diff --git "a/data/hau/dev.tsv" "b/data/hau/dev.tsv" new file mode 100644--- /dev/null +++ "b/data/hau/dev.tsv" @@ -0,0 +1,318 @@ +category headline text url +entertainment Mahaifina ne ya tsaya min a waƙa - DJ AB Latsa hoton sama domin kallon bidiyon Matashin mawaki Haruna Abdullahi wanda aka fi sani da DJ AB ya ce ya fuskanci ƙalunbale kafin ya samu karɓuwa musamman ga matasan arewacin Najeriya. A hirarsa da BBC ya ce ya samu goyon bayan mahaifinsa, wanda ya fara sayo masa abin ƙida na piano. Ya ce yanzu ya samu ɗaukaka, kuma yana alfahari da ɗimbin masoyansa. “Da sai mun biya muke waka yanzu kuma sai an biya mu idan za mu yi waƙa,” in ji mawaƙi DJ AB. DJ AB ɗan asalin jihar Kaduna ne. Kuma yi karatun shi na furamare da sakandare a jihar ta Kaduna. A halin yanzu yana karatun digirinsa na farko a jami’ar Ahmadu Bello da ke garin Zaria. Matashin ya kuma ce yana sha’awar abinci amma wanda aka lulluɓe da nama. Wasu ƙarin bidiyo da za ku so ku kalla https://www.bbc.com/hausa/media-58309397 +sports Maguire da Varane ba za su buga wasan Man U ba Harry Maguire da Raphael Varane ba za su buga wansab da Manchester United za ta yi ba na gasar Europa League da Omonia Nicosia a yau Alhamis. Ciwon da ya ji tun a wasan Ingila ya ja kyaftin Maguire bai buga wasan hamayya ba na Manchester, wasan da a cikinsa ne Varane ya ji rauni a idon sawunsa, City kuma ta yi kaca-kaca da United. Aaron Wan-Bissaka da Donny van de Beek su ma ba za su buga wasan ba. United ce ke ta biyu a rukunin E  kafin zuwa Cyprus, ta yi rashin nasara a wasa daya ta kuma ci daya, cikin wasa biyu da ta buga a gasar. Wasan na zuwa ne kwanaki bayan dukan kawo wukar da aka yi wa Manchester United a wasan hamayya tsakaninta da City, wanda kocin United Erik ten Hag ya ce “dole su sake shiri”. “Hakika rana ce mai cike da kalubale, kamar ko da yaushe za mu koma mu kara yin duban tsanaki game da wasa, sannan mu tauki matakai masu zafi”. https://www.bbc.com/hausa/articles/crgn0kp14y0o +business Tsadar rayuwa a Najeriya: Shin ₦30,000 za ta iya magance matsalolinku? Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon: Karin farashin man fetur da na hasken wutar lantarkin da aka yi a Najeriya sun sake jefa 'yan kasar a mawuyacin hali. Hakan na faruwa ne a yayin da suke cikin karin matsin tattalin arziki sakamakon annobar korona wacce ta tilasta wa duniya zama cikin dokar kulle. Sai dai gwamnatin kasar ta bayyana dalilai da suka sanya tsadar rayuwa a kasar. BBC Hausa ta yi nazari yadda 'yan Najeriya, wadda gwamnatin tarayyarta take biyan ₦30,000 a matsayin mafi karancin albashi, za su yi amfani da wannan adadi wajen gudanar da rayuwarsu a wannan mawuyacin hali da ake ciki. https://www.bbc.com/hausa/labarai-54080961 +sports Al-Nassr ta Saudiyya na zawarcin Ronaldo, Bayern Munich na son Rice Kungiyar Al-Nassr ta kasar Saudiyya ta yi wa dan wasan gaba na Portugal Cristiano Ronaldo, mai shekara 37, tayin kwantiragin shekara uku a farashin da ya kai fam miliyan 186. (CBS) Bayern Munich ta bi sahun takwarorinta wajen zawarcin dan wasan tsakiya na West Ham da Ingila, Declan Rice, mai shekara 23. (El Nacional, via Fichajes - in Spanish) Tottenham ba ta kammala tattaunawa da kaftin din Ingila kuma dan wasan gaba Harry Kane ba kan sabon kwantiragi, yayin da kwatiraginsa na yanzu zai kare a shekarar 2024. Dole Spurs ta bai wa dan wasan, mai shekara 29, wani kwantiragi da ba kasafai suka saba ba kafin ya amince. (Football Insider) Manaja Erik ten Hag, ya bukaci Manchester United su yi kokarin maye gurbin Ronaldo idan an bude kasuwar saye da musayar 'yan wasa a watan Janairu mai zuwa, bayan ficewarsa daga kungiyar. (ESPN) Manchester United ta fara fitar da jerin 'yan wasan da take ganin za su maye gurbin Ronaldo, cikinsu har da dan wasan PSV da Netherlands Cody Gakpo, mai shekara 23, da kuma dan wasan gaba na Portugal da AC Milan Rafael Leao, mai shekara 23. (ESPN) Liverpool ma ta fara shirin kashe makudan kudade domin sayo 'yan wasa a watan Janairu, duk da halin rashin tabbas din da kulub din ke ciki kan wanda zai mallake shi. (Football Insider) An tsere wa Manchester United a fafutikar daukar dan wasa tsakiya na Ingila Jude Bellingham, mai shekara 19, daga Borussia Dortmund. (Sky Sports Germany) Kwamishinan wasannin Leagu Don Garber, ya tabbatar da yawan manyan kungiyoyi a Amurka sun nuna sha'awar daukar dan wasan gaba na Argentina Lionel Messi, mai shekaru 35, idan kwantiraginsa da kungiyar Paris St-Germain ta kare a kakar wasan da ke karewa. (90min Dan wasan Barcelona mai shekara 19, kuma na bayan Sifaniya Alejandro Balde, ya bayyana cewa ya na sha'awar wata rana ya buga wasa karkashin kungiyar Manchester United baya ga wasan La Liga da ya ke yi. (Mundo Deportivo on TikTok - in Spanish) Tottenham na duba yiwuwar dauko dan wasan Juventus na tsakiyar Amurka Weston McKennie, mai shekara 24, bayan kammala gasar cin kofin duniya. (CBS, via Express) West Ham da Everton sun bi sahun wasu kungiyoyi na son dauko dan wasan Colombia winger Jhon Duran, mai shekra 18 daga Chicago Fire, su ma kungiyoyin Liverpool  na zawarcin dan wasan Manchester United . (Sun) Leeds United, Everton, West Ham da Leicester City na daga cikin kulub din da ke son dauko dan wasan tsakiya na Senegal Boulaye Dia. Mai shekara 26 a yanzu ya na matsayin aro a kungiyar Salernitana daga Villarreal. (CBS) Leicester, Brighton da Nottingham Forest  na son dauko dan wasan Huddersfield kuma na tsakiyar Faransa Etienne Camara, mai shekara 19. (Sun) Manajan Barcelona  Xavi ya ce a kashin kan sa ya yi magana da dan wasan Palmeiras Endrick mai shekara 16 domin ya amince shiga kulub din La Liga. (ESPN) https://www.bbc.com/hausa/articles/c84ggv9380no +business Bidiyon yadda ake satar gari a wajen niƙa a Kano Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon: A Unguwar Gobirawa da ke karamar hukumar Dala a Kano, wani mai niƙa ya ƙirƙiro wani sabon salon ba da tikiti kafin mutane su karɓi niƙa don magance matsalar satar gari. https://www.bbc.com/hausa/media-54431755 +health Yadda ake warkewa daga cutar coronavirus "Mamayar da coronavirus ta yi wa kasashen duniya da kuma bayanan da masana kiwon lafiya ke yi kan yadda ake daukarta na cikin abubuwan da suka fi tayar wa da mutane hankali. Ya zuwa ranar Alhamis 26 ga watan Maris 2020, alkaluma sun nuna ce kusan mutum 500,000 ne suka kamu da cutar a duk fadin duniya yayin da sama da mutum 22,000 suka mutu sakamakon harbuwa da ita. Wani abin da yake ci gaba da jefa mutane cikin fargaba a kan cutar shi ne bayanan da masana harkokin lafiya suka yi cewa har yanzu ba a samu maganinta ba. Sai dai duk da wannan mawuyacin hali da coronavirus ta jefa duniya, an soma samun labari mai dadi inda mutanen da suka kamu da ita suke warkewa. A cewar hukumomi da kuma kungiyoyin da ke bibiyar yaduwar cutar, ciki har da Jami'ar Johns Hopkins ta Amurka, ya zuwa ranar Alhamis fiye da mutum 120, 000 ne suka warke daga cutar COVID-19 a fadin duniya. A Najeriya, ranar Alhamis gwamnatin Lagos ta bakin Tunde Ajayi, mai magana da yawun gwamna Babajide Sanwo-Olu, ta ce mutum shida sun warke daga cutar. Hakan na nufin mutum takwas ne kenan suka warke daga Covid-19 a Najeriya, yayin da mutum daya ya mutu tun lokacin da cutar ta bulla a kasar. Yaya ake warkewa ganin cewa ba a samar da maganinta ba? Ko da yake har yanzu ba a samu riga-kafi ko maganin cutar coronavirus ba, amma masana harkokin lafiya sun ce ana warkewa daga cutar idan aka dauki wasu matakai. Dakta Nasiru Gwarzo wani masanin harkar lafiya ne a Najeriya, ya ce yawancin cutukan da kwayar cutar virus ke haddasawa, ko babu magani, jiki yana iya warkewa saboda suna da wa'adi. ""Idan mai dauke da cuta irin coronavirus ya samu kulawa mai kyau, kamar samun abinci mai sinadaran da ke bunkasa lafiya, da shakar iska mai kyau da motsa jiki, babu shakka zai warke. Galibin wadannan cututtukan da virus ke haddasawa suna da lokacin fita daga jikin mutum. Misali, Ebola tana yin kwana 22 a jikin mutum, ita kuma coronavirus tana yin kwana 14, yayin da mura ke yin kwana uku. Idan ka ga mutum bai warke ba, ta ci karfinsa sosai kuma bai samu kulawar da ta kamata ba."" Ya kara da cewa babu wasu bayanai na kimiyya da ke nuna cewa cutar covid-19 tana sanya wa wanda ya yi fama da ita lalura ta dindindin ko da ya warke. ""Gaskiya har yanzu ana bincike kan coronavirus amma abin da ya bayyana shi ne babu wata hujja da ke nuna cewa irin wadannan cutuka da virus ke haddasawa suna haifar da tawaya ta din-dindin. Ya danganta da karfin garkuwar jikin mutum da kuma kulawar da ya samu. Misali, wasu kan yi fama da ciwon kunne ko da kuwa sun warke daga zazzabin Lassa, amma wasu suna warkewa sarai ba tare da fuskantar wata matsala ba, in ji Dakta Gwarzo. Wadanda suka warke suna iya sake kamuwa? Masanin harkar lafiyar ya ce ba shi da masaniya kan ko wadanda suka warke daga coronavirus na iya sake kamuwa da ita, tun da har yanzu ana bincike. Amma ya ce idan aka kwatanta da ta cutar shawara, wacce idan mutum ya warke har abada ba zai sake kamuwa da ita ba, to za a iya cewa ita ma coronavirus za a iya warkewa ba tare da an sake kamuwa da ita ba." https://www.bbc.com/hausa/labarai-52043312 +politics Ba a yi wa Tinubu kora da hali a APC ba – Farouk Adamu Aliyu "Ƴan jam'iyyar APC mai mulki sun musanta cewa wani ɓangaren jam'iyyar na yi wa daya daga cikin jiga-jigan APC na kasa, Bola Ahmed Tinubu kora da hali. Wani al'amari da ya fito da zaman tankiya a jam'iyyar a baya-bayan nan dai shi ne yadda Bola Tinubu ya fito ya bayyana ƙorafinsa dangane da shirin sabunta rijista da jam'iyyar APC ta gudanar. A hirarsa da Usman Minjibir na BBC Hausa, Hon Farouk Adamu Aliyu wanda jigo ne a jam'iyyar ya ce babu ƙamshin gaskiya a kan cewa ana ƙoƙarin yi wa Bola Tinubu kora da hali daga APC. Ya ce: ""Ai ba za mu so a ce Tinubu ya bar jam'iyyar APC ba. A jam'iyyar APC ba wanda ya isa ya raina Tinubu, ba wanda ya isa ya ce Tinubu ba kowa ba ne, ba wanda ya isa ya raina irin gudunmowar da ya baiwa jam'iyyar APC har ta kai ga mulki a shekarar 2015 da 2019."" Duk da cewa an daɗe ana raɗe-raɗin cewa gwamnatin Shugaba Buhari na yi wa Tinubu bi-ta-da-ƙulli, Farouq Adamu ya ce zancen ƙarya ce tsagwaronta. ""Babu jam'iyyar da za ta so ta rabu da Tinubu, ba gaskiya ba ne babu abin da ake yi wa Tinubu na wulaƙanci ko yi masa wani abu na ba daidai ba. Wasu na ganin sabunta katin da ake yi na jam'iyyar APC a faɗin kasar wani shiri ne da ke nuna inda jam'iyyar za ta karkata a zaɓen 2023 na irin mutanen da za ta zaɓo su yi shugabanci. Sai dai Farouq Adamu ya ce ai jam'iyya ce ba dole babu wanda za a sa wa igiya a jawo shi, idan kowace jiha ta Najeriya ba ta son shiga jam'iyyar APC yaya za ka yi da ita? ""Wannan ya rage wa jagororin da suke so su nemi buƙata a APC su je su nemo jama'a su sa su yi rijista. Ba gaskiya ba ne cewa akwai wasu da ake so su fita daga jam'iyyar nan. Mu ba mu ƙi ba ma gaba ɗaya ƴan Najeriya su zama ƴan APC,"" a cewarsa. Ƴan Najeriya da dama dai a shekarun bayan nan na mulkin Shugaba Buhari na yawan koka wa kan mulkin jam'iyyar APC kan taɓarɓarewar tsaro a sassan ƙasar da dama da kuma jawo rarrabuwar kawuna tsakanin kudu da arewacin ƙasa, don haka wasu za su yi tababar batun na Farouq Adamu. Amma ya kare maganar da cewa: ""Babu yadda za a yi gwamnati kowace iri ce ko da ta PDP su kawo abin da zai rarraba kawunan al'umma. Kuma su masu mulkin nna rantsuwa fa suka yi kan cewa za su kare martabar ƴan Najeriya, amma bambance-bambancen addiniai da yaruka ka sawa ba a rasa irin wadannan abubuwa."" ""Amma ina tabbatar da cewa babu wani abu da gwamnatin APC ke yi don kawo wanna matslaar rabuwar kai,"" a cewarsa. Ya ba da misali da abin da ya faru na rikicin ƙabilanci a Kasuwar Sasa ta jihar Oyo, inda rikicin ƙabilanci ya ɓarke amma ba a samu mayar da martani a arewa ba, inda ya ce hakan ya biyo bayan sasanci da gwamnatin APC ta dinga yi ne da kwantar da hankulan mutane. Tun a farkon watan Fabrairu ne sabon rikici ya kunno kai a jam'iyyar APCn sakamakon wasu kalamai da aka ji sun fito daga bakin babban jigonta Bola Ahmed Tinubu. Shi dai Tinubu wanda ake kyautata zaton zai nemi tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, ya ce aikin sabunta rijistar ƴaƴan jam'iyyar da ake yi a lokacin a jihohin ƙasar baki ɗaya ba shi da wani tasiri. ""Sabunta rijistar da jam'iyyar ke yi tamkar a sanya ɗaya ne kana kuma a cire ɗaya, don haka ni ina ganin ba wata ƙaruwa ba ce'', a cewar Tinubu. Wannan kalamin ya sa wasu ƴaƴan jam'iyyar na cewa da walakin goro a miya, kuma alama ce da ke nuna cewa bai ji daɗin abin da ake yi ba, saboda a cewarsu, aikin rijistar zai iya rage masa ƙarfin mamayar da ya yi wa jam'iyyar, da kuma tasirin da yake da shi a cikinta. Sai dai masana, irin su Malam Kabiru Sufi na kwalejin share fagen shiga jami'a ta jihar Kano na cewa fitar irin wɗannan kalamai daga bakin Bola Tinubu a matsayinsa na jagora, duk kuwa da cewa yana da damar yi wa jam'iyyar gyara tun a matakin shirin rijistar, na nuna cewa akwai ɓaraka. Har zuwa yanzu dai Mista Tinubu bai fito ya ce yana neman shugabancin Najeriya ba, amma tuni wasu masoyansa suka fara tallata shi. Ko da yake wasu ruwayoyin na nuna cewa wasu daga cikin jiga-jigan jam'iyyar APC daga arewacin Najeriya ba sa goyon bayan haka." https://www.bbc.com/hausa/labarai-56290495 +politics Na mika nasarar da na samu ga Allah – Abba Gida-Gida Dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP a jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya ce ya mika nasarar da ya samu a Kotun Koli kan zaben fitar da gwani ga Allah madaukakin sarki. Alkalan kotun sun tabbatar da hukuncin Kotun Daukaka Kara ta Kaduna wacce ta yi watsi da bukatar Ibrahim Al'amin (Little) na cewa PDP ba ta yi zaben fitar da gwani ba. Kotun ta ce Little, wanda ya yi nasara a kotun farko a Kano, ba shi da hurumin shigar da kara kan zaben da bai shiga ba. Ga abin da ya shaida wa Wakilin BBC a Kano Ibrahim Isa: https://www.bbc.com/hausa/48693495 +entertainment Sarauniya Elizabeth II: Yadda jana'izar Sarauniyar Ingila za ta kasance Sarauniya ta mutu, wanda hakan ya kawo karshen mulki mafi tsawo a tarihin masarautar Birtaniya. Ta mutu ne salin-alin, zagaye da iyalanta a gidan sarauta da ke Balmoral a Scotland, kamar yadda Fadar Buckingham ta sanar. Ga abubuwan da muke hasashen za su faru game da yadda jana'izarta za ta kasance, yayin da al'umma ke shirin yi mata ban-kwana. Bayan an dauko gawarta zuwa London, za a shimfide ta ne a katafaren dakin Westminster tsawon kusan kwana hudu kafin yi mata jana'iza. A nan ne al'umma za su rika zuwa suna mata ganin karshe, kamar yadda al'adar masarautar ta tsara. The grand hall kamar yadda ake kiran babban dakin shi ne wuri mafi dadewa a Fadar Westminster. Mahaifiyar Sarauniya ce mutum ta karshe da aka ajiye gawarta a dakin bayan ta mutu a 2002, a lokacin kuma mutum 200,000 ne suka yi ban-kwana da gawarta. Za a dora gawar sarauniya ne a kan wani gado da ake kira catafalque, kuma a kowace kusurwa za a girke sojoji daga rundunar da ke tsaron masarauta. Kazalika za a kawo gawar ne 'Westminster Hall' daga fadar Buckingham, tare da rakiyar faretin sojoji da iyalan gidan sarauta. Jama'ar gari za su samu damar kallon shirye-shiryen jana'izar, a lokacin da za a zagaya da ita a titunan London, a kuma nuna bidiyon a manyan alluna da ake sa ran za a kafa a dandalin London Royal Parks. Daga nan kuma sai a ajiye akwatin gawar a nade shi da rigar masarauta ta Royal Standard, a kuma dora kambin sarautarta a kai. Bayan an ajiye gawar a dakin sai kuma a gudanar da addu'o'i na takaitaccen lokaci. Daga nan ne sai a bai wa al'umma damar shigowa su yi ban-kwana da ita. Ana sa ran gudanar da jana'izar Sarauniya ne a cocin Westminster Abbey ranar Litinin 19 ga watan Satumban 2022, kamar yadda fadar Buckingham ta sanar. The Abbey coci ce da ta kafa tarihi, don a nan ne ake nada sarakuna, ciki har da Sarauniya Elizabeth ta II a 1953, kuma a nan ne aka daura mata aure da Yarima Philip a 1947. Sai dai tun a karni na 18 rabon da a gudanar da jana'izar wani Sarki ko Sarauniya mai ci a cocin Abbey, duk da a nan ne aka yi jana'izar mahaifiyar Sarauniya Elizabeth II. Shugabannin kasashen duniya za su hallara a Birtaniya don su hadu da iyalan Sarauniya yayin jana'izar. Haka manyan ‘yan siyasa da kuma tsofaffin Firaiministocin da aka yi a gwamnatin Birtaniya. Ranar jana'izar kuma za a soma ne da daukar akwatin da gawar Sarauniya ke ciki daga Westminster Hall zuwa Westminster Abbey (cocin Westminster), a kan motar dakon bindigar sojin ruwa ta Royal Navy. Rabon da a ga wannan mota tun 1979 yayin jana'izar kawun Yarima Philip, Lord Mountbatten, tare da rakiyar sojojin rundunar Royal Navy 142. Daga nan kuma manyan ‘yan gidan sarauta da suka hada da sabon sarki za su biyo baya. Ana sa ran shugaban Majami'ar Westminster David Hoyle da kuma takwaransa na Canterbury Justin Welby ne za su jagoranci addu'o'i. Watakila kuma Firaiminista Liz Truss ta gabatar da jawabi a wurin. Bayan an gama addu'o'in, za a zagaya da gawar Sarauniya daga cocin a kuma yada zango a Wellington Arch, da London Hyde Park Corner, kafin a wuce da ita gidan sarauta na Windsor a kan motar daukar gawa. Za a yi zagayen karshe da gawar Sarauniya uka a ranar, kafin ta isa makwancinta a Majami'ar St George da ke Windsor Castle. Ana sa ran Sarki da manyan iyalan gidan sarautar za su hallara Windsor Castle, kafin gawar ta shiga Majami'ar St George don gudanar da wasu addu'o'i. Majami'ar St George ce cocin da 'yan gidan sarauta ke yawan amfani da ita don gudanar da bukukuwan aure da na addini da kuma jana'iza. A nan ne aka daura auren Duke da Duchess na Sussex, wato Yarima Harry da Meghan, kuma a nan ne aka yi jana'izar Mijin Sarauniya Yarima Philip. Za a saka akwatin gawar Sarauniya a hubbaren masarauta ta Royal Vault, a Majami'ar King George VI da ke cikin majami'ar St George. https://www.bbc.com/hausa/articles/c807631282yo +health Muhimman abubuwa biyar game da tafarnuwa "Tafarnuwa ta yi fice a yawancin dakunan girkinmu, ta kuma yi fice ta fannin lafiya. Wata kwararriya a fannin abinci mai gina jiki, Kerry Torrens, ta yi nazari da bayani kan muhimmancin tafarnuwa. Tafarnuwa daya ce daga cikin tsoffin tsirrai da ake shukawa, kuma daga cikin sinadaran da ake amfani da su dangin Liliaceae, wanda su ne tushen Albasa, da suransu. Sun yi fice wajen ba da daddadan kamshi da dandano cikin abinci. Dunkulen tafarnuwa kan kunshi sala 10 zuwa 20, ya danganta da girman ta. Launin jikinta kafin a bare, ka iya kasancewa fari, ko launin makuba, amma da zarar an bare ta, komai fari ne a jikinta. Curi guda na tafarnuwa na dauke da: Amfani a likitance Tafarnuwa na dauke da sinadaran da ke da amfani a likitance, sannan ana kiran yawancin abubuwan da ke cikin ta da allicin. Sinadarin ne ke sanya kamshinta ya bambanta da na albasa, sannan dandanonta na daban ne. Abin damuwa ga masu girki shi ne, matakin yanka ta, ko markadawa da ake yi yana rage sindarin allicin din da take dauke da shi. An tabbatar cewa dora ta a wuta na rage mata amfani, don haka shawara ga masu sanya ta cikin abinci, su dinga zuba ta bayan abincin ya kusa dahuwa. Rage hatsarin kamuwa da ciwon zuciya Yawancin binciken da aka gudanar sun mayar da hankali kan amfanin tafarnuwa ga lafiyarmu, da amfaninta wajen rage hadarin ciwon zuciya da daidaita yawan kitse a jikin dan Adam. Bincike da dama da aka gudanar kan amfanin tafarnuwa sun gano tana magance matsalar dunkulewar jini, hakan na nufin ana amfani da tafarnuwa wajen tsinka jini domin rage hatsarin bugun zuciya. Haka kuma, tafarnuwa na magance ciwon hawan jini, saboda yadda take tace jini da yadda kuma zai dinga shiga sassan da suka dace a jikin mutum. Rage hadarin cutar sankara Sinadarin sulfur wato farar wuta wanda tafarnuwa ke dauke da shi, an yi nazari kan yiwuwar tasirin rage kaifin cutar kansa, har da kansa mai tsiro. Yawancin abubuwan da aka gano suna da amfani a tafarnuwar sun hada da magance kansar mafitsara ta maza, da ciwon koda. Binciken bai zurfafa ba, wannan ne dalilin da ya sa har yanzu ba a tabbatar da tafarnuwa a matsayin maganin cutar kansa ba. Ana bukatar fadada nazari. Sinadaran yakar kwayoyin cuta An dade ana amfani da tafarnuwa wajen magance cutukan ƙwayar cuta ke haifarwa wato virus a turance. Ana kiran maganin da aka yi amfani da tafarnuwa wajen hadawa da suna ""Russian penicillin"" saboda yakar cutuka dangin infection a turance. Tafarnuwa na magance cutukan da suka shafi fata, kamar kuraje, da kyazbi da sauransu. Akan matse maikon tafarnuwar a shafa kai-tsaye a jikin ciwon ko magungunan da aka yi amfani da tafarnuwa wajen hadawa. Kara karfin kashi Bincike kan dabbobi ya nuna amfani da tafarnuwa na kara kwarin kashi ga macen bera. Wani nazarin kuma ya nuna tafarnuwa na taimaka wa mata lokacin da jinin al'darsu ya dauke, suna hadiyarta a kowacce rana. Wani nazarin ya bayyana tafarnuwa na taimaka wa masu ciwon gwiwa, da rage radadin ciwon da magance sanyi wanda shi ne ciwon ba ya so." https://www.bbc.com/hausa/articles/cq5ep734j3po +sports Kylian Mbappe, Vinicius Jr da Erling Haaland: 'Yan wasan da suka fi tsada a duniya Kylian Mbappe, Vinicius Jr da kuma Erling Haaland su ne 'yan wasan da suka fi tsada a duniya, a cewar wani bincike da cibiyar da ke nazari kan harkokin kwallon kafa CIES Football Observatory ta gudanar. Mbappe, mai shekara 23, wanda ya ki amincewa ya tafi Real Madrid inda ya ci gaba da zama a Paris St-German, shi ne kan gaba a cikin 'yan wasa mafi tsada a duniya inda darajarsa ta kai yuro 205.6m (£175.7m). Dan wasan Real Madrid dan kasar Brazil Vinicius Jr, wanda ya zura kwallon da ta ba su nasara a wasan karshe na gasar Zakarun Turai da suka fafata da Liverpool, shi ne na biyu mafi tsada wanda darajarsa ta kai £158.3m, yayin da dan kasar Norway da ke murza leda a Manchester City Haaland shi ne na uku inda ya kai (£130.4m). Dan wasan tsakiya na Borussia Dortmund Jude Bellingham (£114.1m) shi ne dan kasar Ingila mafi tsada inda yake a matsayi na biyar a wannan jadawali, inda yake gaban takwaransa na Ingila kuma dan wasan Manchester City Phil Foden wanda yake matsayi na shida (£105.9m). Kungiyoyin da ke fafatawa a Gasar Firimiya su ne suka kankane jerin 'yan wasan da suka fi tsada inda 'yan wasa 41 suka fito a cikin 'yan wasan 100 da suka fi daraja. CIES ta yi amfani da wasu muhimman abubuwa, da suka hada da shekarun dan wasa, kwazonsa da tattalin arzikin kungiyarsa da kuma hauhuawar farashi wajen gudanar da wannan bincike. Dan wasan Faransa Mbappe ya sanya hannu kan kwantaragin shekaru uku a PSG a watan jiya yayin da ya zabi ci gaba da zama a Paris maimakon tafiya Real Madrid. 'Yan wasa 10 mafi tsada a duniya (CIES Football Observatory) Kylian Mbappe - Paris St-Germain - £175.7m Vinicius Jr- Real Madrid - £158.3m Erling Haaland - Borussia Dortmund - £130.4m Pedri - Barcelona - £115.4m Jude Bellingham - Borussia Dortmund - £114.2m Phil Foden - Manchester City - £105.9m Frenkie de Jong - Barcelona - £96.1m Luis Diaz - Liverpool - £94.0m Ruben Diaz - Manchester City - £93.6m Ferran Torres - Barcelona - £93.5m https://www.bbc.com/hausa/wasanni-61708606 +entertainment Ba ɗan Janar Abacha na aura ba - Hafsat Idris "Fitacciyar tauraruwar fina-finan Kannywood, Hafsat Idris, ta musanta rade-radin da ake yi cewa ta auri daya daga cikin 'ya'yan tsohon shugaban mulkin sojin Najeriya, marigayi Janar Sani Abacha. Ta bayyana haka ne a sakon da ta wallafa a shafinta na Instagram, ko da yake ba ta bayyana mutumin da ta aura ba. Hafsat Idris, wadda ake yi wa lakabi da 'Hafsat Barauniya' ta yi aure a asirce a karshen makon jiya, lamarin da ya sa wasu kafafen watsa labarai suka bayar da rahotannin cewa ta auri daya daga cikin 'ya'yan marigayi Janar Abacha. Amma a sakon da ta fitar domin mika godiya ga mutanen da suka yi mata fatan alheri, tauraruwar ta ce ""ina mika sakon godiyana ga dukkan masoya, 'yan uwa da abokan arziki na fatan alheri da suka yi mini. Sai dai ina so na yi na yi magana a kan rade-radin da ke yawo...cewa mijin da na aura yana da alaƙa da gidan Abacha. to, wannan ba gaskiya ba ne."" Wasu rahotanni sun ce ta auri wani matashi ne mai suna Mukhtar Hassan Hadi. Tauraruwar, wadda ke da 'ya'ya shida gabanin wannan auren nata, ta fito a manyan fina-finai na Kannywood, amma an fi saninta da fim din da ta soma fitowa mai suna 'Barauniya'. A kwanakin baya ne babbar 'yar tauraruwar ta haihu, inda ta yi mata takwara." https://www.bbc.com/hausa/labarai-60553004 +politics Shaidar Karatu: Ko Buhari zai yi barci da ido biyu? Kotun kolin Najeriya ta kori karar da Kalu Kalu Agu ya shigar tare da wasu mutane biyu kan takardar kammala karatun Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya. Kotun ta kori karar ne bayan lauyan da ke kare Kalu ya janye bisa dalilai na rashin shigar da karar a cikin lokacin da doka ta tanada. A baya dai kotun daukaka kara a Abuja ta yi watsi da karar, wacce aka shigar bisa zargin cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da takardun kammala makaranta na bogi ga Hukumar Zabe ta Kasa, INEC a matsayinsa na dan takara a zaben 2019. Haka kuma kotun ta ce bai dace shugaban kasa ya yi amfani da lauyan gwamnatin don kare shi a karar da ta shafe shi ta kashin kansa ba. Hakan a cewar kotun ya sabawa dokar da'ar ma'aikata. Sauran mutanen da aka yi karar sun hada da jam'iyyar APC da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta, INEC. Dalilin korar karar shi ne, an shigar da ita bayan kwana 14 da kudin tsarin mulki ya tanada. Sai dai kuma jam'iyyar hamayya ta PDP da dan takararta na shugaban kasa Atiku Abubakar su ma suna kalubalantar Shugaba Buharin a kotun sauraron kararrakin zabe kan batun takardar shaidar kammmala karatun nasa. https://www.bbc.com/hausa/labarai-49554592 +politics Iyorchia Ayu: Tarihin sabon shugaban jam'iyyar PDP Jam'iyyar PDP ta zaɓi Sanata Iyorchia Ayu a matsayin sabon shugabanta a a babban taron da ta gudanar a Abuja. Ana kallon Ayu a matsayin ɗan takarar da taron ya amince da shi a matsayin shugaban PDP. Ya gaji Uche Secondus, wanda aka dakatar a watan Agusta a matsayin shugaban jam'iyyar. An haifi Iyorchia Ayu ne a garin Gboko na jihar Benue da ke tsakiyar Najeriya ranar 15 ga watan Nuwambar 1952. Ya yi karatunsa na digiri a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, ko da yake daga bisani ya tafi Jami'ar Jos da ke jihar Filato inda ya koyar da Ilimin Sanin halayyar dan adam wato Sociology. Ya taɓa zama shugaban kungiyar malaman jami'a, ASUU, reshen Jami'ar Jos. Mista Ayu ya tsunduma cikin harkokin siyasa inda a shekarar 1992 ya zama Sanata a karkashin jam'iyyar SDP kuma 'yan majalisar dattawan lokacin suka zaɓe shi a matsayin shugaban majalisar dattawa tsakanin 1992-1993. 'Yan Majalisar dattawan sun tsige shi Mista Ayu daga kan kujerarsa a watan Nuwamban 1993 sakamakon adawar da ya yi ta kafa gwamnatin riƙon kwarya ta Cif Shonekan. Ya riƙe mukamai daban-daban na ministoci. Kuma Mukaman da ya riƙe sun hada da na Ministan Ilimi daga 1993 zuwa 1998 da Ministan Masana'antu tsakanin 1999 zuwa 2001. Kazalika ya riƙe muƙamin Ministan harkokin cikin gida daga watan Yulin 2003 zuwa watan Yunin 2005. Sannan ya zama Ministan Muhalli daga watan Yunin 2005 zuwa Disambar 2005. https://www.bbc.com/hausa/labarai-59109013 +religion Ku san Malamanku: Tare da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa "Latsa alamar lasifika da ke sama don kallon hira da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa: Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Aminu Daurawa, ya ce ya sha wahala matuka kafin ya haddace wata aya a Al-Ƙur'ani. Malamin ya bayyana haka ne a wata hira ta musamman da BBC, a kuma cikin sabon shirinmu mai taken ""Ku San Malamanku"". Ya ce ayar da ta fi ba shi wuya ita ce wata aya da ke cikin Suratul Baqara, wato Iza Tadayantum..., wadda ita ce ayar da ta fi kowace tsawo a littafi mai tsarki. Sai kuma wata aya da ake magana a kan rabon gado, ita ma malamin ya ce ta ba shi wahala saboda kalmomi iri ɗaya da ake maimaitawa a cikinta. Malamin ya bayyana cewa a tsawon rayuwarsa ya yi nazarin abubuwa kusan 61 waɗanda suke jawo mace-macen aure a ƙasar Hausa. Sheikh Aminu Daurawa ya ce hira da tambayoyi da ya yi wa zawarawa da 'yan mata da aurensu ya mutu na tsawon lokaci ne ya sa ya gano waɗannan dalilai. Tarihin rayuwarsa A cikin wannan shiri na ""Ku San Malamanku"", malamin ya bayar da taƙaitaccen tarihin rayuwarsa, da kaɗan daga cikin gwagwarmayar da ya yi wurin neman ilimi na addini da na boko, da malamai daban-daban da ya koyi karatu a wurinsu da sauran abubuwa. Da farko dai an haifi Malam Aminu Daurawa a ranar 1 ga watan Janairu nshekara ta 1969, a Unguwar Kofar Mazugal, a Ƙaramar Hukumar Dala da ke cikin garin Kano. Sunan mahaifiyarsa Hajiya Sa'adatu Al-Mustapha, daga Unguwar Bachirawa, Ƙaramar Hukumar Ungogo a jihar ta Kano, mahaifinsa kuwa shahararren malami ne, wanda ake kira Sheikh Ibrahim Muhammad Mai Tafsiri. Malamin ya bayyana cewa ya soma karatun Al-Qur'ani mai girma tun yana ɗan karami, kuma ya haddace shi a lokacin yana da shekara 14 zuwa 15. A ɓangaren karatun Boko kuma, malamin ya ce mahaifinsu ya yarda ya yi firamare, amma bai yadda ya ci gaba da sakandare ba sai ya haddace Al--Qur'ani, kuma hakan aka yi. Bayan kammala firamare da sakandare, Sheikh Daurawa ya kuma ci gaba da neman ilimi, domin faɗaɗa karatun addini, a wajen waɗansu manyan mashahuran malamai na Kano. Ya ci gaba da karatu na zamani a Jami'ar Bayero, a ɓangaren aikin jarida, ko da yake wasu dalilai sun tsayar da shi wanda hakan bai sa ya kammala ba., amma ya yi karatun difiloma a computer data processing. Malamin ya ce wani muƙami da ya taɓa riƙewa na gwamnati shi ne kwamandan Hisbah da ya yi tsawon shekara takwas. Malamin ya bayyana cewa ɗaya daga cikin hukunce-hukunce da ya taɓa rufe ido ya zartar a jihar Kano a lokacin da yake kwamandan Hisbah, shi ne tursasawa da ya yi kan cewa sai an yi doka a Kano na a dinga yin gwaji kafin a yi aure. Sheikh Daurawa ya ce wannan ya ba shi dama har ya fito da wani shiri na aurar da zawarawa, wanda al'umma da gwamnati suka bayar da haɗin kai har aka aurar da mata kusan dubu shida zuwa dubu bakwai. Sheik Aminu Daurawa ya bayyana cewa akwai kuma wani abu mafi muni da ya kasa fita daga zuciyarsa na wani mutum da ke neman 'ya'yansa mata guda biyu. Mutumin ya kori mahaifiyar yaran inda ya shafe sama da shekara ɗaya yana zama da 'ya'yansa tamkar matansa na aure. Da abin ya ishe 'ya'yan ne suka kai mahaifin nasu ƙara. Zogale da ƙuli-ƙuli da koren tattasai A ɓangaren abinci kuma, malamin ya ce ya fi son zogale da ƙuli-ƙuli da koren tattasai da albasa da tumatiri, malamin ya ce yana matuƙar son wannan haɗin. Babbar kyautar da malam ya ce ba zai manta da ita ba ita ce kyautar naira 200 da wani mutum ya zo ya kai masa har gida saboda ƙaunar da ya ce yake wa malamin. A lokacin da yake matashi, ya buga wasan ƙwallon ƙafa sosai. A cewarsa, shi bahago ne, wanda hakan ya sa ya fi buga lamba uku ko tara ko kuma 11. Sai kuma ta ɓangaren tafiye-tafiye kuma, malamin ya ce ya fi zuwa ƙasashen Afrika da na Larabawa, amma a kwanakin baya ya yi biza zai je ƙasar Amurka da Turai sai kuma aka samu ɓullar annobar korona. Malam ya ce babban burinsa a duniya shi ne ya cika da Imani." https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-54560258 +entertainment 'Yan Kannywood na jimamin mutuwar Ladi Mutu-ka-raba A ranar Asabar ne aka samu labarin rasuwar fitacciyar 'yar Kannywood din nan wato Ladi Mohammed wadda aka fi sani da Ladi Mutu-ka-raba. An bayyana cewa jarumar dai ta rasu ne bayan ta yi fama da doguwar rashin lafiya. Tuni jama'a da dama cikinsu har da 'yan Kannywood suka fara yin ta'aziyya dangane da rasuwarta. Saratu Gidado wadda aka fi sani da Daso kenan ke ta'aziyyar mutuwar Ladi a shafinta na Instagram. Shi ma Ali Nuhu wanda tauraro ne a Kannywood ya yi ta'aziyyar rasuwarta a shafin instagram. Sani Danja ba a bar shi a baya ba wajen yin ta'aziyya kan rasuwar Marigayiya Ladi. A bara ne dai bayan rashin lafiyar marigayiyar ta yi tsanani aka yi ta yawo da hotunanta a shafukan intanet inda ake cewa tana bukatar taimako. Sai dai Marigayiyar ta fito ta kare kanta dangane da hakan inda ta ce masu son bata mata suna ne suka aikata hakan. Tuni jama'a da dama cikinsu har da 'yan Kannywood suka fara yin ta'aziyya dangane da rasuwarta. Fim din da ta yi na Mutu ka raba na daga cikin fina-finan da suka sa ta yi fice kamar yadda Ibrahim Sheme ya shaida wa BBC da muka tuntube shi bayan rasuwarta. https://www.bbc.com/hausa/labarai-51892452 +politics Siyasar Kano: Yadda Kwamishinonin Ganduje ke murabus domin neman takara a zaben 2023 "Masu muƙaman siyasa a jihar Kano da ke arewacin Najeriya na ci gaba da ajiye mukamansu saboda sha'awar fitowa takara a zaben 2023. Hakan na zuwa ne bayan umarnin da gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ya bayar ga masu sha'awar tsayawa takarar a kan su sauka daga duk wani mukami na gwamnati. Wani ɗan jarida da ke gabatar da shirye-shiryen siyasa a jihar ta Kano, Bashir Sarki, ya shaida wa BBC cewa kawo yanzu kusan mutum tara sun ajiye mukamansu tun bayan umarnin gwamnan. Ya ce cikin waɗanda suka ajiye aiki zuwa yanzu, har da Nasiru Yusuf Gawuna, mataimakin gwamnan Kano wanda ya sauka daga matsayin Kwamishinan Noma; da Murtala Sule Garo, Kwamishinan Kananan Hukumomi, da na Raya Karkara, Musa Iliyasu Kwankwaso. Akwai kuma Nura Muhammad Dankade, Kwamishinan Kasafi da Kwamishinan Ilimi, Sunusi Sa'idu Kiru. Bashir Sarki ya ce yawanci ajiye aikin nasu ba ya rasa nasaba da aniyarsu ta tsayawa takara da kuma la'akari da sashen da ake ta dambarwa a kansa na cikin sabuwar dokar zabe ta 2022 da ya bukaci masu neman mukamin siyasa su ajiye aikinsu idan suna da sha'awar yin takara tun yanzu. Dan jaridar ya ce ""Wasu daga cikin waɗanda suka ajiye muƙaman nasu ana kyautata zaton za su fito takarar gwamna, sai kuma wasu da ake ganin za su fito takarar Majalisar tarayya da masu neman majalisar jiha."" Ya ce a ranar Asabar 16 ga watan Afrilu na 2022, ne gwamnan jihar ta Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bayar da sanarwa cewa duk mai rike da mukamin gwamnati ya ajiye mukamin zuwa ranar Litinin 18 ga watan na Afrilu. Bashir Sarki ya ce sanarwar gwamnan ta zo a ƙurarren lokaci, domin haka ba mamaki wasu daga cikinsu za su haƙura da aniyar tsayawa takara baki ɗaya idan ba su samu damar ajiye aiki kafin karewar wa'adin da gwamnan ya bayar ba. Ya ce ""Akwai wadanda kuma suna da sha'awar tsayawa takara amma har yanzu ba su sauka ba, kamar shugaban hukumar Karota, Baffa Babba Dan Agundi, wanda ake tunanin zai kara komawa ya nemi takarar dan majalisar jiha mai wakiltar karamar hukumar Birni da kewaye, akwai kuma kwamshinan matasa da wasanni, Kwamared Ado Lakwaya, wanda ake ganin zai nemi takarar dan majalisar tarayya daga yankin Kabo da Gwarzo."" ''Sauran sun hada da kwamishinan lafiya, Dakta Tsanyawa, shi ma ana ganin kamar zai nemi takarar majalisar tarayya a yankin Kunchi da Tsanyawa, akwai kuma Kwamishinan Yada Labarai na jihar Kano, Kwamared Muhammad Garba, shi ma ana ganin zai nemi takarar majalisar tarayya a yankin karamar hukumar Birni da Kewaye, to amma shi ba ya nan, ya je Umrah'' in ji Bashir. Ya ce ba mamaki cikin makon da za a shiga gwamnan ya bayar da sanarwa a kan wadanda za su maye gurbin wadanda suka yi murabus din, ko kuma gwamnati ta ce ta bar manyan sakatarorin ma'aikatu da hukumomin da aka samu gibi su ci gaba da tafiyar da al'amura a can." https://www.bbc.com/hausa/labarai-61137087 +health Bidiyo: Mace mai shekara 100 da ke koya wa mutane rawa Latsa hoton sama domin kallon bidiyon Wata 'yar rawa da ke dab da cika shekara 100 a duniya tana amfani da hikimarta wajen neman taimako domin bai wa Hukumar Lafiya ta kasa da ke Birtaniya. Dinkie Flowers ta gudanar makarantar koyon rawa tsawon rayuwarta. Sai dai ta daina a bara lokacin da aka sanya dokar kulle. Yanzu tana tara kudin ne ta hanyar koyar da rawa sau uku a kowanne mako. https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-56455756 +technology Daga Bakonmu Na Mako: Yadda za ku gane bidiyon boge da ake amfani da fasaha don sauya abubuwa "Bakonmu na wannan makon Aliyu Dahiru Aliyu ne ya ba ku wasu hanyoyi da za ku iya bi don gano cewa bidiyo na boge ne ko na gaskiya, a wannan zamani da labaran karya suka yawaita. Kalmar ""Deepfake"" a Turance na nufin bidiyon da ake kirkira da fasahar na'ura mai kwakwalwa ta ""Artificial Intelligence"" domin a hada hotuna wajen kirkirar bidiyo mai kama da gaske. Bidiyon da yake wannan likau din na daya daga cikin dubban bidiyon boge na ""deepfake"" da suke yawo a shafukan sada zumunta. A hakika abin da ya faru a bidiyon bai faru a gaske ba. Kirkirarsa akai amma aka yi shi mai kama gaske. Fasahar ""deepfake"" na kirkirar bidiyon da yake kamar gaske duk ko da kuwa kirkirarre ne. Ta hanyar ake kirkirar bidiyon da yake kama da mutum na aikata abin da bai taba aikatawa a rayuwarsa ba. Masu bincike a jami'o'i ne suka fara gano yadda za su iya amfani da kwamfuta wajen kirkirar bidiyon a wajejen 1990. Daga baya masu fina-finai suka karbi lamarin. A yanzu kuwa fasahar ta fada hannun matasa 'yan dandatsa da suke amfani da ita wajen kirkirar bidiyoyin da suke sakawa a shafukan sada-zumunta ko kuma bidiyoyin batsa. Ba iya bidiyo ba, har sauti ana iya kirkirarsa ta hanyar ""deepfake"". Akwai ""applications"" na waya masu yawa da ake amfani da su wajen kirkirar muryar wani ta hanyar fasahar daga cikinsu akwai ""VoiceApp"" da ""Overdub"". Wannan fasahar ta samar da damar kirkirar bidiyon boge da kuma muryar boge. Ana iya kirkirar muryoyin sanannun mutane ta hanyar suna fadar maganganu da ba su fada ba a zahiri. Jaridu sun rawaito yadda aka yi amfani da bidiyon bogi wajen damfarar mutane ta hanyar yanar gizo ciki kuwa har da wanda aka yi amfani da bayanan wani kamfani a Birtaniya wajen damfarar da ta kai kimanin £200,000. A wani rahoto da jaridar Forbes ta rubuta, wani dan damfara ya yi amfani da muryar bogi wajen kwaikwayar muryar shugaban kamfanin har ya ce a fitar da wadannan makudan kudade. Rahoton ya bayyana yadda dan damfarar ya kira sashin kudi na kamfanin ya ce a fitar da wannan kudi, sannan ya sake kira ya ce ya tabbatar da shigar kudin. A lokacin da dan damfarar ya kara kira don a tura kudi a karo na biyu sai mai tura kudin ya lura cewa lambar mai kiran ta kasar Australia ce ba ta Birtaniya ba. Rahotanni sun nuna cewa bidiyo da muryoyin bogi na ""deepfake"" na ci gaba da yaduwa kamar wutar daji. Rahoton wani kamfani da yake bibiyar fasahar kirkirar da ake kira Deeptrace ya nuna cewa a shekarar 2019 akwai bidiyon bogi a intanet da suka kai yawan 7,965. Rahoton ya ce a kasa da wata tara yawan bidiyon ya karu zuwa zuwa 14,678, wanda hakan ke nuna bidiyon ""deepfake"" ya karu zuwa ninki biyun yawansa tun farkon kirkirar fasahar a kasa da wata tara kawai. A yanzu haka idan ka yi binciken ""deepfake"" a shafin bincike na Google zai samar maka da dubunnan bidiyoyin bogi musamman a shafin YouTube da kuma sauran shafukan bidiyon batsa. Ana ci gaba da amfani da bidiyoyin bogi wajen kirkirar bayanan da ake zambatar mutane da su a siyasa. Masana na ganin yawaitar irin wadannan bidiyoyi ka iya janyo tashin husumar siyasa, rigingimun addini, da kuma lalata dimokradiyya da ci gaba. Masanan na ganin yawaitar irin wadannan bidiyoyi zai janyo mutane su daina yarda ko su dinga shakkun bidiyon da a hakika na gaskiya ne. Wani masani a bangaren bidiyon bogi dan kasar Birtaniya da ake kira da John Dabson, ya bayyana cewa yawaitar irin wadannan bidiyoyi zai iya rusa yardar da aka yiwa dimokradiyya. A shekarar 2018, wani bidiyo da mutanen Gabon suka dauka kirkirarsa aka yi don a boye rashin lafiyar Shugaba Ali Bango ya janyo tashin hankalin siyasa a kasar. Har yanzu haka fasahar gane bidiyon boge ba ta gama yin nisa ba saboda shi kansa bidiyon a yanzu yake yaduwa. Wasu fasahohin da aka ce suna iya gane bidiyon boge ta hanyar motsin fuskar mutum basu yi ingancin da ake da bukatarsu ba. Sai dai kamfanin Facebook na ci gaba da samar da hanyoyin da za a hadu wajen samar da maganin wannan matsala tun ba ta yi nisa ba a wani taro da ake kira da ""Facebook Deepfake Detection Challenge"". Da farko bincike a kamfanin Deeptrace sun gano cewa mutanen da suke bidiyon boge na ""deepfake"" ba sa motsa idanuwansu. Amma a watanni kadan masu kirkirar suka fara yin bidiyon mai motsa idanun. Har yanzu dai bidiyon boge bai kai kyau da fitar bidiyon gaske ba. Amma masana na ganin yarda cewar bidiyoyin ba za su taba kamo na gasken ba yaudarar kai ne. Babbar hanyar da aka umarci mutane su dinga amfani da ita wajen gane bidiyon boge shi ne amfanin da zurfin tunani wajen gane shin lamarin zai yiwu ko ba zai yiwu ba." https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-55185608 +sports Liverpool 4-0 Man United: Liverpool ta dare kan teburin Premier League Liverpool ta hau kan teburin Premier League, bayan da ta doke Manchester United 4-0 ranar Talata a Anfield. A minti na biyar da fara tamaula Liverpool ta ci kwallo ta hannun Luis Diaz daga baya Mohamed Salah ya kara na biyu a minti na 22, na farko da ya zura a raga tun bayan wasa uku a gasar. Rabon da Salah ya ci kwallo tun ranar 12 ga watan Maris da Liverpool ta doke Brighton 2-0, shi ne ya ci na biyu a bugun fenariti. Bayan da suka yi hutu suka koma zagaye na biyu ne Sadio Mane ya kara na uku, sannan Salah ya kara na hudu na kuma biyu da ya zura a raga a ranar ta Talata. Kawo yanzu dan kwallon tawagar Masar ya ci 22 kenan a gasar Premier ta bana, shi ne ke kan gaba a yawan zura kwallaye a raga a kakar bana. Da wannan sakamakon Liverpool ta hau kan teburin Premier a karon farko da tazarar maki biyu tsakaninta da Manchester City, wadda za ta yi wasa da Brighton ranar Laraba a Etihad, a wasan farko City ce ta yi nasara da ci 4-1. A wasan farko da suka fafata a gasar ta Premier League da aka kara tsakanin kungiyar Anfield da Red Devils ranar Lahadi 24 ga watan Oktoba, Liverpool ce ta caskara United da ci 5-0 a Old Trafford. Wadanda suka ci wa Liverpool kwallaye biyar a ranar sun hada da Naby Keita da Diogo Jota da kuma Mohamed Salah da ya zura uku rigis. Liverpool wadda ke fatan lashe kofi hudu a bana ta kai wasan karshe a FA Cup, bayan da ta doke Manchester City 3-2 a wasan daf da karshe ranar Asabar. Tuni dai Liverpool ta lashe Carabao Cup a kakar nan, za ta buga wasan karshe da Chelsea a FA Cup, itace ta daya a teburin Premier karon farko tun 5 ga watan Octoba. Haka kuma Liverpool za ta kara da Villareal gida da waje a Champions League wasan daf da karshe. https://www.bbc.com/hausa/wasanni-61157402 +religion Ku San Malamanku tare da Abubakar Sani Ahmad Mai Ashafa, malamin da ya yi muƙabala da Sheikh Abduljabbar "A wannan makon filinmu na Ku San Malamanku ya tattauna da Malam Abubakar Ashafa da ke birnin Kano a arewacin Najeriya. Malamin ya shaida wa BBC Hausa cewa an haife a unguwar Madatai da ke tsakiyar birnin Kano, a shekarar 1974. Malam Abubakar ya soma karatunsa na allo a gida - wato a makarantar Islamiyya da ke gidansu, tun daga farkon rubutu har zuwa sauke Alkur’ani. Malam Abubakar Sani Ahmad Mai Ashafa, mutumin Gaya ne ta jihar Kano, kakansa Malam Muhammadu na Tanda ne ya shiga garin Kano, inda ya assasa makarantar Islamiyya da ya sanya wa suna Tandawiyya Islamiyya kuma har yanzu ana koyarwar ilimin addini a wannan makaranta. Ya ce daga nan ne mahaifinsa ya kai shi wurin abokansa malamai domin daukar karatu da kara gogewa, ciki har da aminin mahaifinsa Malam Isyaka kan Tudu. Baya ga wannan mahaifinsa ya mika shi ga wani fitaccen malami mai suna Malam Aminu Sanda inda nan ma ya yi karatu mai zurfi. Malamin ya yi karatu a wurin mashahuran malamai a Kano, ciki har da su Malam Musa Gabari, da Malam Dan Tsoho Madabo da sauransu. Malamin ya kware a fannin Fiqihu inda har ya yi rubuce-rubuce kan hakan. Malam Abubakar Ashafa ya yi karatun firamare a makarantar Tudun Madatai, daga 1980 zuwa 1987. Daga nan ya tafi makarantar Sakandare ta Aliya, amma bangaren Arabiyya, a shekarar 1993 ya kammala karatun babbar sakandare. Tun daga wancan lokacin bai kara yunkurin shiga wata makaranta a gaba ko da kuwa jami’a ce ba, amma a shekarar 2006 ya yi nasarar shiga Jami’ar Bayero inda ya karanci fannin ilimi wato Education. Iyaye da kakannin Malam Abubakar sun yi fice a fannin karatun Ashafa, daya daga cikin dalilan da suka sanya ake yi musu lakabi da Mai Ashafa. Kamar yadda al’ada take a birnin Kano, kowacce unguwa akwai abin da suka yi fice a kai, ko dai a fannin ilimi ko kasuwanci da sauransu. Misali kowa ya san unguwar Madabo ta yi fice da malaman ilimin Fiqihu ne, Chiroma gidan Hadisi, wannan dalili ya sanya aka yi wa gidan Malam Amadu da gidan Ashafa. Ya yi karatun littafan addinin tun daga Kawa‘idi, da Risala, da Ishimawi, da Azkari, har zuwa Iziyya. ""Daya daga cikin kalubalen da na fara fuskanta a fannin ilimi ya fara ne lokacin da na shiga jami’a, sakamakon zabar fannin Education da na yi, kusan dukkan karatun da na yi kafin wannan lokacin da Larabci na yi, don haka da na zo jami’a sai komai ya sauya,"" in ji Malam Abubakar. Ya ci gaba da cewa: ""Ba na mantawa ranar farko da muka fara daukar karatu, sai na ji malamin na ta zuba turanci, kusan ban fahimci komai da yake magana akai ba. ""Abin da ya fara zuwa raina shi ne lamarin nan ko dai a yi ne ko kuma na fasa, Allah ya taimake ni a can layi karshe nake, duk mutanen da malamin ke tashi domin amsa tambayoyi babu ni a ciki."" Malam Abubakar ya ce daga nan ya lura da wanda ya fi kowa zakewa wajen amsa tambaya, yana mai cewa ""ai ana fitowa sai na same shi na shaida masa babu abin da na gane a karatun nan baki daya. Ina son ka taimaka min idan na wuce wannan lokacin ba tare da na yi wani abu ba, gaskiya sai dai na hakura da karatun.’’ Haka dai aka yi ta fafatawa har Allah ya kai malamin kammala digiri na farko, ya yi dirigi na biyu, har ga shi a halin yanzu yana kokarin yin digirin digirgir. Malam Abubakar ya ce ya shiga sahun masu mukabala da malamin nan mai jawo ce-ce-ku-ce Malam Abduljabbar Nasiru Kabara ne saboda ya ga yana sukar manzon Allah (SAW). Ya ce da fari malamai irin sa suna yabon malamin saboda yanayin koyarwa da karatukansa. Amma daga bisani da lamarin ya sauya dole suka ja daga lokacin da ya fara ketare wasu iyakoki ""ya fara tabo sahabban Manzon Allah (SAW) da ma shi kansa annabin Allah"". Daya daga cikin dalilan da suka sanya Malam Abubakar ya ce ya yi rubutu kenan, lokacin Malam Abduljabbar ya ""fara daga yatsa ga sahabban Manzon Allah SAW, na yi masa raddi a littafina mai shafi kusan 100."" Ya ce: ""Malam Abduljabbar ya yi ta kuri cewa cikin kwana guda zai mayar da martani kan rubutun amma hakan ba ta yiwu ba, sannan ya sha yin kuri a zo a yi mukabalar amma abu ya gagara. Da tafiya ta yi nisa, ya fara kaucewa hanya bayan sanyo Manzon Allah SAW ne aka taru aka yi wannan mukakabala, kuma tana daya daga cikin abin da nake alfahari da su."" Iyali Malam Abubakar ya ce yana da mace guda da ‘ya’ya har da jika daya. Abinci Malamin ya ce yana cin kowanne irin abinci amma babu kamar wake da shinkafa da yaji. Ya kara da cewa shi ma’abocin shan shayi ne." https://www.bbc.com/hausa/articles/c0vgxlxw88zo +politics Abu biyar da Shugaba Buhari ya ce a jawabinsa na ranar samun ƴancin Najeriya "Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar da jawabi a ranar da Najeriya ke cika shekara 62 da samun ƴancin kai. Wannan ne jawabin Shugaba Buhari na ƙarshe a irin wannan rana ta samun ƴancin kai a matsayinsa na shugaban Najeriya ganin cewa zai sauka a 2023. Cikin abubuwan da ya yi magana a kai a yayin jawabin har da batun gudanar da sahihin zaɓe a 2023. Ga dai wasu daga cikin abubuwan da shugaban ya yi magana a kan su: Cikin abubuwan da Shugaba Buhari ya yi magana a kansu a yayin jawabin da ya yi har da batun haɓaka tattalin arizikin Najeriya inda ya ce tun a lokacin da aka zaɓe shi, ya yi alƙawarin haɓaka tattalin arziƙi, yaƙi da cin hanci da rashawa da kuma inganta tsaro. Shugaban ya bayyana cewa daɗin daɗawa kan waɗannan alƙawuran, gwamnatinsa ta kuma sha alwashi da yin tsayuwar daka wajen ganin cewa ta cire Ƴan Najeriya miliyan 100 daga cikin talauci a cikin shekara goma. Sai dai shugaban ya bayyana cewa da taimakon Ubangiji, gwamnatinsa ta yi matuƙar ƙoƙari wurin cika waɗannan alƙawuran da goyon bayan ƴan ƙasar da dama amma duk da haka a cewarsa kwaliyya ba ta kammala biyan kuɗin sabulu ba. Shugaban ya bayyana cewa ɗaya daga cikin wuraren da gwamnatinsa ta yi matuƙar ƙoƙari shi ne bangaren yaƙi da cin hanci inda ya ce sakamakon inganta ɓangarorin yaƙi da cin hanci da kuma taimakon ƙasashen waje an mayar da kuɗaden haram masu yawa da aka sace aka fitar waje. Ta ɓangaren tsaro kuma, shugaban ya bayyana cewa an yi ƙoƙari wajen rage rikicin da ake yi a arewa maso gabashin ƙasar, da rikicin ƴan tayar da ƙayar baya a yankin Neja Delta da kuma rikice-rikicen ƙabilanci a wasu sassa na Najeriya da sauran matsalolin da ke yi wa ƙasar barazana. Haka kuma Shugaba Buhari ya yaba wa gwamnatinsa sakamakon tsare-tsaren da ta yi amfani da su wurin fita daga matsin tattalin arzikin da ta shiga har sau biyu. A yayin jawabin nasa, Shugaba Buhari ya tabbatar da cewa gwamnatinsa ta bai wa ɓangaren noma fifiko ta hanyar fito da ƙanana da matsakaitan shirye-shirye da suka samar da ayyuka ga miliyoyin mutane. Shugaban ya kawo misali da shirye-shirye irin su Anchor Borrower wanda ya ce Ƴan Najeriya sun samu tagomashi ta bangaren samun wadataccen abinci da kuma jawo hankalinsu kan ɗaukar noma a matsayin sana'a. Shugaban ya bayyana cewa fitar da kayayyaki da ƙasar ke yi musamman amfanin gona da sauran abubuwa na kimiyya da fasaha za su taimaka wa kasuwar hada-hadar kuɗi ta ƙasar. Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya a yayin jawabin nasa ya bayyana cewa yana matuƙar baƙin ciki sakamakon cikas da ake samu akai-akai a ɓangaren ilimin gaba da sakandare a ƙasar. ""Ina kira ga Ƙungiyar Malaman Jami'o'i ta ASUU da ta koma aji kuma ina ba su tabbacin cewa zan share musu hawayensu da ɗan abin da muke da shi duk da muna rashin kuɗi,"" in ji shi. Shugaban ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa ta yi ƙoƙari wurin magance matsalar wadda aka shafe shekara 11 ana fama da ita. Shugaba Buhari ya kuma tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta yi ƙoƙari wurin tattara kuɗi a ciki da wajen ƙasar domin tallafa wa ɓangaren ilimi don tabbatar da cewa ƴan ƙasar sun samu ingantaccen ilimi. Kan batun zaɓe kuwa, Shugaba Buhari ya yi alƙawarin ƙara inganta harkar zaɓe a ƙasar a yayin da ake fuskantar zaɓen 2023 da ke tafe. Shugaban ya bayyana cewa duk wani ci gaba da aka samu a ƙasar idan ba a zaɓi shugabanni ta ingantacciyar hanya ba duk wani ƙoƙari da aka yi ba zai isa ba. Shugaban ya kawo misali da zaɓen da aka yi a kwanakin baya a Jihohin Anambra da Ekiti da Osun da wasu mazaɓun tarayya inda ya ce an yi zaɓen gaskiya da gaskiya. Game da zaɓen 2023 da ke tafe, shugaban ya yi kira ga ƴan takara da su gudanar da yaƙin neman zabensu cikin lumana da kuma kiyayewa daga kalaman ɓatanci ga juna. Haka kuma shugaban ya bayyana cewa yana sa ran za a samu ƙarin matasa da mata a zaɓen da za a gudanar da ke tafe. Shugaba Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa ta yi ƙoƙari matuƙa wurin inganta ɓangaren kiwon lafiya. Ya bayyana cewa musamman idan aka yi duba da lokacin annobar korona, ƙasar ta taka rawar gani da har ya sa ƙasashen duniya suka jinjina mata. Shugaban ya bayyana cewa Najeriya na daga cikin ƙasashen duniya da ta ba mara ɗa kunya ta hanyar juriya da mayar da hankali bayan duniya ta yi hashen cewa tana daga cikin ƙasashen da annobar korona za ta yi wa ɓarna" https://www.bbc.com/hausa/articles/cxx98d608rno +religion Yahaya Aminu Sharif: Kotun Daukaka Ƙara ta ce a koma kotun Musulunci Wata Kotun Daukaka Kara da ke jihar Kano a arewacin Najeriya ta yanke hukunci kan wasu matasa biyu da ake zargi da yin batanci ga Annabi S.A.W. Kotun ta ce za a ci gaba da tsare wani matashi da ake zargi da yin batanci ga manzon Allah, Yahaya Aminu Sharif, har sai an yi gyararraki a kan kararsa da aka yi a kotun shari'ar Musulunci. Sannan alƙalin da ya saurari ƙarar ya ce rashin lauya mai tsaya wa Yahaya ya ci karo da dokar kare haƙƙin waɗanda aka tsare bisa ko wane laifi kuma dole ne kotu ta tabbatar da samar masa lauya. Sai dai alkalin ya bayar da umarnin cewa wani alkali na daban ne zai sake sauraron shari'ar Yahaya Aminu a kotun musuluncin, wato ba wanda ya saurari karar da farko ba. Don haka yanzu za a yi sabon zaman sararen karar Yahaya Aminu Sharif ne a kotun Musulunci da ke zamanta a Filin Hockey a jihar Kano. A watan Satumbar 2020 ne Yahaya Aminu Sharif ya daukaka kara bayan Babbar Kotun Shari'ar Musulunci ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samunsa da laifin a wata waka da ya yi a shekarar 2019. Matashin, mai shekara 22 dan asalin birnin Kano, ya musata zargin da aka yi masa na yin batanci ga manzon Allah. Sai dai kotun ta ba shi damar daukaka kara. Ko da kotun ta tabbatar da hukuncin kisan, dole sai gwamnan jihar Kano ya sanya hannu kafin a aiwatar da hukuncin a kan Aminu Yahaya Sharif. Amma gwamnan jihar Kano a Abdullahi Umar Ganduje ya ce a shirye yake ya sanya hannu kan takardar hukuncin idan ta isa hannunsa. Haka kuma, kotun ta kori hukuncin babbar kotun Musulunci da a farko ta kama Umar Faruk da laifin ta kuma aike da shi gidan gyara hali tsawon shekara 10. Kotun Daukaka karar ta ce dalilinta na korar karar shi ne a lokacin da ya aikata laifin shekarunsa ba su kai 18 ba don haka ta ce a saki Faruk Umar. An haifi Yahaya Sharif-Aminu a unguwar Sharifai, a gidan Mallam Aminu Sha'aibu Sharifai wanda malamin addini ne kuma mai yabon Manzon Allah SAW. Ya fara karatu a makarantar firamaren 'yan awaki da ke unguwar Koki, sannan ya wuce karamar sakandire a GATC Gwale daga aji 1 zuwa 3. Bayan ya kammala sakandire ne sai ya bar karatu ya koma sana'ar saye da sayarwa ta takalma. Haka kuma ya yi karatun addinin Islama a gaban mahaifinsa, wanda ya yi da'awa a jawabin da ya gabatar a gaban kotu na cewar mahaifin nasa shi ne shehinsa. Ya ce shi dan kungiyar Faira ne a darikar Tijjaniya kuma yana gabatar da salloli biyar a kullum. Ya hada wani dandali na Whatsapp da ya yi wa lakabi da Umma Abiha, wato dandalin masoya 'yar manzon Allah SAW. A ranar Asabar 29 ga watan Fabrairu, 2020, a lokacin da suke hirar addini a dandalin aka sami wani ya soki darikar Tijjaniya yana mai zargin suna tafiya daidai a inda shi kuma ya nadi muryarsa ta (Voice note) inda ake zargi ya yi kalaman batanci ga Manzan Allah SAW, wanda ya yi su ne saboda an soki darikar Tijjaniya da yake bi. Bayan yin kalaman nasa ne sai ya sayar da wayarsa ya yi kudin mota zuwa Jigawa domin gudun abin da zai je ya dawo. https://www.bbc.com/hausa/labarai-55746225 +health Abin da ya sa cutar sanƙarau ke tasiri a Arewacin Najeriya "Cutar sanƙarau, cuta ce wadda ta daɗe tana yin illa musamman ga ƙananan yara a Najeriya a wani lokacin kuma ta kashe su, kuma akasarin waɗanda take yi wa illa daga arewacin ƙasar suke. Hukumar da ke yaƙi da cutuka masu yaɗuwa a ƙasar wato NCDC ta bayar da rahoton cewa cutar ta kashe mutum aƙalla 269 tun daga farkon wannan shekara. Baya ga kisa, wasu daga cikin illolin da cutar take yi wa waɗanda suka kamu da ita sun haɗa da makanta, da kurmancewa da farfaɗiya da wasu ciwuka na daban. Yin riga-kafi na daga cikin hanyoyin da ke magance cutar, sai dai rashin riga-kafin a Najeriya na daga cikin abubuwan da suka sa ake samun ɓarkewar wannan cuta a ƙasar, kamar yadda Dakta Salisu Abdullahi Balarabe ya bayyana, wanda farfesa ne kan fannin lafiyar ƙwaƙalwa da laka a asibitin koyarwa na Usumanu Ɗanfodio da ke Sokoto. Farfesan dai ya gudanar da bincike kan yadda wannan cutar ta yi wa mutanen ƙasar illa a shekara 100 baya kuma a tattaunawarsa da BBC, ya yi ƙarin bayani kan cutar. A cewar Dakta Salisu, ""Ana gudanar da riga-kafin cutar sanƙarau a Najeriya ne a duk shekara, kuma ana yin wannan riga-kafin ne kawai a lokacin da aka samu ɓarkewar cutar"". ""Amma a ganina, a 2018, gwamnatin ƙasar ta saka riga-kafin sanƙarau a cikin shirye-shiryenta na riga-kafin cutuka, amma wannan shirin bai yi tasiri ba kuma bai kai wasu sassan ƙasar ba."" A cewarsa, shirin riga-kafin ya ƙi tasiri ne sakamakon tsadar da yake da shi, kuma riga-kafin da aka fito da shi an fito da shi ne domin magance nau'i guda kawai na sanƙarau ɗin a maimakon nau'uka daban-daban. Ya ce a shekara biyu zuwa uku da suka wuce, wani na'ui na daban suke gani na sanƙara'u ɗin ba nau'in da ake yin riga-kafin domin shi ba ne. Sai dai ya ce mafita a nan ita ce, idan ana so riga-kafin ya yi aiki, ya kamata a samo riga-kafin da zai magance nau'uka aƙalla huɗu na wannan cuta ba wai nau'i ɗaya ba. Me ke jawo cutar? A cewar Dakta Salisu, manyan abubuwan da ke jawo cutar sanƙarau suna da alaƙa da abu biyu ne, na farko sauyin yanayi na biyu kuma muhalli. A cewarsa, Arewacin Najeriya ne cutar ta fi ƙamari, da kuma ƙasashe kamar su Senegal da Ethiopia. Bincike da masana da dama suka gudanar ya nuna cewa saboda yanayin zafi da ake samu a wasu yankunan na ƙara taimakawa wurin samun wannan cuta. Dakta Salisu ya ce cutar kuma na yaɗuwa a lokacin hunturu tsakanin Nuwamba zuwa Maris har wani lokaci ma zuwa Yuni. ""A wannan lokaci, akwai wata ƙwayar cuta da ke yawo da ake kira Influenza, waɗanda ke ɗauke da cutar Meningococcal a jikinsu sai ta farfaɗo ta shiga cikin jininsu, daga jini sai ta wuce ƙaƙwalwa zuwa laka, Hanya ta biyu kuma da ake kamuwa da cutar in ji Dakta Salisu ita ce yadda ake samun cunkoson mutane a muhalli ko kuma rashin tsaftaccen muhallin shi kansa." https://www.bbc.com/hausa/labarai-54384051 +entertainment Ƙayatattun hotuna daga Afirka: daga ranar 23 zuwa 29 ga watan Yuli na 2021 Wasu ƙayatattun hotuna daga sassa daban-daban na nahiyar Afirka da wajen ta: Dukkan hotunan suna da hakkin mallaka https://www.bbc.com/hausa/labarai-58024266 +health Lafiya Zinariya: Abubuwan da suka kamata mai gyambon ciki ta kauracewa Likitoci sun bayyana cewa abinci ko cin yaji ba sa janyo gyambon ciki, sabanin yadda mutane ke tunani. Sai dai idan mutum na da gyambon ciki to akwai wasu nau'oin abincin da ya kamata ya kauracewa. Saboda wadannan abincin ko kuma yaji kan tayar da ciwon. Haka zalika mata masu juna biyu na iya samun gyambon ciki, ko da yake ba duka kwaranafi ne ke nufin mai ciki na da cutar ba. A cewar Dr. Na'ima Idris Usman, wasu daga cikin irin abincin da ya kamata a kauracewa sun hada da, kabeji da wake da madara da sinadarin cafe wanda ake samu a cikin shayi ko gahawa. Haka kuma lemon-tsami da abinci mai yaji da mai maiko, suma suna iya tayar da cutar ta ulcer, inji likitar. Dr. Na'ima ta kara da cewa dole ne kuma fai fama da cutar ya kauracewa shan giya da taba da kuma shisha. Sannan kuma mutane su daina shan magungun hana ciwon jiki ba tare da likita ya rubuta musu ba. Cutar ta gyambon ciki dai idan ta yi kamari ta kan janyo matsalolin kiwon lafiya da dama. Cikinsu har da zuban jini da kuma cutar daji wato cutar kansa. Sai dai a kan samu gyambon ciki da ke warkewa da kansu. Amma abu mafi muhimmanci mutum ya je asibiti domin a tantance wanda ya ke damunsa tun kafin lamarin ya yi kamari. https://www.bbc.com/hausa/shirye-shirye-na-musamman-56940786 +technology Hotunan yadda husufin rana ya mayar da samaniyar Asia baƙa 'Yan kallo a wani bangare na Yammacin Afirka, da Yankin Larabawa, da Kudancin Asia, da Kudancin China da kuma Taiwan sun ga yadda rana ta yi husufi a wani yanayi mai ban al'ajabi. Maɗauka hotuna sun ɗauki hotunan husufin rana - yadda wata yake ratsawa ta tsakanin Duniya da Rana, inda ake ganin haske kaɗan. Husufin ya faru ne a ranar tsakiyar bazara - wato rana mafi tsayi a shekara ga mazauna arewacin kusurwar duniya. Ana yin husufin rana ne sau duk shekara daya ko biyu kuma ana iya ganinsa ne kawai a wani bangare na dan yanki a bangarorin duniya. Husufin ba ya wuce daƙiƙa 90 yake kai wa ƙololuwarsa. Mutanen da ke zaune a nisan daruruwan kilomita daga tsakiyar kusurwar ba su ga cikakken yadda rana ta yi husufi ba, ko da yake sun ga 'yan alamu na husufin. Masana ilimin taurari sun ce yadda husufin yake kamar sauya kallo ne daga ƙwan lantarki mai ƙarfin 500W zuwa mai ƙarfin 30W. Gawasu daga cikin hotunan yadda husufin ya kasance a sassan duniya daban-daban. https://www.bbc.com/hausa/labarai-53130401 +business Muhimman wurare da ake zargin gwamnatin Kano da cefanarwa Ana ci gaba da tafka muhawara a jihar Kano da ke arewacin Najeriya game da zargin da ake yi wa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na cefanar da wasu daga cikin ƙadarorin gwamnatin jihar. Ya zuwa yanzu ana cewa an sayar da yawa daga cikin ƙadarorin jihar baki ɗaya, wasu kuma an sayar da wani sashe nasu, yayin da ake tattauna yadda za a cefanar da wasu a nan gaba. Sai dai Gwamna Ganduje da Kwamishinansa na yaɗa labarai Muhammad Garba na fitowa akai-akai suna cewa ba sayar da wuraren ake yi ba, ana ba da su ne ga masu bunƙasa birane zuwa wasu 'yan shekaru kafin daga bisani su koma ƙarƙashin ikon gwamnatin jihar ta Kano. Amma da yawa daga cikin masu yaƙi da wannan manufa kamar su dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP a 2019 Injiniya Abba Yusuf, da ya shigar da gwamnatin Kano ƙara a baya, kan zargin cefanar da ƙadarorin, suna cewa ana yin abubuwa ne a ƙudundune ba a bari mutane su san halin da ake ciki. Kungiyoyi da ɗaiɗaikun mutane na sukar wannan mataki tare da yunƙurin lalubo hanyoyin da za a dakatar da wannan mataki na Gwamna Abdullahi Ganduje. Kamfanin gidan jarida na Triumph: Wannan kamfanin shi ke buga jaridar Triumph da kuma Alfijir da ake bugawa da Ajami, yana daga cikin wuraren da ake zargin an sayar da su baki daya. Ana ruwaito cewa gwamnati ta ce ba a amfani da ginin kamfanin yadda ya kamata, shi yasa ta yanke shawarar bai wa 'yan kasuwar musayar kudi ta Wapa su ci gaba da amfani da shi. Filin fakin na Shahuci: Wannan filin an gina shi da jimawa kuma irin ginin zamani da za a rika ajiye motoci da sauran ababen hawa na masu sana'a a kewayen wajen, domin samun kudaden shiga ga gwamnatin jihar. Amma maganar da ake yi a yanzu an rushe ginin wajen baki daya, kuma hakan ya dugunzuma ran al'ummar jihar ganin cewa an yi almubazzaranci da kuɗaɗe. Otel ɗin Daula: Dadadden otel ne mallakar jihar Kano da ake saukar bakin jihar ko kuma ake bayar da shi cikin sauki ga masu son amfani da shi, domin samun kudaden shiga. Makarantun Sakandire: Mafi yawan jikin katangar makarantun sakandiren da ke jihar Kano ana zargin an sayar da su domin kuwa zaka ga shaguna a jikinsu ta ko ina an fitar, 'yan kasuwa duk sun kama suna ci gaba da harkokinsu. Kukan da masu suka ke yi shi ne, lokacin da yara ke cikin aji suna karatu su kuma 'yan kasuwa sun tayar da injinansu na wuta ko kuma suna harkokin kasuwancinsu, wanda hakan zai iya cutar da yaran da kuma yanayin karatunsu. Filin wasa na Sabon Gari: Filin wasan kwallon kafa da kungiyar Kano Pillars ke buga wasanninta ciki shima an sayar da mafi yawan katangar da ta kewaye shi ga 'yan kasuwa. Masallacin Idi na Kofar Mata: Filin cikin masallacin da kuma kewayensa ya zama cikakkiyar kasuwa wani bangaren kasuwar sai da kayansawa ta kwari, wani bangaren kuma kasuwa Kofar Wambai. A ganin gwamnatin jihar bai kamata a bar wuri mai girma kamar na masallacin ba zaune haka, lokacin da take ta fafutukar samun kudaden shiga domin bunkasa rayuwar mutanen jiharta. Masallacin Juma'a na Waje (Fagge): Shi na an sayar da wani sashe nasa, baya ga zabtarar wani sashe da aka yi, domin fadada gadar saman da ta tashi daga wapa zuwa titin maganda. Gidan Ajiyar Namun Daji (Zoo): Labarin za a sayar da wannan gida ya janyo cece-kucen da duk na baya ba su janyo ba, domin kuwa kungiyoyin kare hakkin dan adam da na masu rajin kare muhalli da tsirrai duk sun tofa albarkacin bakinsu kan wannan batu. Wasu na ganin a cikin kwaryar birnin Kano babu wani waje da ke da dausayi sama da wannan gida, idan kuma aka sare su zai zama cutarwa ga muhalli. Sai dai gwamnatin jihar ta ce so take ta sauyawa dabbobin wuri domin tausayawa halin da suke ciki, ganin mutane sun cimmusu, ba kuma sa samun irin iskar da ya kamata su samu. Gidan Zakka: Wannan ne wuri na baya bayan nan da ake zargin gwamnatin da bayyana aniyarta ta sayar da shi, ko da yake gwamnatin ta ce wani ɓangare ne na jikin ginin za ta yi amfani da shi amma ba ainihin ginin gidan ba. Masu lura da gidan sun yi alƙawarin ba za su ƙyale wannan lamari ba, suna cewa za su shigar da ƙara gaban kotu domin hana wannan mataki. https://www.bbc.com/hausa/labarai-55534350 +health Camfe-camfe kan bayar da gudunmawar jini Akasarin mutane suna bayar da gudunmawar jini idan suna cikin koshin lafiya kamar yadda hukumar lafiya ta duniya ta bayyana. Amma akwai wasu sharudda da idan ba a bi su ba za su iya dagula lamura wanda hakan zai sa a fara tunanin camfe-camfe. Ga wasu daga cikin camfe-camfen da muka gano ba gaskiya ba ne da kuma gyara kan alakarsu da bayar da gudunmawar jini. Marassa cin nama ba sa bayar da gudunmawar Abin da za a duba cikin wannan lamarin shi ne sinadarin Ayon (Iron), daya daga cikin ginshikan jini ne, amma ana damuwa kan cewa jinin wadanda ba sa cin nama ba shi da sinadarin sosai. Amma ko da kuwa mutum ba ya cin nama, muddun yana cin nau'ikan abincin da ke gina jiki, zai samu wadataccen sinadarin a cikin jininsa. Amma kuma idan jinin mutum ba shi da sinadarin na Ayon (Iron) din sosai, bai kamata ya bayar da gudunmawar jini ba saboda tsaron lafiya. Marassa lafiya da masu ciki da kananan yara ba sa bayar da gudunmawar jini Wannan da gaske ne. Mutanen da suke da cutar HIV ko kuma ciwon hanta da tarin fuka da kuma sauran cututtuka irin haka da ake dauka ba sa bayar da jini. Duk wata alama ta mura ko sanyi ko kuma mashako da tsutsar ciki kan iya sa a ki daukar jinin mutum a asibiti idan yaje bayar da gudunmawa. Sai mutum ya warke gaba daya daga duk irin wadannan cututtuka a kalla da kwanaki 14 kafin ya iya bayar da jini. Haka kuma idan mutum yana shan magunguna, sai ya jira ya kammala tukuna kafin ya bayar. Ka'idoji kan shan magunguna sun sha bam-bam idan aka yi la'akari da kasashe. Haka kuma idan mace tana da ciki, ko ba ta dade da haihuwa ba ko kuma tana shayarwa ko kuma cikinta ya zube, to lallai ya kamata ta dan dakata sai ta samu wadataccen sinadarin Ayon ( Iron) a jininta kafin ta bayar da jini. Amma al'ada ga mata ba wata kwakkwarar hujja ba ce da za su ce ba za su bayar da jini ba. Karancin shekarun bayar da gudunmawar jini shi ne shekara 16, amma wannan ya danganta dangane da dokokin kowace kasa. Babu wasu takaimaiman shekaru da za a ce idan mutum ya kai ba zai iya bayar da gudunmawar jini ba amma dai wasu kasashen sun saka shekaru 60 a matsayin shekarun da idan mutum ya kai bai kamata ya bayar da gudunmawar jini ba. Rayuwa baki dayanta na cike da hadari, wasu daga cikin irin wadannan abubuwan kan iya dakatar da mutum daga bayar da jini. Hukumar lafiya ta duniya ta bayyana cewa dabi'u masu hadari da suka hada da luwadi da madigo ko kuma karuwanci kan sa mutum a dakatar da shi idan ya je bayar da kyautar jini har sai an tantance lafiyarsa sa'annan. Haka ma amfani da kwayoyi domin nishadi ta hanyar allura kan iya jawo matsala wajen bayar da jini. Kasashe da yawa sun haramta wa masu irin wadannan kasadar bayar da jini amma kuma wasu suna ganin hakan kamar wata hanya ce ta nuna wariya. An bayyana cewa akalla mutum baligi yana da lita biyar ta jini cikin jikinsa- ya danganta da nauyin jikinsa. A lokacin bayar da jini, jikin mutum kan yi rashin jini da ya kai 500ml. Mutane da dama musamman masu cikakkiyar lafiya kan mayar da jinin da suka rasa cikin sa'o'i 24 zuwa 48. A takaice dai, idan... ......to akwai alamun cewa kuna da cikakkiyar lafiyar da za ku bayar da gudunmawar jini. https://www.bbc.com/hausa/labarai-48625652 +politics 'Ina takara ne don nuna raunin gwamnati don ta yi gyara' Dan takarar gwamnan jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya a ƙarƙarshin jam'iyyar NNPP, ya ce yana siyasa ne don fito da raunin gwamnati don ta yi gyara. Alhaji Garba Umar ya shaida wa BBC Hausa haka ne a wata hira da ta yi da shi. Hirar tana cikin jerin hirarrakin da BBC ke yi da ƴan takarar gwamnoni a jihohin Najeriya. https://www.bbc.com/hausa/articles/cg38v33v9ygo +health To fa! Ashe yin fushi ma abu ne mai kyau? "Mafi yawan sassan fadin duniyarmu ana zaune ne cikin lumanar zaman lafiya da wadata. Kididdigar alkaluma da Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Kasuwanci ta duniya da gwamnatoci daban-daban a fadin duniya suka tattara sun nuna cewa kasashe da dama talauci na raguwa, sannan tsawon rai na karuwa. Mafi yawan wadanda ke zaune a kasashen da suka ci gaba suna da kariya, kuma sun samu karuwar dukiya fiye da kowane zamani a tarihin dan Adam. Shin wane dalili ne ya sanya mutane da yawa ke yin fushi a kodayaushe? Akwai labaran fusata a kan titi, zazzafar takaddamar kafofin sada zumuntar intanet, a wasu lokutan har 'yan siyasa ke bai wa hammata iska (naushin dambacewa ko kokowa).. a iya yi wa mutum uzuri in har ya dauka cewa duniya ta harzuka da fushi. Oliver Burkeman - dan jaridar Birtaniya kuma marubucin da ya yi rubutu kan yadda za a samu farin ciki - ya shirya shirin sauya salo, don bin kadin fushi dangane da yadda za a kawo sauyi. Shin mene ne ke fusata mu? Mene ne ke tunzura lamarin? Ta yiwu mafi muhimmanci shi ne, mummunan abu? Mene ne ke sanyawa a rika bijirowa ko harzuko mana fushi tun a zamanin da, har ta kai ga wani na jin haushin wani har ya fusata? ""Bacin ran da ke harzuka fushi cukurkudadden al'amari ne mai wuyar sha'ani,"" in ji Aaron Sell, Farfesan nazarin kwakwalwa da nazirin miyagun laifuka a Jami'ar Heidelberg a Ohio, da ke kasar Amurka. ""Don fito da lamarin karara, a iya cewa shi ne linzamin zuciya. Wata hanya ta kutsawa cikin tunanin wani, ta yadda za ka sanya ya kimantaka da daraja. Wata hanya ce ta samun nasarar rikicin da ke tsakaninku, tare da sauya masu tunanin."" Farfesa Sell ya kwatanta yadda muhimmin bangaren ""linzamin tunanin zuci"" ke bijirowa daga ""fuskantar fushi ya kambama tayar da jijiyoyi da hucin hura hanci."" ""Kowane daya daga wadannan sauye-sauyen da fushi ke haifarwa a fuska na fito da alamun karfinka/ki da jarumta a zahiri."" A cewar Farfesa Sell, masana kimiyya sun samu kai ga gacin fahimtar cewa "" fushin fuska"" gadonsa ake yi ba koya ake yi ba, saboda ""yara makafi suna bijiro da yanayin fushi da aka saba gani a fuskokinsu."" To ta yaya kyakkyawan ""fushin fuska"" ya haifar wa magabatanmu nasara (samun rinjaye kan al'amuran rayuwa? Ta yiwu ka ji cewa magabatanmu (kakanin kakanninmu) wadanda ba sa bata rai (yin fushi) har su yi fada sun yi nisan kwana fiye da wadanda suka yi (fushi), amma dai ba haka lamarin ya kasance ba. ""Abin da ya faru, a cewar Farfesa Sell, shi ne, ""mutanen da suka damfaru da wani nau'in bacin rai da ke bijiro da fushi sun fi saurin harzukar fusata fiye da wadanda ba sa yi."" Sun yi hakan ne ta hanyar saukaka daidaituwar kyawawan al'amura, har ta kai ga sun yi galaba wajen takaddamar rashin fahimta (ko jayayyar son rai - fifikon ra'ayi) ""A da, mutane wadanda ba sa nuna bacin rai ko fushi a kan tumurmusa su a tauye,"" in ji Farfesa Sell, wato mutane kan yi musu sata, sannan su wulakanta su, sakamakon haka ""sai a kawar da su ko ma a daina jin duriyarsu, sun bata bat."" Wadanda suka tsira su ne wadanda suka yi barazanar janyewa daga hadin gwiwar taimakekeniya (a junansu), inda nan take sukan tunatar da daukacin kyawawan abubuwan da suka aikata, ta yadda sukan sanya mutum dan uwansu ya dawo da baya ya yi ta yaba musu - lamarin da ke haifar da kyakkyawar tarairaya (a tsakanin juna). Bacin ran nuna fushi shi ya fifita irin wadannan mutane da fifikon bunkasar rayuwa, a cewar Farfesa Sell. Don fahimtar fushi muna bukatar yin tunani kan tasirinsa ga jikinmu a zahirance, ta yaya yake zaburar da mu ko kai tsaye yaya tunaninmu ke gushewa. Farfesa Ryan Martin kwararen mai nazarin lafiyar kwakwalwa a Jami'ar Wisconsin-Green Bay ta Amurka mai bincike ne da ke bibiyar abin da ya danganci fushi, yana gudanar da shirin bin kadin daukacin harzukar fushi na ""All the Rage"" da ake watsawa ta wani salon sakon rediyon podcast a kowane wata. ""Da zarar kun yi fushi, tsarin sadarwar jijiyoyinku da ke tausasa tarairayar fafata fadanku ko yunkurin fafatawa sai su zabura su fara aiki,"" a cewar Farfesa Martin, ""Bugawar zuciya sai ya karu, numfashinku ya karu, sai ku fara zufa, kuma tsarin sarrafa abincin ku ya rinka tafiya a hankali."" Wannan yamutsin martanin da kwakwalwa ke yi, mataki ne da jiki ke dauka da manufar nuna karfin tunkarar kowane irin rashin adalci da kuke jin an yi maku. Ita ma kwakalwa na aiwatar da ayyukan ne daki-daki. ""Mun kuma san cewa duk sa'adda mutane suka harzuka da gaske, to tunaninsu zai bijiro a hankali ya rika gudanar da ayyuka daki-daki,"" a cewar Farfesa Martin, ""Sun fi zaburar dabarun tsira"" ko ""na daukar fansa."" Wannan lamari ne da ke bunkasa shi ma dai ba ku yin tunani kan sauran al'amura lokacin da kuke kokarin daukar mataki kan wani abin da kuke jin ba a kyauta maku ba (an yi ba daidai ba, ko rashin adalci). Akwai tabbacin cewa, mafi yawan mutane, musamman wadanda ke zaune a kasashen da suka ci gaba damuwarsu kadan ce in an kwatanta da magabatansu (kakannin kakanninsu), shi ya sa ake bin bahasin dalilin da ya sanya rayuwar wannan zamanin take cike da harzukar bacin rai da ke tunzura fushi? Lamarin na da saukin fahimta, a cewar Farfesa Martin: ""Mutane al'amura sun sha musu kai, ta yadda suna da dimbin bukatun rayuwa, don haka sakamakon kakarewar harkoki sai a ji matukar rashin dadi."" Saukin lamarin shi ne, a cewar Farfesa Martin: ""Al'amura sun sha wa mutan kai ga bukatun rayuwa na karuwa, to sakamakon hakan da mutum ya ji harka ta tsaya cik to al'amura ke nan sun yi matukar muni (a rayuwa)."" Idan ya zama dole mu bi layi a katafaren shagon sayar da kayayyaki ko mun samu tsaiko daga mai kawo mana makamashi, sai kawai mu harzuka da fushi saboda ba mu da lokacin da za mu bata. Wannan shi ne abin da ya kamata a ce ""an kauce masa, tattare da jin cewa ba a iya tabuka komai"" al'amarin da ke sanya harzukar fushi (na nuna rashin jin dadi), a cewar Farfesa Martin. Su ne al'amuran da ""ya kamata a kauce musu, don sukan jefa mu cikin halin rashin iya yin katabus"" har mu fusata, a cewar Farfsa Martin. Yadda bacin rai ke bijiro mana da fushi tattare da irin matakin da muke dauka ""ba a kodayaushe lamarin ke da alfanu a duniyarmu ta wannan zamanin."" Hakika cutar da mutumin da kuke ke fushi da shi ba abu ne mai alfanu ba - don haka akwai bukatar mu san yadda za mu tarairayi fushinmu. Muna iya shawo kan lamarin fiye da yadda muke zato, a cewar Maya Tamir, Farfesan nazarin kwakwalwa a Jami'ar Hebrew ta Jerusalem. Sosuwar zukata ba shi da fa'ida tun da bunkasar harzuka yake haifarwa, a cewar Maya, ""al'amura ne da ake samun horo a kai, sai mu sauya, mu tasirantu da dabarun sarrafa juya akalar yanayinmu."" Bincikenta ya nuna cewa ba kodayaushe ne fushi ke haifar da rikicin fada ba. ""Mu ba 'yan kore ba ne da ke lilo, inji Maya. ""Bacin ran nuna fushi ba ya mayar da mu mafadatan da ba za su iya tarairayar hankalinsu (ko kawunansu ba)."" Bacin rai dai kan iya matukar harzuka mu (cikin dugunzumar fushi) zai iya tunzuro da fada da zage-zage kai har ma takaddamar fada mai zafi a shafin Twitter. Idan wadanda ke bukatar ganin sun kankane karfin ikonsu da matsayinu suka yi fushi, sakamakon hakan na iya haifar da mummunan al'amari - ko ma a karshe da yaki. Amma masanan fannin kula da kwakwalwa sun ce zai iya tunkarar tunaninmu, ya kara masa karsashin zaburarwa don daukar mataki lokacin da aka aikata mana ba daidai ba. Mark Vernon , masanin falsafa (kula da juya akalar tunani) da kula da lafiyar kakwalwa, ya bayyana yadda mutanen da, na zamanin Plato da Aristotle (masanan alkiblar juya akalar tunani) suke da tabbacin cewa akwai abin da ake yi wa lakabi da ""fushi mai kyau."" Sai su ji cewa wanda ke cikin fushi zai yi kyau garesu idan lokacin da suke fushin sun sarayar da harzukar fushinsu wajen gudanar da kwakkwaran aiki (mai amfani). Saboda haka, harzukar fushi dai ""tana iya zabuar da mutum ya aikata wani abu gaba-gadi (da kwarin gwiwa kai tsaye) ko ta zaburar da su yi muhawara mai kyau da za ta bayar da damar warwarewa ko shawo kan takaddamar cikin adalci. Don haka an gano shi cewa: ba za a iya cewa daukacin fushi ba shi da fa'ida. Kawai abin da muke bukata shi ne tarairayar juya akalar wannan kakkarfan lamari, mai matukar sosa zuciya, ta yadda za a sarayar da shi da kyakkyawan tasiri, don gudun ka da mu karasa da dabaibayin bacin rai da zakuwar kai farmakin fada." https://www.bbc.com/hausa/labarai-48004240 +business Daga Titunanmu: Ra’ayoyin ‘yan Najeriya kan kara harajin kaya Latsa bidiyon sama domin kallo A wannan makon, mun tambayi mutane game da karin haraji da gwamnatin tarayya ta yi daga kashi biyar zuwa kashi bakwai da rabi. https://www.bbc.com/hausa/labarai-51143909 +politics Tanko Al-Makura: Tsohon gwamnan Nasarawa ya ce EFCC ba ta kama shi ba "Latsa hoton da ke sama don saurarar hirar da muka yi da Sanata Al-Makura Tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Sanata Tanko Al-Makura ya musanta jita-jitar da ake yadawa cewa jami'an hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arziki zagon-kasa, wato EFCC sun kama shi tare da iyalinsa. Jaridar Premium Times a Najeriya ce ta ruwaito labarin kama Sanata Al-Makura ranar Laraba, inda ta ce EFCC ta tsare tsohon gwamnan da mai ɗakinsa bisa zargin almundahana. Amma Al-Makura, wanda a yanzu shi ne Sanata da ke wakiltar Nasarawa ta kudu a majalisar dattawan Najeriya ya tabbatar da cewa hukumar ta gayyace shi game da wadansu korafe-korafe da aka yi a kansa ne, kuma da kansa ya je hukumar inda ya gana da shugabanta da wasu jami'ai, ganawar da ba ta wuce wani gajeren lokaci ba. Ya zargi masu yada jita-jitar an kama shi da cewa suna so ne su shafa masa kashin kaza ko bata masa suna, amma ba su yi nasara ba. ""Wannan jita-jita ta ba ni mamaki, ta ba mutane da dama mamaki,"" a cewar Sanata Al-Makura. Ya ce dama hukumar EFCC ta gayyace shi tun kafin Sallah amma ya shaida masu cewa ba zai samu damar amsa gayyatar ba sai bayan Sallah, shi ya sa kuma ya shirya ya je don jin dalilin gayyatar. Sanata Al-Makura ya ce ""Ko da na je na gana da shugaban hukumar, sai ya sanar da ni cewa dama korafe-korafe ne da mutane ke yi a kaina, kuma ana son a ji ta bakina. Ganawata da shugaban EFCC duka ba ta wuce minti goma ba."" Haka kuma, ya ce ya tattauna da wasu jami'an hukumar kan korafe-korafen da aka shigar a kansa kuma ya bayar da amsa gwargwadon saninsa. Sanatan mai wakiltar Nasarawa ta Kudu ya musanta zargin da wasu ke yi na cewa gayyatar da EFCC ta yi masa na da nasaba da takarar shugabancin jam'iyyar APC da ya ke yi. ""Masu wannan maganar na yi ne don daƙushe neman kujerar shugabancin APC na ƙasa da mutane da dama ke so in yi. Sai dai ni ba ni da damuwa da kowa,"" a cewarsa. Ya ce mai yiwuwa akwai masu wata manufa a gare shi sabanin wanda masoyansa ke da shi a kansa. Sanata Al-Makura ya ce shi ɗan Najeriya ne mai bin dokar jam'iyya, shi ya sa ma bai zage wajen yin kamfe din shugabancin jam'iyyar APC ba. ""Na tsaya ne saboda a matsayina na dan jam'iyya mai bin umarnin shugabannin jam'iyya, na jira ne in ji irin ka'idojin da za su sa da inda jam'iyyar ta dosa kafin in bude fagen neman shugabancin jam'iyyar,"" a cewarsa." https://www.bbc.com/hausa/media-58007345 +sports Vardy zai ci gaba da taka leda a Leicester zuwa 2024 Jamie Vardy ya saka hannu kan kwantiragin ci gaba da taka leda a Leicester City zuwa karshen kakar 2024. Vardy, mai shekara 35, ya cika shekara 10 a kungiyar King Power a watan Mayu, ya kuma ci kwallo 133 a Premier League a wasa 272. Ya zura kwallo 24 a 2015-16, inda kungiyar ta dauki Premier League da lashe FA Cup. A kakar ce Vardy wanda ya koma Leicester City daga Fleetwood a 2012, ya buga Champions League, bayan cin Premier a wani abu na almara. Tun farko yarjejeniyar Vardy za ta kare a King Power a karshen kakar 2023, wanda aka yi ta alakanta shi da zai koma taka leda a Manchester United. Vardy ya lashe takalmin zinari a yawan cin kwallaye a gasar Premier League a kakar 2019/20 mai 23 a raga ya kuma ci wa Ingila bakwai a wasa 26 da ya yi mata. https://www.bbc.com/hausa/articles/c6p6e5v0exlo +technology ISIS ta sanar da kashe shugabanta tare da naɗa wani sabo "Kungiyar masu iƙirarin jihadi ta IS ta sanar da rasuwar shugabanta, Abu al-Hassan al-Hashemi al-Qurayshi. Wani saƙon murya na kakakin ƙungiyar ya ce an kashe shi ne lokacin yana fada da wadanda ya kira ""makiya ubangiji"", amma kuma bai yi wani karin bayani ba. A watan Maris ya zama shugaba bayan da tsohon shugaban ya kashe kansa a lokacin da dakarun Amurka suka kai masa hari a arewa maso yammacin Syria. Kakakin ya ce sabon shugaban shi ne Abu al-Hussein al-Husseini al-Qurayshi amma ba a bayyana kasar da ya fito ba. Sai dai ya bayyana Abu al-Hussein a matsayin gogaggen dan jihadi sa'annan ya bukaci 'yan kungiyar su yi masa mubaya'a. A wani sako a shafin Telegram ƙungiyar al-Qaeda ta ce an dade da kashe shugaban na IS. Ana tunanin cewa kungiyar IS na da mayaka tsakanin 6,000 zuwa 10,000 a kasashen Iraƙi da Syria. Majalisar Ɗinkin duniya ta ce ƙungiyar na da mabiya sosai a ƙasashen Afghanistan da Somalia da kuma tafkin Chadi." https://www.bbc.com/hausa/articles/cmlkv2yljj2o +entertainment ...Daga Bakin Mai Ita tare da Sani Mai Iska Danna hoton da ke sama domin kallon bidiyon: Daga Bakin Mai Ita wani shiri ne na BBC Hausa da ke kawo muku hira da fitattun mutane kan wasu abubuwan da suka shafi rayuwarsu zalla. A wannan kashi na 94, BBC ta tattauna da Sani Mai Iska, wani fitaccen ɗan wasan fim, inda ya amsa tambayoyin da suka shafi rayuwarsa. https://www.bbc.com/hausa/media-61100928 +politics Badaƙalar NDDC: Akpabio ya yi amai ya lashe kan bayyana 'yan majalisar da aka bai wa kwangila "Ministan ma'aikatar da ke kula da yankin Niger-Delta Godswill Akpabio ya tura wa majalisar wakilan Najeriya wasika bayan da ta ba shi wa'adin kwana biyu domin ya wallafa sunayen 'yan majalisar da ya yi zargin cewa suna cin fiye da kashi 60 cikin 100 na kwantaragin da hukumar raya yakin Niger-Delta take bayarwa. Jinkirin da aka samu gabanin isar wasikar ya sa kakakin majalisar ya umurci Akawun majalisar da ya bi matakan da suka dace don gurfanar da ministan a gaban kuliya, bisa tuhumarsa da yin karya da bata sunan 'yan majalisar. Hon Kabiru Rurum, dan kwamitin majalisar ne da ke gudanar da bincike a kan zargin badakalar kudi a hukumar NDDCn, kuma yana zauren majalisar lokacin da kakakin ya karanta wasikar wadda ya ce tana cike da waskiya. Wani dan jinkiri da aka samu gabannin isar wasikar ta sa kakakin majalisar Femi Gbajabiamila ya umarci Akawun majalisar da ya fara tattara lauyoyin majalisar domin su bi duk matakan da suka dace wajen gurfanar da ministan a gaban shari'a domin tuhumarsa da shirga karya, tare da shafa wa 'yan majalisa kashin-kaji. Ya yi zargin cewa ministan da wasu jami'an gwamnati sukan yi irin wadannan karairayin ne da nufin dauke hankalin jama'a daga gaskiyar lamari, tare da shiriritar da binciken da ake yi. Don haka yace majalisar ba za ta raga wa mai yin irin wannan ba, komai girman mukaminsa a ciki da wajen gwamnati. Sai dai abin tambaya shi ne ko mene ne takamaiman matsayin majalisar yanzu? Hon Rurum ya ce: ''A yanzu dai an karanta bayani kuma an samu bayanai biyu, na farko an umarci lauyoyin majalisa su gurfanar da shi a kotu kafin zuwan takardarsa. ""Na biyu kuma shugaban majalisa bayan ya gama karanta wasika ya mika wa kwamitin da'a don su sake nazarin takardar don su ba da shawara kan irin matakin da ya kamata a dauka a kansa.'' Wannan binciken hukumar NDDC da 'yan majalisar wakilai ke yi dai babban al'amari ne sakamakon yadda zai shafi makomar martabar 'yan majalisar…idan suka yi shiru ko suka bari ya shiririce, to zargin da ake musu zai tabbata kenan. Idan kuma suka ci gaba da kwakwa ba a san abin da gaba za ta haifa ba. Tun da fari dai 'yan Najeriya sun zuba ido don ganin ko me zai biyo baya yayin da wa'adin da majalisar dokokin kasar ta bai wa ministan ma'aikatar raya yankin Neja Delta kan fallasa 'yan majalisar da yake zargi da cin gajiyar kaso mai tsoka na kwangilolin da hukumar NDDC ke bayarwa ke cika ranar Alhamis din. Majalisar dai na gudanar da binciken almubazzaranci na fiye da naira biliyan 81, sama da dala 210,000 a hukumar. An kafa hukumar ta raya yankin Neja Delta shekara 20 baya domin inganta rayuwar al'ummar yankin da ke da arzikin mai. A ranar Litinin ne kuma bayan Shugaban hukumar ta NDDC, Daniel Pondei ya sha tambayoyi daga kwamitin majalisar aka ga ya kife kai kamar ya suma. Daga nan aka garzaya da shi asibiti domin samun kulawa. Ministan ma'aikatar raya Neja Delta yayin da ya bayyana gaban kwamitin a ranar Litinin, ya yi ikirari cewa ""'yan majalisar sune suka fi cin gajiyar kwangilolin da hukumar ta bayar. Da aka tambaye shi ta yaya, ministan sai ya ce, ""Yanzu na gama faɗin cewa muna da takardu da ke nuna cewa 'yan majalisar dokoki ake ba wa akasarin kwangilolin na hukumar NDDC"". Sai dai wannan iƙirarin ya fusata Kakakin majalisar wakilan, Mista Gbajabiamila inda ya ba da wa'adin sa'oi 48 ga ministan ya fitar da sunayen mutanen da suka ci gajiyar da kuma cikakken bayani kan kwangilolin da aka bai wa 'yan majalisar ko kuma su fuskanci fushin doka domin dai ganin ya amsa umarnin majalisar. To ko Akpabio zai bayyana sunayen 'yan majalisar? 'Yan Najeriya na dakon ƙarin bankaɗa daga binciken da ake gudanarwa idan har aka wallafa 'yan majalisar a jadawalin sunayen. Godswill Akpabio dai tsohon ɗan majalisa ne kafin karɓar mukamin minista a Agustan 2019. A baya-bayan nan ne kuma, tsohuwar shugabar hukumar NDDC Joy Nunieh ta zargi Akpabio da almundahana; ta shugabanci hukumar ne tsawon wata huɗu kacal kafin a kore ta. Ms Nunieh ta zargi Akpabio da hannu a tsige ta inda ta ce ya sha matsa mata lamba ta yi rantsuwa don binne almundahanar da aka tafka a hukumar. Ministan ya musanta zarge-zargen inda ya ce an sauke ta ne saboda ""rashin girmama na gaba a aiki"". A lokacin da mukaddashin shugaban hukumar ta NDDC, Mista Pondei da sauran jami'ai suka bayyana gaban majalisa, ya zargi shugaban kwamitin da ke bincikar hukumar ta NDDC, Olubunmi Tunji Ojo da cin hanci tare da ƙin amsa tambayoyin da kwamitin ya riƙa jefa masa. A lokuta da dama, ana zargin 'yan majalisa a Najeriya da aikata cin hanci ta hanyar karɓar kwangila daga ma'aikatu da hukumomin gwamnati da kuma yin cushe a kasafin kuɗi. Wani masanin shari'a ɗan Najeriya da ke zama a Burtaniya Barista Bulama Bukarti ya shaida wa BBC cewa ko da ministan ya gaza fitar da sunayen, majalisar dokokin abu ɗaya kawai za ta iya yi shi ne ""ba wa Shugaba Buhari shawarar sauke ministan daga kan muƙaminsa"". ""Shawara ce ba dole ba ne"". ""a baya, mun ga yadda majalisar dokokin Najeriya ta ba da shawarwari ga shugaban amma ba ɗaya daga ciki daya aiwatar"". ""Misali buƙatar 'yan majalisar ta sauya shugaban hukumar yaƙi da masu yiwa arzikin ƙasar ta'annati Ibrahim Magu bata samu shiga ba a wajen shugaban"". A cewar Barista Bulama Bukarti, idan zarge-zargen da aka yi wa 'yan majalisar ya zama gaske, ""'yan majalisar da suka karɓi kwangiloli daga hukumar sun yi abin da ya saɓwa dokokin Najeriya"". ""SIdan aka saɓa dokokin majalisa kuma majalisar na iya yanke shawarar dakatar da 'yan majalisar da aka samu da hannu tare da umartarsu sumayar da kuɗaɗen da suka karɓa"". ""Za a iya bayyana sunayensu ga jama'a kan abin da suka yi"". ""Kazalika, laifi ne a samu ɗan majalisa da hannu a wata badaƙala ƙarkashin sashe na 24 na 'dokar ɗa'ar ma'aikata' ta 'yan majalisar"". Wani tsohon Kakakin majalisar wakilai Ghali Umar Na'abba ya ce ""idan har akwai zarge-zarge kan mambobin majalisa, kamata ya yi kwamitin ɗa'a ya yi bincike"". Idan har zarge-zargen gaskiya ne, sai a miƙa waɗanda suka yi laifin hannun hukumomin da abin ya shafa domin su fuskanci tuhuma"" Duk da rashin jituwar da aka samu tsakanin jami'an hukumar NDDC da majalisar dokokin Najeriya, Shugaba Buhari ya gargaɗi ministocinsa da sauran shugabannin hukumomin gwamnati da kada su nuna 'rashin girmamawa' ko yi wa majalisar 'maƙarƙashiya'. Shugaban ya ɗan sa baki yayin wani taro da shugabannin majalisun ƙasar. Zuwa yanzu, za a ci gaba da bincike yayin da 'yan Najeriya ke dakon ganin yadda binciken badaƙalar kuɗin naira biliyan 81 a hukumar NDDC da aka ƙirƙireta domin magance matsalolin da al'ummar yankin Neja Delta mai arzikin mai ke fuskanta." https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-53507499 +religion Bidiyon Ku San Malamanku tare da Malam Adamu Girbo Muhammad "Latsa alamar lasifika da ke sama don kallon hira daMalam Girbo: An haifi Malam Adamu Girbo Muhammad a birnin Gombe da ke arewa maso gabashin Najeriya ranar 27 ga watan Disambar 1951. Ya yi karatun allo a birnin na Gombe a wurin malamai da dama da suka hada da Malam Usman da Malam Manu da Wazirin Ciroman Gombe da sauransu. Bayan ya kammala karatun Alkur'ani mai girma, Malam Girbo ya yi karatun litattafai a karkashin manyan Malamai irin su Sheikh Abubakar Mahmud Gumi da Sheikh Isma'ila Idris Zakariyya da Malam Balarabe. A shekarar 1968, malamin ya tafi Kaduna inda ya shiga sojan Najeriya domin fafatawa a Yakin Basasa. ""Da na shiga soja a garin Kaduna ina da sana'a a lokacin don na samu lasisi na tuka mota a 1967; da lasisin ya shekara daya na tafi Lagos inda a kan hanya ne na tsaya a Kaduna na shiga soja. Daga nan aka debe mu aka kai mu Enugu a jirgin kasa,"" in ji malamin. Ya kara da cewa da suka isa Enugu ne aka tambayi wadanda suka iya aikin kafinta ko tuki da wasu sana'o'i inda ya bayyana cewa shi direba ne, yana mai cewa daga nan ne aka dauke su aka koma da su Kaduna inda ya rika tuka tirela. Malam Girob ya ce yayin zamansa a Kaduna ne ya hadu da marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi da Sheikh Isma'ila Idris Zakariyya ""kuma su ne suka kwadaita mini karatu."" ""Kasancewa aikinmu yana zuwa ne lokaci zuwa lokaci, sai ya zamana ina da dama na yi rika karatu irin na zaure, shi ya sa na je a gaban Sheikh Abubakar Mahmud Gumi,"" a cewar malamin. Ya kara da cewa bayan babban malamin ya fahimci irin basirar ne ya samar masa gurbi a Kwalejin Koyar da Larabci da Addinin Musulunci da ke Katsina sannan ya sa aka mayar da shi fannin limamai daga bangaren direbobi. Malamin ya ce ya kammala karatunsa na shekara hudu ne a daidai lokacin da ake shirin kafa kungiyar Izala, kuma yana daya daga cikin wadanda suka kafa ta." https://www.bbc.com/hausa/media-60783243 +health Ana Maulud a Saudiyya? Me ke jawo shanyewar ɓarin jiki? Shrin Amsoshin Takardunku na wannan makon ya amsa tambyaa biyu ka ko ana yin bikin Maulud a Saudiyya da kuma abin da ke jawo shanyewar ɓarin jiki?. Nabeela Mukhtar Uba ce ta gabatar da shirin. https://www.bbc.com/hausa/articles/c0drvmnz7r2o +politics Shin ana zaman doya da manja ne tsakanin Buhari da ‘yan majalisar dokoki? "Matakin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya dauka ranar Talata na gwale 'yan majalisar dattawan kasar bayan sun yi kira a gare shi ya sauke hafsoshin tsaron kasar ya sa masu nazari na tambaya kan ko dai ana yakin sunkuru ne tsakanin shugaban da 'yan majalisar. A makon jiya ma, shugaban ya umarci minista a ma'aikatar kwadago ya ci gaba da shirinsa na daukar mutum 770, 000 aiki duk da dakatarwar da 'yan majalisar suka yi wa shirin. Wasu dai na ganin watakila wannan wata alama ce ta sabanin da ke kunno kai ganin a mulkin shugaban na farko an yi ta samun irin hakan tsakanin sa da majalisa ta takwas. Ko da yake manazarta harkokin siyasa na gani hakan ba abin mamaki ba ne ganin cewa zubin majalisar ba wai ta wani sauya da yawa ba ne, sannan kusan abin da suka tarar suka dora nasu a kai. Malam Kabiru Sa'idu Sufi wanda ke Nazari kan harkokin Siyasa a Najeriya ya ce, sabanin tsakanin bangaren zartarwar da ta majalisa a mulkin dimokradiya, musamman a tsarin shugaban kasa mai wuka da nama ba bakon abu ne. Ya ce idan aka yi waiwaye an sha samun irin haka a majalisun da suka gabata tun daga majalisa ta 4 har zuwa ta 8, sai dai kawai a wannan karon ba a taba tunanin za a soma samun irin wannan ba tun a yanzu. Malam Sufi ya ce akwai dalilai da dama da suka sa ake wannan tunanin, duba da cewa an shekara ana zaman lafiya tsakanin bangarorin biyu sai ake ganin kamar zai dore a haka. Fadar gwamnatin Najeriya dai ta taka muhimmiyar rawa wajen nada shugabannin majalisun kasar biyu wanda hakan ne ya sa ake ganin za a iya samun jituwa kuma ba lallai a samu takun-saka kamar abin da ya faru a zamanin majalisa ta takwas ba. Amma kuma a halin yanzu gashi ana kai ruwa rana, kuma dalilin da ya sa aka yi tunanin ba za a zo wannan gabar ba shine ganin yadda sabon kunshin majalisa ta 9 tazo daidai da bangaren zartarwa. Sannan shi kansa bangaren zartarwa ya taka muhimmiyar rawa waje kafa wannan shugabanci, in ji Malam Sufi. ""Sai dai kuma ba abin mamaki ba ne duba da cewa akwai dalilai da dama da ke kunshi a tsarin shugaba mai wuka da nama, ya tanadar da cewa kowane bangare na cin gashin kansa kowanne na da huruminsa da damamankin sa kuma kowanne na da damar takawa dayan sa burki."" Masanin ya ce, a yanzu akwai wasu dalilai da suka shafi ita kanta wanann majalisar ta 9, domin a wannan hali da ake ciki yanayin tsaro na kasa da matsin lamba da ake fuskanta shi ya sanya aka ja layi tsakanin bangarorin biyu. Ana iya cewa kusan dabi'a ce ta wannan dimokradiya, saboda tun lokacin da aka kafa wannan zangon a 1999 ake samun rashin jituwa ko tsakanin 'yan jam'iyya guda ko kuma ita kan ta tsarin shugabanci, Malam Sufi yace kafin wannan lokaci, a baya ana yi tunanin da wuya sabanin ta kai wanda ake gani a sauran majalisun da suka gabata. ""Na fadi hakan ne saboda rawar da bangaren zartarwa ya taka wajen nade-naden shugabannin majalisun kasar biyu.'' Amma waccan tunanin ta rushe domin kuwa a yanzu wannan yanayi da yake kunon-kai da wuya an tsallake maimaita abin da muka gani a zamanin majalisa ta 8. ""Idan kuma hakan ya tabbata to kusan muna iya cewa ba ta sauya zani ba."" Malam Sufi ya ce a yanzu zai yi wuri a yanke hukunci kan makomar rikicin da ke neman kuno kai, amma dai ya danganta da yadda bangarorin biyu suka rike al'amari ko suka bi da batun har a kai karshen sa. Ba a raina rigimar siyasa, kuma a yanzu ya yi wuri a iya danganta rikicin da matsayin barazan, inji Sufi. ""Amma akwai gudun kar ya zabi gibi ko sanadi da ka iya illa ga jam'iyyar APC ko bude kofa ga 'yan hamayya.'' Sharhi, Umaymah Sani Abdulmumin Yanzu dai an wuce shekara daya a zango wannan Mulki na shekara hudu. Shiyasa masana ke ganin akwai bukatar yin takatsantsan saboda daga irin wadanan kananan rashin jituwa ake fadawa a rikici. Sannan jam'iyyun hamayya na amfani da irin wannan dama wajen inganta kawunansu. Kafin wannan lokaci a makon da ya gabata wasu 'yan majalisar sun nuna damuwa kan tafiyar hawaniyar wasu ayyukan gwamnatin Buhari. A shekarun mulkinsa na farko Shugaba Buhari ya yi ta samun matsala da bangaren majalisa musamman kan nade-naden wasu mukamai da tsare-tsaren da ya rinka bijirowa da su, inda kowane bangare ya rinka gwada karfin ikonsa da doka ta tanadar. Wannan na daga cikin dalilan da suka haddasa rigingimu da kuma baraka a jam'iyyar APC da kuma balewar da wasu 'ya'yan jam'iyyar suka rinka yi. Yanzu dai 'yan Najeriya sun zura ido don ganin yadda zata kaya da kuma rikicin da ake hasashen ka iya sake zama cikas wajen cimma muradai ko ayyukan da gwamnati ta sanya gaba." https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-53501718 +business Shinkafa na cikin kayayyakin da Najeriya ta haramta shiga da su ta kan iyaka "Gwamnatin Najeriya ta ce duk da buɗe iyakokinta na tudu da ta yi, har yanzu ba a ɗage dokar da ta haramta shigo da wasu kayayyaki ba da suka haɗa har da shinkafa da motoci a ƙasar. A ranar Alhamis ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar da umurnin buɗe wasu iyakokin ƙasar hudu, wadanda suka shafe fiye da shekara ɗaya a rufe. Iyakokin da gwamnati ta buɗe sun hada da ta Seme da Mfun da Ileleh da kuma Maigatari. Matakin buɗe kan iyakokin ya faranta ran ƴan Najeriya musamman da fatan cewa harka za ta buɗe, da kuma samun sa'ida daga tsadar rayuwar da ake fama da ita, musaman ma yadda farashin kayan masarufi ke hauhawa. Sai dai Mista Joseph Attah kakakin hukumar kwastam ta Najeriya ya shaida wa BBC cewa dokar hana shigo da wasu kayayyaki da suka ƙunshi har da na abinci tana nan ba ta kau ba. Hukumar kwastam ta Najeriya a shafinta na intanet ta zayyana kayayyakin da gwamnatin Najeriya ba ta yadda a shigo da su ba. Akwai kuma wasu jerin abubuwa da dama da gwamnatin ta haramta shigo da su a ƙasar kamar yadda hukumar kwastam ta bayyana a shafinta na intanet. Mista Attah ya ce buɗe boda da aka yi ba wai an ce kowa ya kawo duk abin da yake so ba ne. Ya ce yanzu wannan matakin da buɗe wasu daga cikin iyakokin zai ba ƙasashen da ke makwabta da Najeriya damar yin harakokinsu na boda yadda doka ta ce. ""Dole su tabbatar da duk abin da ba mu so ka da ya shigo gidanmu kamar yadda ba za su mu bari wani abin da ba su so ya shiga gidansu,"" in ji shi. Tun a watan Agustan bara gwamnatin Najeriya ta rufe iyakokinta da ke kan tudu, da nufin inganta tsaro da bunƙasa masana'antun cikin gida. Amma wasu na ganin cewa kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba. Wasu ƴan Najeriyar na da ra'ayin cewa babu wata ribar a zo a gani da aka samu daga rufe iyakokin ƙasar da gwamnati ta yi, suna kafa hujja da cewa farashin kayan abinci bai faɗi ba, kuma matsalar tsaro sai ƙara ta'azzara take. Ko da yake hukumar kwastan a nata bangaren ta ce an samu nasara ta bangaren diflomasiyya da kasashe makwabta, saboda rashin fahimtar da aka yi fama da ita a baya, yanzu ta kau." https://www.bbc.com/hausa/labarai-55352437 +politics Buhari ya yi sabbin nade-nade, me ya sa Abba gida-gida murna? "A wannan makon a Najeriya, an ga abubuwa daban-daban da suka faru amma a fagen siyasa dai za a iya cewa kalmomin da aka fi ji ba za su wuce majalisa da kotu da nadin mukami ba. Jihohin Bauchi da Kano da shugabancin kamfani mai muhimmanci a kasar sun mamaye duk wasu zantukan siyasa, a shafukan sada zumunta da ma hirar fatar baka. 1. Kotin koli ta tabbatar da takarar Abba gida-gida Ranar Talata 18 ga wannan watan na Yuni ne kotun kolin Najeriya ta tabbatar da Abba Kabir Yusuf a matsayin sahihin dan takarar gwamna a jam'iyyar adawa ta PDP a jihar Kano. A baya dai, Ibrahim Al-Amin (Little) ya kalubalanci hallaccin takarar Abba K Yusuf kuma ya maka jam'iyyar PDP a kotu inda ya ce jam'iyyar ba ta yi zaben fitar da gwani ba. Ya yi nasara a wata kotu a Kano, amma Kotun Daukaka Kara a Kaduna ta yi watsi da bukatarsa, hukuncin da alkalan Kotun Kolin suka tabbatar. Abba ya nuna murnarsa inda ya shaida wa BBC cewa ""nasarar da ya samu daga Allah ne"". 2. Buhari ya yi sabbin nade-nade An wayi gari ranar Alhamis, 20 ga watan Yuni da labarin nada sabon shugaban kamfanin mai na NNPC a Najeriya. Shugaba Muhammadu Buhari ya sanar da nada Mele Kolo Kyari, a matsayin shugaban kamfanin na 19 kuma magajin Maikanti Baru, wanda zai bar aiki a watan gobe. Kafin dora shi a mukamin, Mele Kyari shi ne shugaban bangaren harkokin danyen mai na kamfanin, kuma wakilin Najeriya a kungiyar kasashe masu arzikin man fetur wato OPEC. Nada Mele Kyari shugaban NNPC dai shi ne nadi na biyu da Shugaba Buhari yayi tun bayan sake hawansa mulki a karo na biyu. Mukami na farko da ya bayar shi ne sake dora Akanta-janar na kasar Ahmed Idris. 3. Shugaban Majalisar dattawa ya 'fusata' 'yan APC Shugaban majalisar dattawa a Najeriya, Sanata Ahmad Lawan ya fuskanci matsin lamba bayan da ya nada Festus Adedayo a matsayin mai bashi shawara na musamman kan yada labarai. Wasu masu fafutuka kuma magoya bayan gwamnatin Buhari sun yi korafi kan nadin Adedayo wanda suka ce ""ya yi kaurin-suna wurin sukar gwamnati da Shugaba Buhari"". Hatta Uwargidan shugaban, Hajiya Aisha Buhari ta yi shagube a shafinta na Twitter inda ta dora wani hoton bidiyo da ke nuna daya daga cikin masu fafutukar siyasa a kasar kuma ma'abocin shafin na Twitter yana korafi kan bai wa Festus Adedayo matsayin. Kwanki biyu bayan sanar da nadin, Sanata Lawan ya sanar da cire Festus daga mukamin. Takaddama ta barke ranar da aka bude sabuwar majalisar dokokin jihar Bauchi, inda bangarorin da ke hamayya da juna suka zabi shugabanni daban-daban. 'Yan majalisa 11 na bangaren Gwamna Bala Mohammed na jam'iyyar PDP sun zabi Alhaji Abubakar Y. Suleiman, wanda dan jam'iyyar hamayya ne ta APC. To amma fa ba shi jam'iyyar ke so a matsayin kakakin majalisar ba. Su kuwa wasu 'yan majalisar 20 da ke goyon bayan tsohon gwamna Muhammad Abubakar, sai suka zabi Kawuwa Shehu Damina a matsayin na su kakakin. Jam'iyyar adawa ta APC ce ke da rinjaye a majalisar don haka akwai yiwuwar cewa za a ci gaba da samun rikici game da ayyukan majlisar, da ma tsakanin majalisar da bangaren zartarwa. 5. Haka batun yake a jihar Edo Makamancin wannan ne ya faru a jihar Edo inda 'yan majalisa tara daga cikin 24 da ke goyon bayan Gwamna Godwin Obaseki suka zabi Frank Okiye a matsayin kakakin majalisar jihar. Sai dai 'yan majalisa 15 da ke biyayya ga shugaban APC na kasa Adams Oshimhole, wanda ke takun-saka da gwamnan, sun yi Allah-wadai da matakin suna masu cewa ba a basu dama sun shiga zauren ba. Jam'iyyar APC ta kasa dai ta fitar da sanarwa tana yin Allah-wadai da dukkan abubuwan da suka faru a jihohin na Bauchi da Edo." https://www.bbc.com/hausa/labarai-48720679 +sports Newcastle na son daukar Neymar a karshen kakar bana An ruwaito cewar Newcastle United na duba hanyar da za ta dauko Neymar daga Paris St Germain a karshen kakar bana. Newcastle wadda aka sayar da ita, ta saka kudi mai tsoka wajen sayo 'yan wasan da za su kara karfin kungiyar, ciki har da dan kwallon Brazil, Neymar da take son dauka a karshen kakar nan. Kamar yadda The Sun ta wallafa, Newcastle na bibiyar halin da Neymar ke ciki a PSG, tana kuma son yi masa tayin kudi mai tsoka, domin ya koma buga gasar Premier League. Bayan da aka yi waje da PSG daga Champions League a bana a hannun Real Madrid, magoya bayan kungiyar Faransa kan yi wa wasu 'yan wasan ihu a lokacin da suke buga mata leda, ciki har da Neymar. Tun farko Neymar bai samu alaka mai kyau da PSG da kuma magoya bayanta ba, duk da kwazon da yake yi wa kungiyar, hakan ne Newcastle taga ya dace ta yi wa dan wasan Brazil tayin kudi mai tsoka, watakila ya samu buga babbar gasar tamaula ta Ingila cikin natsuwa. Neymar yana da kunshin yarjejeniya da PSG wadda za ta kare a karshen kakar 2025, ana kuma ganin Newcastle za ta iya biyan albashin dan wasan na Yuro 500,000 duk mako idan ya amince ya koma kungiyar da taka leda. https://www.bbc.com/hausa/wasanni-60815164 +sports Thomas Tuchel ya caccaki raflin da ya busa wasa da Real Madrid Thomas Tuchel ya caccaki alkalin wasa kan murmushi da dariya da yayi da kocin Real Madrid, Carlo Ancelotti, bayan da aka fitar da Chelsea daga Champions League. Tuchel ya ce ya ji takaici da Szymon Marciniak ya kasance cikin nishadi da Carlo, bayan da ya hura tashi daga wasan. Bayan da Chelsea ta yi rashin nasara da ci 3-1 a wasan farko a Stamford Bridge, ta kuma sa kwaza a wasa na biyu da suka kai har da karin lokaci, inda Real ta kai zagayen gaba da ci 5-4. ''Ina jin wannan mummunan lokaci ne bai kamata hakan ta faru ba,'' in ji Tuchel. ''Bayan da muka yi minti 126, muka sa kaimi da kwazo, muka yi ta sa kuzari har karshen wasan. ''Na san Carlo babban mutun ne kuma mutumin kirki ne, amma da na je gaisawa da alkalin wasa, sai naga yana murmushi da dariya tare da abokin hamayya. ''Ina ganin hakan bai da ce ba Da wannan rashin nasara da kungiyar Stamford Bridge ta yi, an fitar da Chelsea mai rike da Champions League. Haka kuma Tuchel bai ji dadi ba da alkalin wasa bai je ya duba VAR ba, lokacin da aka soke kwallon da Marco Alonso ya ci, cewar ya taba da hannu a zagaye na biyu. ''Idan kana wasa da Real Madrid za ka fara tunanin ba ka da kwarin gwiwa. Ina jin wasu hukunce-hukunce an yi mana rashin adalci a wasan farko da wanda muka yi a Sifaniya, in ji Tuchel. ''Banga lokacin da kwallon ya shiga ragar ba, amma bai je ya tantance ba a VAR. ''Kowanne rafli yana da salon alkalancinsa, yana da abin da zai dauke kai da wanda ba zai yi ba, saboda haka dole ya zama jagora, domin shi ne zai dauki alhakin dukkan abin da ya faru. Tuchel ya ce ''Ban yi nadama'' ba duk da an fitar damu daga Champions League, domin mun yi dukkan abinda ya da ce. https://www.bbc.com/hausa/wasanni-61084870 +entertainment ...Daga Bakin Mai Ita tare da Tijjani Asase Latsa hoton sama domin kallon bidiyon Daga Bakin Mai Ita wani shiri ne na BBC Hausa da ke kawo muku hira da fitattun mutane kan wasu abubuwan da suka shafi rayuwarsu zalla. A wannan kashi na 63, shirin ya tattauna da Tijjani Asase, fitaccen tauraro a Kannywood. A wannan shiri ya amsa tambayoyin da suka shafi rayuwarsa da rawar da yake takawa a fina-finai. Ɗaukar bidiyo: Abdussalam Usman Tace bidiyo: Umar Rayyan https://www.bbc.com/hausa/58335121 +business An gurfanar da manoman shinkafa gaban kotu a Najeriya Ana ci gaba da takaddama kan wani shiri na bai wa manoma bashi don bunkasa noman shinkafa a Najeriya. Kungiyar manoma shinkafa ta kasar RIFAN, ta yi ikirarin cewa an gurfanar da 'ya'yanta 70,000 a gaban kotun majistare saboda sun ci bashin kudin noman shinkafa kuma ba su biya ba. To sai dai wasu 'yan adawa a kasar na cewa tun farko ba manoma aka bai wa kudin ba, wasu 'yan koran siyasa aka ba wa shi yasa mutane suka ki biya. Kungiyar manoman shinkafar a jihar Kebbi ta ce an gurfarnar da dubban manoman shinkafar ne a gaban kotuna bayan sun karbi bashin kudi daga shirin Babban Bankin Nijeriya na bunkasa noma wato Anchor Borrowers wanda aka fara a shekara 2015. Shugaban kungiyar shinkafa na jihar Kebbi Alhaji Muhammadu Sahabi, ya ce hukumomi sun dauki matakin gurfanar da 'ya'yan kungiyarsa ta RIFAN ne saboda sun kin biyan basukan da suka ci. Tun da farko, jam'iyyar PRP mai adawa a jihar Kebbi ce ta nemi jin bahasin inda aka kwana game da kudin da gwamnatin tarayya ta ware naira biliyan 17 na bunkasa noman shinkafa. Jam'iyyar ta ce babu wani abun a zo a gani duk da makudan kudin da aka ware. Ana dai fargabar cewa irin wannan shiri da hukumomi a kasar suka bullo da shi don bunkasa noma a cikin gida da wadata kasar da abinci, ka iya rushewa matukar wadanda ake bai wa irin wannan rance, suka ci gaba da yin halin kaza da Hausawa ke cewa kin ci kin goge baki. https://www.bbc.com/hausa/labarai-51375366 +politics Sau biyar ina yunkurin sasantawa da Wike - Atiku "Dan takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce sau biyar yana yunkurin yin sulhu kan rikicin jam’iyarsu da gwamnan jihar Ribas Nyesom amma hakan ya ci tura. Atiku Abubakar ya ce yanzu yana jiran bangaren su Wike ne don ganin sun kawo karshen rikicin da jam’iyyar tasu ke fama da shi. Atiku Abubakar ya bayyana hakan ne a yayin taron tattaunawa da 'yan takarar shugabancin Najeriya da gidan talabijin din Channels, ya gabatar a ranar Lahadin karshen makon da ya gabata. Atiku Abubakar ya ce ""na same shi a Abuja sau biyu, na kuma same shi a Patakwal sau biyu, sannan kuma a Landan sau daya."" Sai dai Atiku bai yi wani karin bayani ba dangane batutuwan da suka tattauna da Wike a ganawar da ya ce sun yi ba. Ya ce yana zargin kansa kan yadda suka gaza shawo kan rikicin. Sannan ya ce matsalar daga bangaren Wike take ba daga gare shi ba. Takaddamar da jam’iyyar PDP ke fama da ita, ta soma asali ne tun bayan da Atiku abubakar ya zaɓi Ifeanyi Okowa , a matsayin mataimakinsa, bayan zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar ta PDPda ake gudanar a ranar Asabar 28 ga watan Mayun 2022. Duk da yunƙurin da jagororin jam'iyyar suka yi na rarrashin Wike, har yanzu gwamnan bai nuna alamun ajiye kayan yaƙinsa ba, inda shi da sauran gwamnonin jam'iyyar hudu suka matsa lamba sai shugaban jam’iyyar ta PDP Iyorchia Ayu ya sauka daga kan mukaminsa." https://www.bbc.com/hausa/articles/c4ne4ywyzk7o +sports Watakila Richarlison ba zai je Gasar Kofin Duniya ba Watakila Richarlison ba zai je gasar kofin duniya da za a buga a Qatar ba a bana, sakamakon raunin da ya ji a Premier League ranar Asabar. Hakan ya sa Richarlison ba zai buga wa Tottenham wasan Premier League ba da za ta ziyarci Manchester United ranar Laraba. An sauya dan wasan tawagar Brazil a zagaye na biyu a karawar da Tottenham ta ci Everton 2-0 ranar Asabar, saboda haka ba zai yi wasan da za a yi a Old Trafford ba. Richarlison mai shekara 29, har yanzu bai ci kwallo ba a Premier League tun bayan da ya koma Tottenham a bana daga Everton. Ana sa ran auna girman raunin da ya ji, wanda Antoine Conte ke fatan ba mai girma bane. Dejan Kulusevski bai buga wasan da Tottenham ta doke Everton ba a gida, sai dai Lucas Moura ya yi wasa na farko Premier League tun bayan Agusta da ya ji rauni da ya fara jinya. https://www.bbc.com/hausa/articles/cx0yyn77v8qo +religion Kotu ta soke auren Musulunci saboda saba dokar kasa Kotu ta warware auren Musuluncin bayan ta soke hukuncin kotun da ta tabbatar da halascin auren a Birtaniya. An daura auren Mohammed da Nasreen masu 'ya'ya hudu yanzu ne a birnin Landan a shekarar 1998 a gaban wani limami da shaidu 150. Yanzu shekara biyu ke nan Nasreen na neman rabuwa da Mohammed din a gaban kotu amma ya dage cewa da ma can babu aure a tsakaninsu tunda ba bisa dokar kasar aka yi ba. Hakan ya biyo bayan wata takaddama da ta sa Nasreen mijin nata ba sa zama tare da juna tun shekarar 2016. Da farko wata kotu ta yanke hukunci cewa auren Musuluncin da aka daura musu halastacce ne domin ya dace da dokokin aure na Birtaniya. Amma kotun daukaka kara ta soke hukuncin na 2018, tare da ayyana auren Musuluncin wa Nasreen da Mohammed a matsayin haramtacce wanda ya saba doka. Alkalan kotun sun ce shirin ma'auratan na sake yin biki bisa tanadin dokar kasar ya tabbatar da cewa ma'auratan sun yarda auren Musuluncin da aka daura musu ba karbabbe ba ne. Antoni janar din kasar ya yanke hukuncin ne a kan shari'ar Nasreen Akhter da mijinta Mohammed Shabaz Khan, 'ya'ya hudu. Bayan daurin auren Mohammed da Nasreen, amaryar ta sha nuna damuwa da neman a gudanar da shagalin bikin kamar yadda dokar kasar ta tanada. A shekarar 2016 suka rabu da juna, kuma Mohammed ya yi kokarin matar na neman saki na tsawon shekara biyu, bisa hujjar cewa ba su taba yin aure da juna ba, a idon doka. Amma matar ta ce aurensu na Musulunci halastacce ne, kuma tana da hakkin ta bukaci rabuwa da Mohammed kamar yadda dokar kasar ta yi tanadi ga halastattun ma'aurata. https://www.bbc.com/hausa/51514422 +entertainment A matse nake in yi aure – Saima Mohammed "Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon: Ga duk wanda ya san harkar fina-finai ta Kannywood da dadewa, to ya san Saima Mohammed, fitacciyar 'yar wasan fim, amma a shekarun baya-bayan nan tauraruwar ta bace bat. A wannan hira ta musamman da BBC Hausa, Saima, wacce 'yar asalin kasar Nijar ce, ta yi magana kan yunkurin da take yi na dawowa Kannywood, da dalilin da ya sa ta daina fitowa a dim da kuma dalilin da ya sa aurenta ya mutu. Cikin dalilan da Saima ta fada na barin ta Kannywood har da cewa ta lura harkar fina-finan ba ta samun irin ci gaban da ya kamata duk da dadewar da aka yi, don haka ne ta janye jiki har sai abubuwa sun gyaru. Jarumar ta kuma ce yanzu babban burinta a duniya shi ne ta yi aure, ""a matse nake sosai da son yin aure. Ina fatan Allah ya kawo min miji."" Bidiyo: Fatima Othman" https://www.bbc.com/hausa/labarai-50398149 +entertainment Na zama abar tausayi – Rahama Sadau "Fitacciyar jaruma Kannywood Rahama Sadau ta ce ta zama abar tausayi kan hotunan da ta saka da suka janyo cin mutuncin addininta. Jarumar wadda tun a farko ta ce ta yi nadamar wallafa hotunan, ta shaida wa BBC cewa ta ji zafin yadda 'yan Kannywood suke maganganu kan lamarin, wanda ta ce ya faru ba tare da san ranta ba. A ranar Litinin ne sunan Rahama Sadau ya fara waɗari a Twitter, inda aka ambaci sunan sau fiye da 10,000, bayan hotunan da ta tauraruwar ta saka suka ja hankalin masu bibiyarta da kuma masu amfani da Twitter musamman daga arewaci da kudancin Najeriya. Hotunan jarumar sun haifar da mahawara tsakanin masu amfani da kafofin sadarwa, lamarin da har ya kai ga yin kalaman ɓatanci Annabi Muhammadu SAW. Jarumar ta bayyana cikin wani bidiyo da ta wallafa a shafinta na Instagram sanye da hijabi, cikin kuka da murya mai rawa, tana neman a yafe mata. A hirarta da BBC kuma ta ce duk wani mai hankali idan ya zauna ya kalli abin da ya faru zai gane cewa ta zama abin abin tausayi. ""Wani ya kamata ya yi tunanin shin ya Rahama take ji a matsayinta na musalma,"" in ji ta. Ta ce da dare ta saka hotunan ta tafi ta yi bacci, ba tare da ta tsaya diba me ake cewa ba game da hotunan da ta wallafa. ""Sai da safe ina tashi na ga tsokaci dubu 10, ban san me ke faruwa ba. A haka wani ya turo min da sako na ɓatancin da aka yi. Ina ganin wannan na san cewa saka hoto ya koma wani abu"" Game da martani daga abokan sana'arta 'yan Kannywood, Rahama ta ce su ya kamata su fara ankarar da ita. ""Amma kila waɗanda suke maganar sun riga ni gani amma ba za su iya kira na ba, gara su bari a yi ta magana akai"" Jarumar ta ce idan da tsokacin mutane ne kawai ba za ta damu ba. Amma ta ce yin ɓatanci ga Annabi SAW ya girgiza ta kuma shi ya sa ta ga ya dace ta fito ta bayar da hakuri saboda haushin da ta ji na cin mutunci addininta da aka yi. ""Duk wani musulmi dole ya ji haushi - shi ya sa na fito na ba jama'a hakuri kuma na nisanta kai na da kalaman da aka yi."" Jarumar ta ce wannan dalilin ne ya sa ta je ta ciro hoton gaba ɗaya. A cewarta idan da maganganun mutane ne kawai da suke yi game da hotunan ba za ta damu ba." https://www.bbc.com/hausa/labarai-54837154 +religion Bidiyon Ku San Malamanku tare da Shiekh Abduljabbar Nasiru Kabara Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon: Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan da yake jihar Kano a arewacin Najeriya, kuma shugaban Ƙadiriyya Riyadul Jannah, Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya ce babban abin da ya sa a gaba yanzu a rayuwarsa shi ne nazari kan Hadisan Manzon Allah SAW. Malamin ya fadi hakan ne a wata hira ta musamman da BBC Hausa ke yi a wani shirinta na Ku San Malamanku. Wannan bidiyon Ku San Malamanku tare da Shiekh Abduljabbar Nasiru Kabara https://www.bbc.com/hausa/media-54834079 +politics Zaben 2023: Hadakar 'yan takarar shugaban kasa hudu na jam'iyyar PDP daga yankin arewa ta wargaje "Gwamnan jihar Sokoto da ke arewacin Najeriya Aminu Waziri Tambuwal ya ce sun kasa cimma matsaya kan ɗan takarar da za su mara wa baya a tsakanin wata haɗaka ta mutum hudu da suka kafa don daidaitawa wajen fitar da dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP. Gwamnan ya ce a yanzu babu batun maslaha ko kuma wani ya janye wa wani a tsakanin masu neman takarar. Gwamnan ya ce kafin wannan lokaci an yi tunanin tsakaninsa da Sanata Bukola Saraki da gwamnan Bauchi Bala Mohammad da Muhammad Hayatudeen da duk ke neman tikitin takara a inuwar PDP na iya maslaha a tsakaninsu. Sai dai lura da yadda abubuwa ke tafiya kowa kawai tashi ta fisshe shi. Gwamnan na wannan kalamai ne bayan wata sanarwar da ya fitar a yammacin jiya Juma'a tare da jaddada cewa a shirye yake a fafata da shi a zaben 2023. ""Mun zauna mu hudu 'yan takara wadanda a kashin kanmu muka yi matsayar cewa za mu tattauna mu yi sulhu a tsakaninmu, muka duba muka tattauna muka yi matsayar cewa abunda mu ke yi ga dukan alamu ya ci- tura. ""Saboda haka ya kamata mu ba kanmu shawara da kuma yin matsaya a kan cewa mu je kowa ya ci gaba da nema, duk abin da Allah ya yi sai mu karba,"" in ji Tambuwal. Gwamnan ya ce bayan da suka kasa daidaita kansu sai suka yanke shawara zuwa gidan tsohon shugaban kasa Ibrahim Babangida da ke Minna kuma a zaman farko da suka yi sai ya nemi su yi zabe. Tambuwal ya ce nan take ya fitar mu su da takardar kuri'a amma dukaninsu sun ki amincewa da haka saboda a ganin su wannan ba ita ce hanyar da za a sami maslaha ba. Ya ce a nan ne kuma suka yanke shawarar sake neman lokaci da za a yi shawara da shugabanni domin a ga yadda za a samu maslaha. Sai dai ya yi ikirarin cewa akwai wasu daga cikinsu da suke hanzari domin ganin kokarin da suke yi ya kawo karshe. ""Hadakarmu ta kawo karshe, wannan abin da aka yi a Minna bai kawo kaina ba, bai hau kan magoya bayana ba, don mun yi matsaya ranar Laraba cewa wannan abin ya ci tura kuma za mu ci gaba da takara"" . A kwanakin da suka gabata tsohon gwamnnan jihar Kwara Sanata Bukola Saraki da gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad da takwaran aikinsa na jihar Sokoto Aminu Waziri Tambawul da Muhammad Hayatudeen suka soma kokarin ganin cewa sun zabi mutum daya daga cikinsu da za su mara wa baya daga yankin arewa. Sai dai tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ba ya cikinsu. Kafin wannan barakar ta kunno kai bayanai sun ce 'yan takarar hudu sun so su fadada yunkurin nasu zuwa kasa baki daya a maimakon yankin arewa." https://www.bbc.com/hausa/labarai-61198911 +entertainment Wani fim kan matan India da suka shiga kungiyar 'ta'addanci' ta Islamic State ya jawo ce-ce-ku-ce "'Yan sanda a Jihar Kerala da ke kasar India suna neman shawarar lauyoyi game da wani korafi da aka shigar wurinsu game da wani fim da ya janyo ce-ce-ku-ce. A tallan fim din da aka fitar - mai suna The Kerala Story - wata tauraruwa ta yi ikirarin cewa wata kawarta na cikin mata 32,000 daga jihar da suka ""shiga"" kungiyar 'yan ta'adda da ke ikirarin kishin Musulunci. Wasu 'yan siyasa a jihar sun yi kira a haramta nuna fim din. Wani dan jarida ya aike da sako ga ministan shari'a inda ya nemi a gudanar da bincike. Ministan ya aike wa 'yan sanda bukatar dan jaridar Arvindakshan BR. ""An soma gudanar da bincike. Mun nemi shawarwarin masana shari'a a kan wannan takardar game da hukuncin da ya kamata mu yanke,"" a cewar Sparjan Kumar, kwamishinan 'yan sanda Thiruvananthapuram, babban birnin jihar Kerala. A cikin tallan fim din, wata mace sanye da hijabi ta ce a baya sunanta Shalini Unnikrishnan kuma ta so ta zama ma'aikaciyar jinya. ""Yanzu sunana Fatima Ba, mamba a kungiyar ta'addanci ta IS da aka kulle a Afghanistan,"" in ji ta, tana mai karawa da cewa akwai 'yan mata ""32,000 irin ta da suka zama 'yan kungiyar kuma an binne su a saharar Syria da Yemen bayan an kashe su"". ""Ana sanya 'yan matan da ba su ji ba ba su gani ba cikin kungiyar da ke da hatsarin gaske a Kerala,"" in ji ta. Kimanin mutum 440,000 ne suka kallo tallan fim din a YouTube a kwanaki shida da suka gabata kuma yayin da wasu suka yabe shi wasu sun soke shi. Adah Sharma, tauraruwar fim din, ta wallafa tallan fim din a Tuwita tare da maudu'in #TrueStory. Furodusan fim din, Vipul Shah, bai bayar da amsa kan sakon da BBC ta aika masa ba. Mr Arvindakshan, dan jaridar, ya shaida wa BBC cewa ya nemi a gudanar da bincike sannan ya bukaci mutanen da suka hada fim din su fitar da shaidu saboda ya fusata game da ikirarin da aka yi a tallan ba. ""Watakila wasu daga cikin abubuwan da aka fada sun faru amma idan aka ce 'yan matan sun kai 32,000 wannan babban lamari ne,'' a cewarsa. A wata tattaunawa da ya yi da Citti Media a 2021 - kamfanin da ke yada labarai - daraktan fim din ya ce ya samu adadin 'yan matan da suka shiga kungiyar IS ne daga bayanan da tsohon ministan Kerala Oommen Chandy ya gabatar wa majalisar dokokin jihar. Mr Sen ya yi ikirarin cewa Mr Chandy ya ce ""duk shekara 'yan mata tsakanin 2,800 zuwa 3,200 ne suke Musulunta"" don haka kenan 'yan mata 32,000 ne suka karbi shahada a shekaru 10. Sai dai wani bincike da  shafin intanet na Alt News da ke bincike don gano gaskiyar labari na India  ya ce ""babu wata shaida"" da ke gaskata ikirarin Mr Sen." https://www.bbc.com/hausa/articles/cnkjk9q29w9o +business Yadda za ku gane jabun sabon kudin Najeriya Kwanakin kadan da fara amfani da sabon kudin na N1000 da N500 da kuma N200, bayanai sun ce an fara samun jabun Naira dubu daya da ke yawo a tsakanin 'yan kasar. ‘Yan Najeriya sun fara yin tambayoyi kan ko an fara yin jabun wasu daga cikin sabbin kudin kasar. Wannan dai na zuwa ne bayan bullar wani faifan bidiyo a kafafen sada zumunta, inda wani mutum yake kokawa kan yadda wani ya bai wa matarsa da ke sana’ar POS jabun sabuwar naira dubu daya da babban bankin kasar ya kaddamar ranar 15 ga Disambar da muke ciki. A bidiyon mijin matar ya nuna jabun naira dubu dayan da ta gasken, ta yadda al’umma za su bambance su Sabon kudin dai na dauke da wasu lambobi na tsaro da za su saukaka maka gane jabun da mai kyau. Babban bankin Najeriya ya yi bayani a shafinsa na intanet game da yadda mutane za su gani sabon kudin na gaske da jabu, da ka gan su ko ka rike su a hannu. “Abubuwan da suka bambanta su su ne launinta da kuma yadda take idan ka rike ta a hannu, da irin tsaron da aka sanya mata da tambarin da ke jikinsu.” CBN ya ce kalar da aka kara wa kudin wani nauyi ne na tsaro da saukin gane na gaske da jabu. Kazalika zaren tsaro da ke jikin kudin, za ka ga kamar an rarrabe suke, amma ba a raba su ba, idan ka ga kudin a haske za ka ga akwai rubutun CBN da aka yi shi kanana a gaba da bayan kudin. Haka kuma babban bankin Najeriya ya ce rubutu da ke jikin kudin da lambobin da ke jiki an kara musu kauri. Sannan babban bankin ya ce sabon kudin na da wani tsaro ta yadda  ba za a iya kwafin sa ba. Dukkan wadannan alamu da babban bankin ya ambata, babu su a jabun sabuwar dubu daya, 500, da 200. A cewar babban bankin Najeriyar masu samar da jabun kudin ba su da masaniyar wadannan matakan tsaron da sabon kudin ke dauke da su. Babban bankin na Najeirya na dauko kudin da aka kammala buga su daga hukumar da ke kula da buga kudin kasar ta NSPM, don rarraba su ga ofisoshinsa da ke jihohi. Su kuma su bai wa sauran bankunan 'yan kasuwa, su kuma su bai wa al’umma, da suka je cirar kudi daga asusunsu da ke bankunan. A ranar 26 ga Octoban 2022, shugaban Najeriya Muhamamdu Buhari ya amince da sake fasalin kudin da buga su, da sakin sababbin naira N200, N500, da N1,000. Wannan sanarwa ta haifar da muhawara a tsakanin 'yan Najeirya, kan ko babban bankin Najeriya zai bi hanyoyi da suka kamata wajen sake fasalin kudin kasar. Hakan ya sa babban bankin na CBN fitar da wata sanarwa a ranar 29 ga Octoban 2022, cewar sun bi dokokin da suka kamata, wajen sauya tsarin kudin da shi kan aikin ya kama a ce an yi shi tun shekaru 12 da suka gabata. Gwamnan babban bankin Godwin Emefiele ya ce dalilin da ya sa suka sake fasalin kudin shi ne, saboda bukatar da gwamnatin tarayyar ke da shi na yaki da cin hanci da rashawa da jabun naira. Inda ya yi fatan wannan mataki na sake fasalin nairar zai taimaka wajen rage hauhawsar farashi, da taimakawa wajen waitar da manufofin kudi, da baiwa al’umma damar samun kudi cikin sauki, don kia kasar ga tsarin takaita amfani da madarar kudi don bunkasa tattalin arzikin kasar. A raanr 23 ga Nuwambar 2022 Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da sabon kudin ₦200, ₦500 da ₦1000 , bayan muhawarar kwan-gaba-kwan-baya da aka yi ta yi kan batun. Haka kuma a ranar 15 ga watan Disambar nan, babban bankin Najeriyar ya gabatar da kudin da aka sabunta, don shiga hannun al'ummar kasar. CBN ya sa ranar 31 ga Janairu, 2023 a matsayin ranar da tsofaffin kudi na N200, N500 da N1,000 za su daina aiki. Sai dai sauran irin su ₦5, ₦10, ₦20 and ₦50 za a a ci gaba da amfani da su har bayan 31 ga watan Janerun 2023. Hakan ya faru ne saboda yadda gwamnati ba ta canja kudin ba, da yake na leda ba. Kudaden Najeriya da suke na leda a Najeirya sun hada da ₦5, ₦10, ₦20, ₦50, wanda suke da da girman 130 X 72 mm. Yayin da manya kudaden da irin su ₦100, ₦200, ₦500 da ₦1000 da ake buga su a kan takarda, ke da girman 151 X 78 mm. https://www.bbc.com/hausa/articles/c2e9e9g1qemo +politics Abubakar Malami: Ministan Shari'a ya musanta cewa Atiku Abubakar ba ɗan Najeriya ba ne "Ministan Shari'a na Najeriya ya musanta wasu rahotanni da kafafen watsa labarai suka bayar cewa ya fada wa wata kotu cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasar Atiku Abubakar bai cancanci tsayawa takarar shugabancin ƙasar ba, don ba haifaffen Najeriya ba ne. Abubakar Malami ya ce shari'ar da ake magana a kai wata ƙungiya ce mai suna ""Incorporated Trustees of Egalitarian Mission for Africa"" (EMA) ce ta shigar da ita tun a shekara ta 2019 kuma shi ma yana cikin wadanda ake ƙara. Ministan ya yi martanin ne bayan ce-ce-ku-cen da ake ta yi sakamakon labarin da wasu jaridun Najeriya suka wallafa cewa Abubakar Malami ya ce Atiku Abubakar bai cancanci takarar shugabanci Najeriya ba saboda lokacin da aka haife shi garinsu na ƙarƙashin Jamhuriyar Kamaru. Ɗaya daga cikin jaridun Najeriya Pulse ta rawaito cewa ministan na cewa an haife Atiku a garin Jada na Adamawa a 1946 a lokacin garin yana karkashin ikon kasar Kamaru - sai bayan shekara ta 1961 garin ya koma karkashin Najeriya. Jaridar ta ambato ministan yana cewa bisa wannan dalili tsayawar Atiku takara ta saɓa wa kundin tsarin mulkin Najeriya. Wannan batu ya ja hankali sosai a faɗin ƙasar musamman a kafofin sada zumunta inda mutane suka rinƙa bayyana mabambanta ra'ayi. FS Yusuf @FS_Yusuf_ Sun soma ganin Atiku a matsayin babbar barazana a 2023 shiyasa irin wadannan kamalai ke fitowa daga bakin Malami. Kotun ƙoli ta wanke Atiku, amma Malami ya san hanyar ruguza ɗan siyasa a Arewa ta hanyar zubar da mutuncinsa. Duk mai gaskiya na cikin bala'i. Malachy Odo II @MalachyOdo1; Batun muhawarar da ake tafkawa a gaban kotun tarayya kan Antoni Janar Malami kan batun Atiku ba ɗan ƙasa bane don haka ba zai iya takara ba a wannan ƙasa bai cancanci takardar da aka yi rubutun ba, bata lokaci kotu ne. A zantawarsa da BBC, Abubakar Malami ya ce wata ƙungiya ce ta shigar da wannan ƙara tun gabannin zaɓen 2019, lokacin da ake taƙaddama kan cancantar ɗan takara. Ya ce shi kansa an kai shi ƙara domin ya amsa tambayoyi ko yi wa kotu bayani kan Atiku Abubakar, don haka babu gaskiya a ce shi ya shigar da ƙara ""Wannan ƙara ce da aka shigar tun kafin zaɓen 2019, tana cikin jeren ƙararrakin da aka shigar a baya kamar irin na Shugaba Buhari kan batun takardun ba shi haƙƙin tsayawa takara,"" in ji Malami. Ministan ya ce bai yi mamakin sake bijiro da wannan batu ba a yanzu domin a makon da ya gabata Jaridun Premium Times da Sahara Reporter sun yi ƙoƙarin shigo da ɓatanci a kan ofishin Antoni Janar da shi kansa Malami. Ya ce ""Jaridun na ƙoƙarin nuna cewa an yi amfani da ni da shugaban ma'aikatan fadar gwamnati da ministan kuɗi cewa mun yi ƙoƙarin tursasa wa gwamnan babban bankin Najeriya ya biya wasu kuɗaɗe da suka kai biliyan sama da 500 wanda kuma babu gaskiya a ciki"". Sannan ya kuma shaida cewa duk ana kitsa irin wadannan batutuwan ne domin zubar da mutuncin Antoni Janar da kuma shiga tsakaninsa da sauran abokan hulda ta fuskar tarayya. Ya ce shiri da aka kitsa da zummar zubar da mutuncinsa a fuskar ƴan Najeriya shi ya sa ake danganta sunansa da abubuwa daban-daban saboda duk wanda ya san tsarin mulki irin na Najeriya zai fahimci yana da iyaka. An sha dai dora alhakin abubuwa da dama da ke faruwa a Najeriya kan Antoni Janar, Abubakar Malami. Ko a lokacin sauya shugaban EFCC Ibrahim Magu an zargi hannun Malamin, hakazalika lokacin marigayi Abba Kyari da tsige Sarki Muhammadu Sunusi na biyu, kuma wasu abubuwa da dama da ke faruwa da taƙaddama da ake yawaita samu a gwamnatin tarayya. Sai dai kamar yadda Malamin ya shaida wa BBC, babu gaskiya a irin waɗannan zarge-zarge." https://www.bbc.com/hausa/56666746 +health Coronavirus: Ku zauna a gida ku wanke hannuwa - Buhari "Yayin ake ci gaba da samun karuwar masu dauke da annobar coronavirus a Najeriya, Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kira da babbar murya ga 'yan kasar su ci gaba da mutunta umarnin zama a gida ba tare da fita ba domin a yaki cutar. Mai magana da yawun shugaban Najeriyar, Garba Shehu ya ce Buhari ya kuma godewa al'umma bisa hakuri da suka yi, da kuma kwarin gwiwar da suke bayarwa wajen yaki da barkewar cutar covid-19. Ya ambato shugaban na cewa ""Mun fahimci a yau, za a samu 'ya'ya maza da mata wadanda ba za su iya ziyartar iyayensu ba, da kuma dattawan da aka kebe daga matasa. Akwai kuma wadanda ke rayuwa hannu baka hannu kwarya kuma suna fuskantar wahala,"" ""Dole ne mu sake kira kan ci gaba da mutunta umarnin takaita zirga-zirga a jihohin da wannan umarni ke aiki tare da bin shawarwarin likitoci da masana kimiyya: zama a gida da wanke hannaye da kuma kare rayukan jama'a,"" A cewarsa ""'yancin walwalarku da muke neman a yau ku takaita zai zama na wani dogon lokaci ne kawai idan masu ba da shawara kan kimiyya suka ce hakan ya zama dole. Amma suna da mahimmanci - a fadin duniya - a kawo karshe tare da yaki da yaduwar cutar,"" Shugaban ya kara da cewa gwamnati ta yi wa dunbim marasa karfi da ke yankunan da matakin kullen ya shafa tanadin tan 70,000 na hatsi wanda za a rarraba ga wadanda suke da tsananin bukata da kuma rarraba kudaden tallafi da gwamnatin tarayya ke yi a jihohin da kananan hukumomi. ""Muna rokonku ku saurari sanarwar da ake a kafafen yada labarai kan hanyoyin samun tallafin gwamnatin da kuma sanin irin tallafin da gwamnati ta tsara yi a nana gaba,"". ""Juriyar da gwamnati take so daga gareku saboda a fadin duniya babu wata hanya daya tilo ta yaki da annobar. Babu rigakafi kuma hakan na nufin akwai zabi da za a yi: tsakanin ci gaba da tafiyar da lamura kamar yadda aka saba ko rungumar takunkuman da aka sanya na takaita zirga-zirga duk da hana ya yi mummunan tasiri da ba a yi tsammani ba."" a cewar sanarwar. ""Amma a wannan lokaci na rashin dadi, ya zama dole a garemu mu fada muku gaskiya ba tare da boye-boye ba: wannan annoba ce ta duniya baki daya. Ta shafi kasashe 210 da yankuna a sassan duniya. Ba zamu nade hannu muna jiran taimakon wasu ba. Mune kadai za mu iya yakar cutar,"" ""A maimakon haka, kawar da kwayar cutar ya ta'allaka a kanmu. Ba zamu jira wasu ba. Za mu iya dogara ne da kanmu. Kuma hakan ya zama dole a yi kuma za mu yi nasara ta kawo karshen barkewar cutar a matsayinmu na 'yan Najeriya tare."" Ya zuwa yanzu dai mutum 318 ne suka kamu da coronavirus a kasar - mutum 70 sun warke sai wasu 10 da suka mutu." https://www.bbc.com/hausa/labarai-52258574 +entertainment Daga Bakin Mai Ita tare da Ali Baba Yakasai Danna hoton da ke sama domin kallon bidiyon: Daga Bakin Mai Ita shiri ne na BBC Hausa da ke kawo muku hira da fitattun mutane kan wasu abubuwa da suka shafi rayuwarsu zalla. A wannan kashi na 111, mun tattauna da makidin waƙoƙin fina-finan Hausa, Ali Baba Yakasai. https://www.bbc.com/hausa/articles/cp0qr6jvy89o +business Bidiyo: Yadda za ku rage raɗaɗin koma bayan tattalin arziki Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon: A makon da ya gabata ne gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa ƙasar ta shiga cikin matsin tattalin arziƙi a bana. Wannan al'amari ya ɗaga wa ƴan ƙasar da dama hankali bayan da dama tuni suka fara fuskantar hauhawar farashin kayayyaki. BBC ta yi nazari a wannan bidiyo kan yadda za ku yi rayuwa cikin kula da taka tsantsan ba tare da kun ji a jikinku sosai ba. https://www.bbc.com/hausa/media-55099307 +religion An ɗaure marubucin da ya yi ɓatanci ga addinin Musulunci a Algeria "An yanke wa wani marubuci ɗan Algeria hukuncin ɗaurin shekara uku a gidan kaso, kan ɓatanci ga addinin Musulunci. Shari'ar Said Djabelkhir ta ja hankalin duniya. Ɗan jaridar mai shekara 53, wanda yake da digiri a fannin addinin Musulunci, ya wallafa littattafai biyu a kan Musulunci. An gurfanar da shi gaban shari'a bayan wasu lauyoyi biyu da farfesa sun shigar da ƙara kan kalaman da ya yi a shafukan sada zumunta. Mutumin ya ce yankan dabbar layya da ake yi bisa tsarin addinin Musulunci ɗabi'ar marasa addini ce. Ya kuma ce wasu sassan Al-Ƙur'ani kamar labarin Jirgin Annabi Nuhu, ba lallai ne ya kasance gaskiya ba, sannan ya soki yadda ake wasu abubuwan a Musulunci kamar auren wuri ga yara a wasu yankunan Musulmai. Karkashin dokokin kasar Algeria, batanci ga Annabi Muhammad SAW ko addinin Musulunci babban laifi ne da a kan yanke hukuncin zaman gidan yari daga shekara biyar zuwa sama. Musulmai sun yi imani da yankan dabba a lokacin Sallar Layya domin tuna wa da kyakkyawar niyyar Annabi Ibrahim ta yin sadaukarwa da ɗansa Annabi Isma'il a matsayin abin hadaya, a lokacin da Allah Ya yi masa umarni da hakan. Bayan yanke hukuncin, da bayar da belin Djabelkeir, ya shaida wa manema labarai a wajen kotun da ke babban birnin kasar wato, Algiers, cewa yana shirin ɗaukaka kara saboda yana da 'yancin fadin albarkacin bakinsa. An ruwaito shi a kafofin yaɗa labarai yana kira ga a sake yin nazari kan wasu bayanai da ke cikin Ƙur'ani da Hadisai. Ya kuma masu sukarsa sun yi amanna cewa duk abin da ke cikin Ƙur'ani gaskiya ne, kuma ba sa bambance tsakanin ""tarihi"" da ""camfi"" - tamkar labarin Jirgin Annabi Nuhu. A baya-bayan nan ya shaida wa AFP cewa ""koyarwar Ƙur'ani ba ta dace da hasashe da buƙatun mutanen zamani ba."" Musulmai sun yi imani da Ƙur'ani zancen Allah SWT ne, kuma an saukar wa Annabi Muhammad SAW ne a matsayin hanyar rayuwar ɗan adam. Ministan Harkokin Addini na Aljeriya Mohamed Aissa ya sha sukar Mr Djabelkhir, yana mai cewa ba zai bari ""wani ya kawo ruɗani a ƙasar ba."" Kungiyoyin kare hakkin dan adam da 'yan siyasa sun nuna goyon baya ga Djabelkeir, tare da cewa hukuncin da aka yanke masa ya take hakkinsa da 'yancin fadin albarkacin baki. Lauyansa Moumen Chadi, ya ce ya kaɗu da hukuncin da aka yanke masa, ya ƙara da cewa ya yi tsammanin za a kori shari'ar baki daya." https://www.bbc.com/hausa/labarai-56851189 +religion Sheikh Abduljabbar Kabara: Gwamnatin Kano ta sanya ranar muƙabala tsakanin malamin da malaman jihar "Gwamnatin jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya ta sanya ranar da za a tafka mukabala tsakanin fitaccen malamin nan Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara da wasu malaman jihar. Kwamishinan harkokin addinai na jihar Muhammad Tahar Adamu wanda ake kira Baba Impossible ne ya bayyana haka ranar Alhamis a tattaunawarsa da BBC Hausa. Ya ce za a gudanar da mukabalar ce ranar Asabar 10 ga watan nan na Yuli a Hukumar Shari'a da ke birnin na Kano. A cewarsa tuni ya mika takardar gayyatar yin mukabalar ga malamin da malaman da za su fafata da shi. Kwamishinan ya bayyana haka ne kwanaki kadan bayan shugabannin zauren hadin kan malaman Kano sun zargi gwammatin jihar da ""jan kafa"" game da zaman tuhumar suka ce za su yi wa Sheikh Abduljabbar a kan zargin cin zarafin Manzon Allah (SAW) da Sahabbansa. Ya sha musanta wannan zargi. A ranar Laraba ne wata Babbar kotun Kano ta amince da bukatar lauyoyin Sheikh Abduljabbar kan sauraren hujojinsu na neman soke umarnin wata kotun Majistire da ke jihar na rufe masallaci da makarantar malamin. Alkalin kotun, Mai shari'a Nura Sagir ne ya bayar da umarnin, bayan la'akari da korafin da malamin ya yi na rashin ba shi damar kare kansa daga wasu zarge-zargen da ake yi masa. Da ma dai Sheikh AbdulJabbar ya bayyana dakatarwar da gwamanatin ta yi masa daga yin wa'azi da rufe masallacinsa da cewa ""zalunci ne"". Matashiya Ranar 4 ga watan Fabrairun da ya wuce ne majalisar zartarwar jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ta amince da haramta wa Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara yin wa'azi a dukkanin faɗin jihar, saboda furta kalaman tunzuri a yayin wa'azi da kuma kalaman batanci ga Annabi Muhammad. A wancan lokacin gwamnatin ta shaida wa BBC cewa ta yi nazari kuma ta samu rahotanni daga wurare daban-daban, ciki har daga manyan malamai da hukumomin tsaro, kan kalaman da malamin ke furtawa, shi ya sa ta dauki wannan mataki. Tun a wancan lokaci ne gwamnatin ta ce ta kafa wani kwamiti domin gudanar da bincike a kan wadannan zarge-zarge, amma har yanzu bai gabatar da rahotonsa ba. Shi dai Malamin ya yi zargin cewa gwamnatin Kano ba ta yi masa adalci ba wajen daukar matakin ba tare da an ji daga nasa bangaren ba. Ya nemi a shirya masa zama da malaman dake ƙalubalantarsa domin ya kare duk abin da yake faɗi, bukatar da gwamnatin ta amince da ita, kafin daga bisani kotu ta haramta yin zaman kasa da awanni 48 kafin a gudanar da shi." https://www.bbc.com/hausa/labarai-57758950 +health Gane Mini Hanya 9/10/2021: Yadda ciwon miƙewar gaba ya hana ni aure’ Latsa hoton sama domin sauraren shirin: Maza masu fama da lalurar amosanin jini sun yi kira ga gwamnati ta kawo musu dauki, ta hanyar samar da cibiyoyin Nazari don sama musu maganin cutar sakamakon barazanar mutuwar mazakuta da suke fuskanta. Wani mai fama da irin wannan matsalar ya shaidawa BBC, idan lalurar ta motsa masa yakan shiga tashin hankali da radadin ciwo sakamakon mikewar da mazakutarsu ke yi da tsananin ciwo. Matashin ya shaidawa wakilin BBC Khalifa Shehu Dokaji cewa matsalar ta sanya ya gagara yin aure. https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-58864503 +health Coronavirus: Ina annobar ta kai a arewacin Najeriya? Baya ga Abuja, babban birnin tarayya, jihohin Kaduna da Bauchi ne kan gaba a yawan masu fama da cutar coronavirus a yankin arewa, ko da yake, Katsina wadda aka fara sanar da bullar annobar ranar Talata 7 ga wata, tana kokarin kamo su. Yanzu dai akwai mutum biyar da aka tabbatar sun kamu, bayan sake samun mutum 1 mai fama da cutar a ranar Lahadi. Gwamnatin jihar Katsina dai ta shelanta kulle Daura, mahaifar shugaban kasar, inda aka samu mutum na farko da ya kamu da cutar. Sai dai babu jimawa kuma sai aka ji annobar ta bulla karon farko cikin Kano, jiha mafi yawan jama'a a Najeriya kuma cibiyar hada-hadar kasuwanci don haka ne ma ake da damuwa sosai game da al'amarinta. Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ce yana duba yiwuwar rufe wasu kasuwanni kuma zai yi ganawa da malaman Kano don sanin yadda za su bullowa lamarin taruka irin na Sallar Juma'a da haduwar ibada a coci-coci. Jimillar mutanen da suka kamu da cutar koronabairas a daukacin yankin sun kai 80 zuwa ranar Lahadi, a cewar hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta Najeriya. Abuja ce ke da mafi yawam mutanen da ke fama da annobar a yankin, an fara samun bullar wannan cuta a babban birnin ranar 20 ga watan Maris, bayan gwajin da aka yi wa Mohammed Atiku. Ga alama har yanzu d'an na Atiku Abubakar, jigon dan siyasa a Najeriya yana ci gaba da jinya a cibiyar kebe marasa lafiya ta Gwagwalada a Abuja. Wasu sun rika yaba wa jarumtarsa ta fitowa ya yi wannan bayani, wasu kuma sun rika zargin dan Atikun da rashin kebe kansa bayan ya dawo daga wata tafiya kasashen waje. A ranar Litinin 23 ga watan Maris ne Hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta ba da sanarwar samun mutum na farko da ya rasu sakamakon wannan annoba a Najeriya, lamarin da ya faru a Abuja. Hukumar NCDC ta ce mutumin dan shekara 67 ya dawo gida Najeriya ne bayan ya je ganin likita kasar Burtaniya, a cewarta mamacin (Injinya Sulaiman A-ci-mugu) ya yi fama da wadansu kwantattun cutuka kafin rasuwarsa. A ranar 7 ga watan Afrilu kuma, Gwamna Masari na jihar Katsina ya sanar cewa Allah Ya yi wa mutum na farko da ya kamu da coronavirus a jiharsa, Dr Aliyu Yakubu rasuwa. Ya ce likitan wanda ke garin Daura, an ba da rahoton ya yi tafiya zuwa Lagos, kuma bai dade da komawa gida ba, sai ya kamu da rashin lafiya inda ya kai kansa asibitin rundunar sojan sama na Daura kafin cikawarsa. Wasu na kuka wasu na dariya Akasarin manyan mutanen da cutar ta harba da farko-farko sun fito ne daga jihohin arewa, inda a ranar Talata 24 ga watan Maris, hukumar NCDC ta sake fitar da bayanin cewa an samu mutum biyu da cutar ta harba a yankin, kuma karon farko cutar ta bulla a wata jiha, baya ga Abuja. Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi shi ne jagoran wata jiha da covid-19 ta fara kamawa a Najeriya, ko da yake a yanzu ya warke har ma ya ci gaba da harkokinsa. Sai dai ya zuwa ranar Lahadi, akwai mutum biyar a jihar ta Bauchi da ke ci gaba da jinya sakamakon wannan annoba, ban da Gwamna Bala Mohammed da ya warke. Haka shi ma, Mallam Abba Kyari shugaban ma'aikatan fadar shugaban Najeriya yana can yana ci gaba da jinya a jihar Legas, bayan an ba da rahoton kamuwarsa ranar 24 ga watan Maris. Fitattun mutane irinsu Atiku Abubakar sun jajanta masa lokacin da rade-radin ya cika gari cewa annobar ta shafe shi bayan wata tafiya da ya yi zuwa kasar Jamus. Haka kuma har yanzu babu wani rahoto da ke nuna cewa Malam Nasir El-Rufa'i, mutum na farko da ya kamu da cutar a jihar Kaduna ranar Asabar 28 ga watan Maris, ya samu sauki. Yana cikin gwamnonin da suka fi zafafa daukar matakai don ganin annobar ba ta riski al'ummarsu ba. El-Rufa'i dai ya dauki matakin kulle jiharsa ba shiga ba fita, tare da hana tarukan biki da na ibada ciki har da Sallar Juma'a da ibadu a coci-coci da masallatai. Zuwa yanzu, akwai mutum shida da ke fama da cutar a jihar ta Kaduna, kuma daga bayanan hukumomi, ba a samu rasuwa sakamakon wannan annoba a jihar ba, kamar kuma yadda ba a samu wanda ya warke ba. Mutum na baya-bayan nan da ya kamu da cutar, namiji da ke aikin gadi a unguwar Mando, bayanai sun ce an gano yana fama da corona ne bayan ya dawo daga tafiyar da ya yi zuwa jihar Legas, wadda ta fi yawan masu cutar a fadin Najeriya. Binuwai ita ce jiha ta farko da wannan cuta ta fara bulla a yankin Arewa ta Tsakiya, inda hukumar NCDC ta ce zuwa ranar Asabar 28 ga watan Maris, adadin masu cutar a daukacin Najeriya ya kai 97. Baya ga Binuwai cutar ta shiga jihar Kwara ranar 6 ga watan Afrilu, inda aka sanar da kamuwar mutum biyu. Ran 09 ga watan Afrilu, an ba da sanarwar mutum na farko da annobar ta harba a cikin jihar Neja. Tabawa ranar samu Laraba 1 ga watan Afrilu a iya cewa tana cikin ranaku da aka fi samun mutanen da aka tabbatar sun sake kamuwa da annobar mafi yawa a arewacin Najeriya, inda adadin ya karu zuwa mutum 43. Hukumar dakile cutuka ta ce an samu karin mutum bakwai da cutar ta shafa a Abuja, sai mutum 1 a jihar Kaduna da kuma karin wani a Bauchi. Bayan sanar da kamuwar karin mutum uku a jihohin Kwara da Katsina a ranar Lahadi 12 ga Afrilu, adadin masu fama da cutar a daukacin yankin yanzu ya kai 80. Nesa ta zo kusa Sai dai wani karin ci gaba da aka samu a baya-bayan nan a yankin arewacin Najeriya shi ne bude sabbin cibiyoyin gwada cutar kovid-19. Hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta fada a ranar Asabar 11 ga wata cewa an yi nasarar bude cibiyoyin gwaji guda biyu a jihohin Kano da Filato. Karon farko ke nan da aka samu irin wadannan cibiyoyin gwajin cutuka irinsu coronavirus a daukacin yankin arewa. Kafin yanzu sai dai a dauki samfur a kai shi zuwa Abuja ko Legas don tantancewa. Hukumar ta kuma ce aiki na ci gaba da gudana don ganin an samu irin wadannan cibiyoyin gwaje-gwaje a biranen Maiduguri da Sokoto da kuma Kaduna. Mutane nawa ne suka warke a arewa? A ranar Alhamis, 9 ga wata, jami'an gwamnatin Bauchi, sun fitar da sanarwar cewa Gwamna Bala Mohammed ya warke har ma an sallame shi daga wurin da aka kebe shi. Haka zalika, a ranar Lahadi 12 ga Afrilu, an ga bayanin da wani mashawarcin shugaban Najeriya kan harkar shafukan sada zumunta, Bashir Ahmad ya fitar da ke cewa an sallami karin mutum hudu bayan warkewarsu daga cibiyar Gwagwalada. Duka-duka dai zuwa yanzu alkaluman hukumar NCDC na cewa mutum 85 ne suka warke a daukacin Najeriya. Zuwa yanzu akwai tabbacin annobar ta bulla a jihohin da suka hadar da Babban Birnin Tarayya - 56 Bauchi - 6 Kaduna - 6 Binuwai - 1 Kwara - 4 Katsina - 5 Neja - 1 Kano - 1 https://www.bbc.com/hausa/labarai-52266056 +health Auren zumunta na iya jawo cutar kansar ido - Masana "Kwararru a fannin lafiya sun ce akwai wani nau'in cutar kansar ido da auren zumunci ke iya kawo shi. Tsohuwar babbar jami'ar shirin takaita cutar kansa ta Najeriya, Dr. Ramatu Hassan ce ta bayyana hakan a wata hira da BBC Hausa albarkacin Ranar Cutar Kansa Ta Duniya a ranar Talata. Dr Ramatu ta ce auren zumuni ko na dangi da ake yi tsakanin mutane kan yi sanadin a haifi yaro mai irin wannan lalurar. Kasashen da ke da yawan auren zumunci kamar arewacin Najeriya na da yawan cutar kamar yadda likitar ta bayyana. ''Irin wannan cuta ta kansar Ido na samuwa ga jarirai tun suna cikin ciki, saboda gado ake yi yawanci, kuma yana faruwa a inda ake yawan yin auren dangi, don haka akwai yiwuwar idan aka ci gaba da auren dangi to kuwa za a ci gaba da samun cutar,'' in ji ta. Cutar na fitowa ne a dai-dai inda ya kamata ido ya gani, sai a haifi yaro da ita a hankali a hankali tana ci gaba da girma, yayin da yaro ya kamata ya fara tafiya sai ya rika tuntube kamar yadda likitar ta bayyana. Cibiyar yaki da cutar daji ko kansa ta duniya ta ce miliyoyin mutane ne ke cikin hatsarin kamuwa da cutar kansa a rayuwarsu, saboda kawai ba su san hanyar da za su gujewa shiga tarkon cutar ba. Dr Ramatu Hassan ta ce mutane da yawa a fadin duniya na sakaci da bayanan kare kawunansu daga kamuwa da cutar kansa. Wasu alkaluma na cewa cutar kansa tana sanadin mutuwar mutum miliyan tara da dubu 600 duk shekara, wato sama da mutanen da ke mutuwa sanadin cutar HIV da Aids da kuma zazzabin cizon sauro da tarin TB. Kwararru sun yi hasashen cewa nan da shekara ta 2030, mutanen da ke mutuwa duk shekara sakamakon cutar kansa zai karu zuwa miliyan 13. Likitar ta kuma yi karin bayani kan hanyoyin da za a bi a kare kai daga wannan cuta, ""babban matakin da ya kamata a dauka shi ne tun daga farko kafin a yi aure a rika tunnain cewa akwai irin wannan ciwo a dangi ko kuwa,"" in ji Dr Ramatu. Saurari hirar cikakkiyar hirar da Badriyya Tijjani Kalarawi tayi da Dr. Ramatu Hassan:" https://www.bbc.com/hausa/labarai-51358421 +religion Ku San Malamanku tare da Sheikh Jalo Jalingo Latsa hoton sama ku kalli bidiyo Shahararren malamin Musuluncin nan, Sheikh Dr. Ibrahim Jalo Muhammad Jalingo ya ce ya fara karatu ne domin ya ƙware a harshen Larabci da kuma adabi ba wai karatun Fiƙihu da sauransu ba kafin daga baya ƙaddara ta sauya masa layi. An haifi malamin a garin Jacci da ke Jihar Taraba a arewa ta tsakiyar Najeriya a shekarar 1960. https://www.bbc.com/hausa/media-57432028 +entertainment ...Daga Bakin Mai Ita tare da Adam A. Zango Daga Bakin Mai Ita wani shiri ne na BBC Hausa da ke kawo muku hira da fitattun mutane kan wasu abubuwan da suka shafi rayuwarsu zalla. A wannan kashi na 62, shirin ya tattauna da Adam A. Zango, fitaccen tauraro a Kannywood. A wannan shiri ya amsa tambayoyin da suka shafi rayuwarsa da rawar da yake takawa a fina-finai. Ɗaukar bidiyo da Tacewa: Yusuf Ibrahim Yakasai https://www.bbc.com/hausa/media-58260161 +health Coronavirus: BUK ta fara aikin kera na'urar taya numfashi "Tsangayar koyon aikin injiniya ta Jami'ar Bayero Kano ta ce tana kokarin samar da na'urorin taya numfashi da ake kira ventilators don amfani da su a cibiyoyin da aka tanada wajen kebe mutanen da suka kamu da cutar numfashi ta koronabairus. Tsangayar aikin injiniyancin ta ce ta tattara wasu kwararru a fadin Jami'ar ta Bayero inda suka dukufa wajen kera na'ura guda daya da za ta zama zakaran gwaji, kafin ta tsunduma aikin samar da na'urorin da za a iya amfani da su a asibitoci. Shugaban tsangayar aikin injiniya a Jami'ar, Farfesa Salisu Dan'azumi ya fada wa BBC cewa sun yi nisa da wannan aiki. ""Sun fara aiki har ma sun cimma kusan kashi 50 na samar da wannan na'ura,"" in ji shi. Ya kuma ce an samu samfurin na'urar ne daga irin wadda ake amfani da ita a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano da ke Kano kuma a cewarsa, ""mako daya muka ba kwararrun domin kammala aikin samar da na'urar."" Shugaban tsangayar ya ce duk da yake ana yajin aiki amma sun kafa kwamiti wanda ya kunshi injiniyoyi daga bangaren lantarki da na kere-kere da ma na bangaren lantarki da kere-kere gaba daya wato Mechatronics karkashin jagorancin Farfesa Abdussamad Umar Jibia. Farfesa Salisu Dan'azumi ya ce sai an kera wannan na'ura ta gwaji sannan su sanar da jami'a don ganin inda za ta shiga ciki don zama jagora, ta yadda za a iya fadada aiki. Annobar koronabairus dai ta sanya hatta manyan kasashen duniya irinsu Amurka da Burtaniya da Italiya shiga cikin tsananin bukatar karin kayan asibiti, saboda yawan mutanen da take shafa. Zuwa ranar Alhamis, adadin mutanen da cutar covid-19 ta kama a cewar Jami'ar Johns Hopkins ya haura mutum miliyan daya. Adadin wadanda suka kamu da cutar coronavirus zuwa daren Alhamis a Najeriya ya kai mutum 184, in ji hukumar NCDC mai yaki da yaduwar cutuka. Hukumar ta sanar da samun karin mutum 10 da cutar koronabairus ta shafa da yammacin ranar ta Alhamis." https://www.bbc.com/hausa/52145280 +religion Tunisia: An ɗaure wata mata saboda ta yi rubutu cikin salon ayar Kur'ani a Facebook "An ɗaure wata mata a ƙasar Tunisia mai wallafa bayanai a intanet tsawon wata shida a gidan yari bayan ta wallafa wani saƙo kan cutar korona ta hanyar kwaikwayon salon wata ayar Ƙur'ani. An kama Emna Charqui mai shekara 28 a watan Mayu bayan ta wallafa saƙo a Facebook tana mai shawartar mutane da su bi hanyoyin kariya cikin salon ayar Kur'ani - littafi mai tsarki kuma mafi girma ga Musulmai. Charqui ta bayyana a wata hira ta baya-bayan nan cewa ba ta yi niyyar tsokanar kowa ba amma saƙon da ta wallafa ya birge ta. Wata kotu ta same ta da laifin ""haifar da ƙiyayya tsakanin addinai"". Zuwa yanzu ba a garƙame ta a gidan yarin ba sakamakon aniyarta ta ɗaukaka ƙara. A ranar 2 ga watan Mayu, Charqui ta yaɗa wani saƙo a shafinta na zumunta tana kwaikwayon ayar Kur'ani. A ciki ne kuma ta yi kira ga mutane da su riƙa wanke hannu da kuma yin nesa-nesa da juna domin kauce wa kamuwa da cutar korona. An ruwaito cewa wani maras addini ne ɗan Algeria da ke zaune a Faransa ya fara saka hoton. Charqui ta wallafa nata saƙon ne a watan Ramadana, yayin da ƙasar Tunisia ke tsaka da dokar kulle. Ta tayar da ƙura a shafukan sada zumunta, inda har wasu suka yi kiran da a hukunta Charqui, wadda ita ma ba ta bin kowanne addini." https://www.bbc.com/hausa/labarai-53411985 +technology BBC ta bude gasar rubutu a harshen Pidgin "Sashen Turancin broka wato BBC Pidgin ya kaddamar da gasar rubutun zube da harshen Pidgin a ranar Alhamis 1 ga watan Agustan 2019. Gasar a bude take ga dukkanin daliban manyan makarantun gaba da sakandare a nahiyar Afirka. Masu sha'awar shiga gasar za su rubuta makala ne mai kalmomin da ba su wuce 800 ba kan maudu'in ""ko mace za ta iya jagorancin siyasa a nahiyar Afirka?"" (""Is Africa ready for female political leadership?""). Wani rukunin alkalai da suka hada da malamai da 'yan jarida da marubuta na harshen Pidgin wadanda suka fito daga Afirka ta Yamma ne za su zabi mutum daya wanda ya yi nasara. Wajibi ne kowacce makala ta dace da tsarin harshen Pidgin tare da bin ka'idojin rubutu. Za a sanar da wanda ya yi nasarar ne a Legas ranar 20 ga watan Satumban 2019. Sannan za a ba shi kyautar dala $500 (kusan naira 180,000) Za a rufe shiga gasar ne a ranar Juma'a 30 ga watan Agustan 2019. A aiko da makala zuwa adireshin imel na bbcpidgin.essay@bbc.co.uk" https://www.bbc.com/hausa/labarai-49270372 +religion Nana Khadijah, matar manzon Allah wadda matan zamani za su yi koyi da ita wajen dogaro da kai """Ita ce matar da ta yi zarra ta kuma kere sa'a. Ko da matan zamani za su so su cimma irin nasarorin da ta cimma shekara 1,400."" Wannan shi ne yadda Asad Zaman, wani limami a birnin Manchester na Birtaniya ya bayyana Nana Khadijah, matar Annabi Muhammad (SAW), wacce aka haifa a ƙarni na shida a ƙasar da a yau ake kira Saudiyya. Mace ce da ake matuƙar girmama ta, mai arziki da kwarjini, wacce ta ƙi karɓar tayin aure daga fitattun mutanen zamaninta da dama. A ƙarshe dai ta yi aure, har sau uku. Mijinta na fari ya mutu, sannan wasu ruwayoyin sun ce mijinta na biyu kuma rabuwa ta yi da shi. Bayan wannan ne ta yi alwashin ba za ta sake aure ba... har sai da ta haɗu da mijinta na uku kuma na ƙarshe sannan ta sauya shawara. Khadijah ta ga wasu ""kyawawan halaye a tattare da shi, da suka sa ta sauya ra'ayinta na ƙin sake aure,"" kamar yadda Asad Zaman ya shaida wa BBC. Ba kamar yadda aka saba ba a wancan zamanin, Khadijah ce ta zaɓe shi da kanta ta kuma nemi ya aure ta. A lokacin shekararta 40, shi kuwa sabon mijin da za ta aura shekararsa 25, daga ƙabilar da take da matuƙar daraja. Wannan labari ya fi gaban na soyayya; labari ne na tushen addini na biyu mafi girma a duniya a yau. Sabon mijin Khadijah shi ne Annabi Muhammad (SAW), wanda bayan aurensu ya zamo manzon da aka aiko da Musulunci. Wani farfesa na daɗaɗɗen tarihin Gabas Ta Tsakiya a Jami'ar New York, Robert Hoyland, ya ce zai yi matuƙar wahala a yi bayanin wace ce Khadijah a zama ɗaya, saboda an yi ta rubutu kan abubuwan da aka sani a kanta tsawon shekaru bayan mutuwarta. Sai dai mafi yawan majiyoyi sun nuna cewa ""ita mace ce da ke da burin zama mai tsayiwa da kanta, kuma mai karfin hali,"" in ji Holyland a hirarsa da BBC. Alal misali, ta ƙi yarda ta auri wani ɗan uwanta - kamar yadda danginta suka so - saboda tana so ya kasance da kanta ta zaɓi mijin aurenta. Khadijah ɗiya ce ga wani ɗan kasuwa da ya mayar da kasuwancin abin alfaharin zuri'arsa. Bayan da ya mutu a wani yaƙi, sai ta dasa daga inda ya tsaya. ""Kowa ya san ta da ƙoƙarin yi wa kanta abubuwa,"" kamar yadda wata masaniyar tarihi kuma mawallafiyar littattafai Bettanu Hughes ta faɗa a wani shirin BBC. ""A taƙaice dai, harkokin kasuwancinta ne suka yi sanadin ɗora ta a kan hanyar da daga ƙarshe ta sauya tarihin duniya."" Khadijah tana aiwatar da harkokinta daga Makka a Saudiyya, kuma kasuwancinta na buƙatar a dinga kai da kawo mata kayayyaki daga can zuwa manyan biranen Gabas Ta Tsakiya. ""A bayyane yake cewa Khadija mai tsayiwa ce kan al'amuranta,"" in ji Bettany Hughes. Waɗannan matafiyan sukan yi tafiya mai nisa daga kudancin Yemen zuwa arewacin Syria. Duk da cewa wani kaso na dukiyarta ta samu ne daga mahaifinta, Khadijah ta tara tata dukiyar ita ma, a cewar Fozia Bora, wata mai shirin zama farfesa ta tarihin Musulunci a Jami'ar Leeds da ke Birtaniya. Ƴar kasuwa ce ""mai dogaro da kanta, kuma mai ƙwazo da jajircewa."" Khadijah takan ɗauki ma'aikata, inda take zaɓar mutane masu ƙwarewar da za su amfani kasuwancinta. Ta ji labarin wani mutum da aka yi masa shaidar gaskiya da ƙwazo, don haka bayan wata ganawa da ta gamsu da bayanan da ta ji, sai ta ɗauke shi aiki don ya dinga bin ayarin ma'aikatanta. Khadijah ta yaba da jajircewarsa, kuma bayan an shafe lokaci sai ta gamsu ƙwarai da ɗabi'unsa har ta yi sha'awar aurensa. Kwatsam sai Muhammad - wanda ya kasance maraya, ya kuma girma a hannun kawunsa - ya samu tagomashi a rayuwarsa ta fannin tattalin arziƙi,"" a cewar Fozia Bora. An yi amannar cewa ma'auratan sun samu 'ƴaƴa shida, duk da cewa dai ƴaƴa matan ne kawai suka girma. Farfesa Rania Hafaz ta Cibiyar Musulmai da ke London ta shaida wa BBC cewa: ""Akwai wani abu na musamman a auren nasu."" Abin kuwa ba komai ba ne sai ""ganin cewa ita kaɗai ta rayu da shi a matsayin mata, a al'ummar da a wancan lokaci maza ba su cika zama da mace ɗaya kawai ba."" An haifi annabi Muhammadu (SAW) kuma ya girma a tsakanin kabilar Kuraishawa (kamar Nana Khadijah), a daidai lokacin akwai kungiyoyi da ke bauta wa abubuwa daban-daban. Shekaru kadan bayan ya yi aure, Muhammad ya fara sauyawa zuwa bautar ubangiji - ya kuma koma da yin mu'amalarsa a kusa da manyan duwatsu kusa da birnin Makkar domin kadaicewa tare da yin zurfin tunani. Kamar yadda addinin Musulunci ya yi imani da shi, Mala'ika Jibrilu ya zo masa da wayahi daga Allah, mala'ikan da ya taba sanar da Maryama cewa za ta zama mahaifiyar Annabi Isa. Ta wannan hanyar ce aka saukar wa da Annabi Muhammadu littafin Alku'rani mai girma. An bayyana cewa lokacin da aka yi masa wahayin, ya tsorata saboda da farko bai fahimci me yake faruwa ba. ""Bai iya fahimtar yadda zai bayyana abin da ya shaida ba. Ba shi da masaniya kan batun saboda bai taso cikin fahimtar kadaitar ubangiji Allah ba,"" in ji Fozia Bora. ""Ya yi tsananin tsorata da dimaucewa game da abin da ya faru. Wasu bayanai da aka tattara sun ce wahayin ba mai sauki ba ne, kuma duk da cewa cikin ruwan sanyi aka zo masa da shi, amma a zahiri akwai firgitarwa.'' Annabi Muhammadu ya yanke shawarar amincewa ""da tsarkakaken halittar da zai iya yin amanna a kan komai,"" in ji farfesa Hoyland. Khadijah ta saurare shi ta kuma kwantar masa da hankali. Ta kuma gaskata shi sannan ta yi tunanin wannan wani abu ne mai kyau. Ta kuma nemi shawara daga wani dan uwanta mai ilimin addinin Kirista. An yi amanna cewa Waraqah ibn Nawfal ya danganta wahayin da aka yi wa annabi Muhammad da na annabi Musa. ""Yana da sani a kan litattafai masu tsarki,"" Bora ya bayyana, don haka ""sahihin tabbaci ne na wahayin da aka yi masa. ""Mun san cewa lokacin da ya fara samun wahayin Alkur'ani mai girma, amma shi kansa Muhammadu na yi wa kansa da kansa wasu-wasi."" Amma kuma Khadijah ta rika ba shi tabbacin cewa shi manzon Allah ne,"" a cewar Leila Ahmed, wata malamar addinin Musulunci a Jami'ar Harvard. Malamai da dama sun yarda da haka, tun da Khadijah ita ce mutum ta farko da ta fara jin wahayin da aka saukarwa da annabi Muhammadu, dole a dauke ta a matsayin musulma ta farko da ta karbi sabon addinin Musulunci. ""Ta yarda kuma ta amince da sakon,"" in ji Foiza Bora. ""Ina ganin hakan ne ya karfafa wa Muhammadu gwiwa wajen fara yada sakonninsa."" Masaniyar tarihi Bettany Hughes ta ce a wannan mataki, Muhammadu ya kalubalanci dattawan kabilar kuma ya fara gudanar da wa'azi a bayyane: ""Allah shi kadai ne abin bautawa. Yin bauta ga wasu daban sabo ne."" Kamar yadda Foiza Bora ta bayyana, lokacin da Muhammadu ya fara yada addinin Musulunci, al'umomin garin Makka da ba su amince da cewa Allah daya ne ba, sun nuna masa wariya da tsangwama. ""Amma kuma Khadijah,"" in ji Foiza Bora, ""ta ba shi goyon baya da kariyar da yake bukata a lokacin."" ""Cikin shekaru 10, Khadijah ta yi amfani da dukiyarta da darajar iyalan da ta fito wajen taimaka wa mijinta ta tallafa wa sabon addinin,"" in ji Hughes, ""addinin da aka gina a bisa tsarin bin bautawa guda daya mai cike da ce-ce-ku-ce a kuma cikin al'ummar da ta yi imani da abubuwan bauta da dama"". 'Shekarar alhini' Khadijah ta yi iya karfinta wajen tallafa wa mijinta da kuma addinin Musulunci - amma a shekarar 619, ta kamu da rashin lafiya ta rasu. Bayan shafe shekaru 25 suna tare, Muhammadu ya shiga halin damuwa da alhini. ""Abu mai matukar sha'awa game da bayanan da aka tattara a wannan lokaci shi ne, yadda mutane ke maganar Khadijah a matsayin mutum mafi kusanci da Muhammad ya samu, fiye ma da abokansa na kusa kamar Abu Bakar ko Omar,"" a cewar Farfesa Hoyland. Masaniyar tarihi Bettany Hughes ta yi nuni da cewa har yanzu Musulmai na tunawa da zagayowar shekarar da ta mutu a matsayin ""Shekarar Alhini"". Daga bisani, Muhammadu ya sake yin aure, kuma a wancan karon ya auri mata da yawa. A wani shirin BBC, Fatima Barkatulla, wata malamar addinin Islama kuma marubuciyar litattafan kananan yara kan rayuwar Khadijah, ta ce akasarin abubuwan da muka sani game da Khadijah sun fito ne daga Hadisai - hikayoyi, al'adu da kuma abubuwan da aka bayyana game da rayuwar annabi Muhammadu. Mabiya da kuma makusantan annabi Muhammadu suka fara bayyanawa, kuma daga bisani ne aka rubuta. Daya daga cikin masu ba da labarin ita ce Aisha, daya daga cikin matan da annabi Muhammadu ya aura daga baya, kuma daya daga cikin fitattun mata a cikin addinin Musulunci. ""A bayyane take cewa annabi Muhammadu ya ba ta labarin Khadijah, kuma ta rika bayyana abubuwan da suka faru a farkon lokacin da aka saukar masa da wahayi, lokacin daya zama manzon Allah,"" in ji Fatima Barkatulla. Duk da cewa Aisha ba ta shaida farkon rayuwar annabi Muhammadu ba ta ""rike aikinta hannu biyu wajen isar da sakonnin musulunci ga sauran Musulmai"" abubuwan da aka fada mata, marubuciyar ta ce. Abin koyi A nata bangaren, Foiza Bora, ta ce karatu game da tarihin Khadijah na da matukar muhimmanci wajen warware sarkakiyar da ake da ita a tsakanin al'ummar Musulman farko inda ake barin mata cikin kulle. Muhammadu bai umarci Khadijah ta bar abin da take son yi ba. Gaskiyar magana, ta ce Musulunci ya bai wa mata dama da 'yanci a lokacin. ""A ganina, a kuma matsayina na masaniyar tarihi, Khadijah abar koyi ce, kamar Fatima [daya daga cikin 'yayan annabi Muhammadu] da Aisha, cikin sauran matan,"" in ji Foiza Bora. ""Masu ilmi ne, masu kokari a fannin siyasa, kana sun taka muhimmiyar rawa wajen yada addinin Musulunci da kuma gyara tsarin zamantakewar al'ummar Musumai.'' ''Abu ne mai kyau a gare ni,'' in ji malamar, ""ka iya samun damar koyar da dalibai, mabiya ko akasin haka, game da wadannan matan.""" https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-56008101 +technology Bidiyo: Matan da suka kirkiri lantarki mai amfani da hasken rana na farko a Yemen Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon: Wasu mata a yankin Abs na ƙasar Yemen sun samar da tashar da ke bayar da lanatarki ta amfani da hasken rana – irin ta ta farko a ƙasar. An samar da shirin ne a shekarar 2019 da taimakon Shirin Samar da Ci gaba da Majalisar Ɗinkin Duniya UNDP. A yanzu matan sun mayar da tashar lantarki harkar kasuwancinsu, inda suke samar da makamshi mai ɗorewa ga al’ummar da ke zaune kusa da yankin da ake yaƙin basasar ƙasar. https://www.bbc.com/hausa/media-55934391 +entertainment Yadda aku ya cire wa dan jarida iyafis yana cikin aika rahoto Wannan bidiyon na nuna lokacin da aku ya cire wa wani dan jarida iyafis daga kunnensa yana tsaka da aika rahoto kai tsaye. Dan jaridar na aika rahoto ne kai yadda ake samun yawaitar sace-sace a yankin da yake aika rahoto. https://www.bbc.com/hausa/articles/clwq0xdl3ego +technology Kamfanin Facebook ya kawo maslaha kan batun tantance fuska "Kamfanin Facebook ya kawo maslaha kan rikicin da aka dade ana yi kan yadda yake gano hotunan mutane tare da ambatar sunansu a kan hoton. Zai biya wata kungiya da ke jihar Illinois kudi dala milliyan 550, wadda ta yi musun cewa na'urar da take amfani da ita wajen gano mutane ta sabawa dokar sirri ta jihar. An dade ana ta takaddama kan batun tun shekarar 2015, sai kuma aka sanar da sulhuntawar a yayin da aka fitar da bayanin samunsu na duk bayan wata hudu. Hakan na zuwa ne yayin da 'yan sanda ke amfani da nau'rar wajen tantance fuskokin mutane da wuraren ayyuka na jama'a don gudanar da bincike sosai. Karar da aka shigar kan cewa an bai wa Facebook dama a shekarar 2018 lokacin da wani babban alkalin tarayya ya yanke cewar za a iya sauraran karar a matsayin wadda mutane da yawa suka shigar. Kotun daukaka kara ta ki yarda da kamfanin Facebook na kokarin dakatar da hakan, sai kuma a watan Janairu Kotun Koli ta ki bayar da damar sake duba daukaka karar. Kungiyar masu sada zumuntar sun shaida wa BBC cewa: ""sun yanke shawarar bibiyar kawo maslaha saboda abunda al'ummar ke nema kenan, sannan masu ruwa da tsakinmu a harkar, su wuce batun. Kamfanin Facebook ya fara amfani da na'urar gane fuska a Amurka a shekarar 2010 lokacin da suke alakanta mutane a hotuna suna amfani da na'urar. Na'urar na duba fuskar mai amfani da Facebook din sai ya ba da bayanai kan mutumin. Fasahar ta nuna sarkakiya a lokacin. Duk da cewar masu amfani da ita na da damar rufewa, ba a tambayarsu ko suna son su yi amfani da na'urar. A shekarar 2017 an sauyawa tsarin suna zuwa 'gane fuska' sai mutane suka samu damar budewa da rufewa cikin sauki. Sai kuma 2019, kamfanin Facebook ta mayar da tsarin ya zama 'opt-in' wato ko za ka shiga cikin jerin sabbin abubuwan da suke so ya zama na sirri. ""Wannan sulhun na wakiltar gagarumin sulhu na biyu da aka yi da kamfanin Facebook a watanni shida. ""Kare bayanan sirrin mutane ya zame musu abu muhimmi kuma suna da injiniyoyi 1000 da ke aikin kan abun da ya shafi bayanan sirrin mutane,"" in ji Christopher Rossbach, na bankin zuba jari na J Stern & Co." https://www.bbc.com/hausa/labarai-51312044 +religion Ku San Malamanku tare da Sheikh Hussaini Zakariyya "Sheikh Hussaini Zakariya babban limamin masallacin Juma'a na Banex da ke unguwar Wuse 2 a Abuja babban birnin tarayyar Najeiya ya ce sau uku yana samun damar zuwa ƙaro karatu a Jami'ar Musulunci ta Madina amma ya ƙi zuwa. Shehin malamin ya faɗi haka ne a hirarsa da BBC cikin shirin Ku San Malamanku na mako-mako. Malamin ya ce Sheikh Abubakar mahmud Gumi ne ya ƙarfafa masa gwiwa cewa gara ya tsaya a Najeriya ya ci gaba da karatu don ya haɗa da na zamani kar a bar shi a baya a wajen fahimtar duniya. ""Baya ga haka akwai malaman da suka dinga gaya min irin wannan magana cewa lallai kar na tsaya a karatun addinin kawai gara na haɗa da na zamani ganin yadda duniya ke sauyawa, cikin su har da marigayi Sheikh Musa Adam,"" in ji Ustaz Zakariyya. Amma ya ce ya sha halartar daurorin da jami'ar ke shiryawa a Jami'ar Bayero ta Kano, kuma ya sha halartar taruka a ƙasashe irin su Saudiyya da Masar. An haifi Ustaz Hussaini Zakariyya Yawale a garin Kaduna ranar 1 ga watan Oktoban 1960 a unguwar Abakwa, wanda ya yi daidai da 10 ga Rabi'u Thani shekara ta 1380 bayan Hijira. Mahaifinsa malamin addinin Musulunci ne na Mazhabar Malikiyya kuma a hannunsa ya fara karatu. ""Karatuna ne ya haife ni ya raine ni, a cikinsa na girma a cikinsa na tsufa, ina kuma son mutuwa a cikinsa. Mahifinsa Sheikh Zakariyya Yawale, shi ne ɗalibin Sheikh Abubakar Mahmud Gumi na farko kuma Na'ibinsa mai ja masa baƙi a Masallacin Sultan Bello da ke Kaduna. Malamin ya ce yana alfahari da malamansa uku a rayuwa da suka haɗa da mahaifinsa da Sheikh Isma'ila Iidris Zakariyya wanda ya assasa ƙungiyar Izala, sannan sai wanda ya sa shi a makaranta Sheikh Mahmud Gumi. ""Na rayu tsakanin makaranta da gidan Sheikh Gumi da kuma gidanmu. Ya yi makarantar horar da malaman Arabiyya a Katsina. Sannan ya yi Jami'ar Bayero Kano inda ya karanta Larabci da addinin Musulunci da Tarbiyya. Cikin malamansa na lokacin har da Sheikh Ahmad Kala Haddasana. Bayan ya kammala digiri na farko ya so ya tafi ƙarin karatu sai dai nauyin iyali da na ƴan uwa ya yi masa yawa. Amma ya sha halartar taron ƙara wa juna ilimi. Sai da ya shekara 60 sannan ya je ya yi digiri na biyu har ma ya yi rubutu a kan matsayin Bitcoin a addinin Musulunci a Jami'ar Keffi. Ya yi hakan ne don fitar da matsaya mai amfani ga Musulmai don ka da a bar su a baya ""don kuwa mu'amalar kuɗn intanet ɗinnan ta zo tare da zamani ne,"" in ji shi. A yanzu kuma ya samu gurbin ƙaro karatun digirin-digirgir a Malaysia, annobar korona ce ta hana shi tafiya amma sai je daga baya. Ustaz ya ce ya yi wasanni na ƙuruciya da suka haɗa da ƙwallo ya da wasan damben Boxing da Tennis da Volley Ball da Hockey da kuma Karate. ""Na shahara sosai a wasan Hockey a yankin Katsina a lokacin."" Babban abin da ya fi faranta masa rai shi ne cin jarrabawar Grade II da ya yi a lokacin da aka yi wa makarantarsu tambari cewa ba a cin jarrabawar. Abin da ya fi baƙin cikinsa kuma shi ne rashin mahaifiyarsa wadda ta tsaya tsayin daka wajen ba shi goyon baya a karatunsa da tarbiyyar rayuwarsa. Malam ya ce Allah ya yi masa baiwar riƙe alwala tsawon yini. Shi ne wanda aka fara tura wa yankin ƙasashen Igbo don kula da al'amuran wadanda suka musulunta don su koyi addini. Shi ya fara fassara huɗuba da Turanci da Hausa a masallacin da ke ofishin jakadancin Saudiyya a Legas. A shekarar 1990 kuma yana cikin limaman farko na masallacin rukunin gidajen 1004 da ke Legas. Sannan a 1995 ya zamo limami na farko na Masallacin Syria da ke Barikin Dodon a Legas. Malam yana da mace fiye da ɗaya da ƴaƴa 10 sai jikoki." https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-55666805 +business Yakin Ukraine: Manyan illolin makaman nukiliya Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon: Shugaban Rasha Vladimir Putin ya umarci sojojin da ke lura da makaman nukiliyar kasarsa su shiga shirin ko-ta-kwana a yakin da kasar ke yi da Ukraine. Hakan ne ya jefa duniya cikin fargaba game da yiwuwar harba makaman na nukiliya, lamarin da ka iya yin matukar illa ga kasashen duniya. Shugaban hukumar makamashi ta Najeriya, Yusuf Aminu, ya yi mana bayani kan illar makaman nukiliya. https://www.bbc.com/hausa/media-60604315 +sports Reece James ba zai buga gasar kofin duniya ba Da kyar idan Reece James zai buga wa Ingila gasar kofin duniya, bayan da Chelsea ta sanar zai yi jinyar mako takwas. Mai shekara 22, wanda ya yi wa tawagar Ingila wasa 15, ya ji rauni a gwiwar kafarsa a wasan da Chelsea ta ci AC Milan 2-0 a Champions League ranar Talata. Nan da mako biyar za a fara gasar kofin duniya, wato ranar 20 ga watan Nuwamba a Qatar, wadda za ta karbi bakunci wasannin a karon farko. Wasu masu tsaron bayan Ingila da ke jinya sun hada da Kyle Walker na Manchester City da Trent Alexander-Arnold na Liverpool. Walker ya ji rauni ne tun farkon watan Oktoba, shi kuwa Alexander-Arnold ya ci karo da koma baya ne a wasa da Arsenal a makon jiya. Walker ya ce yana fatan zai murmure da wuri, domin yana kwadayin buga gasar kofin duniya. Wanda ake sa ran zai maye gurbin shi ne dan wasan Newcastle United, Kieran Trippier. Chelsea ta tabbatar da cewar likitoci sun yi wa dan wasan aiki a makon nan. https://www.bbc.com/hausa/articles/c3g88vl8yv3o +technology Ana bincike kan yadda duwatsun da ke yawo a samaniya suka kawar da kakannin ƙadangaru daga duniya Masana kimiyya da ke Burtaniya na bincike kan yiwuwar ko ba dutse irin wanda ke yawo a sararin samaniya ɗaya ne kawai ya yi sanadin mutuwar kakannin ƙadangaru ba a lokacin da ya faɗo duniya, wataƙila duwatsu biytu ne suka yi sanadin hakan. An daɗe da gano cewa wani ƙaton rami da ke binne a ta wajen Mashigin Mexico ya samo asali ne sakamakon faɗuwar da ƙatoton dutsen da ya faɗo daga sararin samaniya da ya yi a wajen shekara miliyan 66 da suka wuce. Amma masu bincike a Jami'ar Edinburgh Heriot Watt sun ce sun sake gano wani ƙatoton ramin a gefen tekun Atalantika mai irin yawan shekarun. Sun ce akwai wata alamar cewa dutsen samaniyar ne ya yi sanadin wani ƙaton ramin wanda ke ƙarƙashin teku - a gaɓar tekun Guinea a yammacin Afirka. Sun ce mai yiwuwa wani ɓangaren dutsen ne ya faɗa sashen Mashigin Tekun Mexico, amma ba za su tabbatar ba har sai sun binciki na tekun Guinea din tukunna. https://www.bbc.com/hausa/articles/crg848p9vdxo +politics Da za a yi zaɓen gwamna a Kano APC faɗuwa za ta yi - Sha'aban Sharaɗa "Wasu gaggan 'yan jam'iyyar APC mai Mulki a Kano sun kai korefe-korafe ga shugaban jam'iyyar na rikon kwarwa, gwamna Mai Mala Buni dangane da abin da suka kira da neman yi wa jam'iyyar kanshin mutuwa a jihar. A ranar Talata ne wasu ƙusoshin jam'iyyar ciki har da tsofoffin gwamnan jihar ta Kano, Malam Ibrahim Shekarau da Sanata Kabiru Gaya da ɗan majalisar dattijai Sanata Barau Jibrin da ɗan majalisar wakilai, Sha'aban Sharada da wasu manyan ƴaƴan jam'iyyar suka gudanar da taro inda suka yanke shawarar cewa dole ne shugabancin jam'iyyar APC ya taka wa Gwamna Ganduje birki kafin lamura su dagule. Honorabul Sha'aban ya bayyana wa BBC cewa jam'iyyar ta APC a jihar Kano na ƙara nutsewa a ruwa shi ya sa suka ga ya dace su ɗauki mataki saboda gujewa alhaki. ""Mun faɗi abubuwa kamar uku - gaba ɗaya zaɓen da ake cewa an yi daga bangaren gwamnati na shugabannin jam'iyya daga kananan hukumomi da mazaba, mun yi watsi da shi kuma ba mu san shi ba. ""Saboda an dora mutanen da ba su cancanta ba, an cire mutanen da suka dace. Haka ma a zaben ƙananan hukumomi,"" a cewar Sha'aban Sharada. Ya bayyana haka a matsayin rashin adalci kuma ya ce abin da ya ja wasu suka fusata kenan suka gudanar da nasu zaɓen daban da na gwamnati. Ya kuma bayyana cewa da shi da mutanen da suka kai wa Mai Mala Buni ziyara sun barranta kansu daga zaben da gwamnati ke shirin gudanarwa a ranar Asabar mai zuwa. ""Da yawa daga cikin ƴan majalisar jihar Kano, har ma da mutanen da ke aiki da gwamnati kamar kwamishinoni idan ka keɓe da su suna faɗin maganganu marasa daɗ. Mu dai so mu ke a gyara don lokaci bai ƙure ba,"" in ji shi. Honorabul Sha'aban Sharada ya musanta batun cewa shigo-shig ba zurfi suke yi wa gwamnatin jihar Kano ta yanzu. ""In da so muke ta ɓare waɗannan jajirtattun mutane da suke cikin wannan tafiya da sai su yi shiru su riƙe hannunsa (gwamnan Kano) su yi shiru har sai lokacin zaɓe, kamar yadda ragowar ƴan uwanmu su ka yi shiru,"" a cewarsa. Honorabul Sha'aban ya bayyana cewa jam'iyyar APC ta daina farin jini a jihar Kano kuma da za a gudanar da zaɓe a yanzu ba ta yi nasara ba. ""In yau za a yi zaben gwamna a Kano, APC faɗuwa za ta yi. Mu kuma ba ma so ta faɗi,"" in ji shi. Honarabul Sha'aban ya ce Mai Mala Buni ya saurare korafin da su ke je da shi. Sai dai ya ce yana kyautata zaton dama shugaban jam'iyyar na da masaniya kan abubuwan da ke faruwa dama yana jira ne a kai masa korafin. ""Na yi imani mutum ne adali da bai jin tsoron komai kuma zai yi gaskiya,"" a cewarsa. Haka kuma ya ce ko shugabancin jam'iyya bai yi komai kan lamarin ba, da shi da sauran mutanen da suka kai wa shugaban jam'iyyar ƙorafi sun fita har a wurin Allah. Shugaban riƙo na jam'iyyar APC a Kano, Alhaji Abdullahi Abbas ya shaida wa BBC cewa sun ji mamakin wannan taron da aka yi. Ya bayyana cewa su ba su da wata damuwa game da wannan taron kuma zaɓe za a yi a ƙarshen mako kuma duk wanda ya samu nasara za a ba shi dama ya ja ragamar jam'iyyar a matakin jiha. ""Jam'iyyar APC haɗaka ce, kuma kowanne ɓangare an ba shi muƙami daidai da su bisa adalci,"" in ji Abbas. Shugaban na riƙo ya ƙara da cewa sun ji mamaki yadda Malam Ibrahim Shekarau ya halarci taron da aka yi a ranar Talata. A watannin da suka wuce ma sai da wani ƙusa a jam'iyyar APC, Dan Balki Kwamanda ya caccaki salon jagorancin APC a Kano inda ya ce ba za su zura ido a dunga kama-karya ba a cikin jam'iyyar." https://www.bbc.com/hausa/labarai-58915438 +religion Sheikh Sharubutu: Limamin limaman Ghana ya shiga sahun Musulmai 500 masu fada-a-ji a duniya "Limamin limamai na kasar Ghana, Dr Sheikh Osmanu Nuhu Sharubutu, da kuma jagoran kungiyar agaji ta Islamic Council for Development and Humanitarian Services (ICODEHS), sun shiga sahun Musulmai 500 masu fada-a-ji a duniya na shekarar 2020. Cibiyar binciken Musulunci ta Royal Islamic Strategic Studies Center ta kasar Jordan, wadda ta shirya wannan karramawa, ta yi karin bayanin cewa an karrama wadannan mutane ne saboda irin ayyukan agaji da jin kai da suke yi a cikin Ghana da ma yammacin Afirka. 'Yan kasar Ghana na ganin wannan mataki a matsayin abin da Hausawa ke cewa ""alkhairi danko ne ba ya faduwa kasa banza."" A cewar cibiyar binciken Islama ta Royal Islamic Strategic Studies Centre, an zabi Sheikh Dr Osman Nuhu babban limamin Ghana da Shiekh Mustafa Ibrahim suka shiga cikin sahun Musulman duniya 500 da suke fada-a-ji saboda irin ayyukan da suka yi a bangaren agaji, jin kai, da habaka neman ilimi. Suleman Mustapha wani dan jarida ne wanda ya wallafa wannan labari kuma ya yi wa abpkin aikinmu na Fahd Adam karin bayani cewa: ''Na farko dai, babban limami Sheikh Usman Nuhu Sharubutu dukkan ayyukan da ya yi, na zaman lafiya ne. ""Yana hada kan Musulmai da wadanda ba ma Musulmi ba.'' Ya ci gaba da cewa: ""gaba daya al'ummar Ghana sun amince da shi a kan mutum ne mai son yada zama lafiya. ''Yana da taimako sosai, dukkan abin da ya samu yana zuwa ne ga wadanda ba su da galihu. ""Ya bude makarantar koyon ilimin zaman duniya da na koyar da addinin Islama wanda kowa ya amfana da ita. Shi yasa ya shiga cikin malamai 500 a duniya da suke fada a ji."" Kan batun Sheikh Mustafa Ibrahim kuwa, dan jaridar ya ce sananne ne ga al'ummar Ghana. ""Shi ma ya taimakawa al'ummar Ghana, ya gina masallatai da makarantu, da asibiti da rijiya, yana kuma bayar da karatu cikin sauki."" Wannan dai shi ne karo na biyu da babban limamin Ghana Dakta Shiekh Osman Nuhu Sharubutu yake shiga wannan sahun na Musulmai 500 masu fada-a-ji a duniya. Wasu al'ummar kasar sun yi kira ga sauran Musulmai masu hali da su kwaikwayi Sharubutu da Sheikh Mustapha don su ma su samu shiga sahun gaba na masu fada-a-ji a duniyar Musulunci" https://www.bbc.com/hausa/labarai-51192110 +health 'Yadda cutar laka ta hana ni cimma burina na zama likita' "Khadijah Abba, mai shekara 22, ta samu matsalar laka sakamakon wani hadarin mota da ta yi tsakanin Zaria da Kano shekaru 22 da suka gabata. Khadijah ta kasance a cikin tawagar masu buga wa jihar Borno kwallon hannu kuma hadarin ya same ta a kan hanyarsu ta tafiya Italiya. ""Lokacin da muka yi wannan hadari ne na samu wannan larura amma kuma babu abin da gwamnatin jihar Borno ta lokacin ta yi min. Hakan ne ya sa na ma bar garina na Maiduguri na koma birnin Gombe inda nake sana'ar dinki hula sannan kuma jama'a na taimaka min. Na shiga kungiyar masu nakasa tunda dai na riga na samu nakasa.""\nYanzu haka dai Khadijah ba ta iya fitsari sai da robar yin fitsari.\n""Burina shi ne na samu na zama likita idan har na samu aka yi min aiki na samu lafiya."" Yayin da a yau ake tuna wa da masu irin larura, Khadijah na kira ga al'umma da su rungumi masu wannan ciwo kasancewar zai iya samun kowa." https://www.bbc.com/hausa/articles/cv2eezee8mvo +politics Abdulaziz Yari: Mun fi ƙarfin kashi 30 na muƙamai a APC Zamfara "Ɓangaren Abdul'aziz Yari da Sanata Kabiru Marafa sun yi watsi da buƙatar Gwamna Bello Matawalle ta neman raba muƙaman jam'iyyarsu ta APC da kuma na gwamnatinsa. Abdul'aziz Yari wanda tsohon gwamnan Zamfara ne ya faɗa yayin wani taron manema labarai a Abuja cewa su ne ruhin APC a jihar don haka idan ba a su kaso mafi yawa na muƙamai ba, kamata ya yi a raba daidai. A cewarsa, bayan tattaunawa a tsakani, ɓangarensu ya yanke shawarar cewa tayin da Gwamna Bello Matawalle ya yi musu, na su karɓi kashi 30% na muƙaman jam'iyya da gwamnati, ba abu ne mai yiwuwa ba. ""Mu da muke da jam'iyya, mun aminta cewa mu saki kashi 20% (na muƙamai) amma an ba mu shawara cewa a'a, mu yi shi hamsin, hamsin. Mu, mu saki kashi 50%,, shi kuma ya saki kashi 50%,"" in ji Yari. A cewar tsohon gwamnan: ""Amma shi (Matawalle) yana cewa a'a sai dai ya ɗauki kashi 70% na jam'iyya, mu kuma ya sakar mana kashi 30%. Sannan kuma ya ɗauki kashi 70% na gwamnati, (mu) kuma mu ɗauki kashi 30%. Ka ga....ai abin akwai matsala a ciki"". Martanin ɓangaren su Yari ya zo ne bayan wata ziyarar ba-zata da Bello Matawalle ya kai wa Sanata Marafa ne cikin ƙarshen mako a gidansa na Kaduna, inda suka tattauna game da buƙatar raba muƙaman. Abdul'aziz Yari dai ya ja hankali shugabancin uwar jam'iyyarsu ta APC da ke shiga tsakani cikin wannan lamari na raba muƙamai tun bayan komawar Gwamna Matawalle jam'iyya mai mulki a ƙarshen watan Yuni. ""Matsalar Zamfara fa ba irin matsalar Ebonyi ba ce, ba irin matsalar Kuros Riba ba ce. Jam'iyyar APC a Zamfara tana da komai, tana da gwamna, tana da sanatoci, tana da kowa, abin da ya faru mun sani,"" cewar Yari. Ko gobe idan aka yi zaɓe, muna da yaƙini za mu kai labari in ji shi. ""To ba wai wani abu ne da take shakkun za ta iya faduwa ba. Ba wai mazaɓa ba, rumfa. Ba ta shakka!"". A cewarsa, akwai tsari taƙamaimai a ƙasa da saɓa da na sauran jihohi. ""A Ebonyi, ba ma iya cin rumfa, a Kuros Riba ba ma iya cin rumfa, amma tun da aka fara wannan mu'amalar muna iya cin kowannen irn zaɓe a jihar Zamfara. Kuma an kwata an gani,"" in ji jigon jam'iyyar na APC. Ya ce matsayin da suka gabatar wa gwamna Matawalle na raba muƙaman gwamnati da na jam'iyya daidai-wa-daida, shi ne mafi adalci a tsakanin ɓangarorin biyu. Tsohon gwamnan na Zamfara ya kuma zargi uwar jam'iyyar da rura wutar rikici a Zamfara ta hanyar ci gaba da ayyukan rijistar APC duk da umarnin kotu na cewa a dakata. ""Ita jam'iyya duk da an yi wannan, amma ta aika da kwamiti cewa ya je ya yi rijista, abin da kuma an hana ta. Haramtaccen abu ne saboda kotu ta ba da oda,"" cewar Yari. Ya ce odar ta samo asali ne bayan wasu 'ya'yan jam'iyyar sun garzaya kotu, lokacin da shugaban kwamitin riƙon Mai Mala Buni ya sanar da rushe shugabancin APC daga mazaɓu zuwa ƙananan hukumomi." https://www.bbc.com/hausa/labarai-58096046 +entertainment ...Daga Bakin Mai Ita tare da Aisha Najamu ta Izzar So Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon: Daga Bakin Mai Ita wani shiri ne na BBC Hausa da ke kawo muku hira da fitattun mutane kan wasu abubuwan da suka shafi rayuwarsu zallah. A wannan kashi na 45, shirin ya tattauna da Aisha Najamu wadda aka fi sani da Aishar Izzar So, inda ta amsa tambayoyin da suka shafi rayuwarta. Ɗaukar bidiyo da Tacewa: Abdulsalam Usman Abdulkadir Tsarawa da gabatarwa: Halima Umar Saleh https://www.bbc.com/hausa/media-56835012 +health Shin me ke janyo warin balaga? Danna hoton da ke sama domin sauraren shirin: Masana a fannin kiwon lafiya sun bayyana cewa akwai wasu kwayoyin cuta wadanda sukan sa mutum ya yi warin jiki tamkar wani rubabben kifi. Haka kuma wasu cututtuka kamar ciwon hanta da ciwon suga idan suka yi tsanani su ma sukan janyo mutum ya dinga wari kamar warin kifi. Yawancin warin da aka fi sani shi ne warin da matasa ke yi idan suka kawo shekarun balaga, wanda aka fi sani da warin balaga. Mata masu jiki su ma su kan samu warin jiki. Sai dai a jikin mutane akwai wasu wurare da kan yi wari wadanda suka hada da baki da hammata da kuma al'aura. Ko da yake likitoci sun bayyana cewa tsaftace wadannan wurare ta hanyar wanke su da kuma cire gashin da ke nan na taimakawa wajen kawar da warin da ake samu. Wasu masu wannan matsala dai musamman a tsakanin matasa su kan fuskanci tsangwama a tsakanin tsararrakinsu ko a cikin al'umma. https://www.bbc.com/hausa/articles/c80j9qr2vleo +business Ana ce-ce-ku-ce kan yawan bashin da Buhari ke karɓa "Yunƙurin da gwamnatin Buhari ke yi na karɓar rance a gida da wajen Najeriya domin aiwatar da kasafin kuɗin shekarar 2020 ya haifar da ce-ce-ku-ce a ƙasar. A ranar Talata ne majalisar dokokin Najeriya ta amince da buƙatar da shugaban ya aika mata ta karɓar rancen fiye da dala biliyon biyar bayan a watan Afrilu majalisar ta amince ya karɓo rancen naira biliyan 850 daga cikin gida. Gwamnatin APC ta shugaba Buhari ta ce za ta yi amfani da kuɗaɗen da za ta karɓo rancen biliyoyin daloli ne domin cike gibin kasafin kuɗin musamman yadda annobar korona ta katse mata hanzari da kuma ƙalubalen da Najeriyar ke fuskanta ta fuskar kudin-shiga, sakamakon faɗuwar farashin mai a kasuwannin duniya. Amma babbar jam`iyyar adawar kasar da wasu masana na sukar yawan rancen na shugaban wanda suke cewa yana tattare da hatsari ga makomar ƙasar. PDP ta yi zargin cewa bashin da gwamnatin APC ke ci ya wuce kima - zai iya jefa Najeriya cikin wahala, kamar yadda Mista Kola Olabongdiyan sakataren yaɗa labaran jam`iyyar ya shaida wa BBC. ""Ƴunkurin Buhari na sake karɓar bashin sama da dala biliyan biyar, bayan sama da dala biliyon 22 da miliyon 79 da ya yi niyyar karɓa da farko don aiwatar da kasafin kudin shekara ta 2020 ba tare da wani ƙwaƙƙwaran shirin biyan bashin ba, zai rage ƙimar kasarmu,"" in ji shi. Mista Olabongdiyan ya kara da cewa yawan bashin da Najeriya ke karba zai buɗe ƙafa ga hukumomin da ke ba da rance na ƙasashen waje su mamaye bangarorin tattalin arzikin ƙasar. Jam`iyyar PDP dai na fargabar cewa gwamnatin APC na ƙoƙarin jefa Najeriya cikin halin tsaka-mai-wuya ta hanyar mayar da ƙasar tamkar baiwa irin ta zamani, kasancewar ta sarayar da makomar ƴan Najeriya, ta yadda wasu hukumomin ƙasashen waje za su kafa musu ƙahon-zuƙa!"" Amma jam`iyyar APC mai mulkin Najeriyar ta ce bashi hanji ne yana cikin kowa, tun da hatta manyan ƙasashen duniya kan karɓi rance don raya ƙasa. APC ta ce karɓo rancen ba laifi ba ne, kamar yadda Alhaji Ibrahim Masari babban jami`in walwalar jam'iyyar na kasa, ya shaida wa BBC, yana mai cewa ""matuƙar za a yi abin da ya dace da bashin ba laifi ba ne."" ""Kamata ya yi ƴan adawa su sa ido idan har adawar za su yi su ga abin da aka ce za a yi da bashin da za a ciwo idan ba a yi ba sannan suke da bakin magana,"" in ji shi. Wasu masana tattalin arziki a Najeriya, irin su Dr Shamsuddeen Muhammad malami a jami`ar Bayero ta Kano na dasa ayar tambaya a kan hanzarin da gwamnati ke kawowa wajen karɓar rancen. Dr Shamsudden ya ce a jimlace ƴan kwanakin nan bashin da gwamnatin APC ta ke shirin karɓa ya haura naira tiliyan 5. Kuma ba ya wuce naira tiliyan biyar zuwa shida a shekara na kudaden shiga da Najeriya ke samu. ""A kasafin kudin 2020 kusan naira tiriliyan uku zai tafi ne a bashi. kusan kashi 30 cikin 100 zai tafi ne a biyan bashi. Kuma ana bin Najeriya bashin kusan naira tiliyan 28,"" in ji shi. Masanin ya yi gargadin cewa idan bashi ya yi yawa durkusar da kasa yake yi maimakon farfado da ita. Ga alama za a ci gaba da tabka muhawara a kan rance da gwamnatin shugaba Buhari ke karba. Wasu na ganin cewa maimakon cin bashi don cike giɓin kasafin kuɗi, kamata ya yi gwamnati ta taƙaita kasafin kuɗin daidai ruwa daidai gari, yayin da wasu kuma ke ganin sai an hada da rance za a farfado da tattalin arzikin kasar. Wasu kuma na bayyana damuwa kan yadda idan an karɓi rancen da wuya a ji duriyarsa, duk kuwa da shaidar da aka yi wa shugaban kasar ta gudun duniya da kyamar cin hanci da rashawa." https://www.bbc.com/hausa/labarai-52914230 +religion Burin mata na zama limaman coci ya fara cika "Anne Tropeano na goge tufafin da za ta sanya, domin tanadin yadda ranar za ta kasance gare ta. Ta ɗaga doguwar farar rigarta, da wani maɗauri na musamman da malaman coci ke amfani da shi a sassan duniya. Ta duba kalandar da ke saƙale a bango, ta yi rubutu ɓaro-ɓaro a jikin kwanan watan da abin rubutu launin ja, ya nuna gobe ''ranar karɓuwa ce.'' Tana kuma riƙe da wayar tarho don hayar ƙarin jami'an tsaro da za a baza a ciki da harabar cocin da ke Albuquerque, a jihar New Mexico, inda take zaune, saboda ko-ta-kwana idan an ta da hatsaniya. ""Batu ne da ya janyo ce-ce-ku-ce, ba kowa ne ke na'am da wayar gari a kira mace matsayin limamiyar coci ba.'' Ita fa Tropeano ba komai take tsoro ko gujewa ba, sai tashin hankali. Tun lokacin da ta fara bayyana muradinta na zama malamar coci, take fama da matsaloli ciki har da na cin zarafi a shafin intanet. Tropeano ɗaya ce a cikin sama da mata 250 a duniya da ke neman zama wani ɓangare na jagorancin cocin Roman Katolika, wasu dai na kallon hakan tamkar wani yunƙuri ne na fito na fito da limamai maza. Cocin Katolika ba ta amince da limamai mata ba. Hasali ma, Batikan na kallon hakan a matsayin babban zunubi, da aka tanadi tsattsauran hukuncin a kai. Hakan na nufin da zarar an zo tantance shi ke nan ba sa iya zuwa komai ciki har da jana'iza. Wasu dai na ganin kama daga Yahudawa har zuwa sauran addinai bai dace mata su yi limanci ba. Amma duk da haka, matsayin Cocin Katolika na haramta wa mata zama limamai ya sha banban da na sauran, misali idan mace ta daɗe a kan layin tun tana 'yar ƙarama. Sai kuma wani batun da suke yi shi ne a littafi mai tsarki na Bayibul, Yesu Almasihu ya zaɓi duk mataimakansa 12 daga jinsin maza, bai ɗauki mace ko ɗaya ba, kuma tun daga wancan lokacin cocin katolika ke koyi da abin da Yesu ya shimfida. Amma ga Tropeano, lamarin ya wuce haka. ""Bisa tarbiyar koyarwar Coci, da ayyukan da take gabatarwa ana nuna muhimmancin mata. Mata na koyar wannan, haka yara, don haka duk inda mace ta shiga tana da wata ɗaukaka."" A shekarar 2002 ne aka fara gangamin ganin mata sun shiga sahun limaman coci. Wata ƙungiya mai ɗauke da mata bakwai, sun shiga gangamin hakan cikin jirgin ruwa a kogin Danube, don kauce wa rikicin addini. Duk da haka, akwai rahotannin da suka bankaɗo wasu sirrika na baya game da naɗin mata, misali kamar Ludmila Javarova an naɗa ta limamiyar cocin Czechoslovakia a shekarun 1970, ta kuma shiga rukunin bishop-bishop na cocin Katolika. Gangamin da mata ke yi na ganin an dama da su a cocin Roman Katolika an fi yi ne a ƙasashen Turai da Amurka, duk da yake an fara ganin tasirin yaɗuwar sa a sauran ƙasashe. Mace ta farko da ta rike irin wannan muƙami, ita ce Olga Lucía Álvarez Benjumea ta Colombia, ita ce mace ta farko da aka naɗa Limamiyar Cocin Katolika, mai mabiya sama da miliyan 1.3 sassan duniya. Bikin nadinta a shekarar 2010, an yi shi ne a asirce, amma ta ce ta samu gudunmawar ƙananan majami'u; ""Cikin waɗanda suka zo akwai wani bishop na ɗarikar katolika, wanda ba zan bayyana sunansa ba saboda dalilan tsaro…."" ""A tsorace nake, saboda mutane za su fara min wulaƙanci da rashin mutunci, wataƙil har da jifa na idan ina wucewa a cikin coci, musamman a wannan sabuwar duniyar ta masu tsaurin ra'ayin addini. ""Amma irin goyon bayan da mutane suka nuna min ba zai misaltu ba, sun ba ni ƙwarin gwiwa, kuma sun tsaya min a lokacin,"" in ji Álvarez. A yanzu an ƙara mata girma zuwa bishop ta Roman Katolika kuma a yanzu Batikan ta amince da ita. Álvarez ta fito daga gidan addini sosai na Katolika, ta kuma samu goyon bayan dan'uwanta limamin coci, yayin da mahaifiyarta ta kasance mi hidima ga cocin. Dan'uwanta ya ba ta kyautar da take kallo a matsayin toshiyar baki. Álvarez ta kafe cewa babu a inda Littafi Mai Tsarki ya ware mace, da haramta mata wasu muƙamai ko kai wa wani matsayi. Babbar darakta Kate McElwee, ta ce bin da ya fi ba ta sha'awa a aikin da take yi shi ne kasancewa a wani sashen ba da agaji da taimako, inda take ganin tarin masoya da masu goyon baya. Ana sakin hayaƙi launin ruwan hoda da ke fara fita kafin jerin gwanon motocin Paparoma su taho a duk lokacin da zai zagaya gari. 'Yan sanda sun taɓa kama su lokacin da suka yi shigen hakan tare da tsare su tsawon kwanaki. ""Muna tafe da matan, lokacin da suke cikin hutu, sun tsaya jiran a buɗe ƙofar Fadar Batikan, don su ƙalubalance su da laifukan d suke aikatawa na baɗala,"" in ji McElwee. ""Amma ga wasu matan ba za su taɓa yi ba, saboda tsoro, yadda muke ƙwalla ihu da kiran sunan Allah, ba su da zaɓi face su buɗe mana ƙofa."" An rufe kofa Bayan an yaɗa labarin abin da ya faru, sai babban malamin coci Cardinal Joseph Ratzinger, wanda daga bisani ya zama Fafaroma Benedict, ya ayyana cewa tun da matan ba su nuna wata alama ta karaya ko nadama ba, kan laifukan da suka aikata, to an zartar da za su fuskanci hukunci. Fafaroma Francis da kansa ne ya zartar da hukuncin naɗa mace ta farko a matsayin limamiya. A shekarar 2016, da aka tambaye shi ko akwai yiwuwar wani sauyi, ya ba da misali da shekarar 1994 a zamanin Fafaroma John Paul II kan cewa ""an rufe ƙofar"" barin mata su yi shugabanci irin wannan, kuma Fafaroma ya tabbatar da haka. Malama Nathalie Becquart, ta yi aiki a ofishin Fadar Batikan, tana da hoton da aka ɗauke su tare da Fafaroma Francis tana tsaye a bayan shi. A watan Fabrairu 2021, ita ce mace ta farko da ta riƙe matsayin mataimakiyar sakataren ba da shawara ga Fafaroma.\n \nTa bayyana halin da mata limaman coci ke ciki a halin yanzu da cewa akwai abin damuwa, amma ta zaɓi yin shiru ne saboda muƙamin da take riƙe da shi. ""Ina ganin ya dace mu faɗaɗa tunani da hangenmu kan ainihin koyarwar cocin. Akwai hanyoyi da dama da mata za su iya aiki da hidima a coci, Ba tare da an yi fito na fito ba,"" in ji Becquart. Amma kuma ta amince ba lamari ne mai sauƙi ba, kawo irin wannan sauyi a lokaci guda, a ko da yaushe fargaba da tsoro kan ɗarsu a zukatan mutane. •Bisa ɗabi'a ta Cocin Katolika, abin da suka yi haramtacce ne kuma ya saɓa wa doka. sun kare matakin da cewa namiji ɗaya da aka yi wa wankan Baftisma, yana kasancewa a tafarkin dokokin kotun katolika. (Canon 1024). •A shekarar 2021 an yi wa dokokin Cocin Katolika kwaskwarima, Duka dai kan batun bai wa mata jagoranci. Babu wani wuri da ya nuna ɗaukar mataki a kai. •A baya-bayan nan Fafaroma Francis ya nuna alamun buɗe wata kafa da za a samu matan to amma akwai abubuwan da ba za su iya yi ba. Cikin abin da za su yi an amince su halarci ɗaurin aure a matsayin shaidu, da kuma jana'iza. •A wani mataki na bazata, Fafaroman dai ya buƙaci jin ra’ayi mabiya ɗariƙar, kan yadda suke kallon lamarin da kuma makomar Cocin nan gaba. Za a yi ta jin bahasin jama’a daga nan har zuwa shekaru biyu masu zuwa. •Wani bincike da aka gudanar ya nuna rawar da mata ke takawa a Cocin, ana kuma sa ran tattauna kan haka a Babban taron da za a yi cikin watan Oktoban baɗi. •'Yar uwa Nathalie Becquart ta shaida wa shirin BBC na fitattun mata 100, cewa bayan nan ne Fafaroma zai san matsaya ko matakin da za a ɗauka. Anne Tropeano ta tunkari duk wanda aka san ya ba da matsayin malami a coci, ciki har da bishop ɗin ta, kuma ta tabbatar masa cewa ta shirya. Rana ce da ta daɗe tana jira tsawon shekara 14. Ranar da za ta zama malamar coci kamar sauran da suka daɗe suna addu’o’i. A lokacin taron, bishop ɗin ya ce ya sassauta wa Anne Tropeano ne don yi wa sauran jagora. Tare da gabatar da ita a matsayin sabuwar limamiya. Tropeano ta ce farin ciki ya baibaye zaciyarta, Kasancewar ta sabuwar fuska a cocin. Lamarin da ba kasafai ake gani ba." https://www.bbc.com/hausa/articles/c03ny43l0wzo +business Abin da gwamnatin Najeriya ke fatan cimma da ziyarar Anthony Blinken Yayin da Sakataren Wajen Amurka Anthony Blinken zai sauka a Abuja, babban birnin Najeriya a ci gaba da ziyarar kasashen Afirka uku a wannan Alhamis ɗin, ga alama Amurkar ta cire Najeriyar daga jerin kasashen da take zargi da tauye 'yancin addini. Labarin cire Najeriya daga cikin ƙasashe shida wadanda a shekarar ta 2020 Amurkar ta yi musu lamba ta kasancewa wadanda suke tauye 'yancin addini labari ne da zai dadada wa hukumomin kasar. Domin hukumomin Najeriyar za su karbi wannan babban bako nasu da faran-faran, abin da kuma ba zai yi wa masu ja da hakan ba dadi. Babu dai wata sanarwa da ta fito ta musamman karara ta bayyana matakin daga walau Amurkar ko kuma gwamnatin Najeriya, kan abin da ya kai ga zare sunan Najeriyar daga kasashen da Amurkar take yi wa wani kallo na musamman saboda sun sa kansu ciki ko suna kau da kai ga tsagwaron keta 'yancin addinai. Wata sanarwa ce Amurkar ta fitar ranar Laraba, wadda ke dauke da sunayen ƙasashen da Amurkar ta sa cikin kundinta na bana, 2021 na masu tauye hakkin addinai sai kawai aka ga ba sunan Najeriyar a ciki. Sai dai ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP na masu ikirarin jihadi da ke harkoki a yankin arewa maso gabashin ƙasar sun ci gaba da kasancewa a jerin wadanda Amurkar ke nuna damuwa ta musamman a kansu. Mista Blinken na ziyartar Najeriya ne daga ranar Alhamis din nan, a zango na biyu na rangadin ƙasashen Afirka uku da ya faro, cikinsu har da Kenya da Senegal. Kakakin shugaban Najeriya, Mallam Garb Shehu, ya ce suna murna ainun da wannan ziyara kasancewar Amurkar ta ba wa Najeriyar matsayin da ya cancanceta a wannan karon, ba kamar a baya ba. Ya ce, ''Mu abin da ya ba mu sha'awa shi ne, akwai sako na sabuwar gwamnatin Joe Biden na Amurka, sako ga daukacin al'ummar Afirka. ''Kuma aka ce Najeriya aka zaɓa don a zo a yi wannan jawabi, don a isar da shi ga al'ummar Afirka. Wannan Akwai jawabi da Mista Blinken zai gabatar.'' ''Wannan manuniya ce ga irin fifiko da martaba da gwamnatin Amurka mai ci yanzu ta dora da martaba da daraja da take ganin gwamnatin Buhari a duniya baki ɗaya. Lokacin da Obama ke mulki ai an yi irin wannan jawabi ba a neme mu ba, a Egypt aka je ak yi irin wannan jawabi,'' in ji Garba Shehu. Batutuwan da ake fatan cimma Ana sa ran Mista Blinken zai gana da Shugaba Muhammadu Buhari don tattaunawa kan yadda ƙasashen biyu za su inganta ayyukan haɗin gwiwa a fannin kula da lafiya na duniya da tsaro da bunƙasa hanyar samun makamashi da haɓaka tattalin arziƙi. Najeriya tana fama da barazanar tsaro mai yawa ciki har da yaƙin ta-da-ƙayar-baya na Boko Haram sama da shekara goma da rikice-rikicen ƙabilanci da ɗumbin satar ɗalibai daga makarantu da gungun 'yan bindigar da ake kira 'yan fashin daji ke yi. A lokacin da yake Abuja, Sakatare Blinken zai kuma gana da masu sana'o'i ta intanet a Najeriya. An ayyana Najeriya cikin ƙasashen da ake ƙara tsuke sararin watayawar fararen hula saboda batutuwa kamar zaluncin 'yan sanda wanda ya harzuƙa gagarumar zanga-zanga a bara. https://www.bbc.com/hausa/labarai-59328823 +business Harajin VAT: Abin da ya jawo ce-ce-ku-ce tsakanin jihohi Najeriya da gwamnatin tarayya akan haraji "Ana ci gaba da ce-ce-ku-ce tsakanin gwamnatocin jihohin Najeriya da gwamnatin Tarayya kan tsarin karɓar kuɗaɗen haraji kan kayayyakin more rayuwa a faɗin kasar. Wannan ya biyo bayan bukatar da wasu jihohin kudancin kasar, ciki har da Legas, suka bayyana na a ba su damar karɓar kuɗaɗen haraji a matakin jihar domin kara musu kuɗaɗen shiga. Da dama daga cikin jihohin da ke son a ba su wannan dama na ganin ita kadai ce za ta warkar da su daga dumbin matsalolin tattalin arziki. Sannan akwai jihohin da ke cewa idan aka ba su damar karbar kudaden harajinsu zai taimaka musu ba a fannin samar da ayyukan yi kadai ba, har da ci gaba da kuma rage dogaro da gwamnatin Tarayya. Sai dai gwamnatin Tarayya na nuna turjiya kan aminta da wannan tsarin da jihohi ke daga jijiyoyin wuya a kai. VAT haraji ne kan kayayyakin more rayuwa da ake iya ganinsu wanda gwamnati ke karɓa karkashin tsarin karɓar harajin haɗin-gwiwa tsakanin gwamnatin Tarayya da na jihohi da kananan hukumomi. Jihohin da ke wannan hankoro na son a ba su damar tafiyar da haraji a kan kayayyaki wato VAT, da gwamnati ke karɓar kashi 7.5 cikin 100 kan kayayyaki. Jihohin na son duk wani kaya ko ciniki da aka yi tsakanin yankunansu ko kuɗaɗe ya zama mallakar gwamnatin jihar domin gudanar da ayyukan ci gaba. Gwamnatin Najeriya ta hannun hukumar tattara kuɗaɗen haraji ta tarayya take karɓar haraji a duk wani kaya ko ciniki ko ayyukan kasuwanci, sannan sai a kasafta kuɗin tsakanin gwamnatin tarayyar da jihohi da kananan hukumomi. Sai dai wasu jihohin da ke fafutikar ganin tsarin ya sauya na cewa hakan ya saɓa dokar tattara kuɗaɗen haraji na VAT, saboda akwai cutuwa a ciki. Jihohin Ribas da Legas da wasu sauran jihohi hudu na Najeriya ke kan gaba wajen sama wa Najeriya kashi 80 cikin 100 na kuɗaɗen harajin VAT a faɗin ƙasar. ________________________________________ Yadda ra'ayoyin jihohi ya bambanta kan harajin Wasu daga cikin jihohi da kawo yanzu aka ji daga gare su irin su Akwa Ibom da Adamawa sun nuna goyon-bayansu ga gwamnan Ribas, Nyesom Wike da ke son kotu ta hana gwamnatin tarayya karba ko cin moriyar wadanan kuɗaɗe na haraji. Jihohin na ganin cewa karbar harajin da gwamnatin tarayya ke yi na rage musu 'yanci da dogaro kan kuɗaɗen da gwamnatin ke warewa jihohi. Wannan dalili ya sa 'yan majalisar dokokin jiha a Akwa Ibom ke aiki kan wani daftarin doka da zai bai wa jiharsu damar tattara kuɗaɗenta na haraji. Haka zalika jihar Legas, ta ce ita ma kudiri na gaban majalisa wanda tuni ya tsallake karatu na biyu a gaban majalisar jihar. Sai dai gwamnatin Ekiti da Osun da Benue da Bayelsa da Gombe na cewa suna bukatar lokacin domin sake nazari kan batun don yanke hukunci. Wata kotun tarayya a Fatakwal tuni ta bayar da umarnin cewa gwamnatin Ribas na da damar tattara kuɗaɗen harajinta. Sai dai dukkanin waɗannan jihohi na fuskantar tsaiko daga hukumar tattara haraji ta Tarraya wato FIRS da ke kalubalantarsu har a kotu. ________________________________________ Harajin VAT na iya sauya tattalin arzikin jihohi? A tattaunawarsa da BBC, Dr Isa Abdullahi masani tattalin arziki a Jami'ar Kashere ta Jihar Gombe, ya ce bisa tsarin dokokin Najeriya kafin takaddamar jihohi kashi 52 cikin 100 na kuɗaɗe na zuwa asusun gwamnatin Tarraya. Sannan kashi 26 cikin 100 na jihohi, kanana hukumomi kuma kashi 20 cikin 100. Dr Isa ya ce, ana ta samun korafin daga jihohin da ke son a kara musu kason da ake warewa domin haɓaka tattalin arzikinsu da ya yi kasa. ""Gwamnatocin da ke son a bar musu kuɗaɗen irinsu Legas da Ribas babu shaka tattalin arzikinsu zai bunkasa, sai dai wasu jihohi marasa karfi na iya fuskantar kalubale. ""Akwai jihohi masu matsala kan sarrafa kuɗaɗen shiga don haka idan aka sakar musu kuɗaɗen ba lallai a ga wani ci gaba ba, akwai yiwuwar rijiya ta bayar da ruwa guga ta hana."" Sannan masanin na cewa ba ta VAT kawai jiha za ta iya bunkasa tattalin arzikinta ba, domin akwai wasu abubuwa da dama da ka iya taimakawa haɓakarta. Ya bayar da misali da ma'adinai da albarkatun kasa da noma da wasu sana'o'in. ________________________________________ Dr Isa ya ce babu laifi idan aka sakarwa jihohi damar tattara kuɗaɗensu na haraji, sai dai abin fargaba anan shi ne tsarin da ake tafiya a kai a wannan lokaci. Masanin ya ce akwai jihohi masu karfi da dabarun sarrafa kuɗaɗen da bunkasar tattalin arziki, sannan akwai jihohin da idan ba wannan tsarin aka ci gaba da shi ba za su shiga mawuyancin yanayi. Ya ce ""dama idan aka tara kuɗaɗen ana rabawa ne ba tare da la'akari ko bai wa wata jiha fifiko ko amfani da iya abin da ta samar wajen ware mata kuɗaɗe,"" in ji shi. Amma a cewar Dr Isa idan aka sakarwa wasu jihohin kudanci su tafiyar da harkar, akwai yiwuwar arewa a fuskanci raɗaɗi, muddin ba a tashi tsaye ba wajen bijiro da sabbin hanyoyi samun kuɗaɗen shiga. Sannan ya ce tsarin rage nauyi ne ga gwamnatin tarayya amma hakan zai rage mata kuɗin shiga da karfin aiwatar da wasu manyan ayyuka. Masanin ya ce ƙasar da suka samu ci gaba babu shakka na bin wannan tsarin, amma yanayi lamuran Najeriya da rashawa ta yi kaka gida akwai fargaba a kan batun. ________________________________________ Gwamnatin mulkin soja karkashin jagorancin marigayi Janar Sani Abacha ce dai ta fito da wannan tsarin haraji inda ake karbar kashi biyar cikin dari kan kayayyakin da aka saya. Amma gabanin saukarsa daga kan mulki a shekarar 2003, tsohon shugaban kasar Cif Olusegun Obasanjo ya kara harajin zuwa kashi goma cikin dari. Sai dai gwamnatin marigayi Shugaba Umaru Musa 'Yar Adua ya komo da harajin zuwa kashi biyar cikin dari bayan kungiyar kwadago ta bayyana rashin jin dadinta. Kafin daga bisani gwamnatin Shugaba Buhari ta mayar da shi kashi 7.5 cikin 100 a 2020, lamarin da masana suka ce shi ya kara haddasa tsadar kayayyaki a kasar. A yanzu idan aka sakarwa jihohi watakil harajin ya iya bambanta tsakanin jihohi, kuma akwai yiwuwar manyan jihohin da ke kan gaba wajen kasuwanci su za ci moriyar tsarin. Amma a yanayin da ake ciki yanzu gwamnatin Tarayya na nuna turjiya kuma abu ne mai wuya ta amince da wannan tsarin nan kusa, a cewar masana. ________________________________________ _______________________________" https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-58486321 +sports An ci gaba da yi wa Maguire ihu fiye da wanda aka yi a baya Luke Shaw ya ce an ci gaba da yi wa dan kwallon tawagar Ingila da Manchester United, Harry Maguire ihu fiye da wanda ake yi masa a baya a fannin tamaula. Kyaftin din Manchester shi ne ya yi kuskuren da Jamus ta ci kwallo biyu a wasan Nations League da Ingila ta tashi 3-3 ranar Litinin a Wembley. Ana ta kalubalantar kociyan tawagar Ingila, Gareth Southgate kan gayyatar Maguire da yake yi, wanda United ta ajiye a benci daga baya da fara kakar bana. Maguire baya kan ganiya a wasannin da yake yi wa tawagar Ingila da Manchester United - an yi wa dan wasan ihu a wasan sada zumunta da Ingila ta doke Ivory Coast a cikin watan Maris. A cikin watan Afirilu 'yan sanda suka bincike gidan Maguire, wanda wani ya yi masa barazanar dana masa bam - batun ya girgiza mai tsaron bayan United. Haka kuma an yi wa kyaftin din United ihu a lokacin atisayen kungiyar a Australia - wanda ya buga wasa uku a Premier League ta kakar nan. Duk da haka kociyan Ingila, Southgate ya ci gaba da bai wa Maguire goron gayyata, domin tsare masa baya, dalilin da ake kalubalantar kociyan kenan. https://www.bbc.com/hausa/articles/crgdv27yvlwo +entertainment Daga bakonmu na mako: 'Yadda kallon fina-finan Indiya ke ɗauke wa mata hankali a Najeriya' "Wannan maƙala ce ta musamman daga baƙuwarmu ta mako: Aisha Ya'u Kura, marubuciya kuma tana karata Lissafi a Jam'iar Jihar Kaduna. Tan a da aure da ƴaƴa biyar. Kallace-kallacen shiri mai dogon zango na Indiya ya zama ruwan dare a faɗin duniya.. Soyayyar su ta yi tasiri a zuƙatan manya da yara da mata da wasu mazan a Afrika, ya kuma ƙetaro Najeriya har ya zarto arewacin ƙasar, wanda har hakan ya daƙushe tasirin kallon fina-finan Hausa. Da fari a wata tasha mai suna MBC Bollywood ita ce tashar da ta fi kawo shirye-shiryen fina-finan Indiya da ake cewa series da harshen Larabci. Zuwan Zee world sai ya soma daƙushe kallon tashar saboda da yawa an fi fahimtar yaren Turanci a kan Larabci a wannan lokacin. Ganin karɓuwar wadannan fina-finai ya sanya wasu tashoshi na arewa fara fassara su da harshen Hausa domin samarwa Hausawa saukin fahimtar abun da ake yi, kuma ake faɗi a cikin shirin. Kowanne abu na duniya akwai alkhairin da ke cikinsa, kazalika akwai illolinsa.. Zan iya cewa illolin da wadannan fina-finai suke yi mana a arewacin Najeriya ya fi alkhairansu yawa. Mu kawo Zee world a farkon fari, a yanzu ana fara shirye-shiryen Zee World tun daga karfe uku na rana har karfe 11 na dare. Da yawa, ban ce duka ba, akwai matan da ba sa barin gaban talabijin ɗinsu har sai wannan karfe 11 musamman idan an bar wutar lantarki ko da halin tayar da injin yayin da aka ɗauke wuta. Wasu kuma in kaga sun dauke idanunsu daga gaban talabijin to an tafi talla ne, shi ne za su tashi a gurguje su je su yi abin da za su yi kafin a dawo, ciki har da gaida Allah SWT wanda ya halicce mu kuma ya ba mu aron rai da lafiyar da muke kallon da shi. Wasu matan ko girki ba za su ɗora ba, wasu kuma su manta sun ɗora har sai ƙaurin abincin ya addabi hancinsu, komai za su yi a dan tsukukun mintinan tallan za su je su yi shi da sauri domin kar kallon ya wuce su ko da na daƙiƙa ɗaya ne. Wasu kuma ba za su ɗora girkin ba, sun gwammaci su kwanta su yi ta kallon har mijin nasu ya dawo, a gaggauce su dafa masa indomie ta hanyar yin ƙaryar ba sa jin daɗin jikinsu ne. Abu mafi muni a cikin illar shi ne; Daga wannan ƙarfe 11 da suka gama kallon shirye-shiryen, za su fara maimaici saboda wanda bai samu damar kallo ba ya kalla, wasu na iya fara maimaicin tun daga karfe 12 na dare har asuba sannan su kwanta. Sannan a daren ranar Juma'a, tun daga 12 na dare za su fara maimaicin shirin satin, in ya wuceka za su hade maka shi ka kallesu baki daya, a daren da ya kamata mu miƙa wuya ga Allah, a wannan daren muke miƙawa fina-finan nan idanuwanmu da ruhinmu gangar jikinmu gurin kallon wasanninsu. Allah bai kawo mu duniya domin wasa ba, amma mun shagaltar da kanmu gurin yin wasan har ta kai mu ga kwaikwayonsu. Wadannan kallace-kallacen har wata mai alfarma bai bari ba, domin a lokacin ne ma shaidan ke sake sabon salo na kiɗansa, sai mu ƙi yin kallon a lokacin da ake yi, sai mu ce da daddare za mu yi kallon in muna Tahajjud. ""Innalillahi wa inna ilaihir rajiun"" Ni din nan da nake wannan rubutun ni ma a da hakan nake, sai dai mu ce Allah ya tsare mana imaninmu. Illolin da wadannan shirye-shiryen suke yi a tsakanin ƙananan yara da matasa mata da al'umma baki daya Mata su ne ginshiki, tubalin tarbiyar yaransu, mace ita ce tsani na tarbiyyar iyali, wanda masu iya magana kan ce, idan ka ilimintar da mace tamkar ka ilimantar da alumma ne. Kowanne dan adam a hannun mace ya taso, kuma a hannunta zai ƙare rayuwarsa, amma a wannan lokacin da kallace-kallace suka yi yawa sam mun manta da tarbiyyar ƴaƴanmu, mun miƙa musu ragamar komai su yi da kansu yayin da muke kallo, sai ka ji wasu na cewa, ""Ku tashi ku je dakinku ku yi kallo, ko ku fita waje ku yi wasa"". Ko kusa ba ma bibiyar rayuwarsu, mu dai su bar mu mu yi kallonmu su kuma su je su yi wasansu wanda mu kanmu ba mu san wane iri wasa suke yi ba, daga haka sai ka ga yaro ko ya je makaranta ba shi da wani sukuni sai na bai wa abokan karatunsa labarai a kan fina-finai. Sai ka ga yara da ƙananan shekarunsu sun yi gungu suna fadin: ""Jiya Mayank ya ce yana SON Gunjan, au ba ku ga wurin ba? Nan za su fara ba da labarin irin abun da suka gani wanda su masu shirya fim ɗin a gurin su suke ganinsa ba komai ba ne, to daga nan shikenan tarbiyya ta tafi a haka, yara sun taso sun saba da kallace-kallace wanda har za su dinga aiwatar da shi a tsakanin su da sunan wasa. Wannan ma babban sakaci ne a garemu iyaye mata, domin tarbiyyarsu da tamu ba daya ba ce, su a gurinsu raina iyaye ba komai ba ne, to in yaro ya tashi da shi shi ma zai ga ba koman ba ne. Sannan ga ƴan mata matasa masu tasowa, za ka ga sun raina duk wani namiji da zai zo gurin su, duk abin da zai yi mata da niyyar burgewa sai ta ga sam bai kamo kafar SIDDART KHURANA ba. A nan fa yarinya za ta shiga bulayi har ta tsaya kallon ruwa kwaɗo ya yi mata kafa, daga nan sai a shiga damuwa a ce ai wance ba ta yi aure ba, ko dai aljanu ne suka shafe ta. Abin da ba mu sani ba shi ne lokacin da budurci ya tatsowa mace, in har ta tsaya ruwan ido to tabbas za ta shiga jerin matan da suka yi kwantai wanda za su yi auren a ƙagauce ba tare da tantacewa ba.. SIDDART da SALIHU akwai banbanci, haka ""Indiya da Najeriya"" ban ga ta inda harafi ko furuci ya haɗa su ba. A yadda wasu fina-finan suke zuwa da zallar makirce-makirce hakan yana sa yara mata koyon wadannan salon ba tare da duban illarsu ko halaccinsu a addininmu ba, mu dai mun ga wasu a ciki sun yi sun ci riba, mu ma bari mu gwada. Mukan manta cewa su ma shirya shi suka yi, tsara labarin aka yi, mu dai kawai tun da an yi, bari mu ma mu yi, wanda hakan sai ya jefa mutum cikin da na sani marar amfani. Ko a cikin al'umma wadannan shirye-shiryen sun yi tasiri ta hanyar koyar da salon sata da satar mutane don kudin fansa da mugunta da salon makirci da dai sauran su. Illoli da sharrance-sharrancen fina-finan nan yawa ne da su, alkhairansu bai wuce dauke mana hankali daga gulmace-gulmace da surutai marasa amfani wanda shi ma illa ce babba a garemu. Shawara garemu mata, ko za mu yi wadannan kallace-kallacen ya zam mun sauke duk wani hakki da ya rataya a wuyanmu, sannan mu ragewa ƴaƴanmu yawan yinsa, mu kuma cire wa Ubangijinmu lokacinsa, domin lokacin Ubangiji ya fi duniya da abun da ke cikinta, mu yawaita yin istigfari da hailala yayin kallon, mu kanmu a cikin zukatanmu za mu ji nutsuwa yayin yin hakan. Allah ya tsaftace zukatanmu ya tsayar da mu a kan addinin Allah na gaskiya, kuma ya dauwamar da zukatanmu gurin bauta masa." https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-55368503 +health Kanunfari na motsa sha'awa ga mata da maza da kuma jinkirta tsufa Kanunfari fitaccen sinadari ne da galibin mutane ke amfani da shi wajen girki da sha da kuma wasu abubuwan na inganta lafiya da jin daɗi. Ana amfani da itacensa ko ganyensa ko busasshe a sarrafa su domin biyan bukatu daban-daban a ko ina a faɗin duniya. Ko da yake galibin Larabawa ko al'ummar yankin ƙasashen Asiya sun fi amfani da shi. Sirrin shan ruwan kanumfari Masana harkokin lafiya sun bayyana amfanin wannan sinadari na kanunfari a rayuwar dan adam. A tattaunawarsa da BBC, wani likita a Najeriya Dr Ibrahim Badamasi, ya ce ruwan kanunfari na da amfani sosai ga lafiya saboda yana ƙunshe da sinadaran da ke yaƙi da cututtuka da bunƙasa garkuwar jiki. Ruwan kanunfari na taimakawa wajen saurin narkewar abinci da hana cutar ulcer. Yana taimakawa lafiyar haƙora da hana kumburin dadashi da fitar da jini. Sannan ruwan kanunfari na taimakawa wajen rage ƙiba da teɓa. Yana maganin jiri da cutar kwalara. Sannan yana taimakawa wajen saisaita sukari a cikin jini da lafiyar hanta saboda yana ƙunshe da sinadaran da ke hana lalata ƙwayoyin halitta. Amfanin kanunfari ga mata Amfanin kanunfari ga mata da maza kusan guda ne. Binciken da masana kimiyya da dama suka yi ya nuna cewa kanunfari na ƙara wa mata da maza ni'ima. Kanunfari na da amfani ga mata wajen inganta ��wan haihuwa, sannan yana taimakawa wajen shawo kan matsalar rashin daukar ciki. Kanunfari na bunƙasa isar wasu saƙonni ga ƙwaƙwalwa waɗanda ke motsa sha'awa ga mata da kuma maza. Kanunfari na ƙara wa mata kuzari lokacin jima'i. Baya ga taimakawa wajen rage jiki yana sa rashin tsufa. Man kanunfari na taimaka wa mata wajen samun sauƙin ciwon mara a lokacin al'ada da taƙaita kwanakin al'adar. Amfanin kanunfari ga maza Kanunfari na ɗaya daga cikin magungunan gargajiya da ke ƙara wa maza lafiya domin kuwa yakan ƙara yawan sanadarin 'testosterone' wanda ke tasiri wajen haɓakar gaɓoɓin saduwa na namiji. Rashin isasshen sanadarin 'testosterone' a jikin namiji na iya haifar masa da matsalar rashin ƙarfin mazakuta, wanda kan rage masa ƙarfin sha'awar saduwa. Kanunfari kan inganta tafiyar maniyyin namiji. Yana kuma ɗauke da sanadarai da ke ƙara yawan maniyyin da namiji ke samarwa, wanda hakan shi ne abu mafi amfani ga lafiyar maza. Bugu da ƙari kanunfari kan magance matsalar saurin fitar maniyyi ga namiji a lokacin saduwa, matsalar da ke yawan faruwa ga maza sanadiyyar gajiya ko kuma wasu matsaloli na daban. Mai da ake samu daga kanunfari na ƙara ƙarfin miƙewar azzakari tare da inganta kwararar jini zuwa ga al'aura. Ana amfani da kanunfari wajen magance saurin fitar maniyyi ga namiji a lokacin saduwa ne ta hanyar hada shi da wasu ƙarin abubuwan, wadanda akan shafa a kan al'aurar namiji kafin saduwa. Ga dai jeren abubuwa 8 da kanunfari ke yi a jikin ɗan adam, daga Dr Badamasi Adadin kanunfari da za a iya sha a rana guda Masana kiwon lafiya sun ce mutane na amfani da kanunfari wajen hana saurin fitar maniyyi a lokacin saduwa. Ko daɗin jima'i. Sai dai ba a son shansa ko ci ya zarta iyaka. Idan aka yi amfani da shi sama da ka'ida yana iya illa sosai. Ba a son a sha sama da itace hudu zuwa biyar a kowacce rana. Sannan ya dangata daga mutum zuwa mutum. Amma yana da kyau a tuntuɓi likita domin samun shawarwari yadda ya kamata a yi amfani da shi. https://www.bbc.com/hausa/labarai-56487462 +religion Mutum 45 sun mutu a zanga-zangar adawa da saka hijabi a Iran Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon: Fiye da mutum 40 ne suka rasa rayukansu a jerin zanga-zangar da ake ta yi ta nuna adawa da mutuwar Mahsa Amini a lokacin da take tsare a hannun jami’an tsaro kan zarginta da rashin sa hijabi. Duk da cewa an katse intanet a ƙasar, ana ci gaba da yaɗa bidiyon da mutane ke zargin an kashe wasu a zanga-zangar. Ƙungiyar kare hakkin bin adam ta Amnesty ta ce a ƙalla yara huɗu jami’an tsaro suka kashe tun farkon zanga-zangar, da aka fara kwana 10 da suka wuce. https://www.bbc.com/hausa/articles/cx78lggwq2eo +sports 'Yar Najeriya Tobi Amusan ta kafa tahiri a gasar tseren duniya "'Yar Najeriya Tobi Amusan ta lashe kyautar zinariya a gasar mita 100 ta tseren mata ta Duniya da ake gudanarwa a Amurka. 'Yar wasan mai shekara 25 ta kafa tarihin ne a zagayen kusa da karshe inda ta kai layi cikin minti 12 da dakika 12. A baya dai Ba'amurkiya Kendra Harrison ta kafa irin wannan tarihi a 2016 inda ta kai layi a minti 12 da dakika 20. Amusan ta fi yin gudu a zagayen karshe ( ta yi minti 12 da dakika shida), amma ba a amince da nasararta ba saboda iska mai karfi da ke kara mata gudu. Tobi ta zubar da hawaye don jin dadi a yayin da ake buga taken Najeriya a filin wasa na Hayward Field, Eugene da ke Jihar Oregon, saboda bajintar da ta yi wa kasarta. 'Yar kasar Jamaica Britany Anderson ta lashe kyautar azurfa yayin da 'yar kasar Puerto Rico wadda ita ce gwarzuwar gasar Olympic Jasmine Camacho-Quinn ta lashe kyautar tagulla. Yayin da take bayani bayan ta samu nasara, Tobi ta ce: ""Na yarda da kwazona amma ban taba tsammanin zan kafa tarihi a duniya ba.""" https://www.bbc.com/hausa/articles/crg87e8ng5ro +politics Yau kotu za ta raba gardama kan zaben Kano da Sokoto A yau ne ake sa ran Kotun Kolin Najeriya za ta yanke hukunci kan shari'un zaben gwamna na jihohin Kano da Sokoto. Wasu da ba su gamsu da yadda zaben ya kasance ba ne dai suka shigar da kara gaban kotun suna kalubalantar sakamakon da hukumar zaben kasar INEC ta bayyana a jihohin. Hukuncin kotun na yau dai shi ne raba gardama a takaddamar da ake yi kan halattacen gwamnan Kano tsakanin Abdullahi Umar Ganduje na jam'iyyar APC da hukumar zabe INEC ta ce shi ya lashe zabe, da kuma Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar PDP da ke kalubalantar nasara ta Ganduje. A Sokoto ma kotun za ta raba gardama tsakanin Aminu Waziri Tambuwal na jam'iyyar PDP da ke kan kujerar yanzu haka da kuma Ahmad Aliyu na jami'iyyar APC da ke kalubalantar nasarar da INEC ta ce Tambuwal din ya samu. A watan Maris din bara ne INEC ta bayyana Ganduje na Kano da Tambuwal na Sokoto a matsayin wadanda suka lashe zaben watan Maris, bayan an yi zabe karo na biyu kasancewar zaben zagaye na farko bai kammala ba, wato dai ya zama inconclusive, abin da Abba da Ahmed Aliyu suka kalubalanta. Tun a makon jiya ne dai kotun ta shirya bayyana hukunci kan jihohin na Kano da Sokoto tare da wasu jihohin, to amma wasu dalilai sun sanya kotun dage yanke hukuncin zuwa yau. A shari'a da aka yi ta kotun kararrkin zabe ta jiha dai Ganduje ne ya samu nasara a Kano, Tambuwal ya samu nasara a Sokoto, sannan sun kara samun nasara a kotun daukaka kara a Kaduna. Duka masu karar dai sun garzaya kotun kolin ne sabo da rashin gamsuwa da hukuncin da kotunan baya suka yanke. A yanzu matakin na Kotun Koli shi ne zai kasance na karshe a ja-in-jar da ake yi kan kujerun gwamnonin jihohin. Kuma dole ne a karbi hukuncin a kuma yi aiki da shi ko da kuwa ba a samu yadda ake so ba. Rashin tabbas, da rashin sanin mai zai faru ya sa magoya bayan wasu masu takaddamar a kotu ta koli suka dukufa da addu'ar neman nasara ga gwanayensu. A makon da ya gabata ne dai Kotun ta Koli ta yanke hukunci kan shari'ar zaben jihar Imo inda ta sauke gwamnan jihar na lokacin Emeka Ihedioha ta ce kuma a rantsar da Hope Uzodinma, hukuncin da ya rikita lisafin 'yan kasar da dama, musamman ma 'yan siyasa. Hukuncin na jihar Imo ya kara haifar da rashin tabbas kan abinda zai iya faruwa a kotun a yau, kuma ya kara tabbatar da karin maganar nan da ake cewa shari'a mace ce mai ciki ba a san me za ta haifa ba. https://www.bbc.com/hausa/51171712 +business Ngozi Okonjo-Iweala: Tsohuwar ministar kuɗin Najeriya ta zama shugabar WTO "Kasancewar ta tsallake daga dambarwar siyasa a Najeriya, inda aka sace mahaifiyarta matsayin wata barazana, kuma zama ta a Bankin Duniya, Ngozi Okonjo-Iweala bai kamata ta sami matsala a mu'amalarta da masu ruwa da tsaki a sabon aikinta na shugaban Kungiyar Cinikayya ta Duniya (WTO). Mai shekara 66 da haihuwa za ta kasance mace ta farko kuma ƴar Afirka ta farko da za ta jagoranci ƙungiyar. Duk da kwanan nan da samu karɓi takardar zama ƴar ƙasar Amurka, tana alfahari da kasancewarta ƴar Najeriya kuma tana da kishin ƙasa - tana nuna asalinta na Afirka ta hanyar tufafin da suka dace da Afirka. Ta taɓa faɗa wa BBC a 2012 cewa ta rungumi irin tufafinta a matsayin uwar yaƴa huɗu ma'aikaciya, ta ƙiyasta tufafin da take saka wa na atamfa kowanne ya kai kimanin dala $ 25. Masaniyar tattalin arzikin da ta ya yi karatu a Jami'ar Harvard a matsayin mai kwazo da jajircewa, kamar yadda ta faɗa wa BBC HardTalk a watan Yuli cewa abin da WTO ke bukata shi wanda zai tabbatar da sauyi. ""Suna buƙatar wani abu sabo, ba zai iya zama kasuwanci kamar yadda aka saba a kungiyar WTO ba - [suna buƙatar] wani da ke son kawo sauye-sauye da jagoranci."" A cikin shekaru 25 da ta yi a Bankin Duniya, an yaba mata ga wasu tsare-tsare don taimakawa kasashe masu karamin ƙarfi, musamman tara kusan dala biliyan 50 a shekarar 2010 daga masu ba da tallafi ga Kungiyar Ci Gaban Kasa da Kasa (IDA), gidauniyar Bankin Duniya ga kasashe matalauta. Amma sauyin da ta kawo a Najeriya shi ne take alfahari da shi - musamman kasancewar sau biyu da ta riƙe matsayin ministar kudin ƙasar a zamanin Shugaba Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan. Ɗaya daga cikin manyan nasarorin da ta samu shi ne jagorantar wata tawaga da ta tattauna kan bashin dala biliyan 18 a shekarar 2005 kan kasar, wanda ya taimakawa aka yaba wa Najeriya a karon farko kan rage bashin da ke kanta. Bashin da ake bin ƙasar tun a farkon shekarun 1980, kuma ya ci gaba da ƙaruwa har dala biliyan 35 saboda ruwa da jinkiri biya har wajejen 1990. Sauye-sauyen tattalin arzikinta sun yi tasiri sosai kuma sun taimakawa Najeriya a cikin wani mawuyacin lokaci, a cewar fitaccen masanin tattalin arzikin Najeriya, Bismarck Rewane. Wannan ya haɗa da cire kasafin kuɗin ƙasar daga farashin mai, wanda hakan ya ba Najeriya damar ajiyar kuɗi a wani asusu na musamman a lokacin da farashin mai ya yi tsaɗa. ""Wannan ne ya taimaka tattalin arzikin Najeriya ya farfaɗo tsakanin 2008 da 2009,"" kamar yadda Mista Rewane ya shaida wa BBC. Okonjo-Iweala ta bar aikin da ake biyanta albashi sosai a Bankin Duniya kuma ta bar iyalinta a Washington, inda mijinta ke aiki a matsayin likita, ta dawo ta karɓi aiki a Najeriya, inda ba kamar sauran ministocin ba, ba ta da ma'aikata da ke hidimar gida ko tara motoci. Ta ma fi son ta yi girki da kanta a lokacin da za ta iya, da farfesun bindin shanu a matsayin wanda ta fi so, kamar yadda ta bayyana a hirar jaridar Financial Times ta yi da ita a shekarar 2015. Sauye-sauyen da ta kawo da kuma musamman yadda ta yaƙi cin hanci da rashawa a bangaren mai, inda wasu ƴan kasuwa da ake kira marketers - suka yi iƙirarin a biya su maƙudan kuɗaɗe na tallafi daga gwamnati ga man da ba su sayar ba. Mahaifiyarta, Kamene Okonjo - likita ce kuma farfesa a fannin ilimin zamantakewar al'umma - an taɓa yin garkuwa da ita a gidanta a kudancin Najeriya a shekarar 2012, tana da shekara 82. Satar mutane domin kuɗin fansa ya zama ruwan dare a Najeriya, inda ake samun kudi mai tsoka kuma mutane suna biya tun da jami'an tsaro ba su cika kuɓutar da waɗanda aka sace ba. Ministar kudi ta wancan lokacin ta ce masu garkuwar sun fara neman ta yi murabus sannan kuma suka nemi a ba su kuɗi. Amma ta ce ta bijerewa buƙatunsu, 'Zan iya jure wa wahala' Watakila ta samu ƙwarin gwiwar gudanar da ayyukanta ne saboda yadda ta fuskanci tsantsar talauci. Ta zauna tare da kakarta har sai da ta kai shekara tara a duniya saboda iyayenta suna kasashen waje inda suke karatu. Ta shaida wa BBC a 2012 cewa: ""Sun kwashe kusan shekara goma kafin na sanya su a idanuna ko kuma na sansu. Na yi dukkan abin da yarinyar ƙauye take yi, na riƙa ɗebo ruwa, da zuwa gona tare da kakata da kuma yin ayyukan gida. Na ga tsantsar talauci da abin da yake nufi."" Abubuwan da ta gani lokacin yaƙin basasa na Biafra tsakanin 1967-1970 ya tabbatar da hakan. Iyayenta 'yan kabilar Igbo sun yi asarar dukkan abin da suka mallaka lokacin yaƙin domin kuwa mahaifinta, wanda sanannen farfesa ne, ya riƙe matsayin birgediya a rundunar sojin Biafra. ""Zan iya jure wa wahala. Zan iya kwana a dandaryar siminti mai sanyi kowanne lokaci,"" in ji ta. Sai dai macen da take yawan dariya idan 'yan jarida suna hira da ita ta ƙara da cewa: ""Zan kuma iya yin barci a kan gadon gashi."" Irin wannan namijin kokari da tsayawa da dunga-duganta sun taimaka mata a yayin da take gudanar da sauye-sauye a Najeriya - kamar matakin da ta dauka na bayyana kudin da kowacce karamar hukuma take karba daga gwamnati a kowanne wata wajen gina hanyoyi da makarantu da asibitoci. Masanin tattalin arziki Pat Utomi ya ce 'yan Najeriya ba su san adadin kudaden da shugabanninsu suke karɓa ba. ""Amma ta zo da tunanin wallafa dukkan abubuwan da ake ba su kuma hakan ya kunyata mutane da dama,"" in ji Farfesa Utomi. Ta kaddamar da wani tsari da zai taimaka wajen fitar da dubban ma'aikata da 'yan fansho na bogi daga tsarin aikin gwamnatin kasar. Sai dai a lokacin da gwamnati ta yi yunkurin cire tallafin man fetur a 2012, abubuwa ba su tafi yadda take so ba. Ms Okonjo-Iweala ta ce ba za a iya ci gaba da biyan tallafin ba saboda kasar tana kashe kusan dala niliyan takawas a kansa a duk shekara, lamarin da a cewarta yake haifar da cin hanci. Sai dai an tilasta wa gwamnati janye wannan matakin sakamakon yajin aikin da aka tsunduma a fadin kasar - a farkon wannan shekarar ne aka cire tallafin, inda gwamati ta yi alkawarin daidaita farashin man na fetur. Wasu sun yi amannar cewa ko da yake sauye-sauyen nata suna da kyawu ga Najeriya amma ba masu dorewa ba ne. 'Kamar gudanar da harkokin gidanka ne' Amma wata mai fafutukar kare hakkin mata a Najeriya Josephine Effa-Chukwuma ta ce ayyukan da Ms Okonjo-Iweala ta yi abubuwan sha'awa ne ganin cewa ba kasafai ake mutunta mata a kasar ba. Ta shaida wa BBC cewa: ""Ta sa mata suna alfahari da ita cewa mata a kasar da maza suka mamaye komai irin Najeriya suna iya yin aikin da ya dace ba kamar yadda 'yan-uba suke so ba."" ""Ita mai gaskiya ce, mai yin komai a bayyane - abubuwan da ba a fiye samu ba a tsakanin masu rike da mukaman gwamnati a Najeriya."" Masaniyar harkokin tattalin arzikin, wadda kuma ta kasance cikin daraktocin kamfanin Twitter, tana rike da mukamin shugaba a kamfanin alluran riga-kafi na Gavi kuma wakiliya ga Hukumar Lafiya ta Duniya kan yaki da cutar korona. Cikin raha, ta taɓa cewa mata ba su cika shiga sha'anin cin hanci ba. ""Mata sun fi gaskiya, sun fi magana kai tsaye, sun fi mayar da hankali a kan ayyukansu, kuma ba su cika nuna jiji da kai a kan aikinsu ba. Ban sani ba ko batu ne da ya shafi mata kawai amma tafiyar da tattalin arziki wani lokaci tamkar tafiyar da arkokin gida ne,"" in ji ta, a hirar da ta yi da jaridar the Independent a 2006. Ta ce mata na cikin wadanda za ta bai wa fifiko a mukaminta na shugabar WTO." https://www.bbc.com/hausa/labarai-56073013 +sports Fifa ta nemi kasashe su mayar da hankali 'kan kwallon kafa' Hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa ta aike wa duka kasashe 32 da za su halarci gasar cin duniya wasika, tana neman su mayar da hankali kan kwallon kafa, biyo bayan ce-ce-ku-cen da ake ta yi daf da fara gasar. Mai masaukin baki Qatar na ta fama da suka kan matsayarta game da auren jinsi, da yancin dan adam da kuma yadda take tafiyar da lamarin ‘yan cirani da ke aikatau. Za a fara gasar ne a ranar 20 ga watan Nuwamba. Wasikar ta yi gargadin cewa bai kamata a a rika jayayya akwallon kafa ba, kan wani tunani ko kuma siyasa, kuma ba a amfani da ita wajen gyaran halayya. Wasu ‘yan wasa sun shirya gudanar da zanga-zangar lumana gabanin fara wasannin. Kyaftin din Ingila Harry Kane da wasu kyaftin tara na kasashen Turai za su sanya kambi nuna kauna. ‘Yan wasan Australia sun saki wai bidiyo suna shawartar Qatar da ta yi watsi da dokarta an sha’anin auren jinsi. Birnin Paris na Faransa da wasu sauran birane sun ce b aza su haska wasannin kofin duniyar ba a manyan majigi, duk da cewa Faransan c eke rike da kofin. 'Yan wasan Norway sun sanya riga da ke magana kan hakkin dan dama a ciki da wajen filin kwallo, ko da yake tawagar ba ta yi nasarar halartar gasar da za a yi a kasar ba https://www.bbc.com/hausa/articles/c13xym4kr42o +politics EndSARS: Yadda zanga-zangar ta sauya Najeriya har abada "Wani gangami na zanga-zanga a tituna da wanda aka yi a shafukan sada zumunta ya bai wa matasan Najeriya wata kafa da ta haddasa rusa tsarin girmama na gaba da aka saba da shi a ƙasar. Yayin da gangamin #EndSARS ya bazu ko'ina, a lokacin ne kuma bijire wa masu rike da madafan iko ya kunno kai a Najeriya. Lalata fadar Oba ko kuma sarkin gargajiyar Iko da ake matukar girmamawa a Legas, ta kasance manuniya ga halin da aka faɗa. Matasan da suka faɗa cikin fadar sun rika fatali da karagarsa kuma sun kwashe kayansa har ma sun yi wanka a cikin wurin nunƙayarsa. Abin da ya samo asali daga zanga-zangar nuna rashin amincewa da wata rundunar ƴan sanda mai matuƙar bakin jini ta Special Anti-Robbery Squad (SARS), ya kasance wata hanyar da matasa za su huce fushinsu da mutanen da suka shafe gomman shekaru suna mulkin ƙasar, kuma suna buƙatar sauyi. Tsohon Shugaba Olusegun Obasanjo ya taɓa yin gargadi a 2017 cewa ""dukkammu muna zaune ne a kan tukunyar bam"" game da al'amuran matasa. Ya yi kalaman nasa ne kan matasan nahiyar baki ɗaya, amma sun yi daidai da abin da ke faruwa a Najeriya, wadda ita ce ƙasa mafi yawan al'ummarta ya kai miliyan 200 kuma fiye da kashi 60 cikin 100 na al'ummar ƙasar 'yan ƙasa da shekara 24 ne da haihuwa. Yawancin waɗanda suka kai munzalin yin aiki cikinsu ba su da aikin da ya dace su yi, kuma ba su da damar samun ilimin zamani. A farkon wannan shekarar alƙaluman da gwamnati ta fitar na cewa kashi 40 cikin 100 na ƴan Najeriya na rayuwa cikin talauci. Da farko waɗanda ke mulkin kasar a yanzu ba su fahimci abin da ke faruwa ba, inji Gimba Kakanda, wani mai gwagwarmaya kuma marubuci a wata hira da ya yi da BBC. ""Sun ɗauka zanga-zangar #EndSARS irin wadda suka saba gani a da ce, wadda matasan za su gaji su watse da kansu idan aka ƙi kula su."" Ya kara da cewa: ""Wannan tunanin na masu mulkin kasar, wanda kana iya cewa na rainin wayon matasan ne, shi ne dalilin da ya sa gwamnati ta yi sanyin tunkarar wannan gagarumin yunƙurin, kuma ya gigita su."" Abin tambaya a nan shi ne, ina wannan gwagwarmayar za ta dosa? Nasarorin da aka samu na yadda gwamnati ta yi saurin amsawa da buƙatun da masu zanga-zangar suka fitar - kamar rusa rundunar SARS da yin sauye-sauye ga aikin ƴan sanda - ya ba matasan Najeriya karfin gwiwar cewa za su iya kawo sauyi. Kwananki kadan da fara zanga-zangar, masu fafutika cikin matasan sun samar da hanyoyi ga masu bukatar taimakon gaggawa. Sun kuma rika bayar da taimako a fannin shari'a ga masu bukata har ma sun kafa wata tashar rediyo. Dukkan wadannan ayyukan sun samu ne ta hanyar tara kudade da suka yi ta amfani da fasahar sadarwa ta zamani da ake kira crowdfunding, matakan da aka rika kallo a matsayin yadda Najeriya ka iya kasancewa ba don 'yan siyasar ƙasar sun fi mayar da hankali kan abin da zai amfane su ba - maimakon abin da zai amfani ƙasar. Amma akwai munanan abubuwa da suka auku. Wasu daga cikin masu zanga-zangar sun fasa shaguna, kuma sun wawashe manyan ɗakunan ajiyar kaya har ma da kamfanonin fitattun ƴan siyasa. Duk da manufar wadannan gungun matasan biyu sun sha bamban, amma suna da abin da ya haɗa su: shi ne ganin mutuncin masu mulki. Sai dai zai yi wuya tafiyarsu ta zama ɗaya. Duk wani yunkuri na hada su wuri guda ba zai yiwuba, saboda wasunsu ba za su amince su yi tafiya da waɗanda ake kallo da ""muggan halaye"". 'Buhari bai san inda aka nufa ba' Duk da haka akwai alamar masu mulki sun gane cewa talauci da wahalar rayuwa sun zama abubuwan da ke barazana ga tsaron ƙasa, kamar yadda Mista Kakanda yake kallon lamarin. ""Gwamnati ta gane cewa ba za ta iya ci gaba da kau da kai ga fusatar matasa kamar yadda ta saba yi a da ba,"" inji shi. Sai dai ta yi tuntuɓi ba sau ɗaya ba yayin da ta ke ƙoƙarin kashe wutar boren. Shugaba Muhammadu bUhari ya yi wa ƙasar jawabi ranar Alhamis da daddare, ""kuma yawanci bai san inda aka nufa ba"", inji Japeth Omojuwa, wani marubuci kan al'amuran yau da kullum a intanet. Shugaba Buhari ya bukaci a kawo ƙarshen zanga-zangar kana a fara tattaunawa, amma ""tarihi zai tuna da shi a matsayin wanda yayi wa ƴan Najeriya barazana saboda kawai sun buƙaci gwamnatinsu ta amince za ta yi adalci."" Duk da haka Mista Omojuwa yayi amanna cewa gwagwarmayar ta #EndSARS za ta iya cimma wani abu. Kada ta yi dogon buri na samun iko irin na siyasa, inji shi, amma kamata yayi su tabbatar masu mulki sun cika alƙawuran da ska ɗauka na sauye-sauye da yi wa ƴan sanda masu laifi shari'a. Irin waɗannan ƙananan matakan ne za su iya kawo gagarumin sauyi." https://www.bbc.com/hausa/labarai-54671661 +politics Na nemi Buhari ya shiga tsakanina da EFCC - Rochas Okorocha "Tsohon gwamnan Jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya kuma sanata a yanzu, Rochas Okorocha, ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya shiga tsakaninsa da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar zagon kasa EFCC. Okorocha ya bayyana hakan ne bayan ganawarsa da Buhari a fadar shugaban kasar, inda ya ce ya gabatar wa da shugaban wannan bukata kan hukumar ta daina yawan muzanta shi da neman harzuka shi a kan shari'ar zargin almundahana ta naira biliyan 2.9, abin da kusan take yi masa a kullum, a cewarsa. Sanatan ya ce ya nemi Shugaba Buhari a matsayinsa na mai mutunta doka da son kiyaye da ka'ida da ya sa baki kan al'amarinsa da hukumar ta EFCC don ta bi umarnin kotu. ""Ina da hukunci da umarnin kotu biyu, hukunci daban-daban har uku a wurare daban-daban wadanda suka hana EFCC cin zarafi da harzuka ni, amma EFCC ta kekasa kasa ta ki bin doka, saboda haka dole ne na gaya wa shugaban kasa cewa a sa EFCC ta bi dokar da ta kafa ta, wanda kuma idan da ba doka to da ba EFCC,"" in ji shi. Ya ƙara da cewa ""kuma ta daina azarbabi kan bin duk abin da ya shafe ni"". Okorocha ya ci gaba da cewa: ""Kuma na tuna wa Shugaban Kasa cewa (idan ba a manta ba) a wani lokaci, EFCC ta yi ikirarin cewa ta kwato jumullar naira bliyan 5.9 daga asusun bankina, abin da kotu ta gano cewa ba gaskiya ba ne, ko kuma a ce ma suna nuna son-kai da azarbabi da riga-mallam-masallaci a kaina. ""A kan haka kotu ta zartar da cewa kada su kara bincikena da cin mutuncina. Wannan ma ba ta bi ba. Kotu ta kuma umarci EFCC ta saki fasfona, EFCC ta ki bin umarnin. ''Kotu ta umarci EFCC ta biya ni naira miliyan 500 na ɓatanci, EFCC ba ta biya ba. Maimakon ma ta biya sai ta bari a ranar da zan kaddamar da takarata ta neman shugaban kasa sai ta faɗa wa 'yan jarida cewa an gurfanar da ni a kotu a kan aikata wasu laifuka na almundahanar naira biliyan 2.9, ba kuma bliyan 5.9 ba. ""Saboda haka na ce a matsayinsa na shugaban Najeriya, kuma wanda ke tsaye a bangaren kiyaye doka ya ja hankalin EFCC a kan wannan."" Okorocha wanda ya bayyana aniyarsa ta neman takarar shugaban kasar a zaben 2023, ya ce ya tattauna wasu batutuwan da Shugaba Buhari a yayin ganawar tasu, inda ya bayyana bukatar karfafa jam'iyyarsu ta APC daga tushe. Ya ce, shugaban ya yi alkawari musamman ma cewa lokacin da 'yan siyasa za su rika samun mulki daga Abuja, ba tare da goyon baya daga talakawa daga tushe ba ya wuce, ba za a kara yarda da hakan ba a jam'iyyarsu ta APC." https://www.bbc.com/hausa/labarai-60221579 +technology An zargi Koriya ta Arewa da harba makamai masu linzami "Koriya ta Kudu ta ce Koriya ta Arewa ta harba wasu abubuwan fashewa biyu zuwa teku wadanda ta ce sun yi kama da makamai masu linzami. An harba makaman ne daga Lardin Pyongan ranar Asabar zuwa tekun Japan. Amurka da China sun nemi a koma teburin tattaunawa kan maganar kawo karshen shirin nukiliya da kawo karshen kera makamai masu linzami. A ranar asabar ne rundunar sojin Koriya ta Kudu ta ce tana bibiyar lamarin ko da za a samu karin wasu makaman da za a harba. Japan ta tabbatar da dirar makami mai linzami a wajen ruwan da ke yankin tattalin arzikinta na musamman. Lamarin na zuwa ne yayin da Koriya ta Arewa ta sanar da gudanar da wani babban taro da majalisar kasar ranar 10 ga watan Afrilu. Sai dai masu sharhi sun ce taron zai hada manyan jagororin kasar su 700 a waje guda. Wata ma'abociyar dandalin sada zumunta na Twitter Rachel Minyoung ta ce taron zai kasance dama ga Koriya ta Arewa ta ba da tabbaci game da kokarin da take na magance coronavirus. Kawo yanzu dai ba a samu bullar coronavirus a Koriya ta Arewa ba amma wasu kwararru na bayyana kokwanto. Koriya ta Arewa na da iyaka da China inda cutar ta samo asali da kuma Koriya ta Kudu inda aka samu barkewar cutar sosai. Wani babban jami'in sojin Amurka a makon da ya gabata ya ce yana da ""tabbaci"" cewa cutar ba ta bulla a Koriya ta Arewa ba. Kasar dai ta killace kusan baki 380 - mafi yawansu jakadu da ma'aikata a Pyongyang - a harabar gidajensu na kusan wata daya. An kuma dage takunkuman da aka kakaba a farkon watan nan na Maris." https://www.bbc.com/hausa/labarai-51985566 +sports Faransa ta maye gurbin Kimpembe da Disasi a Gasar Cin Kofin Duniya Tawagar Faransa ta kira mai tsaron bayan Monaco, Axel Disasi domin maye gurbin Presnel Kimpembe, wanda ya kasa warkewa daga jinya da yake yi. Faransa ce mai rike da kofin duniya da ta lashe a Rasha shekara hudu da ta wuce. Tun farko Faransa ta bayyana Kimpembe, wanda da shi aka ci kofin duniya a Rasha, cikin wadanda za su wakilce ta a Qatar, amma har yanzu bai warke ba. Za a fara Gasar Cin Kofin Duniya ranar 20 ga watan Nuwamba a kammala ranar 18 ga watan Disambar 2022. Haka kuma Faransa ta gayyaci mai cin kwallaye a Moenchengladbach, Marcus Thuram, kenan tawagar ta ciki 26, bayan da Didier Deschamps ya bayyana 25 tun farko. Disasi wanda aka haifa a Faransa, iyayensa daga Jamhuriyar Congo suke, har ma ta gayyace shi buga mata wasannin matasa 'yan kasa da shekara 20 a 2017. Wannan shi ne karon farko da Disasi zai buga wa babbar tawagar Faransa tamaula, bayan wasa uku da ya yi a ta matasa 'yan kasa da shekara 20. Faransa za ta fara wasan farko a rukuni na hudu ranar 22 ga watan Nuwamba da Australia a rukunin da ya kunshi Denmark da kuma Tunisia. Jerin 'yan kwallon tawagar Faransa da za su buga Kofin Duniya a Qatar: Masu tsaron raga: Alphonse Areola (West Ham), Hugo Lloris (Tottenham), Steve Mandanda (Rennes) Masu tsaron baya: Lucas Hernandez (Bayern Munich), Theo Hernandez (AC Milan), Ibrahima Konate (Liverpool), Jules Kounde (Barcelona), Benjamin Pavard (Bayern Munich), William Saliba (Arsenal), Dayot Upamecano (Bayern Munich), Raphael Varane (Manchester United) Masu buga tsakiya: Eduardo Camavinga (Real Madrid), Youssouf Fofana (Monaco), Matteo Guendouzi (Marseille), Adrien Rabiot (Juventus), Aurelien Tchouameni (Real Madrid), Jordan Veretout (Marseille) Masu cin kwallaye: Karim Benzema (Real Madrid), Kingsley Coman (Bayern Munich), Ousmane Dembele (Barcelona), Olivier Giroud (AC Milan), Antoine Griezmann (Atletico Madrid), Kylian Mbappe (Paris St-Germain), Christopher Nkunku (RB Leipzig) https://www.bbc.com/hausa/articles/c72ewlee252o +politics Gane Mani Hanya: Jayayya tsakanin kudu da arewa kan mulkin 2023 ba ta da amfani - Bagudu Latsa hoton sama ku saurari Shirin Gane Mani Hanya da Gwamnan Kebbi Atiku Bagudu Shirin Gane Mani Hanya na wannan makon ya yi hira ta musamman da Gwamna Atiku Bagudu na Jihar Kebbi. Cikin hirar da Haruna Ibrahim Kakangi ya yi da shi, gwamnan ya tattauna kan abubuwa da dama da suka haɗa da siyasar 2023 da kuma makomar siyasarsa. https://www.bbc.com/hausa/shirye-shirye-na-musamman-57874733 +entertainment 'Yajin aikin ASUU ya ɓata min wata takwas na rayuwata' "Malaman jami'o'i a Najeriya sun ce za su koma bakin aiki ranar Litinin bayan yajin aiki na tsawon wata takwas da ya sa jami'o'in gwamnati kasancewa a rufe, abin da ya sa dalibai zaman gida cikin takaici da bacin rai. ""Wata takwas kenan da na yi asara a rayuwata, to kuma me yajin aikin ya cimma?"" Tambayar da wata daliba ta yi kenan, wadda ba ta son a bayyana sunanta. Yajin aikin da aka fara a watan Fabrairu shi ne na 9 a cikin shekara 13, kuma shi ne na baya-bayan nan a wannan dambarwa ta tsawon shekara goma kan batun samar da karin kudade ga manyan makarantun gaba da sakandire na kasar. Babbar kungiyar malaman jami'o'i ta kasar ASUU, ta jima tana fafutuka domin ganin gwamnati ta kara kudaden da take bayarwa domin tafiyarwa da kuma bunkasa jami'o'i, amma gwamnatin na cewa ba ta da halin da za ta iya biyan dukkanin bukatun kungiyar. ASUU ta ce ta dakatar da yajin aikin ne a matsayinta na kungiya mai bin doka da oda da kuma rokon da 'yan Najeriya ke yi mata, amma har yanzu ba a warware matsalolin da suka sa ta shiga yajin aikin ba. Malaman sun dakatar da aikin koyarwa a jami'o'in gwamnati a kan bukatun nasu, to amma yajin aikin da aka shafe tsawon lokaci ana yi ya haddasa damuwa sosai ga dalibai da iyayensu. Wata daga cikin daliban da ke murnar komawa karatu ta ce, ""Kusan ba abin da na yi tsawon wannan wata takwas. ''Mutane suna ta ce min in je in koyi sana'ar hannu, in je in koyi sana'ar hannu. To da ina son in koyi sana'a ai da ba zan je jami'a ba, '' in ji ta. Ba a dai san yadda aka sasanta a kan ainahin abin da ya haddasa kiki-kaka a tsakanin bangarorin biyu ba, wato batun tsarin biyan malaman albashi, tun 2020. Wannan ne ya sa ake ganin ba za a iya kawar da yuwuwar sake komawar malaman wani yajin aikin ba a nan kusa. Malaman suna korafi ne da cewa tsarin biyan nasu bai kunshi wasu alawus-alawus ba kuma yana nuna bambanci a tsakaninsu. Sai dai a nata bangaren gwamnatin ta kafe cewa tsarin zai taimaka mata kawar da ma'aikatan bogi. Sannan kuma ta yi watsi da wata manhaja da malaman suka kirkiro saboda a cewarta manhajar ba ta tsallake gwajinta ba. A watan Disamba na 2020 ne aka kawo karshen wani yajin aikin da suka yi a baya, bayan da gwamnati ta sanya hannu a wata yarjejeniya ta duba bukatun da kungiyar ta ASUU ta gabatar. To amma kusan a iya cewa gwamnatin ta ja baya a kan wannan yarjejeniya, abin da ya sa kungiyar ta yi ta gargadin cewa za ta koma yajin aikin, abin da a karshe dai ta shiga a watan Fabrairu na wannan shekara. Da wannan janye yajin aikin yanzu ana sa ran dalibai bayan sun rasa kusan shekara daya ta karatu, shekara biyu bayan da annobar korona ta haifar da cikas ga wata shekara daya ta karatun su koma aji ranar Litinin. Kuma da yawa daga cikinsu ba sa jin dadi cewa ba za su kammala karatun ba a lokacin da ya kamata a ce sun gama. Wata daliba a Jami'ar Patakwal ta koka da cewa, ''Abokan karatuna a jami'o'i masu zaman kansu tuni sun gama karatunsu yanzu sun sha gabana a rayuwar bayan karatu da shekara biyu.'' Yawan yajin aikin ya sa mutane da dama ba su da kwarin guiwa a kan karatun makarantun gaba da sakandire na gwamnati a Najeriya. Wannan ne ya sa ma wasu suka gwammaje su je jami'o'i masu zaman kansu masu tsada ko kuma su tafi na wasu kasashe kamar na gabashin Turai masu saukin kudi. Yawanci tattaunawa tsakanin gwamnati da kungiyar kan ja lokaci to amma ta wannan shekarar ta fi daburcewa. Abin da ya sa har gwamnatin ta kai karar kungiyar kotu, kotun da malaman suka yi watsi da umarninta na su koma aiki. 'Ya'yan 'yan siyasa da dama ciki har da na Shugaba Muhammdu Buhari da manyan farfesoshi yawanci suna tafiya kasashen waje ne karatu. Wanda wannan na kara bata wa 'yan kasar rai cewa gwamnati da tsarin tafiyar da jami'o'in ba da gaske suke ba wajen samar da mafita mai dorewa a wannan rikici. A makon da ya gabata Shugaba Buhari ya sanar cewa gwamnati za ta zuba Naira biliyan 470 (kwatankwacin Dala biliyan 1.1 ko Fam miliyan 960) a harkar jami'o'i a irin yarjejeniyar da aka cimma da kungiyar, wanda hakan zai kai ga kara albashin malaman. To amma kuma ya yi gargadin cewa gwamnati ba za ta iya ci gaba da daukar dawainiyar makarantun gaba da sakandire ba ita kadai. Dole ne a dubo wani tsari da ya yi nasara na wasu kasashe a bi wajen samar da kudade ga bangaren, kamar yadda shugaban ya ce. Yadda za a samar da kudaden gudanarwa ga makarantun gaba da sakandire ya kasance babbar matsala tsawon shekaru a Najeriya. Kuma rashin yawan kudin makaranta da ake biya a makarantun gwamnati ya sa mutane da yawa neman shiga makarantun. Sai dai kuma wannan na daga abubuwan da suka janyo malaman ba su da wani albashi mai yawa sosai da kuma rashin samar wa bangaren ilimin kudaden gaske. Kwararru na ganin hanya daya ta magance wannan matsala ita ce a ba wa jami'o'in 'yancin cin gashin-kai su kara kudi, wanda hakan zai sa su samu karin kudaden tafiyarwa. To sai dai kuma a kasar da ake ganin yawancin iyalai talakawa ne kuma akwai miliyoyin yara da ba sa zuwa makaranta, ana fargabar cewa daukar wannan mataki ka iya bata abin ma gaba daya, lamarin ya fi yadda yake muni. A baya an yi tunanin bullo da tsarin bai wa dalibai bashi mai kudin ruwa kadan, to amma malaman suka ki amincewa da shi. A shekarar da ta gabata, shugaban kungiyar ta ASUU, Emmanuel Osodeke, ya yi korafi a kan wannan tsarin da cewa: ''Idan da mun yarda cewa dalibai su biya Naira miliyan daya a matsayin kudin makaranta, da wai sun kara mana yawan albashi, to kuma wa jama'a da dalibai za su zarga?"" ""ASUU za su ce,'' in ji shi. Haka kuma ASUU na son ganin gwamnati ta dakatar da kirkiro sabbin jami'o'i har sai ta iya samar da kudin tafiyar da wadanda take da su. Sannan kuma ta fitar da rahoton kwamitin da ya yi bincike kan manyan shugabannin jami'o'in, wadanda kungiyar ke zargi da rashawa. Sai dai 'yan Najeriya da dama na ganin kungiyar ta malamai na gaggawar shiga yajin aiki a kan bukatunta. Da kuma zakewa kan wasu daga cikin bukatun, misali, yadda malaman ke kafewa cewa su za su gaya wa gwamnati yadda za ta rika biyansu albashi. Wasu 'yan kasar na ganin cewa wannan abu ne da ya wuce gona da iri. Bisa ga dukkan alamu gwamnati ta biyo wa kungiyar malaman ta bayan gida, inda ta yi rijistar wasu karin kungiyoyi biyu da ke zaman tamkar kishiyoyin ASUUn, domin rage mata karfi da kuma raba kai. Kungiyoyin su ne, CONUA (Congress of Nigerian University Academics) da NAMDA (National Association of Medical and Dental Academics) Daya daga cikin kungiyoyin, ta ce za ta yi aiki tukuru domin ganin cewa ba a sake jefa kasar cikin halin yajin aikin ba. Wannan wata dabara ce da ta yi tasiri sosai ga gwamnatocin baya a kasar wajen kassara kungiyoyin kwadago masu karfin gaske, ta hanyar tilasta musu, su mika wuya a tattauna da su. Idan har wannan dabara za ta sa jami'o'in su kasance a bude, to ba shakka dalibai da yawa da iyayensu za su so ta. Ko da kuwa ba ta magance matsalolin da ake kai ruwa rana a kansu ba. ""Ina dai fatan wannan shi ne yajin aiki na karshe da zan fuskanta har na kammala jami'a. Amma dai fata da addu'a nake yi kawai,"" in ji wani dalibi da ya rubuta hakan a sakon waya. ""Saboda malaman da ake kira na ASUU ka iya dawowa su ci gaba da yajin aikin a nan gaba, su ce ba sa son albashinsu na yanzu, suna son kari. To a nan me za mu yi? Babu,"" ya ce, inda ya yi amfani da hoton alamar mutumin da abu ya fi karfin sa." https://www.bbc.com/hausa/articles/crgxnzdjkl6o +religion Ƴan sandan Faransa sun kai samame gidajen 'masu kaifin kishin Musulunci' "'Yan sandan Faransa sun kai samame gidajen wasu gomman mutane da ake zargin masu kaifin kishin Islama ne, biyo bayan sare kan malamin makarantar nan da ya nuna wa ɗalibansa hoton barkwanci da ke nuna fiyayyen halitta. Wasu daga cikin waɗanda aka kai wa samamen sun wallafa saƙonnin nunawa maharin da ya sare kan malamin goyon baya. Sannan gwamnati ta ce za ta gurfanar da wasu ƙungiyoyin Musulmi 51 na ƙasar a kotu. 'Yan sandan sun harbe makashin Samuel Party a ranar Juma'a. Makarantar da malamin ke koyarwa na Conflans-Sainte-Honorine ne, wani yanki da ke can bayan gari a yammacin birnin Paris. Maharin mai shekara 18 wanda ɗan yankin Ceceniya ne ba shi da wata alaƙa da malamin a makaranta. A ranar Litinin Ministan Harkokin Cikin Gida na Fransa Gérald Darmanin, ya ce samamen ya aika ƙwaƙƙwaran saƙon cewa maƙiyan Faransa ba su da damar sakewa, sannan za a ci gaba da kai shi a ko wanne mako. Ya ce ba wai dukkanin mutanen da aka kai wa samamen ne ke da hannu a kisan Mista Party ba. A gefe guda kuma 'yan sanda za su binciki wasu mutum 80 da suka wallafa saƙonnin nuna goyon bayansu ga maharin da ya aikawa wannan al'amari. Gwamnati ta ce matsawar aka samu ƙungiyoyin Musulmi da yaɗa maganganun tsanar wasu, to kuwa za a rushe su nan take. Cikin kungiyoyin har da wata mai fafutukar hana ƙyamar Musulmai, wadda gwamnati ke kallon tana yaɗa manufar ƙyamar ƙasa a tsakanin al'ummar Musulmi mazauna Faransa. A wannan shafin, ƙungiyar ta kira kanta a matsayin ta kare hakkin 'yan adam, kuma babban aikinta shi ne yaƙi da ƙyamar Musulunci, kuma tana aiki ne da haɗin gwiwar Majalisar Ɗinkin Duniya. Menene sakamakon bincike na baya-bayan nan? Mai gabatar da ƙara kan ta'addancin Jean-François Ricard, ya ce mamacin wato Mista Party ya riƙa samun saƙonnin barazana tun lokacin da ya nuna hoton barkwancin da ke nuna Annabi SAW, a matsayin ƴancin faɗin albarkacin baki. Kamar yadda ya sha yi a shekarun baya-bayan nan, Mista Party wanda malamin tarihi ne, ya kan buƙaci ɗalibai Musulmai su riƙa kai zuciya nesa a duk sanda suka ga kamar an yi musu ɓatanci. Ɓatanci ga Annabi SAW na iya haifar da ɓacin rai ga Musulmai, sannan a addinance ma babu kyau a zana hoton Annabi ko kuma Allah Mahalicci. Wannan batu ne mai haɗari a Faransa, musamman sakamakon yaɗa hotunan barkwanci na Manzon Allah SAW da jaridar nan ta Charlie Hebdo ta yi a shekarun baya-bayan nan. Sannan har yanzu ana ci gaba da shari'a dangane da kisan wasu mutum 12 a wajen ofishin jaridar a shekarar 2015. Wasu Musulmai a Faransa na cewa suna fama da haɗarin cin zarafi da ɓatanci, saboda abin da suka yi imani da shi, batun da ya sha haifar da ce-ce ku-ce a ƙasar. An kama wasu mutum 11 dangane da kisan Mista Party, a wani ɓangare na binciken da 'yan sanda ke yi, daga haka babu wani ƙarin bayani. Menene martanin da mutane ke yi a Faransa? Harin ya ruɗa Faransa, dubban mutane sun taru a gangamin da aka gudanar a ƙarshen mako don yin jimamin mutuwarsa. Wani mutumi daga cikin masu gangamin na dauke da wata alama da ke cewa ""Babu wata dama ga maƙiya ƙasarmu'' Wani kuwa na riƙe da wata alama da ke cewa ""Ni farfesa ne. Ina tuna ka, Samuel'' ""Shugabannin usulmai a Faransa sun la'anci harin. Tareq Oubrou, limamin wani masallaci a Bordeaux, ya ce suna tir da wannan hari. Shugaba Emmanuel Macron ya ce da alama harin na da alaƙa da harin ta'addancin masu ikirarin jihadi. An ruwaito shi yana cewa ''ba za mu bar su su zauna lafiya ba''. Bayan gangamin ranar Lahadi, an kuma shirya taron ta'aziyya ga Samuel Party ranar Laraba. Me ya faru ranar Juma'a? Mista Ricard ya ce maharin wanda ke zaune a wani gari mai nisan kilomita 100 daga inda ya yi kisan ya je makarantar da malamin ke koyarwa a ranar Juma'a, har ma ya buƙaci ɗalibansa su nuna masa malamin. Ba shi da wata alaƙa da malamin ko ma makarantar da yake koyarwa. Ya bi sahun malamin bayan ya tashi daga aiki, inda ya yi amfani da wuƙa wajen daɓa masa a kansa, sannan ya fille masa kai daga bisani. Shaidu sun ce an ji maharin na ihu yayin da yake sare kan malamin. Yayin da 'yan sanda suka kusance shi, ya harbe su da bindiga, daga nan ne suma suka mayar masa da martani tare da samunsa sau tara. An ga wata ƴar gajeruwar wuƙa a kusa da shi. Mahunkunta sun ce mutum ya sha gurfana a kotu, amma saboda ƙananan laifuka." https://www.bbc.com/hausa/labarai-54603671 +business Satar garin tuwo ta tilasta ba da katin shaida a wurin niƙa a Kano A baya da wuya ka ji an ce an sace garin tuwo a wurin niƙa duk da cewa a kan samu yanayin da ake yin musaya, wato wani ya ɗauki na wani amma ya bar nasa bisa kuskure. To amma a yanzu mazauna wasu unguwanni a birnin Kano, na ƙorafi dangane da yadda garin tuwonsu ke ɓacewa a wajen niƙa a ƴan kwanakin nan. Wannan ne dai ya sanya wasu masu inji da ke yin niƙan suka samar da hanyar rage sace-sacen, inda suka fito da bai wa duk wanda ya kai niƙa shaidar hakan. Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da wani rahoton Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ya ce an samu karin mutum fiye da milyan guda da ke fama da karancin abinci a jihar Kano sakamakon annobar korona. Har wa yau, wasu na alaƙanta al'amarin da irin matsin rayuwar da jama'a suka samu kansu a ciki saboda tashin gwauron zabi da farashin kayan masarufi ya yi sakamakon karin kudin man fetur da wutar lantarki da gwamnatin Najeriya ta yi. https://www.bbc.com/hausa/labarai-54436615 +politics Zaben 2023: PDP tana tantance 'yan takarar shugaban kasa "A ranar Juma'ar nan ce jam'iyyar PDP mai hamayya a Najeriya ta soma tantance masu son tsaya mata takarar shugaban kasa a zaben 2023. Bayanai sun nuna cewa babbar jam'iyyar adawar za ta tantance mutum 17 da ke fafatawa domin ganin sun tsaya mata takara a zaben shekara mai zuwa. Ana gudanar da tantancewar ce a ofishin jam'iyyar mai suna Legacy House, da ke unguwar Maitama, a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya. Jam'iyyar ta PDP ta sanya Naira miliyan arba'in a matsayin kudin fom na takarar shugaban kasa. Mutanen da ke son yi wa jam'iyyar takarar shugaban kasa sun hada da tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar; gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed; gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal. Kazalika akwai gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike; gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel; tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Bukola Saraki. Haka kuma akwai tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi da tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Anyim Pius Anyim. Sauran masu son tsayawa takarar shugaban kasa a PDP su ne: tsohon gwamnan Ekiti, Ayo Fayose; tsohon manajan daraktan First Bank, Muhammed HayatuDeen; fitaccen dan jarida, Dele Momodu; da sauransu. Tuni dai Atiku Abubakar da Sanata Saraki suka wallafa sako a shafinsu na Facebook suna masu cewa an tantance su. Tun a farko mako ne jam'iyyar ta soma tantance masu son tsaya mata takara a sauran mukamai da suka hada da gwamnoni da 'yan majalisar dokokin tarayya da jihohi. Daya daga cikin jami'an da jam'iyyar ta aika jihar Kaduna, Alhaji Yusuf Dingyadi ya shaida wa BBC cewa tantancewar ""za ta hada da duba shaidar kammala karatun masu son tsayawa takara, da rasiti na biyan haraji da kuma shaidar cewa mutum yana hidimta wa jam'iyyarmu."" PDP za ta tantance 'yan takarar ne kwanaki kadan bayan wata hadaka ta masu neman tsaya mata takara daga arewacin kasar ta wargaje. Hadakar, wacce ta kunshi Sanata Bukola Saraki da gwamnan Bauchi Bala Mohammad da gwamnan Sokoto, Aminu Waziru Tambuwal da Muhammad Hayatudeen ta wargaje bayan gaza yin maslaha a tsakaninsu." https://www.bbc.com/hausa/labarai-61269513 +technology Yadda mai tallar kayan ƙawa ta rungumi fasahar 3D yayin kullen korona Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon: Annobar cutar korona ta sa matasa dama suna baje fasaharsu ta ƙirƙire-ƙirƙire inda suke lalubo sabbin hanyoyin da za su ciyar da sana'o'insu gaba. A cikin wannan bidiyo za ku ga yadda wata matashiya 'yar asalin kasar Congo da ke Amurka ta rungumi fasahar 3D don tallata kayan ƙawa da take dinkawa a lokacin kullen korona. https://www.bbc.com/hausa/media-53739679 +business Guguwar Ian: 'Babu abin da muke so kamar wutar lantarki' An gudanar da zanga-zanga a Havana, babban birnin Cuba, bayan mahaukaciyar guguwar Ian ta lalata dukkan hanyoyin samar da lantarkin kasar ranar 27 ga watan Satumba. Bangarorin birnin da aka dawo da wutar lantarki ba su da yawa, abin da ya sa mutane suka shiga zanga-zanga a cikin duhu domin kira ga gwamnati ta dawo da hasken lantarki. https://www.bbc.com/hausa/articles/cmln2324472o +politics Lai Mohammed ya gamu da fushin masu amfani da shafukan zumunta "Ministan labaran Najeriya Lai Mohammed ya tayar da kura a shafukan sada zumuntar kasar sakamakon sanarwar da ya fitar cewa da a ce Muhammadu Buhari bai zama shugaban kasar ba da tuni Najeriya ta durkushe. Sanarwar da ofishin Lai Mohammed ya fitar ranar Lahadi ta bayyana cewa: ""Zaman Muhammadu Buhari shugaban kasa a shekarar 2015 ne ya hana Najeriya durkushewa bayan an shafe tsawon lokaci ana shugabanci maras alkibla."" Ministan ya ce Shugaba Buhari ya karbi jagorancin kasar ne a lokacin da ""aka mamaye yankuna da dama, a lokacin da garuruwa da biranen Najeriya da dama, ciki har da Abuja, suka zama filin wasa ga 'yan ta'adda kuma a lokacin aka sace arzikin kasar..."" Sai dai tun daga lokacin da aka fitar da wannan sanarwa 'yan kasar musamman a shafin Twitter suke bayyana ra'ayoyinsu a kansu inda galibi suke sukar ministan kan kare gwamnati duk da abin da suka kira gazawar gwamnatin Shugaba Buhari. Wani mai amfani da Twitter, Daniel Tariwe, ya bayyana cewa Lai Mohammed zai kare gwamnatinsu kodayaushe duk da cewa ta gaza saboda yana cikin wadanda suka gaza. Sai dai wasu na ganin kalaman Lai Mohammed wata hikima ce ta ""janye hankalin 'yan kasar daga tunanin mawuyacin halin da suke ciki."" 'Yan Najeriya sun kwashe makonnin baya bayan nan suna caccakar Shugaba Buhari sakamakon karin farashin man fetur da hasken wutar lantarki da tsadar rayuwar, abin da ya sa wani mai amfani da Twitter ya ce kalaman ministan za su iya janye hankulan 'yan kasar daga gare su. Ya ce: ""Idan gwamnatin nan tana son janye hankalin talakawa, sai kawai ta gaya wa Lai Mohammed ya fitar da sanarwa. Daga baya kowa zai yi mamaki."" Shi ma Esmart cewa ya yi Shugaba Buhari ""bai hana Najeriya durkushewa ba, ya taimaka wajen durkushewarta. Najeriya ta durkushe a karkashin jagorancin Buhari."" Sai dai wasu da dama sun yarda da kalaman Lai Mohammed suna masu cewa Shugaba Buhari ya hana kasar wargajewar. Mustapha Musa na cikinsu inda ya ce: ""Da dai kam yanzu wasun mu 'yan gudun hijira ne a Nijar, Chadi da Kamaru."" Shi ma Rayhan ya ce: ""Haka yake da bai hau mulki ba da talakawa sun tayar da yakin basasa a Najeriya. Saboda sun ce shi ne kadai ya rage mai gaskiya."" A makonnin baya bayan nan jami'an gwamnatin kasar na shan suka bisa wasu kalamansu inda ko a makon jiya ma kakakin shugaban Najeriya Malam Garba Shehu ya tayar da ƙura a shafukan sada zumunta bayan ya ce an taba sayar da litar man fetur kan naira 600 a shekarar 2013." https://www.bbc.com/hausa/labarai-54151853 +health Salon soyayya na masu lalurar wuce iyaka - 'Nan da nan nake zaƙuwa' """Lokacin da aka gano ina da lalurar wuce iyaka (BPD), na zaci ba zan iya yin lafiyayyar soyayya ba."" Irin abin da Mae mai shekara 21 ta ji ke nan a farkon wannan shekarar, lokacin da aka faɗa mata tana ɗuke da cutar wuce iyaka ta borderline personality disorder (BPD) - kuma haka da yawa daga cikin masu cutar ke ji a shafukan sada zumunta. Maganar BPD na ci gaba da samun gindin zama a shafukan zumunta, kuma Dr Liana Romaniuk, ƙwararriya kan yara da lalurar ƙwaƙwalwa a Jami'ar Edinburgh, na ganin irin yadda matasa ke tunkarar matsalar ke nan saɓanin na zamanin baya. ""Na samu matasa da yawa da ke tambaya ta cewa, 'zan iya kamuwa da BPD kuwa? Ina ganin ana samun ƙaruwar faɗakarwa kan hakan,"" in ji daktan. Borderline personality disorder (BPD) lalura ce da ke shafar ƙwaƙwalwa kuma ta saka wa mutum rashin natsuwa da sauya yadda mutum ya kamata ya gudanar da mu'amala da sauran jama'a. Ana kyautata zaton tana shafar duk mutum ɗaya cikin 100 a duniya. Akasarin masu lalurar sun fuskanci damuwa ko kuma banzatarwa a lokacin da suke yara, abin da ke jawo musu matsala wajen yin soyayya idan sun girma. Dr Romaniuk ta ce damuwa ba lallai sai a kan abu maras daɗi ba ko kuma an zalince su ba - abubuwan sun ƙunshi kamar iyayensu su rabu, su zama ba a jin tunaninsu, ko kuma mutuwar uwa ko uba lokacin da suke yara. Akwai muhawara tsakanin ƙwararru, a cewar Dr Romaniuk, kan ko BPD da gaske lalura ce ko kuma wasu abubuwa da suka faru a baya ne ke haifar da matsalar. Mae ta fara bincike kan BPD saboda ta lura tana zama ""mayya"" da mai yawan zaƙuwa kan soyayya. ""Na lura alamomin cutar na ƙruwa a tare da ni a harkar soyayyata,"" a cewarta bayan an gano cutar a tare da ita a watan Maris na 2021. ""Nan da nan nake zaƙuwa. Zan ji ina so na yi ta kira ko tura saƙon tes, kuma zan ji ina so na keɓe daga ƙawayena - na daina yin abubuwan da nake jin daɗi saboda wannan mutumin."" Abin da wani bai ɗauka a bakin komai ba, inda yana da matsalar BPD sai ya zama gagarumi. ""Wata rana ina gidan ƙawata lokacin da na ga saƙo daga saurayina kuma kalaman sun girgiza ni - nan take na tattara kayana na ce: 'Dole ma in tafi', na wuce gidansa kai-tsaye cikin minti 15. ""Na dinga jin gabana yana faɗuwa. A ƙarshe dai lafiyata ƙalau. Sai na koma wajen ƙawata. Abin ya ba ta mamaki, amma ban ci gaba da hira yadda ya dace ba saboda gabana ya ci gaba da faɗuwa."" Fargabar barin mutum ma kan ta'azzara lamarin. ""A 'yan makonnin da suka wuce a soyayyarmu, na yi ta ɓatawa da samarina ina faɗa musu cewa zan ƙyale su saboda ina yi musu hassada [ta irin son da nake yi musu],"" a cewar Mae. ""Idan kuma suka rabu da ni sai in ji ba daɗi, in yi ta kiran su ina kuka, ina yi musu magiya su dawo. Irin wannan abu na da alaƙa da lalurata ta BPD."" Tun bayan gano cutar, Mae ta fara yin wani magani da ake kira dialectical behavior therapy (DBT) a turancin Ingilishi - wanda mutum ke tattaunawa da ƙwararru don gano yadda ya kamata su dinga saita mu'amalarsu. Ta kuma fara shan ƙwayoyin rage damuwa. ""Yanzu na kan ji dama-dama,"" in ji ta. Akasari lalurar kan taso ne saboda tsoron rasa abokin zama. ""Abin da masu lalurar suka faɗa min shi ne akwai yiwuwar mutum ya ɓata da abokinsa kafin abokin ya ɓata da shi,"" a cewar Dr Romaniuk. ""Mutum zai iya ƙirƙirar dalilin da zai sa ya katse soyayyarsa da wani ko ya shirya jarrabawa don gane masoyinsa na sonsa...amma masu lalurar na ganin gara su zama cikin shiri a kodayaushe saboda gudun abin da ka iya faruwa.""" https://www.bbc.com/hausa/articles/cyewnpdrjnlo +entertainment ... Daga Bakin Mai Ita tare da Hadiza Kabara "Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon: Hadiza Muhammad Sani wadda aka fi sani da Hadiza Kabara ta ce ta soma sha'awar harkar fim ne bayan ta kalli wani fim mai suna 'Allura Da Zare'. A tattaunawarta da BBC a shirin Daga Bakin Mai Ita Kashi na 25, Hadiza Kabara ta ce a lokacin tana yarinya ita mace ce mai tsokana da faɗa. Ta ce ita mutum ce mai son cin shinkafa da miya da salad ""ya ji nama zuƙu-zuƙu."" A cewarta, abin da ya ba ta tsoro da ba za ta taɓa mantawa ne kuma ya sa ta sheƙa a guje shi ne tsaka. Ɗaukar bidiyo: Yusuf Yakasai Tacewa: Fatima Othman" https://www.bbc.com/hausa/media-55080214 +sports Monaco 3-0 PSG: An yaga barakar Paris St Germain a Ligue 1 Paris St Germain ta sha kashi da ci 3-0 a gidan Monaco a gasar Ligeue 1 karawar mako na 29 da suka fafata ranar Lahadi. Wissam Ben Yedder ne ya fara cin kwallo a minti na 25 da fara tamaula, sannan Kevin Volland ya kara na biyu a minti na 68 daga baya Yedder ya kara na uku a bugun fenariti kuma na biyu da ya ci, saura minti shida su tashi daga fafatawar. Koci, Mouricio Pochettino zai kara fuskantar kalubale a shirin da yake na lashe kofin babbar gasar Faransa ta bana, bayan da Real Madrid ta fitar da PSG daga Champions League a kakar nan. Pochettino ya maye gurbin Thomas Tuchel ranar 2 ga watan Janairu da nufin zai lashe Champions League, wanda kungiyar ke kishirwar kofin da bata taba dauka ba. Shi kuwa Tuchel wanda ya koma Chelsea ranar 1 ga watan Janairun 2021 ya lashe Champions League a kakarsa ta farko da jan ragamar kungiyar Stamford Bridge. Magoya bayan PSG kan yi wa Lionel Messi da Neymar ihu a wasan da suke yi a gida a baya bayan nan, sai dai kuma PSG a kwanan nan akwai damuwa kan rashin kokarin kungiyar a wasannin da take buga wa a waje, wadda ta yi rashin nasara a karawa hudun da ta yi. Da wannan sakamakon PSG tana nan a matakinta na daya a kan teburin Ligue 1 da maki 65. Sauran wasannin Paris Germain a kakar bana: French Ligue 1 Ranar Lahadi 03 ga watan Afirilun 2022 Paris St-G.vLorient French Ligue 1 Ranar Lahadi 10 ga watan Afirilun 2022 ClermontvParis St-G. French Ligue 1 Ranar Lahadi 10 ga watan Afirilun 2022 Paris St-GermainvMarseille French Ligue 1 Ranar Laraba 20 ga watan Afirilun 2022 Angers da Paris St-Germain French Ligue 1 Ranar Lahadi 24 ga watan Afirilun 2022 Paris St-Germain da Lens French Ligue 1 Ranar Lahadi 01 ga watan Mayun 2022 Strasbourg da Paris St-Germain French Ligue 1 Ranar Lahadi 08 ga watan Mayun 2022 Paris St-Germain da Troyes French Ligue 1 Ranar Asabar 14 ga watan Mayun 2022 Montpellier da Paris St-Germain French Ligue 1 Ranar Asabar 21 ga watan Mayun 2022 Paris St-Germain da Metz https://www.bbc.com/hausa/wasanni-60815163 +politics Ba zan sauka daga shugabancin PDP ba - Iyorchia Ayu "Shugaban jam’iyyar PDP a Najeriya Iyorchia Ayu ya ce ko a jikinsa game da kiraye-kirayen da wasu suke yi cewa ya sauka daga kan mukaminsa. Kazalika ya ce masu yin hakan yara ne da ba su fahimci manufofin kafa jam’iyyar ba. A hirarsa da BBC, tsohon dan Majalisar Dattawan Najeriyar ya ce a iya saninsa ‘yan kasar ne suka zabe shi bisa sharuddan da jam'iyyarsu ta shata. Ya kara da cewa ko a lokacin da za su gudanar da zaben shugabannin PDP na kasa, an yanke cewar ba za a yi la'akari da bangaren da shugaban jam’iyyar ya fito ba wurin fid da dan takarar shugaban kasar. An jima ana kai ruwa rana tsakanin jam'iyyar da dan takarar shugaban kasa da ya sha kaye a zaben fid da gwani, wato gwamnan Rivers Nyesom Wike, wanda rahotanni suka ce ya gindaya sharuddan ci gaba da zama jam'iyyar, da kuma mara wa Atiku Abubakar baya a matsayin dan takararta a zaben 2023. Daga cikin sharuddan akwai bukatar Shugaban jam'iyyar Iyorchia Ayu, wanda ya fito daga Arewacin Najeriya ya sauka daga mukaminsa. Sai dai a martanin da ya yi da BBC ta tambaye shi, Mr Ayu ya ce ba bu inda za shi, la'akari da cewa an zabe shi ne bisa dokokin da jam'iyyar PDPn ta shimfida, a don haka ba zai sauka ba saboda kawai wasu ba sa son ganin shi a kai. ''An zabe ni na Shugabanci PDP har tsawon shekaru hudu, yanzu ban kai shekara daya ba ma. ''Maganar zaben Atiku ba ta shafi mukamin Shugaban jam'iyya ba. Ni na ci zabe. A cikin kundin tsarinmu muka yi wannan.' ''Ba wani laifi da na yi, ina gyara jam'iyya ne, hayaniyar da ake yi wallahi ba ta dame ni ba,'' in ji Mr Ayu. Shugaban PDP ya kara da cewa ''ni dai na san ina yin aiki, ban saci kudi ba, ban yi wani laifi ba, don haka ban ga abin magana ba.'' Sai dai kuma ya musanta batun cewa rashin dinke baraka da Gwamna Wike zai iya kawo wa jam'iyyar cikas a zaben na 2023, inda yace su suka asassa jam'iyyar PDP a Najeriya, saboda haka 'wasu yara' da ba su san gwagwarmayar da suka sha ba ba za su iya basu matsala ba. ''Lokacin da muka fara tafiyar PDP wadannan yara bamu gan su ba. Su yara ne basu san abunda yasa muka kafa wannan jam'iyyar ba. ""Ba za mu yarda mutum daya ya zo ya lalata mana jam'iyya ba,'' a cewar Ayu. Duk da yunƙurin da jagororin jam'iyyar PDP suka yi na rarrashin Wike, har yanzu gwamnan bai nuna alamun ajiye kayan yaƙinsa ba, inda a baya-bayan nan yake ci gaba da hulɗa da jiga-jigan jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya. To amma kuma Wike bai fito karara yace zai yaƙi tafiyar Atiku ba, duk da ba ya shiga dukkan ayyukan jam'iyyar, hasali ma ya fi yin hulɗa da 'yan sauran jam'iyyu ciki hadda babbar abokiyar hamayyarsu wato jam'iyyar APC mai mulki. Sai dai a cikin makon da ya gabata dan takarar Shugabancin kasa na PDPn Atiku Abubakar da wasu gwamnonin jam'iyyar sun gana da Wike a birnin London na Burtaniya, inda ake kyautata zaton suna ci gaba da rarrashin gwamnan na Rivers ne game da bukatar ya rungumi tafiyar Atikun. To amma kawo yanzu Wike bai fito ya bayyana matsayarsa ba, don kuwa ko bayan jiga-jigan PDPn, ya sa labule da wasu yan takarar Shugaban kasa a jam'iyyun hamayya, da suka hada da Bola Tinubu na APC da kuma Peter Obi na Labour Party. Sai dai kuma yayin da PDP ke fadi tashin dinke baraka da Wike, kwatsam sai gashi ta yi babban kamu a Arewacin kasar, bayan da tsohon gwamnan Kano Sanata Ibrahim Shekarau ya sanar da sauya sheka daga jam'iyyar NNPP zuwa PDPn. Shugabancin PDP dama yan takararta basu yi wata-wata ba suka dira birnin Kano don karbar Malam Ibrahim Shekarau, wanda ba makawa shigarsa PDPn zai kara wa jam'iyyar tagomashi musamman a jihar ta Kano mai matukar tasiri a zaben Shugaban kasar Najeriya." https://www.bbc.com/hausa/articles/c72z3r6pj98o +entertainment Muhawara ta kaure tsakanin ƴan shekarun 1980s da matasa da ƴan bana-bakwai a Twitter a Najeriya "A baya-bayan nan, kalamai kamar Millennials, Baby-boomers, Gen Z da Gen X sun karaɗe shafukan sada zumunta musamman ma shafin Twitter. Wannan rabe-rabe ne na mutane da suka danganci shekarun haihuwarsu kamar haka: Ƴan ƙasa da shekara 25, wato ƴan Gen Z ba sa so ana sa su a jerin ƴan shekara 40 wato ƴan millenials kuma suna yawan bayyana hakan a shafukan sada zumunta musamman Twitter da TikTok. Asali ma, wasu ƴan Gen Z cewa suke yi an kirkiri waɗannan shafuka ne don su, musamman ma shafin TikTok. Sannan su kan yi shaguɓe ga ƴan Millennials su ce shafin Facebook ne dai-dai da su kuma shi kaɗai suke iya amfani da shi. Ɓangarorin biyu kan zolayi juna ne bisa wasu halaye da suke zargin juna da su. Misali: ƴan millennials kan ce ƴan Gen Z shagwaɓaɓɓu ne, wato sun samu komai a ɓagas saboda sun zo a zamanin da aka samu ci gaba sosai a fannin kimiyya da fasaha. Don haka akwai abubuwan da ba su san zafinsu ba kamar wahalar da aka sha a baya ta kiran waya da wayar tarho ta girke a gida, da bin layi a banki ba don amsar kuɗi tunda yanzu akwai na'urorin ATM a ko ina da dai sauransu. Wato dai ƴan Gen Z sun buɗi ido da kimiyya fiye da ko wane rukuni na mutuna a duniya. Haka kuma, yan Millenials na zargin ƴan Gen Z da zama masu bijire wa dokoki da tsananin son cin gashin kansu, kuma ba su da girmama na gaba ciki har da iyayensu. Abin da suka fi saka wa a gaba kwalliya da ado da ƙyale-ƙyale. A ɗaya ɓangaren kuma, ƴan Gen Z na zolayar ƴan millennials da cewa sun fara tsufa kuma ba su da wayewar kai kamar su. Su kan ce millennials ƴan wahala ne da idonsu ya rufe da neman kudi sannan salon yadda suke ado bai da tsari. Sai dai su millenials na cewa, ba wahala ba ce illa dai sun san ciwon kansu kuma iyayensu sun yi masu horo mai tsauri ta iya dogaro da kai. Haka kuma, su kan ce ba su dogara da kimiyya da shafukan sada zumunta ba wajen gudanar da komai. To, irin wannan muhawarar ce ta kaure a shafin Twitter a Najeriya tsakanin ɓangarorin nan biyu kuma masu amfani da shafin na ɓangarorin biyu na ta yada wa juna magana kuma kawo yanzu an yi amfani da maudu'in #Millennials da #GenZ fiye da sau 180,000. An fara muhawarar barkwancin ne tsakanin rukunin mutanen biyu kuma sun ci gaba da zolayar juna kamar yadda suka saba. Sun yi amfani da hotuna da bidiyo da ake kira 'meme' da 'gifs' wajen aika saƙonnin. Wani mai amfani da shafin Twitter mai suna Bossbaeby ya rubuta: ""Ƴan millennials kan ce abin da babba ya hango a zaune ko yaro ya hau Rimi ba zai gan shi ba. Mu kuwa ƴan Gen Z sai mu ce abin da babba ya hango a zaune, ma yi amfani da jirgi marar matuki mu hango."" Wannan tweet dai ya nuna alfahari da ƴan Gen Z ke yi da iliminsu da ƙwarewarsu wajen amfani da kimiyya. Shi kuwa TimiFash mai amfani da shafin na Twitter ya wallafa wannan sakon ne yana cewa: ""Ƴan millenials a hanyarsu ta zuwa aiki da karfe 7:30 na safe bayan yin baccin awa uku da minti 26"" sannan ya ɗora bidiyon wani mutum yana tuƙi a mota yana zargin kansa da zama wawa saboda ya bari ya makara wajen zuwa aiki. Wannan saƙon dai ya bayyana kallon da yan Gen Z su ke yi wa ƴan millenials na wahalallu waɗanda ba su da wani jin dadi a rayuwa sai zuwa aiki da neman kuɗi. Mai amfani da shafin Twitter Jaysonrogue ya wallafa wani saƙo da hotuna yana nuna bambancin yadda ƴan millennials da ƴan Gen Z ke mu'amala da juna. Yayin da ƴan millennials ke haɗuwa su yi hira su tattauna a tsakaninsu, ƴan Gen Z kuwa sai dai su yi ta danna wayoyinsu. Wannan muhawarar dai na nan tana ci gaba a shafin Twitter a Najeriya, ɓangarorin biyu na ta zolayar juna. Sai dai yayin da ake ta tafka wannan muhawara tsakanin millennials da Gen Z, wani bangare na nan yana tasowa wato wanda suke biyo bayan Gen Z. Su kuma ana kiransu Genration Alpha." https://www.bbc.com/hausa/labarai-56129423 +health 'Yadda na fahimci cutar kuturta ce ta kama ni' "An fi alaƙanta ciwon kuturta da gado, amma masana na cewa duk da ana gadar cutar ana kuma daukarta. Isa (ba sunansa ba kenan) mai shekaru kimanin 50 ya je asibitin Yadakunya da aka fi sani da asibitin Bela da ke birnin Kano domin karbar maganin larurar kuturta. A shekarar da ta gabata ne Isa ya fara fahimtar sauyi a jikinsa wanda daga baya ya zo asibiti aka kuma sanar da shi cewa cutar kuturta ce. ""Shekara daya kenan na fara jin kasan kafafuna ya yi dundurus musamman ma idan ina yin aiki a cikin ruwa. A bana ne kuma sai na ga kafafun nawa kamar sun kone. Wani lokacin sai ya yi bawo ya bare ya warke da haka amma wani lokacin kuma sai ya gwale har sai na yi jinya."" Isa ya kara da cewa duk da yadda ciwon ke barewa amma ""ba ya yi min ciwo sai dai kawai ya bare. Za ka ga ya yi kamar wuta ta kona ni."" Ya ce ba gadon cutar ya yi ba, daga baya ta same shi.""Ni duk a iyayena babu mai wannan cuta,"" in ji shi. Sai dai ya ce iyayensa da sauran magabatansa sun ba shi shawarar ya yi amfani da maganin gargajiya. ""Kuma haka na yi ta amfani da maganin na gargajiya amma ban ga wani sauyi ba."" A yanzu dai haka jihar ta Kano ta samu mutum 118 da ke fama da cutar kuturta, abin da ke nuna cewa a kan samu mutum daya a duk cikin 10,000 da ke samun wannan cuta. ""Wannan ya nuna har yanzu ana samun masu ɗauke da wannan cuta jifa-jifa kuma dole ne a sa ido domin ganin ba ta samu wurin zama ba,"" in ji Dr Ibrahim Aliyu Umar, jami'i mai kula da sashen dakile cutar tarin fuka da ta kuturta a Kano. Galadiman kutaren Bela da ke Kano, Bala Adamu ya ce rashin ilimi da wayewa na daga cikin dalilan da ya sa aka sami dawowar cutar ta kuturta a tsakanin al'umma. ""Mutane suna boye cutar saboda tsabar gidadanci domin kada a ce suna da cutar kuturta."" Da ma dai wani rahoton Hukumar yaki da cututuka masu yaduwa a Najeriya na 2018 ya nuna cewar kimanin mutum dubu 3,500 ne suke kamuwa da cutar kuturta a kasar. Hakan ya nuna cewar an sami karin masu fama da wannan cuta bayan shekaru 20 da hukumokin Najeriyar suka ce an magance ta a kasar baki daya." https://www.bbc.com/hausa/labarai-59744724 +business e-Naira: Bayanai dalla-dalla kan sabon nau'in kudin Najeriya na laturoni Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon: Babban bankin Najeriya ya bayyana hanyoyin da za a yi amfani da sabon nau'in kudin Najeriya na laturoni na eNaira. A ranar Litinin ne shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya ƙaddamar da kuɗin. A wannan bidiyon Umar Mikail ya mana bayani kan yadda tsarin zai yi aiki. https://www.bbc.com/hausa/media-59081623 +health Lafiya Zinariya: Matsalar Yoyon Fitsari a tsakanin mata Latsa alamar lasifika domin sauraron shirin: Hukumar lafiya ta Duniya, duk shekara tsakanin mace 50,000 zuwa 100,000 ne ke gamuwa da matsalar yoyon fitsari a lokacin haihuwa. Haka kuma, hukumar ta yi kiyasin cewa mata miliyan 2 ne ke fama da ciwon a nahiyar Asiya da kasashen yankin Afrika kudu da hamadar sahara. Majalisar Dinkin Duniya ta ce, yoyon fitsari na faruwa ne idan aka samu tsagewa a hanyar da jariri ke fitowa daga jikin mahaifiyarsa saboda nakuda mai tsawo ba tare da samun kulawar malaman jinya ko likitoci ba. Yoyon fitsari dalilin haihuwa na aukuwa ne a tsakankanin mata marasa galihu musamman wadanda ke rayuwa a yankunan da babu isassun asibitoci. Mafi yawan matan da kan gamu da wannan matsala matasa ne kuma wadanda ba su yi karatun boko ba sannan da yawa daga cikinsu bas a neman taimako a asibiti. Wannan ba ya rasa nasaba da tsoro ko kunya ko fargabar fuskantar tsangwama dalilin cutar a cewar Majalisar Dinkin Duniya. https://www.bbc.com/hausa/shirye-shirye-na-musamman-53000424 +business Zabibi da bula da algarura: Ƴan Najeriya sun cashewa sabbin kudin naira "Tun bayan da Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya ƙaddamar da sabbin takardun naira da aka sauyawa fasali, ƴan ƙasar suka yi wa batun ca ta hanyar bayyana ra'ayoyinsu kan hakan. Shafukan sada zumunta na Facebook da Tuwita da Instagram da Tiktok da ma Whatsapp sun zama wuraren da ba a zancen komai sai na sabbin kudin. Da yawan mutane sun nuna rashin jin dadinsu kan tsarin sabbin kuɗin, suna cewa ba su zaci haka sauyin zai zo ba. An ƙaddamar da kuɗaɗen ne a wajen taron mako-mako da ake yi a fadar shugaban ƙasar a Abuja a ranar Laraba. Shugaba Buhari ya ce sababbin takardun kuɗin za su taimaka wa Najeriya ta wajen warware matsaloli da dama da suke addabar ƙasar. A shafukan Facebook da Tuwita, sai da ya zama shi ne babban batun da aka fi tattaunawa a kansa tun daga ranar Laraba har zuwa wayewar garin Alhamis. Tiktok ma ba a bar shi a baya ba, don yawanci matasa ƴan Najeriya da ke amfani da shafin sun mayar da hankali ne yin raha da barkwanci kan lamarin. Yayin da Whatsapp da Instagram suka zama wajen da kusan kowa ya dinga wallafa sabbin kudin a sitatus (status) da sitori (story) ɗinsu. A shafin Tuwita a ranar Laraba an yi amfani da maudu'in #Naira sau fiye da 200,000, yayin da a ranar Alhamis ma aka ci gaba da amfani da shi har sau fiye da 136,000. Facebook kuwa a ranar Larabar sama da mutum 300,000 ne suka yi ta tattauna zance har zuwa Alhamis. Ko a shafinmu na BBC Hausa Facebook, wanda yana ɗaya daga cikin shafukan da suka fara saka hotunan sabbin kudin, inda alƙaluma suka nuna cewa mutum miliyan 1,300,040 suka gani, yayin d ayawan waɗanda suka so suka yaɗa suka kuma yi tsokaci ya kai mutum 309,000, kamar yadda za a iya gani a ƙasa. Yawanci masu tsokacin sun ce sabbin kudin sam ba su da kyau da jan hankali, saboda irin launin da aka sauya musu. Naira 200 dai an mayar da ita mai jan launi, naira 500 ta koma koriya, ita kuwa naira 1,000 sai ta koma toka-toka. Hakan ya sa wasu cikin raha suka dinga cewa kawai dai an barbaɗawa 200 jawa ne, 500 kuma an barbaɗa mata algarura sai aka dulmiya naira 1,000 kuma a cikin bula. A wani saƙon na daban kuma da BBC Hausa ta sake wallafawa don neman masu sauraro su gaya mana bambancin da ke tsakanin sabbi da tsofaffin kuɗaɗen, shi ma mutane sun yi ta bayyana ra'ayoyinsu. Kafin a ce mene ne wannan tuni ƴan Najeriyar suka mayar da abin wani salon raha da ya zama yayi, inda suka dinga ɗaukar hotunan kansu suna gyaggyara shi da launuka suna cewa su ma ga sabon sauyin fuskokinsu tamkar na nairar. Sai a ga mutum ya yi hotonsa cikin launi uku na ja da kore da ruwan bula, abin ma bai tsay a kansu ba kawai har hoton shugaban babban bankin Najeriyar Godwin Emefiele aka dinga sauyawa launin. Sai aka mayar da abin yayi, kowa ya dinga sauya salon hotonsa yana wallafawa. Ga dai abin da sauran masu tsokaci ke cewa: NKEM #PeterObi2023@Nkemchor ya ce: ""Waye ya yi wa Emefiele haka? Ko martanin ake mayar masa kan sauya fasalin nairarmu? Akwai kuma wasu da su yabon sabon kudin suke yi kamar haka:Arabinrin Aderonke@AderonkeWya ce: ""Ya ku sabbin takardun kuɗi, ba na daga cikin masu sukarku. Ku sani cewa ina maraba da ku a cikin asusun bankinsa da gidana da kuma tabbatar da cewa za ku samu tsaro. Ku zo min da yawa a miliyoyi a launukanku. voice-of-Fulɓe@Fulani_Tutor· A wajen kaddamar da sabbin kudin din Shugaba Buhari ya ce sauya fasalin kudin zai taimaka wa tsare-tsaren manufofin kudi na CBN, sanan kasancewar wannan ne karo na farko da aka buga naira a Ma’aikatar Buga Kudi ta Najeriya zai hana yaɗuwar jabun kuɗin. 1. Zai taimaka wajen rage tashin farashin kaya domin zai sa a fito da tsoffin kudin da aka bobboye. 2. Zai kuma taimaka waje tsara manufofin da suka jibanci kudi domin za mu samu sahihan alkaluma kan yawan kudin da ke akwai. 3. Sabon tsari zai taimaka wajen shigo da kowa cikin harkokin kuɗi da rage yawan hada-hadar kuɗi laƙadan da kuma tabbatar da cewa Najeriya ta bi sahun tarin hada-hadar kuɗi a zamanance. 4. Sauya fasalin kudin kuma zai taimaka wajen yaki da almundahana domin hakan zai sa a yi ta kokarin dawo da manyan takardun kudi wadanda su ne ake amfani da su wajen almudahana kuma hukumomin tsaro za su iya gani idan ana kokarin fitar da irin wadannan kudaden daga bankuna." https://www.bbc.com/hausa/articles/cle31nev14do +politics 'Peter Obi ya zabi Datti Baba-Ahmed abokin takara ne ba don samun kuri'a ba' Masana harkokin siyasa a Najeriya na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu a kan matakin da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour, Peter Obi, ya dauka na zabar Dakta Datti Baba-Ahmed a matsayin mataimakinsa. Masanan sun ce daukar Dakta Datti Baba-Ahmed, a matsayin abokin takara da Peter Obi ya yi, ba wani abu ba ne illa yana son ya nuna cewa yana da abokin takara ne daga Arewa. Dakta Faruk Bibi Faruk, wanda malami ne a Jami’ar Abuja, ya shaida wa BBC cewa Peter Obi ya yi hakan ne ba wai don ya samu kuri’a ko goyon baya ba. Ya ce “Dalilina na fadin haka kuwa shi ne Datti Baba-Ahmed, dan takara ne wanda a cikin shekarun da ya shafe yana siyasa ya samu ya je majalisar kasa sau daya.” Malamin jami’ar ya ce mutum ne wanda yake siyasa mai akida, amma kuma marar jama’a. Ya ce,” A maganganu da kuma irin alkibla ta siyasa a Najeriya, ya yi maganganu masu fa’ida a da, sannan ya dauki alkibla mai kyau a tafiyar siyasa, to amma ba shi da jama’ar da zai iya kawo wa dan takara dauki.” Dakta Faruk Bibi Faruk, ya ce ana yi wa jam’iyyar Labour kallon ta ‘yan gurguzu, wato ta irin mutanen da ke kyamar masu arzikin da ba a san ta inda suka same shi ba, a yanzu ta zama jam’iyyar da take farautar duk inda mai danshi-danshi ya ke don ta ba shi dama yazo ya yi takara. Ya ce, ‘’ Wannan ba abin da yakamata jam’iyyar mai rajin tafiyar da harkar kwadago ta kasa ta rinka yi ba ne, saboda Peter Obi cikakken dan kasuwa ne amma kuma ya samu takara a jam’iyyar.” Malami Bibi Faruk ya kuma ce maimakon a ce an samu wani dan gurguzu ya goya masa baya, sai aka dauko wani hamshakin dan kasuwar aka jona tare. Babban burin jami'yyar Labour, kamar sauran takwarorinta abokan hamayya shi ne ta kwace mulki daga hannun jam'iyyar APC. Sai dai wasu masana dai na ganin cewa jam'iyyar za ta fi tasiri ne a wani bangaren Najeriya, duk kuwa da daukar Datti Baba-Ahmed din a matsayin mataimaki. https://www.bbc.com/hausa/articles/c0vwy9jyjwno +entertainment Hotunan abubuwan da suka faru a Kannywood makon jiya Mun kawo muku labaran abubuwan da suka faru a Kannywood da 'yan Kannywood a makon jiya. https://www.bbc.com/hausa/labarai-51905459 +health Coronavirus: Kasashe na watsi da kayayyakin China Gwamnatocin kasashen turai da dama sun yi watsi da kayayyakin da ake kerawa a China domin yaki da annobar coronavirus. Dubban kayan gwaji da tukunkumin fuska ba su da inganci ko sun lalace, a cewar mahukuntan Spaniya da Turkiya da kuma Netherlands. Dubban mutane ne ke dauke da kwayar cutar coronavirus a turai. Sama da mutum dubu 10 sun mutu a Italiya tun bayan bullar cutar a kasar. A birnin Wuhan na China cutar ta soma barkewa a karshen shekara ta 2019. Gwamnatin kasar ta dau matakai masu tsauri na hana zirga-zirga domin dakile annobar. A ranar Asabar, ministan lafiyar Netherland ya sanar da cewa ya janye takunkuman fuska dubu 600. Kayan sun iso kasar ne daga China a ranar 21 ga watan Maris, kuma an raba su a asibiti tsakanin jami'an lafiya. Jami'ai a Dutch sun ce takunkumin ba shi da inganci, sannan baya aiki yadda ya dace, duk da cewa sun shigo da su a matsayin masu inganci. Jami'an sun ce ''An dakatar da amfani da sauran kayayyakin cikin hanzari kuma dama ba a rarrabasu ba, kuma yanzu mun yanke hukunci ba zamu yi amfani da kayayyakin ba.'' Gwamnatin Spaniya ita ma ta fuskanci irin wannan matsalar da kayayyakin na gwaji da ta yi oda daga wani kamfanin China. Ta sanar da cewa ta siyo dubban kayayyakin gwaji domin dakile bazuwar annobar, sai dai daga bisani ta ba da sanarwar cewa na'urar da ta siyo kusan dubu 60 ta gaza tantance ko mutum na dauke da cutar. Ofishin jakadancin Spaniya da ke China ya wallafa cewa kamfani da ke samar da na'urar, Shenzhen Bioeasy Biotechnology, ba shi da lasisi a hukumance daga mahukuntan lafiyar China na sayar da kayayyakinsa. Ya kuma bayyana cewa kayayyakin tallafi daga gwamnatin China da Alibaba ba su danganci wadannan kayayyaki na kamfanin Shenzhen Bioeasy ba. Ita ma Turkiya ta sanar da cewa ta siyo irin wadannan kayayyaki daga China wanda ba sa aiki yadda ya kamata, ko da yake ta ce akwai wasu dubu 350 da ke aiki da kyau. Wadannan zarge-zarge na rashin ingancin kayayyakin China ya zo ne bayan masu suka sun yi gargadin cewa kasar na iya amfani da barkewar wannan annoba wurin karfafa tasirinta a duniya. A ranar litinin mutum 812 annobar ta hallaka a Spaniya a cikin sa'o'i 24 - wannan ya kawo adadin alkaluman mamata zuwa 7,340. Akwai kuma sama da mutum 85,000 da ke dauke da cutar - adadin da ya zarta na China. An dau sabbin matakai a Spaniya da suka danganci haramta fita aiki na mako akalla biyu. Har yanzu dai Italiya ce kasar da cutar ta fi yiwa illa a duniya. Sama da mutum dubu 10 ne suka rasa rayukansu, sannan akwai dubu 100 da ke dauke da annobar. Amma dai Amurka ce cibiyar cutar a yanzu inda mutanen da suka harbu da cutar a kasar ya zarta kowacce kasa. https://www.bbc.com/hausa/labarai-52101605 +politics Kotu ta amince APC ta gudanar da babban taronta Wata babbar kotu a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya ta yanke hukuncin kyale jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta gudanar da babban taronta na kasa a ranar 26 ga watan Maris na wannan shekarar. A ranar Juma'a alkalin kotun, Mai shari'a Bello kawu ya yanke hukunci cewa 'ya'yan jam'iyyar ba su da hurumin kai kararta. Ya ce wani umarnin Kotun Kolin Najeriya kan wani batu irin wannan ya sha gaban wanda babbar kotun ta fitar na 18 ga watan Nuwambar bara. Kotun ta daga zamanta zuwa ranar 30 ga wannan watan na Maris domin ci gaba da sauraren karar. Wani mamba a jam'iyyar mai suna Salisu Umoru ne ya shigar da kara inda yake so kotun ta hana jam'iyyar ta APC da gwamna Mai Mala Buni da kuma hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya, INEC su shirya babban taro na kasa na jam'iyyar har sai bayan an kammala sauraren karar da ya shigar. Cikin mako biyun da suka gabata wasu gwamnonin jihohin kasar sun yi kokarin sauya shugabannin jam'iyyar, matakin da ya janyo karuwar fargaba da matsaloli ga 'ya'yan jam'iyyar. Sau uku ana cin karo da matsaloli yayin da 'ya'yan jam'iyyar ke kokarin samar da shugabanin da za su karbi ragamar jam'iyyar daga hannun kwamitin riko karkashin gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni. Karar da aka shigar a gaban kotun wanda ke son a kawar da umarnin kotun na ranar 18 ga watan Nuwamba 2021 ya gamu da cikas bayan da wasu lauyoyi biyu, Shuaibu Aruwan (SAN) da Michael Adoyi suka sanar da kotun cewa sune ke wakiltar jam'iyyar. Bayan da kotun ta zauna ranar Talatar da ta gabata, Mista Aruwan ya sanar da kotun cewa ya sami wata wasika daga jam'iyyar APC da ta tabbatar da nadinsa a matsayin lauyan jam'iyyar a wannan shari'ar kamar yadda kotun ta umarci a yi. Daga nan sai ya nemi kotun ta kawar da umarnin kotun na farko saboda rashin hurumi. Amma lauya Mike Enahoro-Eba, wanda shi ke wakiltar wadanda suka shigar da karar ya ki amincewa da wannan bukatar, yana cewa dokokin kotun sun bukaci a bayar da kwanaki bakwai domin wadanda ake kalubalanta su sami damar mayar da martani. Daga nan ne alkalin da ke sauraron karar, Mai shari'a Bello Kawu ya ajiye ranar Juma'a 18 ga watan Maris domin yanke hukunci. Ganin muhimmancin wannan ranar ga jam'iyyar ta APC, masana siyasar Najeriya na cewa rashin warware wannan matsalar na iya haifar da babban kalubale ga jam'iyyar ta APC mai mulkin Najeriya ganin cewa kasa da shekara guda ya rage a gudanar da babban zabe a kasar, wanda 'yan kasar za su zabi sabon shugaban kasa da gwamnonin yawancin jihohi da kuma 'yan majalisun tarayya da jihohin kasar. https://www.bbc.com/hausa/labarai-60791884 +entertainment ...Daga Bakin Mai Ita tare da Abdul Amart Latsa hoton sama don kallon bidiyon Daga Bakin Mai Ita wani shiri ne na BBC Hausa da ke kawo muku hira da fitattun mutane kan wasu abubuwan da suka shafi rayuwarsu zalla. A wannan kashi na 18, shirin ya tattauna da fitaccen tauraron fina-finan Hausa Abdul Amart, wanda aka fi sani da Mai Kwashewa, inda ya amsa tambayoyin da za su sa ku dariya. https://www.bbc.com/hausa/media-51954519 +sports Manchester City ta dauki Kalvin Phillips Manchester City ta dauki dan kwallon Leeds United, Kalvin Phillips kan fam milayan 45. Dan kwallon tawagar Ingila, mai shekara 26, ya saka hannu kan yarjejeniyar kaka shida da kungiyar da ta lashe Premier League a kakar da ta wuce. Dan wasan ya zama na uku da Pep Guardiola' ya dauka a bana, bayan Erling Haaland da kuma Stefan Ortega Moreno. Phillips, wanda ya buga wasa 235 a kaka takwas a Leeds United, yana da sauran kaka biyu kwantiraginsa ya karkare a Elland Road, kafin cinikin nan. Phillips ya fara yi wa tawagar Ingila tamaula a Satumbar 2020, an kuma bayyana shi a matakin dan wasan Ingila da ya taka rawar gani a 2020-21, wanda ya buga dukkan wasannin Euro 2020. Philips muhimmin dan kwallo a karkashin koci, Marcelo Bielsa, ya yi wasa 37 a Championship a kakar 2019-20, inda Leeds ta koma buga Premier League, bayan kaka 16 rabonta da gasar. Sai dai dan wasan ya sha jinya a kakar da aka kammala, amma ya buga wasa 20 a lik, sakamakon jinya da ya yi. https://www.bbc.com/hausa/articles/cv291lzj905o +business Kasafin kuɗin 2020: Galibin ƴan Najeriya ba su gani a ƙasa ba - Ƙungiyar farar hula Masu sa-ido a kan harkokin shugabanci a Najeriya sun fara ƙalubalantar ikirarin da shugaban ƙasar ya yi cewa gwamnatinsa ta yi nisa wajen aiwatar da kasafin kudin wannan shekarar ta 2020. An yi ƙiyasin kasafin kuɗin na bana zai ci naira tiriliyan 10, duk da cewa an sake rage shi bayan ɓullar annobar cutar korona. A lokacin da yake gabatar da kasafin kudin, Shugaba Buhari ya ce gwamnati ta damƙa wa ma'aikatu da hukumominta a ƙalla kashi 50 cikin 100 na kasafin kuɗin da aka keɓe musu a shekara mai ƙarewa. Amma wasu ƙungiyoyi da ke sa ido a kan gwamnati na ganin cewa ikirarin ya saɓa da ayyukan da gwamnati ke yi a zahiri. Shugaba Buhari ya bayyana cewa tafiya ta yi nisa wajen aiwatar da kasafin kudin, kuma gwamnati ta aiwatar da manyan ayyuka a ɓangarorin rayuwa daban-daban, ciki har da noma da samar da wutar lantarki, da gina hanyoyi da sauransu. To sai dai Comrade Kabiru Dakata na ƙungiyar da ke bibiyar yadda gwamnatoci a matakan tarayya da jiha ke gudanar da kasafin kuɗaɗensu wato KAJA, ya ce abin da shugaban ya faɗa ya yi hannun riga da abin da ke zahiri. Ya ce ''alƙaluman da ke fitowa daga hukumomi daban-daban sun nuna cewa ayyuka yi sun ragu, kuma kullum sai ƙara samun talakawa ake yi.'' Ya ƙara da cewa ''a kasafin kuɗin na shekarar 2020 an gaza sosai domin ba a samun alƙaluman su yi daidai da abubuwan da ake gani a zahiri.'' Batun aiwatar da kasafin kudi dai na cikin ƙalubalen da mahukunta ke fuskanta, inda sau da yawa gwamnatoci ba sa iya aiwatar da abin a zo a gani a cikin kasafin kuɗinsu na shekara-shekara. Duk da cewa mahukunta kan kafa hujja da wasu alƙaluma, wasu 'yan Najeriyar na cewa alƙaluman da ake rubutawa a kan takarda sukan ci karo da aikin da aka aiwatar a zahiri. https://www.bbc.com/hausa/54473109 +business Me yake jawo gobara a kasuwannin Najeriya kuma yaya za a magance ta? "Ƴan Najeriya sun jima suna nuna damuwa kan rashin tsari da ingantaccen kayayyakin kashe gobara a ƙasar, sai dai a yanzu damuwar ta koma kan ƙaruwar da ake samu na tashin gobara a kasuwannin a wasu jihohin da dama da ke jawo asarar ɗumbin dukiyoyi da ƙadarori. Masana dai na ganin bai kamata a ce a ko da yaushe ana yawaita samun irin wannan gobarar ba a ƙasar da ake ganin ita ce kan gaba wajen yawan al'umma da ƙarfin tattalin arziki a nahiyar Afirka. Kusan kowacce jiha ta fuskanci mummunan iftila'in gobara a kasuwanninta. Kama daga Jihar Legas zuwa Maiduguri da Kano da Onitsha da Sokoto, labarin a ko da yaushe iri guda ne - asarar ɗmbin dukiyoyi da ƙadarori wani lokaci har da rasa rai. Karuwar irin wannan gobara na sake hadasa damuwa musamman tsakanin ƴan kasuwa da ke asarar arziki mai tarin yawa. Irin wannan asarar ana jimawa ba a manta ba kuma tasirin na ɗaukar tsawon shekaru. Gobarar baya-bayan nan da ke sake tunasar da irin munanan iftila'in baya, ita ce ta kasuwar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya. A cewar rahotanni dukiyoyin biliyoyin naira sun ƙone baya ga daruruwan shaguna da suka ƙone. Ko kafin wannan lokaci an samu irin wannan gobarar a babbar kasuwar Sokoto, lamarin da ya janyo asarar dukiya ta miliyoyin naira a watan Janairun da ya gabata. Sannan a shekarun baya an samu irin wannan munanan gobarar a kasuwanni irin Balogun ta Legas da Sango Plank ta Ibadan da kasuwar Ochanja ta Onitsha da Kwari da Sabon Gari a Kano. Akwai wadda ta auku a 2019 a Kano a kasuwanni Yan Katako da Kofar Ruwa da Kurmin Yan-nama. Me ke jawo gobara a kasuwanni? Abin takaici ne ganin yayinda wasu ƙasashen duniya ke fama da annoba ko iftila'i da dama sakamakon matsalolin sauyin yanayi, a Najeriya labarin daban yake saboda galibin wadannan gobarar laifin mutane ne, kamar yadda Muhammad Mustapha Rilawan tsohon shugaban hukumar kashe gobara ta jihar Kano ya shaida mana. 'Ga wasu dalilai da ke jawo gobara' Malam Mustapha ya ce, galibin gobarar da ake gani a kasuwanni a sassa da dama na Najeriya ana iya hana afkuwarta idan gwamnati da ƴan kasuwa za su iya haɗa kai wajen daukar matakan kariya. Misali, matsalar wutar lantarki, wadda galibi ake alaƙanta tashin gobara da ita, ana iya shawo kanta idan za a wadatar da mutane da ƴan kasuwa da wutar lantarki domin hakan zai taƙaita amfani da janereto ko batira da ke hadasa gobara, in ji Malam Mustapha. Sannan ya ƙara da cewa, akwai bukatar inganta tsaro a kasuwanni musamman da dadare. A fitar da tsarin lokacin tashi da buɗe kasuwanni. Ko da yake akwai kasuwanni da ke da wannan tsarin, in ji shi. ""Akwai bukatar samar da hanyoyin da galibi ke haifar da cikas wajen kai ɗaukin gaggawa idan an samu tashin gobara. Kazalika kuma bukatar tilasta tsafta da yawan shara da hana kwanan kasuwa da samar da tashoshin kashe gobara kuma kowanne shago ya mallaki abin kashe gobara"". 'Sauya tsarin kasuwanni' Malam Mustapha, ya ce muddin gwamnati ba ta tashi tsaye wajen inganta tsarin yadda ake harkoki a kasuwanni ba, da bijiro da doka mai karfi ta tsaro, da tilasta dabi'un kariya, to matsalar gobara a kasuwannin Najeriya ba wadda za a iya kawo ƙarshenta ba ne a nan kusa. Sannan akwai buƙatar samar da kasuwanni irin na zamani a kowacce ƙaramar hukuma. Wannan nauyi ne da ya rataya a wuyan gwamnatoci jihohi da tarayya muddin an shirya ganin sauyi. Akwai kuma buƙatar wayar da kawunan ƴan kasuwa kan bukatar taka tsan-tsan, na kuma hana shan sigari a cikin kasuwanni. Masu sana'ar abinci ko girki a kasuwa ma a dinga sanya musu ido." https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-56500126 +religion Eid al-Fitr: Sheikh Dahiru Bauchi ya gudanar da sallar Idi a Bauchi "Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na Najeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya gudanar da sallar Idi tare da dimbin mabiyansa ranar Laraba. Malamin ya gudanar da sallar Idi ne a gidansa da ke birnin Bauchi a arewa maso gabashin kasar. Daya daga cikin 'ya'yan malamin, Tijjani Sheikh Dahiru Bauchi, shi ne ya ja sallar ta Idi yayin da malamin yake cikin mamu. Bayan idar da sallar, Sheikh Dahiru Bauchi ya ce sun gudanar da sallarsu ta Idi ne saboda an tabbatar musu da ganin watan Shawwal ranar Talata. A cewarsa, ""Dangane da wadannan labarai na cewa wata ya tabbata, abin da aka ce adilai guda biyu idan sun gani ya isar mana jama'a, ko kuma jama'a masu yawa [idan sun ga watan]."" Ya kara da cewa an ga wata a wurare irin su Gombe da Gadau da kuma Kebbi. Shiekh Dahiru Bauchi ya ce ba su da ikon karyata mutanen da suka tabbatar da ganin wata ""saboda suna da yawa. Shi ya sa yanzu muka zo muka gudanar da Sallah Idi domin watan Ramadana ya kare, watan Shawwal ya shigo."" Galibin Musulman Najeriya za su gudanar da sallar Idi ce ranar Alhamis bayan Kwamitin da ke bai wa Sarkin Musulmi shawara kan harkokin addini tare da hadin gwiwar Kwamitin Duban Wata a Najeriya sun ce ba su samu rahoton ganin jaririn watan Shawwal a kasar ba ranar Talata 11 ga watan Mayun 2021 wanda ya yi daidai da 29 ga watan Ramadan 1442 AH. Hakan ne ya sa Sarkin Musulmi, Sultan Muhammad Sa'ad Abubakar, ya ayyana Alhamis 13 ga watan Mayu 2021 a matsayin ranar Sallah kuma 1 ga watan Shawwal." https://www.bbc.com/hausa/labarai-57084834 +entertainment Amsoshin Takardunku - Tarihin Sarauniyar Ingila Elizabeth Latsa nan domin sauraren shirin A filin Amsoshin Takardunku na wannan makon da Buhari Muhammad Fagge ya gabatar an amsa tambayoyi biyu. Ta farko kan Tarihin rayuwar Sarauniyar Ingila Elizabeth da ta shiga shekara ta 70 a kan karagar mulki a makon jiya ranar 5 ga watan Fabrairun. Sai kuma tambaya ta biyu wadda aka nemi a tambayi masana shari'a ko kundin tsarin mulkin Najeriya ya yarda a bai wa wanda ya amsa laifinsa gaban kotu lauya domin ya kare shi. Raliya Zubairu ce ta karanta tarihin yayin da Barista Zainab da ke aiki da babbar kotun Jihar Sokoto ta masa daya tambayar. https://www.bbc.com/hausa/shirye-shirye-na-musamman-60367041 +sports Chelsea ta nada Graham Potter a matsayin sabon kocinta "Chelsea ta nada Graham Potter a matsayin sabon kocinta bayan korar Thomas Tuchel da ta yi. Potter ya bar kungiyarsa ta Brighton da take buga Premier domin fara aikinsa wanda ya sanya hannu akai na tsawon shekara biyar. Mai shekara 47 ya ce yana ""matukar farin ciki da murna da zama kocin Chelsea"". Wasan farko da Potter zai buga a gidan Fulham ne wanda shi ma wasan hamayya ne, a ranar Asabar da misalin karfe 12:30. ""Mun yi farin cikin kawo Graham Chelsea,"" in ji shugaabn kungiyar Todd Boehly. ""Bayan kawai cewa yana da basira ba ne a yadda yake tafiyar da wasanninsa, yana da kuma kwarewa wajen alaka mai kyau da yan wasa ta yadda za kai Chelsea ga nasara. ""Ya yi matukar tasiri a tsohuwar kungiyar da ya jagoranta dan haka muka kawo shi nan muma ya sauya mana kungiyarmu.""" https://www.bbc.com/hausa/articles/c031n61p6p8o +sports Chelsea za ta buga wasa a Santiago Bernabeu a karon farko Kungiyar Chelsea ta ziyarci filin wasa na Santiago Bernabeu, domin buga zagaye na biyu a Quarter finals a Champions League ranar Talata. Da zarar Chelsea ta sa kafa a filin Bernabeu, shine karon farko da za ta kara da Real Madrid kenan. Ko a bara da Chelsea ta ziyarci Real Madrid a gasar Champions League wasan daf da karshe a Estadio Alfredo Di Stefano suka yi wasan. Chelsea itace tilo babba daga manyan kungiyoyin Turai da ba ta taka leda da Real a Bernabeu ba. To sai dai kuma Chelsea za ta fuskanci kalubale a Sifaniyar, bayan da Real ta doke ta 3-1 a Stamford Bridge ranar 6 ga watan Afirilu. Kungiya daya ce ta yi waje da Real a Bernabeu, bayan da aka doke ta a wasan farko, itace Ajax, wadda ta yi nasara da ci 4-1 a zagayen kungiyoyi 16 da suka rage a gasar Turai a kakar 2018/19. Sai dai manyan kungiyoyin Turai kan sha kashi a filin na Real Madrid, musamman Bayern Munich. Kungiyar Jamus ta kara da Real Madrid a Bernabeu sau 13, wadda ta yi nasara wasa biyu kacal daga ciki a 2000 da kuma 2001. Ita kuwa Juventus, karawa tara ta yi da Real a Sifaniya da yin nasara a wasa uku. Sai dai kuma wasu kungiyoyin sun yi nasara a kan Real Madrid a wasan farko da suka ziyarci Bernabeu da suka hada da Liverpool da Arsenal da Paris Saint-Germain da kuma Juventus. Sai dai Chelsea kan wahalar da Real idan sun hadu a fafatawa, in banda a wasan sada zumunta da kungiyar Sifaniya ta yi nasara a kan ta Ingila da ci 3-1 a Miami a 2013 Amma a gasar Zakarun Turai da suka buga karo shida, Chelsea ta yi nasara a wasa uku da canjaras biyu, sai wanda Real ta yi nasara da ci 3-1 a bana. https://www.bbc.com/hausa/wasanni-61059678 +entertainment Gayyatar Yariman Saudiyya zuwa jana'izar Sarauniya ta janyo ce-ce-ku-ce Gayyatar da Birtaniya ta yi wa Yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohammed Bin Salman zuwa jana'izar Sarauniya Elizabeth II ya janyo zanga-zanga daga masu rajin kare hakkin bil-adama. Wani rahoto da hukumar leken asirin Amurka CIA ta fitar ya nuna cewa Yariman na Saudiyya na da hannu a kisa tare da daddatsa gawar ɗan jaridar nan Jamal Khashoggi a ofishin jakadancin Saudiyya da ke birnin Santambul na kasar Turkiyya a 2018. Yariman da gwamnatinsa sun musanta wannan zargin, amma har yanzu ƙasashen Yamma na kallon Yariman da wannan tabo, kuma tun lokacin da abin ya faru bai je Birtaniya ba. Mai magana da yawun ofishin jakadanci Saudiyya a Birtaniya ya tabbatar cewa a ƙarshen wannan mako ne Yariman zai je Birtaniya, sai dai ba a san ko zai halarci jana'izar ba ranar Litinin. Budurwar Jamal Khashoggi, Hatice Gengiz, ta ce gayyatar wani tabo ne ga Sarauniya Elizabeth II. Ta yi kira ga hukumomin Birtaniya da su kama shi idan ya je kasar. Ƙungiyar da ke matsa lamba mai suna Campaign Against the Arms Trade (CAAT) ta zargi Yariman da sarakunan yankn Gulf da yin amfani da mutuwar sarauniyar wajen ɓoye zarge-zargen da ake musu na take haƙƙoƙin bil adama. Ƙungiyar ta ƙiyasta cewa tun bayan ɓarkewar mummunan yaƙi a Yemen, shekara takwas da ta gabata, Birtaniya ta sayarwa da ƙawancen da Saudiyya take jagoranta da ke yaƙi a can, makaman da ƙudinsu ya kai fiye da $23bn. Ƴancin siyasa ya ragu sosai tun bayan da Mohammed Bn Salman ya zama yarima mai jiran gado a 2017, inda aka riƙa lafta wa masu sukar gwamnati hukuncin zama gidan gyaran hali, ko da kuwa wallafa bayani ne a shafukan sada zumunta. A gefe guda kuma, yariman ya duƙufa wajen samar da ƴanci ta fuskar zamantakewa. An sake buɗe wuraren nishaɗi da gidajen sinima da aka daɗe da dakatar da su a Saudiyya saboda sun saɓa da addinin musulunci. A yanzu, mata suna tuƙi bisa umarnin Yariman sannan Saudiya ta karɓi baƙuncin wasanni da dama na ƙasa da ƙasa da kuma tarukan waƙa har da kaɗe-kaɗen da DJ David Guetta ya gudanar. Duk da irin sukar da ake yi wa Saudiyya kan tsare-tsarenta na kare haƙƙin bil adama, ƙasar ta ci gaba da zama babbar ƙawa ga Birtaniya a yankin Gulf inda ƙasashen yamma ke kallonta a matsayin kandagarki ga mamayar Iran. Tana sayen makamai daga ƙasashen yamma, tana ɗaukar dubban mutane aiki, tana karɓar baƙuncin maniyyata aikin hajji duk shekara sannan tana taimakawa wajen daidaita farashin man fetur. Lamarin da a wani ɓangaren yake bayyana dalilan da suka sa , a mafi yawan lokuta, duniya ta yi ɗif da sukar yarima mai jiran gadon na Saudiyya. https://www.bbc.com/hausa/articles/c3gn7exvgwdo +sports Antonio Rudiger zai bar Chelsea a karshen kakar bana Mai tsaron bayan Chelsea, Antonio Rudiger zai bar Stamford idan an kammala wasannin bana. Hakan ya biyo bayan da dan wasan da Chelsea ba su cimma yarjejeniya ba kan tsawaita kwantiraginsa a Stamford Bridge. An yi wa Rudiger tayin kunshin kwantiragin da zai ke karbar fam 200,000 a kowanne mako, hakan zai zama na farko mai tsaron baya a tarihin kungiyar da zai karbi albashi mai tsoka, amma bai amince ba. BBC ta fahimce cewar an samu tsaiko tsakanin kungiyar da dan kwallon kan kudin rattaba hannu kan yarjejeniya da na ladan mai kula da wasanninsa. Dan wasan dan kasara Jamus mai shekara 29, ana alakanta shi da cewar zai koma taka leda a Real Madrid a badi. Wannan labarin ya girgiza Thomas Tuchel, wanda ke kokarin ganin Rudiger ya ci gaba da zama a Chelsea, bayan da watakila zai rasa mai tsaron baya Andreas Christensen a karshen kakar nan. Rudiger, ya koma Chelsea kan kudi fam miliyan 29 daga Roma a 2017. Shi kuwa Christensen dan kasar Denmark, kwantiraginsa zai karkare a karshen kakar nan, za kuma a bari ya koma Barcelona, wadda za ta dauki dan wasan mai shekara 26 kamar yadda aka cimma matsaya tun farko. Ba tabbas a hada-hadar kudi a Chelsea, tun bayan da gwamnatin Burtaniya ta karbe kungiyar daga mamallaki Roman Abramovich aka kuma sa ta a kasuwa. An yi hakan ne, sakamakon hare-haren da Rasha ke kai wa Ukraine, inda ake alakanta Abromovich makusanci ga shugaban Rasha, Vladimir Putin. https://www.bbc.com/hausa/wasanni-61209925 +religion Ku San Malamanku tare da Dokta Maryam Abubakar Abba "Ku latsa hoton da ke sama don kallon cikakkiyar hira da malamar: Shirin Ku San Malamanku na wannan makon ya yi hira ne da Dokta Maryam Abubakar Abba, wata malamar addinin Musulunci a Sudan amma ƴar asalin Najeriya. Malamar ta ce karatu ne ya kai ta ƙasar Sudan inda ta fara tun daga matakin koyon Larabci sannan ta yi digirinta na farko, ta yi na biyu a yanzu tana yin digirin-digirgir duk a Sudan. Mahaifinta Malam Abubakar Abba ɗan asalin jihar Adamawa ne wanda aikin koyarwa ya kai shi Kano, inda a nan ya auri mahaifiyar Maryam. An haifi Maryam a cikin birnin Kano kuma ta tashi a uguwar Yakasai. Kanwa ce ga tsohon sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu, kuma shi ne ya kai ta Sudan don yin karatu. Dokta Maryam ta ce tun tana ƙarama mahaifinta ya ci burin kai ta ƙasar Masar don ta yi karatu kan harshen Larabci. Ta fara karatu tun daga firamare har ta je sakandaren ƴan mata ta Larabci ta WATC Gwauron Dutse. Bayan ta kammala aji uku sai ta koma makaratar Jahun inda ta kammala. Daga nan ta fara karatu a Jami'ar Bayero ta Kano, amma ba ta daɗe da farawa ba sai ta tafi Sudan inda ta ci gaba da karatun digirinta a 1991. Ta yi ne digirinta na farko ne a kan Larabci, na biyu da digirin-digirgir kuma ta yi ne a kan koyar da waɗanda ba su iya Larabci ba. A yanzu shekararta 30 a Sudan, amma takan je gida Najeriya domin yin hutu. Sannan ta yi hidimar ƙasa a Najeriya kuma ta yi aikin koyarwa. Dokta Maryam ta fara gabatar da tafsiri tun a shekarar 1999, kuma takan gabatar da lakcoci da yin wa'azi a gidajen rediyo. Kazalika akwai shirin da ta dinga gabatarwa a gidan rediyon Kano na Rauda fir Riyadul Jannah. Sannan takan fassara hudubar Juma'a ta Masallacin Manzon Allah SAW kai tsaye ga masu sauraro a gidan rediyon. Dokta Maryam ta kuma gabatar da wani shirin a gidan talbijin na jihar Kano ARTV mai taken Riyadus Saliheen, kuma har yanzu tana yinsa. Malamar tana magana da yaruka hudu - Larabci da Hausa da Fillanci da Turanci. Dokta Maryam ta ce babban burinta shi ne yin abin da zai amfani al'umma. ""Babban jin daɗina shi ne yadda maigidana ya ba ni izinin yin karatu da ayyukan da'awa."" Malamar tana da aure da yara huɗu. Ta haɗu da mijin nata wanda ɗan Najeriya ne a Sudan. Babban ɗanta yana karatun Injiniya sai ta biyun mai yi karatun haɗa magunguna, ta ukun kuma tana karatun likitanci, sai ɗan autanta da yake sakandare." https://www.bbc.com/hausa/labarai-56762234 +health Da gaske an samar da fasahar 'haihuwa ba tare da renon ciki ba'? "A ƴan kwanakin da suka gaba ne wani saƙo ya dinga yaɗuwa a shafukan sada zumunta da muhawara a Najeriya, mai taken ""Haihuwa ba tare da renon ciki ba."" Saƙon, wanda aka fi yaɗa shi a zaurukan wassof wato Whatsapp groups, mai tafe da wani hoto na cewa: ""Sabuwar fasaha ce wannan wadda mata za su daina wahalar daukar ciki na tsawon watanni tara, da zarar an hada ƙwayoyin halittar namiji da ƙwan mace za a saka domin samar da ciki, sannan za a saka cikin wannan na'urar. ""Na'urar tun tana matakin farko a saka ta anan a ajiye sai bayan watanni tara (9) a kira uwa ta zo ta ɗauki ɗanta.""Ya kuke kallon wannan fasahar?"" Sannan kuma saƙon yana tafe da wani hoto da ke ikirarin cewa hoton na'urar ce. Ga alama mutane da dama da suka ga saƙon kai-tsaye sun yarda da shi ba tare da zurfafa bincike ba, kuma an yi ta tafka muhawara da nuna al'ajabi kan lamarin. Akwai batun fasahar mahaifa amma kuma an sassauya zancen da bayanan yadda take aiki. Bayani zai zo a can ƙasa. A bin diddigin da na yi a wasu zauruka na Whatsapp, na ga yadda mutane suka yi ta bayyana ra'ayoyinsu kan lamarin musamman ma mata. Na tsakuro wasu daga cikin saƙonnin a wasu zaurukan amma na ɓoye sunayen masu tsokacin kamar yadda suka buƙata. 1. 🤐 Ban san ma me zan ce ba wallahi 2. Ikon Allah. Kamar rayuwa Aliens 3. Shaƙuwa tsakanin iyaye da jariransu za ta ƙare kenan. Wannan abu dai bai yi ba a nawa ganin, duk da sauki aka samu. 4. Gaskiya bai yi ba. Ni ma na yi tunanin shaƙuwar nan. Wannan ɗaukar cikin na wata tara ba abin banza ba ne ba fa, yana da muhimmanci sosai. 5. Ban sani ba amma gaskiya ba na tsammanin wannan abin zai samar da ɗa lafiyayye, ko a farko ko a ƙarshe sai an ga illarsa a jikin yaron da aka haifa. Haba! Allah kadai ya san me ya tanada da yake zama har wata tara a ciki fa! 6. Ai kuwa za a ƙyanƙyashe Alien 😄 7. Na kasa gane kan wannan gudun ɗawainiyar da ake yanzu. A matsayin uwa kin guji ɗaukar ɗanki a ciki, ta yaya kike tsammanin yaron zai zama mutum mai ɗaukar nauyin kansa a rayuwa kuma iyayen ya tausaya muku? Allah kara kare mana imaninmu. Ya zamto jagoranmu. 8. Hmm kurum su hutar da kowa su yi kantin sayar da jarirai ka shiga ka zaɓi wanda ya yi maka. 9. Kuma har a zo suna a rinka cewa Allah yasa masu jinkai ne ko? 10. Ni kuma nawa tunanin kamar an yi ne saboda masu matsalar rashin haihuwa amma anazaune kalau me za ja maka wannan fitinar 11. Ga wanda ba zai iya haihuwa ba wannan ai lalura ce koni ce idan ba zan haihuwa zan yi dan na samu dan kaina. A shekarar 2019 ne masana kimiyya a ƙasar Netherlands suka ce suna cikin shekara ta 10 ta samar da mahaifar roba wacce za ta iya ceto rayukan jarirai bakwai ko ƴan tayi. Kafin nan, a shekerar 2017 likitocin fiɗa na yara a Asibitin Yara na Philadelphia a Amurka sun bayyana cewa wannan sabuwar fasaha za ta haɗa da saka ɗan tayi a cikin wata jaka babba mai kama da balam-balam mai ɗauke da ruwan mahaifa. A lokacin sun ce sun gwada na'urar a kan ƴan tayin tumaki, inda suka haɗa cibiyar dabbar da wata na'ura mai musayar iskar gas a wajen waccar na'urar don taimaka wa jini ya ci gaba da samun iskar oksijin da abubuwan gina jiki. An ajiye wasu daga cikin jariran tumakin har zuwa lokacin da suka isa haihuwa, don haka idan har tawagar za ta yi nasarar samar da fasaha mai aminci haka, to mai yiwuwa su iya amfani da ita don ceto rayuwar jariran ƴan adam. Kamar yadda aka sani ne a faɗin duniya haifar bakwaini na daga cikin manyan abubuwan da ke jawo mutuwar jarirai. Amma wannan ci gaban fasaha ya kuma jawo tambayoyi a kan yadda za a dinga samar da jarirai a nan gaba a duniya. Masu bincike na fatan mahaifar robar za ta inganta damar rayuwar bakwaini ko ƴan tayi, inda jariran za su ci gaba da girma tamkar dai suna cikin mahaifiyarsu. Kenan batun wancan saƙon na sama da ke cewa ana dasa ƙwayayen haihuwar mace da namiji ne tun farko a cikin mahaifar robar ba haka yake ba. Bayanan masana kimiyya sun nuna sai ɗan ya fara girma a cikin uwa sannan za a mayar da shi mahaifar robar idan an gano wata matsala da ka iya sa wa a rasa shi. Lisa Mandemaker, ɗaya daga cikin waɗanda suka tsara aikin wacce take aiki da Cibiyar Lafiya ta Maxima don ƙirƙirrar mahaifar robar, ta ce idan aka ajiye jaririn a ciki sai a bar shi ya ci gaba da girma har sai lokacin haihuwarsa ya zo sai a fitar da shi. ""A lokacin da nake horo a fannin ƙwarewa a kan abubuwan da suka shafi lafiyar mata shekara 27 da suka gabata, na san yin irin wannan kimiyyar abu ne mai yiwuwa,"" a cewar Dr Guid Oei na Cibiyar Lafiya ta Maxima. Ƙwararren ya ce babban bambancin da ke tsakanin wannan mahaifa ta roba da kwalbar da aka saba sa jariri bakwaini ita ce, ""ita wannan mahaifar roba cike take da ruwa yayin da kwalbar sa bakwaini ke cike da iska. ""Kwalbar saka bakwani waje ne mai haɗari ga jariran. Iska kan lalata huhu. Yayin da a cikin mahaifar roba kuwa an yi ƙoƙarin samar da duk wasu sinadarai na abinci da ruwan mahaifa da iska da jinin da jairi ke buƙata don ci gaba da girma,"" a cewar likitan. Ga alamu dai kamar yadda na faɗa a can sama, mutane ba su fahimci yadda wannan fasaha ke aiki ba, shi ya sa aka dinga yaɗa da labarin da cewa an ƙirƙire ta ne don samar da sauƙi ga masu gudun ɗawainiyar ciki. Amma dukkan bayanan da masana kimiyya suka yi sun nuna cewa ita wannan fasaha ba a yi ta don hutar da ɗaukar ɗawainiyar ciki ba, an yi ta ne don rage yawan rasa jarirai bakwaini da ake yi da kuma rage yawan ɓarin ciki da wasu matan ke fama da shi, ta yadda za a ciro ɗan tayin a wasu makonni a saka shi a mahaifar robar don ci gaba da girma har ya isa lokacin haihuwa. Wato kenan ita wannan sabuwar fasaha ta mahaifar roba za ta maye gurbin kwalbar adana bakwaini da aka fi amfani da ita, wacce suka ce ta fi haɗari ga jariran. Sannan kuma hoton da ake yaɗawa tare da saƙon ba shi ne ainihin hoton mahaifar robar ba. Shi wannan hoto ma idan aka duba da kyau za a ga cewa zana shi aka yi, kuma ya fi kama da kwalbar sa bakwaini. Ita sabuwar fasahar mahaifar robar tamkar balam-balam take. Miliyoyin shekarun da aka shafe ana samun juyin halittar ɗan adam ya sa ɗaukar cikin ɗan adam ya zama na daban wajen rikitarwa sannan kuma an samu ci gaba mai yawa a tsarin. Mabiya ita ce abar da ta haɗa uwa da ɗan tayinta - ɗan tayin ne ke sa mabiya tana girma a jikin mahaifar uwa. Iskar oksijin da sinadaran abinci na gina jiki da sinadaran hormone na shiga jikin ɗan tayin daga jikin uwa ta hanyar mabiya, abin da ke sa ciki ke bunƙasa har jaririn ya dinga girma. Sannan a hannu guda kuma jaririn yana mayar da iskar da yake fitarwa ta carbon dioxide da sauran gurɓatattun abubuwa zuwa cikin magunar jinin uwar. Sannan zafin jikin uwa ma na da muhimmanci wajen bunƙasar jariri. Don haka mahaifar roba tana buƙatar kwaiwayon dukkan irin waɗannan abubuwan. Waɗanne manyan tarnaƙi mahaifar roba ke da su? Mai yiwuwa matakin da ba a fahimce shi sosai ba a ɗaukar ciki - kuma wanda ke buƙatar taka tsantsan - shi ne kusan kwana 10 bayan ƙwayayen mace sun ƙyanƙyashe, a yayin da ƙwaiƙwayen da ke haɓaka ke shigewa cikin mahaifar su fara girma. A yanzu masu bincike suna gwada hakan ta ƙoƙarin tattalin ƙwayayen halittar mahaifa a wajen jiki, wanda a nan gaba za a iya kula da shi a mahaifar roba tare da samar wani waje da ɗan tayin zai girma. Ita ma wannan tsokar mahaifar za ta buƙaci samun magudanar jininta - wani abu da har yanzu ba a samar ba. Masana kimiyyar sun yi amanna cewa magance wannan lamari zai zama gagarumin mataki na gaba wajen samar da mahaifar roba. Sannan a al'amarin ita wannan mahaifar roba akwai barazanar kamuwa da ƙwayoyin cuta, duk da cewa balam-balam ɗin da za a sa ɗan tayin an tsaftace ta da magunguna tare da rufe ta ruf. Sannan kuma samun nau'ukan sinadaran abincin da sinadaran hormones ɗin da za su taimaka wa jaririn ma na iya zama ƙalubale. A yanzu dai ko da a ce za a ci gaba da aikin, babu tabbas kan yadda iyaye za su ji dangane da hakan." https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-59223779 +politics Zaɓen cike gurbi a wasu jihohin Najeriya ya bar baya da ƙura "Wani zaɓen cike-gurbi da aka gudanar a wasu jihohin Najeriya ya ya bar baya da ƙura. Yayin da jami'yyar APC mai mulki ke murnar nasarar da ta samu a zaɓen, babbar abokiyar hamayyarta, wato PDP na zargin hukumar zaɓe da haɗa baki da APC wajen yin maguɗi. Amma hukumar zaben ta musanta. Duk da cewa hankali bai koma sosai ga zaɓukan cike-gurbin ba, wasu jami'an hukumar zaɓen Najeriya na cewa babban aiki ne da ya kai ɗawainiyar zaɓen gwamna a wasu jihohi biyu na Najeriya, kasancewar ya ƙunshi kujerun ƴan majalisar dattawa shida da na ƴan majalisar dokokin jiha su tara. An kammala zaɓen har an sanar da sakamako na dukkan kujerun, inda APC da PDP suka yi wa kujerun majalisar dattawa shidan raba-daidai. Sai dai ba a sanar da sakamakon kujera guda ta majalisar dokokin da aka yi a jihar har Zamfara ba, kamar yadda Daraktan yaɗa labaran hukumar zaben Najeriyar Mista Nick Dazang ya bayyana. Ya ce ""Wanda ba mu sanar ba shi ne na mazaɓar Bakura a jihar Zamfara inda muka samu tashin hankali a rumfuna 14 kuma INEC ta ɗauki matakin sake aiwatar da zaɓe a wuraren ranar Laraba 9 ga watan Disambar nan."" Jam'iyyar APC mai mulki da kuma shugaban Najeriya duka sun yaba da sakamakon zaɓen, suna cewa ya nuna irin karɓuwar da jam'iyyarsu ta yi a gun jama'ar Najeriya. Ita kuwa jam'iyyar hamayya ta PDP kushewa ta yi, tana zargin cewa ba don an haɗa baki da hukumar zaɓe an murɗa sakamakon ba, da ta lashe kujerun baki daya. Amma Mista Nick Dazang ya musanta. ""Ba gaskiya cikin wannan zargi, kuma duk abubuwan da muke yi cikin hidimar zaɓe kamar yadda muke faɗi muna yin sa zahiri, tun daga sanda muka kawo kayan zaɓe na sirri muna raba su a gaban wakilan jam'iyyu da ƴan takara. ""Kuma duk kayan zaɓen na da namba ana iya bibiya a sa ido, don haka wannan zargi ba shi da tushe,"" in ji Mista Dazeng. An dai fuskanci ƙalubale daban-daban a lokacin zaɓukan cike-gurbin, musamman yadda mutane da dama suka ƙaurace wa wurin zaɓe. Ko da yake hukumar zaɓen ta ce rashin fitar jama'ar daɗaɗɗiyar al'ada ce. Har ma hukumar, kamar yadda Mista Dazang ke cewa ta fara neman mafita. Bisa ga tarihi yawancin al'umma ba su cika damuwa da fitowa ba a lokacin zaɓukan cike gurbi ba. Hakan ya sa ita INEC ta fara tunanin a kawo sauyi ga dokokin. ""Ta yadda idan sanata ko dan majalisar wakilai ya yi murabus ko ya mutu jam'iyyarsa na iya miƙa sunan fitaccen ɗan takarar da zai maye gurbin wancan. ""Amma hakan ba zai yiwu ba sai an yi sauyi ga kundin tsarin mulki da dokokin zabe."" Ƴan Najeriya da dama dai sun sa ran za a samu ci gaba a zaɓukan cike-gurbin, musaman ma sauyin ɗabi'a a ɓangaren ƴan siyasa da masu kaɗa ƙuri'a. Amma rigingimun da aka fuskanta tsakanin magoya baya da ta kai ga rasa rayuka a wasu wurare, da matsalar satar akwati da tayar da husuma a rumfunan zaɓe da suka yi sanadin soke sakamakon zaɓe na nuna cewa da sauran aiki." https://www.bbc.com/hausa/labarai-55223217 +entertainment Daga Bakin Mai Ita tare da Amina Uba Hassan, tsohuwar matar Adam A. Zango Daga Bakin Mai Ita shiri ne na BBC Hausa da ke kawo muku hira da fitattun taurarin masana'antar fim ta Kannywood kan abubuwa da suka shafi rayuwarsu zalla. A wannan kashi na 111, mun tattauna da tauraruwar fina-finan Hausa, Amina Uba Hassan wadda tsohuwar matar Adam Zango ce. https://www.bbc.com/hausa/articles/c4n9n4k98x9o +sports Alexandre Lacazette: Dan wasan Arsenal ya sake koma wa Lyon "Dan kwallon Arsenal, Alexandre Lacazette ya sake koma wa Lyon, shekaru biyar bayan ya hade da Gunners a kan fan miliyan 46 da rabi. Lacazette ya koma kungiyar ta Faransa a kan yarjejeniyar shekaru uku har zuwa watan Yunin 2025. Dan wasan Faransa mai shekaru 31, ya zura kwallo 54 a wasa 158 da ya buga wa Arsenal, sanna kuma ya taimaka mata lashe gasar FA Cup a shekara ta 2020. A hirarsa da tashar Canal Plus a watan Afrilu, Lacazette ya ce ""suna tuntubar juna"" tsakaninsa da Lyon. Lacazette ya kasance kyaftin din Arsenal bayan da Pierre-Emerick Aubameyang, ya koma Barcelona." https://www.bbc.com/hausa/wasanni-61749400 +politics Talauci ne ke kawo tashin hankali a Najeriya - Buhari "Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce akwai alaka tsakanin talauci da tashe-tashen hankulan da ake fama da su a kasar. ""Idan banbanci tsakanin masu kudi da talakawa ya karu, to sai rashin zaman lafiya ma ya karu, "" a cewar shugaban, wanda ke magana a ranar bikin cika shekara 20 da kawo karshen mulkin soji a kasar. Ya kara da cewa: ""za mu ta iya fitar da mutum miliyan 100 daga talauci cikin shekara 10 idan aka samu kyakkyawan shugabanci da sanin ya kamata"". Shugaba Buhari, wanda ya fara wa'adi na biyu a karshen watan Mayu, an zabe shi ne bisa alkawarin samar da zaman lafiya da yaki da cin hanci da rashawa. Sai dai yayin da aka samu raguwar hare-haren da kungiyar Boko Haram ke kaiwa, an kuma samu karuwar sace-sacen jama'a da hare-haren 'yan bindiga a wasu sassan kasar. Shugaban ya kuma ce tun da kasashen China da India da Indonesia suka ci gaba, to babu abin da zai hana Najeriya cigaba. Sai dai bai yi wani cikakken bayani kan yadda zai yi hakan ba, abin da ya sa masanin tattalin arziki Abubakar Aliyu ya ce zance ne kawai. ""A yanzu babu wani tsari a kasa da ake da shi da zai nuna cewa hakan mai yiwuwa ne, a don haka ina ganin kalamai ne kawai irin na 'yan siyasa da sukan yi,"" kamar yadda ya shaida wa BBC. Najeriya ta fi kowacce kasa yawan arzikin man fetur da kuma jama'a a Afirka, amma tana sahun gaba-gaba a jerin kasashen da ke fama da rashin ci gaba, abin da ake alakantawa da cin hanci da rashin ingantaccen shugabanci. Wannan ne karon farko da ake yin bikin Ranar Demokuradiyyar a 12 ga watan Yuni. An sauya ranar ne daga 29 ga watan Mayu domin tunawa da kuma ""rage radadin"" alhinin soke zaben shugaban kasa na 1993. Shugaba Buhari ya kuma sanar da sauya sunan filin wasa na Abuja zuwa Moshood Abiola, mutumin da aka yi imanin cewa shi ne ya lashe zaben na 1993 wanda gwamnatin sojin lokacin ta soke. Wannan sanarwa dai ita ce ta fi birge wadanda suka halarci wurin taron idan aka yi la'akari da yadda wurin ya kaure da tafi bayan da ya ayyana hakan. Shugaba Buhari ya shafe dogon lokaci yana jawabi inda ya bayyana rawar da Najeriya take takawa wurin tabbatar da demokuradiyya da kuma inganta tsaro a nahiyar Afirka. Sannan ya lissafa abubuwan da ya ce gwamnatinsa ta samar a shekaru hudun da ya yi a kan karagar mulki wadanda suka hada da: Duk da cewa shugaban bai ayyana wani takamaiman alkawari ga 'yan kasar ba, amma ya bayyana wasu abubuwa ko fannonin rayuwa da ya ce gwamnatinsa za ta mayar da hanakali a kai a wa'adin mulkinsa na biyu. Bikin ya samu halartar wasu shugabannin Afirka da suka hada da na Rwanda da Chadi da Nijar da kuma Gambia. Haka kuma akwai manyan jami'an gwamnati ciki har da sabbin shugabannin majalisun dokoki na tarayya. Sai dai babu daya daga cikin tsaffin shugabannin kasar da ya halarci taron. Haka kuma babu jami'an babbar jam'iyyar hamayya ta PDP." https://www.bbc.com/hausa/labarai-48623334 +sports Varane ya sharbi kuka bayan rauni da ya ji a wasa da Chelsea Dan wasan tawagar Faransa, Raphael Varane ya sharbi kuka, sakamakon raunin da ya ji a wasan Premier League da Chelsea ranar Asabar. Chelsea ta karbi bakuncin United a karawar mako na 13 a babbar gasar tamaula ta Ingila, inda suka tashi 1-1 a Stamford Bridge. Mai tsaron bayan ya ji rauni, bayan saura kasa da wata daya a fara gasar cin kofin duniya da Qatar za ta karbi bakunci. Varane ya ji raunin ne a kokarin tare Pierre-Emerick Aubameyang na Chelsea, an kuma maye gurbinsa da Victor Lindelof. Kociyan United, Erik ten Hag ya ce ya yi wuri a fayyace girman raunin da ya ji, saboda haka sai likitoci sun auna shi daga nan su bayyana komai. Varane, wanda ya koma Old Trafford da taka leda daga Real Madrid a 2021 na fama da yawan jin rauni a wasannin da yake yi wa United. Chelsea ce ta fara cin United a bugun daga kai sai mai tsaron raga ta hannun Jorginho saura minti uku lokaci ya cika. United ta farke daf a tashi ta hannun sabon dan wasan da ta sayo a bana daga Real Madrid, Casemiro. Chelsea tana mataki na hudu a teburin Premier League a kakar nan da tazarar maki daya tsakaninta da United ta biyar. Za a fara gasar cin kofin duniya ranar 20 ga watan Nuwamba zuwa 18 ga watan Disamba. Faransa ce mai rike da kofin, wadda ta dauka a Rasha a 2018. https://www.bbc.com/hausa/articles/cnl5x9kwv7yo +politics Ban damu da wanda zai gaje ni ba a 2023 - Buhari "Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa bai damu da wanda zai gaje shi ba a matsayin shugaban ƙasa saboda ""ya ajiye rahoton komai da komai"". Shugaban ya faɗi hakan ne a hirarsa da kafar talabijin ta Channels TV a yammacin Laraba, yana mai cewa ""zaɓen 2023 ba matsalata ba ce"". ""Ban damu da wanda zai gaje ni ba, rabu da shi ya zo ko ma wane ne,"" in ji shi. Da yake amsa tambaya kan ko me ke zuwa masa a rai idan ya ji an ambaci zaɓen 2023, Buhari ya amsa da cewa: ""Ba matsalata ba ce."" Da aka tambaye shi: ""Ba ka damu game da wanda zai gaje ka ba? Sai ya ce: ""Bar shi ya zo ko ma wane ne. Na tabbata na ajiye rahoton duk wani abu mai muhimmanci. Bai kamata wani ya kira ni ba da shaida a gaban kotu ba a kan wani abu, idan ba haka ba kuma zai shiga matsala."" Buhari ya ce duk da cewa ba shi da wani ɗan takara da yake goyon baya a jam'iyyarsu ta APC mai mulki ya gaje shi amma idan ya bayyana shi za a iya halaka shi. ""A'a, saboda idan na faɗa za a iya kawar da shi. Gara na bar shi a sirrance,"" a cewarsa. Buhari ya amsa tambayoyi kan batutuwa da dama yayin hirar da aka naɗa a fadarsa ta Aso Rock Villa, ciki har da matsalar 'yan fashin daji na arewa maso yamma. ""Mun ayyana su a matsayin 'yan ta'adda...saboda shi ne kaɗai abin da za su fahimta,"" a cewarsa. Sai dai babu wata sanarwa da ta nuna cewa gwamnatin ta ayyana su 'yan ta'adda a hukumance tun bayan da Ministan Shari'a Abubakar Malami ya nemi kotu ta ba su damar yin hakan duk da cewa kotun ta amince da buƙatar gwamnatin. 'Yan makonni bayan alƙawarin da ya yi wa dattawan al'ummar Ibo na duba yiwuwar sakin ɗan tawaye Nnamdi Kanu, Buhari ya ce ""ba za mu iya sakin sa ba"". Ya ce: ""Akwai sashen da ba zan iya taɓawa ba, shi ne na shari'a. Batun Kanu yana gaban kotu. Amma abin mamakin shi ne, lokacin da yake Turai yana zagin wannan gwamnati, na zaci zai so ya zo ya kare kansa daga waɗan nan zagr-zargen. ""Saboda haka muna ba shi dama ce ta kare kan sa bisa tsarinmu, ba wai ya koma Turai ya ci gaba da zaginmu ba kamar ba ɗan Najeriya ba. Ya zo nan ya soke mu...waɗanda ke cewa ya kamata a sake shi, a'a, ba zamu iya sakin sa ba."" A watan Nuwamba ne dattawan suka gana da Buhari a Abuja, inda suka nemi ya tausaya wa jagoran na haramtacciyar ƙungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB) da ke neman kafa ƙasar Biafra a kudu maso gabashin Najeriya. Shugaban ya ce ba ya goyon bayan tsarin zaɓe na 'yar tinƙe yayin zaɓen 'yan takara a cikin jam'iyyun siyasa, wanda sabuwar dokar zaɓe ta tanada. Buhari ya ce ya kamata a bai wa 'yan Najeriya zaɓi uku, ba wai 'yar tinke kawai ba. ""Abin da nake cewa shi ne, ba zai yiwu ka taƙaita zaɓin al'umma ba a kan abu ɗaya kawai kuma ka ce dimokuraɗiyya kake yi. Dole ne a ba su 'yancin zaɓi uku,"" in ji shi. A cewarsa: ""Akwai 'yar tinƙe da jefa ƙuri'a da kuma masalaha."" Shugaba Buhari ya ce ""babu maganar ƙirƙirar 'yan sandan jihohi"" yayin da yake maganar rikicin makiyaya da manoma. Shugaban ya kamanta ƙirƙirar 'yan sandan jihohi da kuma alaƙa tsakanin ƙananan hukumomi da gwamnatin jihohinsu. Ya ce: ""Ko a yanzu kun ga gwamnatocin jiha na bai wa ƙananan hukumomi haƙƙinsu?""" https://www.bbc.com/hausa/labarai-59885205 +religion An gama duk wani yabo da za a yi wa manzon Allah – Bashir Ɗan Musa "Latsa hoton da ke sama domin kallon hira da Bashir Ɗan Musa: Fitaccen mawaƙin begen Annabi Muhammad SAW, Malam Bashir Ɗan Musa ya ce yana matukar takaicin yadda aka lalata yabon manzon Allah (SAW) a shekarun nan. Bashir Ɗan Musa ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da ya yi da BBC Hausa, inda ya ce rashin ilimi da kuma son rai ne ya kai masu yabo ""suka faɗa duhun jahilci"" a wannan lokaci. ""A baya mukan rubuta waƙa mu bai wa junanmu kamar ni da Rabi'u Usman Baba da Rufa'i Ayagi da Bashir Tashi da sauransu, idan akwai kuskure mu gyara wa juna. ""Za a duba idan ka bai wa Annabi haƙƙin Allah sai a gyara, in kuma ka bai wa wani waliyyi hakkin da ba nasa ba shi ma a gyra maka,"" in ji Malam Bashir. Ya ce idan kana buƙatar yabon Annabi ba sai ka kushe wanda suke tare da shi ba ko kuma 'yan uwansa annabawa ""saboda kowa matsayinsa daban"". ""Idan mutum yana so ya yi bege kamar yadda ya kamata a kan turbar gaskiya to sai ya bi sawun magabata. ""An gama duk wani yabo da za a yi wa ma'aiki, mafi kyau sai mutum ya bi turbar da magata suka bi sai a dace. Amma da ka yi yadda kake so to sai ka zame. ""Da akwai waɗanda suke yin yabo karshe ba sa samun ladan komai, saboda ba sa yin sa kamar yadda ya kamata.""" https://www.bbc.com/hausa/media-58143356 +sports Steve Cooper: Kocin Nottingham ya sabunta kwantaraginsa zuwa 2025 "Kocin Nottingham Forest Steve Cooper ya sabunta kwantaraginsa da kungiyar zuwa 2025. Steve Cooper mai shekara 42, shi ne ya dawo da kungiyar zuwa gasar Premeir a bara, amma yanzu suna kasar tebur bayan buga wasa takwas a gasar. Ana shakku dai kan ci gaba da aikinsa a kungiyar bayan kashin da ya sha a hannun Leicester City da ci 4-0 a ranar Litinin, amma duk da haka ta yanke shawarar shi zai ci gaba da jan ragamar kungiyar. Wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta ce tana ""farin cikin"" sanar da cewa Cooper ya sabunta kwantaraginsa. ""Abu mafi mahimmanci shi ne cewa yanzu hankalinmu na kan kwallin kafa ne kawai"" in ji sanarwar. ""A matsayinmu na kungiya dukanmu mun mayar da hankali ne kan yin abin da zai taimakawa kulab dinmu ya kara yin sama a wannan gasa, domin nuna irin kwararrun 'yan wasan da muke da su a Premier."" A watan Satumbar 2021 ne aka nada Cooper a matsayin kocin Forest kuma ya mayar da su gasar Premier a karon farko tun 1999 a karshen kakar farko da ya fara aiki da kungiyar. Daga nan ya saye 'yan wasa 21 a wannan kakar kan £145m. Duk da wadan nan kudi da kungiyar ta kashe wasa daya kawai ta iya samun nasara a wannan kakar, yayin da rashin nasarar da ta yi a King Power ta zama ta biyar a jere." https://www.bbc.com/hausa/articles/c4n90e5gjg7o +religion Bidiyon Ku San Malamanku tare da Sheikh Usman Baba Liman Ku San Malamanku tare da Sheikh Usman Baba Liman https://www.bbc.com/hausa/labarai-60338003 +politics Shugaban Najeriya ya yi alkawarin samar da biza ga 'yan Afirka Najeriya ta ce, za a fara bawa duk wasu matafiya 'yan kasashen Afirka takardar izinin shiga kasar wato biza idan sun iso kasar daga farkon shekarar 2020. Shugaban kasar Muhammadu Buhari, ne ya ce yin haka ya nuna kokarin kasar na samar da zirga-zirga ba tare da shamaki a tsakanin kasashen Afirka ba. Sanarwar ta zo ne watanni biyar bayan da Najeriya ta sanya hannu a kan wata yarjejeniya da nufin bunkasa harkokin cinikayya ba tare da wata matsala ba a nahiyar Afirka. To sai dai kuma masu sukar shugaba Buhari, na zarginsa da kawo matsala a wajen hada kan kasashen Afirka. Saboda ya sa an rufe dukkan iyakokin kasar tun a watan Augustan da ta wuce, lamarin da ya janyo matsala ta fuskar cinikayya a tsakanin kasar da sauran kasashe makwabtanta. Shugaba Buhari dai ya yi buris da matsin lambar da ake masa a kan ya bude iyakokin kasar, inda ya ce an yi hakan ne domin kawo karshen shigo da abincin da ake yi ba bisa ka'ida ba. An rufe iyakokin kasar duk da cewa Najeriya na daga cikin kasashen mambobin kungiyar ECOWAS. Shugaban Najeriyar, bai bayyana randa za a bude iyakokin ba a lokacin da ya ke sanar da batun za a rika yi wa matafiya 'yan kasashen Afirka biza idan sun shigo kasar. Ana dai yi wa Najeriya kallon wata babbar kasa a Afirka, wadda ke da manyan abubuwan da suka shafi tattalin arziki da kuma yawan jama'a. To kowanne canji za a samu? A yanzu, 'yan kasashen Afirkan da suke son shigo wa Najeriya, sai sun nemi takardar izinin shiga wato biza a kasarsu, to amma daga sabuwar shekara, abin zai sauya inda dukkan 'yan kasar Afirka da ke son zuwa Najeriya za su iya shiga jirgi su zo kasar, in ya so a filin jirgin saman sai su nemi bizar. Wani bincike da bankin raya kasashen Afirka ADB ya fitar, ya nuna cewa 'yan kasashen Afirka na bukatar biza ne a kasashe 49 cikin 100, amma kuma suna samun bizar ne a kasashe 26 cikin 100 idan sun sauka a can. A cikin kasashen Afirka 54, kasashen da suka bayar da dama ta samun takardar shiga kasarsu wato biza idan an shiga cikin kasar, su ne Benin da Senegal da Seychelles da Rwanda da kuma Ghana. Kasashen da ake shan fama kafin a samu bizarsu a 2019 su ne, Equatorial Guine da Libya da Sudan da Eritrea da kuma Sudan ta Kudu. Kasar Habasha ita ce aka bayyana da kasar da ta fi kowacce koma baya ta bangaren samun biza, to amma tun lokacin da ta sanar da manufar samar da biza ga 'yan kasashen Afirka idan an shigo kasar, sai aka samu ci gaba sosai. An dai sanya Najeriya a matsayin kasa ta talatin a cikin jerin kasashen Afirka da ake wuyar samun visa a 2018. Kasar Kenya, wadda ita tafi sauran kasashen Afirka yawan tattalin arzik a Gabashin Afirka, a sanyata a matsayin kasa ta goma sha uku inda ta dawo baya a shekarar 2018. Kungiyar kasashen Afirka dai na ta kokarin ganin an samar da fasfo guda ga dukkan 'yan kasashen Afirka, ta yadda tafiye-tafiye a cikin nahiyar za ta yi sauki ba sai an bukaci biza ba. A shekarar 2018, mutumin da ya fi kowa kudi a Afirka, Aliko Dangote, ya yi korafin cewa sai da ya nemi bizar kasashe 38 kafin ya yi tafiye-tafiye a cikin nahiyar Afirka. A wajen taron da kungiyar kasashen Afirka ta yi a 2013, an cimma matsayar cewa za a rika ba da damar samun visa cikin sauki ga dukkan 'yan kasashen Afirka a 2018. Sai dai kuma ga dukkan alamu ba a cimma hakan ba a wasu kasashen Afirkan. Kamar Misali, Afirka ta Kudu a yanzu tana shirin kirkirar wata hukuma a 2020, da za ta rika sanya ido a kuma kawar da bakin haure wadanda ba su da cikakkun takardu. Sannna, an rufe iyakar Rwanda da Uganda tun a watan Maris din 2019, bayan da shugaban Rwanda Paul Kagame, ya zargi takwaransa na Uganda Yoweri Museveni, da kokarin bata masa gwamnati. Mr Museveni, dai ya musanta wannan zargi, kuma duk wani yunkuri da ya yi na ganin an bude iyakar ya ci tura, kamar yadda kiraye-kirayen bude iyakokin Najeriya ma ya ci tura. https://www.bbc.com/hausa/labarai-50779542 +religion Ku San Malamanku tare da Malam Sufyan Abdullahi Malumfashi An haifi Malam Sufyanu Abdullahi Abdul'aziz Malumfashi a karamar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina da ke arewacin Najeriya a ranar daya ga watan Janairu na 1968. A tattaunawarsa da BBC, ya ce ya fara karatu ne a gida wajen mahaifinsa amma daga baya mahaifinsa ya tura shi karatu zuwa wasu makarantu na tsaganya. Neman Ilimi Tun da farko dai Malam ya bayyana cewa ya fara karatu ne a wajen mahaifinsa amma a wurin Malam Haruna da ke Ungwar BCJ a garin Malumfashi ya fara karatun litattafai na Fikihu da bangaren Larabci, Nahawu da ilimin Hadisai da kuma fannin Tarihi. Ya yi karatun firamare a wata makaranta da ake kira Salau. Yana aji 4  Allah ya yi wa mahaifinsa rasuwa kuma a haka ya ci gaba da karatun har matakin Jami’a. Sai dai ya ce ya fuskanci kalubale a  lokacin da yake karatu saboda wasu suna ganin cewa ya shiga makarantar Boko ne domin gudun gona. Wannan ne ya sa ya dauki dan kwadagon da zai rika zuwa gona domin ya iya zuwa aji. Bayan ya kammala karatun firamare ya wuce makantar Sakandire ta Dan Rimi inda kuma a cewarsa yayin da yake karatu bai saki abin da ya taso da shi a gida ba na karatun Al-Kur'ani. A wannan lokaci ne kuma sai musabaqa ta karatun AlKur'ani ta bullo. A cewarsa akwai wani gidan rediyo a jihar Katsina da ya shirya makarantu irin wannan gasar. Ya kuma ce ya rika samun nasara a kowace gasar da aka shirya. A shekarar 1992 ne ya kammala karatun sakandire. Malam ya ce surorin da suka fi wahalar da shi a AlKur'ani su ne Suratul An'am  da Nahali. Abin da ya fi faranta masa Abin da ya fi faranta wa Malam rai shi ne lokacin da ya ji cewa ya samu gurbin karatu a Jami’ar Musulunci da ke Madina a 1993. A 1997 ya kammala karatun jami’a kuma a wancan lokaci ya yi abota da wasu daga cikin manyan malaman Najeriya na yanzu. A lokacin da ya je marigayi Shiekh Ja'afar Mahmud Adam ya kammala karatu. Ya kuma samu malamai irin su Umar Rijiyar Lemo da Mansur Sokoto da Malam Muhammad Suliaman da Tukur Almanar da Abubakar Birni Kudu. A 1999 ya zama Limamin Masallacin Area 11 har zuwa 2007 kuma a yanzu shi ne Limamin Masallacin Jabi, duka a Abuja. Iyali Malam yana da aure da 'ya'ya. https://www.bbc.com/hausa/articles/cn0g1yl6rd0o +health Alamun Coronavirus: Abubuwan da suka kamata ku dinga yi Coronavirus na ta ci gaba da yaduwa da kashe mutane a duniya, amma dai abin dadin shi ne yawan wadanda suke warkewa ya fi yawan wadanda suke mutuwa. To mece ce coronavirus, ta yaya take yaduwa kuma a wane mataki ne za a gane ta fi kama mutum? Abin da ya fi kamata a yai shi ne yawan wanke hannu da ruwa da sabulu. Coronavirus tana yaduwa ne idan mutum da ke dauke da ita ya yi tari har kwayoyin cutar suka yadu a cikin iska. Da zarar wani ya shaki isakar ko kuma ya taba wajen da kwayoyin cutar suka fada akai, sannan ya taba idonsa ko hancinsa ko bakinsa, to zai iya kamuwa. Don haka yin tari da atishawa a cikin toli fefa, da gudun taba fuskarku da hannayen da ba a wanke ba, da kuma gujewa yin alaka ta kut da kut da mutanen da suka kamu na da matukar muhimmanci wajen hana yaduwar cutar. Kwararru a fannin lafiya sun ce takunkumin rufe fuska ba ya tasiri sosai wajen kariya. Coronavirus na shafar huhu. Alamun na farawa ne da zazzabi sai tari mai zafi ya biyo baya, wanda ke iya jawo matsalar numfashi. Wannan sabon abu ne, tari mai naci da za a yi ta yi har fiye da sa'a daya, ko kuma yin tari a jejjere kamar sau uku cikin sa'a 24, (idan ka saba yin tari to wannan za ka ga ya fi na yadda ka saba). Yana daukar kwana biyar kafin alamun su fara bayyana, kamar yadda masana kimiyya suka ce, amma wasu mutanen su kan nuna alamun bayan fiye da kwana biyar din. A takaice dai Hukumar Lafiya Ta Duniya WHO ta ce a kan dauki kwana 14 kafin cutar ta gama bayyana. Mutane sun fi saurin yada cutar idan sun fara nuna alamunta, amma kuma wasu na iya yada ta tun ma kafin alamunta su fara bayyana. Alamun farko-farkon suna iya rudar da mutum ta hanyar kamanceceniyar da suke yi da irin murar da aka saba. Hasashe yana nuna cutar ba ta kisa sosai, tana kashe kashi 1 zuwa biyu cikin 100 - amma wannan hasashe ba shi da tabbas. Ana ci gaba da bai wa dubban mutane kulawa a asibiti, amma akwai yiwuwar da yawa su mutu. Amma kuma akwai yiwuwar mace-macen ba zai yi yawa ba idan ana samun masu dauke da cutar da ba ta yi tsanani ba. Bayanan Hukumar Lafiya Ta Duniya WHO daga marasa lafiya 56,000 da aka samu sun nuna cewa: Kashi 6 cikin 100 na yin rashin lafiyar da tsananin - huhu ya daina aiki, matsarmama ta daina aiki, da kuma barazanar muutwa Alamun cutar na bayyana sosai ga kashi 14 cikin 100 - wahala wajen shan numfashi da daukewar numfashi Kashi 80 cikin 100 ne ke yin rashin lafiyar saisa-saisa - zazzabi da tari, sai kuma wasu suna kamauwa da lumoniya https://www.bbc.com/hausa/labarai-51925611 +business Me Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa za su iya yi domin rage farashin mai a duniya? Kasashe biyu da suka fi hako man fetur za su yi ganawa mai muhimmanci Laraban nan domin yanke shawara a kan adadin mai da za su kara a kasuwa daga watan Satumba. Wannan ya biyo bayan ziyarar da shugaban Amurka Joe Biden ya kai yankin Gabas ta Tsakiya makonnin da suka wuce a yunkurinsa na shawo kan Saudiyya ta kara adadin mai da take hakowa domin rage farashinsa a kasuwar duniya. Har yanzu ana cinikin danyen mai ganga 1 kan sama da $100 tun watan Fabrairu, lamarin da ya kara tsadar rayuwa a kasashe da yawa. Fadar White House na fatan kasashe 13 dake cikin Kungiyar Kasashe masu arzkin man fetur OPEC za su yanke shawarar kara adadin mai da suke sayarwa. An kafa kungiyar a 1960 da nufin daidaita man da ake sayarwa a duniya da farashinsa. Saudiyya ita ce kasar da ta fi yawan hako mai da ke kungiyar kuma bayan ganawa da Yarima Mohammed Bin Salman, Shugaba Biden ya ce yana kyautata zaton adadin man zai karu. Sai dai jami’an Saudiyya sun jaddada cewa duk wata shawara da za a yanke dangane da karin adadin mai a kasuwa, sai an tattauna da Opec+. Opec+ ita ce babban kungiyar kasashe masu arzikin mai 23, ciki har da Rasha, wadda ke ganawa kowane wata a birnin Vienna domin yanke shawara a kan adadin danyen da za a sayar a kasuwannin duniya. A baya a watan Afrilun 2020, Open+ ta ringa rage adadin mai da take sayarwa lamarin da ya share wa’adin annobar korona lokacin da bukatar man ya ragu. Tun 2021, kungiyar tana kara adadin man da take sayarwa a hankali. A wajen taron kungiyar na karshe, Opec+ ta yanke shawarar kara adadin gangar mai da take samar wa dan kadan a watan Agusta. Sai dai kawai kunna kan fanfon mai ba zai yi saukin da ake tunani ba. A kan takarda, wasu kasashen da ke cikin kungiyar kamar Angola da Najerya da Malaysia na fama wajen samar da adadin da aka yanke musu a wata daya. A daidai wannan lokaci kuma man da Rasha take samarwa ya ragu saboda takunkuman da kasashen yammacin duniya suka kakaba mata. Rasha ita kuma ta kara adadin man da take sayarwa zuwa kasashen Asia kamar China da Indiya. Kasar ta tafi kowacce tagomashi Saudiyya tare da makwabciyar ta UAE su ne kasashe biyu kacal da za su iya kara adadin man da suke fitarwa. Saudiyya za ta ringa fitar da gangar mai miliyan 11 a watan Agusta, lamarin da kwararru a harkar makamashi suke gani na da yawa sosai, kuma haka ya sa ba za ta iya kara adadi mai yawa ba. “Babbar damuwar Saudiya da Opec+ shi ne akwai abubuwa da yawa da ba a sani ba. Babu wanda ya san yanayin kasuwar mai a watanni 6 masu zuwa ko a shekara mai zuwa,” a cewar Karen Young, babbar mai bincike a manazartar yankin Gabas ta Tsakiya da ke birnin Washington DC. Fashin bakin kasuwa na zaton Shugaba Vladimir Putin na Rasha yana so farashin mai ya cigaba da tsada yadda zai cigaba da biyan kudin yakin Ukraine domin dakile tasirin takunkuman da kasashen yammacin duniya suka saka mata. Ita kuma Saudiyya, hadin kai tsakanin ‘ya’yan kungiyar Opec+ shi ne ya fi muhimmanci, kuma za ta guje wa duk wata shawara da za ta kawo tsaiko. Opec ita da kan tana hasashen bukatar mai za ta karu a shekarar 2023 amma a hankali idan aka kwatanta da wannan shekara. Masu fashin bakinta sun ce hakan na da alaka da cigaba da aka samu wajen dakile annobar Corona a China. Hasashe daga Hukumar Makamashi ta Kasa da Kasa da Hukumar Bayanan Makamashi ta Amurka na nuna cewa za a cigaba da samun karuwar bukatar mai sosai, duk da cewa fargabar tauyewar darajar kudade a kasashe da dama da tsaiko wajen bunkasar tattalin arziki. Hakan ya na nufin kasashen da ke fitar da mai za su iya samun kawunansu samar da adadin mai yawa da sauri a cikin shekaru biyar domin daidaita bukatar man da abin da kasuwa ta samar – lamari mai sarkakia, lura da rashin yanayin samar da hakan, da kuma rashin zuba jari wajen tace man. Farashin man fetur a Amurka yanzu yayi sama, mafi tsada a shekaru 13 a wannan shekara. Amurka za ta saki misalin ganga miliyan 1 a rana daga rumbun mai da ta adana tun watan Afrilu – a matsayin daya daga cikin matakan ta na zuba ganga miliyan 180 a kasuwa a cikin watanni 6  dake kawo karshe a karewar watan Oktoba. https://www.bbc.com/hausa/articles/cv28ez8qq8qo +religion Bidiyon Ku San Malamanku tare da Ustaz Husaini Zakariyya Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon: A wannan makon mun kawo muku tattaunawar da muka yi da Ustaz Husaini Zakariyya, wani malamin addinin Musulunci a Abuja, babban birnin Najeriya. An haifi Ustaz Hussaini Zakariyya Yawale a garin Kaduna ranar 1 ga watan Oktoban 1960 a unguwar Abakwa, wanda ya yi daidai da 10 ga Rabi'u Thani shekara ta 1380 bayan Hijira. Mahaifinsa malamin addinin Musulunci ne na Mazhabar Malikiyya kuma a hannunsa ya fara karatu. https://www.bbc.com/hausa/media-55670739 +technology Saurari yadda sautin bakin ramin da ke sama yake A sararin samaniya, ba karar komai ake iya ji ba. Sai dai sararin samaniya yakan iya kasancewa mai hayaniya musamman a kusa da bakin ramin da ke sama wato black hole. Hukumar kula da sararin samaniya ta Amurka, Nasa ta fitar da sautin daga daga cikin bakin ramin, bayan ta tattara gas din da ke kusa da shi daga tarin taurari. https://www.bbc.com/hausa/articles/cy0x0pv7zjjo +sports Real ta ci RB Leipzig wasa na biyu a jere a Champions League Real Madrid ta ci wasa na biyu a cikin rukuni a jere a gasar Champions League, bayan da ta doke RB Leipzig 2-0 ranar Laraba a Sifaniya. Real ta ci kwallon ta hannun Fede Valverde, saura minti 10 lokaci ya cika a karawar da suka yi a Santiago Bernabeu. Daf da za a tashi wasa Real ta kara na biyu ta hannun Marco Asensio da hakan ya sa ta hada maki ukun da take bukata a wasan. Wannan shi ne karon farko da Real Madrid da RB Leipzig suka fafata a Gasar Zakarun Turai a tsakaninsu. Real ta je ta doke Celtic 3-0 a wasan farko a cikin rukuni a makon jiya, ita kuwa RB Leipzig ta sha kashi a gida a hannun Shakhtar Donetsk da ci 4-1. 'Yan wasan da Carlo Ancelotti ya fuskanci Leipzig da su 'Yan wasan Real Madrid: Masu tsaron raga: Courtois, Lunin da kuma Luis López. Masu tssaron baya: Carvajal, Alaba, Vallejo, Nacho, Odriozola, Rüdiger da kuma F. Mendy. Masu buga tsakiya: Kroos, Modrić, Camavinga, Valverde, Tchouameni da kuma D. Ceballos. Masu cin kwallaye: Hazard, Asensio, Vini Jr., Rodrygo da kuma Mariano. Sakamakon wasannin da aka buga ranar Laraba: https://www.bbc.com/hausa/articles/cy9ljx5905yo +health Yadda ake fama da maleriya a unguwannin Abuja Latsa alamar lasifika domin Sauraren rahoton Zaharadden Lawan: Mazauna wasu unguwannin marasa galihu Abuja babban birnin Tarayyar Najeriya sun koka game da karuwar yaduwar cututtuka saboda karancin ababen more rayuwa da rashin cibiyoyin kula da lafiya. Wani rahoto da wata kungiya mai suna Do Inspire, da ke bayar da shawarwari kan kiwon lafiya ta fitar, ya nuna cewa ana samun karuwar kamuwa da zazzabin cizon sauro da kashi 20 cikin 100 a irin wadannan unguwanni. Binciken ya nuna cewa ana samun kimanin mutum miliyan 100 da kan kamu da cutar maleriya, yayin da sama da 300,000 ke mutuwa kowace shekara sanadiyyar cutar a Najeriya. Wanda hakan ya zarta wadanda ke mutuwa sanadiyyar cutar HIV. Zaharadden Lawan ya ziyarci daya daga cikin unguwannin na marasa galihu a Abuja kuma ya aiko da rahoto. https://www.bbc.com/hausa/labarai-50285811 +technology Sababbin sharuɗɗan da Najeriya ta gindaya wa Facebook da TikTok da Twitter "Gwamnatin tarayyar Najeriya ta fitar da wani daftarin dokoki ga kamfanonin shafukan sada zumunta na Tuwita da Facebook da WhatsApp da Instagram da Google da TikTok da sauransu kan ayyukansu a ƙasar. Dokokin, waɗanda aka samar da su don sa ido a kan yadda shafukan sa da zumuntar ke aiki, sun bayyana cewa dole kowane kamfani da ke aiki a Najeriya ya samar da duk bayanansa. Sannan dole ya taimaka wa duk wata hukuma ta gwamnati da abin da take buƙata da nufin aiwatar da bincike ko shawo matsalolin laifukan intanet ko kuma shigar da ƙara a kan laifi. Gwamnatin tana kuma so shafukan sada zumuntar su kiyaye dokokin Najeriya kuma kar su yi duk wani abu ko wata kwaskwarima da za su yi katsalandan ga dokokin ƙasar. Hukumar Ci gaban Fasahar Sadarwa ta Najeriya NITDA ce ta fitar da sababbin sharuɗɗan, sakamakon umarnin da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayar. NITDA ta ce an samar da sabuwar dokar ne don kare haƙƙoƙin ƴan Najeriya da ma waɗanda ba ƴan Najeriyar ba da ke zama a ƙasar, tare da samar da dokoki na mu'amala a tsarin intanet na zamani. Hukumar ta ƙara da cewa: ""Abin da yake a bayyane shi ne cewa abubuwan da ake yi a waɗannan dandali na sa da zumunta suna da matuƙar tasiri a zamantakewar al'umma da harkokin tattalin arziki da rayuwa gaba ɗaya. ""A saboda haka, dokokin wani ƙoƙari ne na gyara mu'amala tsakanin kamfanonin sa da zumuntar da ƴan Najeriya don kowa ya amfana, a yayin da muke son samar da tsarin tattalin arziki na dijita."" NITDA ta ci gaba da cewa: ""Sabuwar dokar ta kuma fitar da tsare-tsaren bai wa ƴan Najeriya kariya da tsaro da kiyaye walwalarsu a yayin da suke amfani da shafukan. ""Muna son a dinga bibiyar ayyukan da ake yi a shafukan da suka shafi sanya abubuwan da suka take doka ko masu cutarwa."" Sannan NITDA ta ce dokokin za su samar da wani tsari na haɗa hannu wajen ƙoƙarin kare ƴan Najeriya daga duk wani abu da zai cutar da su a intanet, kamar kalaman ƙiyayya da cin zarafi da kuma daƙile labaran ƙarya. Gwamnatin ta ce duk wani kamfanin sada zumunta da ke aiki a ƙasar dole ya yi wasu abubuwa da suka haɗa da: 1. A yi gaggawar ɗaukar mataki idan an samu ƙorafi daga wani mai amfani da dandalin ko wata hukumar gwamnati kan duk wani abu da ya take doka a shafin. Dole kamfanin ya amsa cewa ya samu saƙon ƙorafin kuma ya cire abin daga shafin cikin awa 24. 2. A yi gaggawar cire ko hana ganin ko toshe duk wani abu da aka wallafa mai nuna al'aurar mutum, ko tsiraicinsa ko saduwa ko bidiyo na ƙarya na kwaikwayon wani, ko na batsa, musamman a yanayin da aka yi hakan da nufin cin zarafi ko wulaƙanta wani. Dole kamfanin ya amsa cewa ya samu saƙon ƙorafin kuma ya cire abin daga shafin cikin awa 24. 3. A bayyana sunan wanda ya ƙirƙiri da wallafa saƙon idan har aka buƙaci hakan bisa umarnin kotu. Musamman idan har umarnin ya shafi don a kare ko gano ko bincike ko shigar da ƙara kan laifin da ya shafi taɓa darajar Najeriya, ko na zaman lafiya ko tsaro ko huldar diflomasiyya, ko kan abin da ya shafi cin zarafin yara da kuma fyaɗe. 4. Idan kuma har wanda ya fara ƙirƙirar saƙon ba a Najeriya yake ba, to wanda ya fara yaɗa saƙon a Najeriya shi za a ɗauka a matsayin wanda ya fara ƙirƙirarsa. Dole su sanya ido sosai don tabbatar da cewa ba a wallafa wani abu da ya saɓa wa doka ba a dandalin nasu. Idan kuma wani kamfani ya samu saƙo daga wani mai amfani da shi ko wata hukumar gwamnati cewa an wallafa wani abu da ya taka doka, to dole wannan kamfani ya cire saƙon gaba ɗaya. NITDA ta ce sabbin dokokin, waɗanda a yanzu aka fitar da su ga al'umma, an tsara su ne da haɗin gwiwa tsakaninta da Hukumar Kula da Kamfanonin Sadarwa ta Najeriya NCC, da Hukumar da ke sa ido kan Kafafen Yaɗa Labarai NBC." https://www.bbc.com/hausa/labarai-61795867 +health Waɗanne ƙwayoyin cuta muke watsawa yayin da muke sumba? Sumba na iya zama abu mai kyau na bayyana soyayya, amma ko kun san a duk lokacin da kuka sumbaci abokin tarayya, me kuke bayarwa? Wani lokaci mu mutane muna tunanin ƙara dankon ƙauna ne da soyayya, amma kuma akwai abin da watakila ba mu fahimta ba... ta hanyar sumbata, muna yaɗa ƙwayoyin cuta da dama. Ko da yake ba lallai ya zama haka ba, tsarin yadda aka halicci baki yana da rikitarwa kuma yana iya adana nau'ikan ƙwayoyin cuta har 700 waɗanda za su iya rayuwa. Siffar tsarin bakin yana bai wa yawu damar samar da matsakaicin zafin jiki da kuma wadataccen abinci mai gina jiki, don haka wannan yanayin yana taimaka wa ƙwayoyin cuta su hayayyafa da girma. Tun da bakin ya cika da ƙwayoyin cuta, a bayyane yake cewa za mu iya watsa waɗannan ƙwayoyin idan muka yi sumba. Gaskiyar ita ce, a cewar wani binciken da ɗalibai a Netherlands suka yi, yana yiwuwa idan ka sumbaci wani na tsawon daƙiƙa 10 a rana, za ka iya yada ƙwayoyin cuta har miliyan 80. Kwayar cutar da ke cikin baki sunanta 'microbiota' wacce dama can take baki tun daga haihuwa. Tana canzawa dangane da abin da muke ci, ko magani ne ko a'a, muna da tsabta ko kuma muna shan sigari. Shekarunmu da yanayin kwayoyin halitta suna shafar tsarin waɗannan 'microbiota'. Duk da wannan, ƙwayoyin halittar da ke zaune a bakin ɗan adam suna da fa'idoji da yawa. Mafi yawa dai shi ne yana taimakawa wajen hana ƙwayoyin cuta samuwa, yana tallafawa garkuwar jiki da tsarin narkewar abinci tare da daidaita hawan jini. Waɗannan ƙwayoyin cuta suna rayuwa tare kuma a sassa daban -daban na baki, kuma suna hada abin da ake kira 'biofilms'. Suna mannewa da bangon wurare daban-daban a cikin baki musamman a kan wani bangare da ake ce wa ''substrate'' saboda haka suna samun kariya daga sindarai kamar na 'antibodies' da ke aiki da garkuwar jiki. Ire -iren wadannan kwayoyin cuta suna farawa ne daga hakora, dasashi ko harshe. A wasu wuraren kamar kumatu, babu lokacin da za a samar da waɗannan 'biofilms' saboda sabunta ƙwayoyin 'mucosa' yana faruwa cikin sauri. Kusan kowane bangare na baki yana dauke da isashshen oxygen da yanayi na sinadaran abinci, yanayin da ke sa tarin kwayoyin cuta ya sauya a kai a kai. Irin wannan kwayoyin cuta ba iri ɗaya ba ko da a haƙori ɗaya ne, amma ɗayan yana gaba da bayan hakori ɗaya. Wannan bambancin yana da girma sosai don haka 'microbiota' na harshenku na iya zama kamar baƙo ga hakoran ku. Kusancin da ake buƙata yayin sumbata ya na taimakawa ko ba da damar ƙwayoyin cuta su tashi daga baki ��aya zuwa wani. Za mu iya kawar da yawancinsu ba tare da mun sani ba. Damar kwayoyin cuta su rayu a baki ya danganta ne da yadda za su dace da inda suke. Bugu da kari, tsarin garkuwar jiki, ba ya taimakawa wajen sauƙaƙe shi, tun da miyau na haduwa da kwayoyin 'antibody' da ake kira IgA, wanda majina ke samarwa, wanda ke ƙoƙarin hana hulɗa da ƙwayoyin cuta. A takaice, mutanen da ke da gibi a tsarin haƙoransu a cikin baki, ba su da yawan wadannan 'antibodies' din ba. Don haka, lokacin da kuka sumbaci mutum, kuna karɓar ƙwayoyin cuta da yawa daga mutumin da kuke sumbata, yawancin waɗannan ƙwayoyin suna shiga cikin hanji kai tsaye. Amma wasu suna mannewa a baki. Tasirin wannan shi ne yana da wuya ƙwayoyin cuta su zauna a baki bayan sumba, amma dole ne ku yi hankali saboda akwai ƙwayoyin cuta waɗanda ba su isa su ɓoye ta cikin 'microbiota' ba. 'Biofilm' da ƙwayoyin cuta ke samarwa a hakora ana ce masa murufin haƙori a cikin harshe na yau da kullun. Wani lokaci yana da wuyar kawar da shi. Kwayoyin cuta suna amfani da sukari a cikin abinci kuma suna samar da sinadarai masu yawa. Wannan yanayin yana sa sindarain da ke lullube a kan hakori mai suna enamel ɗin haƙora ya lalace kuma ya haifar da lalacewar haƙora. Don haka shan sukari yana da alaƙa kai tsaye da lalacewar haƙora ko ramukan cikin hakori. Wannan ba sabon abu ba ne. Bisa bayanan da aka tattara, an samu ƙaruwa sosai a lalacewar haƙora, bayan an cire haraji kan sukari a Ingila, kuma wannan ya zama ruwan dare. Daya daga cikin kwayoyin da aka gano yana haifar da mafi yawan matsaloli sunanata 'Streptococcus mutans' da wani nau'i na Lactobacillus. Idan ba a cire kurajen ko kumburin daga hakoran ba, zai haifar da kumburi a dasashi kuma ya haddasa wata cuta da ake kira 'periodontitis'. A gefe guda kuma, kada mu manta cewa ƙwayoyin cuta da yawa na wannan nau'in 'microbiota' a cikin baki suna da alaƙa da halitosis (mummunan warin baki da tarin ƙwayoyin cuta ke haifarwa). Waɗannan ƙwayoyin cuta galibi suna rayuwa cikin harshe kuma suna samar da abubuwan da ke motsa ƙona sinadarin protein. Don haka, tsafta tana da mahimmanci wajen rage kamuwa da cututtuka na baki. Ta hanyar goge bayan kowane abinci, yana taimakawa cire fim ɗin biofilm daga ƙyallen haƙora da ƙwayoyin cuta. Bugu da ƙari, yayin da kuke goge hakora, kuna jawo ƙwayoyin cuta waɗanda ke buƙatar iskar oxygen don su girma, wanda abu ne mai kyau. Ya kamata ku yi buroshi da wanke harshenku. Ku ji daɗin rayuwa ... kuma ku rarraba 'microbiota' Gabaɗaya, ma'auratan da ke cikin ingantacciyar soyayya suna samun kansu da ƙwayoyin cuta iri ɗaya ko masu kama da na juna. Suna kara sumbatar juna, suna kara ba junansu kwayoyin cuta da kuma kwayoyin cutar suna kara kamanceceniya. Wannan na iya zama abin jan hankali ga masoya, amma yana da nasa illolin. Lokaci na tafiya, mutanen da ke fama da cututtukan baki na iya yada wa matansu ko mazansu cututtukan. A halin yanzu, ana ci gaba da bincike don samar da wani abu da za a sanya rika sanya wa a baki don taimakawa hana lalacewar haƙora. Wani binciken da aka yi a baya a Valencia, ya nuna cewa yana da sakamako mai kyau. Sumba tana taimakawa wajen samar da soyayya mai ƙarfi, tana motsa rai kuma ta na ƙara ƙarfin soyayya tsakanin masoyayya. La'akari da duk abin da muka gani a cikin wannan maƙala, ana ba ku shawarar ku yi taka-tsan-tsan wajen zaɓar wanda za ku iya kulla alaƙa da shi da musanya 'microbes'. https://www.bbc.com/hausa/labarai-58637220 +technology Saadat Aliyu: Matashiyar Kano da ta ƙirƙiri manhaja kan Fyaɗe ta ja hankali a Twitter "Wata matashiyar Kano a arewacin Najeriya da ta ƙera wata manhajar da za ta dinga bayar da rahotanni kan fyaɗe ya ja hankalin ƴan Najeriya a kafofin sada zumuna musamman Twitter. Saadat Aliyu ƴar asalin jihar Kano ta samar da sabuwar manhaja ce 'Helpio' mai bayar da bayanai kan cin zarafin mata wacce ta ƙaddamar a rumbun manhaja na wayoyin android wato Play Store a 2020. Saadat ita ce shugabar kamfanin Shamrock Innovation mai ƙirƙire-ƙirƙiren fasaha kuma mai fafutikar ci gaban mata a fannin ƙirƙira. Yadda aka gabatar da matashiyar a kanun labaran wasu jaridun ƙasar a matsayin 'Kano Lady' wato budurwa ƴar Kano shi ya ja hankalin ƴan Najeriya a kafofin sada zumunta musamman a Twitter. ""Kano Lady"" na cikin manyan batutuwan da aka fi tattaunawa a shafin Twitter tun daga ranar Litinin zuwa Talata inda kusan mutum 15,000 suka yi tsokaci akai. Duk da ba kasafai akan samu mata ba a fagen ƙirƙirar fasaha a Najeriya musamman arewacin ƙasar ba, amma wasu na ganin ta cancanci yabo kuma ya dace a kira ta da sunanta na yanka. Yawanci dai kafafen yaɗa labarai kan alaƙanta mutum da sunan garinsa musamman wanda ba sananne ba. Abin da yawanci mutane suka fi tattaunawa shi ne rashin kiran matashiyar da sunanta na asali. Suna ganin irin fasahar da ta samar bai dace a mayar da hankali ga garin da ta fito ba. @bheyeh_ ta ce: Ai Kano Lady tana da suna ko? ya kamata a ambaci sunanta don mu jinjina mata. @Mbahdeyforyou ya ce: Idan da laifi ta aikata da an ambaci sunanta. @Fawwarz ya ce: Maimakon sunanta, yanzo ga shi Kano Lady ya zama batun da aka fi tattaunawa. @Pharm_ada tambaya ta yi cewa: Ko me ya samu sunanta... Menene kuma Kano Lady Dalilin 'Kano Lady' ne ya sa sunanta na asali Saadat Aliyu ya kasance cikin manyan batutuwan da aka fi tattaunawa a Najeriya a Twitter a ranar Talata. @Mayorspeaks ya ce: ""Saadat Aliyu ce ta samar da manhajar bayar da rahotanni kan fyaɗe, Kano Lady ba sunana ba ne. Shi ma @TAYOCONGA ya ce: Tana da suna kuma sunanta Sa'adiyat Aliu. bai dace a kira ta da Kano Lady ba. Ta ƙirƙiri manhaja a android domin bayar da rahoto kan batun fyaɗe. Ta cancanci a yaba mata." https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-56337290 +technology Ana zargin wasu ma'aurata da yunƙurin sayar da sirrukan nukuliyar Amurka An kama wani Injiniyan rundunar sojin ruwan Amurka da mai ɗakinsa bisa zarginsu da yunƙurin sayar da sirrikan nukiliya ga wata ƙasa. An kama Jonathan Toebbe da matar tasa Diana a West Virginia, kamar yadda ma'aikatar shari'a ta Amurkar ta sanar. Ana zarginsu da ƙoƙarin sayar da taswiwar jigrin ruwa na ƙarƙashin teku mai amfani da makamashin nukiliya, inda suka ɓoye taswiwar a cikin wani ƙunshin biredi da aka shafe shi da man botar gyaɗa. Sai dai a rashin sanunsu, wanda suka so su sayarwa wannan sirri, ma'aikacin hukumar binciken laifuka ta Amurka FBI ne. Mista Toebbe ya yi aiki a ɓangaren gwajin makamin nukiliya na rundunar sojin ruwan Amurka kuma an amince masa sanin sirrika da kuma shiga duk wani lungu da saƙo. Ma'aikatar shari'a ta ƙasar ta bayyana cewa a Afrilun 2020, wanda ake zargin ya tura da wani sunƙi zuwa ga wata ƙasa ɗauke da wasu bayanai muhimmai inda a ciki yake tallata cewa za su iya sayen wasu bayanan daga wurinsa. Bayan haka ne ake zargin ya soma rubuta saƙon email da zaurance zuwa wani, inda a tunaninsa wanda yake aika wa saƙon yana wakiltar gwamnatin wata ƙasa ne, amma asali ma'aikacin FBI ne. Bayan watanni da dama, sai Mista Toebbe da matarsa Diana suka yi wata yarjejeniya domin sayar da wasu bayanai kan dala 100,000 a kudin kirifto, kamar yadda ake zargi. A watan Yunin bana sai suka kama hanya suka nufi West Virginia domin kai saƙon bayanan, inda a nan ne jami'an na FBI suka damƙe su. A ranar Talata 12 ga watan Oktoban 2021 ne ake sa ran kotu za ta soma sauraren ƙarar waɗanda ake zargin da aka kai. https://www.bbc.com/hausa/labarai-58866391 +sports Barcelona ta kammala daukar Lewandowski kan fam miliyan 42.6 Barcelona ta kammala daukar dan kwallon tawagar Poland, Robert Lewandowski daga Bayern Munich kan yarjejeniyar kaka hudu kan fam miliyan 42.6. Mai shekara 33 yana da saura kwantiragin kaka daya a Bayern Munich, sai dai a watan Mayu ya sanar cewar yana son ya koma wata kungiyar. Tuni dan kwallon yana tare da sauran 'yan wasan Barcelona a Amurka, wadda ta shirya yin wasan sada zumunta hudu, domin tunkarar kakar da za a fara cikin watan Agusta. Barcelona ta gindaya fam miliyan 429.9 ga duk wadda za ta dauke Lewandowski idan yarjejeniyarsa bai kare ba a Camp Nou. Dan wasan ya koma Bayern Munich da taka leda a 2014 a lokacin da yarjejeniyarsa ta kare a Borussia Dortmund. Ya ci kwallo 50 a wasa 46 a kakar da ta wuce, ya kuma taimakawa Bayern ta dauki Bundesliga na 10 a jere. Lewandowski ya zura kwallo 344 a raga a wasa 374 a Bayern, shi ne na biyu a tarihin cin kwallaye a kungiyar bayan Gerd Muller. Dan wasan ya lashe Bundesliga a dukkan kaka takwas da ya yi a kungiyar, ya kuma dauki Champions League a 2019-20. Lewandowski shi ne na hudu da Barcelona ta dauka a bana, bayan dan kwallon Brazil, Raphinha daga Leeds United da Franck Kessie da AC Milan da Andreas Christensen daga Chelsea. Haka kuma Bayern ta sayi dan wasan tawagar Netherlands, Matthijs de Ligh daga Juventus kan yarjejeniyar kaka biyar kan fam miliyan 65.6 https://www.bbc.com/hausa/articles/cw97lx9x0e1o +sports Faransa ta taka wa Morocco burki a Gasar Kofin Duniya a Qatar Tawagar Faransa za ta buga wasan karshe a Gasar Kofin Duniya a Qatar ranar Lahadi da Argentina, bayan da ta taka wa Morocco burki a wasan daf da karshe. Ranar Laraba Faransa mai rike da kofin da ta dauka a Rasha a 2018 na biyu jumulla ta ci Morocco 2-0 a filin wasa na Al Bayt. Minti biyar da fara wasa Faransa ta ci kwallo ta hannun Theo Hernandez kuma haka suka je hutu. Saura minti 11 a tashi daga karawar Randal Kolo Muani ya ci wa mai rike da Kofin Duniya na biyu a wasan. Karon farko da Faransa ta yi wasa ba tare da kwallo ya shiga ragarta ba, bayan wasa 11 da ta yi tun daga watan Yuni. Wannan kuma shi ne karon farko da kwallo ya shiga ragar Morocco a Qatar, bayan da ta ci gida a wasa da ta doke Canada 2-1 a cikin rukuni. Faransa ta kawo wannan matakin bayan da ta ja ragamar rukuni na hudu da maki shida, wanda ya hada da Australia da Denmark da kuma Tunisia. A zagaye na biyu Faransa ta ci Poland 3-1, sannan ta doke Ingila 2-1 a karawar daf da na kusa da na karshe. Morocco ita ta ja ragamar rukuni na shida da maki bakwai da ya hada da Croatia da Belgium da kuma Canada. Morocco ta yi nasara a kan Sifaniya a bugun fenariti 3-0, bayn da suka tashi ba ci, sannan ta yi nasara a kan Portugal da ci 1-0 a Quarter finals. Wannan shi ne wasa na biyar da suka fafata a tsakaninsu, kuma na farko a Kofin Duniya, inda Faransa ta ci biyu da canjaras biyu. Wasa na karshe da suka hadu tsakanin Faransa da Morocco shi ne ranar 16 ga watan Nuwambar 2007, inda suka tashi 2-2 a wasan sada zumunta. Haka kuma Faransa ta zama ta farko da ta kai wasan karshe a Gasar Kofin Duniya karo biyu a jere tun bayan Brazil a 2002, kuma ta farko a Turai tun bayan bajintar Jamus a 1990. Wasan karshe na hudu da Faransa za ta yi a Gasar Kofin Duniya bakwai baya, kenan a1998 da 2006 da 2018 da kuma 2022. Tawagar Faransa na fatan zama ta farko da za ta kare kofinta na Duniya tun bayan shekara 60, bayan bajintar da Brazil a 1958 da kuma a 1960, sai dai Italiya ce ta fara hakan a 1934 da kuma 1938. Didier Deschamps shi ne na hudu da ya ja tawaga kai wa zagayen karshe karo biyu a jere. Kociyoyin da suka yi wannan bajintar sun hada da Vittorio Pozzo tare da Italy a 1934 da kuma 1938, sai Carlos Bilardo tare da Argentina a 1986 da 1990 da kuma Franz Beckenbauer da tawagar Jamus a 1986 da kuma 1990. Ranar Lahadi Argentina za ta kara da Faransa a wasan karshe, kafin nan Croatia da Morocco za su fafata a wasan neman mataki na uku ranar Asabar. https://www.bbc.com/hausa/articles/c6p8v76e3llo +religion Bincike ya nuna harin masallaci a Norway ta'addanci ne "'Yan sanda sun ce akwai yiwuwar bincike ya tabbatar da harin bindigar da aka kai masallacin wata cibiyar nazarin addinin Islama a wajen Oslo babban birnin kasar, ranar Asabar, na 'ta'addanci ne. An dai cafke mutumin da ya bude wutar a Masallacin wanda 'yan sandan suka ce shi kadai ya kai harin. An bayyana matashin a matsayin dan kimanin shekara 20, dan asalin kasar Norway ne wanda kuma 'yan sanda sun ce sun gano gawar wata mata a gidansa, da ake tunanin 'yar uwarsa ce. Daraktan masallacin ya shaida wa kafofin yada labaran yankin cewa wani dan shekara 75 ne ya samu rauni a lokacin da dan bindigar ya kai harin. ""Wani farar fata sanye da kaki da hular kwano ya harbi daya daga cikin mambobinmu,"" kamar yadda Irfan Mushtaq ya shaida wa jaridar Budstikka. Ya kuma shaida wa wata kafar talabijin ta TV2 cewa dan bindigar ya bude wuta ne dauke da bindigogi guda biyu, kafin 'yan sanda su isa wurin. Wasu majiyoyi na 'yan sanda sun shaida wa kafar yada labarai ta NRK cewa an samu makamai a masallacin da ke garin Baerum, bayan harin. Masallacin dai ya kara daukar matakan tsaro bayan harin da wani dan bindiga ya kashe mutum 51 a masallatai biyu a Chrischurch, a New Zealand, a farkon shekarar 2019, kamar yadda kamfanin dillacin labaru na Reuters ya ruwaito." https://www.bbc.com/hausa/labarai-49309356 +politics Me ƴan Najeriya ke cewa kan sauya sheƙar Shekarau daga NNPP zuwa PDP? "A ranar Litinin 29 ga watan Agusta ne ɗan takarar shugabancin Najeriya a jam'iyyar PDP Atiku Abubakar zai karɓi Sanatan Kano ta Tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau zuwa jam'iyyar PDP. A yayin wata hira da BBC Hausa, Sanata Shekarau ya ce ya zaɓi komawa tsohuwar jam'iyyarsa ta PDP ne saboda yadda magoya bayansa suka nuna a koma can don rashin adalcin da ya ce an yi musu a NNPP. Wannan shi ne karo na biyu da Sanata Shekarau ya sauya jam'iyya a cikin shekarar 2022. Ya bar APC zuwa NNPP a watan Mayu, sai kuma ya bar NNPP zuwa PDP a Agusta. Wannan lamari ya matuƙar jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin ƴan Najeriya, musamman ma al'ummar jihar Kano. Wasu daga cikin al'umma na bayyana kaɗuwarsu da matakin ne, yayin da wasu ke nuna cewa babu abin mamaki da al'amauran ƴan siyasa. A shafin Facebook an tattauna batun sau sama da 70,000. Wasu sun nuna damuwa kan yadda an siyasa ke sauya sheka a duk lokacin da suka ga dama, suna cewa hakan na faruwa ne saboda kare ra'ayin kawunansu. Yayin da wasu ke ganin babu wani baike a sauyin jam'iyya tun da dama ita siyasa 'yar ra'ayi ce. Mun duba sakonnin mutane a shafin BBC Hausa Facebook kan labarin. Tahir Musawa ya rubuta cewa: ""Shi yasa Duk wanda yake fada akan ‘yan siyasa, to babban sakarai ne. Na tabbata akwai waɗanda suka yi rantsuwa a baya, cewa Shekarau ba zai taba komawa PDP ba. ""To ai yanzu dai ga shi. Ubangiji Allah Ya sa mu dace, Ameen."" Jamilu Lawan Riji ya ce: ""Mu dai fatanmu Allah ya zaba mana shugabanni masu tausayin mu da kuma kaunar mu."" Amadu Habu Gamawa ya rubuta cewa: ""Wannan lamari dama jama'a sun dade suna jira saboda abu ne mai wahalar gaske su zauna a inuwa daya."" Bashar Ababukar ya ce: Wadannan ƴan siyasar namu na Najeriya akidarsu ta siyasa suna yi ne don kansu ba don talakawa ba. Allah ya gyara zukatanmu baki daya, ameen."" Mallam Sagir Muh'd Saidu Daga Zaria a Kadunan Nigeria ya ce: ""Mun gaji da gafara sa amma har yanzu ba mu ga ƙaho ba. ""Yaushe ne 'yan siyasar Najeriya za su gane cewa akwai bambanci tsakanin ƙuduri da kuma rayuwa! Saboda haka ƙudiri gaba yake da rayuwa!"" Sani Mailangelange Yawuri ya ce: ""Hakika a siyasa babu abokin dindindin kuma babu makiyin dindindin. Da fatan Allah Ya samar wa talaka mafita."" Dama tun da fari ɓangaren Sanata Shekarau ya nuna damuwa game da rashin adalcin da ya ce an yi musu a jam'iyyar NNPP. Sannan majalisar tuntuɓa ta tsohon gwamnan - wadda ake kira shura - ta fara nema wa tsagin makoma ta hanyar tattaunawa da sauran jam'iyyu. Wata majiya da ta zanta da BBC ta ce sun kammala shirin tarɓar Atiku tsaf a Kano ranar Litinin bayan sun yi nazari kan tsare-tsaren da ya gabatar musu. ""Sun gabatar mana da tsare-tsarensu, mun yi nazari a kansu kuma za mu karɓe su. A taƙaice dai sanarwa kawai ake jira."" Cikin hirarsa da BBC Hausa a farkon makon nan, Shekarau ya ce babu gaskiya a batutuwan da jagoran jam’iyyar NNPP Rabi’u Musa Kwankwaso ke yi cewa sun shiga jam’iyyarsa a makare. Wata majiya ta bayyana cewa tun farko an yi yarjejeniya cewa za a bai wa ɓangaren Shekarau kashi kusan 35 na muƙamai, amma daga baya shi kaɗai aka bai wa tikitin takarar sanata. A nasa ɓangaren, Kwankwaso ya ce sun shiga jam'iyyar a makare amma sun faɗa wa Shekarau cewa su bari a kafa gwamnati don a daidaita rabon. Masana a harkokin siyasa sun fara tsokaci kan wannan lamari inda suka ce wannan sauyin sheka ta Sanata Shekarau na nuna cewa an kasa samun daidaito tsakanin ɓangaensa da na Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso. ""Wataƙila kuma an samu rashin cika wasu daga cikin alkawuran da aka yi. To hakan na alamta cewa ya hakura da duk wata maslaha da aka cimma a NNPP, bisa dalilin cewa komawa PDP shi ne mafita gare shi da mabiyansa,"" a cewar Dakta Kabiru Sufi, masanin siyasa kuma malami a Kwalejin Share Fagen Shiga Jami'a a jihar Kano. Malamin ya ce hakan zai iya yin tasiri da dama a siyasar tshon gwamnan jihar Kanon a daidai wannan lokaci musamman da ya kasance halataccen ɗan takarar NNPP na sanata. ""Yana iya rasa wasu daga cikin magoya bayansa da ba su yarda da fitar tasa ba, kamar dai yadda wasu ba su bi shi ba a lokacin da ya fita daga APC ya koma NNPP ɗin. ""Hakan zai jawo masa raguwar magoya baya, musamman ganin cikin lokaci ƙanƙani wasu su zauna a APC sun ƙi bin sa yanzu kuma wasu za su zauna a NNPP su ƙi bin sa PDP,"" in ji Dakta Sufi. Sai dai malamin ya ce babu mamaki kuma a yanzu wasu tsofaffin magoya bayansa da suka zauna a APC su biyo shi PDP ɗin. ""Dud da dai a yanzu ba a ga wasu jiga-jigai sun yi haka ba, amma ana iya hasashen faruwar hakan nan gaba,"" ya ce. A hannu guda kuma masanin ya ce babu mamaki wannan sauyin sheka ya kawo maslaha ga matsalolin da suka daɗe suna addabar jam'iyyar PDP. ""Musamman ganin dukkan ɓangarorin da ke adawa da juna a PDP din sun hallara a gidan Shekarau ranar Lahadi, to yana iya zama sanadin shiryawarsu. ""Sai dai idan har ya yi kasadar nuna ɓangaranci to akwai yiwuwar matsalar ta ci gaba da ta'azzara."" Masanin ya ce ana iya samun sauyi a wannan tafiya amma ba lallai ya kasance gagarumi ba. ""Lallai jam'iyyar PDP na bukatar shigar irin su Shekarau don sake samun tagomashi,"" ya ƙara da cewa." https://www.bbc.com/hausa/articles/c87kdylv54lo +religion Ramadan: Amfanin azumi ga lafiyarmu guda takwas "A kowacce shekara miliyoyin Musulmai suna azumi tun daga fitowar rana har faduwarta, na tsawon kwanaki 29 ko 30 a cikin Watan Ramadan. A shekarun baya-bayan nan dai Ramadan na fadowa ne a watannin bazara a kusurwar duniya daga arewa, hakan zai janyo ranaku masu tsawo da kuma yanayi mai dumi. Hakan na nufin cewa wasu kasashe kamar su Norway, mutane za su yi azumi na tsawon sa'o'i 20 a wannan shekarar. Shin ko wane irin tasiri azumi ke yi a jikin mutum? Dr Lawal Musa Tahir wani kwararren likita da ke asibitin Nizamiye a birnin Abuja, ya lissafa alfanun azumi ga jikin dan adam guda takwas: A ka'ida dai jikin mutum ba ya shiga yanayin azumi sosai sai an shafe sa'a takwas bayan abinci na karshe da mutum ya ci. Wannan shi ne lokacin da cikin mutum ya gama narkar da abubuwan gina jiki da ya samu daga abincin. Jim kadan bayan wannan lokacin, jikinmu zai koma wa sikarin da ke adane a hanta da tsokar jikinmu domin samun karfi. Bayan dan lokaci kadan, idan sikarin ya kare, to kitse ne zai koma wuri na gaba da jiki zai iya samun karfi daga gare shi. Idan jikin mutum ya fara kone kitse, wannan na taimakawa wajen rage kiba da rage maiko da kuma rage yiwuwar mutum ya kamu da ciwon siga. Sakamakon kone sukari da kitse a jikin dan adam, hakan na sa nauyi da kibar dan adam ta ragu wadda hakan ce manufar motsa jiki. Masana na cewa mutane da dama kimanin kaso 31.5 da ke mutuwa na mutuwa ne sakamakon cututtuka masu alaka da ciwon zuciya. Dr Tahir ya ce azumi na inganta lafiyar zuciya kasancewar yana kone kitse sannan ya kawar da teba, al'amarin da ke daidaita sauka da hawan jini. Da zarar an kone sukari da kitse kuma an rage teba sannan an samu lafiyar zuciya to dan adam ya kan samu garkuwa da kuzari fiye da lokacin da ba ya azumi. Ita kuma garkuwa na taimaka wa jiki ne wajen hana kamuwa da wata cuta ko kuma cutar ba za ta yi tasiri a jikin dan adam ba. Idan aka ci rabin watan Ramadan, jikin mutum yana sabawa da azumi. Hanji da koda da huhu da ma fatar mutum na tsaftace kansu. Sannan sassan jikin da ke aikin tace abinci lokacin da mutum ya ci abincin za su huta ne lokacin azumi. Kamar yadda motsa jiki yake sanya kwakwalwa ta yi aiki yadda ya kamata, to sakamakon azumi ana iya samun wannan alfanu. Idan mutum ya ci abinci sannan ya sha ruwa abin da ke biyo baya a mafi yawan lokaci shi ne kasala. To amma a lokacin azumi babu irin wannan kasala kasancewar ba a ci abinci ba. To sai dai Dr Lawal Musa Tahir ya ce ya kamata jama'a su yi hattara wajen bude baki. A lokacin da jikin mutum ya fara sabawa da azumi, kitse na raguwa kuma shi ne ke zama sikari a jini. Dole sai an mayar da ruwan da mutum duk ke rasawa a yayin azumi, in ba haka ba zufa za ta iya janyo rashin ruwa a jiki. Saboda haka dole ne abincin da mutum zai ci ya kasance mai gina jiki. Ya kara da cewa ""Ya kamata a fara amfani da kayan marmari wajen bude baki sannan kuma za a iya amfani da abu mai dumi."" Dangane kuma da mutanen da suke yin dore, Dr Tahir ya ce ""akwai matsala idan dai har a ka dauki doren al'ada, inda rumbun ajiya da ke jikin dan adam zai yi kasa kuma hakan na nufin mutum zai galabaita.""" https://www.bbc.com/hausa/labarai-52471401 +business CBN ya ba da wa’adin kwana 47 a mai da tsoffin kudin da za a sauya banki Sakamakon matakin da babban bankin Najeriya ya dauka na sauya fasalin wasu takardun kudin kasar, an umarci al’ummar kasar da su mayar da tsoffin kudaden da za a sauya zuwa banki. CBN, ya ce idan mutane suka mayar da kudaden ba tare da bata lokaci ba, to za su iya samun musayar kudinsu a kan kari. Ya ce saboda wannan sabon tsarin yanzu an cire duk wani caji da ake yi a kan kudin da ake kai wa bankuna ba tare da bata lokaci ba, kuma duk yawan kudin. To sai dai kuma masana tattalin arziki a Najeriya, sun yi tsokaci a kan wa’adin mayar da tsoffin kudin da za a sauya zuwa banki. Aliyu Da’u, masanin tattalin arziki ne a Najeriya, ya shaida wa BBC cewa, wa’adin da babban bankin na Najeriya a gaskiya ya yi kadan bisa la’akari da yawan kudin da ke hannun mutane. Ya ce,” Idan aka yi la’akari da kwanakin da aka diba na mayar da wadannan kudade gaskiya sun kadan, domin dole za a samu cunkoson mutanen da za su je bankuna don mayar da kudinsu. Ga batun cutar korona wadda har yanzu akwai ta, kuma duk in da aka samu cunkoson mutane idan har akwai mai ita ai dole a yadata, sannan ga batun hadarin da ake akwai na mutane na kan layin shiga banki barayi su dirar musu su kwace kudin.” Masanin tattalin arzikin, duk wadannan matsaloli ne da za a iya fuskanta saboda takaitaccen lokacin da aka bayar na mayar da wadannan kudade. Aliyu Da’u, ya ce,” Baya ga wadannan matsaloli, akwai kuma fargabar da mutane ke da ita cewa batun sauya kudaden nan zai iya durkusar da jarin wasu musamman ‘yan kasuwa.” Ya ce, to amma tun da CBN ya ce a mayar da kudin don sauyawa, to ba mamaki akwai wasu bayanai na sirri da gwamnati ke da shi wanda jama’ar gari ba su dashi, kamar batun ‘yan siyasar da suka tara kudi suka ajiye don ayi amfani da su a lokacin zabe. To ba mamaki an bayar da wannan takaitaccen lokaci ne don a samu damar karbe kudaden daga wajen ‘yan siyasa wata kila a samu saukin raba kudi a loakci zabe. Masanin tattalin arzikin ya ce, bayan siyasa akwai kuma batun ‘yan bindiga d ake satar mutane don kudin fansa, ba mamaki suma suna da irin wadannan kudade da za a sauya, to idan har aka bayar da wannan wa’adi ai dole su rabu da su don sauyawa. Ya ce, to idan aka yi la’akari da irin wadannan misalai, a iya cewa matakin sanya wa’adin ya yi dai-dai, to amma kuma a hakikanin gaskiya lamarin zai shafi mutane sosai musamman ‘yan kasuwa. A ranar Laraba ne babban bankin Najeriyar ya sanar da matakin sauya fasalin kudin kasar daga takardar naira 100 zuwa 1000, in da ya buƙaci masu kuɗi a hannu su mayar da su bankuna cikin ƙasa da kwana 50. Kazalika CBN din, ya ce ce sabbin kudaden da za a samar za su fara yawo a hannun mutane daga ranar 15 ga watan Disambar 2022, sannan kuma za a ci gaba da amfani da tsofaffin kudaden har nan da ranar 31 ga watan Janairun 2023. https://www.bbc.com/hausa/articles/cd1e5np99pmo +health Lafiya Zinariya: Kashi 80 'na masu suna fama da kwarnafi' Latsa hoton da ke sama domin sauraren shirin: Kwararrun likitoci sun ce mafiya yawan mata masu juna biyu sun fi saurin samun matslar kwarnafi da kuma mutanen da kiba ta yi musu yawa. Inda suka yi karin haske da cewa ana samun kwarnafi ne idan aka samu matsala da wani murfi wanda ke rufe tumbin a ciki. Idan murfin bai rufu ba sai wani sinadari da ake cewa acid ya kwararo cikin bututun makoshi. Hakan ne ke haifar da zafi da kuma radadi ko suya da mutum kan ji a kirji. Masana sun ce kwarnafi ba shi da wata alaka da zuciyar mutum, kamar yadda wasu ke dauka cewa suna jin zafin ne a kahon zuci. Sai dai masana a fannin kiwon lafiya sun bayyana cewa kwaranfi na iya lalata bututun makoshi kuma idan yayi tsanani ta kan kai har sai an yi wa mutum tiyata. Hakazalika, kwarnafi na janyo cutar daji ko da yake ba kasafai ake samun hakan ba. Hukumar lafiya ta Burtaniya ta bayar da shawara kan wasu matakai da mutum zai iya dauka a kashin kansa don samun saukin kwarnafi. Matakan sun hada da: Sai dai hukumar ta ce idan ciwon bai tafi ba duk da daukar wadannan matakai, ya dace mutum ya je asibiti don ya ga likita. https://www.bbc.com/hausa/shirye-shirye-na-musamman-60253358 +religion Nupur Sharma: Kalaman ɓatanci kan Annabi Muhammad sun 'ɓata' tsakanin Indiya da ƙasashen Larabawa "Ala tilas Indiya ta bai wa ƙasashen Musulmai da take alaƙa da su haƙuri, bayan wasu kalaman ɓatanci da suka jawo da ce-ce-ku-ce da wasu manyan jami'an gwamnatinta suka yi a kan Annabi Muhammad. Mai magana da yawun jam'iyya mai mulki ta Hindu nationalist Bharatiya Janata Party (BJP), Nupur Sharma ce ta yi kalaman a wata muhawara da aka yi a talabijin a watan da ya gabata. Shi ma Naveen Jindal, shugaban sashen yaɗa labarai na jam'iyyar ya sake wallafa saƙo kan batun a Tuwita. Kalaman Ms Sharma sun harzuƙa al'ummar Musulmai da suka kasance marasa rinjaye a ƙasar, abin da ya jawo zanga-zanga a wasu jihohin. BBC ba za ta maimaita kalaman da Ms Sharma ta yi ba saboda tsaurin su. Jami'an sun bai wa al'umma haƙuri kuma jam'iyyar ta dakatar da Ms Sharma tare da korar Mr Jindal. A wata sanarwa da ta fitar, jam'iyyar ta ce: ""BJP ta yi tur da duk wasu kalaman ɓatanci kan wasu mutane ko wani addini. Sannan BJP ba ta yarda da duk wata aƙida ta cin mutuncin wani addini ba. Babu ruwan BJP da aƙidar waɗannan mutanen."" Masu suka sun ce kalaman Ms Sharma da Mr Jindal sun nuna irin tsantsar rabuwar kan da ke tsakanin mabiya addinai da ake fama da shi tsawon shekaru a ƙasar. Ana samun ƙaruwar kalaman ƙiyayya da kai hare-hare kan Musulmai tun bayan da BJP ta hau mulkin ƙasar a 2014. Ƙwararru sun ƙara da cewa martanin da BJP ta yi bai isa ba, bayan da lamarin da ake ganin na cikin gida ne ya rikiɗe zuwa na ƙasashen waje - Kuwait da Qatar da Iran sun yi wa jakadunsu kiranye don nuna rashin jin daɗinsu a ranar Lahadi. Ita ma Saudiyya a ranar Litinin ta yi tur da kalaman. Qatar kuwa cewa ta yi tana tsammanin Indiya ta ba ta haƙuri. Ma'aikatar harkokin wajen Qatar ta ce: ""Ƙin ɗaukar matakai kan irin waɗannan kalamai na ƙin jinin Musulunci na zama wani babban haɗari ga kariyar haƙƙin ɗan adam, kuma zai iya jawo wariya, lamarin da ka iya kawo tashin hankali da ƙiyayya."" Saudiyya ita ma a tata sanarwar ta yi amfani da kalamai masu ƙarfi. ""Ma'aikatar harkokin waje ta yi tur da Allah-wadai da kalaman mai magana da yawun jam'iyyar BJP."" Jakadiyar Indiya a Qatar Deepak Mittal, ta ce kalaman da wasu masu son tayar da zaune tsaye suka yi ba daga gwamnatin Indiya ba ne. Su ma manyan ƴan jam'iyyar BJP da sauran jakadun ƙasashe sun yi tur da kalaman. Ƙungiyar Haɗin Kan Ƙasashen Musulmai mai mambobi 57 OIC, da kuma Pakistan su ma sun soki Indiya. Masu sharhi sun ce ya kamata shugaban jam'iyyar na ƙasa gaba ɗaya da kuma gwamnatin ƙasar daga ƙololuwa su fitar da sanarwar yin tur da lamarin. Rashin yin hakan a cewarsu, zai lalata dangantakar Indiya da ƙasashen Larabawa da kuma Iran. Indiya da ƙasashen yankin Gulf da suka hada da Kuwait da Qatar da Saudiyya da Bahrain da Oman da kuma UAE, suna kasuwancin da ya kai na dala biliyan 87 daga shekarar 2020 zuwa 2021. Miliyoyin Indiyawa ne ke zaune suke kuma aiki a wadannan ƙasashen, suke kuma tura miliyoyin daloli zuwa ƙasarsu ga iyalansu. Yankin shi ne kuma wanda Indiya ta fi shigar da makamashi ƙasarta daga cikinsa. Firaministan Indiya Narendra Modi yana yawan kai ziyara yankin tun bayan ɗarewarsa mulki a 2014. Tuni ƙasar ta ƙulla yarjejeniyar kasuwanci marar haraji tsakaninta da UAE sannan tana tattaunawa da sauran ƙasashen don faɗaɗa yarjejeniyar. Sannan akwai lokacin da Mista Modi ya halarci bikin buɗe wani wajen bauatr ƴan addinin Hindu a Abu Dhabi a 2018 - wanda aka bayyana a matsayin misali na ƙarfafar alaƙar Indiya da yankin Larabawa. A yayin da dangantaka tsakanin Indiya da Iran kuwa ke sirewa cikin shekarun nan, wannan sabon ce-ce-ku-cen ka iya shafar ziyarar da ministan harkokin wajen Iran Hossein Amir Abdollahian ke shirin kai wa Indiya. Ƙwararru sun ce ce-ce-ku-cen ka iya shafar nasarorin da Indiya ta yi a baya-bayan nan. Wasu masu sharhin kuwa cewa suka yi lalacewar dangantakar diflomasiyya tsakanin Indiya da ƙasashen ka iya shafar burikanta. Ƙasashen Larabawa na ƙoƙarin kwantar da hankulan al'ummarsu Su ma ƙasashen Larabawa a nasu ɓangaren, suna ɗaukar matakai don kwantar da hankulan al'ummominsu. An yi ta amfani da maudu'ai na sukar Indiya a kafafen sada zumunta da suka dinga tashe a ƙasashen, kuma lamarin ya zama wanda ya mamaye kanun labaransu. Wasu maudu'an na kira ne da ƙauracewa kayayyakin Indiya. Sannan rahotanni sun ce wasu kantunan a Qatar da Kuwait sun yi ta cire kayayyakin Indiya daga cikinsu. Masu suka sun ce ana samun ƙaruwar rarrabuwar kawuna a Indiya tun bayan da BJP ta hau mulki. Sannan an samu ƙaruwar tashe-tashen hankula a makonnin da suka gabata bayan da wasu mabiya Hindu suka je wata kotu a Varanasi son neman izinin yin ibada a wani tsohon masallaci da suka ce an gina shi ne a gurbin wani tsohon wajen ibadaha. Tasoshin talabijin sun yi muhawara sannan an samu ƙaruwar kalaman ƙiyayya a shafukan sada zumunta ma kan lamarin. Amma masu sharhi sun cewa fushin da ƙasashen duniya suka yi kan lamarin ya kamata ya zama izinia ga Indiya." https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-61703802 +religion Ku San Malamanku tare da Sheikh Abubakar Abdussalam Muhammad, Baban Gwale "An haifi Sheikh Abubakar Abdussalam Muhammad wanda aka fi sani da Baban Gwale ne a birnin Kano da ke arewacin Najeriya a shekarar 1982. Ya shaida wa BBC a filinmu na Ku San Malamanku cewa tun gabani ""a yaye"" shi ya iya magana kuma hakan ne ya ba shi damar soma koyar sunayen Allah da Larabci daga wurin mahaifiyarsa. Malamin ya kara da cewa bayan ya soma tafiya ne aka fara zuwa da shi makarantar allo ta marigayi Malam Maraya, inda daga bisani ya koma makarantar Alaramma Malam Inuwa, ko da yake a makarantar allo ta Malam Idi ya kammala saukar AlKur'ani. ""Daga baya ne na karasa satu sannan aka kai ni wajen Alaramma Malam Mu'azu a unguwar Gwammaja, sai kuma daga baya lokacin da na kai Suratul Nahli ina rubuta AlKur'ani na kammala sauka ta farko, sai aka mayar da ni makarantar Alaramma Malam Dahiru,"" in ji Malamin. Sheikh Muhammad ya ce a makarantar Shababul-Kur'an ta Malam Abubakar Ramadan ya soma koyar tajwidi. Ya kara da cewa ya shiga makarantar firamare ta Dangado Special Primary School a shekarar 1988, kuma bayan ya kammala ya shiga makarantar Sakandare mai suna Government Arabic College da ke Gwale. Malamin ya ce ya kuma shiga makarantar zaure ta Malam Muhammad Kani Gwale inda ya koyi karantun Tauhidi da Luga da Usulul Fiqh da Adabi da sauransu. Sheikh Abubakar Abdussalam Muhammad ya ce daga nan ya yi karatun Share fagen shiga Jami'a ko da yake ya kuma yi jarrabawar JAMB inda ya samu gurbin karatu a Jami'ar Bayero da ke Kano domin karanta Aikin Jarida. Sai dai ya sauya zuwa Fannin Shari'a sannan kuma daga bisani ya samu damar tafiya Sudan inda ya soma karatun Digiri. Amma daga bisani ya samu gurbin karatu a Jami'ar Madina inda ya karancin Fannin Hadisi da Kimiyyarsa inda ya kammala a 2008/9. Ya ce ya sake komawa Makkah inda ya yi karatun gaba da Digiri na farko a Tsangayar Horas da Limamai da Malamai a kan Da'awa. Baban Gwale ya samu aiki a aiki a Kwalejin Shari'a da Addinin Musulunci mai suna Aminu College of Legal Studies da ke Kano. Kana ya koma Sudan inda ya yi Digiri na biyu a fannin koyar da Hadisi da Kimiyyarsa. Daga bisani ya yi Digirin-Digirgir a kasar ta Sudan. Malamin ya kara da cewa a zamansa na Madina ya hadu da manyan malamai, cikinsu har da 'yan Najeriya, wadanda suka koyar da shi matuka. Baban Gwale ya ce Suratu Nahl da Suratu An'am da Suratu Ankabuti da Suratu Ahqaf ne suka fi ba shi wahala. Amma ya ce yana son Kur'ani kafatan, sai dai ya fi son Suratu Nisa'i da Furqan da Israi'i saboda ""idan ina karanta su nakan shoga wani yanayi mai dadi."" Malam ya ce ranar da ya samu gurbin karatu a Jami'ar Madina ce ranar da ya fi farin ciki da ita a duniya. Ya ce abu biyu ne na takaici da ba zai manta da su ba, wato kuskuren da aka samu a lokacin da ya samu gurbin karatu a karon farko a Jami'ar Bayero. Malam ya ce ya sha wahala sosai a lokacin. Abu na biyu kuma lokacin da yake aji uku zai shiga na hudu a Madina a lokacin da ya je Kano hutu har fasfo ɗinsa da tikitinsa suka fadi. ""Na ga wulakanci sosai a ofishin fasfo da jami'an ofishin jakadancin Saudiyya a Kano, wannna abu ya jawo na rasa zango ɗaya na karatu a Jami'ar Madina."" Baban Gwale ya ce babban abin da ke faranta masa rai shi ne ya ga ana bautar Allah da Manzonsa, amma ya tsani zalunci da tauye hakki musamman na mata a gidajen aure. Yana da mata biyu da ƴaƴa tara." https://www.bbc.com/hausa/labarai-61911037 +health Matakan magance lalular tankwashewar tafin kafa "A farkon wannan shekarar, Serigne, mai shekaru 14, ya sakankance cewa ba zai kara fita daga gidansu ba. Yana iya tafiya a hankali bayan da aka haife shi da wata lalura da tafin kafafunsa biyu ke kallon ciki. Yana jin kunyar fita waje, sakamakon yadda wasu ke tsokanarsa ta hanyar kwaikwayon tafiyarsa, wasu kuma na kiransa da sunaye iri-iri na tsokana. Amma a yanzu cikin kasa da wata shida an yi masa tiyata domin gyara masa kafafuwan nasa, kuma a halin yanzu mafarkinsa na buga wa kasarsa Senegal wasa kwallon kafa na iya tabbata. Serigne na da lalaurar takwashewar tafin kafa, kuma a yanzu za a shiga wani mataki a gyaran kafafun da ake masa. A cewar gidauniyar Miraclefeet,  kowacce shekara ana haifar jarirai 200,000 da lalurar tankwashewar tafin kafa, kuma daga cikin mutum kusan miliyan 10 da ke rayuwa da lalurar a kusan miliyan takwas ba su taba samun magani ba. A baya-bayan nan Senegal ta bi sahun wasu kasashen Afirka wajen fara amfani da hanyar Ponseti wajen gyara wannan lalura. Ponseti hanya ce ta farko ta gyaran kafar da aka sa wa sunan wani likitan Sifaniya wanda shi ne ya kirkiro aikin . Wannan na nufin likitocin Senegal sun kware wajen sanin yadda ake wannan aiki, kuma yanzu suna amfani da ita wajen yi wa  matasa da manya aiki domin warkar da su. Mahaifiyar Serigne na farin ciki samun saukin da danta ke yi. Ta fi kowa sanin irin wahalar da ya sha sakamakon wannan lalura. “Akwai wani lokacin da ya kasa fita daga gida tsawon kwana uku, na ji takaicin hakan sosai, amma yanzu muna jin dadi.” Daga cikin matakan da ake bi na yin aikin gyaran, a kowane makon akan sake wa kafar bandejin da ake nadeta da shi domin ta rika sauyawa zuwa yadda ake bukata sannu a hankali. To amma sakamakon yadda lalurarsa ta tsananta, an sake masa bandejin da ake nade kafafun nasa da shi kusan sau 20 a cikin makonni biyar zuwa takwas. A karshen kowane aiki ana bukatar yi wa mutum aikin tiyata a kafar tasa domin cire wasu abubuwa, in ba haka ba kuwa aikin ba zai yi kyau ba. A ‘yan kwanakin da suka gabata aka saka wa Serigne bandejin karshe a aikin da ake yi masa. Bayan haka yana bukatar a yi masa tiyata a kafafaun nasa domin taimaka masa koyon yadda zai yi tafiya bayan da kafafun suka yi nauyi, kuma yana bukatar a daura masa wata safa a kafafunsa domin taimakawa wajen daidaita kafafuwan nasa, amma bisa ga alama aikin na tafiya yadda ya kamata. Fatou wata yarinya ce da ake yi wa aikin gyaran kafafun a wani asibiti a birnin Dakar bayan ta shafe tafiya mai nisa kafin ta zo wannan asibitin, a lokacin da a yau take cika shekara 13 da haihuwa a yau din ne kuma ake cire mata bandeji na hudu a aikin da ake yi mata. A lokacin da mai aikin jinyar ke cire mata bandejin daga kafafun nata, Fatou ta janye kafar saboda ciwo, to amma sai ma’aikaciyar jinyar ta rarrashe ta domin ta samu nutsuwa. Ma’aikaciyar jinyar ta shaida wa BBC cewa ""mun yi imanin cewa za ta warke kuma za ta taka kafarta yadda kowa ke takawa’’ ta fada cikin murmushi. Fatou ta shaida mana cewa ba ta yi tsammanin za ta warke ba kasancewa tana rayuwa a yankin karkara a kasar, dan haka yanzu tana murna da wannan aiki. Zuwa makaranta  ya yi mata wahala, tana kallon ‘yan uwanta yara suna tsalle da gudu, inda ita kuma take dogara da sandunan guragu. ""Akwai abubuwa da dama da nake son yi, amma bana iya yinsu, amma idan na warke zan yi duk abinda nake son yi’’. Daga ciki akwai babban burinta na zama likita. To amma ba kowa ba ne ya samu wannan dama ta aikin gyaran kafar, alal misali Oumou Barry mai shekara 32, ta nuna mana kafarta a lokacin da muka ziyarce ta a unguwar Lac Rose da ke binin Dakar, kafar tata ta yi girma tare da lankwashewa sosai. Ta yi kokarin takawa da kafar amma sai ta yi ihu sakamakon zafin radadin ciwon da kafar ke yi, abinda ke nuna cewa ba za ta iya tafiya mai isa ba. ‘’A lokacin da nake yarinya, rayuwata ta kasance cikin tsangwama saboda wannan lalura’’ ta fada a yayin da take share hawaye. ''Nakan tambayi mahaifiyata cewa me yasa nake haka? Ita kuma takan amsa min da cewa haka Allah ya halicceni kuma a haka aka haifo ni''. Ta ce lokaci mafi tsanani a gareta shi ne a lokacin da ta fara zama budurwa a lokacin da kawayenta suka fara sanya takalma na kwalliya ita kuma ta ci gaba da saka sandal, daga karshe ta ce dole ta daina zuwa makaranta saboda ba za ta iya jure tsangwamar da take fusktanta ba. Bayan da ta rabu da kawayenta na makaranta ta fara sana’ar kitso to amma daga baya ta daina wannan sana’a. Oumou ta yi aure kuma a yanzu tana da ‘ya’ya biyu dan haka rayuwarta ba ta cikin tsangwama kamar sauran masu lalura irin nata, amma duk da haka tana jin zafin wannan lalura kasancewar ba ta yi karatu ba balle ta samu aikin gwamnati. Sakamakon yawan shekaru da Oumou ke da su ba za a iya yi mata aikin Ponseti na gyaran wannan laulura ba, kasancewar aikin baya yin kyau ga mafiya yawan mutanen da suka manyanta. Duk da cewa kawo yanzu babu wani bincike a kimiyance da yake nuna musabbabin haihuwar mutum da wannan lalulura, bincike ya nuna an fi haifar maza da lalurar fiye da mata. Kuma mafiya yawan mutanen da ke dauke da wannan lalura suna kasashe matalauta ne watakila sakamakon yawan yawan haihuwa da ake samu a irin wadannan kasashe, kuma a irin wadannan kasashen ne ba a iya magance wannan lalura. Aisha Mballo  wata mace ce guda daya da ta sadaukar ta rayuwarta wajen ganin cewa an yi wa masu irin wannan lalurar aiki tun suna kanana. A lokacin da muka hadu da ita, tana tafiya cikin nutsuwa da kwarin jiki a cikin kasuwar garin Thies rike da katon littafin hotuna. Littafin na bayani ne kan yadda ake maganace wannan lalura ta hanyar aikin da ke kira Ponseti, ta zo nan ne domin binciko masu irin wannan lalura domin taimaka musu da shawarwari. Aisha ta ce ita ma da haka kafafunta suke, sai a wajen shekarun 1990 a lokacin tana budurwa aka yi mata aikin gyaran kafafun a Amurka. A yanzu tana aikin sa kai a matsayin jakadiyar gidauniyar MiracleFeet mai fafutikar ganin an kawar da wannan lalura. Aisha ta ce ‘’Idan mutane suka fahimci cewa ‘ya’yansu na dauke da wannan lalura, to kar su boye yaran a gida, su kawo mana su, mu kuma za mu kai su asibiti domin a yi musu aiki’’. Rosalind Owen na kungiyar yaki da lalurar tankwashewar tafin kafa ta duniya wanda ya yi nazari kan yadda ‘yan Afirka ke kallon wannan lalura ya ce a wasu garuruwan Afirka masu dauke da cutar na fama da ‘’matsaloli na tsangwama’’. ""Mutane na tunanin cewa masu irin wannan lalura wani laifi suka yi wa Ubangiji ya halicce su a haka, ko kuma an yi wa mai laluar tsafi ne ya sa ya zama haka ko kuma wai iyayensa ne suka aikata wani laifi’’. A yayin da yanzu a Senegal kusan kashi 20 cikin dari na masu irin wannan lalura ake magance musu ita tun a lokacin haihuwa, a yanzu ana samun ci gaba sosai a yakin da ake yin a kawar da lalurar. Kafin wakilan BBC su bar garin na Thies sun ziyarci wajen asibiti domin ganin wata jaririya ‘yar mako biyu wadda aka saka wa sabon bandeji a kafarta. Likitoci da masu aikin jinya na kokarin nade siraran kafafuwanta da bandeji. Wannan shi ne lokacin da ya dace na magance wannan lalura." https://www.bbc.com/hausa/articles/c1r3e9zenero +technology Za ku dinga jin labaran BBC kyauta a manhajar MyMtn "Sashen BBC da ke watsa labarai ga ƙasashen duniya ya ƙulla ƙawance da kamfanin sadarwa na MTN da ke Najeriya don jin labaran BBC cikin minti ɗaya a kyauta cikin Turanci da Hausa da Igbo da Pidgin da kuma Yorabanci ga waɗanda suka sauke manhajar MyMTNApp a wayoyinsu. Wannan ne karo na farko da wata babbar kafar watsa labarai ta duniya za ta kasance cikin manhajar ta MyMTNApp. Labaran BBC a minti ɗaya yana sanar da dumbin masu sauraron kafar irin abubuwan da suke faruwa kuma ake tattauna su a kafafen sada zumunta na zamani har ma da irin labaran da suke faruwa a Najeriya da ma sauran ƙasashen duniya. Za a riƙa sabuntawa kowace rana tsawon mako ɗaya. Wannan tsari zai sanar da ɗumbin masu sauraron BBC a Najeriya sabbin labaran wasanni da nishadi da kimiyya da batutuwa da dama. Masu sauraro za su samu damar sauraron labarai cikin minti ɗaya akai-akai daga safe zuwa dare. Masu jin Hausa da Igbo da Pidgin da Yarabanci ne za su ci gajiyar wannan yarjejeniyar ta hanyar samun ƙayatattun labarai cikin daƙiƙa 60 a sauƙaƙe ba tare da wata matsala ba. Hadin gwiwar za ta tabbatar cewa masu amfani da layin MTN za su samu sahihan labarai daga BBC musamman yadda ake samun ƙaruwar labaran ƙarya a sassan Najeriya da Afirka. MTN Nigeria shi ne babban kamfanin sadarwa a nahiyar Afirka wanda ke sada sama da mutum miliyan 64 daga sassa daban-daban na Najeriya da junansu da ma duniya. Ya samar da manhajar MyMTNApp wadda sama da mutum miliyan hudu ke amfani da ita. Oluwatoyosi Ogunseye, Shugabar BBC reshen Afirka ta Yamma ta ce ""wannan yarjejeniya da MTN tana daga cikin burin BBC na kusanto da masu sauraro a duk inda suke. Ɗaya ne daga cikin hanyoyin da BBC ke ba da gudummawa a Najeriya kuma muna matuƙar farin ciki da wannan hadin gwiwa saboda dama ce ta ƙara janyo masu saurarenmu a Najeriya musamman matasa garemu."" Da yake jawabi kan yarjejeniyar, babban jami'in da ke kula da hanyoyin sadarwa na kamfanin MTN, Srinivas Rao ya bayyana cewa ""muna alfahari da wannan ƙawance . Wata hanya ce da zamu bai wa matasan Najeriya damar sauraron labarai masu sahihanci. A zamanin da ake yawaita yaɗa labarai marasa tushe musamman a shafukan sada zumunta, irin wannan tsari zai kawo sauye-sauye da dama.""" https://www.bbc.com/hausa/labarai-53233409 +sports AC Milan ta dauki Divock Origi AC Milan ta dauki Divock Origi, wanda kwantiraginsa ya kare a Liverpool, bayan kammala kakar Premier League da ta wuce. Yarjejeniyar dan wasan tawagar Belgium, mai shekara 27 ta kare a Anfield, ya kuma sa hannu kan kwantiragin kaka hudu a San Siro. Origi ya ci kwallaye masu mahimmaci a Liverpool, har da ta biyu da ya ci Tottenham a wasan karshe a Champions League da kungiyar Anfield ta yi nasara da ci 2-0 a 2019. Ya koma taka leda a Liverpool a 2014 da cin kwallo 41 a wasa 175 da ya yi mata. AC Milan ta lashe Serie A a kakar da aka kammala a karon farko tun bayan shekara 11, rabon da ta dauki kofin babbar gasar Italiya. https://www.bbc.com/hausa/articles/cw98vrgy000o +health Ko kun san 'illar' da man bilicin ke yi wa koda da hanta? An yi gargadi da a kiyayi mayukan bilicin ko kuma kara hasken fata da ke sauya fata tamkar sinadarin goge fenti. Kungiyar kananan hukumomi da ke Ingila ce ta yi wannan gargadin inda ta ce duk yadda za a yi, to lallai a yi kokarin kiyayar irin wadannan mayukan. An bayyana cewa a kwanakin baya, jami'an da ke sa ido kan ingancin kayayyaki a Ingila sun kwace irin wadannan mayukan daga hannun diloli da masu sayar da su sakamakon rashin ingancinsu. Kungiyar ta bayyana cewa da yawa daga cikin nau'in mayukan na dauke da sinadarin hydroquinone da kuma sindarin mercury. Haka zalika kungiyar ''British Skin Foundation'' wacce kungiya ce a Birtaniya da ke bincike kan cututtuka irin na fatar jiki, ta bayar da shawara ga jama'a da su rinka kokarin tattaunawa da likita idan suna da wata matsala da fatar jikinsu. Kungiyar kananan hukumomi ta Birtaniyar ta bayyana cewa masu sayar da irin wadannan mayukan na bilicin ko kara hasken fata na tallan su ne a shafukan intanet, wasu kuma na dakon su a bayan mota. An kuma bayyana cewa kamfanonin da suke hada irin wadannan mayukan ba su fadin gaskiya dangane da kayan hadin da mayukan suka kunsa domin masu amfani da su su sani. Kungiyar ta kwatanta sinadarin Hydroquinone da ke cikin mayukan na bilicin tamkar sinadarin goge fenti, inda ta ce mayukan kan goge fatar sama tas, kuma hakan kan iya janyo cutar kansa ko yin illa ga hanta ko kuma koda. Haka zalika sinadarin Mercury kan iya janyo irin wadannan matsaloli da ke barazana ga lafiyar bil' adama. A yanzu haka dai an hana amfani da mayuka masu dauke da sinadarin hydroquinone a Ingila, sai dai idan likita ne ya ba mutum umarnin amfani da su. https://www.bbc.com/hausa/labarai-49869442 +entertainment Kannywood: Hukumar tace fina-finai ta Kano ta ce ba sani ba sabo "Hukumar tace fina-finai ta jihar kano ta ce ba za ta saurara wa duk wani dan fim ko mawaki ba matukar ya saba wa dokar da ta kafa hukumar ta shekarar 2001. Hukumar ta furta hakan ne a wata sanarwa da ta fitar, inda ta kara da cewa duk wanda ya fitar da waka ko fim ba tare da lasisi ba za ta dauki ""matakin ba sani ba sabo"" a kansa. Sanarwar wadda mai magana da yawun hukumar Ibrahim Adamu K/Nasarawa ya sanya wa hannu, ta ce wannan gargadi ya biyo bayan gurfanar da Naziriu M Ahmad Sarkin Wakar Sarkin Kano da aka yi ne a gaban kotu. ""Babban sakataren hukumar Alhaji Isma'il Na'abba Afakkallah ne ya yi gargadin biyo bayan kamawa tare da gurfanar da Naziru M. Ahmad (SarkinWaka) gaban kotu bisa zargin fitar da kundin wakoki a baya-bayan nan da ya yi ba tare da sahhalewar hukumar ba,"" in ji sanarwar. Sannan ya yi kira ga dukkanin masu shirya fina-finai da mawaka da su tabbatar sun mika wa hukumar ayyukansu domin tantancewa kafin fitar da su kasuwa. A ranar Laraba ne dai jami'an tsaro suka dira gidan shahararren mawaki Naziru M. Ahmad, wanda aka fi sani da Sarkin Waka. Sun zarge shi da gudanar da dakin buga wakoki wato studio maras lasisi a cikin gidansa da kuma fitar da kundin waka shi ma maras lasisi. Har sai a ranar Juma'a ne kuma kotu ta bayar da belinsa bayan ya cika sharuddan da ta gindaya masa. Makwanni kafin haka, hukumar ta tace fina-finai ta gurfanar da Sanusi Oscar bisa zargin sakin wata waka shi ma ba tare da tantancewar hukumar ba. Ana ganin wadannan rikice-rikice da ke faruwa tsakanin hukumar da kuma masu shirya fina-finai a jihar Kano ba zai rasa nasaba da rikicin siyasa ba. Wakilin BBC Nasidi Adamu Yahaya ya bi diddigin dalilin da ya sa gwamnatin jihar ta Kano ba ta ga-maciji da wasu daga cikin 'yan fim din." https://www.bbc.com/hausa/49703735 +business Tasirin Coronavirus: Dokar kulle 'ta durƙusar da ƙananan masana'antun arewacin Najeriya' "Dokar kullen da gwamnatin Najeriya ta sanya da zummar daƙaile yaɗuwar cutar korona ta durƙusar da ƙananan masana'antun arewacin Najeriya. Dr Dikko Umaru Radda, shugaban hukumar bunƙasa matsakaita da ƙananan masana'antun ƙasar ne ya bayyana haka a tattaunawarsa da BBC Hausa. Sai dai ya ce akwai tsarin tallafi da kuma rancen da Babban Bankin ƙasar ke bayarwa waɗanda za su taimaka wa masu ƙananan sana'oi. ""Babban ciwon ƙanana da matsakaitan masana'antu na ƙasar nan idan ka tambaye su shi ne, rashin samun kuɗaɗen da za su gudanar da ayyukansu. Kuma an fito da wani shiri wanda Babban Bankin ƙasar ya samar wanda ake ba da tallafin naira miliyan ɗaya zuwa miliyan 10. ""Abin da kake buƙata ka je hukumar da ke horar da ƙananan da matsakaitan masana'antu a tabbatar da an horar da kai, wannan takarda ta horarwa ita ce babban ginshiƙi na wannan bashin da za a ba ka,"" in ji shi. A cewarsa, cutar korona ta shafi tattalin arzikin duniya musamman a Najeriya da kusan mutum miliyan 60 na 'yan kasar sun dogara ne kan kananan da matsakaitan sana'oi. Ya ce: ""A Najeriya, muna da kusan mutum miliyan 41,500,000 wadanda masu yin kananan da matsakaitan masana'antu ne, kuma abin da ya mayar da Najeriya ta samu matsala, shi ne kusan wannan adadi miliyan 40 da wani abu 'yan kananan masana'antu ne wadanda jarinsu karami ne a kauyuka suke."" Ya kuma ce nnoba da ta zo ta taimaka wajen ganin cewa sun cinye jarinsu, wasu sana'arsu ta kare saboda (kulle), amma kusan tallafin da gwamnati ke fito da su za ka ga ana kallon kanana da matsakaitan masana'antu, wadanda za ka su ba sa ma da abin da za su iya zuwa banki su iya samun wadannan basussukan da gwamnati ta ke, ba a basu mahimmanci kamar yadda ya kamata. A ganinsa, irin wadannan masu karamin karfi ba bashi ya kamata a basu ba, ""tallafi ya kamata a basu daga naira dubu 10 zuwa dubu 50 har 100 dai-dai gwargwadon irin abin da kake, ba karamin taimakawa zai yi ba."" Ya ce sun ba da shawarwari ga wani kwamiti da ke karkashin mataimakin shugaban kasa na ganin yadda a kowace karamar hukuma, ""an dauki masu irin kananan sana'oi kusan dari 500 a kananan hukumomi 774 a basu tallafin ko da dubu 50 ne don ganin cewa sun bunkasa tattalin arzikinsu kuma mafi yawan wadannan mutane suna arewacin Najeriya."" Dr Radda ya ce akwai bukatar mutanen arewa su shiga irin wannan tsari saboda ""daga sanda aka fara wannan abun, idan ka kalli mutanen da suka amfana, da wadannan kudade za ka ga mafi yawanci mutanen kudancin Najeriya ne. Acewar sa hakan ta na faruwa ne ""saboda su suna da dagewa wajen bin diddigin irin wadannan tallafi da gwamnati take badawa da ganin cewa kuma abubuwan sun kai."" Shugaban hukumar ta bunkasa matsakaita da kananan masana'antu a Najeriyar ya ce ya kamata al'ummar arewa su jajirce ""yadda kowa yake dagewa yana neman abin nan suma su jajirce su neme shi."" ""Kuma duk wuraren nan, mu hukumarmu abin da muke muna ta fadakar da mutane, yanzu haka akwai shirin da muke gidan rediyo da talbijin da kuma yarurruka kala-kala na (fadawa) mutanen Najeriya cewa akwai kaza a wuri kaza yana da kyau kuje wuri kaza"" don samun moriyar shirin"", in ji Dr Radda." https://www.bbc.com/hausa/53295828 +entertainment ...Daga Bakin Mai Ita tare da mai waƙar Abba gida-gida Latsa hoton sama domin kallon bidiyon Daga Bakin Mai Ita wani shiri ne na BBC Hausa da ke kawo muku hira da fitattun mutane kan wasu abubuwan da suka shafi rayuwarsu zalla. A wannan kashi na 69, shirin ya tattauna da Tijjani Gandu, mawaƙin siyasa wanda ya yi waƙar Abba gida-gida da kuma wasu waƙoƙin fina-finan Kannywood. A wannan shiri ya amsa tambayoyin da suka shafi rayuwarsa da kuma waƙoƙinsa. Ɗaukar bidiyo da Tacewa: Fatima Othman https://www.bbc.com/hausa/media-58901815 +sports Atletico na zawarcin Ronaldo, Chelsea na dab da cimma matsaya kan Kounde Atletico Madrid ta tuntubi wakilan Cristiano Ronaldo kan rattaba hannun yarjejeniyar daukar dan wasan gaban na Portugal, mai shekaru 37, daga Manchester United. (AS - in Spanish) Sai dai sabon manajan United Erik ten Hag ya yi ikirarin, ta yiwu Ronaldo ya ci gaba da taka leda a Old Trafford har zuwa karshen kakar bana. (Guardian) Chelsea sun cimma matsaya da dan wasa Jules Kounde, har sun fara ta yin yuro miliyan 55 ga Sevilla domin daukar mai tsaron Faransa mai shekara 23. (Marca - in Spanish) Dan wasan tsakiya na Wales Aaron Ramsey, mai shekara 31, na tattaunawa da Juventus, domin Karkare batun karewar kwantiragin dan wasan a shekarar nan, hakan zai bashi damar rattaba hannun zuwa wata kungiyar a kyauta. (Mail) Mai tsaron baya na Matthijs de Ligt, mai shekara 22, ya isa Jamus domin kammala batun  komawarsa Juventus daga Bayern Munich, bayan kungiyar ta amince da farashin yuro miliyan 70, da kuma wata yuro miliyan 10 ta daban.   (Corriere dello Sport - in Italian) Har yanzu Barcelona ba ta tsaida magana kan daukar dan wasan tsakiya na Netherland Frenkie de Jong  ba, kan farashin yuro miliyan 17, a kwantiraginsa da ake son yi wa garanbawul, kan dan wasan mai shekara 25 da ke son komawa Manchester United. (Independent) Ita kuwa West Ham ta na da kwarin gwiwa kan dan wasan Lille kuma na tsakiyar Belgium Amadou Onana, mai shekara 20, bayan wani sabon cinikin na fam miliyan 30. Kungiyar na kuma son dauko tsohon dan wasan loanee Jesse Lingard, kuma na gaban Ingila mai shekaru, 29, amma a bagas bayan barin Manchester United. (Standard) Leeds da West Ham sun nuna sha’awar daukar mai kai hari na Faransa Martin Terrier daga Rennes, wanda ke bukatar akalla yuro miliyan 40, ga dan wasan mai shekaru. (L'Equipe - in French) Dan wasan Wolves, kuma mai kai hari na Portugal Fabio Silva, dan shekara 19, ya shirya tsaf domin komawa Anderlecht  bayan amincewa ya shiga kungiyar ta Belgian amma a bashu. (Fabrizio Romano) Arsenal na da kyayyawan fatan dauko dan wasan tsakiyar Brazil  Lucas Paqueta, dan shekara 24, sakamakon rashin fadawar ciniki da Lyon . (Media Foot - in French) https://www.bbc.com/hausa/articles/c28gdr0rz1yo +health Yadda ake gane an samu matsalar gani Latsa alamar lasifika da ke sama don sauraron hira da Dr. Fatima Kyari, likitar ido a Hukumar yaki da makanta ta duniya Wasu alkalumman sun nuna cewa mutum biliyan daya ne basa iya gani garau. Masu bincike sun ce kashi 4 cikin mutum dari na fama da cutar makanta musamman manya da suka haura shekara 40. Taken ranar ta bana shi ne ''Gani shi ne gaba da komai'', kuma bikin zai mayar da hankali ne wajen lalubo hanyoyin tabbatar da ganin cewa kowanne mutum, a duk inda yake a duniya na iya samun hanyar inganta ganinsa. https://www.bbc.com/hausa/labarai-50002525 +politics PDP da APC sun caccaki Farfesa Attahiru Jega kan gargaɗin da ya yi wa 'yan Najeriya "Jam'iyyar APC mai mulki da PDP mai hamayya a Najeriya sun mayar wa tsohon shugaban hukumar zaɓe (INEC) na ƙasar martani game da kalamansa da ya yi cewa sun gaza kuma ""kar 'yan Najeriya su sake zaɓen su"". Cikin wata hira da BBC Hausa ranar Litinin, Farfesa Attahiru Jega ya bayyana cewa ""APC da PDP sun yi [mulki] duk mun gani, ba gyara suke nufi ba"", yana mai cewa ya shiga jam'iyyar PRP. ""Idan ka dubi yaƙi da cin hanci da rashawar nan, duk mutanen da ake cewa ɓarayi ne za a hukunta su saboda sun yi sata a karkashin PDP, yanzu sun lallaɓa sun koma APC, kuma shiru kake ji,"" in ji shi. A cewarsa: ""Shi ya sa mu muke ganin cewa yanzu lokaci ya yi da za a samar da wata dirka da duk mutumin kirki zai koma cikinta, domin bayar da tasa gudunmawar wajen kawo gyara a Najeriya."" Dukkan APC da PDP babu wadda ta yarda da maganar tsohon shugaban INEC ɗin cewa ta gaza wajen kyautata rayuwar `yan Najeriya ballantana a ce kar a zabe ta a nan gaba. Babbar jam`iyyar hamayya ta PDP ta yi iƙirarin cewa ta cimma nasarori masu ɗimbin yawa a lokacin da APC ta ƙwace mulki daga hannunta, saɓanin matsain rayuwar da `yan kasar ke fama da shi a halin da ake ciki. PDP ta ce ba ta musanta cewa APC ta gaza ba amma idan har za a yi ƙwaƙwa, to tsohon shugaban hukumar zaben ma da nasa laifin, saboda da shi aka yi uwa da makarbiya wajen bai wa APC nasara a lokacin da ta yi wa PDP kaye. Mista Kola Olagbondiyan, shi ne Sakataren Yaɗa labaran PDP, kuma ya faɗa wa BBC Hausa cewa abin takaici ne yadda Jega ya nuna ""rashin fahimtarsa a fili"" a matsayinsa na farfesan kimiyyar siyasa. ""Ya kamata a tunasar da Farfesa Jega yadda PDP ta haɓaka tattalin arzikin Najeriya, ta biya tulin bashin da ake bin ta...har ma tattalin arzikinta ya zama ɗya daga cikin mafiya haɓaka cikin sauri kuma cibiyar zuba jari mafi girma a Afirka. ""Amma sai APC ta zo ta lalata shi sannan ta mayar da ƙasarmu babban birnin talauci na duniya da kuma cin bashi a cikin shekara shida."" Ita ma jam`iyyar APC a nata martanin, ta yi ikirarin cewa ta gaji tarin kura-kurai da ta zargi gwamnatin PDP da bar mata, tana mai cewa abubuwan da Shugaba Buhari ya cimma ""zarta na PDP"". Ta yi ikirarin cewa ta gaji tarin kura-kurai da ta zargi gwamnatin PDP ta bar mata, wadanda take fadi-tashin gyarawa, Kazalika, ta yi wa Farfesa Jega ba'a tana mai cewa watakila yana jiran ta yi masa tayi ne tun da ya shiga siyasa. ""Idan jam'iyyar APC ya ke so ya shigo to sai ya zo ofis ɗin ɗinmu ya karɓi takardu ya karanta domin ya fahimta sosai ya shigo,"" in ji Daraktan Yaɗa Labaran APC na Ƙasa, Mallam Salisu Na`inna Danbatta. Sai dai ya ce Farfesa Jega ya yi gaskiya kan abubuwan da ya faɗa a kan PDP." https://www.bbc.com/hausa/labarai-58074357 +religion Abin da ya sa aka kama sha'iri Bashir Ɗandago a Kano "Wata kotun majistare da ke jihar Kano a Najeriya ta bayar da belin fitaccen mawakin waƙoƙin Manzon Allah SAW da hukumar tace fina-finai ta gurfanar da shi a gabanta, kan kudi naira 500,000. Hukumar ta gurfanar da Malam Bashir Dandago ne bisa zargin sakin waƙa ba tare da ya kai wa hukumar ta tantance ta ba. Ta kuma ce babban dalilin da yasa ta kama Malam Bashir Dandago shi ne ya saki wata waƙa ba tare da an tantanceta ba, da kuma zarginsa da zagin malaman jihar da ke adawa da Malam Abduljabbar Nasir Kabara. A cewar shugaban hukumar tace fina-finai ta Kano Isma'ila Na'abba Afakallahu waƙar da Bashir Ɗandago ya fitar ya sake ta ba bisa ƙa'ida ba. Sannan ya yi amfani da kalaman tunzuri da ɓatanci ga wasu daga cikin malaman jihar Kano, wanda ya ce yin hakan ya ci karo da dokokin hukumar tace fina-finan jihar. Afakallahu ya ƙara da cewa: ""Bayan rashin kawo wa a tace ma, waƙar ta fito da wani salo na cin mutunci da cin zarafi da kuma neman kawo tayar da hankalin al'umma ko tarzoma. ""Saboda duk mutumin da ya ji wannan waƙa zai san cewa abin bai yi kama da tarbiyya da mutunci da yanayin zamantakewa da aka san Malam Bahaushe da su ba, ta wajen kyautata tarbiyya da kuma kiyaye mutuntakar juna. ""Bashir ya yi waƙa bai kawo hukuma ta tace ba kuma waƙar nan tana ɗauke da kausasan maganganun da za su iya kawo tunzuri cikin al'umma. ""Dole hukuma ta taka burki ta ɗauki mataki kan cin mutuncin mutane da zagin shugabanni, ai malamai shugabanni ne, akwai shugabannin da suka wuce malamai? Ai babu. ""Saboda su ne al'ummar da suke janyo mutane su nuna su zuwa ga Allah kuma su nuna musu abubuwan da suka kamata,"" a cewar Afakallahu. Duk da cewa a waƙar ta Bashir Dandago bai ambaci sunan ko mutum guda ba, ya yi ta kamar zaurance ne, Afakallahu ya ce babban laifinsa shi ne ƙin neman izinin yin waƙar tun da farko. ""Ƙa'ida ta farko ita ce idan ka yi waƙa ka kawo a tace, babbar ƙa'idar da ya fara karyawa kafin a shiga ma batun mene ne a cikin wakar shi ne rashin neman a sahale masa ya je ya yi waƙar. ""Wannan shi ne babban abu mafi muhimmanci da al'umma ya kamata ta fara fahimta. ""Kuma shi yana cikin waɗanda suka zauna suka tantance sha'iran da ke cikin wannan kwamiti a matsayinsa na wanda ake koyi da shi Bashir Dandago dai na ɗaya daga cikin manyan masu yabon Mazon Allah SAW a Kano, kuma ɗaya daga cikin magoya bayan Abduljabbar Kabara, wanda kuma ya saki waƙar da ake tuhumarsa da yin kalaman tunzuri da gugar zana ga wasu malamai, tare da sakinta ba bisa ƙa'ida ba. Haka zalika lamarin na zuwa ne a dai dai lokacin da wani lauya mai zaman kansa Ma'aruf Yakasai ya janye daga bukatar da ya shigar gaban kotu ta hana gwamnatin Kano, yin muƙabala da Abdulajbar Nasir Kabara. Batun muƙabalar ya ja hankulan al'umma a ciki da wajen jihar Kano, har ta kai ga wasu mutane ke nuna rashin jin dadinsu lokacin da aka dakatar da muƙabalar. Wanda hakan ya janyo musayar kalamai tsakanin magoya bayan malaman Kano da ɓangaren Abduljabbar kan batun dakatar da muƙabalar." https://www.bbc.com/hausa/labarai-56503891 +health Coronavirus: WHO ta yabi Saudiyya saboda hana zuwa Umra Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yaba wa Saudiyya saboda hana zuwa Umra kasar domin dakile yaduwar cutar COVID-19, wato coronavirus. Ofishin WHO na Gabashin Mediterranean ya ce matakin zai hana taruwar mutane da kuma yiwuwar yaduwar cutar a lokacin Umra ko ziyara. ''Hana shigowar miliyoyin maniyyata Umra da masu ziyara daga kasashe zai saukaka wa Saudiyya aikin hana shigar cutar da yaduwarta a kasar,'' a cewar hukumar. Gwamnatin Saudiyya ta hana shiga kasarta domin yin Umra ko ziyara ko yawon bude ido saboda cutar da ta kashe dubban mutane a duniya. Ma'aikatar Harkokin Wajen Saudiyya ta ce kasar na lura da yanayin da duniya ke ciki game da coronavirus tare da daukan matakan hana shigarta kasar ko yaduwarta. Baya ga mace-mace, annobar COVID-19 ta kwantar da dubban mutane tare da tilasta killace wasu garuruwa da makarantu da tarukan al'umma a wasu kasashe. Sauran matakan da kasashe suka dauka na hana yaduwar COVID-19 sun hada da killace wadanda suka shigo daga kasashen da aka samu bullar cutar na tsawon kwana 14. COVID-19 a kasashe WHO ta ce barkewar cutar na karuwa, inda ta gargadi kasashen duniya su kasance cikin shirin ko ta kwana kan barkewar cutar, da ta yadu zuwa kasashe fiye da 50. Hukumar ta nuna matukar damuwa game da yaduwar cutar a Iran, inda mataimakiyar shugaban kasar da wasu manyan jami'an gwamnati suka kamu da cutar. Za a tura wata tawaga a makon gobe, yayin da hukumomin Iran ke shirin rufe makarantu na tsawon kwana uku a kasar. Jamus da Switzerland su ne kasashe na baya-bayan nan da suka bayyana karin daukar matakai na dakile yaduwar cutar. Amma har yanzu Korea ta Kudu ce ta fi yawan masu kamuwa da cutar kowace rana. Najeriya da Mexico sun bayyana bullar cutar a kasashen su. Bullar coronavirus a Najeriya shi ne karon farko da aka tabbatar da bullarta a yankin Yamma da Saharar Afrika. Ministan lafiya na Najeriya Osagie Ehanire ya ce ba a gano cutar ta farko a kasar ba a lokacin da mutumin da ya kai ta kasar ya sauka a filin jirgin sama a Legas. Hukumomi sun ce babu alamun rashin lafiya a tare da mutumin dan kasar Italiya a lokacin da ya isa Najeriya. Mista Ehanire ya ce za a tuntubi duk mutanen da ke cikin jirgin da mutumin ya hau tare da sanya ido sosai a kan su. 'Mun fara aikin gano duk mutanen da mutumin ya yi mu'amala da su tun daga lokacin da ya shigo Najeriya har ma da wadanda suka shigo kasar tare,'' a cewar ministan. https://www.bbc.com/hausa/51678103 +religion Tarihin Timbuktu: Dadaddun takardun Musulunci na Mali da aka wallafa a intanet "An kaddamar da wani kudin nuna zane-zane don baje-kolin tarihin al'adun gargajiya na kasar Mali, wanda ke nuna dubban kasidu na dadadden tarihi. An yi fasa-kwaurin takardun don tserar da su daga birnin Timbuktu, bayan da kungiyar masu tsattauran addinin Islama ta karbe ikon arewacin Mali a shekarar 2021. Sun kunshi ilimin Afrika na karni da dama da kuma darussa da malanta kan batutuwa kama daga lissafi zuwa zane-zanen hatiman ilimin bokanci. ""Mafi matukar muhimmancin abu ga al'adun gargajiyar kasar Mali, suna nuna babban abin tarihi na sani a rubuce da kuma ingantaccen ilimi a Afirka,'' in ji Dakta Abdel Kader Haidara, wani mai kula da dakunan karatu da ajiyar litattafai da aka bayyana ya yi fasa-kwaurin rubutattun takardun zuwa wajen birnin Timbuktu, wanda kuma yana cikin wadanda suka gudanar da aikin. Tarin takardun, da ake kira 'Mali Magic', sun kuma fito da al'adun gargajiya na kasar Mali da ya wuce batun rubutattun takardun. Kamfanin nan mamallakin shafin intanet din matambayi ba ya bata wato Google ne ya hada su wuri guda, tare da hadin guiwar abokan hudda na cikin gida da kasashen waje. Ya kunshi hoton rawar al'adun gargajiya ta kungiyar kabilun Dogon. Ya kuma nuna fasahar zane, kamar na Abdoulaye Konaté da ya samu lambar yabo, da wasu hotunan magina suna yi wa Babban Masallacin Djenné yabe. Masallacin dai wani wurin tarihi da hukumar kula da layan tarihi ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO mai nisan kilomita 500 (mil 310) daga kudancin birnin Timbuktu. Asalin dadaddun takardun an rubuta su ne da harshen Larabci na tsakiyar zamani, amma yanzu an fassara su zuwa harsunan Turanci, da Faransanci, da Spaniyanci da kuma Larabcin zamani, don mutane da dama su iya karantawa, abinda Manajan Tsare-tsare da ilimin kimiyya tarihi na kamfanin Google Coughenour ya shaida wa BBC shi ne ab una farko. ""Tattara bayanai a rubuce ta hanyar fasahar zamani da kuma kwafin rubutattun kasidun na da matukar muhimmanci, kana a karon farko muna fito da sakamakon ayyukan da muka yi ta fafutikar yi na tsawon shekaru,'' ya ce. A cikin karni da dama, birnin Timbuktu ya kasance wata babbar cibiyar kayan tarihi a nahiyra Afirka, har ma da kasancewa cibiyar ilimin addinin Islama. Masallatan birnin sun taka muhimmiyar rawa wajen yada addinin Musulunci a fadin yankin Afirka ta Yamma a cikin karni na 15 da na 16, kamar yadda hukumar UNESCO ta bayyana. Cikin shekaru bakwai da suka gabata shugabannin gargajiya na kasar Mali, da masana tarihi, da kuma masu bincike kan kayan tarihi na zamani sun yi da aiki tukuru wajen tabbatar da ganin cewa dadaddun kasidun, da wasu tun a cikin karni na 11 aka rubuta su, kunshe da ingantattun tarihin kasar sun alkinta su ta hanyar tattara su wuri guda a zamanace. Aikin ya bai wa mutane damar da za su yi koyi da wadanda suka gabace su, in ji Dakta Haidara (hoto na kasa). Mayar da wadannan rubutattun kasidu zuwa cikin kundin fasahar zamani ya samo asali ne daga yin kira da kamfanin Google da Dakta Haidara ya yi a shekarar 2014. Ya gayyaci kamfanin ne ya ziyarci kasar Mali don ya ga mashahuran kasidun birnin Timbuktu kana ya san dalilan da suka sa suke cikin hadari ko kuma barazana. Lokacin da suka isa birnin, sun gano rubuce-rubuce da suka hada da littattafan Alkur'ani mai girma na farko da kuma wasu batutuwa daban-daban da suka hada da na ilimin taurari, da lissafi da kuma ilimin kimiyyar kasa. Daga nan ne tawagar ta kudirin gudanar da aiki ba kawai na duba daruruwan shafukan don mayar da su cikin kundin fasahar zamani kadai ba ne, amma har da saka hotunan a shafin intanet. Yanzu za a iya samun shafuka 40,000 a shafin yanar gizo, da ke kunshe da batutuwa da dama da suka hada da kimiyyar ilimin halittu da wakoki. Aiki ne da 'yan kasar Mali suka shafe shekaru da dama suna sa ido a kai, tun bayan da mayaka masu kaifin kishin Islama suka bank awa dakunan ajiyar litattafai wuta a birnin Timbuktu a yayin da suke kokarin kone takardu masu daraja. A cikin watanni shida aka yi fasa-kwaurin tarin rubutattun kasidun daga cikin Timbuktu zuwa Bamako babban birnin kasar Mali, saboda lokaci na kurewa na kokarin cetowa tare da adana takardun daya lalatarwa. A shekarar 2016 Kotun Hukunta masu Aikata Manyan Laifuka ta Kasa da Kasa ICC ta yanke wa wani ake zargi dan kungiyar masu tsattsauran addinin Islama ne, Ahmad Al Faqi Al Mahdi, da aikata laifin bayar da umarnin kai hare-hare a kan gine-ginen addini da na tarihi a Timbuktu hukuncin daurin shekaru tara a gidan yari tare da neman gafara. Shi ne karon farko da kotun ta ICC da ke birnin Hague ta yanke hukunci kan lalata wuraren tarihi. Amma kuma, wannan aiki na alkinta muhimman kasidun kasar Mali ba shi ne yunkuri a karon farko ba. A shekarar 2003 n3 Jami'ar Cape Town ta kaddamar da aikin alakinta takardun Tombouctou, tare da jaddada ""al'adun rubutattun kasidu a fadin nahiyar Afirka"", kamar yadda shafin yanar gizon ya nuna. Har ila yau, dakin ajiyar litattafai na Amurka US Library of Congress ya saka wasu daga cikin wadannan takardu a shafin intanet. Dukkan hotunan na da hakkin mallaka." https://www.bbc.com/hausa/labarai-60706634 +sports Banyana-Banyana ta doke Falcons a gasar kofin Afirka ta mata Tawagar kwallon kafa ta mata ta Afirka ta Kudu ta yi nasara a kan ta Najeriya da ci 2-1 a wasan farko a rukuni na uku a gasar cin kofin Afirka a Morocco. Banyana-Banyana ta ci kwallayen ta hannun Jermaine Seoposenwe da kuma Hildah Tholakele Magaia. Najeriya ta zare kwallo daya daf da za a tashi daga karawar ta hannun Rasheedat Ajibade. Super Falcons mai kofi uku a jere 11 jumulla a gasar kofin Afirka, za ta yi wasa na biyu a rukuni na uku da Bostwana ranar 7 ga watan Yuni. A kuma ranar Banyana-Banyana za ta kece raini da Burundi. A cikin watan Satumba tawagar Afirka ta Kudu ta doke Super Falcons da ci 4-2 a gasar Aisha Buhari Cup ta kuma lashe kofin a Najeriya. Ranar Talata Rukunin farko zai yi wasa na biyu, inda mai masaukin baki Morocco za ta fafata da Uganda, yayin da Senegal za ta yi gumurzu da Burkina Faso. Morocco tana da maki uku, bayan cin Burkina Faso 1-0 ranar Asabar, ita kuwa Senegal ta doke Uganda 2-0 ranar Lahadi. https://www.bbc.com/hausa/articles/cv2rjg8l4ndo +technology Sabon salon hana satar amsa a Indiya ya kawo rudani Wani jami'in wata makaranta a Indiya ya bayar da hakuri, bayan da wasu hotuna na wasu dalibai da suka rufe kawunansu da kwallaye yayin jarabawa ya rinka yawo a shafukan sada zumunta. An dauki hoton ne a lokacin wata jarabawa a wata makarantar sharar fagen shiga jami'a ta Haveri da ke jihar Karnataka a Indiya. Hotunan sun nuna daliban makarantar zaune a cikin aji da kwalaye bisa kawunansu, an huda kwalayen ta yadda za su samu iska. An bayyana cewa an yi hakane domin hana daliban satar amsa. Daya daga cikin malaman makaranatar ya fito ya roki gafara bayan afkuwar lamarin. Ya ce makarantar ta yi amfani da wannan sabon tsarin ne sakamakon ta ji labarin tsarin ya yi amfani matuka a wata makarantar. Ya kuma bayyana cewa an yi hakan ne da yardar daliban, kuma wasu daliban ma daga gidajensu suka zo da kwalayensu. Ya ce ''ba a tilasta wa kowane dalibi da cewa dole sa ya saka kwali a kai ba, idan za ku iya gani akwai wadanda babu kwalin a kansu .'' Ya ce ''wasu sun cire kwalayen bayan mintuna 15 wasu kuma bayan mintuna 20, bayan sa'a daya mu da kanmu muka ce kowa ya cire kwalin.'' Rahotanni sun bayyana cewa jami'ai a yankin sun garzaya makarantar bayan sun samu labarin wannan sabon tsarin da makarantar ta bullo da shi. SC Peerjade wanda jami'i ne a kasar ya bayyana wannan sabon tsarin da makarantar ta yi gwaji a matsayin ''rashin imani.'' https://www.bbc.com/hausa/50117438 +entertainment Hotunan Afirka na mako 13-19 Agustan 2021: Masu shigar Ninja, wutar daji da ganguna Wasu zaɓaɓɓun hotuna daga sassan Afirka na wasu abubuwan da suka faru a nahiyar a wancan makon, ku kuma na ƴan nahiyar a wasu sassan duniya. Duka hotunan na da haƙƙin mallaka. https://www.bbc.com/hausa/labarai-58283945 +religion Ku San Malamanku tare da Sheikh Abduljabbar Kabara Ku latsa hoton da ke sama don kallon hirar BBC da Sheikh Abduljabbar a shirin Ku San Malamanku, sanna kuna iya shiga shafinmu na Youtube don kallon cikakken bidiyon: Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan da yake jihar Kano a arewacin Najeriya, kuma shugaban Ƙadiriyya Riyadul Jannah, Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya ce babban abin da ya sa a gaba yanzu a rayuwarsa shi ne nazari kan Hadisan Manzon Allah SAW. Malamin ya fadi hakan ne a wata hira ta musamman da BBC Hausa ke yi a wani shirinta na Ku San Malamanku. ''Babbar hidimar da a yanzu na taƙaita a kanta ita ce Hadisan Ma'aiki Alaihis Salatu Wassalam da bibiyar sawunsu da tantance da bin diddigin sahihan hadisan daga waɗanda suke jabu a cikin hadisin,'' in ji shi. Malamin wanda ya fito daga gidan malanta ya ce buɗar ido ya yi ya gan shi a cikin karatu. Sheikh Abduljabbar ɗa ne ga marigayi Sheikh Nasiru Kabara, toshon shugaban ɗarikar Ƙadiriyya na Afirka, mahaifiyarsa kuma sunanta Hajiya Hafsah Adussamad. Shehin malamain ya tashi a Unguwar Kabara da ke cikin ƙwaryar birnin Kano, sannan ya yi makarantar zamani ta Ma'ahad kamar yadda dukkan iyalan Gidan Ƙadiriyya ke yi. Daga nan ya tafi makarantar Aliya da Makarantar Horar da Malamai ta ATC da ke Gwale, sannan kuma ya je har ƙasar Iraƙi ya yi karatu. Sai dai malamin ya ce mafi yawan karatuttukan da ya yi duk a gida ya yi su a gaban mahaifinsa, ''a cikin shekara 25 ɗin da na yi tare da mahifina na karatu, fannoni kaɗan ne ban taɓa ba.'' Babu wani abu na rayuwa da ke zuwa ba tare da matsaloli ba, musamman a gwagwarmayar karatu da da'awah daga fannin malamai, Sheikh ya ce a nasa ɓangaren abin na da yawa, sai dai kawai wata matsalar ta kan zarce wata. ''Amma wanda ya fi tsaya min a rai shi ne halin da na samu kaina a ciki daga waɗanda su ya kamata a ce na fi samun ɗauki a wajensu wato ƴan uwana ƴan ɗarika, musamman Shehunnai da Malaman Ɗariƙar Tijjaniyya da suka ga kyan mu haɗu mu gina hankar Allah da su, suka kuma kawo min ziyara a cikin wannan waje ta zumunci da ƙauna. ''Na karɓe su hannu bibbiyu kuma muka taru da su muka gina tafiya irin ta da'awah amma a ƙarshe ƙalubalen da na fuskanta daga abin wanda har zuwa yau ban san mene ne sababin da har gobe ya jawo wannan juya baya ba, ta yadda al'amarin ya juye ya zama farmaki.'' Malam Abduljabbar ya rubuta littattafai da dama amma ya ce babba daga cikinsu shi ne ''Muƙaddamatul azifa'' mai shafi 705. Ya ce littafan nasa na Sunnah sun fi na kowace mazahaba yawa. Sheikh Abduljabbar na da littafai kimanin 20,000 a ɗakin karatunsa, wanda a mafi yawan lokuta ya kan yi ikirrain cewa zai bayar da su gaba ɗaya idan malamai sun ba shi amsar wata tambaya da ya yi musu, al'amarin da wasu ke ganin tamkar fariya ce. Sai dai shehin ya ce sam babu fariya a lamarin, ''ƙoƙari ne na jawo hankalin malamai su gane wata masalaha ta gaskiya, musamman irin yadda wasu ke kawo ruɗani da gangan. Idan ba haka ba shi ɗan kallo ba zai fahimci waye yake faɗa masa gaskiya ba.'' Rai dangin goro in ji masu magana, shi ya sa muka tambayi malam irin abincin da ya fi so, inda ya ce ya fi son tuwon dawa da miyar kuka, amma matarsa ce kawai ta fi sanin irin yadda yake so miyar kukar ta kasance. A dangin nama kuwa, malam ya ce na rago ne wanda ya fi so. Dangane da tafiye-tafiye kuwa Malam ya ce a da e ya yi sha'awar wannan amma a yanzu hidimar rubuce-rubucensa ta sa ba ya muradin hakan. Amma duk da haka ya je ƙasashe da dama musamman a yankin Gabas Ta Tsakiya da suka haɗa da Saudiyya da Iraƙi da UAE da Syria da Iran. Sanna ya leƙa wasu ƙasashen Turai kamar su Rasha. Wasu da dama na kallon malamin a matsayin mai bin mazahbar Shi'a, sai dai ya ce tuni ya daina musanta cewa shi ba ɗan shi'a ba ne. Ya ce bai ga dalilin da zai sa a dinga tsorata shi da cewa Shi'a ba aba ce mai kyau ba, inda ya ce a da idan aka tambaye shi yana cewa shi ba ɗan shi'a ba ne, ''amma a yanzu bayan da na yi bincike mai zurfi sai na gane ashe Shi'ar ma ta fi Sunnar hujjoji, sai na ga ba wani dalilin da za a dinga tsorata ni da wannan.'' ''Duk wanda ya tambaye ni ko ni ɗan shi'a ne, sai na ce masa mece ce Shi'a a gurinka? Duk amsar da ya ba ni ita ce za ta biyo bayan amsar da zan ba shi. ''Idan ya ce zagin Sahabbai zan ce masa a ina na zage su har ka nasabta ni da shi'a? Sai ka ga babu amsa. Ni dai make-maken nan ne ba zan yi ba don ni ina bayan duk abin da Annabi ya yi umarni ne kawai. ''Kuma a cikin kashi 100 bisa 100 to Shi'a ta fi Sunna gaskiya da kashi 75 a cikin rigingimun da ake da su,'' a cewar malamin. https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-54830916 +entertainment Ana tunawa da ayyukan marigayi mawaki Ibrahim Narambada "Cibiyar Nazarin Harsunan Najeriya ta Jami'ar Bayero da ke Kano a Najeriya ta shirya wani babban taro don girmama shahararren mawakin Hausa marigayi Ibrahim Narambada, a kan gudunmuwar da ya bayar a fagen waka. A ranar Litinin ne Narambada ke cika shekara 56 da rasuwa, kuma a ranar ake fara taron wanda za a shafe kwana biyu ana yi. Ana ganin Narambada a matsayin wanda ya zarce takwarorinsa mawaka a zamaninsa a wakokin fada ko sarakai. Duk da tsawon lokacin da aka dauka da rasuwar mawakin, har yanzu masoya wakokinsa na a ci gaba da kewarsa, kan haka ne Cibiyar koyar da harsunan Najeriya dake Jami'ar Bayero ta shirya wani taro kan mawakin. A lokacin da yake raye mawakin ya cika baki a cikin wata wakarsa cewa, ba zai taba mutuwa ba, kuma ko da ya mutun ma, to zai dawo ya ci gaba da rayuwa. Sai dai masu fashin baki sun fassara hakan da cewa zai ci gaba da rayuwa na nufin za a ci gaba da sauraron wakokinsa. Shi dai shahararren mawakiwanda aka fi sani da Narambada sunansa na yanka Ibrahim, kuma sunan mahaifinsa Maidangwale. An haife shi a shekarar 1890 kuma ya rasu a shekarar 1963 yana da shekaru 73 a duniya. Mahaifinsa, Maidangwale dan asalin Jamhuriyar Nijar ne, a kasar Filinge amma ya zo garin Tubali ya zauna kuma a nan ya auri mahaifiyar Narambada. Maidangwale dai shahararren dan dambe ne. An haifi Narambada a garin Tubali kuma a nan ya yi karatu, ya yi rayuwarsa duka. Mahaifiyar Narambada kuwa makidiya ce, don haka a iya cewa ya yi gadon kida ne daga wurinta. Ya samu sunan Narambada ne dalilin wata karyarsa da ake ce wa Rambada, don haka sai aka yi masa lakabi da Narambada. Tarihi ya nuna cewa Narambada ya budi ido ne ya ga kayan kidan kotso a dakin mahaifiyarsa, wanda ita ma na mahaifinta ne ta yi gado. Narambada ya fara ne da kidan noma. Wata rana sai ya yi kidan noman kauyensu a fadar Sarkin Gobir na garin Isa. Da aka ji dadin wakar da kuma yadda yake da kwarewa da hikima, sai aka ka mayar da shi birni ya zamo makadin Gobir. Don haka ya ci gaba da yi wa Amadu Sarkin Gobir waka. Narambada ya yi wakoki da dama a rayuwarsa kamar su ""Ya ci maza ya kwan yana shiri, uban zakara, dodo na Ummaru"" da ""Batun da akai na yau babu Sarki yau irin ka,/ Jikan Bello arna suna shakkak ka"" da ""Alkalin Alkalai ta aiki nai da tsari"" da ""Masu gari mazan gabas tsayayye, Sarkin Rwahi ya wuce a ram mai"" da dai sauransu. Farfesa Aliyu Bunza na jami'ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato ya ce ""a ganina dukkanin kasar Zamfara ba a yi mawakin da ya kai Narambada ba. Kuma ba a kasarsa kawai yake waka ba. Ma'ana, duk duniyar kasar Hausa."" Yawancin wakokinsa ya yi amfani da kalamai na hikima da zalaka, wanda ya sa wakokinsa suka fita daban da na sauran mawakan Hausa. Misali a wakarda ya yi wa Sarkin Gobir, ya yi amfani da salo na hikima da fasaha inda yake cewa: ""Na aje karya ko ina kidi, Na bar karya ko ina kidi, Nai sittin, saba'in ni ka hwata, Mai saba'in yai karya ana ta zunde nai, Ko yaran da ag garai du wawwatse mashi su kai, Ya na yawo shi dai baram-baram."" Farfesa Bunza ya ce ""Wasu su kan ce ya yi wakoki sun kai dari ko dari da wani abu amma iyakar binciken da mu ka yi, kusan sama da shekaru ashirin da wani abu gaskiya ni hamsin na samu, wadanda na rubuta da kai na, na saurara, na tabbatar sun rubutu, na ajiye."" Farfesa Bunza ya ce ko wane irin mawaki da irin fasaha da hikima da zalaka da Allah ya hore masa. ""Allah ya hore masa waka, amma shi Narambada ba a nan take yake yin ta ba. Idan zai yi maka waka, zai je gida ya tsara ta, a yinin da zai yi wakar, ba zai yi hulda da kowa ba. ""Haka wasu yaransa suka shaida mana. In ya kare tsara ta, sai ya kira yaransa, sai su rera. Wakar Narambada in zai yi ta, zuba waka ake zube-ban-kwarya,"" in ji Farfesa Bunza. Wato dai Narambada ba ya rubuta waka sai dai ya tsara ta a zuciyarsa. Idan ya gama tsarawa sai ya gaya wa yaransa ya ce shaida masu amshin wakar su yi ta maimaitawa har ya zauna masu, sannan a je a rera ta. Akwai wakar Narambada da ya yi ikirarin cewa ba zai mutu ba. Ya ce: ""Narambada ba ya zuwa lahira, ko ya je dawowa ya kai, Hwadawa ku bugan in buge ku, Mui ta fadan mu gidan duniya, Kun san ba a hwada lahira, Kun san kuka zuwa lahira, Narambada ba ya zuwa lahira, Ko ya je dawowa ya kai, Gama kun san dauke mai akai."" Masana sun fassara wadannan kalamai na Narambada a matsayin cewa dalilin wakokinsa ba zai ""mutu"" ba tunda har yanzu tsawon shekaru bayan rasuwarsa ana sauraren wakokinsa. Farfesa Bunza ya ce ""maganarsa ta tabbata. Fadawa ke mutuwa- da Bafade ya mutu, a fada an manta da shi. Da Sarki ya mutu, a fada an manta da shi, an yi wani. Amma idan zakaran mawaka ya mutu, ba mutuwa ya yi ba. ""Har yanzu ga Narambada ba shi duniya, ana maganarsa, ana jin maganarsa. Ina fadawa suke? Saboda haka duk wani mawaki da ya san kan sa, ya yi luguden wakar, to bai mutu ba, yana nan a raye!"" Ana iya cewa wannan na daga cikin irin hikima da basira da iya salon magana da Allah Ya bai wa Alhaji Ibrahim Narambada." https://www.bbc.com/hausa/labarai-49715938 +sports Robert Lewandowski na matsa kaimin zai bar Bayern Munich a bana Dan kwallon tawagar Poland, Robert Lewandowski na kara sa matsi cewar zai bar Bayern Munich a bana. Dan wasan wanda ya ci kwallo 344 a fafatawa 374 a dukkan karawar da ya yi wa kungiyar da ke buga Bundesliga ya fayyace yadda ya ke son barin Bayern a bana. ''Labari na a Bayern Munich ya zo karshe. Bani da wata dama ta ci gaba da buga wa kungiyar tamaula ko kadan,'' kamar yadda ya sanar a ganawa da 'yan jarida a tawagar Poland. Kalaman da Lewandowski ya yi sun yi tsauri, bayan kaka sama da 10 da ya yi a Bayern, domin sun zama daya ganin yadda suka dade tare, sai dai wasu na ganin ya yi haka ne domin wakilinsa, Pini Zahavi ya matsa lamba ga kungiyar. A baya Bayern Munich ta sha fadin cewar Lewandowski bana sayarwa ba ne, wanda kwantiraginsa zai kare a karshen kakar 2023. Dan kwallon wanda zai cika shekara 34 da haihuwa cikin watan Agusta na fatan rattaba hannu kan yarjejeniyar kaka daya, amma a kungiyar Barcelona, wadda ake gani can zai koma da taka leda. An ce ya cimma yarjejeniyar baka da kungiyar Camp Nou kan kwantiragin kaka uku - sai dai kuma cinikin ka iya cin karo da cikas, bayan da Barcelona ba ta farfado daga matsin tattalin arziki ba, da kyar idan za ta iya biyan fam miliyan 34. Barcelona tana karkashin kulawar mahukuntan La Liga kan yadda take kashe kudi ya zamana kan ka'ida da cewar za ta iya biyan albashin wadanda ke tare da ita. Barcelona za ta iya daukar dan kwallon Poland, idan ta sayar da wasu 'yan wasa ko rage albashin wasu da ke karba da tsoka domin cika dokar mahukuntan gasar La Liga. Abin tambaya ko Bayern Munich ta shirya tunkarar kakar badi ba tare da Lewandowski ba? ko kuma daga baya za su sasanta a tsakaninsu?. https://www.bbc.com/hausa/wasanni-61673138 +politics Dangantakar Sarauniya Elizabeth da Firai Ministocinta "Matsayin Sarauta a kundin tsarin mulkin dimokuradiyyar zamani an kwatanta shi da babban aikin daidaito Daga ikirarin Firai ministocin da ta yi aiki da su, ta bayyana karara Elizabeth II, baya ga cewa tana girmama takaitacciyar kimar da aka ba ta, ta samu ci gaba da bayar da gagarumar gudunmuwa a harkokin gwamnatin kasar nan. A karkashin tsarin kundin mulkin Birtaniya da ba rubutattace ba ne ba, Basarake/Basarakiya (Sarki ko Sarauniya) na da hakkin a sanara da shi/ita komai ake ciki (na harkokin mulkin kasa), don bayar da shawara da yin gargadi. A daukacin zamanin mulkinta, Sarauniya ta jajirce kan lallai a ba ta bayanin komai da komai game da duk wata matsayar harkokin mulki da gwamnatinta ta cimmawa, ita kuwa ba ta wani bata lokacin wajen bayar da shawarar da ra'ayinta a kebe, ga jerin Firayiministocin da suka yi aiki a zamaninta. Matashiyar Sarauniya ta yi kyakkyawar sa'ar yadda aka nuna maka dabarun mulki a farkon zamanin mulki, inda ta samu agajin hamshakin dan siya, Winston Churchill, wanda ya sake samun damar jan ragamar mulkin bayan da aka gudanar da babban zaben shekarar 1951. Wannan babban mutumin ya taba yin sharhi a kafar watsa labarai game da karfin ikon yarinyar Gimbiya al'amarin da ke da ""ban mamaki a same shi a karamin yaro/yarinya."" Duk da bambancin shekarun da ke tsakaninsu - Churchill ya yi yakin Boer (Karon-battar Birtaniya da sojojin Transvaal na Afirka ta Kudu) zamanin mulkin kakar mahaifin Sarauniya, wato Sarauniya Victoria - dangantakarsu dai akwai kauna da girmamawa. A jawabijn da ya gabatar nan take bayan darewar Elizabeth bisa karagar mulki, mya yi matukar daukar hankalin masu suararensa, inda ya furta cewa ""ya fito da managarcin tsarin tabbatar da cewa Sarauniya ba za ta aikata wani abu da ba daidai ba."" Hakikanin dangantakar aiki tsakanin Basarakiya (Sarauniya) da Firayiminista babu cikakkiyar fahimta, sai dai wasu 'yan siyasa, musamman Disraeli da Sarauniya Victoria an nuna kwarewa karara fiye da wasu wajen nuna kyakkyawar mu'amala irin ta dangantakar aiki.. Mashahurin jagoran Jam'iyyar Conservative din nan, sabanin abokin adawarsa Gladstone, ba shi da wata tababa kan yadda zai tarairayi al'amuran huldar aiki da mai sarauta. ""Kowa na son kambamawar yabo,"" Disraeli ya fada. ""Kuma idan ka je wajen harlkar sarauta sai ka bajeta karara a fili."" Abu guda mafi muhimmanci, shi ne, kowane Firai minista ya yarda da cewa Sarauniya jajirtacciya ce wajen aiki. Takan shafe kimanin sa'o'i uku a rana wajen bibiyar sakonnin takardun majalisa da sakonnin gwamnati da bayanan sassan harkokin mulki da nade-naden mukamai. Wasu da sauran al'amura akan bijiro da su ne lokacin da Firayiminista ya je Fada don suararen bayanan mako-mako. Wasu lokutan akan gabatar da suararen bayanan ne a wani wuri daban. Lokacin zamanta a Balmoral a karshen dogon hutun bazara, shi ne mafi muhimmancin isar da sako ga Firayiminista a shekara. A gaskiya, babu wnai tanadi a kundin tsarin mulki da ya bayar da damar irin wannan ganawar, kawai dai lamari ne da ya dnganci al'ada. Wasu lokutan tattaunawar wayar tarho kan maye gurbin ganawar keke-da-keke. Tashin farko, lamarin na nuni da cewa, kaifin basirar Sarauniya da kwarewarta a harkar siyasa lamura ne da ke burge mazaunan fadar Firayiministar kasa da ke Lamba 10 (titin Dawning). An yaba yadda take iya yin takun tarairayar kimar matsayin mukaminta bisa tanadin kundin tsarin mulki, baya ma ga a ce lokacin da aka wsamu rudanin siyasa a shekarar 1957, har ta kai ga Anthony eden ya yi murabus daga Firayiminista sanadiyyar rikicin mashigin ruwan Suez (a Masar - takun sakar yakin Larabawa da Isra'ila). A wancan lokacin Jam'iyyar Conservative ba ta da wani tsari na zaben sabon shugaba, ta yadda a kodayaushe ake dogaro da samun mutum nagari ""sakaka."" Bayan da Sarauniya ta tuntubi Churchill don neman shawara, sai ta bukaci Harold Macmillan ya kafa gwamnati, al'amarin da mamakinsa ya shammaci dimbin masu sharhi kan al'amura, wadanda suka sa ran ganin mataimakinsa na bayan fage ""Rab"" mai hidima, ya dare bisa mukamin. Ta fuskanci irin wannan matsalar shekaru kadan kawai sa'adda Macmillan ya yi murabus, bisa dalilin rashin lafiya. Duk da irin matsalolin da murabus din Eden ya haifar Jam'iyyar Conservative zuwa lokacin ba ta yi tanadin tsarin zaben shugaba ba. Bayan da ta tuntubi Macmillan a gadonsa na asibiti, inda yake jinya, sai ta sa aka kirawo Earl of Home (Dan majalisar manyan mutane a cikin al'umma da ke taro a fadar Sarauniya). Kasancewar ba a taba yin Firayiministan Birtaniya daga Majalisar manyan mutanen kasa (House of Lords) tun daga shekarar 1902, kuma ana ganin tsari da ba za a amince da shi ba. Don haka sai ya yi watsi da kimar matsayinsa, ya kuma samu nasara a zaben cike gurbi, inda daga bisani ya dawo a matsayin Sa Alec Douglas-Home. Ba a samu sauyi ba har zuwa shekarar 1965 sannan 'yan Jam'iyyar Conservative suka fito da tsarin zaben shugaba, ta yadda nan gaba ba za su sake jefa Sarauniya cikin matsala ba. A shekarar 1964 Harold Wilson ya kasance Firayiministan farko na jam'iyyar Labour da ya yi aiki da sarauniya, wanda ya sha caccakar sukar lamiri daga 'yan majalisarsa kan shirin kara yawan kudin da gwamnati ke bayarwa na tafiyar da aikace-aikacen ofishin Sarauniya. Sai dai kamar yadda Barbara Castle, daya daga manyan ministocin Mista Wilson ke iya tunawa, Firayiministan da Sarauniya sun hada karfi don kawar da kowace irin tashintashinar da ka iya tasowa. ""Harold na kaunar Saruniya,"" a cewarta. Kuma shi shugaba ne mai wayo, shi ya sa ma yake da fahimtar cewa tashintashina na iya bijirowa ta harzuka al'umma su soki Sarauniya."" Bayan tattaunawar Mista Wilson da Sarauniya kan yadda al'umma ta harzuka, sai ta amince da cewa za ta dauki nauyin wani yanki na kudin da za a kara a kashin kanta. Kasancewar an sake zuba wa kimar matsayin Sarauniya a kundin tsarin mulki ido bayan da masu hakar ma'adanai suka baro da Gwmanatin Edward Heath a shekarar 1974. Sai ya dan rike madafun ikon na wasu ''yan kwanaki, da zimmar ganin ya sake kafa wata sabuwar gwamnati Rahotanni daga fada sun yi nuni da cewa Sarauniya ba ta ji dadin wannan yanayin na rashin tabbas ba, kodayake Heath da kansa ya fayyace cewa babu wata tuntuba da aka yi masa. Dangantakar aiki da Firayiminista mace ta farko a Birtaniya, Margret Thatcher, ba kodayaushe lamari ya yi dadi ba, musamman kan takaddamar kungiyar kasashe rainon Birtaniya ta 'Commonwealth.' Thatcher kadai ce a cikin shugabannin kungiyar kasashen rainon Birtaniya dage wajen kin amincewa a kakaba wa Gwamnatin wariyar launin fata ta Afirka ta Kudu takunkumi bisa dalilin cewa ba zai yi tasiri ba, kuma illar lamarimn za ta cutar da mutane matalauta ne. A shekarar 1986 jaridar Sunday Times ta ruwaito cewa Sarauniya ta fahimci cewa halayyarta (Magret Thatcher) salo ne na hantarar karo da juna, lamarin da ke da ""daure kai."" A al'adance, matsayin Sarauniya shi ne na mai bayar da shawara ga Firayiminista. Amma a 'yan shekarun baya-bayan nan, kimar matsayin an kawar da shi. John Major ya samu kasansa a matsayin amintaccen mashawarci kan al'amuran da al''umma ba su san inda aka sa gaba ba, game da iyalan gidan Sarauta, kamar al'amuran da suka shafi rabuwar auren Yarima da Gimbiyar Walse. Amma ko da bayan lokacin yamutsin da Sarauniya ta shiga, tsohon shugaban jam'iyyar Conservative ya tauye mata damarta, wadda to kowace fuska an dakileta, sannan ya bayyana yadda yake daukar shawar Sarauniya da matukar kimar muhimmanci. Akwai lokacin da Sarauniya ta ji cewa al'umma sun fara ja-baya da ita. An zargeta da rashin yin katabus lokacin da kasar ke cikin alhinin rashin Diana, Gimbiyar Wales, a shekarar 1997, kodayake tana da tabbacin cewa, a matsayinta na kaka, aikinta shi ne ta kebe kanta don kwantar da hankalin kananan 'ya'yan Diana. A wannan yanayi, mutumin da ya fahimci yadda kafafen yada labarai ke juya akalar al'amura, Tony Blair, shi ne ya bayar da managarciyar shawara, kuma kai tsaye ya dauki hankalin al'umma da kalamansa game da ""Gimbiyar al'umma."" An kuma ruwaito cewa Blair ne ya kasance a gaba-gaba wajen shawo kan Sarauniya ta baro Balmoral ta koma Landan sanadiyyar tursasawar labaran 'yan jarida. A shekarar 2007 Gordon Brown ne ya gaji Blair, wanda ya sha kayi a shekarar 2010 al'amarin da ya jefa dimokuradiyyar Birtaniya cikin mawuyacin hali. Akwai hasashen rashin cimma matsayar majalisar dokokin kasa kafin a fara zabe, wato idan aka samu babu jam'iyyar da ke da rinjaye (me ya kamata ayi?). Tuni dai aka yi tsarin da ya kare Sarauniya daga afkawa rudanin siyasa. Sai dai ta bayyana karara cewa za a rika ba ta cikakkun bayanai lokacin da takaddamar ke gudana bayan kammala zabe a karshen mako. Bayan murabus din Brown ne kawai, sai Jam'iyyar Conservative ta yi hadin gwiwa da jam'iyyar Liberal Democrats, har ta kai ga an nemo David Cameron zuwa fada, inda aka bukaci ya kafa gwamnati. Ya ce ya fahimci fa'idar da ke tattare da tattauna matsaloli da wanda ke gefen tsarin siyasa ""da matukar muhimmanci."" ""Ba ni da tabbaci cewa kodayaushe akwai dimbin alfanu (fa'ida mai yawa), amma akwai fa'ida mai yawa a gareni,"" a cewarsa, ""Saboda na fahimci yana taimaka mana wajen tantance matsaloli da ke damfare cikin kaina kan abin da muke bukatar yi."" A babban zaben 2015, David Cameron ya samu kuri'u masu rinjaye, al'amarin da ya ba shi damar komawa gidan Gwamnati da ke titin Dawning a matsayin Firayiminista. Sai dai wa'adin mulkinsa takaitacce ne. Cikin Yunin shekarar 2016 al'ummar Birtaniya sun ki yarda da da shawararsa, inda suka zabi ficewa daga Tarayyar Turai (EU). Cameron ya sanar da murabus dinsa a matsayin Shugaban Jam'iyyar Conservative, bayan da aka kada kuri'un aka fara shirye-shgiryen zaben magajinsa, al'amarin da aka tsara aiwatarwa cikin watanni uku. Kodayake an yi watsi da tsarin cikin kankanen lokaci, bayan da aka fitar da 'yan takara biyu, wato Andreal Leadson, wanda ya fice daga takarar, ya bar Theresa May ta zama sabuwar shugaba. Ranar 13 ga Yulin 2016 ta je fadar Buckingham don Sarauniya ta bijiro mata da bukatar kafa sabuwar gwamnati. Ita ce Firayiminista mace ta biyu da ta yi aiki da Sarauniya, kuma ta 13 a jerin wadanda suka yi shugabancin kasar a zamaninta. Harold Wilson, wanda ya yi zango uku na wa'di mulki a fadar Gwmanati da ke lamba 10 na titin Dawning, ya taba cure bayanin fa'idar da ke tattare da dangantakar aiki tsakanin Firayiminista da Shugabar kasa (Sarauniya). ""Gaskiyar lamari ita ce akwai mutum daban a gefe da bai damfaru (da hada-hadar siyasa ba), wanda damuwarsa/ta kawai ita ce majalisar dokoki ta cimma matsaya daidai da bukatar mutanenta. Wannan shi ne abin da kawai babu a kasashen da ke kan tafarkin tsarin shugabannin kasashe."" ©Dukkan hotunan suna da hakkin mallaka" https://www.bbc.com/hausa/labarai-47244442 +business Najeriya za ta kulla yarjejeniya da Amurka kan kudin sata "Ministan Shari'ar Najeriya Abubakar Malami, yana halartar wani taron hadin gwiwa na kwana uku tsakanin Najeriya da Amurka a birnin Washington, inda zai rattaba hannu kan wata yarjejeniya game da kudin gwamnatin da aka sace a Najeriya. Bayanan na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun ministan, Dr. Umar Jibrilu Gwandu, ya fitar ranar Lahadi a Abuja. A madadin gwamnatin tarayyar Najeriya, ana sa ran ministan zai saka hannu kan wata yarjejeniya da yankin Island of New Jersey da kuma kasar Amurka kan kudaden sata da aka kai daga Najeriya. Sanarwar ta ce kudaden sun kai dala miliyan 321 (kusan naira biliyan 116) a yunkurin gwamnatin Najeriya na dawo da kudaden da aka sace zuwa lalitarta. Ya kara da cewa taron na shekara-shekara ne tsakanin Najeriya da Amurka da nufin karfafa alakar difilomasiyya a tsakaninsu. ""Ministan ya ce wannan taro na musamman ne, wanda ba zai tabo wasu batutuwa da suka shafi al'amuran cikin gidan kasashen,"" in ji sanarwar. Baya ga minsitan shari'ar, akwai sauran wakilai daga Najeriya da suka hada da ministan kasuwanci Otunba Adeniyi Adebayo da ministan tsaro Manjo Janar Bashir Magashi (mai ritaya). Sauran su ne Ministan harkokin wajen Najeriya Geoffrey Onyeama, da mai bai wa shugaba Buhari shawara kan harkar tsaro Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya), da kuma ministar ma'aikatar jin kai da bayar da agajin gaggawa Sadiya Umar Faruk." https://www.bbc.com/hausa/labarai-51349784 +business Ma'aikaci ya shekara 30 yana cin albashi tudu uku 'Yan sanda a jihar Bihar ta kasar Indiya na neman wani mutum ruwa a jallo da ake zargi da cin albashin ayyukan gwamnati daban-daban har uku na tsawon shekara 30. An dauki Suresh Ram a matsayin injiyan gine-gine da kuma karin ayyuka biyu a sashen albarkatun ruwa a lokaci guda a wurare mabambanta. Mahukunta sun ce Suresh har ma yana dab da yin ritaya daga ayyukan uku rigis. Sai dai babu tabbaci ko yana zuwa wajen ayyukan amma dai yakan samu karin matsayi. An dai gano wannan zambar ne jim kadan bayan kaddamar da wani shirin bai-daya a aikin gwamnati. https://www.bbc.com/hausa/labarai-49458990 +business NNPC ya samu ribar naira biliyan 674 Babban kamfanin mai na Najeriya NNPC ya bayyana samun gagarumar riba, da ya ce bai taba samun irinta ba a 'yan shekarun da suka gabata. Shugaban kamfanin, Mele Kolo Kyari, ya fada wa BBC cewa a bana sun samu ribar naira biliyan 674, bayan asarar da suka tabka a shekarun da suka gabata. ''Tafiya ta canza a wannan kamfanin. Daga asarar naira biliyan 803 a 2018, yau kamfanin nan ya ci ribar naira biliyan 674. Ka ga gagarumin canji ne kuma mai amfani ga kasa,'' in ji Mele Kyari. Mista Kyari ya ta'allaka nasarar da suka samu kan sabbin sauye-sauyen da suka aiwatar a kamfanin, da suka hada da inganta hulda da abokan kasuwanci, da kuma kara sanya ido kan yadda lamura ke gudana a kamfanin. Amma ya ce ya kamata a ce ribar ta zarta haka, ba don ba ta garin da ke fasa bututan man ba, da hakan ke janyo wa kasar asara makudan kudade. Sai dai ya ce sun hada karfi da jami'an tsaron kasar don ganin sun yi maganin masu satar man da barnata dukiyar al'umma. https://www.bbc.com/hausa/articles/crg27lx0v01o +politics Gwamnatin Zamfara ta gargadi masu neman tayar da zaune tsaye Gwamnan jihar Zamfara Bello Mohammed ya sanar da cewa gwamnatin jihar na da bayanan sirri da suka tabbatar ma ta cewa wasu 'yan siyasa na kokarin tayar da zaune tsaye tsakanin al'umomin jihar. Gwamnan ya kuma ce 'yan siyasan, wadanda ya kira marasa kishin kasa na yin yunkurin ne ta karkashin kasa domin cimma burinsu na siyasa kawai. Ya zarge su da hada kai da wasu 'yan kungiyar Boko Haram da aka fatattaka daga yankin Arewa maso gabas domin kai hare-hare kan mutanen da basu san hawa ba, basu san sauka ba. Kuma ya ce dalilinsu na daukan wannan matakin shi ne don su tarwatsa zaman lafiyar da ke wanzuwa cikin jihar da kuma lalata shirin sulhu da gwamnatin da yake jagoranta ta samar. Amma gwamnan bai bayyana sunayen 'yan siyasan da yake tuhuma da shirya wannan aika-aikar ba, kuma kawo yanzu, BBC ba ta da hanyar tabbatar da sahihancin sanarwar. Sanarwar da gwamnan ya fitar ta hannun Yusuf Idris Gusau, wanda shi ne mataimakinsa na musamman kan hulda da kafofin yada labarai, ta bayyana yadda aka shirya kai hare-hare cikin jihar. Sanarwar ta ce akwai shirin kai hare-hare cikin kananan hukumomi bakwai na jihar ta Zamfara, bayan wasu muhimman wurare a babban birnin jihar na Gusau. Cikin shirin da gwamnan ya ce sun bankado, akwai wani da aka kitsa domin hallaka wasu fitattu da sanannun 'yan asalin jihar. BBC ta ga sanarwar da gwamnan ya fitar, inda a ciki ya bayyana sunayen kananan hukumomin da ya ce a shiry akai hare-hare: Akwai Gusau, wanda shi ne babban birnin jihar, da Tsafe da Talata Mafara da kuma Anka. Sauran kananan hukumomin da ka ambato sun hada da Zurmi da Maru da kuma Maradun, kuma sanarwar ta ce an shiry akai hari kan babban masallacin Gusau da kasuwar Mammy Market. Sannan sanarwar ta ce 'yan kungiyar Boko Haram aka shirya za su kai wadannan hare-haren ne daga Litinin 23 ga watan Satumba zuwa 25 ga watan na Satumba, shekarar 2019. Gwamnan Bello Mohammed ya tabbatar wa al;umomin jihar cewa gwamnati za ta dauki dukkan matakan da suka dace domin kare rayuka da dukiyoyinsu. A wani labari mai alaka da wannan, gwamantin jihar Zamfara ta bayyana gamsuwarta da sakin wasu mutum 30 da a baya masu satar mutane domin karban kudin fansa ke tsare da su. Wadanda aka sakin sun hada da mata 15 da maza 15, wadanda dukkansu 'yan asalin karamar hukumar Kaura Namoda ne, kuma sun shafe wata takwas a hannun barayin gabanin sakin nasu da aka yi. https://www.bbc.com/hausa/49863014 +politics Mene ne ya hana gudanar da zabukan kananan hukumomi a jihar Sokoto? Sabuwar takaddamar siyasa ta kaure a jihar Sokoto dake arewacin Najeriya inda jam'iyyar hammayya ta APC ke kukan cewa gwamnatin jihar dake karkashin jagorancin jam'iyyar PDP ta ki gudanar zabukan kananan hukumomi da gangan. Kimanin shekaru uku ke nan da babu zababbun shuwagabanni a matakin Kananan hukumomi a jihar, kuma hakan rashin adalci ne, a cewar jam'iyyar APC. Shugaban rikon kwarya na jam'iyyar a jihar ta Sokoto, Honourable Isa Sadiq Achida, ya ce jama'a na ta kiraye-kirayen a gudanar da zabukan, amma hukumomin jihar sun yi biris da wadannan kiraye-kiraye cikin shekaru. 'Yan hamayya na ganin gwamnatin jihar ta Sokoto ba ta bin ka'idojin dimokuradiyya sau da kafa saboda rashin gudanar da zabukan. Shugaban APC Honourable Achida ya ce ''tun kusan shekara uku da suka wuce, ana ta rikon kwarya, rikon kwarya, babu zababbun shuwagabanni.'' To sai dai mai bai wa gwaman jihar shawara kan harkokin watsa labarai, Muhammad Bello, ya kare gwamnatin yana mai cewa gwamna Aminu Waziri Tambuwal ''mutum ne mai son bin tsari'' a matsayinsa na masanin shari'a. Ya shaida wa wakilin BBC AbdusSalam Ibrahim Ahmed cewa dalilin da ya sa ba a yi zabukan ba shi ne jihar ta fuskanci wasu matsaloli da suka kawo cikas. Ya kara da cewa gwamnan jihar bai taka doka ba, kan rashin gudanar da zabukan. ''An samu abubuwan da suka janye hankalin gwamnati daga kan abin da ya shafi gudanar da mulki kai tsaye a matakin jihohi da kananan hukumomi'' inji Muhammad Bello. Sai dai bai yi bayani dalla-dalla ba kan matsalolin da suka kau da hankalin gwamnatin jihar daga batun na zaben kananan hukumomi, amma ya ce yanzu gwanatin ta samu saukin matsalolin kuma za a mai da hankali kan batun gudanar da zabukan. Ko da ya ke ya kamata a ce hukumomin zabe na jihohi su kasance masu cin gashin kansu, mutane da dama sun yi imanin cewa gwamnonin jihohi na da babban tasiri wajen juya akalarsu, saboda yadda gwamnonin ke da iko wajen nada shuwagabannin hukumomin da kuma samar masu da kudaden gudanarwa. Jihar Sokoto na daya daga cikin jihohin Najeriya inda jam'iyyar hamayya ta kasar wato PDP ke mulki, kana jam'iyar APC mai mulki a matakin tarayya kuma ta ke matsayin babbar jam'iyyar hamayya a jihar. Yayin da ake wannan takaddama a jihar Sokoto, kuma ake ci gaba da jan kafa wajen gudanar da zabukan na kananan hukumomi, jam'iyyar APC ta ce bata yarda da take-taken gwamnatin jihar dake hannun jam'iyyar PDP ba. Ta yi zargin gwamnan jihar Aminu Waziri Tambuwal ne bai da niyar ganin an gudanar da zabukan, domin kawai ya samu damar ci gaba da nada kantomomi a matakin kananan hukumomin - kantomomin da sau da yawa ake masu kallon 'yan amshin shatan gwamna. Shugaban jam'iyyar hamayyar a jihar Sokoto ya ce ''Bisa gaskiya ba mu dauki da gaske gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal zai shirya wannan zaben ba.'' Honourble Isa Achida ya ce dalilinsu na nuna shaku kan aniyar hukumomin jihar kan gudanar da zabukan shi ne cewa tun bayan da aka kafa hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar wato SOSIEC, ''Ba mu ga wani abin a zo a gani wanda zai nuna lallai tabbas ana niyyar gudanar da zaben ba.'' To sai dai ya ce a shirye jam'iyyar ta APC ta ke ta shiga zabukan a duk lokacin da aka shirya gudanar da su. A martaninsa, kakakin gwamna Tambuwa ya ce babu batun yaudara a cikin lamarin zabukan na kananan hukumomi a jihar. Jihar Sokoto wadda ke daya daga cikin jihohin Najeriya 36, tana da yankunan kananan hukumomi 23. Ko da ya ke jam'iyyar hamayya ta APC ta ce ba da gaske gwamnatin jihar ta Sokoto da kuma Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta Jihar wato SOSIEC su ke ba a ikirin shirin gudanar da zabukan, a nasu bangaren hukumomi cewa su ke sun kuduri aniyar gudanar da zabukan da gaske. Kawo yanzu dai babu wani bayani daga hukumar zaben kan lokacin gudanar da zabukan. To amma kakakin gwaman jihar Muhammad Bello ya ce Majalisar Zattaswa ta jihar ta tattauna batun gudanar da zabukan, kuma tuni aka ba hukumar dama da hurumin tsarawa da kuma gudanar da zabukan. Ya kara da cewa za ta fitar da jadawalin zabukan nan da ba jimawa ba. Muhammad Bello ya shaida wa BBC cewa yanzu matsalolin da suka kawo cikas ga gudanar da zabukan sun kau, kuma ''yanzu lokaci ya yi da za a mai da hankali ga wannan al'amari, in In sha Allahu za a yi zaben.'' To sai dai jami'in gwamnatin bai bayyana takamaimai lokacin da ake sa ran gudanar da zabukan masu matukar muhimmanci ga talakawa ba. Ya ce ana jiran hukumar SOSIEC ta bayar da sanarwar jadawali da kuma ranar gudanar da zabukan. Wakilin BBC AbdusSalam Ibrahim Ahmed ya ce yanzu kallo ya koma ne ga yadda zata kaya a jihar ta Sokoto game da wannan takaddama kan rashin gudanar da zabukanan kananan hukumomi, da kuma yadda sakamakon zabukan zai kasance idan ma an yi su. Takaddama kan zabukan kananan hukumomi a Najeriya dai ba sabon abu ba ne. Ko baya ga jihar ta Sokoto yanzu haka akwai jihohi da dama a kasar inda ake fama da wannan matsala ta dimokuradiyya a matakin gwamnatin mafi kusa da talaka. Tun bayan komawar Najeriya tafarkin dimokuradiyya a 1999, aka mika ikon gudanar da zabukan kananan hukumomi ga hannun gwamnatocin jihohi, wadanda kan kafa hukumomin zabe a matakin jiha tare da zaben shuwagabanninsu. Haka nan, gwamnatocin jihohin ne kayyade wa'adin mulkin shuwagabannin kananan hukumomin da kansilolinsu, inda a wasu jihohin a kan ba su wa'adin mulki na shekara biyu sabanin wa'adin mulki na shekara hudu da su gwamnonin ke da shi bisa kundin tsarin mulkin kasar. Majalisun dokokin jihohi ne kan yi dokokin zabe na jihohinsu tare da tanadar yadda za a gudanar da zabukan da kuma wa'adin mulkin shuwagabannin. Wannan lamari ya sanya ba a samun yanayi na gudanar da zabukan kananan hukumomi bai-daya a fadin kasar. Hasali ma, a mafiya yawan lokuta rashin gudanar da zabukan kananan hukumomi ya zama tamkar al'ada ga gwamnatocin jihohi. A maimakon gudanar da zabuka, gwamnonin jihohin ne kan nada shuwagabannin kananan hukumomin a lokacin da suka ga dama, kana su sauke su a lokacin da suka ga dama. Shi kansa kakakin gwamnan jihar Sokoto, Muhammad Bello ya furta cewa lallai akan samu matsalar gudanar da zabukan kananan hukumomi a jihohin Najeriya ''daga lokaci zuwa lokaci.'' A halin d ake ciki a jihar Sokoto, har yanzu ba a biya shuwagabannin kananan hukumomi da kansiloli wadanda gwamna Aminu Tambuwal ya sauke daga mukamansu a baya-bayan nan, albashinsu na wasu watanni ba. Sai dai gwamnatin jihar na cewa za a biya su nan ba da dadewa ba. Haka nan ko da a jihohin da aka yi zabukan, galibi, jam'iyya mai mulkin jiha ita ce kan lashe dukkan kujerun shuwagabannin kananan hukumomi da kansiloli, lamarin da wasu masana dimokuradiyya ke cewa yana da wahala a iya samunsa a yanayin zabe na gaskiya da adalci. Wannan al'ada ce ga galibin gwamnonin jihohi daga duka jam'iyyun siyasa dake jihohin jihohin - ma'ana babu jam'iyyar da zata iya bugun kirji ta ce ita waliyya ce a wannan bangare. Masharhanta dai na ganin wannan yanayi yana tauye wa talakawa 'yancinsu na samun zababun shuwagabanni na dimokuradiya a kusa da su. Wasu dai na ganin gwamnonin ba su bari a yi zabukan kananan hukumomin yadda yakamata ne saboda su samu cikakken iko da kudaden shiga na kananan hukumomin musamman kason da ake ba su daga gwamnatin tarayya a duk wata. Wani dalilin kuma shi ne ba su so a samu wani shugaba na karamar hukuma da zai kalubalance su. Irin wannan kalubale ga gwamnoni zai iya faruwa musamman idan 'yan jam'iyyar adawa suka lashe zabukan, domin ba za su yarda gwamnatin jiha ta rika handame masu kasonsu na gwamnatin tarayya ba. Masana da talakwa da dama na ganin muddin dimokuradiyya ta yi karfi a matakin kananan hukumomi, to hakan zai iya ingantawa da kuma karfafa dimokuradiyya a sauran matakan gwamnati - wato matakin jiha da na tarayya, kuma talakawa ka iya samun abubuwan more rayuwa da kuma karin 'yanci. Dalili shi ne matakin kananan hukumomi shi ne mafi kusa da jama'a. https://www.bbc.com/hausa/labarai-55511853 +sports Chelsea ta hada maki uku a Goodison Park a wasan farko a Premier Everton ta yi rashin nasara da ci 1-0 a hannun Chelsea a wasan makon farko a gasar Premier League ta 2022/23 da suka fafata ranar Asabar. Chelsea ta samu bugun fenariti daf da hutu, bayan da Ben Abdoulaye Doucoure yayiwa Ben Chilwell keta a da'ira ta 18 ta Everton. Jorginho ne ya buga fenaritin, wanda ya kora golan Everton, Jordan Pickford gefe daya, sannan kwallon ta fada raga ta daya bangeren. Chelsea wadda ta yi ta uku a bara da cin wasa 21 da canjaras 11 aka doke ta karawa shida, ta hada maki uku kenan a gidan Everton a farkon Premier ta bana. Da wannan sakamakon Chelsea ta yi nasara karo na 20 a duk ranar fara babbar gasar tamula ta Ingia, Manchester City ce ke gabanta a wannan bajintar. Sabbin fitattun 'yan wasan da Chelsea ta dauka a bana duk sun buga mata wasan a Goodison Park da suka hada da Raheem Sterling da Kalidou Koulibaly da kuma Marc Cucurella. Everton karkashin Frank Lampard ta karkare a mataki na 16 a kasan teburin Premier da ta wuce, bayan cin wasa 11 da canjaras shida ta yi rashin nasara a wasa 21. Wannan ita ce kaka ta 69 a jere da Everton ke buga Premier League tun daga 1954/55 - Arsenal ce kan gaba mai 97. https://www.bbc.com/hausa/articles/c516l6np54lo +health An samar da hijabin dakin tiyata a Birtaniya Wani asibiti ya zamo na farko a Birtaniya da ya samar da hijabin da ake amfani da shi a dakin tiyata a kuma jefar idan an kammala amfani da shi, ga jami'an lafiyar da ke aiki a dakin fida. Daya daga cikin kananan likitoci kuma musulma Farah Roslan ce ta kirkire shi a lokacin da take aikin gwaji a asibitin Royal Derby na Birtaniya. Ta dauki matakin ne saboda tsoron daukar cuta da ka iya makalewa a jikin hijiabin da take yini da shi a jikinta. Tana fatan za a yi amfani da shi a sauran asibitoci, sai dai hukumar inshorar lafiya ta ce hakan zai zama bisa radin kan ma'aikata. Miss Roslan tana aiki ne a Lincolnshire, ta fara tunanin yin hijabin a lokacin da take daliba mai aiki da asibitin koyarwa na Derby. 'Ina amfani da hijabi ko dankwali guda daya tun safe har lokacin tashi daga aiki, wanda ka iya datti.'' ''Ba na jin dadi sosai, sai na yi ta tsarguwa, kuma ba na iya cirewa a lokacin da muke dakin tiyata akwai lokacin da dole na fita don kariya daga daukar cuta,'' in ji Roslan a hirarta da BBC. Ta ce dole a samar da wata hanya da za a suturta jiki, ta hanyar koyarwar addinin da mutum yake bi musamman a dakin tiyata da kankanin abu ka iya janyowa mara lafiya wata cuta ta daban. Miss Roslan dai 'yar kasar Malaysia ce, kuma daga can ta fara kirkirar hijabin da yin gwaji. ''Ina farin ciki da fatan wannan tsari zai samu karbuwa a sauran asibitoci ga wanda yake sha'awar yin hakan.'' Kwararriyar likitar fida Dr Gill Tierney, wadda ke bai wa Roslan horo, ta ce wannan shi ne karon farko da aka kirkiri abu irin hakan na amfani da dankwali ko hijabi a asibitin Birtaniya. ''Ka san yawanci ba a cika magana a kan batutuwan da suka shafi dakin tiyata ba a kasar nan, kuma ba na jin ana kokarin kawo sauyi.'' ''Ba wani tsada ne da shi ba, ina kuma fatan za a yi amfani da shi,'' in ji Dr Tierney. A karon farko a watan a farkon watan Disamba, inshorar lafiya ta asibitin koyarwa na Berby da Burson, sun amince likitoci mata su yi amfani da dankwali ko hijabi a cikin asibiti. https://www.bbc.com/hausa/labarai-50855597 +technology Chandrayaan-2: Kumbon Indiya zai fara shawagi a duniyar wata "Shirin shawagi a sararin samaniya na biyu wanda kasar Indiya ta shirya ya fara zagaye duniyar wata, kusan wata daya bayan da aka harba shi, a cewar jami'an kasar. Chandrayaan-2 ya fara shawagi a duniyar wata ne karfe 09:02 wato karfe 04:32 agogon GMT a ranar Talata. Kumbon ya gama zagayawa a cikin minti 30, a cewar kungiyar Indiya da ke gudanar da bincike a sararin samaniya (ISRO). Firai Ministan Indiya Narendra Modi ya yaba wa shirin tare da kuma bayyana shi ""a matsayin babban ci gaba."" Jagoran ISRO, K Sivan ya ce hankalinsa ya ba shi cewa Chandrayaan-2 zai sauka a duniyar wata a ranar 7 ga watan Satumba kamar yadda aka kiyasta. ''Mun yi iya kokarinmu don tabbatar da cewa komai ya tafi daidai,'' kamar yadda ya bayyana wa 'yan jarida a yayin wata ganawa da manema labarai. An harba Chandrayaan-2 daga tashar Sriharikota a ranar 22 ga watan Yuli, mako daya bayan da wata matsala ta hana a harba shi a lokacin da aka tsara harba shi tun farko. Indiya na sa ran cewa shirin wanda aka kashe dala miliyan 145 shi ne zai zama na farko da ya sauka a kudancin duniyar wata. A cikin watan da ya gabata ne dai kumbon ya fara tafiyar tsawon kilomita 384,000." https://www.bbc.com/hausa/labarai-49409193 +entertainment ...Daga Bakin Mai Ita tare da Bashir Bala Chiroki Latsa hoton sama domin kallon bidiyon Daga Bakin Mai Ita wani shiri ne na BBC Hausa da ke kawo muku hira da fitattun mutane kan wasu abubuwan da suka shafi rayuwarsu zalla. A wannan kashi na 81, shirin ya tattauna da fitaccen dan wasan barkwanci na Hausa Bashir Bala Chiroki. A cikin hirar ya yi mana bayani game da rayuwarsa. Tsarawa da gabatarwa: Halima Umar Saleh Ɗaukar bidiyo/Tacewa: Abdulsalam Usman Abdulkadir https://www.bbc.com/hausa/59975293 +health An dakatar da likita don an haifi jariri ba fuska a Portugal "An dakatar da wani likitan mata a Portugal bayan da wata mata ta haifi jaririnta ba hanci da idanuwa da wani bangare na kokon kansa. Iyayen jariri Rodrigo ba su da masaniyar irin nakasar da dansu ke da ita sai da aka haife shi a farkon watan nan. Jami'ai a majalisar likitoci sun yanke shawarar dakatar da Dakta Artur Carvalho bisa zargin wasa da aikinsa. An gano cewa an sha yin korafi tun a baya dangane da wasu jariran. Wannan ya jawo ce-ce-ku-ce a kasar bayan da kafofin yada labaran Portugal din suka watsa labarin. Dakta Carvalho bai ce uffan ba kan zarge-zargen har yanzu kuma BBC ba ta samu damar magana da shi ba. An haifi Rodrigo ran 7 ga watan Oktoba a asibitin São Bernardo da ke Setúbal a kudancin Lisbon. Mahaifiyarsa ta samu kulawa ne daga Dakta Carvalho tun da ta samu ciki kuma iyayen sun ce likitan bai taba nuna masu wata damuwa kan lafiyar jaririn ba, duk da ya sha yin hoton cikin. Mahaifiyar ta ce an yi hoton cikin ta sau hudu, kuma na hudun ma ya zamo mai dauko hoton ciki ne sosai na na'urar 5D a lokacin da cikinta ke wata shidda wani asibitin daban. A lokacin ne aka gano akwai yiwuwar cewa jaririn na da nakasa, amma Dakta Carvalho ya yi watsi da batun. ""Ya yi mana bayanin cewa wani lokaci ba a ganin wasu sassan fuskar jariri a idan aka yi hoton ciki,"" 'yar uwar iyayen Rodrigo ta shaida wa kamfanin AFP. Bayan haihuwar Rodrigo, an shaida wa iyayensa cewa ba zai rayu ba. Sai dai, bayan sama da mako biyu, jaririn na nan da ransa. Rahotanni sun nuna cewa iyayen sun shigar da korafi kan Dakta Carvalho ga ofishin babban mai shigar da kara na Portugal." https://www.bbc.com/hausa/labarai-50180189 +religion Ku San Malamanku tare da Malam Jamilu Yusuf Zarewa Filin Ku San Malamanku na wannan makon ya tattauna da Malam Jamilu Yusuf Zarewa da ke Jihar Kano a arewacin Najeriya. An haifi malamin a garin Zarewa cikin 1981. Ya soma karatun firamare a Zarewa inda ya kammala cikin 1991. Daga nan ya tafi College of Quranic Studies ta Kano inda ya yi karatun sakandire. Kazalika malamin ya yi karatun gaba da sakandare a Aminu Kano School of Legal Studies, yayin da kuma ya tafi Jami'ar Madina inda ya yi digirinsa na farko da Masters da kuma Digirin Digirgir. https://www.bbc.com/hausa/articles/czdy9vv2952o +politics APC: Waɗanda suka yi nasara a zaɓen fitar da gwani na gwamnoni a Najeriya An kwana ana gudanar da zaben fid da gwani na masu neman takarar mukamin gwamna a karkashin jam`iyyar APC mai mulki a wasu jihohin Najeriya, yayin da aka kammala a wasu, wasu kuma ana ci gaba da kirge. Zaben dai ya gudana lafiya-lafiya a wasu jihohin, yayin da a wasu kuma aka fuskanci turjiya daga wasu `yan takara. Jihar Kaduna na cikin jihohin da suka gudanar da zaben a cikiin dare, inda Sanata Uba Sani ya samu nasara. Sai dai zaben ya bar baya da kura, kasancewar daya daga cikin abokan hamayyarsa, Alhaji Sani Sha`aban ya ce bai amince ba: ''Idon duk wanda yake wannan guri ya san wannan ba zabe ba ne, kuma ba abin da za mu ce duka dan APC da wani ma dan siyasa da yake Jihar Kaduna abin zub da hawaye ne.'' ''Ya kara da kokawa da cwa, ''In dai haka siyasa za ta ci gaba babu wanda zai yi sha'awarta ballantana ya fito ya ce zai yi wani abu.'' ''Kowa a sanin kowa ba a yi zaben daligets a Jihar Kaduna ba. An je an yi wani list a gidan gwamnati kuma don ana ma sauri a yi list din wadansunsu ko lamba ma na APC ma ma'anan wai sunan 'yan jam'iyya ne babu su.'' in ji shi. Ya ce, ''Wannan ba zabe ba ne, in aka ce ba za a bi hakki ba to ai APC ba ita kadai ce jam'iyya ba.'' Jihar Taraba; An yi harbi da bindiga; A jihar Taraba kuwa, zaben ne ma ya gagara kwata-kwata, saboda wata hatsaniya da ta kaure, har ta kai ga wani harbi da aka yi da bindiga ya samu daya daga cikin malaman zaben. Hakan ne kuma ya sa babban malamin zaben ya sanar da dage shi har sai abin da hali ya yi. Jihar Kebbi A jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriyar lami-lafiya aka yi zaben. Bayan da malamin zaben, Honourable Idris Yahuza Yakubu, ya sanar da Dakta Nasir Idris a matsayin wanda ya samu nasara, nan take daya daga cikin abokan hamayyarsa, Abubakar Malam Shatiman Gwandu ya yi masa mubaya`a. Jihar Kano A jihar Kano mataimakin gwamnan jihar, Nasiru Yusuf Gawuna ne babban malamin zaben, Sanata Tijjani Yahaya, ya sanar ya ci zaben fid da gwanin na APC da kuri'a 2289. Sai dai dan majalisar Wakilai ta tarayya Sha'aban Ibrahim Sharada, wanda ya zo na biyu da kuri'a 30, ya nuna bacin ransa kan yadda zaben ya gudana, inda tun kafin fara zaben ya aika da wata takardar korafi ga uwar jam'iyyar ta kasa game da yadda aka fitar da wakilai masu zaben, yana zargin an shirya magudi. Jihar Katsina A jihar Katsina Dikko Umar Rada ne ya yi nasara da kuri'a 506. Jihar Jigawa: A Jihar Jigawa, Alhaji Umar Namadi ne ne ya lashe zaben fitar da gwanin jihar bayan ya samu ƙuri'u 1,220. Cikin waɗanda ya kara da su akwai Ibrahim Hassan Hadejia da Faruk Adamu da Sabo Nakudu. Jihar Gombe Gwamnan Jihar Gombe Inuwa Yahaya shi ne ya yi nasara a zaben fitar da gwanin da aka gudanar a Jihar. Gwamnan ya lashe zaɓen fitar da gwanin ne ba tare da hamayya ba. Borno A Jihar Borno ma, gwamnan jihar Babagana Umara Zulum ne ya yi nasara a zaben fitar da gwanin ba tare da hamayya ba. Yobe Gwamnan Yobe Mai Mala Buni shi ma bai samu hamayya ba wanda hakan ya sa ya lashe zaɓen fitar da gwanin jihar. Legas A Jihar Legas, gwamnan jihar Babajide Sanwo-Olu ne ya yi nasara a zaɓen fitar da gwani na jihar. Zamfara A Jihar Zamfara kuwa, gwamna mai ci Bello Matawalle ne ya samu nasara a zaɓen fitar da gwani na jihar bayan shi ma ya yi takara ba tare da hamayya ba. Adamawa A Jihar Adamawa, Aishatu Binani ce ta yi nasara bayan a zaɓen fitar da gwanin da aka yi na APC. Cikin waɗanda ta kara da su har da tsohon gwamnan jihar Jibrilla Bindow da tsohon shugaban EFCC Nuhu Ribadu da Honarabul Abdulrazak Namdas. Bauchi A Jihar Bauchi kuwa, Air Marshal Saddique Baba Abubakar ne ya yi nasara a zaben fitar da gwani bayan ya kara da Nura Manu Soro da Sanata Halliru Jika da Dakta Musa Babayo. Haka kuma akwai Honourabul Farouk Mustapha da Mahmood Maijama'a da Farfesa Muhammad Pate. https://www.bbc.com/hausa/labarai-61602015 +sports Bayern ta kammala daukar Sadio Mane Sadio Mane ya kammala komawa Bayern Munich kan fam miliyan 35 daga Liverpool kan kwantiragin kaka uku. Liverpool za ta karbi fam miliyan 27.4 da karin yuro miliyan shida kan yawan buga wasanni da karin yuro miliyan uku kan rawar da zai taka da nasarorin da Bayern za ta samu. Tun farko Liverpool ba ta sallama tayi biyu da Bayern ta yi wa Sadio Mane ba, dan kwallon tawagar Senegal, wanda yarjejeniyarsa zai kare a Anfield a karshen kakar da za mu shiga. Mane ya koma Liverpool kan fam miliyan 34 daga Southampton a Yunin 2016, ya kuma ci wa kungiyar Anfield kwallo 120 a wasa 269, wanda a kakar da aka kare ya zura 23 a raga a dukkan fafatawar da ya yi mata. Dan kwallon tawagar Senegal ya taimaka da Liverpool ta lashe Champions League da Premier League, shi ne ya ci fenaritin da Senegal ta lashe kofin Afirka a karon farko a Fabrairu a Kamaru. A makon jiya Liverpool ta tabbatar da daukar dan kwallon tawagar Uruguay, Darwin Nunez daga Benfica kan fam miliyan 64. https://www.bbc.com/hausa/articles/c3gn8424d4mo +entertainment Batun biyan Ladin Cima dubu biyu a fim ya tayar da ƙura a Kannywood "Jama'a da dama a shafukan sada zumunta musamman Facebook da Instagram na ta ce-ce-ku-ce kan wasu kalamai da ɗaya daga cikin ƴan wasan Kannywood ta yi na cewa ana biyanta naira dubu biyu zuwa dubu biyar a duk lokacin da ta yi fim. A hirar da BBC ta yi da ita a cikin shirin Daga Bakin Mai Ita, Ladin Cima Haruna wadda aka fi sani da Tambaya, ta bayyana cewa ɗaya daga cikin dalilan da ya sa ta kasa mallakar muhalli shi ne tun daga lokacin da ta soma wasan kwaikwayo a zamanin mulkin Yakubu Gowon, ba ta taɓa samun kuɗi a dunƙule dubu ashirin ko talatin ko hamsin idan ta yi fim ba. Wannan batu nata ya tayar da ƙura a shafukan sada zumunta inda jama'a ke ta zargin daraktoci da kuma sauran masu ruwa da tsaki a harkar cewa ba su kyautata wa ƴan wasa. A cewar Shehu Umar, ya kamata hukumomi da masu ruwa da tsaki a harkar fim su taimaka wa irin su Ladin Cima ganin irin gudunmawar da suke bayar wa. Sai kuma Nasiru Tukur ya ce bai ji daɗin maganar da Ladin Cima ta yi ba inda shi ma yana da ra'ayi irin na Shehu Umar na batun cewa hukumomi su shiga lamarin domin dubawa, haka ma ya yi kira ga ƙungiyar ƙwadago domin kai ɗauki. Aisha Rabiu kuma ta ɗora laifin kan gwamnati inda ta ce sai da irin su Ladin Cima suka soma yi wa gwamnati wahala tukuna suke yi wa Kannywood. Me daraktoci da furodusoshin Kannywood ke cewa Dangane da wannan lamari, BBC ta tuntuɓi wasu daga cikin daraktoci da furodusoshin Kannywood kan iƙirarin da Ladin Cima ta yi kuma sun yi mana ƙarin bayani. Falalu Ɗorayi Falalu Ɗorayi yana daga cikin manyan daraktoci a Kannywood kuma yana daga cikin daraktocin da ke saka Ladin Cima a cikin fim. A cewarsa, ya yi mamaki dangane da kalaman Ladin Cima inda ya ce tun da yake sa ta a fina-finai, bai taɓa biyan ta ƙasa da dubu ashirin ba inda ya ce yana biyanta talatin zuwa arba'in. ""Ba a yi kwana goma ba na yi aiki da ita kuma abin da na bata shi ne naira dubu talatin,"" in ji shi. Ya bayyana cewa a girma irin na Ladin Cima da yadda ake kallonta a matsayin kaka a Kannywood babu wanda zai biya ta hakan idan ba yara ƙanana waɗanda suke tasowa ba. Falalu Ɗorayi ya bayyana cewa bai taɓa samun matsala da ita ba ""hasali ma haka kawai ta kan kira ni ta ce wane ya ba ni kuɗi ta yi mani godiya ta kuma ce na kira shi na yi mashi godiya"", in ji shi. Ya ce haka kawai idan mutum ya yi mata alkhairi tana kiransa ma ta faɗa masa inda kuma ya ce a lokacin da ta samu matsalar muhalli ta samu kuɗi daga wurin ƴan Kannywood sun fi miliyan guda. Ya bayyana cewa ko a fim ɗin Gidan Badamasi ta yi masa sin biyar inda ya biya ta dubu araba'in. Ali Nuhu Haka zalika BBC ta tuntuɓi Ali Nuhu inda ya ce ba duka aka taru aka zama ɗaya ba, kuma a cewarsa ko aikin da ta yi masa na ƙarshe a fim ɗin Alaƙa duba arba'in suka biyata. Ya bayyana cewa bai kamata ta yi musu kuɗin goro ba duk da a cewarsa akwai masu biyan jarumai dubu biyar. ""Ka san wasu suna yi wa jama'a yadda suka ga dama ne, wani sai ka ga ya kyautata maka wani kuma ka ga bai kyautata maka ba. ""Ya kamata idan mutum yana bayani ya rinƙa bambancewa ya ce wasu suna kyautata mana ya kuma ce wasu ba su yi ,"" in ji Ali Nuhu. Ali Nuhu ya ce kalaman da Ladin Cima ta yi sun ja masa zagi sosai a wurin jama'a domin fim ɗin baya-bayan nan da tayi tare ta yi da shi. Ali Nuhu ya ce bai ga laifin ɗan kallo da ke zaginsa ba saboda watakila bai san yadda abin yake ba. Sakamakon irin ce-ce-ku-cen da wannan lamari ya jawo, BBC ta sake tuntuɓar Ladin Cima. Ta ce mutane ba su fahimci kalamanta ba duk da cewa akwai fina-finan da ake biyanta dubu biyu zuwa biyar amma akwai furodusoshin da su kan kalli darajarta su yi mata alkhairi a fim. A cewarta, ba ta taɓa kallon furodusa ta ce masa ga abin da zai biya ta ba. Ta ce akwai ƴan Kannywood da suke kyautata mata a ko yaushe kamar su Ali Nuhu da Falalu Ɗorayi da Hadiza Gabon da dai sauransu. Ta ce ""Ali Nuhu ya kan je gidana ya yi mani alkhairi kuma babu abin da bai yi min ba,"". Haka kuma ta ce Hadiza Gabon a kwanakin baya ta ba ta kyautar dubu 300. A cewarta, gidan da take ciki a yanzu ƴan fim ne suka siya mata bayan matsalar da ta shiga a kwanakin baya." https://www.bbc.com/hausa/labarai-60338000 +entertainment Jerin ringingimu tsakanin hukumar tace fina-finan Kano da Kannywood "Matakin da hukumar tace fina-finai ta jihar Kano da ke Najeriya ta dauka na dakatar da nuna fitattun shirye-shiryen talbijin din nan masu suna 'Kwana Casa'in' da 'Gidan Badamasi' ya jawo mata yabo da caccaka. Shugaban hukumar, Isma'ila Na'abba Afakallah, ya shaida wa BBC cewa fina-finan biyu sun ci karo da tsarin dokokin hukumar, inda ya ce a shirin Kwana Cas'in an nuna maza na cacumar wata yarinya. A shirin Gidan Badamasi kuma ya ce an yi amfani da kalaman da ba su dace ba, wadanda dukkaninsu a cewar Afakallah sun saba wa sashe na 102 na dokar da ta kafa hukumar tace fina-finai a 2001. Shirin 'Kwana Casa'in' ya shafi siyasa da kuma bankwado yadda rashawa ta yi katutu a harkokin gwamnati, wani dalilin da wasu ke ganin shi ya sa gwamnatin Kano ta yi amfani da hukumar tace fina-finai aka dakatar da nuna shirin. Ba wannan ne karon farko da hukumar ta shiga ce-ce-ku-ce da wasu 'yan fim ba, wadanda a cewar suke karya dokokinta, ko da yake galibi masu harkar fim da mutanen gari na ganin hukumar tana haikewa ne kan mutanen da ke da bambancin ra'ayin siyasa da gwamnatin Kano. Amma shugaban hukumar, Alhaji Isma'ila ya sha musanta zargin. Ga jerin wasu ringingimu da suka faru tsakanin hukumar da 'yan Kannywood: A watan Agusta na 2019, Hukumar ta gurfanar da daraktan fina-finai Sanusi Oscar a gaban kotu saboda ya ""saba ka'idojin gudanar da sana'arsa a Kano, inda ya saki wata waka wadda akwai badala a ciki"", kamar yadda shugaban hukumar Isma'ila Na'abba Afakallahu ya shaida wa BBC. Oscar ya musanta zargin kuma alkali Aminu Fagge na kotun majistire da ke Kano ya bayar da belinsa bisa sharuda biyu — wajibi ne mutum biyu su tsaya masa kuma daya daga cikinsu ya zama dan uwansa na jini, tare da haramcin magana da kowacce irin kafar yada labarai Batun ya ja hankalin fitattun 'yan fim, ciki har da tauraruwar fina-finan Kudancin Najeriya, Kate Henshaw, wacce a sakon da ta wallafa a Instagram ta caccaki hukumar tace fina-finan. A watan Satumba na 2019, rundunar 'yan sanda ta jihar Kano ta kama fitaccen mawakin nan Naziru M. Ahmed, wanda aka fi sani Naziru Sarkin Waka ""saboda kalaman batanci"" da ya yi a cikin wasu wakokinsa. Hukumar tace fina-finan, wacce ta bayar da umarnin kama shi, ta kara da cewa ana tuhumar mawakin da gudanar da dakin yin waka, wato sutudiyo, a gidansa, zargin da Naziru M. Ahmed ya musanta. Naziru shi ne Sarkin Wakar Sarkin Kano na wancan lokaci, Muhammadu Sunusi II, mutumin da ya dade yana kai ruwa rana tsakaninsa da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje lamarin da ya kai ga raba shi da sarauta. Shi ma kotun Majistare a birnin Kano ta bayar da belinsa da sharuda wadanda suka hada da bayar da kudi naira dubu 500, da mika fasfo dinsa na tafiye-tafiye, da kuma gabatar da mutane uku da za su tsaya masa, wadanda dole su kasance ma'aikatan gwamnatin jihar Kano da kuma dagacin yankin da yake zaune. A watan Fabrairu fitaccen tauraron fina-finan Kannywood, Sani Danja, ya yi zargin cewa hukumar tace fina-finan jihar Kano ta rufe kamfanin daukar hotonsa saboda siyasa. Sai dai hukumar ta ce ta dauki matakin ne saboda kamfanin bai cika sharudanta na yin rijista ba. Kazalika a watan na Fabrairu, hukumar tace fina-finan ta sha alwashin kama fitaccen tauraron fina-finan Kannywood Adam A. Zango idan ya je jihar domin gudanar da waka ko fim ba tare da yin rijista ba. A wancan lokacin, Adam A. Zango ya fito a wani bidiyo da Rahama Sadau ta wallafa a Instagram yana yi wa masoyansa Kanawa albishirin cewa zai je jihar domin kallon fim din 'Mati A Zazzau'. Afakallah ya shaida wa BBC cewa ba su hana tauraron shiga jihar ba amma suna da dokoki game da zuwansa. Da ma dai akwai jikakkiya tsakanin hukumar da tauraron tun bayan da ta hana shi gudanar da wasa tana mai cewa sai ya yi rijista idan yana so ya gudanar da wasan. Adam A. Zango ya yi ikirarin cewa hukumar ta bullo da batun yi wa daidakun taurari rijista ne saboda ta musguna masa, ko da yake hukumar ta musanta zargin. Sai kuma wata takaddama da ta kunno kai tsakanin shugaban hukumar tace fina-finan da kuma jarumin fina-finan Kannywood, Yusuf Haruna, wanda aka fi sani da Baban Chinedu. Takaddamar ta samo asali ne bayan da aka aike wa Baban Chinedu wata takarda a kan wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Instagram yana zargin cewa gwamnatin Kano ta bai wa shugaban hukumar tace fina-finan N5m domin mika su ga iyalan marigayi Rabilu Musa Ibro. Baban Chinedu dai makusancin Ibro ne, kuma ya ce gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta bai wa Isma'il Na'abba Afakallah kudin ne a matsayin gudunmuwar bikin 'yar gidan marigayi Ibro kusan shekaru biyu da suka wuce. Sai dai lauyoyin Malam Afakalla sun bukaci Baban Chinedu ya janye kalaman da ya yi ko kuma a gurfanar da shi a gaban kuliya. Har yanzu dai batun yana kotu. Masana harkokin fina-finan Kannywood sun ce irin wadannan rigingimu za su ci gaba da yin mummunan tasiri kan masana'antar, ko da yake hukumar tace fina-finan ta ce matakan da take dauka za su kawo gagarumin ci gaba a Kannywood da kuma tsaftace masana'antar." https://www.bbc.com/hausa/labarai-52228209 +sports Tottenham ta yi wasa shida ba a doke ta a bana ba Tottenham ta yi wasa shida ba tare da rashin nasara ba, bayan da ta doke Fulham 2-1 a wasan mako na shida da suka kara ranar Asabar. Pierre-Emile Hojbjerg ne ya fara ci wa Tottenham kwallo na biyu da ya zura a raga a kakar nan. Harry Kane ne ya kara na biyu a minti na 75, kwallo na biyar da ya ci kenan a kakar Premier League da ake bugawa. Saura minti 10 a tashi Fulham ta zare daya ta hannun Alexander Mitrovic a wasa na biyu da Marco Silva ya yi rashin nasara a kakar nan. Tottenham ta barar da damarmaki ta kan zama hadari a duk lokacin da ta nufi ragar Fulham, inda ta kai hari 23 kuma 10 daga ciki suka nufi raga kai tsaye. Kwallon da Mitrovich ya ci shi ne na shida a kakar nan kuma na 101 a League, bayan da ya zura na 100 a karawa da Brighton a tsakiyar mako. Shi kansa Marco Silva ya ja ragamar wasa na 101 a Premier da cin 34 aka doke shi fafatawa 46 sauran sakamakon a canjaras suke. Mitrovich ya zama cikin jerin 'yan wasan Fulham da suka ci kwallo a wasa hudu a jere, bayan bajintar Steed Malbranque a 2003 da kuma Barbatov a 2013. Sabon dan wasan da Tottenham ta dauka daga Everton a bana, Richarlison ya fara buga wasa ya kuma taka rawar gani, wanda ya ci kwallo amma aka soke ta da cewar an yi satar gida. Ranar 7 ga watan Satumba Tottenham za ta karbi bakuncin Marseille a wasan makon farko a Champions League. Ita kuwa Fulham za ta buga wasan gaba a Premier League, inda za ta karbi bakuncin Chelsea ranar 10 ga watan Satumba. Wasu sakamakon wasannin mako na shida: Everton 0-0 Liverpool (12:30) Brentford 5-2 Leeds Chelsea 2-1 West Ham Newcastle 0-0 Crystal Palace Nottm Forest 2-3 Bournemouth Wolves 1-0 Southampton https://www.bbc.com/hausa/articles/cn09y1732lpo +health Coronavirus: Amurka ta tabbatar da mutuwar mutum daya "Amurka ta tabbatar da mutum na farko da cutar corona ta kashe a kasar. Shugaba Trump ya ce wani namiji ne da ya haura shekara 50 cutar ta kashe a jihar Washington da ke arewa maso yammacin Amurka. Ya ce akwai yiyuwar kara samun wadanda suka mutu, amma Amurka shirye ta ke. Hukumomin kasar sun ce za ta saka Iran cikin kasashen da aka yi wa Amurka gargadin su kaurace kamar Italiya da Koriya ta kudu. Sama da mutum 85,000, aka bayar da rahoton suna dauke da cutar a duniya, kuma kusan mutum 3,000 suka mutu, a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya. China da cutar ta fara bulla ke da yawan wadanda suka kamu da ita kuma a kasar cutar cornavirus ta fi yin kisa. Me ke faruwa a Amurka? A lokacin da yake jawabi a wani taron manema labarai ranar Asabar, Shugaba Trumo ya tabbatar da rahotannin da ke cewa mutum daya ya mutu a Washington sakamakon kamura da cutar coronavirus Jami'an lafiya ba su tantance mutumin ba, amma sun ce ya mutu ne a karamar hukumar King, sun ce bai yi wani balaguro ba zuwa inda cutar ta bulla. Game da sauran mutum 22 da ke dauke da cutar a yankin, Trump ya ce mutum hudu daga cikinsu ""rashin lafiyarsu ta tsananta"" Gwamnan Washington Jay Inslee ya kaddamar da dokar ta baci domin dakile bazuwar cutar a jihar. Wannan na zuwa bayan bayar da rahoton kara samun wasu mutum uku da suka kamu da cutar coronavirus a jihohin California da Oregon da Washington wanda ke kara haifar da fargaba kan yiyuqar bazuwar cutar tsakanin al'umma. Akwani wani Ba'amurke da ya mutu a garin Wuhan na China inda cutar ta fara bulla. Mataimakin shugaban kasa Mike Pence ya ce dokar hana tafiye-tafiye zuwa Iran yanzu ta shafi duk wani dan kasar waje da ya kai ziyara kasar tsakanin mako biyu. An kuma bukaci Amurkawa su kauracewa zuwa kasashen Italiya da Koriya ta Kudu. Mista Pence ya ce Amurka na aiki da jami'ai domin kara tsaurara bincike kan matafiyan da suka shigo Amurka daga kasashen." https://www.bbc.com/hausa/labarai-51693007 +business Saudiyya za ta kara haraji ga fasinjojin jiragen sama Hukumomi a Saudiyya za su kara kudaden haraji ga fasinjojin jiragen sama da ke zirga-zirga a cikin kasar daga farkon shekarar 2020. Hukumar kula da sufurin jiragen saman kasar wacce za ta kakaba wannan tara ta kasa da dalar Amurka uku, ta ce za a yi amfani da kudin ne wajen kula da ingancin jiragen saman. Sai dai wannan tara ba ta shafi jarirai da fasinjojin jirgin yawo da kuma ma'aikatan jirgin ba. Wannan matakin, irinsa na farko, na zuwa ne yayin da gwamnatin kasar ke fuskantar gibin sama da dala biliyan 50 a shekara mai zuwa kimanin kashi shida cikin 100 na abin da kasar ke samarwa a shekara ta fannin tattalin arzikinta. Harin da aka kai wa matatun mai na Saudiyya a kwanakin baya na daya daga cikin abubuwan da kan iya shafar tattalin arzikin kasar. Ko a kwanakin baya sai da kamfanin tace mai na kasar wato Saudi Aramco ya ce harin ya sanya man da kasar ke samarwa ya yi kasa da ganga miliyan 5.7 a kowace rana. A 'yan kwanakin nan dai Saudiyya na ta fito da sabbin hanyoyin samun kudin shiga domin rage dogaro da arzikin danyen man fetur wanda take da shi. Cikin tsare-tsaren harda bude kofofinta ga masu sha'awar zuwa can domin yawon bude idanu daga kasashen duniya. Haka zalika kasar a kwanakin baya ta gayyaci fitattun mawaka na duniya domin rakashewa ta fannin nishadi. Hakan ya jawo rudani matuka musamman ga masu kallon kasar a matsayin kasa da wasu kasashe ke koyi da ita ta bangaren addinin musulunci. Yarima mai jiran gado, Mohammad bin Salman ya ce yana son yin sauye-sauye a kasar ta fuskar zamantakewa da tattalin arziki a wani bangare na ganin Saudiyyar ta tafi dai-dai da zamani da aka yi wa lakabi da Vision 2030. Kasar Saudiyya dai ta dogara ne kan man fetur to amma kasancewar tangal-tangal din da aka samu a farashin man a kasuwar duniya ya sanya Saudiyyar tunanin dogaro da man babu tabbas. Sakamakon bukatar kasar ta ganin an samu sauye-sauye a tattalin arzikin kasar musamman shigar masu zuba jari, Saudiyya take ta kokarin ta nuna wa duniya cewa kofofinta a bude suke ga 'yan kasuwa. https://www.bbc.com/hausa/50280295 +technology Tsuntsu mai siffar jirgin yaƙi ya kafa tarihin yin tafiya mafi nisa a duniya Wani tsuntsu da masana kimiyya suka ce an halicce shi kamar jirgin yaƙi ya kafa sabon tarihi a matsayin tsuntsun da ya fi yin tafiya mai dogon zango a duniya. Tsuntsun mai doguwar jela ya tashi daga Alaska da ke Amurka, inda ya sauka a New Zealand, bayan shafe kwanaki 11 yana tafiya ba tare da yada zango ba, abin da ke nufin cewa ya yi tafiyar a ƙalla kilomita 12,000. Masana kimiyyar sun ce sun riƙa bin sawunsa ta hanyar wata na'urar bibiya ta zamani. Sun ƙara da cewa tsuntsaye nau'ukan wanda ya nuna wannan bajinta a yanzu, ba sa bacci yayin da suke tafiya, hasalima sukan iya tsamurewa don rage girman jikinsu ta yadda za su yi doguwar tafiya ba tare da wata gajiya ba. Dakta Jesse Conklin, na ƙungiyar Global Flyway Network ta masana kimiyya da ke bincike kan halittu masu ƙaura ya ce: ''Suna da wani irin ƙarfi na rashin gajiya. ''Akwai abubuwa da yawa a tattare da su. An halicce su tamkar tsarin jiragen yaƙi. Suna da dogayen fukafukai da ke taimaka musu yin abubuwa tamkar na jirgin sama.'' Tsuntsun wanda jinsin namiji ne da ake wa laƙabi da 4BBRW da ake alaƙantawa da launin shuɗi da ja da kuma fararen zobuna da aka maƙala masa a ƙafafunsa, an kuma maƙala masa wani ɗan ƙaramin tauraron ɗan adam mai nauyin giram biyar a ƙasan bayansa, don bai wa masana kimiyyar damar bibiyar halin da yake ciki. Yana ɗaya daga cikin huɗun da za su bar cikin laka a Alaska, inda a can ne suke rayuwa suna tsintar tsutsa da tanar da suka kasance abincinsu tsawon wata biyu. Dakta Conklin ya ƙara da cewa: ''Alamu sun nuna tsuntsayen sun san a inda suke a faɗin duniya. Ba za mu iya bayani sosai ba amma dai kamar suna da taswira. ''Suna shawagi ta saman tekun Pacific tsawon kwanaki a inda babu dandaryar ƙasa. Daga nan sai su shiga New Caledonia da Papua New Guinea inda ake da tsibirai kaɗan.'' https://www.bbc.com/hausa/labarai-54536211 +politics Waiwaye: Tsayar da ranar zaɓen 2023 da martanin Buhari ga Ortom "Ga wasu daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a makon da ya gabata a Najeriya, daga Lahadi 25 ga Afirilu zuwa Asabar 1 ga Mayu. A Najeriya mutanen Geidam sun ci gaba da tserewa daga garin sakamakon kutsen da 'yan Boko Haram suka yi tun ranar Juma'a. Shaidu sun ce sun tsere ne saboda gudun kada a ritsa da su a musayar wutar da ake yi tsakanin sojojin Najeriya da mayaƙan Boko Haram. Haka zalika, an fafata tsakanin 'yan Boko Haram da sojoji a garin Mainok na jihar Borno mai maƙwabtaka, har wasu rahotanni na cewa harin ya ritsa da wasu sojoji. A baya-bayan nan dai ƙungiyar Boko Haram na zafa-zafa hare-hare a sassa daban-daban na arewa maso gabashin Najeriya. Rundunar 'yan sandan Najeriya ta tabbatar da mutuwar wani DPO da jami'ansa takwas a Jihar Kebbi da ke arewacin kasar. Kakakin yan sandan na Jihar Kebbi ASP Nafi'u Abubakar ne ya tabbatarwa BBC da faruwar lamarin, wanda ya faru a ranar Lahadi. ""Da misalin karfe 2:30 na rana ne DPO na Kasaba ya samu labarin an kai hari wani kauye da ake kira Makuku da wasu kauyuka da ke kewaye da shi, nan da nan ya debi yaransa su takwas da nufin kai dauki bayan fafatawa kuma anan suka gamu da ajalinsu,"" in ji ASP Nafi'u. Wasu 'yan majalisar dattawan Najeriya sun yi musayar zafafan kalamai sakamakon rashin tsaron da ke ci gaba da ta'azzara a kasar. Sanatocin, Smart Adeyemi daga jihar Kogi da Remi Tinubu daga jihar Lagos, suna cikin wadanda suka bayar da gudunmawa yayin muhawarar da majalisar dattawan kasar ta gudanar ranar Talata. Majalisar ta yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya zage damtse domin magance rashin tsaron da kasar ke ci gaba da fama da ita tana mai shan alwashin ganawa da shi a kan batun. A nata bangaren, majalisar wakilan kasar ta bukaci Shugaba Buhari ya ayyana dokar ta-baci a kan matsalar tsaro. 'Yan majalisun na yin kiran ne a yayin da ake ci gaba da kai hare-hare a kusan dukkan sassan kasar - daga rikicin masu garkuwa da mutane da 'yan fashin daji, zuwa hare-haren 'yan Boko Haram da na masu son ballewa daga kasar na kungiyar IPOB. Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta tsayar da ranar zaɓen 2023 a ƙasar. Shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin taron yini ɗaya na sauraren dokar laifukan Zabe ta 2021, wanda kwamitin Majalisar Dattawa kan INEC ya shirya. ""Bisa dokar da aka kafa hukumar, zaɓen 2023 zai kasance ranar Asabar 18 ga watan Fabrairun 2023, wanda ya rage saura shekara ɗaya da wata Tara da mako biyu da kwana shida daga yau."" Shugaban Hukumar ya ce suna fatan tsara jadawalin zaɓen da zarar an kammala zaɓen gwamnan jihar Anambra wanda za a gudanar a ranar 6 ga Nuwamban 2021. Tsohon Shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya ce yana da yakinin cewa matsalolin tsaron da ake fama da su a sassan kasar ba za su ga bayan Najeriya ba har ta kai ta durkushe yana mai cewa kasar za ta fita daga kangin da ta tsinci kanta a ciki. Ya bayyana haka ne a wani taro da aka yi domin karrama shugaban kungiyar kiristoci ta Najeriya, CAN wato Dakta Samson Ayokunle. A jawabinsa, Obasanjo ya ce yana da imanin cewa Najeriya ba za ta durkushe ba duk da karuwar tabarbarewar tsaro. Ba Obasanjo ne kadai yake da irin wannan fahimta ba, wasu gwamnoni da suka halarci taron irinsu Dapo Abiodun na Ogun da Seyi Makinde na Oyo na ganin za a samu mafita. Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ce Najeriya ba za ta taba ci gaba ba saboda cin hanci da rashawar da ya dabaibayeta. Ganduje ya ce babu yadda za a yi kasar nan ta ci gaba da irin wannan cin hanci da rashawar da ake fama da shi a Najeriya. ""Za ku yarda da ci idan na ce cin hanci yana kashe mu. Maganar gaskiya ita ce ba inda kasar za ta je da wannan cin hanci. Ba za mu motsa ko ina ba,"" in ji Ganduje. Ganduje ya bayyana hakan ne ya yin kaddamar da wani kwamitin na mutum takwas kan wasu dabarun yaki da rashawa a jihar. Ministan makamashi a Najeriya, Injiniya Sale Mamman ya sanar da cewa ana ci gaba da shirye-shiryen aikin wutar lantarki na Mambilla. A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, minista ya bayyana cewa ya gana da jami'an kamfanin China Gezhouba Group International, wanda zai ja ragamar aikin. Ya ce gwamnatin Najeriya da duka masu ruwa da tsaki a shirye suke su tabbatar an kammala aikin. Sai dai ya ce ƙalubale ɗaya da ma'aikatarsa ke fuskanta ita ce rikicin shari'a tsakaninta da kamfanin da aka fara bai wa kwangilar aikin, Sunrise Group, inda ya ce wannan ya ƙara mayar da aikin baya. Injiniya Sale Mamman ya ce a halin yanzu, ana kan gaɓar kammala sa hannu a ƙa'idojin kwangilar kuma ya ce nan ba da jimawa ba za a fara aikin na Mambilla. Shugaban Najeirya Muhammadu Buhari ya ce abin takaici ne irin yadda gwamnan jihar Benue Samuel Ortom yake zarginsa da aikata wasu laifuka. Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a wata sanarwa da mai magana da ywunsa Malam Garba Shehu ya aike wa manema labarai ranar Juma'a da safe. Ya mika jajensa ga al'ummar jihar ta Benue wadanda suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren da aka kai musu a baya bayan nan. Rahotanni sun ambato Gwamna Ortom yana zargin Shugaba Buhari da mara wa makiyaya baya a kashe-kashen da yake cea sun yi a jihar ta Benue. Sai dai shugaban kasa ya kara da cewa babu kamshin gaskiya a zarge-zargen yana mai cewa ""babu wata gwamnatin da take da hankali da za ta ji dadin irin wadannan kashe-kashe na sojoji da mutanen da ba su ji ba ba su gani ba da ke zaune a sansanonn 'yan gudun hijira."" A dai cikin makon ne, fitaccen malamin Cocin Katolikan nan da ke Najeriya, Rabaran Fada Ejike Mbaka, ya ce ya kamata shugaban kasar Muhammadu Buhari ya sauka daga mulki idan ba haka ba a tsige shi. Rabaran Fada Mbaka, wanda a baya a goyi bayan shugaban kasar, ya kara da cewa ya yi kiran ne saboda Shugaba Buhari ya gaza shawo kan matsalolin tsaron da suka addabi Najeriya. Malamin Cocin ya bayyana haka ne a gaban dimbin mabiyansa a Enugu da ke Kudu Maso Gabashin Najeriya. ""Idan da a kasashen da aka ci gaba ne da tuni Shugaba Buhari ya ajiye mukaminsa. Ku ambato ni a koina cewa na yi kira ga shugaba Buhari ya sauka daga mulki tun da girma da arziki. Muna kuka ne saboda ba mu da jagora...idan ba za ka iya mulki ba, ka sauka ko a sauya ka...ko dai Buhari ya sauka da kansa ko kuma a tsige shi.."" Wani rahoto da ma'aikatar tsaro da harkokin cikin gida ta jihar Kaduna ta fitar ya nuna cewa daga 1 ga watan Janairu zuwa 31 ga watan Maris na 2021 an kashe mutum 323 tare da yin garkuwa da mutum 949 a jihar. Samuel Aruwan, Kwamishinan da ke kula da ma'aikatar ya bayyana cewa alƙaluman na nuna mutanen da suka rasa rayukansu sanadiyyar ayyukan ƴan bindiga da fashin daji da garkuwa da mutane da hare-haren ramuwa, ciki har da mahara da ƴan bindigar da jami'an tsaro suka kashe. Sai dai ya ce bai haɗa da jami'an tsaro da suka mutu a bakin aiki ba. Haka kuma, alƙaluman ba su haɗa da mutanen da suka rasu sanadiyyar haɗurran abubuwan hawa da kisan kai ba." https://www.bbc.com/hausa/labarai-56957154 +religion Mata da mijin da suka yi fice a waƙoƙin Annabi tare "Duk da tarin mawaƙan yabon Manzon Allah Annabi Muhammadu S.A.W. da ake da su a ƙasar Hausa da duniya baki ɗaya, ba kasafai ake samun mata da miji na yin yabon a tare ba. Wannan ta sa Hafiz Abdallah da matarsa Murja Bukhari Adam - wadda wasu ke kira da sunan mijinta - suka yi fice a fagen waƙoƙin yabon Annabi. Ma'auratan, waɗanda 'yan asalin Jihar Kano ne, malami ne da ɗalibarsa kafin su yi aure. ""Ni ɗalibarsa ce, tun a Islamiyya yake ban ƙasidu kuma da Allah ya tashi ikonsa sai ya haɗa wani abu mai girma - shi ne aure,"" kamar yadda Murja ta shaida wa BBC Hausa game da mijinta. Baya ga waƙa, Hafiz ya ce yana yin harkoki da dama, ciki akwai sayar da tufafi da harkokin man fetur da kuma dillancin tafiye-tafiye. An haife shi a unguwar Kwanar Ɗiso da ke Ƙaramar Hukumar Gwale a birnin Kano, kuma a nan ya taso. Malam Hafiz ya bayyana cewa tun yana ƙaramin yaro ɗan shekara 10 ya fara rubuta waƙoƙin yabon Annabi sakamakon baiwar da Allah ya yi masa, ba tare da tunanin zai zama mawaƙi ba. Ya ce a lokacin da suke zuwa makarantar Islamiyya ne wani malaminsu mai suna Farfesa Hussaini Auwal ya ƙalubalanci ɗalibai da tambayar cewa wane ne zai iya rubuta waƙar yabo. ""Sai Allah ya ƙaddara ta hannuna wannan rubutun zai fito, na rubuta waƙar biyu na zo da ita aji bayan kwana ɗaya,"" a cewarsa. ""A lokacin ma ba na jin na cika shekara 10. ""To tun daga wannan lokacin ne abin ya ɗore har zuwa yanzu da muke magana da kai."" Da take ba da labarin irin ƙalubalen da ta fuskanta a harkar yabon, Murja ta ce ɗaya daga cikinsu shi ne lokacin da mijinta ya kira ta a waya ya ce mata ya gama nasa baitocin a situdiyo, ""ke ma ki zo ki ɗora naki"". Ta ƙara da cewa hakan ya faru bayan mai gidan nata ya dawo daga aikin Umara a Saudiyya kuma ya wuce kai-tsaye zuwa ɗakin ɗaukar waƙar yana buga waƙar 'Ambato'. ""Mu muna nan muna jiran ya ƙaraso mu tarɓe shi a gida, ashe shi ya wuce situdiyo. Sai kira na ya yi ya ce shi ya gama na zo na ɗora. ""Ka ga ban san amshin ba, ban san ya kiɗan yake ba amma da taimakon Allah da manzonsa ya gama na je na ɗora. ""Ni kam a kan wannan ba abin da zan ce sai dai na gode wa Allah."" Hafiz Abdallah ya ce rayuwa mataki-mataki ce kuma dole akwai abin da zan daina a yabo. ""Rera yabon Annabi, babu ranar da zan daina shi. Amma a cikinsa akwai abin da dole mutum sai ya bari,"" a cewarsa. ""Misali, akwai matakin da idan mutum ya kai ya wuce a gayyace shi biki yau kan dandamali ya yi waƙa. Amma akwai lokacin da sai dai ka rubuta ka bai wa wani ya rera, ka saurara don ka ji daɗi. Wani lokacin kuma sai dai ka shiga ɗaki ka kunna kai kaɗai ka ji. ""Amma fita daga cikin da'irar Annabi, babu rana har abada."" Mai yabon ya ƙara da cewa ""ina son Annabi ƙwarai"", kuma abin da ya sa yake shirya waƙoƙin yabonsa ke nan. ""Za ka ga kowa yakan bi Annabi ne gwargwadon alfarmarsa a zuciyarsa - mai kuɗi ya hidimta masa da arzikinsa, malami ya hidimta da iliminsa. Haka shi ma mai hikima sai ya hidimta masa da hikimarsa."" Malama Murja ta ce babar nasarar da ta samu a rayuwarta sakamakon harkokin waƙar yabo ita ce zuwa ziyarar ƙabarin Annabi da ta yi a Madina. ""Na je na kuma zuwa, na kuma zuwa [ƙabarin Annabi Muhammadu S.A.W.] duk a sanadin yabon Annabi,"" in ji ta. ""Wannan ai ya fi komai girma."" Malama Murja ta ce kiran da za ta yi wa kan ta da sauran 'yan uwanta masu yabo shi ne ""a tsarkake zuciya kuma a nemi masana"". Ta ci gaba da cewa: ""Tafiyar Annabi sai an tsarkake harshe. Kamar yadda malamai ke faɗa mana sukan ce ka nemi ilimi kafin ka yi wa Annabi yabo saboda akwai kalmar da za ka faɗa wa Annabi da niyyar yabo amma idan aka fassara ta saɓanin haka ne."" Shi ma Hafiz ya shawarce mawaƙa da cewa ""a dinga neman shawarar malamai don a zauna lafiya"". A cewarsa: ""Ka san daga ina kake sannan ka san inda za ka je - wanda ilimi ne yake ba da wannan fassarar. A dinga tuntuɓar masana harkar rayuwa, waɗanda suke da ƙwarewa a harkar Annabi S.A.W.""" https://www.bbc.com/hausa/articles/c031g5xgpdyo +business Damuwar da mutane ke nunawa kan biyan kudin haya na shekara a Lagos "Samun matsuguni mai kyau babban ƙalubale ne a ko'ina, amma haɗa kuɗin haya na shekara guda kafin a ba ka gidan ƙarin nauyi ne ga miliyoyin ƴan Najeriya. Masu gidajen haya sun fi son a ba su kuɗin hayan a dunkule saboda yana rage yiwuwar gazawar ɗan haya wajen biyan kuɗin haya. A ganinsu, gara a matsa wa ɗan haya sau daya a shekara maimakon sau 12, wato kowane wata ke nan cikin shekara. Sai dai da alama wannan tsarin ya kusa zuwa karshe. Majalisun kasa a Abuja babban birnin Najeriya na kokarin kafa wata doka da za ta haramta karɓar kuɗin haya na shekara guda gabanin a bayar da hayar gidaje a kasar. A Legas babban birnin kasuwanci na ƙasar, hukumomi sun fara aiwatar da wani tsari na sa-kai da zai fara aiki daga watan gobe. Gwamnatin jihar ta Legas na fatan cewa masu gidajen haya za su fi amincewa su karɓi kuɗin haya daga wata zuwa wata idan suka ga hukumomi sun shiga tsakaninsu da ƴan hayar. Yawancin mazauna birnin, musamman matasa masu son yin aure nan kusa sun yaba da wannan tsarin na biyan kuɗin haya na wata-wata. Tunde Omotayo wanda ke shirin yin aure a watan Afrilu na fuskantar jan aikin haɗa naira 600,000 zuwa naira 800,000 (wato $1,500-$2,000) domin ya biya kuɗin hayar wani gida a cikin birnin Legas. Ga mutumin da albashinsa na wata bai wuce naira 300,000 ba, wannan jan aiki ne. ""Na yi tsammanin albashina zai iya ɗaukar nauyin kuɗi hayar da zan riƙa biya, sai dai na sha mamaki matuƙa. A halin yanzu zan so in riƙa biyan kuɗin haya daga wata zuwa wata saboda a halin yanzu na shiga cikin damuwa sosai."" Idan ya sami shiga cikin wannan sabon tsarin, zai riƙa biyan naira 50,000 a kowane wata ke nan, wanda yayi amanna zai sauwaƙa ma sa rayuwa tun da yana son yin aure nan ba da jimawa ba. A matsayin ɗaya daga cikin birane mafi saurin bunkasa, kuɗin haya na karuwa a kowace rana kuma gidaje sun fiye tsada. Ana karɓar gidaje masu ɗakin kwana biyu a yankin da ke kusa da cibiyar kasuwancin birnin wato Victoria Island kan dala( 4577540 )11,000 zuwa dala 22,000 (9155080) a shekara, inda gidaje masu sauƙi na kai wa tsakani dala 500 zuwa 5,000 (208070-2080700)a yankunan da ke da nisa daga nan. Ya rage ga 'yan haya su nemo kudin da za su biya masu gidaje, kuma wannan ya tilastawa yawancin ma'aikata 'yan Najeriya bin wasu hanyoyi domin hada kan kudin haya daga cikin albashinsu na wata. Wasunsu na karbar basussuka daga kamfanonin bayar da bashi - wadanda ke karbar kudin ruwan da ya kai kashi 28 cikin 100 a kowane wata, inda wasu kalilan cikinsu ke samun damar karbar bashi maras kudin ruwa daga wuraren da suke aiki domin su biya kudin hayan gidajen da suke son shiga. Sai dai akwai masu gidajen hayan da ba su rungumi wannan sabon tsarin na biyan kuɗin haya daga wata zuwa wata. Tosin Emmanuel, wani dan kasuwa a Legas ya ce wani mai gidan hayan da ya je wajensa ya soki tsarin. ""Mai gidan ya tambaye ni ko gwamnati ce ta sayo filin kuma ta gina gidan masa. Ya kuma ce babu gwamnatin da za ta tankwara shi kan yadda yake karɓar kudin hayan gidajensa."" Mista Emmanuel ya kuma ce ""Mai gidan ya ce sai in tafi wajen gwamna Sanwo-Olu ya bani gida"". Suna gina gidajen da suke so, kuma suna yin cajin kudin hayan da suke so a wannan bangare da kawo yanzu gwamnati ba ta sa ido a kai ba sosai. Sai dai akwai 'yan haya masu yawa da ba sa son sauya wannan tsarin saboda sun riga sun sami mafaka kuma sun saba da tsohon tsarin. 'Yan Najeriya sun saba da biyan kudin kayayyaki baki daya gabanin su mallake su; misali motoci da wayoyin hannu da kudin makarantar 'ya'yansu. Madam Adaobi Asuoha da ke zama a gundumar Ajah ta tsibirin Legas ta fi son ta biya kudin hayan gidan da ta ke zaune da iyalanta daga shekara zuwa shekara saboda tafi samun sauki da natsuwa na sauran watannin shekarar. Ita ma kan ta gwamnatin jihar Legas ta gane cewa shirin nata na biyan kudin haya daga wata zuwa wata na hannun wadannan masu gidajen hayan ne da ke da karfin fada a ji, kuma sai yadda suka so za a yi. ""Mun san cewa a gwamnatance ba za mu iya tilasta wa masu gidajen haya su karbi kudaden daga wata zuwa wata ba,"" inji Toke Benson-Awoyinka, wani mai ba gwamnan Jihar Legas shawara kan harkokin muhalli. Sai dai gwamnati ta ce an samar da sabo tsarin ne bayan tuntubar da ta yi da masu ruwa da tsaki kuma babu dalilin da zai sa shirin ya ki aiki." https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-60285921 +sports Magoya bayan Liverpool za su kai Uefa kotu Sama da magoya bayan Liverpool 1,700 ne ke shirin daukar matakin shari'a kan Uefa da cewar an kuntata musu a wasan karshe a Champions League. Real Madrid ce ta lashe kofin Zakarun kuma na 14 jumulla, bayan da ta doke kungiyar Anfield a Faransa a kakar da ta wuce. Hukumar kwallon kafar Turai na fuskantar matakan shari'a da magoya bayan Liverpool kan wasan da aka kara a birnin Paris. Ba a fara wasan da wuri ba kamar yadda aka tsara har ta kai an yi lattin minti 35, inda Uefa ta ce ta ci karo da kalubalen matakan tsaro a ranar. Wani kamfanin lauyoyi da ke Birmingham ya ce ya tattauna da mutane da yawa wadanda suka sha wahala a dalilin wasan har da jin ciwo da wasu suka ji. Tuni sun yi shirin hadin gwiwa da wani babban kamfanin lauyoyi mai suna Pogust Goodhead don wakiltar mutum 1,450 da cewar Uefa ta yi sakaci. Lauyoyin sun ce za su shigar da karar cewar Uefa ta karya dokar sayar da tikiti da kasa kula da lafiyar 'yan kallo da ta kai wasu suka jikkata a Paris. Magoya bayan Liverpool da dama sun yi bayani kan yadda suka dade a kan layin shiga kallon wasan da 'yadda jami'an tsaro suka musguna musu har da bada barkonon tsohuwa. A ranar wasu wadanda suka sayi tikiti ba su samu damar shiga kallon fafatawar ba, sakamakon turmutsisin mutane. https://www.bbc.com/hausa/articles/c510j2xyyd3o +technology Ƴan sama jannatin Rasha da Amurka sun ce lafiya lau suke zaune a sararin samaniya Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon: Wani Ba'amurke tare da wasu Rashawa biyu - wadanda dukkansu 'yan sama jannati ne - sun dawo duniyarmu ta Earth daga tashar ƙasa-da-ƙasa da ke can cikin sararin samaniya. Hakan ya faru ne yayin da dangantaka tsakanin Rasha da Amurka ke ƙara tsami kan yaƙin ƙasar Ukraine. Wata rokar Soyuz mallakin ƙasar Rasha ce ta dawo da Mark Vande Hei na hukumar binciken sararin samaniya ta Amurka NASA, tare da Anton Shkalerov and Pyotr Dubrov 'yan kasar Rasha, inda ta sauka a wani yankin da ke tsakiyar kasar Kazakhstan. An dai rika fargabar cewa Rasha za ta ƙi ɗauko Ba'amurken daga tashar sararin samaniyar -- sai dai da wuya Amurka ta sake neman taimakon Rasha wajen jigilar 'yan sama jannatinta. Ba'amurken ya kafa tarihi a matsayin mutumin da ya fi daɗewar zama a wajen duniyarmu, inda ya shafe kwana 355 yana rayuwa a sararin samaniya. Ga ƙarin bayani kan tashar ƙasa da ƙasa da ke zagaya duniya daga sararin samaniya https://www.bbc.com/hausa/media-60944404 +health Yunkurin samar da ingantaccen makewayi a jihar Adamawa Asusun Kula da Kara na Majalisar Dinkin Duniya Unifef ya ce yana fargabar Najeriya ba za ta iya cimma muradin kawo karshen yin ba-haya a waje ba daga nan zuwa 2025. A bara, binciken Unife ya gano cewa 23% na mutanen Najeriya - kimanin mutum miliyan 47 – har yanzu suna yin ba-haya a waje a duk fadin Najeriya. BBC ta duba lamarin a jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya don ganin yadda wata hanya mai sauki ke taimakawa wajen shawo kan lamarin. https://www.bbc.com/hausa/labarai-55838226 +religion Musulman Rohingya 14 sun mutu a hatsarin jirgin ruwa A kalla mutum 14 ne suka nutse a teku bayan da wani jirgin ruwa dauke da Musulman Rohingya 'yan gudun hijira ya kife a kudu da gabar tekun Bangladesh, in ji jami'ai. Jirgin na kan hanyarsa ta zuwa Malaysia ne kuma yana dauke da 'yan gudun hijirar Rohingya daga sansanonin Bangladesh, kamar yadda hukumomin kasar suka shaida wa BBC. Dukkan gawarwakin da aka samo zuwa yanzu duk mata ne da yara. Wani jami'i ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa kusan mutum 70 aka ceto. Sai dai har yanzu ba a ga wasu da yawa ba. Jirgin ruwan ya yi hatsarin ne a tekun Bay of Bengal kusa da tsibirin Saint Martin. A watan Agustan 2017 ne sojojin Myanmar suka yi wa Musulan Rohingya mummunar dirar mikiya inda dubun-dubatar su suka tsallake suka bar kasar zuwa Bangladesh. Da yawansu suna zaune ne a sansanonin 'yan gudun hijira kuma wasun su sun yi kokarin tserewa zuwa Malaysia. https://www.bbc.com/hausa/labarai-51459447 +sports Anya Klopp zai kai labari a Liverpool kuwa a bana? Liverpool ta sha kashi a wasan farko a cikin rukuni a Champions League kakar bana, bayan da Napoli ta doke ta 4-1 a ranar Laraba. Napoli ta fara cin kwallo a minti na biyar da fara wasa ta hannun Piotr Zielinski a bugun fenarity. A minti na 18 Victor Osimhen ya buga fenariti amma bai ci kwallo ba, daga baya Andre Zambo Anguissa' ya ci na biyu. Daf da za a je hutu ne Napoli ta kara na uku ta hannun Giovanni Simeone ya kara na uku, sannan Piotr Zielinski ya ci na hudu kuma na biyu a wasan. Liverpool ta zare daya ta hannun Luis Diaz. Kungiyar Anfield ta kai wwasan karshe a kakar da ta wuce a Champions League, inda Real Madrid ta yi nasara da ci 1-0 a Faransa. Hakan ne ya sa kungiyar Sifaniya ta lashe kofin zakarun Turai na 14 jumulla, ba wadda ta lashe kofin da yawa kamarta. Wasannin da Klopp ya ja ragama a kakar bana Community Shield Asabar 30 ga watan Yuli Premier League Asabar 6 ga watan Agusta Premier League Litinin 15 ga watan Agusta Premier League Litinin 22 ga watan Agusta Premier League Asabar 27 ga watan Agusta Premier League Laraba 31 ga watan Agusta Premier League Asabar 3 ga watan Satumba Champions League Laraba 7 ga watan Satumba Ranar 10 ga watan Satumba Liverpool za ta karbi bakuncin Wolverhampton a gasar Premier League. Daga nan ta karbi bakuncin Ajax a wwasa na biyu a Champions League a cikin rukuni ranar Talata 13 ga watan Satumba. https://www.bbc.com/hausa/articles/c3g4vgxdw79o +health Abin da janye tallafin jinƙai da Birtaniya ke shirin yi ke nufi ga wani asibitin Sudan ta Kudu "Gwamnatin Birtaniya ta ce za ta daina bayar da agaji ga asibitocin jihohi tara a Sudan ta Kudu daga ranar 1 ga watan Agusta, lamarin da ke kara haifar da fargabar cewa matakin zai kara gurgunta tsarin kiwon lafiyar da dama can yana cikin wani hali. Wakiliyar BBC Catherine Byaruhanga ta je daya daga cikin asibitocin da lamarin ya shafa domin ganin ko wane irin bambanci yanke ba da tallafin zai haifar. Marasa lafiya na kwance a gadajen marasa galihu suna lullube kansu da wata guntuwar rigar gargajiya, wadda aka fi sani da kitenge. Ganin yadda asibitin ya lalace, da mamaki yadda komai ya sauya tun daga 1964. Amma a cikin shekaru hudu da suka gabata an dan samu ci gaba. Dr Dut Pioth ya zama likita na farko a Sudan ta Kudu da aka tura wurin. Yayin da yake jagorantarmu zagayen duba yadda abubuwa ke tafiya a sashen tiyata, Dr Pioth ya ce: “Lokacin da nake aiki a matsayin likita, na san cewa akwai majinyata da yawa da suka rasa rayukansu saboda babu wani likitan fiɗa da zai yi ƙoƙarin taimaka musu” An haifi Dakta Pioth a Aweil ta arewa, da ke arewacin Bahr el Ghazal, ya samu horon zama babban likitan fida a Juba, babban birnin kasar, sannan ya dawo don taimaka wa al’umarsa. Har yanzu dai wannan shi ne asibiti daya tilo a jihar da ke da mutane miliyan daya da dubu dari uku, kuma Dakta Pioth ne kawai likitan fida na gwamnati da aka dauka don gudanar da ayyukan gaggawa. Yanzu dai ya fuskanci matakin da ba zai taba yiwuwa ba na ko dai ya tafi, saboda za a yanke tallafin da Birtaniya ke bayarwa a asibitin, wanda ke nufin ya yi asarar kusan dukkan kudaden shigarsa. Sudan ta Kudu ta samu ‘yancin kai daga Sudan a shekara ta 2011 kuma tun daga shekarar 2012, kasar Birtaniya ke gudanar da asusun kula da lafiyar kasar HPF don tallafa wa kanana da manyan cibiyoyin kiwon lafiya a kasar. Tana samun ƙarin tallafi daga sauran masu ba da gudummawa kamar Tarayyar Turai EU, da Kanada da Amurka da Sweden. Bayan shawarar da gwamnatin Birtaniya ta yanke a shekarar 2020 ta rage kasafin tallafinta daga kashi 0.7 na yawan kudin shiga na kasa zuwa kashi 0.5 an rage yawan shirye-shirye a duniya. A Sudan ta Kudu, HPF, wacce ke ba da magunguna, da kayan aiki da kuma bayar da gudummawa wajen biyan albashi, na shirin yanke tallafi ga asibitocin jihohi tara nan da 1 ga watan Agusta, ciki har da na Aweil. Data Pioth yana samun dala 1,700 kowane wata daga HPF yayin da gwamnatin Sudan ta Kudu ke biyansa dala biyar kacal, ba zai iya ci gaba da tallafa wa matarsa ​​da ’ya’yansa ba da zarar wannan matakin ya fara aiki. “Idan ba na nan, galibin majinyata musamman ma masu fama da larurar gaggawa za su sha wahala. Zan iya yi wa mutum 50 tiyatar gaggawa sannan in yi 70 wadda ba ta gaggawa ba, don haka ban san me zai faru ba idan na tafi’’. “Ban san wanne mataki zan dauka ba,” in ji dakta Pioth, yana magana idonsa ya yi ja. Asibitin farar hula na Aweil ya sami jigilar magunguna na karshe daga HPF a watan Yuni, kuma Jackson Atak, majinyaci mai ciwon kafa, ya ce yanzu dole ne ya rika sayen magani da kudinsa. Kasar Birtaniya ta fara janye tallafin jin kai kan lafiya da take ba wa Sudan ta Kudu a watan Afrilun bana. Fiye da ƙananan cibiyoyin kula da lafiya 200 sun rasa kuɗinsu, kuma ana jin tasirin hakan. Na yi tukin sa’o’i biyu a arewacin garin Aweil duk da laka a manyan titunan zuwa iyakar Sudan ta Kudu da Sudan, inda na isa wata cibiyar lafiya ta Manyiel. Daraktan lafiya na gundumar, Joseph Atem, ya yi mini jagora zuwa ofis ɗin da ke cike da kura kuma zuwa wurin da ake ba da magunguna a baya. Yayin da muke buɗe tagogin, muna iya jin ƙarar jemagu. Saboda janye tallafin na HPF, babu komai a cikin kwalayen magungunan, sai wasu tsirarun magungunan rigakafi, da na zazzabi da ruwan gishiri da suga. Asibitocin haihuwa ma da alama na cikin wani yanayi mafi muni, don hatta gadajen ma sun yin duƙun-duƙun. Dakta Atem ya gaya mani ma’aikacin Lafiyar da ke kula da asibitin ya bar wajen, lokacin da HPF ta daina biyansa. A kan hanya, na ziyarci Angelina Akuec wata ungozoma. Daya daga cikin wadanda take yi wa aiki Mary Adua ’yar shekara 27 na tare da mu, tare muka sunkuya muka shiga bukkar Akuec. Ta riƙe wani ƙarfe na gargajiya a cikin Adua don sauraron bugun zuciyar jaririn sannan ta yi amfani da hannayenta don jin halin da jaririn ke ciki. Duk cikinsu ba su san tsawon lokacin da Adua ta kwashe da fara nakuda ba, amma ungozomar na tunanin ta zo nan ba da jimawa ba. ""Asibitoci basu da kayan aiki, yin gwajin ciki na da matukar wahala, haka kuma, a lokacin nakuda ya fi muni saboda asibitoci masu kyau sun yi nisa daga inda nake sauka,"" inji Adua. To, ko me gwamnatin Sudan ta Kudu take yi game da wannan kalubale? Tuni dai ake zargin shugabannin da ke babban birnin kasar da yin sakaci sosai bayan yakin basasar da aka kwashe shekaru biyar ana yi wanda ya durkusar da kasar. Kuma a yanzu bayan cin hanci da rashawa, da tabarbarewar tattalin arziki, babu kudi a asusun gwamnati. Sabon ministan lafiya Yolanda Awel ya ce har yanzu kasar na bukatar taimako. ""Gwamnatin Sudan ta Kudu na son inganta fannin lafiyar, kuma ta fara shirin yin hakan, ta hanyar samar da kudade,"" in ji Awel daga babban ofishinta da ke Juba. ""Za mu yi hakan ne ta hanyar kula da yawancin cibiyoyin kiwon lafiyar mu amma har yanzu muna bukatar taimako’’. Mun tura sakamakon rahotonmu da tasirin da muka gani na rage kudaden zuwa Ofishin Harkokin Waje na Birtaniya. Wani mai magana da yawunsa ya shaidawa BBC cewa ""Birtaniya na ci gaba da kasancewa daya daga cikin manyan masu bayar da agaji a Sudan ta Kudu kuma a bana asusun kiwon lafiya mai samun goyon bayan Burtaniya zai tallafa wa cibiyoyin kiwon lafiya 577 a fadin kasar."" Da muka koma asibitin Aweil, Dakta Pioth bai yanke shawarar ya zauna, ko ya tafi neman wani aiki ba, amma yana fatan gwamnatin Birtaniya ba za ta rage kudaden ba. ""Waɗannan mutanen suna buƙatar taimakonsu da gaske, suna buƙatar taimakonsu da yawa. Ba mu da ƙarfin da za mu zauna mu kaɗai,"" in ji shi." https://www.bbc.com/hausa/articles/c90lqn5y7w9o +politics Peter Obi: 'Ba na son a zabe ni don na fito yankin Kudu maso Gabas' Danna hoton da ke sama don kallon bidiyon: Dan takarar shugaban Najeriya a Jam'iyyar Labour Peter Obi, ya ce ba ya so mutane su zabe shi domin ya fito daga yankin Kudu maso Gabashin kasar. A wata hira ta musamman da ya yi da BBC, Mista Obi ya ce ya tsaya takara ne domin shi dan Najeriya ne mai 'yancin yin hakan. Haka kuma ya yi tsokaci kan batun magoya bayansa da ke cin mutuncin mutane a shafukan sada zumunta, inda ya ce yawancin su ba masoyansa na tsakani da Allah ba ne. Yin hirar da daukar bidiyo da tacewa: Abdulbaki Aliyu Jari https://www.bbc.com/hausa/media-62120700 +health Mutum ya yanke ƴaƴan marenansa cikin barci Wani manomi a Ghana yana can kwance a asibiti cikin wani mawuyacin hali bayan da ya yanke marenansa (golaye ko kwalatai) a lokacin da yake barci. Mutumin mai suna Kofi Atta, wanda a gadon asibitin da yake ya gaya wa BBC yadda lamarin ya faru, yana can ana ƙoƙarin duba yadda za a yi masa aiki. Ya ce a yanzu dai ana sa masa ƙarin ruwa ne tare da wasu allurai da ake ta yi masa, amma dai sai an yi masa tiyata. Sai dai ya ƙara da cewa a yanzu ba shi da ko kudin da zai biya motar asibitin da za ta dauke shi zuwa babban asibitin koyarwa na Komfo Anokye, da ke Kumasi a kasar ta Ghana inda a can ne za a iya yi masa tiyata. Mutumin ya ce, yana barci ne na ƙailula wato da rana a kan wata kujera sai ya yi mafarki cewa yana yanka nama da ke ajiye a gabansa, wanda zai dafa abinci da shi, inda a cikin barcin ya janyo wuka ya yanke marenan nasa. Mista Atta ya ce abin ya ba shi mamaki ƙwarai domin har lokacin da wasu maƙwabtansa biyu suka kawo masa agaji bai san me ya faru ba, sai da ya tashi daga kan kujerar ya riƙa jin wani zafi a gabansa ga kuma jini na zuba. Mutumin ya ce, har lokacin da aka kawo masa daukin ba shi tabbacin kan abin da ya faru, ji yake kamar yana mafarki ne. Ya ce shi kansa bai san yadda aka yi ya dauko wuƙar ba ma, ''abin ya ɗaure min kai, '' in ji shi. Manomin mai shekara 47 wanda ke garin Assim Akomfode a yankin tsakiyar kasar (Central Region), har bayan da ya yanke marenan nasa yana cikin barci har ya yi kururuwar neman taimako bai farka ba yana cikin mafarki ne domin shi duk bai san abin da ya faru ba a lokacin. Ya ce duk da cewa maƙwabtansa sun kawo masa dauki inda ya riƙa jin zafi a gabansa ga kuma jini yana zuba, bai fahimci abin da ya faru ba, sai daga baya a gadon asibiti hankalinsa ya dawo ya san abin da ya faru. A fagen ilimin kula da lafiya, akwai wata larura wadda ake kira Parasomnia a harshen Ingilishi, inda mutum kan aikata wasu abubuwa saɓanin na hankali a lokacin da yake barci. Wannan larura takan sa mutum ya rika tafiya ko maganganu ko fitsarin kwance ko mugun mafarki ko ƙiƙƙifta ido da dai sauran abubuwa na daban a lokacin da yake barcin. A lokacin da mutum yake cikin wannan hali wasu da ke tare da shi ko kusa da shi za su ga kamar ba barci yake ba yana farke ne, to amma yana cikin yanayi ne na barci bai san abin da yake yi ba. Mutanen da ke cikin wannan yanayi ba ma sa iya tuna abin da ya faru da su ko abin da suka aikata a lokacin da suke cikin halin. Bayanai sun nuna cewa abin da mutum kan yi a wannan lokacin kamar yana aikata abin da mafarkinsa ya kunsa ne a zahiri. https://www.bbc.com/hausa/articles/ck5np5wjly2o +business COP27: Wata mashiya a Kenya ta bukaci a mayar da hankali kan Afirka "Matasa da ke fafutukar kare muhalli a Kenya irin su Elizabeth Wathuti suna fatan taron da ake yi kan sauyin yanayi na COP27 a kasar Masar zai ""yi adalci"" ga mutanen da suke fama da tasirin sauyin yanayi. Nahiyar Afirka ta yi fama da matsalolin sauyin yanayi a kwanakin baya bayan nan - kamar tsananin zafi da fari. Ta ce ""Kowa yana kiran taron da suna COP na Afirka saboda yana faruwa a nahiyar, sai dai ya kamata a kira shi da wannan suna ne saboda bukatar nahiyar Afirka ita ce ta kamata a fi mayar da hankali a kanta wajen daukar mataki""." https://www.bbc.com/hausa/articles/cxw0w482r3wo +entertainment Mulki ya zo ƙarshe, shekaru 70 ba tare da gajiyawa ba "Tambari zai tsaya cak na minti biyu, masu busa sarewar masarauta za su yi shiru, za a ci gaba da tafiya da basarakiyar har zuwa kushewarta. A yau Litinin din nan, komai zai tsaya cak babu motsin komai da zarar an kawo karshen addu'o'i a Westminster Abbey, kafin a rera taken kasa, a dauke akwatin gawar zuwa kushewar karshe da za a binne ta a Fadar Windsor, shiru zai ci gaba da yin jagora. Shi kenan, zamanin Sarauniya ya zo karshe, komai ya tsaya kuma sauyi zai maye gurbin abin da aka baro a baya. Zamanin mulkin shekaru 70 ya zo karshe, an rufe wannan babin. Kusan kwanaki 10 babu abin da muke yi sai batun Sarauniya, da sabon sarki, tamkar duka biyun za su ci gaba da kasancewa da mu a raye. A yau mun kawo wannan makon mai tsawo, wannan makon mai cike da tashin hankali da damuwa. A farkon fara sarauta, an bude babin mulkin Elizabeth tun tana karama, ta zama mai jiran gado. Lamari ne mai cike da zakwadi da jin dadi ga matashiyar sarauniyar, ta ga yadda zamani ya dinga sauyawa har zuwa zamanin fasaha. Matashiyar da tana cikin kuruciya akai yakin duniya na biyu, ta kuma yi sadaukarwa a lokacin, tashin hankali da bakin cikin da suka biyo bayan shekarun yaki. Komai ya yi farko yana da karshe, zamanin Elizabeth ya zo karshe, an rufe littafinta, sai dai a tarihi. Tana nan daram-dam, a gwamman shekarun da aka dauka zamani na sauyawa, a kasa ra'ayin 'yan mazan jiya. Sannu a hankali, za a daina ganin suna da hotonta a jikin muhimman abu kamar tambari, an daina jin muryar nan mai dadin sauraro lokacion aikawa da sakon murnar bikin Kirsimeti, babu mai sunkuyar da kai kasa a ranakun Lahadi lokacin addu'a. Sannu a hankali, a yau Litinin an rufe dukkan kofofin. Sun kuma bude ga Yarima Charles, da ya shafe sama da rabin shekarunsa a matsayin Yariman Wales. Wadanda ke aiki da shi na masa kallon mutumin da ya kai kololuwar cancanta, ta fuskar nasarar da ya yi a ayyukan da ya sanya gaba, ciki har da na jin kai, ya dauki shekaru masu yawa yana ginin rayuwar da ta riske shi. Kalubalen farko da zai fara fuskanta bayan an gama zaman makokishi ne yadda zai nuna yana jin dadin aikin da yake yi, yana kuma jin dadi sarautar. Mahaifiyarsa ta gane komai game da aikin, aikin sadaukarwa ne ga al’umma, a sama wa jama’a sassaucin rayuwa, korafin ‘yan uwa, masu dadi da marasa dadi, rayuwar dai babu yabo babu fallasa. Za a so ganin ya taka irin rawar da ya yi a lokacinsa na Yarima mai jiran gado, sauye-sauyen da ya kawo, nauyi ne mai girma da ya hau kansa. A yanzu kofa ta rufe a matsayin shin a Yariman Whales, a yanzu wata babba ce ta bude ta matsayin sarki mai cike da karfin iko. Birtaniya za su so ganin jajirtaccen mutuum a matsayin mai haska musu fitilar rayuwa. Yayin da shiru ya ziyarci duk wata kusurwa, lungu da sakon babban dakin taro na Westminster, kofa ta rufe, zamanin mulkin Sarauniya Elizabeth, ya zo karshe wadda ta yi fice da tambari a duniya, ita kuma ba duka ta sani ba. Wannan shi ne ya kawo karshen zamanin mulkin wannan yarinya, da lokacin ta na karama babu wanda ya yi zaton za ta kawo wannan matsayi, abinda kawai aka sani shi ne yarinya Lilebet, mafi soyuwa ga kakanta. Cikin shiri na musamman na BBC mai suna The Unseen Queen a Turance, ina dauke da hotuna da bidiyon rayuwar iyalan da ba a taba gani a waje ba. Akwai hotunan matashiyar Gimbiya Lilibet, wasanni, tsokana, da zolaya har da rawar da take yi. Fararen idanunta cike da fara’a. Cike da soyayya, ga mahaifinta, sarkin da ya mutu da wuri, da mijinta Yarima Philip, wanda ya zame mata katanga kuma bango a dukkan lamuranta, ya sadaukar da komai nasa, ya yi gwamman shekaru tare da ita, bai taba kaucewa daga inda take ba har sai da wa’adi ya riske shi. Makonnin da suka wuce, sun zama tamkar tunatarwa ga masoya, da ‘yan uwa, da abokan arziki, da makusanta, da wadanda suka san dukkan sirrinta, kan cewa duk shekarun da ta yi, babu abinda ya sauya Lilibet daga yadda take da kuruciya, dariyarta, tsokanar fada, murmushi, sadaukarwa da farin ciki. Ta yi tsokaci akan shirin talbijin din na musamman. ""Ko da yaushe kuna fatan matasan zamani za su ji dadi da mishadantuwa,"" tsokacinta game da fim din iyalanta. ""Watakil su yi mamakin ganin ashe ni ma matashiya ce a wani zamani da ya shude"". Ka da wani ya yi mamaki. Saboda a watannin karshe na rayuwarta, wannan matashiyar Elizabeth din, Lilibet mai tsokanar fada da wasa da faran-faran, ta sake bayyana a tattare da dattijuwar sarauniyar, tana wasa da zolaya cikin mutane, da kallon nan na kuruciya, fito da mamalade da ake nade biredi da shi, daga cikin jakarta a lokacin bikin shekara 70 da hawa mulkinta. A yanzu an rufe jakar. Komai ya zama tarihi. Babu abin da ya yi saura, sai dai a tuna da lokutan da suka shude. A yau Litinin an rufe duk wata kafa, an rufe kofar zamanin mulkin Sarauniya Elizabeth ta II." https://www.bbc.com/hausa/articles/c1eq0y7ed3ko +politics 'APC ta riga ta tsorata da PDP' Wani jigo a cikin dattawan babbar jam'iyyar hammayya a Najeriya, PDP Alhaji Adamu Maina Waziri ya ce jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta tsorata dan takarar da suka fitar shi ya sa take kwan-gaba-kwan-baya wajen fitar da dan takararta na zaben 2023. A hirarsa da BBC Alhaji Maina Waziri ya yi zargin cewa tun da farko ma APC ce ta yi manakisa har hukumar zaben kasar t kara wa'adin sati daya na zaben fitar da dan takara bayan su sun riga sun shirya gudanar da zabensu a lokacin. Tuni dai babbar jam`iyyar hamayyar ta PDP ta yi nata zaben, inda tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar ya yi nasarar samun takarar shugaban kasar. Jigon ya ce abin da PDP ta yi na fitar da dn takararta ya ba wa abokan hamayyar tasu mamaki, yadda suka hada kai su ka yi wannan zabe. Kuma wannan nasara da Atikun ya samu, kamar yadda masana siyasa ke cewa ka iya wargaza lissafin jam`iyyar APC, lamarin d masanan ke ganin alamunsa yadda ake ta ki ruwa rana a yanzu kan yadda jam'iyyar za ta kai ga fitar da dan takarar. Wannan ya sa hankali ya koma kan  jam`iyyar APC mai mulki don ganin yadda zaben fitar da gwani na masu neman takarar shugaban kasa zai kaya. A ranar  Litinin mai zuwa ne ake sa ran gudanar da zaben fitar da gwanin. Dattijon na PDP ya ce, yanzu APC ta shiga tsaka mi wuya kan yadda a ta bullowa lamarin fitr da dan takarar da zai kara da nasu a babban zaben, inda yake cewa, '' Duk wanda yake kasar nan ya san cewa ana kwan-gaba-kwan-baya, yaya za su yi su fitar dan takara ba za su iya yi ba, wallahi muna jiransu, wallahi ina gaya maka mu ba ma yanzu fargaba, mutanen nan sun nuna ragwanci don sun firgita mun yi abin da ba su taba tsammani ba.'' Ya kara da cewa, fatansu yanzu shi ne ita kanta APC ta samu nasarar fitar da dan takararta lami lafiya, '' yanzu su muke jira kuma muna addu'a su yi taronsu lafiya, don rashin zamansu lafiya zai iya kawo rashin zaman lafiya a kasar nan,'' in ji shi. Alhaji Maina Waziri ya ce, kishin arewacin kasar da kuma burin kare martabarta ne ya sa a lokacin zaben fitar da gwaninsu, ya sa gwamnan jihar Sokoto Alhaji Aminu Tambuwal ya janye tare da mara wa Atiku baya ya yi nasara. Ya ce sun lura cewa wani daga daya bngaren kasar na kudu ya yunkuro zai yi amfani da kudi a zaben ya yi nasar wanda hakan ba karamar illa zai yi ga arewacin Najeriya ba. Saboda haka ne Aminu Tambuwal ya nuna kishi da jarintaka ya janye a wannan takara domin hada kai da Atiku Abubakar, wanda hakan ba karamin alfanu ba ne ga yankin arewacin Najeriya. https://www.bbc.com/hausa/labarai-61688448 +entertainment Kaunar da Philip yake yi wa harkar gandun daji "Namun Daji da kiwonsu wani fanni ne da Maimartaba Duke na Edinburgh yake sha'awa a rayuwarsa. Ana shirya masa yawon shakatawa irin na gidan sarauta, don taimaka masa ya cika burinsa na sha'awar Gandun Daji, ciki har da ziyara a yankin Antartic wanda ya ba shi damar yin ido-hudu da namun daji. Amma tun da farko ya san irin hadarin da wasu namun dajin ke da shi ga Dan'adam. ''Mutum ne mai sha'awar kiwon namun daji tun kafin kiwon ya shahara ko ma ya zama abin sha'awa a duniya.'' A cewar tsohon Shugaban Kungiyar Masu Kare namun daji ta Duniya, Charles Secrett. ''Muhimmin batun shi ne, ya sa mutane sun mai da hankali wajen sanin matsalolin da namun daji ke fuskanta, musaman ma na barazanar karar da su a doron kasa da kuma lalata musu muhalli.'' Yarima Philip ya zama kamar wani mutum da Allah ya hallito domin ya zama shugaban Gidauniyar Kula da Namun Daji ta Duniya, kamar yadda ake kiranta a wancan lokaci. Ya yi amfani da kaunar da yake yi wa namun daji wajen cin nasarar manufofin kungiyar, kamar shirin ceton rayuwar dabbar nan da ake kira ''Panda''a Turance. A cewar Maimartaba Duke, kare rayuwar dabbobi irin Panda batu ne daraja nau'o'in halittu, ba wai kare rayuwar wata dabba guda daya ba. Ya taba cewa''A gani na abin sha'awa ne matuka a ce akwai halittu daban-daban masu ban sha'awa a doron kasa, wadanda rayuwarsu ke amfanarmu sannan kuma tamu take amfanar su.''Ya kara da cewa ''Ina tsammanin da ace mu mutane muna da ikon kashewa da rayawa, ya kamata mu yi aiki da hankali wajen kisan da rayarwar. Don haka mai zai sa mu karar da wasu dabbobi idan babu bukatar yin hakan.'' Ko da yake a da can akan kashe namun daji da sunan farauta. Wata rana sun fita rangadi shi da sarauniya sai ya harbi wata damisa har ta mutu. Daukar hoton damisar da aka yi a lokacin sai da ya haifar masa da matsala a Kungiyar kare halittun daji ta Duniya. Damisa a yanzu na fuskantar hadarin karewa a doron kasa, amma a wancan lokaci ba haka abin yake ba. ""Wannan batu na kisan damisa na daya daga cikin abin da Yarima Philip takaicin aikatawa a tarihin rayuwarsa"" in ji Mr. Secrett. ""Amma fa cikin shekarun 1960 Al'amura sun sauya."" Bayan shekarun 1960, farautar namun daji ta zama babban batu a Birtaniya, kuma an halattata a Ingila da Scotland da Wales. A wancan lokaci Yarima Philip ya goyi bayan Kungiyar 'yan farauta, batun da ya haifar da bacin rai a zukatan masu rajin kare hakkin namun daji na duniya. Ya fito fili ya kare ra'ayinsa, inda ya ce; A gani na ba laifi ba ne ga mafarauta su yi farautar dabbobin daji da suka tsufa, matukar an bar kanana da matasa domin su cigaba da hayayyafa, kmara dai manomi ne ''Kana noma kana girbi, kuma kana tanadin iri don gobe.'' Amma a sauran batutuwan da suka shafi gandun daji, Yarima ya samu fahimtar juna tsakaninsa da kusan dukkanin asu fafutukar kare namun daji. Tun daga wannan lokaci ne makomar namun daji a duniya ta samu kariya, bayan da aka canjawa kungiyar suna zuwa Gidauniyar Kare Halittun Daji ta Duniya, wato WWF a takaice. A halin yanzu, babban abin da aka sa a gaba shi ne, yadda gwamnatoci za su shiga cikin shirin, musamman ma kasashe masu tasowa, don su rattaba hannu akan yarjejeniyar cigaba mai dorewa. ''Idan komai ya tafi yadda ya kamata, ba laifi ba ne ace gwamnatoci su zo sub a da kudin gudanar da wannan aiki'' In ji Mai martaba Duke. ''Ina ganin dayawa daga cikinsu ba za su zo su tafi hakannan ba tare da sun bad a wani tallafi ba, musamman ma dai idan sun amince sun rattaba hannu akan yarjejeniyar da wuya su ce a'a.'' Halin da tekunan duniya ke ciki da kuma kamun kifi da ake yi wanda ya wuce ka'ida na daga cikin matsaloli na karshe a bangaren muhalli da Yarima yake son a magance su a karkashin wannan Gidauniya. Sai dai kafin a fara shirin magance matsalolin, ya yi ritaya, bayan shekaru 20 da ya yi a matsayin shugaban Kungiyar. Duk da cewa Yarima ya kai shekarunsa na yin ritaya daga kungiyar, an cigaba da damawa da shi a harkokin kungiyar, kuma ya cigaba da aiki kamar yadda aka san shi. Kamar yadda Mista Secrett ya ce'' Yarima yana fadin ra'ayinsa gaba-gadi, yana tsage gaskiya komai dacinta, akan abin day a yi imani gaskiya ne, ba tare da la'akari daw a yake sauraronsa ko kasaitar wanda yake Magana da shi ba, ko me sakamakon hakan zai haifar kuwa.'' ''Ko da ba a samu fahimtar juna ba, babbar nasara ce ga mutum ya yi gamsasshen bayani akan gaskiya da adalci.'' Babban abin da Gidauniyar Kare Gandun Daji ta fi yin kewa game da rashin Yarima shi ne, dagewa da jajircewarsa akan dukkanin abin da ya sa a gaba." https://www.bbc.com/hausa/labarai-47256082 +religion Rashin hukunta sojojin da ake zargi da kashe Sheikh Aisami na damun mu – Iyalan marigayin "Iyalan malamin addinin Musuluncin nan da aka yi wa kisan gilla a jihar Yobe da ke arewacin Najeriya, Sheikh Goni Aisami, sun bayyana damuwarsu ga yadda suka ce har yanzu ba a gurfanar da wadanda ake zargi da kashe shi a gaban kotu ba kusan kwana hamsin da faruwar lamarin. Wani soja ne da malamin ya rage wa hanya ake zargi da harbe shi domin ya sace motarsa yayin da malamin ke kan hanya daga Kano zuwa Gashua. Sai dai hukumomi sun ce nan ba da jimawa ba za a soma shari’ar gadan-gadan. Ɗaya daga cikin iyalan marigayin ya ce ba su ga dalilin da zai sa a yi tsaiko wajen hukunta waɗanda ake zargi. Abdullahi Goni Aisami ya ce sun shiga tashin hankali saboda rashin jin wata hujja daga hukumomi kan abin da ya sa aka ƙi hukunta mutanen. ""Muna cikin baƙin ciki da takaici, su daga ɓangaren matan malam, hankalinsu ya fi na kowa tashi saboda suna ganin kamar an ma ƙi yin hukuncin ne haka kawai,” in ji shi. Daga ɓangaren hukuma kuwa, kakakin rundunar 'ƴan sanda na jihar Yobe, DSP Dungus Abdulkareem ya ce bayan sun gama bincike suka tura wa hukumar shari'a ta jihar domin tabbatar da cewa an gurfanar da waɗannan sojoji guda biyu gaban kotu. ""An yi nasarar haka, inda ranar 19 ga watan Satumba aka gabatar da su a gaban kotu, kuma kwamishina da kansa ya zama lauya mai gabatar da ƙara na gwamnati,"" a cewarsa. ""Ya gabatar da hujjojinsa da shaidunsa gaba ɗaya a gaban kotu inda waɗanda ake zargi suka ce su ba su da laifi, sannan aka tsaya daga nan aka rufe ƙarar, za a sake sauraron shari'ar a zama na biyu.” DSP Dungus ya ƙara da cewa lokacin da aka yi zaman shari'ar kotunan Najeriya suna hutu, kuma ""muna tunanin idan sun dawo hutu, za su gaya mana ranar da za a sake dawo da sojojin zuwa kotun." https://www.bbc.com/hausa/articles/cpey31kpzlqo +sports FA ta tuhumi Ronaldo kan fasa wa dan kallo waya "Hukumar FA ta ingila ta ci rarar dan wasan gaban Manchester United Cristiano Ronaldo kan hoton bidiyon da aka ganshi ya kwala wayar wani magoyin baya da kasa. Bidiyon an ta yada shi a kafafen sada zumunta an ikirarin cewa ya buga wayar ne a kasa bayan fita daga filin wasa bayan kashin da suka sha a hannun Everton da ci 1-0 a watan Afrilu. Ronaldo mai shekara 37 daga baya ya nemi afuwar magoyin bayan a kafafen sada zumunta. A watan Agusta kuma 'yan sanda suka ja masa kunne. ""An yi zargin halayyar da dan wasan gaban ya nuna bayan an tashi daga wasan ba ta dace ba,"" in ji FA. Manchester United ta ce za ta goyi bayan Ronaldo a matakin da zai dauka kan tuhumar." https://www.bbc.com/hausa/articles/ckrzp9grg2jo +business Jeff Bezos: Abin da ya sa mai kuɗin duniya zai sauka daga shugabancin Amazon "Wanda ya kafa katafaren kamfanin sayar da kayan nan a shafin intanet Amazon a shekara 30 da suka gabata Jeff Bezos, zai sauka daga muƙaminsa na jagoran kamfanin. Zai koma ya zama shugaba mai cikakken iko, matakin da ya ce zai ba shi ""lokaci da karsashi"" wajen mayar da hankali kan sauran ayyuka. Andy Jassy, wanda ke jagorantar bangaren kasuwancin na'urori masu ƙwaƙwalwa da shafin yanar gizo na kamfanin ne zai maye gurbin Mr Bezos. Za a samu sauyin ne a tsakiyar shekarar 2021, in ji kamfanin. ""A matsayina na babban jagoran kamfanin Amazon, jan aiki ne kuma mai cinye lokaci. Idan kana da gagarumin daukar nauyi irin wannan, yana da wahala ka mayar da hankalinka kan wani abu daban,'' kamar Mr Bezos ya bayyana a cikin wata wasika da ya rubuta wa ma'aikatan kamfanin na Amazon ranar Talata. ""Shugaba mai cikakken iko zan kasance ina gudanar da aikina a bangaren muhimman yunkurin ayyukan Amazon, amma zan kuma samu lokacin karsashin da nake bukata don mayar da hankali kan ayyukan da nake begen yi kamar su ''Day 1 Fund'', da ''Bezos ""Ban taba samun karin karsashi ba, kuma ba wai game da yin murabus bane, Ina matukar kaunar ganin ci gaban da nake ganin kamfanin zai kara samu,'' ya kara cewa. Shahara a shafukan sada zumunta Mr Bezos, mai shekaru 57, ya jagoranci kamfanin na Amazon tun bayan kafa shi a matsayin kantin sayar da litattafai ta shafin yanar gizo a shekarar 1994. Yanzu kamfanin na da ma'aikata miliyan daya da dubu dari uku a fadin duniya, kuma suna gudanar da ayyukan rarraba rarraba kayyaki ga wadanda suka saya daga kamfanin, da tallace-tallace da tsara faye-fayen bidiyo da sauransu. Ya samu gagarumin nasibin dala biliyan dari da casa'in da shida da miliyam dari biyu, kamar yadda hukumar tantance jerin sunayen attajiran duniya Forbes ta bayyana. Kamfanin ya riga ya shaida babbar bunkasa a shekarar da ta gabata, yayin da annobar korona ta haifar da yawan sayen kaya da shafukan intanet. Kamfanin ya bayyana samun ribar dala biliyan dari uku da tamanin da shida ($386bn) kwatankwacin fan biliyan dari biyu da tamanin da uku (£283bn) a cinikinsa na shekarar 2020, karin kasha 38 bisa dari (38%) daga shekarar 2019. Ribar ta kusan linkawa, bayan da ta hau zuwa dala biliyan ashirin da daya da miliyan dari uku. Yayin da yake sanar da tsare-tsaren, Mr Bezos ya ce zai cigaba da mayar da hankali kan sabbin kayyaki da kuma yunkuri. ""Idan kuma duba sakamako game da kudaden shigarmu, abin da za ka ainihin gani su ne sakamakon da suka tattaru na abubuwan da muka ƙirƙira. Yanzu haka ina kallon Amazon a matsayin kamfani mafi shahara da kirkira,"" in ji shi. Sauye-sauyen na zuwa ne yayin da Mr Bezos ya kara zama sananne a shafukan sada zumunta. Ya fuskanci takun-saka da masu fafutikar kan nuna daidaito da kare hakkin ma'aikata, kana ya zuba dukiyarsa cikin wasu harkokin kasuwanci kamar na kamfanin ayyukan binciken sararin samaniya 'Blue Origin' da kuma jaridar 'Washington Post'. Amazon ya kuma fuskanci karuwar yawan bincike daga hukumomin sa-ido kan kauwanci, wadanda ke tuhumar karfin ikon mamaye kasuwanni da kamfanin ya yi, da suka hada da na bangaren na'urori masu kwakwalwa da sauran kamfanonin fasahar kere-kere kamar su Microsoft da Alphabet jigo da kamfanonin Google da YouTube ke kalubalantarsa. Matakin da Mr Bezos ya dauka na mika ragamar ayyukan yau da kullum na kamfanin ya zo da mamaki. Amma kuma da alamu masu zuba jari ba su nuna damuwa ba, yayin da aka dan samu sauyi a farashin zuba jari a kamfanin bayan wasu sa'o'i na hulɗar cinikayya. Yayin wani kira ga masu sharhi don tattaunawa kan sakamakon cinikin kamfanin, babban jami'in harkokin kudi na Amazon din Brian Olsavsky ya ce: ""Jeff ba wai zai bar kamfanin ba ne, zai kama sabon aiki ne… babban aiki ne mai matukar muhimmanci a cikin jerin a fannin bunkasar ayyukan na Amazon.'' Mr Jassy, ya kammala karatu daga Jami'ar Harvard, kuma tun a shekarar 1997 ya fara aiki da Amazon, kuma ya taimaka wajen kirkiro shafin yanar gizo na ayyukan kamfanin, wanda aka dade ana yi wa kallon wani babban tushen samun ribar kamfanin. ""Andy sananne ne a cikin kamfanin, kuma kamar yadda na dade, haka shima ya dade a kamfanin. Za kasance shugaba nigari, kuma na matukar yarda da aikinsa,'' in ji Mr Bezos. Sophie Lund-Yates, wata mai yin sharhi ce a Hargreaves Lansdown, ta kuma ce '' babu mamaki'' cewa Amazon ya zabi shugaban bangaren ayyukansa na na'urori masu kwakwalwa ya jagoranci kamfanin. Wannan babban abin mamaki ne. Amma dole a tuna cewa shi kansa Jeff Bezos na da kimanin kusan dala biliyan dari biyu ($200bn). Kuma muddin kana da irin wannan arziki, ka tuna abinda za ka iya yi. Jeff Bezos yana da buri da yawa da ya wuce cikin Amazon. Kamafinsa na Blue Origin na son ''gina hanya zuwa sararin samaniya''. Ya kuma zuba dala biliyan goma ($10bn) cikin ayyukan 'Earth Fund', da aka kafa don taimakawa wajen shawo kan matsalar sauyin yanayi. Af, yana kuma da kamfanin jaridar Washington Post. Ta yaya Amazon zai jure? Amma dai, abu mafi muhimmanci, ba wai zai bar kamfanin bane. A matsayinsa na sugaban mai cikakken iko kuma wanda ya kafa kamfanin, har yanzu yana da karfin fada a ji a kamfanin. Amma kuma, janyewarsa zai iya kasancewa rashin karfin fada a jin. Wanda zai maye gurbinsa - Andy Jassy - ya dade yana jagorantar katafaren bangaren ayyukan yanar gizo. Karin girman da ya samu na nuni da yadda yake da tasiri wajen harkokin kasuwancin kamfanin na Amazon. A bara ne daya babban jami'in, Jeff Wilke, wanda ya jagoranci bangaren hulɗa da masu sayen kaya na kamfanin, ya sanar da yin murabus dinsa. Ayyukan yanar gizo na Amazon ""sun cigaba da bunkasa a [baya-bayan nan], kana sun samu gagarumin ciniki. Daukacin ciniki a kamfanin ya karu zuwa kashi 44 bisa dari ( 44%) a cikin watanni uku na shekarar zuwa dala biliyan dari da ashirin da biyar ( $125.6bn), sakamakon sabunta dokar kullen korona a wasu sassan duniya. Ayyukan shafukan yanzr gizo sun shaida karuwar kashi 28 bisa dari (28%) zuwa dala biliyan goma sha biyu da miliyan dari bakwai ($12.7bn). Carolina Milanesi, wata mai sharhi a cibiyar Creative Strategies, ta rubuta a shafinta na Twitter cewa ""gagarumar"" sanarwar ta nuna yadda bangaren ayyukan yanar gizo ke da muhimmanci ga kasuwancin Amazon. Amma kuma ta kara da cewa ba ta da yakinin cewa Bezos ""ba zai daina yin tasiri a kan makomar kamfanin ba''. Masu sukar lamirin kamfanin suma sun mayar da martini game da sanarwar. ""Kada ku bari Amazon ya yaudare ku. Har yanzu Jeff Bezos yana da karfin fada a ji a matsayinsa na shugaba mai cikakken iko,'' in ji kungiyar Public Citizen, kungiya mai rajin kare 'yancin masu sayen kaya a Amurka. ""Akwai bukatar yin garanbawul game da wannan mulkin mamaya da danne hakki.''on." https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-55918607 +technology Qian Xuesen: Mutumin da Amurka ta kora ya koma China ya ƙera mata makamai "Wani masanin kimiyya ya taimaka wa manyan kasashe biyu kai wa ga duniyar wata, amma kuma kasa ɗaya ce kawai ke tunawa da shi. A birnin Shanghai akwai ɗaukacin wurin ajiyar kayan tarihi da ke cike da zane-zane 70,000 da aka sadaukar ga mutum guda, ''masanin kimiyya mai farin jinin jama'a'' Qian Xuesen. Qian shi ne jagoran shirin makamai masu linzami da na sararin samaniya na kasar China. Bincikensa ya taimaka wajen kirkirar kumbunan tashi zuwa sama jannati da ya harba tauraron dan adam na kasar China na farko zuwa sararin samaniya, da kuma makaman masu linzami da suka zama daya daga cikin bangaren ajiyar makaman nukiliyarta, kuma ana daukarsa a matsayin wani jan gwarzo a akasar. Amma kuma a wata babbar kasar, inda ya yi karatu ya kuma yi aiki na fiye da shekaru goma, ba a cika tunawa da gagarumar gudumawarsa ba ko kadan. An haifi Qian a shekara ta 1911, a kasar China. Iyayensa duka biyu masu ilimi ne, kuma mahaifinsa bayan ya yi aiki a kasar Japan, ya kafa tsarin ilimi na kasa a kasar ta China. A bayyane ta ke cewa tun daga farko Qian ya tashi da wata baiwa ne, kuma ya kammala karatu da sakamako mafi girma a cikin ajinsu a jami'ar Shanghai Jiao Tong, in da ya samu tallafin karatun zuwa cibiyar nazarin fasahar zamani ta Massechussets ta Amurka (MIT) da ba a cika samu ba. A shekarar 1935 wani siririn matashi mai sanye da tufafi masu kyau ya iso birnin Boston. Me yiwuwa Qian ya fuskanci nuna kyamar wanda ba dan kasa ba da na wariyar launin fata, in ji Chris Jespersen, Farfesan mai nazarin tarihi a jami'ar North Georgia. Amma kuma akwai ""batun son kai da tunanin cewa kasar China na kara sauyawa ta fuskar cigaba,"" kuma tabbas zai iiya zama cikin fitattun mutane da ke mutunta basirarsa. Daga cibiyar MIT, Qian ya koma cibiyar fasaha ta birnin California (Caltech), don yin nazari a karkashin daya daga cikin injiniyoyin jiragen sama masu fada a ji, dan kasar Hungari émigré, Theodore von Karman. A can ne Qian ya zauna a ofishi daya da wani fitaccen masanin kimiyya, Frank Malina, wanda jigo ne a tawagar masu bincike kan kunar bakin wake. Tawagar ta samu wannan suna ne saboda yunkurinsu na kera kumbo a harabar makaranta, kuma saboda wasu daga cikin ayyukan binciken kimiyyarsu da sinadarai masu bace wa ya gamu da cikas, in ji Fraser Macdonald, wani marubuci kan wani fim mai suna 'Escape from Earth: A Secret History of the Space Rocket."" Duk da cewa babu wanda ya mutu. Wata rana ne ya shiga cikin wata tattaunawa kan wani aikin lissafi mai sarkakiya da Malina da sauran 'yan tawagarsu, kafin ka ce wani abu ya taka babbar rawa a wajen binciken yadda za a kera kumbon da kuma yadda zai tashi zuwa sararin samaniya. A wannan lokaci, kumbon kimiyya ya zama wani abin ba'a. Macdonald ya ce. ""Babu wanda ke daukar shi da muhimmanci - babu wani injiniyan da zai saka kasadar yada mutuntakarsa wajen fadar cewa wannan ita ce makoma."" Amma nan da nan Abubuwa suka sauya saboda fara yakin duniya na biyu. Qian dan asalin kasar China ne, amma kuma Jamhuriyar kasar ta China kawa ce ga Amurka, don haka babu wani ''gagarumin zargi game da masana kimiyyar kasar China a cibiyar sararin samaiyar Amurka,"" in ji Fraser Macdonald. An bai wa Qian takardar izini ta tsaro, don ya gudanar da aikin bincike kan wasu makamai na musamman, kuma har ya yi aiki da hukumar bayar da shawarwari kan kimiyya ta gwamnatin Amurka. Bayan da aka kawo karshen yakin ne, ya zama daya daga cikin fitattun masana kan harba kumbo a duniya, kuma an tura shi tare da Theodore von Karman wurin wani gagarumin aiki a kasar Jamus, rike da mukamin wucin gadi na laftanal Kanal. Burinsu shi ne, su tattauna da injiniyoyin Nazi, da suka hada da Wernher von Braun, wani jagoran masana kimiyyar harba kumbo na kasar Jamus; Amurka na bukatar gano takamaimen abin da Jamus ta sani. Amma daga bisani gagarumin aikin da Qian ya gudanar Amurka ya gamu da cikas, sannan rayuwarsa ta soma zama cikin hadari. Tuhumar da aka yi wa Qian na da nasaba da wasu kasidun jam'iyar kwaminisanci ta Amurka da suka bayyana a shekara ta 1938, da ke nuna cewa ya halarci taron da hukumar bincken laifuka ta FBI ta yi zargin taro ne na jam'iyar Pasadena Communist. Duk da cewa Qian ya musanta zargin zama dan jam'iyar, wani sabon bincike ya nuna cewa ya shiga ne a daidai lokacin Frank Malina a shekara ta 1938. Zuoyue Wang, Farfesan tarihi a jami'ar jihar California ya ce babu wata shaida da ta nuna cewa Qian ya taba yi wa kasar China leken asiri, ko kuma shi dan leken asiri ne a lokacin da yake Amurka. Don haka aka kwace takardar izinin gudanar da binciken da aka ba shi, aka kuma yi masa daurin talala. Abokan aikinsa na cibiyar Caltech da suka hada da Theodore von Karman, sun rubuta wa gwamnati suna rokon ta da kuma nuna cewa Qian ba shi da laifi, amma haka ba ta cimma ruwa ba. A shekarar 1955, lokacin da Qian ya shafe shekaru biyar cikin daurin talala, shugaba Eisenhower ya yanke shawarar tasa keyarsa zuwa gida kasar China. Masanin kimiyyar ya bar Amurka tare da matarsa da 'yayansu biyu da suka haifa a Amurka a cikin jirgin ruwa, yana mai shaida wa manema labarai cewa ba zai sake taka kafarsa zuwa Amurka ba. Ya kuma rike alkawarinsa. ""Ya kasance daya daga cikin fitattun masana kimiyya a Amurka. Ya bayar da gagarumar gudumawa, kuma ya ci gaba da bayar da gudumawar tasa sosai. Don haka, ba wai wulakanci ba ne kawai ba, har ma da alamun cin amana,'' in ji dan jarida kuma marubuci, Tianyu Fang. Qian ya isa kasar China a matsayin gwarzo, amma ba a yi saurin saka shi a cikin jam'iyar kwaminisanci ta kasar China ba. Matarsa diyar wani fitaccen mutum ne a kasar, kuma kafin Qian ya yi faduwar bakar tasa yana zaune ne cikin farin ciki a Amurka - har ya fara yunkurin neman takardar iznin zama dan kasa. A lokacin da ya zama dan jam'iya a shekara 1958, ya karbe ta hannu biyu, kuma ya rika kokarin ganin yana bin bangaren gaskiya. Lokacin da ya isa kasar China, akwai fahimta kadan game da batun kumbon kimiyya, amma bayan shekaru 15 ya jagoranci kaddamar da tauraron dan adam na farko a sararin samaniya. A cikin shekaru da dama, ya horar da matasa masu nazarin kimiyya, kuma aikinsa ya kafa tubali ga kasar China wajen aike wa mutane zuwa duniyar wata. Yanzu haka, akwai rashin jituwa sosai tsakanin kasashen China da Amurka. Wannan karon ba game da batun ra'ayi ba ne, amma game da harkar kasuwanci, damuwa game da harkar tsaro, da kuma gazawar kasar China - bayan da shugaba Donald Trump ya ce - ya kamata a kara kaimi wajen shawo kan annobar cutar korona. Yayin da Amurkawa da dama ba su da wata masaniya game da rawar da Qian ya taka a shirin Amurka na sarararin samaniya, Tianyu Fang ya ce 'yan kasar China mazauna Amurka da dama da daliban kasar China a Amurka, ba su san komai game da shi ba, da kuma dalilan da suka sa ya bar Amurka. ""Dangantakar Amurka da China ta kara tabarbarewa sosai, sun kuma san cewa za su iya fuskantar irin zargin da Qian ya fuskanta,"" in ji shi. A lokacin da kasar China ta fara bunkasa ta fannin tattalin arziki a doron kasa da kuma sararin samaniya, Qian na daga cikin wadanda suka kawo wannan sauyi. Amma kuma ya kamata a ce labarinsa ya kasance mafi girma a Amurka ita ma - inda hazaka da basira a duk inda ta ke, za ta yi tasiri. A bara, lokacin da kasar China ta kafa wani tarihi bayan da ta sauka a duniyar wata, ta yi hakan ne da sunan Von Karman , injiniyan jirgin sama, wanda shi ne ya koyar da Qian." https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-54734581 +religion Yadda mabiya ɗariƙar Ƙadiriyya a Kano suke ibadunsu "Babu takamaiman adadin mabiya ɗarikar Ƙadiriyya a Najeriya, amma ana ƙiyasin cewa sun kai miliyoyi. Ɗarikar ta Ƙadiriyya na daga manyan ɗarikun sufaye da ake bi a Najeriya, kuma ana ɗaukanta a matsayin ɗarikar da ta fi daɗewa a ƙasar. Sidi Abdulkadir Jilani ya rayu ne a birnin Bagadaza na kasar Iraki tsakanin shekarun 1078 zuwa 1166. Yana daga manyan waliyyai da mabiya ɗarikun Sufaye suke girmamawa, har ma ana masa kirari da sarkin waliyyyai. Matan da ke alfahari wajen iya ƙira'ar Ƙur'ani Bidiyon yadda ake satar gari a wajen niƙa a Kano Nahiyar Afirka na daga yankunan duniya da ke da mabiya ɗarikar ta Ƙadiriyya da dama, kuma a yanzu birnin Kano a Najeriya ne cibiyar ɗarikar ta Afirka, kasancewar shugabanta Shaikh Karibullah Nasiru Kabara yana zaune ne a Kano. Shiekh Karibu ya gaji shugabancin ɗarikar ne daga wajen mahaifinsa Shaikh Nasiru Kabara shekara 25 da ta gabata. Gabanin zama shugaban ɗarikar na nahiyar Afirka baki daya, marigayi Sheikh Nasiru Kabara ya zama shugaban ɗarikar na nahiyar Afirka ta yamma. Ya rasu a watan Oktoban 1996. Babu bayanai na ainihin shekarar da ɗarikar ta shiga kasar. Sai dai wasu bayanai na cewa an fara bin ɗarikar ta Ƙadiriyya a Najeriya ne tun zamanin Sidi Abdulkadir Jilani, wanda ya kafa ɗarikar, fiye da shekaru 900 da suka wuce. Ɗaya daga malaman ɗarikar, Sheikh Jamilu Alkadiri ya bayyana cewa ""Ɗarikar Ƙadiriyya ta shigo Najeriya tun da rayuwar Sidi Abdulkadir din da kan shi RA"". ""Sannan babu Najeriyar sai dai a ce Biladus-Sudan."" Ya kara da cewa ɗaya daga manayn malaman da aka yi a Najeriya, Waziri Junaidu ya tabbatar da haka. ""Har da akwai wasu wurare da ake nunawa a Ƙauran Namoda (a jihar Zamfara) da ake cewa shi kansa Sidi Abdulkadir ya zo nan,"" a cewar Alkadiri. Ya ce mutane suna zuwa ziyara. Bayanai kuma sun tabbatar da cewa Shehu Usmanu Ɗan Fodiyo wanda ya jaddada Musulunci a Najeriya ya yi ɗarikar ta Ƙadiriyya. Mabiya ɗarikar suna gudanar da wasu al'amura na ibada da suka bambamta su da sauran mabiya ɗarikun sufaye. Daga cikin akwai Zikirin Anfasu da ake yi da numfashi, wanda Sheikh Karibullah ya ce daya ne daga cikin nau'ikan zikirai da ake yi da dukkan gabbai. Sannan akwai buga bandiri ko mandiri wanda ake yin zikiri da shi, musamman ambaton Allah da yabon Manzon Allah SAW da kuma waliyyai, kamar Sidi Abdulƙadiri. Sai dai wasu Musulmin na ganin mabiya ɗarikar sun saba koyarwar addinin Musulunci wajen gudanar da ibadun, to amma mabiya Ƙadiriyyar na cewa rashin fahimta ne ya sa ake sukar su, domin suna da hujjoji kan duk abin da suke yi." https://www.bbc.com/hausa/labarai-54475317 +sports Messi zai yi kan-kan-kan da Matthaus a yawan buga Kofin Duniya Argentina za ta fafata da Croatia ranar Talata a karawar daf da karshe a Gasar Kofin Duniya da ake yi a Qatar. kyaftin din Argentina, Lionel Messi, mai shekara 35 mai buga gasar Kofin Duniya karo na biyar zai yi bajinta a wasan da za a yi a filin Lusai. Dan kwallon da ke taka leda a Paris St Germain zai buga wasa na 25 a Gasar Kofin Duniya, kenan zai yi kan-kan-kan da Lothar Matthaus na Jamus. Haka kuma ya yi kan-kan-kan da Gabriel Batistuta a yawan ci wa Argentina kwallaye a Kofin Duniya masu goma-goma a raga. Yana kuma fatan yin kan-kan-kan da Diego Maradona mai tarihin bayar da kwallo sau takwas ana zurawa a raga, bayan da Messi keda bakwai. Matthaus ya buga wa tawagar Jamus dukkan Gasar Cin Kofin Duniya tun daga 1982 zuwa 1998. Kenan Messi zai kafa tarihin yawan buga wasanni a Gasar Kofin Duniya ko dai a neman na uku idan Croatia ta yi nasara ko a wasan karshe idan Argentina ta kai zagayen karshe. Messi ya kusan daukar kofin duniya a 2014, inda suka buga wasan karshe da Jamus ta yi nasara da ci 1-0 a karin lokaci. Kawo yanzu Messi ya ci kwallo 10 a fafatawa 24 da ya buga a dukkan kofin duniya da ya halarta, yana cikin na takwas a jerin wadanda suka ci kwallaye da yawa a Gasar Kofin Duniya. Miroslav Klose shi ne kan gaba a yawan cin kwallaye a karawa 24 da ya yi Gasar Kofin Duniya, wanda yake da 16 a raga. Argentina tana da Kofin Duniya biyu, amma na karshe da ta dauka shi ne a 1986 tare da Diego Maradona. 'Yan kwallon da suka buga wasanni da yawa a Gasar Kofin Duniya Lothar Matthaus 25 Lionel Messi 24 Miroslav Klose 24 Paolo Maldini 23 Cristiano Ronaldo 21 Diego Maradona 21 Uwe Seeler 21 Wladyslaw Zmuda 21 https://www.bbc.com/hausa/articles/c4neydwq0x7o +business Gwara na mutu da na yi bara a kan titi in ji gurguwa mai sana'ar dinki "Danna hoton da ke sama don kallon bidiyon: A ci gaba da kawo muku rahotanni kan masu bukata ta musamman da suka rungumi sana'o'i maimakon barace-barace a kan titi da kuma zaman kashe-wando, a yau za mu kawo muku labarin Ruth Peter wata mace gurguwa da ke sana'ar dinki a Yola fadar jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya. Ruth ta bude shagonta na dinki ne a shekarar 2002 kuma ta shafe fiye da shekara 20 tana sana'ar dinki. Duk da lalurar kafa da take da ita, matar tana dinkuna na mata da maza musamman na yayi da ake yi wa ado da duwatsun ado na mata. Ya zuwa yanzu Ruth ta yaye dalibai da dama kuma tana koya wa sama da mata goma dinki a shagonta. Ruth ta ce idan ta ga mai lalura yana bara sai ta ji ranta ya baci matuka. ""Idan na ga mai lafiya yana roko abun na damuna sai in ce me ya sa mai nakasa zai yi sana'a shi kuwa mai lafiya zai tsaya barace-barace?'' Ruth ta kara da cewa ""da in yi bara a kan titi gwamma na mut.''" https://www.bbc.com/hausa/media-61889213 +sports Ba saboda kudi zan koma Man United ba - Casemiro "Ranar Litinin Casemiro ya yi ban kwana da Real Madrid a shirin da yake na komawa Manchester United da taka leda a makon nan. Dan kwallon tawagar Brazil, mai shekara 30 ya ce zai koma daya daga babbar kungiya a fannin tamaula a duniya, bayan kaka tara a Real Madrid. United ta amince da farashin fam miliyan 70 kudin daukar Casemiro kan yarjejeniyar kaka hudu, wanda zai zama kan gaba a karbar albashi a Old Trafford. ""Da saboda kudi ne da tuni na bar Real shekara hudu zuwa biyar baya,"" kamar yadda ya fada. ""Duk masu wannan tunanin ba gaskiya bane, ina jin ko kadan ba su san ko ni wane ne ba. ""Real ta mutuntani a koda yaushe, Ni da kaina na yanke shawarar gwada sa'a a wata kungiyar."" Bayan da ya koma Sifaniya da taka leda daga Sao Paulo a 2013, Casemiro ya dauli Champions League biyar a Real Madrid da La Liga uku da Cope del Rey daya. Ya buga Champions League a bara da Real ta doke Liverpool ta lashe kofin Zakarun Turai na 14 jumulla, wanda ya yi mata wasa 336. Cristiano Ronaldo ya lashe Champions League hudu tare da Casemiro a Real, sai dai ana alakanta dan wasan tawagar Portugal da cewar zai bar Old Trafford a kakar nan. United wadda ta yi rashin nasara a wasa biyu a Premier League za ta karbi bakuncin Liverpool, wadda ta yi canjaras biyu da za su kara ranar Litinin a Old Trafford." https://www.bbc.com/hausa/articles/cz7p4w9enlno +business Matashiyar da ke hankoron magance matsalar karancin gidaje "Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon: Perala Mansa, wata 'yar kasar Indiya ta kera gida mai suna ""O-Pods"" wanda za a iya matsawa da shi daga wuri zuwa wuri kuma ba ya bukatar fili mai yawa ko kayan aiki kafin a kera shi. Matashiyar mai shekara 23 'yar asalin jihar Telangana ta yi amanar cewa gidan wanda ba a kashe kudi da yawa wajen kera shi ba ta hanyar amfani da bututan magudanan ruwa, zai iya magance matsalar karancin gidaje a duniya. Ta kera gidanta na farko a watan Afrilun 2021. Yanzu kamfaninta ya yi ikirarin samun kamfanoni da gidajen gona da kuma masu harkar gina gidaje a fadin Indiya da suka kai 500 da ke so a kera musu irin wadannan gidajen." https://www.bbc.com/hausa/media-60154540 +health Coronavirus: Sabbin abubuwa biyar dangane da cutar korona Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon Zai yi matuƙar wahala a bi diddiƙin bayanan da ake samu na baya-bayan nan kan cutar korona. Ga dai sabbin abubuwa biyar da bincike ya bankaɗo dangane da ƙwayar cutar. https://www.bbc.com/hausa/media-53990619 +business Buhari ya ƙaddamar da e-naira: Abin da ya kamata ku sani game da kuɗin intanet na Najeriya "Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya ƙaddamar da kuɗin intanet na ƙasar e-Naira ko kuma nairar da ake kashewa ta intanet. Shugaban ya ƙaddamar da kuɗin intanet ɗin ne ranar Litinin a Abuja, babban birnin ƙasar. Tun farko an tsara ƙaddamar da kuɗin intanet ɗin ne a farkon wannan wata, amma sai Babban Bankin Nijeriya ya ɗage batun zuwa gaba. Bankin ya ce ya shafe shekaru yana bincike a kan e-Naira kuma ""an ɓullo da ita ne da zummar sauƙaƙa wa kowane ɓangare na al'umma gudanar da harkokin kuɗinsu"". Tun da farko Babban Bankin Najeriya, CBN, ya ce a watan Oktoba 'yan kasar za su soma amfani da kuɗin intanet na e-Naira. CBN ya bayyana haka bayan ya haramta amfani da kudin Cryptocurrency saboda rashin gamsuwa da yadda tsarinsa yake. e-Naira kudi ne da zai bai wa mutane damar yin harkokin kasuwanci ta intanet. Tsarin zai yi aiki da kamfanin fasaha na Bitt Inc., a kokarin fara amfani da kudin intanet na e-Naira. CBN ya zabi Bitt Inc. daga cikin manyan kamfanonin fasaha da dama da suka fafata wajen ganin sun samu kwangilar aiki tare da Bankin domin samar da wannan kudi cikin tsaro da tsari mai inganci. Sanarwar da CBN ya fitar ta kuma bayyana wasu daga cikin alfanun kudin na intanet din da suka hada da inganta tsarin kasuwanci, wadatuwar kuɗaɗe cikin sauki da kuma saukin kasafi da haraji. Ga wasu abubuwa da suka kamata ku sani game da kuɗin intanet na e-Naira: Kuɗin na e-Naira zai saukaka kasuwanci cikin sauki amma yana da bambanci da sauran kuɗaɗen intanet saboda CBN ne kaɗai yake da alhakin samar da shi. CBN ya ce kuɗin na e-Naira zai taimaka wajen gudanar da harkokin kasuwanci cikin sauki da kuma zai kunshi kowa da kowa sannan zai bunkasa tsarin kasuwanci ba tare da amfani da tsabar kuɗi ba. Kazalika tsarin e-Naira ba ya bukatar tsabar kuɗi kwata-kwata. Haka kuma e-Naira ba ya hawa da sauka kamar saura kuɗin intanet irin su Bitcoin, sai dai za a rika amfani da shi kamar yadda ake aiki da Naira. Tun da tsarin e-Naira zai kasance irin na Naira ne, darajarsu za ta zama iri daya da ta Naira. Tsarin e-Naira zai kasance daban da na yadda ake bude asusu a bankuna; za a samar da wata jaka da za a rika adana kuɗin kowanne mutum ta hanyar ba shi wasu lambobi da shi kaɗai ne yake da irin su. Kuɗi ne da aka amince kowa ya yi amfani da su a Najeriya, kuma ba zai rika tara kuɗin ruwa ba. Za kuma a samar masa da wasu lambobi na tsaro da za su hana gurbata shi." https://www.bbc.com/hausa/labarai-58406847 +religion Ku San Malamanku tare da Limamin Kano Farfesa Sani Zahradden "Shirin Ku San Malamanku na wannan makon ya tattauna da Farfesa Sheikh Muhammad Sani Zaharaddeen, wanda shi ne babban limamin Jihar Kano. Liman ya fara karatun Al-Ƙur'ani a garin Ƙiru na Kano a wajen Malam Abdullahi. Kazalika, karatun soro ya kai shi garuruwan Kura da Bebeji, duka a Kano. Sai dai ya ce biye ya yi, wato ba haddar Ƙur'ani ba a wajen malaman da ya yi karatu a hannunsu. Daga baya ya shiga kwalejin ilimin harshen Larabci da ke ƙwaryar birnin Kano, inda ya samu shaidar kammala sakandare. Daga cikin muƙaman da liman ya riƙe har da kwamashinan ilimi na Jihar Kano da kuma shugaban wasu jami'o'i a Najeriya. Farfesa Sani Zahraddeen ya ce babbar aƙidarsa ita ce kalmar shahada, kuma ya yi ayyuka da dama wajen haɗa kan malaman ƙungiyoyin addin daban-daban a Kano. ""Lokacin da nake shugabantar Hukumar Shari'a [ta Kano] mukan haɗa tarukan ƙara wa juna ilimi, kuma wannan ya sa malaman sun haɗa kansu,"" a cewarsa. ""Idan ana ganawa ba za ka ji wani na cewa ni daga Izala nake ko wata bƙungiya ba saboda masalahar Musulmi baki ɗaya. Da BBC Hausa ta tambaye shi kan abin baƙinc cikin da ya faru da shi da ba zai manta ba, shehin malamin ya ba da labarin yadda wasu 'yan bindiga da ya kira 'yan ta'adda suka yi garkuwa da su a cikin jirgi. A cewarsa, lamarin ya faru ne a farkon ƙarnin shekarar hijira ta 1400, inda aka gayyace shi zuwa bikin sabon ƙarni a Jami'ar Peshawar da ke Pakistan. ""'Yan ta'adda sun kai mu Afghanistan, suka tsare mu a cikin jirgi tsawon kwana 12. A nan za kai barci, a nan za ka yi bawali. ""Daga ƙarshe dai Allah kuɓutar da mu, amma da sun ce ƙona jirgin za su yi ko su saka bam. Amma wannan tashin hankali ne babba."" Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, liman ya ce yana da mata ɗaya, wadda suka shafe shekara 56 tare, kuma suka haifi 'ya'ya takwas. Sai dai ya ce ɗaya ya rasu daga cikin 'ya'yan." https://www.bbc.com/hausa/articles/c4n24w15v8po +politics Zaben 2023: Yadda waka ke tasiri a siyasar Najeriya "A Najeriya, mawaka na da matsayi na musamman a cikin harkokin siyasar kasar, sakamakon rawar da suke takawa wajen tallata manufofin jam`iyya da na `yan takara. Tun daga  jamhuriya ta farko ake tafiya da su, kuma har yanzu ba a yar da su ba. Kamar kowace kakar zabe a Najeriya za a iya cewa gari ya waye domin mawaka sun fara baje-kolinsu. Yawanci a cikin wakokinsu mawakan kan yi yabo ga gwanayensu ko gugar-zana ga abokan hamayya. Kuma waka na yin tasiri sosai ga masu neman mukami a siyasa, saboda a wasu lokutan mutane na zaben mutum ne saboda yadda wakar da aka rera masa ta ja hankalinsu. Masana harkokin siyasa a Najeriya sun bayyana cewa dangantakar da ke tsakanin mawaka da `yan siyasa, dangantaka ce ta jini da tsoka. Dakta Abubakar Kari, masanin siyasa ne a jami`ar Abuja da ke Najeriya, ya shaida wa BBC cewa wakoki na saurin karbuwa a tsakanin matasa samari da kuma masu kananan shekaru. Ya ce ""wakoki irin na siyasa bugu da kari tattare suke da kade-kade da bushe-bushe da kuma raye-raye, sannan ga zambo da kirari, shi yasa 'yan siyasa ke zakewa a kan cewa sai an yi musu wakoki."" Dr Kari ya ce irin wadannan wakoki na da tasiri kwarai da gaske, ta yadda za a ga ana ta rerasu a tsakanin jama'a. Duk da cewa mawakan na matukar kaunar jam`iyyunsu, a cewar masanin kaunar ba ta hana wasu mawakan su juya wa jam`iyya ko gwanin nasu baya idan suka hangi kamar an sake hanya. Masanin siyasar ya ce yawancin mawakan siyasar na fama da rashin akida. Ya ce,"" Da dama daga cikin wadannan mawaka 'yan kasuwa ne domin kudi suke nema musamman ma a wannan jamhuriya."" Dr Kari ya kara da cewa a baya yawancin mawakan siyasa musamman ma na jamhuriya ta daya data biyu mutane ne masu akida, to amma a wannan jamhuriya yawancin mawakan siyasar ana daukarsu haya ne. Ya ce"" to shi yasa zaka ga mawaki guda ya yiwa 'yan takara da dama waka wani lokaci ma har da abokan hamayya."" Tun daga jamhuriya ta farko mawaka ke tallata jam`iyyum siyasa da `yan takara har zuwa yanzu, kuma alamu na nuna cewa za su ci gaba da samun tagomashi." https://www.bbc.com/hausa/labarai-61976279 +religion Hotunan yadda ake bikin Babbar Sallah a Najeriya Musulmin Najeriya suna ci gaba da gudanar da bukukuwan Babbar Sallah kamar sauran takwarorinsu da ke sassan duniya daban-daban. https://www.bbc.com/hausa/labarai-49318567 +technology Duniya na fitar da wani sauti mai tayar da hankali Tururin maganaɗisun duniya wani abu ne da ba za mu iya ji ko gani ba, amma masana kmiyya sun gano wata hanya ta amfani da wasu hanyoyi don sarrafa ƙarar. Karar da aka naɗa ɗin na fayyace abin da ake ji daga can cikin duniyar Earth. Sai dai ƙarar na da matuƙar ban tsoro. Ku saurara a wannan bidiyon. https://www.bbc.com/hausa/articles/c2j0r9rgjmxo +health Ranar Barci ta Duniya: Muhimmancin barci da illolin rashin yin sa Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon: A yau ne ake bikin Ranar Barci ta Duniya inda ake bayyana muhimmancinsa da kuma illolin rashin yin sa. Albarkacin wannan rana ne, wata kwararriyar likitar kwakwalwa, Dakta Dayyaba Shu'aibu, ta bayyana mana muhimmancin yin barci. https://www.bbc.com/hausa/media-60783246 +entertainment Ko mutuwar ɗan Davido za ta sa a inganta tsaro ga masu ninkaya a Najeriya? "Mutuwar da ɗan mawakin nan na Najeriya, Davido, mai shekara uku a duniya, ya yi a wurin ninƙaya da ke cikin gidan mawakin a jihar Legas, a ranar 1 ga watan Nuwamba, 2022 ta ja hankali kan kiwon lafiya ga masu ninkaya a Najeriya. Mutuwar Ifeanyi Adeleke ta faru ne shekara hudu bayan da ɗan wani mawakin na Najeriya D’Banj mai shekara daya ya rasu a irin haka. Ba a cika samun wajen ninkaya a cikin gida a Najeriya ba, yawanci masu kudi ne kawai ke da shi a gida, amma abu ne da mutane da yawa ke da burin samu a cikin gidajensu, don haka sanin yadda ake ninkaya da kuma yadda za a kare kai abu ne mai muhimmanci ga rayuwar ɗan Adam. Duk da cewa ruwa ya zagaya birnin na Legas – akwai gabar teku da hanyoyin ruwa da yawa kamar dai tekun Atalantika – da yawan mutanen Legas ba su iya ninkaya ba. “Wannan mutuwar ta taba zukatan mutane da dama,” in ji Bolanle Edwards daga babbar gidauniyar madauri da aminci kan kiwon lafiyan yara. Tana mai kira ga a yawaita koyar da kariya ga yara wajen ninkaya a kasar fiye da shekara goma. Ta kara da cewa “hakan na faruwa sosai daga shekarar 2018 zuwa 2022... a otal, a gabobin teku, har da ma gidajen mutane.” Batutuwa biyu masu muhimmanci: Bunkasa matakan kare kai a wuraren ninkaya da gabar teku Koyar da yadda ake ninkaya A daya daga cikin kyawawan bakin tekun Legas akwai wayewar kai kan wadannan batutuwan. Iyaye na kallon ‘ya’yansu suna wasa cikin ruwa mai kumfa na gabar tekun Landmark ya sa mun yi nazari kan mutuwar ɗan Davido. “Ban ji dadi ba ko kadan, ba abu ba ne da za ka yi wa makiyinka fata ba,” in ji Femi Nedd, wanda ya sa ‘ya’yansu uku cikin makarantar koyar da ninkaya tun kafin su fara tafiya. “Ninkaya ba abin shakatawa ba ne, abu ne da kake bukatar ka koya a rayuwarka.” Ko-da-ya-ke ‘ya’yanta suna ninkaya tun shekara hudu ba da taimakon kowa ba, ta ce sa musu ido a ko-da-yaushe muhimmin abu ne da kuma samun masu zama wajen ninkaya don sa ido na kara ba ta kwarin gwiwa. Adeola Folivi ta ce ‘yarta mai shekara 12 a duniya, masoyiyar Davido ce, kuma ta shiga damuwa game da jin abin da ya faru da ɗansa – sai ta dawo gida da muhimmancin koyar da ninkaya. Ta ce “kullum ina bai wa ‘ya’yan ‘yan uwana da abokaina shawara [da su shiga makarantar koyon ninkaya] – idan dai har za a yi shi a wuri mai kyau, da kuma bin ka’idojin tsaro tare da kayan ninkaya da ya kamata.” Masu wajen ninkaya a gidajensu ma sun ji mutuwar ɗan Davido din. Adekunle Akanbi, wanda ke raba wajen ninkaya da makwabcinsa a kudu maso yammacin birnin Ibadan, ya shiga damuwa bayan jin labarin abin da ya faru da Davido. Ya shaida wa BBC cewa za a fara sa ido ga yaran da ke cikin filin gidansu ta wajen ninkaya: “Sun iya ninkaya sosai amma duk da haka za a sa musu ido sosai don tsaro.” Nora Chukwuma da ke kudancin birnin Port Harcourt ma haka ta ce. Kuma wai duk kofofin da zai kai mutum wajen ninkayan a rufe suke don hana yara zuwa kusa da ruwan ba tare da babban mutum ba. “Yanzu haka muna aiki kan saka shinge ta wajen ninkayar.” Kididdiga kan nutsewa a cikin ruwa na da wahalar samu a Najeriya amma mai yakin neman tsaro, Ms Edwards ta ce idan aka zo batun ninkaya, an rawaito nutsewar mutum 18 cikin shekara hudu da ta wuce. Takwas daga ciki sun faru ne cikin wannan shekarar kawai. Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana nutsewar ruwa a matsayin ta uku da ke haddasa mace-mace ta hanyar raunin da ba da gangan ba a duniya. Ta ce kimanin mutane 236,000 ne ke mutuwa sakamakon nutsewa a duk shekara. Kusan kashi 90 cikin dari na wadannan mace-mace na faruwa ne a kasashe masu karamin karfi da matsakaita kamar Najeriya. A kokarinta na kare afkuwar irin wadannan hadurran, gwamnatin jihar Legas a watan Satumba ta bukaci masu kula da wuraren ninkaya da masu bakin ruwa da su kara kaimi wajen daukar matakan kariya a kewayen wuraren aikinsu. A cikin 2017 ta gabatar da ka'idojin kiyaye lafiya a faɗin jihar waɗanda suka nemi hana gudanar da sana'ar ninkaya ba tare da izini ba da kuma mai ceto a wurin. Amma ba tare da aiwatar da doka da oda ba ana yin watsi da waɗannan sau da yawa. Ms Edwards ta ce tun bayan bullo da kwararrun jami’an tsaro, yanzu an samu karancin hadurra a bakin tekun Legas. Wasu jihohi kadan na da tsari iri daya da wasu jihohin a cikin kasar. Sanin yadda ake yin iyo, da kuma haɗarin ruwa, ba su da yawa. A shekarar 2014 ne rundunar sojin ruwan Najeriya ta ce tana gabatar da darussa na dole ga dukkan jami’anta bayan da suka lura da yawa daga cikin ma’aikatan ba su da kwarewa wajen ninkaya. Kamar yadda wasan ninkaya fasaha ce ta rayuwa, iyaye suna buƙatar la'akari da shi a matsayin mahimmanci kamar sauran ƙwarewa, in ji mai koyar da wasan ninkaya Tough Atelemo, wanda ya koyar da ɗaruruwan yara ƙanana - wasu 'yan ƙasa da watanni shida - a cikin shekaru ashirin da suka gabata. ""Lokacin da kuke horar da yaro, dole ne ku horar da su yadda za su tsira,"" in ji ta. Sai dai ta yarda cewa a farashin kusan dala 220 (£200) na darussa 10, ba su isa ga yawancin 'yan Najeriya ba. Ta kara da cewa ya kamata a saka shi a cikin manhajojin makarantun farko, wanda kuma shi ne shawarar hukumar ta WHO. Sanya titin tsaro, rufe wuraren tafkuna, shinge a wuraren shakatawa da sanya yara a cikin alkaluman wasa lokacin da suke kusa da ruwa wasu matakai ne masu amfani da za su iya rage hadarin da ke tattare da ruwa, in ji WHO. Ms Edwards ta nanata hakan, tana mai cewa ya kamata wuraren tafkuna su kasance da shinge ta kowa ne bangare da ke raba su da gidan. Fasahar, irin su hasken motsa jiki da CCTV, na iya taimakawa wajen kare mutane, musamman yara, daga hadarin nutsewa, in ji masanin injiniya Daniel Ette. Ya ce “amma babu abin da ya fi sa idon babba da kuma karfen tsaro.” Ba a san wane irin matakan tsaro ba ne Davido ya sa a gidansa. Binciken gawar ‘yan sanda ya tabbatar da cewa dansa ya mutu ne sakamakon nutsewa amma ana ci gaba da bincike. 'Yan sandan na nazarin hoton na'urar daukar hoto ta tsaro ta gidan, yayin da suke rike da mai gadin na Davido da kuma mai dafa abinci na gidan, inda suke musu tambayoyi." https://www.bbc.com/hausa/articles/cgl1dlj5jvxo +religion Ku san Malamanku tare da Malam Muhammad Tukur Sani Jangebe "Malamin addinin Musuluncin nan da ke jihar Zamfara a arewa maso yammacin Najeriya Malam Muhammad Tukur Sani Jangebe, ya ce babban abin da yake sanya shi farin ciki shi ne idan ya je yin da'awa. Malamin ya shaida wa BBC cewa a ko da yaushe yana taka tsan-tsan wajen fadin abin da zai taɓa mutuncin wani. ""Wajen ida sako, ina da dabarun da nake amfani da su cikin raha da annashuwa sai na yi sako-sako, mutane ba sa gane ya musu nauyi har sai na tafi,"" in ji shi. Malamin ya bayyana cewa ya fuskanci kalubale da dama a tsawon lokacin da ya dauka yana yada addinin Musulunci. ""Babban kalubalen shi ne na je da'awa a gabana aka kashe mutume 11, jini ne kadai ya shafi jikina amma babu abin da ya same ni. Sannan 'yan fashi da makami sun taɓa tare mu zan je wa'azi, da guntun wando na isa ofishin 'yan sanda. Na dade ina mafarkin wannan cikin iyalina, ina fadin ga su nan amma sai su ce Malam babu komai."" Malam Muhammad Tukur ya ce dalilin da ya sa da'awarsa ta fita daban shi ne ""zamowa fitaccen malamin makaranta, to da'awarsa ta fita daban. ""Da yake ana fuskantar matsanancin talauci, to talakawa na jin dadi idan suka kewaye ni ina fadin a saki kalmomin a taimaka wa bayin Allah, a saki kayayyaki da sauransu, wannan ya sa mutane ke ƙaunar zama wajen wa'azina."" An haifi Malam Muhammad Tukur Sani Jangebe a garin Jangebe a ranar 26 ga watan Oktoba 1959, a masarautar Talatar Mafara da ke jihar Zamfara. Ya fara karatun Alkur'ani a wajen kanin mahaifinsa Malam Muhammadu Ana Ruwa, daga nan zuwa ga kakansa Malam Alhassan a garin Gusau. Amma inda ya yi karatu mai zurfi, shi ne a wajen Malam Abdurrahman Malam Ango Kalgawa a garin Gulma, inda ya shekara bakwai a hannunsa. A nan ya koyi daukacin karatun Alkur'ani da rubuta shi da sauke shi, daga baya ya ci gaba da karatun littafan musulunci daga garin Gulma zuwa Sakkwato, da Zaria ya kuma dangana ga marigayi Sheikh Abubakar Gumi a jihar Kaduna. Cikin ikon Allah ya samu gurbin karatu makarantar nazarin harshen Larabci da addinin Musulunci ta Sultan Abubakar da ke jihar Sakkwato. Daga nan ya ci gaba da karatu a makarantar nazarin addinin Musulunci a harshen Hausa da Larabci CICAS duk dai a Sakkwato, bayan nan ya ci gaba da karatu a Jami'ar Usman Danfodiyo. Malamin ya kuma yi fice wajen mata a jihar Sakkwato saboda yadda yake da'awar a ba su hakkinsu da sauransu. Malamin dan ƙwallo ne a zamanin kuruciyarsa, ""Da kyar da sidin goshi kakana ya raba ni da ƙwallo, domin sai an tara yara za a yi karatu ni kuma ina can ina buga ƙwallo. Shi ya sa a duk lokacin da na ji ana yi wa yara fada kan kwallon kafa sai dai na yi wa'azi ba na tsaurarawa domin ni ma ta dan debe ni."" Wani abu da ya tsaya masa a zuciya da ransa ke ɓaci duk lokacin da ya tuna, shi ne yi wa 'yan fashi addu'a. ""Lokacin ina unguwar Zabarmawa, 'yan fashi sun taba zuwa gidana lokacin ina cikin wahala ba na aikin komai, ina azumi sai na aika aka sayo min kunu na naira 100. Sai suka zo suka ce suna son gani na har da tambayar yaya aka yi nake shan kunu, na ce ba ni da hali. ""Ashe ɓarayi ne ɓoye da bindiga, suka ce za a kawo min sadakar kudi da abinci na ba su tukwuici, na ce ba ni da komai, ba su cuce ni ba ko iyalina. Sai gudan ya ce na raka shi, mu na fita sai ya yi shewa sai wani ya fito da babur ƙato sai ya hau, sai wani ya sake fitowa su uku. ""Suka ce malam a yi mana addu'a, na ce Ubangiji Allah ya tsare ku Allah ya kare ku, kawai sai ganin bakin bidiga na yi ta wajen danjar babur."" Malam Muhammad Tukur Sani Jangebe yana da mata da ƴaƴa 49. Amma a yanzu 28 ne a raye, yayin da 11 suka rasu. Babban burin shi shi ne, ""Allah ya sanya al'ummar Hausawa su hada kai, mu yi maganin rarrabuwar kawuna, mu kawo karshen barace-barace, rubuce-rubucen batanci na al'ummar Bahaushe, burina karshe na mutu na shiga aljanna.""" https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-57765789 +health Coronavirus: BBC ta amsa tambayoyin da kuka aiko "Shekarar 2020 ta zo da wani babban al'amari wanda ya dauki hankalin duniya baki daya- wato sabuwar kwayar cuta ta coronavirus da ta bullo daga Wuhan, babban birnin lardin Hubei na kasar China wadda ke haifar da cuta mai suna covid-19. Cutar ta bulla ne a watan Disambar 2019 amma kawo yanzu ta zama annobar da gaba daya duniya ke kokarin yaki da ita. Daga farko da ta fara bayyana, likitoci a birnin Wuhan sun yi tunanin mura ce mai zafi ke kama mutanen saboda yadda alamominta ke kama da na mura. Amma daga baya, da cutar ta fara yaduwa ne aka fahimci cewa wata sabuwar cuta ce da take shafar numfashi. Bullarta ke da wuya, kasashen duniya suka fahimci cewa ta zama annoba saboda yadda take saurin yaduwa a tsakanin mutane. Haka kuma, Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta ayyana ta a matsayin wata annoba da ta addabi kasashen duniya baki daya. Kawo yanzu, coronavirus ta yadu zuwa kasashen duniya sama da 160 kuma ta kashe mutum fiye da 14,000. Haka kuma, a fadin duniya sama da mutum 300,000 ke dauke da cutar a yanzu, kuma mafi yawansu a wajen China suke. Wasu na iya yin mamaki, ganin cewa cutar ta bulla a China kuma ta yi mummunar barna saboda lokaci da aka dauka kafin a fahimci irin cutar. Nahiyar Turai ta kasance cibiyar annobar coronavirus kuma yawan masu dauke da cutar na karuwa a kasashen nahiyar da dama. Ga amsoshin tambayoyin da kuka aiko mana kan cutar ta coronavirus ko covid-19. A cewar Hukumar lafiya ta Duniya, WHO, Coronavirus wani gungun kwayoyin cutane da ake kira 'virus' da ke iya haifar da rashin lafiya ga mutane da dabbobi. A cikin mutane, rabe-raben coronavirus da yawa na janyo cutukan numfashi kamar mura da kuma munanan cutukan numfashi kamar MERS da SARS da kuma sabuwar cutar numfashi ta coronavirus da aka gano kwanan nan, wacce take janyo cutar COVID-19. Ana tunanin wannan sabuwar cutar ta coronavirus ta samo asali ne daga wata kasuwar sayar da naman dabbobin dawa da aka haramta sayarwa a Wuhan. Wato dai cutar ta samo asali ne daga naman dabbobi. Duk da cewa an sha ambato naman jemagu a matsayin asalin cutar, babu tabbas a kan hakan kuma ana ci gaba da bincike. Cutar coronavirus na shafar huhu don haka ake ce mata cutar numfashi. Alamominta na farawa ne da zazzabi, sai tari (marar majina) ya biyo baya daga nan kuma sai mai dauke da cutar ya ji shan numfashi na yi masa wahala. Alamominta na farko-farko kan yi kama da alamomin mura da aka saba gani yau da kullum, sai dai ita coronavirus na zuwa ne da zazzabi mai zafin gaske da nauyin kirji ko ciwon hakarkari da shan numfashi da kyar. Kwayar cutar na shiga jiki ne idan wani mai dauke da ita ya yi tari a kusa da mutane, sai kwayoyin cutar su bazu a kan teburi ko hannun kofa ko a fuska ko hannun mutanen da ke kusa. Daga nan sai ta shiga makogaro ta kafar hanci ko baki ko ido, sai ta gangara zuwa huhu, daga nan kuma sai ta yi ta hayayyafa tana yaduwa har su kai ga shiga kwayoyin halitta da yawa da ke cikin jikin mutum. Idan kwayar cutar coronavirus ta shiga jikin mutum, ta kan bayyana bayan kusan kwanaki biyar inda daga nan ne alamunta suke fara nunawa. Amma Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta ce kwayar cutar na iya zama a jikin mutum har tsawon mako biyu kafin a fara ganin alamominta. Wasu masu bincike sun ce ta kan kai kwana 24 ma a jikin mutum sannan ta bayyana. Dakta Nasiru Gwarzo wani masanin harkar lafiya ne a Najeriya, ya ce duk wanda ya yi tafiya zuwa wani yanki da cutar take, da ya koma gidansa dole ne ya killace kansa har sai ma'aikatan lafiya sun duba shi. Wani binciken Hukumar Lafiya ta Duniya ya nuna cewa cikin mutum 56,000 da suka kamu da cutar covid-19: Wannan na nuna cewa mafi yawan mutanen da za su ko kuma suka kamu da cutar covid-19 za su warke. Bincike ya nuna cewa cutar kan shiga jikin wasu kuma ba za su fuskanci wasu alamomi ba, ko kuma su fuskanci kadan daga cikin alamominta. Alkaluma sun nuna cewa mutum fiye da 300,000 ne suka kamu da cutar a duniya zuwa 19 ga watan Maris na 2020, amma kusan mutum 14,000 ne kawai cutar ta kasha. Kuma mutum takwas cikin 10 na wanda cutar ta kama za su warke bayan fuskantar alamominta sama-sama. Wakilin BBC kan harkokin lafiya, James Ghallager ya ce garkuwar jikin dan adam na aiki tukuru don yaki da cutar coronavirus don kuwa ta kan fahimci cewa wani abu (wato kwayar cutar) mai hadari ya tunkaro ta don haka sai ta aika wa sauran sassan jiki cewa wani abu marar kyau na shirin faruwa da su. Daga nan ne garkuwar jiki take fitar da wani sinadari mai suna Cytokines, wanda ke ya zama kamar dakari ne a jikin. Wannan ne ke haifar da zazzabi da rashin karfi a jika ga mai fama da cutar. Dakta Gwarzo y ace ""A halin yanzu babu magani ko riga-kafin cutar coronavirus amma ana nan ana bincike."" Amma BBC ta gano cewar wasu masu bincike sun samar da riga-kafi kuma sun fara gwada ta a jikin dabbobi da mutane. Idan suka yi nasara za a fara bayar da ita zuwa karshen shekarar nan. Kwararru sun ce za a kwashe watanni da dama kafin a sani idan lallai riga-kafin za ta yi aiki. Sai dai wani abin dubawa a nan shi ne, ko da an yi nasara riga-kafin ta yi aiki kafin shekara mai zuwa, samar da ita da yawa, yadda har za ta isa duka kasashen duniya jan aiki ne. An yi wa wasu mutum hudu allurar riga-kafin a cibiyar bincike ta Kaiser Permanente da ke birnin Seattle a Washington din Amurka, a cewar kamfanin dillancin labarai na AP. Ana warkewa daga cutar coronavirus ta hanyar bin dokokin da likitoci suka bayar kamar hutawa sosai da yawan shan ruwa da kula da tsaftar jiki da ta muhalli. Idan mutum ya ji alamun cutar coronavirus, sai ya yi gaggawar sanar da ma'aikatan lafiya ta hanyar buga masu waya. Amma Dakta Gwarzo ya ce kada mutum ya yi saurin zuwa asibiti don idan yana dauke da cutar zai iya cutar da mutaen da dama ""ta hanyar yada ta ga ma'aiakatn lafiyar da saura marasa lafiyan da ke asibitin da wadanda zai gamu da su a hanya."" Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce cutar COVID-19 ta fi wahalar da tsofaffi da mutanen da ke da wata cuta ta daban kamar hawan jinni ko ciwon zuciya ko ciwon huhu ko daji ko ciwon suga. Don haka idan mutum na da isasshiyar lafiya kuma yana cin abinci mai gina jiki, zai yi wuya cutar ta durkusar da shi ko ta kashe shi. Cutar coronavirus tana kama mutane daga ko wane jinsi da kabila da addini da shekaru. An samu bullar cutar a kasashen duniya sama da 160 kuma a duka kasashen nan akwai farar fata da bakar fata da manya da yara kanana da mabiya addinai daba-daban na duniya. Kasar Saudiyya da Iran na daga cikin manyan kasashe musulunci da cutar ta bulla kuma kawo yanzu sama da mutum 1000 sun kamu da cutar a wadannan kasashe biyu hade. Bullar cutar coronavirus a Saudiyya ne ma ya sa kasar ta dauki wasu tsauraran matakai don hana yaduwar ta. Saudiyya ta hana 'yan sauran kasashen duniya da 'yan kasarta yin aikin Umra na wucin gadi, sannan ta killace dakin Ka'aba ta hanyar zagaye shi da wani shinge. Hikimar yin hakan shi ne don hana yaduwar cutar ganin yadda ake cunkuso a wurin dawafi. Mutum sama da 40 ne suka kamu da cutar coronavirus a Saudiyya kuma har a garin Makka an samu sama da mutum 20 da cutar. Amma an samu mutum daya da ya warke cikinsu. A kasar Iran kuwa, sama da mutum 17,000 ne suka kamu da cutar ciki har da ministan lafiyar kasar Iran Hirirchi da mataimakiyar shugaban kasar Masoumeh Ebtekar. Hukumar lafiya ta Duniya ta sanar cewa ita ce kasa ta uku a duniya da cutar ta fi shafa. A Afirka, kawo yanzu cutar ta shiga kasashe sama da 30 kuma an samu 'yar Afirka ta farko da cutar ta kashe a Burkina Faso. Haka kuma, a Najeriya ma an samu mutum takwas masu dauke da cutar kamar yadda Hukumar Kula da Yaduwar Cutuka ta kasa, NCDC ta sanar, kuma cikin wadannan mutane har da jaririya 'yar mako 6. Don haka, cutar coronavirus na kama musulmi kuma tana kama bakar fata da kananan yara kuma ta na tasiri a yankuna masu zafi, akasin yadda wasu ke cewa. Idan kana kula da marar lafiya mai dauke da cutar, ga hanyoyin da za ka bi don kare kanka: Kada ka kusanci mai dauke da cutar, ka bar tsakanin a kalla mita 2 da shi ko ita, a cewar Hukumar Lafiya ta Ingila. A takaita lokutan da ake zama tare a matsattsen wuri kamar dakin girki kuma a tabbata iska na kewayawa a duka dakunan gidan. Zai fi kyau su killace kansu a daki daya su kadai. Mai fama da cutar zai yi amfani da tawul da zannuwansa daban da sauran mutanen gidan. Idan da hali a ware masu makewayinsu, idan kuma babu hali da zarar sun yi amfani da makewayin sai an wanke shi tas. A jira awa 72 kafin zubar da abubuwan da suka yi amfani da su kamar tolifefa ko audugar mata bayan an kulle su a jakar leda. Wakilin BBC a fannin lafiya, James Ghalleger ya ce babu takamaimiyar amsa kan wannan tambayar amma akwai hanyoyi uku kwarara da za a iya bi don kawo karshen cutar: Sai dai ko da yawan masu dauke da cutar ya fara raguwa nan da wata uku masu zuwa, to hakan fa ba yana nufin an kawo karshen matsalar ba ne. Za a dauki tsawon lokaci kafin annobar ta gama tafiya - watakila ma shekaru. Abin da kasashe ke bukata shi ne ''daukar matakin fita daga wannan kangi'' - hanyar da za a dage wadannan matakan a koma rayuwa yadda aka saba. Amma ga alama coronavirus ba ta shirya tafiya ba a yanzu. Idan aka dage matakan takaita walwalar jama'a da ke dakile yaduwar cutar, to kuwa lallai za a samu karin mutanen da za su kamu. Wannan tambaya ce da har yanzu ba ta da tsayayyar amsa saboda kan kwararru ya rarrabu inda wasu ke ganin cewa idan mutum ya kamu da cutar sau daya ba ya iya sake kamuwa saboda jiki na kafa garkuwa da ita. Yayin da daya bangaren ke ganin cewa wasu na iya sake kamuwa da cutar. Ana ci gaba da bincike a kan wannan batu kuma ko a Burtaniya, Sir Patrick Vallance, babban mai mai wa gwamnati shwara kan kimiyya da farfesa Chris Whutty, babban mai bai wa Fairanminista Boris Johnson shawara, sun ce zai yi wuya wanda ya taba yin cutar ya sake kamuwa. Daga karshe, akwai abubuwan da yin su ba zai kare ka daga kamuwa da coronavirus ba kuma suna iya cutar da kai, kamar yadda WHO ta wallafa a shafinta:" https://www.bbc.com/hausa/labarai-51964392 +health Karanta yadda BBC ke aiki don karfafa aminci da fadin gaskiya a labaran intanet "Masu bibiyar BBC a Burtaniya da sauran kasashen duniya na ganinta a matsayin kafa mai samar da amintattun labarai. Shafinmu na intanet, kamar talabijin din mu da tashoshinmu na rediyo ya kasance mai gaskiya da rashin nuna bambanci da dogaro da kai da adalci. Ka'idojinmu na aikin jarida sun ce: ""Duk abin da muke yi ya ta'allaka ne kan amincewar da masu bibiyarmu ke da ita kan shirye-shiryenmu. Muna da 'yanci kuma ba ma nuna wariya kuma mun tsayar da gaskiya. Mun mayar da hankali wajen kaiwa kololuwar fitar da gaskiya da kin nuna bambanci kuma mun dage wajen kaucewa yaudarar masu bibiyarmu, walau a sane ko a cikin rashin sani. ""Jajircewarmu kan rashin nuna bambanci ita ce ginshikin dangantakar nan ta amincewa. A duka shirye-shiryenmu, za mu duba ko wane labara bil hakki da gaskiya. Za mu duba dukkan bayanai masu muhimmanci bisa adalci da gaskiya."" Mun san cewa gane sahihan labarai a intanet na iya zama abu mai rikitarwa. Mun kuma san cewa masu bibiyar labarai na so su kara fahimtar yadda BBC ke samar da labarai. Saboda wadannan dalilai, BBC NEWS ta ke kara matsa kaimi wajen yin bayani kan irin bayanan da kuke karantawa ko kallo a shafinmu na intanet, da kuma wurin wadanda da inda bayanan ke fitowa sannan yadda ake tsara labara ya fito yadda yake. Ta yin haka, za mu taimaka maka ka gane abinda ya sa za a iya amincewa da BBC News. Haka kuma, muna shirya wadannan bayanan na irin labaran da za a iya amincewa da su ta yadda za su dace da na'urori, ma'ana ana iya tsinto su ta hanyar lalubowa a intanet da shafukan sada zumunta da muhawara, ta hanyar taimaka masu gane kafofin yada labaran da suka kamata. BBC ta dade tana da dokokinta na aikin jarida da ake bi wajen tsara duka shirye-shiryenmu, wadanda kuma ke sa 'yan jaridarmu a hanya. Mun jere duka bangarori masu muhimmanci na dokokinmu a wannan shafi, don saukake maku yadda muke aiki da su a ofisoshinmu Manufa: Manufar BBC it ace ta yi aiki don biyan bukatar al'uma, biya wa duka masu bibiyarta bukata ta hanyar samar da sahihan labarai masu inganci da ke sanarwa da ilimintarwa da nishadantarwa. Cikakkun bayanai na BBC Charter. Tsarin Mallaka da Kudade: Muna da 'yanci don haka babu wasu daga wajen da ke mana kutse da zai iya yi wa gaskiyarmu a aikin jarida zagon kasa. Masu bibiyarmu su sani cewa matakan da muke dauka basu da alaka da siyasa ko matsin lambar kasuwanci ko ra'ayin wani mutum. Za ku iya samun Karin bayani kan yadda BBC News ke samun kudinta, a Burtaniya da kasashen waje a cikin BBC Charter on the independence of the BBC. Ranar da aka kafa: An kafa BBC ranar 18 ga watan Oktobar 1922. Karanta Karin bayani kan tarihin BBC. Manufar Da'a: Dokokin BBC na Aikin Jarida sun zayyano yadda za a nuna da'a a aikin da kuma ahnyoyin da ya kamata a bi wajen nuna da'a a duka shirye-shiryenmu. Karin bayani: Manufarmu kan daukar ma'aikata masu bambanci a jinsi da launin fata da addini: Karanta Karin bayani kan mayar da hankali da BBC ta yi kan daukar ma'aikata daga dukkan jinsi da asali da launin fata da kabila da addini a BBC Charter. Rahoto kan daukar ma'aikata masu bambanci a jinsi da launin fata da addini: Fahimci yadda BBC NEWS ke aiki tukuru don kara yawan ma'aikata daban-daban a wannan Rahoton kan bayanin daidaito. Gyare-gyare: BBC ta mayar da hankali kan cimma gaskiya. Ana iya samun manufofinta da suka shafi gyare-gyare a wannan bangaren na Dokokinmu na Aikin Jarida. Dole ne Shirye-shiryenmu su zama suna da majiya, bisa shaidu masu karfi da aka tabbatar sahihai ne, kuma aka bayyana su karara yadda za a fahimta. Dole mu zama masu gaskiya kana abin da ba mu sani ba kuma mu guji jita-jita. Idan har muna zargi ko muna da bayanan da ba za mu iya tabbatarwa ba, lallai ne mu bayana hakan karara. A shirye muke mu amshi laifin kuskure idan muka yi kuma mu yi koyi da kuskurenmu. Idan aka gyara wani kuskure a wani labari a shafinmu na intanet tun bayan wallafa shi, za mu sa bayani a karshen labarin don alamta wa mai karatu cewa an yi gyara a labarin tare da ranar da aka yi gyaran. Idan aka samu karamin kuskure wanda ba zai taba muhimman abubuwan da ke cikin labarin ba (misali ba a rubuta suna daidai ba), za a yi gyara ba tare da an sa alama a karshen labarin ba. Labarin da aka wallafa zai kasance a cikin kundin labaranmu a shafin intanet har abada, sai dai idan dama can an wallafa labarin ne don takaitaccen lokaci. Akwai lokutan da saboda umarnin kotu ko kuma tsaron lafiyar/rayuwar wasu, ko kuma kauce wa ka'idojin aiki da ba za a iya gyara labarin ba sai dai a cire shi gaba daya Karin Bayani: Dokokin Tantancewa/Bin-Diddigi: Manufar BBC ta tsage gaskiya da tantancewa na rubuce a Dokokin Aikin Jarida kan Tsage Gaskiya. Majiyoyin da basu da suna: Manufar BBC da dokokinta kan amfani da majiyoyin da ba a sani ba ko wadanda bas u da suna na zayyane a cikin Dokokin Aikin Jarida. Karin Bayani: Kawo Korafin da za a iya yin wani abu a kansa: Tsarin BBC na korafe-korafe na cikin Tsarin BBC kan Korafe-Korafe. Shugabanci: Ka san manyan tawagogin da ke tafi da bangaren labarai: Majalisar BBC News. Labaran da ake wallafawa a BBC News wadanda 'yan jaridar ne da kansu suka bibiyi asalin labarin, na zuwa da sunan dan jaridar da ya rubuta labarin, kamar yadda ake yi wa labaran da 'yan jaridar da ke kwarewa a wani bangare suka rubuta. Labarai na bai daya, wadanda ke da bayanai daga bangarori da dama ciki har da kamfanonin dillancin labarai, da bangaren BBC Newsgathering mai tattaro labarai da bangaren watsa shirye-shirye na BBC ko kuma wanda ma'aikatan BBC da dama suka sa hannu a cikinsa, ba su daukar sunan wadanda suka rubuta shi. TRABE-RABEN AIKI BBC News na banbance yin rahoto kan bayanan gaskiya da bayyana ra'ayi. Muna amfani da alamomi shidda da nau'ra ke iya karantawa: Ya kamata shirye-shiryenmu su zama suna da majiyoyi da suka dogara da shaidu masu karfi, kuma wadanda aka gwada sosai sannan a gabatar da su da yare mai saukin fahimta. Muna kokarin zama masu gaskiya kana bin da ba mu da masaniya a kai don gujewa zargi. A lokutan da BBC News ta dogara kan majiya daya kan wani bangare mai muhimmanci na shirye-shiryenta, za mu dage wajen ambatar sunan majiyar inda zai yiwu. Sau da yawa muna Ambato rahotannin da aka fitar a hukumance da alkaluma da sauran majiyoyin bayanai, don ba ku damar gane bayanan da muke kawo maku rahoto a kai. Duk lokacin da ya dace, muna Ambato wasu shafukan intanet masu muhimmanci da ke da karin bayani. Ga labaran da suke da rikitarwa, kamar labaran binciken kwakwaf ko labaran da suka kunshi alkaluma da dama, za mu taimaka maku ku fahimci yadda muka gudanar da aikin ta hanyar nuna maku bayanan bayan fage da kuma bayyana wasu yarjejeniyoyi da zato ko wasu tsare-tsaren da muka bi muka rubuta labarin- misali, tsarin da muka bi muka rubuta labarin; yawan mutanen da muka yi bincike a kansu; wakilci; bambanci tsakanin sakamakon bincikenmu da ainihin yadda abin yake a zahiri; yadda muka tattara bayanai; muhimmancin inda muka gudanar da b da lokutan da muka tattara bayananmu." https://www.bbc.com/hausa/game-da-mu-49283501 +technology Ƙoƙarin samar da daidaiton jinsi a rububin zuwa duniyar wata "Shirin komawar ɗan Adam duniyar wata tun bayan shekarar 1972 zai fuskanci babban ƙalubale a ranar 29 ga watan Agusta, a lokacin da hukumar Nasa za ta harba kumbonta mai suna Artemis 1. Kumbon, shi ne farko a wani ɓangare na yunƙurin kai ɗan Adam dandariyar ƙasar duniyar wata nan da shekarar 2025 ko 2026. A karon farko, mace da kuma wani baƙar fata za su bi sawun fararen fata 12 da ke duniyar watan. Farfesa John Logsdon mai shekara 84 na fatan sake ganin lamarin a kan idonsa. Kafin ya zama ƙwararre kan harkokin sararin samaniya, a shekarar 1969 ne ɗan Amurkar ya samu damar harba kumbon Apollo 11. Shi ne kumbo na farko da ya kai 'yan Adam duniyar wata: wato Neil Armstrong da Buzz Aldrin. ""Na samu shiga ginin da za a harba kumbon kuma na ga mutane na wucewa ta kusa da ni kafin su shiga abin hawan da zai kai su can,"" kamar yadda Farfesa Logsdon ya faɗa wa BBC. ""Yanzu ina fatan na ƙara tsawon rayuwa don na shaida hakan."" Zuwa duniyar wata zai sha bamban a yanzu sakamakon yunƙurin Nasa na daidaita jinsin masu zuwan. An bai wa mata damar zuwa duniyar watan. Su ne rabin tawagar mutum 18 da aka zaɓa a shirin Artemis. An shirya tafiye-tafiyen da dama. Wani mutum da kafofin yaɗa labarai suka mayar da hankali kai ita ce Stephanie Wilson mai shekara 55. Ƙwararriyar 'yar sama-jannati ce da ta je sararin samaniya sau uku kuma mace wadda ba farar fata ba ta biyu da ta je sama. ""Wata hujja da mata suka kafa game da ci gaba,"" a cewar Wilson cikin hirarta da shafin Space.com a 2020. ""Lallai na yi farin ciki da aka saka ni a rukunin kuma zaƙu na ga wace ce mace ta farko da za ta bi mu a shirinmu na ci gaba da nazartar wata."" Rabin tawagar waɗanda duka Amurkawa ne, ba fararen fata ba ne. Ya zuwa Nuwamban 2021, mata 75 ne kacal cikin 600 da suka taɓa zuwa sararin smaaniya, a cewar Nasa. Musaman a Amurka, mata masu son zuwa sararin samaniya na fuskantar wariyar launin fata a hukumance. Nasa ta ɗauki rukunin farko na masu zuwa sama daga sojoji a shekarun 1960, lokacin da ba a amince wa mata su tuƙa jiragen soja ba. A gefe guda kuma, Tarayyar Soviet ta tura Valentina Tereshkova - wata tsohuwar ma'aikaciyar masaƙa kuma ƙaramar mai wasan surmiyowa daga sama - zuwa sararin samaniya a 1963. Shekara 20 bayan haka, Amurka ta tura mace ta farko mai suna Sally Ride a kumbon Challenger. ""Cikin sauƙi za a iya tuna yadda aka dinga nuna wa mata wariya da ke son zama 'yan sama-jannati ƙarni ɗaya kaca da ya wuce,"" in ji Dr Margaret Weitekamp, shugabar sashen tarihin sararin samaniya a gidan tarihi na Amurka mai suna National Air and Space Museum. ""Har yanzu akwai wariyar amma dai ana samun ci gaba a shirin."" Akwai kuma matsalar wariyar launin fata: 14 kacal daga cikin Amurkawa 330 da Nasa ta aika sama ne baƙar fata - sannan wasu 14 ɗin daga ciki 'yan asalin nahiyar Asiya ne. Akwai kuma matsalar wariyar launin fata: 14 kacal daga cikin Amurkawa 330 da Nasa ta aika sama ne baƙar fata - sannan wasu 14 ɗin daga ciki 'yan asalin nahiyar Asiya ne. Ita kuwa Tarayyar Soviet ta aika mutum na farko wanda ba farar fata ba tun a 1980: ɗan ƙasar Cuba mai suna Arnaldo Tamayo Mendez. Hukumar na sane cewa akwai jan aiki. ""Akwai buƙatar mu dinga yin adalci game da yadda ake tura mutane a shirin baki ɗayansa,"" in ji Kenneth Bowersox, wani mataimakin shirye-shirye na Nasa yayin taron manema labarai a 2021. Daga 1960 zuwa 1973, Amurka ta kashe dala biliyan 25.8 a kan Apollo - ko kuma kusan biliyan 300 a yanzu idan aka kwatanta da hauhawar farashi. Duk shugaban ƙasar da aka yi a Amurka na buƙatar dalili mai ƙarfi kafin ya kashe kuɗin. Yaƙin cacar-baka tsakanin Amurka da Tarayyar Soviet ne babban dalilin. Ya kai har kan sararin samaniya a 1957, lokacin da Rasha ta harba tauraron ɗan Adam na Sputnik wanda shi ne irinsa na farko. ""Yaƙin cacar-baka ne ya sa Amurka ta ƙirƙiri Apollo 11 da kuma gaggawar kashe maƙudan kuɗi wajen isa duniyar wata cikin gaggawa,"" a cewar Farfesa Logsdon. Shugaban Amurka Richard Nixon ya soke shirin Apollo sannan ya umarci Nasa ta ƙera rokar zuwa sama. Nasa ta sauya tunani game da tura mutum zuwa wata kuma ta mayar da hankali kan duniyar Earth kamar shirin tashar zuwa sama ta duniya wato International Space Station (ISS). An samu sauyi lokacin da Shugaba Donald Trump ya ƙaddamar da shirin komawa duniyar wata. ""Wannan karon ba tutarmu kawai za mu kafa mu tafi ba,"" a cewar Trump a 2017. Shirin Artemis ba mai sauƙi ba ne - kasafin kuɗinsa ya kai biliyan 93, amma ƙwararru kamar Dr Jennifer Millard ɗan Birtaniya na ganin amfaninsa ya fi akasin haka." https://www.bbc.com/hausa/articles/c8850nzexg5o +business Matakan da suka kamata Buhari ya ɗauka domin fitar da Najeriya daga matsalar tattalin arziki "Masana tattalin arziki a Najeriya sun bayyana matakan da suke gani sun kamata Shugaba Muhammadu Buhari ya ɗauka domin ceto ƙasar daga koma-bayan tattalin arzikin da ta faɗa a cikin irin sa mafi girma cikin fiye da shekara 30. A ƙarshen makon jiya ne hukumar ƙididdiga ta ƙasar ta fitar da wata sanarwa da ta nuna cewa Najeirya ta fada matsin tattalin arziƙi karo na biyu cikin shekara biyar. Farfesa Mustapha Muktar, malami ne a sashen nazarin tattalin arziki na jami'ar Bayero da ke Kano, ya ce idan aka samu irin wannan matsala akwai matakai da dama da ake ɗauka wajen ganin an rage kaifin wannan matsala ko kuma an fita daga cikinta baki ɗaya. ""Ana iya fara komawa kasafin kuɗin ƙasa da aka yi a duba shi cikin nutsuwa, sai a rage duk wani abu da ake zaton muhimmancinsa bai kai ya kawo ba a halin da ƙasar ke ciki, domin a yi komai daidai ruwa daidai tsaki,"" in ji shi. ""Za kuma a iya komawa ga duka ɓangarorin tattalain arziƙin ƙasar a duba wanne ɓangare ne ya janyo koma-bayan domin a magance shi. Misali, ɓangaren masana'antu ne ko kuma ɓangaren ayyukan yau da kullum. ""Na uku, hukumomi su yi ƙoƙari su samar da ayyukan yi da kuma samar da bashi ga ƙanana da kuma manyan masana'antu, ko kuma su sassuta harajin da ake karɓa daga hannunsu,"" a cewar Farfesa Mustapha. A nasa ɓangaren, Farfesa Nazifi Darma, malamin tattalin arziki a jami'ar Abuja, yana ganin da a ce gwamnatoci a dukkan matakai - daga Tarayya da jihohi da kuma ƙananan hukumomi - za su ƙarfafa wa al'umma gwiwa wajen dogaro da kansu da an samu mafita. ""Saboda haka duk ƙoƙarin ɗan kasuwa idan gwamnati ba ta samar da tsare-tsare masu kyau da za su taimaka wa kasuwancinsa ba to babu in da za a je,"" in ji Farfesa Darma. Ya ƙara da cewa Najeriya na buƙatar tsarin tattalin arziƙi na dogon zango domin kuwa zai taimaka wajen dakushe matsalolin da za su riƙa tasowa a kusa a faɗn kasar baki ɗaya. Mecece matsalar koma-bayan tattalin arziki? Duka waɗannan farfesoshi sun amince cewa matsalar koma-bayan tattalin arziki na faruwa ne lokacin da alƙaluma na mizanin auna tattalin arziƙi (GDP) da ake amfani da su duk bayan wata uku suka nuna an samu koma-bayan arziki a watanni shidan na cikin shekara. Ba wani abu ba ne ɓoyayye a duniya ko wacce ƙasa na fuskantar bunƙasa ko kuma koma bayan tattalin arziki lokaci zuwa lokaci. Amma wannan ya danganta da matsalolin da ƙasa ke fuskanta da ke sanya ma'aunan tattalin arziki bunƙasa ko kuma akasin haka. Da yawa mutane na ganin GDP a matsayin kuɗin da ƙasa ke samu na cikin gida kawai, amma ma'anarsa ta wuce haka saboda yana auna duka hada-hadar da ake yi a ƙasa, kama daga abin da gwamnati take kashewa da abin da take tsammanin samu, in ji Farfesa Darma. Alƙaluman ma'aunin tattalin arziki da ake kira GDP suna da faɗi, amma sun hada: Bugu da ƙari da sabon tsarin haɗewar duniya wuri guda (Globalization) da kuma yadda ciniki ke ƙara buƙasa tsakanin ƙasashen duniya, ""ya sanya ana ƙirga hada-hada tsakanin kasuwanni cikin wannan ma'auni,"" in ji Farfesa Nazifi. Abubuwan da ke sa wa a faɗa irin matsalar tattalin arziƙi na da yawa amma domin masu karantawa su gane za mu raba su kashi biyu, in ji Dakta Shamsudden Muhammad na jami'ar Bayero a Najeriya. Buƙatun 'yan ƙasa da gwamnati da masana'antu: Lokacin da ya kasance 'yan ƙasa ba sa iya sayen abin da suke so komai ya yi tsada ga ƙarancin kuɗaɗe a hannun mutane, wannan dalilin zai iya sanya tattalin arziki ya yi baya ƙasa ta shiga abin da ake kira matsin tattalin arziki ko recession a turance. Durƙushewar ɓangaren waɗanda suke samar da kayayyaki: Idan ya kasance masana'antu ba sa iya samar da kayayyakin da suke sarrafawa saboda dalilai kamar na su yaƙi ko kuma tsauraran dokoki na gwamnati na haraji, ko kuma ita gwamnati a nata ɓangaren ba ta iya samar da man fetur da take haƙowa ko kuma buƙatarsa ta yi baya a kasuwar duniya, to su ma za su iya kai wa ga faɗawa matsalar tattalin arziƙi. Dakta Shamsudden ya ce amma a Najeriya ""matsalar cutar Covid-19 da ta ja aka kukkulle harkokin kasuwanci, kamar su ƙere-ƙere da harkokin sufuri na daga cikin abubuwan da suka janyo wannan koma-baya. ""Sai kuma dokoki da gwamnati take yi da kwata-kwata ba sa taimakawa masana'antu, kamar ƙarin kuɗin haraji da ƙarin kuɗin makamashi da rashin wutar lantarki da kuma faduwar darajar naira su ma sun ba da gudunmawa"". Farfesa Nazifi Darka ya ce kai-tsaye wannan matsala kan talaka take ƙarewa saboda idan an tashi korar aiki a masana'antu talaka ake kora. Idan abubuwan rayuwa sun yi tsada talaka ne ke gaza saya domin haka yana ji a jikinsa. Ko ƙarin ƙudin makaranta aka yi kan shi ƙarin ke ƙarewa, idan yunwa ce ake fama da ita ba za ka taɓa jin wani shugaba ko mai kuɗi na yi maka kukanta ba, in ji shi." https://www.bbc.com/hausa/labarai-55043312 +entertainment Bollywood: Fina-finai 4 da Salman Khan ya ƙi yi amma suka sa Shahrukh Khan ya shahara "Salman Khan da Shahrukh Khan suna daga cikin fitattun taurarin fina -finai a Indiya kuma sun shafe sama da shekaru 30 suna jagorantar harkar fina-finai. Su biyun, waɗanda aka haife su a 1965, sun fara fim a lokaci guda kuma sun zama sabuwar fuska a masana'antar fina -finan Bollywood, tare da samun nasarori na tarihi. Har zuwa yau sun shahara a harkar fina-finai kuma suna da magoya baya da yawa, sannan babu abin da ya ragu a ƙwarewarsu. Ana sa ran Salman zai fito a sabon fim din Shahrukh Pathan, kuma su biyun abokan juna ne. Amma idan aka zo tarihin fitowarsu a fina-finai, akwai fina-finai da dama da Salman Khan ya ƙi yi wadanda Shahrukh Khan ya karba ya yi kuma ya samu gagarumar nasara. Shi kansa Salman Khan ya bayyana cewa an fara haska shi a fim ɗin Baazigar kafin a nuna Shahrukh Khan. A cikin wata hira, ya ce: ""Na ƙi yin Baazigar. Lokacin da Abbas-Mustan ya zo mini da labarin, na tuntubi mahaifina. Ba su yarda ba. ""Lokacin da na yi watsi da fim ɗin, sun je wurin Shah Rukh, sannan sun sami yardar mahaifiyarsa! Amma ban yi nadama ba ko kaɗan."" An saki fim din Baazigar a watan Nuwamba 1993 kuma Shah Rukh Khan da Kajol da Shilpa Shetty ne manyan taurarin fim din. Kafin Shah Rukh Khan ya fito a fim din Dilwale Dulhania Le Jayenge, rahotanni sun ce an bai wa Salman Khan damar fitowa a matsayin Raj Malhotra. Hatta Saif Ali Khan an nemi ya fito a fim din, amma rahotanni sun ce duka jarumai biyun sun ki. Ba a san dalilin da ya sa jaruman biyu suka yi kunnen uwar shegu da bukatar fim din ba. Daga baya Sharukh Khan ya karɓi fim ɗin kuma sai ya yi shura. Shah Rukh da Kajol ne suka taka rawa a fim din Dilwale Dulhania wanda ya fito a watan Oktoban 1995. A wata hira da aka taba yi da shi, Salman Khan ya ce an yi masa tayin fitowa a matsayin Chak De! Indiya amma ya ƙi. Dalilin, in ji shi, shi ne cewa yana da matsala da taken fim din. Kafafan yada labarai na Indiya sun ruwaito cewa ya ki ya bata wa magoya bayansa rai daga Pakistan da Bangladesh. Labarin fim din ya shafi wani tauraro ne da ake ganin yana cin amanar kasarsa amma daga baya ya nuna goyon bayansa ga al'ummarsa. Sauran wadanda suka taka rawa a fim din sun hada da Vidya Malvade da Chitrashi Rawat da Sagarika Ghatge. Kamar yadda shahararrun jaridun Indiya suka bayyana, an zabi Salman Khan ya fito a fim din Saif Ali Khan Kal Ho Na Ho. Amma Salman bai so ya zama jarumi na biyu a fim din da Shah Rukh Khan ya shirya ba, don haka ya ƙi. Kal Ho Na Ho ya zama daya daga cikin fitattun fina -finan Bollywood, inda Sakh Rukh da Saif suka fito da Preity Zinta." https://www.bbc.com/hausa/labarai-58546375 +sports 'Yan Barcelona da za su kara da Cadiz a gasar La Liga mako na 32 Barcelona za ta kara da Cadiz a wasan mako na 32 a gasar La Liga da za su kece raini a Nou Camp ranar Lahadi. A wasan farko da suka fafata a gasar bana ranar 23 ga watan Satumbar 2021, sun tashi 0-0 ne. Barcelona mai kwantan wasa tana mataki na biyu a teburin La Liga da maki 60 iri da ya da na Atletico Madrid ta biyu da Sevilla ta uku wadda itama keda maki 60. Cadiz tana mataki na 18 a kasan teburin da maki 28, bayan da ta yi wasa 31. Tuni dai koci Xavi Hernández ya bayyana 'yan wasan da zai fuskanci Cadiz a karawar da za su yi ranar Litinin. 'Yan wasan Barcelona: Ter Stegen, Dest, Sergio, Riqui Puig, O. Dembélé, Dani Alves, Memphis, Adama, Braithwaite, Neto, Nico, Lenglet, L. De Jong, Jordi Alba. Sauran sun hada da Ferran, F. De Jong, O. Mingueza, Eric, Aubameyang, Gavi, Balde da kuma Arnau Tenas. Wadanda ke jinya: Gerard Piqué, Ansu Fati, Pedri, Sergi Roberto da kuma Samuel Umtiti Shi kuwa Ronald Araujo yana hukuncin dakatarwa. Wasa biyar baya aka yi tsakanin kungiyoyin biyu, inda Barcelona ta yi nasara a biyu da canjaras biyu, Cadiz ta ci daya. Jerin wasa biyar tsakanin Barcelona da Cardiz: 2021/2022 Spanish La Liga Alhamis 23 Satumba 2021 2020/2021 Spanish La Liga Lahadi 21 Fabrairun 2021 Spanish La Liga Asabar 5 Disamba 2020 2005/2006 Spanish La Liga Asabar 29 Afirilun 2006 Spanish La Liga Asabar 17 Disambar 2005 https://www.bbc.com/hausa/wasanni-61141409 +entertainment Yarima Charles ya bi sahun sauran mutanen duniya wajen jinjina wa mahaifiyarsa "Yariman Wales ya jinjina wa Sarauniya Elizabeth game da ""gagarumar nasarar"" da ta samu a bikin cikarta shekara 70 a kan karagar mulki. Yarima Charles ya yi maraba da fatan mahaifiyarsa cewa Camilla, wadda ita ce Duchess ta Cornwall, a ba ta mukamin Uwargida Sarauniya idan ya zama Sarki. Ya ce shi da matarsa ​​""suna matukar sane da karramawar"". Sarauniyar ita ce yar sarautar Biritaniya ta farko da ta yi bikin cikar shekara 70 a kan mulki, inda ta shafe ranar a keɓe. A cikin sakon bikin cika shekara 70 na mulkinta, Sarauniyar ta ce ""burinta na gaske"" ne Camilla ta sami wannan mukami. A cikin wata sanarwa da Yarima Charles ya fitar ya ce: ""Sadaukarwar da sarauniya ta yi don jin dadin jama'arta na kara janyo mata farin jini a kowace shekara. ""Muna matukar sane da irin karramawar da uwata ta yi mana. A yayin da muka tsaya tare domin mara mata baya tare da yin hidima da tallafa wa al'ummar yankinmu, uwargidana ta kasance mai goyon bayana a duk tsawon lokacin."" Sarauniyar ta soma mulki tana da shekaru 25, bayan rasuwar mahaifinta, George VI, a ranar 6 ga Fabrairun 1952. Sarauniyar ta ce, shekaru 70 kenan, kuma wannan rana ce da ba za ta manta da ita ba ""kamar rasuwar mahaifina, Sarki George na shida, dangane da farkon sarautata"". Sarauniyar mai shekara 95 a duniya ta fada a cikin rubutaccen sakon da ta aike wa al'ummar kasar cewa: ""Ina so in mika godiyata a gare ku duka bisa goyon bayan da kuke ba ni. ."" Wannan shi ne biki na farko da sarauniyar za ta yi ba tare da mijinta Duke of Edinburgh ba, wanda suka yi shekaru 73 da aure, wanda ya mutu a bara. Ta yi la'akari da irin nasarorin da ta samu daga tallafin da Yarima Philip ya ba ta ""ba tare da son kai"" ba kuma ta gode wa irin kyakkyawar niyya da ""dukkan al'ummomi da addinai da shekaru a kasar nan suka nuna mata"". Mutane da yawa sun taya Sarauniya murna a wannan rana mai cike da tarihi, ciki har da Boris Johnson, Theresa May da David Cameron - uku daga cikin firaministan Birtaniya 14 da suka yi a fadar firaminista ta No 10 a lokacin mulkinta. Mista Johnson ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa: ""Ina jinjina mata da yawa na hidimar da ta yi, kuma ina fatan za mu kai a matsayin wajan taya ta gudanar da bikin cika shekaru 70 a kan mulki a lokacin bazara."" Matar da ta gabace shi, Misis May, ta bayyana sarauniyar a matsayin ""mace mai ban mamaki, wadda ta sadaukar da rayuwarta wajen yi wa jama'arta hidima da kuma danginmu na kasa"". Mista Cameron ya ce : ""Ba za a iya samun kyakkyawan misali na aikin jama'a mai daraja da hidima ba."" Jagoran 'yan hammaya, Sir Keir Starmer, ya yi na'am da wadannan ra'ayoyin, yana mai cewa zai so ya mika godiyarsa ta tsawon shekaru 70 da ta yi na hidimar jama'a mara misaltuwa. Shugaban kungiyar ta Labour ya kara da cewa: ""Sarauniyar ta kasance mai matukar muhimmanci kuma mai kima a cikin duniyar da ke canzawa, wanda ke wakiltar tsaro da kwanciyar hankali ga kasarmu, a cikin abubuwan da suka faru a cikin shekaru saba'in da suka gabata.""" https://www.bbc.com/hausa/labarai-60277976 +entertainment ...Daga Bakin Mai Ita tare da Ibrahim Planner Daga Bakin Mai Ita shiri ne na BBC Hausa da ke kawo muku hira da fitattun taurari da mawakan harkar fim din Hausa na Kannywood kan abubuwan da suka shafi rayuwarsu zalla. A wannan kashi na 118, mun tattauna da tauraron fina-finan Hausa, Ibrahim Ayuba Ibrahim, wanda aka fi sani Ibrahim Planner inda ya amsa tambayoyi da dama da suka shafi rayuwarsa. https://www.bbc.com/hausa/articles/c727xj3dm4mo +business 'Yan gudun hijira za su samu tallafin dala miliyan 4.6 Majalisar wakilai a Amurka ta amince da wani kudurin doka inda za a samar da dala miliyan hudu da dubu dari shida domin tallafawa masu fama da matsi da kuma fatara da ke kan iyakar kasar. Tuni dama 'yan majalisar dattawan kasar suka amince da kudirin dokar inda kuma a yanzu ana jiran shugaban Amurkar Donald Trump ya rattaba mata hannu domin ta fara aiki. An dai amince da dokar ne bayan da 'yan jam'iyyar Democrats hakar su ta gaza cimma ruwa ta bangaren kara daukar matakai domin kare 'ya'yan baki da suke gudun hijira kasar. Shugabar Majalisar Wakilan Kasar Nancy Pelosi, ta bayyana cewa samar da kudade domin tallafa wa a kan iyakar kasar shi ne babban abin da yakamata a yi. Ko a kwanakin baya dai Fafaroma Francis ya bayar da tallafin dalar Amurka dubu 500 ga 'yan gudun hijira. An bayyana cewa kudin za su amfani 'yan gudun hijiran da suke gararamba ko kuma suka rasa mafaka a Mexico a kokarin da suke yi na tsallake iyakar Amurka. Hakazalika ko a kwanakin baya hukumar 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa yawan mutanen da tashin hankali ya raba da muhallansu ya wuce miliyan 70, adadi mafi girma da aka taba gani a tarihi. A kididdigar da hukumar ke fitarwa duk shekara, ya nuna mutanen da yaki ke tilastawa barin gida, na gagara samun wurin da za su zauna cikin kwanciyar hankali. https://www.bbc.com/hausa/labarai-48797405 +politics Bijirewar Iran na damun Tarayyar Turai A sama-sama ana iya cewa Iran na janyewa daga yarjejeniyar nan ta 2015 kan samar da makamashin nukiliyar kasar. A jiya Talata hukumar IAEA mai sa ido kan yaduwar makaman nukiliya ta sanar cewa Iran ta tara kimanin sinadarin Uranium da yawansa ya nunka wanda aka amince ma ta tarawa har sau goma sha hudu. Ban da wannan batun ma, Iran ta ta kuma aiwatar da wani kashedi da ta yi cewa za ta jinginar da hadin kan da ta ke bayar wa ga masu binciken MDD su ci gaba da kai ziyarar ba-zata z cibiyoyin binciken nata. Birtaniya da Faransa da Jamus duka sun soki matakin na Iran, suna cea zai kara nisanta kasar daga matsayar da ka amince ta tsaya na yarjejeniyar ta 2015. Amma akwai wasu alamu ma su karfafa gwuiwa ga kasashen na Turai a bangaren diflomasiyya. Ministan harkokin wajen na Iran, Javad Zarif ya sanar da shirin kasar na komawa bisa teburin tattaunawa da Amurka nan ba da jimawa ba - wanda shi ne karon farko da hakan zai faru cikin shekara hudu, kuma wannan ganawar na cikin abubuwanda TT ke kokarin tabbatar wa an yi cikin watanni masu zuwa. https://www.bbc.com/hausa/56178777 +entertainment Yadda mata ke kallon uwar mijinsu a India "Ana cewa akwai matan aure masifaffu da kuma mazan aure da ke daka tsawa da turbune wa matansu fuska, sai dai duk cikinsu babu wanda ya kai isa da mallakar uwar miji. Akasari ana yi wa uwar miji a Indiya kallon wata kasaitacciya mai ikon cewa a yi ko a bari, da ke fafutukar kwace iko a hannun surukarta wato matar danta, ga kuma nuna isa a kan dan nata da ma sauran mutanen gida. Tauraruwa ce da ta yi fice a wani shirin wasan kwaikwayo a Indiya wanda akan fassara sunansa da: ""Ai ita ma uwar mijin, ta taba zama matar dan wata.'' A yanzu, uwar miji a Indiya wata aba ce da masana ke gudanar da wani gagarumin bincike mai yiwuwa ma shi ne irinsa na farko a kanta. Da yake mafi yawan mata a wannan yanki na Indiya kan tare a gidan dangin miji ne idan sun yi aure, alakar da suke kullawa da uwar miji tana da matukar muhimmanci. Kuma fadi-tashinsu na rayuwa a wasu lokuta na ba da gudunmawa a kan gagarumin sunan da uwar miji ke yi. A 2018, masu bincike daga Boston din Amurka da kuma birnin New Delhi sun zanta da matan aure 671, wadanda shekarunsu suka kama daga 16 zuwa 30 daga kauye 28 cikin lardin Jaunpur na jihar Uttar Pradesh, jihar masu ra'ayin mazan jiya da ke da yawan hada-hada da yawan mutanen da suka kai al'ummar kasar Brazil. Mafi yawan matan dai Hindu ne kuma rukunin kasa na al'umma. Kusan kashi saba'in cikin 100 na matan na zaune ne a gida daya da uwar miji. Masu binciken sun yi wa matan tambaya a kan huldarsu da danginsu da kawaye a wajen gidajensu. An tambaye su yawan ikon da uwar mijinsu ke da shi kan yadda suke kulla alaka da wasu. Da Kuma tasirin hakan ga 'yancin cin gashin kansu da hanyar samun ayyukan lafiya da dabi'arsu ta neman magani. Abin da masu binciken suka gano ga alama ya dusashe shingen da ke tsakanin almara da rayuwar zahiri. Sun gano cewa matan da ke zaune tare da uwar miji na da takaitaccen 'yancin walwala da na kulla alaka da wasu a waje. An dauka cewa yawan shigi da fice na iya taimaka musu wajen samun karin bayanai, da kulla zumunci da kawaye, da samun kwarin gwiwar yarda da kai da habaka burin rayuwa. Haka zalika, shawarar da za su cimma dangane da lafiya da haihuwa ko tsarin iyali tana da alaka da irin wadannan kawanyen hulda. Kimanin kashi 36 cikin 100 na matan da aka zanta da su ba su da kawa ko dangi na kut da kut a daukacin lardin, kashi 22 cikin 100 ba su da kawa ko dangi na kusa a ko'ina. Kashi 14 ne kawai ake bari su fita zuwa asibiti su kadai, kashi 12 cikin 100 ne kawai ake bari su ziyarci kawaye ko danginsu a kauye ba tare da dan rakiya ba. Haka kuma masu binciken sun gano kashi 18 cikin 100 ne na matan da ke zaune da uwar miji ke da aminai kalilan a kauyensu. Uwar mijin takan takaita huldodinta na zamantakewa ta hanyar hana ta zuwa unguwa ita kadai ta yadda za ta sa ido kan halayyarta game da batun haihuwa da tsarin iyali. A wasu lokutan uwar miji ta fi suruka muradin a haifa mata karin jikoki takamaimai ma ta fi son a haifa mata maza. Kashi 48 cikin 100 na matan sun dauka cewa uwayen mazansu ba sa son ba da tazarar haihuwa. Binciken ya kuma gano cewa idan miji na tafiya zuwa ci-rani, uwar miji ta fi nuna isa kan zirga-zirga da huldodi da walwala da 'yancin cin gashin kai da yanke shawara." https://www.bbc.com/hausa/labarai-50969338 +sports Arsenal 2-0 Leicester City: Gunners ta ci wasa na biyar a jere a Premier Arsenal ta koma mataki na hudu a kan teburin Premier League, bayan da ta doke Leicester City 2-0 ranar Lahadi a Emirates. Wasa na biyar kenan a jere da Arsenal ta ci a gasar Premier League a kokarin da take na samun gurbin buga Champions League a kakar badi. Thomas Partey ne ya fara ci wa Gunners kwallo, daga baya Alexandre Lacazette ya kara na biyu a bugun daga kai sai mai tsaron raga. Da wannan sakamakon Arsenal ta koma ta hudu a kan teburin kakar bana da tazarar maki daya tsakaninta da Manchester United, wadda ta doke Tottenham ranar Asabar. Leicester City wadda ta sha kashi a Emirates karkashin koci Brendan Rodgers ta ci gaba da zama ta 12 a teburin Premier League. Arsenal wadda rabon da ta buga Champions League tun bayan kaka biyar ta ci gaba da taka rawar gani a bana, bayan da ta yi nasara a wasa tara daga 11 da ta buga a bayan nan a Premier League. Gunners wadda take da kwantan wasa uku na sa ran yin abin a zo a gani, domin ta samu buga Champions League a badi, kuma ranar Laraba Arsenal za ta fafata da Liverpool wadda ta ci 4-0 a wasan farko a bana a Anfield. Ita kuwa Leicester City za ta buga gasar Turai ta European Conference League karawar daf da na kusa da na karshe da Rennes ranar Alhamis. https://www.bbc.com/hausa/wasanni-60731349 +health Lafiya Zinariya: Illar rashin tsafta ga mata Masu iya magana dai kan ce rana ba ta karya sai dai uwar diya ta ji kunya! To albishinku, a yau uwar diyar ma ba zata ji kunyar ba domin sashen Hausa na BBC ya shirya tsaf don fara gabatar muku da wani sabon shiri, 'Lafiya Zinariya.' Lafiya Zinariya shiri ne da zai duba batutuwan da suka shafi kiwon lafiyar mata da suka hada da cucuttuka, hanyoyin kauce musu da matakan neman magani tun da wurwuri. Kazalika, a wannan sabon shiri wanda zai rika zuwa muku a duk mako, za mu tattauna da kwararrun likitoci da sauran masana a fannin kiwon lafiya da majinyata, don jin yadda rayuwa ta kasance musu, har ma da masu jinyar a wasu lokutan. A yau cikin shirin za mu duba batun da ya shafi tsaftar jikin mace. Wani batu da ke ci wa mata tuwo a kwarya musamma a Arewacin Najeriya shi ne yadda za a gyara jiki. A mafiya yawan lokuta akan samu yanayin da aure ke mutuwa sakamakon gyara tsaftar jiki. To sai dai bincike ya nuna cewa mata da dama na son ganin su tsaf-tsaf amma kangin talauci da suke ciki ya sa sai dai su gani a makwabta. Hakazalika, ana ganin wasu matan mazansu ne ba su damu da su sayo masu kayan gyaran jiki ba, duk da cewa maza na matukar kaunar macen da take da tsaftar jiki. Ku latsa wannan alamar lasifikar da ke kasa domin jin yadda shirin ya kasance. https://www.bbc.com/hausa/labarai-50782492 +technology Nau'in gahawar da ke jure wa tasirin sauyin yanayi "Masana kimiyya sun ce nau'in gahawar ""da aka manta"" cewa yana tsirowa a cikin yanayi mai dumi ka ya taimaka wa makomar shan gahawa a yayin da ake fama da matsalar sauyin yanayi. Sun yi hasashen cewa ba da jimawa ba kurbar Coffea stenophylla, wata gahawar da ke tsirowa da kanta da kuma dandanonta ke kama da na nagartacciyar gahawar Arabica, amma tana tsirowa ne a yanayi mai dumi. Yayin da yanayin zafi ya karu, gahawa mai kyau za ta kara kasancewa mai wuyar tsirowa. Bincike ya nuna cewa nan da shekara ta 2050, kusan rabin filin da ake amfani da shi wajen shuka nagartacciyar gahawa zai kasance marar amfani. Samun gahawar da ke tsirowa da kanta da kuma ke da dadin dandano kana mai jure wa lokacin fari ""wata babbar kyauta ce,"" in ji Dakta Aaron Davis, shugaban lambun binciken shuke-shuke kan gahawa ta Royal Botanic Gardens, Kew. Ya shaida wa BBC cewa ""Kasancewar wanda ya taba dandana irin wannan nau'in gahawar da dama ba su da wani kyau, ba su da dandano irin na Arabica, don haka tunaninmu a kan nagartarsa ba shi da yawa. ""Kuma hankalinmu ya dauke gabaki daya aka tunanin cewa wannan nau'in gahawa na da dadin dandano. Tana da wadannan darajoji da ke da alaka da jure wa sauyin yanayi: Za ta tsiro ta kuma girma a karkashin yanayi mai dumama fiye da nau'in gahawa na Arabica."" Coffea stenophylla nau'in gahawa ce da ke tsirowa da kanta a yankin Afirka taYamma, a baya an dauka cewa wannan nau'i ya riga ya bace daga kasar Ivory Coast. An sake gano shukar na fitowa a kasar Saliyo, inda tarihi ya nuna cewa nan ne ake nomanta a matsayin shukar gahawa a karnin da ya gabata. Ana gasa ta samfurin kwayoyin gahawa daga kasashen Saliyo da Ivory Coast a kuma sarrafa shi zuwa gahawa, wanda kuma akan tara mutane masu dandanawa su yi alkalanci . Kusan kashi 80 bisa dari na alkalan sun gaza gano bambanci tsakanin nau'in gahawa na Stenophylla da na Arabica a wasu gwaje-gwajen da aka yi idanu rufe, masu bincike sun bayar da rahoton a mujallar ''Nature Plants''. Sun kuma tattara bayanan sauyin yanayi kan shukar, da suka nuna cewa za ta iya jure wa yanayin zafin da ya kai ma'aunin 6C fiye da nau'in Arabica. Za a shuka irin a cikin wannan shekarar don fara duba yanayin yadda irin wannan gahawa za ta kare martabar nagartacciyar gahawa nan gaba. Dakta Davis na fatan wata rana za a sake noma nau'in gahawar na Stenophylla a kasar Saliyo mai yawan gaske. ""Ba wai za a samu shagunan shan gahawa ba ne a cikin 'yan shekaru, amma ina ga a cikin shekaru biyar zuwa bakwai za mu ga tana shiga kasuwannin da manyan kantunan sayar da gahawa, a matsayin gahawa mai daraja, bayan nan ne kuma za ta kasance a ko ina,"" in ji shi. Kwayoyin gahawar Arabica na da mafi dadin dandano. Ana nomawa a cikin tsaunuka kuma tana samar da kashi 60 bisa dari na irin gahawar da ake nomawa a duniya. Arabica tana da karancin juriya kan sauyin yanayi; manoma sun fara fuskantar mummunan tasirin karuwar yanayin zafin da kuma karanci ko mamakon ruwan sama. Sauran abubuwan da kan haifar dabarazana ga noman gahawa sun hada da yawan sauyin farashi, kwari da cututtuka da kuma yanayi mai tsanani. An gudanar da binciken ne da hadin gwiwar cibiyar bincike ta kasar Faransa Cirad da kuma Jami'ar Greenwich. Akasarin nau'ukan gahawar kan tsiro ne a kungurmin dazuka na Afirka da kuma tsibirin Madagascar. Baya ga Afirka, an samun wannan nau'i a sauran yankunan kasashe masu zafi da suka hada da India, da Sri Lanka, da kuma Australia. Nau'ukan bishiyoyin gahawa fiye da dari ke fe tsirowa a cikin dazuka, amma kadan ne daga ciki ake iya sarrafawa domin sha. Manyan nau'ukan gahawa biyu ne suka mamaye masana'antar sarrafa gahawar ta duniya - Arabica (Coffea arabica) da kuma Robusta (Coffeea canephora). Ana noma nau'i na uku - Liberica (Coffea liberica) a fadin duniya, amma ba a cika amfani da shi wajen sarrafa gahawar domin sha ba." https://www.bbc.com/hausa/labarai-56815292 +religion Ra'ayi Riga: Bikin Eid ul fitr na 2021 Latsa lasifikar da ke sama domin sauraren shirin. https://www.bbc.com/hausa/shirye-shirye-na-musamman-57124916 +politics Ifeanyi Okowa: Abubuwan da suka kamata ku sani kan mutumin da aka zaba domin yi wa Atiku mataimakin shugaban kasa "Dan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar PDP Atiku Abubakar ya sanar cewa ya zabi gwamnan Jihar Delta Ifeanyi Okowa a matsayin mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa a zaben 2023. Jam'iyyar PDP ta sanar da hakan ne a ranar Alhamis bayan tantance ɗaukar ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasar a hedikwatar jam'iyyar da ke Abuja. Wani Kwamiti da PDP ta kafa ne ya zaɓi mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasar don mara wa ɗan takararta Atiku Abubakar baya a babban zabe mai zuwa a bara. Bayan wannan sanarwar hankali ya koma kan sanin ko wane ne Ifeanyi Okowa? An haifi Arthur Ifeanyi Okowa ne a ranar 8 ga watan Yulin 1959 a garin Owa-Alero da ke karamar hukumar Ika North-East ta Jihar Delta. Ya fara karatu a makarantar firamare ta Iroro a Owa-Alero kuma daga baya ya tafi shahararriyar makarantar nan ta Edo College a Benin City daga 1970 zuwa 1976, inda ya samu shaidar karatu kuma ya kasance dalibin da ya fi nuna hazaka a dukkan tsohuwar Jihar Bendel a 1976. Daga baya ya tafi Jami'ar Ibadan domin karanta ilimin zama likita, kuma ya kammala karatunsa a 1981, a lokacin yana da shekara 22 da haihuwa. Bayan ya kammala karatun jami'a, da aikin yi wa kasa hidima, Dakta Okowa ya fara aiki a matsayin likita a hukumar da ke kula da asibitoci ta tsohuwar Jihar Bendel, kafin daga baya ya koma aiki a asibitin Victory Medical Centre a 1986. Daga baya ya bude wani reshen asibitin a Boji-Boji da ke garin Owa. Okowa yana da mata daya mai suna Dame Edith Okowa da 'yaya biyu: Marilyn Okowa da Mildred Okowa. A farkon rayuwarsa ta siyasa, Okowa ya rike mukamin sakataren karamar hukumar Ika, kuma daga baya ya zama shugaban karamar hukumar Ika Nort-East daga 1991 zuwa 1993. Ya taba zama shugaban jam'iyyar siyasa ta Grassroots Democratic Movement (GDM) a Jihar Delta, amma daga baya ya shiga jam'iyyar PDP a 1998, kuma ya taimaka wa tsohon gwamna James Ibori a yakin neman zaben da ya yi na zama gwamna tsakanin 1998 zuwa 1999. An nada shi Kwamishinan Ayyukan Gona daga 1999 zuwa 2001, kuma an tura shi Ma'aikatar Raya Albarkatun Ruwa daga 2001 zuwa 2003, sannan ya tafi Ma'aikatar Lafiya daga 2003 zuwa 2006. A 2007, Okowa ya ajiye mukaminsa na Kwamaishina domin ya tsaya takarar gwamnan Jihar Delta, sai dai bai yi nasara a zaben fitar da gwani ba. A watan Yunin 2007, an nada Ifeanyi Okowa a mukamin sakataren gwamnatin Jihar ta Delta. A shekarar 2011, an zabe shi a matsayin Sanata mai wakiltar mazabar Arewacin Jihar Delta. A shekarar 2015, Mista Okowa ya cika burinsa na zama gwamnan Jihar Delta a karkashin jam'iyyar PDP bayan da aka zabe shi da kuri'u 724,680, an kuma rantsar da shi ranar 29 ga watan Mayun 2015. An sake zaben sa a 2019, inda ya samu galaba kan Great Ogoru na jam'iyyar APC da kuri'u 925,274. Gwamna Ifeanyi Okowa ne ya kafa Jami'ar Jihar Delta a garinsu na Agbor, kuma ya kafa wata Jami'ar ta Kimiyya da Fasaha a Uzoro, da kuma Jami'ar Dennis Osadebey a garin Anwai duka a Jihar ta Delta. Dan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar PDP Atiku Abubakar ne ya sanar da sunan Ifeanyi Okowa a matsayin dan takarar da zai yi masa mataimaki a babban zaben 2023. Atiku ya sanar da sunan Okowa ne bayan taron babban kwamitin gudanarwa na jam'iyyar da aka yi a Abuja a ranar Alhamis. Tun da farko shugaban jam'iyyar PDP Iyorchia Ayu ya bayyana cewa jam'iyyar ta kafa wani kwamitin mutum 17 domin ya zabo mutumin da ya fi dacewa. Ya kuma ce kwamitin ya mika wa Atiku Abubakar sunayen mutum uku domin ya zabi wanda ya fi kwanta masa a rai. Atiku Abubakar ya zabi Ifeanyi Okowa, kamar yadda ya ce ""domin yana da kwarewar da ake bukata ya rike mukamin shugaban Najeriya a duk lokacin da shugaban kasa baya nan"". Ya kuma ce dukkan 'yan takara ukun da aka mika masa sun cancanta, sai dai Okowa ya fi kwanta masa a rai. A ranar 29 ga watan Mayun 2023 za a rantsar da sabon shugaban Najeriya bayan babban zaben da za a gudanar tsakanin dukkan 'yan takara daga jam'iyyun siyasar Najeriya, inda dan takarar da ya yi nasara da mataimakinsa za su karbi ragamar mulki daga gwamnatin Muhammadu Buhari wanda wa'adin mulkinsa zai kare a watan Mayun 2027." https://www.bbc.com/hausa/labarai-61830873 +business Sauyin Yanayi : 'Duniya na cikin bala'i' -MDD "An bude taron kolin sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya a Masar tare da gargadin cewa duniyarmu tana ""aikewa da sakon damuwa"". Sakatare Janar Antonio Guterres na mayar da martani ne ga rahoton Majalisar Dinkin Duniya da aka fitar a ranar Lahadi yana mai cewa shekaru takwas da suka gabata sun kasance mafi zafi a tarihi. Shugabannin kasashen duniya fiye da 120 ne za su isa wurin taron da aka fi sani da COP27, a wurin shakatawa na Sharm el-Sheikh a tekun Bahar Maliya. Za a fara tattaunawa ta tsawon makonni biyu ne a tsakanin kasashen kan batun sauyin yanayi. Shugaban taron kolin na COP27, Ministan Harkokin Wajen Masar Sameh Shoukry, ya yi kira ga shugabannin da kada su bari rikicin abinci da makamashi da ke da alaka da mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine ya kawo cikas ga daukar matakan shawo kan kan sauyin yanayi. ""Ya zama wajibi a kanmu baki daya a birnin Sharm el-Sheikh, mu nuna amincewa da irin girman kalubalen da muke fuskanta da kuma tsayin dakanmu na shawo kan lamarin."" An bayyana bukatar daukar matakin ne a sabon rahoton da hukumar kula da yanayi ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar. Mista Guterres ya aike da sakon bidiyo ga taron inda ya kira rahoton da aka fitar a kan yanayi na duniya na shekarar 2022 a matsayin "" halin da duniya ta cike ta fuskar sauyin yanayi"". A cikin rahoton, masana kimiyya sun kiyasta cewa a halin yanzu yanayin zafi a duniya ya karu da 1.15C tun kafin kafuwar masana'antu kuma sun ce shekaru takwas na baya-bayan nan suna kan hanyar da za ta kasance mafi zafi a tarihi. Rahoton ya kuma yi gargadi game da sauran tasirin sauyin yanayi, da suka hada da karuwar yawan ruwan teku a cikin sauri, da karuwa a yawan yawan kankara da ke narkewa da kuma matsanancin zafin da ba a taba ganin irinsa ba. Mista Guterres ya ce bisa la’akari da wadannan binciken, dole ne taron kolin na COP27 ya zama wurin daukar matakan gaggawa kuma sahihanci. A ranar Litinin din nan ne za a fara taron kolin COP27 gadan- gadan tare da babban taron shugabannin kasashen duniya, inda shugabannin kasashe da na gwamnatoci za su gabatar da jawabai na mintuna biyar don bayyana abin da suke so daga taron. Ana sa ran Firaiministan Birtaniya Rishi Sunak zai bukaci shugabannin duniya da su yi kara "" hanzari"" wajen soma amfani da makamashin da baya gurabata muhali. Zai kuma fadawa wa shugabannin da kada su ""ja baya"" kan alkawuran da aka yi a taron COP26 na bara a Glasgow. Shugabannin kasashen duniya za su yi magana a ranakun Litinin da Talata, kuma da zarar sun tafi, wakilan kasashen duniya za su ci gaba da tattaunawa don cimm matsaya . An samu kasashen duniya da suka yi alkaura a taron kolin bara. Kasashe masu tasowa - wadanda su ne matsalar sauyin yanayi ta fi yiwa illa - suna bukatar a kiyaye alkawuran da aka yi a baya na samar da kudade. Shin ko kasashe na kan hanyar cimma muradun sauyin yanayi na Glasgow? Su wanene shugabanni da kuma wadanda ke kawo cikas ga shirin? Amma kuma suna son a tattaunawa kan ""asara da barna "" da kuma kudi - don taimaka musu jimre da asarar da suka samu sanadin sauyin yanayi maimakon kawai a taimaka mu su akan yadda za su tunkari matsakar nan gaba. Kazalika bayan tattaunawar da za a yi akwai kuma daruruwan taruka da za su gudana a cikin makonni biyu da suka hada da na baje koli da na tarurrukan bita da wasanin al'adu daga matasa da sauransu. Zanga-zangar nuna adawa da matsalar sauyin yanayi da aka aba gani a kowani taron koli wataƙila ba za a yi shi ba a wannan karon. Shugaban Masar Abdul Fattah al-Sisi, wanda ke kan karagar mulki tun shekara ta 2014, a karkashin jagorancinsa ne aka rika murkushe masu adawa da gwamnatimsa. Kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun yi kiyasin cewa kasar na da fursunonin siyasa kusan 60,000, kuma da dama daga ciki ana tsare da su ba tare da shari’a ba. Mista Shoukry ya ce za a kebe fili a birnin Sharm el-Sheikh domin gudanar da zanga-zangar. Sai dai masu fafutuka na Masar sun shaida wa BBC cewa kungiyoyin cikin gida da dama sun kasa yin rajistar halartar taron." https://www.bbc.com/hausa/articles/cxe8zn7mjkjo +sports Faransa ta maye gurbin Nkunku da Kolo a Gasar Kofin Duniya a Qatar Faransa ta maye gurbin Christoper Nkunku da mai taka leda a Eintracht Frankfurt, Randal Kolo Muani a Gasar Cin Kofin Duniya a Qatar. Nkunku mai wasa a RB Leipzig ya ji rauni a lokacin atisaye ranar Talata tare da tawagar, wanda zai yi jinya har bayan kammala babbar Gasar tamaula ta duniya.. Kolo Muani ya ci kwallo takwas a wasa 23 a Frankfurt a kakar nan a Bundesliga. Dan kwallon mai shekara 23 ya yi wa tawagar Faransa wasa biyu a karawa da Australia da Denmark a Nations League a watan Satumba. Nkunku ya zama na baya-bayan nan daga tawagar Faransa da ba zai buga Gasar Kofin Duniya ba, bayan Paul Pogba da N'Golo Kante da kuma Presnel Kimpembe. Har yanzu dan wasan Manchester United, Raphael Varane bai murmure ba, wanda Faransa ta je da shi Qatar. Tawagar da Didier Deschamps ke jan ragama za ta sauka a Qatar ranar Laraba.' Za ta fara wasa ranar 22 ga watan Nuwamba da Australia a rukuni na hudu da ya hada da Denmark da kuma Tunisia. Faransa ce mai rike da kofin da ta lashe a Rasha a 2018. https://www.bbc.com/hausa/articles/cq57rwkzq8qo +health Bayanai kan magungunan cuar kansa Daya daga cikin manyan hanyoyin da ake maganin ciwon daji shi ne halin wasu magunguna da ake kira chemotherapy, amma dumbin mutane musamman a wasu kasashen yammacin Afrika suna fargabar bin wannan hanya. Wasu daga cikin dalilin da ke sa mutane dari-dari da magungunan su ne illolin da ke tattare da su ta fannin kiwon lafiya. A Najeriya kasar da ta fi kowa yawan al'umma a nahiyar Afrika, wadannan magunguna na da tsadar gaske, bugu da kari kuma ba a ko'ina ake samunsu ba. Wani hadarin da masu cutar sankara ke fuskanta a kasar shi ne idan aka yi rashin dace wajen zuwa ga likitocin da basu da kwarewar bayar da magungunan. Cutar sankara ita ce cuta ta biyu da tafi kashe mutane a fadin duniya, a cewar hukumar lafiya ta duniya. WHO reshen Afrika ta ce, akalla mutane 8.8 miliyan ne suka mutu sakamakon ciwon daji a shekarar 2015. Sannan akalla kashi 70 cikin dari na wadannan mace-macen ana samunsu ne a kasashen da ke karanci da matsakaicin kudin shiga. Domin jin wasu halaye biyar da hukumar ta bayar da tace suna janyo wa masu yinsu ciwon daji, sai ku saurari shirin lafiya zinariya ta hanyar latsa makunnin da ke sama. https://www.bbc.com/hausa/articles/cz7y5x934j8o +entertainment Hikayata 2021: Labarin 'Halacci' Ku latsa hoton da ke sama don sauraron labarin: A ci gaba da kawo maku labarai 12 da alkalan gasar Hikayata suka ce sun cancanci yabo, wannan makon muna tafe da labarin ‘Halacci’ na Fatima Ibrahim Garba, Gida mai lamba 16 layin Dan Masani a unguwar Rigachikun jihar Kaduna Najeriya. Badriyya Tijjani Kalarawi ce ta karanto. https://www.bbc.com/hausa/shirye-shirye-na-musamman-60433889 +religion Bikin Kirsimeti: Mu’ujuzojin Yesu Almasihu "A ranar Asabar din nan ce Mabiya addinin Kirista suke gudanar da bukukuwan Kirsimeti wadda ake yi kowace ranar 25 ga watan Disamba. Ana gudanar da bikin Kirsimeti ne domin tunawa da ranar haihuwar Yesu Almasihu. Mabiya addinin Kirista a ko ina a fadin duniya na bayyana muhimmancin abubuwan al'ajabi da mu'ujizojin Yesu Isa Almasihu, wadanda malaman addinin Kirista suke jaddadawa ga mabiyansu a koda yaushe a cikin wa'azi. Sun kuma yi amanna cewa wadannan mu'ujizoji wata babbar garkuwa ce a rayuwarsu, muddin ba su saba wa abubuwan koyin da ya zo musu da su ba. Rabaran Joseph John Hayab, shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya reshen jihar Kaduna, ya bayyana wa BBC cewa Yesu Isa Almasihu ya zo duniya da abubuwa na ban al'ajabi da kuma abubuwan koyi ga al'ummar duniya. Rabaran Hayab ya kara da cewa kasancewarsa mai ceton al'umma a duniya wannan ma wani babban abin al'ajabi ne a cikin mu'ujizojinsa da suke alfahari da ita. ""Haihuwar Yesu ta kawo mana ceto, haihuwar Yesu ta kawo mana haske, haihuwar Yesu ta sada mu da Allah,"" in ji Rabaran Hayab. ""Don haka a kullum idan mun yi maganar Kirsimeti muna ganin ikon Allah ne, kuma shi ne dalilin Kirsimeti.'' Haka shi ma Rabaran Garba Alex Shukau, limamin Cocin Katolika na Saint Loius da ke unguwar Bompai a birnin Kano, ya bayyana wa BBC cewa Yesu Almasihu ya zo duniya tare da abubuwa na al'ajabi da mu'ujizoji da dama, yana mai cewa ""mu'ujizarsa ta farko ita ce kasancewarsa mai ceto"" ga dan adam. ""Abu na biyu kuma shi ne Yesu Isa Almasihu ya zo duniya domin ya kawo mana salama a cikin zukatanmu, da cikin harkokinmu da juna da 'yan uwa da makwabta har ma da magabata,'' in ji Rabaran Garba. Har wa yau daya daga cikin mu'ujuzojin Yesu Isa Almasihu in ji Rabaran Hayab ita ce tun lokacin da ya zo duniya babban abin da ya yi shi ne koyarwa a ""fannin yafiya, da zamantakewa, da kuma biyayya da umarni."" Rabaran Hayab ya kuma kara da cewa ""Abu na uku da Yesu Kiristi ya yi shi ne ya yi abubuwan al'ajabi da yawa - na warkar da marasa lafiya, da na tayar da matattu"". ""Don haka idan muka lura da rayuwar Yesu Kiristi sai mu fara da yaya aka haife shi? An haife shi da abubuwan al'ajabi, ya yi rayuwar al'ajabi, kana ya yi mutuwar al'ajabi, ya kuma tashi domin ya tabbatar da abubuwan al'ajabin nan da ya zo ya koyar,"" a cewarsa. Haka shi ma Rabaran Garba Alex ya kara jaddada batun warkarwa a matsayin daya daga cikin mu'ujizozin na Yesu Isa Almasihu. Ya ce:""Lokacin da ya zo duniya ya yi ta warkar da marasa lafiya a yayin da yake yawon wa'azi, marasa lafiya sun samu lafiya, wadanda ba sa gani sun dawo suna gani, wadanda ba sa iya tafiya sun samu iya tafiya."" Wa'azi kan kawo zaman lafiya da salama a tsakanin al'umma na daya daga cikin mu'ujizojin Yesu Isa Almasihu, a cewar Rabaran Father Garba Alex, wanda yake kokarin wanzar da zaman lafiya da kaunar juna a tsakanin al'umma. ""Akwai mu'ujiza a tare da kalaman da yake yi lokacin wa'azinsa, ta yadda yakan ja hankulan mutane zuwa gare shi cikin hikima da nuna kamala, yana bayyana cewa fada da rashin jituwa duka ba zaman rayuwar duniya mai kyau ba ne,'' in ji shi. Har ila yau malamin addinin Kiristan ya bayyana cewa zuwan Yesu Isa Almasihu duniya da haske wani muhimmin al'amari ne. A cewarsa ""lokacin da ya zo duniya ya haska ta domin littafi mai tsarki ya bayyana mana cewa lokacin da ya zo ya haskaka duniya, da zukatan al'umma."" ''Ya zo domin ya zauna tare da mu, ya zo ne domin ya kawo mana haske, haske wanda zai haskaka a cikin rayuwarmu da zukatanmu, da gidajenmu domin ya ba mu zaman salama da zaman ceto."" Malaman addinin Kirista sun kuma bayyana cewa wadanna mu'ujizoji da Yesu Isa Almasihu ya zo da su duniya, wani jigo ne a cikin harkokin rayuwar mabiya addinin a ko ina a fadin duniya. Rabaran Hayab ya ce don haka yana da matukar muhimmanci mabiya su rika koyi da abubuwan da ya zo da su duniya. ''Ubangiji Allah ya turo shi duniya ne domin ya cece mu daga bata da aikata sabo, da kuma tuba daga zunubai da komawa kan tafarki mai kyau na bin kusanci da Ubangijinmu"", in ji shi. Ga wasu daga cikin mu'ujizojin Yesu Isa Almasihu:" https://www.bbc.com/hausa/labarai-59773023 +religion Kacici-kacicin Ranar Kirsimeti na 2019 Ga wani kacici-kacici da BBC Hausa ta shirya albarkacin Ranar Kirsimeti, don gwada ku kan wasu abubuwa da suka shafi addinin Kirista. Wannan kacici-kacici an gina shi ne kan fahimtar Addinin Kirista, kuma mun tuntubi wani babban malamin addinin kirista da ke jihar Kano, Reverand Mati Dangora don tantance tambayoyin da amsoshinsu. Ku shiga ciki don gwada kwazonku. https://www.bbc.com/hausa/labarai-50840455 +religion Bidiyon Ku san Malamanku tare da Sheikh Aminu Daurawa "Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon: Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Aminu Daurawa, ya ce ya sha wahala matuka kafin ya haddace wata aya a Al-Ƙur'ani. Malamin ya bayyana haka ne a wata hira ta musamman da BBC, a kuma cikin sabon shirinmu mai taken ""Ku San Malamanku"". Ya ce ayar da ta fi ba shi wuya ita ce wata aya da ke cikin Suratul Baqara, wato Iza Tadayantum..., wadda ita ce ayar da ta fi kowace tsawo a littafi mai tsarki." https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-54563984 +technology Wani gungun masu amfani da intanet a Kenya na yaudarar ƴan mata da zuwa wajen sharholiya "'Yan sanda a Kenya na binciken wani gungun masu amfani da intanet da suke neman 'yan matan da suke zaune a gida saboda annobar korona, inda suke yaudararsu da abin da 'yan sandan suka ce gayyatar su wajen sharholiya. Batun ya fito fili ne bayan 'yan sanda sun kubutar da wasu 'yan mata uku da suka bata a babban birnin ƙasar Nairobi. 'Yan matan uku sun shaida wa 'yan sanda cewa sun ga wasu shafukan sada zumunta da suka gayyace su zuwa wajen ""pati"" a birnin. 'Yan sanda sun gargadi iyaye da su ringa sanya ido sosai kan 'ya'yansu. ""Sashen binciken manyan laifuka yana sanar da jama'a cewa muna farautar mambobin wata kungiya kuma za a kama su domin fuskantar hukuncin abubuwan da suka aikata"", a cewar 'yan sanda a shafin tuwitar. A baya-bayannan kafofin watsa labaran Kenya sun ringa ba da rahoton bacewar 'yan mata - wasunsu an yi musu alkawarin aiki. A farko wannan makon dangin wata budurwa sun wallafa wani sako a tuwita suna fargabar cewa an sace 'yarsu ko kuma anyi safarar ta. Dangin sun ce yarinyar ta bata a Nairobi ranar Asabar bayan wasu mutane sun yaudareta cewa za su ba ta aikin tallan kayan kawa. ""Kanwata tare da wasu 'yan mata shida masu shekara 16, sun yi batan dabo,"" matar ta fada a cikin bidiyon. A ranar Juma'a, 'yan sanda sun wallafa a shafinsu na tuwita cewa masu yaki da safarar yara sun kubutar da uku daga 'yan matan bakwai da aka ba da rahoton sun bata. Sannan ana ci gaba da neman sauran, a cewar su. Ba su dai bayyana inda aka samu 'yan matan ba ko kuma ko an kama wasu mutane. Sashin binciken manyan laifukan ya ce gungun suna aiki ne daga birnin Nairobi kuma suna amfani da lambobin wayar da aka yi wa rijista a kasashen waje. ""Yayin da ake ci gaba da bincike muna so mu gargadi mutanen da ke amfani da annobar korona suna yaudarar 'yan mata 'yan makaranta, nan ba da jimawa ba za a kama su,"" a cewar sasahin a sakon tuwita da ya wallafa. Tun da farko a watan Nuwambar 2020, kasar ta gabashin Afirka ta kara tsanananta matakan kariya yayin da cutar korona da ta sake barkewa karo na biyu ta janyo karin mace-mace da karin masu kamuwa da ita. An hana tarukan jama'a sannan an sanya dokar hana fita da daddare. An rufe makarantu a watan Maris, sai dai an dan bude su a watan Oktoba. Gwamnati ta ce ba za a bude makarantu ba gaba daya har sai watan Janairu. Kenya, wacce take da yawan al'umma miliyan 53 ta ba da rahoton cewa fiye da mutum 75,000 ne suka kamu da korona, kuma mutum 1,349 suka mutu, kamar yadda alkaluman jami'ar John Hopkins suka nuna." https://www.bbc.com/hausa/labarai-55032417 +sports Ƙungiyar masu ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa ta dakatar da shugaban Kano Pillars "Ƙungiyar masu ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa a Najeriya ta dakatar da shugaban ƙungiyar Kano Pillars, Yahaya Surajo, sakamakon zargin sa da naushin mataimakin alƙalin wasa. Football Club Owners Association of Nigeria (FCOAN) ta dakatar da ciyaman ɗin ne bayan an zarge shi da naushin mataimakin lafarin a wuya yayin wasa tsakanin Pillars da Dakada FC da aka buga a Kano ranar Alhamis. Wani bidiyo da ya karaɗe shafukan zumunta ya nuna yadda Yahaya Surajo mai shekara 53 ya je kusa da lafarin da ke kan layi ana tsaka da wasa kuma ya kai masa naushi. Pillars ce ta ci kwantan wasan na mako na 31 da 1-0 bayan an ɗaga shi a baya. Ƙungiyar ta ce siffanta abin da Surajo ya aikata da cewa ""abin takaici"" kuma ""wanda ba za a amince da shi ba"". ""Saboda haka ƙungiyar ta dakatar da Yahaya Surajo har sai baba ta gani daga dukkan ayyukanta har zuwa lokacin da za a kammala bincike kan abin takaicin,"" a cewar sanarwar da sakataren FCOAN Alloy Chukwuemeka ya sanya wa hannu. Shugaban FCOAN ya ce shugaban na Pillars zai gurfana a gaban wani kwamatin ladaftarwa don ya kare kansa kafin a sake mayar da shi cikinta. Gwamnatin Kano ta naɗa Yahaya Surajo - ɗan siyasa a Kano kuma tsohon ɗan wasan ƙwallon ƙafa - muƙamin a watan Agustan 2019, inda ya maye gurbin Tukur Babangida. Pillars ba ta ƙoƙari a kakar bana ta 2021-22, inda a yanzu take mataki na 15 da maki 42 bayan buga wasa 34 a kakar. A watan Afrilun da ya gabata ma hukumar shirya gasar Firimiyar Najeriya ta ci tarar Pillars naira miliyan tara tare da mayar da ita buga wasa a Abuja sakamon cin zarafin da magoya bayanta suka yi wa tawagar Katsina United." https://www.bbc.com/hausa/articles/cm5v1n3mxmno +technology Texas school shooting: Al'adu bakwai game da mallakar bindiga a Amurka cikin taswira "Sama da shekara 50 kenan bayan da gwamnatin Shugaba Lyndon Baines Johnson ya bayyana cewa ""bindigogi na daga cikin abubuwan da ake amfani da su wurin kisan Amurkawa "". A lokacin, kusan bindigogi miliyan 90 ne ke yawo a hannun jama'a a Amurka. A yau, akwai ƙarin bindigogi da kuma ƙarin mace-mace. Mutuwa sakamakon harbin bindiga ya zama abin da aka saba da shi a Amurka, inda ake samun mace-mace fiye da yadda ake samu a duk adadin sojojin da ake samu a wani yaƙi na Amurka tun bayan yaƙin Amurka na neman yancin kai a 1775. A 2020 kaɗai, sama da Amurkawa 45,000 ne suka rasu sakamakon harbin bindiga, ta hanyar wani ya kashe su ko kuma sun kashe kansu, sama da duk wata shekara a baya. Wannan adadin yana nufin an samu ƙari daga shekara biyar da kuma ƙarin kashi 43 cikin 100 daga 2010. Ga abin da muka sani game da al'adar bindiga da kuma tasirin da ta yi. Ganin cewa ƙidaya adadin bindigogin da ke da akwai a hannun mutane abu ne mai wahala gano adadin su, alƙaluma daga wani bincike na Small Arms Survey wanda kamfanin bincike ne na ƙasar Switzerland ya nuna cewa akwai bindigogi miliyan 390 da ke yawo a 2018. Idan aka ƙimanta adadin bindigogi 120.5 a duk gida 100, kusan kashi 88 cikin 100 a 20111, hakan na nufin adadin ya wuce na sauran ƙasashen duniya. Bayanai na baya-bayan nan sun ce adadin masu mallakar bindiga ya ƙaru a shekarun da suka gabata. Wani bincike da aka wallafa ya gano cewa baligai miliyan 7.5 na Amurka - kasa da kashi uku cikin 100 na ƴan ƙasar ne suka zama mammalaka bindiga na farko tsakanin Janairun 2019 da Afrilun 2021. Hakan ya sa mutum miliyan 11 suka samu damar riƙe bindiga a gidaje ciki har da yara miliyan biyar. Kusan rabin masu riƙe bindiga a lokacin mata ne, kuma kashi 40 cikin 100 kodai baƙar fata ne ko kuma ƴan yankin Latin Amurka. Wani bincike na daban da aka wallafa a 2021 ya alaƙanta ƙaruwar riƙe bindiga a lokacin annobar korona da ƙaruwar raunin da yaran ke samu da wanda yara suka jawo. Kamar yadda hukumar da ke kiyaye cutuka masu yaɗuwa ta Amurka ta bayyana, jummular mutum 45,222 ne suka mutu daga raunin da suka samu sakamakon bindiga a 2020. A yayin da harbi mai kan mai uwa da wabi ke ƙara jan hankalin kafofin watsa labarai, a cikin kashi 54 cikin 100 kusan mutum 24,300 da suka rasu sun rasu ne sakamakon kashe kansu da suka yi. Wanni bincike da aka wallafa a 2016 ya gano cewa akwai dangantaka mai ƙarfi tsakanin adadi mai yawa na mallakar bindiga a ƙasa da kuma adadi mai yawa na masu kashe kansu da bindiga . Masu neman a yi doka mai ƙarfi dangane da riƙe bindiga a Amurka na yawan kawo wannan ƙididdigar idan suna ƙoƙarin jan hankalin yan majalisa da su zuba ƙarin kuɗaɗe wajen kula da lafiyar ƙwaƙwalwa da kuma wasu da ke son kawo sauyi a dokar riƙe bindiga. A shekarar 2020, kashi 43 cikin 100 na waɗanda suka rasu wato mutum 19,384 kenan an kashe su ne, kamar yadda wata ƙididdiga daga hukumar CDC ta nuna. Wannan adadin na wakiltar kashi 34 cikin 100 daga 2019 da kuma ƙaruwar kashi 75 cikin 100 a shekara goma da suka wuce. Kusan mutum 53 ake kashewa a kullum da bindiga a Amurka, kamar yadda ƙididdiga ta nuna. Wannan ƙididdigar ta nuna cewa aksarin kisan da ake yi , kashi 79 cikin da bindiga aka yi su. Wannan adadi ne mai ɗumbin yawa da ya wuce na Canada da Australia da Ingila da Wales da wasu ƙasashen. Ko kashe mutane da yawa a lokaci ɗaya na ƙara muni? Sai dai yana da wahala a iya tantance mace-macen da ake samu ta hanyar harbin mutane da yawa a lokaci ɗaya da ke jan hankalin duniya. A yayin da ƙasar ba ta da wata kalma ɗaya taƙamaimai da ake dangantawa da ""harbe mutane da dama a lokaci guda"", cikin shekara 10 hukumar FBI ta bi diddigin ""harbe-harben da suka faru"" wato irin wanda mutum ɗaya ke buɗewa mutane da dama wuta a waje guda."" A cewar FBI, an samu irin wannan kashe-kashe 345 a Amurka daga tsakanin shekarar 2000 zuwa 2020, da suka yi sanadin mutuwar mutum 1,024, mutum 1,828 kuma suka ji rauni. Cikin munanan hare-hare irin wannan har da wanda ya faru a Las Vegas a 2017, inda aka kashe muutm 50, wasu 500 kuma suka jikkata. Yawanci a kan samu mace-mace kamar 30 a irin waɗannan kashe-kashe. Wa ke goyon bayan taƙaita amfani da bindiga? Duk da irin kiraye-kirayen da ake yawan yi yayin da ake fama da harbin kan mai uwa da wabi - masu goyon bayan sanya tsauraran matakan mallakar bindiga sun ragu sosai a Amurka tun daga 2014 har zuwa 2020, a cewar wata ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a ta Gallup. Kashi 52 cikin 100 na Amurkawa da aka yi bincike a kansu sun ce suna so a sanya tsauraran matakai na mallakar bindiga, yayin da kashi 35 cikin 100 suka ce a bar dokokin yadda suke. Kashi 11 cikin 100 kuwa sun ce ya kamata a sassauta dokokin, Sai dai lamarin ya rabu ɓangare biyu ne inda manyan jam'iyyun ƙasar kowa ke da nasa ra'ayin. ""Bakin ƴan Democrat kusan ya zo ɗaya wajen goyon bayan a sanya tsauraran matakai kan mallakar bindiga, inda kashi 91 cikin 100 suka goyi bayan hakan."" Yayin da a ɗaya hannun kuma kashi 24 na ƴan Republican ne kawai suka yarda da hakan. Wasu jihohin sun ɗauki matakan haramta ko sanya tsauraran matakan mallakar makamai. Dokoki sun bambanta a jihohi, amma a California alal misali, an haramta mallakar makamai sai dai a bisa wasu dalilai ƙalilan. Wa ke adawa da taƙaita mallakar makamai? Duk dayawan shekarun da aka shafe ana tataɓurza kan kashe kuɗaɗe a kan batun taƙaita mallakar makamai, ƙungiyar masu ƙera bindiga ta ƙasar NRA, ta kasance wacce ta fi ƙarfi wajen ganin ba a sa dokokin taƙaita mallakar makaman ba a Amurka, inda take ware makuɗan kuɗaɗe don neman goyon bayan ƴan majalisar dokoki a kan tsare-tsaren mallakar bindiga. A watan Janairu, NRA ta shigar da ƙara kan karayar tattalin arziki sakamakon wata almundahana da aka samu hannun manyan jami'anta a ciki. Wasu jihohin da dama sun yi ƙoƙarin kawar da dokoki kan batun waye zai iya mallakar bindiga. A watan Yunin 2021 alal misali, gwamnan Texas Greg Abbott ya sanya hannu kan wata doka da ta bai wa mazauna jihar izinin ɗaukar ƙaramar bindigar hannu ba tare da lasisi ko ƙwarewa ba. Haka ma a ranar 12 ga watan Afrilu jihar Georgia ta zama ta 25 da ta kawar da buƙatar samun izinin ɗaukar bindiga. Hakan na nufin duk ɗan jihar zai iya ɗaukar bindiga ba tare da izini ko lasisi ba. Kuma ƙungiyar NRA ta goyi bayan wannan doka." https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-61582701 +religion Ku San Malamanku Tare da Malam Sadiqu Siddiq "Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon: Fitaccen alaramma a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya, Shiekh Sadiqu Siddiq, ya ce bai taɓa samun farin cikin da ya kai nasarar da ya samu ta lashe musabaƙar Al Qur'ani mai girma ta duniya da aka gudanar a Saudiyya, inda ya ce nasarar da ya samu ta kasance tushen arzikinsa. Alaramman ya bayyana hakan ne a hirarsa da BBC Hausa a shirinmu na musamman na Ku San Malamanku, kuma ya ce tun yana ɗan shekara 9 ya sauke Al Qur'ani. ""Mun fafata da Larabawa da ƴan Afrika da Turawa da Indiyawa kuma aka sanar cewa na yi na daya a matakin hizb 60 a duniya baki ɗaya."" ""Farin cikin ya ƙara yawa, ga sabuwar jihar Zamfara, ga shi na yi na ɗaya a Najeriya kuma na daya a duniya,"" in ji shi. Malamin ya shaida wa BBC cewa shi ɗan asalin jihar Kebbi ne, kuma an haife shi ne a shekarar 1979 a ƙauyen Tafki Tara cikin ƙaramar hukumnar Shanga da ke jihar Kebbi. Ya ce ya fara karatun addini ne a gun mahaifinsa wanda shi ne babban malami a kauyensu na Tafki Tara. ""Na tashi gidan ilimi, na yi karatun Al'Qur'an a hannun mahaifina har na sauke ina ɗan shekara tara."" Malamin ya ce ya ci gaba da karatunsa na Al Qur'ani a gidan mahaifiyarsa garin Koko, inda kakansa shi ne babban malamin garin, kuma tun yana ɗarami ya yi karatun litattafai na Fiqhu. Amma malamin ya ce daga baya hankalinsa ya karkata ne ga haddar Al Qur'ani, wanda wannan dalilin ne ya sa mahaifinsa ya turo shi yin karatu a garin Gusau wajen Malam Sanusi Balarabe. Ya ce ya rubuta Al Qur'ani kwafi biyu, kuma ya yi wa mahaifinsa kyautar kwafi ɗaya. Malam Sadiq Sadiq ya ce malaminsa Shiekh Balarabe ne ya ja hankalinsa shiga masabaƙar Al Qur'ani mai tsarki. Ya ce kaset kaset na musabaƙar da malaminsa yake kunna wa suka fara tsuma shi, ya ja hankalinsa. ""Ba ni mantawa, karatun Maryam Nura Sharif wata ɗalibar Kano da ta yi musabaƙa a Katsina, yadda na ji mace tana karatu irin na Larabawa kuma da tajwidi, sai abin ya tsuma ni,"" ""Na ce wai ni ma ya za a yi na shiga wannan musabakar ne,"" in ji shi. Ya ƙara da cewa wannan ne ya sa ya dage wajen koyon tajwid. Malamin ya ce kwatsam wata rana sai aka kawo takardar gayyata ga zawiyar Shiekh Balarabe ta neman shiga musabaƙa. Ya ce wannan ya sa aka nemi su, ɗaliban da suka yi haddar Al'Qur'ani, kuma suka shiga musabaƙar a matakin farko na karamar hukumar Gusau a 1994. Daga nan ya ci gaba zuwa musabaƙar ƙasa da aka yi a Minna jihar Neja 1994. Kuma ya sake shiga a Kaduna inda ya zo na biyar a mataki na ƙasa. A musabaƙar shekarar 1996 da aka yi a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya, ya zo na ɗaya a matakin ƙasa. Wannan ne ya ba shi damar wakiltar Najeriya a musabaƙar duniya da aka yi a Makkah a ƙasar Saudiyya a 1997. ""Mun fafata da Larabawa, da ƴan Afirka kuma Allah ya sa na zo na ɗaya a matakin hizb 60 a duniya baki ɗaya."" Ya ce yana shekara 19 ya lashe musabaƙa ta duniya a Saudiyya. Kuma a cewarsa wannan ne karon farko da ya taba yin karatu gaban manyan shehunan malaman Saudiyya. Malamin Sadiq Siddiq ya ce yana da mata huɗu da ƴaƴa 14. Ya ce babban ɗansa Abdullahi Sadiq ɗan shekara 18 ya haddace Al Qur'ani, tare da laƙantar ƙira'o'i 10 da ruwaya 20. Malamin Sadiq Siddiq ya ce ya fi ƙaunar shinkafa da wake da miya da salat da kuma namma amma ya kasance da zafi. Ya ce babban burinsa shi ne kafa babbar makarantar mahaddata Al'Qura'ni mai girma ta yara kanana. ""Ina son ganin yara ƴan shekara bakwai zuwa 10 sun haddace Al Qur'ani mai tsarki da tajwidinsa, karatu mai inganci shi ne burin da na sa a gaba,"" in ji malamin." https://www.bbc.com/hausa/labarai-58274031 +politics Ina jin kunya a ce ni shugaba ne a arewa - Gwamna Bala Muhammad Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon: Gwamnan jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya Sanata Bala Muhammad Abdulkadir, ya ce akwai gazawar shugabanci a arewacin ƙasar, ganin yadda lamura ke kara taɓarɓarewa. Gwamna Bala ya ce talauci da rashin aikin yi na daga manyan matsalolin da suke addabar arewa da shugabanni suka kasa shawo kansu. Gwamnan ya kuma yi karin bayani kan kalaman da ya yi kwanakin baya, dangane da dalilan da suka sa Fulani makiyaya ɗaukar bindiga. Ya ce ba ya goyon bayan aikata laifuka ko kadan, amma dai ya kamata a duba tushen lamarin in har ana so a kawo karshensa. Ya ce zaluncin da ake yi wa fulani shi ne babban abin da ya sa wasu miyagu daga cikinsu daukar makamai. Gwamna Bala ya ce akwai hadin bakin wasu sarakuna. Ɗaukar bidiyo da tacewa: Yusuf Ibrahim Yakasai Wasu labarai da za ku so ku karanta: https://www.bbc.com/hausa/media-56157569 +entertainment ...Daga Bakin Mai Ita tare da Alhassan Kwalle ...Daga Bakin Mai Ita tare da Alhassan Kwalle Daga Bakin Mai Ita wani shiri ne na BBC Hausa da ke kawo muku hira da fitattun mutane kan wasu abubuwan da suka shafi rayuwarsu zalla. A wannan kashi na 78, shirin ya tattauna da fitaccen jarumin fina-finan Kannywood, Alhassan Kwalle. Tsarawa da gabatarwa: Halima Umar Saleh Ɗaukar bidiyo: Abdulsalam Usman Abdulkadir Tacewa: Abdulsalam Usman Abdulkadir https://www.bbc.com/hausa/labarai-59759624 +religion Matsin lamba ya tilasta wa El-Rufai fasa karbar kudi kan Sallar Idi "Gwamnatin Jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya ta janye matakinta na karbar harajin N500, 000 kafin ta bayar da izinin amfani da wani babban fili da ke birnin Kaduna domin gudanar da Sallar Idi. Gwamnatin ta fasa karbar haraji domin bai wa wasu Musulmai damar yin amfani da filin Murtala Square wajen gudanar da Sallah Idi bayan ta fuskanci matsin lamba. Batun ya tayar da jijiyoyin wuya bayan da 'yan kwamitin masallacin Kano Road, wadanda ke amfani da filin wajen gudanar da sallar a duk shekara, sun bayyana mamakinsu kan matakin ganin cewa sun kwashe shekara da shekaru suna sallar Idi a cikinsa ba tare da bayar da ko sisi ba. Daya daga cikin mambobin kwamitin, Malam Sabi'u Garba, ya shaida wa BBC cewa ba su ji dadin harajin da gwamnati ta sanya musu na amfani da filin ba. ""Wannan wani abu da da ba mu taba jin sa ba, a ce mutum zai yi sallah sai ka biya kudin ibadar da za ka yi a arewacin Najeriya. Wannan wuri da muke sallah, Sardauna ma a nan ya rika sallah...iyayenmu da kakaninmu sun tabbatar da cewa an ba su takardun izinin (amfani da wurin don yin sallar Idi),"" in ji shi. Sai dai jim kadan bayan wadannan kalamai gwamnatin Jihar ta Kaduna ta janye matakin nata. Mista Anthony Richard, mai magana da yawun kwamitin kula da kasuwanni na Jihar ya gaya wa BBC cewa tun da farko sun dauki matakin karbar harajin ne saboda an yi gyare-gyare a filin don haka ba za a bar 'yan siyasa da masu gudanar da sha'anin addini su yi amfani da shi ba sai sun biya haraji.\n\nAmma ya ce sun fasa karbar kudin yana mai cewa ba matsin lamba ba ne ya sa aka janye aniyar. ""Akwai tsarin da aka fitar domin kokarin ganin cewa ba a rika ayyuka na addini ko na siyasa. An canza tsarin Murtala Square ne baki daya, yadda yake yanzu ya bambanta da yadda yake a baya,"" a cewar Mista Richard." https://www.bbc.com/hausa/articles/c2en2g8n8vqo +religion Kalli masallacin da ya fi kowanne kyau a Afirka da ke Ilori Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon: Wannan masallacin da ke birnin Ilori a jihar Kwara da ke yankin tsakiyar Najeriya shgi ne mafi girma a Afirka. Masallacin yana da girman da ke ɗaukar mutum 700 a lokaci guda. An ƙawata cikinsa da ado sosai. https://www.bbc.com/hausa/media-56115474 +sports Portugal za ta kara da Morocco a Quarter Finals a Qatar Portugal ta caskara Switzerland da ci 6-1 a wasan zagaye na biyu a Gasar Cin Kofin Duniya da suka buga ranar Talata a Qatar. Minti bakwai da fara wasa Goncalo Ramos ya fara cin kwallo a karon farko da Porugal ta saka shi a wasa a kuma gurbin Cristiano Ronaldo. Haka shi ne ya kara biyu wato uku rigis ya ci a karawar - ya zama na farko da ya ci kwallo uku a wasan farko a kofin duniya, bayan Miraslove Klose na Jamus a 2002. Sauran da suka ci kwallayen sun hada da Kepler Laveran Pepe da Raphael Guerreiro da kuma Rafael Leao. Switzerland ta zare daya ta hannun Manuel Akanji a minti na 58. Da wannan sakamakon Portugal za ta fuskanci Morocco a wasan Quarter finals ranar Asabar 10 ga watan Disamba. Morocco ta kai daf da na kusa da na karshe, bayan nasara a kan Sifaniya da ci 3-0 a bugun fenariti. Sai daga baya aka sa Cristiano Ronaldo a wasan - a karon farko da ya yi zaman benci a manyan wasan Portugal tun 2008. A lokacin a kuma fafatawa da Switzerland kenan yanzu wasa 31 ne tsakanin. https://www.bbc.com/hausa/articles/cjr2l18d1kno +health Gobarar dajin Amazon: Me ya sa hankalin masana da shugabannin duniya ya tashi? A farkon mako ne sararin samaniyar Sao Paulo ya yi baki kirin, saboda wani gagarumin hadarin hayaki da ya turnuke. Hayakin ya samo asali ne daga nisan kilomita 2,700, daga kungurmin dajin nan na Amazon mai matukar muhimmanci. Dajin Amazon yana da girman murabba'in kilomita miliyan 5 da rabi, shi ne dajin da ya fi kowanne girma a duniya, kuma dajin yana a kasar Brazil ne da ke kudancin nahiyar Amurka. Idan aka kwatanta, dajin ya fi girmar nahiyar Turai baki dayanta. Ana wa dajin Amazon take da cewa shi ne 'mabubbugar iskar da dan'adam ke shaka' ta duniya. Yana kunshe da nau'ukan tsirrai da halittu daban-daban kimanin miliyan 3. Akwai mutane kauyawa miliyan daya da ke zama a kungurmin dajin. Dajin yana taka muhimmiyar rawa wajen zuke sanadarin Carbon mai illa ga dan'adam. Ana fitar da sanadarin Carbon ne daga hayakin motoci, da jirage, da kuma cibiyoyin samar da wutar lantarki. Rashin isassun hanyoyin zuke sanadarin Carbon daga muhalli zai iya janyo illa ga duniya, daya daga cikin wadannan illoli shi ne dumamar yanayi da ake fama da shi. Sakatare janar na majalisar dinkin duniya Antonio Guterres ya ce 'A yayin da ake cikin rudani na sauyin yanayi, duniya ba za ta yadda ta kara lalata wannan muhimmiyar kafar samar da iska mai tsafta da halittu a duniya ba. Dole a kare dajin Amazon.' Me kasashen duniya ke cewa kan gobarar Amazon? Shugaba Donald Trump na Amurka ya ce ya yi magana da shugaban Brazil Jair Bolsonaro, inda ya ce Amurka a shirye take ta taimaka wa Brazil wajen kashe wutar dajin Amazon. Faransa da Ireland sun yi barazanar cewa ba za su sake sabunta wata muhimmiyar yarjejeniyar kasuwanci a tsakanin su da kasashen kudancin nahiyar Amurka ba, face sai Brazil ta kara kaimi wajen kawo karshen gobarar dajin na Amazon. A ranar Alhamis, shugaba Emmanuel Macron ya ce ya kamata a mayar da hankali wajen tattauna gobarar dajin Amazon a taron kashen manyan kasashen duniya 7. Ministan kudi na Finland shi kuma ya yi kira ne ga kasashen Turai da su haramta shigo da nama daga kasar ta Brazil. Wane ne ya tayar da gobarar? Kasashen duniya suna dora laifin wannan gobara ne a kan shugaban Brazil Jair Bolsonaro. Wani dan jarida na Brazil Silio Boccanera ya ce kasancewar yanzu lokacin rani ne a Brazil, dole za a yi tsammanin samun wutar daji. Amma yanzu haka ana zargin cewa da gangan aka cinna wuta a wurare daban-daban na dajin. Shugaba Bolsonaro ba ya sukan sare itatauwa a dajin na Amazon, kuma yana goyon bayan sare itatuwa domin gudanar da noma da kuma hakar ma'adanai. Wane mataki ake dauka domin kashe gobarar? Bayan shan matsi daga kasashe da kungiyoyi na duniya, a ranar Juma'a shugaban Brazil Jair Bolsonaro ya umurci jami'an tsaro da su taimaka wajen kashe bakunan wutar gobara da suka balle a dajin nan na Amazon. Wani umurni da shugaban na Brazil ya bayar, ya bayar da damar aikewa da sojojin suwa dazuzzukan domin ganin an shawo kan gobarar. Wannan umurni da shugaban kasar ya bayar kamar yadda aka tsara za ta yi aiki ne tsawon wata guda, daga 24 ga watan August zuwa 24 ga watan Satumba. https://www.bbc.com/hausa/labarai-49456922 +entertainment Kannywood: Nafisa Abdullahi ce ta fi fice a Google a 2021 Tauraruwar fina-finan Hausa Nafisa Abdullahi na cikin jerin taurarin da aka fi neman karin bayani a kansu a shafin matambayi-ba-ya-ɓata na Google Search a shekarar 2021 a Najeriya. Tauraruwar ta fim ɗin Labarina ta shiga jerin ne tare da taurarin fim na kudancin Najeriya da ake kira Nollywood irin su Destiny Etiko da Tonto Dikeh da Zubby Michael. Sai dai Google ya saka Nafisa a ɓangaren Nollywood maimakon Kannywood, wanda nan ne take ciki ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton. Ita ce a matsayi na shida a sashen taurarin fina-finai bayan Destiny Etiko da Zubby Michael da Pere da Tonto Dikeh da Iyabo Ojo da kuma Olu Jacobs. Haka kuma, Nafisa ce kaɗai daga taurarin Kannywood da ta shiga cikin taurari 10 na farko a Google Search. Sauran 'yan Kannywood Rahama Sadau da Fati Washa da Maryam Yahaya da Hadiza Gabon ne ke biye mata a shahara, duk da cewa ba sa cikin goman farko. Shafin Google kan fitar da kalmomi da sunaye da ababen girki da mutane waɗanda miliyoyin masu amfani da shafin suka fi bincikawa duk shekara. Sannan shafin kan yi wa sunayen rukuni, inda ake da rukunan mawaka da wakar kanta da wasanni da 'yan fim da fina-finan kansu da tambayoyin da aka fi yi. Nafisa na da mabiya miliyan biyu a Instagram da 176,600 a Twitter da kuma wasu miliyan biyu a Facebook. A ɓangaren fina-finai, 'yan Najeriya sun fi neman bayanai kan Squid Game da Coming to America 2 da Sex Life da Black Widow da kuma Red Notice. Daga cikin waɗanda suka rasu a 2021 kuwa, shahararren malamin Kirista TB Joshua da mawaƙi Sound Sultan da kuma Sani Dangote - ƙani ga Aliko Dangote - na cikin waɗanda aka fi dubawa. Kamar yadda bayanai suka nuna, Nafisa ta fara shahara ne a shafin daga ranar 3 zuwa 9 ga watan Janairun 2021. Hakan ba zai rasa nasaba ba da kammala kashi na 2 na fim ɗinta mai dogon zango wato Labarina, inda aka haska zangon ƙarshe a ƙarshen watan Disamban 2020. Masu neman bayanai kan tauraruwar sun ƙaru zuwa kashi 93 a watan Satumba, wanda a daidai lokacin ne ake tsaka da haska kashi na 3 na Labarina. Bugu da ƙari, masu bincika Nafisa Abdullahi sun ƙaru zuwa kashi 100 cikin 100 daga 5 zuwa 11 na watan Disamba. Wannan kuma idan ba ku manta ba, yana da nasaba da kayayyakin ƙawa da ta ƙaddamar mai suna NAFCOSMETICS. Mazauna Abuja babban birnin Najeriya ne suka fi neman bayanai game da Nafisa, sai kuma jihohin Rivers da Legas da Kaduna. Nafisa Abdullahi ta kwana biyu ba a ganinta a harkar fina-finai kafin fara haska fim ɗin Labarina a 2020. Fim ɗin wanda kamfanin Saira Movies na Aminu Saira ke shiryawa, ya samu Nafisa a matsayin babbar jaruma wadda aka gina labarin a kanta. Tun bayan fara haska Labarina babu wani fim da Nafisa ta fito a ciki wanda ya yi kusa da farin jinin da Labarina ke da shi. Yayin da tauraruwarta ke tsaka da haskakawa, ta ƙaddamar da sabon kamfanin kayan kwalliyarta mai suna NAFCOSMETICS a watan Nuwamban 2021. Bugu da ƙari, an san tauraruwar da tafiye-tafiye zuwa ƙasashen Turai da Amurka, inda takan je domin ƙarin karatu ko kuma yawon buɗe-ido. https://www.bbc.com/hausa/labarai-59664920 +business Amsar tambayoyinku kan nau'ukan haraji a Najeriya "Wannan maƙala ce ta musamman bayan da muka buƙaci mabiyanmu da masu saurare su aiko da tambayoyinsu kan abin da suke son sani game da tsarin biyan haraji a Najeriya. BBC Hausa ta duba tambayoyin naku kuma ta miƙa su ga masana da masu ruwa da tsaki a fannin na haraji. Tambaya ce da muka samu daga Maruma Ibirahim da wasu da dama da ba su rubuta sunayensu ba Dakta Shamsuddeen Muhammad, masanin tattalin arziki a Jami'ar Bayero ta Kano da ke Najeriya, ya bayyana haraji a matsayin wani kuɗi da gwamnati ta wajabta wa jama'a biya. ""Wani kuɗi ne na dolen-dole da gwamnati take ɗora wa ƴan ƙasa ko dai a kan kuɗin da suke samu a wurin sana'o'insu ko kuma a kan riba da suke samu a kasuwancinsu,"" in ji shi. Masanin ya ƙara da cewa kuɗaɗen harajin da gwamnati take karɓa suna taimaka wa gwamnatin wajen samun kuɗaɗen shiga. Tambaya ce da muka samu daga Mukhtar Muhammad Ngibirma da Abdulrasheed Kaku Unguwan Sarki Kaku da Nazifi Lawal Batsari da Siraja Abubakar da Ibrahim mai Indomie da Abbakar Usman Masanin tattalin arzikin ya ce zai yi wuya a iya rarrabe amfanin haraji ga mutane da kuma gwamnati saboda ""kamar gwamnatin ita ce mutane."" Amma ya bayyana wasu kamar haka: Masanin ya bayyana cewa ana karɓar haraji ne domin bai wa gwamnati damar gudanar da ayyukan more rayuwa ga al'ummarta kamar ruwan sha da wutar lantarki da tituna da tallafi da gwamnati ke bayarwa lokacin da aka shiga wasu matsaloli. Baya ga samar da ayyukan ci gaba a ƙasa, masanin ya ƙara da cewa harajin yana da amfani saboda yana rage amfani da abubuwa masu cutarwa inda ya ba da misali da kamfanonin giya da taba a Najeriya, wadanda suke biyan haraji mai nauyi wanda ya kai kusan kashi 20 cikin ɗari na kayan da suke samarwa ""saɓanin kashi bakwai da rabi na sauran kayan masarufi."" Ya ce ana yin haka ne domin rage yawan shan barasa da kuma taba sigari a ƙasar, ""shi haraji idan an sa wa kaya sun yi tsada sosai, lalle mutane za su rage shansu maimakon wataƙila mutum ya sha kara 10 na sigari a rana, sai ya sha kara biyu ko uku ko biyar."" Ana amfani da haraji wajen gyara muhalli - ""duk inda masana'antu suke suna taimaka wa wajen lalacewar muhalli, ta lalata ruwan sha da iska da sauransu. ''Idan ana ɗora haraji mai nauyi kan irin waɗannan dagwalon masana'antu ke zubarwa su masana'antun suna ƙoƙarin rage abin da suke zubarwa na dagwalon wanda wannan yana taimakawa haraji ƙwarai da gaske,"" in ji Dakta Shamduddeen Muhammad. A cewar masanin, wani ƙarin amfanin harajin shi ne yana rage shigo da kaya daga ƙasashen waje domin bunƙasa kamfanonin cikin gida. ""Misali, kayan da gwamnati ba ta so a shigo da su waɗanda take ganin za a iya yinsu a cikin gida sai ta ɗora musu haraji mai yawan gaske, waɗanda idan an kawo su a cikin gida ba za su sayu ba sai dai misali sani na cikin gida,"" a cewar masanin. Ana amfani da haraji wajen cimma wannan buƙata ""duk lokacin da hauhawar farashi ta yi yawa cikin ƙasa mafi yawa abin da yake faruwa kuɗi ne yake yawa a hannun jama'a sai gwamnati ta ɗora haraji a kan mutane ta rage yawan kuɗin da yake hannun mutane (ta yadda) mutane ba za su iya sayan abubuwan da suke so ba, wannan zai rage yawan buƙatar abubuwa a kasuwa."" Ya ce a duk lokacin da aka samu buƙatar abubuwan da mutane suke so a kasuwa hakan yana sa farashi ya sauka. Bunƙasa ayyukan yi A cewar masanin karɓar haraji na taimakawa wajen samar da ayyukan yi inda ya ba da misali da yadda a wani lokacin matsalar rashin aikin yi take yawa. ""A wannan lokacin abin da gwamnati take yi shi ne rage yawan haraji a kan mutane domin su samu kuɗaɗe da yawa a hannunsu da za su kashe a kasuwanni, idan sun kashe kuɗi da yawa a kasuwanni, masana'antu za su samu damar yin kayayyaki da yawa saboda akwai ciniki a kasuwa, wannan zai taimaka su ɗebi ma'aikata da yawa,"" kamar yadda masanin ya shaida wa BBC. Rage bambancin arziki tsakanin ƴan ƙasa Ana kuma amfani da haraji wajen daidaita tsakanin ƴan ƙasa ta fuskar tattalin arziki saboda masu wadata sun fi biyan haraji mai yawa yayin da waɗanda talakawa suke biyan haraji ɗan kaɗan ko ma ba sa biya. Nau'ukan haraji Masanin ya ce haraji ya rabu gida biyu - na kai tsaye da wanda ba na kai tsaye ba. Wannan haraji a Turancin Ingilishi ana kiransa Direct Tax. Wannan haraji ne da ya shafi mutum kai tsaye da zai biya daga albashinsa ko kuma idan kamfani ne zai biya daga ribarsa. Ana kiransa haka ne saboda shi ya shafi mutum kai tsaye. Ya ce akwai ire-iren haraji da suka faɗo a ƙarƙashin wannan nau'i na haraji kamar harajin da mutum zai biya kai tsaye daga albashinsa wato Personal Income Tax ko Pay As You Earn da kuma harajin da ake cira daga ribar kamfanoni wato Profit Tax. A cewarsa, duk ribar da kamfani ya samu a shekara zai ware wani abu ya bai wa gwamnati wani abu cikin ribar. Tsarin wannan harajin shi ne mutum ba a cikin kuɗinsa zai biya ba. ""Misali harajin kayayyaki da ake sana'antawa, idan mai kamfani ya biya harajin kayan da ya sana'anta zai ƙara waɗannan kuɗaɗen a kan kayan da ya sana'anta domin sayarwa,"" in ji Dakta Shamsuddeen Muhammad. Sai dai masanin ya ce a ƙarshe nauyin harajin yana ƙarewa ne a kan mai saye ""wanda ya biya daban wanda kuma nauyin harajin ya faɗa a kansa daban."" A ƙarƙashin wannan nau'i na haraji akwai wanda ake biyawa kayan masarufi wato VAT - ""shi kamfanin da yake ba wa gwamnati harajin ba shi ne yake bai wa gwamnati haraji ba, kwastomomi waɗanda suke sayen kayan su ne suke biyan harajin."" Akwai kuma harajin kuɗin fito wato Customs Duty ko Import da Export Duty- ""idan mutum ya shigo da kaya na sayarwa daga ƙasar waje, zai biya musu haraji amma zai ƙara wannan haraji kan farashin kayan inda shi wanda zai kayan ya yi amfani da su shi ne wanda harajin zai ƙare a kansa,"" in ji masani Dakta Shamsuddeen Muhammad. Wannan haraji na kuɗin fito yana haura harajin VAT a Najeriya amma akwai ƙasashe na duniya musamman waɗanda suka ci gaba wanda shi harajin na VAT shi ne mafi yawan harajin da gwamnati take karɓa a kowanne lokaci. Ya ce akwai wasu kuɗaɗen shiga da ake biya kamar tara ko kuma Levy wanda ake ɗorawa a kan amfani da kayan gwmanati kamar masu haƙar ma'adinai da ƙarafuna da gwal suna biyan kuɗin hayar ƙasa wato Royalties ko kuma Lease. Sai kuma tara ta kotu da ake biya ko kuma idan mutum ya yi laifi a ɗora masa wata tara - ""ba haraji ba ne na kai tsaye amma yana cikin kuɗaɗen shiga da gwamnati take samu,"" a cewar masanin. Harajin kayan masarufi wato VAT Tambaya ce da muka samu daga Abbas Jobi da Abdulazeez Abubakar Baba da Nura Muhd Sani da Jamilu Bala Abdulkadir da Ibrahim mai indomie da Hussaini Mukhtar Isah Fagge da Abubakar Jidda da Farouk Ado Danmaliki da Yahaya Musa da Mustapha Magaji Muhammad Shi wannan haraji ana biyawa kayan masarufi ne kuma kamfanonin cikin gida ne suke ɗora wannan haraji a kan kuɗin kayansu amma wannan ƙarin da suka yi na haraji ba nasu bane na gwamnati ne. Dakta Shamsuddeen ya ce: ""Idan mutane sun sayi kayan za su cire wannan kaso na haraji sai su bai wa hukumar da take karɓar haraji na gwamnatin tarayya."" Ya ce irin wannan harajin yana daga cikin manya-manyan haraji da gwamnati take karɓa kuma ana ɗora shi a kan dukkan kayan masarufi da ake sana'antawa a cikin ƙasa ban da waɗanda gwamnati ta ga dama tace ban da su saboda wasu dalilai. ""Kamar misali mu a nan Najeriya, an ce duk abin da ya shafi kayan abinci da kayan ilimi da kayan lafiya - waɗan nan su ba za a ɗora musu harajin VAT ba amma bayan su duka sauran abubuwan da sauran ƴan ƙasa suke amfani da su har wutar lantarki duka wannan haraji na VAT yana kansu, Yadda yake shi gwamnati tana ɗora wani kaso na kai tsaye da za ta ce komai za a sayar za a ƙara wannan kaso a kan kuɗinsa wanda shi wannan kason shi ne VAT ɗin wanda gwamnati ce za ta karɓe shi. Misali a Najeriya yanzu, kason da ake biya na harajin VAT kashi bakwai da rabi cikin ɗari ne wanda ya ƙaru daga kashi biyar da da ake biya a wannan shekarra a watan Fabrairu aka ƙara shi daga kashi biyar cikin ɗari zuwa kashi bakwai da rasbi cikin ɗari,"" in ji masanin. Tambaya ce da muka samu daga Salisu Dayyabu Masana sun ce wannan haraji na Stamp Duty ɗaya daga cikin tsofaffin harajin da ake biya a duniya kuma ya samo asali ne daga Daular Sufaniya tun ƙarni na 17 kimanin kusan shekara 400 kenan. Hatimi ne na gwamnati da ake bugawa a kan takardu waɗanda ake amfani da su wurin wata yarjejeniya ko kuma ciniki - takardu irinsu chekin kuɗi da takardar lasisin aure ko takardar sai da filaye duka suna buƙatar gwamnati ta buga hatiminta a kai domin ya zama cewar su waɗan nan takardu sun zama masu amfani kuma ko da kotu aka je waɗan nan takardu za su iya zama shaida saboda ga hatimi na gwamnati an buga a kai. ""Duk wanda ya yi irin wannan ciniki ko kuma suka yi irin wannan yarjejeniya ko kuma suka yi irin wannan yarjejeniya har gwamnati ta buga hatimi a kai sai a biya gwamnati kuɗi na hatimin da ta buga. Amma tun wannan lokaci gwamnatoci na duniya daban-daban suna amfani da wannan tsari har muka kawo zamanin da yanzu yawanci cinikayyar ba a yin ta fuska da fuska, yawanci cinikayya ce da ake yi ta kafofin sadarwa na zamani ko ta imel ko ta sauran kafafe na sadarwa na zamani, Sai gwamnati a baya-bayan nan ta ga cewa tun da yanzu ba a amfani da takardu na zahiri, me zai hana shi wannan Stamp Duty da ake biyawa takardu na zahiri ya koma kan har irin waɗan nan kasuwanci da ake yi ta kafafen sadarwa na zamani. Mu a nan a Najeriya daga watan Fabrairu, gwamnati ta ƙirƙiro cewa duk musayar kuɗi da aka yi ta bankuna - wani ya tura wa wani kuɗi in dai sun kai N10,000 sai ya biya wa wannan kuɗi abin da ake cewa Stamp Duty ɗin saboda a wajen gwamnati tana ganin duk wanda ya tura kuɗi har ya kai N10,000 ko sama da haka, lalle cinikayya aka yi,"" in ji masanin. Abin da gwamnatin Najeriya take samu daga harajin VAT Kuɗaden da gwamnati take samu daga harajin kayan masarufi suna hawa da sauka ne - ya danganta da yadda harkar tattalin arziki ta gudana a kowane wata tun da kuɗin ana karɓarsu ne wata-wata. ""A baya-baya lokacin da ake cikin wannan lalura ta Covid-19, kuɗin da ake karɓa na harajin VAT baya wuce N100bn amma a watan Agusta, kuɗaɗen da gwamnati ta karɓa ya kai sama da N150bn, Dakta Shamsuddeen Muhammad ya ce: ""Shi harajin VAT mafi yawa gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi ne suka fi morarsa, duk da cewa gwamnatin tarayya ce take karɓa amma idan an zo rabon arzikin ƙasa na wata-wata kusan kashi 86 cikin 100 na abin da aka karɓa na VAT yana tafiya ne ga gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi. A watan Agustan da ya gabata duk da dai an karɓi kuɗi har N150bn abin da gwamnatin tarayya ta mora a ciki bai wuce N20bn, ragowar kusan N130bn an raba su ne tsakanin ƙananan hukumomi da jihohi - jihohi sun rabauta da N70bn su kuma ƙananan hukumomi suka samu abin da bai fi N60bn."" Ina kuɗin haraji ke tafiya da yadda ake sarrafa shi? Tambaya ce da muka samu daga Ahmed Alim da Ahmad Tukur Akwai wani asusu da ake kira Federation Account a Turancin Ingilishi wani asusu ne da ake buɗe shi a babban bankin ƙasa wanda ake zuɓa kuɗaɗen harajin a kowane wata. Aannan a haɗa da sauran kuɗaɗe da gwamnati take samu ta hanyar sayar da mai a tara su sai sun taru a ƙarshen wata sai a raba su tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi, wanda kwamitin FARC da aka ɗorawa alhakin rarraba arziƙin ƙasa yake yi a kowane wata. Game da sarrafa kuɗaɗen harajin kuma, gwamnatocin a matakan uku suna amfani da kuɗaɗen wajen biyan bashi da yi wa ƙasa hidima da samar da abubuwan more rayuwa musamman manya-manyan ayyuka irinsu tituna da sauransu. Masanin tattalin arzikin ya bayyana cewa akwai harajin da gwamnatin tarayya da gwamnatin jiha da kuma ƙananan hukumomi suke karɓa. A cewarsa: ""Manya-manyan haraji na ƙasa kamar wanda ake cirewa a albashi, kamar wanda ake biya na shigo da kayayyaki ko fito da su da na wanda manya-manyan kamfanoni suke biya a cikin ƙasa, waɗan nan duka gwamnatin tarayya ce take karɓarsu."" Baya ga waɗannan akwai kuma wasu harajin da gwamnatin jiha da ƙananan hukumomi suke karɓa kamar harajin kasuwanni da harajin tashoshi da harajin masu sufuri da sauran abubuwa da suka danganci ƙananan haraji. Mafi yawan ƙananan hukumomi akwai sassa da suke kula da karɓar haraji a kasuwanni ko a tashoshi ko a hannun masu sufuri sannan su ma gwamnatocin jihohi suna da ma'aikata guda da take karɓar haraji domin gudanar da ayyuka ga ƴan ƙasa. Ita ma gwamnatin tarayya tana da babbar hukumar da take tattara mata haraji - Hukumar FIRS sai hukumar kwastam wadda take da alhakin karɓar harajin kayan fito na shige da ficen kayayyaki sannan ta miƙa su hannun hukumar karɓar haraji ta ƙasa. Akwai kuma ƙananan ma'aikatu na gwamnati da suke karɓar haraji da tara da ake ɗorawa mutane kamar Hukumar Aika Saƙonni ta Najeriya (NIPOST) da kotuna da suke ɗora tara a kan wanda suka yi laifi da sauran hukumomi masu tsaron kan hanya. Ita kanta kamfanin sarrafa albarkatun man fetur NNPC ita ma tana karɓar haraji na haƙar man fetur daga wajen waɗanda aka yarjewa su dinga haƙa sannan ma'aikatar kula da ma'adanai tana da alhakin karɓar kuɗin hayar ƙasa da take bai wa kamfanoni ko mutanen da suke haƙar ma'adanai a cikin ƙasa. Duka waɗannan mafi yawa sun fi karɓar tara ko kuma kuɗin haya yayin da hukumar FIRS da ta kwastam suke karɓar haraji ka tsaye a madadin gwmanatin tarayya."" a cewar masanin. Tambaya ce da muka samu daga Idrisir abdullahi da Jabir garba kauran wali da Farouk Ado Danmaliki A cewar masani Dakta Shamduddeen Muhammad, dangane da hanyoyin karɓar haraji, ya danganta da irin harajin inda ya ba da misali da harajin da wanda ma'aikaci yake biya daga albashinsa, idan kuma ma'aikacin gwmanati ne dama gwamnati ce ke biyan albashi kuma za ta ɗebe harajin tun daga tushe sannan ta turawa hukumar da take biyan albashi, harajin kuma sai ta turawa hukumar da take karɓar harajin. Idan kuma kamfani ne, kowane kamfani a ƙarshen shekara zai rubuta ribar da ya samu a shekara sannan ya ware kason biyan haraji ya je ya shigar wa hukumar tattara haraji wannan kuɗi a banki, sannan ya kai shaidar cewa ga abin da ya ci riba ga kason haraji da ya biya su kuma su ba da takardar cewar ya biya haraji a wannan shekarar. Idan ya ƙi yin hakan akwai hanyoyi da ita hukumar karɓar haraji ta ƙasa take bi don tabbatar da ta karɓi wannan haraji - tun daga amfani da jami'an tsaro har zuwa kotuna har ma a ƙarshe idan kamfani ya kasa biyan haraji a rufe kamfanin ko ma a sayar da shi kuma gwamnati ta ɗebi kuɗinta a cikin kadarorin kamfanin. Shin gwamnati tana abin da ya dace da kuɗaɗen harajin? Masanin tattalin arzikin ya ce ba za a ce gwamnati ba ta yin komai ba saboda ""komai lalacewa a ƙalla kusan kowane wata gwmanati za ta biya ma'aikata albashi sannan abubuwan da ba a rasa ba na gudanar da gwmanati na harkokin ilimi da harkokin lafiya duka gwmanati za ta yi ko da bai kai yadda mutane suke tsammani ba. Sai dai ya ce matsalar ita ce ""ana zargin cewa idan an ware wasu kuɗaɗen domin yin wasu ayyukan a cikin ƙasa ana samun ɓatagari a cikin waɗanda suke riƙe da madafun iko ko waɗanda aka ɗorawa alhakin yin waɗannan ayyuka sai su ɗebe wani kaso na wannan kuɗaɗe da aka ware don yi wa jama'a aiki, sai su kwashe kuɗaɗen gaba ɗaya su zuba a aljihinsu ko ma a (asusunsu) kuma su ƙi yin wannan aiki ko kuma su yi shi rabi da rabi su yi shi ba yadda ya dace ba su kwashe ragowar kuɗaɗen."" A cewar Dakta Shamsuddeen Muhammad ya ce Najeriya tana ɗaya daga cikin ƙasashen da aka yi ƙiyasin cewa kuɗaɗen harajin da 'yan ƙasa suke ƙin biya ya yi yawa saboda a shekarar 2019, shugaban hukumar karɓar haraji ya ce gwmanati tana kusan asarar naira triliyan biyar a harjin da ba a karɓa ba kuma laifin ya haɗa da mutanen da suke biyan haraji da kuma hukumomin da suke karɓar harajin. ""Su mutane dama kowa zai yi ƙoƙarin ƙin biyan haraji har sai dai idan ya ga ba yadda zai yi gwmanati ta tilasta shi, idan ya ga cewa gwmanati ba ta san da shi ba ko kuma gwmanati ba za ta san nawa ya kamata ya biya ba, wannan abu ne na rashin nuna kishin ƙasa da kuma daƙile harkar ci gaba a cikin ƙasa domin wannan haraji da mutane za su biya da shi ne gwmanati za ta yi wa mutane aiki. Wani lokacin kuma matsalar tana faruwa ne daga hukumomin da suke karɓar harajin su ne suke haɗa baki da abokansu ko ƴan uwansu da suke da kamfanoni su nuna musu ba ma sai sun biya haraji ba su nuna musu kamar taimaka musu suke yi abin da ya kamata ka biya sai ka biya abin da bai kai rabinsa ba. Kuma su hukumomin da suke karɓar harajin ko kuma jami'ansu sun san cewa abin da ka biya ba shi yakamata ka biya ba abin da za ka biya ya ninka haka amma sai su yi shiru saboda wata alaƙa da take tsakaninsu ko kuma saboda za ka ɗebi wani abu na wannan kaso na abin da ba ka biya ba su ma ka ba su su zuba a aljihinsu."" Amma ya ce yadda yake ganin za a gyara lamarin shi ne kowa ya sa tsoron Allah da kishin ƙasa da son ci gaban ƙasa a zuciyarsa wanda ya ce rashin haka babbar matsala ce. Masanin ya ce babbar illar rashin biyan haraji shi ne gwamnatin Najeriya za ta koma dogaro ne da kuɗaɗen da take samu daga sayar da mai da sauran ma'adanai - ""duk sanda kuɗin man fetur ya faɗi a kasuwar duniya, ƙasar tana shiga garari tana shiga wani hali saboda mutane ba sa biyan harajin da ya kamata, kowa a ƙasar sai ya shiga wahala, tsadar rayuwa ta yi yawa, talauci ya yi yawa rashin aikin yi ya yi yawa. Wata matsalar ta haɗa da yawan basussukan da gwamnati take ciyowa domin ta samu ta yi ayyukan da suka zama wajibi ko kuma take son yinsu. Ya ce da gwamnati tana samun isassun kuɗaɗen harajin wataƙila da ba sai ta dangana da ciyo bashin ba." https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-54251684 +entertainment Kayatattun Hotunan Afrika na mako 27 Mayu-2 Yuni 2022: Wasan jirgi da gunki da fina-finai Wasu daga cikin zaɓaɓɓun hotuna daga Afrika da na ƴan Afrika daga wasu sassan duniya. Duka waɗannan hotunan suna da haƙƙin mallaka. https://www.bbc.com/hausa/labarai-61683423 +entertainment Priyanka Chopra ta bayyana yadda rayuwa ta kasance ma ta bayan aure Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon: Fitacciyar ƴar fim din Bollywood Priyanka Chopra Jonas ta saki tarihin rayuwarta da ta rubutawa, inda ta bayyana labaran da suka shafi zama shahararre da yadda al’umma ke kallonta, da batun aurenta da mawaƙi Nick Jonas. Kullen annobar cutar korona ya rutsa da ƴar fim ɗin a Landan tun watan Nuwamba lokacin da ta je ɗaukar sabon fim ɗinta. https://www.bbc.com/hausa/media-56254401 +religion Borno ta bai wa malamai 30 a Saudiyya kwangilar addu’a kan Boko Haram Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya bai wa wasu 'yan Najeriya mazauna Makkah su 30 kwangilar yin addu'o'i da kuma dawafi a kullum domin rokon Allah (SWA) ya dawo da zaman lafiya jihar Borno da kuma Najeriya baki daya. Mutane 30 din da aka basu kwangilar wadanda suka fito daga Borno da Katsina da Zamfara da Kano da kuma wasu sassa na yankin arewa maso yammacin Najeriya, tuni dama mazauna Saudiyya ne fiye da shekaru 10 inda a kullum suke ziyartar ka'aba domin addu'o'i. Cikin mutanen, harda wani tsoho da ya shekara 40 kullum yana Ka'aba domin gudanar da addu'o'i. Dakin Ka'aba ne wuri mafi tsarki ga musulmai wanda dakin na nan a cikin masallacin Makkah. Mai magana da yawun gwamnan jihar Malam Isa Gusau ya bayyana cewa wannan yunkurin da gwamnan ya yi, na daya daga cikin abubuwan da ake kokarin yi na samar da tsaro da suka hada da taimaka wa sojojin Najeriya da kuma daukar 'yan sa kai da kuma mafarauta da samar musu da makamai da kuma sauran tsare-tsare na samar da aikin yi da ci gaba. A lokacin da gwamnan jihar ya gana da malaman da ke Saudiyya a ranar Juma'a, ya yi godiya matuka a garesu inda ya nemi su ci gaba da gudanar da addu'o'i, inji Malam Isa. Har yanzu dai ana samun hare-haren kungiyar Boko Haram a jihar Borno da sauran yankuna na arewa maso gabashin Najeriya. Ko a makon da ya gabata sai dai aka kai hari a garin Gubio da ke jihar Borno duk da cewa sojoji sun ce sun dakile harin. Samar da tsaro na daya daga cikin manyan alkawura uku da shugaban kasar ya yi tun a yakin neman zabensa na 2015 da kuma 2019. Sai dai har yanzu akwai sauran rina a kaba dangane da tsaro a kasar sakamakon kara fadadar matsalar a wasu yankuna musamman arewa maso yammacin kasar. https://www.bbc.com/hausa/49951782 +business Afghanistan: Ya girman noman ganyen opium da ribarsa ga Taliban? "Taliban ta yi iƙirarin cewa an daina noman ganyen opium kuma an dakatar da shigar da haramtatun kwayoyin zamanin mulkinta na baya a Afghanistan. Duk da cewa an samu raguwa sosai a 2001 - lokacin da ta yi mulkin ƙasar a baya - noman ganyen opium a yankunan da Taliban ke riƙe da su ya ƙaru a shekarun baya-bayan nan. Noman opium na ɗaya daga cikin ganyayyakin da ake amfani da su wajen haɗa kwayoyin maye, ciki har da hodar iblis. Afghanistan ita ke kan gaba wajen noma ganyen opium a duniya, a cewar ofishin hukumar Majalisar Dinkin Duniya da ke yakar shan kwayoyi. Afghanistan ke samar da kashi 80 cikin dari na opium a duniya. A 2018 Majalisar Dinkin Duniya ta ƙiyasta cewa noman ganyen opium shi ke sama wa ƙasar kashi 11 cikin 100 na ƙudaden shiga. Bayan Taliban ta sake karbe ikon Afghanistan, kakakinta Zabuhullah Mujahid ya ce: ""Lokacin da muke mulki ba a samar da kwayoyi."" Ya ce ""za mu kawo karshen noman opium baki ɗaya"" sannan za a daina fasa kwaurinsa. A farko, noman ganyen opium din ya ƙaru a ƙarƙashin mulkin Taliban - daga kadada 41,000 a 1998 zuwa 64,000 a 2000, a cewar bayanan ma'aikatar cikin gida ta Amurka. Noman galibi ya kasance a ƙarƙashin yankin da Taliban ke mulka na Helmand, wanda ke samar da kashi 39 cikin 100 na ganyen da ake nomawa a duniya baki ɗaya. Amma a watan Yulin 2000 Taliban ta haramta noman opium a yankuna da dama da take mulka. Kuma wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya a Mayun 2001 ""ya lura da nasarar da ake samu na haramta noman a yankunan bakin ɗaya da Taliban ke iko"". Bayan haramcin Taliban kan noman wannan ganyen, an lura da ragin da aka samu wajen fitar da hodar iblis a duniya tsakanin 2001 zuwa 2002. Sai dai, daga baya abubuwa sun sauya. Duk da cewa an ci gaba da wannan noma a yankunan da Taliban ke mulka kafin kifar da gwamnati, yawanci ana noman wannan ganyen ne a yankuna da Taliban ke iko. Yankin Helmand a kudancin Afghanistan, misali, ya fi girman gonaki da ake amfani da su wajen noma opium a 2020 lokacin da Taliban ke rike da shi. Noman opium na kan gaba wajen samar da aikin yi a Afghanistan, a 2019 noman opium na samar da aiki ga yan kasar 120,000, a cewar rahoton Majalisar Dinkin Duniya. Taliban na samun riba ta kudaden harajin da ake samu daga noman opium da sararafawa da kuma fatauci, a cewar ma'aikatar cikin gida ta Amurka. Suna karbar harajin kashi 10 cikin 100 na kudaden noman opium a gonaki. Ana kuma karɓar kuɗaɗen haraji daga dakunan kimiyar da ake sarafa ganyen opium zuwa hodar iblis, da kuma masu fataucin kwayar. Kudaden da Taliban ke samu a kowacce shekara daga wannan harkar na kai wa daga dala miliyan 100 zuwa miliyan 400. Kwayar ke samarwa Taliban kashi 60 cikin 100 na kudaden shigarta a shekara, a cewar Amurka. Sai dai akwai wasu ƙwararru da suke da ja kan waɗannan alkaluma. David Mansfield, wani mai bincike kan migayun kwayoyi, ya ce: Harajin da Majalisar Dinkin Duniya da Amurka ke magana akai ba a gani a kasa - kuma ba a ganin tasirin haka ga fanin hada-hadar kudade. ""Ya ce watakila kuɗaɗen da suke samu ba zai haura dala miliyan 40 ba."" Kashi 95 cikin 100 na hodar iblis din da ake samarwa daga Afghanistan ana shigar da su kasuwannin Turai. Ko da yake, kashi 1 bisa 100 na hodar iblis din Afghanistan ke shiga Amurka, a cewar hukumar da ke yaki da migayun kwayoyi ta Amurka. Akasari daga Mexico ake kai musu. Tsakanin 2017 zuwa 2020, sama da kashi 90 cikin 100 na kwayoyin ake safararsu ta hanya. Amma a yan kwanakin nan ana samun karuwar kama masu safarar hodar a teku da ta hada Indiya da Turai. Duk da cewa ana samun sauye-sauye, noman opium da kwace duk wani abu da aka samar ta ganye ya karu a cikin sama da shekaru 20 a Afghanistan. Kwace irin wadanan kwayoyi ya yi matsakaicin tasiri kan kasar da ayyukan noma ganyen. A 2019 kudaden shigar da ake samu ta wannan hanyar ya yi kasa da kashi 8 cikin 100." https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-58333075 +sports Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Ronaldo, Lewandowski, Coutinho, Phillips, Dybala Tauraron dan wasan gaba na Manchester United da Portugal Cristiano Ronaldo, mai shekara 37, ya tattauna da wakilinsa, Jorge Mendes kan makomarsa a Old Trafford. (Sun) Sannan kuma tauraron dan wasan gaba na Bayern Munich, dan kasar Poland, Robert Lewandowski mai shekara 33 na daukar hankalin Manchester United. (Bild - in German) Kocin Aston Villa Steven Gerrard na son kugiyar ta yi amfani da damarta ta sayi Philippe Coutinho a kan yuro miliyan 40 (fam 33.5m). To amma kuma dole sai dan wasan na Brazil mai shekara 29, wanda ya taka rawar-gani a zaman aro da ya yi daga Barcelona, ya rage albashinsa na fam 480,000 a mako. (Telegraph - subscription required) Haka kuma Villa za ta iya neman dan wasan tsakiya dan Ingila Kalvin Phillips idan Leeds ta fadi daga gasar Premier. Kungiyar ta tattauna a kan dan wasan mai shekara 26 kuma masu yi wa kungiyar zawarcin 'yan wasa sun nuna sha'awarsu a kansa. (Athletic - subscription required) Juventus na shawarar kan ko ta kara wa dan wasanta na gaba dan Argentina Paulo Dybala, kwantiragi ko kuma ta nemi dawo da Paul Pogba, wanda ta sayar wa Manchester United a 2016. (Tuttosport - in Italian) Kocin Chelsea Thomas Tuchel ya bukaci dan bayansa na Denmark Andreas Christensen, mai shekara 25, da ya yi watsi da maganar Barcelona, ya zauna a Stamford Bridge. (Mirror) Luke Shaw, na sha'awar kulla sabuwar yarjejeniya ta ci gaba da zama a Manchester United. (90min) Arsenal ta tsara sayen 'yan gaba biyu da dan tsakiya daya a bazaran nan a wani garambawul da take shirin yi. Haka kuma watakila Gunners din su nemi sayen dan wasan gaba na gefe, da kuma 'yan wasan baya na gefe, hagu da dama. (Standard) Ita kuma kungiyar Sevilla ta kara farashin kudin na-gani-ina-so na Diego Carlos zuwa yuro miliyan 80 (fam 67m). Newcastle ta yi kokarin sayen dan wasan na Brazil mai shekara 28 a watan Janairu amma kungiyar ta Sifaniya ba ta shirya sayar da shi ba. (Goal) Atletico Madrid na kan gaba wajen zawarcin dan wasan tsakiya na Marseille da Faransa Boubacar Kamara. Rahotanni sun ce Manchester United da Newcastle ma na son dan wasan mai shekara 22 amma Atletico ita ce dan wasan ya fi son tafiya, idan kwantiraginsa ya kare a bazara. (Footmercato - in French) Watakila dan wasan Sifaniya Bryan Gil, mai shekara 21, ya ci gaba da zama a Valencia a kaka mai zuwa, bayan da ya je kungiyar ta Sifaniya a matsayin aro daga Tottenham a watan Janairu. (Star) Dan wasan tsakiya dan Holland, Ryan Gravenberch, mai sheakara 19, yana da damar tafiya Barcelona daga Ajax a bazaran nan. (Fabrizio Romano) https://www.bbc.com/hausa/labarai-60686003 +health Zazzabin Lassa ya kashe mutum 29 a Najeriya Mutum 29 ne suka mutu sakamakon annobar zazzabin Lassa daga cikin mutum 195 da suka kamu da cutar a Najeriya. Marasa lafiyan da cutar ta yi ajalinsu sun rasu ne a jihohi daban-daban, yayin da kashi 89% na wadanda suka kamu da ita ke jihohin Ebonyi da Edo da Ondo. Rahotanni daga mahukunta a jihohin sun nuna ana ta kara samun bullar cutar a jihohi. Wuraren da aka samu bullar zazzabin na Lassa sun hada da jihohin Jigawa da Kaduna da Kano da Edo da Filato da Imo da Kogi. Sauran su ne Abia da Bauchi da Benue da Borno da Delta da Ebonyi da Taraba da Ogun da Ondo da Osun da kuma jihar Nassarawa. Da yake nuna damuwa kan annobar, Ministan Muhallin Najeriya Muhammad Mahmud Abubakar ya ce ma'aikatar tare da hukumar yaki da yaduwar cutuka NCDC da Hukumar Lafiya ta Duniya WHO na aiki tare domin wayar da kan jama'a a kan cutar. Ministan ya ce hukumomin sun dukufa don ganin an dakile hanyoyin kamuwa da kuma yaduwar cutar da ake samu daga beraya. Tana kuma yaduwa a tsakanin mutane ta hanyar ta'ammali da beraye ta hanyar taba kazantarsu ko ababen da suka taba ko wadanda suka kamu da cutar. Hukumomin sun kafa ofisoshin tuntuba da wayar da kai kan tsaftar muhalli a jihohi, inda jami'ansu ke sa ido da bayar da rahoto kan bullar cutar ga ma'aikatar muhalli ta kasa don daukar mataki. Ministan wanda ya jaddada muhimmancin tsaftar abinci da muhalli ya ce NCDC za ta kai aikinta na wayar da kai a kan cutar zuwa masallatai da kasuwanni da sauran wuraren haduwar jama'a. A cewarsa ma'aikatar na bibiya domin tabbatar da ana yin aikin yadda ya kamata a dukkan matakai da kuma samar da isassun alkaluma. Ministan ya umarci jami'an kula da muhalli a dukkan matakan gwamnati su dukufa wurin wayar da kai kan tsaftar muhalli. Sauran matakan sun hada da gano matattarar beraye a masana'antu da kasuwanni da nufin sanya magani da kuma samar da tsaftatacciyar hanyar busar da kayan abinci da amfanin gona. Ma'aikatun suna kuma aikin tsaftace muhalli a jihohin Edo da Ondo, ta hanyar feshin maganin kwari da raba tarkunan beraye da wayar da kan jama'a kan mahimmancin tsaftar muhalli. Daga karshe ya shawarci jama'a da su rika kawar da abincinsu daga beraye da adana kayan abincinsu a wuraren da beraye ba za su kai garesu ba sannan su rika dafa abinci ya dahu sosai. Sauran sun hada da zubar da shara a-kai-a-kai kuma nesa da gida da toshe kofofin da beraye ke bi da sa maganin beraye da barin cin naman bera. Akwai kuma bukatar wanke hannu sosai da ruwa da sabulu. Su kuma ma'aikatan lafiya da ke jinyar masu cutar su rika sanya kayan kariyar fuska da na jiki. Ya kuma yi kira ga kafafen yada labarai da sauran masu fada-a-ji su taimaka wurin yakar annobar ta hanyar wayar da kan jama'a kan hanyoyin hana kamuwa da ita. https://www.bbc.com/hausa/labarai-51263649 +entertainment Sarauniya Elizabeth II: Shugabannin Afirka suna jimamin rasuwarta "Gimbiyar wancan lokaci Elizabeth ta sauka a otal din Treetops da ke wani yankin karkara na kasar Kenya, mai cike da korayen ganye, da dogayen bishiyoyi da namun dawa, lokacin da mahaifinta, Sarki George VI, ya mutu kuma ta zama Sarauniya tana da shekaru 25. A shekaru 70 da Sarauniya Elizabeth II ta kwashe tana mulki ta ziyarci kasashen Afirka fiye da 20, kuma a wani lokaci cikin raha a gaban Nelson Mandela, wanda yake murmushi, ta bayyana cewa ta fi ""kusan kowa"" a Afirka zuwa kasashen nahiyar, abin da ya sa mutanen da ke tare da ita a wancan lokacin suka tuntsire da dariya. Da yake ta gaji yankuna da dama a nahiyar Afirka yayin da ta zama Sarauniya, a zamaninta ne dukkan kasashe 14 da Birtaniya ta yi wa mulkin suka samu 'yancin kai, inda Ghana ta soma samun nata 'yancin a 1957. Sarauniya ta kulla dangantaka mai yauki tsakaninta da kasashen na Afirka, galibi ta hanyar kirkirar kungiyar Commonwealth. A shekarar 1961, an dauki hotonta tana rawa tare da Kwame Nkrumah, wanda ya jagoranci fafutukar neman 'yancin Ghana kuma ya zama shugaban kasar na farko. Wani muhimmin abu shi ne a bikin nadinta a 1953 ba a yi amfani da kalmar daula ba. Yanzu, shugabannin kasashen Afirka sun bayyana jimaminsu game da rasuwar Sarauniyar kuma shugaba mafi dadewa ta kungiyar Commonwealth. Shugaban Kenya, Uhuru Kenyatta, kasar da tana can ne aka bayyana rasuwar mahaifinta, ya nuna jimaminsa inda ya bayyana ta a matsayin ""wata babbar bishiya da ta bauta wa al'umma bil hakki, kuma tana da martaba ba wai kawai a Birtaniya da Commonwealth ba inda Kenya ta kasance mamba har ma duniya baki daya"". Ko da yake dangantaka ta yi tsami tsakanin Zimbabwe da Birtaniya tsawon shekaru, abin da ya sa marigayi shugaban kasar Robert Mugabe ya janye kasarsa daga kungiyar Commonwealth, mutumin da ya gaje shi Emmerson Mnangagwa ya wallafa sakon Tuwita cikin gaggawa kan ""ta'aziyyarsa"" ga Gidan Sarautar Birtaniya da kuma ""al'ummar kasar da kungiyar Commonwealth"". Shugaban Najeriya, kasa mafi girma da Birtaniya ta yi wa mulkin-mallaka a Afirka, Muhammadu Buhari ya rubuta doguwar ta'aziyya a shafinsa na Tuwita, yana mai cewa ya samun labarin mutuwarta ""cike da bakin ciki"". ""Tarihin Najeriya ba zai taba cika ba ba tare da fadin Sarauniya Elizabeth ll ba, matar da ta yi fice a duniya kuma shugaba ta gari. Ta sadaukar da rayuwarta wajen tabbatar da zaman lafiya a kasarta da kasashen Commonwealth ada ma duniya baki daya."" Kazalika ya yi maraba da hawan Sabon Sarki Charles III kan karagar mulki. Shi ma shugaban Gabon, Ali Bongo, kasar da Faransa ta yi wa mulkin-mallaka wadda ba ta dade da shiga kungiyar Commonwealth ba, ya bayyana ta'aziyyarsa a sakon da ya wallafa a Tuwita. Duk da sakonnin ta'aziyyar da shugabannin kasashen nahiyar Afirka, wasu daga cikin kasashen sun bayyana wahalar da suka dade suna sha a karkashin mulkin-mallakar Birtaniya, suna masu cewa an yi mulkin-mallakar ne a madadin gidan sarautar Birtaniya. Wasu daga cikin sarakuna a nahiyar Afirka su ma sun mika sakon ta'aziyyar su game da rasuwar Sarauniyar Ingila. Yarima Mangosuthu Buthelezi ya mika sakon ta'aziyyarsa a madadin Sarki Misuzulu KaZwelithini, na masarautar Zulu da ke Afirka ta Kudu. Ya bayyana ""gwaggwabar abotarsa"" da Sarki Charles III, inda ya aike da sakon ta'aziyya kai-tsaye a gareshi. Sarki Misuzulu ya fahimci irin halin da Sarki Charles ya fada a ciki, kasancewar mahaifinsa, Zwelithini, ya rasu a shekarar da ta wuce,  bayan ya shekara 50 a kan mulki. Sarauniya ta shahara a duniya a matsayin wacce ba ta tsoma baki a harkokin siyasa, sai dai a shekarar 1995 ta yi wani jawabi mai karfi yayin da ta kai ziyara Afirka ta Kudu shekara daya bayan mulkin turawa kalilan masu nuna wariyar launin fata. Ya yaba wa kasar kan ci gaban da ta samus: ""Kun kasance kasar da ta zama abin misali saboda yadda kuka sasanta da juna a duniya, kuma na sake zuwa nan ne domin na ganewa kaina abin mamakin da kuka yi.""" https://www.bbc.com/hausa/articles/cg6kv6ddwlwo +sports Man United ta taka wa Arsenal burki bayan cin wasa biyar a Premier Manchester United ta doke Arsenal 3-1 a wasan mako na shida a gasar Premier League da suka buga ranar Lahadi a Old Trafford. United ta fara cin kwallo a minti 35 ta hannun Anthony, sabon dan wasan da ta dauka a bana daga Ajax. Tun a minti na 12 da fara tamaula Gabriel Martinelli ya ci Manchester United kwallo, amma aka soke ta cewar an yi wa Eriksen keta tun farko. Bayan da suka yi hutu suka koma zagaye na biyu ne Bukayo Saka ya farke kwallon da aka ci Gunners. Sai dai kuma minti shida tsakani Marcus Rashford ya kara na biyu sannan ya ci na uku da ya sa United ta hada maki umun da take bukata. Rabon da Rashford ya ci Arsenal kwallo tun ranar da ya fara yi wa United wasa a cikin watan Fabrairun 2016, kafin wasan Lahadi ya fuskanci Gunners sau 13. Dan wasan Manchester United, Antony – wanda shi ne na 100 daga Brazil da ya koma buga Premier League – shi ne na farko daga kasar matashi da ya ci kwallo a wasansa na farko mai shekara 22 da kwana 192. United ta ci wasa hudu a jere kenan, bayan da aka doke ta karawa biyu tun farko – sun zama na uku da suka yi wannan bajintar bayan Tottenham a 2011/12 da kuma Arsenal a 2018/19. Arsenal ta yi rashin nasara a wasan Premier da yawa a Old Traford fiye da sauran kungiyoyi har sau 17 aka zura mata kwallaye 49 – a filin Anfield ne ka zura mata masu yawa 69. Arsenal ta kasa yin nasara a wasa bakwai baya, idan ta fuskanci Manchester United tana ta daya a kan teburi, ta yi rashin nasara biyar da canjaras biyu. Ranar 8 ga watan Satumba, United za ta kara da Real Sociedad a wasan farko a cikin rukuni a Europa League kakar bana. Arsenal za ta kece raini da FC Zurich a dai gasar ta Zakarun Turai ta Europa ranar 8 ga watan Satumba. https://www.bbc.com/hausa/articles/cgl00gk99r8o +sports Timo Werner zai sake komawa RB Leipzig Chelsea na tattaunawa da RB Leipzig kan bayar da aron Timo Werner, domin ya sake komawa buga Bundesliga. Dan kwallon tawagar Jamus, mai shekara 26 ya bar Leipzig zuwa Chelsea a 2020, amma ya kasa taka rawar gani a Stamford Bridge da cin kwallo 10 a wasa 56 a Premier League. Chelsea ta kara karfin gurbin masu ci mata kwallaye, inda ta dauki Raheem Sterling daga Manchester City, bayan da ta bayar da aron Romelu Lukaku. Sai dai kuma albashin da Chelsea ke biyan Werner, shi ne zai kawo koma baya wajen sayar dan kwallon. Idan kuwa ya koma wasannin aro, watakila Chelsea ta rage alabashinsa, ko Leipzig ta biya wasu kudin. A lokacin wasannin sada zumunta da Chelsea ta yi a Amurka, Warner ya sanar cewar a shirye yake ya gwada kwazonsa a wata kungiyar. Newcastle United na son zawarcin dan kwallon Jamus, sai dai kuma albashin dan wasan ya yi mata tsada. Eddie Howe na son daukar mai cin kwallaye biyu ko fiye da haka, wanda ya taya dan wasan Leicester James Maddison, kan fam miliyan 40. https://www.bbc.com/hausa/articles/cp4xq9784j2o +business Ce-ce-ku-ce ya barke tsakanin PENGASSAN da IPMAN kan tsadar fetur "Wata taƙaddama ta barke tsakanin kungiyar manyan ma'aikatan mai ta PENGASSAN da kungiyar manyan dillalan man fetur a Najeriya kan tsadar da mai ke yi a ƙasar. Kungiyar manyan ma’aikatan mai a Najeriya ta PENGASSAN ce dai ta buƙaci hukumomin tsaron  kasar da su dakatar da dillalan man fetur a ƙasar daga boye mai don sayar da shi sama da farashin gwamnati. Shugaban kungiyar na kasa Comrade Festus Osifo ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da kungiyar ta gudanar a Abuja. Ya ce: ""ƙarancin man fetur din da ake fama da shi a kasar da ya-ƙi-ci, ya-ƙi cinyewa, ya zama abin damuwa ga 'yan Najeirya saboda yadda ya fi shafar su, inda suke sayen man fetur din fiye da ainihin farashin da gwamnatin ƙasar ke sayarwa."" Osifo ya ce dillalan ba su da hujjar da za su ƙara farashin man fetur ba, ba su da ikon da za su yi ƙarin kudin man fetur din. Ya zargi ""gwamnati da nuna halin ko in kula kan matsalar, saboda shiru da ta yi kan batun. Kungiyar ta PENGASSAN ta buƙaci hukumomin tsaron Najeirya da su gaggauta daukar matakin hukunta ma dillalan man. ""Muna buƙatar bangarorin tsaron Najeriya, musamman hukumar hana fasa-ƙauri ta Najeriya da ta shige da fice da su kawo ƙarshen fasa-ƙaurin da ake yi a ƙasashen Afirka. Sai dai ƙungiyar ta manyan dillalan man fetur ta musanta zargin, inda ta ce laifin kungiyar manyan ma'aikata ne, kasancewar su ma'aikatan gwamnati da suka shigo harkar sayar da mai da ba nasu ba. Shugaban ƙungiyar manayan dillalan man fetur na arewacin Najeriya Bashir Dan Mallan ya ce PEGASSAN na da hannun wajen tsadar da man fetur din ke yi a Najeriya, da yadda suka sa musu harajin da suka sanyawa masu dakon man. ""Mun fi so hukumomin tsaron ma su shigo, domin su fahimci wadan ke haifar da tsadar man fetur a Najeriya. duk motar da zata shigo sai sun nemi a basu wani abu akai. Haka kuma ya musanta zargin cewar suna boye man fetur da su siyar da shi da tsada, inda yace da maganar tsada da mai ya yi suka ma zarge su da shi, wanda kowa ya san da tsada muke samo shi. Najeriya ita ce ƙasar da ta fi kowacce arziƙin man fetur a Afirka, sai dai an shafe gwamman shekaru tana fama da samun matsalar ƙarancin man fetur akai-akai. Hakan ya samo asali ne kan rashin matatun man fetur da ke cikin hayyancinsu a ƙasar. Wannan dalili ne yasa tilas ƙasar ke sayen tataccen man fetur daga ƙasashen wajen da take sayar musu da ɗanyen. Batun shirin gwamnati na janye bayar da tallafin mai yana yawan jawo tarnaƙi a wajen samar da man." https://www.bbc.com/hausa/articles/cd121d5lm0go +entertainment Jerin shugabannin da aka gayyata wurin jana'izar Sarauniya Elizabeth II - da wadanda ba a gayyata ba "Jana'izar da za a yi ta Sarauniya Elizabeth II ranar Litinin za ta kasance daya daga cikin manyan taruka da aka hada sarakuna da 'yan siyasa a Birtaniya a cikin shekaru aru-aru. A karshen makon jiya ne aka aika da takardun gayyatar zuwa jana'izar ga shugabanni da sarakuna da sauran manyan mutane a fadin duniya, inda ake sa ran shugabannin kasashe da manyan mutane fiye da 500 za su halarce ta. An shaida wa galibin shugabannin cewa su halarci jana'izar a jiragen sama na fasinja inda kuma aka gaya musu cewa za a dauke su a motocin bas daga filin jiragen saman zuwa yammacin London. Za a yi taron jana'izar ne a babban dakin Westminster Abbey, wanda zai iya daukar kusan mutum 2,200. Ga abubuwan da muka sani game da mutanen da za su halarci jana'izar da wadanda ba za su je ba. Sarakunan kasashen Turai, wadanda da dama daga cikinsu suna da alaka ta jini da Sarauniyar Ingila, na cikin wadanda ake sa ran za su halarci jana'izarta. Sarkin Belgium Philippe da Sarauniya Mathilde sun tabbatar da cewa za su halarci jana'izar, yayin da shi ma Sarki Willem-Alexander da matarsa, Sarauniya Maxima, tare da mahaifiyarsa, tsohuwar sarauniyar Dutch Gimbiya Beatrix za su halarci jana'izar. Sarki Felipe da Sarauniya Letizia na Sifaniya sun amince su halarci jana'izar, kuma su ma iyalan gidan sarautar Norway, Sweden, da Demark ake sa ran za su je wurin jana'izar. Fadar White House ta tabbatar da cewa Shugaba Joe Biden tare da mai dakinsa Jill Biden za su halarci jana'izar, ko da yake an fahimci cewa ba sa cikin wadanda za a dauka a motocin bas. Ana ta tattaunawa kan ko Shugaba Biden zai gayyaci mutumin da ya gabace shi, Donald Trump, domin shiga tawagar Amurka da za ta halarci jana'izar, sai dai da alama tsofaffin shugabannin kasar ba za su iya halartar jana'izar ba saboda adadin mutanen da aka ware wa Amurka ta tafi da su ba shi da yawa. Ana ta rade radin cewa wasu daga cikin tsofaffin shugabannin kasar da matansu - musamman Obama - sun samu katin gayyatar zuwa jana'izar. Jimmy Carter, wanda ya yi shugabancin kasar daga 1977 zuwa 1981, bai samu katin gayyata ba, kamar yadda ofishinsa ya shaida wa jaridar Politico. Ana sa rai shugabannin kasashen kungiyar Commonwealth, wadda Sarauniya ta shugabanta, za su halarci jana'izarta. Firaiministan Australia Anthony Albanese ya ce zai amsa gayyatar, haka kuma Firaiministar New Zealand Jacinda Ardern da takwaranta na Canada Justin Trudeau. Su ma masu rike da mukaman gwamna janar wadanda suka taka rawa a matsayin wakilan Sarauniya a kasashen Commonwealth ana sa ran za su halarci jana'izar. Rahotanni sun ce dadaddiyar Firaministar Bangladash Sheikh Hasina da shugaban kasar Sri Lanka Ranil Wickremesinghe sun amince su halarci jana'izar Sarauniya Elizabeth II. Sai dai ya zuwa wannan lokaci babu tabbataci kan ko Firaiministan India Narendra Modi zai halarci jana'izar. Sauran shugabannin kasashen duniya da aka ce sun amsa gayyatar halartar jana'izar sun hada da Firaiministan Ireland Micheal Martin, shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier, da takwaransa na Italiya Sergio Mattarella da kuma shugabar majalisar tarayyar Turai Ursula von der Leyen. Kazalika shugaban kasar Koriya ta Kudu Yoon Suk-Yeol da na Brazil Jair Bolsonaro sun tabbatar da cewa za su je wurin jana'izar. Haka kuma ana sa ran Basaraken Japan Naruhito, da shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan, da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron za su halarci jana'izar. Ba a sani ba kawo yanzu ko shugaban kasar China Xi Jinping, wanda ziyarar aikin da zai kai Kazakhstan da Uzbekistan a wannan makon za ta zama karon farko da ya bar kasar tun bayan barkewar annobar korona, ya samu gayyata ko kuma zai halarci jana'izar. Jamhuriyar Musulunci ta Iran, wadda aka dade da sanya mata takunkumai kan shirinta na kera makamin nukiliya, za ta tura wakilai, a cewar majijoyi na Whitehall. Ba a gayyaci wakilan Rasha, Belarus, da Myanmar zuwa jana'izar Sarauniya Elizabeth ba, a cewar wakilin BBC James Landale. Dangantakar difilomasiyya tsakanin Birtaniya da Rasha ta yi matukar tsami tun bayan da ta kaddamar da yaki a Ukraine, kuma a makon jiya kakakin Vladimir Putin ya ce ""ba shi da niyyar"" halartar jana'izar. An kaddamar da mamayar ne daga wani bangare na kasar Belarus, wadda shugabanta, Aleksandr Lukashenko, aboki ne kut da kut na Shugaba Putin. Kazalika Birtaniya ta janye harkokin difilomasiyyarta da dama daga Myanmar tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar a watan Fabrairun 2021." https://www.bbc.com/hausa/articles/c974d25rmzeo +sports Busquet ba zai yanke shawarar gasar karshe da zai yi wa Sifaniya ba Kyaftin din tawagar Sifaniya, Sergio Busquet ya ce ba zai yanke shawara ba kan ko wannan gasar da ake a Qatar ita ce ta karshe da zai yi. Wannan ce Gasar Kofin Duniya ta hudu da dan wasan Barcelona zai buga, bayan lashe Kofin a 2010. Mai shekara 34 ya dauki Kofin Gasar Nahiyar Turai a 2012 ''Ina mafarkin na kara daukar kofin duniya karo na biyu a Gasar Qatar.'' in ji Busquet. ''Ina murna da na halarci Gasar, ban damu da ita ce ta biyu ko ta hudu ba, ba zan yanke wani wa'adi ba. Sifaniya za ta buga wasan farko a rukuni na biyar ranar Laraba da Costa Rica. To sai dai kasar kan kasa cin wasan farko a rukuni a gasa uku baya da ta buga a wasannin da Fifa kan gudanar. Wannan shi ne karon farko da Sifani da Costa Rica za su fafata a Gasar Cin Kofin Duniya. Sai dai a karawa uku baya a wasannin sada zumunta, Sifaniya ce ta yi nasara a fafatawa biyu da canjaras daya. Karon farko da za su fuskanci juna tun bayan 2011, an kuma ci kwallo 12 a wasannin da suka yi a tsakaninsu. https://www.bbc.com/hausa/articles/c3g5w0ydr66o +politics Hira da tsohon Shugaban Hukumar Zaben Najeriya Farfesa Attahiru Muhammad Jega Latsa nan domin sauraren hirar: Tsohon Shugaban Hukumar Zaben Najeriya,wato INEC, Farfesa Attahiru Muhammad Jega, ya ce duka manyan jam'iyyun kasar na APC da PDP ba su cancanci ci gaba da jagorancin kasar mafi yawan jama'a a Nahiyar Africa bayan zaben 2023 ba; saboda abin da ya kira muguwar rawar da suka taka cikin shekaru 20 din da suka wuce. A cikin wata kebantaciyyar hira da sashen Hausa na BBC, fitaccen malamin jami'ar, ya ce kasar na bukatar wani zubin shugabanni na daban da akidunsu suka yi hannun riga da na jam'iyyun biyu, kafin ta fita daga cikin matsalolin da take ciki. Sai dai duka jam'iyyun biyu sun musanta kalaman nasa. A hirar da ya yi da Haruna Shehu Tangaza, Farfesa Attahiru Muhammad Jega ya fara da bayyana dalilansa na rikidewa zuwa dan siyasa: https://www.bbc.com/hausa/labarai-58127460 +technology Hukumar FBI ta nuna shaidar yi wa shari'a tarnaki a gidan Trump Hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka, FBI ta gaya wa wani alkali cewa tana sa ran gano shaidar da ke nuna yin tarnaki ga shari’a a binciken da take yi na gidan tsohon shugaban Amurka Donald Trump a Florida, kamar yadda wasu sabbin takardun kotu da aka fitar suka nuna. Masu bincike  sun ce an adana wasu takardun sirri tare da wasu jaridu da mujallu a gidan shugaban da ke Mar-a-Lago. Ma’aikatar shari’ar ta ce ta sanya takunkumi a kan takardar izinin binciken domin kare shedu farar hula masu yawa kan batun. A ranar Juma’a 28 ga watan Agusta ne Ma’aikatar shari’a ta Amurkar ta saki irin takardar izinin biciken da hukumar FBI ta yi amfani da ita wajen yin kutse a gidan tsohon shugaban kasar ta gudanar da bincike ranar 8 ga watan nan na Agusta, amma kuma na takaita abubuwan da ke cikin takardar sosai. Jami’in hukumar binciken ta FBI wanda ya rubuta takardar, ya bayyana cewa suna ganin akwai alamun su yarda cewa akwai shedar wasu abubuwa da suka saba doka da za su gano. Jami’in ya kuma kara da cewa akwai kuma alamar da kila za ta tabbatar musu da cewa an yi wa doka tarnaki a gidan. Takardar ta nuna cewa wannan bincike da ake yi wanda ba a taba yin irinsa ba a kan wani tsohon shugaban kasar an fara shi ne bayan da aka gano wasu muhimman takardun bayanan sirri na fadar gwamnatin Amurkar. An gano su ne daga cikin wasu akwatuna 15 da aka gano a gidan Trump din na Mar-a-Lago a watan Janairu na wannan shekara. A binciken da hukumar ta FBI ta yi kan wadannan takardu na sirri ta bankado wasu takardun sirri 184, wadanda suka hada da wasu 25 da aka ware su a matsayin wadanda suke kunshe da manya-manyan sirri. Wasu daga cikin wadannan takardu da aka hada su da tsoffin jaridu da mujallu na dauke da rubutun shi Trump. Tsohon shugaban na Amurka ya dai musanta aikata wani abu ba daidai ba. Mai magana da yawun fadar gwamnatin Amurkar, Karine Jean-Pierre, ta ce gwamnatin Shugaba Biden ba za ta ce komai ba a game da binciken. Ta ce, ''kamar yadda abin yake da alaka, kuma yadda na fahimci dalilin da ya sa mutane ke da sha’awa a kan lamarin, mun san haka sosai. Amma dangane da duk wasu kalamai a kan duk wani abu da ke da dangantaka da wannan bincike mai zaman kansa, hatta a kan wasu abubuwa na musamman, muna ganin bai dace ba mu yi magana a kan wannan.'' Shi dai Mista Trump ya mayar da kakkausan martani kan batun a shafinsa na intanet , Truth Social, yana cewa ‘yan barandan siyasa ne da ‘yan daba ke jagorantar binciken. Ya ce bai kamata Mai shari’a Bruce Reinhart, wanda ya sa hannu kan takardar izinin gudanar da bincike a gidan nasa ba ya bayar da damar kutse a gidansa ba. Mista Trump ya zargi alkalin da nuna masa kiyayya. Tsohon shugaban ya ce daman shi tuni ya bayar da umarnin ayyana takardun gaba daya a matsayin na sirri. Ana sa ran Ma’aikatar shari’ar za ta ci gaba da gudanar da bincikenta a sirri, yayin da take ci gaba da nazartar takardun tare da sa ran za ta gayyato karin shedu. https://www.bbc.com/hausa/articles/cjkn514mvnlo +health Kwana uku a jere ba a samu sabbin masu cutar korona a Abuja ba Kwana uku kenan a jere ba a samu sabbin masu dauke da cutar korona a Babban Birnin Tarayyar Najeriya ba. Alkaluma na karshe da hukumar yaki da cututtuka a Najeriya, NCDC, ta fitar ranar Litinin sun nuna cewa an samu sabbin mutum 20 da suka kamu da cutar a jihohin Lagos da Edo da Kano da Ogun da kuma Ondo. Gabanin sanarwar ta ranar Litinin, NCDC, ta fitar da sanarwa sau biyu wadanda suka nuna babu sabbin masu dauke da cutar ta korona a Abuja. Sai dai duk da haka, Abuja ce ta biyu a Najeriya cikin jihohin da ke fama da cutar korona inda take da mutum 56, yayin da jihar Lagos, wacce ita ce ta daya, take da mutum 189 da suka kamu da cutar ya zuwa ranar Litinin da maraice. Karin labaran da za ku so ku karanta https://www.bbc.com/hausa/labarai-52275832 +technology 'Yan sandan Kano sun kama mai saka sunan mata a Facebook 'don yaudarar mutane' Rundunar ƴan sandan Najeriya ta damƙe wani matashi a Kano wanda ake zargi da amfani da shafukan bogi a kafafen sada zumunta domin yaudarar jama'a. Mai magana da yawun ƴan sandan Jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da hakan a shafinsa na Facebook inda ya ce sun samu nasarar kama matashin mai suna Musa Lurwanu mai shekara 26 ne bayan tattara bayanan sirri da kuma bin diddiƙin lamarin. Ya bayyana cewa tun da farko sun samu ƙorafe-ƙorafe ne tun a watan Afrilun bana kan yadda wani ya yi ƙaurin suna a kafafen sada zumunta ta hanyar amfani da sunayen maza da mata da hotunansu domin buɗe shafuka a Facebook da Twitter da Whatsapp da dai sauransu domin yaudarar mutane. A cewar ƴan sandan, har sun samu ƙorafi daga wata Zahra Mansur mai shekara 20 wadda ta ce abokanta da ƴan uwa na ta kiranta sakamakon wani na amfani da sunanta da hotonta da bidiyoyi wurin buɗe shafukan Facebook da kuma yaudarar jama'a. Bayan haka ne kwamishinan yan sandan jihar CP Sama'ila Dikko ya bayar da umarnin kamo duk wanda ke aika hakan wanda a ƙarshe aka kamo Lurwanu Maje da ke ƙauyen Sittti a ƙarƙashin Ƙaramar Hukumar Sumaila a Jihar Kano. Yan sandan sun bayyana cewa sun samu wanda ake zargin da waya samfarin Redmi Note 11 Pro wadda ƙudinta kimanin dubu 200 da kuma wasu abubuwa da matashin ya saya ta wannan hanya. Haka kuma an same shi da kuɗi naira dubu saba'in haka kuma an same shi da hotunan tsiraicin wasu daga cikin waɗanda ya yaudara a tare da shi. SP Kiyawa ya bayyana cewa bayan an gudanar da bincike, wanda ake zargin ya amsa cewa ya buɗe wani shafin bogi mai suna Zahra Mansur inda ya rinƙa amfani da hotunanta domin yaudarar mutane, haka kuma ya amsa da cewa ya yaudari mutane da dama inda ya samu hotunan tsiraicinsu da bidiyo inda ya yi musu barazana da su kan cewa su tura masa kuɗi. Wannan lamari dai yana daga cikin matsalolin da ake fama da su a kafafen sada zumunta a Najeriya inda jama'a da dama ke kokawa kan lamari. https://www.bbc.com/hausa/labarai-61858640 +sports Yunkurin Chelsea na fafutukar samun dan wasan Portugal Rafael Leao ya gamu da cikas Aston Villa na nuna sha'awa kan tsohon shugaban kungiyar Tottenham da PSG Mauricio Pochettino a matsayin wanda ka iya maye gurbin Steven Gerrard. (Telegraph - subscription required) Shugaban Chelsea Graham Potter na son sake haduwa da dan wasan gaban Brighton forward Leandro Trossard dan shekara 27 a Stamford Bridge, yayin da tsohon Daraktan kungiyar Dan Ashworth ke son kai ɗan wasan da ke bugawa Belgium wasa zuwa Newcastle. (90 min) Dan wasan tsakiya na Faransa N'Golo Kante bai kai ga kulla yarjejeniya da Chelsea ba sannan akwai rahotannin da ke cewa dan wasan mai shekara 31 na iya tafiya a matsayin wanda ba shi da kungiya a bazara mai zuwa.  (Fabrizio Romano) Joao Felix, 22, da Manchester United ke hange na tsaka mai wuya tsakaninsa da Atletico Madrid , sannan yayin da ƙungiyar ta Spaniya ke jaddada cewa ɗan wasan gaban na Portugal ba na sayarwa bane, wakilinsa Jorge Mendes yana duba wani zabin a 2023. (Here We Go podcast) Simeone shi ma ya ce ka da Atletico ta duba yiwuwar kulla yarjejeniya da dan wasan gaba na Portugal Cristiano Ronaldo daga Manchester United a watan Janairu saboda alakar dan wasan mai shekara 37 da tsohuwar kungiyarsa  Real Madrid. (Tigo Sports, via Metro) Wakilin dan wasan Napoli Victor Osimhen, wanda ake dangantawa da  Manchester United da Arsenal, ya ce dan wasan Najeriyar ba shi da niyyar barin kungiyar ta Serie A. (Goal) Wolves ta tattauna da tsohon shugaban kungiyoyin Lyon da Bayer Leverkusen da Borussia Dortmund Peter Bosz a matsayin wanda za ta iya nadawa a matsayin shugabanta. (Telegraph - subscription required) Yunkurin Chelsea na fafutukar samun dan wasan gaba na Portugal Rafael Leao ya gamu da cikas bayan da daraktan AC Milan Daniele Massaro ya ce za su gana da mahaifin dan wasan mai shekara 23 domin tattaunawa game da sabon kwantiragin. (Express) Akwai yiwuwar dan wasan Brazil Neymar mai shekara 30 zai yi kewar buga wasan da PSG za ta kara da Ajaccio ranar Juma'a a gasar Ligue 1 saboda an tsara a ranar zai bayyana gaban kotu domin kare matakin komawarsa Barcelona daga Santos a 2013.  (Football Transfers) Brentford ta soma tattaunawa da shugaba Thomas Frank kan wata sabuwar yarjejeniya, wata tara kawai bayan da ya sa hannu kan kwantiraginsa na yanzu. (Telegraph - subscription required) https://www.bbc.com/hausa/articles/cz93yyrn0l9o +entertainment Daga Bakin Mai Ita Tare da Malam Tsalha na Dadin Kowa Daga Bakin Mai Ita wani shiri ne na BBC Hausa da ke kawo muku hira da fitattun mutane kan wasu abubuwan da suka shafi rayuwarsu zalla. A wannan kashi na 60, shirin ya tattauna da Ahmad Isma’il Basso, wanda aka fi sani da Malam Tsalha, da ke fitowa a shirin talbijin na Daɗin Kowa. A wannan shiri ya amsa tambayoyin da suka shafi rayuwarsa da rawar da yake takawa a shirin. Ɗaukar bidiyo da tacewa: Abdulsalam Usman Abdulkadir Tsarawa da gabatarwa: Halima Umar Saleh https://www.bbc.com/hausa/media-58095710 +entertainment Daga Bakin Mai Ita tare da Maryam Sulaiman Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon: Daga Bakin Mai Ita wani shiri ne na BBC Hausa da ke kawo muku hira da fitattun mutane kan wasu abubuwan da suka shafi rayuwarsu zalla. A wannan kashi na 97, BBC ta tattauna da Maryam Sulaiman, fitacciyar ƴar wasan fim ɗin Hausa wadda aka fi sani da Maryam CTV, inda ta amsa tambayoyin da suka shafi rayuwarta. https://www.bbc.com/hausa/61412153 +politics Ban ga abin fargaba ba game da Amotekun – Oba Hammed Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon: A baya-bayan nan ne gwamnonin kudu maso yamma na Najeriya suka sanar da kudirinsu na kafa kungiyar tsaro ta Amotekun. Kafa rundunar tsaron ya janyo ce-ce-ku-ce a kasar inda wasu ke ganin za ta iya zama barazana ga Najeriya a nan gaba. A farkon makon nan ne gwamnatin Najeriya ta sanar da haramta kungiyar tsaron. Sai dai Oba Hammed Makama, wanda shi ne Alafin na Kuta ya ce shi bai ga abin tashin hankali ba da kafa wannan rundunar. Ya kara da cewa wannan tsari zai taimaka wa gwamnatin tarayya ne wajen samar da tsaro da ya zame mata wani al'amari mai wuya. https://www.bbc.com/hausa/labarai-51137649 +religion Ku San Malamanku tare da Sheikh Abdullahi Uwais Limanci Ana daukar Sheikh Abdullhi Uwais Limanci a matsayin daya daga manyan malamai a Kano da ba a fiya jin duriyarsu ba. Sheikh Abdullahi ya kasance malamin da manyan malmai a Kano ke zuwa wajensa domin daukar karatu. A tsawon yini, Sheikh Abdullahi Uwais yana shafe kusan sa'a goma yana karantarwa a kowace rana. Malamin bai yi karatun zamani ba, amma dai ya ce ya ringa bibiyar manhajoji da ake amfani da su a makarantu na zamani, har ma yana taimaka wa wadanda suke karatu a irin wadancan makakarantun. Duk da cewa bai yi ilimin zamani ba, Sheikh Abdullahi Uwais ƙwararre ne a ilimin lissafi da tattalin arziki da wasu fannonin na ilimin zamani. Malamin ya kasance madogara da ake tuntuɓa daga jami'o'i kan wasu mas'aloli da suka shafi darusan addinin Musulunci da harshen Larabci. https://www.bbc.com/hausa/labarai-57072806 +technology Rufe layukan waya zai taimaka wa matsalar tsaro – Dr Pantami Latsa wannan alamar lasifika domin kallon bidiyon A cewar Minista Pantami, satar da ake yi ta hanyar intanet ta fi satar da ake yi gaba-da-gaba. https://www.bbc.com/hausa/labarai-49830795 +politics Za a yi zaɓen shugaban Najeriya ranar 25 ga Fabarairun 2023 "Hukumar zaɓe a Najeriya INEC ta sanar da jadawalin babban zaɓe na 2023, inda za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa ranar Asabar 25 ga watan Fabarairun 2023. Shugaban INEC Farfesa Mahmud Yakubu ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a Abuja ranar Asabar. Kazalika, za a gudanar da zaɓen 'yan majalisun tarayya tare da na shugaban ƙasar. Zaɓen gwamnoni da na 'yan majalisun jihohi zai gudana ranar 11 ga watan Maris na 2023 ɗin. A cewarsa, an zaɓi ranar ce saboda a tabbatar an yi aiki da sabuwar dokar zaɓe, wadda ta tanadi cewa wajibi ne a bayyana ranar zaɓen aƙalla kwana 360 kafin kaɗa ƙuri'a. Ya ƙara da cewa hukumar za ta wallafa sauran tanade-tanaden dokar zaɓen ""a lokacin da ya dace""." https://www.bbc.com/hausa/labarai-60539812 +politics 'Karbar na goro a hannun direbobin manyan mota a Najeriya ya zame mana masifa' Wani matuƙin babbar motar dakon kaya a Najeriya ya koka kan yadda cin hanci yake yin mummunan tasiri a kan aikinsa da yake yi na jigila tsakanin arewa da kudancin ƙasar. Malam Bello Haruna, ɗan asalin garin Potiskum a jihar Yobe da ake arewa maso gabashin Najeriya, ya ce a ƙalla yakan kashe naira 170,000 a duk jigila ɗaya da zai yi don kai kaya. Direban babban motar ya faɗa wa BBC hakan ne bayan wallafa neman jin ra’ayin mutane a wani shirin tattara labarai na musamman gabanin zaɓukan 2023. Bello, wanda ya aiko da labarinsa kan yadda batun cin hanci ya yi ƙamari a Najeriya, ya ce ba a madafun ikon da ke can sama kawai ake cin hanci ba, “A ƙasa ma ƙananan jami’ai suna yin son ransu.” Mutumin ya ce baya ga barazanar tsaro da suke cin karo da ita a kan hanyoyin da suke bi ɗin, ya yi zargin cewa jami’an tsaro kuma kan dinga tatike su da karɓar na goro ba tare kuma da sun samar musu wata kariya daga komai ba. Bello dai kan ɗauki kayan gwari ne ko dankalin Hausa ko shanu daga wasu jihohin arewa zuwa kudu a babbar mota, kuma ya ce yakan wuce shingayen bincike masu yawa wanda kowanne sai an tsayar da shi. “Sau da dama idan na tashi daga Sakkwato zuwa Fatakwal wallahi duk checkpoint din da na zo sai sojoji sun karɓi a ƙalla naira 5,000 ko fiye da haka. “Don haka a tafiya ɗaya wata rana sai direba ya kashe sama da N150,000,” ya ce. Bello ya ce yakan bi hanyoyin Fatakwal da Enugu da Aba daga ko dai Kano ko Sakkwato kusan sau uku a duk wata ɗaya. Duk da cewa ba Bello ba ne kawai direban da ya yi wannan ƙorafi, a bayyane yake cewa karbar cin hanci daga jami’ai daga hannun ƴan ƙasa abu ne da aka shaida ya zama ruwan dare kuma ba ya cikin tsarin Najeriya. Bello ya ce baya ga jami’an sojoji da ba sa karɓar abin da ya gaza N5,000, jami’an ƴan sanda ma kan tayar da su su karɓi nasu kason, “sai dai su ko ƴar naira 200 zuwa 500 ka ba su ba sa rainawa,” ya ce. “Wani abin takaicin kuma baya ga jami’ai mukan haɗu da matasa zauna gari banza da ake kira eriya boyis musamman a yankin kudanci. “Su kuma waɗannan inda suke tsayawa gaba kaɗan ne da sojojin kuma su ma dole mu ba su kudi, in ba haka ba su yi wa rayuwarmu barazana. “Abin haushin kuma sojojin da muka bai wa kudin suna kallon abin da ake yi don tazarar babu nisa amma babu wata hoɓɓasa da za su yi don ba mu tsaro,” Bello ya faɗa. Bello ya ce akwai wani lokaci da irin wadannan zauna gari banza suka tare su a kusa da shingen binciken sojoji don karbar na goro sai suka ba su haƙuri cewa sai wani jiƙon, “wallahi sai suka far mana da duka har suka karya yaron motata,” in ji shi. Direban ya kuma koka kan yadda a ƙoƙarin karɓar na goron nan da jami’an ke yi yake jawo cunkoson ababen hawa a kan hanyoyin inda ake sa su ɓata lokaci sosai. “Ga hada go slow da suke yi ga kuma cin zarafin duk wanda bai ba su kudin ba, ba sa karbar duk wani uzuri daga wurin direba in har ka ce su yi haƙuri ba ka da kuɗi to kuwa za ka fuskanci wulaƙanci da tozarci, abin dai ba daɗin ji. “A wasu shingayen za ka ga sojoji uku har zuwa biyar ma a wasu lokutan,” ya ce. Wani zai yi mamakin to ta ina direbobin ke samun kudin da Bello ya ambata cewa suna kashewa a duk tafiya ɗaya? Ya ce dama ana gaya wa ainihin mai mota cewa ga fa yanayin da ake ciki don haka shi zai bayar da waɗannan kuɗaɗe. “Shi ya sa aikin namu duk wahala ta fi samun yawa.” A nazarin da muka yi, mun fahimci cewa yawanci shi mai mota zai fanshe kuɗaɗen da direba ya kashe ɗin ne a jikin masu kayan da za a kai wa kudu ɗin, daga nan su ma dole sai sun ƙara farashin kayayyakin nasu don su fanshe. Kenan hakan zai iya yin tasiri wajen ƙarin hauhawar farashi. Malam Bello ya ce idan har ana son kawar da cin hanci a Najeriya, to kowa sai ya saka hannu an yaƙi abin a tare, “don ba a sama ba ne kawai, lamarin ya munana a harkokinmu na yau da kullum ma,” ya ce.g https://www.bbc.com/hausa/articles/c3g8q1e5veeo +entertainment Rahama Sadau na tara wa almajirai kayan sanyi "Yayin da al'umma a kasashen Afirka ta yamma musamman Najeriya ke fama da matsanancin sanyi da masana yanayi suka ce an yi shekaru ba a fuskanci irinsa ba, wasu fitattun mutane a Najeriyar da kungiyoyin sa kai sun yunkuro domin tallafawa marasa galihu musamman almajirai wadanda ba su da halin kare kansu daga yanayin hunturun da ake ciki. Sanyin bana ya zo da ba-zata kasancewar lamarin ya shafi wuraren da ba su saba fuskantar matsanancin sanyin ba. Fitacciyar tauraruwar Kannywood mai yawan janyo ce-ce ku-ce Rahama Sadau ta kaddamar da wani asusu na tara kayan sanyi da za a rabawa almajirai a wasu jihohin arewacin Najeriya. Jarumar ta wallafa a shafinta na Twitter cewa za a raba kayan da aka tara ne a jihohi kamar Kaduna da Katsina da Jos da Bauchi da Kano da ma wasu da dama. ""Ba za mu iya taimakon kowa ba, amma kowa daga cikinmu zai iya taimakawa wani,"" a cewar Sadau. Ta kara da cewa, ""babu wata mafificiyar hanya da za a taimaki almajiri fiye da samar musu kayan da za su rage musu jin sayi, ko kuma kudi domin tallafa musu."" Ta yi kira ga jama'a kowa ya hada hannu domin taimakawa almajiran, wadanda ta ce bai kamata a yi watsi da su ba. Baya ga tufafi, Rahama Sadau ta ce za ma a iya ba da tallafin kudi. Ba dai wannan ne karon farko da taurarin Kannywood suka fara tallafawa marasa galihu a cikin al'umma ba. Taurari irin su Hadiza Gabon da Masura Gabon da Aisha Tsamiya da wasu taurarin suna tallafawa marasa karfi a cikin al'umma. Masana dai sun ce sanyin na bana na karuwa ne saboda gudun iskar da ke tasowa daga arewa maso gabas mai kunshe da laima ya karu, inda a wasu lokuta har takan kai gudun kilomita 100 cikin sa'a daya. Yanayin sanyin dai ya sanya mutane bayyana ra'ayoyinsu kan halin da suke ciki abin da kuma ya sa kungiyoyi da wasu fitattun mutane suka dauki ragamar kaddamar da shirin karbar gudummawar tallafawa marasa galihu. Wani almajiri ya shaidawa BBC Hausa cewa tun da aka fara sanyi nan sau daya ya yi wanka, yayin da wani kuma ya ce gabobinsu suna rikewa idan sun tashi da safe saboda tsananin sanyi da kuma rashin abin rufa. Wani malamin makarantar allo ya ce almajiransa na kwana ne a rumfar kwano da aka rufe samanta, amma ta gefe da gefe kuma take a bude. Irin wannan yanayi da ake ciki ya sa tuni wasu mutane musamman shahararru a shafukan Sada zumunta suka kaddamar da irin wannan yunkurin na tallafawa almajirai da abin rufa. Nana Asma'u Gwadabe, daya ce daga cikin 'yan sa kan da suke samar wa Almajirai gudunmuwar barguna, kamar yadda ta wallafa a shafinta na Instagram. Nana ta shaidawa BBC sun ba da barguna 500 sannan akwai wasu karin bargunan 1,000 da za su ci gaba da rarraba wa almajiran domin su samu abun rufa a halin da ake ciki na matsanancin sanyi. Shi ma, wani mai amfani da shafukan sada zumunta Abubakar Widi Jalo ta shafinsa na Facebook ya kirkiri maudu'in #KeepTheVulnerableWarm inda mutane suke tururuwar bayar da gudummawarsu. Shirin na #KeepTheVulnerableWarm, a cewar Jalo ya samu gudummawar sama da naira miliyan guda wanda da kudin ne aka sayi barguna da rigunan sanyi domin rarrabawa mabukata a jihohin Kano da Jigawa da Kaduna da Yobe da Maiduguri da Jos da kuma Bauchi. Baya ga wadannan, akwai kuma zaurukan WhatsApp da dama dake tattara irin wadannan gudunmuwa ga almajirai domin rage musu tsananin sanyi a wannan lokaci na hunturu." https://www.bbc.com/hausa/labarai-51018860 +entertainment Daga bakin mai ita tare da Falalu Dorayi: 'Ni mafarauci ne kafin na fara fim' Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon: Daga bakin mai wani shiri na BBC Hausa da ke kawo muku hira da fitattun mutane kan wasu abubuwan da suka shafi rayuwarsu zallah. A wannan kashi na uku, fitaccen mai bayar da umarni a fina-finan Hausa na Najeriya Falalu Dorayi ne, ya amsa tambayoyi da za su sa ku dariya ciki har da batun cewa shi mafarauci ne kafin ya fara fim. Bidiyo: Fatima Othman Wasu na baya da za ku so ku gani https://www.bbc.com/hausa/labarai-50551349 +religion Ku san Malamanku tare da Sheikh Abubakar Kyari Muhammed "Latsa hoton sama ku kalli bidiyo: Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Abubakar Kyari Muhammed, ya ce ya sha wahala matuka kafin ya haddace wata sura a Al-Ƙur'ani. Malamin ya bayyana haka ne a wata hira ta musamman da BBC cikin shirin nan mai taken ""Ku San Malamanku"". Ya ce surar da ta fi ba shi wuya ita ce Suratul An'am, wadda ita ce sura ta shida daga sama a cikin littafi mai tsarki. Sai dai ya ce Allah ya sahale masa ayar da ta fi bai wa mafi yawan mahaddatan Kur'ani mai girma wuya, wato ayar rabon gado ta .... Yusi kumullahu, wadda take a cikin Suratul Nisa'i. Malamin ya ce babu abin da yake faranta masa rai a rayuwa irin ya ga mutum ya musulunta kuma ya yi riko da addinin yadda ya kamata. Abin da kuma ya fi bakanta masa rai shi ne ""yadda mutane ke wasa da ilimi, yadda ake ba da fatawa bisa kuskure ba tare da damuwa kan abin da zai faru ba"". A lokuta da dama malamai kan yi fatawoyin da suke ingiza mutane su je su rika yi wa shugabanni tawaye ko wani abu mai kama da haka. Daga sunansa, mai karatu zai iya hasashen cewa Sheikh Abubakar Kyari Muhammad ya fito ne daga Jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya. An haifi malamin ne a shekarar 1963, inda ya tashi a Borno kuma ya fara karatu a hannun wani malami da ake kira Malam Danjuma, wanda yake koya wa Sheikh harufan Larabci da Hausa. Idan ya koma gida sai iyayensa su koya masa abin da ya koya da harshen Kanuri. Daga baya mahaifinsa ya kai shi wata makarantar allo ta wani malami abokinsa, wanda dan asalin Fataskum ne amma yana zaune a Maiduguri. Ya hadu da manyan malamai irinsu Baba Sayinna da irinsu Malam Babagana, ""kafin daga bisani a ba ni damar komawa makarantar Sheikh Muhammad Abba Aji"". Ya ce sun karanta littatafai da yawa a makarantar irinsu Muwadda Malik da Fiqhussuna da dai sauransu. Malamin ya ce iyayensa ba su sa shi makarantar boko ba amma shi ya kai kansa wajen da ake koyar da bokon, kuma har yanzu yana cin gajiyar karatun. Daga baya ya koma Kano tare da wani uban gidansa a shekarun 1980, ya kuma shiga makarantar S.A.S. da ke Kano inda shi ma ya samu kammala karatunsa a nan. Ya yi jarrabawar wani zauren koyarwa da ake kira daura wadda ake kai mutum Saudiyya idan ya yi nasara, wadda Jami'ar Madina ke shiryawa. ""A lokacin na samu nasarar cin jarrabawar kuma Dr Aminundeen Abubakar ne ya yi alfahari da hakan a 1992,"" in ji shi. Malamin ya ce a shekarar 1994 ya yi aure, kuma Allah ya azurta shi da 'ya mace, amma kuma daga baya Ya amshi kyautarsa. Amma a yanzu yana da mata ɗaya da kuma ɗa guda. Shehin malamin ya ce babban burinsa kamar na kowanne Musulmi ne na fatan a cika lafiya. Sheikh Abubakar Kyari Muhammed ya ce an fi yi masa tambaya a kan sihiri, ko a karatun da yake yi ko kuma ta hanyar tura masa wasika. Mutane suna yawan magana a kan an yi musu sihiri, abin da yake janyo haka kuma shi ne rashin tawakkali. Ya ce: ""Yanzu baki ya yi yawa mutane in suka ga abin da ya yi musu kyau ba sa cewa Tabarakallah sai kaga da sun yi magana sun ɓata abin."" Hakan ya janyo Malamin yake fitar da kananan bidiyo a intanet domin wayar da kan mutane da kuma nuna musu illar kambun baka. Ya ce suna koyar da addu'o'in da mutane za su rika karantawa domin kare kansu da iyalansu daga irin wadannan matsaloli." https://www.bbc.com/hausa/shirye-shirye-na-musamman-59170446 +sports An kori koci biyu a Premier League a cikin watan Oktoba Ranar Alhamis, Aston Villa ta kori Steven Gerrard daga jan ragamar kungiyar, bayan da Fulham ta doke ta 3-0 a wasan mako na 12 a gasar Premier League. Gerrard ya bar kungiyar tana ta 17 a kasan teburi da maki tara, bayan buga wasa 11 a kakar nan. Aston Villa ta ci wasa biyu da canjaras uku aka doke ta karawa shida, ta kuma ci kwallo bakwai aka zura mata 16 a raga a bana. Tsohon dan wasan Liverpool an nada shi kociyan Aston Villa ranar 11 ga watan Nuwambar 2021, wanda ya maye gurbin Dean Smith. Kawo yanzu Gerrard ya ja ragamar Villa wasa 38 da cin 12 da canjaras takwas aka doke shi fafatawa 18. Haka kuma kungiyar ta Villa Park ta ci kwallo 45 aka zura mata 50 a raga karkashin jagorancin Gerrard. Ranar Lahadi 23 ga watan Oktoba, Aston Villa za ta karbi bakuncin Brentford a ci gaba da wasannin Premier League. Wani kociyan da aka sallama a cikin watan Oktoba a Premier League shi ne Bruno Large daga Wolverhampton. Kociyoyin da ke jan ragamar kungiyoyin Premier League 2022/23 Kungiya . Kociya Ranar dauka Wanda ya gada Kungiyoyin da ba su da koci kawo yanzu Aston Villa        Wadda ta sallami Steven Gerrard Bournemouth  Wadda ta raba gari da Scott Parker Wolverhampton Bwadda ta kori runo Lage https://www.bbc.com/hausa/articles/c10me84j3jzo +business An jefe masu hakar ma'adanai 9 a Afirka ta Kudu 'Yan sanda a Afirka ta Kudu na neman wadanda suka jefe wasu mutane har lahira a Johannesburg ruwa a jallo. Wadanda aka kashe din na hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba ne, kuma an yi ta jifansu ne har suka mutu. An tsinci gawar mamatan 9 'yan asalin kasar Lesotho ne a wani titi, sannan aka garzaya azibiti da dayansu da ya samu munanan raunuka. Dubban masu hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba ne ke aiki a kasar, inda ake yawan samun rikici tsakanin bagarori masu gaba da juna. Buhari ya kafa kwamitin sulhu kan hana 'yan Najeriya bizar Amurka Yadda 'yan bindigar arewacin Najeriya ke samun makamai Birtaniya ta sallami shugabar taron sauyin yanayi na MDD Kisan na zuwa ne kimanin sa'a 24 bayan wani samamae da 'yan sanda suka kai wurin hakar ma'adanan. Kwamishinan 'yan sandan lardin Gauteng, Elias Mawela ya yi tir da kisan a matsayin dabbanci sannan ya ce za su yi duk abin da ya dace domin kawo aminci ga mutanen yankin. Mawela ya ce 'yan sanda ba za su runtsa ba sai sun kamo wadanda suka aikata kisan kuma nan ba da jimawa ba za su shiga hannan. Tuni aka bukaci karin jami'ai daga Johannesburg domin farautar wadanda suka yi kisana. Afirka ta Kudu na daga cikin kasashe mafiya hadari a duniya. Gwamantin kasar ta ce a duk minti daya an kashe mutum 58 a bara. https://www.bbc.com/hausa/51343191 +politics INEC ta soma raba katin zaɓe na dindindin Najeriya "Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya ta fara raba katin zaɓe na din-din-din ga wasu daga cikin masu zaɓe a ƙasar.\n\nHukumar ta ce waɗanda za a bai wa rijistar su ne mutanen da suka ba da sunayensu daga farkon 2022, zuwa lokacin da aka rufe aikin a watan Yuli.\n\nZainab Aminu, jami'ar hukumar ta sanar da BBC cewa ""Kamar yadda aka sani, an fara wannan aikin rajistar ne a watan Yulin 2021, aka yi zuwa watan Disamba - zango na daya da na biyu ke nan - kuma an samar da katunansu kuma tuni aka fara raba su."" Ta ce za a raba katunan ne daga ranar 12 ga watan Disambar 2022 zuwa 22 ga watan Janairun 2023, kuma za a yi rabon ne a dukkan kananan hukumomin Najeriya 774. ""Daga ranar 6 ga watan Janairun shekarar 2023 zuwa 15 ga watan, hukumar zabe za ta fadada raba katunan zaben zuwa dukkan gundumomi 8,809 da ke fadin kasar nan."" Daga ranar 15 zuwa 22 ga watan na Janairu, za a sake komawa ofisoshin hukumar zaben da ke jihohi domin ci gaba da raba katunan. Wadanda suka cancanci karbar katunan zabe Zainab Aminu ta kuma bayyana irin shaidar da masu neman karbar katunan zabensu za su gabatar yayin da suka hallara a ofisoshin hukumar. ""Ana bukatar mutum ya tafi da wata takardar zabe ta wucin gadi da aka ba duk wanda yayi rajista. Idan babu wannan takardar wucin gadin, ana iya amfani da lambar da ke jikin kowane katin zabe mai suna Voter Identification Number."" Sai dai ta ce ko babu lambar, mutum na iya zuwa da kansa domin jami'an hukumar su nemo katin nasa. ""E, wannan haka yake, amma mun fi son a taho da takardar wucin gadin ko lambar ta VIN saboda saukin dubawa,"" in ji Zainab Aminu." https://www.bbc.com/hausa/articles/cgrvpevvrmno +sports An dage gasar kofin Afirka da aka tsara yi a 2023 a Ivory Coast Shugaban hukumar kwallon kafar Afirka, Patrice Motsepe ya sanar da dage gasar cin kofin nahiyar Afirka daga 2023 an mayar 2024 a Ivory Coast. Tun farko an tsara gudanar da gasar tsakanin Yuni zuwa Yulin 2023, sai dai lokacin damuna ne da ake mamakon ruwa a kasar. Shugaban ya fada a babban birnin Rabat a Morocco cewar, ‘’Ba za muyi kasada ba’‘ Da yake za a buga gasar kofin duniya a Qatar a watan Nuwamba zuwa Disambar shekarar nan, mun yanke shawarar kai wasan zuwa 2024 maimakon dawo da karawar kusa‘‘. Hakan na nufin cewar a karo biyu a jere za a buga gasar cin kofin nahiyar Afirka tsakanin Janairu zuwa Fabrairu, kamar yadda aka yi a Kamaru a shekarar nan. A shekarar 2017, Caf ta sanar da cewar za ta mayar da buga wasannin tsakanin Yuni zuwa Yuli, maimakon Janairu zuwa Fabrairu, don kawo karshen takaddama da kungiyoyin Turai. Kungiyoyin Turai kan hana ‘yan wasan Afirka zuwa buga gasar nahiyar, domin ci gaba da fafatawa a wasanninsu, wanda a lokacin gasa ta dauki dumi. A lokacin shugabancin, Issa Hayatou bai saurari kungiyoyin Turai kan matsin lamba da suke yi na sauya wasannin kofin Afirka da ake yi tsakanin Janairu zuwa Fabrairu ba. https://www.bbc.com/hausa/articles/cm5vxm31mglo +religion Yadda ake ƙayyade sadaki mafi ƙaranci da nisabin Zakkah da haddin sata a Musulunci "Addinin musulunci ya fitar da hanyoyi na ƙayyade nisabin Zakkah da lissafin diyya da mafi ƙarancin sadaki da haddin sata. Kwamitin Fadar Sarkin Musulmin Najeriya na fitar da bayani kan nisabin Zakkah da mafi ƙarancin sadaki da haddin sata da kuma diyya daga lokaci zuwa lokaci. Daga ranar 19 ga watan Maris na 2021 nisabin Zakkah ya kai N1,810,160, kuɗin sadaki mafi ƙanƙanta da haddin sata ya kai N22,627. Lissafin diyya kuma a yanzu ya kai N90,508,000, kamar yadda Kwamitin Fadar Sarkin Musulmin Najeriya ya wallafa a shafinsa na Tuwita. Domin sanin yadda ake ƙayyade nisabi da kuma lissafin diyya da mafi ƙarancin sadaki da haddin sata, BBC ta tattauna da Imam Murtadha Gusau, babban limamin masallacin Juma'a na Nagazi-Uvete na Alhaji Abdur-Rahman a Okene. Malamin ya ce ana kiyasi ne da darajar zinari - farashin da ake sayar da cikakken nauyin zinari. Wato kamar naira dubu 21 da ake sayar da giram (4.25). Nisabin zakkah na kuɗi shi ne zinari 20 - idan a naira ne kuɗin Najeriya, za a yi lissafin nawa naira za ta sayi zinari 20. Zinari 1,000 ne lissafin diyya na kashe ran musulmi. Idan misali a kuɗin Najeriya ne za a yi lissafin nawa naira za ta sayi zinari 1,000, abin da ya bayar shi ne kuɗin diyya. Ana ƙayyade mafi ƙarancin sadaki da haddin sata daga rubu'i - wato kashi ɗaya bisa huɗu na zinari. Wato idan an raba zinari kashi hudu nawa misali naira za ta saye shi - shi ne nisabin sadaki da haddin sata da za a yanke hannun ɓarawo idan an bi ka'idoji da shari'a ta gindaya cewa ba a cikin yunwa da talauci ya shiga ya yi sata ba, sai a yanke masa hannu. Ta waɗannan hanyoyin da aka bayyana a sama ake fitar da ƙiyasin sadaki mafi kankanta da diyyar rai da kuma nisabin zakkah. Amma lissafin yana hawa kuma yana sauka ta la'akari da dajarar zinari da kuma darajar kudi. Misali a watan Janairu a Najeriya mafi ƙarancin sadaki ya kai N23,946, inda kuma yanzu ya dawo kan N22,627 a watan Maris. Kuma kamar yadda ake amfani da naira haka masu amfani da dala da yuro da fan za su yi amfani wajen yin lissafin nisabin zakkah da mafi ƙarancin sadaki da haddin sata da kuma kudin diyyar ran musulmi. Imam Murtadha ya ce idan an bi ra'ayin malaman hadisi ko nawa aka biya na sadaki ba laifi ba ne. ""Malaman fikihu ne suka yanke cewa dole sadaki sai ya kai adadin kashi ɗaya bisa huɗu na zinari sannan aure ya ƙullu."" ""Amma ga malaman hadisi ana iya ƙulla aure idan sadakin bai kai adadin da aka ƙayyade ba domin suna dogaro da wani hadisin daga Manzon Allah SAW inda Annabi ya yi sadaki da abin da ba kudi ba,"" in ji malamin. Ya ce lokacin da annabi ya aurar da wata mata ga wanda surorin Al Kur'ani kawai ya haddace ya nuna ko ba kuɗi ana yin sadaki. Imam Murtadha ya ce: ""Ana sadaki da kuɗi da kuma abin da ba kuɗi ba."" Kuma malamin ya ƙara da cewa a shari'a ko nawa nawa mutum ya biya ba laifi ba ne. Ya danganta da yarda da amincewaar juna tsakanin mace da namiji. ""Duk abin da mace ta amince yana iya zama sadaki - tana iya cewa ma ta yafe sadakin"" ""Idan mutum yana da halin biyan miliyan 10 a matsayin sadaki idan ya biya ba laifi ba ne."" Amma malamin ya ce annabi ya kwaɗaita da yin rangame a wurin aure - annabi ya faɗa cewa duk auren da ya fi sauki shi zai fi albarka - hakan ya nuna ana son a sawwaka wurin aure. ""Amma ko nawa aka biya na sadaki, aure ya yi.""" https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-56427047 +technology Abubuwan da mutane suka fi tambayar Google a 2021 "Shafin matambayi-ba-ya-ɓata ya bayyana jerin abubuwan da aka fi yayi, abin da ke alamta irin yadda shekarar 2021 ta kasance ga al'ummar duniya. Katafaren kamfanin fasahar shi ne mafi shahara a shafukan da ke bayar da damar neman amsar kowace irin tambaya kuma duk shekara yakan fitar da abubuwan da aka fi tambaya da maudu'ai. Yayin da annobar korona rata sassan duniya, mun shiga 2021 tare da maudu'in 'doomscrolling', wata kalmar Ingilishi da ke nufin ""ganin labarai marasa daɗin ji"". Maudu'in na bayyana yadda masu amfani da shafukan zumunta ci gaba da latsa wayoyinsu da zimmar ganin ƙarin labarai marasa daɗi. Google ya ce an tambayi 'doomscrolling' fiye da koyaushe a faɗin duniya, inda abin ya fi yawa a watan Janairu. Lokaci ne na rashin tabbas a faɗin duniya da zaƙuwa. An kulle iyakoki, an hana jirage tashi sannan an saka dokar kulle. Mutane sun dinga hawa intanet don sanin me ke faruwa game da annobar ta korona kuma da yawansu sun nemi abin da ke damun su ne - ""doomscrolling"". A 2021, an duba kalmar 'mental health' wato 'lalurar ƙaƙwalwa' fiye da kowane lokaci biyo bayan shafe shekara guda cikin kaɗaici da kuma alhinin rashin 'yan uwansu da korona ta kashe. Mutanen duniya sun yi ta tambayar 'yadda za a yi jinyar lalurar ƙwaƙwalwa' da kuma 'ta yaya za a warke?' fiye da kowane lokaci a baya. Wani ƙarin dalili da ke nuna lalurar ƙwaƙwalwa ta dame mu a 2021, maudu'ai kamar 'body positivity' (lafiyar jiki) da 'affirmations' (tunani mai kyau) sun fi shahara sama da kowane lokaci. Ba maganar lafiyar jiki kawai ake ba, lafiyar duniyarmu ma na damun mu. Daga Guguwar Ida zuwa yunwa da kuma gobarar daji - duniya ta shaida tasiirin sauyin yanayi. A cewar bayanan Google, mun duba hanyoyi mafiya tsafta na rayuwa fiye da kowane lokaci. 'Yaya za a alkinta' da 'rayawa' na cikin abubuwan da muka fi nema a shafin. Mazauna birane da tsaunuka sun nemi bayanai kan 'tasirin sauyin yanayi' fiye da koyaushe. Abin da bai ba da mamaki ba shi ne, ƙasar Fiji wadda sauyin yanayi ya fi yi wa illa, ita ce aka fi yawan nema. Mutane sun firgice game da ayyukansu da kuma tattalin arzikinsu, akasari saboda rashin tabbas da annobar korona ta haddasa. Sanboda haka yadda za ku zama ubangidan kanku da kanku ya zama abin yayi. A 2021, duniya ta buɗe sabbin hanyoyin sana'a, inda neman ""ta yaya za a fara sabuwar sana'a"" da kuma ""ta yaya za a samu aikin yi"" ya zama abin yayi. A Amurka kaɗai, mutum fiye da miliyan huɗu ne suka rasa ayyukansu a watan Oktoba, a cewar wasu bayanai daga Sashen Kwadago. Wasu mutanen sun ɗauki lokacin annobar a matsayin na yin karatun ta-nutsu ta yadda suka sauya sana'ar da ta fi ta da. Wani maudu'in da ke da alaƙ da samun kuɗi shi ne NFT. NFT - non-fungible tokens - hotuna ne ko kuma zane-zane da ake iya mallakarsu ta hanyar yi musu shaidar mallaka ta yadda za a iya saye ko sayar da su. NFT ya kwana biyu, amma ba mu fara mayar da hankali kansa ba har sai da aka sayar da hoton bayanin farko da mamallakin Twitter Jack Dosey ya wallafa kan dala miliyan 2.9. Da yake muna so mu gano sabbin damarmaki a intanet, maudu'in ""ta yaya za a ƙirƙira"" ya zama abin yayi shi ma. A watan Maris ne Yarima Harry na Birtaniya da matarsa Meghan Markle suka yi hirarsu ta farko da mai gabatarwa 'yar Amurka Oprah Winfrey bayan sun sauka daga muƙamansu na sarauta. Wannan hirar ce ta zama hirar da aka fi yayi a shafin Google Trends a duniya baki ɗaya. Ma'auratan sun bayyana yadda alaƙa ta lalace tsakaninsu da gidan Sarautar Birtaniya, suna masu zargin cewa an yi gulmar launin fatar ɗansu mai suna Archi. Sai dai ba ita ce kaɗai aka yi yayi ba a ɓangaren fim na 2021. Yayin da mafi yawanmu ke kulle a cikin gidaje, an samu isassehn lokacin kallon fina-finai a talabijin. Squid Game, fim mai dogon zango da aka shirya a Koriya ta Kudu, shi ne fim ɗin da aka fi neman bayanai a kansa a duniya baki ɗaya. Labari ne a kan wani rukunin mutane da ya zama dole su tsira daga wasu wasanni mai hatsarin gaske kafin su lashe kyautuka masu gwaɓi. Fim ɗin ya ƙayatar da duniya, har ma ya zama wanda aka fi kallo a tarihin kamfanin Netflix." https://www.bbc.com/hausa/labarai-59664927 +sports Salah zai tsawaita kwantiragin zamansa a Liverpool in ji ministan wasannin Masar Mohammed Salah na shirin saka hannu kan tsawaita yarjejeniyarsa a Liverpool in ji ministan wasannin Masar, Ashraf Sobhi. Sobhi ya ce ya bai wa Salah mai shekara 29 shawarar ya bar Anfield, amma dan kwallon Masar din ya ce yana shirin tsawaita zamansa a Liverpool zuwa karshen kakar 2023. ''Na bashi shawarar ya koma wata kungiyar domin fito da kanssa, amma ya sanar da ni cewar zai sa hannu kan ci gaba da zama a Anfield'', in ji Sobhi. Kocin Liverpool, Jurgen Klopp ya ce yana ''murna'' kan ci gaban da ake samu kan batun cimma yarjejeniya da Salah. ''Dukkan bangarorin biyu na tattaunawa da juna, kuma abinda muke bukata kenan,'' kamar yadda Klopp ya fada. Salah ya fada a cikin watan Janairu cewar yana son ya ci gaba da taka leda a Liverpool, amma makomarsa na hannun kungiyar. ''Sun san abin da nake bukata, ban nemi kudi masu yawa ba, kamar yadda Salah ya sanar da mujallar GQ. Wasu rahotanni a baya sun ce Salah na daf da amincewa da kunshin yarjejeniyar fam 400,000 a duk mako. Sobhi ya ce ya tattauna da Salah, bayan da Masar ta barar da fenaritin da ta kasa samun gurbin shiga gasar kofin duniya a gidan Senegal. ''Na ce masa ya mance da abin da ya faru, ya kuma mayar da hankalinsa kan abin da ya kamata ya yi. Salah ya ci kwallo 153 a wasa 240 da ya yi wa Liverpool, tun bayan da ya koma Anfield daga Roma kan fam miliyan 34 a 2017. Daga baya ya tsawaita yarjejeniyarsa a kungiyar kaka daya tsakani, bayan da ya ci kwallo 44 a kakar da ya fara buga tamaula a kungiyar Anfield. Liverpool ta lashe Champions League a 2019 da kuma Premier League a 2020. https://www.bbc.com/hausa/wasanni-60990237 +politics Abu uku da zan mayar da hankali a kai idan na zama gwamnan Kaduna - Isa Ashiru "Dan takarar gwamna a Jam'iyyar PDP a Jihar Kaduna, Hon Isa Muhammad Ashiru wanda ke takara a karo na uku domin neman zama gwamnan jihar ya ce tsaro zai fi bai wa muhimmanci. Honorabul Isa Muhammad Ashiru yana takarar neman zama gwamnan Jihar Kaduna a Jam'iyyar PDP a karo na uku. Ya ce tsabar son ganin ya kawo sauyi a jihar ne ya sa ya nace sai ya zama gwamna. Ya ce: ""Zan mayar da hankali kan abubuwa uku da suka hada da tsaro da inganta sha'anin noma da kuma samar da ayyukan yi ga matasa."" Dangane da wasu sarakunan gargajiya da gwamnatin APC ta rushe, Isa Ashiru ya ce dole ne a koma musu ""idan dai har ana son samun ingantaccen tsaro.""" https://www.bbc.com/hausa/articles/cn4q6pg718ro +health Rigar da ke taimaka wa masu larurar shanyewar jiki su yi tafiya Mutanen da ke fama da larurorin da ke da alaka da kwakwalwa irin su shanyewar jiki sukan sha wahala wajen yin motsi. Sai dai yanzu an kirkiro wata sabuwar riga da ke taimaka musu wajen rage jin radadi da kuma samun damar yin tafiya.\n\nRigar mai suna Exopulse Mollii tana aike wa da wasu sakonnin lantarki da suke tausasa jijiyoyi. Hakan babban abin karfafa gwiwa ne ga mutanen da ke fama da wannan larura. https://www.bbc.com/hausa/articles/c88kx9j3n7xo +politics Bayanai kan ƴan takarar gwamnan jihar Ekiti na 2022 A ranar Asabar 18 ga watan Yuni ne za a yi zaɓen gwamnan jihar Ekiti na 2022. Duk wanda ya yi nasara a zaɓen zai maye gurbin gwamna mai barin gado Kayode Fayemi na jam'iyyar APC, wanda a cikin shekarar nan wa'adin mulkinsa zai ƙare. Tun a watan Janairu ne jam'iyyu suka gudanar da zaɓukan fitar da gwanayensu, kuma sunayen waɗanda hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasar INEC ta tantance ne kawai za su kasance a kan ƙuri'ar zaɓen. Ga dai bayanan wasu ƴan takarar da INEC ɗin ta tantance. An zaɓe su ne bisa waɗanda BBC ta iya samun su ko bayanansu a intanet, ba don wani ya fi wani ba. https://www.bbc.com/hausa/labarai-61609807 +health An canja wa coronavirus suna zuwa Covid-19 "Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce daga yanzu sunan cutar Coronavirus a hukumance shi ne Covid-19. Shugaban hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus ya shaida wa manema labarai a birnin Geneva cewa, ""Yanzu mun sauya wa cutar suna zuwa Covid-19"". Sauyin sunan ya zo ne bayan karuwar mutuwar wadanda suka kamu da cutar da aka samu wanda ya haura 1000, yayin da wasu dubban mutane kuma suka kamu da ita. Masu bincike sun bukaci a samar da wani suna ga cutar a hukumance domin a magance rudani da kyamar da ake yi wa masu cutar. Shugaban hukumar WHO ya ce, ""Dole muka samo sunan da ba shi da alaka da sunan wani waje ko wata dabba ko wani mutum ko kuma wata kungiya ta mutane, kuma suna ne da bashi da wuyar fada ba shi kuma da alaka da sunan wata cuta"". Ya ce ""Samun sunan na da matukar muhimmanci domin a kare amfani da sunan da zai iya janyo wata matsala"". An samar da sabon sunan cutar ne daga farkon sunan cutar wato haruffan ""Co"" daga ""corona"", sai ""vi"" daga""virus"" da kuma ""d"" daga disease"", sannan kuma daga karshe aka sanya shekarar da cutar ta fara bulla wato 2019. A yanzu haka akwai mutum dubu 42 da dari 200 da aka tabbatar sun kamu da cutar a sassan China daban-daban. A ranar Litinin 10 ga watan Fabrairun 2020, mutum 103 suka mutu a rana guda a lardin Hubei, yayin da adadin wadanda suka mutu gaba daya kuma ya kai 1,016. To amma kuma an samu raguwar masu kamuwa da ita a kasar baki daya inda yanzu ya dawo zuwa kaso 20 cikin 100. Sakataren lafiya a yankin Hubei, da kuma shugaban yankin, na daga cikin wadanda suka rasa aikinsu saboda zargin sakaci. A kwanakin baya-bayan nan, mahukuntan China na kara fuskantar suka saboda yadda suke tunkarar annobar. Mutuwar wani likita wanda tun a farko ya yi gargadi a game da cutar, ya kara janyo suka ga mahukuntan kasar abin da har ya janyo fushin al'ummar kasar ta China. Yanzu haka dai masana kimiyya daga sassan duniya daban-daban na wani taro a birnin Geneva domin tattauna yadda za a magance yaduwar cutar. Dokta Ghebreyesus, ya ce har yanzu akwai damar da za a magance wannan cuta idan har aka samu dama da kuma kudi da za a ware domin magance cutar. Daga nan ya yaba a kan irin matakan da China ta dauka, abin da ya ce ya rage yawan yaduwarta zuwa wasu kasashen duniya. Amurka ta ce halin da tattalin arzikin China ya shiga zai iya shafar sauran kasashen duniya." https://www.bbc.com/hausa/labarai-51467878 +entertainment Me ya sa muke ƙyaƙyata dariya? "Tattaunawata da Sophie Scott ta kusan zuwa ƙarshe loakcin da ta matso gaba daga kan kujerarta tana nuna min hoton wani mutum tsira-tsirara yana tsindimawa cikin kogin wanka na alfarma. Bayan ya shafe kamar minti ɗaya yana mommotsa hannayensa, sai ya tsunduma - amma sai ya faɗa kan wani ƙwallon ƙanƙara. Ruwan bai motsa ba amma abokansa ba su yi wata-wata ba wajen ɓarkewa da dariya. ""Suna ganin babu jini sai suka ɓarke da dariya,"" a cewar Sophie. ""Suna ta ɓaɓɓaka dariya da shewa; sun kasa dainawa."" Me ya sa muke fuskantar irin wannan yanayin na dariya - ko a lokacin da wasu ke fama da raɗaɗi? Kuma me ya sa muka kasa dainawa? Yayin da ƙwararriya kan ƙwaƙalwar ɗn Adam Sophie ke ƙoƙarin amsa waɗannan tambayoyi a shekaru da suka gabata - ta yi jawabi a Vancouver a makon da ya gabata kan dalilin da ya sa dariya ke da muhimmanci da kuma yadda aka kasa fahimtar ta. Abokan aikin Sophie ba su goyi bayan aikinta ba a kodayaushe. Tana so ta yi magana kan wani rubutu da ta gani a cikin takardunta. ""Wannan tarin takardun shara ce kawai (saboda yanayin takardun) kuma za a zubar da su ne idan ba a kwashe su ba,"" kamar yadda aka rubuta a takardun. ""Wannan kimiyya ce?"" Yanzu kuma Sophie na sanye da wata t-shat ɗauke da rubutun wata tambaya da ke cewa ko kun shirya zuwa wani wasan barkwanci da take son shiryawa da dare. ""Za ku iya samun ganin jinsina, da shekaruna, da arzikina, da asalin inda na fito, da yanayin mu'amalata, da lafiyata, da kuma ma abubuwan da suka shafi hira,"" a cewarta. Ɗaya daga cikin ayyukanta shi ne ta nazarci yadda mai sana'ar kwaikwayon mutane Duncan Wisbey ya saba da kwaikwayon jawaban mutane. Ta gano cewa ƙwaƙwalwa na haska daidai yadda jiki ko motsi da jikinsa yayin da yake ƙoƙarin aikata duk abin da wanda yake kwaikwaya yake yi. Aikin gano masu kwaikwayo ya taimaka mata wajen gano yadda mutane ke da yaruka da karin harshe daban-daban. Sai dai wani bincike da aka yi ne a Namibia ya sa Sophie ta gano cewa dariya ɗaya ce daga cikin mafiya muhimmanci kan yadda ƙasusuwanmu ke motsawa. Bincike ya nuna za mu iya gane hanyoyin ji da ɗan Adam ke amfani da su - tsoro, fushi, mamaki, takaici, ɓacin rai - ta hanyar yanayin fuskar mutum. Sophie na son ta gano ko za mu gano wasu bayanai daga muryar mutum. Saboda haka sai ta tambayi 'yan Namibia da kuma Turawa mazauna ƙasar da su saurari maganganun juna kuma su bai wa abin da suka ji maki - ciki har da hanyoyin ji da aka amince da su. Dariya ce abin da ɓangarorin biyu suka fi ganewa da sauri. ""Kusan nan take ake iya bambance dariyar da sauran abubuwa masu amfani,"" a cewarta. Yayin da take ƙara gano abubuwa tana kuma ƙara yin mamakin abin. Don da nan ta gano cewa akasarind dariyard a ake yi ba tad a aaƙa da barkwanci. ""Mutane na yawan tunanin cewa suna yi wa barkwancind a sauran mutane suka yi dariya ne, amma mutumnin da ya fi yi wa mutane dariya shi ne ya fi yawan yin magana,"" a cewarta. A madadin haka, tana kallon dariya a matsayin ""yanayi na al'umma"" da ke taimaka mana yin mu'amala da juna, game da ko wani abu na dariya ne ko ba akasin haka. ""Idan kuka yi dariya tare da mutane kuna nuna musu cewa kuna son su, kun yarda da su, ko kuma kuna cikin rukuni ɗaya tare da su,"" in ji ta. ""Dariya ce ƙololuwar sirrin alaƙa tsakanin al'umma."" Wannan na iya bayyana yadda ma'aurata ke yi wa juna dariya - yayin da su kuma masu kallonsu ba sa jin dariyar. ""Za ku ji wani na cewa 'yana da barkwanci kuma gaskiya dalilin da ya sa yake burgeni kenan'. ABin da kake nuifi shi ne 'yana burge ni, na san shi kuma ina nuna masa cewa yana burge nin ta hanyar yin dariya duk lokacin da muke tareda shi'"". Tabbas dariya ka iya zama abu na farko da ke kyautata alaƙa, in ji ta tana mai ambato wani bincike. Ta ce ma'auratan da ke ɓaɓɓaka dariya da juna na da damar magance wata damuwa bayan sun shiga matsanancin halin aiki. Yanzu Sophie na da sha'awar gano bambanci tsakanin 'yar dariya da muke yi yayin hira da kuma wadda ke suɓucewa mu ƙyaƙyata, har ma takan ɓata shirin talabijin da rediyo. Misali, ta ce 'yar dariyar da ake yi da gangan an fi yinta ne daga hanci, yayin da ita kuma wadda ke suɓucewa mu ƙyaƙyata ba daga hanci take fitowa ba. Wani hoton ƙwaƙalwa da ta nazarta ya nuna yadda ƙwaƙalwa ke mayar da martani wajen yin kowace irin dariya. Dukkan hotunan sun nazarci yadda ake kwaikwayon aikin wani mutum. Yankunan ƙwaƙalwa kan motsa idan na gan ka kana buga ƙwallo ta yadda zan ji ko ni ne zan buga ta da kaina - kuma irin yanayin ne ke sa dariya ta suɓuce mu yi ta ƙyaƙayatawa. Za ku iya tunanin cewa bambance dariya ta gaske da ta gangan abu ne mai sauƙi. Sai dai Sophie na ganin ƙwarewa ce da ke samuwa a ɗabi'unmu da ba ta samuwa har sai mun kai shekara 30 da wani abu da haihuwa. Wannan dalilin ne ya sa ta kafa wani wurin bincike a Landan, inda za ta dinga neman baƙi su dinga nazartar ingancin dariyar mutane da kuma kukansu. Ta ƙaa da cewa kuka ya fi zama wata hanya da yara ke amfani da ita wajen aika saƙo, yayin da su kuma manya suka fi amfani da dariya. Duk da cewa ba mu fiya son yadda mutane ke yin dariyar boge ba, Sophie na ganin hakan ya fi bayyana abubuwa game da mu fiye da a kansu da kuma yadda muke ji game da salon rayuwarsu, ba wai wani abin ƙi ne game da rayuwar tasu ba. Sai dai kuma, ta ce masu wasan barkwanci sun fi samun sauƙi wajen yin wasanni a bainar ɗaruruwan jama'a saboda yanayin da ake shiga na nufin dariya ta fi kama nan da nan idan akwai mutane da yawa a wurin. Zuwa yanzu, ta yi ƙoƙarin samar da na'urar bin diddigi ga masu kallon wasannin barƙwanci don bin sawun ɓarkewar dariya - masu kallon ba sa son yin hakan. Amma tana fatan ci gaba da aiki da manyan 'yan wasan barkwanci kamar Rob Delaney, wanda ka iya yin hakan. Sashen BBC Future ne ya shirya shi." https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-61241422 +religion Indonesia ta amince da dokar tsaurara hukunci kan masu zina da aure "Ƴan majalisa a Indonesia sun amince da sabuwar dokar da ta haramta zina da aure, inda yanzu hakan ya zamo babban laifi, da kuma taƙaita 'yancin siyasa. A ƙarƙashin sabuwar dokar laifi ne yin zina da aure, inda za a iya yanke wa mutum hukuncin sama da shekara, kuma an haramta zaman daduro kafin aure. Bijiro da wannan doka ya biyo bayan karuwar kishin addini a ƙasar da Musulunci ya fi rinjaye. Masu suka na ganin dokar a matsayin ""babban bala'i"" ga ƴancin bil adama, kuma babbar barazana ga masu zuwa yawon bude ido da zuba jari a ƙasar. Kungiyoyi da dama galibi na matasa sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da wannan doka a wajen ginin majalisa da ke Jakarta a wannan makon. Ana tunanin za su kalubalanci sabuwar dokar a kotu. Wannan doka ta shafi 'yan kasa da baƙi da ke zuwa ƙasar don zama ko hutu a wuraren shaƙatawa irinsu Bali. A karkashin dokar duk mutanen da aka kama suna zina da aure za a yanke musu hukunci ɗaurin shekara guda. An kuma haramta musu zama tare – laifin da idan aka samu mutum da aikatawa zai sha ɗauri na kusan wata shida. Sannan zina ga ma'aurata zai kasance babban laifin da za a fuskanci ɗauri. Magoya bayan dokar a majalisa sun ce ana aiwatar da sauye-sauye domin duba korafin masu suka – kafin a gabatar da mutum dole sai idan korafin da aka shigar daga wajen yaransa ne, iyaye ko kuma mata ko mijin waɗanda ake zargi. Ajeng, wata mata ce Musulma da ke rayuwa a yankin Depok da ke birnin Java a yamacin kasar, ta ce a yanzu tana fuskantar barazanar zama da iyayenta tsawon shekara biyar. ""Ta ce da wannan sabuwar dokar, dukkaninmu na iya shan dauri idan ɗaya daga cikin iyayenta suka shigar da kara ga 'yan sanda, kamar yada ta shaidawa BBC. ""To ya kenan idan wani daga cikin 'yan uwana suna da matsala da ni suka kuma yanke hukuncin kai ni gidan yari? ""Ina ganin zama tare ko jima'i kafin aure ba laifi ba ne. A addinina, hakan babban laifi ne. Amma ba na ganin dacewar dokar, domin aiki za ta yi a kan wani addini guda."" Ta ce ta shiga zanga-zangar gama gari a 2019 lokaci da aka soma bijiro da dokar. Na rataɓa hannu a takardar adawa da ""bai wa mutane damar ruguma, Na gudanar da gangami."" Sai dai a ranar Talata, majalisa ta amince da sabuwar dokar da bayananta ke ƙunshe cikin maƙala mai shafi sama da 600. Kungiyoyin kare hakki sun ce sabuwar dokar zai yi tasiri kai-tsaye ne ga mata da masu maɗigo da luwaɗi da kabilu tsiraru. 'Yan kasuwa da dama su ma na adawa da wannan doka, suna masu cewa zai hana baƙi shigowa ƙasar da zuba jari. Sai dai 'yan majalisa sun yi watsi da dokar da ƙasar ta jima ta na amfani da shi tun zamanin turawan mulkin mallaka. ""Lokaci ne a gare mu na yanke shawarar da zata kafa tarihi da yi wa kudin tsarinmu kwaskwarima da watsi da kundin turawa da muka gada,"" kamar yadda Minista Yasonna Laoly ya shaida wa zauren majalisa. Sabuwar dokar ta kunshe abubuwa da dama da suka shafi hukunta rashin da'a da tarbiyya da saɓo da takaita wasu ayyuka na 'yan siyasa da ra'ayi addinai. Darakta a hukumar kare hakkin bil adama yankin Asiya, Elaine Pearson ta shaida wa BBC cewa babban koma baya ne ga ƙasar da ta jima tana bayyana kanta a matsayin mai kare 'yanci da mutunta Musulunci."" Jami'in bincike na hukumar a Jakarta, Andreas Harsano, ya ce akwai miliyoyin ma'aurata a Indonesiya da ba su da shaidar aure na satifikate ""musamman ainihin 'yan kasa ko Musulmi a yankunan karkara"" da suka yi aure bisa tsarin addinai daban-daban. ""Wadannan mutane za su karya wannan doka tunda zama tare zai zama laifin ɗauri na kusan watanni shida, kamar yada ya shaidawa BBC. Ya kara da cewa binciken da suka aiwatar a ƙasashen yankin Gulf, inda ake da irin wannan doka kan jima'a da mu'amala, ya nuna cewa mata ake hukuntawa da kai wa hari da irin waɗannan dokoki, sama da maza. Akwai dokoki da suka haramta laifuka saɓo da aka kasafta gida shida, ciki har da sauya addini. A karon farko tun bayan samun 'yanci, Indonesiya za ta haramta tursasawa mutum sauya addini. Sannan sabuwar dokar ta haramta zargin shugaban kasa ko sukar wata manufa ta gwamnati. Sai dai 'yan majalisa sun ce kwai kariya kan 'yanci fadin albarkacin baki da nuna adawa a madadin sauran al'umma." https://www.bbc.com/hausa/articles/cw5vrvr3n0no +health An fara gwajin rigakafin cutar Maleriya a Kenya An fara gwajin amfani da allurar rigakafin cutar zazzabin Malaria a Kenya a karon farko ranar Juma'a. Kenya ce kasa ta uku da ta shiga shirin bayan kasashen Ghana da kuma Malawi. A yanku nan kasashen uku, ana sa ran yara fiye da 300,000 ne 'yan kasa da shekara biyu za a yiwa rigakafin a kowace shekara. An kwashe tsawon shekara 30 na bincike kafin samun rigakafin, mai suna RTS,S. Kuma tana aiki ne idan aka dabi'antar da garkuwar jikin dan Adam, domin yaki da kwayoyin cutar, wanda sauro ke yada ta. Gwajin da aka yi a farko ya nuna cewa kusan hudu daga cikin kowane yara 10 tsakanin shekaru biyar zuwa 'yan wata 17, wadanda aka bai wa kwayoyin maganin hudu na samun kariya. Hukumar lafiya ta Duniya WHO ta ce wannan na iya sauya fama da ake yi da cutar, sai dai sun kara da cewar akwai bukatar yin amfani da gidajen sauro da kuma maganin kashe kwari. Maleriya tana kashe fiye da mutum 400,000 a shekara - fiye da rabin wannan adadin kuma yara ne a yankin kudu da Saharan Afirka. https://www.bbc.com/hausa/labarai-49688058 +technology Za a fara duba yawan ruwan da ke doron duniya daga sararin samaniya Hukumar sararin samaniya ta Amurka ta ƙaddamar da wani tauraron ɗan adam za ta yi bincike na farko kan yawan ruwan da ke kwarara a doron duniya. Hakan zai taimaka wajen gano ƙarin bayanai kan illar sauyin yanayi. Ku kalli cikakken bidiyon don kallon ƙarin bayani. https://www.bbc.com/hausa/articles/c3gpg73370do +business Me ya sa wasu 'yan Najeriya ke sayen ƙaramin ƙunshin audugar mata? "Abu ne mai wuyar gaske ga kowace mace a duniya ta iya kammala kwanakin hailarta da audugar mata biyu kacal. Hatta fakitin audugar mai guda takwas ba lallai ya isa ba, amma a Najeriya ana sayar da ƙunshi ko kuma audugar leda a matsayin audugar mata mafi sauƙin kuɗi da mutane za su iya saya. A manyan ƙasashe masu arziki, ana ganin ƙunshin a matsayin isasshe kuma abin a dogara da shi, amma a Najeriya ana kallonsa a matsayin abin damuwa. Fitowar audugar cikin irin waɗannan ƙaramin ƙunshi ""abin damuwa"" ne, in ji wata likitar mata mai suna Dr Chioma Nwakanma. Amfani da su ba ya kawo sauƙi, hasali ma ya fi wahala saboda wasu matan ba sa iya kammala kwanakin haila da su. ""Ko da a ce ma ƙunshin na mai ƙwara takwas ne ba sa isa, saboda haka yanzu mutane na sayen fakitin sai su dinga zaɓar ranar da za su yi amfani da ita,"" kamar yadda Dr Nwakanma ta faɗa wa BBC. ""Zaɓin abin da za a yi amfani da shi a madadin audugar - tolifefa da tsimma - ba su da tsafta kuma suna da haɗari, saboda haka abin da ke faruwa ba zai musaltu ba."" Ɓullar irin waɗannan ƙunshi na kayayyaki masu muhimmanci da kuma kayan abinci na kwali na bayyana yanayin rayuwa da ake ciki ƙarara a Najeriya. Yayin da hauhawar farashi a watan Maris na 2021 ya kai kashi 18 cikin 100 sannan farashin kaya ya kai kashi 23, tsadar rayua da hauhawar ta haifar ta sa wasu na cewa an samu ""tattalin arziki na ƙunshi"". Ba audugar mata kaɗai ba, har da kayan abincin yara da man girki da kayan karin kumallo ana sayen su ne a ƙananan mazubi, wanda ta hakan ne kaɗai ake iya saya saboda farashinsu ya zarta samun mutane da dama. ""A da katan-katan na abubuwa nake saya saboda sun fi daɗewa. Yanzu kuwa mazubin da na samu mafi arha nake saya."" in ji Chika Adetoye, wadda ta nuna damuwa kan yadda take ciyar da yaranta uku. An fara lura da sayar da abubuwa a ƙaramin mazubi ne a ƙarshen 2020 yayin da aka fara yaɗa hotuna a shafukan zumunta na abubuwan da mutane ke cewa ba su taɓa ganin su a ƙananan mazubi ba, ciki har da giyar leda. Kasuwar Oyingbo da ke Legas na cikin wuraren da ake tafka ciniki tsakanin mai saye da mai sayarwa, amma yanzu da kyar ake samun ragi. ""Abubuwa sun yi tsada yanzu, mutane ba sa iya saya,"" a cewar wata mai shago Nancy Ike. Wata alama da ke ƙara fito da tashin farashi ita ce, a yanzu mutane kan sayi doya guda ɗaya jal maimakon a da da suke sayen kashi guda. Gloria Joseph-Raji, wata masaniyar tattalin arziki da ke aiki da Bankin Duniya a Najeriya, ta alaƙanta lamarin da manufofin gwamnati. A 2015 ne Babban Bankin Ƙasa na CBN ya lissafa abu 41 ciki har da shinkafa da bota (da ake cin burodi) da tumatur - har ma da jirage na ɗaiɗaikun mutane - cewa suna cikin kayayyakin da ba za a ƙara bai wa masu kasuwancinsu tallafin kuɗin ƙasar waje ba. An ɗauki matakin ne saboda a rage yawan shigo da kayan daga ƙasar waje da kuma ƙarfafa gwiwar samar da su a cikin Najeriya. Tun daga lokacin ne kuma gwamnati ta dinga ƙara yawan kayayyakin, inda aka saka sikari da alkama a watan Afrilun 2021. A ƙarshe ma har sai da gwamnati ta rufe iyakokin ƙasar a 2019. ""Waɗannan hauhwar da muke gani a yanzu, sun fara ne tun 2019 jim kaɗan bayan rufe iyakokin,"" a cewar Ms Joseph-Raji." https://www.bbc.com/hausa/labarai-60026918 +politics Yariman Bakura: Abin da ya sa zan tsaya takarar shugaban kasa a 2023 Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon: Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara kuma jigo a jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya Senata Ahmed Sani Yarima ya sake ayyana aniyyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasar a zaben badi. Senata Yarima wanda tun a shekara ta 2007 ya fara fitowa takarar shugabancin kasar ya yi watsi da tsarin karba-karba a zaman abin da ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar duk da cewar ana ganin lokaci ne da ya kamata yankin kudancin kasar ya fitar Shugaban kasa na gaba. Ya bayyana wa BBC Hausa dalilansa na nace wa kan neman shugababancin kasar da kuma matsayinsa game da rikicin shugabancin da jam’iyyar tasa ke fama da shi a jiharsa ta zamfara. Kalli wani bidiyon na Yariman Bakura: https://www.bbc.com/hausa/media-60089530 +entertainment Yarima Andrew ya sasanta da matar da ta kai shi ƙara kan lalata Dan Sarauniyar Ingila na uku, kuma mutum na tara a jerin masu jiran sarautar, Yarima Andrew ya sasanta da wadda ta kai shi kara a Amurka, Virginia Giuffre, a kan zargin cin zarafinta ta hanyar lalata, kamar yadda takardun kotun suka nuna. Ms Giuffre ta dade tana karar Yariman (Duke of York), tana zarginsa da cewa ya ci zarafinta sau uku a lokacin da take shekara 17, zargin da ya sha musantawa. Wata wasika da aka shigar a wata kotun Amurka ranar talata ta bayyana cewa Yariman da Ms Giuffre sun cimma sasanto a tsakaninsu (wajen kotu). Wakilan Yariman sun ce ba su da wata magana da za su yi bayan sanarwar kotun. Sanarwar da ke kunshe a wasikar wadda aka aika wa alkalin kotun a Amurka, Lewis A Kaplan, ta ce Yariman zai bayar da tallafi mai yawan gaske ga asusun tallafi na Ms Giuffre, na kare 'yancin wadanda aka ci wa zarafi ta hanyar lalata. Sanarwar ta kara da cewa Yarima Andrew bai taba tunanin ya bata sunan Ms Giuffre ba, kuma ya yarda cewa ta sha wahala a matsayinta na wadda aka ci wa zarafi da kuma yadda jama'a suka rika sukarta ba tare da hakkinta ba. Yariman ya kuma yi alkawarin nuna nadamarsa kan alaka da Jeffrey Epstein, wanda aka daur bisa laifukan lalata, ta hanyar bayar da goyon baya da tallafa wa yaki da kawalci da kuma taimaka wa wadanda aka ci wa zarafi ta hanyar. Haka kuma ya yaba wa jarunta da karfin halin matar da wasu ire-irenta da aka yi kawalcinsu, kan yadda ta jajirce a kan kanta da sauran wasu. Da aka tambayi lauyan matar, David Boies kan abin da zai ce game da wannan batu na sasantawa a bayan kotu sai ya ce : ''Ina ganin komai a bayyane yake a nan.'' Ms Giuffre, wadda a yanzu take shekara 38, ta yi zargin cewa Epstein ya yi kawalcinta tare kuma da cin zarafinta ta hanyar lalata tana shekara 16. Epstein ya mutu a gidan yari a 2019, yayin da yake jiran a yi masa shari'a a kan laifukan kawalci, inda yake kai 'yan mata kasashe da wurare daban-daban ana lalata da su. ta ce daga irin cin zarafin da aka yi mata shi ne yadda aka rika bayar da hayarta ga manyan mutane, ciki har da Yarima Andrew. Ms Giuffre ta yi zargin cewa Yariman mai shekara 61 a yanzu, ya ci zarafinta ta hanyar lalata sau uku. Na farko a gidan Ghislaine Maxwell da ke London, sai wanda ya yi mata a katafaren gidan Epstein a New York da kuma karo na uku a wani gidan na Epstein da ke tsibirin Amurka na Virgin Islands. Fadar Sarauniyar Ingila ta raba Yariman da wasu mukaman da yake rike da su. https://www.bbc.com/hausa/labarai-60383073 +health Yadda aka canza wa wata mata hanci a Ingila Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon Wata mata mai suna Jayne Hardman tana fama da wata cuta da ake kira ANCA Positive Vasculutis ne. Wannan ne ya jawo hancinta ya burma har ya nane. Amma burinta ya cika yayin da aka kirkiro hantunan roba da za ta iya amfani da shi. An hada hancin robar ne tare da mayen karfe saboda kada ya goce. https://www.bbc.com/hausa/labarai-49363839 +sports Diago Jota ba zai buga gasar kofin duniya ba Dan wasan tawagar Portugal, mai taka leda a Liverpool, Diago Jota, ba zai buga gasar kofin duniya ba, sakamakon raunin da ya ji in ji Jurgen Klopp. Mai shekara 25 ya ji ciwo a wasan Premier League ranar Lahadi da Liverpool ta ci Manchester City 1-0 a Anfield. Klopp ya ce '' Jota zai yi jinya mai tsawo, muna magana ta watanni da dama.'' Jota ya rubuta a kafarsa ta sada zumunta ''Bayan daren murna a Anfield tawa ta kare a mummunan yanayi, kuma daya daga mafarki na ya rushe gabaki daya.'' Dan kwallon bai fara buga Premier a bana ba, sakamakon jinya, wanda ya koma taka leda ranar 3 ga watan Satumba a wasan da Liverpool ta tashi 0-0 da Everton. A cikin watan dan kwallon ya buga wa Portugal wasan da ta doke Jamhuriyar Czech 4-0, ya kuma ci kwallo daya daga ciki. Ranar 20 ga watan Nuwamba za a fara gasar cin kofin duniya da Qatar za ta karbi bakunci. https://www.bbc.com/hausa/articles/cv2p9lp2vyno +health Najeriya ta dauki matakan hana Coronavirus shiga kasar "Latsa alamar lasifika don sauraren hira da Dakta Abubakar Jafiya Hukumomi a Najeriya sun ce sun fara daukar matakan ko-ta-kwana kan cutar Coronavirus. Dakta Abubakar Jafiya na cibiyar yaki da cututtuka a Najeriya ya shaida wa BBC cewa a shirye Najeriya take domin hana cutar shigowa kasar. Ya kuma ce gwajin da Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi na matakin da Najeriya ta ke na hadarin kamuwa da cutar ba shi da yawa, don haka yiwuwar kamuwa da cutar a Najeriya ba shi da yawa. ""Baya ga wannan mun hada kai da abokan huldarmu na kiwon lafiya mun shirya wasu mutane na musamman da ke shirin ko ta kwana dangane da cutar ko da za ta shigo mana,"" a cewarsa. Ya ce suna duba abubuwan da za a gyara a fannin asibitoci da kayan aiki. Haka kuma, Dakta Abubakar ya ce akwai ma'aikata a duka hanyoyin shigowa Najeriya da aka ajiye don tantance masu shigowa kasar daga kasashen waje. Ya ce ""Yawanci mun fi mayar da hankali kan baki da ke shigowa daga China tunda a sauran kasashen an gano cewa mafi yawan wadanda suka shiga da cutar daga China suka fito."" Ya ce akwai asibitoci na musamman da aka zaba a wasu jihohin Najeriya don ajiye wadanda ake tunanin sun kamu da cutar Coronavirus, kuma jihohi ne da ke da filin jirgin sama kamar Legas da Abuja da Kano. An yi haka ne saboda baki masu shigowa ta jirgin sama. Dakta Abubakar ya ce kawo yanzu ba a samu wani da ya nuna alamun cutar ba a Najeriya. Cutar Coronavirus dai ta samo asali ne daga birnin Wuhan na China, kuma cuta ce da ke shafar numfashi kuma ta ke da saurin kisa. Kawo yanzu ta kashe sama da mutam dari da hamsin a China kuma tana kara yaduwa zuwa sauran kasashen duniya kamar Amurka da Faransa da Thailand da Japan da sauransu." https://www.bbc.com/hausa/labarai-51305246