2021 wani ɓangare na rokar da China ta aika ya faɗo daga sararin samaniyar inda ya faɗa cikin Tekun Atalantika, sannan an sake samun matsalar ƙaddamar da wasu rokokin biyu a 2020. Kafar yada labarai ta China Xinhua ta ce akalla mutum 300,000 ne suka yi aiki a kan shirin kasar na sararin samaniya - wato kusan ninki 18 kan yadda Nasa ke aiki a kan sararin samaniya. An kafa hukumar sararin samaniya ta China a 2003 inda da farko aka ware mata yuan biliyan biyu kwatankwacin ($300m, £240m) a matsayin kasafin kudinta. Sai dai a shekarar 2016 China ta bai wa kamfanoni masu zaman kansu damar zuwa tasharta ta sararin samaniya, kuma yanzu haka an kashe fiye da yuan biliyan 10, kwatankwacin ($1.5bn, £1.2bn) a shekara daya, a cewar kafofin watsa labaran China. Me ya sa China za ta tafi sararin samaniya? China tana matukar mayar da hankali a kan fasahar tauraron dan adam, domin bunkasa harkokin sadarwa, da hanyoyin sufirin juragen sama, da hasashen yanayi da makamantana su. Amma da dama daga shirinta na bunkasa tauraron dan adam yana da alaka da harkokin soja. Yana taimaka mata wurin leken asirin 'yan hamayya, da makamai masu linzami da ke cin dogon zango. Lucinda King, kwararriya kan sararin samaniya a Jami'ar Portsmouth, ta ce China ba tana mayar da hankali ne kan manya-manyan bincike na sararin samaniya ne ba: ""Sun kware a dukkan bangarori na sararin samaniya. Suna da manufa ta siyasa da kuma kudin da za su cimma hakan."" Daya daga cikin manufofin China na zuwa duniya Wata ita ce ta samo wasu karafa daga can, wadanda suka hada da karfen lithium. Sai dai Farfesa Sa'id Mosteshar, darakta a Cibiyar Nazarin Sararin Samaniya da Dokoko a Jami'ar London, ya ce China ba za ta ci riba sosai ba idan ta rika aikawa damutane duniyar Wata domin samo ma'adinai. Karin bayanai daga Jeremy Howell da Tim Bowler" https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-61744363 +technology Da gaske hukumar FBI ta wanke Abba Kyari daga zarginsa a kan Hushpuppi? "Labarin da ke iƙirarin an wanke shahararren dan sandan Najeriya Abba Kyari da ke fuskantar tuhumar rashawa a Amurka ya mamaye shafukan sada zumunta a ƙasar. Labarin wanda aka fi yaɗa wa a kafar WhatsApp ya ambaci hukumar bincike ta FBI a Amurka da ke cewa ""ba a tuhumar DCP Abba Kyari. ""An ambaci sunansa ne kawai amma ba a tuhumarsa da aikata zamba kuma babu wani laifi da ake tuhumarsa,"" in ji sanarwar da ake ta yaɗawa a kafofin sada zumuntar. BBC ta yi bincike domin tabbatar da gaskiyar labarin, ko da gaske ba a tuhumar babban jami'in na ƴan sandan Najeriya. Kuma binciken da BBC ta gudanar ta gano cewa babu ƙamshin gaskiya a labarin domin babu wata sanarwa da ta fito daga rundunar ƴan sandan Najeriya da ke tabbatar da hakan. Haka kuma hukumar bincike ta FBI ta Amurka ba ta wallafa wani sabon bayani ba da ya ambaci Abba Kyari ko kuma batun wanke shi daga zargin alaƙarsa da matashin ɗan Najeriya da ke fuskantar tuhuma a Amurka bisa hannu a manya-manyan ayyukan zamba na duniya Ramon Abbas, wanda aka fi sani da Hushpuppi. Ko da yake jami'in ɗan sandan na Najeriya, Abba Kyari ya musanta karbar rashawa a hannun Raymond 'Hushpuppi' Abbas, amma an dakatar da shi daga muƙaminsa. Sashen shari'a na Amurka ya ce ya kama wasu ƴan Najeriya mazauna Amurka uku da suka taimaka wa Raymond 'Hushpuppi' Abbas ya yi damfarar dalar Amurka miliyan 1.1. Cikin wata sanarwa wadda sashen ya fitar a ranar 28 ga watan Yuli, ta ce Hushpuppi ya amsa laifin halasta kudaden haram da wasu laifukan masu alaka da kasuwancin intanet. Kuma sun yi zargin cewa Hushpuppi ya bai wa mataimakin kwamishinan ƴan sandan Najeriya Abba Kyari cin hanci domin kama takwaransa Kelly Chibuzo Vincent, mai shekara 40 da haihuwa. Bayanin sashen shari'ar ya bayyana hakan ne bayan da Vicent ya yi kokarin tona asiri da kuma ba da bayanai kan zargin abin da suka yi masa. ""A cewar sanarwar, Abba Kyari wanda babban mataimakin shugaban 'yan sandan Najeriya ne, shi ake zargi da kitsa kama Vicent tare da aike wa da shi gidan yari, ya kuma dauki hotonsa ya aika wa Abbas. ""Abba Kyari kuma an yi zargin ya aika wa Abbas bayanin asusunsa na banki wanda nan ne Abbas ya aika masa kuɗaɗen ladan kama Vicent tare da tasa ƙeyarsa gidan yari,""kamar yadda bayanin kotun ya bayyana. Jami'in ɗan sandan na Najeriya Abba Kyari ya musanta zargin yana cewa bai karɓi ko sisi ba daga Hushpuppi. Abba Kyari ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewa: ""Wani jami'in ɗan sanda ya tabbatar da cewa Hushpuppi ya tuntuɓe shi - amma ba gaskiya ba ne cewa an yi wa Vicent barazanar mutuwa. Kyari ya ce daga baya ƴan sanda sun saki Vicent bayan bincikensu ya tabbatar da ba shi da laifi. ""Abokai: Abbas wanda muka fi sani da Hushpuppi ya kira ofishinmu kamar shekara biyu baya, yana cewa wani mutum a Najeriya yana masa barazanar cewa zai kashe masa iyali, ya kuma aiko lambar waya yana cewa don Allah mu yi wani abu kafin wannan mutum ya kashe masa iyali. ""Mun bi diddigin wanda ake zargi bayan gudanar da bincike mun gano cewa babu wanda yake wa wani barazana, kuma ya ce su biyun abokai ne tun da daɗewa amma sai suka samu matsala a kan kudi. ""Daga baya muka ba da belin wanda ake zargi. ""Babu wanda ya nemi naira ɗaya daga wajen Hushpuppi. Abin da muka mayar da hankali akai shi ne mu ceci rayuwar mutane,"" in ji Abba Kyari. Tun faruwar wannan lamari kawunan ƴan Najeriya ya rabu, inda mutane suke bayyana mabambantan ra'ayoyi. Wasu na ganin sharri ne aka yi wa Abba Kyari tare da maƙala masa wannan abu da a ganinsu bai dace da shi ba, musamman ganin cewa shi ɗin haziƙin ɗan sanda ne da ya yi fafutuka sosai ta wajen gano masu laifi. A hannu guda kuma wasu na ganin babu ko tababa kan wannan zargi da ake yi wa Abba Kyari, inda har suke cewa ""a Najeriya dai kowace gauta ja ce,"" wato ma'ana babu mamaki don an samu mutum irin Abba Kyari da wannan laifi da ake zarginsa. Sai dai akwai waɗanda suka tsaya a tsakiya, wato masu jajantawa Abban, amma kuma duk da haka suna cewa ya kwantar da hankalinsa a yi bincike, idan har ba shi da laifi suna da tabbacin FBI za ta yi masa adalci. Idan kuma an same shi da laifi to dama bawa ba ya wuce ƙaddararsa kamar yadda masu wancan ra'ayi ke faɗa." https://www.bbc.com/hausa/labarai-58113138 +technology Shin wane hali matasa kan shiga idan ba su tare da wayoyinsu? "Wani bincike da likitocin kwakwalwa suka gudanar ya ce kusan kashi daya bisa uku na matasa sun shaku da wayoyin zamani har ma abin ke neman zame musu kamar ba za su iya rayuwa sai da waya. Binciken da kwalejin Kings a birnin London ta yi ya ce mutane na shiga yanayin damuwa a duk lokacin da aka ce ba su tare da wayoyinsu. Rahoton ya ce matasa ba sa iya takaita lokacin da suke shafewa suna dannar waya. Binciken ya kuma ce irin wannan shakuwa da wayoyin zamani na iya shafar lafiyar kwakwalwar mutum. Shi dai binciken, wanda aka wallafa a mujallar BMC Psychiatry, ya yi nazari kan wasu bincike har 41 da aka yi kan matasa 42,000 game da matsalar amfani da wayoyin zamani. Binciken ya gano cewa kashi 23 cikin dari na matasan, waya ta zame musu kamar abin da ba za su iya rayuwa ba sai da ita - irin halin da suke shiga idan ba sa iya amfani da wayarsu da kuma rashin iya kayyade lokacin da suke shafewa akan wayoyin har ta kai ga hakan na zama hadari ga wasu harkokinsu. Irin wannan dabi'a ta shakuwa da waya ana iya danganta ta da sauran matsaloli, kamar yadda binciken ya bayyana, kamar gajiya, da damuwa da rashin bacci da kuma rashin yin kokari a makaranta. Daya daga cikin wadanda suka wallafa rahoton, Nicola Kalk daga cibiyar kula da lafiyar kwakwalwa a kwalejin Kings da ke birnin London, ya ce, ""wayoyin zamani sun samu wajen zama kuma akwai bukatar a fahimci irin matsalolin da ke tattare da amfani da wayoyin."" A cewar Dr Kalk, ''ba mu sani ba ko wayar zamanin ce ta ke da shiga ran mai ita ko kuma manhajojin da mutane suke amfani da su. ""Duk da haka, akwai bukatar a wayar wa da mutane kai game da yadda yara da matasa ke amfani da wayoyin zamani da kuma bukatar iyaye su san iya lokacin da 'ya'yansu suke shafewa akan wayoyinsu."" Ita ma Samantha Sohn, ta ce shakuwa da waya na ""iya shafar lafiyar kwakwalwa da kuma harkokin yau da kullum, akwai bukatar a zurfafa bincike kan matsalolin da ke tattare da yin amfani da wayoyin zamani''. Sai dai Amy Orben, wata malama a sashen kimiyyar kwakwalwa a jami'ar Cambridge, ta ja hankali game da tunanin cewa akwai wata alaka tsakanin yawan amfani da wayoyin zamani da kuma matsalolin damuwa'.' A cewarta, a baya, an nuna cewa illar yin amfani da wayoyin zamani ba wai daga wayoyin ba ne kadai, yanayin mutum ma kan iya yanke yawan lokacin da mutum zai shafe akan waya''." https://www.bbc.com/hausa/labarai-50610116 +technology Kudin da masu fada a ji a shafukan sada zumunta ke samu na karuwa "Kudin da masu fada-a-ji a shafukan sada zumunta ke samu ya yi matukar karuwa a 'yan shekarun da suka wuce, a cewar wani sabon rahoto. Wani kamfani mai suna Izea ya gano cewa farashin hoto da aka biya don a wallafa shi a Instagram ya yi tashin gwauron zabi daga dala 134 (wato Fam 104) a shekarar 2014 zuwa dala 1,642 (wato Fam 1,276) a shekarar 2019. Kamfanoni da sana'o'i na biyan kudi masu yawa don masu fada-a-ji a shafukan su yi masu tallar bayanai da labarai da bidiyo, in ji jaridar Business Insider. Amma wani kwararre ya dage cewar wannan ba ya nufin karshen yadda aka saba yin talla a baya ya zo karshe. ""Talla a shafukan sada zumunta daidai yake da talla ta fatar baki amma dole a rika hada sabon salon talla da yadda aka saba a baya,"" in ji Yuval Ben-Itzhak, shugaban shafukan sada zumunta na Socialbakers. Rahoton ya duba bayanai da hotuna da bidiyo da aka biya kudi don a wallafa su a kan Facebook da Youtube da Instagram da shafukan intanet, kuma ya duba yadda ake ciniki kan farashin da ake biya tsakanin 2014 da 2019. Daga kananan masu fada-a-ji- mutane masu mabiya kasa da 100,000 zuwa sanannu, ya gano cewa ana samun kudi masu yawa. Cikin abubuwan da aka gano su ne: Yayin da mutane ke ta tururwar zama masu fada-a-ji a shafukan sada zumunta, masana'antar na kara fuskantar suka daga masu sa ido. A cikin watan jiya, wasu masu fada-a-ji uku sun wallafa wasu bayanai a Instagram sun yi tallar wasu magungunan rage kiba da Hukumar kula da ingancin kayayyaki ta haramta, saboda a cewarta ba su da inganci. Kuma a farkon shekara, wata hukumar ta yi gargadin cewa wasu masu fada-a-ji na karya wasu dokokin idan ba su bayyana karara cewa hotuna ko bayanan da suka sa a shafukansu, talla ce ba. Zoe Sugg (Zoella) da mawakiya Rita Ora da Rosie Huntingon- Whiteley na cikin masu fada-a-ji 16 da suka amince su sauya yadda suke saka bayanai a shafukansu. Kamfanoni da sana'o'i za su ci gaba da zuba kudi a tallace-tallacen shafukan sada zumunta, a cewar bayanai daga Socialbakers. Bincikenta ya nuna cewa bayanan da masu fada-a-ji ke wallafawa a matsayin talla sun karu da kashi 15 cikin 100 a bara, ta hanyar amfani da alamar maudu'i #. Ya yi hasashen cewa kudin da kamfanoni ke biya don talla a shafukan sada zumunta zai karu a 2020, inda hakan ya sa girman masana'antar ya kai dala biliyan 10. A halin yanzu, Instagram na gwada boye ""likes"" a kan hotuna da bidiyo a shafin, amma Mista Ben-Itzhak na ganin wannan ba zai yi wani tasiri kan masu fada-a-ji ba. ""Masu fada-a-ji za su iya ganin mutanen da ke bibiyarsu kuma suna yawan bai wa kamfanoni damar ganin wannan bayanin,"" a cewarsa. ""Babban abin tambaya a nan shi ne idan masu amfani da shafukan za su ci gaba da bibiyar shafukan idan ba sa ganin ""likes"".""" https://www.bbc.com/hausa/labarai-50431527 +technology Matashiyar da ta san kan motocin zamani a Abuja Hadiza Shehu, mai shekara 18, wata matashiya ce da ta san kan motoci ta kuma ƙware a sanin duk abin da ya danganci motocin zamani. Ba kamar yadda ake yawan fadar cewa mata ba abin da suka sani dangane da mota idan baya ga tuƙa ta ba, Hadiza ta fita daban ta wannan fannin, don hatta kayan gyaran mota ta san su da yadda ake sauya su. Saboda sanin da ta yi wa motoci har ta kai ta kan taya kamfanonin da ke ƙera motoci tallata su. BBC ta tuntuɓi Hadiza don ta ji dalilin da ya fara jan hankalinta take sha’awar duk wani abu da ya shafi mota. https://www.bbc.com/hausa/articles/cn026vn4p6ko +technology Mutumin da zai kashe dala miliyan daya don tono Bitcoin dinsa a wata babbar bola "Kusan shekara 10 da suka gabata, James Howell ya jefar da ma’adanin bayanai na komfutarsa yayin da yake shara a gidansa -inda ya manta da kudin intanet na Bitcoin da ke cikinsa. A yanzu da darajar Bitcoin ɗin nasa da ke ciki ya kai kusan fam miliyan 150, James na shirin kashe miliyoyin kudi domin haƙe wata ƙatuwar bola da nufin gano ma’adanin bayanan komfutar da ya ɓata. Mista Howell ya ce in har ya gano ma’adanin bayanan na komfuta, zai bayar da kashi 10 na abin da zai samu don mayar da birnin zuwa cibiyar hada-hadar kudin intanet na crypto-currency. Sai dai, mutanen yankin sun ce haƙo wurin zai jawo barazanar muhalli. Tsausayi ne ya sa Mista Howell, wanda injiniya ne a fasahar sadarwa, ya jefar da ma’adanin a 2013, bayan samun kudin Bitcoin 8,000 a lokutan farko da aka ƙirƙiro da kudin. Kudin Bitcoin ya samu tagomashi sosai a watan Janairun 2021, inda dukiyar Mista Howell ta kai fam miliyan 210, sai dai ya fuskanci karayar tattalin arziki a farkon wannan shekara. Hukumar birnin da Mista Howell yake, wadda kuma ke da mallakin filin da ya jefar da ma‘adinan da kuma ya haƙiƙance yana ciki, ta hana masa damar tono wurin kan dalilai na barazanar muhalli da hakan zai kawo. A yanzu Mista Howell ya yi alkawarin bayar da kashi 10 na kudin, muddin aka gano shi, domin tallafa wa ayyukan kudin intanet na crypto-currency. Duk wani aikin da za a haƙa don gano ma’adinan bayanan na intanet, zai bukaci babban aikin hannu na tono dubban tan na ƙasa mai yawa da aka tara a wurin shekaru da yawa. Amma Mista Howell ya yi imanin cewa a yanzu yana da kudaɗe da ƙwararru domin yin tono mai inganci da kuma ke da fa’aida ga muhalli. ""Tono wurin zubar da shara babban aiki ne kansa,’’ in ji shi. ""Mun kuma samar da tawagar ƙwararru kan muhalli, wadanda suke da ƙwarewa, wanda idan aka hada hannu tare, za su iya kammala aikin yadda ya kamata.’’ Nemo ma’adanin na bayanan intanet wani aiki ne a kanmu. Babu tabbacin cewa, idan yana nan, za a iya samun abubuwan da ke ciki. Amma in har yana nan, to mamallakinsa na shirin samun makudan kudade, duk da cewa hakikanin kudin zai dogara ne kan yadda za a yi amfani da shi na kirkiro da ayyukan crypto-currency. Ko ma ta yaya, ana hasashen kudaden za su kai miliyoyin fama-famai. Sai dai Mista Howell mai shekara 37, da ya sanya hannu kan mallakar wasu kudaden a matsayin shirin tallafawa ayyukan, ya ce za a yi amfani da gudummawarsa ga birnin don ƙarfafa gwuiwar amfani da kudin na crypto-currency. ""Mun samu ƙwarin gwiwa daban-daban kan irin abubuwa da ya kamata mu yi wa al’umma,’’ a cewarsa. ""Daya daga cikin abubuwan da muke son yi a filin shi ne, da zarar mun share wajen, za mu tabbatar an samar da hasken lantarki a wurin. ""Muna son kafa al’umma da za ta mallaki cibiyar kudin Bitcoin, ta hanyar amfani da lantarki wa mutanen birnin Newport.’’ Cikin sauran tsare-tsarensa, ya hada da shirin bayar da kudi fam 50 na Bitcoin ga kowane mutum a birnin, da kuma kafa shagunan mu’amala da kudin intanet na crypto-currency. Hukumar birnin Newport ta ce ta mayar da martani ga bukatar Mista Howell na ba shi damar tono wurin. ""Muna da hakkin da doka ta ba mu na kula da filayen zubar da shara,’’ a cewar mai magana da yawunta. ""Wani bangare na aikinmu shi ne kare barazanar muhalli ga filayen da sauran yankuna. ""Bukatar Mista Howell na babbar barazana ga muhalli wanda ba za mu amince ba, kuma an hana mu amincewa yarjejeniya kan haka.’’" https://www.bbc.com/hausa/articles/cqeg8351rr6o +technology Yadda wata guguwa ta lalata wutar lantarki a Amurka Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon: Wata gagarumar guguwar hamada ta yi ɓarna sosai a jihar Arizona ta Amurka. Iska mai ƙarfi da ƙura da guguwa sun yi ta kaɗawa tun daga ranar Litinin. An rufe hanyoyi tare da katse wutar lantarki a gidajen mutane a babban birnin jihar, Phoenix. Ana samun ƙaruwar guguwa a jihar saboda shekarun da aka shafe ana fama da rashin ruwan sama da ayyukan haƙar ma'adinai waɗanda suka sa manoma rasa na yi saboda yadda gonakinsu ke komawa hamada. https://www.bbc.com/hausa/articles/cw57x6pe6klo +technology Ƙwayoyin ƙwaƙwalwar da aka ƙirƙiro sun yi wasan kwamfuta "Masu bincike sun samar da kwayoyin halitta na kwakwalwa a dakin kimiyya, kwayoyin da suka koyi wasan kwamfuta irin na kwallon tennis na shekarun 1970, da ake kira Pong. Masanan sun ce 'yar mitsitsiyar kwakwalwar kwayoyin tana iya sanin muhallin da kwayoyin suke har ma su yi abin da ake bukata su yi. A wani bayani da ya wallafa a mujallar nan ta Neuron, Dr Brett Kagan, na kamfanin Cortical Labs, ya yi ikirarin cewa sun kirkiro kwayoyin halitta na kwakwalwa na farko a dakin binciken kimiyya a cikin baho. Sauran wasu kwararru sun bayyana aikin a matsayin abin ban sha’awa da birgewa amma kuma sun ce bayyana kwayoyin da cewa suna sanin muhallin da suke har kuma su yi abin da muhallin ke bukata su yi, abin ya wuce gona da iri. Dr Kagan ya ce ""Ba mu san wani suna da za mu iya bayyana wannan abu ba da ya wuce yadda muka bayyana shi,’’ ""Abu ne fa da yake iya karbar sako daga wani abu, ya kuma mayar da martani na zahiri,"" in ji kwararren. An bullo da irin wadannan kananan kwakwale da farko a shekara ta 2013, domin nazarin wata matsala ta kwayoyin halitta, da ke sa kwakwalwa zama 'yar karama. Kuma tun daga wannan lokacin ake amfani da su wajen bincike kan yadda za a bunkasa kwakwalwa. To amma a wannan lokacin ne kawai aka taba hada su mu'amulla da wani abu na waje, inda a nan din aka sa su wasan kwamfuta. Kwararrun sun : • Samar da kwakwalwar mutum daga 'yan kananan kwayoyin halitta wasu kuma daga 'yan tayin bera inda suka samar da tarin kwayoyin halittar na kwakwalwar har 800,000 • Hada wadannan kananan kwayoyin halitta na kwakwalwa da 'yan wayoyi da wasan na kwamfuta, inda ta haka suke sanin ina kwallon take da kuma yadda za su buga ta. A martaninsu kwayoyin halittar suna yin motsi inda suma suke fitar da wani birbishi na laturoni. Yayin da suke yin wasan yawan karfin da suke zagewa suna amfani da shin a raguwa. To amma idan kwallon ta kai inda za a iya cewa wasan ya kare za a sake sabon lale, sai kwayoyin halittar su sake zage damtse da kusan karin kuzari fiye da na baya. Kwakwalen na koyar yadda wannan wasa yake a cikin minti biyar. Wani lokaci suna kasa samun buga kwallon, amma dai yadda suke buga kwallon kusan za a iya cewa ba canke suke suke yi ba, suna sanin yadda suke buga kwallon. Sai dai kwararrun sun ce duk da cewa kwayoyin halittar suna wasan da kyau amma ba da sanin yadda mutane ya kamata su yi ba. Dr Kagan na fatan wannan fasaha za ta iya taimakawa wajen gwajin hanyoyin da za a magance cutukan kwakwalwa kamar cutar mantuwa. Kwararren ya ce amfanin irin wannan nazari shi ne a san yadda za a iya amfani da shi a Zahiri wajen samar da wasu ci-gaba a wasu fannonin nan gaba. Abu na gaba in ji Dr Kagan shi ne suna son su ga yadda tasirin barasa yake a kan kwayoyin halitta na kwakwalwa a wasan kwallon na tennis na kwamfuta. Idan har barasar za ta yi tasiri a kansu kamar yadda take yi a kan kwakwalwa, wannan zai nuna irin amfanin da za a samu a binciken a gaba. Bayanin Dr Kagan na danganta kwayoyin kwakwalwar da suka kirkiro da cewa suna sanin muhallin da suke su kuma yi abu daidai da inda suka samu kansu, hakan ya saba da ma’anar da yawancin kamus-kamus suka bayyana na wannan kalma da ya yi amfani da ita (sentient). Maimakon haka Dr Dean Burnett mai nazari kan ilimin halayyar dan-Adam a Jami’ar Cardiff yana ganin zai fi dacewa a kira abin da suka kirkiro da sunan ‘’ tsarin aikin tunani’’. Wannan gagarumin ci-gaba da kwararrun suka samu ga alama zai iya kaiwa ga samar da karin alfanu da ilimi a nan gaba kasancewar masanan na aiki da hadin guiwar wasu masu binciken domin fadada ilimin. Dr Burnett y ace, kamata ya yi a dauki wannan ci-gaba a matsayin wani dan-ba, kamar yadda ya kasance a fagen samar da kwamfuta, wadda daga farko aka fara abu kadan-kadan amma bayan wasu shekaru na fadada bincike abu ya burunkasa a fadin duniya. Tuni kwararrun masu bincike da ke samar da na’urori masu fasahar kwamfuta suka kirkiro na’urori da kan doke gagararrun kwararru a wasan dara (chess). To amma Farfesa Karl Friston, na Jami’ar London wanda yake aiki tare da Dr Kagan, ya ce: ""Karamar kwakwalwar da aka kirkiro tana koyon yadda za ta yi abu ba tare da an koya mat aba, saboda haka ta fi dacewa da kuma saukin sarrafawa.""" https://www.bbc.com/hausa/articles/cd1vdwd0g3eo +technology Ana ƙidayar giwaye daga sararin samaniya "Hoto na farko da aka ɗauka da tauraron ɗan Adam, ya nuna wasu abubuwa kamar ƙwallo mai launin toka a tsakiyar korayen bishiyun - amma idan aka yi kallon tsanaki, za a gane waɗannan abubuwan masu kamar ƙwallon giwaye ne ke ta watangaririya a tsakanin bishiyu. Masana kimiyya kuma na amfani da waɗannan hotuna suna ƙirga yawan giwayen da ke Afrika. An samu hotunan ne daga wani tauraron ɗan Adam mai nisan kilomita 600 daga doron ƙasa. Wannan tauraron ɗan Adam na iya ba da damar ganin kilomita 5,000 na inda giwaye ke rayuwa a duk ranar da babu hadari. Kuma ana gudanar da aikin ƙidayar giwayen mai matuƙar wahala ne da wata komfuta da aka horar don gano giwaye a wurare daban-daban. ""Muna gabatar da wannan misalin ne … kuma mu bayyana shi, wannan giwa ce, wannan ba giwa ba ce, in ji Dakta Ogla Isupova, na Jami'ar Bath. ""Ta hanyar yin hakan, za mu iya yiwa injinanmu setin da za su iya ba da bayanai kan ƙaramin abu, wanda ba za a iya gani da idanu ba."" Da farko masana kimiyyar sun duba gidan namun daji na Addo da ke Afrika ta Kudu. ""Yana da yawan giwaye, ""In ji Dakta Isla Dupoge na Jami'ar Oxford. ""Kuma yana da yankunan da suke da bishiyoyi masu duhu sannan kuma ga fili. ""Don haka wuri ne mai kyau da za mu iya gwada abin da muka zo da shi. ""Wannan wani sabon ilimi ne da ya ke daf da bayyana. ""Kuma manyan ƙungiyoyin masu fafutukar kare muhalli sun nuna sha'awarsu kan amfani da shi domin maye gurbin amfani da jiragen sama."" Masu fafutukar kare muhalli za su riƙa biyan kuɗi don amfani da taurarin ɗan Adam ɗin da hotunan da suke ɗauka. Amma wannan tsarin zai taimaka wajen yadda za a riƙa bin giwayen da ake fargabar rayuwarsu na fuskantar barazana a wuraren da suka ratsa iyakoki, inda da wahala a samu damar yin bincike da jiragen sama. Masana kimiyya sun ce za a iya amfani da wannan tsarin wajen yaƙi da masu farauta ba bisa ƙa'ida ba. ""Kuma tunda za ka iya ɗaukar hoton daga sama, ba ka buƙatar kowa a ƙasa. Wannan zai iya taimakawa a wannan lokaci na annobar Korona,"" in ji Dr Duporge. ""A ɓangaren binciken rayuwar dabbobi, ba a fiye samun ci gaba a fannin fasaha ba. ""Don haka samun damar amfani da sabbin hanyoyin fasaha wajen kare haƙƙin dabbobi abu ne mai kyau.""" https://www.bbc.com/hausa/labarai-55753966 +technology Kotu ta tilasta wa kaka goge hotunan jikokinta da ta sa a Facebook "Wata kotu a ƙasar Netherlands ta yanke hukuncin cewa wata mata ta goge hotunan jikokinta da ta wallafa a shafukan sada zumunta na Fesbuk da Pinterest ba tare da izinin mahaifansu ba. Lamarin ya kai ga kotu ne bayan matar ta samu saɓani da 'yarta. Kotun ta yanke hukuncin cewa batun yana cikin iyakar Ƙa'idar Kare Bayanai ta Tarayyar Turai (EU's General Data Protection Regulation). Wani ƙwararre ya ce hukuncin manuniya ce kan ""matsayin da Kotun Turai ta ɗauka tsawon shekaru game da kare bayanan mutum"". Maganar ta je gaban kotu ne bayan matar ta ƙi goge hotunan jikokinta da ta wallafa a shafukan sada zumunta. Mahaifiyar yaran ta yi ta neman a goge hotunan 'ya'yan nata, amma kakarsu ta yi ƙememe. Tana iƙirarin cewa Ƙa'idojin Kare Bayanai ba sa aiki kan abin da yake na ""tsagwaron raɗin-kai"" ko kuma ""amfanin gida"" ne wajen sarrafa bayanan mutum. Sai dai, wannan togaciya ba ta aiki don kuwa wallafa hotuna a shafukan sada zumunta ya sa wasu dumbin mutane na iya samunsu, cewar hukuncin. ""Ta hanyar Fesbuk, ba za a iya kauce wa yaɗa hotunan da aka wallafa ba kuma suna ma iya ƙarewa a hannun wasu 'yan kiɗanka-na-jiyo,"" in ji kotu. Jazaman ne sai matar ta cire hotunan ko ta biya tarar yuro hamsin kwatankwacin naira 21,000 kullum da ranar Allah Ta'ala da ta ƙi biyayya da umarnin, har zuwa mafi tsanani a ci ta tarar yuro 1,000. Idan kuma ta sake wallafa hotunan yaran a nan gaba, kotu za ta sake cin ta tarar ƙarin yuro hamsin a kullum. Wani lauya kan ayyukan ƙere-ƙere, Neil Brown ya ce ""Ina jin hukuncin zai bai wa ɗumbin mutane mamaki waɗanda mai yiwuwa ba sa zurfafa tunani kafin su wallafa saƙon tiwita ko kuma su buga hotuna"". ""Ko ma ba matsayin doka, shin ba zai fi hankali ba ga mutanen da ke wallafa irin waɗannan hotuna su yi tunani, 'Anya, ƙila wanda ko wadda zan sa hotonsa ko nata, ba zai so haka ba""." https://www.bbc.com/hausa/labarai-52764695 +technology Mandla Maseko: Dan Afirka na farko da za shi sararin samaniya ya mutu "Wani dan Afirka Ta Kudu da ya zama dan Afirka na farko da ya samu nasarar samun damar zuwa sararin samaniya ya mutu a hatsarin babur kafin ya cimma burin nasa. Mandla Maseko mai shekara 30 ya mutu ranar Asabar, kamar yadda wata sanarwa da iyalansa suka fitar ta ce. A shekarar 2013 ne jami'in rundunar sojin saman Afirka Ta Kudun ya samu nasara a gasar da kusan mutum miliyan daya suka shiga wacce aka zabi mutum 23 kadai ciki daga wata makarantar kula da sararin samaniya ta Amurka. Matashin wanda ake yi wa lakabi da Afronaut ko Spaceboy, Maseko ya bayyana kansa a matsayin matashin da ya fito daga yankin marasa galihu a Pretoria. Da yawan wadanda suka bayyana jimamin mutuwar tasa a shafukan sada zumunta sun yi ta tuna shi da lakabin sunayensa. Ya shafe mako guda a Cibiyar Zuwa Sararin Samaniya Ta Kennedy da ke Florida, inda ya dinga gudanar da gwaje-gwaje kan shirye-shiryen bulaguron da zai yi zuwa sararin samaniya na sa'a daya, wanda tun farko aka shiruya yin sa a shekarar 2015. Daga cikin kalubalen tafiyar akwai shawagi a sarrain samaniya daga nisan kamu 10,000. Sai dai kuma bai samu damar zuwa samaniyar ba. Kamfanin da ya shirya hakan XCOR Aerospace, ya fada matsin tattalin arziki a shekarar 2017, a cewar kafar yada labaran Space.com. Maseko ya koma aiki da rundunar sojin a matsayin mai tukin jirgi. A lokutan da ba na aiki ba kuma yana son wasan tseren babur da kuma sanya kade-kade a wajen taron liyafa.\ Masekoya taba cewa yana son yin wani abu da zai bai wa matasan Afirka kwarin gwiwa ya kuma tabbatar musu da cewa za su iya cimma duk abin da suke so ko da kuwa daga wane irin yanki suka fito. Ya shaida wa BBC cewa cewa ya shirya kiransu daga sararin samaniya. ""Ina fatan a samu wani layi da za a dinga amfani da shi a shekaru masu zuwa - kamar yadda Neil Armstrong ya yi,"" a cewarsa. Wani Ba'amurke da ya ya mutu a 2012 yana da shekara 82, shi ne mutum na farko da ya taba zuwa duniyar wata a 1969. A lokacin da ya shiga duniyar wata ya ce: ""Wannan karamin mataki kenan daga mutum, kumma babban kokari ga dan adam.""" https://www.bbc.com/hausa/labarai-48889552 +technology Fafutukar #MeToo bayan shekara biyar: Akwai abin da ya sauya? "A daidai wannan lokacin shekaru biyar da suka gabata abu ne mai wahala mutum ya ce bai lura da fafutukar #MeToo da ta karade shafukan sada zumunta ba. Abin da ya samo asali daga wani sakon Tiwita ya rikide zuwa tafka muhawara kan cin zarafin mata a sassan duniya. ""Muhawarar Me Too ba ita ce ta farko ba kan batun cin zarafin mata, kuma ba ita ce ta fara yaduwa kamar wutar daji ba, kuma a sassan duniya fafutukar ta haska aikin da aka dade ana yi amma a wani yanki na duniya"", inji Farfesa karen Boyle, wadda ita ce shugabar cibiyar binciken jinsi kuma malamar Jami'ar Stathclyde. Fafutukar ""Me Too"" ta samo asali ne yayin da Tarana Burke wata mai fafutuka wadda ta yi amfani da kalaman Me Too a 2006 domin jan hankulan jama'a kan matsalar muzgunawa mata. Shekaru 11 bayan lokacin a 2017, fafutukar ta bayyana yayin da Alyssa Milano, wata 'yar fim Ba'Amurkiya ta wallafa sakon Tiwita tana kira ga mata su bayyana ra'ayinsu kan batutuwan cin zarafin mata da na fyade. Milano ce mace ta farko da ta zargi attajirin mai hada fim Harvey Weinstein da cin zarafinta da yi ma ta fyade. A ranar da ta wallafa sakon nata, 15 ga watan Oktoba, an yi amfani da kalaman ""Me Too"" fiye da sau 200,000 a shafukan sada zumunta, kuma zuwa kashegari a yada su fiye da sau 500,000. #MeToo ya bazu zuwa kasashe fiye da 85 da kuma harsuna masu yawa. Lallai wannan fafutukar ta samo asali ne a Amurka, amma tasirinta ya zagaya duniya. Ga Farfesa Boyle, abu mafi muhimmanci shi ne rarrabe hayaniyar da aka yi ta ""Me Too"" da ainihin fafutukar neman gyara. ""Na kan bambanta Me Too a matsayin fafutuka mai zaman kanta da kuma jan hankalin da aka rika yi a shafukan sada zumunta na takaitaccen lokaci. Ina ganin har yanzu fafutukar na kara karfi"" A 2015 Juliana de faria, wata wadda ta assasa kungiyar ""Think Olga"" ta kaddamar da wata fafutuka mai suna #MeuPrimeiroAssedio ko kuma ""Cin Zarafina na Farko."" Cikin 'ya kwanaki sai aka rika yada sakon cikin dubban sakonni a Tiwita da ke bayyana yadda ake muzgunawa mata da yi musu fyade a Brazil. Ba da jimawa ba sai sakon ya bazu zuwa dukkan kasashen Lain Amurka wanda ada Sfaniyanci ake kira #MiPrimerAcoso. Cikin 'yan shekarun nan an ga misalai masu yawa daga sassan duniya da suka taimakawa batun ya ci gaba da yaduwa a kasashe kamar China da Birtaniya da Indiya. A Indiya, akwai kiraye-kiraye da ake yi na korar daraktan fina-finan Bollywood Sajid Khan daga taka rawa a shirin talabijin din nan Bigg Boss mai matukar farin jini. Wannan matakin ya biyo bayan zargi da wasu mata takwas ke yi masa na fyade da cin zarafinsu shekaru hudu da suka gabata. Ya musanta aikata wani laifi kuma kawo yanzu ba a gurfanar da shi a gaban shari'a ba. A 2018, fafutukar #MeToo ta bazu a cikin China. Xianzi - wacce ainihin sunanta Zhou Xiaoxuan, na cikin mata masu yawa da suka fara bayyana yadda aka ci zarafinsu ko aka yi musu fyade. Ta wallafa wani labari mai kalamai 3,000 wanda a ciki ta zargi Zhu Jun - wani shahararren mai gabatarwa a tashar talabijin na China CCTV da yayi ma ta fyade a 2014 yayin da ta ziyarci dakinsa domin ta sa damar yin hira da shi. An yi watsi da karar ta a bara saboda rashin isassu hujjoji, sai dai ta kafe, tana cewa ba za ta mika wuya ba har sai an yi ma ta adalci. A watan Mayu, daruruwan mutane sun bazama zuwa titunan kasar nepal suna neman a yi sauyi ga dokokin kasar kan bayyana abin da ake nufi da fyade bayan da wata mai tallan kayan kawa ta walafa wasu jerin bidiyo a TikTok tana cewa an yi ma ta fyade tun tana mai shekara 16 da haihuwa. A kasar Iran kuwa, zanga-zanga ta barke bayan da aka kashe Mahsa Amini, wata 'yar kabilar Kurdawa mai shekara 22 bayan da 'yan Hizban kasar suka tsare ta na wani lokaci. An dai kama Mahsa Aini ne saboda ba ta sanya dan kwali a kanta ba. Bayan shekara biyar, daya daga cikin nasarorin da masu fafutukar suka samu shi ne yadda aka fara amincewa ana yin muhawara kan tasirin cin zarafin mata. Farfesa Boyle na ganin koma bayan da aka samu a fafutukar MeToo saboda ba a cika amincewa da bayana da mata ke yi ba ne. Farfesa Boyle ta ce yaduwa kamar wutar daji da fafutukar #MeToo ta yi ta haifar da wata dama ta musamman ta muhawara amma akwai sauran aiki a gaba. Ta ce, ""A gare ni, idan ana son fafutukar #MeToo ta yadu a ko ina a duniya, tilas ne a yi sauye-sauye a wuraren aiki da makarantu da wuraren wasannin motsa jiki - a dukkan wurare. Duk da cewa wannan aikin ya dauki gomman shekaru, amma yanzu aka fara tafiyar,” in ji ta." https://www.bbc.com/hausa/articles/c514g5pp8vlo +technology Taswirar Google ta gano gawar wani a cikin mota An gano gawar mutumin da ya bata shekaru 22 da suka gabata a Florida ta hanyar amfani da taswirar Google. Tun a watan Nuwambar shekarar 1997 aka kai rahoton bacewar William Moldt daga Lantana a Florida. Mai shekara 40 a duniya, ya fita shakatawa gidan casu da daddare amma kuma sai bai koma gida ba. 'Yan sanda sun fara gudanar da binciken bacewarsa a lokacin amma daga bisani batun ya bi shanun sarki. Amma a ranar 28 ga watan Agusta da ya wuce, aka kira 'yan sanda kan an gano wata mota a cikin ruwa a yankin Moon Bay Circle a Wellington. A lokacin da aka fito da ita daga kududdufin., sai aka ga kwarangwal din mutum a ciki. Mako guda bayan nan aka gano kwarangwal din Mista Moldt ne bayan gudanar da bincike. Wani mutum ya gano motar ne ta hanyar amfani da taswirar Google da ke nuna inda mota ta ke kamar yadda 'yan sanda suka bayyana. Mutumin ya yi gaggawar shaidawa 'yan sanda akwai mota a cikin ruwan da ke Moon Bay cirle, bayan amfani da dan karamin jirgi mara matuki na fasaha. Wani rahoto da kamfanin fasaha na Charley Project ya wallafa, ya ce google ya nuna motar muraran tamkar ta na waje kamar yadda hotunan tauraron dan adam ya nuna tun a shekarar 2007, sai dai kamar babu wanda ya damu ya duba har sai wannan shekarar. Mai magana da yawun 'yan sandan Palm Beach County ta shaidawa BBC cewa su na kyautata zaton mota ta kwacewa mamacin ne a lokacin da ya fada ruwan. Theresa Baebera ta kara da cewa a lokacin da suke gudanar da bincike kan batansa, babu wata shaida da ta nuna akwai mota a cikin kududdufin. 'Kai tsaye babu wanda zai fadi ainahin abin da ya faru tsahon shekarun nan, abin da muka sa ni shi ne Mista Moldt ya bata, a halin yanzu an gano shi''. https://www.bbc.com/hausa/labarai-49685328 +technology Yadda za ku iya hada wayoyin ƴaƴanku da naku Tun bayan da labari ya bayyana a watan Afirlu a shafin itanet cewa kananan yara daga makarantar Chrisland sun dauki kansu wani faifen bidiyo da waya, a yayin da ake cin zarafinsu ta hanyar lalata, ake ta samun martani kan yadda ya kamata mutane su yi don kare ƴaƴansu daga wannan lokaci na fasahar zamani. BBC ta bi diddigin bayanan ƙwararru don samun shawarwarin da za su taimaka wa iyaye sa ido kan abubuwan da ƴaƴansu ke yi a cikin wayoyinsu na salula tare da kare su daga abubuwan da ke faruwa a shafin intanet. Taiwo Ogunlade, wani mai yin sharhi a shafin Google, ya bayyana cewa sun ƙirƙiri wata manahaja da suke kira 'Family Link' don taimaka wa iyaye sa ido kan abubuwan da ƴaƴansu ke yi a shafin yanar gizo. Lokacin da iyaye suka hada da wayoyin salularsu, za su iya toshe ko barin wasu abubuwa shiga cikin wayoyin salular ƴaƴansu. Wannan zai za iyayen su riƙa sanin abubuwan da ƴaƴansu ke kallo. Za ku iya amfani da manahajar wajen toshe shafukan nuna faye-faye bidiyon batsa da sauran abubuwan da ba su kamata ba. Iyaye za su iya amfani da ita wajen sanin tsawon lokacin da ƴaƴan nasu suka shafe wajen amfani da wayoyin. Hakan na nufin cewa iyayen za su iya kashe wayoyin salular ƴaƴan nasu a lokacin da wa’adin da aka daukar musu ya ƙare. 1. Bude wa ɗanka shafin aika saƙonnin email na Gmail da shekarunsa na gaskiya. 2. Sauke manahajar Google Family Link a kan wayar salular iyaye. 3. Saka adireshin Gmail ɗin da ka yi wa ɗanka rijista da shi cikin manahajarka Google family link. 4. Yi amfani da sunan ɗanka na adireshin email ɗinsa wajen shiga cikin wayar salular, kana ka kunna. Wayar salularka za ta fara aiki tare da ta ɗanka. 5. Za su iya fara amfani da wayoyin, amma ba za su iya shiga cikin shafukan intanet da manya ke shiga da wayoyin nasu ba. Ya kuma fitar da wasu shawarwari da za su taimaka wa iyaye sa ido kan sauran wayoyin ƴaƴan nasu. Sun hada da: BBC ta tattauna da wata ƙwararriya a fannin al’amuran da suka shafi ƙananan yara, kana mai horarwa, Dakta Maymunah Kadiri, don yin karin haske kan abubuwa da dama da mutum zai iya sa ido kan ƴaƴansu da ke amfani da shafin intanet. Dakta Maymunah wacce kuma ƙwararriya ce a fannin lafiyar ƙwaƙwalwa da kuma gaɓoɓi, ta bayyana cewa da zarar ka sauke manahajar ta family link, za ku samu wata sanarwa da ke son shiga shafukan da ba su kamata ba, ta ce haka ta yi wa nata ƴaƴan. Sauran shawarwarin da ta bayar sun ƙunshi: Dakta Maymunah ta bayyana cewa shekarun da suka dace ga ƴaƴanku su fara riƙe wayoyin salula kuma karkashin sa idon iyaye su ne daga shekara 13. Ya kamata iyaye da makarantu sun rika neman taimakon ƙwararru a fannin fasahar sadarwar zamani su rika dubawa tare da goge wasu abubuwa marasa amfani daga cikin wayoyin ƴaƴansu, saboda wasu daga cikinsu na saukewa tare da ɓoye wasu abubuwa marasa kyau a cikin wayoyin. Wasu daga cikin abubuwan da yaran ke kallo, ko ji ko karantawa na haifar da wasu matakai na lalata ƙwaƙwalwa idan suka girma cikin haka. Dr Maymunah ta bayyana cewa yara a wannan zamani suna da matukar basira, da son sanin abubuwa, su kan shiga shafin matambayi baya ɓata na Google su samu hanyoyin da za su iya karya lagon makullin kare yara daga shiga wasu shafukan intanet da ba su kamata ba. Ta ce yaran za su iya nuna ɓacin ransu, amma su dage sosai. Kamar yadda ta bayyana, makarantu ne ya kamata su samo hanyoyin sa ido kan wayoyin da ɗalibai ke zuwa da su zuwa makaranta. Ta kuma ƙara da cewa wasu daga cikin su sun fi samun damar shiga cikin shafukan intanet marasa kyau a gare su a lokacin suna makaranta. https://www.bbc.com/hausa/articles/crgrg6x613ko +technology Yadda fasahar na'ura za ta iya wargaza bil'adama "Manyan masana kimiyya, irin su Stephen Hawking da Elon Musk, sun nuna damuwa kan yadda mutum-mutumi masu kwakwalwa za su iya zama barazana ga cigaba da wanzuwar dan Adam. Amma wani sabon littafi ya nuna cewa, ba wai yin amfani da tunaninsu ko kuma bijirewa da far wa mutane ne hadarin ba. Babban hadarin shi ne yadda wadannan mutum-mutumi suka kware wajen aikata abin da aka sa su su yi, wanda idan ba a yi hankali ba za su iya kawar da mutane idan aka yi kuskuren sa su aikata wani abu da kuskure. Farfesa Stuart Russell na jami'ar California ya rubuta wani littafi mai suna ""Human Compatible: AI and the Problem of Control"", kuma kwararre ne a kan ci gaban da aka samu a bangaren kirkire-kirkiren na'ura. Ya shaida wa BBC cewa ""Hasashen masu shirya fim shi ne na'ura za ta mallaki tunani inda za ta iya samar da kiyayya tsakanin ta da dan Adam, daga nan sai ta kashe mu baki daya."" To amma mutum-mutumi ba su da dabi'u irin na dan Adam ""Saboda haka babu hujjar damuwa da irin haka."" ""Ba magana ce ta mummunan tunani ba. Abin da ya kamata, mu fi damuwa da shi, shi ne kwarewarsu - kada su kware wurin aikata wasu abubuwan da aka yi kuskuren umartar su da aikatawa."" 'Gwanancewa fiye da kima' A wata tattaunawa da wani shirin BBC, ya bayar da misalin barazanar da mutum-mutumai masu kwakwalwa za su iya haifarwa. Misali, idan a ce muna da gangariyar na'ura wadda aikinta shi ne ta sarrafa yanayi, wadda kila za mu so tsaftace iskar da muke shaka yadda za ta koma daidai da lokacin da babu masana'antu masu gurbata iska. A cewar Prof Russell ""Idan a misali na'urar ta gano cewa hanya daya da za a cimma hakan ita ce a kawar da dan Adam daga doron kasa, domin su ne suke fitar da sanadarin 'CO2' mai gurabata muhalli."" ""Kila ka ce za mu umarci na'urar ta dauki duk matakan da suka kamata amma ban da kashe dan Adam. To mene ne na'urar za ta yi? Sai ta shawo kanmu cewa mu daina haihuwar yara da yawa, har sai ya zamo cewa babu sauran dan Adam a doron kasa."" Wannan misali ne na irin barazanar da ke tattare da fasahar na'ura wadda mutane ba su yi tsammani ba. Kaifin tunani Yawancin fasahar na'ura da ake da su na dauke ne da manhajar da aka tsara domin ta warware wata takamaimiyar matsala, in ji wata cibiyar bincike a jami'ar Cambridge da ke Birtaniya. An samu ci gaba ne sosai ta wannan fanni a shekarar 1997, lokacin da na'urar Deep Blue ta lashe gasar wasan Chess bayan ta doke gwarzon wasan na duniya Garry Kapparov a wata karawa. Amma duk da wannan nasara, an tsara manhajar Depp Blue ne ta yadda mutane za su rinka amfani da ita wurin buga wasan Chess, kuma za a iya doke ta cikin wasa mai sauki. Sai dai ba haka ba ne a sauran fasahar na'ura da aka kirkiro na baya-baya. Misalai, manhajar wasan kwamfuta na AlphaGo Zero ta yi gwanancewar da ta fi ta dan Adam bayan kwana uku kacal tana wasan ita da kanta. A irin wannan yanayi na'urar na bukatar umarni kalilan ne daga dan Adam wurin gudanar da abubuwan da aka tsara mata. Abin tsoro ne kwarai. Abubuwa ne da na'urar ta yi da kanta. ""Yayin da fasahar na'ura ke kara karfi da fadada, fasahar za ta ci gaba da habbaka - har ta fi ta dan Adam a bangarori da yawa ko ma a kowane bangare,"" in ji cibiyar Existential Risk Centre. Shi ya sa Farfesa Russel ya ce akwai bukatar kada mutane su bari ikon da suke da shi ya kubuce masu. 'Ba mu da tabbas kan abin da muke so' Ya ce samar da wadannan na'urori domin su aikata wani abu guda daya takamaimai ba zai warware wannan matsala ba, domin a cewarsa dan Adam bai riga ya hakikance manufar abin da yake son ya cimma ba. Ya ce, ""Ba mu sanin abin da ba ma so har sai abin ya afku."" ""Ya kamata mu sauya yadda muke kirkirar fasahar na'ura,"" mu kauce wa tsara na'ura kan abin da za ta yi, inda daga bisani takan yi abin da kanta. ""A maimakon haka bai kamata na'urar ta san abin da ake so ta yi ba."" ""Idan na'ura ta kasance a haka, za su bambanta da dan Adam. Za su rinka neman izini kafin aikata wasu abubuwa kasancewar ba su san abin da ake so su yi ba."" ""Idan har fasahar na'urar tana da karfi za ta aikata duk abin da ka umarce ta."" ""Saboda haka, idan na'ura tana aikata wani abu da ba daidai ba, za su zamo barazana ga dan Adam - barazana wadda ta fi karfin dan Adam." https://www.bbc.com/hausa/labarai-50248861 +technology Ya za ku yi idan kuka ga damisar Google a dakinku? "Google ya fitar da wani sabon tsari da zai bai wa masu amfani da manhajar Android damar ganin dabbobi masu motsi da fitar da sauti a wani salo ""kamar a zahiri"" wanda a Turanci ake cewa 'Augmented Reality' (AR) ta kamarar wayarsu. A yanzu tsarin na aiki ne kan wasu dabbobi kawai amma za a fadada shi zuwa kan wasu abubuwan nan gaba. Na'urorin da ke da irin wannan tsarin yanzu sun hada da wasu samfurin wayoyin Huawei da Samsung da LG da OnePlus. Haka kuma, Apple na da manhajojin da ke iya nuna tsarin Augmented Reality kuma wasu masu amfani da wayoyin iPhone na iya amfani da wannan tsarin yayin da wasu ba sa iyawa. Tsarin AR dai wata hanya ce ta hada hotuna da zahiri kuma an kirkiri fasahar ne tun kafin kirkirar wayoyin hannu na zamani amma ci gaban da wayoyin suka samu ya kara fito da fasahar musamman a wasannin da ake bugawa a kan wayoyin na hannu kamar wasan kwamfiyuta na Pokeman Go. Manhajar shagon siyar da kayan daki na IKEA na bai wa kwastomomi damar jera kayan daki a gidajensu ta hanyar amfani da tsarin AR don ganin yadda kayan za su yi a gidan kafin su siya. Wata masaniya a fagen tsaron intanet, Lisa Forte ta yi gargadin cewa dole ne masu kirkirar shafukan intanet da masu amfani da manhajojin AR su yi taka tsan-tsan kan tsaro. ""Shi ma AR ana iya yi masa kutse kamar shafukan intanet da manhajoji,"" a cewarta. Ta ce ""Abin dubawa shi ne a karfafa zubinsa da yadda ake fitar da shi.""" https://www.bbc.com/hausa/labarai-48662073 +technology WhatsApp: Sabon sauyin kafar sadarwar ya bar baya da ƙura WhatsApp ya ja hankalin masu amfani da shi a duniya inda suka wayi gari da sabon saƙo daga kamfanin sadarwar na wayoyin salula, wani sabon salo da ba a saba gani ba. WhatsApp ya turo da saƙon ne ga miliyoyin masu amfani da shi a ranar Laraba 27 ga watan Janairu. Saƙon ya ja hankali musamman a Twitter inda aka dinga muhawara kan WhatsApp tare da ƙirkirar maudu'in #WhatsApp. Tun da dama WhatsApp na fuskantar ƙalubale kan sabon tsarinsa da ya shafi bayanan sirri da ya ce ya ɓullo da shi wanda kuma yake buƙatar masu amfani da kafar su amince ko ya toshe. Miliyoyin mutane ne suka yi ƙaura daga WhatsApp zuwa wasu ire-irensa saboda gudun shiga rayuwarsu ta sirri. Shafin ya ɓullo da wasu sabbin sharuɗɗa ne da suka shafi bayanan sirrin mutane. Miliyoyin masu amfani da shafin a fadin duniya ne suka yi wa wannan shiri tutsu, har ma suka koma amfani da wasu shafukan masu hamayya da Whatsapp kamar Signal da Telegram. A kwanan nan ne Telegram ya ce yawan masu amfani da shi sun haura miliyan 500, kuma ya ƙara samun jama'a daga masu ficewa daga WhatsApp Sakon da WhatsApp ya turo ya shafi ƙarin bayani ne kan sabon tsarinsa inda ya ce sauyin bai shafi bayanan sirri da sakwanni da kiran da mutane ke yi ba, suna cikin tsarin kariya na end-to-end encryption. WhatsApp ya ce ya bullo da sabon tsarin ne saboda kasuwanci domin ba da damar cinikayya a shafukan da aka buɗe domin kasuwanci musamman tsakanin WhatsApp da sauran kafofin sadarwa da suke gida ɗaya Facebook da Instagram. Sannan a saƙon na Whatsapp ya ce zai ci gaba da sanar da masu amfani da shi kan sabbin tsare tsarensa. Masu amfani da WhatsApp da dama sun ce sun yi tunanin kutse aka yi masu. A tsarin WhatsApp sai mutum ya ajiye lambar mutum a wayarsa zai iya ganinsa amma kuma abin da ya tsorata wasu shi ne ganin bayanan WhatsApp da kansa ba tare da saninsu ba ko amincewarsu. Wasu sun ce WhatsApp ne ma ya yi masu kutse, yayin da kuma yake neman su fahimci sabon tsarinsa. @Tomilola_19 ta ce: WhatsApp yanzu a WhatsApp status ruɗani cikin ruɗani, da farko na yi tunanin matsala ce ta samu waya ta lokacin da na ga wannan saƙon. @LachickWavela tambaya ta yi cewa; shin wai ita ce kawai ta ji tsoro lokacin da ta saƙon WhatsApp? cikin murmushi, baki a buɗe da zufa, sai da wasu suka fara buɗewa kada ace wani mugun abu ne. @jamoh_mwa ya wallafa saƙon WhatsApp a shafinsa na Twitter inda ya ce: Wannan ya tsorani #WhatsApp Wasu sun tsorata ne kan yiyuwar tatsar bayanansu zuwa Facebook saboda alaƙarsa da WhatsApp. Me ake cewa a Twitter? Da dama na caccakar WhatsApp ne yayin da kuma wasu suka mayar da saƙon WhatsApp din almara. @FolaWalker123 ya ce yana mamakin a yi masa kutse kuma a ce an damu da sirrinsa. Sai Mark Zuckerberg @ahmedyhasan ya ce: Ta yaya WhatsApp zai tabbatar da kare sirrin mutane. @EzeJohhn kuma saƙo ya rubuta wa shugaban Facebook Mark Zuckerberg, mai mallakin WhatsApp inda ya ce: Idan har za ka iya kutsowa ta taga ka shigo WhatsApp status kuma ba ka cikin waɗanda na ajiye lambobinsu, Ina mamakin inda zaka iya shiga. @leykstar ya yi amfani da maudu'in WhatsApp tare da cewa an yi wa mutane kutse ba da saninsu ba, bayan kuma tabbatar da kare bayanan sirrinsu. WhatsAPP dai ya tsawaita wa'adin da ya ba masu mu'amala da shi na amincewa da sabon tsarinsa. Ya tsawaita wa'adin amincewa da sharaɗin daga ranar 18 ga wannan wata zuwa 15 ga watan Mayu, domin abokan hulɗarsa su samu damar yin nazari, ko kuma ya daina aiki a wayoyinsu idan sun ƙi amincewa. A ƴan tsakanin da WhatsApp ya ɓullo da sabon tsarin, ya yi hasarar miliyoyin masu amfani da shafin. Kuma ana ficewa WhatsApp saboda tsoron mika bayanansu ga Facebook, inda miliyoyin mutane a duniya ke ci gaba da rungumar wasu hanyoyin sadarwa na salula kamar Telegram da Signal don kauce wa sabbin sauye-sauyen WhatsApp. https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-55830271 +technology Wani ya kafa kamfanin binciken gano ko ma'aurata na ha'intar juna a Kano "Shirin ba yana nufin hada husuma tsakanin ma'auratan ba ne, amma shi ne irinsa na farko da zai binciki sirrin miji ko saurayi da aka fara a Kano, arewacin Najeriya. Dalibin Sulaiman Mohammed mai shekaru 22 wanda shi ne shugaban kamfanin karba da kai sakonni na Tall Yaro Express ya ce, a shekarar da ta gabata ne ya zauna ya yi duba kan yadda zai inganta kasuwancinsa na kai sakonnin, lokacin da wannan tunani ya zo masa a rai. ""Ina da abokai da dama da ke harkar fasahar zamani, don haka na fara tunanin lokaci irin wannan da ma'aurata za su san duk wani abu da masoyansu ko abokan zamansu ke yi, dama ce da ba kawai mutum zai iya yin abubuwa kadai ba, har ma da bude wa wasu hanyoyi, na tuntube su kuma suka nuna amincewarsu.'' ""Ta hakan ne na fara aikin binciken gano ko saurayi da budurwa ko miji da mata na ha'intar juna a Kano kusan sama da wata guda kenan, kuma yanzu haka na samu kostomomi biyar da suka gamsu.'' Dalibi a fannin aikin gona ya ce ba za su fada maka cewa mijinsu na ha'intarsu dari bisa dari ba. ""Don haka abin da nake yi wa kostomomina bayan sun ba ni sunayen wuraren da masoyan ko abokan zaman nasu ke zuwa yana aiki ko kuma hutawa. ""Mu kan rika bin diddiginsa muna samar musu da bayanai game da abin da suke yi a duk lokacin da suka bukata.'' ""Misali idan ka kira ka ce ga a a inda yake a yanzu, za mu fada masa cewa yana wurin cin abinci tare da abokai. ""Mu kan yi kokarin kauce wa duk wata hatsaniya, don haka ba ma cewa abokin zama ko saurayi ko budurwa na ha'intarka kai tsaye, wannan ya rage ga shi kansa mtutumin ya gano.'' Sulaiman ya ce tun bayan da ya ƙirƙiro sabuwar hanya ta wannan kasuwanci nasa mata kusan 20 ne suka kira shi suka nuna sha'awarsu na aikin binciken gano ha'incin. ""Mata kusan 20 ne suka kira ni a cikin kwanaki kadan da suka gabata suna nuna sha'awar wannan sana'ar tawa ta binciken ƙwaƙwaf, don haka wani abu ne da ke da alamar samun karɓuwa sosai.'' Matsalar da wanda ya ƙirƙiri wannan shirin ita ce bai samu lasisin amincewa daga gwamnati ba. ""A yanzu dai ban samu amincewar gwamnati ba, amma ina fata wannan abu ne da za ta amince in cigaba da yi tun da kasashen duniya da dama na barin masu aikin bincike masu zaman kansu masu rijista gudanar da aikinsu.'' Walida Sani ta shaida wa BBC cewa ta biya Sulaiman don ya bincika mata saurayinta lokacin da ta fara zargin yana ha'intar ta, kuma ta ji dadin yin hakan. ""Lokacin da na fara zargin saurayina na ha'intata, na samu labarin abin da Sulaiman ke yi, na yi magana da shi na kuma biya shi don ya bincike ko me saurayina ke ciki, kudin babu tsada kuma duka aikin ya faru a tsakanin kwanaki uku.'' ""Bayan binciken ne hankali na ya kwanta cewa saurayina ba ya ha'inta ta, amma saboda gaba zan cigaba da amfani da wannan hanya a duk lokacin da bukatar ta taso.'' Gwamnatin jihar Kano a karkashin hukumar Hisbah da ke da karfin fada-a-ji a jihar ta ce abinda Sulaiman ke yi ba tare da amincewar hukuma ba ba daidai ba ne. Kakakin hukumar ta Hisbah Lawal Fagge ya bayyana cewa hukumar ba za ta amince da duk wani abu da ya saba ƙa'idar addinin Musulunci ba. Kuma muddin mutane suka rubuto musu game da ayyukan Sulaiman za su gudanar da bincike in ji Fagge.'' ""Muddin mutanen da ba su gamasu da irin ayyukan da yake yi ba, suna iya rubuto mana don gudanar da bincike, amma a fili take cewa hukumar Hisbah ba za ta amince da duk wani abu da addinin Musulunci bai yarda da shi ba.'' Sulaiman ya ce yana da ma'aikata huɗu a yanzu, amma yana fatan zai ƙara wasu da zarar kasuwancin nasa ya ƙara bunƙasa." https://www.bbc.com/hausa/labarai-56863708 +technology Microsoft ya bankado yunkurin yin katsalandan a zaben Amurka Kamfanin Microsoft ya yi gargadin cewa kasashen Rasha, da Iran da kuma China sun soma kaddamar da shirin kutsensu, a kokarin fakon 'yan siyasa da kungiyoyin da ke da alaka da zaben kasar Amurka na watan Nuwamba. Kamfanin ya ce ya bankado dukkanin yunkurin da aka yi na satar bayanai, sannan ya dakile dukkanininsu. Akalla kungiyoyi 200 da ke aiki ga 'yan takara biyu na zaben shugaban kasar wato Trump da Joe Biden aka so yi wa kutsen. Masu kutsen wata kungiya mai suna Phosphorus da ke da alaka da rundunar sojin Rasha, da hukumomin Iran sun so satar bayanai daga kwamitin yakin neman zaben shugaba Donald Trump a cewar Microsoft. Yayin da su kuma masu satar bayanan kungiyar Zirconium da ke da alaka da China suka yi yunkurin kutsawa rumbun adana bayanan kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasar na jam'iyyar Democrat Joe Biden, sai dai dukkaninsu, hakansu bai cimma ruwa ba. Manyan shugabannin jam'iyyar Democrat na zargin wasu manyan ƙasashen waje da kokarin yin katsalandan a zaben watan Nuwamba da ke tafe. Shugabar majalisar wakilian Amurka Nancy Pelosi da kuma jagoran 'ƴan Democrats Chuck Schumer a majalisar dattiajai, sun bayyana damuwa cewa ana kokarin amfani da majalisa domin yada labaran karya. A cikin wata wasika da suka aikawa hukumar FBI, shugabanin Democrats ɗin sun bayyana damuwa kan barazanar da suka ce ke tattare da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa. Sun ce barazanar ta kunshi wani yunkuri na ƙaddamar da wani kamfen na kokarin yada wata farfagandar karya. https://www.bbc.com/hausa/labarai-54112674 +technology Sauyin yanayi: Me ake nufi da adana iskar carbon, shin zai iya ceto duniya? "Idan duniya na son kauce wa fuskantar sauyin yanayi mafi muni, ana bukatar masana'antu su tabbatar sun daina fitar da gurbataccen hayaki baki daya daga nan zuwa 2050, hakan na nufin za mu cire irin iskar carbon daga sararin samaniya ta kowacce fuska. Hakan dai masana kimiyya na Majalisar Dinkin Duniya ke fata, wadanda suka yi gargadin muna cikin tsaka mai wuya sakamakon yadda ake samun karuwar digiri biyu na gurbataccen hayaki. Wannan zai sanya wurare da dama a doron kasa su yi matukar wuyar zama. Masanan sun ce abubuwa kamar dasa bishiyoyi da kimiyya, kamar kama carbon da adanawa, za su sanya a kauce wa mummunan bala'in sauyin yanayi. Sai dai ga yawancin masu rajin kare muhalli, wannan babbar barazana ce kuma bai dace ba sam. Ana farawa da dasa bishiya, zuwa sauya yadda muke yin noma, da daina kona bishiyoyi a gonaki, wanda ke kara haddasa dumamar yanayi. Matukar za a kauce wa hakan lallai za a samu gagarumin sauyi. Tun a shekarun 1970, aka samu ci gaban kimiyya wadanda aka yi wa lakabi da kamawa da adana carbon, daga lokacin ake ta samunsu cikin kankanin lokaci. ""Akwai hanyoyi da zabi da dama, wanda aka fi sa ni shi ne kama gurbataccen hayakin da masana'antu ke fiutarwa. Daga nan sai a adana shi cikin bututu a kuma adana shi,"" in ji Samantha McCulloch, da ke jagorantar shirin kamawa da adana Carbon a cibiyar kamakashi ta duniya. Shirin ya hada da zukewa da adana carbon cikin bututun da ke dauke da sinadari solvent, ana kama carbon ana kuma sakin sauran iskar gas. Amma masana kimiyya na amfani da zafi wajen kebance carbon. ""Wata hanyar ta kama carbon shi ne a cirewa kai tsaye daga sararin samaniya ta hanyar iska.Koma wacce hanya aka bi, babu shakka wannna hanya ce ta dumama duniya,'' in ji ta. Sai dai wasu masu rajin kare muhalli sun nuna damuwa, damuwar kuwa ita ce hanyar da za a bi a kama carbon zai sake ingiza fitar da gurbataccen hayaki cikin sauri maimakon hana fitarsa baki daya. A shekarar 2021, babban taron kasashen duniya kan sauyin yanayi, ya ga irin tarin bincike da nazarin kimiyya da aka gudanar da zai taimaka wajen cimma wannan manufa. Babbar hanyar kaucewa fitar da hayakin da ke gurbata muhalli, ita ce kaucewa kona daji, kamar yadda Piera Patrizo da ke bincike kan sauyin yanayi Kwalejin Imperial da ke Birtani ta bayyana. ""Yawancin masu kare muhalli sun amince kudaden da ake kashewa wajen kama carbon, kamata ya yi ayi amfani da su wajen bunkasa samar da makamashi mai tsafta,"" in ji ta. Masana kimiyya sun bukaci sai an tanadi makamashi mai inganci, sannan ne za a kaucewa gurbacewar muhalli, da fiytar da gurbatacciyar iskar da ke janyo mummunann dumamayar yanayi a duniya. Sun karkare da kare bayanan ta hanyar tarasu a wani kundi da aka wallafa rahoton a farkon watan nan. Wasu na ganin cire carbon dioxide na daga cikin hanyoyin da suka rage da za a magance rage gurbataccen hayaki, misali irin hayakin da manyan masana'antu da kamfanoni ke fitarwa, wanda ke yin illa ga muhalli da duniya baki daya. ""Wannan hanya na bukatar tsananin zafi. Sannan kusan kashi daya cikin uku na hayakin da masana'antu ke fitarwa na dauke da sinadarai masu gurbata muhallai, ana kum abutara daukar matakn kare hakan,"" in ji Samantha McCulloch. Hanya mafi sauki, da kare afkuwar abin da masana kimiyya da masu rajin kare muhalli ke kokarin kaucewa, shi ne samar da sabbin dazuka ko alkinta wadanda ake da su, hakan hanya ce ta kaucewa lalata muhalli da gurbataccen hayaki ke haifawar a duniya. Sai dai Patrizio ta ce akwai kuma yanayin da akan shiga da ba sa yi wa muhalli illa sosai, amma hakan ba abin dogaro ne ba. ""Manufar shuka bishiyoyin kamar na wucin gadi ne, matukar ba za a dauki matakin kaucewa yin abin da ke haddasa gurbacewa da fitar da hayakin gurbatacce, har sai an tabbatar da alkinta dazukan da ake da su,"" ta kara bayani. Sai dai masana na cewa a wasu kasashen duniya, lamarin babu sauki wajen zuba jari a fannin makamakashi mai inganci, ba kuma kowa ake bari ya yi hakan ba. Sannan a kasashen da suke sahun gaba a fitar da gurbataccen hayakin, lamarin mai sauki ne. ""Sai dai har yanzu sabuwar hanyar kimiyya ce da ba a waye da ita ba,"" in ji Christoph Beuttler, shugaban kungiyar Climework, cibiya ta farko ta 'yan kasuwa da ke aikin kama carbon kaiu tsaye daga iska. ""Aikinmu shi ne samar da fankoki a manyan ma'aikatu da masana'antu da kamfanoni, domin cire carbon daga sararin samaniya, tare da adanawa ta dindindin a karkashin kasa,"" in ji shi. Hoton sama ya nuna yadda kai tsaye ake kama carbon ta amfani da iskar fanka, kuma ba tare da wata babbar barazana ko matsala ga muhalli ba. Sai dai a yanzu abin tambayar shi ne, ta yaya za a ci gaba da yin amfani da iskar fankar wajen kama carbon, sannan ko hakan zai yi tasari nan gaba. Masu goyon bayan yaki da sauyin yanayi (CCS) sun ce ko da an daina amfani da makama daga nan zuwa shekarar 2030 ko 2040, tsohon hayakin da ya gurbata iska ya na nan. Wannan shi ne kwararru suka kira carbon mai tsohon tarihi da ake bukatar kakkabewa. ""Shin hayakin ya gurbata mana duniya ne? kuma ta yaya za a magance hakan? wadanda ke goyon bayan ci gaba da amfani da gurbatacciyar iska ba su yi adalci ba. Wasu na ganin kamar ba mu damu ba, mun damu matuka,"" in ji Patrizio ta Kwalejin Imperial da ke Landan." https://www.bbc.com/hausa/labarai-61191343 +technology ‘Ban yi makaranta ba amma na kirkiri injin ban-ruwa mai amfani da hasken rana a Sokoto’ Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon: Wani matashi mai shekara 30 mai suna Mansur Mabera, da ake wa laƙabi da injiya ya ƙirƙiri abubuwa masu yawa. Abin da ya ƙirƙira a baya-bayan nan shi ne wani injin ban-ruwa a lokacin noman rani, mai amfani da hasken rana. Wannan abu da Mabera ya yi ya zamo wata hanya ta ban ruwa tsirrai a yankunan karkara a lokuacin rani. Ga dai rahoton Haruna Shehu Tangaza kan hakan. Tace bidiyo: Abdulsalam Usman Abdulkadir https://www.bbc.com/hausa/media-60114455 +technology Za a dauki hoton ramin black hole daga duniyar taurari Masana kimiyyar da suka dauki hoton Black Hole a farko sun bayyana aniyarsu ta daukar sabon hoton na bidiyo ramin daga tsakiyar duniyar taurari. Sun bayyana cewa za su harba tauraron dan adam da zai taimaka wa kamarorinsu takwas wajen daukar hoton bidiyon. Masu binciken sun ce sun kara inganta abin hangen nesan da za su yi amfani da shi wajen daukar hoton da yadda za a iya ganin yadda black hole din zai iya hadiye abubuwan da ke gefensa. Masu binciken da suka gano ramin Black Hole an ba su lambar yabo ta karramawa ta ilimin Physics. Farfesa Heino Falcke na Jami'ar Radboud da ke Netherland, shi ne ya bada shawarar amfani da ''Event Horizon Telescope,'' wanda shi ne tabarau na hangen nesan da zai taimaka wajen yin bidiyon. Ya shaida wa BBC cewa mataki na gaba shi ne ganin ramin Black Hole a bidiyo ba wai a tsaye cik a hoto ba. Ya bayyana cewa kamar yadda duniya ke juyawa, shi ma ramin Black Hole na juyawa, kuma saboda nauyin da ke tattare da ramin, yana kawo cikas ga lokaci da kuma sararin da ke kusa da ramin. Babban abin wahala shi ne daukar hoto mai kala na irin wannan ramin na Black Hole. A farkon shekarar nan, masu binciken sun wallafa hoton ramin black hole din da suka dauka a tsakiyar duniyar taurari da aka kimanta da kusan kilomita biliyan 40, girman duniyar da muke ciki sau uku kenan. Hoton ya nuna iskar gas mai zafin gaske na shiga cikin ramin a launin ruwan lemo. Shi dai ramin Black Hole bai da wani launi, amma abin da masu ilimin taurari ke iya gani shi ne yadda wani iskar gas mai zafi ke kwarara cikin ramin. Iskar gas din na sauya launi idan ta dumfari shiga ramin, tamkar rana idan za ta fadi da yamma cikin gajimare. Wasu kamfanoni na da niyyar kara abin hangen nesa na girke da za a ajiye a Greenland da kuma Faransa da wasu sassa na Afirka, inda suka nemi tallafi daga wata kungiya a Amurka da ke taimakawa wajen bunkasa kimiyya. Sun bukaci kungiyar da ta kara tauraron dan adam uku da za su taimaka wa aikin da ake yi a kasa da abin hangen nesa. Farfesa Falcke ya bayyana cewa wannan zai samar da abin hangen nesa ingantacce kuma na daban, wanda zai iya daukar hoton ramin Black Hole daga tsakiyar duniyarmu. https://www.bbc.com/hausa/labarai-49600352 +technology Ana samun karuwar bidiyon bogi mai kamar gaske Sabon binciken da aka gudanar ya bayyana cewa ana samun karuwa matuka a bidiyon bogi da ake hadawa wadanda ke wuyar tantancewa, yawan irin wannan bidiyon ya ninka sau biyu a watanni tara da suka wuce. Akwai hujjoji da ke nuna cewa hada irin wadannan bidiyoyin ya zama babbar sana'a. Duk da cewa wannan bincike ya fi karkata ne kan yadda ake amfani da irin wadannan bidiyoyi wajen siyasa, hujjoji sun tabbatar da cewa an fi yin irin wadannan bidiyoyin wajen fina-finan batsa. Kamfanin ''Deeptrace'' ne ya gudanar da wannan bincike wanda kamfani ne da ya shahara wajen samar da tsaro a intanet. Bincikenta ya gano bidiyo kusan 14,698 idan aka hada da Disambar 2018 da aka samu 7,964. A cikin irin wadannan bidiyoyi an gano cewa wadanda aka yi wa sharri 'yan wasan kwaikwayo ne na Amurka da Birtaniya, haka zalika binciken ya gano harda wasu mawaka na kasar Korea su ma an yi musu irin wannan sharri. Rahoton binciken ya bayyana amfani da irin wadannan bidiyoyin wajen kamfe din siyasa, amma a lamura kusan biyu da binciken ya nuna - na kasar Gabon da Malasiya, zarge-zargen da ake yi na bidiyoyin bogi an gano ba gaskiya bane. Amma babban abin a yanzu shi ne, yadda mutane ke hada fina-finan batsa da fuskokin mutane domin cimma wata manufa ko kuma ramuwar gayya. Kasancewar kamfanin Deeptrace wanda ya gudanar da wannan bincike, wata hujja ce da ke nuna yadda irin wadannan bidiyoyi na bogi suka zama abin damuwa matuka ga gwamnatoci da kuma kamfanoni. Kamfanin ya bayyana manufarsa a matsayin ''kare mutane da kamfanoni daga irin abubuwan da kan musu illa ta intanet,'' An fara amfani da kalmar ''deepfake,'' a 2017, wacce kalma ce da ke nuni da matukar yadda ake hada bidiyo ko hotuna na bogi, kuma wannan rahoton ya yi bayani kan cewa a cikin shekaru biyu, wannan lamari ya zama babbar sana'a da take kawo wasu manyan kudade. Binciken ya gano cewa wasu shafukan intanet hudu na batsa da ke kan gaba wajen wallafa irin wadannan bidiyoyi na bogi sun samu kusan mutum miliyan 134 sun ziyarci shafin domin kallo tun Fabrairun 2018. Irin manhajojin da ake amfani domin hada irin wadannan bidiyoyi sun fara yawa. https://www.bbc.com/hausa/labarai-49964532 +technology 737 Max: An amince wa Boeing dawowa sararin samaniyar Turai Hukumar da ke lura da lafiyar jiragen sama ta Turai ta fadawa BBC cewa ta tabbatar da lafiyar jirgin Boeing samfurin 737 Max. An dakatar da 737 Max a watan Maris ɗin bara, bayan da yayi hadari har sau biyu da hakan yayai sanadin salwantar rayuka 346. Dama Amurka da Brazil sun amince masa da ya dawo da aiki sararin samaniyarsu. A yanzu itama hukumar ta EASA da ke kula da sufurin jiragen sama a Turai ta tabbatar da cewa jirgin ba shi da wata matsala, kuma ta aminta ya dawo bakin aiki a fadin nahiyar a tsakiyar watan Janairu. Hadarin 737 Max na farko ya faru ne a watan Oktoban 2018, a lokacin da jirgin mallakar Lion Air ya faɗa a wani teku da ke kusa da Indonesia. Kuma watanni huɗu bayan haka ne samfurin jirgin mallakar Ethiopian Airlines ya faɗi jim kaɗan bayan tashinsa daga filin jirgin sama da ke Adis Ababa. A duka haɗurran biyu, masu bincike sun ta'allaƙa faruwarsu ne da matsalar wata na'ura da ke kunna kanta da ke sa jirgin ya rikito ƙasa da kansa. A cewar shugaban hukumar EASA Patrick Ky, ba matsalar da ta haddasa faduwar 737 Max har sau biyu ce kaɗai suka duba ba, sun yi wa jirgin binciken ƙwaƙwaf kuma sun tabbatar da lafiyarsa a wannan karon. Hukumar ta kuma shata cewa dole ne matuƙan jirgin su halarci wani horo na musamman, tare da yin 'tuƙn gwaji' ga duka jiragen Boeing samfurin 737 Max. https://www.bbc.com/hausa/55391387 +technology Adan Hussein Dida: Dalibin firamaren da ya samar wa ƙauyensu wutar lantarki a Habasha "Wani ɗan shekara 14 ya samu kyautuka bayan ya samar wa gidaje da dama wutar lantarki a ƙauyensu na Borana da ke kudancin Habasha wato Ethiopia. Adan Hussein Dida, wanda ɗan aji na 8 ne a makarantar firamare ta Tula Web, ya ce ya ƙirƙiri lantarkin ce saboda ya rage wa mazauna ƙauyen wahalhalun da suke fama da su kamar rashin hanyoyi da asibitoci da lantarkin kanta. Ya ƙaddamar da aikin ne daga cikin gidansu, inda ya zuba kashin dabbobi cikin wani rami mai tsawon mita biyu. Daga nan ne kuma ya samar da wuta ga gidaje takwas. Ya caji kowane gida dala 0.87 duk wata. Akasarin mazauna ƙauyen makiyaya ne da suka dogara da kiwon dabbobi, amma sun kasance cikin taluci sakamakon fari da Ethiopia ta fuskanta a watannin baya. 'Yan gidan su Adam sun yi amfani da kuɗin da suke samu daga lantarkin tasa wajen kula da kansu. ""Ina alfahari da abin da na cimma zuwa yanzu, sun ce na tseratar da su daga sayen batiri da kuma cocila. Yanzu 'ya'yansu za su iya yin karatu daga gida ba sai sun jira zuwa safiya ba saboda rashin haske,"" a cewar Adam. Malamin Adam mai suna Boru Sora ya ce ɗalibin nasa yana ƙara faɗaɗa aikin nasa zuwa gidaje masu yawa duk da matsalar rashin kyawun hanyoyi da suke fuskanta, wanda ke hana shi samun kayan aiki cikin sauƙi. ""Ɗalibi ne mai fikira. Baya ga samar da lantarkin, ya ƙoƙarta gyaran abubuwa da yawa kamar rediyo da sauran kayan lantarki, har ma da ƙera jirgin da ke tashi tsawon mita 100,"" in ji Mista Boru. Da yawa daga cikin ɗaliban makarantar da Adan ya ba su ƙarfin gwiwa suna ta ƙirƙiro nasu ayyukan. Burinsa shi ne ya karanta fannin injiniyanci a sabuwar Jami'ar Borana da ke Yebelo." https://www.bbc.com/hausa/labarai-60496133 +technology Google ya cika shekara 23: Ga abubuwa 21 da ba ku sani ba game da Google An fara wallafa wannan makala a ranar 27 ga watan Satumban 2019 lokacin da shafin ya cika shekara 21. Mun sabunta shi a yanzu da ya cika shekara 23 da budewa. Google ya cika shekara 21 a ranar Juma'a 27 ga watan Satumba! Mutane da dama ne daga kowane sassa na duniya ke amfani da fitaccen shafin na matambayi ba ya bata, kuma yana da muhimmanci sosai ga dumbin jama'a. Domin bikin wannan rana, mun tattaro wasu bayanai na hakika daga kamfanin wadanda ba lallai ku sani ba - sai dai idan kun tambaya a shafin google din. 1. Abin da zai ba ku mamaki shi ne cewa Google ne shafin da aka fi ziyarta a duniya - ko a takwaransa shafin Bing ma Google din ne abin da aka fi dubawa. 2. Wasu daliban kwaleji biyu ne suka kirkiri shafin Google masu suna Larry Page da Sergey Brin. Sun so su kirkiri wani shafin intanet ne wanda zai jero shafuka kan yadda wasu shafukan ke alakanta kansu da su, da zai dan yi kama da shafin intanet. 3. Kalmar Google ta samo asali ne daga 'googol', wacce ita ce ta farko da ta biyo bayan sifili 100. Wadanda suka kirkiri shafin sun zabe ta ne don ta dinga nuna bayanai masu dumbin yawa da suke nema ta hanyarta. 4. Shafin 'google doodle' wanda shi ne irinsa na farko (a lokacin da Google ya sauya bangon shafinsa domin shaida wani abu mai muhimmanci) an kirkire shi ne a lokacin bikin 'Burning Man Festival' na shekarar 1998. Wadanda suka samar da shafin na so mutane sun san dalilin daya sa suka fice daga ofishin. 5. Wasu daga cikin abubuwan da Google suke tunawa shi ne bikin gano ruwa a duniyar wata da kuma ranar bikin haihuwar John Lennon na cika shekara 70, wanda shi ne bidiyon farko irin shi a doodle. 6. An ajiye ma'adanar bayanan intanet ta farko da Google ya mallaka ne a wani akwati da aka hada da robobin Lego.. 7. Ana kiran shelkwatar Google da 'Googleplex' wanda ke a Silicon Valley da ke California. 8. A Googleplex din, akwai wani katon gunkin dabbar Dinosaur, wanda yawanci yake kewaye da balbelu. Ana rade-radin cewa hakan na tunatar da ma'aikatan Google din kar su bari a manta da kamfanin ko ya zama tarihin kamfanin ya shafe. 9. Shelkwatar katafariya ce kuma akwai itace da ciyayi da yawa. To a maimakon a yi amfani da nau'rar yanke ciyawa, Google na hayar awaki ne domin yanke musu ciyayi. 10. Google ne babban kamfanin fasaha na farko da ya fara bai wa ma'aikatan shi abinci kyauta su kuma bari ma'aikatansu su zo da karnukansu wurin aiki. 11. An kaddamar da shafin duba hoto na Google a watan Yulin shekarar 2001 kuma koriyar rigar da kamfanin Versace ya yi wanda Jennifer Lopez ta sanya a karbar lambobin yabo na Grammy ne ya zaburara da samar da shafin. Rigar ce ta zama abin da aka fi dubawa a shafin, sai a zahiri baza'a iya ganin sa ba. 12. Google ya fara sanar da ayyukansa na e-mail wadanda aka fi sani da G-mail a ranar 1 ga watan Afrilu wato (April Fool's Day) na shekarar 2004. Ganin haka, sai mutane ba su dauka cewar da gaske ba ne. 13. An kara kalmar 'google' a kamus din Merriam-Webster a shekarar 2006, wanda ke bayanin ma'anar kalmar da cewar ayi amfani da shafin domin samun bayanai akan adireshin intanet a na duniya wato World Wide Web.'' 14. Youtube ya zama cikin daya daga cikin manhajojin Google a 2006, bayan an sayar da shi fiye da dala biliyan daya da dubu 500. A yanzu haka, shafin YouTube na da masu amfani da shafin kusan mutum biliyan biyu a kowane wata, ana kuma shafe fiye da awanni 400 ana sauke bidiyo a kowane minti. 15. Wani marubucin manhajar kwamfiyuta a Google ya yamutsa hazo a intanet bayan da ya kara '/' bisa kuskure ga rajistar shafin kamfanin. Sakamakon haka, a kusan ko wanne shafin intanet aka samu '/', lamarin da ya sa aka kasa samun komai a intanet din. 16. Kashi 15% cikin 100 na binciken bayanai da ake yi a kullum a Google ba a taba bincike a kansu ba. 17. A watan Afrilun 2018 ne Google ya zama kamfani na farko da ya cimma kashi 100 bisa 100 na samun makamashi maras gurbata muhalli. Wannan na nufin kamfanin na da damar sayen kilowatt na makamashin da zai yi amfani da shi a duk kilowatt daya da ya yi amfani da shi. 18. Hasali Google na da akalla bukukuwan ranar haihuwa guda shida, sai dai ya zabi ya yi murnar bikin a ranar 27 ga watan Satumba. 19. Google na da dabaru da dama wajen bincike. Misali, idan kana neman ma'anar kalmar 'askew', to duka amsoshin da zai baka za su zo a murde. 20. Ga duk binciken da aka gudanar a shafin Google, ana bukatar daukacin fasahar kwamfiyutar da aka yi amfani da ita don aikawa ga 'yan sama jannatin Kumbo Apollo 11 a duniyar wata. 21. A zamanin yanzu, Google ya zarce injin din nema ko tattara bayanai kawai, a nan gaba ana shirin kara abubuwa kamar su basirar na'urori, da sabon wasanni na intanet har ma da motocin da basu da matuka. https://www.bbc.com/hausa/labarai-49851082 +technology An bai wa ɓera lambar yabo saboda bajintarsa ta gano bama-bamai "An bai wa wani bera dan asalin Afirka lambar yabo ta zinare saboda bajintar da ya nuna ta sansano bama-bamai da nakiyoyi da aka binne a karkashin kasa. Beran mai suna Magawa ya sansano nakiyoyi 39 da abubuwan fashewa 28 a tsawon rayuwarsa ta aiki. Kungiyar liktotin dabbobi ta Birtaniya PDSA ta mika wa beran lambar yabo ta zinare saboda ""kare rayukan jama'a da ya yi lokacin yana aiki, da kuma kawar da baraguzan da aka binne nakiyoyi da ka iya fashewa a kasar Cambodia"". An yi kiyasin cewa akwai nakiyoyi miliyan shida binne a cikin kasa a Cambodia. Lambar yabo ta zinaren ta PDSA na dauke da wasu kalamai da ke cewa an bai wa beran kyautar ce ""Bisa jajircewarsa da mayar da hankali wurin aiki"". A cikin dabbobi 30 da aka bai wa lambar yabon, Magawa ne bera na farko. Wata kungiyar kasar Belgium mai suna Apopo ce ta horas da beran mai shekara bakwai, wanda dan asalin kasar Tanzaniya ne kuma tana horas da dabbobi domin gano abubuwan fashewa da aka binne a karkashin kasa da kuma masu dauke da cutar tarin fuka a shekarun 1990. Ana bai wa dabbobin lambar yabo bayan shekara daya idan aka gama horas da su. ""Bayar da wannan lambar yabon abin alfahari ne a gare mu,"" a cewar shugaban Apopo Christophe Cox a hirarsa da kamfanin dillancin labari na Press Association. ""Kuma hakan wani babban abu ne ga al'ummar Cambodia, da ma sauran mutane a duniya wadanda ke fama da fargabar zama a wuraren da aka binne nakiyoyi."" A cewar Apopo, Magawa - wanda aka haifa sannan ya girma a Tanzaniya - yana da nauyin 1.2kg da tsawon santimita 70. Magawa yana iya zagaye fili irin wanda ake buga kwallon tennis cikin minti 20 - kuma Apopo ya ce hakan na iya daukar mutum mai rike da na'urar gano bama-bamai ko abubuwan fashewa tsakanin kwana daya zuwa kwana hudu." https://www.bbc.com/hausa/labarai-54292969 +technology Whatsapp ya sanya harshen Hausa a tsarinsa Whatsapp ya sanar da fara amfani da ƙarin harsuna uku na Afirka da suka haɗa da harshen Hausa a wayoyin komai da ruwanka na Android. Kamfanin Meta mamallakin shafukan Whatsapp da Facebook da Instagram ya sanar da wannan matakin ne a wata sanarwa da ya wallafa a Tuwita a ranar Litinin. Wannan mataki na Whatsapp ya zo ne bayan da a wani lokaci can Google da Facebook suka ɗauki irin sa. Hausa na daga cikin manyan harsunan da ke ƙara samun tagomashi a duniya kuma masu magana da harshen sun kai kusan miliyan 72 a faɗin duniya. Whatsapp na daga cikin shafukan da suka da matuƙar farin jini a duniya, kuma a Najeriya ma akwai miliyoyin masu amfani da shi. Yanzu za a ziro ido a ga ko shafuka irin su Tiktok da Snapchat za su bi sahun ɗaukar irin wannan mataki. https://www.bbc.com/hausa/articles/c3gnqyvvplqo +technology Bidiyo: Makahon da ya kera mota a Najeriya Dannata hoton da ke sama domin kallon bidiyon: Abdul'aziz Balogun wani matashi ne da ke da larurar makanta a Jihar Legas da ke kudancin Najeriya. Amma hakan bai hana shi neman ilimi ba inda ya karanta fannin injiniyan jiragen sama. A tattaunawarsa da BBC, matashin ya ce ya kera mota domin ya nuna wa jama'a cewa bai kamata larurar makanta ta hana kowa cika burinsa na rayuwa ba. https://www.bbc.com/hausa/media-61071727 +technology Abin da ya sa wayoyinku ke zafi da yadda za ku magance matsalar "Shin kakan zauna ka yi tunanin me ya sa a yawan lokuta idan kana amfani da wayarka ta salula, kwatsam sai ka ji ta fara daukar zafi - watakila ko kana wasa da ita ko kuma kana karantu? Wayar takan rage sauri ko kuma batirinta ya nuna ya kusa karewa. Kana daga cikin mutanen? A yanayi na zafi, mutane na fitar da zufa sosai, sai dai sabanin dan adam, wayoyin salula ba sa fitar da zufa, hakan yana da kyau ga wadanda ke rike da wayoyinsu amma ba shi da kyau ga wayoyinmu. Saboda haka, me ya sa wayoyin salula ke rikidewa lokacin zafi kuma me ya kamata ku yi? Kamar yadda muke rasa samun sukuni lokacin yanayi na zafi, haka zai iya kasancewa ga injinan wayoyin salula, musamman ga wata na’ura da ke jikin wayar da kuma ke taimaka masa aiwatar da abin da ake so. ""Abin da ke cikin wayar da kuma ke taimaka masa wajen yin aiki, yakan dauki zafi,’’ a cewar Dr Roz Wyatt-Millington, wata babbar malama a sashen Nazarin Injiniya na kayan laturoni da ke Jami’ar Leeds Beckett a Birtaniya. ""Sannan lokacin da wayar salula ke daukar zafi, injinta zai yi kokarin tsayawa daga aiki domin kar ya yi zafi, daga baya kuma sai ya rage karfin intanet na wayar,’’ a cewarta. Ta kuma ce an kera kayan laturoni ne domin aiki a kan ma’aunin zafi na selshiyos 35. ""Baturan wayar salula kan rike caji sosai kuma an yi su ne domin aiki a yanayin zafi da bai wuce kima ba. Yayin da suke kara zafi, da wahala suke samu su yi aiki yadda ya kamata,’’ in ji Dr Roz. Abin da hakan ke nufi shi ne karfin batirin wayar zai kare da wuri, musamman ma saboda da wuya yake sanyi. Dr Roz ta kara da cewa mutane suna kara karfin hasken wayoyinsu na salula a lokacin da suke waje a cikin rana, hakan kuma zai shafi yadda ke aiki. Idan ba ka lura da canjin fuskar wayarka ba, yanayin zafi zai yi masa mummunan tasiri. ""Idan tsohuwar waya ce, idan ta sami karamar matsala, zafi zai kara masa matsala,’’ a cewar Dr Roz. Ta kara da cewa abubuwan da ke kare fuskar waya, sun fi rike zafi a ciki, wanda hakan ba shi da kyau a lokacin yanayin zafi. Kar ka yawaita saka wayar a caji ""A lokacin yanayi na zafi, idan kana cajin wayar ka, kana kara zafi ne. Idan wayarka ta dade a wuta, za ta yi zafi sosai,’’ in ji Dr Roz. Ajiye wayar salula wajen da ya dace ""Ajiye waya nesa da rana yana taimakawa sosai. Kar ka bar waya a cikin motarka, ka ajiye ta a inuwa yadda ya kamata. Idan so samu ne, ka sanya ta gaban fanka idan za ka iya.’’ Kar ka ajiye wayar salula a cikin haske Wannan ya shafi ciki da kuma wajen wayar. Ka cire ta daga cikin rigarta sannan ka kashe dukkan manhajoji da ba za kayi amfani da su ba. ""Idan ba ku amfani da na’urar bayar da intanet ta GPS, to ku kashe shi. Saboda an ce idan kun rage yawan manhajoji da kuke amfani da su, to hakan kuma zai rage yawan wuta da wayar ke aiki amfani da shi, kuma hakan zai rage yawan daukar zafi da waya za ta yi,’’ a cewar Dr Roz. Yanayin karancin wuta Idan wayarka na amfani da wuta kalilan, to hakan zai sa ta dade ba tare da samun matsala ba. ""A wasu lokutan idan wayarka tana samun matsaloli, to ka kashe ta na dan wasu mintoci, saboda ta yi sanyi, sannan sai ka kara kunnata.’’ Ku guji amfani da firiji domin ajiye wayoyinku ""Kada ka sanya wayar ka cikin kankara, saboda hakan ba zai taimaka ba.’’ Canjin yanayin zafi ba shi da kyau ga wayoyin, kuma kankara yana sa ruwa ya shiga cikin wayar. Dr Roz ta kara da cewa wayoyi na da injunan da aka kera su da shi domin taimaka musu kada su lalace, a lokacin yanayin zafi.’’" https://www.bbc.com/hausa/articles/c3g4vzyyjmzo